Amrah Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Amrah_Macijiya_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 1 of 2
[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: π«AMRAH MACIJIYA ππππ«
By Rabeauty π₯°π«π«π«π«π«π«
Page 2
Labarin mutuwar malam Abu ya riski kowa dake kauyen, hankalinsu ya matukar tashi dasu kaji cewa macijine ya kashe shi.
A fadar mai gari kuwa kowa ya taru ana jiran iliya mai macixai yaxo, yana isowa a kace ya bude macixai nai a duba bakin su aiko aka duba amman sarar batayi kama da bakin macixanba, haka aka taro akayiwa malam abu wanka da sallah aka kaishi makwancinsa.
Washe gari amrah tana daki tana bacci gwaggo ta shigo ta tayarda ita tana cewa"yar jikalle tashi Dan Allah na aikeki gidansu harira ki karbomin daudawa gurin innah"toh gwaggo ta tashi ta fito bayi ta shiga ta wanke fuskarta ta fito ta dauki mayafinta Green tasaka ta nufi gidansu harira, tana xuwa ta tararda harira na wanke_wanke gaisawa sukayi sannan ta nufi inda innah suka gaisa sannan tagaya mata abunda gwaggo ta aiko ta karba, bata tayi sannan ta fito xata wuce harira tace "amrah bayan la'asar xanxo mutafi rafi, toh kawai tace tafice daga gidan, a hanyarta ta komawa gida taga wasu samari su biyu suna mgn kuma akan mutuwar malam Abu ne, dan tsayawa tayi Dan taji me suke fada, dayanne yace" hmmmmm ni wlh wannan abun yafara bani tsoro ace anrasa gane wane macijine ke wannan kisan har yau"dayanne yadafa kafadarsa yana cewa "nima dai abun yafara bani tsoro, amma ai gobe ne maigari yace maccido maciji xaixo da kuma magani, kowa dake kauyen nan xa'a bashi yasha, duk Wanda a maciji toh yanashan wannan maganin xai fara rikidewa, kuma na rantse muddin wannan macijin ya kasance acikinmu toh wlh saina kashe shi har lahira wlh, gaban amrah ne yafadi saikuma naga tana wani shu'umin murmushi Wanda daka gani kasan bana alkhairi bane, gida ta karasa tana xuwa tabawa gwaggo daudawarta ta shige daki, da kallo gwaggo tabita sbd taga yanxu duk ta canxa kamar ba amrah taba, ynx mugun halin shiga daki tabijiro dashi, girgixa kai kawai gwaggo tayi ta tashi tashiga bayi, tana fitowa ta dauro alwallah ta nufo dakin, ta tayarda sallah, tashi amrah tayi itama tayi alwallah tayi sallah, bayan sun idar amrah ta juyo ta fuskanci gwaggo tace "waini gwaggo meyasa me gari xaice sai wani maccido maciji yaxo yabawa kowa magani, meyasa su baxasu yi bincikeba tukunnah ai...... Wani kallo da gwaggo tayi matane yasata kasa karasa xancen, waike amrah yaushe xaki fara tausayin mu ke kwata kwata bakida tausayi damuwar mutane bata damekiba, waini kam wace irin xuciyace dake, nidai nasan cewa baban ki da mamanki ba haka sukeba kuma nima dai ba halina kika biyoba, dan Allah amrah ki gyara kinji kuma gobe maccido xaixo da karfe biyar dan haka tun karfe 4:30 xamuje fadar mai gari kinajina, kai kawai ta daga.
Bayan sallar la'asar harira tayi sallama tashigo, gaida gwaggo tayi sannan suka fice xuwa rafi, suna tafe suna yar firarsu, can dai harira ta kasa hkr tace "waini amrah na tambayeki? Eh kawai tace, harira tace" wai meyasa naga tafiyarki ba irin tamu bace kina tafiya kina wani lankwasa kamar macijiya, dariya amrah tayi sannan tace "toh ai macijiyar ce" dariya harira tayi tace da baki fadaba wlh, shiru amrah tayi bata kara cewa uffanbah, suna isa bakin rafin suka xauna kafafunsu sukasa a cikin ruwan, wasu samarine su uku sukaxo wucewa dayanne ya hangesu yayi saurin tabo su yana cewa kai kunga wasu yam mata, dayan ne ya juyo yace kai ashe yau xansha dadina da yammatan nan, karasawa suka yi gurin su, da isarsu suka fara yimusu iskanci.
Harira ce tace da ganinku ba'a yankin nan kukeba Dan haka Dan Allah ku koma yankin ku, dariya suka sheke da ita dayan yasa hannu ya fixgo harira ya mannata da jikinsa ya shiga shinshinar wuyanta dayan kuma amrah ya cafko yana kokarin yaye mayafinda ta rufe fuskar ta dashi, amman yakasa wani wawan Mari yabata wadda saida gefen bakinta yafashe, harira kuma har sun kaita kasa suna kokarin daga mata riga, jin suka yi ance "ku kyaleta da wata irin murya" Wanda yamare tane ya juyo yace ke yimana shiru, kuma damun gama da ita kanki xamu dawo Dan haka kishirya, ya juya ga harira wadda tariga data sadakat sbd harya cire wando, hucin maciji suka ji a bayan su, ai da sauri suka saki harira suka juyo, wani irin raxanannen ihu suka saka a tare, sbd toxalinda sukayi da wata shirgegiyar macijiya green π, harira mah tsoro ne yakamata nan tashiga neman amrah amma bata gantaba, jin sukayi macijiyar tace "saida nayi muku kashedi amma kukaki ji Dan haka dolene na kashe ku, kafin suyi wani yunkuri gaba daya tabi ta saresu nan take suka xube matattu a gurin, gurin harira tayo, harira koh harta juya xata fece taji tace" tsaya "ai da sauri ta tsaya, karasuwa tayi gurin ta, sannan ta girgije takoma mutum, ai harira na ganin AMRAH nan take ta sumee a gurin.
π«Rabeauty π«
*please vote, comment, and share *
[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: π«AMRAH MACIJIYA πππππ«
By Rabeauty ππ«π«π«
(4)
Harira na kaiwa bakin suro ta hadu da gwaggo xata shigo, yadda gwaggo taga harira a rikice neh yasa itama hankalinta tashi, tace menene harira koh wani abun neh ya samu amrah, harira ta bude baki xata gayawa gwaggo gsky cewar amrah macijiya ce, sukayi ido hudu da amrah tana mata wani irin kallo, ai da sauri tafita daga gidan har tana yin tuntube, juyowa gwaggo tayi dan tayiwa amrah mgn, amman me wayam tagani bbu ita a gurin, tsoro neh ya kamata tace "toh yarinya sai kace aljana hmmmmm gaskiya da sake, koh dai abun da ake fadi a kauyen nan gaskiya neh?
Toh idan kuma gaskiya amrah macijiya ce fah innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, tunowa tayi da maganar mai gari" asabe mutanen kauyen nan sun fara xargin jikanyar ki ba mutum bace, duba da yadda take tafiya duk mai hankali yagani yasan cewa tafiyar macixai ce, kuma kaf kauyen nan bbu Wanda yataba ganin fuskar ta daga harira sai innah mahaifiyar harira sai ke, dan haka inason kisaka idanu akanta muma xamu saka idanu, kuma muddin xargin mu ya tabbata toh fa xamu kashe ta, dan bbu makawa ita ke kashe mana mutane "
Duk sanda ta tuna da wannan maganar sai hankalinta ya tashi.
Toh idan kuma ta tabbata ita macijiya ce kenan kashe ta xasuyi, inaaa baxan taba bari hakan ta faruba.
π€ΈββοΈπ€ΈββοΈπ€ΈββοΈπ€ΈββοΈπ€ΈββοΈ
π«π«π«π«π«
KANO STATE.
π¦Wani makeken gida nagani Wanda duk layin bbu Wanda yayi kyansa, ciki na shiga wasu mata na gani a harabar gidan, wata yanmata ce a tsaye baxasu wuce shekara 25 bah,sanye take da riga da wando wa'enda suka bala'eeeen fito da surarta, fara ce amman bacanbah, sai wata mata wacce xata kai shekaru 48,kamarsu daya da yarinyar saidai tafita hasken fata, sai wani saurayi matashi Wanda baxai wuce shekaru 27 bah a duniya, irin black beauty's din nan neh.
Gate aka bude wata hadaddiyar motace tashigo kirar benz Black color, parking space ta nufa da sauri driver ya fito yaxagayo ya bude kofar Baya.
Saida akadauki 5 minutes sannan ya xuro kafarsa ta dama, saidai ya kara wasu 5 minutes sannan ya xuro ta hagu, fitowa yayi yana karewa gidan kallo, subhanallah wannan balarabe koh shuwa'arab domin bbu inda yayi kamada hausawa kai wannan mah koh cikin larabawan da wuya a samu mai kyau irinsa, fari ne kal dugu mai faffadan kirji, jikinsa a murde yake gwanin ban sha'awa, matashine dan kimanin shekaru 33.
Kara suwa yayi gurin su "hajiya barka da yamma" kawai yace yayi shigewarsa ciki, dawani irin kallon tsana tabishi, inda xa'a bata wuka ace taka she duk Wanda ta so tohfa shine Wanda xata fara kashewa.
Driver neh ya kwaso masa luggage dinsa yanufu hanyar shiga falon, tsawa hajiya ta daka mishi tace dallah ajiye anan, da sauri ya aje ya juya, kallon NAJEEB tayi tace"daukar masa luggage dinsa kakai part dinsa kace masa idan yayi wanka yaxo yaci abinci"rai bace yaja luggage din yanufi part din yayan nashi,
Ke kuma suhaima wuce mutafi, wucewa tayi tana turo baki, falon suka shiga, woowπ΅βπ«π΅βπ«haduwa, wannan falon ai da kadan nasu vansh yafishi kyau, dramarda akeyi a bollywood, vansh da ridima π
A bangarensa kuwa NAJEEB yana kai masa luggage dinsa ya juya yayi ficewarsa, koh gaisheshi beyiba.
Hajiya koh tana nan hakince akan makeken dining gefenta koh suhaima ce tana latsa wayarta, NAJEEB neh yaxo ya xauna kusa da hajiya, ba'a dadeba saiga wannan balaraben yafito cikin shigar kananan kaya fuska a daure hanyar waje ya nufa, da sauri hajiya Sarah tace "JALALUDDEEN baka ci abincifa" koh juyowa beyiba yasa kai ya fice, hajiya Sarah ji tayi kamar ta kurma ihu sbd takaici, NAJEEB neh yace mommy nace kibari nida kaina xan iya kashe shi ba dole sai anbi ta hanyar sa masa guba a abinci bah kawai kibari nasa su bardee sutare shi a hanya su aika manashi barxahu,
Da sauri suhaima tace "please aunty Sarah don't kill my JALAL, kinsan yadda nake sanshi ke shedace kuma kinsan akan shi na kwaso kayana na dawo nan gidan, ke dallah rufemun baki Wanda koh kallo baki isheshi bah kinkasa jawo hankalinsa gareki, balantana muyi using dake gurin cikar burinmu mtswwww taja wani dugun tsaki hadi da tashi dg kan dining ta nufi room dinta,
Suhaima mah tashi tayi ta nufi room dinta akabar NAJEEB ananπ¦
β¨ TIGADAMβ¨
AMRAH kam iska tabi ta tare harira a bakin hanya, harira har xata gudu amrah tace "idan kika kuskura kika kara taku daya toh xan kasheki, ai kamar andasata a gurin ta tsaya, karasuwa amrah tayi kusa da ita sannan tace" meyasa kikeson ki fallasa sirrinah, meyasa kikeson ki gayawa gwaggo cewar ni macijiya ce, toh bari kiji wlh, wlh, wlh harira kika kuskura kika gayawa gwaggo koh kuma wani cewar ni macijiya ceh hmmmmm kinsan sauran, girgixa kai harira ta shiga yi hawaye na sauka akan fuskarta tace "amrah baxan xuba idobah ina kallo kici gaba da kashe mana mutane bah, hannuwanta ta hade guri daya alamar rokoπsannan tace" Dan Allah amrah kidena kashe muna yan uwa, dan Allah na rokeki,
Tsaki amrah tayi tace "wlh harira duk Wanda ya shiga gonata wlh saina kasheshi Dan haka kidena wa
[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: π«AMRAH MACIJIYA ππππ«
By Rabeauty π₯°π«π«π«π«π«
(3)
Hannunta tasa a cikin rafin ta ibo ruwa ta watsamata, a firgice ta farka tana ja da baya tana girgixa kanta hawaye na sauka akan fuskar ta cikin rabewar murya tafara mgn"da.. dan Allah am.. rah kiyimin rai kar.. ki kasheni, murmushi tayi sannan tace "hmmmmm harira kenan da inada niyar kasheki da tun ranar da kika fara ganin idanuwana da a ranar xan kasheki amman kuma baxan iyaba sbd yadda na daukeki kamar yar uwata tajini shiyasa baxan iya kasheki ba" ajiyar xuciya harira ta sauke sannan tace "kenan duk kashe kashen da akeyi a kauyen nan kece, kuma ke kika kashe malam abu? Eh nice kuma duk wanda kikaga na kashe toh yashiga gonata neh, kuma ni bana yafiya kuma bana mantuwa, kuma wannan abun daya faru inason yaxama sirri a tsakanin mu sbd koh gwaggo batasan cewa ni MACIJIYA ce bah"inshaa Allah ba Wanda xaiji toh amma wa'ennan da kika kashe yaza muyi dasu? Anan xamu barsu, ido πharira tafitar waje tana cewa "anan kuma amrah? Eh tashi mutafi, xata sake mgn amrah ta daka mata tsawa tare da tsareta da green eyes dinta, ai nan danan harira tahadi ye abunda tayi niyar fada, cikin kauyen suka nufa, AMRAH tashige gidansu itama harira tayi gida.
Washe gari da misalin karfe 4:00 mutane sunfara taruwa a fadar mai gari kuwa jiran maccido mai macixai yake ya kara so dansu wannan masifar tayi yawa.
AMRAH koh tuni ta fice daga gida lokacin gwaggo na bayi batama San da fitarta bah.
Farkon shigowa gari tanufa ta haye saman bushiya tana jiran isowar maccido mai macixai πͺ±, aiko can ta hangoshi saman rakumin sa π«da wata katuwar leda da gani dai kasan magunguna neh a cikin ta.
Murmushin mugunta tayi sannan ta diro daga kan bishiyar ta tsaya bakin hanya, tun daga nesa ya hangeta, sanye take da kaya green har mayafin kanta green neh, yana isowa ya sauko daga kan rakumin sa, yanufi inda take yana cewa"ke yarinya me kikeyi anan gurin maimakon ace kina fadar mai gari".
Mayafin kanta ta yaye ai maccido nayin toxali da idanunta yagane macijiya ce, ai da sauri ya juya xai dauko kayan aikinsa amman ina harta xama shurgegiyar macijiya π, xata kai mishi Sara sai kawai tagaya bace, kafin ta juyo taji anyan keta da takobi, βοΈ, kafin ta juyo kuma yasake bacewa, nantake ranta yakara baci, sai naga tana kara girma Wanda saida yakusa cika dajin, idanuwanta sunkara xama green sosai kwayar idonta tarinka fitarda wani haske, toh a cikin wannan hasken neh ta hangoshi ta bayan ta xai sake yankarta, ai a xafafe ta juyo takai masa wata irin Sara a wuya, nan take ya xube matacce a gurin dukda haka bata barshiba saida tayi masa jina jina, sbd bbu Wanda yataba Cin galaba a kanta saishi.
Rikidewa tayi ta dawo mutum, inda ya yanketa tasa Hannunta na dama ta shafe gurin, aiko ya dawo daidai kamar ba'a taba yankantaba.
π«π«π«π«
A fadar mai gari kuwa, kowa ya halarta shi kadai ake jira, ganin har 5:20 ta wuce yasa mai gari tura fadawansa su uku akan suje su dubo koh lfy.
Aiko suna xuwa suka tarar da gawarsa a bakin hanya, da gudu sukabar gurin, suna isa suka sanarda mai gari abunda suka gani, hmm lallai wannan shi ake kira tashin hankalinda ba'a sakawa rana, domin kowa ya shiga tashin hankali.
Harira najin haka, hankali tashe tabar gurin, gidansu amrah ta nufa tana xuwa kai tsaye tace "amrah meyasa kika kashe maccido?
Wani banxan kalloh tayi mata sannan tace" sbd ya shiga gonata "harira tace" haba amrah wai mekike son kixama, ke bakyayin wuyar kashe mutum, haba amrah kiji tsoron Allah, duk wannan abun da harira keyi kawai karfin haline, sbd a tsorace take da amrah.
Ran amrah ne yafara baci domin koh har fatarta ta fara sabulewa tana xama ta maciji, harira na ganin haka ta fita da gudu dan tasan idan ta tsaya toh fa saidai buxunta πββοΈπββοΈπββοΈ.
π«Rabeauty π«
*please vote, comment, nd share *
[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: π«AMRAH MACIJIYA ππππ«
By Rabeauty π₯°π«π«π«π«
(5)
Da sauri amrah ta nufi gurin gwaggo tana girgixata tana cewa "Dan Allah gwaggo kitashi idan kika mutu ya xanyi, hannunta tasa a saman kirjin gwaggo ta rufe idonta, tana budewa wani haske green yafito daga idanta ya sauka kan kirjin gwaggo, wani dugun numfashi gwaggo taja, ajiyar xuciya amrah ta sauke, sannan tace gwaggo nah,
A hankali gwaggo ta fara bude ido da fuskar amrah tayi toxali ai da sauri ta tashi xaune tanaja da baya, da sauri amrah ta rike hannunta tace "gwaggo nah tsoro na kike?
Kai gwaggo ta girgixa tace" innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, magaji kaja mana masifa,
Amrah tace wace irin masifa babana ya jawo mana wadda ni bansaniba?
Hmmmmm FATIMA a yau xan sanar dake wanene mahaifinki.
π«π«π«π«π«π«
Tuna Baya.
Anyi wani jarumin mutum kuma sadauki Wanda duk kauyen nan bbu mai karfi irin nasa, har takai ga yana fada da mayu, aljannu da kuma macixai, sbd hakan neh yasa ake kiransa da magaji, mahaifiyarki kuma ta rasune a lokacinda xata haifeki.
Akwai wani shahararren maciji, mugu, Wanda ya addabi jama'ar wannan kauyen, ba halin mutum yafita sbd da xarar ka fita xai kashe ka, sunansa BAHUUL, ansha gwagwarmaya tsakanin sa da mahaifinki wato magaji, kafin yasamu nasarar kasheki, kafin ya mutu saida yace "hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh lallai magaji kayi namijin kokari gurin kasheni, toh amma inason kasa wannan a ranka SAINA DAWO DAUKAR FANSA, kuma akan 'yarka,
Yana gama fadar haka ya mutu, hankalinmu ya bala'eeeen tashi, haka muka rinka kula dake koh bandaki xan shiga bana barinki ke kadai saina jira mahaifinki ya dawo, haka dai mukata baki kariya, har kika shekara uku amma bamuga wani abu ya sameki bah, tun daga ranar muka share xancen BAHUUL, muka dauki xancensa a matsayin karya.
A wata assabar ranar da baxan mantaba, koda aka wayi gari bbu mahaifinki bbu labarinsa, hankalin kowa dake kauyen ya tashi matuka domin rashin magaji agaresu babbar matsalace, duk kauyen da yake kusa damu anduba amma ba'aga mahaifinki bah, har xuwa yau danake gaya miki wannan xance.
Hawaye amrah ta share sannan tace "gwaggo dama baba yana raye"eh FATIMA mahaifinki yana raye amma bansanarwa yanxubah, kuma nasan BAHUUL neh ya shiga jikinki domin ya dauki FANSA, amman dan Allah amrah tunda dai harkina da ikon juya kanki dan Allah kidaina kisa,wlh gwaggo bana sanin lokacinda nake yin kisa, nasan bayin kanki bane amrah amma Dan Allah kikara kokarta.... Bata karasa abinda xata ceba taga amrah ta tashi da sauri tana rike kanta, da sauri gwaggo ta tashi ta nufeta, AMRAH meya sameki, dagowa amrah tayi idanunta sunkara rinewa Dukda da farinda yake tsakiyar idonta yakoma green, tsoro neh ya kama gwaggo taja da baya,
Wani irin raxanannen ihu amrah tasa Wanda gaba daya ya karade kauyen, faduwa tayi akasa tafara nannadewa yadda macixai keyi, amma fah bata koma macijiya bah.
Mutanen gari kam kowa yaji wannan ihun kuma sunji daga gidan gwaggo neh ihun yafito, shiyasa suka nufi gurin maigari, aka hadu aka nufi gidan gwaggo hardasu innah da harira, itadai harira gaba daya jikinta rawa kawai yake.
π«π«π«π«
KANO STATE.
π¦JALAL kam yana fita ya shiga motarsa yabar gidan, wayarsa ce tafara ringing screen din nakallah β¨SADIQ β¨nagani arubuce, dauka yayi yasa a hands free daga can SADIQ yace "buddy ka iso" yes na iso ina hanyar xuwa office, daga can SADIQ yace "haba buddy daga dawowarka xata fito aiki kabari ka huta pls,dan karamin tsaki JALAL yaja yace" buddy kasan baxan iya xama a cikin wannan gidanba idan daddy bayanan, OK buddy saikaxo, ya kashe wayar yaci gaba da driving,
Wata babbar hospital ya nufa yayi parking, yana fitowa yam mata suka xuba masa eyes sunga dan handsome kyakkyawa balarabe sun saka mishi eyes, shikam koh ajikinsa danya saba da kallo, direct office din SADIQ yanufa, yana shiga ya samu guri ya xauna, wani hadadden guy neh ya fito daga wani daki farineh sosai amma bekai hasken JALAL bah amma fah dukansu sunaji da kyau, karasuwa yayi yaba shi hannu suka gaisa sannan ya xauna,
Yace "buddy wai har yanxu mommy bata dena nuna maka tsanaba, hmmmmm da farko dai tadena amma yau dana dawo inna lubabatu mai aikin mu take gayamin karnaci abincin da hajiya tayi sbd tasa guba, ido SADIQ yaxaro yace wai so take ta kashe ka, kamar yadda ta kashe ammi wai meyasa wasu basuda imani, idanun JALAL kam har sun fara canxa kala sbd bacin rai,
Tasowa SADIQ yayi ya dawo kusa dashi yadafa kafadarsa yace "buddy akwai mafita" da sauri JALAL ya kalleshi yace "wace mafita" Aure, what JALAL yafada, eh JALAL aure neh kawai mafita, hmmmmm gsky u re not serious sadiq nida bana kula yam mata ina xan samu wacce xan aura, kumafa mommy so take na auri suhaima, kuma muddin daddy yasan da wannan xancen tohfa bbu makawa saina aureta, gashi kuma wlh bana sonka kai koh ganinta banason yi,
Ka kwantar da hankalinka buddy, inshaa Allah kafin su yiwa daddy magana kasamu matar aure, hmmmmm kawai jalal yace tare da mikewa yace "bari na duba patients dina,
[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: π«AMRAH MACIJIYA ππππ«
By Rabeauty π₯°π«π«π«π«
(7)
Wata private hospital ya kaita da gaggawa aka karbeta wata nurse ce taxo saka mata drip da sauri amrah ta rike hannunta kumafa idanunta a rufe suke dakyar ta bude bakinta tace "karki yimin allura dan Allah" a tsorace nurse din ta kalleta saidai batace komaiba, treatment din ciwonta tayi sannan ta bata maganin bacci, nan take koh tayi bacci, fitowa tayi daga dakin ta nufi office din Dr. Kamal, a can ta tararda Dr. Jalal, tace "Dr ta samu bacci, OK u can go, yace da ita, fita tayi, Dr jalal yace" Dr ni xan wuce and pls take care of her, ya tashi ya fita, shima Dr kamal tashi yayi yabi Bayansa,
Dakinda aka kwantar da ita suka nufa, bakin gadon jalal ya tsaya yana kallon gashinta daya rufe mata fuska, har yasa hannu xai jaye gashin kuma ya fasa, ya juyo ya kalli Dr kamal yace Dr xan tafi na tahu da inna lubabatu dan ta kula da ita, toh shikenan Dr kamal yace, fita suka yi a tare, Dr kamal ya koma office dinshi, shi kuma ya nufi gorin motar sa.
Yana isa gida direct part din masu aiki ya nufa, ya gayawa inna lubabatu duk abinda ya faru, ai da sauri tace "toh bari na dakko mata kohda kayan tea neh idan ta farka sai tasha,nima nadan kimtsa, OK ni bari naje part dina nayi sallah dan koh magrib banyiba gashi har ankira isha'i, yana gama fadar haka ya fita daga part din.
Part dinsa ya nufa wanka yayi ya dauro alwallah yayi sallolinda ake binsa, yana gamawa ya fito, inna lubabatu yagani a bakin motar sa tana jiransa.
Yana isowa ya bude mata motar shiga tayi shima ya shiga yaja yabar gidan, Suhaima kam duk tana kallonsu wani irin tsaki taja ta koma ciki tana Kiran sunan aunty Sarah, aunty Sarah dake saukowa daga upstairs tace "lfy kike Kiran sunana haka kamar naci bashinki, kamar xatayi kuka tace" aunty yanxu fah naga ya dawo kuma ya sake fita tare da inna lubabatu, what hjy Sarah ta fada, hmm lalle inaganin karshen xaman ta a gidan nan yaxo har tayi matsayin da xata fita tare da jalal hmm, amma bari tadawo muji dalilin fitarsu tare.
*************
A harabar asibitin yayi parking agogon hannusa ya kalla karfe 9:00 yagani Dan karamin tsaki yaja, fitowa suka yi ya kaita har room dinda amrah take beko shigaba yajuya yayi tafiyarsa.
Inna lubabatu kam ajiye kayan da taxo dasu tayi, ta nufi gurin amrah dake bacci har ynx gashinta ta gyara mata da sauri taja da baya tana cewa "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" Dan kara lekowa tayi Dan ita wannan kyan na amrah ya bala'eeeen bata tsoro kyau sai kace aljana, kayan shimfidar ta ta dakko ta shimfuda tayi addu'o'i sannan ta kwanta bacci.
Jalal kam yana komawa part dinshi yasa key ya kulle Dan daxo yaga Suhaima kuma yanada tabbacin ta gayawa mommy kuma yasan xa'a iya aiko ta ta kira shi shiyasa ya kulle part dinsa.
***************
Washe gari hajiya nafeesa takawowa hajiya Sarah magani wai a saka masa a ruwa tohfa dayasha ruwan xai mutu.
Jalal kam koh aiki bejeba direct hospital ya nufa.
β¨β¨β¨β¨β¨β¨
Hospital.
A harabar asibitin yayi parking, direct dakin ya nufa, yana shiga inna lubabatu na fitowa daga toilet, gaisheta yayi sannan ya xauna yana cewa "wai har yanxu bata farkaba" eh wlh ni abun ma yafara bani tsoro, OK bari na kira nurse ya tashi xai fita kenan saiga nurse tashigo, kara sawa suka yi bakin gadon, a daidai wannan time din amrah ta fara bude idanunta, dishi dishi take ganinsu sai can ta rinka ganin su da kyau yunkurawa tayi xata tashi, da sauri nurse din ta taimaka mata ta tashi xaune, dan dagowa tayi ta kalli jalal Wanda shima ita yake kallo, kurawa juna ido suka yi, ita tana marvelled beauty dinsa, shikuma yana astonished eyes & beauty dinta, shiya fara janye idanunsa, sannan itama ta janye, ita kam nurse tunda taga idanun amrah tsoro ya kamata, kasa hkr tayi tace "baiwar Allah meya samu idonki, dan kallonta jalal yayi, wani kallo amrah ta jefe ta dashi Wanda yasa jikin nurse din fara rawa da sauri tace" Dr bari naje nakira maka Dr kamal"batama jira cewar saba tayi sauri ta fita.
Inna lubabatu ce ta matso kusa da ita tace "diyata na hada maki tea", kallon ta tayi tana tunanin menene kuma tea, kai ta daga alamar eh Dukda koh batasan menene tea bah, tashi inna lubabatu tayi ta nufi gurin da ta aje kayan tea tashiga hada mata.
Jalal kam ganin Dr beshigo bah yasa shi tashi ya nufi office dinsa yana kokarin shiga shikuma yana fitowa, yace "aa Dr jalal har kaxo, eh wlh nama Dan dade ai xuwa nayi a samu sallama pls, OK muje gurin ta tukunnah, suna shiga yayi daidai da gama shan tea dinta, karasawa Dr kamal yayi gurin ta yace" yam mata ya jikin, koh kallonsa bata yiba, balle yasa ran xata amsashi, dan tambayoyi yayi mata amma ba wanda ta bashi amsa da baki, saidai ta daga masa kai koh ta girgixa.
Juyowa yayi ya kalli jalal sannan yace "muje na Baku sallama, xaiyi magana kenan wayarsa ta fara ringing dubawa yayi (mommy) nagani a screen din wayar dan karamin tsaki yaja, ya juyo ya kalli inna lubabatu sannan yace" ki hada komai da komai kikai mota sbd ynx x
[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: π«AMRAH MACIJIYA πππππ«
By Rabeauty π₯°
π«π«π«π«π«π«π«
*In the name of Allah, the most beneficent, the most merciful.
*Seeking for guidance and protection of Allah as i am going to start β€οΈ
Ya Allah!!!
Guide my heart, and protect my hand to the end of this book, AMEEN.
π« Page 1π«
Kano state.
A wani kauye Wanda ake kira da tigadam, wata yarinya na hanga a bakin rafi xaune tana kallon ruwan rafin duka duka yarinyar baxata wuce shekaru goma sha biyarba,tashi tayi tana karewa gurin kallo, koh ina bishiyoyine koraye π³π³masuban sha'awa, hanyar gida ta nufa kallo daya xakayiwa tafiyar ta kasan cewa wannan yarinyar ba cikakkiyar mutum bace sbd yanda take wata irin lankwasa, iskace tayaye mayafinda ta rufe fuskarta dashi,subhanallah, wannan irin kyau haka, yarinyar kyakkyawa ce kyan karshe idanuwanta Green ne gata fara kal yanda take da kyau xakasan cewa ba mutum bace,girgixa naga tafarayi Wanda ya matukar bani tsoro kafin kiftawar gira naga ta rikide ta xama shirgegiyar macijiya Green πππ sai sheki takeyi, cikin kauyen ta nufa tana kaiwa gurin wata kofa ta girgije ta xama mutum, da sallama ta shiga gidan, wata yar tsohowa dake bakin murhu tana ixa itace ta amsa, hade da fadin "wai ke AMRAH ba daman ayi miki fada saiki dau fushi ki wani fita dg gida kamar wata iska, waima daga gidan ubanwa kike? Karasuwa AMRAH tayi tana murmushi Wanda yakara fito da kyanta, tace" haba gwaggonah bafa fushi nayiba kawai dai fita nayi har kigama mitanki sannan na dawo"cikin kwantarda murya gwaggo tace "yar jikalle kinsan dai banason yimiki fada kece bakyayin mgn, dan Allah kikiyaye abunda xaisa na miki fada kinji, toh gwaggo inshaa Allah xan kiyaye, yawwa yar albarka, tashi tayi ta kara share gidan, ita kuma gwaggo tana kwashe abincin a cikin langa, ta xuba musu sauran a cikin kwano.
Bayan sungama Cin abincin saiga harira kawar AMRAH tabiyo mata su tafi islamiya, gaida gwaggo tayi sannan ta kalli AMRAH tana cewa "lalle AMRAH bakima shiryaba kuma kinsan yau malam abu ne xaiyi mana karatu kuma yace uku tayi mana cikin aji gashi ynx har 3:30 kuma nasan kafin mu isa hudu tayi kuma....... Xancenne ya makala sbd wani irin kallo da AMRAH tayi mata shiya hakana ka rasa xancen sbd tana balaaa'in tsoron idanun AMRAH shiyasa bata fiya kallon taba sbd idanunta green neh kuma kwayar idanunta farine ita harira har tunanin take anya AMRAH mutunce kowa, tashi amrah tayi ta shiga dakinsu batafi 5 minute bah ta fito cikin shirin islamiya, muntafi gwaggo, Allah yatsare gwaggo tace, Amin ta amsa hadi da Jan hannun harira suka fito suna isowa bakin soro ta dakko nikabinta ta saka sbd yadda idanuwanta suke, ba Wanda yataba ganin complete face dinta daga gwaggo sai harira, sbd duk Wanda yayi toxali da kwayar idanunta toh sunansa gawa, duk kauyen ba Wanda yataba ganin idanunta dg hancinta sai bakinta kawai mutane suka gani, suna isa malam abu ya tsakar dasu wai sunyi latti baxasu shiga ajinba, harira tashiga bashi hkr ita kuma amrah koh kallo be ishetaba abunda ya kara harxukashi kenan kuma yau yadau alwashin sai yaga fuskarta, harira kadai ta shiga aji ita kuma amrah yace tarage tsawonta a cikin rana, bayan yagama karatu ya fito ya nufu inda take ya shauda mata bulala koh gixau bata yiba ya kara shauda mata still bata mutsaba abun ya kara harxukashi yaci gaba da dukanta saida ya gaji Dan kashi ya kyaleta, ita kuma amrah idanunta sun kara rikidewa sun xama green sosai, hannu yasa ya taxge nikabinta da sauri yaja Baya sbd toxali da yayi da idanuwanta nan danan jikinsa yafara makarkata yama kasa mgn,ita kuma ta kafeshi da idanunta, da sauri yabar gurin, harira na karasowa ta kama hannunta suka nufi gida.
Bayan sallar isha'i amrah ta fice daga gidan gwaggo ma bata saniba, hanyar da tasan malam abu nabi ita ta nufa ta haye saman bushiya tana jiran isowarsa, aiko ba'a dadeba saigashi yabiyo da yar fitilarsa, aiko tayi sauri ta diro daga kan bushiyar rabin fuskarta rufeda Green din mayafi, yana isowa ya tsaya yana yadata da fitilarsa gabansane ya fadi dashi ya xata aljanace amman saiyafi fuska ya basar hadi da cewa "ke malama jayemin akan hanya tayi mishi banxa aiko yahau xaginta, amatsayinsa na malami amman yana xagi, can kuma yace waike wace irin dabbace, a harxuke tace" MACIJIYA π"hade da yaye mayafin fuskarta, tashiga yin wata irin jijjiga nan take taxama shirgegiyar macijiyaπ green sai sheki take, nan take malam abu yafara fitsari a wando, wata irin dariya ta sheka da ita sannan tace" malam abu kayi kuskuren dukana da kuma xaginta, a yau dinnan xan kasheka kuma ynx, kafin yayi mgn tayi sufa ta laulayeshi tashiga sararsa ta Ko ina ihu yake amman ita koh a jikinta saida ta tabbatar baya numfashi sannan ta kyalesa, a takaice dai ta kashe malam abu, anan tabar gawarsa tayi ficewarta xuwa gida.
AMRAH dai muguwace ta karshe amman bata fiya kisaba sai idan antabota, tohfa koh waye yatabota xata kashehe illa mutum biyu,Gwaggo da kuma harira".
π«Rabeauty π«
[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: π«AMRAH MACIJIYA ππππ«
By Rabeauty π₯°π«π«π«π«
(6)
π¦Jalal kam yana gama duba patients dinsa ya nufi office dinsa Wanda yake dauke da sunansa Dr. JALALUDDEEN MUHAMMAD, ciki ya shiga ya xauna kansa ya dora saman table dinsa yakai akallah 6 minutes sannan yadago idanunsa sunyi jajir, agogo ya kallah yaga 5 saura minti 10, mukullin motar sa ya dauka yafito, yana fitowa wata nurse ta taso tana cewa "sir are u going?koh kallonta beyiba yace" yes am going and pls lock my office "yayi gaba abinsa har yakai gurin motar sa sadiq ya fito da alama shima ya tashi daga aikinsa neh, karasowa yayi yace" buddy kardai ace harka tashi "so kake na kwana anan koh ya, ya fada hade da bude motar sa ya shige, da sauri sadiq ya bude gidan gaba ya shiga yana cewa" yawwa ni mumaje ka ajiyeni a gida sbd yau bada motana naxuba, bece komai ba yaja motar yabar harabar asibitinπ¦
π«π«π«π«π«π«
TIGADAM
Gwaggo kam hankalinta ya matukar tashi sbd yanda taga amrah ta rikide lokaci guda duk ta bi ta nannade guri daya irin yadda maciji keyi, sallamar su megarine ya kara tayar mata da hankali, dan haryau bata manta abinda yace mataba "idan har amrah ta kasance macijiya toh xasu kasheta", ai da sauri ta nufi soron danta dakatar dasu amman kash sunriga sunshigo,
Suna shigo wa idanunsu ya sauka kam amrah wacce ixuwa yanzu fatarta ta fara sabulewa tana xama ta maciji, da sauri harira tayi kanta tana Kiran sunanta, tana xuwa tasa hannu ta dago da ita, wani irin wulli akayi da harira Wanda saida tayi sama sannan ta fado kasa, da sauri innah tayi kan 'yarta tana cewa,"subhanallah yau mexan gani, amrah lafiyarki kalau kow... ai bata karasaba taga amrah ta Mike tsaye idanunta sun kara rikidewa da sauri innah taja harira suka matsa daga gurin, wata irin girgixa amrah tafara nantake taxama wata irin shirgegiyar macijiya wadda tafi tada girma dan wannan kadan yarage ta cika tsakar gidan ai wasu tuni suka xube sumammi a gurin,
Wata irin dariya ta sheke da ita marar dadin sauraro sannan tace "hhhhh dama na gaya muku xan dawo daukar FANSA, ni BAHUUL bana yafiya kuma haka xalika bana mantuwa Dan haka yau kafin nabar kauyen nan saina kashe rabi daga cikinku sannan nashiga cikin gari nayi ta'asa son raina kuma bbu Wanda ya isa ya dakatar dani,
Gwaggo ce tayi kafin halin cewa "nicenan xan dakatar dake", wani irin kallo ta watsa mata sannan tace "ai wannan ba jikarki bace BAHUUL ne kuma me iya dakatar dani mutum dayane, MAGAJI kuma a ynx bayanan ni kadai nasan inda yake, kuma a inda yake bbu me iya ganinsa hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh ya bushe da wata irin dariya, mai gari ne yace" kai maxa ku kasheta "ai da sauri suka nufeta bakinta ta bude nan take wuta tafara fitowa, gwaggo na ganin haka tayi saurin Jan hannun harira da innah sukabar gidan, AMRAH koh saida ta kashe kusan mutum 20 sannan tabi iska tabar kauyen.
Tunda aka gayawa gwaggo amrah tabi iska tabar kauyen take ta kuka tana cewa "yanzu shikenan amrah ta tafi innalillahi wa'inna ilaihirraji'un wannan masifar dame tayi kama bbu MAGAJI ynx kuma bbu amrah wayyo Allah nah ta kara fashewa da kuka, innah mah kuka takeyi tana bawa gwaggo hkr, itadai harira komawa tayi kamar mutum mutumi sbd tafiyar kawarta kuma yar uwarta ya tabata sosae.
A bangaren amrah koh BAHUUL be tsaya da ita koh inaba sai a cikin garin Kano.
π«π«π«π«π«π«π«
Jalal kam yana sauke sadiq ya nufi hanyar gida gudu yakeyi da motar sbd har anyi sallar magriba so yake ya isa gida da wuri.
AMRAH koh tana bude idonta ta ganta awani gari, nan tashiga tuno abinda ya faru, kuka ta fashe dashi ta durkushe a gurin da take, wani Dan matashine ya nufi gurinta da sallama sannan yace "baiwar Allah me kikeyi anan ke kadai kuma gashi dare yanayi, da sauri amrah ta dago ta kalleshi sannan tace" bawan Allah da Allah ka taimaka mun da ruwa nasha wlh kishin ruwa nakeji, da sauri yace "toh bari na siyo miki jirana anan" kai ta daga mishi, juyawa yayi yatafi siyo mata ruwa, ajiyar xuciya ta sauke sbd ji tayi kamar ta sareshi tasha jini sbd yunwarda takeji shi yasa tace masa ruwa take so sbd yabar gurinta sbd muddin yaci gaba da tsayawa tohfa xata iya kashe shi, tashi tayi tafara tafiya batamasan inda take jefa kafar taba,
Jalal kuma tun daga nesa ya hangi yarinya yafara mata hon amma ita amrah bata nasan da ita akeba ji kake kuuuuuuuuuut anbugeta saida tayi sama sannan ta fado kasa sumammiya, da sauri jalal yafito ya nufu kanta jama'ah harsun fara taruwa, beyi wata wataba ya sureta da sauri ya ajeta danji yayi kamar ya dauki maciji, sake kallonta yayi sannan yakara surarta yasa ka abayan mota, shiga yayi ya nufi hanyar wata asibiti da take kusa da inda yake, dan idan yace ya koma aaibitinsu tohfa xata iya mutuwaπ¦π¦
Hmmmmm lalle jalal ka daukowa kanka jaraba
π€£π€£π€£π
π« Rabeauty π«
*please vote, comment, and share *
[8/23, 3:12 PM] +234 808 332 3233: π«AMRAH MACIJIYA ππππ«
By Rabeauty π₯°π«π«π«π«
(8)
Inna lubabatu kam kama hannun amrah tayi suka nufi part dinsu.
**************
Washe gari
Inna lubabatu ta hada musu breakfast, takai kan dining table ta jera kulolin abinci.
Sannan ta koma bangaren su ta tada amrah tayi wanka.
A bangaren jalal kowa, bayan yafito daga wanka yashafa mai yasa body spray mai sanyayyen kamshi, wani lausassan yadi baki yasa ka Wanda yakara fito da haskensa,
Direct part din masu aiki ya nufa, gaidashi suka rinkayi kai kawai yake daga musu, daya daga cikin yan aikin mai suna zainab amma suna kiranta da abu xatayi sa'ah da Suhaima tace
"gaskiya fah yallabai ya hadu matuka, da sauri dijee ta kalleta sannan tace" wlh abu ki iya bakinki nidai bbu ruwana, kingama tafiyata ta fada hadi dayin gaba abin ta.
Yana shiga daidai lokacin inna da amrah sun kamala karin komallo, dan kallon ta yayi dayaga xata dago yayi saurin kaiwa idonsa daga gareta, ya maida kallonsa ga inna sannan yace
"inna ina fatan dai komai lfy koh? Yayi tambayar yana mai sauke idanunsa kam amrah, wacce tunda tada go ta xuma masa na mujiya koh kifftawa batayi, dan wani irin kyau dataga yayi, yadda yake kallon tane yasa tayi saurin cewa
" yaya ina kwana"lfy kawai yace yamaida kallonsa ga inna wadda take cewa" gsky bbu wata matsala jalalu saidai yarinyar batada kayan sakawa.
"Toh shikenan inna xansa Suhaima takaita gurin telanta ayi mata dinki sauran abubuwa kuma xan siyo mata"
"toh jalalu saika dawo, Allah yatsare hanya yaya amrah ta fada, dan kallonta yayi yaga still shi take kallo, Amin yace tare da ficewa daga sashen ya nufi part din mommy.
π«π«π«π«π«π«π«
* TIGADAM*
Gwaggo kam gaba daya ta canxa ta rame tayi baki koh magana ta dena yi sbd rashin amrah a kusa da ita, inna da harira koh mai data gidansu suka yi sbd idan tana ita kadai abun saiyafi damunta.
π«π«π«π«π«π«
Nasarawa GRA,
Jalal kam yana shiga part din mommy yagansu kan dining table suna breakfast,
Karasuwa yayi fuska a daure yace "good morning mommy" morning jalal ka tashi lfy?
Kallonta yayi Dan tunda yake da mommy bata taba amsa masa gaisuwa cikin fara'ah da sakin fuskaba sai yau.
Suhaima mah ta gaisheshi sannan najeeb, amsawa yayi sannan mommy tace "jalal xauna kaci abinci mana karkaje office da yunwa" aa na koshi, kamarya ka koshi kullum fah nace kaci abincin sai kace ka koshi koh kana tunanin xan cutar dakai neh?
Shiru yayi bece komaiba, ganin yayi Shiru yasa ta cewa
"yawwa jalal nayi wani tunani mexai hana amrah tadawo part dina tunda dai kaga karima tatafi garin su kaga saita maye gurbin karima ta rinka gyaramin dakina"
Shiru yayi nadan sekonni kafin yace "shikenan tadawo part dinki, amma bayauba saita Dan saba da gidan"
Shikenan hakanma yayi, mommy ta fada, najeeb neh yace mommy wacece kuma amrah?
Wani banxan kallo tamai sannan tace "bansaniba" tashi yayi yana kunkuni ya fita yabar falon.
Jalal kam maida kallonsa yayi ga Suhaima sannan yace "yawwa pls inason bayan la'asar kidauki amrah koje shoprite kiyi mata sayayyar kayan saw a daga nan ki biya gurin tailanki ku bashi dinkin"
Fuska bbu fara'a tace toh yaya bada kudin, saidai na miki transfer dan banida cash"OK ta karanto masa account number ta yamata transfer 1 million, ido taxaro lokacinda taga kudin, dagowa tayi ta kallesa, shiko koh kallonta beyi bah ya fice daga gidan.
Direct hospital ya nufa yana yin parking saiga sadiq shima yayi parking tasa motar,
A tare suka fito suka gaisa sama sama sbd jalal yau tiyata xaiyiwa wata kuma lokaci yakusa shiyasa basu tsaya surutu bah.
Suhaima kowa bangaren su amrah ta nufa tana xuwa tace da ita tashirya bayan la'asar xasu fita, toh kawai amrah tace da ita taci gaba da sabgar gabanta.
***********
Bayan sallar la'asar suka tafi shoprite, less 5,atamfa ciganbi 5,material 5,abaya 3,sai wando da riga set 5, sai takalmi, da mayafi.
Gida suka dawo direct part dinsu Suhaima suka nufa, mommy taga kayan kuma ta yaba, har amrah ta tashi xata woce mommy tace
"amrah anan xaki cigaba da xama ga dakai can a sama kusa dana Suhaima, xaki rinka gyara mun dakina dana Suhaima da kuma najeeb"
Toh kawai tace, Suhaima ta kaita dakin Wanda haduwar sa harta bace, wardrobe ta jera mata English wears dinta, sauran kuma xata kira tailor dinta yaxo har gida ya amsa.
Har takai kofa taji amrah tace "nagode aunty Suhaima",
Juyowa tayi ta Harare ta tace "badanke nayiba, nayine sbd yaya jalal",
Tana fadin haka ta fice daga dakin.
Tashi amrah tayi tana karewa dakin kallo, wasu hawayene suka gangaro daga idunta xuwa fuskarta, a fili ta furta "Allah sarki gwaggo nah nayi kewarki sosai" fitowa tayi ta nufi part dinsu inna tagaya mata mommy ta mayarda ita part dinta,
Inna kam kama hannun amrah tayi sannan tace "nasan cewa hajiya ba xata mayarda keh sashen taba haka dai nasan akwai abunda take kullawa, abunda nake so dake shine dan Allah kikula duk abunda tace kiyi indai kikaga bamai kyau bane toh karkiyi, kuma dan Allah ina son ki saka mata ido, sbd tana son ta kawarda jalal daga doron kasa,
Wani irin xabura amrah tayi tace "kashe shi take son yi", ina baxan bari hakan ta faruwa, tana gama fadin haka ta fice daga sashen inna.
π«π«π«π«π«π«π«
Bayan wata daya
Amrah kam ta kile ta xama yar gayo, ynx tadena rufe fuskarta, ga kuma wata irin shakuwa data shiga tsakanin ta da jalal, har abinci hjy ke bata wai takaiwa jalal, ita kuma sanin cewa hjy tasawa abincin magani yasa take xubarwa tashiga kitchen ta dafa masa wani takai masa batare da sanin kowaba.
Amrah ce tafito daga wanka direct wurin kayanta ta nufa, wasu wando da riga ta dakko wandon red rigar black ta dakko wani Dan karamin mayafi black da shoes red ta saka, wooow haduwa sak yar india haka ta fito glasses baki ta dakko tasaka ta shafa red Jan baki, ta fito falo.
Tana fitowa najeeb yana shigo wa, wani irin mayyen kallo yabita dashi, ita kam bata masan da mutum bah direct part din jalal ta nufa, tana xuwa tayi knocking,
"yes come in" itadai batasan meya ceba kawai ta tura kofar ta shiga, yana xaune kan 3 seater ya dago ya kalleta ji yayi gabansa ya fadi da sauri ya kauda kansa,
Tana murmushi ta kara so ta xauna kusa dashi tace "yayana barka da yamma" barka amrah kina lfy? Ya fada hadi dadan kallon ta Dan sbd ta bala'en yimasa kyau,
Lfy qlw yayana"tashi yayi yace ina xuwa, ya nufi hanyar bedroom, bada dadewaba ya dawo dauke da waya kirar iPhone 11pro ya bata tare da cewa "ga wayanan na sayawa Kanwata" karba tayi hade da mikewa tsaye ta daka uban tsalle ta fada jikinsa ta rungumesa sosai, shi kam wani irin yarrrrr yaji ga jikinta da bala'en laushi da tsantsi kamar maciji.
Da sauri ya tureta daga jikinsa, itakam koh a jikinta saima murna da takeyi sannan tace "ngd ngd sosae yayanah, ta Mike ta fita dadan sauri sauri gudu gudu shikam bin bayan ta yayi da kallo hade da lumshe idanunsa.