Jauro Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Jauro Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 1 of 2
ðŸ‚JAUROðŸ‚
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~
*Ban yarda wani ko wata ya daura min littafi a shafin sa ko ya mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
01
Shigowar ta dakin yayi dai-dai da ɗaga kwalbar da tayi tana ƙoƙarin kaiwa bakin ta,
Cikin matsancin sauri da zafin nama ta fisge kwalbar tayi jifa dashi,wanda yana dakar bangon dakin ya tarwatse ya tafe,
Kallon ta take cikin mamaki da matsanancin tsoro tace"me nake shirin gani haka SUMAYYA,ba dai kashe kanki kike kokarin yi ba?
Fashewa da kuka tayi"me yakawo ki a dai-dai wannan lokacin,me kika zo yi Salma?
"Ki bani amsar tambayar dana maki tukunna,me yasa zaki kashe kanki,Alhalin kin san hukuncin wanda ya aikata haka ko a wurin Allah"
Cikin gunjin kuka tace"eh kin faÉ—i gaskiya kashe kai na zan yi,mutuwa zan yi,gara na mutu kowa ma ya huta,idan na mutu ai shine nan"
Ganin yanda take kuka ne yasa ta rungume ta "ya isa haka,ba ki bukatar mutuwa,rayuwa ce ta kamace ki ba mutuwa ba, me yayi zafi haka"
Jan majiya tayi suna zama kan gado,
*Salma,da in aure shi Gara na mutu,gara ace na mutu,in yaso Baba in gawata zai sa akai gidan sa sai akai "ta faÉ—a tana share hawayen idon ta.
Dafe goshi tayi" Ohh My God,pls SUMAYYA not again,ina ce mun riga mun gama maganar nan dake,"
"Bamu gama ba Salma,in dai a kan Jauro ne bazamu taba gamawa ba har sai ranar da aka fasa wannan auren,"
"Wai ɗan Allah me matsalarki da Jauro ne da baƙi kaunar sa har haka,ni banga aibin yaron ba"
Wani dan iskar kallo ta jefeta dashi"wai shin kinsan waye Jauro,?kin taɓa ganin shi ne?
"Eh ko ba shi bane wani dan dogo fari haka ya nada saje"
Wani uban tsaki ta buga,"to Sulaiman ne kika gani ba Jauro ba,nasan cewa Sulaiman yana da É—an kyau daidai gwargwado,kuma ba Class dina bane shi,domin koyarwa yake a makarantar Secondary,amma wlh Gara na aure shi akan na aure Jauro "
"To yanzun fisabilillahi in banda abinki me aibun shi waccan din"
Ajiyar zuciya ta sauke idanun ta na ƙara taruwa da hawaye,"Salma yanzu ki kalle ni,ga kyau Allah ya bani,har iya kyau,ina da kyaun jiki,na kammala makarantar College of Education,aiki kawai nake jira,ga ni da samari manyan masu kuɗi,masu motoci,ina da burin auren Namiji kyakkyawa sosai,har balle irin na Novel wanda zaki ji su da kwarjini da kyau ga kuɗi,su juya yanda suke so,"ajiyar zuciya ta Kuma saukewa"nasan Baba ba wani mai kuɗi bane,amma yana da rufin Asiri,tunda duk wani bukarmu yana biya mana,amma shine wai ya rasa mijin da zai haɗa ni aure dashi sai wani bakin Fulani"nan take hawaye ya ɓalle mata.
"Ban gane bakin Fulani ba"
"Wallahi Jauro ko a cikin Fulani sai an bincika kafin a samu mai munin sa,baƙi ne shi sosai,gashi ba shida tsaye sosai,kullum cikin kaya daya yake,wata shegiyar bulun riga,wacce haɗuwa ta huɗu dashi amma da ita nake ganin shi,"
"To ai muni ba wani abu bane"
Hararanta tayi"kawai sai na nuna ma ƙawaye na shi nace ga mijina,waiyo Allah,ke kinma San Bala'in Family su Jauro kuwa Salma,wallahi tunda nake ban taba jin fitina da tashin hankali ba irin na Ahalin su,ke ko a littafin Hausa,a haka zan yi fata kutsa kai na,
Ni wallahi bana son shi,gashi ɗan ƙauye sai bakin iskanci ya tara"
"To wai a ina shi Baba ya sanshi,nasan dai ba É—an uwanku ba ne"
"Haka ne Salma,amma duk yanda za'ayi ba zan taɓa yarda ayi wannan auren ba"
"To ko zaki bani labarin shi,dan wallahi har na matsu naga wannan Jauro"
Tsaki taja"ai kuwa da kin yi dana sanin ganin sa,kuma ni gaskiya ba ni da wani cikakken labarin sa"
Bata fuska tayi "pls mana Sumayya É—an Allah ki faÉ—a min"
"Wallahi ban sani ba,sai dai in zaki ni ma da kanki,abu É—aya kawai na sani a kanshi,shine shi É—in mugu mugun ÆŠan iska ne"
Mikewa tsaye tayi"koma dai menene zan nimo Asalin labarin"
"Da labarin sa da zaki nimo ai gara ki taimaka ki nimo min hanyar da zanbi a fasa wannan auren"
Komawa tayi ta zauna tana kallon kawar nata"Sumayya"ta kira sunan ta,
"Umm" Ta fada tana kallon ta.
"In baki shawara zaki bi?
" Me zai hana in na ƙwarai ne"
"Me zai hana kibi maganar mahaifinki,ƙila wannan auren naki akwai abinda ya hango maki wanda ke baki hango ba,kuma kun san iyayenmu suna matukar sonmu ba zasu taba yi mana abinda zai cutar damu ba,please ki bi shawarata ƙawata"
Sai da ta bari ta kammala tsaf,sannan ta zame hannun ta dake cikin na Salma,
"Ke ƙawata ce wacce muka tashi tare tun muna ƙanana har muka girma,kusan ko wani lokaci muna tare," Lumshe ido tayi ta buɗe "Alhamdulillah,na godewa Allah daya nuna min Asalin wace ke,ashe Salma ba zama amana muke ba,Ashe baki ƙaunata, kina farin ciki da ci baya na,har kike ban shawaran auren Bafullatanin Ƙauye,in Allah ya yarda kamar yanda kike min fatan Auren Jauro sai Baban ki ya aura maki mutumin da ki kafi tsana a duniya,ki ji in da daɗi,"
Kallon mamaki take mata yanzun daga kyara kayanka sai za zamo sauke mu raba,ita da shawara ta bayar ba da wata manufa ba,riko hannun ta take ƙoƙarin yi,da sauri taga ta matsar da hannun ta,
"Haba mana Sumaiya,yanzun kin min adalci kenan da irin wannan fahimtar da ki kai min,"
"Ni ma kin kyauta min kenan,kin ga ni bana son ma wata magana Salma tashi kawai ki tafi"
"Yanzun korata kike Sumayya"
Kauda kai tayi "kamawa yake yi"
Ajiyar zuciya ta sauke, tana mikewa"to zan wuce kamar yanda kike buƙata,"
"Allah ya raka taki gona"
Girgiza kai kawai tayi,ba damuwa,in dai halin Sumayya ce ai sai dai taba wani labari,ta san yanzun bata cikin daɗin zai,amma ta tabbatar da zuwa anjima da kanta zata zo gidansu bata haƙuri,ko kuma ta kirata a waya,shi yasa gara ta barta ta dawo haiyacin ta,
Tana fitowa daga É—akin Sumayya dakin Mama ta shiga,gaisawa suka yi,
"Ya iyayen naki"
"Suna lafiya Mama"
"Kin ko ga kawar taki"
"Eh Mama,dama kuma ina son in maka magana a kanta"
Zama tayi bakin gado"zauna ina jinki"
Zama tayi a kasa"Mama É—an Allah kisa Baba ya fasa aurawa Sumayya wannan mutumin tunda bata son shi,Mama kinga kuwa yanda Sumayya ta rame,gabaÉ—aya ta fita hayyacinta "
Dukar da kai tayi sai kuma ta kalle ta "ni kaina abun na damuna Salma,sai dai na rasa yanda zanyi,daga Sumayya har Mahaifinta taurin kai ne dasu,idan suka kafe akan abu sun kafe kenan,ita tace bata so,shi kuma ya rantse sai anyi,gabaÉ—aya na rasa yanda zan shawo kansu,ko abincin kirki Sumayya bata ci sai nayi da gaske,bansan ya suke so nayi da rayuwa ta ba"
"Sai dai mu taya ta da addu'a,sannan dazu dana shiga kokarin shan guba take,dan Allah Mama a ƙara saka ido a kanta"
Cikin tsoro ta dafe kirji "guba" Da sauri ta mike ta nufe dakin Sumayya,a zuciyar ta tana rayawa akan lallai duk yanda zata yi dole tayi domin a fasa wannan auren,tana ji tana gani ba zata yarda ta rasa yarta ba,koda kuwa sunan Baban su zata kai wurin Malami.
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*2*
Salma bata jima da fita ba sai ga Mama ta shigo ɗakin da sauri tana ƙiran Sunan ta,
Zabura tayi daga kwancen da take tana durowa daga saman gado "Na'am Mama"
Tsayawa tayi a gabanta tana ƙare mata kallo,"in jin dai baki sha gubar ba"
"Turo baki tayi ta koma ta zauna" Mama shine zaki ban tsoro da wannan kiran naki"
"Kaniyarki,ina tambayarki kin tsaya min shirme,Ashe Sumaiya bakida hankali,yanzun saboda wani É—a namiji tsinanne sai ki kashe kanki,yanzun kin min adalci kenan" Sai kuma ta saka kuka,
Ganin mahaifiyar nata na kuka ne yasa da sauri ta taso ta rungume ta "ɗan Allah Mama kiyi haƙuri,ba zan ƙaraba,na ɗauka baki fahince halin da nake ciki bane ke da Baba shi yasa,ni kuma na rasa mafita,zuciyata zafi take min shiyasa na zaɓa wannan hanyar"
"Waya faÉ—a maki ban fahince ki ba,a duniya a kwai wacce tafi cencenta ta fahimci É—a sama da uwa,babu,na san komai na kuma san tunanin ki,dan haka kar ki kara yin irin wannan tunanin,dan in dai Jauro ne wannan auren kamar anyi an fasa"
Kallon Mamaki take wa mahaifiyar nata"Mama taya hakan zai faru,bayan Baba yace mutuwa ce kawai zata iya dakatar da wannan auren,kuma naga kema da ki kai mai magana kin yarda yayi"
"Ba ni nace ki kwantar da hankalin ki ba,ai in takamar shi taurin kai,bai fi karfin Malamai ba,mun riga munyi magana Hajiya Rahama,matar kansila na kasan layin nan,akwai in da zata kai ni,sha yanzun magani yanzun"
Æata fuska tayi tana kallon mahaifiyar nata"Mama nifa tsoron zuwa irin wannan wurin nake,gaskiya karki je"
Cikin masifa ta hayayyako mata"to shikenan na fasa zuwa,tunda dama ashe son shi kike ai dole ki ce haka,ke kika sani sai ki karata a can,ana mikin gudun wahala kina fadin tsoro kike ji,yanzun ke ko gidan Boka aka ce kije baki zuwa saboda wannan,sam ko tsari ba ku yiba,mutum tamkar wani Almajirin Ƙauye,ke kika sani"ta faɗa tana kokarin juyawa zata bar ɗakin.
Cikin sauri ta riƙo ta"na yarda,in dai har za'a fasa wannan auren na yarda Mama kije,ɗan Allah ki taimaka min"ta faɗa tana zubar da ruwan hawaye daya cika mata ido
Tsaki tayi"ni daÉ—i na dake saurin kuka,to ya isa,zuwa gobe da yamma zamu je"
GyaÉ—a kai tayi tana kara lafewa a jikin Mama.
Ture ta tayi ta mike tsaye"ni É—aga ni da wannan son jikin naki"
"Mama É—an Allah mana"
"Ohh lallai yarinyar nan,kinga ni ina da aikin yi bari ma ki gani" Nan tayi waje abinta.
Ajiyar zuciya ta sauke,yayin data koma jikin gado ta jingina bayanta ta lumshe ido,
A baiyane tace "ya Allah ka raba ni da auren wannan bawan naka" Kara gyara zama tayi yayin da zuciyarta ya tafi tunanin farkon haÉ—uwar ta dashi,wanda ita tun a ganin farko wanda bata sanshi ba bai san ta ba,taji haka kurin mutumin bai mata ba,karamin tsaki taja,"kai Yawo ma dai bai yi ba a rayuwa,da ace ranar batayi Baba karyar zata taya Aunty Amina gyaran daki ba da haka bai faru da ita ba,da basu haÉ—u da juna ba,"a wannan ranar kuwa tana kwance ne a gida tana barcin asara,in ji ta,bata da in da zata yi,kawai sai ga kiran Rahina,cikin yana yi na mai barci ta É—auka,wanda daga É—ayan bangaren tace"Sumayya kina ina ne?
"Gida mana"
"A'a baki samu zuwa bikin Rose bane,gashi har za'a tafi park "
Zabura tayi ta duro daga kan gado,tana missike ido"ke wallahi na manta yau ne,gani zaune a gida dama babu wurin zuwa"
"To ki dai yi sauri kam,dan Æ´an makarantar mu ma duk gasu nan sun iso"
Ihu tayi"ke ki ce yau da ansha dani,bikin Rose tamu gaba É—aya ai ganinan zuwa"da sauri ta ajiye wayar,
Fitowa tayi tsakar gida,tana niman ruwan wanka,sai dai duk durom din da suke ajiye ruwa ba komai a ciki,
Tsaki taja"wai yo Allah na,to yanzun ina zan samu ruwan wanka "
Ƙanwarta ƙarama ce ta shigo gidan da leda a hannun wanda daga dukkan alamu aikanta aka yi,
"Yauwa ke Aisha zo nan"
Zuwa yarinyar tayi ta tsaya "gani Sumayya"
Harara ta dalla mata"wai me yasa yaran nan bakuda kunya ne,ke nafa na baki aƙalla shekara goma sha uku,amma shine ba ki iya ce min Aunty,sai Sumayya gatsau,in da yaran masu kuɗi suka fiku kenan,sai da kaji ance Aunty Baby,ko Aunty wacce,amma ku ya'yan talaka sai rashin kunya tsiya "
Daga bayanta taji muryar Mama na faÉ—in "daÉ—in abin dai ubanki talaka ne,kin ga a rashin tarbiyar harda ke"
Juyawa tayi ta kalle Mama tana turo baki"ni fa Mama da Aisha nake magana,ba ki ji wai Sumayya take kira na bancin na girmeta "
"To sannan Uwar ta,ke zo nan oh,kyale ta"
Da gudu kuwa yarinyar ta wuce tana mata gwallo.
Nuna kanta tayi"ni ko,ni kike wa gwallo ko,dan kin ga Mama na É—aure maki,zamu haÉ—u,ai zan kami ki "
"In kin gama faÉ—a sai ki zo ki dibo mana ruwa a gidan Malam Sa'adu,tunda kin ga ko tarfe ba mu da shi a gidan"
Zaro ido tayi tana kallon Mama kamar taga abin tsoro,domin a duniyar Allah idan akwai abinda ta tsana shine ace taje dibo ruwa,haba,haba,ai wannan ba ƙaramin zubar da Class bane,kamarta,yanzun ace kamar ta ce zata dibo ruwa kuma tun daga nan har bakin layin su gidan Malam Sa'adu,kawai sai a ganta da baho akai wai tana dibar ruwa,ai wallahi samarinta ma dariya zasu mata,
"Mama dibar ruwa kuma,É—an Allah ki saka su Abdullahi mana kin ga ni yanzun ma fita zan yi,"
"Wasu Abdullahi,yaran da basu nan,duk basu dawo makaranta ba,dan haka wa kike son in aika,gashi lokacin daura girki yayi,ai kema dai kin gani ba nida ruwa, mdan haka bana son wata doguwar magana,ina jiran ki" ta faÉ—a tana jan hannun Aisha zasu shiga daki,juyowa tayi"kar in ji kin bar gidan nan da sunan zuwa unguwa,kin dai san halin Baban ku in ba so kike ki saka ni cikin matsala ba"
Hawaye ta fara,oh Allah me yasa ka yini a gidan iyaye talakawa,da yanzun ina Dubai ko London ina hutawa ta,ko kuma ina kan gado yana juyawa dani,sai kuma da sauri tace Astagafurullah,
Daki ta goma ta É—aki jakkanta wanda kayan kwalliyarta ke ciki,madubi ta dauka ta dauki man baki ta shafa,ta dauki É—ankwalin ta dake gefe ta goge fuskarta dashi tas,
Jakkan kayanta ta buÉ—e ta dauki wani Les da Aunty Amina ta bata,ta saka ta yafa gyale,
Ta windon dakinta ta lelleka tsakar gida,sai da ta tabbatar ba kowa sannan ta fito da sauri_sauri ta nufe kofar gida tana fita da sauri ta shige gidan makotarsu,har tana ba matar dake tsakar gida tana shara tsoro,waigen bayanta take"Sumayya lafiya,waya biyo ki "
Itama juyawa tayi ta kalle bayan nata,"babu kowa,"
Dafe kirji tayi"wai har kin ban tsoro"
Bata ce mata mo kai ba,sai butar data gani a tsakar gidan ta É—auka,wanke kafarta tayi dashi,sannan ta koma saman dakalin kicin ta zauna,jakkan hannunta ta buÉ—e ta É—auko wani karamin robar mai ta shiga mutsukawa a kafa da hunnu,
Kallon ta matar tayi rike da baƙi "naga ta kaina,ƴan matan zamani sai da daka tsami,babu wanka"
Kallon ta tayi"ba zaki gane ba maman Aminu,wallahi ba muda ruwa ko dis,yauwa Mama tace wai É—an Allah ki ranta mata roban fenti guda ta fara aiki dashi,idan su Abdullahi suka dawo makaranta zasu dibo maki "
"To ba damuwa gayacan ki É—auka ki kai mata"
"A'a idan dai kin samu yaro ki daura masa ya kai mata dan ni dai sauri nake yi"
Kallon ta take"naga dai ta ƙofar gidan zaki bi ki fita ba sai ki mika mata ba"
"A'a ta bayan gidan nan zanbi dan bana son saka ido irin na mutanen unguwar nan"
Girgiza kai kawai tayi taci gaba da aikinta,dan in dai halin Sumayya ce sai dai taba wani labari,
Tana gamawa ta tashi ta saɓa jakkanta,a yanda ta fito wata shar da ita ka ɗauka yar gidan wasu masu kuɗi ne,gashi dai ko kwalli bata shafaba,man baki ne kawai sai kamshin da take yi,yanda kasan wacce tayi wanka,"Maman Aminu na wuce"
"Allah ya tsare" Tace tana mata fatan shiriya a zuciyar ta,mutane da dama suna mata kallon yar iska ce,saboda yawo da Shige shige irin nata,sai dai ba haka take ba,ita ta san halin yarinyar,sai dai rashin ji da taurin kai irin na ta,uwa uba rashin kunya,.
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su É—aura min littafi a shafinsu ko a mai da min littafi Audio ba tare da izina ba*
*3*
Kamar yanda ta faÉ—a haka kuwa akayi,É—an ta bayan gida tabi,bata yarda ta biyo ta cikin unguwar su ba,sai bayan gidajen mutane data tabi,tana kwana,da haka har ta fito bakin titi,
Bata wani jimaba a bakin titi ta samu abin hawa,"Malam Tunga zaka kaini,nawa"
"Dari biyu"
Waro ido tayi"dari biyu fa,sai ka ce zanbar gari,kaga ajiye ni a Mobile,tunda Saba'in ne"
Kallon ta yayi daga sama har kasa"haba Hajiya,ai ba girmanki bane,kawai ke da zaki ce muje kawai,"
Hararanshi tayi"kaga in bazaka Tunga a dari da ishirin ba,ka sauke ni Mobile,shima in ba zaka ba,ka ƙara gaba"
Girgiza kai yayi"shigo muje,amma dai dari da hamsin zaki bada "
"Kai dai ka sani" ta faÉ—a tana shiga,
Ita sai lokacin ma ta lura da ashe akwai mutum zaune a ciki,kallon shi tayi,wata kodaddiyar bulun riga ce a jikin shi mai dogon hannu,irin wanda yake da botiri a ƙarshen hannu, da wata baƙar wando irin wanda yawanci a gwanjo ake samun irin su,itama ta fara canja kala,sai talalmi cover shoe,wanda fatar takalmin ma ya fara tashi,
Bayan ta gama kare ma kayanshi kallon ne ta maida idanun ta kan fuskarshi,
Baƙi ne sosai,sai dai ba irin wuluk ɗin nan ba,gashin kanshi a cike yake mai laushi irin ma fulani,wanda shi kawai zai nuna maka cewa shi Fulani ne,ba shida wani dogon hanci,haka kuma bakin shi madaidaici ne,ba zaka kira shi ƙarami ba tunda yanada dan girma,kamar yanda idanun shi basuda wasu girma,kai a takaice dai yana cikin gerin mutanen da za'a saka cikin Babu Yabo Babu Fallasa,haka kuma ta bangare guda duk da a zaune yake ta tabbatar da baida tsawo,
Yana juyowa kuwa suka haÉ—a ido da ita,ai kuwa harara ta zuba mashi tana matsawa gefe,dan ita kama yake mata ma yan kidnapping,
Waya ce ta shiga kara babu kakkautawa,da sauri ya ciro wayar daga Aljihun shi,wanda ganin kalar wayar dake hannun shi ne yasa zarginta ya ƙara girma a zuciyarta wato ɗan Kidnapping ne,in ba haka ba ta ina kamar wannan bagidajen,ba ƙauyen za'a ganshi riƙe da waya IPhone kuma ba ƙarama ba,a ƙalla daga gani zatayi dubu dari biyu da wani abu,
Receiving call É—in yayi,ya saka wayar a kunne,sai dai cikin rashin sani hannun shi ya danna amsa kuwa,
Kawai sai ji tayi daga ɗayan ɓangaren ance "Kai JAURO amma ka cika ɗan iska,shine zaka bani Condom marasa kyau"
"Kamarya marasa kyau?
" Eh mana ina sakawa ko gamawa banyi ba sai gashi abu ya yage,Allah saura kaÉ—an nayi ma Madam bari"
"To killa dai baka saka da kyau bane Malam"
"Wallahi sau uku kenan yana min haka,dan haka zan kawo maka sauran kwalen a canja min wasu,dama kwalli goma ne,to gashi ko daya bai kare ba"
"To ba damu ka kawo min gida zuwa anjima, sai na canja maka da wani"
"Yauwa na gode aboki na"
Tsaki yaja yana kashe wayar.
Ji yayi mai keken yace"Malam Condom kake sayarwa ne"
"Eh ko zaka siya ne"
Dariya mutumin yayi"ikon Allah,kowa da kalar tashi sana'ar,yanzun nawa kake samu riba a kwali daya"
"Dari da hamsin mana,"
"AH lallai ba laifi,to yanzun ina son kwali biyu zan samu"
"Me zai hana abu na kuÉ—i"
Dariya suka saka a tare,
Jin anja tsaki daga gefen shi ne yasa ya juya ya kalle ta,wannan karon ma hararan shi ta kuma yi,
"Malama kwali nawa kike so?
Ya tambaya babu alamu wani Dar a tare dashi,
Zaro ido tayi har tana dafe kirji," Me kenan ?
"Condom mana,kinsan yana da kyau Æ´an mata su dinga amfani dashi saboda tsaro"
Tunda take a rayuwarta ba'a taɓa faɗa mata magana mafi muni ba irin wannan,wani irin bacin rai ne ya sauko mata,wanda har sai da ta kasa magana,
Kallon me Adaidaitan tayi cikin bacin rai"Malam sauke ni anan"
Juyowa yayi "Amma kince Tunga zaki sauka ai,kuma gashi ko Mobile bamu kai ba"
Cikin masifa tace"nace ka sauke ni,na fasa zuwa,ka sauke ni"
Tsayar da Adaidaitan mutumin yayi,
Cikin fishi ta fito"wato fatan iskanci kuke min ko,kai kuma harda cewa in siya Condom,to ta Allah ba taka ba,har in yi aure bazan taba yawon karuwanci ba sai dai kanwarka tayi"
Gira daya ya daga"laifi ne ɗan na maki tayin abin arziƙi,waya faɗa maki yanzun akwai budurwa Virgin,duk yawancin ku ba in da baku leka ba,ni shawara na baƙi ko kwali nawa kike so zan saida maki,kuma zan maki ragi sosai "
Tsabar baƙin ciki bata masan sanda tace"na leka harda dakin ubanka"ta faɗa tare da rarumo wani katon dutse dake gaban zata buga masu,
Ai da mugun gudu mai Adaidaitan yaja Keken shi ya bar wurin,yayin da daga shi har me Keken suke kwasar dariya,
Bakin cikin wannan abinda sukai mata ne yasa taji gabaÉ—aya ta tsani fitar da tayi,dan haka tare wani keken tayi wanda zai dawo da ita gida,in da anan ta zo ta tarad da Mama da Baba suna jiranta da wata masifar.
Tana shigowa gida a tsakar gida ta iske su zaune har da Kannanta yayin da kwanukan abinci daga gefe alamun yanzun Baba ya gama cin abinci,
Dukawa tayi ta na gaishe shi,tunda tasan irin wannan ranar baya jimawa yake dawowa "barka da dawowa"
"Daga ina kika fito"
"Baba naje gidan Anty Amina ne taya ta gyaran daki"
"Da izinin wa"
Kallon inda Mama ke zaune tayi,suna haÉ—a ido ta kauda kai,
"Na faÉ—a ma Mama"
Kallon Maman yayi"kika ce bata faÉ—a maki ba"
Kallon Sumayya tayi,ita ma suna haÉ—a ido ta dukar da kai.
"Oh ta fada min amma na manta ne"
Hararan Sumayya yayi"tashi kiban wuri,ai na kusa maganin wannan yawon naki"
Turo baki tayi tana tashi ta shige daki,tsabar bakin rai a ranar kashe wayar ta tayi,
Sai kuma haÉ—uwar su ta biyu,wanda shima ba zata manta ba.
Jin kiran da Aisha ke mata ne yasa da sauri ta dawo cikin haiyacinta tana kallon ta,
"Wai Mama ki fito kiyi Sallah lokacin Magariba yayi"
"To " Kawai tace tana mikewa.
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko a mai damin littafi Audio ba tare da izini na ba*
*4*
Washegari da safe misalin ƙarfe takwas na safe,a lokacin ta kammala haɗa masu abin ƙarin safe,tana sharan tsakar gida,sai ga yaro ya shigo da sallamah,amsawa tayi dan lokacin ita kadai ce a tsakar gida sai Aisha dake wanke-wanke,kasancewar ranar sati ce,
"Wai ana sallamah da Sumayya"
"In ji ubanwa da sassafen nan"
"Yace ace Jauro"
"Je kace tace ba zata zo ba,idan kuma ya isa sai yazo ya jani"
Daga bakin kofar Baba taji ance"idan baki fita ba ni kuma a yau zan sa a ɗaura auren in yaso sai yaji daɗin cika umurnin ki,dan ba wanda ya isa ya dakatar dashi idan ya shigo daukar naki,koni nan ubanki ban isa in dakatar dashi ba,wanne kika zaɓa "Baba ya faɗa daga inda yake tsaye a bakin kofar dakin shi.
Ba tare data ce komai ba,ta jawo wani hijabin Mama dake saman igiya,
wuya ma ya mata yawa,har ana iya ganin suman kanta,da yake hijabin roba ne,ƙafarta silifas ne,kamar yanda take daure da zani iya kirji sai riga a sama,dan haka zanin bai gama sauka kasa ba,fuskarta kuwa yanda kasan anyi gobara haka yake,
Kai tsaye kofar gida ta nufa,
Yana tsaye a kofar gidan,sai dai wannan karon riga ce fara a jikin shi,amma daga gani ta gwanjo ce,dan har wani kaba kaba take yi,sai takalmi dai na rannan ne,wando ma dai ya canja,sai wata baƙar leda dake hannun shi,
Cikin bacin rai ta tsaya a gabanci babu sallamar,har wani huci take,gashi har girgiza take,
Kallon ta yake tun daga sama har kasa,yayin daya tsayar da idon shi a kanta,na wani lokaci,sai kuma ya dawo da kallon shi kirjinta,nan ma na wasu yan daƙiƙai,tabe baki yayi "Assalamu'alaikum" Ya mata sallamah.
Abu É—aya ne yasa kawai ta amsa mai sallamah shine sanin muhimmancin ta,shima a ciki_ciki ta amsa,
"Me ya kawoka gidan mu da safe"
"Nazo taÉ—i ne mana"
Wani banzan harara ta zuba mai"a garinku hala da safe ake zuwa taÉ—i?
Dariya yayi kaÉ—an "kusan haka,kinsan me?
Hararan shi tayi tana jan tsaki,
" Nifa gaskiya zan faÉ—a maki,dama kallon É—an iska kike min,amma maganar gaskiya bai dace kina É—aurin kirji ba,saboda hakan na zubar da nonon mace,kuma kin ga ni ba zan so haka ta faru dake ba"
Kallon kirjinta tayi ta kalle shi,da sauri ta maida hannun ta cikin hijabi tana karewa"ai ba kallon da nake maka kenan ba,haka din yake kai cikakken É—an iskan ne,in ba haka ba me yakai idanun ka wurin"
Ɗan shafa kanshi yayi"nifa ba ɗan iska bane,tunda ban taɓa iskanci ba,sai dai lokacin da naje England ne ƴan matan garin suka so lalatani,da kyar dai Allah ya kwace ni kuma....
"Kai dai ɗan iskan ne,a ina ka taɓa zuwa England,kuma ka rantse da Allah baka taɓa iskanci ba,tsakaninka da Allah"ta faɗa tana kafe shi da ido.
" Eh to ai dai iskanci kika ce ba zina ba,kuma in dai iskanci ne,a wannan lokacin ai kowa na ɗan taɓawa,kuma kema zaki iya yi"
Kallon shi take baki buɗe "amma baka da hankali Jauro,yanzun ni zaka ce in zan yi iskanci ina iya taɓawa?
" Na ga kamar bakida suma,kalli suman kankifa yanda kikasan an sude kwallan mangoro,
Ni da naso ace matar da zan aura tana da suma,amma ba komai nayi maneji a haka,sannan zan siya maki wani man suma da naga ana talla a online,"
Baƙin ciki ne yasa tace"ka fara sai ma kanka sutura tukun na kafin ka yi maganar man kai"tana gama fadar haka ta shige gida cikin jin haushi,tana jin kiranta da yake yi mata da sunan data tsana wato Sumy Baby,ko juyowa ba tayi ba,
Tana shiga cikin gida kai tsaye dakin Baba ta shiga da kuka ta tsugunna a gaban shi"Baba É—an Allah kamin rai ba na son Jauro,bana son na aure shi,dan Allah,na yarda koma waye ka aura min ko da Almajiri ne amma banda Jauro"ta karasa fada tana fashewa da kuka sosai.
Kallon ta yayi cikin Alamun rashin wasa yace"nariga na yanke hukunci a kan haka,kuma shi É—in ba mutumin banza bane ya cika duk wasu sharuÉ—É—a irin na wanda ya dace aba mutum aure,dan haka ki saka zuciyar ki a inuwa ki kuma hakura dan aure ba fashi,tashi ki ban wuri"
"Baba dan Allah" Ta faɗa tana ƙoƙarin dafa ƙafar shi,
Wani tsawan ya daka mata"tashi ki ban wuri,mutuniyar banza,ni na haifeki nasan girmanki da burinki har zuwa yanzun,dan haka shi yasa na zaɓa maki wanda naga yafi dacewa dake"
Ganin yanda yayi maganar ne yasa da sauri ta tashi ta bar dakin tana kuka,
A bakin kofa suka ci karo da Mama wacce take tsaye tana jinsu,dan haka jan hannun ta tayi suka shiga dakin ta,
Cikin masifa ta ce "me nace maki?ba nace ki bari zuwa anjima akwai inda zanje ba,wai me yasa Sumayya kike da gajin haƙuri"
Sallamar Aminu yaron makociyarsu ne ya dakatar da su,gaida Mama yayi sannan ya miko mata wani bakin leda "Mama gashi wai aba Sumayya inji Jauro"
Sai da ta yi kamar ba zata karba ba,sai da ya ƙara mai maita abinda yace sannan ta masa,ba tare da tace mai ko mai ba ya wuce,ganin ya tafi ne yasa ta buɗe ledan,
Wani dogon tsaki taja tana wurga ledan É—akin ta,
"Kai wannan mutumin akwai matsiyaci,yanzun Sumayya ya rasa me zai kawo maki sai ledan Burodi sinki biyu,sai kace wasu Fulani,gaskiya dole in tafi wurin wannan malamin dan ba zan iya gaiyar Fulani ba"kallon yar nata tayi,yanda duk tayi wani sanyi," Kinga tashi kije kiyi wanka ki huta,sannan ki cire komai a ranki banda tunani "
Jinjina kai tayi"to Mama "sannan ta tashi ta wuce,ruwa ta diba tayi wanka sannan ta koma ɗakin ta,ranar anan ta karya,gabaɗaya ta rasa meke mata daɗi,domin a duk lokacin data tuna shi bata taba ganin dacewarsu sai dai ma ta ƙara ganin wani makusa nashi,
HaÉ—uwar su ta biyu dashi,bayan kusan sati da haÉ—uwar su a cikin Adaidaita,harma ta manta dashi,amma a duk lokacin data tuna abinda ya mata shida É—an Adaidaita sai ta tsine mashi,
Ranar Mama ce ta aike ta gidan Aunty Aminatta amso mata wasu kaya,ta je ta amso kayan sai tayi tunanin me zai hana ta shiga kasuwa ta siya ÆŠan kunni,tun da gidan da kasuwa babu nisa.
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su É—aura min littafi a shafin su ko ya mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*5*
A Babban shagon siyayya ta tsaya wanda naga an rubuta B.S Store,dan bata cika son tayi ta zagaya ba,gara ta tsaya wuri É—aya kawai ta siya,
Shagon babban shago ne sosai wanda ba abinda basu siyarwa,
Cikin yanga da jan aji ta shiga shagon wanda ko yaushe baka raba su da jama'a,
Layin da ake saida Æ´an kunnaye ta nufa,cikin natsuwa ta cire wanda take so,sannan taje wurin biyan kuÉ—i ta biya aka saka mata a leda,
Har ta kusa fita bakin ƙofar shagon sai ji tayi ance "Malama muga ledan dake hannun ki"
Dago kai tayi ta kalleshi sannan ta kalli ledan kayan da Aunty Amina ta ɓata ta kaiwa Mama,
"Ban gane kaga ledan hannu na ba?
" Saboda muna zargin kamar akwai abin mu a ciki"
Daga ɗayan ɓangaren taji ance"Sani caje ta da kyau damun ƴan matan yanzun ɓarayi ne,haka jiya daga gaiyatar wata yarinya shan shayi daki na ta sace min DVD da nake kallo dashi"
Wani Alhaji dake zaune ne ya tuntsire da dariya"kai Jauro in bada kana É—an iska me ya kaika gaiyatar mace dakin ka wai shan shayi,dan ka mai da mu Æ´an iska"
Jin sunan da aka kirashi dashi yasa nan take ta tuna shi,domin ba zata taba mantawa da mutumin da ya mata tayin siyan Condom ba,
Shafa kai yayi yana dan dariya "ai wato Alhaji in faÉ—a maka jiya ne an dan yi sanyi shi yasa na gai yace ta,ban san ashe yarinyar nan barauniya bace,ko yanzun inda zan ganta wlh sai ta biya ni Sidi na"
Alhajin ne ya kira sunan yaron daya tsayar da ita"Salisu"
Amsawa yayi,
"Ko jiya a unguwar ku anyi sanyi?
GabaÉ—aya kwashewa da dariya sukayi,har da wasu mutanen dake zaune wurin," Ai sai dai in a unguwar su Jauro ne aka yi sanyi dan mu yanzun kan lokacin zafi muke"
"Kyale shege ya dai san Me ya ciyo har yake jin sanyi,ai ni yarinyar ma ta burge ni,gara data maka haka"
"Ai bani na gaiyace ta ba,kai kuma Salisu kar kayi abinda ke gaban ka,wallahi in ba kayi hankali ba har kai sai Æ´an matan garin nan sun maka tunbur sun sace kayan jikin ka,dan haka gara ka caje ta da kyau"
Nan ma dariya suka kuma sakawa,in da Alhajin yace"a kwanannan mata na mana sata shi yasa muka kara saka CCTV a ko ina na cikin shagon nan"
Wani ne daya fito daga cikin shagon yace"Salisu ina yarinyar da nace ka tare?
"Gata nan,yanzun ma nake duba kayan ta"
Tsaki mutumin ya ja"wai ne yasa kai a rayuwarka baka yin komai cikin nasuwa ne,ni da ba ita na nuna maka ba,wata farin hijabi,shine zaka tare wannan ka bari Barauniya ta gudu,?
Da sauri ya shiga mai da mata kayanta cikin leda "ɗan Allah Madam kiyi haƙuri kuskure ne"
Fisge ledan dake hannun shi tayi "ba ni da lokacin mahaukaci irin ka"
Taku biyu tayi ta tsaya a gabansu,idon ta yayi ja,wanda har ya tara ruwan hawaye,wannan wani irin tozarci ne,a gaban mutane,ai ko bata É—auka ba sun bata mata suna,
"In Allah ya yarda sai ƴan mata sun sace ka sannan suyi gunduwa gunduwa da kai su sai da naman ka"tana gama faɗar haka ta fita shagon tare da Addu'ar kar Allah ya ƙara haɗa ta da wannan mutumin domin ko yaushe hadurwata dashi baya tamo mata Alkhairi,.
Kallon shi sukayi yanda ya sake baki yana kallon ta,sai kuma suka kwashe da dariya,wanda Alhajin tsabar dariya har yana dukawa tare da rike ciki,
Kallon su yayi"To me na mata"
"Me yasa baka tambaye ta"
Ƙara kallon hanyar da rabi yayi "naga dai wannan karon ba da ita nayi magana ba,kodan nace yan mata take jin haushi na"
"Kama santa kenan ko Jauro"
"Eh to na dai taɓa mata tayin ko zata siya Condon a cikin Adaidaita wancan satin"
Duk zaro ido sukayi suna haÉ—a baki"tallan Condon,wannan budurwar?
Salisu ne ya ce"lallai Jauro baka dibo da sanyi ba,yanzun ka taba ganin in da aka ma budurwa tallan Condon ko da kuwa Æ´ar iska ce"
Bata fuska yayi "yo ni ba taimaka mata nace zan yi ba,kuma ai sa'a ce kuma su nake taimako"
"To wai in banda hauka ma irin naka me na sai da Condon?
" Nifa Dila ne,tunda bama da kamfanin nan Nigeria nake aiki ba,daga ƙasar Moroko ake kawomin Condon wanda da amincewar manyan kasarnar,da hukumar Lafiya na WHO,
Kuma an yi hakan ne saboda taimakon jama'a"
"Ta ya hakan ya zama taimakon jama'a"
Gyara zama yayi yana fasa ledan ruwa dake gabanshi ya zuke,"yanzun zamani ne na Family Planning da mata ke yi domin tsayar da haihuwa,wasu su saka na hannu,wasu kwayoyi na haÉ—iya,wasu Allurai,wanda dukkan su babu wanda bai da matsala,kaga kamar na kwaya,shi taruwa yake a mahaifa baya narkewa,karshe ya bata masu mahaifa a kai ga cirewa,Allah ya tsare,
Shi kuma Allura ko dai yasa mace ta shanza kamanni ta hanyar hurata,ko kuma ya sakar mata da jini,ko jinin yata wasa,gadai shinan,kaga wannan duk cutarwa ne,
Sai kuma wata hanya wanda ba ko wasu ma'aurata ne suke iya yin shiba,kuma shine hanya mafi sauƙi,wanda baya cutarwa,kuma Addini ya yarda dashi,malamai kuma sun tabbatar da babu matsala idan mutum yabi wannan hanyar,wanda ita ce Withdrawal Method (Pulling out) ba zaka zuba komai ba a jikin matarka,sai dai ka juye a waje,wasu kuma basu sanin sanda suke juyewa,to saboda haka aka yake da kyau amfani da Condom,ko ga ma'aurata wannan ba laifi bane,
Kaga wasu da yawa da auren su amma sai su haifi Unwanted child,ya'yan da ba'a so,wanda iyayensu basu shirya haihuwar su ba,kaji uwa na cewa ai wlh banma shirya haihuwa ba na haife shi,ko kuma iyaye su dinga jin haushin ya'ya saboda sun haifesu alokacin da basu shirya haihuwa ba,ko kuma É—awainiya sun masu yawa,hakan sai ya ja su dinga hantaran ya'yan kamar basu suka haife su ba,
Su kuma yan mata,saboda gudun Sexual Transmitted Infection,kuma ni dila ne ba wa kananan abu ba,shi yasa na mata tallah,ashe taji haushi na"
"To wallahi kayi a hankali in ba haka ba wata rana sai mata sun maka duka,ko kuma su daddatsaka kamar yanda waccen Budurwar taka ta faÉ—a" Alhajin ya karasa fada yana kwashewa da dariya.
Tsaki yaja "ni kam na wuce dan yau Ruga nake son na kwana"
Ajiyar zuciya ta sake tana zamewa ta kwanta,wanda daganan barci ya kwashe ta,
Koda ta farka har ƙarfe goma sha ɗaya na safe tayi,dan haka kuskure baki tayi tare wanke fuska,ta fito ɗan daura girkin rana,
Kallon tsakar gidan nasu tayi yanda yayi shiru,"Aisha ina Mama"ta tambaye yarinyar dake zaune kofar daki tana wasa da kwankwalati,
"Mama ta fita,tace idan kin tashi nace ki daura girki sannan ta tafi gidan Matar Kansila"
Shiru tayi tana tunani,kenan Mama ta tafi,Allah dai yasa naji kyakkyawar labari...
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*6*
Yana barin ƙofar din su bakin titi ya nufa,dama ranar a cikin gari ya kwana shi yasa yace bari yazo ya dubata,
Yana tare abin hawa yace ya kaishi Cancaga,suna zuwa ya sauka,daga bayan shi yaji ance"Jauro ina zuwa?
Juyowa yayi,ganin wanda yayi magana ne yasa yayi murmushi,cikin harshen Fulatanci yace mashi"gida zani"
"Oh bamu gaisa ba,barka da safiya ka tashi lafiya"
Yana hawa mashin dinshi yace "lafiya klau ya iyalan naka"
A lokacin ya tada mashin din yana amsawa,a haka suke tafiya suna dan taɓa hira kasancewar Musa kanin abokin shi ne,da Cancaga da rugarsu bai da nisa sosai dan ana iya shigar da kai a naira Dari da ishiri,a yanzun ma kenan da mai yayi tsada,
Sun yi tafi wanda aƙalla bai wuce tafiyar mintina goma ba su karasa cikin rigar ya kalle Musa yana dafashi a kafaɗa "Musa" Ya kira sunan shi.
"Na'am Jauro"
"Ina ga ka maida ni kawai Cancaga ko kuma ka sauke ni na koma da ƙafa"
ÆŠan juyowa yayi "lafiya kuwa bayan mun kusa karasawa"
"Lafiya glau,kawai dai nayi mantuwa ne,a kwai maganin dana siyo ma dabbobi kuma na manta dashi"
"To ka bari kaje ka huta mana ko zuwa anjima sai ka koma ka É—auko"
"Na Baffa Bube ne"
Da sauri yace"A'a to bari na mai da kai kuwa"nan take ya juya akalar mashin É—in,ya mai da shi in da ya dauko shi,sallamah suka yi ya kuma hawa wani Adaidaita ya dawo dashi cikin gari inda yake zaune yake haya,
Harya É—auki ledan maganin shanayen sai ga kira ya shigo mashi a kan ana niman shi a wurin aiki da sauri,
Ba yanda ya iya dole ya mai da maganin ya ajiye ya tafi wurin aiki da zummar in ya dawo komai dare a ruga zai kwana saboda ya kai ma Baffa Bube maganin shanayen shi kamin ya tsine mashi.
A ranar bashi ya dawo ba sai ƙarfe takwas na dare,yana shigowa wanka yayi,yana fitowa ya dauki wayarshi dake ƙara tun yana bayi,ganin me kira ne yasa ya ɗauka da sauri,kafin yayi sallamah yaji yace"Jauro kana ina"
"Ina gida,lafiya na jika haka?
" Wani gida?
"Cikin gari"
"Kana jina"
"Eh,amma lafiya Adamu?
" Ba lafiya ba,duk inda kake karka kuskura ka shigo Ruga,domin dazu da ko Sallar Isha'i ba'a idar ba,aka shiga gidansu Baffa Sanda shida matarshi aka dauke su,sun kuma harbi Yaya Audu yanzun haka ana shirin kawoshi Asibiti dan haka kar kazo"
GabaÉ—aya duk ya ruÉ—e "me kake nufi da an É—auke su,su waye suka É—auke su?
" Kidnapping dinsu aka yi,dan haka sai ka kiyaye Allah ma ya taimaka baka kusa"
Shiru yayi yayin da zuciyar shi ke zafi,sai kuma yace"suwa suka aita wannan aikin"
"Baka buƙatar amsa domin ka sani,kuma kasan abinda ya faru da Jabbi kwanaki uku da suka wuce,tayu tasu hanyar daukar fansan kenan"
Dafe kai yayi "ya Allahu,shi kenan na gode Audu,insha Allah zan kiyaye"
"Yauwa sai kaji ni kuma"nan suka sauke wayar,
Komawa yayi kan gado ragaf ya faÉ—i,yana lumshe ido,
A gaskiya ƙaddarar shi mai ƙarfi ce tunda Allah ya ƙaddara haihuwar shi a cikin Ahalin JAURO waɗanda suka kasance wasu irin hallittu da Ubangiji ne kawai yasan manufarsa na Halittar,
Su ba dabbobi ba ne amma kuma zuciyar su bana mutane ba ne,
Idan aka ce Ahalin JAURO indai ana maganar Dukiya na Dabbobi to Allah ya basu wannan Arzikin,
Baƙin ciki,harsada,da kyashi,wanda har yakai matakin da zasu iya hallaka junansu,
Ya taso acikin wata iri yar rayuwa mai cike da kalubale,tsana,tsangwama,rashin madafa,da kuma rugujewar buri,ya zamo É—an marayan Dawisu a cikin mugun dawa,wanda yake É—auke da mugayen namomin daji masu matukar hatsari da yunwa,wanda a ko wani lokaci suna iya kawo ma wannan Marayar Dawisu farmaki,ko nace sun sha kawo mashi Farkami inda Ubangiji ne kawai yake kareshi da kariyar sa,ya kuma saka shi acikin mutane masu tsayin rai acikin wannan dawar,yasa ya kasance a cikin zababbu bayan doguwar gwogarmaya.
*Asalin Ahalin*
Asalin Kakanshi shine Abdul Aziz,wanda ya kasance Ba'adare Bafullatani ne,wanda ya tara dukiya na Dabbobi daya gada a wurin iyayenshi,
Yana zaune ne a can wani ƙauye tare da Yayanshi guda biyar,maza uku mata biyu,,
Danshi na farko shine,Baffa Sanda,sai Baffa Dottiya,sai Baffa Bube,sannan gwogo Badejo,da kuma gwogo Halira,
Ada iyayensu ma'abota tashi ne daga wannan garin zuwa wannan kafin su tsaya a gari daya,wannan yasa gabaÉ—aya yaran nasu ba abinda suka sani dangane da Addini daya wuce noma da kiyo,
Haka ma iyayensu,
A tare da yaran babu wani shakuwa ko nuna soyayya irin ta Æ´an uwantaka,babu ragi ko kadan a tsakanin su,idan daya daga cikin su yama É—an uwanshi laifi to uwarsu zata ce lallai sai É—ayan ya rama dan yana dan wanshi bai isa ya masa yaki ramawa ba,da haka tarbiyarsu ta taso babu ragi a tsakanin su,kamar yanda babu sabo ko shakuwa a tsakani,
Ana cikin haka ne Allah ya fara dauke Abdul Aziz wanda suka fi kira da JAURO,daga baya ne suka tashi daga wurin da suke suka yanka tafkeken fili a nan Cancaga,aka kuma raba masu Gabon su kamar yanda suka buƙata,
Kowanne ya samu shanaye da suka kusa tasanma rabin garke a cikin su,Matan ma aka ba kowacce nata tayi gidan mijinta dashi,domin suna shekara goma sha biyu JAURO ya auran da kowacce,
Baffa Sanda ne yafa yin aure inda da ya aure wata Bafullatana mai suna Kande,sai da yayi haihuwa daya kafin Baffa Dottiya wanda yake Mahaifi a wurin Jauro,
Ada kafin auren Baffa Bube suna dan lallaba yanayin zaman nasu,duk da ba kasafai suke kula da lamarin juna ba, amma lamarin nasu da É—an sauki,
Domin Kande matar Baffa Sanda tana da Yara Biyu,daya ana kiranshi da Dotti,daya kuma Yabbale,
Sai matar Baffa Dottiya wacce a lokacin É—an ta daya mai suna Abdulaziz suna mashi lakabi da sunan kakanshi Jauro,
Tun daga lokacin da Baffa Bube ya auri matarsa mai suna Jabbi,ta tako cikin gidan da suna matar gidan,tun daga wannan rana duk wani farin ciki da ya ɗanyi saura a cin gidan ya karasa tarwatsewa,duk wani kwanciyar hankali dake gidan ta karasa koranshi,ta maida gidan filin yaƙi da farauta,ta hana kowa zaman lafiya ciki kuwa har da ita karan kanta,ta kara zama wata muguwar shaidaniya..............
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*7*
Zuwan Binta da kwana uku ta haddasa fitinar da tasaka sai da aka raba babban gidan da suke zaune kashi uku,domin kuwa a ranar ne ta je ta samu Baba Mari,mahaifiyarsu da kuka cewar wai tana cikin wanka sai taji ana lekenta tun da tazo,to shine yau Allah ya bata sa'a ta kama wanda yake leken ta,sai dai taji tsoro da ganin wanda bata yi zata ba,wato yayan mijinta Sanda,gaskiya ba zata iya zama ba zata koma gidan su ne ta fada tana kara fashewa da kuka,
Hankalin tsohuwa ya tashi,ranta yayi mugun bace,domin kuwa a garesu abin kunya ne babba ace daga aure amarya ta gudu,kuma dalelin kasancewa wai sai aji yayan mijinta ke lekenta idan tana wanka,dan haka cikin gaggawa tace maza a nimo mata Sanda yanzun nan,
Haka kuwa aka yi,yana zuwa ya duka a gabanta yana gaishe ta da harsher Fullanci,kin amsa shi tayi,wanda hakan ba ƙaramin mamaki ya bashi ba,dan yasan koda safe lafiya suka rabu,
"Inna lafiya" Ya tambaye ta.
Cikin masifa tace"wani irin abin kunya kake kokarin janyowa zuri'a ta,yanzun saboda rashin gode Allah matarka bata isheka ba har sai ka haÉ—a da na dan uwanka,wacce ko kwana uku bata cika ba a gidan nan,dama haka halinka yake bamu saniba sai yanzun Allah ya toni Asirin ka "
Duk wannan maganganun da take yi kanshi ba ƙaramin kullewa yayi ba,to me kuma ya haɗa shi da matar dan uwan shi,wacce bai ma ko gama tantance fuskarta ba,
Dago kai yayi da zummar yi mata tambaya,sai dai ji yayi an shakoshi anyi wurgi dashi a tsakar gida,an kuma bishi da sanda ana ƙoƙarin rafka mashi akai,wanda da badan yayi sauri cikin zafin nama ya kauce ba daya raba mashi kai biyu,
Cikin mamaki yake kallon dan uwan shi Bube,
"Me haka Bube,me na maka ne haka "
Har wani huci yake fitarwa na bacin rai yana nuna É—an uwan nashi"yanzun ni zakaci amana Sanda,ni zakaci amana ka dinga labewa kana kallon tsiraicin mata na saboda baka tsoron Allah,to yau sai na ga bayan ka"ya faÉ—a a zafafe yana nufarshi,
Oh sai yanzun ya fahimci inda maganar ta dusa,shima nan take ranshi ya motsa,ya kalle dakin da Inna ke zaune tana bantalar goronta hankali kwance,yayin da Binta ke kofar inna tana kallon rigimar da suke yi,
Sai matarshi Kande wacce shigowar ta kenan daga dibo ma dabbobi harawa wadanda ba'a fitar dasu kiyoba na mijinta,
Ganin abinda ke faruwa da kuma jin furucin Bube yasa cikin kidima ta zubar da abin dake hannunta tanufe dakin inna da gudu tana kuwa,tsugunnawa tayi a gaban ta "dan Allah inna ki shiga tsakani ki raba wannan fitinar"
Ture ta tayi"É—an Allah matsa can,ke yazun ba abin kiyi Allah wadai bane da Abinda mijinki ya aikata,matar dan uwansa da ya kalla,"
Cikin kuka take girgiza kai"wallahi ba halinsa bane,ba halin Sanda bane,na tabbata ba zai aikata haka ba"
"Ka jimin munafukar yarinya,har ni zaki faÉ—a ma halin É—a na,yaron dana raine shi tun kafin ki haÉ—u dashi,,to sai kije kiyi duk yanda zaki yi dasu ni dai bani daddakawa daga nan"ta faÉ—a da masifa,
Cikin tashin hankali ta nufe inda Binta ke zaune tana kuka ta rike hannunta " Dan Allah Binta ki faÉ—a gaskiya domin nasan hakan ba zai taba faruwa ba,na yarda da mijina na kuma yarda da halinshi,"
Ture hannun ta dake saman nata tayi"kenan kina tunanin karya na ma mijin ki ko me,to bari kiji,ko ki yarda ko karki yarda abinda ya aikata min kenan,kuma sai miji na yau daukar min fansa"
Daga bayanta taji ance "fansar me za a É—aukar maki"
Duk juyawa suka yi,suna kallon ta,gabaÉ—aya ta kere su tsayi da girman jiki,macce wacce take a tsaye,ga kazar_kazar,wato Halima kenan matar Baffa Dottiya,
Kallon cikin idanun Jebbi tayi,tana nunata da yatsa"ke daga ganin waÉ—annan idanun naki akwai munafurci da makirci a tare dasu,da yaushe mutumin da baya zama gida ya leka ki kina wanka"
Cikin tashe rashin kunya da nuna eh ba tsoronki nake ba tace"idan bai lekaba sai akayi ya,ko zaki shigar mashi ne,dan ni ban shigo gidannan da tsoron kowa ba"ta faÉ—a tana nunata da yatsa,
Ba zato ba tsammani sai ji tayi an kama yatsan an riƙe,sai kuma raji an juya,kafin ta fahimci me take kokarin yi sai jin wani azaba tayi ya ratsa ƙwaƙwalwar ta ya sauko saman ɗan yasan daya bada sautin Kas sannan ta sake,
Dago hannun tayi tana kallon yanda yatsar ya kwanta yana lilo,alamun kashin dake rike shi ya ƙarfe,
Wani ihu ta zunduma tana faduwa kasa tana birgima tare da rike hannun ta,
Jin ihun matar tashi ne ya saka da sauri yayi jifa da sandar dake hannun shi wanda ye kaiwa Baffa Sanda hari dashi,shi kuma yana goshewa domin ba shida abin da zai kare kanshi,har kuma ya samu damar samun shi a hannun wanda wurin tuni ya kumbura,
Dago ta yayi yana riƙe hannun tare da tambayarta lafiya,cikin kuka da ihun azaba take nuna mashi Halima dake tsaye tana masu kallon uku saura kwata"wannan maiyar ce ta karya min hannun,kalla ka gani,waiyo shi kenan zan zama mai yatsu huɗu kenan"
Da sauri Inna Mari ta fito,"ke Halima me ta maki kika karya ma yar mutane hannu"
Sai da ta harari gefe tukunna kafin ta kalli Inna ido cikin ido tace"yatsa ta nuna min,ni kuma naje sauke mata sai aka samu akasi domin ashe kashinta bai da kwari,kinsan Inna ni ban cika son ana nuna min yatsa ba,"
Ganin duk sun tsaya suna kallon ta ne yasa ta kuma cewa"nifa ba da gangan nayi ba,Inna kawo hannun ki in nuna maki yanda na mata,zaki tabbatar da kashinta ne bai da kwari"
Da sauri inna ta mai da hannun ta baya ta juya tana korarin shiga daki tare da faɗin,"dama Awala hakkillo,"ta fada tana karasa shigewa daki tare da sauke labulen dakin ta,dan sarai ta san halin Halima ba cikakken hankali gare ta ba,dan tana tare da mugun iskokai idan ka yi rashin sa'a kuna cikin hayaniya da ita suka tashi to kashiga uku,domin cutar rabkuwa suke saka mata,wato idan ta rike mutum zata ringa rabkashi da kasa ne yanda kasan ana bugun fulawa,kuma ta taba rabka inna Mari wacce sai da aka mata ɗaurin haƙarƙari shi yasa duk cikin sirikanta tafi shakkar Halima....
*Na yi kuskure a sunan matar Baffa Bube mai suna Jabbi,yanzun sunan ta Binta*
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*8*
Ganin irin kallon da take masu ne yasa bai ce mata komai ba ya kama hannun matar shi dake ihun hannunta ya taimaka mata ta mike sannan suka bar wurin,
Da sauri Kande ta karasa wurin da mijinta ke tsaye tana rike hannun shi,
Daga inda take tsaye tana kallon su amma bata San me suke fada ba,dan haka kaÉ—a kai kawai tayi ta koma dakin ta,
Sai bayan Sallar La'asar wuraren biyar Baffa Dottiya ya dawo,shine inna ta aika Yabbale É—an gidan Baffa Sanda da ya kira mata iyayen shi maza duka tana son ganin su,
Haka kuwa aka yi duk suka halarta kiranta,sai dai tsakanin Sanda da Bube ba wanda ya zauna kusa da ɗan uwan shi,kuma hakan be dame ta ba,illa daurawa da tayi da faɗin "nasa an kira kune dan na sanar daku lallai duk inda za ku nimo masu gini ku nimo,domin a gobe nake so a raba wannan gidan kashi uku ai ma ko wanne katanga,dan ba zan iya da wannan abin kunyar da kuke ƙoƙarin jawo min ba, gara a raba ya zamana ba mai shiga ɓangaren ɗan uwan shi"
"Yauwa Inna,wannan hukuncin naki yayi,dan gaskiya zama gida daya da kwartaye hatsari ne,dama kuma ko baki faÉ—i haka ba inada niyar aikatawa"
Baffa Dottiya ne da bai gane meke faruwa ba yace"wani irin Kwarto,sannan muna zaune lafiya ne yakawo batun rabon gida?ya tambaya yana kallon su,
Nan Inna ta kwashe komai ta sanar masa,ai kuwa mai zai yi banda dariya har yana tafawa,nuna Sanda yayi da hannu"yanzun kai ka rasa wacce zaka tsaya leke sai wannan mai kama da Kurbirgar(Muciyar tuwo)"
Nan take ran Baffa Bube ya ɓaci jin sunan daya kira matar shi,
Cikin jin haushi yace "ai gara nawa matar suffar muciya gare ta,ko ba komai mata ke rike muciya ba maza ba,kaga kenan ko tanan tana da suffar mata, akan matarka da take a tsaye kamar Garii (namijin bigimi),kuma wannan munafikin babu ni babu shi har abada kai har ranar tashin ƙiyama,ko zuri'a ta ban yarda ka kirasu da ya'yan ka ba,kamar yanda Ya'yan ka ba ya'yana bane har tashin duniya,Inna ki zama shaida
"Sai me dan kace haka,aikin banza,Allah na gode maka daka fara bani yaya baka yini juyaba,da na kashe kai na dan bakin ciki,kuma ko baka faÉ—a haka ba,dole haka zai faru saboda wannan shedaniyar da ka Aura,kuma ina mai tabbatar maka kai da kwanciyar hankalin iyali sai dai a lahira in ana yi kayi,dan na lura baka cikin masu rabo"yana gama fadar haka yaja dogon tsaki ba tare daya ce masu komai ba ya mike tsaye yana barin É—akin,domin bazai lamince tozarci irin na yan uwan shi ba,
Ganin ya bar dakin ne yasa kowannen su ya tashi ya bar dakin cikin jin haushi ba tare da ko wanne su ya ma tsohuwar da ke zaune magana ba,kamar yanda ita ma bata ce masu kuci kanku ba.
Washegari da safe ko gama wayewa gari bai yi ba,sai gashi masu aiki sun zo wadanda Baffa Sanda ne da kanshi ya gaiyato su domin su kangemai shiyanshi dana matarshi,sannan yasa a kara buga masu Bukka,
A taikaice dai a wannan gidan rana bata faÉ—i ba sai da aka kange waÉ—annan shiyoyin guda uku,
Hakan ne yasa gidan aka É—an samu kwanciyar hankali na kwana biyu,domin kowa na shiyan shi,
A tsakanin kwana biyun nan kuwa,sam Baffa Sanda ya hana Yayanshi shiga shiyan sauran ƙannen nasa,sai dai shi jauro yana shiga wurin yara ƴan uwan shi,kun dai san yanda yara suke,
Ana cikin haka ne Baffa Dottiya ya tattara kayansa da dabbobin sa wai zai tafi cirani,
A cikin su ba wanda ya damu da hakan domin su a al'adar su ba wani abu bane,
Cikin taimakon Allah kuwa suka bar gida shida matar sa wanda a lokacin Jauro yanada shikara biyu da rabi,
A kwana a tashi babu wuya a wurin Allah dan wasa_wasa sai da Baffa Dottiya ya kwashe shigaka hudu a wurin yawon shi na kiyo daga nan garin zuwa nan garin kafin su waiwaye gida, tare da tarin Alkhairai domin kuwa a lokacin dabbobin shi na shanaye kaÉ—ai sun tasarma garke biyu da yan kai,kamar yanda tumakai wato raguna sunkai garke daya,ya nada yara wadan da suke binshi kusan su huÉ—u,yana biyan su domin su tayashi kula da dabbobin shi,sai dai shi ya rigasu isowa gida dan su suna hanya,saboda rashin lafiyar matarshi shi yasa ya fara wutowa gada, wanda a lokacin abubuwa da yawa sun faru,kuma suna kan faruwa,domin kuwa Matar Baffa Bube a lokacin yaranta biyu,kuma tana dauke da cikin na uku,
Ko da suka dawo a shiyansu na da suka sauka kuma ita ma Halima lokacin cikinta na da wata takwas,wanda yake matukar bata wahala,kusan ko yaushe a kwance take ba lafiya,
A washegarin ranar da suka dawo ne taja hannun É—anta suka shiga shiyan Inna Mari wacce ke shiya daya da Baffa Bube,domin kuwa duk cikin ya'yan ta tafi son shi,
A hankali suke tayifa har suka shiga shiyan wanda tun daga bakin kofar zaka fara jin hayaniya na tashin hankalin da ake yi,
Duk da hayaniyar da take ji hakan bai sa ta fasa shiga ba,
Sai ma kallon É—anta da tayi "Har yanzun iyayen ka sunki suyi hankali"
Shima baice komai ba sai kallon ta da yayi,
Da sallamah ta shiga ɗakin Inna wacce take zaune tana sauraren bayanin da Binta ke yi "wallahi ba zan yarda ba,haka kurin ban haifarwa wata katowa ɗa na ba danta dinga jibgarshi ba,ba zan lamunta ba,haka jiya tsabar mugunta ina kallon ta data shigo kawo maki tuwo ta tunkuɗe Bakari,sai da kanshi ya bugu da tukunyar miya,na dai yi shiru ne kawai na kyaleta domin kar ka yi magana ace bakada kara akan dan fari,shi ne fa In faɗa maki Inna yau tana shigowa wai yaron nan Ɗan Fodiyo yazo da gudu cikin rashin sani ya buge ta,baƙi ga yanda ta daddage ta zuba mai Mari ba iya karfinta dan rashin imani,to wallahi ba zan yarda ba,ko dai adau min mataki ko kuma na dau ka da kaina"ta fada tana jijjiga jiki,
Ita ko Kande sai cewa tayi "kin daÉ—e ba ki dauki matakin da kanki ba,an gaya maki tsoronki nake yi,in banda rashin Albarka irin naki ke kika turo ÆŠan Fodiyo ya zo ya bangajeni,yaro ina mai magana saboda rashin tarbiya sai cewa yayi ni ba É—an ki bane da zaki min magana,har da hararata,ni tsaran shi ne"
Inna ce tace"to ba gaskiya ya faɗa ba Kande,ke uwar shi ce,ke ba uwarshi ɓace dan yaro ya faɗi gaskiya kuma sai kiji haushi,ke dai kawai ki fada wani dalili ne a kasa"kallon Binta tayi wacce take cika tana batsewa"ke ni ban iyawa da jarabarku idan ki nada yanda zakiyi da ita kiyi,me na cewa in dauki mataki,ku tafi na sallame ku ku bani wuri"ta fada tana nuna masu hanya,
Kande ce ta fara fita tana faÉ—in "sai ki yi duk abin da zakiyi domin dai nasan nafi karfin duka a wurin ki...
Kafin ta ankara sai ji tayi an wurgo mata marfin tukunya wanda bai tsaya a ko'ina ba sai saman goshin ta,nan take kuwa jini ya ɓalle,dafe wurin tayi tana kallon Binta wacce ke huci,
Kutmar uba,ai kuwa ba tayi katsa a guiwa ba tayi cikin Binta wanda nan take kokawa mai ƙarfi ya shiga tsakanin su,
Babu imani kuwa Kande ta shiga rusa mata kulli a ciki,wanda yake bai wuce wata uku ba,duka kuwa take har saida ta kaita kwance,
Dakin Inna kuwa duk abinda suke tana jin su sai cewa da tayi " Tsinannu sai ku kashe kan ku ai"
Ita dai da kyar ta mike tasan ko taje ba iya rabasu za tayi ba,domin ba daÉ—in jikinta take ji ba,
"Inna barka da safiya,"
"Ke raba ni da barka samun waÉ—annan tsinannu ba zasu bari na wayi gari lafiya ba"
"Inna bari in duba ko zan samu makota su zo su raba wannan faÉ—ar"
Bata ce mata komai ba sai tabe baki da tayi,
Ta gefen su ta raba ita da ɗan ta suka fita,domin duk da tana kallon yanda jini ke diga daga goshin Kande kamar yanda jini ke gangara daga ƙasan Binta,
Bata iya sauri gashi kuma yanayin gidan fulani,daya can daya can,basu gida kusa da juna,dan haka kallon É—an ta tayi"Jauro kayi gudu kaje ka kira duk wanda ka ci karo da shi "
"To inna na"
Da gudu kuwa yaro ya fita,cikin sa'a kuwa ya haɗu da matan Fulani su biyu suna ƙoƙarin shiga gida,rike hannun daya yayi cikin yaren fullanci yace,kuzo gidanmu Inna na tace in kira ko waye saboda ana faɗa,
Jin abinda yaron yace ne yasa suka bi bayan shi,ita ta masu jagora har shiyan Binta wanda zuwa lokacin duk sun jigata.....
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*9*
Ko da suka isa tuni Binta ta daɗe da suma sakamakon jinin da ya ɓalle mata,
Hankali su ya tashi sosai dan haka daya daga cikin matan ne tace bari ta je tama mazajen su magana tunda sunada mashin sai azo a tafi dasu Asibiti,
Duk amincewa suka yi da shawarta,dan haka da gudu tayi gida ta faÉ—a masu,
Da taimakon waÉ—annan matan ne aka É—aura su a mashin aka yi asibitin dasu,sai dai Halima bata bisu ba,dan cewa tayi ita kam bata iya hawa mashin dan haka su tafi kawai,
A ranar dai ita Kande ta dawo,ita ko Binta sai da tayi kwana uku a Asibitin sai da tasha karin jini leda biyu,sannan ga ciki ya zube,
A kwana na uku ne da suka dawo Goggo Badejo ta zo,É—an ita ma sau daya ta leka Asibitin,
Kallon Inna tayi tace "Inna ya kamata muje ki gaida Binta da jiki tunda ta dawo"
Kallan uku saura tayi mata"in gaida ita na me,ni na aiketa da zan mata sannu,ai da mutuwa tayi ni ba abinda ya dame ni da ta mutu Ɗa na aure zai ƙara,kuma ko yanzun tayi ta gama aure zansa yayi "
Bata ce mata komai ba ta tashi ta fita abinda,itama bata shiga dakin Binta ba sai tayi shiyan Baffa Dottiya wurin Halima,
Tun daga ranar da ya kira waÉ—annan Fulanin a gidansu shi kenan ya samu wurin zuwa wasa dan a gidan sunada yara sosai,
A cikin su a kwai wanda ake kira da Moha yaron zai kai shekara goma,yana da son karatu sosai,yana zuwa makarantar Boko dan alokacin yana primary four ne,
Tunda yaga yana karatu shikenan abun ya shiga ranshi ya manne mashi duk inda yayi yana like dashi wai sai ya koya mashi,
Washegari da safe kuwa tunda safe kuwa ya tashi ya tafi gidan su Moha,tare suka karya,sai da zai tafi makaranta labari ya canja,domin kuwa da kuka da ihu da komai aka raba su,
Ko da ya dawo gida ba karamin na ci ya dinga ma Baffa da Halima ba akan su bar shi ya dinga bin Moha amma sun ƙi amincewa,
Ko da Goggo Badejo ta shigo dakin yana kwance yana barci amma sai faman sauke ajiyar zuciya yake,
Kallon shi tayi ta kalli Halima dake zaune tana dama fura,
Zama tayi a kusa da ita tana nuna shi"shi kuma wannan ne akai masa da saffafen nen yake faman sauke a jiyar zuciya?
Ita ma kallon shi tayi tana tabe baki"kwana biyun nan rigima yake ji wai sai an saka shi makarantar Bokoko,ganin wani É—an mikotan mu na zuwa"
"Oh Boko,ai makaranta ce,kuma bashi da wata illa,kinga ko mu a wurin mu yara na zuwa sosai,ni ma bana zan saka Muntari,kin ga ma shi yana so me zai sa kuma hana shi,kawai ku bar shi ya je"
Kallon ta tayi"to sai dai kima ubansa magana dan ni babu ruwa na"ta faÉ—a tana mika mata lafiyayyen kwaryan kindirmon data dama.
"A'a bana Jauro bane?
" Ke dai karɓi bari na dama mashi wani"
Amsa tayi,shi yasa duk cikin gidan tafi shiri da ita saboda ba tada rowa"an jima zan ma Dottiya magana gobe da kaina zan kai shi makarantar tunda yana so"
Da haka dai suka ci gaba da hira,
Haka kuma akayi,kamar yanda ta faÉ—a haka tayi ma Dottiya magana,kuma ya amince,tare da faÉ—in,ai idan ya gaji da kanshi zai bar zuwa,
Washegari kuwa da taimakon Moha ta je makaranta su dake Chancaga makarantar Government ne,ta kammala mai komai inda a lokacin kyauta aka bashi kayan makaranta harda takardu,sannan aka nuna mashi ajin shi aji Daya wato Primary one dan a makarantar Government ba suyin Nursery class,wannan kenan.
Ta ɓangaren Baffa Dottiya kuwa tambayar shi Baffa Bube yayi a lokacin suna dakin Inna Mari da safe sun haɗu wurin gaishe ta "ni ko Dottiya yanzun dabbobin ka sunkai guda nawa?
Kallon É—an uwan nashi yayi" Garke biyu da yan kai,sai tumakai"
Duk kallon mamaki suke mai harda Inna "yanzun dabbobin ka har sun kai garke biyu bancin tumakai?
" Eh"
"Amma shine nawa dabbobin yanzun da suka rage ko garke daya basu kai ba,ko dai kana bin ta wata hanyar ne Dottiya"
"Ah to faÉ—a mashi,ni dai duk wanda ya dauko fitinar shi ta tsaya can a kan shi" Cawar Inna,
Kallon su yake cikin mamaki"yanzun ni zaku ma irin wannan zargin kuma har da ke Inna,haba sai kace bake kika haife ni ba"
"Yo ko ni na haife ka ai kullun cikin canza hali kuke,balle kai da kayi sheka hudu baka gida"
Kafin ma ya samu damar mata magana sai ji yayi Bube yace "To ni dai ina rokan ka bani kiyon iri koda shanaye guda ishirin ne"
Kallon mamaki yake mai "in baka fa kiyo kace,bancin naka wanda kake dasu"
"Kwarai kuwa ai kiyo nace ba kwayta ba"
"To ba zan iya ba" Ya faÉ—a yana mikewa,
Inna ce tace"kai ko ai kyauta ma kana iya ba dan uwan ka"
"Inna ki ƙyale shi yaje ya gani in dai ni ya ma haka"
Bai kula suba ya juya ya wuce yana kananun magana,dan bai zaci haka daga É—an uwan shi ba,
A washegarin ranar ne Halima ta tashi da matsanancin ciyon ciki,wanda tun tana daukar abin da wasa har ya fara cin karfinta,gashi Dottiya ya fita cikin gari,shi kuma Jauro ya tafi makaranta,
Abu kamar wasa duk maganin da take tunanin zai taimaka mata tasha amma abu kamar ƙaruwa yake,ji take cikin jikinta ya dawo mata zuciya ya tsaya,
Tun tana iya tashi har yakai ta fara fita haiyacinta domin kuwa jini ne ya balle mata,gashi a lokacin cikinta ko wata tara bai gama shiga ba,
Dama kuma matan gidan ba shiga shiyan juna suke yi ba balle Allah ya kawo mata wani,dama ace Goggo Badejo na nan ne,to sai dai shekaran jiya ta koma,
Tana cikin haka ne Allah ya dawo da Jauro sai dai lokacin ko magana bata iya yi,gashi jini duk ya bata wuri,
Duk da kasan cewar shi yaro a lokacin yasan jini,domin yasan lokacin da Mamar su Moha suka sai Binta asibiti lokacin da take zubar da jini,
Dan haka da sauri ya fita yayi gidan su Moha,sai dai cikin rashin sa'a bai tarad da kowa ba a gidan,domin kuwa sun je suna a wani ruga dake gaban nasu,
Hakan ne yasa da gudu ya dawo gida ya shiga shiyan Binta,wacce ke zaune tana cin abinci,tsabar rudewa har yana mata ƙwallo da kofin ruwa dake gabanta,
Aikuwa ba tayi kasa a guiwa ba wurin dauke shi da mari"kai wani irin É—an b.... Yaro ne,baka ganin gabanka ne"ta tureshi tana daga kofin ruwan gabanta"maza tashi ka barmin shiyana,kafin in balla ka,hala ma leken Asiri uwarka ta turo ka min"
Kuka ya fashe da shi domin marin ba karamin shigar shi yayi ba,
Duk da haka sai da ya É—an maso kusa da ita cikin kuka yace"Innan ÆŠan Fodiyo dan Allah kije ki duba Inna ta ba tada lafiya jini ya bata É—akin mu "
"Me kace?
Nan ya kara maimaita mata abinda yace,
Wani harara ta zuba mai,wanda yasa sai da ya matsa baya" Dallah matsa ka ban wuri,ni lokacin da ciki na ya zube ina ce mamarka tana nan kuma tana kallo,dan haka ita ma nata cikin ya zube,taji yanda naji, fitar min a shiya munafiki"ta faÉ—a tana nuna mashi kofar fita,
Da kuka ya fita ya koma shiyan su,zuwa yayi ya tsaya a kanta yana kallon yanda take fitar da numfashi da kyar,
Tsugunnawa yayi a gabanta yana kuka ya rike hannun ta"Inna,Inna"ya kira sunan ta,
Da kyar ta iya buÉ—e ido ta kalle shi,
"Na je kiran innar su Moha babu kowa a gidan,da zasu kaiki inda suka kai Innan ÆŠan Fodiyo,
Itama na naje kiranta tace ba zata zo ba," Gani yayi ta maida ido ta kara lumshewa,jijjigata ya yi"Inna ki tashi muje inda aka kai Innan ÆŠan Fodiyo ke ma zaki samu sauki"ganin bata buÉ—e ido bane yace"bari na je na faÉ—awa Innan su Yabbale,
Sake hannunta yayi ya fita da gudu,bai tsaya ko ina ba sai shiyan Kande.....
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*10*
Bai tsaya ko'ina ba sai shiyan kande,
A lokacin tana kicin tana tankaden gari,da sauri ya rike hannun ta"Innan Yabale É—an Allah ki zo ki duba Inna ta bata magana kuma jini ya bata É—akin mu,"
"A'a Jauro sake ni kar kasa na zubar da garin tuwo,"
Matsawa gefe yayi ya tsaya yana kallon ta har ta kammala tankaden ta sannan ta kalleshi,ganin har yanzun kuka yake,"me ya sameta "
"Ni ma ban sani ba,sai dai bata magana"
Tsaki taja tana kallon aikin dake gabanta,gashi har ƙarfe biyu ta wuce ko tuwo bata gama ba,
Kara kallon shi tayi"Jauro,ina ganin ka je kawai idan na gama girki zan zo na same ka"
Gyada mata kai yayi yana juyawa cike da fatan ta gama da wuri ta zo,
Har ya kusa fita daga shiyan ta kuma kiran sunan shi,
Dawowa yayi,
"Jinin da yawa yaje zuba ne? Ta tambaya,
" Eh da yawa ne"
"To karka damu yanzun zan zo kaga har nayi talge saura tukawa sai nayi miya,
Nan ma kai ya gyada mata,
" Yauwa to ka faÉ—a ma Inna Mari kuwa?
Girgiza kai yayi,
"To kaje itama ka faÉ—a mata ko akwai wani iccen da zata ba ka sai ka jika ma innar ka,yi maza ka tafi"
Da sauri kuwa ya fita, duk da yana tsoron shiga shiyan sai da ya leka dan ya gani ko Binta bata tsaka gida,sai dai tana ma zaune ne a tsakar gidan,
Rasa yanda zai yi yayi dan haka dole ya samu wuri ya tsaya a ƙofar gidan yana jiran ya gani ko Allah zai sa ta shiga cikin daki,
A haka sai da ya kwashe kusan minti talatin kafin ya samu ta shiga daki,
Da gudu kuwa ya shige cikin gidan yana shiga dakin Inna Mari,wacce ke zaune tana saka mafecin rufe ƙwarya,
Allah sarki yaci kuka har hawaye ya bushe a idon shi,muryanshi ya shake baya fita sosai,
Tsugunnawa yayi a gabanta yana rike hannun ta"Inna Mari É—an Allah ki taimaki Inna ta bata magana,sannan akwai jini a dakin mu,É—an Allah muje ki ganta"
Ture shi tayi"kai matsa ka ban wuri,ni bani iya zuwa ko'ina dan yau da ciyon kafa na tashi ba zan iya zuwa ko'ina ba dauko min wancan ledan "
Da sauri ya dauko mata ledan,
Wani kullin magani ta ciro ta mika mai"amsa jeka jika mata ka bata tasha,ƙila nakuda take yi"
Amsa yayi yana kallon ta"to ba zaki je ki dubata ba Inna "
"Kai me yasa ka cika kunata je ka kai mata kawai ai tasan yanda zatayi dashi"
Tashi yayi ya fita daga dakin,yana kallon mugun kallon da Binta ke bin shi dashi,sai dai tunda ya kalle ta sau daya bai kara yarda ya kalle inda take ba har yabar shiyan,
Yana shiga shiyan su da sauri ya karasa inda take kwance yana kiran sunan ta,sai dai wannan karon ko motsin da take yi da ido bai ga tayi ba,
Girgizata ya shiga yi"inna,Inna,ki tashi ga magani na amso maki,gashi ki tashi ki jika,Inna Mari tace kinsan yanda ake amfani dashi,"tashi yayi ya fita tsakar gidan su inda take ajiye kwarya,daya ya dauka ya dawo inda take kwance "Inna ga kwarya na dauko tashi ki jika maganin kisha" Nan ma shiru babu amsa,
Kallon ta ya tsaya yana yi kamar mai tunani,ya dauki lokaci mai tsayi yana kallon ta,kafin a zuciyar shi ya raya mashi ƙila bacce take yi bari ya jira har ta tashi,sai ya bata maganin,nan ya ƙara ɗaukar ƙwaryan ya rungume yana kallon ta,
A wannan lokacin ne kuma wani barci mara daÉ—i ya É—auke shi mai tattare da yunwa.
Ana cikin haka ne Baffa Dottiya ya dawo misalin karfe biyar na yamma,
Tunda ya doso cikin gidan gaban shi ke faduwa,sai dai bai kawo komai a rai ba,domin duk kwanan nan abun da yake yawan ji kenan,
Yana ɗaga labulen dakin wani irin karnin jini ne ya daki hancin shi wanda yasa da sauri ya saki labulen ba tare daya shiga ba,dan shi mutum ne mai kyankyami baya shiri da ƙarni,
Halima kuma macce ce mai tsafta sosai ga son kamshi,ko yaya ne ba ka rabata da irin turaren nan na mutanin da wanda suke amfani dashi,
Mamaki ne ya kama shi,dan haka sai bai shigaba ya tsaya a wurin yana kiran sunan ta,wanda hakan ne ya tayar da Jauro,
Missike ido yayi yana kallon ta,har yanzun dai barcin take yi,dan haka zuwa ya ƙara yi inda take yana jijjigata tare da kiran sunan ta,"Inna ki tashi Baffa ya dawo,gashi can yana kiran ki"ganin wannan lokacin ma bata motsa bane yasa kawai ya tashi ya fito,
Kallon shi Baffa yayi "Innar ka fa?
" Baffa tana daki,tun Dazu nake tada ita kuma taki tashi,yunwa nake ji"
Ji yayi gaban shi ya yanke ya ƙara faɗuwa,
Bai ce mashi komai ba ya kutsa kai cikin É—akin,sai dai a irin halin da ya iske matar tashi a ciki ne yasa saura kaÉ—an jiri ya yarda shi,
Har ji yake numfashin shi na ƙoƙarin daukewa,gaɓoɓin jikin shi shi sun sake,
A hankali kamar wanda ke tsoron karasawa wurin da take ya isa,
Hannun ta ya É—aga,sai dai yana sakewa hannun ya faÉ—i ragaf,
Duk inda yake tunanin zai ji numfashi a jikinta ya taɓa sai dai dip babu alamunsa,wanda dama tun ganin farko daya daura ido a kanta ya tabbatar da cewa yayi rashi babba,
Kallon É—an nashi yayi,"je ka kira mutanen gidan nan"
Harya juya da sauri ganin Baffa shi na hawaye,sai kuma ya dawo yana kiran sunan shi"Baffa dazu naje na faÉ—i ma Innar ÆŠan Fodiyo tazo Inna ta ba tada lafiya kuma a kwai jini a dakin mu shine taki zuwa kuma harda Marina tayi,na san yanzun ma idan na je dukana zata yi,ita kuma Innar Yabale tace idan ta gama abinci zata zo"
Ji yayi wani irin hawaye masu raɗaɗi sun sauko mai,menene amfanin irin wannan rayuwar,me amfaninta,ace maka mutum na zubar da jini tun ƙarfe daya na rana,yaro yaje ya faɗa maku amma ba wacce ta iya cewa bari in Leko in duba kai koda Akuyar ka akace tana zubar da jini ka je ka gani balle a ce mutum,haba,haba,wannan rashin imani ya ɓaci,
"Ka fada ma Inna Mari kuwa"
"Na faɗa mata tace ba zata iya zuwa ba saboda ƙafarta na ciyo,sai dai ta bani magani na kawo ma inna ta jika,sai dai ina ta tada ita amma bata tashi ba"
Bai san da idon fassaran da zai kalle ahalinsa ba,bai san da wani kalan suna suka dace ya kira suba,sai dai abu É—aya,shi ne yana masu fatan tarwatsewa tankar yanda suka tarwatsa rayuwar shi,suka ki kula matar shi da danshi alokacin da suke nimam taimako,
Shi kuma insha Allah sai ya basu mamaki,ba zai nima taimakon su ba koda da menene,
Tashi yayi ya dauki fura ya dibo kindirmu a inda suke ajiyewa ya dama na É—an na shi,
Yana gamawa ya haÉ—a wuta ya saka ruwan dumi,sannan ya watsa magarya aciki tamkar yanda wani malami ya nuna masu a lokacin da mahaifin su ya rasu,kuma ya masu bayani yanda zasu mace,dan alokacin shine ma ya tambaya in macece ya ake mata,
Sai da ya gusar da duk wani najasa dake dakin dakuma wanda ke jikin ta,sannan ya mata wanka tas,
Ya ce ma Jauro "zauna kusa da Innar ka bari in je in dawo"
Kallon Baffan na shi yayi "Baffa yaushe zata tashi"
Guya kai yayi ya share hawayrn shi"karka tada ita kaga ba tada lafiya bari naje na dawo,
Yana fita gidan limamin dake basu sallah yaje,dama ba'a rasa likafani a wurin shi,dan haka faÉ—a mashi yayi,abinda ke faruwa dashi har izuwa mutuwar Matar shi ya karasa faÉ—a yana fashewa da kuka, "kamar yanda suka ki kula É—ana alokacin daya je niman taimakon su,ina fata kar Allah ya taimaka masu a ko wacce hanya,ya bar su da iyawarsa,ya tarwatsa su"
Da sauri malamin ya rufe mai baki"haba Dottiya me yasa kake irin wannan addu'ar ga ahalin ka,kaga irin haka bai da kyau,ko ba komai Æ´an uwan ka ne hakan be kama ta ba"
"Malam yanzun damuwa ta daya,shine Jauro,wani irin rayuwa É—ana zai yi,bana son dana ya tashi da irin wannan hali nasu,bana so yayi koyi da dabi'un su,da nasaka raina akan mahaifiyarsa ce,kuma sai gashi ta riga tafiya ta barni"
"Me kake faÉ—a haka ne Dottiya,insha Allah kana tare da É—an ka,kai zaka reni abin ka, "
Girgiza kai yayi,yana ƙara zubar da wani hawayen wanda yake jin zafin shi har cikin zuciyar shi,"naso haka,naso ace hakan zai kasan ce,sai dai kuma...... "
Sai yayi shiru ya kasa karasa fada,rike hannun malamin yayi"É—an Allah ina rukon wata Alfarma a wurin ka"
Cikin tausayawa yace "ina jinka Dottiya"
"Malam dan Allah ina rokan ka dauki Jauro acikin É—aliban da kake koyarwa,ka tsaya mashi yayi ilimin addini,karya zamo kamar mu dan Allah Malam"
Jinjina kai yayi"na maka Alkawari Dottiya,insha Allah zan tsaya masa ya samu ilimi addini yanda ya kamata,ka kwantar da hankalin ka,kaga mutane har sun taru domin na aika daya daga cikin yarana suje suyi shela za'a sallar gawa a gidan ku,taso muje a samu a kai ta É—akinta na gaskiya kafin magriba tayi"......
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*11*
Duk wannan abunda ake yi matan gidan ba su sani ba,har Matan liman su biyu suka zo suka taimaka mai aka saka mata sutura,
Shine fa ÆŠan Fodiyo yaje cikin gidan su yake fadama Binta yaga Baffa Dottiya na kuka,
Sai ga Kande ta shigo da gudu tana ihun kira Inna,
"Waiyo jama'a mun shiga uku Halima ta mutu,Inna,Inna"
Da sauri ta fito É—aki har zanin jikinta na faduwa "ke wata Halima ce ta mutu?
Kuka ta fashe dashi tana zama abakin dakalin wurin tare da daura hannu a kai" Innar Jauro,waiyo Allah kaicona dazu yaron nan ke bina akan na zo na duba Uwar shi tana Zubar da jini,amma ban kula shi ba nace ya bari sai na gama girki,ashe dai mutuwa zata yi "ta karasa faÉ—a tana fashewa da wani sabon kukan" Gashi can yanzun za'a fitar da ita,saboda bakin hali irin namu ko sanar damu abinda ke faruwa Dottiya bai yi ba,sai makota ya gaiyato suka taimaka mashi"
Inna Mari da sauri ta doshi hanyar waje har tana tuntuɓe,
Koda ta shiga shiyan Halima har an fito da gawar,
Kuka ta saka tana rike makaran"yanzun shikenan Halima tafiya zaki yi ki barmu,Allah sarki mutuniyar Arziki dana sani dazu ai koda rarrafe ne dana gangaro,ashe bamuda rabon ƙara ganin juna ne"
Dottiya ne ya kalle wadanda suka taya shi daukar makaran"kai mu tafi dare na yi "
Ai kuwa cire hannun ta daya yayi daga jikin makaran sukayi gaba da ita, zama tayi a wurin ta dafe kai domin ba karamin sanyi jikinta yayi ba yau,har balle irin kallon da taga Dottiya na mata,tabbas tasan bata kyauta mai ba a matsayin ta na uwa,bai dace ta tsaya a bangare daya ba,bai dace a lokacin da yaro yazo mata da maganar mamar shi na zubar da jini taki sauraren shiba,yanzun wani irin kallo mutane zasu mata,ita kan da tasan mutuwa Halima za tayi wallahi da taje ta ganta.
A waje kuwa cikin aminci aka yiwa Halima sallah sannan aka kaita gidan ta na gaskiya,
Allah sarki Dottiya sai da aka daga shi daga jikin kabarin ta,
Kwana uku akayi zaman makoki wanda duk lokacin yana manne da ɗan shi,duk zaman da akayi ba laifi yana tare dasu Bube suna karɓar tare,sai dai matan duk wacce ta mai gaisuwa idan ya amsa so daya baya kuma amsawa har ta da Inna,
Sai dai abin mamaki duk wannan abinda ya faru Binta ko sau daya bata taɓa lekawa da sunan gaisuwar rasuwar Halima ba,har ta su Badejo dake aure wani gari sun zo gaisuwa amma ita ko kofar shiyan Halima bata leka ba har yanzun da nake magana.
Bayan sadakan uku ne shanayen Baffa Dottiya suka iso da daddare,
Fita yayi ya same su,dan lokaci kusan ƙarfe ɗaya da rabi ne na dare,
Zama yayi kusa dasu yana masu bangayi,
ɗayan ne mai suna Manu yake tambayar shi "ina uwar ɗaki na"dan sunan da yake kiran Halima dashi kenan,yana dariya yace" Yanzun nasan ta kusa haihuwa,Jauro ya samu kani ko ƙanwa"
Daya daga cikin su ne yace"to na dai rigaka Manu in dai mace ce ni za'a ba auren ta"
Su biyun dariya suka yi,dama kuma su huÉ—u ne masu masa kiyo to biyu sun kwanta dan lokacin biyu tayi,
Ganin ya dukar da kai yayi shiru ne Manu ya ce"Uban daki na ni kam ba kada lafiya ne naga wallahi duk kayi wani irin rama kayi baki,"
Dago kai yayi ya kalle su yana sauke ajiyar zuciya,
,"Halima ta riga mu gidan gaskiya,Allah ya karɓi abinshi "
Ji kake wurin yayi wani tsit na É—an lokaci tamkar babu mutane a wurin kafin Manu yace"ni fa Innar Jauro nake magana"
Dafa kafadarshi yayi "kwarai kuwa ita,ni kaina na kasa yarda gani nake kamar a ko wani lokaci tana iya dawowa bayan da hannuna na saka ta acikin kabari"
Yakubu ya fashe da kuka yana salati,domin su biyun sun kasance yan dakin ta sosai na tsayin shekaru huÉ—u da sukayi yawo,
Sosai yaran suke jajanta rashin Uwar dakin nasu,
"Ina roƙon wani alfarma mai girma a wurinku"
Duk mai da hankali kanshi suka yi, "muna jinka uban É—akin mu"
A jiyar zuciya mai ƙarfi ya kara sauke,yana jin wani irin ciyo da raɗaɗi mai kuna yana taso mashi daga ƙasan zuciyar shi,
"Alfarman da nake nima babba ne wanda bansan ko zaku iya rikewa ba ko ba zaku iya riƙewa ba,abu ɗaya na sani shine na yarda daku har cikin zuciya ta,ba ni da wanda zanba amana sama daku,idan har kunci amana ta Ubangiji na kallo domin ni saboda yarda na bayar,idan kuma Allah ya baku ikon rikewa Alhamdulillah,
Ina so ku dauki Shanu garke É—aya,raguna da tumakai rabin garke,ku tafi da su "
Duk kallon mamaki suke mai,"mu tafi dasu ina,bayan gashi mun dawo gida,yanzun lokacin damuna ne ai ba rani ba"
"Haka ne,sai dai kuma ina da dalilina na yin haka,Manu ba ni da lafiya sosai,ako wani lokaci komai na iya faruwa dani,ƙila ana iya kwantawa dani ba'a tashi da ni ba,
Abinda nake matukar tsoro kenan,
Saboda Æ´an uwana,nasan da zaran bana raye zasu karbe komai na dukiya ta daga hannun ku,nasan ba zasu ajiyema É—ana komai ba,kuma koda ya girma ba bashi zasu yi,
Shi yasa nake son ku tafi dasu,ku yi nisa dasu,in so samu ne kuna iya komawa dasu nahiyar ku ta Niger daga nan har zuwa sanda Jauro zai mallaki hankalin shi,"
Yakubu ne yace "uban gidana kamar nan da shekara nawa kenan?
" Yanzun shekaran Jauro shida,yana ƙoƙarin shiga na bakwai,dan haka nan da shekara Goma sha biyar"
Duk kallon mamaki suke mai,dan basu zata zai ja da nisa ba,
"Amma kana ganin bai yi yawa ba"
"A'a bai yi yawa ba,sannan bana son Æ´an uwa na su sani,kawai in so samu ne ku yi yanda nace sannan ina son ku tafi tun kafin gari ya fara haske dan bana son su san iya adadi abinda kuka tafi dasu"
Allah sarki,a haka suka karɓi wannan amanar da Yakubu da kuma Manu,sannan cikin wannan daren suka bar rugar da taimakon shi Dottiya,suna mashi fatan samun tsawon rai don coyon hanta mai tsanani yake fama dashi wanda yayi chronic sosai.
Washegari da safe da kanshi ya shirya Jauro kuma ya raka shi har gidan su Moha inda zasu tafi Boko da keken shi,
Bayan ya dawo ne ya tafi shiyan Bube wurin Inna domin sanar da ita isowar shanayen shi.
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*12*
Sallamarh yayi yana shiga cikin É—akin nata,
Amsawa suka yi suna matsa mashi dan ya samu wurin zama,
Saida ya fara gaida Inna Mari kamin ya juya ya gaida su a jam'i,sannan ya zauna,
"Nikam Dattiya me ke damun ka ne,naga duk ka lalace"cewar Baffa Sanda.
" Babu komai,"
"Amma ka yi kaman wanda ke cikin rashin lafiya" Wannan karon Bube ya tambaya,
"Ya dai kamata ka cire Halima arai haka nan,tunda kasan dai wanda ya mutu ba shi dawowa,dubi yanda ka kanjame,ai da irin wannan tunanin da zai iya hallakaka gara kawai kayi aure ko zaka rage tunani"
Shiru yayi yana kallon Inna,ko fa sati É—aya matarshi bata gama cikawa da rasuwa ba,amma shine har take dauko mai batun wani aure,ya tabbata idan da yarta ce ta mutu ai ba zata ce ma mijin yar yaje yayi wani aure ba,
"Inna shanaye na sun iso da daddare"
Washe baki ta hau yi"kai abu yayi kyau,anjima kuwa zan saka yara su kaini naje na gani"
Kallon ta yayi yana mamaki hali irin na Uwar su,"ke da kafarki ke ciyo,ko ina baki iya zuwa shine har zaki iya zuwa ganin dabbobi,ko da yake dabbobi ne ai sunfi mutum daraja "
Duk shiru suka yi,domin sun fahimce inda zancen nashi ya dosa,
"Yanzun Dabbobin ka sunkai nawa Dottiya,nasan sunyi Albarka? Baffa sanda ya tambaya dan kawai ya dauke shirun da É—akin yayi,
" Garke daya ne da guda dari biyu,sai tumakai gudan saba'in"
Duk kallon mamaki Inna da Bube suke mai"amma nan kace min shanayen ka sun wuce garke biyu, bancin tumakai"Cewar Bube kamar a hasale,
"Na dai faÉ—a ne kawai amma iya abinda nake dasu kenen,ko dai basu yi Albarka bane?ya faÉ—a fana kallon su shima,dan bai gama fahimtar in da suka dosa ba da wannan tambayar da kuma zafin rai na Bube,
Sanda ne yace" A'a abu yayi Albarka,kai da ka wuce garke daya,babu laifi ai,Allah ya saka masu Albarka,idan munbar nan zamu je mu duba su"
Bai basu amsa ba sai ma tashi da yayi ya bar su a dakin.
A haka dai yaci gaba da lalla rayuwar shi yayin da duk safiya idan an idar da sallah zai kai Jauro wurin Malam liman ya ɗauki karatu zuwa ƙarfe bakwai na safe kafin ya dawo ya tafi Boko,nan ma in ya dawo zuwa ƙarfe hudu yake sake tura shi islamiyan yamma,
Ana cikin haka ne suka wayi gari da tsananin tashin hankali a wannan gidan,wanda shine yayi sanadiyar sauya rayuwar Jauro,ya mai dashi daga sama ya dawo kasa sannan a ƙasan ma ya kife,wato rasuwar Mahaifinshi Dottiya,wanda suka kwanta dashi sai dai basu tashi dashi ba,
Mutuwar ta shiga mutanen gidan sosai har balle tsohuwa Inna Mari,wacce rabon da amata rasuwa tayi kuka irin haka tun mutuwar mijinta,
Sunyi Jimami na tsayin kwana uku kafin su wassake,
Allah sarki Jauro,duk da yana yaro yanda yayi kuka a mutuwar mahaifinsa bai yi a lokacin daya rasa mahaifiyar sa ba,domin kuwa a lokacin mahaifinsa ne ke dauke masa kewar Innar sa,baya bari yayi kuka rashinta,
Yanzun kuwa yana wurin Æ´an uwan mamarshi ne da suka zo gaisuwa,
Randa aka gama sadakan uku kuma da zasu koma suka roƙi Inna Mari Alfarma ko zata basu dama suna son su tafi da Jauro ya zauna a wurin su,
Har fa matar nan ta amince,sai ga Baffa Bube ya shigo a jigace har yana kumfar baki,kan cewa me yasa za'a basu Jauro su wuce dashi,ai suma suna da halin da zasu iya riƙe shi,kuma shi zasu dinga gani suna tuna ɗan uwansu,dan haka su tafi kawai shi zai rike Jauro a hannun shi,
Babu kalan rokon da basu mashi ba amma ya rufe ido yaƙi,karshe ma sai bin bayan shi Inna Mari tayi,
Wannan abun yaba ƴan Uwan mahaifiyar sa haushi,akan irin maganganun da Bube ya masu,wanda yaja suka yi fishi tare da Alkawarin basu kara tako ƙafar su inda suke,sai dai in Allah ya raya Jauro da kanshi zai zo ya nime su ta yanda basu isa su hana shi zuwa ba,
Da wannan bacin ran suka wuce,domin dama su burinsu su dauki ɗan ƴar uwarsu su riƙe saboda sun san irin zaman da ake yi a wannan gidan,
To sai gashi abin bai yuba,sai dai kawai su bishi da Addu'ar Allah ya raya shi,ya bashi haƙuri da juriyan zama a cikin waɗannan mutanen,wannan kenan.
Bayan wucewar su ne Inna ta kalle shi "to yanzun kai Bube ka nada in da zaka ajiye yaronnan daka hana a tafi dashi,ka dai san halin matar ka da bakin hali,"
"To Inna ba sai ya dinga kwana a dakin su ÆŠan Fodiyo ba,ai yaron da wayonshi tunda ba kashi zata dinga wanke mai ba,abinci kuma wanda kowa yaci haka zai ci,to me aciki,kenan baki gane me mutanin nan suke nufi ba,so suke yanzun da sun karbe shi zasu ta da fitinar a raba gado a basu nashi su tafi dashi gaba É—aya,shi yasa na hana"
Kallon shi tsohuwar keyi"to nikan in haka ne me zai hana a kira Malam liman a gobe yazo ya raba gadon nan kowa ya huta,"
Turbune fuska yayi "A'a ba sai an ƙirashi ba,ki bari ni zan kira malami na zai zo ya raba da kanshi,ko a cikin gari ba karamin babban malami bane"
"To shikenan hakan ma zai fi,yanzun dai sai ka faÉ—a ma É—an'uwan ka,saboda yasan abinda ake ciki"
Haka kuwa aka yi,a ranar su da basu magana da juna sai gashi saboda abin duniya suka shirya,
Washegari da kansu suka je suka dauko wannan malamin a cikin gari,
A dakin Inna aka zauna za'ayi rabon,bayan sun je sun kirga dabbobin,wanda suke garke daya da guda Dari biyu,
Sai tumakai guda saba'in,
Kaso na farko da aka fara yi,shine Baffa Bube aka bashi shanaye guda dari huÉ—u,shima Sanda aka bashi Dari huÉ—u,ya rage dari huÉ—u,shi ma aka bama Jauro dari biyu,Inna Mari guda Dari,sauran É—ari,aka ba Goggo Badejo guda talatin,sai Goggo Halira ita ma guda talatin,ya rage guda Arba'in,Malam mai rabon gado ya É—auki guda goma sha-biyar,ya rage ishirin da biyar,aka ba Inna Kande guda Goma,Inna Binta ma goma,ya rage biyar,aka ba Yabale guda É—aya,Dotti É—aya,yaran Baffa Sanda kenan,sai ÆŠan Fodiyo daya,Bakari daya,yaran Baffa Bube,
ÆŠayan daya rage kuwa za'a sai da a raba kudin kowa a bashi,
Tumakaima irin rabon da aka masu kenan wanda a ƙarshe Jauro ya tashi da guda goma.
Baffa Bube ne yace shi zai rike gadon Jauro har ya girma,shi kuma Baffa sanda yace sam bai yarda ba sai dai a raba kowa ya rike É—ari É—ari,in yaso in ya girma sai a bashi,in kuma bai yarda ba ya tattaro mai da Jauro da dukiyar shi duka shi zai iya rike su,
Ganin fitina na kokarin kara tashi ne yasa Inna Mari tace su raba kowa ya É—auki dari su rike mai kafin ya girma,
Sannan idan yayi sati a shiyan Binta yayi Sati a shiyan Kande,yan da aka tsayar da magana kenan,sannan yau zai fara ne da shiyan Binta,tunda dama jiya a dakin Inna Mari ya kwana tare da goggonnin shi,to suma yau zasu wuce....
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*13*
Kamar yanda suka tsara mashi haka suka barshi a shiyan Binta inda zai yi Sati É—aya,
Bayan wucewar Goggonnin shi ne ya koma dakin Inna Mari ya zauna,dan yaje shiyan su babu kowa kuma shiyan ma a kulle yake,
Da lokacin cin abincin rana yayi kuwa haɗa masu aka yi a babban kwanu shida su Dan Fodiyo,sai dai fa kafin yayi loma ɗaya sunyi uku,dan Innar su tace karasu bari ya cinye ya bar su,su dinga yin ƙaton loma,idan ya kusa karewa su buɗe hannu su kwashe duka,
To abinda ya faru kenan a lokacin da suke cin abinci,yanda kasan da Awaki yake cin abinci haka suka mai,domin kamar basu haÉ—iye na bakinsu suke saka wani,gashi dama abincin bai da yawa,koda ya duba kwano tuwo ya kafe tas,amma kwata_kwata loma huÉ—u ya yi,
Tsayawa yayi yana kallon su ya kalli kwanun,ga kuma katon tuwo a hannun su suna gutsura suna ci,suna mashi dariya,
Hannun ya mika "ɗan Allah ɗan Fodiyo danmin tuwonka ka ga ni ban ƙoshin ba"
"Ai ni ma ban ƙoshin ba,ka dauki kwanu ka kai inna ta kara mana"
Baicimusu ba kuwa ya dauki kwanu ya shiga daki inda Binta ke zaune,É—an rabewa yayi dan Allah ya gani yana matukar tsoron wannan matar,domin ko kaÉ—an bata mai ragi,
"Inna Binta ban koshi ba a ƙara min abinci"
Wani irin mugun kallo ta bishi dashi"tunda ubanka dake kabari ya kawo uwarka dake kabari ta zo ta dafa ba,ai dole kace baka koshi ba,to na waye kake son a baka,"
Kafin ma ta ƙara ɗaura mai wani zagi yayi waje da sauri ya ajiye kwanun wurin wanke-wanke,dakin Inna Mari ya shiga,a lokacin ita ma tana cin nata abincin,haka ya zauna a gefe yana kallon ta,sai da tace kusan rabi sannan tace zo ka ɗauka,ai kuwa jikin shi har rawa yake da farin ciki ya ɗauka "na gode inna"
Kallon shi tayi"ka gode me,je ka ajiye min abinci a can domin anjima shi zan ci "
Dan bata fuska yaro yayi "inna ba cewa kika yi na É—auka na ci ba?
" Ni ko me zai sa na dauki abincina na baka bayan kaci tare da yan'uwan ka"
"Inna ban koshi ba,yunwa nake ji"
"To ai ka ga matsalar kenen,shi yasa babu kyau ka sangarta ɗa da ci,saboda halin rayuwa,iyayenka suna ganin kai kaɗai ne a gaban su sun buɗe makarantar ciki da cin abinci yanzun gashi yanda lamari ya kasance,wa zai iya ci da kai,ni dai ba zan iya ɗaukar abinci na ina baka baka ba,dan ma kar ka saka rai a kan haka,a jiyemin kwanun tuwo na a can anjima shi zan ci nima dan ba gama abinci dare da wuri za'a yi ba,in ma taga dama tace ba tayin na daren,gara na ɓoye nawa duk yanda yama to"
Bai ce mata komai ba ya É—auki tuwon ya ajiye mata a gefe sannan ya fito,
Yana fito ya haÉ—u da Binta a tsakar gida,
Kallon ci tayi cikin harara wanda ta ya riga ya sani bata taba mai kallon arziki sai dai na harara ko yaushi "kai yan zun Jauro dan baka da kunya ni kake jira ka ci abinci na wanke maka kwanu,to baka isa ba,maza zo ka yi wanke-wanke kafin na canza maka kamanni,idan ka gama ka share tsakar gida,dan ni ba zan iya aiki kana zaune ina kallon ka ba kamar wani mara amfani"
Ba yanda ya iya cikin rawar jiki ya shiga tattara duk kayan da aka ci abinci har na kofar ɗakinta wanda anan ne yaga su Ɗan Fodiyo zaune a cikin dakin da ƙaton malmalan tuwo a gaba suna ci,
Bai ce komai ba dan ya fahimci ko ya roka ba samu zai ba,
Tunda yake bai taɓa yin wanke-wanke ba amma yana ganin yanda Innar shi ke yi,dan haka shima zama yayi ya fara wankewa a hankali,duk da haka wanke-wanken babba da yaro ba ɗaya ba,balle wanda bai taɓa ba ba,dan haka wasu sun wanku wasu basu wanku ba,a haka ya gama wanke-wanke,sannan ya fara shara wanda shima bai sharu da kyau ba,
Ai kuwa a kan wannan wanke-wanke da shara sai da ta zane shi sosai wai dan mugunta ne yasa yaki mata aiki da kyau,sannan tasa ya ƙara dibo ruwa tana tsaye akan shi tasa ya ƙara wanke wa,idan bai fita ba ta sakar mashi rankwashi,da haka ya gama da kuka da hawaye da majina,shara kuwa yana yi tana biye dashi da bulala a hannu,duk inda ya bar datti sai ta zauga mai tace ya koma ya share,da haka dai ya gama sharan,sannan ya lallaba ya bar cikin gidan,dan gani yake kamar kamar yana fita ya rabu da wannan bala'in na binta kenan sannan yana zuwa shiyan su zai tarar da Innar shi da kuma Baffan shi suna jiran shi,
Hakan ne yasa ya koma kofar shiyan su da aka kulle ya zauna,dan yata tura kofar taki buÉ—ewa,zama yayi ya fara kuka yana kiran sunan Mamar shi,dan bai san inda ta je ba,
Yana cikin haka ne har barci ya dauke shi,wanda bai jima ba yaji ana ta da shi,
Bude ido yayi ya kalli me tada shi,daya ne daga cikin yaran Malam Liman,
"Jauro Malam yace kazo lokacin sallah yayi sannan za'a shiga Islamiya idan an fito sallah"
Tashi yayi ya bi ya ban yaron suka je har gidan Liman,a zauren yaron ya ajiye shi ya wuce dan shirin dauro Alwallah,
Yana shiga ya gai da Malam sannan ya zauna a gefe,
Kallon yaron yayi cikin tausayawa domin maraici ba karya bane,dubi cikin kwanaki kalilan yanda ya zube ya lalace,yasan ladan dake tattare wurin renon maraye da kuma azaban dake tattare akan wanda ya azabtar dasu ko kuma wulakansu,koda kuwa kuka mutum ya saka su,
Kwanun abinci dake gefen shi ya jawo ya mika mashi,
"ÆŠauka kaci,idan ka gama ka zo ka same ni a masallaci"
Daukan kwanun yayi ya buÉ—e,lafiyayyen sakwara ce da miyar ganye,
Ai kuwa nan ya fara ci,hannu baka hannu kwarya,
Sai da yaji babu wurin zubawa sannan ya hakura ya ajiye sauran ya sha ruwa,
Yana fitowa ya dauki buta yayi alwalah ya shiga masallaci,in da har an tada sallah,
Suna idarwa kuma aka fara karatun yamma,wanda sai ƙarfe shida suka tashi,
Har ya fito zai koma gida,sai kuma ya koma in da Malam ke zaune yana ƙoƙarin tashi,zama yayi kusa dashi,
"Malam"ya kira sunan shi,
Shima amsawa yayi yana kallon shi,
" Malam ina Inna na da Baffa na suka je,naga shiyanmu a kulle babu kowa,kuma idan naje ina ta bugawa babu me zuwa ya buÉ—e min,sannan Inna Mari tace sai dai in dinga kwana a shiyan su É—an Fodiyo,ni yaushe ne su Inna da Baffa zasu dawo,ina son in gan su,ko kuma ka kai ni in da suke"
Jikin shi gaba É—aya yayi sanyi da kalaman yaron,dole ne ya faÉ—a mashi gaskiyar menene mutuwa ta yanda zai iya fuskantar gaskiyar duniya da kuma rayuwa,domin yasan ta yanda zai gina rayuwar shi........
*Nagode sosai da Addu'ar ku na ji sauki sosai yanzun kam,sannan masu jiran YAR TSANAR ZINARI zasu samu zuwa anjima insha Allah*
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*14*
Dafa kafadarshi yayi tare da sakar mashi lallausar murmushi,sannan ya kira sunan shi,
"Allah shi ya halicci komai da komai da kake gani a nan duniya,da wanda idon ka ke iya gani da wanda idanun ka ba su iya gani,mutum da Aljani,ice,sama da ƙasa,tsaunuka,rana da wata,zafi da sanyi,iskar da muke shaka,ruwa,abubuwan dake rayuwa a cikin ruwa,Jauro ina nufin komai da komai da kake gani,kuma shine yake amsar su a duk lokacin da yaso,domin ko wani abu da ka gani a duniya kome dadewar shi a duniya yana da nashi iyakar da Allah ya dibar mashi,haka ma mutum yake,duk wanda ka ga ya mutu to ya cika iya wa'adin zaman da Allah ya ɗibar mashi ne a duniya,kuma wanda ya mutu baya taɓa dawowa,"
"Malam yan zun Inna da Baffa ba zasu dawo ba kenen?
" Ba zasu dawo ba Jauro,sai dai abu É—aya zaka masu wanda zai sa su farin ciki,su san cewa kana son su sosai kana kuma kewar su"
"Me zan yi,?
" Duk abunda zaka yi kada ka bari sallah ya wuce ka,idan ka yi sallah ka ɗaga hannu ka masu Addu'a,domin Allah mai karɓar Addu'ar bayinsa ne,idan ka masu Addu'ar zai isa gare su,kuma zasu ji daɗi su san cewa lallai Jauro na matukar son su,sai kuma ka dage kayi karatu sosai na Boko dana Islamiya,tunda naga kana da son karatun Boko,gashi kwana biyu ma ka ba je ba,gobe idan Allah ya kai mu ka shirya kabi Moha ka tafi makaranta,ina son in ga ka cika burinka,ka kuma cika burin iyayen ka,kaji Jauro ka dage ka mai da hankali,karka damu da komai da za'a yi ko za'a ce"
Jinjina kai yayi duk da a lokacin ya fahimce wasu daga cikin abinda Malam liman ke faÉ—a wasu kuma bai fahintaba a wannan lokacin amma ya tabbatar yasa kudirinsa akan karatu.
Tun daga wannan lokacin ya cire komai a ran shi yasa ma ran shi lallai cewa shi maraya ne wanda bashi da uwa bashi da uba,ba kuma shida dangi,shi kaɗai ke son kanshi,sai dai kamar yanda Malam Liman yace mai Babu maraya sai rago,to lallai ba zai zama raggo ba,zai yi ilimi ta yanda mutane zasu so shi zasu kuma girmama shi,zai zama abinda yake son ya zama da taimakon Allah,wannan shine ƙudirin Yaro mai shekaru bakwai a wannan lokacin,
Tun daga sannan ya mai da rayuwar shi tashi shi daya,idan gari ya waye shi zai fito yayi wanke-wanken kwanukan da aka bata ya share tsakar gida duk sanyi duk iska,domin in bai tashi ba ma da bulala Inna Binta ke tada shi,idan kuma lokacin sanyi ne da ruwan randa zata tada shi,shi yasa tunkafin ma ta tashi barci yake kammala mata aikin da zai yi,baya tsayawa ya jira sai an bashi abin karin safe sannan ya tafe makaranta domin yasan ko ya tsaya ba lallai ya samu ba,ko ya samu sai kusan goma na safe,shi yasa ya gwammace ya wuce,in ya dawo ya samu to,in bai samu ba sai tafi gidan su Moha ko Malam Liman a can kam baya rasa abinda zai ci.
A hankali rayuwa ke tafiya abubuwa na sauyawa da dama, amma banda gidan su Jauro domin kamar dai yanda yake tun 1999,haka yake babu abinda ya canja a wannan gidan sai ma abinda ya karu,
Domin kuwa Inna Binta ta ƙara haihuwa,har ya'ya uku,kamar yanda ita ma Inna Kande ta ƙara har yara biyu,kuma ita ma idan lokacin kwanan Jauro yayi a shiyan ta,to da ita ma ta samu dan aiki,domin ita ba karamar kazama bace,shara wanke-wanke,har ta da wanki shi ke masu,ko da jika jika ne ita be dame ta ba,kuma a haka yake daurewa yake yin duk abinda aka saka shi,domin shi ba yaro bane mai son jiki,to ina ma yaga ta son jiki,wa zai ma son jiki.
Batun makaranta kuwa cikin ikon Allah shi ke daukar na ɗaya,domin Jauro irin yaran nan ne da ake kira gifted,in da magana ne akan Mathematic to ba'a magana domin ko malaman su suna mamakin yaron,domin yaron ga shi dai dan ƙauye amma Allah ya bashi,
Moha ya riga shi kammala primary har ma ya shiga wata government school anan wanda baida nisa da nan É—in,yana primary five suka tafi gasa irin wanda ake kai yara,cikin ikon Allah shi yazo na daya,wanda jin daÉ—in hakan ne yasa wani mutum wanda ya ji an kira da suna Alhaji Abubakar Imam,shi ya É—auki nauyin makarantar Jauro tun daga Jis one har S.S three kuma a makarantar kuÉ—i,domin shima ya nada nashi makarantar kuma babba ce ta masu kudi a wannan lokacin,
Wannan labarin ba karamin daÉ—i abin yama Malam Liman ba,Allah sarki har da hawayen shi,
Ta ɓangaren Islamiya kuma babu laifi domin har yakai izifi goma sha biyar,.
A haka rayuwa ta mike kuma tana tafiya da daÉ—i da kuma babu daÉ—i,
Shigar Jauro babban makaranta ya saka rayuwar shi sauyawa ta bangarori da dama,ya samu daukaka a cikin É—alibai da kuma malamai,ba dan komai ba sai dan ilimin shi,sai dai.......
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*15*
*Bayan shekara goma*
A cikin waɗannan shekarun da suka wuce abubuwa da dama sun faru ko ince suna kan faruwa,domin gida ya ƙara cika da yaya,da kuma samari,
Ta bangaren halin mutanen gidan kuwa babu abinda ya canja,domin kuwa suna nan a yanda suke,sai ma abin da yaci gaba,
Domin kuwa yanzun yan gidan su Baffa Sanda basu isa suyi magana da koda yaro ƙarami bane in dai dan Baffa Bube ne,babu mutunci a tsakanin nin su kamar yanda babu ragi,
Baffa Bube dai shikam Allah yayi ya kara Aure,hmmm,sai dai ranar anga hauka tuburan a cikin gidan,
Sai dai shi mai gidan yace bata isa ta hana shi abinda yake so ba,kuma Amarya dole ta zauna,
Ganin da gaske yake ne yasa ta tattara kayanta ta bar gidan ta goma rugar su,wai tayi yaji,
Wannan yajin da taji ba ta san ba karamin dadi yama mutanen wannan gidan ba,
Ita a nata tunanin shine za'a biyo ta a bata haƙuri a kuma neme ta koma,ita kuma a lokacin zata wulakanta su,
Abinda bata sani ba shine mutane da yawa a gidan ba su fatan ta dawo,dan haka kowa yayi banza da lamarin ta,aka cigaba da shagalin biki,
Wasa_wasa sai da Amarya tayi shekara daya lokacin ta haihu tana da danyen goyo,sai gashi da rana tsaka Inna Binta ta tattaro kayanta ta dawo da kanta ba tare a anje biko ba,
Wanda har yau Inna Mari na mata gori a kan haka,ta dawo gidan miji ba tare da yaje biko ba,
Wannan dawowar da tayi,ta dawo ne da kwandunan bala'i a wannan lokacin,domin tsakar gidan Baffa Bube sai da ya kusan gagaran mutane shiga saboda kullun cikin yaƙi suke ita da Amaryar shi mai sune Hauwa,
Yanda kasan Æ´an daba haka suke,domin kuwa da zaran Inna Binta ta dauko Icce,Hauwa zata dauki katon muciya,ko ita ma ta dauki Faskare,
Duk sun lalace sun zama kamar zararru,
Su kenan kullum cikin zuwa asibiti dinkin goshi,
Gaba É—aya ta hana Hauwa zaman lafiya a gidan,
Wani faÉ—a da suka yi wanda shine na karshe wanda Æ´an uwan Hauwa suka dauke tare da kwashe kayan ta,wai ba zasu bari haka kurin a kashe masu yar uwa ba,ai kuma suka tafi da ita har da danta,dan cewa suka yi ba zasu bar matarsa Binta ta kashe shi ba,duk bala'in Baffa Bube dole ya bari suka tafi dashi,domin gaba da gabanta ne,
Abinda ya faru kuwa shine,
Akan abinci ne faÉ—a ya haÉ—a su,wanda dama ita Binta tana jiraye da ita,dan haka kuwa ta shammaceta ta saka muciya ta shemeta da shi,ai kuwa ta suma,domin ta bugu,kamar wasa ansa ruwa amma taki farkawa,wanda sai da aka haÉ—a da Asibiti,kwananta biyu sannan ta farfaÉ—o,
Ganin ta farfado ne yasa yan uwanta suka yi hamdala,
Daga nan suka dauki zuga su shida,uku yanninta mata uku matan yanninta maza,suka tafi har Rugansu Jauro,
Kaman abin arziki suka ce sun zo daukar kayan Hauwa ne,babu wanda ya hana su tunda dama ita Inna Mari ba amfani gareta va,kuma Baffa Bube bai nan,dan shi kam yana son matar shi,
Ita kuma Binta tana ganin haka ta hau shewa da cika bakin ta kori kishiya,har da kiÉ—a kwarya a tsakar gida,
Hmmm,bata san dama da biyu suka zo ba,dan kuwa a ranar Binta ta yaba wa aya zakin sa,
Domin babu zato babu tsammani suka rufe ta da duka ta ko ina,yanda ta nuna ma yar uwar su rashin imani haka suka mata,
Domin sai da suka mata shegen duka sannan suka karya mata hannu daya da ƙafa ɗaya, suka bar ta nan kwance a sume,domin bata san in da kanta yake ba,
Dukan mutum shida ba wasa ba,
Makota naji ba wanda yayi ma tunanin ceton ta,
Suna gama mata wannan É—anyen aikin suka kwashe kayan Hauwa tas suka bar gidan,
Ai kuwa wannan ciyon sai da ta shekara tana jinya kariya,domin abin bai zo mata da sauƙi ba,
Wannan kenan.
A lokacin Jauro yana shekaru goma sha bakwai a duniya,ya zama sauri sosai,domin yanzun duk abinda za'a mai dole a rage domin dai ƙarfin shi ya kawo,ta ɓangaren karatu kuwa ya sauke Kur'ani da jimawa wanda hakan ne yasa Malam liman ya saka shi hardar Kur'ani,kuma cikin nasara ya hardace,
A Boko kuwa sai dai san barka,domin kuwa a wani gasa da makarantar su da suka je a Abuja ne ya ciyo masu na daya,wanda har a gidan TV an haska gasar,
Anan Gamnati ta bashi scholarship na wani babban University a China in da zai yi karatun shekara huÉ—u,
Wannan ci-gaban da ya samu a cikin gidan ba wanda ya damu dashi domin gani suke kamar aikin banza kawai zai tafi yi,
Alhaji Abubakar Imam shi ne wanda ya tsaya mashi,yake kuma taimaka mashi akan batun tafiyar,domin kuwa shima babban danshi na can,a can yake karatu,tun last year,
Dama kuma dashi yake son ya haÉ—a su,
Acan Ruga kuwa,zaune suke a ƙofar gidan su Moha,su uku,
Yana rike da wani dan littafi ƙarami na Turanci a hannun shi,suna hira yana dubawa lokaci lokaci,
Sai su kuma da suke kallo a wayar Moha din shida yaron Malam Liman mai suna Musa,
"Wai kai yaushe zaka siya waya ne Jauro,gashi tafiyarka bai wuce saura sati É—aya ba" Cewar Moha.
"Kyale É—an iska ko da me yake son ya dinga kiranmu dashi oho,ba dai nufinka inka tafi shikenan sai ka dawo ba kuma,kar ka manta shekara huÉ—u suke ce,shekara huÉ—u ba kwana huÉ—u ba" Musa ya faÉ—a.
Rufe littafin dake hannun shi yayi"ni ba zan iya riƙe abin ƴan iska ba,domin duk masu riƙe waya yan iska ne,kuma basu san amfanin kuɗi ba da zasu ɓata wurin sayan wannan abun"
Zaro ido Moha yayi"ba dai mune Æ´an iska ba Jauro?
"Ka rantse babu abubuwan banza a cikin wannan wayar,karka manta Malam abinda na kamaka kana kallo a cikinta shekaran jiya,in ma aure kake so ai Gara ka yi magana kawai ayi maka"
ÆŠan dariya yayi yana shafa keya dan yasan bai da gaskiya,"to amma duk da haka ya kamata ka siya waya ko dan Æ´an uwa"
Kallon mamaki yake mai"Æ´an uwa?Æ´an uwa fa kace?ni ina da wasu Æ´an uwan da zan kira ne ko su kira ni,?ai in dai ma zan siya waya sai dan mutum uku,dan in ji muryar Malam liman,sai kai sai kuma Alhaji,yana nufin Alhaji Abubakar Imam,
Dan ku kawai zan iya siyan waya,to ku din ma ba zan siya ba dan ban iya amfani da ita ba,amma na dinga aron na É—an Alhaji ina kira in ji muryar ku"
Tsaki Musa ya ja "ɗan ƙauye dai duk yanda akayi dashi sai ya nuna halin shi,ɗan Allah Jauro kar ka bada mu,yanzun fa babban yaro zaka koma,ka zama ɗan gayu,amma ka tsaya kana magana kamar irin wanda bai taɓa shiga aji ba,kai ko dan irin sha'awan nan ba kaji,kalli yaran makarantar ku,kowa ka gani da babban wayar shi yana yanga,daga mata har maza amma kai kullun cikin riƙe takarda kake,"
"Ai duk yan iska ne,ni kaga kar ka ishe ni da batun waya,domin ni a nawa ganin duk masu rike waya basu da aikin yi,na biyu kuma iskanci suke kallo a waya kamar dai ku"
"Oh mun shiga uku da Jauro,wai kai an ce maka duka ne aka taru aka zama daya,yanzun fa zamani ya canja,kuma zaka ce na faÉ—a maka da kanka zaka zo ka siya waya,"
Mikewa yayi tsaye "Allah ya raba ni,ni dai ku shirya min tsaraba kunsan ran sati ne rafiyar mu"
"Ni dai me kake son in siya maka" Cewar Musa.
"Naga Innar ka tana shanya kanzon tuwo,shi zaka karba min,sai ka haÉ—a min Sugar da Kuli-kuli,kai kuma Moha Garin Rogo da suyayyen gyaÉ—a,sai kwalin Lipton,sauran siyayyan in naje can na karasa,"
Baki buÉ—e Moha ke kallon shi,yayin da ya juya ya wuce abin shi yana ce masu sai sun haÉ—u anjima a wurin Malam liman,
Juyo da kallon shi gun Musa yayi,tare da nuna Jauro da yatsa"anya yana da hankali kuwa?
"Me yayi? Domin shi Musa bai yi karatu ba.
"China ne zai je da kanzon tuwo,har da gari,kodai ya É—auka boarding school za shi ne?
" Au ba'a zuwa da su?
Tsaki ya ja shima ya tashi tare da bar mashi wurin dan ba zai iya da wannan haukan nasu ba,tsakanin Jauro da Musa bai masan wanda yafi wani hauka ba.....
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*16*
*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuÉ—i,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda É—aya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*
A ranar da zai bar Minna zuwa Abuja ne ya je ya same Baffa Bube ya tsugunna a gaban shi"Baffa zan tafi makaranta "
Kallon shi yayi daga sama har kasa,takalmi silifas ne a ƙafar shi,sai wasu kodaddun kaya riga da wando na yadi a jikin shi,duk yayi wani kura_kura dashi yanda kasan Almajirin ƙauye,ko ɗan mai bai shafaba,to ina ma ya ganshi balle ya shafa,
Bushewa yayi da dariya harda nuna shi"yanzun kai Jauro a haka kake faÉ—in zaka kasar turawa karatu,ni kan anya mutumin nan ba dan yankan kai ba ne?in ba haka ba ta yaya zai ce zai kai ka kasar turawa wanda sai an shiga jirgi,sannan ace bai amsa ko sisi ba daga wurin mu,?
Shiru yayi kawai yana kallon kanin mahaifin na shi,
"To ba damuwa tashi ka tafi,idan kana da rabon dawowa Allah ya sadamu da Alkhairi,idan kuma Allah bai yi zamu kara ganin ka ba,to ka gaida mahaifinka sai mun iso,ka ce ya ajiye mana wuri zama mai kyau kar ya bari a cike wuri"
Yama rasa mai zai ce mashi,dan haka tashi yayi kawai ya fito tare da shiga shiyan Baffa Sanda,in da yake zaune shi kuma yana wasa Addan shi,
Tsugunnawa yayi shi ma a gaban shi "Baffa zan tafi makarantaba sai dai Allah ya dawo da mu"
Bai bar abinda yake ba sai kallon shi da yayi"ina ne ma kace min zaka karatun duniya "
"Baffa China na"
"Ohh,to kai dai ka san su,kai da waye zaka tafi?
" Ni kaÉ—ai ne,amma akwai yaron Alhaji a can tare dashi za mu yi karatun"
"To madallah,idan dai kaje ka ga zasu cuceka ka gudo ka dawo gida,kar ka yarda su sayar da kai,dan wani aboki na ya faÉ—a min idan sun ga ba kaÉ—a wayau,tsaf zasu siyeka su baka kuÉ—in ka cinye,daga baya su zo su tafi da kai su yanka bayan ka gama tara maiko,
Dan haka kayi hankali dasu,banda kallon mata masu tafiya tsirara jauro,dan kana iya makancewa"
Jikin shi ne yayi sanyi da huÉ—ubar Baffan na shi,to yanzun idan yaje aka siye shi aka bashi kudin shi ya cinye fa,gaskiya da an samu matsala,dan aradu ba zai yarda yana ji yana gani ya tsaya a yanka shiba,gashi yaji ance harda Naman gwangwani suke yi,
Wani tsoro ne ya kama shi,tare da haÉ—iye yawon tsoro,shi tsoro ma ya kama shi,sai dai kuma ba halin yace ya fasa"insha Allah Baffa,"
Ajiye Addan yayi a gefe ya saka hannu a Aljihu ya ciro Æ´an dubu dai_daya a Aljihun shi tare da wasu canji,
Jujjuya kuÉ—in yayi,ya buÉ—e su,sai da ya kirga su da kyau dubu Arba'in da huÉ—u ne da dari biyar,sai canjin Naira Saba'in a sama wanda suke Naira ishirin_ishirin guda uku naira goma guda É—aya,
Canjin saman ya mika mashi wato Naira saba'in ɗin tare da maida sauran kuɗin Aljihun shi"karɓi wannan kasha ruwa a hanya"
Amsa yayi yana É—an bata fuska,dan ya É—auka zai bashi ko da dubu daya ne"na gode Baffa,"yana gama faÉ—ar haka ya tashi ya wuce,
Babu wanda ya mai rakiya koda nan da kofar gida ne,
Sai dai Moha wanda shi ya kai shi har cikin gari gidan Alhaji Abubakar,in da yake jira sai yaga wucewar su Abuja kafin ya koma ruga
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*17*
*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuÉ—i,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda É—aya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*
Suna isa gidan har cikin falon Alhaji Abubakar Imam suka shiga da jagoran É—an shi,
Cikin girmamawa suka gaida shi suna zama a ƙasa,
Amsawa yayi yana ƙare masu kallo,
Yasan ko yace su zauna saman kushin ba zama zasu yi ba,wayar shi ya É—auka yayi kira,wanda ko mintina biyar ba ayi ba sai ga É—aya daga cikin yaran shi ya shigo,
Nuna mashi Jauro yayi"ka bashi wasu kayan ya canja,kafin mu wuce"
"Ok Dady" Ya bashi amsa,tare da juyowa wurin Jauro"taso mu je"
Tashi yayi ya bi bayan shi suka fita,
Dakin shi ya kai shi ya fito mashi da wasu riga da wando masu kyau,harma da takalmi,cikin farin ciki ya amsa kayan ya saka,irin wanda bai taba tunanin zai saka su nan kusa ba,
Ya saka kaya kam,sai dai maganar gaskiya shine kayan basu wani yi mashi kyau ba,saboda kai da ka ganshi ba sai an faÉ—a maka ba kasan wannan duk yanda aka yi daga Ruga ya fito,shi ko dan irin wayewar nan da mutum zai nuna irin yayi karatu,to babu shi a tare da Jauro,
Yana fitowa kallon shi É—an Alhajin yayi tare da tabe baki,ba laifi kam,ba kamar dazu ba,kyara mashi kwalan riga yayi,sannan ya ja ahi suka koma falon inda su Moha suke,
Koda suka shiga Alhajin baya falon sai Moha da aka kawo ma lafiyayyen abinci,ya ji nama manya-manya bai ciba yana jira Jauro ya zo suci,
Suna shigowa kallon Jauron yayi yana sakin murmushi,"kai Jauro kayi kyau sosai,ka zama É—an gaye,"
Shafa rigar yayi yana washe baki "baka ga ma takalmin ba,wani irin dashi,kalan na ƴan ƙwallo"
"Gaskiya kaji daÉ—i sosai,matso mu ci abinci,gashi da zafin shi,zo ka gani"
Matsowa yayi ya zauna yana kallon plate din dake gabansu,
Nan suka zauna suka kwashi lafiyayyen abinci,
Suna kammalawa yaron daya bashi kaya ne yazo ya kira shi wai ya fito zasu tafi in ji Alhaji,
Sai da yaga zasu rabu da Moha ne ya fara hawaye,wanda sai da ya saka Moha din shima kuka,sai yake ganin kamar ba zai dowo ba,
Sai da Alhaji yayi aikin lallashi kafin su hakura sannan ya shiga mota suka kama hanya,
Har suka isa Abuja ko gyangyaÉ—a bai yi ba,yana kalle_kallen hanya,
Sai da suka fara tsayawa a Hotel kafin zuwa ƙarfe huɗu su nufi Airport,
Tashin hankali,domin kuwa sai da aka zo shiga jirgi yace bai san wannan ba,dan shi kam bai ga wurin shiga ba,balle ya shiga ya jeho shi kasa ya mutu,ba da shiba.
Da kyar da lallashi da nasiha sannan Alhaji Abubakar tare da ma'aikatan jirgi suka samu suka shawo kanshi sannan ya amince,ba dan san ranshi ba,sai dan kawai yayi imani idan har ya mutu yau to lokacin shi ne yayi,kuma karin firgicin nashi ashe shi kaÉ—ai zai je ba tare da Alhaji Abubakar ba,wai shi sai daga baya zai zo,idan ya je zai haÉ—u da ÆŠan Alhaji da ke can,
Masu aikin cikin jirgin wanda aka ba Alhakin kula dashi ne su suka sanya mashi belt din jirgi,su kuma suke ta ɗan kula dashi tare da kwantar mashi da hankali har zuwa sanda jirgin su ya sauka a China wuraren ƙarfe takwas na dare ne a garen.
Daya daga cikin ma'aikatan jirgin da aka ba number Sadik É—an Alhaji shi ya kira shi ya shaida masu sun sauka ya zo ya dauki É—an uwansa,nan ya sanar dashi ai yana ma a cikin Airport É—in,
Tare da su ka fito in da anan suka hadu da wani matashin saurayi tsaye yana jiran su a wurin tarbon baki,dan haka yana ganin su da sauri ya zo ya rungume Jauro dan Dady ya turo mashi hoton shi,
Godiya yama mutumin kafin ya fara dariya yana amsar jakkan dake hannun shi"barka da zuwa kasar China Abokina"
Dan sanyi yaji jin ya mashi magana da yaren Hausa,"kai a gaskiya har naji daÉ—i da na samu mai jin yare na,"
Dariya ya kuma yi"ai ina jin yaren ka sosai tunda mahaifina Bahaushe ne,kaga taho mu shiga mota,ma karasa hiran a gida"
Shi ya buÉ—e mashi gidan gaba ya shiga kafin ya maida kofar ya kulle sannan ya zagaya ya shiga mazaunin Direba ya ja muto,
Shi dai kalle_kallen shi kawai yake yana baza ido yana kallen mutane masu wucewa,har suka isa wata unguwa mai kyau wanda tsarin gerin gidajen ma abin kallo ne,
Har dakin daya tana da domin shi ya kaishi,tare da nuna mashi banÉ—aki da wurin wanka sannan ya fito"kayi wanka ka canja kaya sai kazo mu ci abinci"
Amsa mashi yayi yana komawa banÉ—akin,dan ba karamin kashi yake ji ba tun cikin jirgi,
To fa,tsayawa yayi yana karewa lafiyayyen bayin kallo,tare da shiga duniyar nazari,
Dube_dube ya fara yi ko ta ina zai ga in da ake tsugunnawa,dan bayin a share yake tas,har wani kyalli yake,ko ina fari kamar daki,
Idanun shi ne suka sauka akan wani dan net na roba,wanda idan ruwa ya zube a kasa yake bi ta wurin ya wuce,idan kuma datti yayi yawa a wurin ruwa baya wucewa,sai an cire roban an wanke,
Dan haka ganin kaman dan rami ne a wurin yasa ya saka hannu ya cire roban yana leken ramin"kai gaskiya matsugunnin nan yayi karami,"ya faÉ—a yana kyara saitin tsugunnin shi a wurin, cikin kwanciyar hankali ya gama juye abinda ke cikin shi a wurin,
Sai da ya kammala sannan ya dauki butan daya ciki da ruwa dama ya tsarkake jikin shi,
Sauran ruwan da yayi tsarki da shine ya shiga juyewa a wurin,sai dai gani yayi abu ko motsi bai yi ba,
"To shi kuma ta yaya zan saka ya wuce ce" Da sauri kuma ya juya tare da daukar bokitin wanka ya kunna panpo,sai da ya cika da ruwa ya jawo ya juye a wirin,sai dai a maimakon yaga ya wuce,sai gani yayi yama kara tasowa sama,bai da alamun sauka,
Kara cika wani bokitin yayi ya juye,nan ma shiru babu labarin wucewar kashi,
Shiru yayi tare da Daura hannayen shi duka biyu saman Kwankwaso yana tunanin ta yaya zai saka wannan kashin ya wuce ta É—an wannan kwararon....
*Fans sai ku ba Jauro shawara*
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*18*
*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuÉ—i,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda É—aya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*
Shikam yasan ba shida zaɓi daya wuce yaje ya nasar da ɗan Alhaji ya zo ya taimaka mashi su saka wannan najasar wucewa,dan haka fitowa yayi daga cikin daki ya shiga ƙwanƙwasa mashi kofar dakin shi,
Fitowa yayi "lafiya Jauro,kana buƙatar wani abu ne?
" ÆŠan Alhaji nayi bahaya kuma yaki tafiya sai yawo yake saman ruwa"
"To muje na nuna maka yanda zaka yi"
Bin bayan shi yayi suka shiga cikin dakin shi,tun daga shiga ban É—akin wari ya fara busu shi,yana buÉ—e bayin ya dawo baya da sauri yana dariya tare da jawo kofar,
"Ai Jauro yaushe aka ce maka anan ake bahayar,"
"To yanzun ya zan yi É—an Alhaji?dan shi sam tunanin shi bai bashi cewa akwai wani abu a bayin ba wanda zai iya tsugunnawa a kai ba,dan shi kam tunda yake a rayuwar shi bai taba ganin ban É—aki haka ba.
" Zo muje bandaki na na nuna maka yanda zaka gyara naka"
Bin bayan shi yayi suka koma nashi dakin har banɗaki,nan ya shiga nuna mai asalin inda ake kashi da yanda ake kora ruwa ya wuce da yanda zai wanke bandakin da kuma yanda zai yi amfani da kayan wankewar dake jere acikin bayin har da ma na wanka,"yanzun kaje ka duba bayan ƙofar ka zaka ga abin shara da kuma abin kwashewa sai ka yi amfani dasu ka kyara bayin idan ka gama sai ka yi wanka"
"To na gode ÆŠan Alhaji"
Fita yayi daga É—akin ya koma nashi,yanda ya nuna mashi kuwa haka yayi,sosai ya wanke bayin ya kuma buÉ—e window bayan,yana kammalawa yayi wanka sannan ya canja kaya,
A washegari da taimakon Ɗan Alhaji ya kammala komai na makarantar,sannan suka bashi umurnin fara daukar darasi a kowani lokacin a kuma bangaren daya zaɓa wato Pharmacy,
Ba karamin farin ciki yayi ba,
Sosai ya mai da hankalin shi akan karatun shi,da yake shi din mutum ne me ƙwaƙwalwa yasa komai yake zuwa mashi da sauƙi,
Sai dai ta bangaren abinci wanda da farko ya so ya É—an samu matsala saboda yawan ciye-ciye wanda yake jawo mashi zawo,sai da ÆŠan Alhaji yayi da gaske kafin ya fara sassauta ma cikin shi,
Rayuwar shi a wannan kasar ba karamin daÉ—i yake mai ba,domin babu abinda yake Missing daga gida ko mutanen gida,
Sai dai lokaci-lokaci suna gaisawa da Alhaji Abubakar,
Sai da yayi wata biyu kafin dan dole ÆŠan Alhaji ya saka ya siya waya,wanda sai da kyar sannan ya iya sanin ma yanda ake amfani da ita,dan ko da ma idan sunyi waya da Alhaji Abubakar bai san ma ta yanda zai kashe kira ba,
Da wannan sabuwar wayar ne yasa Alhaji Abubakar ya turo mashi number Moha,suka yi Vedio call harda ma Malam Liman,
Da Moha ya buƙace ko ya kaima ƴan gidansu su gaisa ne,sai cewa yayi a'a ya bar su,dan yasan ko an kai masu ba abin arziƙi zasu faɗa mashi ba,to aciki wama zai ce aba.
A hankali rayuwar shi ke tafiya a wannan ƙasar cikin nasara yayin da kwanaki ke tafiya zuwa shekaru,yana aji uku ne ɗan Alhaji ya kammala nashi karatun ya dawo gida,wanda da kyar suka rabu a wannan ranar dan ba karamin shakuwa suka yi ba,
Dama kuma tun É—an Alhaji na nan suke kasuwanci wanda suke turo kaya Nijeriya ana sai da masu,kuma yana aiki a wani babban shago wanda ake biyan shi,
Da wannan kuɗin ne ya biya ma kanshi kudin shiga wata makaranta a England in da anan ya zaɓa domin yin master's degree din shi,
Kuma Alhaji Abubakar bai hana shi ba É—an ba karamin Alfahari yake da yaron ba,ya dauke shi tamkar É—an shi,
Rayuwar shi a England ne ya so ya sauya,
Haduwar shi da wata yarinya mai suna Jesica,ita ta fara buÉ—e mai ido da kananun romance,wanda daga baya idanun shi suka buÉ—e,
Sai dai in da Allah ya taimaka shine bai taɓa zina ba,duk yanda yakai ga romancing mace sai dai a tsaya anan,
Yayi Æ´an mata kala-kala wan da shi kanshi bai sai iyakarsu ba,
Jauro mutum ne mai matukar wayau sosai,wanda duk wayou mace bata isa ta ci kuÉ—in shi ba,duk wani karairaya da zata mai,sai dai yace wani dare ne jemage bai gani ba,sai kuma idan shi yayi niyar baki,
Ko da ya kammala karatun shi a England bai dawo gida ba,wata makarantar ya nima a Saudiya wacce ita wannan ta islamiya ce kuma karatun shekara biyu ne,hakan yasa ya karɓi aikin makarantar su ta dauke shi a England din,sai dai zai masu aiki ne a Branch din su dake Saudiyya,
Zaman shi Saudiya yasa ya kara samun ilimin addini sosai,tare da shiriya,ya zama wani ustadz dashi,
Duk tsayin shekarun da ya kwashe yana yawo a kasashe bai wuce a cikin wata huÉ—u yayi waya da su Baffa sau biyu ba,
Amma Malam Liman kuwa har yasa an rushe gidan ahi an yi mai ginin zamani ba tare da ya bari mutanen gidansu sun sani ba,haka ma Moha yayi aure tun tuni domin har yana da Æ´a,ba karamin Alkhairi yake samu a hannun Jauro ba ban bai manta dasu ba.
Wasa_wasa sai da Jauro ya share shakara takwas a kasar waje,hudu a China biyu a England,biyu a Saudiyya,
Ya tafi yana da shakara goma sha bakwai ya dawo yana da shekara ishirin da biyar,
Ko da zai dawo sai da ya fara bin jirgin da zai sauka Dubai daga nan ya hau na Ethiopia,sai kuma wanda zai sauka a Abuja,sai da yayi kwana biyu a Abuja kafin ya shigo Minna domin a kwai wasu takardun da yayi Submitting,
Ba karamin murna Alhaji Abubakar Imam yayi ba da ganin yanda yaron ya kara jirma da wayau,duk da lokaci lokaci yana kai mai ziyara,
Sai dai kusan ta ɓangaren saka kaya babu abinda ya canja dan gane dashi,
Baya son cire kuÉ—i ya siya kaya masu kyau na fitar raini ya saka,ya fi gane ya ta saka kaya kamar wanda ba shida shi,Alhalin kuÉ—in dake cikin asusun bankin shi Allah kaÉ—ai yasan yawan su,
Ko da zai shiga ruga bai je masu da wani kayan karya irin na azo a gani ba,dan wallahi yasan halin mutanen su,
Tunda yana jin labarin komai a bakin wadanda yake waya dasu,
Yayan Baffannin shi duk sun girma sun zama samari manya dasu,dan Yabbale da É—an Fodiyo tuni sunyi aure har da yara,
Amma sai dai abin mamaki babu abin daya canja dangane da zaman mutanen gidan,sai karo wulakanci da suka yi,
Dan yanzun Ya'yan Baffa Sanda basu isa su bi ta gonar Baffa Bube ba su wuce,kamar yanda shima ya'yan shi basu isa subi ta cikin gonaki Baffa Sanda ba.
Inna Mari tsufa ya ƙara kamata sosai,sai dai in da Allah ya taimaka kunsan jikin Fulani da kyau,tunda yawanci da danyen madara suke fara karin safe,
Basu wani damu da dawowar shi ba sai ma cewa da suke wai ya gaji da yawon duniyar da ya tafi ya dawo,
Su Moha ne da Æ´an gidan su Malam Liman kawai suka yi farin cikin ganin shi,wanda Malam Liman harda hawayen daÉ—i,
Kwanan shi biyu da dawowa ya samu kira daga Abuja wanda yasa dole ya tattara yatafi,
In da ya samu labari mai daÉ—i,a kan ya samu aiki a wani babban general Hospital na Gwagwalada,sun bashi babban matsayi a Lab din,
Sai kuma aikin safaran Condom wanda wannan contract ne daga World Health Organization (WHO) ya samu,
Sannan daga baya kuma ya fara aiki a nan general Hospital Minna,
In takai ce maku masu karatu,a shakara É—ayan da dawowar Jauro,ya nada manyan gidan kifi wanda kifi kawai ake kiyo da kaji masu zaman kansu har guda biyu anan cikin garin Minna,sai É—aya a Abuja,
Jauro nada Babban Pharmacy wanda babu abin da ake siyarwa a ciki banda magunguna,ma'aikatan da ke aiki a wurin sunkai mutun goma da yan safe daban yan yamma daban,
Yana da daya a Kaduna.
Sai kuma mashina da yake rabawa matasa haya wanda wannan aikin ya bar ma É—an Alhaji ne,shi dai nashi sai dai yayi order,gashi ko wani wata yana karbar Albashi mai matukar tsoka daga gwamnati,
A taikaice masu karatu jauro yana da kudin da shi kan shi bai san yanda zai yi dasu ba,
Abinda zai baka mamaki shine zaman da yake yi a nan cikin gari ba zaman aiki bane kawai domin Jauro harda noma yake yi,idan damuna ta sauka,ta can cikin unguwar ya siya wani tafkeken fili anan yake noma shida ma'aikatan da ya dauki haya,
Shi bai yarda da wani abuba wai shi rayuwar karya,inaaa ba dashi ba,ya sha wahala ya tara kuÉ—i sannan ya ta kashewa,gani yake asara ne,
Jauro yayi Dating Æ´an mata da yawa dawowar shi,sai dai makonshi ke sa su rabu dashi,
Yana iya É—aukar budurwa yanzun ya kai ta Restaurant cin abinci,da sun isa zai jawo mata kujera yace ta zauna bari yaje ya masu order,
Yana zuwa farko abinda zai tambaye su shine menene ya kare a wurin,ma'ana shine wani kalan abinci ne suka san ba su da shi,
Idan sun faÉ—a mai sai ya koma wurin budurwar yana yamutse fuska,sai yace mata ai da naso mu ci bu kaza ne amma sunce basu da shi,tashi kawai muje wani wurin,
Idan me hankali ce sai tace to ya siya masu drinks susha,idan kuma mai wayau ce sai ta bishi suje wani wuri,wanda nan ma suna zuwa ko dai ya ƙara mata haka,ko kuma yace ai sun ce Nama ya kare,ko kuma babu Kifi,dole dai karshi a bige da shan drink,
Kuma duk bala'in ki bai bari ki ga Menu balle ki zaɓa.
Shi yasa yawancin mutane suke masa kallon wanda bai san abinda yake yi ba,kuma matalauci,
Wannan shine asalin Jauro,
To masu karatu,ko yaya zata kaya tsakanin Jauro da Sumayya,
Ko zata iya cin kuÉ—in shi,
Ta yaya ya haÉ—u da mahaifinta har ya amince mashi,
Zata aure shi kuwa,
Yaya Ahalinshi,ya zasu ƙare,
Ya labarin dukiyar shi na shanaye da aka tafi dasu,shin zasu cika Alkawari su dawo mashi dasu.
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*19*
*Wannan littafin na kuɗi ne 300,ga mai buƙata ya turo ta wannan asusun Hauwa Umar, Zenith Bank, 2284905309.*
Abinda ya faru kuwa da su shine,yaran Baffa Sanda ne zasu tafi kiyo wato kannen su Yabbale,da Dotti da Nura, sai suka biyo ta gonar Baffa Bube,anan suka sami yaran shi da nasu dabbobin suna hutawa,ita kuma Binta tana É—iban kara wanda zata je tayi girki dashi,
Kokarin biyowa ta cikin gonar suke su wuce saboda hanyan zai fi masu sauƙi akan suyi zagaye,
Ganin sun shigo masu ta cikin gona ne yasa da sauri kanin ÆŠan Fodiyo wanda bai wuce shekaru goma sha É—aya ba ya taso ya tsaya a gaban su,cikin rashin mutumci yace basu isa subi ta cikin gonarsu su wuce ba,bancin kuma ko a girma Dottiya ma ya girma yayanshi na biyu wato ÆŠan Fodiyo,
Kallon yaron yayi yace masa ya matsa masu mana bai da kunya ne ai wucewa kawai zasu yi,
Cikin rashin da'a yace ko da ace Baffa Sanda ne zai zo da kanshi yace zai wuce ta cikin gonar nan ba zasu bari ya wuce ba balle su,
Wannan maganar da yaron yayi ne ya tunzura Dottiya har ya daga hannun ya mashi mari mai lafiya,
Shi kuwa jin zafin marin ne yasa ya faɗi ƙasa yana ihu,
Jin ihun É—anta ne yasa Binta bata jira komai ba kuma bata nime bayanin komai ba ita dai kawai taga su Dottiya tsaye kan É—an ta,dan haka sanda ta dauka lafiyayye ta zagayo ta bayan Dotti wanda ba zato ba sammani yaji saukar sanda a kanshi,
Shi kuma jin zafin hakan ne yasa cikin zafin rai ya kawo sara ta bayan shi ba tare daya san wanda ya mai wannan aikin ba,
Ita kuma da yake Allah ya kiyaye sai ta tare saran da hannun ta,wanda saran ba karamin shiga yayi ba dan har ana ganin kashin hannu,
Wannan shine musabbabin komai domin kuwa yaranta manya tasowa suka yi suka ce basu yarda ba,dole kuma sai sun daukar ma uwar su fansa,
Bayan kwana biyu da faruwan haka ne ranar Jauro ya shigo ƙauye,shine Bakari ɗan Binta na farko ya tare shi,wai yaga Alama yanzun wani tashen rashin kunya yake ma mutane tunda yaga wasu yan kuɗi suna shigo mai,dan haka yayi hankali da su,
To shi bai ma san wani rashin kunyar yake masu ba,
To kwana uku da wannan maganar ne shine ya shirya dan ya tafi ƙauye,Allah ya kiyaye shi bai isa ba ya dawo,to shine yake samun labarin kidnappen din Baffa Sanda da akayi tare da matarsa Kande,
Wanda dama kuma an daÉ—e da fara zargin su ÆŠan Fodiyo da irin wannan harkar,
*CIGABAN LABARI*
A jiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi yana gyara kwanciyar shi,gara ya bari washegari da rana kawai ya shiga ƙauye,
______ɓangaren Sumayya kuwa,tunda ta kammala girkin rana take jiran dawowar Mama,sai dai shiru har kusan ƙarfe uku na rana sai gashi ta dawo,
Buta ta dauka ta zaga bayi,tana fitowa ta daura Alwallah ta shige daki,
Ita kuma ganin ta dawo ne yasa ta bi ta É—aki ta samu wuri ta zauna tana jira ta idar.
Jira kawai tayi ta sallame sallah ko tasbihi bata yi ba,ta matso gabanta ta zauna tana zuba mata ido"Mama kin je?me ya ce ? Za'a fa...
Hannu ta daga mata,tana tasbihi da hannu,sai da tayi goma sannan tace"ai dai kya bari na numfasa ko"
Bata fuska tayi"dan Allah Mama ki faÉ—a min,wallahi hankali na ya kasa kwanciya "
Cire hijabi tayi tana mike ƙafa "banje ba"
Zaro ido tayi "Mama!
" Eh banje ba,ina fita na haÉ—u da malama Sadiya,Babban malamar islamiyarmu,ita na bi gida,tun dazu ina gidan ta,kuma na faÉ—a mata duk abinda ke faruwa,dan haka tace na faÉ—a maki ki zo gida ki same ta,kuma karna kuskura naje gidan wani malami,dan zan bata imani na ne,dan haka anjima sai ki shirya ki je gidan ta"
Cikin jin haushi tace"Uwar me zan mata a gida,ni ba inda zan je "
Buge mata baki Mama tayi"kina da hankali kuwa?
Kuka ta fashe da shi,"ni wallahi ba inda zan je,muguwar mata kawai,"
Ganin Mama na niman abun bugu ne yasa da sauri ta tashi ta fita dakin tana kuka,
Shi kenan ta shiga uku yanzun ina zata samu mafita,
Tunda ta shige daki take kwance tana kuka,har aka idar da sallar la'asar,sai da Mama ta shigo ta ci mata mutunci sannan ta fito tayi Alwallah tayi sallar,
Tana zaune kan Darduma tana jan carbiw wani tunani ya fado mata,dakatawa tayi da jan carbin tana nazari abinda ya fado mata a zuciya,
Dan haka cikin sauri ta Mike tsaye tare da kwabe hijabinta ta canja wani,ko kwalliya bata tsaya yi ba ta fito,
Dakin Mama ta leka wacce ke zaune tana cin abinci "Mama na tafi gidan Maman Momy"
Dagowa tayi ta kalle ta"me zaki je yi a can?
"Kawai dai zan je gaishe ta ne"
Kallon sama da ƙasa tai mata"ke ɗin ce a yau zaki je gaishe ta?
Turo baki tayi"eh"
"To ba zaki ba,dan bana son fitina,baki je bama ance kin je kinyi balle kuma kin je,ko ma ki zauna"
Bubbuga kafa ta fara kamar karamar yarinya,domin Sumayya irin yaran nan ne da Allah yayi su da fitina da kafiya "ni Mama zuwa kawai zan yi in dawo,kuma ba fitina zanje yi ba,"
Kauda kai tayi tana ci gaba da cin abincinta kamar bata san da ita ba,
Ganin Mama ta ƙyale ta ne yasa ta sadada ta fita gidan da sauri, tana tare mai mashin ta hau tace ya sauke ta ƙarshen layin su,duk da ba tafiya bane mai nisa ko da kafa zata taka,amma gudun Mama ta aika a dubata yasa ta hau mashin,
A bakin kofar wani gida mai bakin Get lafiyayyen ta sauka ta mika ma mai mashin Naira hamsin.
Maimakon ta shiga gidan sai tsayawa tayi tana karewa Get din kallo cikin mamaki kuma lokaci guda tana hararan Get É—in gidan kamar shi ya mata laifi,
Kafin ta isa bakin kofa ta tura ta shiga,
A tsakar gida ta samu matar gidan tana wanki wacce jin an buÉ—e Get an shigo ne yasa ta É—aga kai tana kallon ta cikin mamakin wacce ta gani,
Ita kuma ganin wacce ke tsakar gidan ne yasa kuma taji kamar ta koma,ta fasa yin abinda ya kawo ta,sai tsaki take ja a zuciyar ta,
Kallon yanda take wani har haɗe fuska matar tayi,lokaci guda kuma ta saki wankin da take tana murmushi wanda kai da gani kasan ba da zuciya daya take ba,ta kama hanci ta sake wani irin guda mai sauti tare da saka dariya tana riƙe haba "ah yau amarya ce a gidan nawa,lallai aure mai saka hankali"
Bata ce mata komai ba ta jawo kujeran dake gefe ta zauna,
Kamar ba zata mata magana ba tana turo baki tace"ina wuni"
Tsakar kanta ta tsaya ta ƙara rangada wani budar "Lallai yau Allah na gode maka daka nuna min ranar dani Sumayya zata gaida ni,Allah kasa ba mutuwa na kusa ba"
Sai da ta Harare ta kafin tace"nifa Maman Momy ba faÉ—a na zo ba,kawai dai nazo ne na rokeki akan kisa Baba ya fasa wannan auren domin nasan maganar ki kaÉ—ai yake ji"
"Eye,eye,lallai,wato ma kinsan magana ta kadai yake ji,to me zai hana ki ce Uwar taki ta kwada nata sa'ar akan shi"
"Ni dai na fada maki ba faÉ—a ya kawo ni ba"
"Eh dole ki ce haka tunda laluran gaban ki ne ya kawo ki ba,to bari ki ji ba zan faɗa mashi ba,domin kuwa aure ke da wannan bakin baƙauyen babu fashi,ai na faɗa maki,sai na lalata rayuwar ki,sai na mai dake abin tausayi fiye da Uwar ki,ke bari ma na fada maki abinda baki sani ba,ni na haɗa babanki da Jauro,na kuma zuga shi akan ya aura mashi ke,na ce ya faɗa mashi kuna idan ya aure ki kar ya kuskura ya bari ki yi aiki,ba dai takamarki kinyi karatu zaki nime aiki ki taimata ma Uwar ki ba,to babu batun aiki a rayuwar ki,sai dai ki zauna a ƙauye tare da fitinannun ƴan uwan shi waɗanda ko tashin hankalin su ya ishe rayuwar ki"
Ji tayi ranta ya baci,hankalin ta ya ƙara tashi "wato ke kika zuga Baba akan haka ba? Lallai ke muguwar ce Lami,me yasa baki ba shi Jauro auren yarki Momy ba sai ni,me na tsare maki,me muka miki?
Dariya ta kuma sawa" Ai cewa kika yi yata,ta ya za'a yi na zaɓa ma yata irin wannan mutumin da bai san Me yake yi ba,ki bari kiga irin mijin da Momy zata aura,sai kun koma kuma masa maula ke da Uwar ki harma dashi mijin naki,kuma bancin haka me amfanin ɗan kishiya"
Mikewa tsaye tayi"in Allah ya yarda burin ki ba zai taba cika akan mu ba"tana faÉ—ar haka ta bar gidan tare da bugo Get,
Juyowa tayi ta kalle Get din hawaye na zuba a idonta,a zahirin tace"Baba baka da adalci"ta faɗa tana juyawa tana tafiya a hankali tana ɗan goge hawayen idon ta,wannan matar Baban nasu makira ce,muguwa,kuma Azzaluma,dubi gidan da Baba ya gina mata ita da yaranta biyu,amma su ya bar su a tsohon gida da ko ƙofa babu,
Juya baban su take kamar waina sai yanda tayi dashi,Mamar su ba tada katabus,
Wlh wata rana suna sati É—aya ma basu ganshi ba,alhalin suna unguwa daya,
Wato ita ke kara zuga Baba yana masu hauka,, ko ina kuma ta san Jauro oho,in Allah ya yarda sai ta ga abin ta.
*Last free page*
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*20*
*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuÉ—i,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda É—aya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*
A hankali take tafiya kamar wacce kwai ya fashema a jiki,tsabar yanda jikinn ta yayi sanyi,bata damu data hau mashin ba wannan karon da kafa ta taka har gida,
Bata ma nime Mama ba É—akinta ta shige,dan ta san ba tada wani hujjar da zai saka ta nime ta tunda ta hanata zuwa,
Ganin in ta zauna tunani yana iya sakawa zuciyarta ya buga ne yasa kawai ta tashi ta kwaso kayan da aka ci abinci ta shiga wankewa,
A takaice ko mintina goma sha biyar bata gama haÉ—awa ba da dawowa sai ga Baba ya shigo cikin bacin rai wanda ko sallamar bai yi ba,
Sai ma kwala kiran sunan Mama da yake kamar zai tada gidan,
A razane ta fito daga É—aki dan barci take yi,
Tsayawa tayi a gefen shi "Baban Aisha gani"
Nuna ta yayi da É—an yatsar"wato baki da mutunci ko Hajara,yanzun har yakai kina koyawa ya'yan ki rashin tarbiya,abun ya tashi daga kaina ya koma kan matata kuma"
Jin ya ambaci sunan matar shi ce yasa ta juya ta kalli inda Sumayya ke zaune,wacce ko juyowa in da suke bata yi ba,asalima kamar bata jinsu sai cigaba da wanke-wanken ta da take yi,
"Baban Aisha wallahi ban aika kowa gidan ba"
"Ai dama haka zaki ce mara mutunci,ita kuma Sumayya da kika aika taje ta zageta tas,har da kiran min mata munafuka,da zagar mata iyaye,yanzun ke Hajara ba abin Alfahari bane ace kishiyar ki ta zabarma Æ´ar ki miji,amma da yake baku gode Allah shi yasa"
"Kayi haƙuri Baban Aisha,kaima kasan tunda na rokeka ka ki,shi kenan na fita batun wannan maganar,ni dai addu'a ta shine inda Alkhairi a wannan aure Allah ya tabbatar,in kuma baba Allah ya zaɓa mata wanda yafi shi"
"Ai gara ki daina wahalar da kanki,domin aure kamar anyi an gama ko da kuwa babu Alkhairi"
Tama rasa mai zata ce mashe tsabar takaici,wanda kuma bana kowa bane face na Sumayya,duk ita taja mata,inda ace bata je gidan ba ai da bai zo ya mata wulaƙanci ba,
Juyowa tayi ta kalle shi"to Baba mai zai hana ka dauki Momy ka bashi ya aura tunda ni bana so,ai naga ita ma ta isa aure,amma tsabar san kai sai ace ni za'a ma dole sai kace zamanin da"
Cab,lallai Sumayya ta taro march,Bokitin dake gaban shi yayi ƙwallo dashi"ni kike faɗa ma haka,Sumayya ni mahaifin ki kike ma rashin tarbiya,na tabbatar da Momy ne daga bata min haka ba,shi yasa ko yaushe kuke a tambade kuda Uwar ku,"
"Baba ni fa ban faɗa wani abu ba kawai dai auren ne bana so,na amince kai ka zaɓar min wani mijin da kanka amma ba wannan matar ba"
"Ina magana kina magana,Sumayya Allah ya tsine maki Albarka daga ke har uwarki dake daure maki gindi,kuma in dai ina zaye zabin Maman Momy shine zaɓi na,shi zaki aura koda a ce ana kaiki zaisa wuƙa ya daddatsaki yayi gunduwa gunduwa dake,to bari ki ji ni zan tsaya mashi a ƙoto dan kar a daure shi domin annoba ya kashe ya ragimemin mugun iri a zuri'a ta"
Wadannan maganganun da yake faɗa su suka tunzura Mama suka kona mata zuciya har ta shiga mai da masa da martani ita ma cikin zafin rai "Sumayya! Sumayya! Sumayya! Yanda na kira sunan ki sau uku Allah ya miki Albarka,ya aibarkaci rayuwar ki,in Allah ya yarda ba zaki taɓa tabewa ba,sai kin zama abin Alfahari a gidan nan" Juyowa tayi kanshi "bakinka ba zai taba kama yata ba tunda dai bata hakkin ka,me ta maka da zaka tsine mata,duk bakin cikin da kake kuntsa min mai ishe ka ba sai ka koma tsine ma ya'ya na,to bari kaji tsinuwarka ba zai taba kama su ba sai dai ya sauka akan waɗancan ƴan gold din ba baka ganin laifin su,kuma sai Allah ya saka mana,munafiki"
Ganin yanda ita ma ta taso masa ne yasa cikin bacin rai ya juya ya bar gidan yana faÉ—in "ko kunki ko kunso aure babu fashi,na ma maida shi cikin wannan wata,sai dai tasha fiya_fiya ta mutu"
Daga inda take zaune ta fashe da kuka tana haÉ—a kai da guiwa "shi kenan na shiga uku rayuwata tazo karshe tunda mahaifina yamin baki ya tsine min"
"Kul na kuma jin kiyi kuka akan haka,ba abinda tsinuwarshi zai maki,yanzun zan je wurin yayanshi duk yanda za'ayi dole ayita ta kare,domin na gaji da wulakanci da matar nan ke ja min"
Ku yi haƙuri ba yawa
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*21*
*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuÉ—i,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda É—aya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*
Sai da tayi sallan la'asar sannan ta shirya ta tafi gidan Yayanshi wanda yake zaune a Sabon Anguwa,
Sai dai cikin rashin sa'a koda ta je ta iske bayanan,dan haka ta samu uwar gidan shi ta faɗa mata komai tunda suna shiri ta kuma roƙeta akan dan Allah idan mijin ta ya dawo ta sanar dashi abinda ke faruwa,sannan tai mataa sallamah ta koma gida,
Koda ya dawo matar sanar dashi tayi abinda ke faruwa,dan haka É—aukar waya yayi ya kira kanin nashi akan ya zo tare da matanshi,
Shi kuwa Baba daya tashi zuwa sai ya dauko Maman Momy kaÉ—ai ya taho da ita a mashin din shi,
A dakin da yake ganin baƙi suka same shi, bayan sun gaisa ne suka samu wuri suka zauna,
Kallon shi yayan shi yayi"me gaskiyar maganar da matarka ta fada,sannan kuma me yasa ita Maman momy zata zaɓa ma Sumayya miji,"
Cikin sanin makamar kissa ta fashe da kuka"yaya tsakani da Allah nake zaune da mijina da kuma ya'yanshi, ban taɓa yin wani abu domin na cutar dasu ba koda matar shi,amma ita ko yaushe cikin bina da sharri take yi,bana bi ta nata domin duk abinda nasan zai amfanar ita da ya'yan ta shi nake yi,
Jauro mutumin kirki ne,yaro ne mai hankali Yaya,domin idan bana kwarai bane bazan taba zaɓar ma Sumayya shi ba,ka yarda da ni,kuma shi kanshi mahaifin nata yayi bincike akan shi,na tabbatar da ace yaga da cutarwa ai ba zai yarda ba Yaya"
Ajiyar zuciya ya sauke "da gaske kayi bincike a kan mutumin? Ya faÉ—a yana kallon Baba
" Na yi bincike akan yaron sosai,kamar yanda ta faÉ—a "
"Yaya ina da magana kuma,ɗan Allah ka taimake ni ka shiga wannan lamarin" Ta faɗa tana kara ƙarfin kukanta harda gudun hawayenta,
Shi kuma Baba sai wani lallashinta yake yi,
"Ina jinki,"
Faace majina tayi da kyallen dake hanunta,"wata uku da suka wuce naje Asibiti likita ya tabbatar min da ina da ciyon hawan jini,ya ce ina bukatar wanda zai dinga kula dani yana taimaka min,in ba haka ba ina iya faÉ—uwa rabin jiki na ya shanye,
Na roƙe Alfarmar maman Sumayya akan tabarmin Baban Momy har zuwa lokacin da zanji saki,da fari ta amince har yayi wata uku a wuri na,amma shine yanzun cikin satinnan har gida tazo ta sameni da cikin mutunci kan ita ta fasa barmin baban momy,wanda kuma Yaya shi yake taimaka min da wasu abubuwa da yawa,tunda kaga Momy na makaranta,shi kuma Sanusi ƙarami ne,shi kanshi yana buƙatar kulawa,
ÆŠan Allah ka taimake ni"
Duk abinda take faÉ—i yana jinta tare da jinjina kai,"wata uku,to ke har yanzun ba kiji sauki ba ne?
"Ko shekaran jiya munje Asibintin tare dashi an kuma auna jinin sai dai har yanzun bai sauka ba"
"To shikenan kukan ya isa haka,zan mata magana,yanzun kai ka kira min ita ma na"
"To yaya" Ya faÉ—a yana ciro waya a Aljihu ya kira number ta,
Mintuna goma sha sai gata ta iso,matar gidan ce ta mata iso har inda suke,
Tunda ta shiga taga yanda Yaya ya amsa mata gaisuwa tasan cewa akwai matsala,
Bata ce masu kala ba sai zama da tayi a gefe,cikin kissa maman Momyi tace"Maman Sumayya sannu da zuwa"
Bata kalle ta ba kuma bata ce mata Komai ba sai ma dauke kai data ƙara yi tana fuskantar Yaya,
Wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar ta wanda har saida ɗan murmushi ya nuna a fuskarta da sun lura,domin dama addu'a take akan Allah yasa karta amsa mata gaisuwa,domin zata iya ƙara samun ƙwarin gwiwa da rashin amsawar ta,
Jinjina kai Yaya yayi,sannan ya kira sunan ta"naji bayani daga bakin Mijinki da kuma kishiyar ki,kuma na gamsu da bayanin su sosai,ɗan haka kuma ya yanke hukunci a kan abu na farko,shine Sumayya zata aure Jauro,batun girki kuma ita Maman momy zata cigaba da riƙe miji har taji sauƙi,domin ba tada mataimaki "
Kallon mamaki take mashi"amma Yaya ta ya hakan zai kasance,wata uku da bai san cin mu ba balle shanmu,sai dai idan ya zagayo ya zo yaci wanda na dafa ma yara,idan nayi magana yace yanada mara lafiya,to ni da ya'ya na fa,Yaya ta ya taka faÉ—i haka É—an Allah,ni ban damu da batun auren Sumayya ba,amma ni amin adalci,"
"Bana son wata magana ki bi umurni na kawai"
Shiru tayi tana dukar da kai,wannan wani irin rashin Adalci ne,me yasa Yaya zai mata haka,bayan yasan tana jin kunyar shi,tana girmama shi,bata iya ci masa musu akan komai,"
Dago kai tayi"yaya ba komai Allah ya bata lafiya,sai dai ina rokon alfarma,ko da ba zai ba mu abinci ba,ina roƙon ka daka saka mana baki ya yafe ma Sumayya,ya kuma cire bakin da ya mata"
Kallon shi yayi"bana son shashanci,me yasa zaka ma yarka baki,wannan ba halin ƙwarai bane,domin duk abinda ya'yan mu zasuyi wata ƙila idan aka duba tarihin rayuwarmu munyi abinda yafi nasu,kuma iyayen mu basu tsine mana ba,dan haka maza idan ka maida matarka gida kaje ka samu yarka ku dai-dai ta"
"Insha Allah Yaya"
"Ku tashi na sallame ku"
Ta rigasu fita dan haka bata jira komai ba ta wuce gida,ko sallamar matan gidan bata yi ba,ta wuce,
Allah ne kaɗai ya kai ta gida lafiya,tana isa kai tsaye ɗakinta ta shige ta kwanta tana turo ƙofa,
Kuka ta fashe dashi tana kifa fuskarta acikin fulo,dan bata son ya'yanta su ji kukanta,
Ji tayi an buɗe ƙofar an shigo an maida an kulle,
da sauri ta dago kai tana share hawayenta,
A hankali ta tako ta zauna a bikin gado tana dafa ta,tashi zaune tayi daga kwancen da take tana kakaro murmushin yaƙe,"me kike buƙata,"
Rungume ta tayi a jikinta "Mama is not bad for a parent to cry in front of their children,ki yi kukan ki,bazan hana ki ba,kuma bazan yi ba,ɓalle in rage maki kwarin gwiwa rage raɗaɗin dake zuciyar ki"
Kamar jira take ta faɗa mata haka,nan kuwa ta fashe da kuka mai raɗaɗi tana ƙara rungumi Sumayya a jikin ta,
Tayi kuka sosai wanda har saida taji wani sanyi yana ratsa zuciyar ta da nasuwa,wanda bana komai bane face na sumun kafadar da tayi kuka
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*22*
*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuÉ—i,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda É—aya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*
Sai da ta gaji dan kanta sannan ta dago tana goge idanunta da suka kunbura,
Cikin sanyin jiki tace"Mama dan Allah ki yi haƙuri ki yafe min,laifina nane,idan da nasan abin zai kai haka da banje gidan ta ba,dan Allah ki yafe min kar kiyi fishi dani "
Cikin shakakken muryarta wanda ya dushe da kuka tace"ba laifin ki bane Sumayya,nasan cewa dama kawai suke jira wanda zasu ci mutunci na,basu samu ba sai yanzun,amma babu komai haka Allah ya tsara min,a wasu lokutan da dama na kanji kamar na bar gidan mahaifin ku,na kama gaba na,saboda irin wulaƙancin da yake min na bayyane dana ɓoye,sai dai a duk sanda na kalle ku sai naji bazan iya tafiya na bar ku ba,saboda nina haife ku,na jure ko wani irin wahala tun daga na ɗaukar ciki har na raino,har kuka kai matakin da kuke a yau,sai dai har yanzun ban gama tarbiyantar da ku ba,akwai ƙananki ƙanana,idan na tafi wa zai kular min dasu,nasan ba a taɓa basu irin tarbiyan da nake masu kwaɗayin samu ba,wannan yana daya daga cikin dalilan dake kara sani in yi haƙuri,
A da mahaifin ku ba haka yake ba,mutumin kirki ne,wanda nake girmamashi sosai kamar yanda yake girmama ni,ya nuna min soyayya da kulawa,har ma daku,ya shayar da ni daÉ—i dai_dai gwargwado,wata kila shi ya manta,amma ni ban manta ba Sumayya kuma ina son shi har yanzun"
Rungume mahaifiyar ta tayi a jikin ta hawaye na zuba a idon ta"idan har ke mahaifiyar mu zaki iya sadaukar da farin cikin ki domin na mu rayuwar,mu a matsayin mu na ya'ya me zai hana mu sadaukar da namu farin cikin domin naku,Mama na Amince da auren Jauro,zan karɓe shi a matsayin miji,amma ba dan kowa ba sai dan ke mahaifiya ta"
Dago ta tayi"A'a Sumayya,ada dai nayi niyar kibi zabin mahaifinki,amma yanzun kam ban yarda ba tunda matarsa ce ashe tayi zabin ba shi ba,ba zaki aure shi ba"
Girgiza kai tayi"kar ki ce haka Mama,idan har ban amince ba komai na iya faru na sani kuma kema kin sani,bana son na kasance mai taurin kai a tsakanin ku,dan Allah ki cire komai a ranki kamar yanda nake kokarin yi yanzun,"
"Karki damu,yanzun zanje gidan matar kancila ta kai ni gidan wannan malamin,koma yaya ne ba za'ayi wannan auren ba"
Share hawayen da suka zubo mata tayi"Mama dazu fa da kanki kika ce Malamar ku tace bai da kyau zuwa wurin malami,tabbas gaskiya ta faɗa maki,ni kan na haƙura,nayi imani da ƙaddara,domin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa,idan zaka yi ruko,to ka roƙi Allah,haka kuma idan zaka ni me taimako,ka nime taimako a wurin Allah,
To Mama me yasa ba zamu nime taimako a wurin Allah ba,a gani na yafi mana zuwa wurin wasu malamai waɗanda sai mu ɓata kuɗin motar mu domin zuwa wurin su,sannan kuma su karbi kudin mu,Amma kuma shi Allah a duk inda kake,ko da kuwa a cikin kabari ne,in dai har zaka yi addu'a Allah zai karɓa maka ba tare daka biya shi ba,
Sannan yace (ka sani da za'a tare Al'umma domin su amfanar da kai da wani abu,ba zasu iya amfanar da kai komai ba sai abunda Allah ya rubutu maka, sannan yaci gaba da faÉ—in,Da za'a tara Al'umma domin su cutar da kai da wani abu,ba zasu iya cutar da kai da komai ba sai abunda Allah ya rubuta maka)na yarda da wannan hadisin,
Nayi imani Maman Momy bata isa ta min abinda Allah bai min ba,ki kwantar da hankalin ki,bazan so saboda ni ki sauka a kan hanyar bin Allah ba,domin idan haka ta faru bazan taɓa yafe ma kaina ba"
"Allah ya Albarkaci rayuwar ki Sumayya,idan har Allah yana karɓar addu'ar uwa a kan yarta,Ya Allah ina roƙon ka da kasa Albarka a rayuwar Ya ta,wannan auren idan har za'a yi shi da niyyar a tozarta mu ne,ya Allah ka saka albarka a cikin shi,kasa hanyar Arzikin sune,ka ba maƙiya kunya,Amin ya hayyu ya Kayyum"
_______ɓangaren Jauro kuwa,sai washegari da rana tsaka ya shiga ƙauyen,dan Allah ya gani mugun tsoro gare shi,karma yayi sammako ya haɗu dasu a hanya,ko kuma yaje da dare wani abu ya faru dashi,shi yasa ya gwammace ya tafi da rana ido na ganin ido,,
Ko da yaje ma ko awa biyu bai yi ba a cikin Rugan su ya fito,dan gaisuwa kawai da jage ya masu,sannan ya tafi gidan Malam Liman,shima yana ganin an idar da Sallar La'asar ya masu sallamah ya wuce,
Koda mai mashin din da ya fito dashi daga cikin ruga ya ajiye shi,a maimakon ya samu É—an adaidaita ya maida shi gida sai cewa yayi mai a daidaitan ya kaishi Barikin Sale,wanda wannan Anguwarsu Sumayya,
Sam bai damu da yanda yayi butu butu da ƙura ra,saboda hanyar su ba kyau duk jar kasa tayi yawa,wanda yasa har ta suman kanshi ya canja kala zuwa ja,
Sai ya koma yanda kasan wanda aka tono daga kabari,
Sai dai shi ko a jikin shi,
Har kusa da kofar gidan ya sauka sannan ya kara so da ƙafa,Allah yasa yana zuwa ya haɗu da Aisha zata shiga gida,dan haka tare ta yayi,
"Kanwata zo in aike ki"
Koda ta juyo ta haÉ—a ido dashi,sai ihu za saka tana sake ledan manja dake hannun ta na Hamsin wanda Mama ta aike ta,ta shige gida da gudu ta kiran a taimaketa ga mai yankan kai a kofar gida zai gudu da ita,
Mama ce ta fito da sauri da ga banÉ—aki jin yanda yarinyar ta shigo a gigice,
Tambayarta tayi lafiya meke faruwa,
Sumayya ce ta faÉ—a mata wacce ke rike da Aisha a jikin ta,
"Je ki wurin Mama bari in duba ko waye"
"Duba,kinsan halin Aisha da tsoro"...
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*23*
*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuÉ—i,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda É—aya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*
Tana fita ƙofar gida ta gan shi tsaye da wata mata wacce makociyar suce basu daɗe da dawowa unguwar ba,
Kallon shi take tun daga sama har ƙasa,sannan ta kalli kanta,
Riga da zani ne a jikin ta na atamfa duk da ya dan fara kodewa amma fes yake,yaya Amina ce ta bata,
Sai hijabi iya gwiwa wanda yake ruwan madara,
Ji tayi wani abu kololo ya tsaya mata a makoshi,
Yanzun wannan mutumin ne zata aura a matsayin miji,bata so ta tuna hakan,domin hakan ba karamin sosa mata rai yake yi ba,
Jin matar na mashi magana ne yasa ta maida hankalin ta wurin su,
"Almajiri,ko zaka dunga min tallan Pure water ina baka abinci?
Dan ita tsakanin ta da Allah ta dauka Almajiri ne,saboda yanayin shi,kai ko wasu Almajiran sun fishi kyau gani.
Kallon matar yayi daga sama har katsa,yama rasa ne zai ce mata,
Ganin yana ƙoƙarin juyawa ne yasa ta kuma cewa"kai Almajiri da kai nake magana "
Ranshi ne ya ɓaci,domin ya riga yaga Sumayya dake tsaye,ta yaya matar nan zata disgashi a gaban budurwar shi,
Cikin jin haushi ya kalle ta yace"ki lalli miliyoniya kamata kice na maki tallah,to ko mijinki bai yi matsayin da zai zama dan aiki na balle ke kice zaki saka ni tallan ruwa,Idiot"nuna mata Sumayya yayi wacce ke tsaye tana kallon su"kalli matar da zan aura ko kyau ta fiki da wayewa,shine har zaki raina ni"ya karasa faɗa yana isowa inda take tsaye tana ji kamar ta haɗiye zuciyar ta,dan har wani kwanbo yake yi,wato shi a dole yana taƙama,
Matar ce ta zo gabansu ta tsaya itama,sai da ta ƙare ma kowannensu kallo sannan ta kwashe da dariya tana nuna Sumayya da hannun,
"Sumayya ko,eh in banyi karya ba kece Sumayya,wacce nake jin labarin ta anan layin,mace mai kyau da ji da kai," Dariya tayi tana nuna ta ta nuna Jauro"a gaskiya banyi tsammanin haÉ—ewarki har yakai kina tsayawa da irin wadannan kananun yaran ba,ashema abinda ake faÉ—i akanki karya ne,gaskiya kin yi asara idan har kika auri wannan abun an ci baya"ta faÉ—a tana dariya tare da barin wurin tana jinjina lamarin.
A cikin su an rasa wanda zai ce ma matar ko uffan,yanda kasan waÉ—anda aka rufe ma baki har ta bar wurin,
Juyo da kallon shi yayi kanta suka haÉ—a ido,
Kauda kanta gefe tayi tana haÉ—iye wani abu mai É—aci da ya tsaya mata a makoshi,
Shima shiru yayi yana kallon kanshi tun daga kan takalmin shi har kayan shi,
Shi kanshi sai yanzun yake tunanin tabbas bai kyauta mata ba daya zo a haka,gashi har an fara gulman ta a kanshi,ko yace cin fuska,
"Kiyi haƙuri"
Cikin mamaki ta juyo tana kallon shi,domin tabbatar da cewa shin da gaske daga bakin shi maganar ya fito,
"Kiyi haƙuri bai kamata na zo wurinki a haka ba,gashi na ja maki raini"
Ita dai bata ce mashi komai ba,
Ajiyar zuciya ya sauke "ni ba ɗan karya bane,ni ɗan ƙauye ne,ban iya dressing irin na samarin zamani ba,ban maki Alkawarin ba zan ƙara zuwa wurin ki a haka ba,amma dai zan kiyaye,"
Shiru yayi na wasu daƙiƙai yana kallonta yanda ta kauda kai,
"Ki sani idan ina da ra'ayin canja tsarin rayuwata ya koma irin na ƴan karya ina iya canjawa a cikin Awa Ishirin da huɗu,sai dai ki sani ni ba zan yi haka ba,dan banda ra'ayin yin haka,saboda ke kuma ba zan canja ba,duk da ina sonki,na kuma yi Alƙawarin idan har na aure ki zan kula dake sosai,zaki samu jin daɗin da duk wani abu da kike mafarkin samu,
Ni ban damu ba idan har baki sona,na maki alkawarin da zaran kin haifarmin yara guda biyu ko uku zan sallameki ki je ki auri wanda kike,ni kuma na kula da yara na,i promise you,kinga da anyi aure sai kiyi sauri ki zazzago min Ya'yana ni kuma na sallame ki,a yanda na yi lissafi acikin shekara huÉ—u idan Allah ya bani sa'a muna iya samun yara uku,shi yasa nake son ki kwantar da hankalin ki"
Wannan karon daga kallon mamaki ta koma mashi kallon tsoro "anya kuwa wannan bai da matsalar kwakwalwa,in ba haka ba shi harya tsara mata yanda zata haihu,kuma tsabar rashin hankali wato har yana faÉ—a mata cewar zai rabu da ita da zaran ta haihu,to ita mahaukaciya ce da zata yarda ta haihu dashi"
"Ba kada hankali" Tana faɗin haka ta juya ta shige cikin gida,idonta na kawo hawaye,waiyo ita kan Allah ya jarabceta,yanzun dama Jauro banda matsalar ƙauyanci da kazanta,harda matsalar hauka gare shi,kai Allah ya tsine ma Maman Momy.
MaMa ce tace"waye ne awajen,naga kuma kin daÉ—e har ina shirin lekawa"
"Jauro ne Mama amma ya wuce ko"
"Me ya kawo shi kuma?
" Mama nima ban sani ba,dan ban gane me yake faÉ—a ba"
Shuru kawai Mamar ta yi dan ta lura kamar bata son yin magana kuma ranta a ɓace yake,
Cire hijabinta tayi ta mika ma Aisha ta ajiye mata a daki sannan ta koma kicin tana duba wutar icen data hura,"in Allah ya yarda koda na aure ka babu wani abu da zan yarda ya shiga tsakani na dakai balle in haihu har ka mai dani bazawara,sai dai mu tabbata a haka "wannan shine abinda take rayawa a ranta.
Jin sallamar Baba da tayi ne yasa taji gabanta ya faÉ—i,shi yasa bata juya ba taci gaba da aikin dake gabanta,
Mama kuwa a inda take ma Aisha kitso ko kallon shi bata yi ba,
Zuwa yayi ya ajiye babban ledan dake hannun shi a gefen ta,ya ja kujera ya zauna
Ba tare data kalle shi ba tace"barka da zuwa"
"Yauwa ya gida?
" Lafiya "
Bai damu da yanayin ta ba ya jawo ledan gabanta,"kiramin Sumayya "
Kallon kofar kicin tayi"Sumayya,"
Amsawa tayi tana fitowa,
Tana zuwa a gabansu ta tsungunna "Baba ina wuni"
"Lafiya qlau yar Albarka,Sumayya Allah ya Albarkaci rayuwar ki,kuma maganar dana fada jiya na yafe maki harga Allah," Turo mata ledar gaban shi yayi"kinga dauki wannan ledar ki kaima mamarki daki ta raba ma Æ´an uwa ta,domin goron saka ranar auren ki ne"
Daga ita har Mama dago kai suka yi suna kallon shi cikin mamaki.
Cikin masifa Mama take ƙoƙarin faɗin magana,
Da sauri ta tari numfashinta"to Baba Allah ya kaimu"
Daga shi har Mama kallon mamaki suke mata da jin abinda ya fito bakinta,
Ta gefe É—aya kuwa Baba cizan lebe yake yi domin yaso Mama tayi wata magana da babu abinda zai hana bai sake ta ba,kamar yanda Mama Mumy ta faÉ—a mai,da zaran ta mai maganar banza ya sallame ta ya huta kawai,
Sai gashi Æ´arta ta cece ta,
Ƙoƙarin magana take ta kuma katse ta"Mama babu komai fa,karki manta mun riga munyi magana,so is ok"ta faɗa tana jinjina mata kai alamun tabbatar wa.
Tare da daukar ledar ta shige daki,
Cikin jin haushi ya ce"maganar me kuka yi?
Cikin kauda zancen nashi tace"wani wata ne aka saka saka auren?
Kauda kai yayi kamar bazai yi magana ba yace"nanda sati biyu,sannan in kin kaima Æ´an uwanki Goro ki nima taimako a wurin su,domin ni ko kudin gado ba nida shi,nama godema Maman Momy tace zata ara min dubu hamsin sai a siyo mata gado wurin Dillaliya na hannu tare da katifa,idan yaso in an kawo sadaki sai a bata kuÉ—in ta,
Sannan dama ina son in faÉ—a maki kardai kije ki gaiyata waÉ—annan Æ´an uwan naki masu yawa,dan ko sunzo banda kudin da zan siyo abincin da za'a ci,sauran kayan daga baya idan anyi aure a hankali nata siya ana kai mata"yana gama fadar haka ya tashi ya fita ba tare daya bari ma ta samu dawowa daga shock É—in data shiga ba.
*idan kece Uwar Sumayya wani mataki zaki É—auka*
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*24*
*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuÉ—i,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda É—aya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*
Tana daki tana jin duk abinda suke faɗa,rufe bakin ta tayi da tafin hannun ta tana ta faman kuka,wannan wani irin rayuwa ne haka,tunda Maman Momy ta shigo rayuwar su shikenan komai ya sauya masu,ba zata manta ba,haka lokacin auren Aunty Amina ya faru,ba karamin wahala tasha ba,dan ita a nata lokacin tana da saurayin da take so,amma maman Momy ta kawo mata wannan mutumin wai sai dai shi zata aura,gashi da mata har biyu ita ce ma ta uku,data ki yarda Baba har daure ta yake a ƙarfen Dish ta kwana a wurin,
Duk wahala baisa ta amince ba sai da shi saurayin ganin wahalar da take sha yayi yawa ne yasa yace ya haƙuri kawai ta aure wanda iyayenta suka zaba mata,a ranar sai da ta kwanta asibiti tasha karin ruwa yakai leda takwas,yayin da shi kuma karshe ya bar garin,
Daga karshe dai ba dan taso ba haka ta hakura ta aure shi,
Indai wurin ciyarwa ne mutumin yana da ƙoƙari,haka tufafi dan gaskiya ba laifi,sai dai kuma yana da zuciya abu kaɗan duka,shi yasa har zuwa yau Aunty Amina bata kaunar shi,duk da sunada yara biyu,gani yake kamar siyan ta yayi,ba tada inci,haka in maganar zuwa gida ne gasu a gari daya jaha daya amma sai tayi wata biyar, shida bai bari ta leka gida ba, dan ba karamin kudin shi Maman Momy da Baba suka ci ba,kuma har yanzun a haka take kullun da kalan shaidar dukan da zaka ganta dashi a jiki ko a fuska,
Wannan lamarin na damun Mama sosai,sai dai babu yanda ta iya tunda anfi ƙarfinta,Maman Momy kamar ta asirce kowa ba mai ganin laifin ta,da tayi magana sai ace zata kashe ma yarinya aure,shi yasa ta hakura kawai take binta da addu'a,
Yanzun gashi abin ya zo kanta,sam bata son ta saka ma maman su damuwa dan idan abin ya mata yawa hawan jini na iya kamata,kwanaki ba jimawa da Aunty Amina tayi yaji mijin ya mata É—an banzan duka,shine ta gudo gida,
Shi kuma ya kira Baba ya faÉ—a mashi karya da gaskiya,ba tare da Baba yayi bincike ba ya hau kan maganar mutumin nan ya zauna,
Har gida yazo ya same ta da cin mutuncin akan maza ta shirya tabi mijinta ta koma,ita kuma tace ko zai kashe ta ba zata koma ba,yayi bala'i har ya gaji ya wuce ba wanda ya kula shi,
Da ya tashi sai zagaye Æ´an uwan mama tare da nashi yayi yana fadin ai mama ta zugo Amina akan ta kashe aurenta ta hanata zaman gidan miji,haka yasa a wannan lokacin Æ´an uwa suka juya mata baya,daga nata har na miji,babu inda take jin daÉ—i,
Shi yasa akan Amina ta fauwala ma Allah komai.
Zama tayi kusa da ita"Kuka kike yi Sumayya?
Share hawayen ta tayi"A'a"
Rungume ta tayi a jikin ta,nasan kin amince ne saboda kina gudun tozarcin da zai biyo baya daga gare ni,duk da kasancewar ki yarinya mai taurin kai,amma kina da tausayi na,kin damu da damuwa ta,ban so auren ki ya kasance haka ba,bana son rayuwarki ya kasance tamkar irin nawa dana ƴar uwar ki,naso koda ke din ce ki samu kwanciyar hankali,amma babu yanda na iya,kin gama min komai,ina maki fatan nasara a rayuwar ki,kamar yanda kike da ƙudurin taimaka min a rayuwar ki,Ubangiji ya taimaka maki,kar ya taɓa barin ki tabewa,Allah ya zama gatanki,kamar yanda kika so ki zama gatan mu,
Na san idan ace a yau ina da iyayen da zasu tsaya min ne da hakan ba zai faru dani ba balle ku,sai dai na taso ne ni ma a gidan da ba'asan daraja taba,
Nasan ba ni da abinda zan iya baki daga yanzun har a kaiki dakin mijin ki,haka kuma ba zan taba roƙon ƴan uwa na ba domin su taikama min,sai dai ina iya baki dama akan kiyi kuka a kafaɗa ta iya yanda kike jin zuciyar ki zata yi sanyi,"ta fada tana ƙara rungume ta,
Kuka ta fashe dashi tana kara rungume Mama,yayin da ita kuma take shafa bayanta a hankali.
___________*Gidan Maman Momy*
Baka jin tashin komai a tsakar gidan sai tashin dariya,
Zaune suke sun baje a tsakar dakin ko wacce da kwalbar kok a gabanta,su uku ne.
Daya daga cikin su ne ta sheke da dariya "shegiya Asma'u ba kida dama,wato dai ba zaki mata da sauƙi ba"
Maman Momy ce naga ta kai ma matar data yi magana duka a cinya"waya faɗa maki ana sanya a zamanin nan Blessing,ai idan kace zaka zauna sai kaga ta zama,shi yasa kika ga tunda na shigo gidan nan a tsaye nake na hanata rawar gaban hantsi,bata isa ta motsa ba,ya'yanta ma ba tada ikon da zata aurad dasu sai mijin dana zaɓar masu,dan nasan idan suka aure masu kuɗi ko gidan hutu to Uwar su ta huta,ni kuma abinda ban so kenan "
"Amma fa Asma'u zance ko Julia ba kiÉ—a mutunci,kamar ba tare kuka tashi da Maman Sumayya ba,yanzun da kike mata haka wa zai ce kawarki ce,ita ta musuluntar dake,ta baki kaya,kar ki manta kawarki ce sosai a wancan lokacin,amma kika mata cin amana kika aure mata miji kika hanata kwanciyar hankali,lallai kin cika butulu,na jinjinama makircin ki,dole na zo daukar darasi na musamman "
Hararanta tayi"bana son iskanci Abigil,ni har mantawa nake na ta fitowa daga jinsin kiristen,batun wancan matar kuma tamin komai ai bai taso ba tun da ban taba rukonta ba"
Ihu Blessing ta saka"Jesus,Julia kar ki manta nan har rokon Maman Sumayya pant kike da Bireziya,batun rokon abinci kuwa ba'a magana, shine yanzun tsabar samun wuri zaki faÉ—i haka,Jesus karya babu wuya yanzun"
Tsaki taja tana murguda baki"ay koma dai menene a da ne,yanzun kuma fa,ai dai nafi ƙarfinta,kuma sai yanda nayi da ita da ya'yanta har ma da mijinta,"
Duk kallon juna suka yi suna tabe baki,dama haka É—an adam yake bai iya samun wuri ba,domin duk a unguwa daya suka tashi dukkan su,wanda ya ke haÉ—e da Arna da Musulmai,kuma a wannan lokacin suna zaman lafiya sosai,
Amma shine taci amanar kawar ta,koma dai yaya ne su babu ruwansu tunda dai in sun zo ana É—an siya masu kok...
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*25*
*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuÉ—i,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda É—aya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*
Kiran Baffa Bube ne ya ta da shi barcin da ya koma bayan sallar Asuba,dan ranar bashi aiki yana hutu,
FaÉ—a mashi yayi akan yana nimanshi a gida yanzun,
Dole ya tashi ya kintsa sannan ya dauki hanya,
Kwata_kwata tafiyar awa daya ne ya kaishi ƙauye,
Koda ya isa a ƙofar gidansu ya same su zazzaune harda yaran Baffa Sanda,su Yabbale,
Sallamah ya masu sannan ya samu wuri ya zauna,bayan ya ƙara jajanta masu abinda ya faru,
Baffa Bube yace Audu dan gidan Goggo Badejo ya je cikin gida ya kira Dan Fodio,tun dazu zaman jiranshi suke yi da tuni sun fara,amma ya tsaya yana ja masu rai kamar wasu ƙananun yara.
Yana fitowa zama yayi ba tare daya ce ma kowa komai ba,
Suma kuma basu kula shiba,
Baffa Bube ne ya fara magana "kai tsaye na tara ku ne domin na sanar daku mutanen da suka dauke Sanda sun kira,sun kira mun yi magana dasu sunce suna buƙatar Miliyan goma ko wanni mutum daya,wato dai shida kande,wanda kuɗi ya tashi miliyan Ishirin,
Na dai roƙe su akan su rage mana akan mu bada miliyan goma,basu yarda ba wai sai dai a basu sha-biyar ko kuma su kashe su,
To ku me kuka gani?
GabaÉ—ayan su shiru su kayi,kowa na jinjina yawan kuÉ—in,
"Ba shiru ya kamata ku yi ba,kamata yayi a san abun yi"
"Abun yi É—aya ne,shine kawai Æ´a'Æ´an shi su fitar da kudi su amsoshi,in basu dashi su fitar da dabbobinsu a sai da"
"Wannan wani irin maganar banza ne haka kake faÉ—a ÆŠan Fodiyo" Cewar Audu.
"Ai ba maganar banza na faÉ—a ba,idan ku kunada kudun da zaku bada to ni dai banida shi,"
"Kai wai m...
" Ya isa haka Audu,kyale shi,mu da yake uban mu ai dole duk yanda zamu yi muyi domin mu amsoshi,"cewar Yabbale
"Ban taraku dan kumin rashin hankali ba,dan haka ko wannen ku ya saurare abinda zan yanke mashi wanda zai bayar"
"Dukkan ku manya zaku bada budu dari biyar_biyar, ko wannen ku,bana son jayayya"
Mikewa tsaye yayi"haba Baffa,wani irin dubu dari biyar,ina na ganshi,ita kake son mu samu,ni dai gaskiya banida halin shi"
"Dottiya ne ya ce Baffa gaskiya sai dai ya'yan shi su sai da dabbobin su a biya,dan ni dai Bani da shi,"
"Ai dama ba nimam taimakonku muke yi ba,ko da zamu sai da rabin dabbobinmu mu zamu amso mahaifin mu" Yabbale ya faÉ—a cikin jin zafin abinda suke faÉ—i.
"Ya isa haka duk ku zauna" Baffa ya faÉ—a
Sai dai ko kallon shi babu wanda yayi,sai ma wucewa dasu Yabbale sukayi,
Kallon Jauro yayi wanda tunda aka fara magana bai ce komai ba,sai dai ya kalli wannan ya kalli wancan "kai ba kada abinda zaka ce ne?
" Eh ina da abin faÉ—a Baffa "
Maida hankalin shi yayi kanshi daga kallon su ÆŠan Fodio da suka wuce suna faÉ—a,"ina jinka"
"Baffa yarinyar da zan aura iyayenta sun ce na turo magabatana,kuma nan da sati biyu suke son ayi bikin,to ni kuma gaskiya bansan yanda zan yi ba saboda ga batun kama su Baffa da batun amsosu da ake yi,sai dai wallahi Baffa bana son na rasa yarinyar dan ina son ta"
ÆŠan karamin tsaki ya ja"ni ba wannan maganar nake ji daga bakinka ba,maganar kuÉ—in da muka yi yanzun nake son naji yaushe taka ba da naka,idan har ka bada naka bani da damuwa a kan batun auren ka,kaga ko Malam liman yana iya zuwa yayi komai "
"Baffa bada waɗannan kudin abu mai sauƙi ne,dan haka a dauki shanaye na dake wurinka guda uku a sai da shi sai a bada nawa kuɗin"
Abin mamaki nan take sai ga fuskar Baffa Bube ya hade kamar hadarin gabas,cikin bacin rai yace"wannan wani irin maganar banza ne haka kake faÉ—a Jauro,to in dai Shanayen ka na wurina ka saka ma ido to sun kare tun tuni "
"Sun fa kare,ni da ko daya ban taba amsa ba a wurunku,ba mutuwa su kayi ba sannan yanzun ace sun kare?
Cikin inda_inda yace" To me kake son in ce maka,lokacin kana makaranta wannan mutumin yazo wai kana buƙatar kuɗi,to shine na keta saidawa ina bashi kudin yana tura maka"
"To na wurin Baffa Sanda fa?
" Kai ina ga da wuya in za'a samu abin da ya rage a hannun shi,"
"Yanzun kenan ni dai ne a gidan nan ba ni da ko Æ´ar kaza,?
Ya faɗa yana jin zafin abin a zuciyar shi,duk da dama ya riga ya saka a ranshi ba samu zai yi ba,amma kuma jin haka daga gare su ya fi mashi zafi,idan yayi duba da ko yaro ƙarami in dai a gidan aka haifeshi to yana da abin kiyo,
Girgiza kai kawai yayi " In dai haka ne Baffa sai dai ince Allah ya kyauta,dan ba ni da ko dubu hamsin din da zan bada balle dubu dari biyar,"
"To shi kuma auren da kace zaka yi fa,da wani kuÉ—i zaka yi su? Baffa ya tambaya cikin yanayi na rashin damuwa,dama fargabanshi daya kar Jauro ya tada rigima akan bai yarda ba sai sun fito mai da dabbobin shi,
To ya gode Allah tunda yaron bai dau abin da zafi ba,
"Dama akan dabbobina na saka rai,amma tunda abun ya kasance haka,kuma ina son yarinyar,zan roki mahaifinta akan ya Bani bashin aurenta in yaso daga baya na bata kuÉ—in Sadakinta"
"Yanzun kai Auren bashi zaka yi,wai duk ina kuÉ—in aikin kwamnatin da kace kana yi a cikin gari?
" Baffa ko zaka aramin ne?
Tsaki yaja ya tashi "kaje dai ka sami Malam Liman na tabbatar idan yana da shi zai baka"ya faÉ—a yana barin wurin.
Girgiza kai kawai yayi ya nufi gidan Malam Liman domin sanar dashi yanda suka yi da Baffa Bube......
*ðŸ‚JAUROðŸ‚*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''ðŸŒ'* âœï¸âœï¸
Ø¨ÙØ³Ù… الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*26*
*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuÉ—i,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda É—aya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*
Duk da cewar lokaci ya ja bakaman da ba,amma Malam liman bai bar zama yana koyar da É—aliban shi ba,
Dan haka samun wuri yayi ya zauna a cikin Almajirai har aka idar karatu suka yi Addu'a suka watse,
Sake sabon gaisuwa suka yi da Liman,inda yake faÉ—a mashi yanda suka yi da Baffa Bube,
"Hakan da kayi shine daidai Jauro,domin shi Gado ba abin fitina ba ne,yau ina asalin wadanda suka tare dukiyar suke?sun tafi sun bar ta ba dan suna so ba,to kamar yanda suka tafi suka bar ta muma haka zamu tafi mu barka,ko kuma ita ta tafi ta bar mu,na gode ma Allah da baka tada hankalin ka ba akan haka,Allah kuma ya ƙara hore maka naka,"
"Amin Malam"
"Batun niman Auren ka kuma,In Allah ya yarda jibi Laraba zamu je akai kudin sadakin,"
"Amma Malam kana ganin babu matsala idan akayi komai bayan ba'a sake Baffa Sanda ba,ba zasu kullace ni ba"
"Ina ce a gabanka ya faÉ—a kayi auren ka kawai,kuma in dai ba kayi karya ba ai inaga ba matsala,ko za ku wani wasa ne?
Da sauri ya girgiza kai" A'a dan yanzun ba ni da wasu kuÉ—i a kasa saboda na kashe kuÉ—i sosai wurin turo takardu na UK,"
"To ba damuwa,hakan yayi Allah ya taimaka"
"Amin" Ya fada ya na yi mashi sallahma.
_______kamar yanda Malam liman ya tsara haka kuwa aka yi,domin an kawo sadakin Sumayya wanda Baba ya karba dubu dari,sai dukiyar aure kuma suka bada dubu dari uku,
Ranar Baba bakin shi har kunne,domin bai É—auka zai samu koda rabin haka ba,dan su sun bashi dukiyar aure ne bisa Al'adun su na Fulani,
An kuma saka biki nan da sati É—aya,wanda ya kama ranar Juma'a.
Kamar yanda bai ba Sumayya ko sisi ba haka ita ma Mama bata ga kudin ba,illa dai faɗa mata da yayi ga kudin da suka bada,amma ya ba maman Momy ta siyo mata wasu yan kayayyaki na mata na buƙata,dan tace a kwai in da zata siyo komai cikin sauki,a rahusa mai kyau.
Ita dai Mama har ya gama magana ba tace masa ci kanka ba,har ya kammala fada ya juya zai tafi,sai kuma ya juyo ya kalle ta ganin yanda tayi ko in kula da shi"to ke baza kice komai ba ne?
"Allah ya sanya Alkhairi"
Waro ido yayi"kawai,"