Naga Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Naga_Rayuwa_Part_3_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 1 of 1
Home / NAGA RAYUWA novels / NAGA RAYUWA book 3 part 1
NAGA RAYUWA book 3 part 1
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 13:53
Adakata! Adakata! mukaji wasu yansanda suna
fada daga bakin kofa,inda hankalin kowa yakai
kanasu mata suka shigo dasu su 8 fuskarsu
sanye da mask jikinsu kayane bakake daya daga
cikin sojojin yaje gaban teburin Alkali abbana
yace yamaigirma mai shariah hakika anyi kuskure
wajen tsare wannan baiwar Allah ba ita
akenemaba bawannan bace wacce ake zargi
yanunani wani farin ciki ne yaxiyarceni hade da
madaukakin mamaki daga can naji yan uwana
suna furta Alhamdulillah. . ni ma sai alokacin
nafurta Alhamdulillah cikin muryar data dashe
alamar kuka dansandan yaci gaba dabayani
hakika kamanni ne sak kwabo da kwabo da ita
wacce ake neman maitsanin kama wanda Allah
yabayyana tsantsar ikonsa akansu ayau muka yi
dacen cafkesu acameroun zasu hau jirgi sutafi
south africa yallabai ita wannan itace ainihin
wacce ake nema yafada yana nuna wata daga
cikin matan dasuka shigo dasu cikin daka tsawa
ya umar yace ke bude fuskarki! yakwada mata
kulki Araina nace karamata shegiya kinsaka ni
abala'i iri-iri dazafin nama tasaka hannu tayaye
rigar fuskar da take fuskarta kafcecen bakin gilas
ne a fuskartata amma hakan bai hana ni ganin
fuskarta ba . yadda kasan tawa fuskar aka dasa
ajikin tata tasaka zara zaran hannunta tacire
gilass din tayi wulli dashi tana ciccizon bakinta
kaidaganinta ka ga wacce bata shakka,duk abinda
zaibiyo baya bani kadaiba duk mutanen wurin
cikin matsanancin al'ajabi suke kallonmu ni kaina
nazare ido kawai nake ina nunata itama kuma
nuna ni take fuskarta dauke da tsananin mamaki
to wai yatake ne? mai shari'a alkali abbana ya
razana balle ummana data kasa zama bakinta
sosai yake bude ta ma kasa rufewa don tsananin
mamaki na raya araina "Tabbas hukumullah
la'ajaban". . Bayan tsawon mintoci da dakin
shari'ar yabakunci hayaniyar mutane alkali
Abbana yamayar da glass dinsa yakuma dakatar
da surutun ta hanyar buga gudumar kotun da
karfi nan take kowa ya,nutsu aka kuma kasa
kunne don cigaba dasauraron shari'ar kowa
yanason sanin dalilin wannan matsanan ciyar
kama tamkar irin yaran nan yan biyu masu kama
daya kamar kwabo da kwabo . da bature yake
kira IDENTICAL TWINS.Abbana ne yadubesu
dukkansu sannan yamayar da kallonsa akan
carbon copy{mai kama dani} "baiwar Allah
konace bayin Allah dagaske ne kune kuka yiwa
minister sata bayan yaudarar sa dakukayi kuka
kaishi hotel kuka bashi maganin barci bayan yayi
barcin kukayi amfani dawannan damar kuka dauki
hoton tsaraicinsa ma'ana kuka daukeshi tsirara
kuka kuma watsawa internet don ku bata masa
suna bayan kun masa awon gaba da kudadensa
dalolin amurka? kodayake kafin nan zanso nasan
sunayenku sunan uba ko wakili jiha ko unguwa?"
Abba yafada yana duban su gaba dayansu suka
shiga kallon junansu daya bayan daya sannan
suka nuna mai kama dani da alama,itace zata
wakilcesu ba tare da tsoron komaiba tawani
watsa hannayenta tayi far-far da idonta "sunana
SHANY,haka nataso agidan dana rayu naji ana
kirana Aisha ne cikakken sunana sunan uba ko
wakili kuwa bansan ko daya daga cikiba ko kuma
nace bani dashi sam..." . Gaba daya naga yan
gidanmu sunsake zaro ido sun zubamata Abbana
cikin matukar mamaki yace . "Kamarya ya?
mutuwa yayi ko kuwa sallamaki yayi kika koma
rayuwar bariki?" Tabe baki tayi tare da kada
harshe tace "lala lala,ni yar tsuntuwa ce kamar
yadda wadannan dukkansu yantsuntuwane muna
karkashin kulawar wata mata" Abbana yasake
xuba mata ido yace yar tsintuwa kamar yaya?
inakallon yarinyar sai data dan yamutsa baki da
alama ta fara kosawa datambayar sai dai inaji
kwarjini yayi mata don haka tayi kasa da idonta
tace kamar yadda kasani duk wani dan tsuntuwa
aibashi da sunan daya wuce shege. Dafarko
sunana Shany kamar yadda na sanar tun abaya
muna karkashin wata mata mai suna ATINE YAR
HARKA mutalatin da,biyar ne cif karkashin
kulawarta tunmuna yara tare da wadannan muka
taso wanda dama su sa'annina ne agidan
dukkanmu babu maicikakken asali hakan yasa sai
yadda tayi da rayuwar mu tun muna yara muka
tsinci kanmu acikin bautawa wannan mata
tamkar bayi haka muke agidan kalilan daga
cikinmu take warewa tasaka amakaranta wanda
kyansu yakai kyau ciki kuwa harda ni don tasha
fada wai ni BABBAN JARINTACE. . Nayi
makaranta tun daga nursery har primary da
secondary yanzu hakama ina jami'a tana bani ci
da sha da suturu masu kyau amma fa duk acikin
kudin damuke tara mata! shine kuma hakan baya
samuwa sai yarinya takai shekara sha uku
alokacin dazata ce wai tasan zata dawo mata da
abinda takashe bata sakamu yin karuwanci saidai
tana koyamana dabarun damfara ta yadda zamu
yaudari mutum mukwace dukiyarsa mugudu
yaudarar maza muke yi sosai ta hanyar nuna
tsiraici ma'ana shigar banza wanda da zarar
mutum yayi katarin haduwa damu sai ya fada
tarkonmu saimu yasheshi mugudu club-club
muke zuwa da inda mukasan attajirai da manyan
gwamnati suna zuwa har dai kawo wannan
lokacin da tsautsayi yakaimu muka yaudari
wannan ministan Abinda yasa muka yada
tsiraicinsa kuwa a internet yar'uwarmu yayiwa
fyade..." daga haka taja dankaramin bakinta ta
tsuke alamar bazata,sake cewa komai ba kotu
kuwa tuni takacane da hayaniya mai shari'ah
abbana yayi rubuce rubuce sannan yadago yana
kallonta yanzu ina ita uwar dakin taku take . dan
rausayar dakanta tayi kafin tace tana abuja tun
ranar da abin yafaru tace muje muyi takanmu don
minista yakai abin ga hukuma ita kuma bazata
iya shari'ah da gwamnati ba da dai wanine da ta
tsaya mana har iya inda karfinta yakare abba
yasake gyada kai yace yanzu ina kudin?"yana
wajenta dama ita ake bawa"Abba yasake yin
rubuce-rubuce sannan yadago yakalli jamian
tsaron dasuke wajen "sakamakon kotu takama
yaran da ake zargi da aikata,wannan laifi kotu
tawanke aisha daga zargin da ake mata bisa
rashin sani da akasin da akasamu na
matsananciyar kama da Ayshan take da ita wacce
ake zargin takuma yi umar nin tsare Shany da
yan uwanta tare dakawo uwar dakinsu tahanyar
bin kwatancen dasukayi kotu ta dakatar da
wannan shari'ar har zuwa 1/5/ 2016,alokacin da
muke sa ran ganin wannan uwar dakin nasu ta
bayyana kanta akotu" daga haka yabuga
gudumar kotu daukacin jama'a kuwa suka amsa
da koooootu" . Tundaga nesa nake hango fararen
hakoran ustaz tare da yan uwana da ummana da
suke fara'a saide nayi matukar mamaki danaga .
Idanun mamina jawur alamar tasha kuka Na
ayyana meyaparu kuma?itada yakamata tayi
murna kuma take kuka Nazata zangan ta tana ta
fara'a sakamakon yau mun wanku daga zargin da
akemana tas. . Yau inason ganin mutane dayawa
naga dawanne idon zasu kalleni bayan tarin
abubuwan dasuka faru abaya babu wanda
nakeson gani fiye da,ya usman masoyin gaske
yadda yan jaridu suka baibayeni da tarin
tambayoyinsu hakan yasa na saka kuka don
sanin bazan iya basu amsar komai ba fatana
kurum na hadu da mamina naji kukan me takeyi
ganin bazan basu amsaba hakan yasa suka juya
akalar tambayarsu gurin yan uwana kowa
hamdala yake koda Ahmad yaji labari. . Ni kam
duk basa gabana don dama nafada duk ranar da
gaskiya ta bayyana akwai kallo da yawa Ganin
Abbana yanufo wajenmu yana ta doka murmushi
hakan yasa na sulale na gudu akunnen .ya usman
na rada masa kaini gida.Sweet bros wallahi na
gaji da azama yaja hannuna muka fice daga
taron jama'ar bayan yashigar dani mota yana
murmushi yace Aysha kinga lamarin ubangiji ko?
dama nasanar dake kicigaba . da addu'a dasannu
gaskiya zata bayyana yafada yana jan motar
kafin mu isa gida saida yabiyadani ta shopwrite
ya saya min kayan amfani bayan yafitone
yakalleni Aysha inazan kaikine gidanki kocan gida
kike nufi? wani kallo nawatsa masa "gidana kuma
ya usman?ainagama auren ahmad ai da din ma
don ba yadda zanyine yasa nakoma gidansa
amma yanxu bamai tilastamini wallahi ya usman
dan murmishi yayi yace kibi komai asannu aysha
ta Gum nayi dabakina.Don ko kadan babu
maisakani komawa gidan ahmad yaushe? . ai
wallahi dolene yasakeni awannan karon kam ya
usman yana fakin naga dandazon motocin yan
uwana data Abbana data ahmad da alama tuni
sundawo fuskata a daure tamau nashiga gidanmu
atsaye cirko-cirko da alama suna jiran dawowata
babu wanda nakalla nayi hanyar kazamin dakina
dakin shirgi inda lokutan baya ummata,tace nan
ne makwancina tamkar ba uwata data haifeni ba.
. Inazama Abba yashigo yana dubana cike da
tausayawa,yace . Ayshatu mezakiyi a wannan
dakin dan Allah tashi maza.AGA RAYUWA book 3 part 2
NAGA RAYUWA book 3 part 2
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 13:55
Bani da damar yimasa musu amatsayinsa na
mahaifina amma wannan lokacin kam sai na dana
naraya azuciyata cikin taushin kalami nace Abba
ina zani ina ce nan din shine makwancina dakuka
za bamin? Abba yadurkusa gabana ya dago kaina
"Ayshatu komai yafaru abaya Inaso kidaukeshi
amatsayin kaddara ma kinki Aysha mu
mahafankine kituna kafin fara abin wanne ga tane
bamu nunamiki agidannanba? . ko wani uba ko
uwa kaiga duk wani maisonki ma dole yaji,yataba
amma ba tsanabace Ayshatu mun yine don
samun nutsuwarki Ayshatu tunda abin nan yafaru
ban taba fashin kaiwa Allah kukanaba akan
yashirya minke...." Wani kukanne ya kwace min
nace "Amma Abba kasani ankuntatamin an
wulakanta ni duk akan laipin daba nawaba Abba
baku taba tausaya minba akullum kallon tsana
nake gani muraran,a idonku babu wanda yaji
tausayina sai Ya usman da mamina da ita ma
aka dora mata laifin da batajiba bata ganiba
yanzu Abba dawane idon za ka kalli mamina?
Abba yaruntse idonsa Nasani tabbas al'amarin
yagirmama azuciyarsa ahankali ya bude idonsa .
"Ba ni da idon dazan kalli fateema Ayshatu
tabbas nayi nadamar abubuwan dasuka faru da
ina da iko dana goge duk abinda suka faru abaya
Ayshatu na zalinceku kiyi hakuri don Allah
kiyafemin duk hakan yafarune akan rashin sani
Don Allah kiyafemin..." Take naji zuciyata
takaraya mahaifina ne yazanyi dashi? tilas na
hakura,kasa nayi dakaina badon banyafe ba sai
don tsananin tausayin Abbana waiyau shine yake
kwantar da murya akaina bayan nidin.Ikonsace
yana da dama ya aikata hakan koma fiye
dahakan komafiye da hakan koda baya zargina da
aikata kowane laifi Balle akan abinda ake kyutata
zaton nice na aikatashi muryata na rawa nace
Abba kadaina rokon yafiyata nidin wacece? . Abar
ikonka cefa? kana da dama ka aikata fiye da
hakan akaina..." Abba yadaga kai yace Na sani
kedin yar albarkace ubangiji yayi miki albarka ya
mike tashi muje dakin ummanki kiyi wanka kicire
wadannan tsinannun kayan murmushi nayi
namike Har a lokacin suna nan afarfajiyar
gidanmu Ahmad sai zabga min murmishi yakeyi
niko kodigon fara'a babu atare . dani na tattare
fuskata nahade dakin umma nafada natarar da ita
a toilet fitowa tayi tana murmushi tace kinshigo
Ayshatu shigo kiyi wanka nahada miki ruwan
wankan cikin tausasawar murya takemin magana
nima tausayi tabani hakan ya sa nace to
ummana Nafada ina murmushi Tunda nashiga
toilet din nake faman dirzar fatar jikina tamkar
Allah ya aiko ni,nacuda yakai sau ashirin gashin
kaina kuwa haka nadunga dirzarshi har umma
tagaji tafara bugamin kofar sannan nabude nafito
umma tace wai! lallai kin dirzu dubi yadda fatarki
harja take murmushi nayi nace Badoleba umma
sai sati fa ake wanka wallahi nikaina har bashi-
bashin kaina nakeji Umma cikin tausayawa tace. .
Mungode Allah de dakomai yazama sai labari
zama nayi agaban dressing mirror din umma
nadau wani Nuetrogena body oil ina shafawa
kasan cewar lokacin sanyine banyi wani make-up
ba umma takawo wata riga sabuwa light Orange
colour mai kyau tabani nasa ni kaina nasan nayi
kyau gawata iska tana kada ni tanashiga kofofin
jikina da kuwa dauda ta cikasu dankwalin rigar .
nadaura akaina sannan na fito falonmu har
alokacin mutane ne dan kam agidanmu dukkansu
yan Zuwa murna Allah yakiyaye gaba ne dai dai
lokacin ya usman yashigo,yanayinsa yanuna
yanuna yana cikin matukar farin ciki yazauna
yana dubana da dan murmushin gefen kumatu
yace Aysha kije inji mijinki wani kallo na zuba
masa nace "Ya usman miji kuma?Aini banida miji
ahalin yanzu umma tadan dubeni tace banganeba
Aysha ya,usman yamike yanafadin "Rabu da ita
umarni nabaki kije yana sitroom yana jiranki
idanma zaku rabu bai kamata kurabu
tahakaba"ban mikeba sai da umma tace Aysha
usman nefa yabaki umarni idan da amana kuwa
usmanu baicancanci hakan daga wajenki ba
dasauri namike jin furucin umma nayi saurin
ficewa tamkar bazanyi sallama sai dai nadaure
nayi sallamar ya amsa idanunsa. . Acikinnawa
fuska ta daure nace masa lafiya malam gani ance
kana kira na yadago yana murmushi hade dacewa
to zauna mana my beautiful wife ba zama nazo
yiba malam inada abubuwan yi acikin gida kuma
kada kasake kirana matarka matarka tana gida .
"Aikin daki ke haryafi kiran mijinki muhimmanci
Aysha? kuma da kikace kada nakiraki matata
yaushe nacireki amatsayin matata?nawaro idona
ina harararsa ko baka cireni ba kwanan nan
zakaji sammaci don wallahi saika sakeni mikewa
yayi ya iso gabana yasunkuya yana duban
fuskata madam dina babu murmushin nan mai
sanya ni nishadi?wai me yafaru ne? yaufa ranar
murnace tsaki nayi nace kadameni madam dinka
nacan gidanka wannan dai Ayshatu ce aysha
mazinaciya,karuwa,maibin yan fashi dafatan
kagane yanzu lumshe idonsa yayi yace please
ayshata forget the past nayi danasani banyi masa
magana ba saima juyawa danayi nashige gida
don kam alokacin ba na maraba da ahmad
sulaiman . Daddare kamar kowanne lokaci muna
zaune ayadda ake zaman cin abinci Abbane
yadubi umma "ina tsammanin wani al'amari game
da yarinyar nan maikama da aysha ina hasashen
ko daga tsatsonmu tafito don tsananin kamar ta
yi yawa kinsan kuma masu kamanceceniya da ita
adangi suna dayawa kasancewar ance dama da
kakarmu suke kama toshi,ne nake hasashen ko
ita . ma jininmuce don haka nake dada tsaurara
bincike akanshari'ar umma ajiyar zuciya tayi
sosai kafin tace ashe bani kadai wannan abu
yadama ba tsananin kamar yayi yawa kamar yan
biyun da ake kira IDENTICAL TWINS sai dai kuma
ai babu wanda yataba rasa yarsa adanginmu
Abba yaja gwauron numfashi gaskiya babu
wanda yataba rasa yarsa akaf zuri'armu ta
potiskum wallahi sosai nakejin yarinyar nan acikin
zuciyata tamkar yata kuma natausaya mata da
ita da yan uwanta matukar.Tausayawa . koda
anbincika ba zuri'ata bace nizan dauketa da
sauran yan uwanta da ba asamu danginsuba
umma tace gaskiya hakan yakamata kayi tunani
mai kyau ubangiji yataya ka riko nikuwa nasan
zancensu baishigeniba haushi yaringa bani dalili?
sune silar fadawata duk wani bala'i don haka
sam banji wani ko digon tausa yinsu ba .
KASHEGARI Tun danatashi naji zuciyata
takwadaita da son ganin mamina baiwar Allah
don haka bayan dana karya naroki umma tabarni
naje umma tace . "ayshatu yar gidan mami nina
isa nahanaki zuwa gun maminki? kije amma dai
karki . dade tunda mutane suna zuwa miki murna
har namike tace aysha ki tambayi ahmad kinsan
hakkinsane yasan da fitarki gabadaya nabata
fuska nace umma wanne irin na tambayeshi
kuma? nifa umma wallahi bazan koma gidansaba
don haryanzu abinda yayi min banmanta ba
kobama hakaba nibana son zama da kishiya inje
inawani raba miji da ita baki umma tasaki tana
kallona tace tabdi bashakka aysha kanki daya
kuwa? . bazaki.Raba miji dawata ba to kinci
gidanku idanzaki sauke wannan tunanin banzan
tun wurima gwanda kisauke don ba inda zaikaiki
sai tashar wahala menene laifin ahmad dazakice
bazaki koma gidansa ba? naja kwafa nace umma
bakiji irin maganganun daya dunga dankaramin
ba duk akan laifi daba nawa ba sannan yayi min
kishiya,batare dasani naba mahaifiyarsa babu
tsanar dabata nunamin ba sannan yanzu ace
nakoma auren sa? . Allah yakiyaye umma tace
duk naji aimuma iyayenki duk munmuki laifi
meyasa mu kika yafe mana? murmushi nayi nace
kudaban shi daban bari nayi sauri natafi ina isa
gidansu mami kamar kowanne lokaci hajiyarsu .
da kallon banza tatareni ko gaisuwata ma da
kyar ta amsa tana wani cin magani bankulata ba
illa ma cewa danayi mamina ta na nan? . hajiya
tawurgeni da wani kallon banza tace aysha
fatima ba uwarki bace sau nawa zangaya miki
banason ganin sillan kafafunki agidannan? Nidin
ma kallo nawurgamata don tsohuwar tafara
kureni,naturobaki nace dadinta ba wajenki nazo
ba kuma wallahi babu wanda ya isa yace mmina
ba uwata bace,Allah ne ya hada bazamu rabuba
ehe! na mike,ina mata,dariya nahaye saman da
mamina take ina hawa na juyo ina dubanta tarike
haba tana fadin ba shakka nayi nata gwalo
nashige dakin mamina.WA novels / NAGA RAYUWA book 3 part 3
NAGA RAYUWA book 3 part 3
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 13:58
Wannan karon tsaf na sameta azaune tana
karanta wata mujalla bataji shigowata ba
kasancewar kofar abude take sai da taji nayi
tsalle ajikinta afirgice tamike tace Ho ho ho!
aysha sam bakya girma kwabe fuska nayi kamar
zanyi kuka nace mamina mekuma nayi? tajawoni,
jikinta tana cewa babu abinda kikayi sweet
daughter me yafito dake madadin kizauna kihuta
daga fitowarki jiya shine kika debo kapa kika taho
yau?. Hawayene yazubo min daga idona mamina
tace subhanallah meya faru ayshatu? Nace mami
na wallahi gidan babu dadi tun da babu ke Don
Allah mami yaushe zaki dawo gidanmu? . Dif
naga mamina tayi da fuskarta tamkar dai ba ita
ba ce take annashuwa yanzu tace "aysha ni da
gidanku har abada babu sunan dana sakawa
gidanku illa BAKIN GIDA anyi min abinda ba ataba
yimin ba arayuwa kedin ma dandole nake kulaki
saboda kaunarki ajinina take daga Rabbil Izzati
idan ban da haka abinda akamin akanki yaci ace
tuni nayi watsi da al'amarinki tobazan iyaba
konayi kamar nafita harkarki sai naji nakasa jinki
nake tamkar kedin jini . nace wane irin cin
mutunci ne abbanki da zuri'arku basuyimin ba?
hattasu muhammad usmanu ne kawai bai zargeni
ba,kuma hargidan nan yazo yana bani hakuri don
haka babu abinda zance masa,sai kuwa
ummanku macece jaruma da ta dau duniya ba
komaiba don tabbas hakika yar uwa ta daukeni
har nan gidan tazo tana bani hakuri" shiru nayi
sosai nagaza,cewa mami komai don kam nida
kaina na sani anci zarafin,mami akan laifin da ba
nata ba Nadade sosai,don sai karfe uku natafi na
sake baiwa mami hakuri . murmushi kawai tayi ta
ce aysha ni da gidanku har abada" Banga,laifin ta
ba don kam anyi mata laifin dayaka mata tadau
kowane irin hukunci kamar.Yadda nima nasha
alwashin bazankoma gidan Ustaz ba don nima
yashaka min maganganu masu kama da kamshin
mutuwa ina isa gida natarar da galleliyar motar
Ustaz akofar gidanmu tsaki naja azuciyata nace
sarkin naci Baya cikin motar Aharabar gidan
nagansu azaune shi da ya farouk gaba daya basu
isheni kallo ba donsu kansu yayyen nawa bawani
kallon arziki nake,musu ba Adage nake kallonsu .
Dalili?lokacin da abin yafaru babu wani wanda
yabawa iyayena hakuri acikinsu sai ya usman
don haka gaisuwa ma dakyar nake gaishesu akan
tilas Har nawuce ya farouk yataso dasauri ya
biyo bayana Ahankali yakemin magana Aysha
kina kallon mijinki kika shareshi tundazu fa
wajenki yazo yana jiranki wani kallo na watsa
masa hakan yasa baici gaba da magana ba Nace
yaje yanemi matarsa amma bani ba don ni
nawuce tunaninsa daga, haka da azama najuya
zanshiga gida ji nayi an riko hannuna ko ba
afadaba nasan Ahmad ne don kuwa ga
mayataccen kamshin turarensa nan ya cika
hancina da azama nafuzge hannuna fuskata
ahade nawurga masa wani wulakantaccen kallo
nace for the last time malam kada kasake
yunkurin hakan..." mekike nufi? kina matsayin
matata kiyimin warnin akan jikinki? kada ki manta
fa mallakina ne yafada yana sake,wurgamin kallo
tsaki nayi nace kaidin wai wane irin sarkin
nacine.? Sau nawa zangaya maka kabar kiran
aysha amtsayin matarka How I wish anaganin
zuciya nabude maka kaga matsananciyar tsanar
da nayi maka" . Baki asake yadubeni da alama
yana mamakin kalamaina ne murmushi yasaka. .
Yace aysha kenan Ni kuma da ina da hali
danabude miki tawa sirrin zuciyar kin ga
soyayyarki zalla da tacika ta muryarsa atausashe
yasake cewa Allah ne yajarrabeni dasonki da ina
da iko da na rabu dake tunda hakan shi ne
burinki Ahankali yaja dabaya yafice ko kadan bai
bani tausayiba don ni din ma baitausa yamin ba
alokacin da nake neman ya a gajeni alokacin
yabude min faifan rashin kirki da wulakanci Naja
tsaki na shige gida ina guna guni . AN KOMA
KOTU . ranar da za akoma kotu da wuri muka tafi
da sam bazanje ba sai dai nashirya naje saboda
inaso ayi komai akan idona mune asahun farko
akotun kotun ta dinke da jama'a kowa nason jin
karashen shari'ar ne yakawo shi ina hango
Ahmad yana ta sakar min murmushi ni kuwa
dauke kaina nayi tamkar banganshi ba wanda
rabon da naganshi tun ranar daya ritsani
aharabar gidanmu saboda koyazo bana fita ko
umma tace nafita rokon ta nake ince tabari na
huta Abba ma kuwa bai tilas taminba tsawon
mintuna . Ashirin muka dauka akotun kafin alkali
Abbana yashigo yana, zuwa kotu ta samu
bakuncin shiru da kanshi yayi umarni afito masa
da,su shany wadanda aka tsare awani daki daya
bayan daya suka dunga fitowa Shany ce atsakiya
gaba dayansu cikin.Wasu dogayen hijabai dasuka
saukar musu har kasa ammafa fuskarsu ta nuna
bazaman dadi akayi akotunba Abbana yakalle su
daya bayan daya . sannan yace da jami'an tsaro
sufito da da mama Atine wacce akayi nasarar
kamo ta kwanaki biyu da suka wuce kanta akasa
tafito amma daga ganin ta ka ga cikakkiyar yar
duniya mutane kuwa suka zuba mata ido ciki
kuwa hardani da nake mamakin karfin hali irin
nata . nakuma yi tur da ita harcikin zuciyata Allah
dai yashirya musulmi Abbana yace kece Atine? ba
ta re dabata lokaci ko tsoro ba ta amsa da nice
Atine kinsan wadannan yaran dasuke gabanki?
Nan ma cikin comfidence ta amsa Nasan su."
Abbana yace mene ne hadinki dasu? dan tabe
baki tayi sannan tace akarkashin kulawata suke
karkashin kulawarki kamar ya? kina nufin
ya'yanki ko ya'yan yan uwanki . kike riko? Anan
kam tsit tayi takuma sunkuyar dakanta azuciyata
nace munafuka Abbana yadan girgiza kai yace
malama atine muna sauraronki koko zargin,da
ake miki gaskiyane kamar yadda yaran suka ce
babu wata alaka atsakanin ku dukansu yan
tsintuwane? ta daga kai alamar eh yace kina
nufin dukkansu tsintarsu kikayi? to a ina? kuma
da yaushe? awanne gari kikatsinci har mutum 35
musamman waccen yarinyar danake hasashen jini
nace saboda matsananciyar kamar dasuke yi da
diyata,Aysha dasauri takai dubanta,kaina ta sake
mayar da dubanta akan yar rikonta Shany atake
naga tasaka,hannu tana yarfe.Gumi alamar rashin
gaskiya kuru-kuru yabayyana afuskarta . Abbana
yadanyi rubutu sannan yadago yasake ce mata
malama atine kinyi shiru inason sanin labarin
wannan yarinyar shany da yadda kika sameta
gaskiyarki ce hanya mafi sauki dazata kubutar
dake karya kuwa itace zata tsunduma ki akogin
nadama matukar na,gano gaskiyar lamari
Ahankali ta dago kanta sanin cewa babu mai
kubutar da ita hakan yasata shiga rattabo bayani
"kamar yadda . ka fada dagaskene wadannan
yara tsintarsu nayi wasu kuma aasibiti nasamesu
shekaru da dama dasuka wuce nima karkashin
wata mata nake da sana'arta kenan . FATAUCIN
YARA MATA . kai har da mazan ma idan tasamu
faraga "asibitoci takebi don samun yara marasa
galihu kodai shegu kokuma wadanda iyayensu
sukayi accident suka mutu akarasa danginsu
kokuma idan anhaifi yan biyu tayi cinikin daya da
nurses ko likitoci subata daya batare da mai
haihuwar ta saniba Nikaina a irin hakan tasameni
ma'ana ni shegiyace duk abinda takashe mana
muna yara to idan mungirma fanshewa take
akanmu kodai ta mayarmu karuwai kodai tayi
futaucin wasu zuwa wata kasar ta yadda za
adunga bata,kudi duk karshen wata wadanda
tamayar karuwai kuwa da zarar sungirma andaina
yayinsu ba ta samun komai atare dasu to sai ta
sallamesu sukama gabansu don takan fada ba a
aikin banxa akano . A irin haka nima nafito Ne
acikin wadanda aka sallama nima nakama gidan
kaina saina tsunduma kaina cikin harkar da takeyi
na shahara sosai harnaso nafita nima asibiti nake
. zagayawa aduk cikin kasashen Nigeria wannan
yarinya da kake magana ina,matukar alfahari da
ita aduk cikin yarana saboda tana da kwazo da
basira wayo da hikima shiyasa bana manta
tarihinta . A ASIBITI NA SAYO SHANY.... . Gaba
daya naga abba yadago yana sake kallon ta
muryarsa na rawa yace mata wa...wanne...wane
asibitin? shiru tayi da alama,tatafi tunani sai can
tazaro wayarta,ta kunne tashiga bincike kotun
kuwa zuwa lokacin tuni tadau kace nace har
saida Alkali yatsawatar sannan Atine ta dago
kanta tace Na sa mota a . NASHE SPECIALIST
HOSPITAL . aranar lahadi 17 gawatan july
shekarar1995..." gaba daya naga Abbana yazaro
ido umma kuwa arazane tamike tana nuna Atine
da yatsa muryarta na rawa,kincu.Cemu... .
tabbas wannan yatace jininace! ranar dana haifi
ayshata kenan kuma a asibitin nashe..." novels / NAGA RAYUWA book 3 part 4
NAGA RAYUWA book 3 part 4
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:04
Gaba daya hankalin jama'a yakoma kan umma
Abba ne yadaka tar da umma tahanyar yimata
umarni tazauna umma tazauna tanajan
"Innalillahi" Ni kaina bugun zuciyata alokacin
yakaru Abba yace Atine ina jinki Awajen wa kika
siyeta? likita? ko nurse? shiru tayi har saida
yadaka mata tsawa,sannan tace awajen likita ne
bisa jagorancin wata mata "wata mata wa?
yasunanta? Abba yafada cikin matsanan cin
mamaki Girgiza kai tayi tace gaskiya na manta
saidai na bincika shiru . Abba yayi yashiga
rubuce-rubuce sai can ya dago yace ina
tunanin.Tilas sai annemo matar nan sannan kotu
za ta san hukuncin dazata yanke matar ce da
likitan zasu tabbatar mana da shany diyar wace
ce don haka asakamakon haka kotu ta dage
zama zuwa nan da wata guda za atsare Atine har
zuwa lokacin kuma kotu ta ba da belin yarancan
tunda ga babbar me lefi ankama sai dai zasu biya
minista makudan kudaden da suka daukar masa
idan yana bukatar hakan koda muka isa gida
jikina asanyaye nake jan kafata ina lura da umma
ita ma nata jikin asan yaye yake matuka . har
raina ajagule yake gaba daya fatana daya kada
Allah yasa zargin danake yatabbata bakomai
kuwa nake tunani ba sai kada Allah yasa
MAMINA tana da hannu dumu-dumu acikin
wannan shari'a ba idan hakan ta faru ya
makomar mamina zata kasance? wasu hawaye
naji sun sulmiyo min. . haka na kwana da zancen
azuciyata da safe ma ko karyawa, banyiba
nasamu umma dazancen murmushi tayi tace ni
ma ina tsoron faruwar hakan sai,dai kunyi daya
da abbanki shima zargi da hasashen dasuka
shiga zuciyarsa kenan sai dai zankwabeki kamar
yadda na kwabe shi kada ku daga zan cen nan
wani yaji don ba lallaine tunanin yaxama gaskiya
ba amma ya,rantse idan dasaka hannun ta bazai
mata,sassauci ba" Ahankali naja numfashi hade
da furta kai jama'a duniya abar tsoro ce . wallahi
sam hankalina yagaza kwanciya saboda tsoron
kada akama mamina da wannan gundumemen
laifin hakan yasa nayi saurin shiga wanka ina
fitowa, ko mai bansha fa ba nazira doguwar riga
ta da hijab Adaki nataradda umma karya naimata
akancewa zanje gida nadebo wasu kayana bataki
ba sai dai tacewai natambayi mijina kamar
nafasa zuwa sai dai kawai,natura masa, text
nasanar dashi zanfita, banga amsa ba amma
haka nashir gama umma karya nace yace sai
nadawo . Daga nan nasaka kai ko direba
bannemaba don ba na so asirina yatonu,hakan
yasa natare adaidaitasahu . . sai Nasarawa
gidandsu mamina da sauri nafada gate,din gidan
bayan na sallami mai adaidaita sahun A falo na
sami hajiya da mami wannan karon hajiya da
walwala fal afuskarta ta amsamin har mamaki
abin yabani mamina kuwa tashi tayi ta rungumo
ni tana fadar oyoyo ayshata . nidai murmushin
yake nake saki bayan munshiga daki mamina
tadubeni tana murmushi ayshata ya aka kare da
zaman kotu? wannan karon tun da naga kintsira
nace to mekuma zankoma nayi? dan murmushi
najefeta.Dashi "Aikuwa da kinsha kallo don
wannan yarinyar dai ana kyautata zaton nida ita
twins ne...." da sauri mami tazaro ido tace Inji
uban wa kuma? Nagyara zama cike da mamakin
irin razanar da mamina tayi nace Inji matar data
rainesu ta shaida haka Don kuwa rana daya da
lokaci da asibitin da aka haife mu duk dayane
matar ta tabbatar siyenta tayi a asibitin bisa
jagorancin wata mata" Sake firgita tayi tace
What? kina nufin ta fadi sunan matar? . girgiza
kai nayi nace kodaya sai azama na gaba Abba
yace lallai anemo wannan matar da likitan don
sune za su . ba da tabbacin komai mamina
zagaye ta shiga yi a dakin idan ba idona ba ne
yagaya min sai naga kamar gumi take sai can
tace Allah ya kyauta amma hakan da mamaki
matukar gaske Ban dade sosai ba nabar gidansu
mami yanzu kamzuciyata ta aminta,da zargina
don haka na ratse wani lungu na sha kuka na
Innalillahi kawai naketa ja harna isa gida sai
danaje kofar gidan sannan na tuna karyar dana
shirgawa ummana nacewa, kaya zandebo don
haka dasauri najuya nanufi gidansu Asma'u Allah
yataima keni tana nan Nadebo kayanta sannan na
nafo hanyar gida Adai-dai sabon gidansa
nahango shi da wannan kodaddiyar matar tasa
da alama fita zasuyi haka, kawai sai naji wani iri
araina bansaniba ko kishi ne oho. . Na sa kai zan
wuce ba tare da na kulasuba amma, namakaro
donjin Uztas nayi yana fadin yan mata ina kikaje?
Najuyo namasa wani irin kallo mai fassara kala-
kala gani nayi yasake wani fari yayi kyau fiye da
lokutan baya Ban saniba ko don yanzu hankalinsa
ya kwantane take naji wani kululu ya cake min
zuciya bansaniba ko kishine . kishin da ake fada
wucewa nayi ba ta re danace masa ko "A" ba
Babu abinda,yafi bani haushi saiganin danayi
Uztas kobi takaina bai sake yiba yakoma gurin
matarshi hakan yasa naji wasu zafafan hawaye
sun zubo min tabbas . KISHI MASIFA NE . ni
kaina kuma na san ina da matsanan cin kishi don
haka na sake damkewa araina na rabu da auren
Uztas har abada koda soyayyarsa zata zama
ajalina Azaune nasa mu ummana afalo ita da
shany mamakine yayi matukar ka ma ni danaga
shany da yan'uwanta kamar umma ta sani
tashiga rattabo min bayani Ga shany nan da yan
uwanta Abbankine ya kawosu suzauna kafin
agama shari'a asan yadda za ayi dasu murmushi
kawai nasakar musu nashige dakina saboda sam
bana jin dadi aduk sanda natuno mamina nakuma
tuno Uztas da shegiyar matarsa sai naji tamkar
na sa kuka sai yamma sannan na fito daga, daki
bayan da sakon Abbana ya sameni akan yanason
ganina Da sallama nashiga falon abbana ya amsa
cikin walwala da sakin fuska na durkusa agefe
"Kinga yan uwa ankawo miki ko? Don Allah
kidage wajen koyar dasu . addini don nalura babu
batun sanin addini a al'amarinsu sonake koda
angama shari'ar na roki alfarma gwamnati tabar
min rikonsu koda yakasance shany ba 'ya ta bace
balle ina ji ajikina Aysha su zama tamkar
yan'uwanki kada kiyi la'akari da laifin dasuka
aikata a baya duk ba laifinsu bane idan da ma
mai laifin bai wuce uwar rikon suba,Nadaga kaina
nace "Insha Allah abba zan kokarta yauwa aysha
nagode na sanke diyar albarkace wai yakukayi da
mijin ki batun komawarki? shiru nayi nakuma
sunkuyar da kai na ce Abba bazan.Koma ba Abba
yayi saurin zaro ido yace meyasa ayshata?
Nadan sake sunkuyar dakaina kafin nace Abba
lokacin da abin yafaru ba irin kyara da hanta rar
da baiminba duk ba ma wannan ba Abba gaskiya
indai zaku kyaleni nafi kaunar na zurfafa ilimina
shiru Abba yayi sai can yace shikenan.Aysha
bazanso takura miki akaro na biyu ba kije Allah
yazaba abinda yafi alkhairi.Tun daga ranar naja
su shany ajikina nake koya musu al'amuran
addini don nalura babu abinda suka sani idan dai
ba boko ba don kam sosai na . lura sudin kwarine
aharkar boko don shany idan tana turanci yadda
kasan baturiyar ingila tsabar kwarewa har
mamakin tanake yi idan naji tacanja harshen ta
Zuwa turanci wanda yake da dadin sauraro mun
shaku sosai kuma Abbana yawadata su da suturu
iri-Iri nima kuma na basu nawa idan muka zauna
waje daya da shany bazaka taba bambance muba
sai dai ita tana da rawar kai kuma ni ina da
tawadar Allah agefen kuma tuna ita kuwa akasan
habarta take dashi Idan suna ba ni labarin irin
damfarar da Atine ta sa su ina tausaya musu
matuka da gaske Atine ta cucesu sai dai abu
daya ne yan group dinsu ba su yarda dashiba
shine keta musu haddi har yanzu suna nan a
matsayinsu na yan mata cikakku ta wannan
bangaren kam na sa ra musu don bakaramar
dabara sukayi ba don budurcin mace shine abin
tinkahonta kuma babban jarinta Bayan ta gama
bani labarin nace Amma an taba kawo min wani
hotonki da anyi tsammanin nice (na ba ta
labarin) nace kusan dai nace a tsirara kike
ahoton.Murmushi suka saka gaba dayansu
sannan shany tace ina . yaudarar maza da jikina
saboda nasan ina da diri mai kyau sai ka
sakankance barci ya dauke ka sai mu yashe ka
tas mutafi haka nan sukayi tabani labarinsu na
Al'ajabi nayi na dariya kuwa na saki murmushi .
*** *** **** . KOTU . Ranar da aka koma kotu
wannan karon cikar haryafi na kullum don mutane
abin ba a magana ba dauki lokaci sosai ba Alkali
Abbana yazo aka fara wata shari'ar kafin azo
kantasu shany dasuke tsaye a layi reras cikin
shigar mutunci da ta dawo musu da martabarsu
da mutuncinsu na ya'yamata bayan dogayen
jawabai da Abbana ya bayar dangane da shari'ar
da aka guda nar sannan yadubi Atine yace
Dafatan atine kin gamsu da abinda kika fada?
Atine ta daga kai kamar kadan garuwa wannan
karon jikinta yayi sanyi sosai da alama ta hango
ba ta da mafita kokadan Abbana yadanyi rubuce
rubuce sannan yadago yadubi dandazon jama'ar
da suke kotun yace, "A sakamakon bincike da aka
gudanar kotu tabinciko likitan da yayi cinikin
yarinyar da ake kira SHANY sannan har ila yau
kotu ta binciko matar datayi.novels / NAGA RAYUWA book 3 part 5
NAGA RAYUWA book 3 part 5
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:05
jagorancin cinikin..." Sosai hantar cikina ta kada
don babu makawa nasan mamina ce don ban
ganta awajen ba babu mamaki tana can saye
acikin wani wajen Abbana yakalli dansanda
[police] yace Ashigo da likita kafin azo da matar
ko minti biyu ba ayiba police din yashigo da
likitan wani shirgegen kato baki-kirin da alama ba
bahaushe bane yazo kuwa yahau kan step din
fuskarsa tacika da furfura alamar yafara tsufa ya
tsaya shirim dashi Azuciyata nace cikakken mugu
Abbana yadago yana kallonsa nasan yana
mamakin tsananin muguntarsa ne naraba ya
da,uwa tana cikin jinin haihuwa Abbana yayi
gyaran murya kafin yace kaine Dr.Emmanuel? .
yadaga kai alamar eh Amsa nakeso naji da baki
ko baka jin.Hausa? inaji sosai ma muryarsa
tangararan tamkar bahaushen asali "menene
dalilinka na Siyarwa da waccan matar jaririya
tuntana cikin jinin haihuwa? sannan kuma muna
son mu san yarinyar yar waye? . zare ido yafarayi
da alama baisan dalilin da aka kaso.Shiba kenan
ya kuma dubi Atine sukayi kallon-kallo Abbana
kuwa ya daka masa tsawa hade da fadin . kai
muke sauraro! ina da record din komai agurina
don haka idan kana shirin yin karya ne kashirya
ta dakyau don kuwa ina da labarin komai ina dai
so ne kawai ka gaskata dakanka Emanuel yayarfe
gumi sannan yadago a sanyaye "yace tabbas da
na san wannan ranar za ta zo daban
aikata,abinda na aikata ba kaicona ni Ema ina
cikin tarin dana sani dana biyewa son zuciya yau
gashi yacillani cikin kogin nadama . " "sunana
Dr.Emmanuel ina aiki ne a nashe specialist
hospital tun tasowata na kasance mutumne ni
mai matukar son kudi hakan yasa sam banida
wani tunani sai na hanyar da kudi zasu shigomin
"Ba na manta wata rana data kasance ranar
lahadi ina zaune agidana dayake Ring Road,nayi
baki ba wasu baki bane sai wannan matar
yanuna Atine da ita da wata mata da ake cewa .
HAJIYA FATEEMAH" . Shikenan tatabbata .
MAMINA CE! . gaba na yasake faduwa jin gashi
sunanta ma ya bayyana Amma kuma ai fateema
da yawa da sauri nadaga nakalleshi jin yaci gaba
da labarin "Nayi matukar murna da zuwansu don
kuwa fateema akwai alheri ni likitan gidansu
babansu ne ALHAJI MUHAMMAD" Dasauri nadafe
kirjina donkuwa shikenan tafaru takare wallahi
maminace Allah sarki MAMINA why.? . meyasa
kika aikata hakan duk tarin alherinki agareni? .
Likita yaci gaba "Naba su lemo da ruwa sannan
na zauna ina fuskantar su don son sanin mene ne
yake tafe dasu bayan sun dan sha drinks din
sannan ita fateema ta dubeni tace Dr.ema shin
kasan dalilin Ziyarar damuka kawo maka yau? na
girgiza kai Akwai wata mata datake zuwa
asbitinku awo Abinda nakeso dakai da zarar
tahaihu kazare dan ko yar ka saka matacce idan
ansamu idan kuma ba a samu ba kasan dai
dabarar dakayi kasace abinda tahaifa ba ta re
da,kowa ya sani ba zaka yi wannan aiki akan
naira miliyan biyu Da sauri na zaro ido jin yawan
makudan kudi bakina a sake na sake maimaita
sunan batare da ba ta lokaci ba na amince da
bukatarsu Nakuma tambayi sunan matar batare
da bata lokaciba suka sanar da . MATAR IMAM
KHALIL . A take nagane ta don ni nake mata awo
da kaina nadaukar musu alkawarin ANYI
ANGAMA" Sam ji nayi na daina gani saboda
wannan.rikitaccen al'amari daya dumfaroni don
kuwa yanzu yawuce zargi tabbas,mamina ce
da,hannu dumu-dumu awannan KUNGURMIN
LAIFIN umma nahango tamike tsaye tana zare ido
kai duk . yayyena ma mike war sukayi yayin da
naga Abbana yana ta sakin murmushi nayi
mamaki matuka lallai ko ya ya kuke da kishiya ka
guji sharrinta Na ayyana araina hawayen tausayin
iyayena ya sulmiyo min daga ida nuna Abbana
cikin matukar hade rai yadaka wa Emmanuel
tsawa ina jinka! . Emmanuel kuwa yaci gaba da
ba da labarin mai kamar almara "Ba ta dau lokaci
tana zuwa awo ba rana daya aka kawota tana
nakuda wanda kafin lokacin idanuwana suna kan
masu labor.Na sha alwashin ko kashe wani jaririn
sai naje nasaka mata na dauki nata kuma naje
dakin jarirai wanda iyayensu suke guduwa suna
barinsu ko dai na saci na wani ko ma ya nidai
burina kawai kudi da murna ta na karbeta kasan
cewarta matar manya yasa na kaita special room
nakuma hana kowa shiga Ta sha matukar wahala
harta fita hayyacinta kusan awa biyu daga bisani
tahaifi yayanta yan biyu MATA ZALLA Tausayi ta
bani ganin irin wahalar da tasha hakan yasa
nabar mata 'ya daya ina murna ganin.Allah ya
taimakeni na gudu da daya ba tare da sanin ta ba
don lokacin hankalinta . Baya jikinta Bayan wani
lokaci sukazo suka amshe ta, sai dai nasanar
dasu gaskiya cewa yan biyu tahaifa sai dai ina
kokarin dauke dayar wani likita yashigo haka
yasa tilas da daya natsira wannan shine iya
gaskiyar abinda nasani" Gaba daya kotun aka
dauki kabbara bayan sauraren wannan abin
Al'ajabi Bayan rubuce- rubuce da Abbana yayi ya
umarci wani police yashigo da fateema zuciyata
taci gaba da bugu tamkar zata faso kirjina ta fito
nakumayi saurin sunkuyar da kaina don sam ba
naso nayi ido biyu da MAMINA acikin wannan
yanayin cikin wani zumbulelen hijabi MAMINA
take da kuma nikab afuskarta takuma rufe kirif
dashi Alama ce ta cewa ba ta muradin aga
fuskarta Abbana yadan dube ta ya girgiza kai
ahankali bakinsa yayi furucin . FATEEMA
MUHAMMAD wanda muryarsa bata bayyanaba
sannan yaja ajiyar zuciya yace Fateema zanso
kiyiwa kotu cikakken bayani da dalilin daya sa
kikayi silar da aka sace diyar mutane tun tana
cikin jinin haihuwa? "Bakomai yaja ba sai .
RAMUWAR GAYYA . Tafada da dakakkiyar
muryarta . Abbana yajinjina kai Ramuwar gayya
kamar ya ya? inaso kiyi wa kotu karin
gamsasshen bayani hannu tasa tayaye nikab din
da yake fuskarta Atake na zabura na mike wa na
gani? Hamdala nayi ga sarki Allah alokacin
danayi arba da ita . BA MAMINA BACE . madadin
inga fuskar mamina kamar yadda nake zato a'a
wata mata na gani fara da alama fulanin dajice
Don naga tsagun fulanin atare da ita sai dai daga
ganin ta ka ga cikakkiyar 'yar duniya ina kallon
yadda umma itama tahau zare ido tana nuna ta
da alama ta shaidata don naji ta ambaci sunanta
da fateema fulani Abbana yayi rubutun da zaiyi
sannan yadago yadubeta fateema munaso muji
dalilinki nacewa ramuwar gayya kikayi kuma
waye ya miki laifi da har kike ikirarin kinyi
ramuwar gayya ta hanyar illata rayuwar yarinyar
da bata san komaiba? . Azafafe tadubeshi "I dan
kai kamanta abubuwan dasuka faru abaya Imamu
ni bazan manta ba komai yana cikin kwanyata Ba
irin rayuwar da ban fa da ba duka adalilinka da
furucin 'yan kauyenku Imamu wane irin wulakanci
ne banganiba acikin gidanku . duk adalilin nace
inason ka zan aureka..." Tafada tana.Huci
fuskarta ahade tasake cewa ko yanzu kasuwa
tatashi wallahi dan koli yaci riba Abbana yace
"Duk munji fada min dalilinki nasace yarinyar da
kika sa akayi kowa yaji" Taja ajiyar zuciya
sannan ta dubeshi "ya zama dole nafada kodon
duniya tashaida sunanka MAYAUDARI danginka
kuma AZZALUMAI . "sunana Fateema muhammad
nida iyayena mazauna.Potiskum ne amma cikin
kabilar IBRA munta so matsayin unguwa daya ni
da su Imamu duk da ba wata alaka da take
tsakaninmu saboda kasancewar mahaifina
akabilar Ibra mahaifiyata kuma yar jihar yobe ce
itama sai da aka kai ruwa rana kafin iyayenta su
amince ta,auri babana duk a dalilin kasancewar
sa ba bahaushe ba mahaifina mutum ne mai
nagartattun halaye kowa yashaida hakan Bacin
rai ne yasa yabaro can kabilarsu yadawo
potiskum da zama ya ce mamana acan garinsu
bashida kowa tuni iyayensa suka mutu kuma
bashi da yan uwa sai yan'uba Akwana atashi
cutar ajali ta riski mahaifina bai wani dade yana
ciwo ba yamutu yabarmu da . tarin tashin hankali
saboda duk kauyen ba asonmu Ana haka
kwatsam mahaifiyar mu ita ma tafara cutar ajali
Zuwa lokaci kalilan tace ga garinku nan wannan
mutuwa ta daga hankalinmu nida yayana muftahu
da, kanwata samira shi kenan daga mutuwar
mahaifiyar mu sai rayuwa ta sake juya mana
baya ba wanda yake ta,tamu agarin nan wani
lokacin abincin dazamu ci ma gagarar mu yakeyi
ganin zaman hakan ba zai yiwu ba ya sa ranar
nayanke shawarar shiga gida-gida neman aikatau
Alokacin shekaruna sha biyar Duk gidan da naje
ban samu ba har na sare zankoma gida sai
natuna da gidan maikudin garin wato gidansu
Imamu Atake awajen Zuciyata tayarje min naje
gidansu imamun Nakuwa isa bakin gate din gidan
har mai gadin ya fa ra yimin hargagin bazan
shigaba sai ga mahaifin Imamu nan dattijon arziki
shi ya leko yake tambayar maigadin yadda akayi
maigadi yace Rabu da ita Alhaji irin makarya tan
mutanen ne masu basaja wai aiki tazo nema
kona wanke-wanke Alhaji yadubeni yace baiwar
Allah daga ina kike? Nayi kasa dakaina nashiga
rattabo.A RAYUWA book 3 part 6
NAGA RAYUWA book 3 part 6
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:07
masa daga inda nake Alhaji yagirgiza kai yace
kice yar gidan muhammadu mai hula ko? Na
daga kai Alhajin yace Allah yajikan muhammadu
mai hula shigo ciki muje wajen hajiyar Tun daga
bakin tsakar gidan nafara jin hargagin fadanta da
alama da ya'yanta take nan take naji zuciyata ta
harba nayi fatan Allah yasa tayi maraba dani
Alhajin da sallama yashiga hakan baisa tarage
zazzaga kwandon masifarta ba tabi ni da kallo
kafin tace lafiya Alhaji wannan bakuwar wace?
sannan yakai duban sa kan Imamu yace Babana
me kayi ne take zazzage maka fada? jinayi
hajiyar tace min ke daga ina ban waye fuskarki ba
Nayi kasa dakaina ina wasa da zoben hannuna
Alhaji yace Aiki take nema na ga kuma kina da
bukatar yar aikin tun da waccan tatafi shiyasa
nace tashigo tsaki tayi takuma zabga min harara
tace yo don ina bukatar yan aiki nace maka yan
mata nake nema? . Alhaji dasauri yace hajiya
kidai duba marainiya ce diyar muhammadu mai
hula haba ko danaji kace min diyar tubabben
mutumin nan ce shiya sa naga fuskar tayi yanayi
data kabilu. . To na amince amma da sharadi
idan na samu dattijuwa zata dire min aikina don
ni ba na son kwashe-kwashe cikin kwashe-
kwashen ace har kabilu kawai kajanyo min
jangwan-gwan Nidai farin ciki yamamaye ni danaji
ta yarda ta amince Bawani aiki bane shara ce filin
tsakar gidan sai wanke-Wanke kasancewar matar
gidan mace mai kazar- kazar ba komai take zama
jagwab ayi mataba Da kadan-kadan shakuwa ta
fara shiga tsakanina da imamu wasa-wasa sai
nafara jin matukar son imamu azuciyata wanda
har idan ban ganshi ba banajin dadi Har wata
rana takai natambaye shi da kaina Imamu inajin
soyayyarka araina kaifa? . murmushi ya saki hade
da dage gira daya daga cikin abinda yake sake
burgeni dashi yace fateemah ina matukar sonki
sai dai kafin haduwata dake ina soyayya da wata
yar'uwata Amma hakan bazai hana ni aurenki ba
kidaici gaba da addu'a jikina ne yayi sanyi don
nasan mawuyacin abune hakan yatabbata tunda
dai ya sanar da ni yar'uwarsa ce shikenan na
kaddara azuciyata ba zan auri imamu ba Tafi-
Tafi soyayyar Imamu tana sake . bunkasa
azuciyata duk da ina kokarin naga na yakice
hakan amma abu ya faskara kwatsam wata rana
ina cikin aikin yamma sai naji hajiya tana batun
sa ranar Imamu tana aika yara gida-gida akansu
je sufada Nashiga wani lungu agidan don kuwa ji
nayi hawaye,na surnano min kwatsam sai ga
imamu ya zagayo yakama hannuna muka shiga
dakinsa. Rarrashin duniya da ban ba ki babu
wanda bai,yimin ba amma na gagara yin shiru har
sai da yayimin alkawarin aure na bayan bikinsa
sannan hankalina ya kwanta Haka inaji ina gani
akashiga gudanar da bikin Imamu duk da zuciyata
na tukukin haka na hakura ina kuma taya imamu
murna Bayan bikin Imamu da amaryarsa sai naji
labarin wai a kano zasu tare, hankalina ya tashi,
amma Imamu yasake jaddada min alkawarin aure
kafin tafiyarsu hakan yakwantar min da hankali
sai dai ko da suka tafi Imamu bai sake
waiwayata ba ko ya zo kuma sai ya yi tahade
min yana wani cin magani harnagaji. Wani zuwa
da yayi nake tambayarsa ko ya janye kudurinsa
na aurena bawani ja'inja ya shaida.Min eh ya
fasa . Raina yabaci amma sai nasake tambayarsa
menene dalili? amsar da ya ba ni ta gigitani
domin cewa yayi fatima gaskiya ina matukar son
matata kuma tana jajircewa wajen yi min biyayya
ba na jin zan iya yimata kishiya domin yin hakan
tamkar kawo wata barazanane ga rayuwar
aurenmu zan miki addu'a Allah ya zaba,miki
abinda yafi alheri...." Wani kallo nabishi dashi
hawayen bakin ciki na zubowa akwarmin idona
ahankali na lumshe ido nace Imamu ka cuce ni
sai dai ina maka albishir da komu dade ko mu
jima sai na dau fansa" Wannan dalilin shiyajanyo
min koma wa rayuwar banza Na kuma kaddara, a
Zuciyata sai na yima ramuwar gayya wanda ake
cewa ta fi ta gayya zafi . kwatsam sai muka wayi
gari anshiga har anyi wa kanwata datake bina
fyade, lokacin yayanmu yatafi Lagos. Nayi kukan
bakin ciki kamar raina zai fita nakuma ja bakina
na tsuke ban gaya wa kowa ba saboda ba na son
zancen ya bazu a garin ina gudun kada sunan mu
yaba ci Al'amarin Allah bayan watanni sai ciki
yabayyana na sa ta agaba tagayamin ko ta gane
fuskarsa take . Tasanar dani kanin Imamu ne don
yasha yaudararta da kudade tana kin bashi hadin
kai shine ranar dayaga ba kowa agidan yashigo
yakulle ta yayi mata fyade wani ashar nazunduma
sannan namike nazira hijabina ina fadin wallahi
ba a isa ba sai naje hargidansu Imamu tunda dan
kanwar babarsa ne da take riko ita zanje na
sanarwa idan taki ji hukuma tabi mana hakkinmu
Akofar gida nahadu da baban Imamu banbi
takansa ba ina huci ina komai nashige gidan don
kuwa tabbas zuciyata a sama take na bankada
labulen dakin ko sallama banyi ba Hajiyar ta dago
tana kallona ke lafiya? . wane irin iskancine zaki
shigomin ko sallama babu? Na shaka da yawa
kafin nace Ba alheri ya kawo ni ba nazo nasanar
dake ta'asar da danki ya tafka" Ahanzarce ta
kalleni tace Hmmm ba shakka yanzu na gano
bakin zaren ai wato saboda kin makale yasoki
yaki shine Zaki yimasa sharri? Ina lura fa da
take- takenki duk binbinin da kika dunga yimasa
ido nazuba miki na ga iya gudun ruwanki.Don
kuwani banga me Imamu zaiyi da diyar da ba
asan asalin ubanta ba..." . Da sauri na daga mata
hannu"saurara! Ba zancen Imamu yakawo niba
zancen Hamidan ya kawo ni yaje yadibga ma
kanwata ciki tahanyar fyade kuma wallahi ba zan
yarda ba sai nakai shi ga hukuma" "Kikaishi ga
hukumo ba hukuma ba saboda tsabar sharri yaro
dan shekara sha bakwai zai iya yin ciki? Kwaje
can inda kuka samu cikinku kuji dashi amma ba
za alikawa dan marayan Allah ba yo dama har ku
din wasu nagari ne ai barewa ba ta gudu danta
yayi rarrafe wayasan asalin ubanku muhammadu
mai hula mutumin da muka ganshi zikau agarin
nan da girmansa har yakarar da nagartarsa... . "
Lafiya nake jin hayaniya.?Baban Imamu yafada
yana shigowa gidan Hajiya taja tsaki Duk bakai
ka janyo mana wannan shirgin ba ga ta nan ta zo
da sharri wai hamidan yayiwa kanwarta ciki kai
kaji wata tatsuniya yaro dan shekara sha
bakwai..." Alhaji murmushi yayi yace kada ki ja
da ikon Allah yaran yanzu ba irin shaidancin da
ba su sani ba ke dagaske kike ko wasa? Alhaji
yatambayeni rantsuwa nayi akan cewa dagaske
nake yagirgiza kai "To kinji hajiya . Sai asan
abinyi Nidai data kai batun nan gahukuma gwara
ayi hakuri adaura musu aure da zarar ta haihu
Hajiya ta zabura "Au me? aure da wa? Allah ya
kiyaye jinina yahadu da jinin shege kuma karya
take kaf zuri'armu ba karuwa ba dan'iska Don
haka ni ban amince da cewa hamidan yayi wa
kanwarta ciki ba sudai da suka gado iskancin sa
sunsan inda tayo ciki amma mu kam kaf
zuri'armu 'yan mutuncine Duk yadda Alhaji
yabulla sai matar nan ta bulla sam ta ki yarda
hamidan ne yayi wannan ta'asar Haka inaji ina
gani naja sangalalin kafata cikin mutuwar jiki
nakoma gida ina kuka Abu yabazu akauye nan da
nan aka shiga yimana gori ba shiri na hade
kayanmu muka yi kaura kano inda na kama mana
hayar daki awani gidan karuwai ta silar wannan
abubuwa dasuka,faru ni da kanwata muka
tsunduma kanmu acikin karuwanci kafin wani
mutum Alhaji muhammadu ya mayar damu
gidansa,mutum ne mai kudin gaske sai dai ba
ya,haihuwa . matarsa mutuniyar arziki yar garin
Bendel tayi mana rikon mutunci Daga,lokacin
nafara binciken yadda zanga Imamu . don daukar
fansa kwatsam ranar an Kai uwar dakinmu asibiti
na hango shi shi da matarsa bai ganeni ba kasan
cewar hijab nasaka da nikab nikuwa nan nashiga
bincike amma har na gano gurin family doctor
yake kai matarsa awo alokacin tsawon shekara
goma bansan ya shi a idona ba.Kawai zuciyata ta
rayamin DAUKAR FANSA wannan shine dalili"
Gaba daya kotun tadauki hayaniya Abbana
yadanyi murmushi don ya fuskanci daukacin
jama,a shi suke jin haushi . "kina ganin yanzu
ramuwar da kikayi akaina batayi.Yawa ba? 'yafa
kika saka aka sace min sukutum sannan kika ba
da ita ga magajiyar karuwai ta koya mata
tarbiyya irin tata duk adalilin naki na aureki" Ya ja
ajiyar zuciya hakika kincuceni iya cuta fateema Ni
bazance miki komai ba sai dai Allah ya shiryeki
Akarshe daga yau shari'ar ta bar hannuna
takoma gun abokin aikina kasan cewa abin
yashigo da ni aciki kuma shine zai kawo karshen
wannan shari'ar" Daga haka Abbana yabuga
guduma jama'a suka furta kotu. Nan da nan aka
fa ra watse,wa muma jikinmu asalube muka
mike,da niyyar. RAYUWA book 3 part 7
NAGA RAYUWA book 3 part 7
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:09
Tafiya gida ummana kuwa tana hada ido da
shany take tasaki kuka Nasan radadin abinda
takeji Nikuwa,damuwata daya ce mamina yanzu
Abbana da wane idon zai kalli mamina
kai.Jama'ar gidanmu ma gaba daya me za suce
da ita? . Duk da tarin zargin da akayi
marattabbas ancuceta ankuma zalunce ta shi
kansa na lura Abba na jikinsa amatukar sanyaye
yake don ko da yadawo gida sashen sa ya,shige
yakulle kofa Nikuwa idan na kalli yar'uwata
Shany sai naji tausayinta ya sake kwarara
azuciyata Don itama kuka take sosai tare da
sauran yan'Uwanta su shida. . Ummana tana can
kuryar daki nayi sallama nashiga da kyar ta dago
idonta da yayi jajur takalleni na,zauna a gefenta
na ce Umma wai me yasa kuka damu kanku? Ba
za ku yi hakuri ku gode wa Allah ba da ya
kaddara muku saduwa, da diyarku tun kuna raye?
Umma ta dago tana duba na Aysha Allah shi ne
abin godiya ba komai yake damu na ba sai yadda
wannan matar ta gurbata min tarbiyyar yarinya
yanzu ta ina kike tunanin zan fara gyaran
tarbiyyarta? Abu na gaba da yake damuna shine
maminki . yanzu da wane ido Abbanki da
yayyenki zasu dubeta? wannan shine matsalata
Ajiyar zuciya naja nace Umma duk wannan mai
sauki ne tarbiyyar shany dai ki kaddara Allah
shine mai shiryarwa ki ci gaba da rokonsa ya da
fa miki awajen tarbiyyarta da ta sauran
yan'uwanta Mamina kuwa insha Allahu
matsalarta mai sauki ce Umma girgiza kai tayi
tace Bamai sauki bane fateema na da riko kuma
tadau zafi sosai a maganar nan ba ita kadaiba
ma gaba daya danginta kuma tabbas yakamata
su aikata hakan ko fiye da hakan don kam tabbas
an bata musu . shiru nayi don kam ni ma
shaidace da yadda yan gidan mamina suka dau
Zafi kuma tabbas yacancanta ayi hakan don an
bata musu Umma ta ja ajiyar zuciya kafin tace
Tashi kije kija yan'uwanki ajiki Aysha don Allah
musamman yar'uwarki duk da Abbanki yace zaisa
ayi tayi musu addu'a amma tarbiyyarsu kam sai
antashi tsaye. Jikina asanyaye namike nafice
daga dakin don na lura Umma babu abinda yake
ta yar mata,da hankali sai yadda za ta daidaita
nutsuwar Shany ta dawo abar kwatance. .
Tabbas wannan matar tacuci iyayena kuma
wannan shi ake cewa ramuwar gayya wacce tafi
ta gayya zafi Nayi Alkawarin zantaimaka mata da
gyaran tarbiyyarsu Afalo natararsu gaba daya
suna zaune sunyi jugum-jugum sosai tausayinsu
ya,tsirga min na zauna kusa da Shany tare da
janyota jikina."Please! ya kamata ku cire damuwa
daga ranku haka tunda dai duniya ta shaida ba
ku da laifin komai tarbiyya akayi muku ahaka
kuma ita ta cuci kanta duk da itama tashi tayi ta
tsinci rayuwarta a haka amma bai kyautu ace ta
dora da nata mugayen halayen ba" Shany ta ja
ajiyar zuciya kafin kwalla ta,zuba sharr daga
idanunta tace Sister ina jin matukar bakin ciki
idan na tuna,rayuwata ta baya haka kawai banji
ba bangani ba don wata manufa aka rabani da
nagartattun. Halaye na aka,kaini wata banzar
rayuwa banjiba banganiba wallahi Allah ya isa
bazan taba yafewa wadannan mutane ba Ta sake
fashewa,dakuka Ni kaina kukan ne yaci karfina
can daya daga cikin kawayenta tace Kukan dadi
kikeyi shany,saboda ke yanzu yar gata ce
kinsamu iyayenki. . Mu a ina kike tunanin zamu
ga namu iyayen? shegu ne mu bamu sani ba
itama tafashe dakuka gaba daya gurin,sai muka
saka kuka, Daidai lokacin Umma tafito tana
sallallami yanzu mezan gani haka kuda zaku
godewa Allah da rayuwarku ba ta kare ahakaba
amma shine kuke kuka?, Dasauri ta fice nalura
itama Umma kukan takeyi da kyar na mike bayan
naji ana kwala kiran sallar la'asar nace musu
muje muyi sallah jikinsu asalube suka mike tare
da haramar alwala Abinda ya ba ni mamaki bai
wuce ganin yadda suke sallah ba gaba daya
dungurawa kawai sukeyi tausayinsu ya sake
kamani Don kam na tabbatar ba karamin gyara
suke nema a addininsu ba . nadauki damarar
koyar dasu sallah kafin komai da daddare gaba
daya muna zaune awajen da ake cin abinci bayan
angama Abba yadube mu yace masha Allah" kafin
ya karasa naji mayataccen kamshin Ahmad
yacika harabar gidanmu take nahade raina sosai
don ba na son abinda zai hada ni da Ahmad cikin
takunsa na isa yakaraso wajen yan matan Abba
kuwa, tuni suka zuba masa ido tsiyar namiji
maikyau kenan. . Duk inda yashiga sai kallo Na
kaddara hakan araina har rige-rigen yimasa
sannu da zuwa sukeyi Shany da sauri tamike ta
shimfida masa darduma "Nagode" yace mata
cikin tausasshiyar murya sannan ya zauna ya
sake rankwafawa ya gaida su Abba yasa ke
jaddada musu murnarsa na bayyanar yarsu shany
Ni kuwa tuni nazare jikina nashige dakin umma
wai kuma sai naji ina kishin kallon da yan'Matan
Abba sukewa Ustaz Na zauna turus akan kujera
hade da dafe kunci inatunanin Ustaz da irin
tsananin kyan da yayi . Yau shigar wata jallabiya
yayi dark-blue sai shaking take. Ta kwanta lub
ajikin lallausar fatarsa wanda yala-yalan gashin
yakwanta ajikinta Asalin balarabe dole duk macen
da ta ganshi ta kyasa Atake na dokanta naji
Ustaz ya kirawo ni koda masifar da na saba na
zazzaga masa. Sai dai shiru makatau take naji
wani abu ya tsaya azuciyata na tabbatar yanzu
Ustaz ya gama yayina Don haka kone mana ba
ya yi Shany ce tashigo dakin tana murmushi tace
"Sis,wannan ma dan' uwan mune?" Da sauri na
dago nawur ga mata wani kallo ina son . Gane
me take nufi da tace hakan Ban hango komai
akwayar idontaba don haka hankalina yadan
kwanta Ahankali nace mata "MIJINA NE" amma a
da fa Takuwa bude ido tace Wow! Amma meyasa
kikace a da kina nufin yanzu kun rabu? Cikin
sanyin murya na fara sanar da ita labarin
Ustazuna kafin nagama kuwa tuni hawaye ya fara
zarya, akan kumatunta Da safe kuwa kasancewar
lahadi ce yawanci surukan gidanmu anan suke
wuni sai dare suke tafiya harda mazajensu da
'ya'yansu muna zaune na saka .khadija da
A.Nafisa matar ya usman atsakiya sai hira muke
cikin nishadi don ni sauran matan yayyena ba sa
gaba na don dana shiga halin da za a tausaya
min ba wacce ta kula dani tamkar khadija Abba
ne yashigo yana kiranmu nida 'yan matansa
Afalonsa muka zauna anan kuma muka tarar da
wasu matasa daga ganin su ka ga malamai don
yanayinsu ya nuna haka Abba ya nuna 'yan
matansa yace "Alhamdulillahi, gasu nan su
takwas ne nakeso kafahimtar dasu addini don
basu san komaiba game dashi malami daya
yagyara zama yace "Alhmdllh" sunana m.Kawu
kuma . Zan dunga koya musu Alkur'ani zamu
soma daga fatiha insha,Allahu" Dayan ma
yagyara zama yace sunana M.Aminu zan koyar
daku fik'hu da hadith insha,Allah" haka dayanma
yagaba tar da kansa "sunana M.Amadu da yar
dar Allah zandauke ku darasin Sirah da tauhidi."
Abbana yasake gyara zama yace Alhmdllh nagode
Allah dama na sanar da su labarinku duka sun
kuma matukar tausaya muku da wannan dalili na
san insha,Allahu zasu jajirce wajen koyar daku. .
Ga aysha nan ma za ta sake tunasar daku
abubuwan da ba ku, gane ba kaina yana kasa na
dago inda muka hada ido da malm.Aminu yace
A'a Aysha tana gidane? . murmushi nayi da yake
na sansu malaman mune na tahfiz nasan
M.Aminu da tsokana Abbana yace Aysha ta ki
zaman aure yafada yana dariya Da,sauri na mike
nashige gida da gudu Don ba na son fadan
malamaina nasan su kamar yunwar cikina
musamman malam amadu Tun daga ranar Abba
yace adunga kiran shany da humaira tunda itama
sunanta Aysha bazai yiwuba mutashi a suna daya
sun kuma da ge sosai wajen karatu kuma duk
inda zasu hadda hijab . suke zuwa Sosai nake jin
kunyar haduwa da Mamina don haka haryanzu na
kasa Zuwa gidansu duk da ba ni nayi mata lefin
ba amma na ja janta tabargazar da Abbana yayi
mata Na jin jina mata laifin da ba nata ba
abinda,yafi komai ciwo arayuwa azarge ka da
abinda ba,ka aikata ba . Ranar Lahadi sati biyu
da faruwar lamarin gaba daya muke zaune
aharabar gidanmu har da yayyena da matansu
kawai mukaji sallamar MAMINA kafin kace me
tuni yaya.farouk da yaya.Ali sukayi wani tsalle
suka gudu can bayan gida mamina ta shigo cikin
zumbulelen hijabi da nikab Da murna ta natashi
ina tsalle na rungumota ita din ma rungumo ni
tayi tana sakin murmushi Ummana ma da sauri
ta mike ta tarota cikin murmushi mai kama da
yake take fadin mamin Aysha kece da rana haka?
Ba tayi magana illa bi na da tayi da kallo tace .
aysha,wajenki nazo don tayaki murnar kubuta
daga kangin da kika shiga In kuma tayaki murnar
ganin yar'uwarki akarshe nayi miki sallama zan
tafi England karo karatu" Tuni hawaye suka
sulmiyo min daga idona nace novels / NAGA RAYUWA book 3 part 8
NAGA RAYUWA book 3 part 8
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:11
. "Mamina kina nufin ba za ki dawo gidannan ba
kin.Rabu damu har abada? Hannu ta saka tasha
remin hawayena kafin nata digon hawayen ya
dirgo akan kuncinta tace "Na rabu da kowa daya
dangance ki Aysha amma ke da usman bazan iya
rabuwa da ku ba Ina tare da ku a waya ko
lokacin da zanzo hutu ki kular min da kanki
Ayshata" . Daga haka ta zame hannunta takuma
juya da azama da sassarfa Zata,wuce Umma
turus ta tsaya idonta na kwalla nikuwa da sauri
nabi mamina shima yaya usman ya fello da gudu
muka tsare mamin da magiya Daidai lokacin
Abba ya shawo kwana zaishigo sukayi ido biyu
da mamina Cikin sassarfa yajuya da azama yabar
gurin shi kansa nasan kunyar gamayyarsu da
mamina yake Mamina ta kalleni tayi murmushi
ahankali ta furta . "SAI WATA RANA AYSHATU" .
Daga haka ta zame tafice Tuni na durkushe
awajen na saka kuka don sam gwiwata ta ka sa
daukana yaya usman yakama hannuna muka
shiga gida shi kansa na lura jikinsa yayi sanyi
sosai Abba naji yana kwalamin kira cikin sanyin
jiki na mike na isa falonsa Tarar dashi nayi
idonsa . Yayi jajur da alama shima kukan yayi
yace Ayshatu mamin naki ta tafi? cikin sanyin
murya nace "Ta tafi Abba ta sanar dani cewa wai
karatu zata tafi England Amma Abba me yasa
bakaje biko ba? Abba yaja ajiyar zuciya,yace
"Dalilai da dama Ayshatu ina matukar son
fateema amma ina jin kunyar.Tunka rar ta da
sunan biko Bayan tarin abubuwan da suka shude
da wane ido zandu bi mahaifinta? . mutanen
masu nagartar halaye ina jin kunya Aysha..."shiru
ni ma din nayi don kam akaf hasashena ban
hango mafitaba cikin dakiyar zuciya nace Abba
kadai jarraba tura manya nasan babanta mai
fahimta ne insha Allahu zai fuskance ka" Allah
yasa ayshatu tashi kije" jikina asanyaye na mike
na fice Amma ko dana shiga kasa katabus nayi
na roki yaya usman yakaini gidan mamina sai
dai,abin takaici anan take hajiyarta take sanar
dani sunwuce Abuja tacan ne jirginsu zai tashi
Hakan yasaka,na saka kuka don na tabbatar
yanzu kam mamina tayi min nisa musamman
idan ta auri wani mijin bai zama lallai ya bari
mu'amalar mu tayi nisa ba. . ******* ********
******* . Wani lokaci ina kwance lamo akan
gadon Ummana matsanan cin tunanin Ustas ne
yadabaibaye min zuciyata kwana da kwanaki ban
samu labarin sa ba Hakan ya dan daga hankalina
hade da tunanin Ustaz yagaji da wulakan cin da
nake yarfa masa shiyasa ya ajiye ba tu na agefe
amma kuma ai har alokacin bai furta min kalmar
saki ba bai kuma aiko da takarda ba meya ke nufi
da jingine ni da ya yi? . Ni kadai nake wannan
tuna nin Na rasa wazan tunkara da
wannan.Tambayar tawa gashi ni kuma jan'ajina
bazai bari na kirashi ba Fitowata daga wanka
kenan ina zaune da karamin towel ahannuna ina
tsane ruwan jikina Humaira tashigo da sauri
tamkar an cillo ta Na bi ta da kallo saboda,ta
inda muka bambanta kenan ita akwai dan banzan
rawar kai "Aysha Sis,kije Abba yana kira" Ina
zuwa shine zaki shigo kamar an cilloki har yanzu
kin gagara koyar sallama idan zaki shiga waje. .
Murmushi tayi ta fice da dan tsallenta, Nabi ta da
kallo ina mamakin yadda kullum ta Allah Humaira
acikin walwala da farin ciki take ba ruwanta da .
Miskilanci irin nawa Allah kenan mai halitta gashi
yayo mu iri daya amma sai ya bambanta mu
tabangaren halayya Na zira riga sannan nafita
falon Afalon natarar da duk samarin Abba ko nace
magidanta mamaki ya ka mani tare da tunanin
taron me ake ne gefe daya yan matan umma ne
sun za gayeta gaba daya cikin shigar mutunci
suke don yanzu sunyi matukar nutsuwa tamkar
ba wadannan tantiran na wancan lokacin ba Na
isa nazauna agefe ina fuskantar Abba da son
sanin dalilin kira na . . Abba yabude da addu'a
kamar kowanne lokaci idan za.Ayi,taro sannan
yasake dubana yace "Aysha wannan taron naki
ne, so nake inji me kika yanke game da aurenki
ko kuwa har yanzu kina nan akan bakanki akaro
na uku bazan takura miki ba kamar yadda na
gaya miki wancan lokacin ra'ayinki zan bi" Ustaz
ya isheni yazo da kansa ya aiko,don haka yau
nasanar dasu zan fada musu abinda kika yanke"
Tamkar nace masa zankoma amma ina sai nayi
tuna nin yadda Ustaz ya yasar dani don haka,
dole ni ma inja ajina. "Ina jinki"Abba ya fada Na
dago fuskata nace . "Abba ba zan koma gidansa
ba karatu nakeso nayi..." Daidai lokacin Ustaz
yayi sallama da wannan mayataccen turaren nasa
Da sauri gaba na yahau bugu ganin azabar kyan
da ya yi Cikin jallabiya dark cofee 'yar Asalin sai
dai miskilanci na ya kawar da wannan kudurin Ina
so ayau na ga karshen miskilancin Ustaz na san
idan yaji ba nason sa hankalinsa ba karamin tashi
zai yi ba Cikin fara'a Abbana yace "yauwa dan
halak yanzu ake zancenka gwanda da Allah ya
kawoka Aysha sake maimaita abinda,kikace"
kaina akasa nace ."Abba ba na son sa karatu
nakeso nakoma akasar waje . " Murmushi Abba
yayi yace to kaji kai Ahmad sai ka ba ta
takardarta ayanzu kuma ayau zansanar dakai na
maye maka gurbin Aysha da yar'uwarta
Humair..." Tuni hantar cikina ta kada tamkar na
janye batuna nazaro idona ganin Ustaz ya zaro
jotter da biro a aljihu ya shiga rubutu tsaf nade
na fahimtar me ake. . Cewa gashi miskilancina
yahana namaganu karshe runtse idanuna nayi
daidai lokacin Ustaz yamika wa abba takardar
yana fadin . "Abba nagode Allah yabar girma" .
"Ya juya yana kallon daukacin mutanen falon
yace ku yani murna,da wannan karamcin na
Abba" Abba yace Bakomai Ahmadu kaidin mutum
ne mai nagartar halaye sam ba zan so na,rasaka
cikin ZURI'ATA ba Tamkar wani maganadisu haka
idanuna suka game da idon Ustaz kawai sai naga
ya dagan hannu ya saki murmushi alamar . SAI
WATA RANA . Daga haka yayi wa Abba sallama
ya fice jikina asalube namike har juri nake ji
nashige gida zuciyata cunkushe da tunani
nakuma tabbatar da cewa wata makarkashiya
Ustaz yakullamin ya dai ga yanzu humaira tafi
kwanta,masa azuciya kenan da sake-sake sam
ba na ganin laifina nikuwa,ko son sa,zai kasheni
bazan taba nunawa na damuba sai dai hakan
yazama AJALINA . Ji kake kut nahadiye wani abu
da ya tsayamin amakogwaro sai asannan hawaye
ya zuba akan kuncina zuciyata cunkushe da tarin
bakin ciki nadama da da na sani kuwa fal raina
Nafara jin haushin humaira tamkar itace tace ta
na sonsa Ban da ni jinin tace wallahi da sai nayi
mata abinda za ayi na damar hada ta da mijina
sai kuma nafara jin haushin kowa . Agidan da
tunanin sun fi son humaira akaina Ni kam nasan
narasa MAI SO NA MAMINA . Don haka wunin
ranar ban yi magana da kowa ba koda nayi sallar
asuba sake komawa barci nayi duk da ada ba na
komawa barci da yanmatan umma muke haduwa
mu gyara gida yau kam ko kallonsu banyiba balle
susa ka ran zanyimusu karin karatu kamar yadda
na saba duk Asabar din duniya Da humaira da
maryam da khadija muke kwana daki daya wani
lokacin kuma humaira ta tafi dakin Umma
sukuma sauran biyar din suna dakinsu da yake a
bangaren mami muke tare jin hargowar shirinsune
yasa nabude idona cike da jin haushin su nace
malamai kunda.Meni fa kunhana ni bacci .
Humaira tadiro,gadon ta haye bargon da nake
kwance nace ke meye haka? Langabe kai tayi
tace "Am sorry Sis, kinmanta da batun komawa
kotun kiyi sauri kishirya kibisu bros ni Ustaz zanbi
wani kallo nazu ba mata ina shirin kunduma mata
ashar sai kuma natuna ita din wacece da kuma
matsayinta a wajena Tsaki naja nace kuje kawai
ba na jin dadi bazan samu zuwa ba daga haka
YUWA book 3 part 9
NAGA RAYUWA book 3 part 9
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:12
. ba na son wani Silly queastion ina kallo suka
fice sai ga Umma ta shigo maganar duniya nayi
shiru kamar mai barci don ba na son ta gane
yanayin da nake ciki Inaji tace . "Humaira muje
takoma bacci ma" suka juya suka fice Nabi
bayansu da kallo ina sake jaddada jin haushin
humaira acikin zuciyata sai azahar suka dawo
inajiyo hayaniyar su umma nayi bulun-bukui
adaki inajin umma ta sake dawowa dakinta
dubeni wannan karon na bude idona har nayi
mata sannu da zuwa, cikin wata cunkushasshiyar
murya Umma da mamaki ta dubeni Aysha kalau
kike har yanzu kike kwance?,kaina ne yake ciwo
kunda wo umma? Ta gyada kai mundawo Nace
ya shari'ar ta kaya angama kuwa? Umma tace
shari'a angama tsaf an yanke wa fateema
hukuncin zaman gidan wakafi na shekara biyar ko
tarar miliyan biyar .Shikuwa doctor daurin shekara
biyar babu tara Atine kuwa daurin rai da rai tare
da tilasta mata wajen fadar inda,sauran
'yan'uwanta suke. Najijjiga kai hade da fadin
hakan shine daidai da su ai umma " Umma tace
kowa haka yake fada amma Aysha anya babu .
Abinda yake damunki kuwa? Na ce babu komai
Umma amma don Allah kiyiwa Abba batun
komawata makaranta inda hali gaskiya,nafison
nabar kasar nan? Umma ta girgiza kai da alama
tana tunanin yadda za ta fuskanci Abba da
wannan maganar ne batace komai ba tamike
tatafi Nikuwa na rintse idona don kam zanfi son
barin kasar nan ko ba komai bazan san lokacin
da aka daura auren ba balle Zuciyata tayi kunci
Don yanzuma jinake tamkar ciwon zuciya zai
kama ni. . Shiru har kwana biyu banji amsa daga
bakin Abba ba na tabbatar bai amince ba kenan
hakan ya sanyayar min da gwiwa Ina kallon,
Humaira kullum nanike da waya akunnenta na
san ba komai take ba sai hirar soyayya da Ahmad
hakan yasake bakanta min rai harnaji tamkar
nacanja daki sai dai hakan ba zata yiwu ba don
nasan kiri-kiri za ace BAKIN CIKI nake, . sai dai
kullum fa ina cikin uwar daki har umma tagaji da
tambaya ta taja,bakinta ta tsuke ina lura da ita
kullum tana kitchen tana koyawa yan matan
girke- girke ta tattara al'amarina ta saka agefe
Hakan yatabbatar min danayi . Rashin UWA MAI
SO NA MAMINA Yau da daddare bayan mun
gama cin abinci har namike tsam zantafi Abba
yasa baki yaki rani Bina yayi da kallo yace
kishirya da wuri gobe akwai tafiya potiskum duk
na lura yanzu kintsiro da wani hali na zama ke
kadai ba tare da munsan laifin da aka yi miki ba"
Mikewa kawai nayi nace to Allah yakaimu sam
banso wannan tafiyar ba amma babu yadda zanyi
Da asuba babu wanda yakoma barci har humaira
da ta kusan raba dare tana waya,da ustaz Na
lura ustaz,har yafi sonta akaina saboda bini-bini
yayi mata waya ita kuma tamkar mayya kullum
tana makale da waya babu jan aji babu komai sai
wani rawar kai shiri suke haushinsu kawai nakeji
sosai araina suna ta caba kwalliya nikuwa wanka
kawai nayi nazira wata bakar doguwar riga
ta,mai na shafa kawai kai kace nidin matar
mamaci ce wacce take takaba karfe 9:00 muka
hau motar yaya usman na fada da sauri yaja mu
dani da matarsa yana yimin tsiyar ramar da yaga
nayi bayan hankali ya kwanta murmushi kawai
nayi masa ba tare da na tofa ba shi ma din bai
sake . cewa komai ba duk da na so yace din
kodon na gaya,masa abinda yake,sani rama sai
dai gani da zurfin ciki Ba kasafai nake iya fadar
matsalata ba ba tare da an tambaye ni ba Haka
har muka isa potiskum Ni dai ina zaune cikin
mota jigum sai yaya usman ko matarsa sun
sakoo ni azance sannan nake shiga sai gaf da
la'asar muka shiga garin potiskum din munriga
kowa isa Hajiya da sauri ta tareni cikin farin ciki
take cewa kaga baiwar Allah tun dazu nake zuba
idon ganinku Ayshatu fargabata daya dawane
idon zan dubeki? Murmushi kawai nayi na
durkusa nagaishe ta Don ni dama ba sosai na
kware da wani wasan jika da kaka ba Ta kama ni
Zoki zauna nasake jaddada ban hakurina a
wajenki Duk da dai,kince kinyimin afuwa
Akunyace na zauna nace hajiya kibar maganar
tariga ta wuce Daidai lokacin Abba da Umma
suka shigo Abba dafada yashigo yana fadin ina
usmanun wai kai yaushe zakayi hankaline? . ina
ce har waya nayi maka akan cewa karage gudu
yaya usman yace Abba ai banyi wani gudu ba
Nan suka zauna suna gaisheta hajiya kuwa
bakinta . A bude,take kallonmu,ni da humaira fadi
take Ba shakka ga zahiri nan babu bambanci ko
digo tsakanin ku Umma ta tuntsire da dariya tace
uhm-Uhum,da bambanci sosai Ayshatu bata da
kwaramniya humaira akwai dan banzan rawar kai
humaira ta zunbura baki tace kai umma nidin? ya
muhammad yace sosai ma kuwa kike da rawar
kai Abba yace humaira kam ba da ma humaira
kuwa gaba daya ta fara dire-diren kafa tana
kukan shagwaba ya faruk ne yakamo hannun ta
yace Quite my friend kada kiyi kuka rabu dasu Me
za ayi da mutum mai kunbiya-kumbiya? Da abu
aransa ya fada yana kunshe dariya aciki Nakuwa
zabga masa,harara don na san dani yake. . ***
*** *** . Kwana biyu mukayi a potiskum,bayan
munzagaye dangi muka dawo gida Nidai fara'ar
dole, nakeyi a kan babu yadda zanyi tunda muka
dawo Umma tafara zancen shirye-shiryen sa
ranarsu Don ance wai suhudu za a aurar su yaya
muhammad kowa daidaya guda uku kuma
malaman mu ne suka nemi aurensu don nuna
tausayawar su garesu Ranar laraba 'yan sa ranar
sukazo 'yangidan su Ahmad ne harda kanwarsa
khadija ta saka ni adaki tana tuhuma ta akan son
jin dalilin dayasa naki dan uwanta har aka
musanya masa da kanwata murmushi kawai nayi
na ce KADDARA CE! . zo kaga lefen humaira
akwatina goma sha biyu harda nasaka rana
kayane sosai dankar aciki tamkar ba asan ciwon
kudi ba wata uku aka saka cif Humaira sai rawar
kai take bini-bini ta daga waya kaji tana kashe
murya hade da,cewa my Only wannan iyayi da
take,shiyake dugunzuma min zuciya Nayi tunani
ita ko kunyata ba ta ji Nashige daki kuka kawai
nakeyi har zazzabi ya rufeni ruf ba ta re da sanin
komaiba sai ga shi nice har da kiran wayar Ustaz
amma sam yaki dagawa . sai rejecting call dina
yake Balle na bashi hakuri ya janye kudurinsa na
auren kanwata Yau da safe ko fita banyiba daga
daki maryam tashigo take sanar dani wai ana
kira na Afalon abba da kyar na mike nazira
hijabina na isa falon Abban shi da yan uwansa,da
suke yan maza har su baba yahya suke zaune
sun tasa kayan lefen humaira agabansu Allah ya
sa su ruguza maganar Auren... . na ayyana hakan
araina su kansu na san sunsan hakan baidace ba
sai dai sabanin haka ji na yi Baba yahya ya rufeni
da fada da nasiha yace "Yanzu Ayshatu saboda
wannan kaddara ta afku shike nan sai kice
kinrataye sunnar manzo {S.A.W} kice wai ke
abarki kitafi karatu waje? . to tur da wannan
shawara taki Adanginmu kaf ba mu bar maza sun
tafi waje karatu ba balle mubar mace kuma gata
daya da za muyi miki shine kifitar da miji kiyi
aure shine mutuncinki mutuncinmu mu ma yanzu
tunda Ahmad ba kyason sa wa kika tsayar? .
kasa ce musu komai nayi ruwan hawaye ya fa ra
ambaliya akuncina nace babu wanda na tsayar To
mun baki sati kifitar da miji tunda dai..ovels / NAGA RAYUWA book 3 part 10
NAGA RAYUWA book 3 part 10
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:14
Mijinki na baya ya sanar da mu bai dora miki
idda ba Tashi ki tafi Allah ya kawo nagari Da kyar
na ja jiki na isa daki "Na shiga uku" . Nafada
ahankali Najawowa kaina masifa meya,kaini furta
ba na son Ustaz? Nasan halinsu baba yahya sarai
da zafin rai tunda ya furta sai na fitar da miji abu
ne mawuyaci ya janye kaina yayi dum sakamakon
rasa mafita da nayi alokacin kam na san tabbas
na yi rashin uwa da da mami akusa, da duk
hakan ba ta sameniba ga shi ko kira lambar da
takira ni bana samunta Hakan yatabbatar min da
bayan mungama waya canja layi tayi Nasake
rintse idona wasu zafafan hawaye, suka zubomin
Da daddare kamar wasa na dau Ipad dina da
niyyar duba facebook ko whatsapp, wanda rabon
da na bude su harna manta sakon Mamina ne
yashigo ta Whatsapp da sabon account din data
bude kawai.Cewa tayi Aysha yakike? cikin
tsananin farin ciki na tura mata hoton dan aljani
mai alamar kuka akasa na rubuta;"Rayuwa ta
yimin zafi MAMINA, . saboda rashinki akusa dani
wallahi mami yanzu na tabbatar ni marainiyace
na rabu da, . Ustaz an maye masa gurbina da
humaira kanwata kuma Allah mami inason sa
haryanzu Gashi Baba yahya ya rantse sai na fitar
da miji mami na rasa yadda zanyi kibani
shawara" . Tsawon lokaci ina sauraron amsar
mami shiru har na fitar da ran samun amsar ta
saikuma ga sako ya shigo . "Aysha kenan
haryanzu kinason Ustaz meyasa kika cuci kanki
wajen rabuwa dashi?" . cikin kuwa na sake rubuta
mata "mami wallahi kaddara da kuma son ja
masa aji." Dariya taturo min sannan taturo min
"kisami Abbanki ki sanar dashi ba ki da wani Zabi
yazaba miki miji da kansa idan yaji kince hakan
nasan zai fuskanci har yanzu kina son mijinki
idan yaso sai adawo da auren kanki."Murmushi
natura mata alamar jinjina cewa tayi kawai "Sai
da safe ina karatune" . Daga haka ta bar online.
Kwanciya nayi akan gado ina dariya Na tabbata
shawarar nan ta mami tayi don haka nake Allah-
Allah safiya tayi Da azama na mike nashiga toilet
nayi alwala ina rokon Allah yasa abinda nake
nema yatabbata da sassafe nayi wanka na shiga
don tanadar, wa Abba hadadden . Break fast
koyaji dadin amsa bukatata Da sauri ina ta
addu'a azuciyata ina kallonsu humaira suna jifana
da kallon mamaki ganin yadda nake sakin fara'a
a zuciyata kuwa fadi nake . "yarinya kwaleleniki
mijina yafi karfin ki ko ta kaka sai na kwato shi" .
Ina yi ina wakar MAI SONA MAMINA Umma dai
murmushi kawai take yi dakaina nakaiwa Abba
breakfast bayan na gaishe shi cikin mamaki yake
cewa Ayshatu yau cutar tawarke ne naga kina
walwala? . Murmushi nayi na sadda kai na kasa
Abba yasake cewa ko ansamo min surukine?
Nasake sunkuyar dakai nace "Dama Abba akan
zancen ne..." Da sauri yace sunce zasu turo ? Na
girgiza kai ina wasa da hannu na nace
da...da...dama Abba cewa zanyi na... baka dama
kazaba min...mijin" . murmushi yayi yace yar
albarka kenan ni da kaina kai amma naji dadi
Insha Allah kuwa zan miki zabe na gari dazakiyi
alfahari da shi Akwai wani kanin abokina dama
ya dameni da maganar aure, . mutumin kirki ga
nutsuwa da kamala yana da iyali zakuyi daidai da
shi...sam ba na fahimtar sauran zancen don dai
naji da gani . nayi sai can naji yace shikenan
Ayshatu zaki iya tafiya Ubangiji yayi miki albarka
Adaddafe na mike nashige cikin gida Awani lungu
nashiga na zauna turus ina tunanin wace
tabargaza nasake ragargazowa,kaina.?Innalillahi
wa inna ilaihirraji'un nake ja, wannan shine ba
wan ba kanin Na dade ina kuka amma da na
shiga gida ko kallona Umma batayi ba hakan ya
sake tunzira zuciyata Na tabbatar yanzu ba ta ta
tawa tunda ta samu humaira yanzu wa zankaiwa
kukana? . Ya usman ba ya nan yayi tafiya haka
na kwanta lamo ina tunanin wai ni zan auri
babban mutum mai iyali Duk wani shirye- Shirye
na bikin yan matan ya kankama don yanzu har
saura kwana uku Idan kaganni na rame nayi
fayau don yadda naji wai tare za ahada da
tariyata Hakan ne yake dagamin hankali Da
safiyar Ranar da za akama amaren Abba yakira ni
dakinsa kaina akasa yake Anan naji ya sanar dani
wai yau zaiyi bako da azahar . ."Ayshatu kiyi
masa tarba ta mutunci don babban mutum ne ba
naso kiyi abinda zai zubar da mutuncin gidan nan
daga kai kawai nayi hade dajin wani . Nauyi
yadanne kirjina yana cewa tashi kije ki tanadar
masa abin saukar baki wannan karon kasa
amsawa nayi na mike da niyyar tafiya amma ina
sai daddafa bango nayi sai dai banyi aune ba
najini kasa ji kake yif. . Ban farka ba sai agadon
asibiti na ganni ana yimin karin ruwa Nabude
idona jama'a ne birjik afilin dakin Gaba daya aka
shiga yimin sannu. Ummana taka ma hannuna
cikin nata ta sake cewa sannu Aysha,ina yake yi
miki ciwo yanzu? girgiza kai nayi alamar bakomai
Abba,da yake gefe yace Allah karo afuwa Daidai
lolacin likita yashigo sanye da kayansa na likitoci
yaja hannun da ake min karin ruwan ya zare
robar da take sadar da ruwan zuwa cikin jijiya
sannan yamaida dubansa gare ni yace meke
damunki yanzu? . Muryata adashe nace masa
"Bakomai" domin ba shida maganin da muwata
yasake aunani da abin awonsu na likitoci sannan
yadubi Abba yace ta samu sauki sosai kamar
yadda na ga ya maka ciwon nata yana tattare da
damuwa sakamakon bincikenmu yanuna ba ta
samu hawan jini ba amma dai ta rage damuwa
saboda nan gaba . Ta iya samun hawan jinin
Abba ya daga kai yace Insha Allahu za a kula
daga haka ina kallo likitan ya saka kai yafice
Daidai lokacin mayataccen kamshin turaren Ustaz
ya mamaye asibitin hakan ya tabbatar min
dashine ya iso Hakan yasa nayi saurin lumshe
idona don ba na kaunar na ganshi ma Da sallama
yashigo dakin sannan naji muryar humaira hakan
yatabbatar min da cewa tare suke Da sauri
na,sake runtse idon don ita kanta ba na son
nagan ta Bayan gaishe da su Abba da ya yi ina
jin takunsa yakaraso bakin gadon danake anan
naji yace Bata farka ba haryanzu" Abba yace Ta
farka sai dai idan sake komawa tayi Humaira ta
karaso ta dafa kafada ta jinayi kamar namake
hannun ta amma na kyale ta sai dai zuciyata na
matukar tafarfasa har ban san sanda hawaye ya
silmiyo ta gefen kunci na ba Inajin Humaira tace
lah Abba mafarkin kuka ta ke yi? Abba yace,wane
irin mafarkin kuka kuma ke dai humaira da
shiririta kike matsa in gani Abba yasa hannu ya
shafi hawayen yace da gaskiyarki sai daiba
mafarkin kuka take ba kuka take dagaske . Wato
Aysha ba zaki cire damuwa daga ranki ba ko? Ni
banga abinda akayi miki ba da ya tsunduma ki
cikin wannan damuwar Na san kina jina Humaira
tace Abba kayi mata ahankali babu mamaki
abubuwan da suka, faru da ne suke damunta
azuciya Abba ya girgiza kai to ai shikenan Allah
yayi mana magani Amma ya kamata kicire
damuwar nan tunda komai yariga yawuce Gaba
daya haushin maganganun su nakeji Don haka da
sauri na mike namayar da gashina da ya kwanta
agefen fuskata Ustaz yana gefe ya zubomin ido
wata harara na watsa masa Madadin naga
yahade rai sai na ga ya saki murmushi yace
aysha yajiki? Banko amsa ba nashige toilet ban
san me zanyi aciki ba amma zaman toilet din yafi
min zama ina shakar kanshin Ustaz yana hadda
samin tunani iri-iri Ina shiga na saki kuka
ahankali mai tsuma.Zuciya Ba na so suji muryata
don haka natoshe bakin tsawon lokaci ina toilet
har umma tagaji ta shiga bugamin toilet din tana
fadin ke ayshatu lafiya? kifito ga mijin naki yazo"
wani bugun zuciya naji da karfi na kasa yunkurinnovels / NAGA RAYUWA book 3 part 11
NAGA RAYUWA book 3 part 11
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:17
Saboda ina tsoron ganin fuskar mijin nawa
mummuna ne? kyakkyawa ne? Allah ne masani
Banbude ba sai da naji Umma tana cewa Ba kys
jine? nace ki bude ga mijin ki da abokansa nan
Da kyar na bude nace Umma miko min hijabina
janyoshi tayi tamiko min tas na goge idona don
inason bawa Ustaz mamaki zan nuna masa ina
son mijina nima turus... . YAN UWA SORRY
WANNAN PAPER DIN COMPLETE YAYI DAMAGE
TO DAN HAKA MUN SALLAKESHI DON BAZAI
KARANTUBA . Sai naji yace Gaskiya Alhaji Amarya
tayi Allah yasanya Alheri Inaji katon banzan yana
dashe baki yana "Amin-amin Nagode yalabbai"
sannan ya mike "Bara mu tafi na, ga kamar tana
so tahuta kasan marar lapiya ba kasafai yake son
hayaniya ba . Amma yayannan naki yanada kirki
Ban ko kalle shi ba suka mike ya iso gurina ya
ajiye bandir.Din kudi na 500 yana fadin "To my
madam Allah yakaro lafiya" cikin wata
dasasshiyar murya ga kana nan ido wasu jajaye
mitsi-mitsi dasu sai fakadeden hanci baje, a
fuskar tamkar faranti Ya juya yasake dashe
gaftara- gaftaran hakoransa A zuciyata nace wai
Allah yayi halitta a nan!" . "Amarya sai gani
nabiyu" Tamkar nace amaryar ubanka sai dai na
dauke kaina Jin buga kofar ne yatabba tar min da
fitarsu Hakan yasa na fashe da kuka Har ma na
rasa wane irin zafi Zuciyata take yi Da daddare
likita ya rubuta min sallama kasancewar an fara
gudanar da hidimar bikin gidan adinke yake da
jama'a wanda suka zo daga garinmu Potiskum
Ana ta yi min sannu ni dai na samu na shiga
dakinmu Nan din ma . 'yan mata ne aciki amma
cikin tunzura nace "Da Allah ku fita waje kuba ni
waje na kwanta" Ba su musa ba suka yimin
sannu suka fice falo na kwanta Daidai lokacin
Humaira ta shigo da gudu ta fada jikina tace
"Aysha sis,oyoyo, ashe an sallamo ki? amma naji
dadi bara na kira My Ahmad na gaya masa" wata
harara na watsa mata nace "ke ba na son
munafunci na ce miki ina nemansa ne? . "Haba
Aysha sis, shifa yace idan an sallamo ki na kira
shi ya sake miki ya jiki" Girgiza kai kawai nayi
nace "Humaira fice a dakin nan tun kan cimiki
mutunci Keda Ahmad din"Ta zaro ido tace My
Ahmad din? Tsaki naja nace "Ko uban Ahmad ne
banzaye munafukai" ganin yadda na matse ina
masifa ne hakan yasa Humaira ta fice sum-Sum
jikinta asanyaye Naja tsaki nace "munafukai
kawai ko kunya ba ta ji ba wani My Ahmad ko
gidan ubanwa yazama na ta?" jinayi anturo kofa
har najuyo zan banka ashar sai naga umma
ce,hakan ya sa nawa bakina linzami Umma
tazauna agefen gado ta ce "tashi Aysha magana
za miyi " Dakyar na mike ta zubo min ido kafin
tace . "me ya farune?" Nace Name fa Umma?
"Yanzu 'yar uwarki taje,da kuka tana sanar dani
wai tafasa auren Ahmad saboda ta lura kina son
mijinki shin dagaske ne abinda ta fada?" Tamkar
nace "ba haka bane amma sai wata zuciyar ta
sanar da ni wannan ce dama ta takarshe hakan
yasa cikin matukar kunya da jin nauyi nace Eeh
Umma" Umma tazaro ido tace . "Kina son sa fa
kika ce?" Na daga kai, sai naga Umma jikinta
yayi sanyi, tace "Aysha Kirufa mana asiri don
Allah kada kisa mu abakin duniya Ace duk sanda
muka tashi sha'ani sai wani abu ya faru tunda an
gama magana har ankarbi sadakin humaira to ki
bar mata Ustaz tunda tun farko ke kika ce
bakyason shi aka kuma biye miki yanzu kice
kuma kin dawo kina sonsa . wallahi kada na sake
jin zancen nan 'yar uwarki ce don kin rasa ta
samu bai kamata yazama abinda muwaba . Ki
share hawayenki shima wannan mijin naki
maikudi ne kuma yanada kirki matarsa mutuwa
tayi wajen haihuwar dansu na takwas" Da, sauri
na zaro ido tace "takwas Umma? . wayyo na
shiga uku Abba ya rasa wanda zai ba wa aurena
sai wannan basamuden?" Umma tayi saurin cewa
"Rufemin baki kada ki tara min jama'a to sai me
don 'ya'yansa takwas ba tare dake za su
zaunaba suna wajen kakarsu, kuma ya ce ma
kuna auren Abu dhabi za ku wuce acan inda yake
gudanar da harkokinsa ba ki ga gidanki ba da
akaje gida tamfatsetse tamkar ba a duniya ba . "
Runtse idona na yi ina jin Umma ta gama surutun
ta fita. Tunani kawai na keyi ta yadda zan iya
zaman aure da wannan mutumin Ni maison miji
kyakkyawa na nunawa sa'a amma kudurar
ubangiji ta sauka akaina Kana ta ka ne Allah na
tasa kuma ayanzu na tabbatar ba duk abinda
kakeso kake samu ba sai wanda Allah yaso Ina
kallo Umma ta fice daga dakin zuciyata ina sake
tuna zancen Umma da take ta koda arzikin
mutumin wai har da cewa gida tamfatsetse
tamkar ba a duniya ba to ni ina ruwana . Da
arzikinsa? Na ja tsaki yafi a kirga. Haka aka shiga
gudanar da shagalin biki ni.Kuwa ba na shiga
kowace sabga koda yaushe ina daki akwance ina
ganin yadda wasu suke kallo na a dafe da alama
suna hasashen yadda nake yi wa 'yar'uwata
bakin ciki ne ni dai bin kowa nake da kallo
fuskata kuwa ta yi fayau ni kaina na san na rame
matuka da gaske. Ranar da ya kama za akai
amare a ranar naji labarin wai, ni ma zanbi mijina
Abu- Dhabi, Hankalina ba karamin tashi yake yi
ba idan na tuno yadda mijin nawa yake Tunda
magriba na fara jin hayaniyar motoci Humaira ce
ta shigo da gudu ta, fada jikina ta rungume ni
tana wani kuka maitsuma zuciya Hakan ya sa ni
ma na saka kuka ba tare da na shirya hakan ba. .
A marairaice kanwar umma ta shigo, ta ja hannun
Humaira tana fadin "Kuyi hakuri haka rayuwar
mace ta ke takaitacciya ce agaban iyayenta" Ina
kallo takama humaira suka fice.Nasan shi kenan
na rasa Ustaz, har'abada zuciyata ta karye na
sake fashewa da kuka Gidan yayi tsit duk an
fashe,kai amare daga ni sai Umma ji nayi anturo .
Kofa an shigo In bude ido naga Abba ne da
Umma Abba yazauna abakin gadon cikin muryar
rarrashi yake sanar dani natashi naje mijina yazo
tafiya dani "Ayshatu ina sake baki hakuri akaro
na biyu akan duk abubuwan da suka,faru a baya.
. Sannan ina miki nasiha da kibi mijinki sau da
kafa saboda ko ba komai aljannarki atafin kafarsa
take. Na sani Ayshata mai biyayyace don Allah ko
da bakya sonsa kidaure kibishi. Alhaji Danjuma
mutumin kirki ne" Da sauri na sake fashewa da
kuka jin sunan da Abba ya fa da wai Danjuma.
Kai daga ji ka san an rayu akauye. . Umma tace
"To mene ne na kukan tunda ta faru ta kare.
Ubangiji ya ba ku zaman lafiya Tashi maza ki
kintsa yana jiranki a mota airport za ku tafi."
Cikin rarrashi Umma ta tilasta ni nashirya cikin
wata rantsattsiyar laffaya, fara. Ta sha ado da
zare marun. kayan kam sun amshi jiki na caras
na fito tamkar 'yar tsana Na raya araina ina ma
gidan Ustaz za a kaini ba gidan wannan mutumin
ba." Da kyar nayi sallama da su ina kuka cikin
karaji yaya usman ya rike hannuna ya rakavels / NAGA RAYUWA book 3 part 12
NAGA RAYUWA book 3 part 12
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:19
Ni har bakin motar yana sake jaddada min na yi
hakuri duka rayuwa nawa ce. Idan dan Adam yayi
duba da abubuwan zamanin baya da suka shude
zai gane rayuwar duniya ba,komai ba ce jin Yaya
usman kawai nake har ya bude bayan motar ya
saka ni yana rufe motar na sake fashewa da
kuka. Daidai lokacin Danjummai ya juyo daga
kujerar gaban motar ta masu zaman banza sai ji
nayi ya ce "Shatu sai hakuri a,rabuwa da iyaye
akwai ciwo amma ga 'yanmata hakan yafi ciwo
ba ga ke da ba wannan ba ne aurenki
nafarko".Tsit nayi saboda jin haushin kalamansa
Ji don Allah ko hakan shine salon da ya dace
ararrashi amarya? Sam babu riba ga auren
babban mutum. Harmuka isa airport ban sake
tofa komai ba naja bakina na tsuke ina sake
taraddadin yadda zan zauna da wannan mutumin
Ina,jinsu suna ta shewa suna hirar kasuwancin su
Isarmu airport tayi dai-dai da lokacin da ake ta
kiran passenger ciki kuwa har da mu ana sanar
sauran mintoci kadan jirgi yatashi raina a bace
nake bin sahun mutuminda da za abani dama
nakashe wani shi zanfara kashewa . Muna hawa
jirgin hancina yafara shakar kamshin Ustaz Nan
take na fara waiwaye awautata wai ko zanganshi
amma sam ban ganshi ba take na amince yawan
tunanin sa da nake yine yasa nafara jiyo kamshin
sa Bat na nemi mijin nawa Na rasa hakan ya sa
na fara waiwaye- waiwaye saboda ni sam ba
taba shiga jirgi nayi ba balle nasan ka idojinsa
Tsawon mintuna ina laluben mutumin amma ban
gan shi ba hakan ya tunzira zuciyata na sami
waje kawai na zauna ina fargabar yadda jirgi zai
daga ni sama na zama tamkar tsuntsu a sama
wani mutum ne yazo ya tsaya akaina tare da
sanar dani wai wajen sane,nazauna har yana
nuna min numbersa ajikin boarding pass. Take
kwalla ta fara zubar min ganin yadda mijin nawa
kiri-Kiri zai saka adauke ni 'Yar kauye Murmushi
kawai na saki da furta kalmar"am sorry". shima
yasaki murmushi ya ce "Ba komai 'Yan mata
kiduba lambar sit dinki ajikin boarding pass dinki
Na daga kai na nawuce ina laluben lambar
kujerata Da sauri na isa wajen sai dai na tsaya
turus domin daf dawani mutum aka ajiyeni wata .
Lafiyayyiyar suit kuma daga jikinsa kamshin
turaren Ustaz yana fitowa ya rufe fuskarsa,da
wata magazine Mamaki ya kama ni nan na shiga
waiwaye ina tunanin INA MIJINA? haka na zauna
saboda ba na so adaukeni 'yar kauye Amma
kamshin da mutumin yake ya ta kura min saboda
kamshin.Turaren Ustaz Ahmad Tunda Nazauna
bai tan kamin ba Ni ma kuma ban kula shi ba Na
dai kaddara kawai barci yake ko kuma irin
miskilayen mutanen ne shi din jigum na zauna ina
ta addu'a a raina don kam a tsorace nae Dalili?
ban taba shiga jirgi ba wani sauti naji yana sanar
da mu muyi tightehing belt dinmu Gaba daya na
rikice don ban ma san inda belt din yake ba
Mutumin bai wani bude fuskarsa ba ya dana belt
dinsa alamar shidin kwararre ne Na rasa yadda
zan yi tamkar na tambaye shi amma, nafasa na
hakura kawai na cigaba da addu'a a raina Jinayi
kunnuwana sun yi dum dai-dai lokacin da jirgin
ya fincika zai daga ban san lokacin da na
kankame jikina ba ina salati jinayi wannan
mutumin kawai yayi caraf ya riko hannu na
Ahanzarce na juya zan masa . Masifa duk da
tsoron da nakeji Cab ko kunsan WA NA GANI? .
Da sauri na ware idona don natabbatar shidin ne?
tabbas shine ustazuna . ya matse cikin wasu
marun din suit sun amshe shi sosai abinka da
farin mutum cikin matukar mamaki na zame
hannu na nace Ustaz me yakawo.Ka nan? Ina
humaira? Bai min magana ba sai zallar murmushi
kafin yace "Humaira tana gidan mijinta" Na sake
waro ido nace Wanene mijinta ban da kai da na
sani? . " Ustaz ya lumshe ido kafin yace Ni ba
mijin Humaira ba ne ni mijin Ayshata ne" Wani
farin ciki ne ya,mamaye Zuciyata da sauri na ciji
kaina inaso na tabbatar ba mafarkin da na saba
ba ne Ustaz na,lura da ni ya jawo hannun ya
matse yace "Ba mafarki kike ba Aysha nine,Ustaz
dinki" Yakai min sumba a hannu sannan yace "Is
a long story bari muje gida kisha labari" . Tuni
maganar jin tsoron jirgi ya sha ruwa saboda, ga
ni ga masoyina Ustaz dan gaske,Ban sake
magana ba illa sakin murmushi Shi ma
murmushin yake ya jawo ni gefen kafadar sa ya
kwantar akan kafadarsa Akunne ya rada min
"Aysha kiyi barci . Na san kin dade baki yi barcin
farin ciki ba" Na saki murmushi don kam azahirin
gaskiya ya fada Wani annuri ne yake shiga
zuciyata na lumshe idona kamar mai barci sai dai
sam ba barcin nake ba zallar soyayyar Ustaz ce
take ratsa duk wani ilahirin jikina, . Ina kuma
sake jaddada godiyata ga jalla ta'ala buwayi
gagara misali Da son na san yadda reshe ya juye
da mujiya al'amarin Allah kenan kana taka Allah
na tasa .Ta jalla itace gaskiya Azaton Ustaz barci
nake don haka bai tashe ni ba don ko da aka
kawo abinci ma karba kawai ya yi ya ajiye min
nikuma na yi lamo sam ba na son narabu da jikin
Ustaz Ina shakar kamshin sa mai sake
tsuma,soyayyar sa azuciyata sai asubar can garin
sannan muka isa Gaba daya Ahmad ya kankame
hannuna tamkar wani zai kwace ni awajensa
Wani rantsattsen hotel ya kama mana tamkar
aljannar duniya zuciya ta fari kal nake mayar da
kafata duk inda Ustaz, ya ajiye tasa Shikuwa sai
jifa na yake da wani salon murmushi Zama,yayi
abakin gadon hade da fadin "Wash,Allah " ya
lumshe,ido ni ma bin sa nayi . Da ido lna masa
kallon zallar so Ustaz ya miko min hannu "Zo
Ayshat" Ba musu na isa,ga ustaz cikin ta kun,jan
hankali amma sam na ka sa,karasawa gareshi illa
narungume hannaye ina jifanshi da murmushi
shidin ma kashe ido yayi yace "mekenan aysha?
Ina fatan ba kunyata kike jiba? . " Na dan makale
kafada alamar ba za niba Da sauri ya mike ya,iso
gareni "Why aysha? Don Allah kada muyi haka da
ke kada ki disashe farin cikin danake shirin samu
atattare dake awannan daren Ayshata please
enough is enough komai ya wuce don
Allah"yafada yana langa be kai Ni kuwa sake
shagwabe fuska nayi nace Ustaz me ya sa kuka
wahalar dani kuka ki bayyana,gaskiya? murmushi
ya sake yi yace "Har na hango aysha a asibiti da
angonta tana muzurai" ya tuntsure da dariya
abinda ban taba ganin ustaz ya yi ba Don haka
nabishi da kallon mamaki kuma sosai dariyar ta
yi masa kyau ya sake bina da kallo "kina tuna
bama- baman hara rar da kika dunga aika min a
asibiti? . . Na kwace fuskata zan fashe da kuka
Da sauri ya kamo hannu na "Come on Aysha,yau
ba . Ranar kuka ba ce so nake kawai.na nu
namiki zallarso Aysha I am in need" ya fada yana
lumshe,ido Tare da janyo hannu na Nace "Ustaz
don Allah kabani labari" Da sauri cikin dushewar
murya yace "Ba zan iya komaiba yanzu sai na
samu,nutsuwa" Shiru nayi da ba kina don na lura
abin nasa ba sauki. . *** *** *** . WAYEWAR GARI
A ABU DHABI . Duk da sanyin asuba da yake
ratsowa ta window hakan bai sa na tashiba
Ustaz, tuni ya tashi ina ta jin motsinsa har.Bacci
ya sake dauke ni Diso-dison ruwa da yake
digomin akan fuskata, shiya sa na bude idona.
Ustaz ne tsaye akaina ya dan sunkuyo yana min
wani sihirtaccen kallo da murmushi akan lebensa
yace "Beauty a,tashi ayi wanka ayi sallah
mana"Na,dan turo baki nace "wallahi na gaji
Ustaz" Ya dafe hannu na yamikar dani yana fadin
"am very sorry beauty, laifi nane na wahalar da
ke dayawa But am very sorry Laifin so ne" ya
fada yana kashe ido daya sai da ya rakani har
kofar bandaki sannan ya ja min kofa yana fadin
"ayi wanka sosai beauty banda jika- jika" Nayi
murmushi . Na shige cikin toilet din koda na fito
tuni Ustaz ya shimfida min daddumar sallah nan
na tada sallah na dade ina gode Allah acikin
sujjada bisa ni'imar da yayimin ta dawo da Ustaz
cikin rayuwata akaro na biyu Duk da godiyar da
na yiwa ubangiji anafilar ma'aurata da mukayi
adaren jiya Ina zaune ina karatun littafi mai tsarki
Ustaz,ya turo kofa yashigo cikin wata jallabiya
light green colour yazauna agefena hade da sanya
kansa akafada ta yace "kada ki roki ubangiji ya
kara min sonki please Abar ni haka wallahi a
hakan ma wahala nake sha Tuni sonki ya
cunkushe,min zuciyata . Bana iya aikata komai
sai zallan tunanin ki Idan za ki roki Ubangiji ki ro
keshi ya rage min sonki" Wani kallo na dallare shi
dashi yayi murmushi kafin ya lumshe ido ya
kankameni cikin slow voice yace "Ya Allah ka
ragemin..." Da sauri na toshe bakinsa nace "Ba
amin ba" murmushi yayi yace zo ki sha,tea Allah
yabarmu tare forever" Na saki murmushi ni kadai
na san annurin da ya baibaye min zuciyata Zuba
min tea yake a cup amma gaba daya hankainsa .
Akaina yake Na sa hannu zan karbi tea din bayan
yagama hadawa gaba daya ya hada hannuna ya
matse "Allah yaki yaye ai inde ina raye kuma ina
kusa dake kin daina ci da sha da kanki." Yajanyo
ni gefensa yashiga san yamin cup din a baki
maza kisha gimbiyata 'yar albarka mai tarin
alheri da ni'ima Na lumshe idona ina hasashen
dalilin da ya sa Ustaz yake min wannan sumbata
tun daren jiya Bayan mun gama breakfast na
koma gado da niyyar komawa,barci don barci
nakeji har alokacin Ustaz yakawar da kayan ya
biyo ni kan gadon Barci za ki koma? Na daga kai
cikin muryar shagwaba na ce masa "wallahi
Ustaz barci nakeji" Yajawoni jikin sa yana cewa
maza kiyi bacinki dama labari zanbaki na
abubuwan da suka faru bayan kince ba kya sona
da sauri na mike nace please Ustaz gaya min Ya
lumshe ido yana murmushi . *** *** *** . Tun
Sanda kotu ta wanke ki tas daga zargin da ake
miki naga kina watsomin kallon tsana tuni
gwiwata tayi sanyi don nasan da kyar idan za ki
sake amincewa da soyayyata akaro Na biyu.AGA RAYUWA book 3 part 13
NAGA RAYUWA book 3 part 13
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:24
Bansare da al'amarin ba saida na biki gida Nan
ma naga babu wata mafita don kuwa karara kike
min kallon tsana Haka natafi gidanmu gwiwata
asanyaye mamata na zaune afalo ta dubeni itama
cike da tausayawa don tsukun wannan lokacin
sam ba ni da sukuni wallahi Aysha ko abinci ba
na iya ci sai mama ta tursasa ni. . Lauyoyi kuwa
na nemi sama da mutum ashirin sai su ce wai
sunji labarin shari'ar lamarin yashigo da minister,
kuma babu wanda bai san shiba wajen tsaurin
rai. Abune mai sauki ya iya sa mutum yarasa
aikinsa kuma ya bata record dinka gaba daya
Hakan ya daga hankalina duk wani kasuwancina
na dakatar dashi izuwa wannan lokaci na yarda
da cewa Asiri aka yimiki ko kuma aljanu ne suka
shiga jikinki mama taja ajiyar numfashi tace "Ya
ya akayi shari'ar?" Na lumshe ido nace "mama
shari'a yau ta kare don kuwa an wanke aysha
daga zargin da ake mata,bata da laifi ko daya"
Wallahi Aysha sai alokacin nasan mama tana son
ki .Wancan abinda ya giftane ya sa kika fita
aranta Hamdala tayi sosai ranar ta taba fadar
sunana tace . Ahmad to ya akayi? Nan nabata
labari na dora da cewa mama ina tsoron kada
Aysha ta juya min baya mama ta dan yi jim kafin
tace Ni kaina Ahmad ba kai ba ina fargabar kallon
da Aysha za ta yi min na sani sosai mu ke da
laifi awajenta amma insha Allahu baza ta juya
maka ba ya ba Shi yasa kika ga mama har yau ta
kasa zuwa inda kike saboda matsananciyar
kunyarki da takeji Ban daddara ba nasake
komawa wajenki sai dai ko fitowa baki yiba balle
kizo ki saurare ni Usman ne yadunga ba ni hakuri
hade da,sanar da ni da zarar komai yalafa zaki
saurareni yanzun kam zuciyar ki azafi take wajen
son kiga kinyi ramuwar gayya Hankalina kin
yarda da shawarar Usman yayi na koma ta
bangaren Abba shima exactly kamar yadda
Usman yafada shima haka,ya fadamin hankalina
ya sake tashi gani na ke kamar na sake rasa ki
forever{har'abada} don tilas daddyna ya shiga
maganar ganin yarda na ke ta sake
daga,hankalina tsoron kada ciwona ya,sake, tashi
akaro na biyu. Da kansa ya je ya sami Abba suka
kuma kashe magana akan nabarki ki huta . Na
daina matsa miki Abba ya sake jaddada min ya
san kina sona kawai bacin raine ya jawo hakan
da kuma miskilanci irin naki. Shi yasa kika ga
kwata-kwata na daina neman ki akan dole na
tilasta wa zuciyata duk da sautari kasa jurewa
nake.... . TOFA KUDAI KARAYIN HAKURI NAN MA
YAYI DAMAGE AMMA DAGA NAN HAR KARSHE
BABU DAMAGE . Murmushi nasaki bayan na
gama,jin labarin Ahmad ya matsa hannuna
yace"hope kin gamsu My Angel"Runtse idona nayi
na ce yanzu kana nufin Humaira itace matar
mahmud? Ahmad ya daga kai yana wurgo min
kallon kasan ido Nace amma Allah ya sani
kunshamma ceni kun kuma bawa zuciyata
matsananciyar wahala Don ko barci gagara ta
yake yi Na fada fuskata adan hade Ahmad ya
mintsini kuma tuna kafin yayi dariya
har,wushiryar sa ta fito yace Ba komai yajawo
minba sai miskilanci yanzu don Allah da ace da
gaske wannan mutumin aka ba ki ya za kiyi?
Babu yadda zanyi sai dai nasan ba abin Mamaki
ba ne auren sa ya zama ajalina Don kam ina
kinsa ina yimasa zazzafar kiyayya wacce ba zata
kwatantu ba wai don Allah a ina kasamoshi?
Ahmad ya saki murmushi yace Direban kamfanina
ne na san Aysha na sani ta tsani mutum
mummuna Don haka na hada ki dashi ko don na
sha dariya Na mike daga cinyarsa da nayi
matashi da ita Fushi kikayi? Haba Aishata How I
Wish ana rewinding na komo miki yadda kika
hade rai a jirgi duk fa ina kallon ki yadda kika . Yi
tamkar ki zunduma ihu Ina sane, dama na saka
suit don nayi miki BASAJA nasan bazaki taba
kawowa ni ne ba Gaba daya na miki hanya da
niyyar ficewa daga dakin don na lura Ustaz bazai
fasa tsokanata ba ji nayi ya finciko ni Na,
wuntsilo gaba daya nadawo gareshi Ina zaki?
yace min cikin wata murya Ji na yi wayarsa ta
hau ringing, ina kai dubana akan screen din naga
an saka MY WIFE. Take wani kishi ya
dabaibayeni duk annurin fuskata ya bace bat cikin
hanzari na mike nafice daga dakin da sauri amma
abin mamaki Ustaz baiyi yunkurin biyo niba Inaji
yana kashe murya,yana amsa waya murya kasa-
kasa sam bana jin me yake cewa Turus nazauna
akan kujera wasu zafafan hawaye suka zubo min
zuciyata tashiga bugawa saboda tsananin kishi .
Tsawon mintuna kafin ya fito daga dakin yana
kiran "My angel ina kike Ne?" Haushin sa naji ya
turnike ni azuciyata turus yayi ganin ina kuka
cikin sanyin jiki ya matso kusa dani ya zauna
yana kokarin ja na Cikin zafin nama na kwace ina
masa kallon munafiki Yanzu haka duk abinda
yakemin . Yi tamkar ki zunduma ihu Ina sane,
dama na saka suit don nayi miki BASAJA nasan
bazaki taba kawowa ni ne ba Gaba daya na miki
hanya da niyyar ficewa daga dakin don na lura
Ustaz bazai fasa tsokanata ba ji nayi ya finciko ni
Na, wuntsilo gaba daya nadawo gareshi Ina zaki?
yace min cikin wata murya Ji na yi wayarsa ta
hau ringing, ina kai dubana akan screen din naga
an saka MY WIFE. Take wani kishi ya
dabaibayeni duk annurin fuskata ya bace bat cikin
hanzari na mike nafice daga dakin da sauri amma
abin mamaki Ustaz baiyi yunkurin biyo niba Inaji
yana kashe murya,yana amsa waya murya kasa-
kasa sam bana jin me yake cewa Turus nazauna
akan kujera wasu zafafan hawaye suka zubo min
zuciyata tashiga bugawa saboda tsananin kishi .
Tsawon mintuna kafin ya fito daga dakin yana
kiran "My angel ina kike Ne?" Haushin sa naji ya
turnike ni azuciyata turus yayi ganin ina kuka
cikin sanyin jiki ya matso kusa dani ya zauna
yana kokarin ja na Cikin zafin nama na kwace ina
masa kallon munafiki Yanzu haka duk abinda
yakemin . Haka yake mata koma fiye da haka?
yanzu waya san irin dadin kalaman da ya
gaya,mata? gashi yanzu nima yazo yan wani
rangada min ANGEL Ahmad ya waro ido yana min
kallon mamaki Ayshat lafiya? Na watsa masa
harara karshe na,mike na fice lambun gidan inda
wani makeken Swimming pool yake na zauna na
zira kafafuna ina wasa dasu Gaba daya natafi
duniyar tunani Allah ya sani tun farkona natsani
kishiya musamman ga mijin da,nakeso Ji na yi,an
dafa kafaduna na san Ahmad ne don haka najuyo
cike da tsawa zan sauke masa kwandon rashin
mutunci sai na kasa saboda salon kallon da
Ahmad yake min tuni jikina ya mutu sai tarin
kwalla kasan idona Ahmad ya kama hannuna
"please Ayshat Ki zama good house wife mana
MACE TA GARI mai kokarin faranta ran mijinta a
kowane situation kada ki biye rudin zuciya
shaidanne kawai mai kokarin son kai mutum ga
halaka Na sani kishi ne yakai ki ga haka please ki
fatattake shi ina son ki Aysha kuma babu macen
da zata ka mo matsayinki a zuciyata To me zai
saka ki kishi? Babu ruwan Allah da kishi . aduk
yayin da mace ta bata ran mijinta mala'iku tsine
mata suke Na lumshe idona tuni hawaye suka
wanke,min fuskata cikin shisshikar kuka nace Ina
son mijina Ustaz ba na so na aikata sabon
Ubangiji Ya Allah ka gani kai ka dora min kishin
nan Ubangiji ka yaye min..." Tuni kuka yakwace
min Ahmad ya jani yamikar dani tsaye cikin sigar
tausayawa ya hada ni da jikinsa yana lallashi na
Yi addu'a Aysha duk tsanani yana tare da sauki
Tabbas da ina da hali da na sauwakewa
Hameedah to bai kyautu gareni ba, babu abinda
tayimin na tayimin na saketa hakan ya sabawa
koyarwa ta addinin Islama ki yi hakuro ki jajirce
zuciyarki gurin ganin kin zama MACE TAGARI mai
kokarin faranta ran mijinta akowane yanayi Har
daki yakaini ya kwantar dani yaja bargo yalullu
beni cikin ajiyar zuciya na saki murmushi nace
masa Nagode. Yatsun kafata ya fara ja abinka da
ka sa tuni barci yadauke ni Sai can yamma na
bude ido Ahmad na gani zaune,yazuban ido Haba
Aysha barcin ai ya isa kitashi mufita mu zaga"nGA RAYUWA book 3 part 14
NAGA RAYUWA book 3 part 14
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:26
. Namike ina kallon sa yayi kyau sosai cikin
English wears mene ne kike kallo na ne?
Murmushi nayi nace Wai yaushe kafara saka kana
nan kaya? Dama ina sawa amma ba sosai ba sai
time to time haka ki tashi ki watsa ruwa mu fita
shan ice cream ki ga Dubai sisai Cikin slow na
mike na shiga bandaki na dade ina wanka loko-
loko na jikina sai da nagama kuma na rasa ta
yadda zanfito don daga ni sai wani karamin towel
na manta ban shigo da hijab Ba Don haka na
make a toilet din na kasa fitowa sai na hau
kwankwasawa hakan yasa Ustaz ya iso bakin
toilet din cikin murya kasa-kasa yace Ya akayi
matata? Ban bude kofar ba na ce masa Don Allah
miko min zani Cikin matukar mamaki ya banko
kofar yabude ta bakinsa asake yake kallo na Wai
ke me kike nufi? Ni kikejin kunya? Na kuwa takure
waje daya Murmushi yasaki ya tabe baki kafin
yace 'yan'matan Ustaz kenan To kiyi ta zama
idan kin gama jin kunyar kya fito Daga haka ya
fice tsawon mintuna ina tsaye wallahi na kasa
fita jinayi alamun anrufe kofar hakan ya sa nayi
wuf nafice duk . Gudun kada Ustaz ya dawo ya
tarar dani har da murza key na rufe kofar na isa
bakin madubi na zauna akan kujera nashiga shafe
jikina da body oil Gaba daya ina shafa na cinyata
dagowar nan da zanyi na hango Ustaz ta madubi
yana murmushi cikin wani lumshasshen kallo
Fuskata a turbune na mike ina turo baki na hau
tura shi ina fadin please Ustaz meye haka? Fita-
fita nace Kakkarfan Namiji yana tsaye kikam
dashi ko motsi baiyi ba yana ta sakin murmushi
yace Aysha me karfi to tura ni inga ko za ki iya
Cikin matukar galabaita na durkuse akasa na rike
jikina Ustaz ne ya dago kaina Sarkin kunya na
fita maza ki shirya am waiting Sai da na ga yafita
sannan na saki ajiyar zuciya ina murmushi kai
Ustaz ba dama Tsaf na fito cikin wata rigar
Larabawa pitch colour mai adon baki na yane kai
na da mayafi baki ni kaina da na dubi kaina
amudubi sai da nagodewa ubangiji da ya halitta
min kyakkyawar halitta jin takun tafiyata ne yasa
Ustaz ya dago kansa Gani nayi kawai yana ta
sakarmin Flasher da yagaji da daukar hoton yaza
gayo ta . Gefena ya ja ni jikinsa yana daukar mu
atare Zo ki ga tsagwaron kyau Ustaz ya latsa
dimple dina I like you baby bazan iya fita ba
Saboda me? Na tambaye shi da sauri Ya lumshe
ido yace Saboda ke My Ange Anya zan iya rayuwa
babu ke? Da sauri nace masa hameedah ba?
Dariya ya gintse yace ba kyau zancen mutum ba
ya nn sarauniyar yan rigima Na sani ba ya so ya
tunzira zuciyatane ya kama hannuna muje mu
sha ice cream" A shago sai da ice-cream Ustaz
sai wani nan-nan dani yake tamkar wani zai
kwace masa ni musamman da ya lura wani
balarabe ya kafa min ido cikin masifa yaja
hannuna mufita Aysha Har munje gida bai min
magana ba sai mita yake "Iskancin banza sai
kace bai san haramcin haka ba I llar mace mai
kyau kenan daga yau kin daina fita saida
nikab.Na gani idan wani dan iska zai daga nikab
din yakalleki" Sati daya muka yi a Abu dhabi
sannan muka tafi saudiyya a madina muka fara
yada zango a Raudha zo kaga ruwan hawaye
ganin ga ni kabarin sayyidina Rasulullah na zube
dirshan bisa gwiwoyina ina,mika gaisuwata . Da
kirarina agareshi gwarzon mazaje wanda akayi
duniyar da abinda yake cikinta duk dominsa
{S.A.W} Sati daya mukayi amadina muka nufi
makka inda muka gabatar.Da umarar mu sosai
Ahmad yake kaffa-kaffa da ni sam ba ya son ya
aikata min abinda zai bata min rai ko waya da
Hameeda ba ya yi agabana tunda ya fuskanci ina
hassala Ahmad ya jibgo siyayya son ransa kuma
duk inda ya ga kayan baby idan yayi sha'awa sai
ya siya Idan nace masa me ya sa? Sai yace wai
yasan nan da wata tara ya samu baby. Murmushi
kawai nake don ni ma inason tabbas nasamu
baby Don haka nake addu'a Allah ya amsa min
bukatuna na sami babies Don ni nafi sha'awar
Identical twins kamar ni da 'yar uwata humaira
Abinda yabani mamaki bai wuce ganin yadda har
yau babu wanda yanemeni awaya daga, gida ba
sai dai Ahmad yace sunyi waya suna gaisheni
kuma ba ni da waya balle na kirasu Mamina ma
nasha nemanta ba na ganin ta online akullum
naje ka'aba kuwa sai na roki ubangiji akan Allah
yahuci zuciyar mamina ta amince ta dawo
gidanmu kada Allah ya ba wa wani . Damar
aurenta. Har hawaye nake ina sake jaddada
bukatata ga jalla Rabbana Yau ma Ustaz shi
kadai ya fita don kwana biyun da suka gabata
wani matsanan cin zazzabi nake da amai Ina
galabaita sosai shi kansa UstaZ gaba daya
hankalinsa ba akwance yakeba Ba inda nake
zuwa sai harami ina kwance na lumshe idona
tamkar mai barci sai dai sabanin hakan
tsagwaron tunani ne ya cunkushe min kwakwalwa
ba tunanin komaib face yadda rayuwa take juyin
waina na sama ya koma kasa Tabbas na amince
da cewa duniya ba matabbata ba ce Ba komai
acikinta fiye,da rudani rayuwar yanzu ta zama
abin tsoro yau gareka gobe ga waninka Babu
abinda bawa ya kamata yayi face ya tsaya ya
jajirce wajen bautar Ubangijinsa. Idan bawa yayi
hakan fakat ya gama sai ya mika lamarinsa ga
Allah ya yi addu'a Allah ya sa ibadar da yayi
karbabbiyace a wajen jallah Rabbana Saboda
mutum bai san ranar mutuwar sa ba tafiya kawai
kake adoron kasa baka san yaushe ne zaka
mutuba kai da zaka koma kahadu da Ubangijinka
to me ya kaika shagala da duniyar nan har
kamanta . da makasudin da ya sa aka halicce
ka? wanda ya halicce ka fa ba don ka shagala
yahalicce kaba ba don ka sha ba da biki ko shan
giya zuwa club neman mata ko kallon batsa ba
duk manyan zunubai ne da Allah yake fushi da
wanda ya aikata hakan Yi da mutum,zunde da
kifce,da yafice,duka manyan laifu kane da ayanzu
mutane suka dauke su ba komai ba musamman
hassada da take cinye kyawawan Ayyuka kamar
yadda wuta ke cinye kirare Lumshe idona na sake
yi kawai sai ga hawaye na tsananin.Tsoron
haduwata da Rabussamawati hakan kuma ya
zama dole gare ni gareka ga kowanne dan'adam
ma" Ji nayi anshafi hawayen da yake saman
fuskata ko ba afadaba na san Ustaz ne,ina bude
idona naganshi a durku she agabana gwiwoyin sa
zube akasa ya kuma kura min ido cikin
mummunan tashin hankali yakama hannuna ya
damke cikin nasa kawai gani nayi shima Ustaz
yana hawaye na ware idona sosai don son sanin
me ya saka shi hawaye "Aysha ciwon ne yake
wahalar dake tashi muje asibiti wallahi da ina da
iko da na mayar da ciwon nan jikina" mikewa
zaune vels / NAGA RAYUWA book 3 part 15
NAGA RAYUWA book 3 part 15
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:27
. Na saki murmushi hade da girgiza kai yallabai
ba ciwo ne ya sakani kukaba natuno yadda
rayuwar duniya yake kawai.Shiya daga min
hankali Ustaz ya saki ajiyar zuciya kafin yayi kasa
da kansa yace "Dole ya daga miki hankali Aysha
ni kaina,na kanyi wannan tunanin ga duk mai
tunani ma dole ya dinga wannan
tunanin.Al'amarin duniyar nan dole ya baka tsoro.
Abubuwan da suke faruwa acikinta dole kasan
karshenta yazo saidai mutum ya na addu'ar
haduwar sa da Allah salin-alin wallahi a duk
sanda na tuna akwai hisabi akwai wuce siradi
wanda masifarsa ta wuce kwatance amma akwai
sauki ga wanda ya,dace ya yi aiki nagari, natuna
akwai tsayuwa agaban wanda ya,halicce mu.
Aysha ta shin hankali nakeshiga fiye da,zatonki.
Nakan yi kuka tamkar raina zai fita.Amma wasu
sam ba sa wannan tunanin sun shagala da duniya
da abubuwan more rayuwa na duniya bayan ba
don haka aka halicce mu ba. Tunda Allah {SWT}
yana fada cikin littafinsa mai tsarki "WA MA
KALAKATUL JINNI WAL'INSI ILLA
LIYA'ABUDUN" [ba mu halicci mutum da aljanba
sai don..] . Toh yanzu bawa idan dai har ya san
bautar Ubangiji aka halicce shi mai zai saka ya
shagala da Al'amarin duniya? sai dai fatan shiriya
rayuwa yanzu tabbas ta zama abin tsoro kedai ki
jajirce wajen sallolin ki biyar. Idan kin sami iko
dare da rana azimin nafila musamman Litinin da
Alhamis,ki jajirce wajen tilawar Alkur'ani, Zikirin
safiya da maraice yawan salatin Annabi da
Istig'fari hade da hailala. Idan kika aikata haka
ina tabbatar miki zakije Lahira fresh MACE
MUMINA matukar kin yi hakan da kyakkyawar
niyya Allah yasa mudace." Cikin sanyin murya na
amsawa Ustaz da "Amin" Gaba daya jikinmu yayi
sanyi A ranar ko siyayyar da Ustaz yayo ban
duba ba Muna,kwance Lamo sai da la'asar ta yi
sannan muka fita harami wanda ba ma dawowa
sai bayan isha sannan ne za mu zaga mudanyi
siye-siye saikuma mudawo gida To yau bayan
ishar asibiti muka nufa don jin yadda jikina yayi
zafi Ustaz yakafe sai munje asibiti Dubawar farko
da likitan ya yimin, ya bukaci naje agwada jinina
akuma yimin test din fitsari Duk da larabci suke .
Magana da Ustaz ni kam kadan-kadan nake
tsinta don ban kware ba a,wajen Larabci Ustaz
dai yana koya min kadan- kadan na sn dai nan
gaba kadan zan iya kwarewa Larabawan da suke
cikin lab din asibitin da mutunci da fara'a suka
fara hidima da ni kai daga gani ka san addinin
Islama ya shigesu sosai ta yadda suke koyi da
sunnar mai'aiki wajen karrama dan Adam ba irin
sauran wasu asibitocin mu na nan Nageriya ba
da wasu ma'aikatan jinyan suke wulakanta dan
Adam saboda 'yar dama da Allah ya ba su amma
fa wasu na ce wanda yasan ba halinsa bane to
baika mata ya damu ba. Bayan sun gama cikin
mintuna kalilan suka miko min takardar
sakamako suna murmushi hade da ce min
"Congratulations" Shiru nayi hade da cewa
"Thank you", Na juya na fice na san dai abin
nema ne ya samu ciki ne dani Likitan ma
murmushi yayi sannan ya,dago ya dubi Ahmad ya
mika masa hannu sai da ya jijjiga hannun Ustaz
din sannan ya ce "Weldone my friend
congratulation" Sannan ya mika masa takardar.
Ahmad yana budewa ya saki murmushi hade da
daga hannunsa . Sama yace "ALHAMDULILLAHI
BI NI'IMATIHI, TATUMMUSSALIHATI" ya juyo ya
dubeni yace "Ayshata ki godewa Ubangiji don ya
yi mana babbar kyautar da ba kowa ne yake
samu ba Allah kuma ya raba ku lafiya" Murmushi
na saki cikin matukar jin kunyar Ustaz. Doctor ya
miko masa takardar Ustaz ya janyo hannuna ya
ra bani da jikinsa cikin tausayawa yake, sake rada
min "Sorry my dear how I wish zan iya mayar da
shi jikina ki huta da wannan wahalar Amma ki
saka azuciyarki Ibada kike Insha Allahu za ki
samu rabo mai girma awajen ubangiji. "Ka ji
mazan kwarai masu tausayawa matansu lokacin
da suke cikin lalura kuma suke jin tamkar su
mayar da cutar jikinsu. BA MUNA MAZA BA masu
nuna halin ko in kula alokacin da matansa suke
cikin lalura Su tsangwame su Wasu ma har
kyamatar su suke nuna rashin tausawar su
garesu Mu dai mun gode Allah dabai nufe mu da
auren irin wadannan mutanen ba" Shukran Lillah.
BAYAN SATI Jirgin mu ya ta so daga birnin
Makka inda zamu yada zango akasar mu ta gado
wato Nigeria. . Cikin walwala nake ta son haduwa
da 'yan uwana sai dai awani barin ina alhinin
barin kasa,mai tsarki Abin mamaki airport din
damkam take da 'yan uwana da na Ustaz wai duk
murnar an zo tarar mune farin ciki ya mamaye ni
hango mami da nayi tana sakarmin da murmushi
da sauri na saki Humaira da khadija kanwar
Ustaz Na isa ga Mamina na rungume ta cikin
matukar farin ciki ita dinma ta rungume ni ji nayi
Ustaz yana cewa Mamin mu ta yi ahankali ba,ita
kadai bace Mami ta sakar masa dakuwa Ni kuwa
kunya ce ta dabaibaye ni ganin yadda,Ustaz ya
fallasa ni ba ta re dayaji kunyar iyayen mu da
suke wajen ba Ciki kuwa har da babana da nasa
Sai alokacin ma na hango ashe harda mamansa
Suna tsaye ne da ita da Ummana Da sauri na isa
garesu ina niyyar durkusawa mama tayi saurin ka
ma ni tace "Barshi Aysha ba sai kindur
kusa,ba".Taraba ni da jikin tana sakarmin
murmushi Ta ce Ya jikin naki? Ustaz yace kinsha
jiki" Na sunkuyar da kai cikin matsanan ciyar
kunya Yaya usman ne ya karaso wajen yana
murmushi.Yace Aysha ina mijin naki? . Alhaji
maitumbin Nair? Na wurge shi da hararar wasa
duk gurin aka saki dariya Humaira Sis tace "Wai
har na hango Aysha sis lokacin da take muzurai
zan aure mata miji" Na kaimata duka da sauri ta
buya a bayan maman Ahmad tana fadin "Taimake
ni mamanmu" Duk gurin dariya ake haka muka
rankaya aka shiga motoci da niyyar raka ni gida
Tunda aka bude wawakeken gate din nake kallon
gidan nawa da na yi wa lakabi da Aljannar duniya
Titine fetal, kafin ka shiga cikin harabar gidan
Shuke- Shuken da suka kewaye gidan sun
matukar kawata shi. Kana shiga harabar gidan
daga gefen da aka yi wani hadadden parkin space
sai daya gefen da akayi wani hadadden garden da
yaji grass carpet da kujeru masu lilo kala-kala sai
fitulu daga can ciki kuwa wani babban
Swimming,pool ne sai tsuntsaye kala- kala masu
kyawun launi da suke ta yawo ciki kuwa harda
aku da dawisu Gurin ya kawatu sosai Zaka hango
wani step.Da wawakekiyar kofa sai karfe da ya
zagaye wajen nan ne harabar gidan. Kina shiga
kofa falone mai girman gaske sai kofofi guda 4 .
Duk wacce kika bude falo ne guda biyu daya cikin
daya sai bed room guda daya da kitchen, A
babban falonma akwai wata kofa idan kika bude
babban kitchen ne da ya hada kaya na al'farma
akwai kofa a kitchen din da bukkoki guda uku
masu kyawun fasali da kuma Swimming,pool
haka tsarin gidan Ustaz tabbas gidan ya yi kyau
matuka da gaske. Ina gefe jikin mamina ina
kallon Humaira da su Jamila da A.Khadija da
suke hada-hadar zuzzuba abinci suke kayatacci
yar Walima suka hada mana ta murnar
dawowa,lapiya Ni ba ta abincin nake ba so nake
kawai na kebe da Mamina don haka na ja
hannunta nace "Mami dan zo kiji" Wani
kayataccen daki muka shiga Mami fadi
take"Alhamdullahi, yanzu duk wani burina ya cika
Aysha ta yi aure a inda ba za ta wulakanta ba" Ni
dai murmushi kawai nake saki na zauna agefen
hadadden gadon Mami kuwa stool ta ja ta zauna
"mene ne wai kika rabo ni daga cikin mutane kika
kawoni nan?" Na shagwabe fuskata nace "Mami
tambarki zanyi, Inajinki sarkin shagwaba Ashe
haryanzu wannan halin naki yana nan"UWA novels / NAGA RAYUWA book 3 part 16
NAGA RAYUWA book 3 part 16
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:29
. Na yi murmushi nace "Mami don Allah anmayar
da aurenki ne?, Taza ro ido tace Da wa? Na kara
bata fuskata kamar karamar yarinya nace Da
Abba mana A'a tace min Hawaye ya fara zubo
min shikenan murnata ta koma ciki
Ashe,hasashena bai zama gaskiya ba sai da ta
bari na yi kukana mai isata sannan ta tuntsire da
da dariya tace BURIN AYSHA MAFARKIN AYSHA
YA CIKA NA KOMA GIDAN ABBANTA" Yeeeeh?
yeeee'" Na saki ihu harda tsalle akan gado na ce
"Alhamdulilla,mamina how comes?" Ta gyara
zamanta kafin tace "Kawai dai na gaji da zarya da
aiken da Abban-Aysha yake min hakan ya sa
babana yace lallai sai na komo gidansu Aysha
dama wani course naje na wata hudu ina
dawowa babana ya mayar da aurenmu ba tare da
sanina ko neman yardata ba. Sai bayan komai ya
daidaita Ya kira ni ya sanar dani tilas na koma
gidansu Aysha ba shawara yake ba ni ba umarni
ne amatsayinsa na babana. "Haka na hakura ba
koma bayan tarin hakuri da NADAMAR ABBAN
AYSHA" Nayi murmushi na share hawayen dake
Zubo min bayan nagama sauraren bayanin
MAMIN AYSHA . Cikin zuri'ar GIDAN SU AYSHA.
Mami.Tashare min hawaye hade da cewa Na sani
duka,zuri'ar gidanku suna so na illa shaidan da
ya so ya ruguza dukkan farin cikinmu Tun lokacin
da abin yafaru na tabbatar da cewa dole,Abbanki
ya shiga rudani har ya zartar da BAGAGON
HUKUNCI akaina Banga laifinsa ba sam don ko
waye zai iya zargin da hannuna dumu-dumu a
ciki musamman yadda al'amarin yazo da
sarkakiya, acikinsa. Tilas kowa ya jefa ayar
tambaya akaina, duk da hakan ya jefani cikin
tashin hankali ganin yadda mutane suke, kallo na
ahagunce. Hakan ya sosa zuciyata abu daya da
ya burgeni ganin yadda Ummanki sam ba ta
amince da hakan ba. Hakan ya tabbatar min da
nagartar Umma" Na ja ajiyar zuciya bayan
sauraren jawabin Mami Daidai lokacin Humira ta
shigo, da tsallenta turus tayi sai kuma ta juya ta
na dariya Mami ta kwala mata kira Ba ta dawo
ba illa amsa mata da ta yi tana cigaba da
magana "Babu maishiga tsakanin uwa da 'ya
dama Abba ne yace na kira masa amaryar sa
suci abinci" Baki Mami tabude sai kuma ta saki
murmushi . Tace "Mhn..Aysha wannan kanwar
taki, da rawar kai ta ke amma Ummace take sake
sangartata yarinya an mata aure amma koda
yaushe sai taxo gida don tabara" Nace mami ai
baki ga komaiba da bakya nan ba ki gani ba ko
da yaushe Umma nanika ta take ajikinta wai ta
sami gatan daba ta, samu ba Mami tace Umma
ba ta da zance sai na Humaira yanzu tunda ta
fuskanci ta na da ciki sai al'amarin ya bunkasa
koda yaushe bakinta ba ya gajiya da fadin Allah
sarki humaira Allah yaraba lapiya Yauwa da
gaske kema Aysha juna biyun gareki?" Wata
kunya ce talullubeni na sunne kai na ajikin mami
ina dariya Mami ta dago da kaina ta ce "ke tsaya
wani kike jin kunya.?" Idona na rufe na daga
mata kai, Mami tace, Ba shakka amma fa aiki ja
Ya sameki 'ya najin kunyar uwarta shige muje mu
ci abinci." Ustaz ya na ganin mu ya taso ya tare
mu yana kallon mami yace "Amaryar Abba tun
dazu Abba yake aikawa a kira ki" Ya fada yana
kunshe dariya Mami ta girgiza kai tace "Lallai
Ustaz har da kai kenan kun mayar da ni kakar ku"
Gabadaya aka dau dariya . Mamy ta zauna
akujerar da take kusa da Abba aka fara cin
abinci. Sai karfe 8:00 na dare kowa ya baje sai ni
kadai don Ustaz ya tafi shopping.Sai alokacin na
fara jin tsoron gidan musamman da na ji motsin
kofa aibansan sanda na kudundune jikina ba
Hankalina bai kwanta ba har sai da naji sallamar
Ustaz jikinsa asanyaye ya zube ledojin da suke
hannunsa ya zauna agefen kujera ya kuma zuba
uban tagumi da duka hannayensa idonsa a
lumshe. Da azama na mike na isa gareshi na
durkusa gabansa Dafa gwiwoyinsa na yi nace
Lafiya Ustaz.? Baibude idon ba illa ya matse
hannayena cikin nasa Tsawon lokaci kafin ya
bude idon. Araza ne,nadu be shi ganin yadda
idonsa ya,yi jajir nace "Na shiga uku Ustaz waye
ya mutu?" Ya hau girgiza kai "Ni namutu Aysha
wallahi na kashe kaina Bansan dalilin da,ya sa
mama ta tilasta min auren Hameedah ba Aysha
ba zan iya adalci tsakanin ku ba wallahi yau daya
da zanbarki ba kiji yadda zuciyata take bugu ba
ba na son nafada halakar Ubangiji don kuwa ya
umarce mu da muyi adalci atsakanin matanmu. .
Ya sanar damu idan har ba za muyi adalci ba
kada ma muyi biyun Aysha bazan iya adalci
tsakaninku da hameeda ba ya ya zanyi? ya sake
runtse ido Ni kaina hankalina yayi masifar tashi
don wallahi na manta da wata Hameeda Yanzu
kenan Ustaz raba mana kwana zai sunga yi?
Zaidunga zuwa da kin wata ba niba Zan bude ido
wata rana naga babu Ustaz agidan nan yana can
wajen wata yana nunamata soyayya kamar yadda
yake nuna min? na rintse idona kai ni ma wallahi
bazan iya ba ban san lokacin da na fara kuka
wiwi ba Ustaz ma kukan yake yi ahankali yana
kuma bubbuga bayana alamar rarrashi. Daidai
lokacin wayarsa tayi kara alamar ana kira Amma
Ustaz yayi banza da wayar sai ni nasa hannu na
dauka "MY WIFE 2" Naga an saka da sauri na
ajiye masa wayar akan cinyarsa na kuma mike
nashige daki da gudu Na fada kan gado tsawon
lokaci sannan Ustaz ya biyo ni ya tsaya abakin
gadon ban san me yake tunani ba har zuwa
lokacin da ya hawo gadon ya dago fuskata na
rintse Ido "Ta shi Aysha magana zamuyi" Na
bude idona . "Kiyi hakuri kowa da irin tasa
kaddarar mu.Tamu kaddarar kenan Zan tafi ga
wata dattijuwa nan da zata tayaki zama a falo na
miki kiyi ta jan Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un
Zan leko nagan ki gobe tunda sai jibi zandawo
nan Da kudi a drawer dakina ko zaki bukaci wani
abun" Rintse ido na sake yi na fashe da kuka
hade da damke hannunsa kada katafi Ustaz
wallahi in ka tafi zuciyata zata,iya fashewa.
"Babu abinda zuciyar ki za tayi Aysha don ba
akanki aka fara kishiy ba kiyi Nazari da hakan..."
Ina kallo Ustaz yajanye hannunsa ya tafi Wani
kukan ya sake kwacemin shi kenan ya tafi
wajenta A yau ba Ustazun Aysha bane Ustazun
hameeda ne kuka yaci karfina sosai tabbas kishi
bala'i ne sai a yau na sake jaddada hakan Ni ce
har karfe ukun dare ina kwance a haka sam na
kasa rintsawa Juyi kawai nake akan gadon ina
hango fuskar Ustaz yana ta zanga wa hameeda
soyayya kamar yadda yakemin na sake rintse
idona still hakan nake,sake gani Kawai ji nayi ina
furta kalmar"Na shiga uku yanzu haka zanyi
rayuwar aure da Ahmad duk . Sanda zai tafi gurin
wata? Na ji kamar zan mutu Anya hakan zata
yiwu? Na dau wayata ina duba lokaci karfe
3:00na dare na ga ni Ban ji shakkar komai ba na
danna lambar mamina da niyyar kiranta Tsawon
lokaci tana ringin kafin Mamina ta dauka ji nayi
tace Aysha lapiya Atsahon daren nan? Cikin
shisshikar kuka nace "Mamina na kasa barci
zuciyata ciwo take ga kaina yayi nauyi Cikin
kidima itama Mamin tace "Subhanallah! Shi Ustaz
din yana ina?ya barki baku tafi asibiti ba?" Na
sake sakin kuka da karfi nace Mami ya tafi
wajenta Cikin kidima itama Mamin tace ita wa?
Na ce Mami Matarsa mana hameeda"Mami
tasaki nannauyan ajiyar zuciya tace "Wallahi
kinbani tsoro Idan na fahimci matsalarki Aysha
kishi ne ya kamata kuwa ki ajiye shi agefe duk da
ansan yana da ciwo amma yana zuwar wa
mutum a inda mutum yadau keshi idan kadau
keshi da zafi zaizo maka da Zafi, idan kuwa
kadau keshi da sauki sai ya zo maka asaukake
Don haka inaso ki dauke shi da sauki please and
please Aysha ki yi koyi dani da Ummanki, kada ki
ba mu kunya"
A novels / NAGA RAYUWA book 3 part 17
NAGA RAYUWA book 3 part 17
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:31
. Na rintse ido nace"wallahi Mamina bazan iyaba,
kowacce mace da yadda Allah yayita ni Allah
yayini acikin mata masu tsananin kishi Ba zan
Iyaba mamina"Cikin tsawa mami tace "Zaki iya
aysha kowacce mace koya take har ta saba.
Haka ke wacce irin yarinyace mata nawa aka
yiwa kishiya suka zauna lafiya..." Fashewa
dakuka nayi ganin yadda Mami ta harziko Cikin
tattausan lafazi mami tace "aysha saurare ni kiyi
shiru haka maza ki tashi kije ki yi alwala kiyi
sallah zaki samu sauki azuciyarki kinji?maza
tashi aysha." To Nace sannan nabi shawarar
mami na mike nashiga toilet cikakkiyar alwala na
daura ina fitowa na fuskanci alkibla ina sallah ina
hawaye acikin sujjada na dade ina kaiwa Allah
kukana akan ya yaye min wannan matsanan cin
kishi koda na gama agurin na kwanta ina mayar
da ajiyar zuciya Tabbas wallahi kishi ciwo ne
babu maganinsa sai addu'a bansan lokacin da
barci ya daukeni ba Karar waya ne ya farkar dani
daga nannaiyan barcin da ya dauke ni ina kai
dubana kan screeb din wayar naga sunan
REALITY ya bayyana. . Na san Ustaz ne nayi
tsaki naduba agogo karfe 5:45 yaje
yasha,soyayyarsa da barcinsa sai yanzu ya tuna
dani. idan har ya damu dani meyasa bai kirani ba
tun jiya? Gaba daya kashe wayar nayi namike
nashiga toilet Ko da na idar da sallar barci ne ya
sake yin awon gaba, dani akan sallayar. Shafar
fuskata da naji anyi shi ya sa nabude idona.
Ustaz ne zaune agabana ya zuba min ido cikin
tausayawa Ban mike daga wajen ba illa ma
dauke, kaina da nayi daga kansa na sake lumshe
idona Ji nayi yasaki ajiyar zuciya yace "Aysha kiyi
hakuri please ban san yadda zanyi ba Ni kaina sai
ajiya na sake yarda ba Zan iya adalci
atsakaninku ba Ina tare da hameeda ne kawai
amma ruhina kacokam yana kan aysha ko da na
kwanta juyi kawai nake ina tunaninki Gashi ba
damar kiranki don ina tare da ita Zai zama kamar
cin fuskane" Sake tunzira zuciyata yayi jin yace
wai yana tare da ita Wato yana sanar da ni tare
su ka kwana a daki daya. Yakamo hannuna tashi
Aysha ba dai anan kika kwanaba akasa." Na
dauke kaina cikin tsiwa nace "ina ruwanka . dani,
tunda kai kayi kwanan farin ciki ka kwana a
luntsumemen gado tare da farin cikin ranka Ajiyar
Zuciya ya saki sannan ya saki murmushi yace
kwantar da hankalinki MY ANGEL! Daga yau
Ahmad ya zama naki ke kadai banbar gidan ba
sai da NA SAKI HAMEEDA Wai don gulma kuma
sai nazaro ido nace Saki? Ustaz why? Yalakuce
min hanci "Kaji gulma Natabbatar har zuciyarki
cikin farin ciki kike" Na girgiza kai "Ko daya
Ustaz, ko ba komai Hameeda mace ce yar uwata
ba zanso abinda yafaru da ita yafaru daniba me
ya sa, ka sake ta Ustaz? Da ka barni ahankali
zan saba", Ahmad ya dangirgiza kai "Ni ba zan
saba ba Aysha, sam ba zan saba da rashin adalci
ba koda Allah yace mu auri mace sama da daya
saida ya umarce mu da muyi adalci. Idan nakasa
adalcin me kike zaton zai faru dani? tashi fa,zanyi
ranar lahira da shanyayyen barin jiki Me ya fi
hakan takaici? shiyasa na amince rabuwar mu
shine mafi alheri Tun daga mota da na fita, raina
abace yake har naje gidan babu fara'a afuskata
Hameeda na da kirki tatareni da abinci amma .
wallahi ko fuskarta ba na gani Kece kawai acikin
idona Har muka kwanta na kasa yi mata kulawa
irin ta aure duk da na lura da bukatarta kenan
"Shiyasa da safe na yanke shawarar rabuwa da
ita bayan na mallaka mata makudan dukiya da
gidaje sannan muka rabu kuma ta min
kyakkyawar fahimta haka iyayenta ni ma su
Abbana ba su yi fushi da ni ba don haka Ayshata
takwantar da hankalinta Ahmad na tane ita
kadai" Da safe na ga Mamina da ummana
mamaki ya kamani ganin, dukansu fuskarsu
ahade take gabana ya,shiga faduwa har ina hada
harshe wajen fadin "Lafiya Mam?" Ai kuwa ta
aiko min da wata harara hakan yasa na gumtse
bakina Cikin fada Umma tace "kin kyauta Ayshatu
saboda bakin kishinki shine kika sa sai da Ustaz
ya saki matarsa" Da sauri na zaro ido nace "Ni
kuma? wallahi Umma ba ruwana" Mami ciki zafin
rai tace karya kike Aysha ya mukayi dake jiya?
Babu ruwanta mami nida kaina na saki Hameeda
saboda ba na daga cikin wadanda za su iya rike
mata biyu. Bazan iya adalci atsakanin wata
macen da aysha ba dakai na nayanke . Shawarar
sakinta" Haka ya zauna ya dunga fahimtar da su
har suka fahimta Mami tace "Dama Abba ne yace
mu zo muyi mata fada, zata da hadin bakinta
amma yanzu mun fahimta, hakan shine adalci, a
wajen duk maza da zasu fahimci rashin adalci
babbar masifa da sun rabu da auren mata
matukar suka san ba za su iya adalci ba"Daga
haka suka mike Ustaz yace "Umma har zaku tafi
Tace "Dama abinda ya kawo mu kenan don
hankalin Abba ya tashi da ka sanar dashi ka rabu
Da matarka ya zata laifin Ayshatu ne" Ina kallo
suka shige motarsu suna daga min hannu sai a
lokacin wasu zafafan hawaye suka zubo min
tunanin duka al'amuran duniya yanzu ni zasu
zarga Ustaz na ji ta bayana ya hada ni da jikinsa
ya ziro hannu yana share min hawaye "Mene ne
na kuka My Angel? please stop it, I hate to see
you crying." Cikin wata salon murya yasanar dani
haka sannan yaja ni cikin gida yana sake
jaddada,min zazzafar kaunar da ya sabar dani
Ranar da nayi sati biyu da tarewa agidan
gwarzon mijina Ustaz Ahmad Sulaiman da wuri na
tashi, . Na fara shiri don zaikaini ziyara.Zuciyata
cike da farin ciki don na dade ban fita ba, saboda
Ustaz ba ya son yawo don haka ya rokeni ma
nabar zancen karatu don shi sam ba ya sha'awar
koda yaushe mace tana zarya ahanya ya
mallakamin wasu manyan kamfaninsa guda biyu
da gidan mai guda daya duk ya sa aka mayar da
sunana akai. Tsaf na fito cikin wata hadaddiyar
doguwar riga zubin misra, kalarta yelo ma adon
ja. Na yi rolling da jan mayafi na yi kyau sosai,
abinka da mai shigar karamin ciki fatata ta yi
subul-subul tamkar bayan kifi don santsi Gidansu
muka fara zuwa, nan na ga soyayyar surika ashe
kawai surukai masu kirki. Mahaifiyar sa ta
rungume ni sosai ajikinta da kanwarsa Khadija ita
ma nan da sati biyu za ta amarce. Kayan motsa
baki kala-kala mama ta sa aka ajiye min.
Nakuwa ci sosai don kayan kwalama ne Sai
la'asar sannan muka bar gidan Daga nan kuwa
gidan Humaira muka wuce, don babu nisa sosai a
tsakaninsu.Humaira sarkin rawar kai sai tsalle
take da murnar ganina mahmud yana gaisheni ta
cafe da cewa . "Darling ba kace ya bebinta ba"
Da sauri na zabga mata harara "Wallahi Humaira
sam ba ki da kunya" Ta tsuke baki "To kunyar wa
zanji a nan mahmud ko Ya Ahmad?" Nayi tsaki
hade da mikewa na kalli Ahmad ya hade rai tsaf
wai shi yazo gidan kaninsa. Dariya ta so kubce
min don sam hade girar bai karbe shi ba Sai da
muka shiga mota na tuntsire da dariya nace
"Yaya babba manya, irin wannan tsare gida
haka?"Murmushi yayi yace "Usainan nan taki ce
akwai rawar kan tsiya" Duka gidan yayyena sai
da Ahmad ya kaini abinda ya ba ni mamaki bai
wuce yadda suke zaman lafiya da kishiyoyin su
ba tamkar 'YAN'UWAN JUNA. Na ayyana
azuciyata Da ni ce bazan iya ba. Daga nan sai
gidanmu karkaso kaga yadda na yi tsalle na
rukunkume Mami Umma ta dakamin Tsawa tace
"ke cikata ku har abada daga ke har uwar taki ba
za kuyi hankali ba, bayan ga yadda kuke ita ma
ba lafiyace da ita ba." Na waro ido ina kallon
umma cikin mamaki na ce "Mamin? Dubifa yadda
tayi kiba Umma, amma kice ba ta da lafiya?"
Umma ta gallan harara To uwar maganaUWA novels / NAGA RAYUWA book 3 part 18
NAGA RAYUWA book 3 part 18
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:32
. Kibar tata ce miki aka yi ta lafiyace? Duk da
ban so gaya mikiba..." Cikin magiya Mami tafa
rokon Umma wai kada a gayamin na kuwa zaro
ido nace "Na shiga uku me kuke boye min wane
irin ciwo ne da,Mamina?" Ni sarkin hawaye tuni
na sake su kamar famfo Umma ta saki salati tace
"Yanzu Ayshatu kuka kike ke kam zanga lokacin
da girma zaizo miki" Cikin shesshekar kuka nace
"Don Allah Umma me ya same ta?" "Cikine da ita
sai ki taya ta da addu'a."Aikuwa ban san lokacin
da na saki dariya ba kuka yakoma dariya cikin
tsananin farin ciki na sake rungume MAMINA in
cewa "Alhadulillahi Allah na gode maka,da ka
amsa min tawa addu'ar Allah ya raba su
lafiya."Umma ma cikin fara'a take cewa "To me
ye na kukan aikin gama tun da kika godewa
Allah" Nace wallahi Umma kukan tsananin farin
ciki ne ni na sani Umma yau wallahi ba zan iya
barci ba." Umma Tace "Na sani aysha Na sake
cewa "Da fa na yanke shawarar da zarar na haihu
zan dankawa mami abinda na haifa ta raine shi
kamar yadda ta yi min Allah na gode maka Umma
tace Shine abin . Godiya Sai da na bugawa Ustaz
waya atake agurin. Cikin dariya nake shaida
masa shi din ma hamdala ya yi. Da Abba yadawo
ma da fara'a nayi masa Murna shima dariya
kawai yake yana fadin "aysha kenan" Sai dare
UstaZ ya zo muka koma gida zuciyata fal da farin
ciki. BAYAN WATANNI SHIDA Abubuwa da dama
sun faru sun wuce. Ciki kuwa harda
matsananciyar kulawa, kauna da tausayi da Ustaz
yake yimin ganin ina dauke da cikin dansa ko
kwakkwaran motsi Ustaz ba ya so yaga na yi. A
yanzu haka ma shirye-shiryen tafiyar mu Egypt
ake ni da mahaifiyarsa don yace ba zan haihu
anan kasar ba Har da Mami na yake shirya mana
tafiyar don ita awatan haihuwa ma take. Kwance
kawai nake kaina yana wani azabar ciwo, cikina
yayi turtsitsi a gabana. Kafafuwana sun yi luba-
luba, haka hanci na yayi muni sosai kai gaskiya
ciki ba karamin muzanta halittar mutum yakeyi ba
Ammafa wasu fes za ka gansu babu abinda ya
canja sai abinda ba za a rasa ba. Jin motsi nayi
da kyar na juya sai naga Ustaz tsaye abayana
yana doka murmushi da alamun . tsananin farin
ciki a fuskarsa "Ayshatu My Angel, albishirinki?"
Cikin kaguwa da son sanin mene ne nace "GORO
fari katoto."madadin ya fada sai ya miko min
hannu,"kama ni kitashi ki ba ni goron" Na waro
ido sosai Ya kuwa tuntsire da dariya "Ayshatu kin
yi kyau sosai da cikin nan." Harara na watsa
masa don na san tsokana ta yake yi sannan ya
cigaba da wakar da yake min "'yar beauty mai
katon hanci 'yar beauty mai katon lebe." Gaba
daya na shagwabe fuska nace "Kaga ka ga Ustaz
ba na so" Shi ma kwaikwaya ta ya yi "Kin ga -
kinga aysha ina so" Na wurge shi da pillow ya
cafe yana murmushi hade da min wani fitinannen
kallo "I LOVE YOU MY WIFE. Kin shagaltar dani
ban gaya miki albishir din ba MAMINKI TA
HAIHU" Da sauri na mike "Amma ka tsaya kana ja
min rai me ta haifa tashi ka kaini" Cikin mamaki
Ustaz yake kallona yace aysha ashe da kwarinki
kike langabewa, dubi yadda kika tashi ahanzarce
daga sanar da ke haihuwar Mami" Na kwabe
fuska nace Don Allah katashi ka kaini" Babu
musu ya mike ya zira min hijab dina . Muka fice
daga gidan sai da muka shiga mota ya ce "Ba ki
ji me ta haifa ba" Na ce metahaifa? 'yan biyu
duka mata "SHUKURAN LILLAH" Nafada afili.
Ustaz ya saki murmushi yace su aysha anyi
kanne Da hawayena na shiga gidanmu ina
tunanin ashe za mu ga wannan lokacin aduniya
Tabbas Bahaushe bai yi karya ba da yace
Mahakurci mawadaci kuma BAYAN WUYA SAI
DADI. Na zauna a gefen gadon ina kallon mamina
da fuskata cike taf da farin ciki sannan ahankali
itama hawayen ya zubo mata. Umma ma
hawayen take Tace "kukan farin ciki kam ya zama
dole. Allah kenan da ba ayi masa dole shiya ke
ba da haihuwa alokacin da yaga dama" Na dauki
'Yan biyun ina kallo kamar mu daya da su sak.
Wallahi tamkar yadda nake ina yarinya Da sauri
na dauki hotona babba da yake rataye a dakin
mami na kara a fuskarsu. Cikin dariya mami tace
"Ba saikin kara ba, kamar ku daya" Abba yace
"Kwabo da Kwabo kuwa" Aka kwashe da dariya.
Kafin a ce Mene ne wannan? tuni gidan mu
yadinke da hayaniyar jama'a 'ya'ya da surukai da
jikoki. . Kafewa na yi anan zan kwana, amma
Abba ya ce tilas na tafi gidana na dawo washe
gari. Amota Ustaz yake sanar da ni wai bizarmu
tafito jibi za atafi Ni kuwa na zabga masa harara
cikin wasa nace "Ai kai ma ka san ko birnin
Lantsandan ne ba zan tafi ba ayi suna ba." "Kada
muyi haka da,ke aysha kin ga watan haihuwarki
ya kama, tun da dai ta haihun lafiya ba shikenan
ba" Allah Ustaz kada ma ka fara don babu inda
zani sai anyi suna Shiru yayi na lura ransa ne
yabaci duk da haka bazan sauka daga kan
ra'ayina ba.Har mukaje gida bai kula ni ba illa
yadebo min abinci ya ba ni a baki harda tausar
da ya saba min magana ce dai ta fatar baki ta
gagara. ***** ***** ***** Tsakar dare naji bayana
yayi wani irin amsawa ba shiri.Na mike jin
marata ta amsa. Na daka wa Ustaz duka,shima a
razane ya farka, yana duba na yace "aysha
lafiya?Me ya faru?"Da kyar nace masa "Mutafi
asibiti yallabai, marata kamar za ta balle" Da
azama ya daukeni cak inata gumurzu Iya mai yi
mana aiki da ita muka tafi asibitin. . Tsawon awa
guda a asibiti ina abu daya kafim Allah ya yanke
min na haifo santalelen yarona jajir da shi, gashi
har gaban goshi da kibarsa dumimi tamkar diyan
indiyawa. K da idona ya haskomin yaron anfita da
shi wani farin ciki ne ya mamaye ni na tuna wai
wannan da na ne mallakina kai Allah na gode
maka "Alhamdulillah" na sake furtawa ahankali.
Ahmad na ga yaturo kofar yashigo bayan da
likitar tafita Cikin tsananin farin ciki ya dube ni
yana da fa goshina"sannu ayshata da wahala ko?
Ubangiji yasaka miki da mafificin alheri. Ayau na
sake alfahari nakasan cewar ki matata da kika
santalo min kyakkyawan da" Daidai lokacin
Umma da Mami suka shigo mamaki ya kama ni
ganin mami ita da ta haihu jiya amma tafito
yau.Lallai na amince soyayyar gaskiya ce
tsakaninmu kowa sannu yakemun, Maman Ahmad
ta zo kafin asallatu asibitin yacika dan kam da
'yan'uwa da abokan arZiki Ahmad,kuwa sam
bakinsa yaki rufuwa. Humaira ta dubeni cikin
murmushi ta ce, "Aysha sis yaron nan da Ya
ahmad yake kama ko kadan bai dauko ki ba
Lumshe idoovels / NAGA RAYUWA book 3 part 19 the end NAGA RAYUWA book 3 part 19 the end Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:35 . Kawai nayi ta sake cewa "Ya aysha haihuwar da wahala? Wata dariyace ta kufcemin ganin ta da turtsetsen cikinta nace "Ba bayani yarinya sai ranar da kikazo yin taki sannan zaki gane shayi ruwa ne." Murmushi tayi tace tana shafa cikinta "How I wish na bude ido naga babyn.Kawai akwance a gefena batare da na sha wahala ba yana inya inya." Gaba dayan dakin aka saka dariya ganin yadda Humaira ta tsorata sosai Mamina ce ta shigo bayan ta dawo daga wajen likitan mace jaruma tamkar ba ita ce ta haihu ba Ta miko min hannu hade da cewa "Mike mu tafi na amso sallama" Dakyar na mike don jikina kam bai karasa warwarewa ba, duk inda nabi idon Ahmad a kaina "sannu aysha" shine kawai Kalaman da yake jerowa "Hope dai ba inda yake miki ciwo" Na lumshe idona hade da kada kaina koda mukaje gida Hajiyar potiskum ce ta tilastawa Mami tafiya gida fada take tana sakewa "Maza yar albarka ki tafi gida kema fa danya ce sharaf." Murmushi Mami kawai takeyi ganin yadda hajiyar potiskum take nuna mata kulawa hakan ya tabbatar Mata da dinma . bacin rai.Yasanya ta wanke kafa taje har gidansu taci zarafinta. To haka dai 'yan'uwa suka dunga nunamin kulawarsu. An yanke shawarar hada sunana da taron sunan Mami za ayi.Inda za ayi ababban hall dina wato AYSHA IMAM KHALIL {A..K RESTAURANT}. Ranar sunan da safe Ahmad ya sanar da sunan mahaifinsa aka saka wato,Sulaiman, hakan ya sa Humaira ta yi masa lakabi da AKBAR. An taru sosai ashagalin taron sunan. Manyan mutane sun halarci babban shagalin inda 'Ya'yan Mami suka ci suna NILFA da NAUFA. Sunan Mamina da ummana aka saka Mun samu kyaututtuka sosai daga manyan mutane Ustazu na kuwa yana makale da ni tamkar wani zai kwace masa ni. Tsummun idanunsa suna kaina. Daren ranar sunan Ya Ahmad ya sameni adaki azaune agefen gado na jingina da gadon ina lumshe ido tsabar gajiya ce take nukurkusata Akbar nake bawa mama. Fuskarsa adaure yake dubana Yana fareti atsakar dakin hakan ya dan razana ni. Zuwa can ya zira hannu a aljihu ya miko min ambulan fara tas. Gabana ne yafadi , narintse ido na ba ta re da nakarba ba . A zuciyata nace "shikenan an kuma" karbi mana yana fada cikin dakakkiyar murya da tsawa Hannuna na rawa na karba na bude Addu'a nake kafin na karanta. Abinda na gani ne yasaka ni mikewa ba shiri "Ni kuma da gaske Ya Ahmad? Ka ba ni kamfanin sarrafa shinkafa?" Dariya ya saki yace "Da tsorata kika yi My Angel?" Na zube gwiwa ta akasa ina sake godiya. Ya dago ni "Is enough Aysha, duk abinda nayi miki kin cancan ci fiye da hakan. Da ni da dukiyata duka mallakarki ne. Na yi miki wannan kyautar ne saboda jajircewa da kike wajen yimin biyayya akan duk abinda na umarce ki. Kin cancanci sunan MACE TA GARI, MACE MUMINA mai share hawayen mijinta a kowane,yanayi wanda hakan yayi karanci awannan zamanin da mata suke daukan kansu sune a sama bayan Ubangiji yace "Arrijalu kawwamuna alannisa'u" Ya Zama dole mace tayarda itace akasan mijinta shine shugabanta, wanda matan yanzu sundauki hakan rashin wayewa da gidadanci BURIN MACE A ce ita take juya mijinta awannan zamanin babu asarar da ta wuce hakan. Ba wayewa ba ce hakan . illa dabbanci da tabewa hade da rashin zurfaffan ilimin addini. A bayyane take macen da ta ke aikata hakan tana jayayya da hukuncin Ubangiji ne da kuma koyi da yahudu da Nasara. Da suke cewa "What man can do woman can do better". Karya ce wannan da tsagwaron jahilci.shi ya sa nake godewa Allah da ya tsame min matata daga sahun wadannan mutanen. Bayan wannan, yanzu fada min abinda kikeso." Na lumshe ido nace "Babu abinda nake so ka gama yimin komai yallabi sai abu daya kayimin Alkawarin ba za ka taba yimin kishiya ba." Cikin murmushi yace "Na yi miki alkawari Aysha ke kadai kin isheni rayuwa." Hawayen dadi ya sulmiyo min don Burina yagama cika nace . "ALHAMDULILLAH"