Complete Hausa Novels

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel

Reading file: Adade_Anayi_Sai_Gaskiya_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 2 of 2

Cigaba da shafa fuskarshi tayi, hawayen ba su bar zuba ba, amma fuskarta cike da annuri, ta so tayi hakan tun ranarda ga fara ganinshi, dama be bata ba, "Haka ka koma? Haka ka zama? Wannan yarona ne? Haka ka Girma? Ina Alfahari da kai Zaid, wallahi ina alfahari da kai" rungumeta yayi yace "Naji dadi, Naji Dadin da kike Alfahari dani, Naji dadi Mami, ina sonki fiye da rayuwa da kanta, kece komai na Mami, naji dadi da ba ki tsaneni ba, naji dadi wallahi" dariya tayi sosai tace "nima naji dadi, ba zaka gane kalar farincikin da nike ciki ba, nima ina sonka Yarona, Allah ya Albarkaci Rayuwarka, Allah ya Albarkaci Rayuwarku kai da k'anwarka Najwa, ya Albarkaci Rayuwarku tare da Yanuwa da yaran Musulmai duka".
"Ameen" ya amsa, yana jin kanshi a cike da murna, yana jin dadin yanayin da ke shiganshi, Allah ka sa karshen bakincikin mu kenan, Allah ka sa mu samu dauwamamiyar farinciki, Allah nagode maka, Alhamdulilah Ala kuli hal".

Ba ta damu da Girman da yayi ba, bata damu da saura k'iris ya shiga shekara 30 ba, rungume dan yaronta takeyi tana shafa kanshi kamar dan shekara 11 da ta bari a Hassan Ibrahim Gwarzo, ta yi kewanshi sosai, kalamai ba zasu baiyana farincikin da suke ciki ba, ba ta so ta daina jin dadin nan, Godia take ta ma Ubangiji Azzawajala da ni'ima da baiwar da ya ba Danta, zaune tayi kan Gado, shima ya zube kan guiwowinsa tare da daura kanshi akan cinyoyinta, tana shafa mai laulausan gashinshi, suna fira irinta Da da Mahaifi.
(Ubangiji ka bar mu da Mahaifanmu, ka kara mana So da k'aunarsu, kasa suyi Alfahari damu, kasa duk wata kalma da zai fito daga bakinsu ya kasance Albarka suke sama na, Cikin Mahaifan da suka rasu Ubangiji Allah ka yafe musu, ka sa sun huta, ka haskaka k'abarinsu, domin Albarkar Fiyayyen Halitta. Wanda suke da rai kuma Allah ya kara musu nisan kwana Ameen).
****

Zaune take kan stool din Madubin dakinta, ta ji shigowarshi, kamshin turarenshi ya fara sanar da ita da Jaan dinta ne. Kin dagowa tayi har sai da ya shigo dakin gabaki daya, wani abu take ji game dashi wanda ba zata iya bayaninshi ba. Ba kullum suke haduwa su ke6e don yin soyayya ba, ba kullum suke waya ba, amma Soyayyar gaskiar na dashe a cikin rayukansu, daidai Gadon da ke kallon Madubin ya zauna, ya kasance tana kallon madubi amma shi take kallo, shima Madubin yake kallo amma ita yake kallo. Murmushin k'auna suke aikawa ma junansu, kafin Abdulmajeed ya fara magana "PureHeart, bansan ta inda zan fara magana ba, randa na fara ganinki, tun a jirgi, domin Allah naji wani abu game dake, bansan ko meye ba, amma duk kukan da kike yi a Cikin Jirgi haka kurum na tsinci kaina da shiga damuwa, bansan dalilin da ya sa na kasa hakura ba har sai da na tanka miki, bayan nan, zan iya cewa wannan k'auna ce ta jini da bata yankewa, girman yanuwantaka na da girman gaske, saidai rashin sani ya sa a k'i fuskantarsa.

"PureHeart na fuskanci cewa you are so innocent, and naive, zuciyarki me sanyi ce, in miki na wani Rafeeq Lema, yace "Baki da hayaniya, baki da damuwa" Najwa ta murmusa ta cigaba da kallonsh. Ya cigaba "Abun ne ya zame min biyu, Son 'yanuwantaka, da kuma So mai wuyar fassaruwa, Najwa, ina sonki, ina k'aunarki, akwai abubuwa da yawa da suka faru a baya, kuskuren Mahaifiyarta, ban san ko zaki dinga kallona da abun ba, ina--" katseshi tayi ta hanyar cewa "shhh, Jaaaan, ka bar maganar nan, kamar nace maka maganar nan ta wuce kar a sake dawowa da ita? Nace maka a bar abunda ya faru a baya, a maida hankali kan abunda zai faru a gaba. Bansan irinka ba, irin zuciyarka kadan ne a duniyarmu, kai Namiji ne da ko wace mace zatai burin Aura ko burin Samu, ka hada komai, to me zan jira? Me zai dameni? Ina da kai fa? Meri jaan, tumase pyar kharta---" bata karashe abunda tayi niyyan fada ba yayi saurin rufe mata baki yana girgiza kai, yace "Aa, aa donAllah, wannan Indiyancin na k'warata, karki boye min, ki gaya min da yaren da zan gane, PureHeart, ki fada min, ina so naji donAllah" runtse idonta tayi ta fara magana "Ina Sonka Ya Majeed, wallahi ina sonka, ina so na karashe rayuwata da kai, bansan me zanyi ba in babu kai, ba kyaun fuska kadai gareka ba, kanada kyaun zuciya, ina sonka da duk wata jijiya dake cikin jikina, ina sonka da duk wani Jinin da ke gudana a jikina, ina sonka da duk wata na'urar dake aiki a jikina".

A hankali ta bude idanuwanta ta saukesu fes kan Abdulmajeed da bakinsa a hangame kamar yaga wani abu, mamakin kalamanta yake, be taba zaton tahi hausa har haka ba, babu cikin abunda ta fada wanda be shigeshi ba, sak'on da ta aiko mishi ya k'arba, ya kuma so ya maida mata ta martanin da zai fi baiyanar da abunda yake ji a ranshi, sai ji yayi ma jikinshi yayi sanyi, ya gyada kai, yace "Najwa, Allah shine Shaidana, ina sonki Dominsa" Murmushi me k'ayatarwa ta sakar mai, ya mike jiki ba kwar'i yace "bari naje na dauko Yara" Murmushin dai ta sake mai tace "muje nima ina zuwa" be ce mata komai ba yayi gaba, ta dauko Hijab din Sallahnta ta bi bayanshi.
A parlo suka iske Ziyada tana ta Murmushi ita kadai, abunda ya faru tsakaninta da Zaid dak'iku da suka wuce yana sata nishadi, Abdulmajeed yace "Yadai Zuzu?" shashantar da maganar tayi don ya bata kunya ta hanyar cewa "Ina zuwa?" Najwa tace "Su Zeenah zamuje daukowa a School" Ziyada ta mike tace "nima zanje" yace "Aa, je ki gaya ma Mijinki" shagwabe fuska tayi tace "YaMaji fa yana cikin dakin Mama tun dazun fa" Shiru yayi kafin yace "Keke Napep fa zamu hau, su Paapa sun fita da Motar" Ziyada tace "Ooo, inada Miji kamar ZSA dangi na zasu hau Napep? Muje waje akwai Drivers" Najwa ta kalli Abdulmajeed suka tabe baki a tare suka ce "Ahhh Allah ya baki hakuri Matar ZSA" daria tayi tace "ku fada ku k'ara" muje tayi gaba, suna binta a baya Najwa ta bude murya yanda su Zaid zasu jita tace "Maama mun tafi dauko su Zinatu"..
***

Hannunsa ya cire zai rik'o nata, da sauri ta janye kamar wuta zai tabata, da mamaki ya kalleta, ya k'ara kai hannu zai ta6ata, da sauri ta sake daukewa, nan ya gane abunda take nufi da yin haka.
Ya kalli Driver yace "DonAllah kayi parking ka dan bamu wuri zan yi magana da matata" ba musu Driver ya samu wuri yayi parlking ya fita, Khaleed ya sausauta murya yayi yace "Zainee Nah, kina fushi dani ne?" banza tayi dashi ta kawar da kanta gefe, hannunsa ya sa ya juyo da habarta yanda zasu fuskanci juna yace "ki min masifa, nayi kewan fadanki, ki min" shiru tayi sai ma ta kawar da kanta gefen windown mota.
Dungurin kanshi ya farayi yana marin kanshi, hakan da yakeyi ne ya jawo hankalinta gareshi,
Lankwashe murya yayi kamar ita yace "Don me Dee? Ashe baka yarda dani ba? Ashe in duniya zasu zargeni da mummunan zargi zaka tayasu gurin zargina? Ashe ba son gaskia kake min ba? Baka yarda dani ba? Baka tsaya kaji ta bakina ba? Kayi watsi da komai ka sakeni? Ka wahalar dani? Ka maidani bazawara" ya cigaba da dunguri da marin kanshi har sai da Zaineema ta fara kuka tana dukkanshi a kirji ya daina, be hanata ba, kuka take tana dukkan kirjinshi da hannu biyu tana cewa "Dee, ka wahalar dani" dama zai iya kuka da yayi, yace "Zainee nah, na sani, kiyi hakuri, ki dauka hakan a matsayin ajizanci na dan adam, kowa a matsayina zaiyi abunda nayi, abunda ya wuce ya wuce amma ki min uzuri, nikuma zan nuna miki yanda nake sonki, da yanda nayi kewanki, kinsan ina sonki, and i miss you so much" hawayenta suka k'ara yawa ta gada jikinshi, shiko ya rungumeta, tana kuka a kan kafadunshi, ita tasan tana son Khaleed sosai. Shafa bayanta ya shiga yi yana cewa "Ki bar kukan nan, kinsan banaso" tunawa tayi fa basu da aure yanzu, a hankali ta dago daga kan kafadunsa, yayi niyan sake rungumarta ta yi daurin cewa "Ba fa a daura mana auren ba" Khaleed ya dafe kanshi yace "Ya Illahi, now i cannot even hug my wife" dariya tayi tace "Nope!" turo baki yayi ya dan tashi ya ratsa ta kujerun gaba ya ma driver horn alamun sun gama. Driver ya dawo Motar ya ja ba tare da sanin inda suka nufa ba.
*****

Maigadi ya sanar da Hajia Aynarh tayi bak'i maza, ganin akwai mayafi Jikinta ya sa tace "su shigo" bata fasa filing nails dinta ba suka shigo da Sallama, Murmushin su ya fadada, mazauni suka ma kansu, ita ko ta gyara zama yanda zata fuskanci masoyinta yanda ya kamata, bayan 'yan gaishegaishe, ta mik'e don kawo musu abinci, Daddy ya dakatar da ita ta hanyar cewa "Aa Hajia Aynarh, mun hutassheki" Zama tayi tana fari da ido. Sada yace "To Hajia, dama so muke ki gaya mana inda zamuje neman aurenki, don ki zautar da Yayana, ko gaban Yara ne maganarki yake" daria tayi, ta sadda kai alamun taji kunya kafin tace "yawancin danginmu suna Kwara, but akwai uncle dina, Baba Abdoulfatah, a Kwanar Ganduje, shine madaurin aurena, shi ke aurar dani, a Gidanshi ma nayi Karatu, ya dade a Kano yana aiki bayan yayi retire be koma chan garinmu ba.
Sada yace "to sai ki bamu Address da numbernshi mu biya mu kai gaisuwa, da kuma Buhun doya nawa zamu kai na neman aurenki?" dariya Daddy ya sa, ita ko throwpillow ta dauko ta wurga ma Paapa "Wallahi Sada ka rainani, da buhun doya zaaje neman aurena?" Dariya suke sosai.
**
Tana dan kishingide taji muryan Daddy, to me yake a nan? Ta tambayi zuciyarta, k'ila yazo maidaki dakinki ne,da sauri ta tashi ta nufi Parlo da Sallama, amma kunnenta ya jiyo mata wani abu kafin sallamarta, "Wallahi Sada ka raina min Aynarta, to dole ka aje wasan k'anin mijinnan, ba zan yarda ka raina min Amarya ba" wani Yammm kanta yayi kafin ta fara jin idanuwansu a kanta, sun lura da ita, da mamaki suke kallonta, banda Hajia Aynarh da ta dauke ido, Daddy ya dan cin face ya kalli Aynarh yace "me takeyi a nan?" a takaice tace "Kwana" kafin waninsu ya k'ara magana tuni Hajia Mairo ta tako har gabanshi "Haba Daddy, haba Daddy, kana Fulanin usul, me jinin shuwa arab, me zakayi da Bayerabiya, Yoruba fa, Daddy dama sonta kakeyi?" duk da ba wai cikin tashin hankali tayi maganan ba, amma sai yaji ranshi ya 6aci, dubi matar nan, har tana da bakin magana, bayan abubuwan da tayi? Lallai bata da kunya, Banza yayi mata, tace "Daddy nafa ce na tuba, donAllah ka maidani dakina, na chanza, zamu zauna dakai da yaranmu lafiya, ba sai ka sake Aure ba, donAllah Daddy" bakinsa ya ta6e, Hajia Aynarh ta mik'e ta kalli Sada tace "Ka gaida Yesmin, ko kallon Daddy batayi ba tayi hanyar daki" meke nan? Kishi ake a kanshi? Daddy wani dadi yakeji amma be nuna ba, yace "kai tashi mu tafi" Mairo tace "Sada DonAllah ka bashi hakuri, wallahi na chanza halina".

Tausayi a bashi ya kasa magana, sai gyada kan da yayi, kafin ya ankara har Daddy ya bar parlorn. Mairo ta durkushe tana jin zafin Hajia Aynarh hat ranta, zuciya ya sata shiga dakin Hajia Aynarh, wanda sai da tayi nadamar shiga din kunnenta suka jiye mata shagwabar da Hajia Aynarh ke ta narka ma Daddy, wato ya bata mata rai shine ya kirata don ya lallasheta?.
Ganin Hajia Mairo ya sata daure fuska tare da cewa "Abbana, zan kiraka" Kamar an watsa mata ruwan zafi haka taji da kyar ta samu tace "Hajia Aynarh, kiyi hakuri, ba sai kin Auri Daddy ba, na son yana son aurenki ne don ya huce takaicina, amma wallahi ba sonki yake ba, ni yake so, sannan nasan kema haka, donAllah a bar wani maganar auren, ki taimaka min in koma dakin Mijina". Wani Dariar rainin wayau wanda ya k'ular da Mairo Hajia Aynarh keyi, wanda a da, in ta kuskura ta mata irinshi sai sun kwashi yan kallo, amma da yake yanzu tayi sanyi, kasan cewa komai tayi sai sadda kanta k'asa.
"Hajia Mairo, wa ya ce miki ni da Abba bama son juna? Aiko munfi Indiawa soyayya, in muna tare ji muke kamar mu hade juna, to in ma tunani kike Auren huce haushi zaayi dani, na miki kama da irin matan nan da zaa auresu don guce haushi? Soyayya zai sa mu aure, kuma nima ai zanso ki koma dakinki, don ba zan so duniya tace na firdaki daga dakinki don na auri Mijinki ba, ni zan ma fi so ki dawo dakinki don ki koyi yanda ake zama da miji, jidai abunda kike cemai, wai "Daddy, Babanki ne?" kafadu ta daga alamun ina ma ruwana, ta dora da cewa "Some hausa girls sha, wanda ya biya allonsa ya wanke" ta raba ta gefen Mairo ta bar mata dakin, Anan ji take kamar ta shak'o Hajia Aynarh ta mata dukan tsiya, don wallahi Hajia Aynarh ta mugun rainata, ta ga gadon baccinta, amma ba wani abu, ita tayi abunda ya sa ta rainata•.
**

Shafa kanshi tayi tace "Zaid, tashi na dafa mana Abincin rana, munyi latti, yaushe aka gama har aka kaima Umma" kamar karamin yaro ya mak'e kafada tare da sake gyara kanshi kan cinyarta, ya ciro wayarsa daga Aljihu ya latso Idi, ringing daya ya dauka "Idi, Lunch muke so" daga bangaren Idi yace "me kukeso?" "Random foods dai" yace "To, bari inyi ordering, zaa aiko yanzu" "Ehen, harda tuwo, a tsaya gidan Hajjo a kai mata nata" Idi yace "Angama Oga, sai me kuma?" Yana jin dadin yanda Idi ke mishi abubuwa, bari ya faranta mai rai Zaid yace "Shikenan, Thank You Idi, nikam Idi, ina brother dinka da kace ya gama Secondary School?" Idi yace "Anas, yana nan, be samu Jamb ba" Zaid yace "baka gaya min ba, Oya ka mai processing School a Cuba, naga akwai wani sabon School na manta sunan, kayi searching, ka mai processing ka gaya ma Faisal" Idi ya gane cewa Oganshi na wani yanayi na nishadi, zai fara godia yaji yace "Shuttup Idi get us lunch" sukayi daria tare kafin suka kashe wayar.
Maama ta sake shafa kanshi, tace "ina alfahari da kai, sosai" yace "Haka nake sonji" tace "to still dai ka tashi muje mu hada So6o, Babanka na so" shagwabe fuska yayi yace "cant we just buy?" mikewa tayi wanda tasa dole shima tashi tace "Nope, ni zan mishi" tayi gaba, yana binta a baya yana bubbuga k'afa kamar dan yaro har suka isa kitchen.
Da mik'o kaza, dauko wanchan suka dafa Sobon wanda yaji kayan kanshi su Na'ana, citta da karamfani, tana tacewa a dan Jug, yana bata labarin komai da Allah ya hore mishi, ta san Sada yana da kudi tun tuni, amma bata taba zaton danshi zai samu Arzikin ninkin ba ninkin na babanshi ba, Allah kenan, buwayi gagara Misali.
"Maa,me kike ganin zan ma Danuwana?" Maams tace "Zaid, abunda zakana AbdulMajeed ai ba sai na gaya ma ba" yace "Amma ai shawara da dadi" tace "kayi mishi abunda ya dace, Zaid, Abdulmajeed ne, ka mishi komai" jinjina kai yayi yana amincewa da duk abunda tace, ba wai don ya san abunda zai ma Abdulmajeed ba.

Hayaniya suka danji daga Parlo, alamun sun dawo, yaran suka shigo suna rungume Maama, tace "Zeenah, Muhsin ya School? Suka amsa tace "Najwa, kuje ku musu wanka, kafin a kawo lunch" Muhsin ya fita gun Najwa a guje, don yana sonta, Zaid ya dauka Zinatu a kafadarsa ya fito daga kitchen din, inda yaga Najwa na kiciniyar cirema Muhsin kaya, yace "Baby a parlo a ke cire kaya?" tace "No Bhaiyy" ba tare da ya amsata ba ya kashe ma Ziyadan da ke zaune ido, tare da wurga mata kiss ta iska, a kan Idon Abdulmajeed, ya wurga musu harara duka, suak tuntsire da daria, Zaid yace "Ha'an, mutum ba zai iya kallon matarshi ba?" Abdulmajeed yace "kaidai ka sani" daria Zaid yayi ya maida hankalinshi kan Zeenatu, yace "Baby Zeenah, kin yafe min abubuwan da na miki?" duk hankulansu ya dawo kansu, tace "ai ba ka min komai ba" yace "aa na miki, nidai ki yafe min" ta zaro ido tace "me ka min, ka gaya min?" Abdulmajeed yace "Zinatu, Wala tajassasu" ta kalleshi tace "banda tsananta bincike" ta maida kallonta gun Zaid taxe "Na Yafe maka har duniya ta nade" Murmushin jin dadi yayi yace "nagode, Ziya, kuje a musu wanka, suna warin rana" Najwa ta daga Muhsin, ita kuma zinatu ta bude baki ta na cewa "Ina warin a nan? Ya Majeed wai ina warin rana? Nifa ban ma shiga ranan ba" Ziyada tace "Mu shiga nikam na miki wanka" Zinatu ta dan bata fuska tace "nifa na iya, da kaina zanyi" Ziyada ta kalli Zaid, Zaid yace "No, kije a chudaki sai a barki ki k'arasa ko?" ba musu ta shige dakin Najwa a guje. Ziyada ta bi bayanta. Zaid kuma ya koma kusa da AbdulMajeed yana mai chakulkuli. Abdulmajeed na tureshi yana "kai wai ba zaka girma ba? Goaway" Zaid kam Dariya yake tayi.
**
2PM

A Tsakiyar Parlorn a ka sauke duka kayyan da Idi ya kawo, Coolers 6 ne, Tuwon Semovita da Miyan agushi, sai Fried rice, sai fried spaghetto da taji kanyan lambu, sai couscous da Miyan kayan lambu, sai Salad da Coslow, sai Pepper Meat na chicken da beef, sai kuma So6on da su Zaid sukayi yayi sanyi sosai. Zaineema sun dawo daga yawon ganin garin da sukaje, duk ta gaji.
A lokacin su Daddy suka shigo, duk yaran suka musu sannu da zuwa, Daddy yace "Shagali zaayi banda mu?" Najwa tace "wa ya isa yaci Iyaye na ba sa nan?" Zaid yace "ganta fa, ci fa za tayi kafin shigowanku" 6oye kanta tayi a cikin hannuwanta, Papaa yace "Yesmeenah ina muka samo coolers? da baki ta nuna Zaid Paapa yace "Au, ashe daga wurin His Grace Gatan Marayu ne" Zaid ya turo baki yace "Nifa kuna addresing dina formaly, nifa a cikin Gida Zaid nake, Da, K'ani, Yaya a wurinku, Daddy ka gaya musu" Daddy yace "wai baka san halin babanka ba? Aifa ba zai bar tsokananka ba, tsokana kamar dan shekara 6" duk akayi daria.
Maama tace "Oya azo a ci Abinci duk kowa ya tankwashe k'afarshi, Yaya kai kuje Kan Table, a kawo muku naku chan" Daddy ya zauna a k'asa wurin Muhsin yace "saboda mu bare ne ko bak'i, to nima anan zanci, baki san cin Abinci a tare na k'ara donk'on Soyayyah da zumunci ba".
Paapa ya dawo kusa da Maama shima ya zauna, yace ina na "Umma?" Zaid yace "Idi ya aika mata da nata" Daddy yace "Yauwa, nidai a zubo min Tuwo" Najwa ce ta bude coolern tuwon ta ciro mulmula biyu ta zuba mai, yace "aa daya ya isa". Maama tace "Zaineema ki zuba khaleed abunda yake so" ta dan gefen ido ta kalleshi, ta mike ta ciro plate ta zuba mai Couscous, Abdulmajeed yace "haan, ba zaki tambayeshi me zai ci ba?" Khaleed yace "Kai ina ruwanka? Mutum da mijinta? Ita tasan cimar shi?" Daria sukayi Abdulmajeed yace "Ahh, Allah ya baka hakuri" da kanshi ya zaro plate ya zuba ma kanshi Fried Rice, Mama ta zuba ma kanta da Paapa tuwo a plate daya, Zaineema ta zuba fried rice, Ziyada ta sa ma Muhsin da Zinatu Taliya, kafin ta zuba ma kanta Friedrice da coslow, Najwa kam Salad din kawai ta zuba a plate, Ziyada ta dan kallo Zaid kowa shagalinshi yake banda shi, "Oga ba zaici abinci bane?" turo baki yayi yace "an damu inci ne? Maama ta sa ma Mijinta, matata kuma kanta kadai ta sani, kanwata ma Mijinta ta serving, shi kuma danuwana da kanshi ya zuba, ita kuma wannan babanta ta sama mawa, ni da baa sona ba, wanda ya sa min, abincin ma ba zanci ba" Daria sukayi, Najwa tace "Laah, Bhaiy, sorry me zakaci?" Turo baki yayi yace "baa ci" tace "Haba mana Bhaiy, kayi hakuri, in zuba ma tiwo?" yace "ni ban cin tuwo" Abdulmajeed yace "sai rice" Zaid yace "eh din, amma yanzu kizo muci Salad din" karo musu salad din tayi, da plate din pepper meat, tazo ta dire gabanshi, suna ci tare a kwano daya, daga inda yake yana wurga ma Ziyada kallon soyyaya, ita kuwa duk nauyinsu Maama take, ta kawar da kanta tana cin fried rice dinta, Ziyada ta tsiyaya Sobo ta dan kurba, Zaid yace "Ziyaaa, Sobon yayi dadi? Ni na yi fa" tace "kaii, amma yayi dadi, ban taba shan Sobo me dadinshi ba, saboda maama na tayi" Zaid ya marairaice yace "Nifa nayi, ku tambayi Maama kuji" Abdulmajeed yace "You Spoilt Brat, bana tunanin ko ruwan zafi ka iya dafawa" Zaineema da Khaleed suka sa daria, Najwa ma darian take, turo baki yayi yace"Maama kice musu ni nayi" Maama bata tanka ba ta cigaba da cin tuwonta, Zaid kamar yaro sce "Maama kice musu ni nayi donAllah" ganin gardaman ba k'arewa zai ba Daddy yace "Mallamai ku mana shiru, in ana cin abinci ba a magana".
Nan suka natsu, Abdulmajeed ya faki idon Daddy ya ma Zaid Gwalo, Zaid ya balla mai harara.

Haka aka gama cin Abinci, yan matan suka kwashe plates aka kai kitchen, suka wanke, dawo Parlo aka hau fira Iyaye da Yara, maganan Waliman bikin bude Sabon Company din Daddy ake, Daddy yace a bari sai randa aka daura auren Abdulmajeed sai aje chan ayi Walimar" Paapa yace "yauwa hakan ma yayi?" Zaid yace "Yaushe ne?" Paapa yace "sai munje neman auren Aunty Aynarh, randa sukayi fixing date din, rannan zaa daura, sai ayi abun once and for all" Zaid yace "dama Gobe Khaleed zai koma America, akwai Exams din da zai yi a week dinnan, shine yake so a daura musu Aure da Zaineema ya tafi da ita, so by 1am zasu tashi yau" Paapa yace "to sai a daura auren In khalid din ya shirya ko Bayan Laasar ne a masallaci, amma in zaa jira nashi waliyan ne ba matsala, duk yanda yafi mai dai" Khalid ya sadda kai, Abdulmajeed ya zunguro shi yace "kayi magana mana" Khaleed yace "Dama nagaya musu zaa maida auren, sunce tunda ba auren farko bane a daura kawai, kuma goben nake so komawa sabida Exams din" Paapa yace "hakan ma yayi, bayan Laasar sai a maida auren, ke kuma sai ki fara shiri, gobe sai ki bishi ku tafi" raurau Zaineema tayi da ido, bata so tayi missing bikin Yayanta, Maama tace "Yadai Zaineema?" kamar zatayi kuka tace "Banso na barku, yaje dai ya dawo" Maama tace "dont be silly yarinya, ki bi Mijinki, Exams fa kawai zaiyi ku dawo, ki hakuri kinji?" a hankali ta gyada kai.

Bayan Laasar aka daura Auren Khaleed Ishaka Maikudi da Zaineema Abba Abu, bisa sadaki naira 40k wanda Zaid ya bada, Khaleed baki har wuya, a k'afa suka dawo Gida kasancewar masallacin ba nisa. Zaineema ta kulle a dakin Maama kamar auren fari sai kuka take tayi, Ziyada ta shigo tace "ta fito su Daddy na kiranta" kasa tashi tayi, Ziyada tazo ta rungumeta, tana lallashi, "haba sis, meyasa kike kuka? Ya Khalid dinki ne fa, please dont be Sad, ba sabon abu bane, please sis, kuma fa Exams zaiyi ku dawo, please kiyi hak'uri" Zaineema ta gyada kai ta tashi, Ziyada tayi gaba, ta bi bayanta.
Gaban su Daddy ta durkusa ta sadda kanta k'asa. Daddy ya mata nasiha me ratsa zuciya kafin Papa ya dora da cewa "ki tashi yanzu kuje kiyi ma Mahaifiyarki Sallama, yanzu zaku wuce Zaria gun Mahaifan Khaleed, kuyi musu Sallama sannan ku wuce Abuja inda Jirginku zai tashi by 1am" jiki a sanyaye yace da AbdulMajeed "kuje ko?" Abdulmajeed ya mike yace "Zaid, kana ina?" Abdulmajeed ya dinga shiga daki bega Zaid, har kitchen be nan, ba wanda ya ga fitanshi, Papa yace "Oya kuzo ku tafi, ba lokaci" Abdulmajeed yayi gaba, k'annenshi suna binshi a baya" ya waiga yaga Najwa ta choge, be ji dadi ba, ko dai ba su yafe ma Mummynsu bane? Amma ya musu uzuri.
***

Maama da Najwa na shiga dakinta suka ga Zaid la6e bayan k'ofa, Maama ta kalli Najwa, Najwa ta kalleta kafin suka tuntsire da daria a tare, Zaid ya fito daga bayan kofan yana cewa "sun tafi?" Maama tace "hmm, yaro nasan baka son ganin Mairo shiyasa kazo nan ka boye" yasan gaskia ta fada, amma sai ya fara inina yace "aa, Maa, gani nayi ya kamata a barta da 'yayanta, be kamata naje na musu zaune ba, nasan akwai maganganun da ke tsakani uwa da yayanta da zasuyi" tabe baki tayi tace "na jika, amma dole ka cire duk wani abu game da ita, Diyarta kake aure, she wont have you disrespect her Mom" cike da shagwaba yace "Maaa" tace "Yaro ban tashi tare da kai ba, amma ni na haifeka, and nasan deeply inside you kana jin haushin Mairo, don ka samu Yafiyan kowa hakan ba zai sa ka yafe maa farat daya ba, ko tun da chan na san ka da dan banzan rik'on tsiya, balle abunda ka kitsa ma ranka tun kana yaro, da wuya ya fita lokaci guda, so kawai ina ce maka ka bi a hankali" Tabbas abunda ta fada haka yake, ba karya ciki, amma shima har ga Allah yana jin haushin Mairo, duk da yafe mata, amma zuciya bata da k'ashi, baya tunanin zai manta abunda ta mishi da iyayenshi, ba zai taba mantawa, amma for her kids, zai k'okari ya danne asalin abunda yakeji game da ita, har sanda Allah zai sa ya manta komai.
Baki ya turo ya rik'o hannun Najwa tare da fita daga dakin yana cewa"Zokiji Baby" Maama ta san gudun maganar yake shiyasa bata tanka su ba ta dauko wayarta don kiran su Baffa.

"Baby, ki gaya min duk abunda kike so, zan miki kinji, ki tuna waye Yayanki" Murmushi tayi tace "Bhaiyy, ina so ayi min Wedding Partyna a India, kasan all my friends are there, kuma banyi proper farewell dasu, so ina so inje India" yace "Ehen, ina jinki, daya kenan" tace "uhm sai kuma ina son yin Hajj, ban tabayi ba, ban taba zuwa Makka ba, ina so, and then shikenan" yace "are you sure?" tace "Noo Bhaiy, akwai abubuwa da yawa a kaina, amma duk sun shige min, but da na tuna, zan gaya ma kaji??" bude hannuwanshi yayi ta fada a rungumesu yace mata "yana sonta sosai" itama ta bashi tabbacin tana son Yayanta.
Tunda ya zauna yake waya, Umurni kawai yake ba dawa, yana gaya musu yanda yake so a mishi abu da kuma lokacin da yake so a mishi abu. Maama ta shigo dakin Najwa, ta gansu zaune, itama hawa Gadon da suke tayi, lokacin ya gama waya, yace "Maama Gidan Baba Abba na sa aka rushe, akwai wani Gida a gefen gidan, na siya nace shima a rushe a mishi Katon Gida me Part 2, tunda Aure zai sake, kowa da Part dinshi i think hakan zaifi" Maama tace "yauwa hakan yayi, Yaya Yagode" ya cigaba da cewa "and ku kuma--" Maama ta katse shi tace "Ahh, kar ma ka fara tunanin cewa zamu bar gidan nan, don wannan Gida da zufan Babanka ya siyeshi, shi ya bada tsari aka gina mishi shi, ina da tabbacin don danshi shine Gatan Marayu na biyu ba zai bar Gidan nan zuwa ko wani Gida da zaka bashi ba, so kawai ka bar mu a nan, Ina laifin Gida 3bedrooms? Daga ni sai Babanku?" Najwa ta turo baki tace "nifa" Maama tace "kin manta Aure zakiyi? " "kuma dai don zanyi aure, sai ace banda daki a Gidanmu?" Maama ta jawota jikinta tace "Dakinki na nan, ba inda zaije, duk sanda kikazo, you can sleep in your room, amma this house is more than enough for us, Zaid ba sai ka chanza mana Gida ba".

Zaid duk yaji ba dadi, to me zai ma Mahaifanshi? Me zai musu suyi alfahari dashi? Ina amfanin Arzikinshi in Mahaifanshi basuci moriyar shi ba?" kamar ta san tunanin da yakeyi tace "Zaid, babban abun Alfaharinmu shine abunda ka zama yau, muna Alfahari da kai, tunda kowa ya sanka da taimaka ma marayu da gajiyayyu, Zaid kowa ya sanka ta fanni taimako, mun san abubuwan dakayi achieving, i think its more than enough, we are proud of you, we are proud of what you became, kawai dai Allah ya kara maka tsawancin rai ka cigaba da baza legacy din Marigayi Babanka Gatan Marayu na farko, Allah ya kara maka budi da Arziki na Alheri, Allah ya ja kwana, i'm proud of you" fadawa yayi jikin Maamanshi tako rungumeshi, hannu ya bude ma Najwa ta shigo cikin hug dinsu, Ina Sonku 'Ya'Yana Abun Alfaharina, kune Duniyata, ina Sonku fiye da rayuwa da kanta" Paapa ya shigo Dakin, yace "Ohhh, group hug ake shine aka wareni" hawa yayi kan Gadon ya rungumosu gabaki daya yace "Allah ya muku Albarka, ya Albarkaci Rayuwarku" suka amsa da Ameen, Paapa yace "wai su mutanen chan na waje ba sa zuwa hutu ne? Suna waje suna jiranka?" Zaid ya danyi tsaki yace "Wallahi Baba haka suke, ko ina naje suna waje suna jirana, wai kareni suke, yanzu in suka tafi suka barni Faisal naji korensu zaiyi ya kawo wasu, abun haushi yake ban, ko ina mutum zaije fa Convoy" Dariya sukayi gabaki Daya.
Nan suka zauna suna fira gwanin ban shaawa, Zaid na fada musu Plans dinshi suna mai contributing suna bashi shawara, Daddy kadai a parlo yana gyangyadi.
****

Muhsin da Zinatu suka shiga Gidan Aunty Aynarh da gudu, ita kadai ke parlorn sukayi saurin hawa kanta suna mata "Oyoyo" "Iyye, my babies, nayi missing dinku" ta hau daga su one by one, daidai da shigowar AbdulMajeed, Zaineema da Ziyada, "Ashe ku duka kuke tafe" suka amsa da fara'arsu, kafin suka hada baki wurin cewa "Aunty ina wuni?" ta amsa su da fara'arta, ita dai har ranta tana son 'Ya'yan nan, son da take ma Mahaifinsu ne ya shafesu, suka gaisa cike da mutunta juna, AbdulMajeed yace "Aunty, dama Zaineema muka kawo ta muku Sallama, Mijinta ya dawo, jirginsu zai tashi 1am zuwa America, amma Exams kawai zaiyi ya dawo". Tunda ya fara magana Aunty Aynarh ke zabga Murmushi tace "kai madallah MashaAllah, Allah ya sanya Alheri" nan tai ta addua suna amsawa. Mikewa tayi ta shiga ciki don kiran musu Mairo, "Hajia Mairo, ga Yarana sunzo" tsaf ta gane ko su wa take nufi da Yaranta, Hajia Aynarh yar bariki ce, so take ta dinga k'ular da ita ta hanyan kiran 'yayanta, yaranta, inshaAllah ta daina nuna mata haushi ko wani abu takan hakan, don ta hakan take so ta dinga k'ular da ita, indai bariki ne to itama ai ta iya, murmushi ta mata, tace "sunzo gaida uwasu ko? Barinje in gaida yaran Aunty Aynarh" ba ta jira cewar Aynarh ba ta fita daga dakin, ita ko Mamaki ya sa ta bita da budadden baki.

Tana shiga Parlorn duk suka yo kanta don suui mata Oyoyo, banda Abdulmajeed da yake zaune yana ta fadada Murmushin shi, Wallahi Uwa Uwa ce ko da ta banza ce, yanda sukayi missing dinta haka suka dade a jikinta rungume da ita, basa tuna komai sai Soyayyar dake tsakanin Uwa da 'ya'yanta, ganin yanda Zaineema da Ziyada suka runk'unk'umeta yasa Abdulmajeed cewa "Yadai? Ku saketa mana" suka saketa suna Daria. Don k'ulafuci kujera daya suka zauna da ita, wannan ta jingina da hannunta wannan kuma ta kwanta kan kafadarta, Muhsin da Zinatu tuni sun shiga gun Aunty Aynarh.
Baki suka hada wurin cewa "Mummy ina wuni" ta amsa su cike da So da Kaunarsu, tana kallonsu daya bayan daya tana tunani a zuciyarta, in banda Zuciya kowa da irin tasa, me zai sa tana da Wadannan kyawawan hallitun amma ta sa a ranta Jin dadi ba zai cika ba sai da Arzikki, ai Babban Arziki Allah ya mata, kawai dai son Zuciya ne ya hanata gani, to me ya kai wannan samun Namiji kamar AbdulMajeed a matsayin Da Arzikki? Yaro daya tamkar da dubu, Yaro mai hangen nesa, da dukkanin zuciyarta ta yi nadama, akan ce *Dan kuka me ja ma uwarshi jifa, wannan Uwar ce ta jama 'ya'yanta jifa* murmushi ya k'i bacewa daga fuskarta, meyasa tuntuni bata fuskanci in tana da yaranta bata bukatar komai ba? Meyasa son kudi da son abun dunia suka makantar da ita? "Ya Allah! Ka yafe min" AbdulMajeed yace "Mummy, wai wannan farincikin na ganin mune? Naga sai dai a kalleni a juya a kalli Zuzu da Zaineema ana Murmushi".

Wani Murmushin ta sakar me k'ayatarwa tace "hmm kaidai bari Boy" duk suka sa daria don ta jima bata kirashi da Boy ba, tace "ina ta nadamar wautana da son zuciya ya sani aikatawa, tare da kunyarku da nakeji, ina ji kamar nayi failing dinku, ban bar muku komai da zakuyi Alfahari dani ba, inaji kamar So, k'imata, da daraja na sun ragu a idanuwanku, ina ji kamar kun tsaneni ba kwa kallona da Mutunci--" AbdulMajeed ya rausayar da kansa, wallahi ya tsani maganar nan kwatakwata, ya dan zamo daga kujera yayi kamar tsugunne yake kan kujerar yace "Mummy listen sosai, don yau ne rana ta k'arshe da zamuyi maganar nan, Kinyi laifi babba, amma kinyi nadama, Allah na yafe ma Bawan da yayi laifi ya kuma rok'i gafarar Allah da wanda ya ma laifi, ya kuma sa a ransa cewa ba zai sake aikata irin laifin ba, to Mummy kin tuba, kin nemi yafiya, an yafe miki, me zai sa ki ta fama da guilt? Mummy abunda kikayi rubutaccen alamari ne, babu yanda zaayi a guje mishi, me aukuwa ta riga da ta auku sai dai a kiyaye gaba, ke Mahaifiyarmu ce, ko me kikayi zamu cigaba da kasancewa mu 'yayanki ne, in Dunia ta juya miki baya, mu Yayanki mu zamu kasance tare dake, darajarki ba zai zube a idonmu ba, k'imarki k'ara yawa take a zuciyoyinmu, ban taba nadamar samunki a matsayin Mahaifiyata ba, ina Alfahari dake, kece Uwar da kowani Da zai so ya kasance shine Da a gareki, saboda Soyayarki a garemu me yawa ne, Mummy muna sonki, we love you the same or even more, donAllah yau ta kasance rana ta karshe da zaki sake mana irin maganar nan" Ziyada tace "Mummy wallahi muna sonki, ni yanzu ko mutum kika kalli gabas kika yanka ai ba zan daina sonki ba" Zaineema tace "You are the mother we could ever ask for, wallahi Mummynmu tafi ta kowa, Allah ya ja da rai Mummynmu"
Farinciki ya sa hawaye gangarowa daga idanunta, Waiyo Allah, cike da so da kauna take kallonsu tace "AbdulMajeed me zanyi in ban da kai? Me zanyi in ban da ku? I'm the luckiest Mother living, Alhamdulilah bi ni'imati.. Nagode Nagode, ina alfahari da kai, ina alfahari daku gabaki daya".

Abdulmajeed yace "Mummy dama nace miki Khalid yazo ko? To an maida auren yanzu da laasar, yanzu Zaineema bankwana tazo miki, zata bishi America yau, chan yake wani course" ganin hawayenta sun cika taf a idanunta ya sa shi saurin cewa "Exams zaije yi, zasu dawo InshaAllah da ya gama" ta dan ja numfashi tace "toh Allah ya bada saa ya tsare hanya, sai a kula da kai, Allah ya muku Albarka, ya baku zaman lafiya da Mazajenku" suka amsa da Ameen, Abdulmajeed yace "Sai kuma niko? Allah ya kaimu bikina ko?" Ziyada tace "kai ya Maji ko kunya?" sukayi daria Wayar Daddy ya katsesu, Abdulmajeed ya dauka "Hello, wai ku kwana zakuyi? Bakaji yanzu zasu tafi Zaria kuma suje Abuja duk a yau ba? Ku dawo yana jiranku" a ladabce yace "Toh Daddy" yace "Oya ku tashi, Maigida ya kira yana fadan zaman mu" Mummy tayi dan jim, bata son rabuwa dasu, Abdulmajeed yace "ku shiga ku ma Aunty Aynarh Sallama, Zaineema ta mike ta shiga ciki, Ziyada ta bi bayanta, kan Mirror sukaga Aunty Aynarh na ta zuba wani abu kamar magani a wani bottle tace "Yauwa Zaineema, ga guzuri ina miki" tace "Aunty na menene?"tace "ke yanda kika dade a Gida ai dole in gyaraki, duk da a k'urarren lokaci ne, amma its never late" so ki sha yanzu, ki sha da daddare, kiyi overdose, kar ki damu, kayan Natural Products ne, ko ni da ba Miji ba ina ta sha, kinga randa nayi aure a dadin Mijin" Zaineema da Ziyada suka sa daria, Zaineema tace "ana ma Daddy tanadi kenan" tace "Ahh, ku tsaya nan, kai dan Gidanku uwaku ce ni" suka sa daria tace "ba illah, InshaAllah ki saki jiki ki sha kingane?" ta murmusa tace "Allah ya bar Aunty Aynarh" Ziyada ta turo baki tace "ni kin manta ina da Aure?" tace "Ya zan manta Matar ZSA, aike muna tare" ta runguma Zaineema ta mata Adduan fatan Alheri, a tare suka fita daga dakin, Mummy duk jikinta yayi sanyi bata son rabuwa da Yarta, ta tuna farkon Auren Zaineema, kuka sukayi tayi a tare, da yake Bariki ne, a lokacin Harda ita aka sada Zaineema da Gidan Miji, yanzu ko an girma, ya zatayu tunda Gidan Miji zata, Addua ta mata, ta shafa bayanta, suka shige Mota suka koma Gida.
**

"Yanzu Daddy ba zamu rakiya ba?" Daddy yace "Rakiyar me Najwa har Abuja? Come on my friend, ku zauna Gida, salon Yawo, kuyi bankwana ai ko sati biyu ba zasu wuce ba" Paapa yace "ba wani rakiyan da zaa, Khaleed ya dauko Matarshi su tafi, say your Goodbye's Zaineema, gashi to 5" Zaineema ta rungume Kannenta, kafin ta runguma Maama, sukayi musabaha da AbdulMajeed, Zaid ya mik'a mata 15,000 dollars yace "Spoil yourself a America" dariya tayi tace "Thank you Yazaid, thank you" yace "Oya, ki shiga Mota Khaleed na jiranki" ta shiga Mota, Khaleed ya dan risuna ya ma su Daddy Sallama, ya yi Musabaha da Abokinshi inda yace mai "take care of my sister" yace "i will Abdulmajeed me imani" sukayi daria, ya yi musabaha da Zaid yace "mungode da Dawainiya" Zaid ya musu fatan Alheri, Khaleed ya daga ma su Ziyada da Najwa hannu bibbiyu kafin ya fada Mota, Driver ya ja su, sai wani Mota wanda shima na Zaid ne suka rufa musu baya "Zaineema Allah ya sauke ku lafiya".

Daddy yace "Abdulmajeed muje ku maidani Gidan Hajjo, Zaid yace "bro ban key" yau ni zan tuk'a Babana, jefa mai Key yayi ya chabe, suka mike Daddy na gava suna binshi a baya, Paapa yace "Yaya sai da safe" yauwa mu tashi lafiya, su Najwa ma suka mai sai da safe.
Zaid na bude Motar mutanenshi suka marmatso daya yace "Oga, fita zamuyi?" Zaid ya san ba jinshi zasuyi ba yace "Aa, ni dai zan fita, ku ku tsaya nan, Babana zan kai Gida in dawo yanzu, kun gane?" a tare suka ce "Yes" ido ya wulla sama tare da bude kofar motan yace "Good" Majeed ya bude ma Daddy Gidan Baya, shi kuma ya shiga gaba, Zaid ya kunna Mota yayi horn mai gadi ya bude ya fita, ta mirror Abdulmajeed yace "haha, gashi basu biyoka yau ba" Zaid yayi Murmushi yace "tsaya dai ka gani" ko da suka hau titi sosai, sai yace ma Abdulmajeed "kalli bayanka" Abdulmajeed na kallo ya ga motocin mutanen Zaid kusan uku suna binshi a baya,harda Daddy wurin lek'e, sukayi daria, Zaid yace "ai duk wanda yace musu kar su bini bata baki yake, kamar gadin Ran k'anin ubansu suke mtss" Abdulmajeed ya fashe da daria, Zaid yayi tsaki yace "Wallahi its Annoying" Daddy yace "Ba wani abu bane, a bakin aikinsu suke" Zaid yace "Wallahi Daddy haushi suke bi in suna treating dina kamar Kwai, Umurnin Baba ne, duk wanda zaa dauka aiki sai yayi rantsuwa da zai kula dani da lafiya na, kamar wani shugaban k'asa" Sukayi Daria Daddy yace "Allah yaji k'an Gatan Marayu na farko, ya ja ran Gatan Marayu na biyu, Ya Dade yana yi" Abdulmajeed ya amsa da Ameen yana daria, Zaid yace "mugu" haka suke firansu gwanin ban sha'awa, har suka iso Gidan Hajjo, Zaid yace "an kawo miki Abinci dazun?" tayi daria tace "Eh wallahi, ga sauran ma ban cinye ba, wani yayi ta rafka sallama wai Gatan Marayu ya aikoshi, ina zuwa naga Kuloli nace "aaah wannan Gara haka? Lallai Zaid kanayin auren dani" Abdulmajeed yace "Aa Hajjo, kar muyi haka, yanzu wurin Me siyo miki Abinci zaki koma? Nifa da kaina zan dinga dafa miki" Daria sukayi tace "ku dinne duk ina sonku, amma don kar na hada fada, da Muhsin nike auren" duk suka sa daria. Suna Gidan Hajjo har bayan Isha'i, kafin suka dawo Gida.
****

A Parlo suke ta firansu, har yara sukayi bacci. Abdulmajeed ya dauki Muhsin da Zaid kuma ya dauki Zinatu suka kaisu daki suka shimfidar dasu kan Gado, Paapa yace "Ku wai ina kuke tunanin zaku kwana? Kunsan bamu da wurin kwananku ko?" Abdulmajeed ya kalli Zaid, Zaid ya kalleshi yace "Baba, mu ko ke da wurin kwana" Paapa yace "ina, mu da ba boysquaters ba" Zaid yace "Nan parlo" Maama tace "saidai Parlorn" suka sa dariya, wurin 10 Maama da Paapa suka musu Sallama suka shige daki.
Zaid ya koma wurin Ziyada, Abdulmajeed yace "oh dama su maama kake jin kunya ko? Ni baka jin kunyana ko?" Zaid ya harareshi yace "kai a suwa zan jin kunyanka" Abdulmajeed yace "ni a babban yaya" Zaid yace "iyee, kwana nawa duka ka bani?" Abdulmajeed yace "oh nama baka ko?" "Eh amma befi days ba" yace "oh ashe dai na baka days din" Zaid yace "Mallam leave me, zanyi magana da matata" Abdulmajeed yace "Ohh da muma ba zamu yi aure ba da bamuji gari ba" Zaid yace "Ohh Allah, Ziyaa tashi in rakaki daki, sai in dawo in raka Baby" Abdulmajeed yace "Meyasa sai one by one? Ba daki daya zasu ba? A raka su a tare, muje duka" Zaid ya mishi kallon "i want a moment with ny wife" amma Abdulmajeed yayi biris dashi kamar be san abunda yake nufi ba, Zaid ya tashi ya riko hannun Ziyada, ya jata har daki, ita dai binshi take taa daria, Abdulmajeed yace "PureHeart mu bi su" Najwa tayi daria tace "kaima ka barsu mana?" murguda mata baki yayi yace "ba zaa bari ba, ki zo muje" ta mik'e ta bi bayanshi, Zaid na niyyan kissing Ziyada yaga Abdulmajeed tsaye bayanshi, Zuzu taji kunya, Zaid ya kalli Ziyada yace "Arghh, wani irin yaya gareki?" ya juya ya kalli Najwa yace "wani irin Miji kike niyyan aure? Abdulmajeed ya finciko Zaid ya tura Najwa ciki ya kulle musu k'ofa.
Zaid ya bishi da gudu Abdulmajeed ya arta a guje suka dinga zagaye parlorn, karshe suka zube kan kujeru suna maida numfashi, Zaid yace "kai barin je in karbo pillows" Abdulmajeed yace "yaro sai dai muje tare, so kake kaje gun matarka, naganeka" Zaid yace "nafasa, kaidai wallahi bakayi ba, mutum na son moment with his wife, kai kuma kana hana ruwa gudu, ba dai kyau, ba laifina bane da baka da mata" Abdulmajeed yace "until nayi aure, ba zaka dinga sani jealousy ba" sukayi daria" waya ya kira yace "a kawo musu Duvet da pillows, a kuma kawo mishi Laptop dinshi" ba a rufe Minti Talatin ba aka kawo mai. Dakanshi ya shimfida musu Katon bargo me kama da katifa, suka baza pillows Abdulmajeed ya kwanta, shi ko Zaid bude laptop dinshi yayi dan yin wasu ayyuka har wurin karfe 1 kafin ya kwanta bacci, daga dakinsu Ziyada kana jin Masharrinsu.
*
A G U R G U J E

Washegari da safe Daddy da Paapa sukaje Gidan Uncle din Aunty Aynarh, dama ta sanar dashi zuwansu, nan dai a ka sa biki nan da wata 1.
A wannan zaman ne Zaid ya musu shirin zuwa India, sannan su tsaya dubai siyayyan Kayan Daki da na kitchen, sannan Daddy da Paapa da Maama da kuma Hajjo suje Makka domin yin Umrah.
Sai da ya tambayi shawaran Abdulmajeed yace mishi hakan yayi amma a bar Zinatu da Muhsin wurin Mummynsu, saboda school, da haka suka nemi izinisu Paapa suka amince, Washegari suka dunguma sukayi Abuja don neman Visa, bayan an ma Ziyada E Passport an kuma yi ma Daddy renewing nashi.
Zaid ya samu AbdulMajeed yace "Brother, ni wallahi bansan me zan maka ba, ina ganin duk me na maka wont make up for the wrongs i did, bansan me zan ma ba, amma zan baka Gidaje Uku, daya a Kano, daya a Kaduna, daya a nan Abuja da sunanka, Mallakinka ne, and Motoci Uku--" Abdulmajeed yace "Aa fa Zaid, me zanyi da gidaje da motoci uku? Aa nikam bazan karba ba, yayi yawa wallahi" Zaid ya dafa shi, yace "Aa, wallahi ina ganin yayi kadan, i dont know what to do wallahi, ina ganin all these are not enough, meye amfanin Arzikina in ban maka ba? Meye amfanina? Nidai ina rokonka Alfarma daya kawai if theres anything you need, anything, kawai ka gaya min, kar aji nauyi, kar kaji kunya, ni da kai daya ne" AbdulMajeed yace "Nikam i want to work, ina son yin aiki, don Danuwana ne Gatan Marayu ba zan zauna a gida na tankwashe kafana ba, nasan me kake tunani, kana tunanin yanke mana duka ayyuka, in ka yanke ma Iyayenmu wannan is understandable, yaci ace sunyo retire, kuma mu mun kawo karfin da zamu dau dawainiyansu, amma ni gaskia i refuse to be relaxed, ba zan zauna zaman banza ba, i know kana da kudin da zaka ciyar damu ka biya mana bukatunmu da mu da yaranmu da jikokinmu, amma ina so na tsaya da kafafuna, ina so nima in ga na tara ince wannan zufa na ne, nima ina kwadayin Lada, ina so wata rana in baka ince ka zuba a ZSA foundation, ina so nima in shiga sahun masu taimakawa Marayu, da gajiyayyu, ina so inyi aiki saboda gaba, Please kama maganata kyakyawan fahimta" Zaid yayi dan jim kafin yace "Da ina ganin muna da komai, ba sai kayi--" AbdulMajeed yace "Please Brother" Zaid yace "Fine, shikenan, zan kira connection na Alhilal Construction Company Dubai, zasu dinga baka contracts, and nan Nigeria zan nemi audience da Babatunde Fashola, zan kirashi na roke shi Alfarma, ya dinga baka Contracts din Zanen Roads, Housing, Highways, kuma nima in na samu irin contract din, zan gaya musu ina da Architect da Quantity surveyer" Rungumeshi Abdulmajeed yayi yana da bubbugashi a baya, dadi ya rufeshi, yace " Nagode danuwana, Allah ya ida nufi".

Zaid ya ba AbdulMajeed takkaddun Gidajen da ya bashi, da kuma Motoci, sun yanke hukuncin zama a Abuja, nan zasu za zauna da Iyalinsu, Gidajen a jone suke da juna a unguwan Maitama.
Ziyada zata koma Baze University zata fara a fresh, Najwa kuwa WAEC zatayi tayi joining Ziyadan, dama ko a Indian bata gama HighSchool ba, nan suka tsara komai, kafin suka sanar da Mahaifansu, dadi sukaji sosai.
Kwanan su 5 a Abuja Visa dinsu ya fito inda jirginsu zai tashi a k'arshen Sati, k'arshen Sati Jirginsu ya daga zuwa India.

I N D I A

Bayan Faisal yayi Changing Dollars to Rupees a money changer, Taxi Uku sukayi, kamar kullum, Mama, Papa, Hajjo da Daddy a mota daya, Zaid, Abdulmajeed, Najwa da Ziyada a mota daya, dayan kuma Idi sai Faisal da ya baro bauchi don kasancewa tare da Gatan Marayu.
Daddy ya gaya ma Driver inda zasu, wato Saritar Vihar, Shubham Palace Hotel, kasancewar sun saida Gidansu kafin su tafi, dole a hotel zasu sauka, Dadi kamar ya kashe Najwa. Tafian Awa daya ya kawo su Birinin Delhi, suka iso har gaban hotel din, a reception suka tsaya, Faisal ya tambayi Zaid Daki nawa zaa kama Zaid yace a kama 5 ko? , hakan ko akayi, suka karbi room 102 to 106Ziyada da Najwa daki daya, Paapa da Daddy na du daban, sai Maama da Hajjo, sai Zaid da AbdulMajeed sai Faisal da Idi.
Bayan sun huta ne suka shiga cikin Sarita Vihar, tun daga farkon Layi Najwa take haduwa da idon sani, har suka k'arasa Gidansu Kaveri, dama basu sanar da su zuwan ba saidai aka musu suprise.

Kaveri ta rungume Najwa, suna ta murnan ganin juna, Maman Kaveri da indiyanci tace "Ina yaro me sa mamanshi kuka?" Najwa ta nuna shi, Indiyanci take tana ma Maama barka da azziki ta ga danta, Zaid be san me ake cewa ba, sai dai Murmushin dole, da Indiyanci Najwa ta gaya ma Kaveri ga Fiancee dinta, nan Kaveri tayi tsalle tayi kan Majeed ta riko hannunshi, Najwa ta buge hannunta tana cewa ta bar taba mata Miji, sun dade a Gidansu Kaveri kafin Najwa ta zare jiki tayi Wurin Vijhay Bhaiya.
Tun daga center Unguwan take kwala mai kira a guje "Vijay Bhaiya main bapaas aa gaya hoon(Brother Vijay, i'm back)" kamar cikin bacci yaji muryarta a guje ya kwaso ya fito, durkusawa tayi ta shafi kafanshi, kamar yadda aladarsu take, ya dagota yana jin dadi suka fara gaishegaisge da firan bayan rabuwa.
Haka su Maama suka iso wurin, suka gaiggaisa, Zaid ya ma Vijhay Alheri, don yaji labarin yanda ya kulan mai da kanwarsa, Vijhay ya rungumeshi yana cewa da Indiyanci"Kai ne ke sa mamanka kuka ko?" Najwa ke fassara mai, shidai sai yake yake tayi.
Daga nan Najwa ta kaisu Gidan Aisha kawarta, wanda ta bata kwarin guiwa sosai wurin zuwa Nigeria, tayi mamakin ganinta, nan dai aka danyi fira kafin suka bar gunta.
Haka suka dinga Yawo a India, sukaje TajMahal, Shi dai Zaid Kasar nan be mai ba, shiyasa duk yawanshi kasashen duniya be taba zuwa India ba.
Bayan Five Days
A kwana 5 dinnan, duk sun gama shirin yin Engagement Party din Najwa da AbdulMajeed, Daddy yace "shi kawai tafiya zasuyi ba za su tsaya ayi shirmen nan dasu ba,ai ba aladarsu bace da zaace sai anyi wani Party na Alaadar Hindi, Zaid dai lallabashi yake don kar ya hana ayi, burin kanwarshi kawai yake son cikawa, ganin Daddy sai kushe abun yake tayi Zaid ya tarkatasu ya sasu Jirgi suka wuce Makka don yin Umrah.
Nan Najwa da Kaveri da Ziyada suka dinga zuwa gaiyyatan kawayensu bikin engagement dinsu, wanda zaayi a wani kayatacen wuri a cikin Delhi.
Haka dai ranan Engagement sukayi shigan Indiawa gabaki dayansu, har Zaid, sosai sukayi kyau, nan dai a kayi shagali taro ya watse lafia.
Kwana biyu kawai sukayi suka tattara suka dawo Dubai.
Nan ma yawon buda idanuwa sukayi, kafin sukayi siyayya da yawa.
Zaineema ana chan America da Khaleed ya gama exams, suma cikin Satin nan zasu wuce Makka inda zasu dawo tare da su Maama Nigeria, lokacim befi kwana 6 biki ba.

Bayan Yan Kwanaki.

Yan dubai suka fara dawowa kafin 'yan Saudi, a lokacin har an kammala Gidan Daddy anyi furnishing dinshi da kayan Katakai masu kyau da tsada, wanda a companyn Daddyn aka siyesu, nan suka sauka, dadi kamar ya kashe Daddy da Zaid yace mishi Gidanshi ne, ya rungumeshi yana Godia, Abdulmajeed ma murna ya taya babanshi don be san da shirin nan ba, a ranar Zaid yace "Daddy ina rokon Alfarma ka bamu izini muje maka bikon Mummyn mu, kaga kar a kawo maka Amarya Uwargida bata nan" yace "haka ne, da kai na zanje na maido Maryam dita" duk aka hau shewa, har zuciyan Abdulmajeed da Ziyada sunji dadin yanda Zaid yayi, shiko na ciki na ciki.

A ranar suka dunguma Gidan Aunty Aynarh da Tsaraba Nik'i Nik'i, su Zinatu su ka rungume danginsu, Mairon ce a Parlo, Zaid dai yana daga chan bayabaya ba wanda zai kula yana bayan, nan dai bayan yan surutai, da neman yafiya Mairo zata bisu a yanzu.

Dakin Aunty Aynarh ta isketa din yi mata Godia, duk tana mata wani ladabi da biyayya "Aunty Aynarh, nagode kwarai Allah kadai zai biyaki" Aunty Aynarh tace "na fa sha gaya miki, ba don ke nake abu ba, da don ke ne da baayi ba, kuma wannan nok'e nok'en da kikeyi, na san fa halinki sarai, so kike in saki jiki, in shishige miki ki min wani mugun abu ko? To ba dani ba, ni da kisgiya nesa nesa, bance muyi gaba ba, amma ba ruwana dake ba ruwanki dani, wanda ya biya allonsa ya wanke" Mummy ta murmusa tace "ai Aunty Aynarh, kinsan ni kai tsaye ce, in zan miki wani abu ai ba sai nayi nok'e nok'e ba, na shiryu, nayi nadama, bansan meyasa har yanzu kike min kallon Hajia Mairon Da ba, nidai wallahi ba zan cutar dake ba, ina jiranki nan da kwana 7 a Gidana, kizo mu hada kai, mu samar ma Daddy-- au Abbanmu farinciki da kwanciyar hankali, mu nemi aljannarmu a tafin kafarshi, nidai nagode da taimakon da kika min, da so da kauna da kike nuna ma Yarana, tabbas da ba na sonki, amma yanda naga kinayi da yarana ko ba donAllah kike ba nikam kin gama min komai, akwai wani Girmamawa na musamman da nake ma duk masoyin Yarana, Nagode sai kinzo Kanwata"
Kafin Aunty Aynarh tace wani abu Mummy ta juya ta bar mata dakin.

Aunty Aynarh ta murmusa tace "ban tsaneki ba Hajia Mairo, halinki ne bana so, amma in kin chanza, bamu da matsala" bin bayanta tayi, suka isa parlo, nan a ka k'ara gaisawa, Ziyada ta dauko ma Aunty Aynarh tsarabanta na dubai da Saudia, tayi ta godia, sai wurin 9, suka bar Gidan gabaki daya a ka koma Gidan Daddy, kafin Maama, Najwa, Zaid da Ziyada sai Hajjo suka koma Gidan Paapa .
Mummy ta fara zaban part dinta na dama, na Alhaji Daddy ne a tsakiya, tsarin Gidan ya mata kyau, kunyan Zaid takeji sosai wallahi, tana ganin yanda yake dojewa tun dazun, dama ai batayi tsammanin ya share komai lokaci guda ba amma dai tunda ance komai ya wuce zata zage damtsen wurin ganin ta farantawa kowa rai.
Ta fada toilet tayi wankanta dta shirya zuwa Turaka.
_A gurguje_.

*Anzo gurin*

A yau Asabar, dubannin Jamaa daga wurare daban daban suka shaida daurin Auren Alhaji Abba Abu, da Amaryarsa Hajia Aynau Mustapha bisa sadaki Naira dubu 40..
Da kuma auren Abdulmajeed Abba Abu da Amaryarsa Najwa Sada Abu, bisa Sadaki Naira dubu 100 lakadan ba ajalan ba sai fatan Allah ya basu zaman lafiya Ameen....

Hello Bibilicious freaking fans, afuwan, nasan wasu sunyi tsammanin ganin karshen ADAY a wannan page din, nima hakan nayi tsammani, i thought zan iya juye komai a cikin page din nan, amma naga hakan ba zai yiwu ba, in nayi hakan zanyi rushing kaina kuma komai in summary zanyi, wanda nasan ba haka zaku so ba.  So don kar kuyi ta jira shisa na baku wannan ku fara kafin pagen karshen yazo nan ba da dadewa ba.
So kuban kwana daya zuwa biyu in gama concluding, komai fa plus the everyevery (wink) if you know you know kawai.

#1love
#ADAY
#bibiliciousfreakingfans
#anatare
#nagode.

Biebee Isa.

💭A DADE ANA YI....sai gaskia💭

NA

Wattpad:@biebeeisa

KARSHE

Kafin daurin Auren.

Sai da suka kwana 5 a Yola, sunje nuna Zaid wurin dangi, da kuma sanar dasu Biki saura Sati 2 a wannan lokacin, Zaid be yarda yaje wani Lodge ba, nan gidan Baffansu Maama suke kwana, dakin samari ma, a cewarshi zai san kowa da kowa, zuwa ake ganin dan Yaya Ai da akayi zaton ya mutu, kowa na Alfahari dashi kasancewarshi jininsu, duk inda yaje sai ya raba Alheri, Abokan wasanshi suyi ta mai tsiya be iya fullanci ba. Haka dai sukayi sabo da Gwaggoninshi da Matan kawunnanshi, nan suka dawo Kano.
'Yan Yola sun iso garin Kano, su Baffa Hussaini, da k'annen Maama da Matan Yayunsu mutane sunfi 20, tun biki na sauran Kwana 2, Gidan Paapa cike yake da Mutanen Yola, Amare kuwa Najwa da Ziyada da Yanmata wanda kansu ke daya kuma suna Gidan Baba Abba, kamar yanda Zaid ya ma Kaveri da Mamarta da Vijhay Alkawari cewa lokacin Biki, zai tura musu kudin Jirgi suzo bikin to hakan yayi, already ya tura musu har sun iso Nigeria, Mota ya tura a dauko suwo, murna gun Najwa baa magana.

Matar Baffa Shamsu Karima(Matar k'anin Maama) gwana ce wurin gyaran Jiki, tun da sukazo take mamulan jikin Najwa da gyara, Maama ta shigo lokacin da ake mata gyaran Jiki, Maama tace "Ahh Aunty Karima, ya da son kai?" Aunty Kariman da ta dage tana murzan jikin Najwa da wami kwababben abu ya dago ta kalleta tace "Yaya A'i son kai name?" Maama tace "Ya naga kin kama diyarki kina ta gyara ni kin bar min nawa? Nima fa diyata Amarya ce" Aunty Karima tace "wake nan?" tace "Ziyadatu mana, kin kama Najwa sai gyara kike ni tawa ta zama 'yar kallo" Ziyada ta boye kanta, bata son tayi surukuta da Maama, amma Maama na bata kunya.
Aunty Karima tace "Yo na isa na k'i gyara Matar Gatan Marayu Aunty A'i? Wai da na fara da sabuwar Amarya, itama sai a mata" Maama tayi daria tace "Yauwa yanzu naji batu" sukayi daria gabaki daya, Ziyada ta rufe face dinta da tafin hannunta.

Wayarta tayi k'ara, special ringtone din da tasa domin Zaid ya sa ta gane *Forever* dinta ne, Najwa tace "Didi, ba zaki dauka ba? Ba Bhaiy bane" Ziyada ta dan turo baki tace "wai sai dai in fito mu tafi" Najwa tace "bani wayar in mishi magana" Aunty Karima tace "Yara kenan, kuna wasa da zama, yanzu Mijinki na kiranki kin k'i dauka, in kin k'i amsa kiran Miji to me zai hanashi sauraro ko kula matan banza? Yanda yake da kudi da Kyau kuna tunanin ba a kawo mai hari?" nan da nan jikin Ziyada yayi Sanyi, tace "wallahi wata sa'in muke jama kanmu kishiyoyi, tashi ki bi Mijinki kinji Ziyadatu, gobe da Safe kizo na fara miki gyaran"

Jakkarta ta dauka ta ma Aunty karima da Najwa sai da safe, fita tayi ta lek'a dakin Maama don mata sallama, ji tayi an rik'o hannunta, a dan firgice ta juyo ganin Zaid ne ya sata saukar da ajiyar zuciya, baya so hankalin mutane suyo kansu, ya ja hannunta zuwa dakin Paapa da tun da yan Yola suka zo ya koma Gidan Hajjo da zama, mayar da k'ofa yayi ya rufe ya mata rumfa a inda take kusa da bango da hanayensa yana mata wani irin kallon da ya sa ta janye idanuwanta yace "Babe, don nace tare zamu tafi shiyasa ki k'a ki daukan wayana?"ta dan shagwabe fuska tace "bafa haka bane" yace "I'm just missing you ne, jiya kika biye ma Baby kuka gudu gidan Daddy, na gaya miki ba daya kuke da ita ba, you are married amma ki dina biye mata kuna yawo, ba kwa nan ba kwa chan, tunda bakya so ki bini, muyi bankwana ki tsaya ki cigaba da abunda kike wanda ya fini" ya fada cike da shagwaba tare da juya mata baya.

Da sauri ta rungumeshi tare da kwantar da kanta a kan bayanshi tace "mu tafi Kaji myforever, duk inda zaka tafi ina biye da kai, kaine har abada dina, dama gyaran Jiki Aunty Karima zata min, amma tace gobe da safe zata min nawa, yanzu tana chan tana gyara maka baby" juyo da ita yayi gabanshi yace "Yauwa, inga Gyaran Gashin da akace anje dazun" be jira cewarta ba ya warware mata ribbon din da aka daure mata gashin dashi, gashin ya sauka kan kafadunta, sai salk'i da walk'i yake, da yatsun hannunshi ya dinga sharce mata gashin, Man da ya bi hannunshi ya chusa anashi gashin kai din, ya matso da ita daf dashi har suna jin hucin juna, yace "My Forever!! Ina sonki sosai" lumshe idanunta tayi ta bude so biyu "Nima ina sonka sosai" Mayafin ya daura mata a kai yace "mutafi ko?" gyada mai kai tayi don jikinta ya soma mutuwa.
Jakarta ya karba kafin ya ja hannunta su ka fita daga dakin Paapa suka nufa na Maama don yi mata Sallama.
***

A bayan seat ya tattarota gabaki daya jikinshi yana shak'ar kamshinta, waya yake da Abdulmajeed "Yeah, na dauki matata mun bar gidansu Baby, eh din bazan barta din ba, da mijinta ta dinga kwana wani gida, hahaha Mallam gata dai" sa mata wayan yayi a kunne "Hello YaMaji, ina wuni, eh mun tafi, tana chan Aunty Karima na gyara mata jiki harda lalle zaayi, hahah dagaske YaMaji, Allah shi kaimu sai da safe" Zaid yace "Mallam sai na ganka Gobe" ya datse wayan.
"Babe, wai gyaran jikin na meye? Naga jikinku ba wani abun gyara, gashi ne kuma kunje saloon, to meye zaa gyara" gyara kwanciyarta tayi a jikinshi, tace "ka tambayeni gobe in Aunty Karima ta gama gyaran, zaka ga Changes" yace "i cant wait" ya rungumeta a jikinshi har suka iso Guest house dinshi.
A wannan daren suka jiyar da juna kauna, sunyi missing juna kwarai dagaske, su ka kwanta manne da juna.
Washegari bayan sunyi breakfast, suka shirin zuwa Gidan Maama lokacin ana gobe daurin Aure.

Kyan da Najwa ta kara abun ba a magana, duk inda ta zauna ta tafi sai ta bar kanshin jikinta, an hana Abdulmajeed ganinta, Zaid ma sai da ya shiga chan ciki ya samu ganinta, ya kebe da Aunty karima, yace "DonAllah Aunty kiyi ma Ziyaa times 3na Baby, zan biya" hannunta ta ware tace "baka da kunya ko?" daria yake yi ya fita ya dinga gaisawa da kawunnishi da goggonshi, ba abunda ya kai Yanuwa dadi, babu abunda yakai zumunci dadi, a da yana da kudi yana da komai, amma be taba jin farinciki irin na kwakin nan ba, dama shi yana da son mutane, dalili ne ya maidashi miskilia, amma yanzu ji yake yafi kowa Jin dadi, haka ya dinga binsu one by one yace "Goggo Aisha Indo, ba ki da matsalar komai ko? Inna QueenBilkis baki da damuwan wani abu ko? "Ummu Abdoul akwai abunda kike so? Maman haneef in kuna da bukatar wani abu ku fada donAllah bansan me zan muku ba. DonAllah ku fada min bukatunku" sai suyi murmushi suce "Zaid, ba komai, Yaya A'i ta bamu komai, indai muna da bukkatar wani abu, zamu sanar da kai InshaAllah" yace "Yauwa donAllah, nagode" ya tashi da sauri ya nufa Dakin Paapa don ya san nan zai isketa.

Da Sallama ya shiga, ya iske tana shan Koko da kosai wanda Kwaiseh Maryama tayi da farar safiya, yace "Omg, Maama k'osai, i miss it wallahi" dariya tayi tace "Zaid" shima dariyar yayi, kan Gado ya zauna inda take zaune, yace "Ina kwana Maa" ta ansa da "muna lafia? Ya kuka kwana?" yace "lafiya lau, ya hidima da kuma baki?" tace "Alhamdulilah" yace "wai gidan nan be muku kadan ba? Naga ko ina da mutane, ta ya kuke kwanan?" tayi daria tace "lafiya lau Zaid, tsaf muke kwana ba takura, abunda kwana ma ake ana fira" ya sa hannu ya dauki kosai ya dangwala yaji yace "Maa, ina fatan ba wani abu ko?" tace "ba wani abu Gatan Marayu" turo baki yayi kamar dan yaro yace "in akwai ki fada donAllah" tace "haha, Harda hadani da Allah?" tace "Ka hado Akwatina Sha 12 na lefe, 6 na hajia Aynar, 6 na Hajia Mairo" yace "sai me kuma?"tace "Sai Allah ya maka Albarka" zai rungumeta ta tashi tace "kai son jikinka yayi yawa, haka matarka zata haihu, a dauki yaronka kaima a daukeka" daria yayi yace "Maaa, shekarun da baki daukeni bane nake so ki fanshe min shi, amm... Tsaya, Maa, Ziyaa ta kusa haihuwa ne? Tana da ciki?" Maa ta durk'usa ta kwashe kwanoninta tace "ka bincika ka gani" ta fita ya bi bayanta, ya koma dakin Yanmatan inda su Ziyaa suke, yace "Babe, Come" hannunta ya ja be damu da cousins dinshi da abokan wasan dake wurin ba ya fita da ita sukayi dakin Paapa yace "Babe, Are you Pregnant?" wani murmushi ya subuce mata daga baki, yace "ki gaya min Please" tace "nima fa jiya Aunty Karima ke fada min don taji nace ina son cin kwado" wani nishadi ke fuzgan shi yace "Ziyaaa, Aunty kariman ne za ta gaya miki kina da ciki? Ke baki sani ba?" cikin kunya tace "ina gama Period muka tafi Bauchi, kuma a lokacin.. Erhm, erhm" ya matso daf da ita yace "Shhh, na san me ya faru a lokacin" hade bakunansu yayi cikin kwarewa kafin ya saketa yace "ina sonki sosai, my forever, Allah ya inganta, amma tun lokacin baki sake period ba?" tace "ya kamata na sake tun a india, amma banyi ba" yace "24 days kenan rabonmu da India, you are pregnant Babe" ya dagata cikin murna yana jin dadi, ita ko sai dariya takeyi, tace "My Forever, barinje Aunty Karima ta fara min lallen kaji" yace "Nima zanje Gidan Daddy, Mijin baby na jirana, zamuje wani wuri ne" tayi Daria ta mai peck a kumatu tace "ka gaida YaMajin" zata juya ya ri'kota tare da manna mata hot kiss a baki ya juya ya fita yana jin dadi mara misaltuwa, ita ko mamamkin farincikin da ke bayyane a face dinshi take.

Hajia Mairo zaune kan Kujera ta Alfarma wato Royal Chair, ta daura k'afa daya kan daya, tunani take kan zaman da zasuyi da Hajia Aynarh, bata san ya zaman zai kasance ba, amma abu daya ta sani, ta san duk yadda zatayi don kar ta nuna Kishinta ko rashin son Auren nan sai tayi, bariki ce itama ai ta iya, ba wai dangin Yarbawa kadai suka iya Kissa ba, itama ta iya, ba zata bari abunda ya faru a baya ya sa tayi sanya ko ta ja baya ba, tasan tayi sakaci akan tarairayar Miji a baya, amma yanzu ba zata bari hakan ya faru ba, bata damu da tana da Yara ba, k'ara'i ne sai tayi, sai ta fanshe shekarun da ta batas a banza, zata zage damtse ta faranta ran Mijinta, ta tuna randa ta dawo gidan ta zage damtse wurin faranta mai rai, kuma ga dukkan alamu yayi kewanta kamar yanda tayi nashi, kuma InshaAllah zatayi k'okarin zama lafiya da Hajiya Aynarh, ta san tayi laifi me girma, amma Allah ya san ta tuba, tana rokon gafararshi kuma tayi Alkawarin ba zata sake komawa halaiyarta ta baya ba, zata manta da abunda tayi a baya, duk da abun zai dinga fado mata har karshen rayuwarta, amma yanzu dole ta gyara komai.

Waya ta dauka ta kira Managern Gidan Radio na Meela FM, cike da isa take magana a matsayinta na matar Alhaji Abba Abu, ta bada sak'o, kafin ta hau kiraye kirayen waya, k'awayenta wanda tayi watsi dasu a baya ta nemi numbersu daga wajen wata kawarta, ta dinga kiransu tana gayyatarsu, badai ta kira Hajia Aleeyah ba, don sun raba Jaha.
Zaineema ta shigo Parlorn sanye cikin doguwar riga ta Alfarma, tace "Mummy zanje Gidan Paapa, Aunty Karima zata min lalle" Mummy ta danyi wani tubani kafin tace "bari in kira Daddynku in tambayeshi sai muje tare k'ila akwai Aikin da zaayi a Gidan Paapanku" Zaineema tayi murmushi a ranta tace "gaskia Mommy ta chanza, da da ne fitar ta take ba tare da izinin kowa ba, Zaineema tace "Mummy ina waje ina jiranki" kai kawai ta gyada mata, cike da kissa ta kira Daddy ta lankwashe murya tace "Sweet Daddyn Yara" daga bangarenshi ya murmusa har ranshi yaji sabon sunan da Maryam ta lak'a mai yace "Sweet Mummyn Yara" ta lumshe idanuwa tace "ina neman izini zuwa Gidan Sada, zanje na gansu da shiryeshirye" Daddy yaji dadi, Maryam bata taba nemin izininshi ba in zata fita, amma yau itace da neman izini, tabbas yaji dadin sauyawarta, kuma ya lura tun da ta dawo take k'okarin faranta mai rai yace "A dawo lafiya, nima mun fita da Sada" "Allah ya maido min kai lafiya Masoyina" Daddy har ranshi ya ji dadi, yana ta murmushi gaban Paapa, Paapa yace "Allah ya ja da ran Mijin Maryam Angon Aynarh" Daddy yace "fadi ka k'ara" Hajjo tayo daria.

Mummy ta yafa gyalenta ta fito inda Zaineema take waya da khaleed, Baya suka shiga Driver ya ja su, suka nufi tarauni Gidan Paapa, a hanya ne Driver yayi tuning zuwa Meela FM suka ji wata zazzakar murya na sanarwa.
*Hajia Mairo Abba Abu na farincikin Gayyatar 'yanuwa da Abokan Arziki zuwa yinin Bikin Danku Abdulmajeed Abba Abu, da kuma walimar tarewar Amaryarta Hajia Aina'u Mustapha da zaayi ranar Lahadi da k'arfe 3 na rana a Gidan Alhaji Abba Abu da ke Nassarawa lowcost, wannan na matsayin katin gayyatar ga duk wanda be samu Kati ba, Allah ya bada ikon hallarta Ameen, Sanarwa Hajia Mairo Abba Abu*.

Zaineema ta hau tafi tana cewa "Wooo Mommynmu, wallahi kin burgeni, Allah ya kwabe fitina tsakaninku da Aunty Aynarh" Mairo tayi daria tace "Zainee, ance miki mu na yau ne? Da na bi bokaye, amma ina neman yafiyan Allah, Allah ya yafe min, yanzu kuwa, kishin Matayen Annabawa zanyi, kuma dan farincikin Mijina, Ke dai muje zuwa, ba zakuji wata matsala daga gareni ba" Zaineema ta rungumeta tace "Thank You Mom" shafa kanta tayi, tace "Khaleed zaizo daurin Aure ko?" Zaineema tace "Gobe yace zasu taho harda Hajiarsu" Mairo tace "Allah shi kaimu, ya kawo su lafiya" Zaineema tace "Ameen" kafin su isa sai da aka sake sanarwa a gidan Radio.
*****

Abdulmajeed yayi tsaki a karo na uku yace "wai don me zaa ce bazan ga Pure Heart ba? Don me?" Zaid dai dariya yake yace "nikam zauna in baka Goodnews dina" tsaki yayi ya zauna yana fuskantar Zaid yace "Ina jinka" Zaid yace "My Forever is Pregnant" Farinciki ya baiyana a fuskan Abdulmajeed yace "MashaAllah, ikon Allah, howcomes?" Zaid yayi rage girman idonshi yace "tambayana kake? To barin gaya ma, ni da Ziyaa--" Abdulmajeed ya wawuro wani pillow ya jefe Zaid dashi yace "You Marapoka, ba haka nake nufi ba" Zaid ya fashe da daria ya mike yace "tashi muje muga Kayan da Idi ya siyo" Abdulmajeed ya tashi yace "wani kaya?" "Maama tace a yi ma su Mummy lefe ita da amaryarta" Abdulmajeed ya dafe kai yace "Ohh Mata, muje Gidan ni Allah duk yanda zanyi naga PureHeart sai nayi ehe" yayi gaba Zaid na binshi a baya.

Akwatuna 6 saiti biyu wanda kala kadai ya bambanta cike mak'il da kaya, ko wani akwati da abunda ke ciki, Abdulmajeed yace "kai ni banda lokacin kallon wadannan abubuwan" Idi ya kalli Zaid yace "baka kalla ba, Ummu Sudais ta hada, ka dai duba abunda babu sai a kara" Zaid yace "i trust you, and i trust Ummu Sudais,ba sai nagani ba, kawai ka sa yaranka su kai chan Gidan Hajjo, su Daddy na chan, in sun gama a kawoshi chan Gidan Paapa, yanda Maama tace su zasu kaima Aunty Aynarh ku ksi motocin da zasu kai su chan, kasan shaani na mata" Idi yayi Daria, yace "Angama Oga" suka wuce kafin Idi ya kira yaransa suka kwahi kayan suka nufa Gidan Hajjo.
****

Hajia Mairo ta ware a Gidan Maama ana ta fira da ita, nan tace ma Aunty Karima in an gama ma yara gyaran jiki itama sai an mata, don itama amaryarce, shewa ake tayi.
Su Zaid da Abdulmajeed sukayi Sallama a Parlorn, amsawa akayi, suka sake gaisawa, Zaid ya dan kalli Hajia Mairo yace "Mummy ina wuni" da fararta dukda ta na kunyanshi tace "lafiya lau Zaid, ya akaji da hidima?" dan dariya yayi ya danyi gaba yace "Aunty Karima. Ina Baby wannan yace sai yaga matarshi zai bar gidan nan yau" Abdulmajeed yace "lahh, karya yake, wallahi cewa yayi na rakoshi wurin Zuzu, wai yana missing dinta" Mummy ta watsa mai hannu alamun dak'uwa tace "baka da kunya ko? Oya zo ka fice, kar ka sake ka shiga dakin yanmatan nan, ba su kadai bane" Zaid yayi kamar be jita ba, yayi gaba, burinshi yaga matarshi, yaji muryan Mummy na cewa "harda kai Zaid, zo ka wuce, oya out both of you" Zaid ya turo baki ya fasa shuga dakinsu Najwan ya zo ya dungure Majeed ya tusa k'eyarshi suka fita suna mitan an hanasu ganin matayensu".
Maama ta sa daria tace da Mummy "ai kece daidai su, dazun wai ina dakin Paapansu Zaid yake ta wani fi'ili wai matarshi na dauke da juna biyu, kamar kanshi farau" nan fa Mata suka fara tofa alabarkacin bakinsu "Ahh MashaAllah, su Ziyadatu har an harbu? Allah ya inganta" Mummy dai tayi ta murmushi.

Idi yayi Sallama a bakin kofar Parlorn, wata diyar Baba hussaini da ake ce ma Cutielurv ta lek'a, suka gaisa yace "kice ma Maman gatan marayu ga sak'o nan" Cutielurv ta koma ta sanar da Maama, tashi tayi ta nufa waje, har kasa ya durkusa ya gaidata kafin yace "ga Sak'o nan, inji Gatan Marayu" a ranta tace "Allah ya kara budi na Alheri Gatan Marayu, tace ku shigo dashi, Yaran Idi suka dinga shigowa da Akwatun nan, yan parlo sai kallo suke dai.
Maama tace ga Lefe nan "Yara sunyi wa Iyayensu" ko bata fada ba, sun san Zaid take nufi, "Hajia Mairo saiti guda, Amaryarta saiti guda" Guda aka sa, Mairo tace "MashaAllah, Allah ya biyashi da Gidan Aljanna" suka amsa da Ameen, nan suka kwantar da Akwatunan suka shiga budewa dayan bayan daya, sutura guda hamsin Harda dinkakku ready made, da kayan shafa, da mayafai, da yankune da sarka Zinari. Maama tace "Hajia, ki dau wanda kikeso sai akai ma Amarya nata ko?" Hajia Mairo tace "na dau wannan" na farkon kenan, na aka hau guda.
Tace "Toh, ku tashi mu dinguma muje Mukai ma Amarya lefen nata".
Haka ko akayi, Mata su ka cika motocin da aka tanada dominsu gaban Gida, aka loda akwatunnan Aunty Aynarh aka nufi Gidan Amarya, Yanmatan aka bari a gida.

Hajia Aunty Aynarh zaune cikin Kawayenta, yanuwa da abokan arziki, wanda kallo daya zaka musu kasan cewa wayyayu ne, hutu da kudi sun zauna musu, fira suke na yarda gobe zata kasance, su ma sunji sanarwar Hajia Mairo a radio, wata tace "Ahh, Uwargidanki ta burgeni Aynarh, ba ruwanta har gayya take" wata tace "ke ba duk bariki bace, mun san komai ruwan kissa ce dai kawai" dayar tace "ke ai hakan yafi, indai akan burge Miji ne, kowa ya biya allonshi ya wanke, ba boka ba mallam, nidai Aynarh ina rokonki kar kiyi kishin jahilan matan nan" Hajia Aynarh ta dara tace "kawayen Arziki, kunsan banda damuwa, ba ruwana da ita, zamuyi zaman lafiya, don mu ba yara bane, amma ina anzo kan Miji, kowa yayi ta kansa" shewa suka sa suna Jinjina ma Aynarh, nan suka fara zancen Manya, kafin sukaji Sallamar Mata da dan hayaniya daga waje.

Maama ce ta rafka sallama kafin sauran suka rufa mata baya, wanda harda Mairo, da yake abun na Mata ne masu kissa suka tarbesu hannu bibbiyu ganin Mairo, Mairo na ganin haka itama ta kwasa a guje ta rungumo Hajia Aynarh, Hajia Rufaida babbar Aminiyar Aunty Aynarh ta rangada guda, Mummy tace "Kanwata, na k'agara kizo Gida mu hadu mu kwantar da hankalin Mijinmu" itama da yake ta iya tace "wallahi Yayata nima ji nake kamar na jawo gobe, na kagara na kasance tare da ku" nan Manyan mata a ka sa shewa, Mummy tace "Lefenki ne muka kawo miki inji Mijinmu" Aunty Aynarh tace "Ahh, Allah sarki Abbana, har da dawainiya?" Mummy tace "wallahi dawainiya kam, saiti biyu daya na Uwargidarshi sarautar Mata, da kuma ta amaryarshi wacce bata laifi" kamar wasu kawaye suka kashe ta hanyar tafawa, Maama da marakabanta saidai su bi Mummy da kallo, su bi Aunty Aynarh da kallo, sun san dukkansu Kissa da Kissisina ne, wanda yafi shi ya iya" nan aka jawo Akwatuna aka bubbude suna kallo suna yaba kayan.

*BAYAN DAURIN AURE*

Daga inda aka daura auren aka dunguma zuwa _ Abba Abu & Sons Furninshing Company_ don yin Reception na daurin auren da kuma Walimar Bude _ Abba Abu & Sons Furninshing Company_ cikin Haraban Company aka saka canopies da kujeru, akayi decorating wurin.

Sanye yake da Milk Shadda da ta sha Aikin sky blue, annurin fuskarshi baya daukewa, hakan ne ya fito mai da cikar zati da kamalarsa, ya hadu iya haduwa, ga Kyaun Fuska ga na Hali, Namiji daya tamkar dubu, burin ko wacce diya mace, Abdulmajeed Abba Abu kenan Angon Najwa Sada Abu, an daura aure burinshi ya cika.
A nan wurin taron bude sabon Kamfanin Babanshi yake gaisawa da abokansa da suka zo taya shi murna, sai hotuna suke tayi, ya dan samu ya kebe da Zaid yace "Kai, nidai na tafi Gida, zanje ganin Matata" Zaid yayi daria yace "kai dai ba an daura ba shikenan, ka tsaya mana ana ta zuwa maka murna, kuma kasan yanzu zaa bude Company dinnan, your presence is needed" Abdulmajeed yace "Kai, wallahi Gida zani, company zaa budeshi with or without me, and Abokaina su samu Aliyu gashi chan sai na dawo" be jira cewar Zaid ba ya faki idonsu Daddy ya sabe, Zaid ko sai daria yake.

Taron ya samu hallartan Manyan mutane zagaye da duniya, Shugaban Kasa be samu suwa ba sai ya turo wakilinshi, nan aka ci aka sha, Baba Abba yayi godia ga mutanen da sukazo tayashi murna, nan aka zo bude Company, Baba Abba na gama mutanen na baya, Scissors aka bashi don ya yanka abunda akayi ado wanda zai sadaka da cikin Company din, Alhaji Abba rike da Scissors din, gefenshi Danuwanshi ne rabinjikinshi Alhaji Sada, dayan gefen kuma Zaid gatan Marayu ne, sai autanshi Muhsin, akace ya yanka bayan an irga ukku, k'asa k'asa Daddy yace "Zaid, ina danuwanka?" Zaid ya dan sosa k'eya yace "Erhm Daddy, yaje ya dawo" tsaki Daddy yayi ya yanka dan igiyar ledan aka hau tafi raf raf raf, yayi gaba aka biyoshi a baya, shiga sukayi da jamaa duk wani lungu da sak'on Company, nan aka yi addua a masu bada gudunmuwa na badawa..

Zaid na waya ya hango Baba Ado sun shigo Kamfanin da mutanenshi, da sauri ya katse wayan beyi zaton zai samu daman hallartar taron ba, yana zuwa ya rungume Baba Ado, "Barka da Zuwa Baba" Baba Ado yace "Allah ya ji k'an Gatan Marayu, muna lafia?" yace "Alhamdulilah, barka da zuwa, Bismillah" alamu ya ma Idi, tuni aka ma Baba Ado wurin zama kan wata kujera ta Alfarma, Zaid ya shiga cikin Kamfanin ya ma Daddy da Paapa magana cewan ga Abokin Babanshi yazo, da sauri suka k'araso inda yake, yana ganinsu shima ya mik'e ya mik'a ma Daddy hannu don suyi musabaha, dan rankwafawa Daddy yayi alamun Girmamawa, don Baba Ado zai girmeshi nesa ma ba kusa ba, yanda Daddy yayi haka Paapa yayi, suka gaisa cike da Girmamawa, Baba Ado yace "Alhaji Abba na tayaka murna, ga Amarya ga kuma sabon Kamfani, Allah ya sa Alheri, ya kwabe tsautsayi da fitina" Ameen suka amsa gabaki daya, Zaid yace "Baba, wannan shine Babana Mahaifi, ashe basu mutu ba, suna k'asar India" maida hankalinshi yayi gurin Paapa, Paapa ya dan sadda kai, Baba Ado ya dafo shi yace "Allahu Akbar, ashe da rabon ku gana" Paapa yace "Munji labarin komai daga wurin Zaid, munji kalar guddumuwar da kuka ba Zaid, ba abunda zamuce sai Allah ya saka da Alheri ya biyaku da gidan Aljanna, Allah ya kareku daga sharrin mutane da Aljannu, Allah kuma yaji k'an Baban Zaid ya gafarta mai, Allah ya biyashi da Gidan Aljanna" Baba Ado ya murmusa yace "Ameen Ameen" Zaid yace "Ina Aunty Taatuh?" yace "tana Gidan Hajia Aynarh, ka san tun bikinka suka zama kawaye, ina Matarka?" Zaid ya dan sausauta murya yace "ka kuma zama Kaka" Daddy yayi alamun zai bugi Zaid, yayi daria ya doje, Baba Ado yace "kunsan, ban taba ganin farincikin Zaid haka ba? Ban taba ganinshi ya sake da walwala haka ba, Allah yaji k'an gatab marayu, burinshi ya sama mishi farinciki" Zaid ya murmusa yace "Allah ya ji kan Babana" suka amsa da "Ameen".
******

GIDAN AMARE.

Duk sunci gayu cikin shiga ta Alfarma, Ziyada da k'awayensu na dakin Najwa ana ta kai da kawowa, Najwa tayi kyau harta gaji, Meenerhparrot's glam tayi mata makeup, sanye take cikin wani cream lace, da mayafinta sky blue, sosai tayi kyau, k'amshi baa magana, tun a cikin gidan ake ta selfie, Maama ta shigo dakin cikin shiga ta Alfarma tace "Zaineema, ki hada ku ga motoci chan ku shiga ku nufi Gidanku, mu mun tafi daukan Amarya, ku wuce chan Mummynku na jiranku" Zaineema tace "to Maama yanzu zamu tafi" Maama ta fita suka bar Gidan ita da tawagarta zuwa daukar Amarya Hajia Aynarh.
Zaineema tace "Oya ku tashi muje Gida" Ziyada ta mik'ar da Najwa, Kaveri da sauran cousins din su Najwa kowa ya tashi ya gyara mayafinshi, su ka fita daga dakin, kamar daga sama sukaji Sallamar Ango,ga Ango ga Ango, Najwa na jinshi ta sadda kai k'asa, hannu ya ba Zaineema sukayi musabaha, Ziyada kuwa ta sa ihu "YaMaji ka ganka kuwa, wannan haduwa haka?" be amsata ba ya hau amsa gaisuwan yanmatan Amaryan dake wurin kafin yace "Ina zuwa haka Zuzu?" tace "Gida zamuje" Zaineema ya kalla da ido, tuni ta harbo jirginshi, tace "Kaveri, lets wait for the bride outside, oya ku muje waje, har ke Ziyada" Zaineema ta tasa keyarsu gabaki daya suka fita suka barsu su biyu a Parlorn.

Kallonta yakeyi kamar ya hadiyeta, sosai ta mishi kyau, sonta na fuzgarshi, yana sonta matuka, yana kaunarta yana begenta, a hankali ya karasa gunta cikin nustuwa, "PureHeart" ya kira sunanta cikin wani siga, a hankali ta dago idanuwanta ta watsa mai cikin sanyi tace "Jaaan" a hankali kamar me rada yace "You are Mine (Ke tawa ce)" itama tace "I'm Yours (Ni taka ce)" yace "i wanted to this for long(ina so inyi haka tun da dadewa)" da dan mamaki ta kalloshi tace "Mene?" Hada jikinsu yayi ta hanyar rungumeta dauke da mixed feelings yace "this" bata yi magana ba illa itama ta kai hannunta bayanshi tare da lumshe ido, sun kusa mintuna uku a haka, jefi jefi suna sauke ajiyar zuciya kafin ya sausauta rikon da ya mata, yana kallon idanunta, sauke su tayi kasa, har yanzu jikinsu na daf da juna, har tanajin hucin numfashinshi a goshinta, don Abdulmajeed dogo ne, hannunshi ya sa ya dago ha66arta sama yanda zata fuskanceshi, idanuwanta ta mayar ta rufe, bakinshi ya kai kan nata yayi kissing dinta lightly kafin ya sake rungumeta, cike da sanyin murya tace "Jaaan" shima yace "PureHeart" tace "Mein bohot pyar kharta hoon(ina sonka sosai)" Yau da gobe ya san maanar hakan shima yace "I love you too PureHeart, ina sonki, lets get you home" murmushi tayi ya ja hannunta, suka rufe Gidan, suka fita, da suka isa Haraban Gidan, su Zaineema sun tafi, Motar da ta kawoshi Gidan ya bude mata, ta shiga shima ya shiga baya, yace da Driver "Muje Gidan Daddy" Driver ya ja Motar..
A bayan Motan ya rik'o hannunta ya dinga kissing din hannun wai lallen yayi kyau sosai, ita dai bata ce komai ba, haka har suka isa Gidan Daddy..

Tun daga farkon Unguwar suke ganin motoci wanda da alama gidan suka zo, Sai da ya fita ya bude mata k'ofa kafin ta fito, Gidan Cike yake, harabar Gidan anyi decorating dinshi, daga chan gefe ga UmmuSudais Catering service, dayan bangaren kuma DJ ne, Mata ne ko ta ina wasu na cikin canopies zaune ana fira, hankalin mutane ya dawo kansu, ga Ango da Amarya, Mummy na jin haka ta fito daga cikin Kawayenta ta karaso gunsu, rungume Najwa tayi ta mata kiss a goshi, kafin ta rungume Majeed, tana jin zata iya chanza komai amma ba zata iya chanza nuna ma Yaranta So a baiyane ba, aa ita haka take, a baiyane take nuna son 'yayanta tace "Kai ka kawo matarka ka koro mun yarana ko?" daria yayi, yace "Oya ga Iyayenka chan kuje gaishesu, da kanta ta hada hanayen su wuri guda ta musu iso wurin kawayenta da ke zaune, wasu ma batayi zaton zasu zo ba sai gasu, bin iyayen yake tayi yana gaishesu, nan Mairo ta ya fito Cameraman ya dauke su hoto, ta shiga tsakiar Abdulmajeed da Najwa ta rungumosu aka daukesu, farincikin ganin danta cikin farinciki ya wanke mata tambarin jin zafin zuwan kishiyarta.
Abdulmajeed yace "Mummy taron Mata ne, nikam barin tafi" Mummy tace "kuma kuna taronku ai nayi mamakin ganinka a nan" yayi daria ya kalli Najwa, sukayi magana ta ido ya juya ya fita.

Mummy ta ja Najwa zuwa inda yanmata suke ta zaunar. Gudar da sukaji ne ya sanar dasu cewa Amarya ta iso, zata rantse sai da gabanta ya fadi, jin hannun Mrs Splendid ya k'ara mata kwarin guiwa tace "kece hajia Mairo, wanda ba kya tsoro ko fargaban komai, durkusa ma wada ba gajiyawa bane, Bariki" Hajia Mairo ta murmusa tace "Iyawa, Nagode Maman Husna" Mairo ta chanza face zuwa na farinciki ta amsa microphone a hannun DJ tace "Oya Oya OYa, a tashi tsaye, ina son kowa ya tashi tsaye , ku tayani maraba da Amaryata,ga Amaryata tazo, Dj samana wakar Lagbaja" nan da nan Dj ya saka kidar Lagbaja, Mairo ta fara takawa, sowa kakeji, kawaayen Mairo yan bariki, suka tayata takawa suka karasa inda su Hajia Aynarh da danginta ke zuwa, Mairo na zuwa ta rungumo Aunty Aynarh, nan aka kaure da rawa Mairo ta kamo hannun Aunty Aynarh tayi suka dunguma zuwa part din Aunty Aynarh, Maama ta sa key ta bude Part din, Aunty Aynarh tayi addua ta shiga da bismillah, MashaAllah nan aka sada Amarya da dakinta, Gidanta yayi kyau matuka, nan yan ganin daki suka dinga shiga dakin one by one.

Aka bar Aunty Aynarh da Aminnanta a daki, sauran kuma suka fito waje, nan aka ci Abinci, mostly Abincin Yarbawa ne, Amala da Ganda, wata Yayar Aunty Aynarh ta ba Dj Disc dinsu na wakokin Yarbawa aka basu fili, Dj ya samusu wakokinsu, nan suka hau juya mazaunai cikin iyawa, nan suka zama abun kallo, kafin Mairo da Kawayenta suma suka shigo fili don baja tasu kolin, daga baya kuma Mairo ta jawo yayanta su Zaineema, Ziyada, Zinatu da Najwa suka shiga Part din Aunty Aynarh suka fito da ita fili suka chashe, Taron Matan yayi sosai, an ci an sha, an gyatse, harda su turmin atamfa da leshi a sourvenirs, nan Yan ZBI ake ta hadama, suna warwaso, Haly Ghana dake rabo tace "ku kwantar da hankalinku, duk zaku samu, akwai da yawa" softie ta kalleta tace "gaskia ba zamuyi inviting dinsu Dinner din anjima ba, dube su da yawa fa su256, ai sai su ba mu kunya" Sholingaye tace "strictly on Invitation ne. Ko sun zo sai dai su tsaya a harabar wurin".

Da Daddare wurin 8 kuma aka dunguma akayi wurin Dinner Party da zaayi a Afficent
Bristol palace inda akayi na su Ziyada, wuri yayi wuri, taro ne har iyaye, bayan kowa ya zauna, Abokan Ango da kawayen Amarya suka shigo ciki, wurin da aka tanada domin su suka nufa suka zauna, nan akayi introducing shigowan Gatan Marayu da Matarsa, da kuma kanwar Ango Zaineea da Mijinta, suma shigowa sukayi a tare, Zaid cikin Rigar Suit Bak'a sai ta ciki fara da bowtie maroon, Ziyada kuma da riga bak'a, da gyalenta black and white.

Daga Bisani kuma akayi sanarwar isowan Amarya da angonta, Abdulmajeed cikin shiga ta Alfarma, Navy blue Suit da skyblue shirt, Najwa kuwa Navy blue wedding gown ne me dogon hannu, da mayafi sky blue, sosai sukayi kyau, cikin tafiyan couples suka iso wurin da aka tanada dominsu, bayan sun zazzauna, aka fara gudanar da dinner, Baba Ado shine ya bude taro da Addua, Welcome speech by Gatan Marayu, Kaveri ta bada takaitacen Tarihin Najwa da turancinta na Indiyawa, Aliyu ya bada takaitaccen tarihin Abdulmajeed, aka ci abinci, aka dan taka, Maama dai bata rawa, Hajia Mairo kam ta chashe, Amaray Aunty Aynarh ma ta dan taka, haka aka ci taro taro ya watse lafiya, abun dai sai wanda yaje ya gani.

*A GURGUJE*

WasheGari da Safe gabaki daya Family din aka hadu a Parlorn Daddy, Paapa ya bude taro da addua, Daddy ya fara da musu gajian biki, kafin ya fara da ""Ammm, Tohm Abdulmajeed a yau ka sake zama Miji, Hak'k'i ya rataya a wuyanka, ba zan gaya maka hakkin matarka kanka ba, amma na san zaka kula ka sauke duk wasu hak'k'unan dake rataye a wuyanka, Abdulmajeed na san ka da Hakuri, na sanka da kawaici da kau da kai, nasan ba zaka bani kunya ba, nasan zaka tayani k'arafafa zumuncina da na danuwana, nasan ba zaka bari ta dalilinka zumuncinmu ya ruguje ba, Abdulmajeed ka kula da Najwa, Abdulmajeed ku zauna lafiya, zaman lafiyanku shine namu kana jina?" Ya dago ya kalleshi yace "Eh Daddy, naji, kuma InshaAllah ba zaku sameni da wani abun da ba daidai ba" Daddy ya maida hankalinshi kan Najwa yace "Najwa, a sanin da na miki ke yarinya ce me kirki da son yanuwanta, na fuskanci kina da hakuri Paapanku ya tabbatar min da haka, amma NAJWA ki sani, aure ya sha bamban da abubuwan da kike gani a talabijin, aure ya wuce soyayyar da kike gani na India, Aure dan zo mu zauna, zo mu saba ne, shauki da soyayyar da kuke ma junanku, ba wai ya na nufin ba zaku sabu sabani ba, aa zaku samu sabani, zaku bata ran junanku, amma hakan be nufin ki dauki waya ki kira maamanki ko mumnynku ki gaya musu, ki rike sirrin gidanki, dana Mijinki, in kun samu sabani ku shirya kanku, kiyi hakuri kinji Najwa? Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a Dayyiba".

"Ameen suka amsa gabaki daya, Daddy yace "Sada ko zaka k'ara wani abu?" Paapa yace "Yaya ka fadi komai, sai dai ince ba wai Abdulmajeed da Najwa ake ma nasihan nan ba, harda kai Zaid da ke Ziyada, kuma ai amaren ne, nasan lokacin Aurenku an muku, amma ina so kuyi amfani ds abunda Daddynku ya fafa muku, Allah ya muku Albarka gabaki dayanku" da Ameen suka amsa,"Yesmeenah zaki kara wani abu?" tace "ai Papi kunce komai, Allah ya mudu Albarka, ya kwabe fitina, Mummynsu ki musu Nasiha" Mummy ta kasa magana don hankalinta tashe yake in ta tuna, Ziyada zata tafi, Abdulmajeed zai tafi, Zaineema zaa tafi, girgiza kai tayi tace "ai kun gama cewa komai" Daddy yayi murmushi ya kalli Aunty Ayanrh yace "Amarya fa? Me zakice da yaranki?" ta murmusa tace "Yanmaza ku ji tsoron Allah, ku kula da matayenku, kar ku ga kamar kuna gabansu ku tauye musu hakki, kuyi supporting dinsu, yanmatana kuma, ku tashi kuzo muje daki" akayi daria, ta mik'e ta dago Najwa da Ziyada ta yi gaba dasu, ta juyo ta kalli Zaineema ace "Oya, kema zo" Zainee ta mike ta bi bayansu" nan su Daddy sukayi daria.

Mummy ta mike tayi dakinta don hawaye yazo mata, Maama ma ta tashi tabi bayanta.
**
Aunty Aynarh ta cigaba dacewa "Ehen, ba wai don kunga kuna da komai ba, ba wai don akwai masu aiki birjiki a gidanku ba, zaku lankwashe kafafu kuyi folding arms kuce komai masu aiki zasuyi, no ban yarda ba, masu aiki suyi muku komai amma banda Gyaran dakin Miji, banda dafa Abincin Miji, kunga abubuwan nan biyu? Ku zage kuyi da kanku, kar ku bari wata me aiki ko wani me aiki ya dafa ma Mijinku abinci, kunga gyaran dakin Miji? Ku yi da kanku, ku gyara turakar mijinku, zaku ga ribar haka, kuna jina?" kai suka gyada, tace "yauwa good girls" irin abun da taba Zaineema da zata America ta kara daukowa, tace "ku dinga shan wannan, zan ba Hajia Karima, in kun isa Abuja ta ba ko wacce nata kunji? ku tashi ku tafi".

Parlo suka koma, Daddy yace kuje kuyi sallama da Mummynku, Abdulmajeed ya tashi a tare suka shiga suka isketa bakin Gado, Zaineema ta zauna a gefenta ta dora kanta kan kafadunta , Ziyada ta zauna a dayan gefen itama tayi hakan, Abdulmajeed ya tsugunna a gabanta ya dora kanshi shima a kan cinyarta, hakan ya karya zuciyanta, hawayen da take boye suka fara sunturi a idanunta, ta dora hannunta kan Kan Abdulmajeed tace "Dama ba zamu dauwama tare ba, dama dole wata rana na aurar daku, kuyi nesa dani, Aure Ibada ne, da banga abunda zai sa na rabu da ku ba, ku sani ina sonku fiye da rayuwa da kanta, ina matukar kaunarku, and babu abunda ba zan iya ba dominku, ina sonku 'Yaya na" dukkansu hawaye suke, Abdulmajeed yace "Mummy, muna tare, ba abunda zai rabamu, duk randa kika so ganina, ki kirani ki gaya min, InshaAllah duk abunda nake a Abuja zan bari nazo kiranki, i promise" shafashi tayi tace "I'm proud of you, take care ofNajwa kaji?" kai ya gyada mata, ta rungume yayanta mata tace "Allah ya muku Albarka" suka amsa da "Amin".

Zaid da Najwa suma a dayan Dakin Mummy, Najwa sai kuka take tayi, Zaid na ta lallashinta yace "Haba Baby, ba wai nace miki ga gida ga gida zamu zauna ba? Meyasa kike kuka? Kina so ki tada hankalina ne? Maa DonAllah kice tayi shiru, zata sani kuka nima" Maa dai ta kasa magana don itama hawayenta na gab da digowa, chan dai tace "Kya huwa Najwa? Share hawayenki, zan dinga zuwa Abuja ganinki, kuma Bhaiy dinki zai kula dake, ga Mijinki me so da kaunarki, ga yaruwarki Ziyada, ba zakiyi kadaici ba, kiyi hakuri kinji?" "Maama ke kadai a gida akwai kadaici" tace "kar ki damu, baffa haruna ya bani Umaimah yace Aure ya rabanu, so wont be alone, zan sata makaranta ta tashi gabana" Najwa ta rungumeta tana gyada kai, nan Maama ta musu nasiha me ratsa zuciya kafin sukayi group hug.

Yan Yola Zaid ya sa aka dauko daga Gidan Paapa, sunyi sallama dasu Maama, a cewarsu daga dakin Amarya zasu wuce Yola ba zasu biyo ta kano ba, itama Kaveri, da Mamanta da Vijhay bhaiyya sunyi sallama daga Abujan zasu koma India, Zaineema daga Abuja zata koma Gidanta, ba wanda zai dawo Kano dai a takaice, nan akayi Sallama dasu Daddy, suka musu fatan sauka lafia.
Amarya aka dauka a Mota, mota yafi Ashirin akayi convoy zuwa Abuja.
Sai Goma saura na dare suka iso Maitama, GidanAbdulmajeed na jikin Gidan Zaid, rabawa akayi, wasu zasu kwana Gidan Najwa, wasu zasu kwana Gidan Ziyada.

*WasheGari*
Da Safe Zaid ya sa aka kai Yan Yola Airport inda zasu koma Gida bayan ya musu Alheri me dumbin yawa, ya kuma rokesu da in suna bukatar wani abu su gaya mai" Kaveri ma da Mamanta an kaisu Airport inda zasu wuce India, Zaineema ma sun wuce Kaduna da khalid,
Gidan ya rage Maauratan su kadai.

*A GIDAN ZAID*

Zaune suke suna kallon juna Zaid yace"My Forever, kinsan da Bansan meye love ba? Kinsan ni banda lokacin love, ko da Na'ila kece min tana sona kallonta kawai nake, banson me take nufi da tana so na ba, bansan me takeji ba, Ziyaa akanki na san meye So, duk wata soyayya da kika ga na nuna miki a da, in gaya miki gaskia words din Armstrong ne, amma yanzu i dont need Armstrong to tell me what to say to you my Forever, yanzu na san Sonki a jinina yake, my Forever, ina sonki sosai, i want to be with you.. No i need to be with you for the rest of my life" blinking idanunta tayi so biyu, tace "kaine best thing da ya taba faruwa dani, Allah ya bar mu tare" dagota yayi ya maidota jikinshi yana mata wasu abubuwa masu wuyar fassaruwa..

A KANO
Gidan Daddy

Tarasu yayi gabaki daya a parlo;
"Maryam, Ainarh, ina mik'a godia ta musamman gareku da kuka nuna min So da Kauna, Maryam kece babba, ki sani ina sonki kamar yanda nake son Aynarh, dukkanku matana nane, ba zan yarda da daya taci mutunci ko zarafin daya ba, ina so ku hada kanku, ku zaman tsintsinya madaurinki daya, bana son ku dauki maganganun mutane ku tada min hankali, Ainar'u, Maryam matatace uwar 'yayana, bazan dauki ki rainata ba ko ki ci mata fuska, tabbas in na kama dayanku da wani laifi zakuga fushina, mu taru mu zauna da juna zuciya daya donAllah, DonAllah ina bukkatar hadin kanku. Mummy tace "Sweet Daddyn Yara, InshaAllah ba zakaji wata matsala daga kaina ba, da yardan Ubangiji" yace "Nagode Maryama ta Abba" murmushi tayi, Hajia Aynarh yace "Nima InshaAllah zaka sameni a me muku biyayya, ba zakaji komai nima daga wurina ba, Allah ya bamu zaman lafiya" suka amsa da Amin yace "Nagode Aynarta, sai maganar kwana, Maryam ya kika gani?" tace "ai kawia kamar yanda aka saba yi a ko wane gida, kwana bibbiyu" ya kalli Aunty Aynarh tace "hakan yayi, Allah ya hada kawunan mu" suka amsa da Amin.
Daddy ya mike yace "bari yaje Gidan Hajjo in dawo" mik'ewa sukayi suka rashi har gaban Gida inda Drivern shi ke jiranshi suka mai adduan dawowa lafia, ya shiga motarshi cikin jin dadi, suka koma suna dan fira abun gwanin ban shaawa.
****

Zaune suke gaban Hajjo, Sada yace "Kiyi Hakuri Umma, ba zaiyiwu ki zauna ke kadai a cikin gidan nan ba, saboda halin rayuwa" tace "Sada nikam ku barni a nan, bana so naje kuna zaune da matayenku na zame muku dawainiya, balle na shiga tsakaninku da matayenku" Daddy yace "Haba Umma, ta ina zaki zaman mana dawainiya? Kina mahaifiyarmu, Umma abunda ya faru da ba zai sake faruwa ba da yardan Allah" ta danyi shiru tace "ni dama wata kuka samo ta dinga tayani zama , ko kuma dayan dakin nan a sa yan haya Mata da Miji, tunda dai zaman ni kadai din ne bakwa so" Daddy yace "aa Umma, nidai zuwa nayi na tafi da ke, kuma kar kice aa, nan kuma a sa 'yan hayan, ki dinga karban kudin hayanki" da kyar suka shawo hankalinta har ta yarda.
Komawa sukayi Gidan Daddy, Daki kuda da nashi ya bata, ya kuma jama matayenshi kunne kan mahaifiyarshi.

A B U J A
Gidan Abdulmajeed

Shigowa yayi dakin inda take zaune,  ya yaye mayafin kanta,  ya dago fuskarta suka k'urawa juna ido,  murmushi suka sakar ma junansu yace "taso muje" ba musu ta sauko daga kan Gadon, hannunta ya rik'e ya sauko da ita daga Kan Gadon, janta yayi,  ya dinga nuna mata daki daki, da kitchen, ya gabatar da masu aikinta guda biyu,  da haliey er niger,  da wata bilki,  su ka zube kasa suna kwasan gaisuwa, haka yace "kuna iya komawa dakinku sai da safe" a ladabce suka musu sallama suka tafi baya inda dakinsu yake.
Abdulmajeed ya kalli Ziyada yace "PureHeart, ina jin yunwa" ta kalleshi tace "barin dafa maka wani abu" hanyar kitchen ta nufa yayi saurin kamo hannunta ya gyada mata kai ya jawota ta fado k'irjinshi ya matseta yace "wa ya ce miki Amare na shiga kitchen?" turo baki tayi tace "but you are  hungry" jawota yayi yace "zo muje" ba gardama ta bishi daki,  mayafin da ya aje ya sa mata,  ya ja ta ya fita,  mukullinshi ya dauko na daya daga cikin motocinshi,  hannunshi rike da nata ya jata suka fita daga gidan,  ya bude mata mota ta shiga yayi horn maigadi ya bude musu suka fita.
Abuja ba bak'on garin Abdulmajeed bane, a nan yayi samartakanshi,  KFC ya nufa dasu,  Pizza suka ci da kaza, suka sha drink,  kafin tace "Muyi ma su Bhaiyy take away" Abdulmajeed ya daga kai sama yace "da sukaci dadin su sun tuna da ke?" shagwabe fuska tayi tace "haba Jaan" yace "OK Ok" nan ya bada order aka kawo musu cikin wasu lokkutta suka karba suka koma Gida,  har isha'i suna hanya,  suna isa Maitama me makon su shiga gidansu sai suka shiga na Zaid,  Suna Parlo rungume da juna,  suka shiga da Sallama,  Ziyada zata tashi Zaid ya matsota ya girgiza mata kai,  maskewa tayi suka karaso inda suke,  Najwa tace "Bhaiyy,  we bought you Pizza and chicken" Zaid yace "Awwwn Thanks Baby,  mungode though yanzu muka ci dinner,  amma zamuci ko da safe sai muyi microwaving" Abdulmajeed  yace "Kin gani? I told you" Zaid yace "Mallam munce mungode,  dama nasan baby ta saka siyo mana" Ziyada tace "ni wallahi ina jin marmarin pizza" Zaid ya bude baki yace "MyForever yanzu fa kika gama cin Abinci har kina cewa cikinki kamar ya fashe" Ziyaa ta sake gyara kwa ciyarta jikinshi tace "Now i want to eat "Abdulmajeed ya kalli Ziyada yace "Zuzu baki da kunya ko? Kina ganina kin tsaya jikin Mijinki ko? Kina ta shishige mai! " kunya ya bata ta rufe fuskanta cikin k'irjin Zaid tace "YaMaji" Zaid yace "A'a A'a,  ba zaka zo Gidana ka takura min ba,  Baby ja Mijinki ku tafi mungode,  byebye" Najwa ta turo baki tace "Bhaiy niko?" Zaid yace "Baby baki ga zai takura ma Ziyaa ba" Abdulmajeed ya jawo hannunta tare da cewa "muje my forever" Zaid yace "pizxa din fa?" Abdulmajeed be juyo ba yace "je ka siyo mata" da sauri Zaid ya tashi ya sha gabansu da sauri yace "Please big bro,  ka bamu, Zuzun ka fa zataci bani ba" Abdulmajeed ya tabe baki jin yanda ya fadi zuzu kamar wata zazu ya mik'a  mai package din yace"Zuzu ake cewa" Zaid  yayi dariya daga chan Ziyada tace "Goodnight YaMaji and Najwa" Majeed yace "Dont talk to us" daidai k'ofa Zaid yace "sai munzo da safe" Abdulmajeed yace "kar na ganku a gidana" sukayi daria gabaki daya ya ja matarshi suka wuce nasu gidan.

Suna isa Gida Najwa ta fada toilet,  shima dayan dakin ya shiga ya watsa ruwa,  sai gashi ya fito cikin farar jallabiya,  itama Alwala tayi har tayi Sallah,  ya shigo da sallama, sanye ya ganta cikin Night gown doguwar riga Ja,  ta mai kyau,  komai indai nata  ne na mishi kyau, yace "PureHeart,  kinyi sallah?" tace "eh nayi" yace "oya taso mu k'ara wani" ba gardama ta tashi ta matso kusa dashi,  ya tada musu sallah,  rakaa biyu sukayi,  Abdulmajeed ya dade yana musu addua da larabci da kuma hausa,  har suka shafa,  tambayoyin Addini ya fara mata,  nan ya fuskanci Najwa ta na da Karatun K'urani duk da ba hadda ba,  amma tana da rauni wurin Fiqh da sauran litattafai,  though dai ta karanto mai yanda akw wanka haila,  ta kuma san cewa duk wanka iri daya ne,  niyya kawai ya bambanta,  gyara ya mata akan tambayoyin da bata san amsarsu ba, ya kuma ce mata kar taji kunya yana tare da ita, ta tambayeshi duk abunda ya shige mata duhu,  kuma kafin lokacin da zata zana WAEC zai shigar da ita wani Islamiyyan Matan Aure wanda akeyi Lahadi zuwa Laraba da safe 9-1, in lokacin shiga Makaranta yayi sai ta dawo na yamma ko asabar da lahadi,  Godia ta mai ya dagota suka  mike kan kafaffunsu,  zuwa makunni fitila ya nufa ya kashe wutan Ya jata zuwa kan Gado.
*Asuba ta gari Pure-Jaan*

*A GURGUJE *

Cikin Kwanaki 21, Masoya hudun nan sun k'ara kyau sun girgije,  har wani k'ibak'iba sukayi,  k'auna ce suke ginawa a gidajen su mai tsafta,  zumuncinsu ya dore,  kaunar junansu suke,  Ziyada ta koma Makaranta,  kamar yanda Abdulmajeed ya ma Matarshi Alkawari hakan ko akayi,  ya sakata a Fallahil Islam dake nan k'asan Maitama,  kullum shi ke kaita,  ko yana aiki sai ya yanke ya je ya daukota,  ya kumayi enrolling dinta a wani Catering School wanda zata dinga yi Online.
In suna Gida ko Najwa ta shjga Gidan Zaid,  ko Ziyada ta shigo Gidan Abdulmajeed.
Yau ma hakan ne, Najwa ta shigo Gidan Abdulmajeed, wanda cikin Ziyada ya dan fara turowa, ta  ciko ta kara k'iba, Ziyada tace "Muje baya muyi hoto" Najwa tayi daria tace "su kuma masu ciki har craving din hoto suke?" turo baki tayi tace "wai ba MyForever yace ki dinga min abunda nake so ba?" Najwa tayi daria ta daga hanuwanta sama tace "Sorry Matan Bhaiy,  muje muyi hoto" Ziyada ta mike ta ja hannun Najwa suka fita daga Gidan tace "backyard zamuyi" "duk yanda kikeso Hajiata" Ziyada ta kwalawa Mai aikitan kira tace "H-Jiddarh, zo ki mana hoto" jiki na bari H-Jiddar tazo ta karbi wayan ta shiga daukansu".

Suna gama Hotuna kuma suka bige da Video Call da Zaineema.

K A N O

Zaman Lafia ake a Gidan Daddy,  sun hade kansu suna kyautatawa Mijinsu da  Surikarsu,  ko waccen su tsakanin Mummy da Aunty Aynarh burin kyautata ma Hajjo suke,  tana jin dadinsu.
Mummy ta shiryu,  ba ruwanta da kawayen banza amma kunsan wata sain me hali baya barin halinshi,  takan nuna isanta gun kawaye don ta keta su fiye da tunaninsu,  amma baya ganan bata da matsala.
Daddy kuwa ya narka wata k'iba,  hutu da kwanciyar hankali ya darsu mai a cikin zuciya,  zumuncinsu da danuwanshi Sada sai abunda yayi Gaba.

A Gidan Paapa Zaid ya wadatar musu da komai,  duk asuba sai tayi waya da Yaranta da Surikanta,  bata da kadaici don akwai masu Aiki,  da wata babbar mata haka,  sannan diyar Yayanta Umaimah da take rik'o yar shekara 6, Allah yayi ma Umaimah farinjini don tun tana jinjira mahaifiyarta ta rasu,  kowa na sonta ,  yarinyar na da farinjini sosai,  one of  the best schools a Kano aka sata,  so Ko kadan Maama bata da kadaici.

Ana Azumi na saura Kwana Goma suka tarkato sukazo Kano don gabaki daya zasu tafi Umrah suyi Azumi Ashirin A chan,  Gabaki dayansu a Gidan Daddy suka sauka, nan aka yi ta murna da zuwansu,  Hajjo ta dinga dirka ma Ziyada Kayan kwadayi,  su Zogale da kwadan rama da sauransu.  Ana jibi Azumi jirginsu ya tashi zuwa Madinatul Munawwarah,  Daddy,  Paapa,  Hajjo, Mummy,  Maama, Aunty Aynarh,  Abdulmajeed, Zaid, Ziyada, Najwa, Zinatu,  Muhsin da Umaimah..

A chan suka ci rabi da kwatan Azumi kafin suka dawo,  a Kano sukayi Sallah.  Kafin suka koma Abuja.
Ba jimawa Najwa tayi WAEC,  ba da dadewa ba sakamako ya fito da kya, Makarantan su Ziyada aka nema mata,  bayan wasu lokutta ta fara classes a kan course din da ta zaba .

*MONTHS LATER(Bayan wasu 'yan watanni)*
      
K A N O

Maama zaune suna fira da Mummy, Mummy tace "wai ni Hajia Aleeya tazo neman taimako gurina?" Maama tace "Rayuwa, kin taimaka mata ko?" tace"Waaa?  Ni, ai wallahi koran kare na mata,  na kuma nace ma maigadi in ya sake ya barta ta sake shigo min Gida A bakin aikinshi" Maama tayi daria tace "Allah ya huci zuciyan uwar gatan marayu" Mairo na karkada kafa tace "Wallahi irinsu Hajia Aleeya ke kai mutum ga halaka,  Allah ka nissantar damu daga sharrin irin kawayen banzan nan" Maama tace "Ameen Ameen" Aunty Aynarh ta turo kofan Parlorn da Sallama, tana yatsina Maama tace "Ahhh,  ga Maman Biyu" Dan dariya tayi ta shigo ta samu wuri ta zauna tace "Maaman Umaimah bansan kin shigo ba" tace "ban dade ba,  yanzu zan shiga da mu gaisa" Aunty Aynarh tayi dan guntun tsaki, tace "Nidai Wallahi sam bansan warin Part dina,  zuciyana tashi yake" Mairo tace "ai kece bakya jin magana,  sai da nace miki ki dawo part dina,  kin k'i" tace "ai gashi na dawo, in ma na ga nan din nogo,  Kwara zan tafi,  wallahi ba zan iya ba" Mummy tace "nima na biki wallahi,  dan ba zaki barni nikadai ba" Maama tace "Ya zakuyi da Yaya fa?" Aunty Aynarh tace "yo ga matarshi" Mummy tace "Haba dai,  ai wallahi kina tafia, zan biki,  nima ban ina son zuwa Kwara" Maama tace "Sai ku dawo ku iske Yaya har ya auro mata Biyu, daya part dinki,  daya dayan" Daria suka fashe,  "ai ba ya fara ba" Maama tace "uhm uhm dai" suka sa daria.

K A D U N A

Suprise suka mata,  sai dai ganinsu tayi sunyi diran Mikiya,  Ihu ta sa ta hau rungumesu,  Najwa tace Didi ashe kema kinyi nauyi" hararrasu tayi tace "kema cikin gareki" tace "wallahi banda komai" tace "ahap mu dai zuwa" sukayi daria,  nan Abdulmajeed da Zaid suka shigo Khalid na musu Jagora,  Zaineema ina zata sakasu don jin dadi,  yanuwanta sun kawo mata ziyara,  dadi kamar ya shideta.
Abdulmajeed yace "Khalid,  are you busy?" Khalid yace "Haba Aa why? " Zaid yace "Aron Lokacinku zaku bamu kai da matarka" Khalid yayi zaton wani abu ya faru ya tattaro hankalinshi yace "ina fatan lafia" Zaineema taji gabanta ya fadi,  Abdulmajeed yace "Relax kuzo muje" ya mik'e ya tashi,  duk suma suka m'ike,  suka fita, suka shiga Mota,  Driver yaja, mota uku sukayi,  Zaineema    sai dai ta kalli Khalid shima ya kalleta suna son k'arin bayani.

Wurin wani K'atoton Mall suka yi Parking me dauke da *ZEEMA SUPERMARKET AND BEAUTY SPA SALON* suka firfito,  suna tunanin me suke a wurin,  wannan k'aton ginin, su kan wuce wurin ita da Khalid tunda hanyansu ne,  kuma ta na ganin wurin da ba a dade da fara gina shi ba,  tace "Dee,  dube ginin nan,  wai har an gama kamar an ma fara aiki a ciki" Khalid yace "Ahap,  ai na ce miki daga gani wani Maikudin ke gina wurin" ya kalli su Zaid yace "wurin fa ko two weeks baayi ba muka ga an fara ginashi, wai har an gama" Zaid ya kalli Abdul suka ma juna murmushi, ko Najwa sai dai ta kalli Ziyada duk basu san meye ba,  Zaid ya kama hannun Ziyada da tayi nauyi sosai haihuwa yau ko gobe,  ya kalle su yace "to mu shiga ko?" Zaineema tacw "Allah Sarki,  shopping ku ka kawoni, aikam wallahi Dee yau zanyi ma babyna siyayya" Abdulmajeed yace "Its Yours" ta dan kkalleshi bata gane me yake nufi ba tace "What?" Zaid yace "Naki ne Sister" ta kalli Abdulmajeed ta kalli Zaid tace "Wai mene?" Abdulmajeed ya nuna duka ginin yace "All of it Sis,  its yours,  kece mamallakiyan Zeema Supermarket,  allofi it" Waiyo Allah dadi yasa Zaineema hawaye,  ta kalli Mijinta shima farincikin yake tayata,  me zatayi?  Bata sani ba,  dadi ji take kamar ta fara nakuda yanzu,  ta kalli Zaid tace "Me zan ce muku?" Zaid ya nuna Abdulmajeed yace "It was all him, Filinshi ne,  shi ya zana, ya sa a ka gina" Abdulmajeed  yace "Kayan cikin kuma Zaid ya sa akayi ordering dinshi daga Dubai,  da kayan cikin da Maaikatan cikin duk Zaid ne" Hawaye take na farinciki, su Ziyada suka rungumeta suna tayata murna,  Khalid ya musu godia Zaid yace "Haba Maikudi,  don munyi ma kanwarmu kyauta sai kace zaka gode mana" Khalid yace "dole kam, farincikin Zaineenah,  nawa ne,  mungode Allah ya kara  girma" suka amsa da Ameen,  Zaineema kasa daurewa tayi saida ta rungume Abdulmajeed.
Nan suka shiga ciki aka nuna musu ko ina da ko ina,  kuma akayi  introducing maaikata wurin Mai wurin wato Zaineema Abba Abu..

A ranar suka koma Abuja,  kamar jira ake,  da daddare Ziyada tafara Nak'uda,  Zaid ya kira Abdulmajeed a waya,  don shi ya tsorata sosai,  Najwa ya tada da ta fara bacci, a rude suka fito suka nufa Gidan Zaid,  sun iskeshi yana waya da Maama inda tace su kaita asibiti,  zata turo musu adduar nakuda a karanta a bata cikin ruwa tasha,  tsam Zaid ya dauke Ziyada ya fita da ita,  Abdulmajeed ya dauko ruwa a cup ya tofa adduar da mama ta mai texting, daidai bakin ziyada ya kafa kofin,  ta sha dukda tana cikin wahala,  wani Private Hospital a ka kai Ziyada,  cikim ikon Allah ta suntulo yaronta Namiji.

Bayan an kimtsata aka maidata daki, Zaid suka shiga, hannu na rawa ya karba babyn, dagowa yayi ya kallo Abdulmajeed suka sakar ma Juna murmushi Abdulmajeed yace "Ka kira mishi Adhan(Kiran Sallah) ka mishi huduba" wani farinciki Zaid keji da ya rungume danshi a k'irjinshi, yana sonshi da duk wata numfashin da yake, ya dago dan wurin fuskarshi ya mai kiran Sallah, ya mai huduba, ya dago Abdulmajeed yace "let us guess, ka maida sunan Gatan Marayu ko?" Zaid ya Jinjina kai yace *"SADAM ZAID SADAM"* suka hada baki wurin cewa Allah ya rayashi, nan suka karbeshi, Ziyada kuwa ta samu bacci.
A cikin daren labarin Haihuwan Ziyada ya zagaya Yanuwa da Dangi.
WasheGari kam suka fara ganin yan Barka, Zaineema ta ruga Yan Kano suka isowa.
A ko wani Headline na News da Internet sanarwan samun k'aruwan Gatan Marayu ne....

Bayan wasu Watanni.
Zaineema ta haifi Yanbiyu, Hassanar taci sunan Uwar Khalid wato Aisha duk da ita Zaineeman nacewa ita Maamanta tama takwara asalin sunanta kenan, Hussainar kuma taci sunan Mummy wato Maryam saidai muce Allah ya sa kar tayi halin Grandmoza.

Ba da jimawa Aunty Aynarh ta haifi diyarta Mace, inda taci sunan Hajjo wato Hajara, Randa Aunty Aynarh ta haihu, kuka take wiwi don bata taba haihuwa ba, ko don bata taba kwantar da hankalinta tayi zaman aure ba? Aa rabo ajali, Allah yayi a Gidan Alhaji Abba zata haihu.
**
Shekara Kwana
Sadam na da Shekara 1 da rabi Allah ya Azzurta Najwa da samun diya Mace, ranar suna yarinya taci sunan Maamansu wato Aishatu Yesmin.

Bayan wasu Watannin da basu kai Shekara ba.
Hutu suka samu Abdulmajeed da Zaid suka yanke hukuncin zuwa Paris yawon bude ido da Iyalansu.
Ayshatu Yesmin ta fara rarrafe, Sadam kuwa ya zama bigboy, yana magana ya na da farin jini, yaron kowa yaganshi sai ya dauka, a wurin da sukaje shakatawa wuri kamar Park, Sadam ya faki ido ya k'ara gabanshi, wata Mata ta daukeshi tace "Hello Boy, whats your name?" yace "Sadam Zaid Sadam" matar ta zaro ido tace "Wheres your Daddy?" da yake beyi nisa dasu ba, da hannu ya nuna mata inda Su Daddynshi ke zaune, da sauri ta karasa gunsu Sadam na dauke a hannunta, sallama ta musu, Zaid ya mik'e yace "Na'ilah" ta murmusa tace "Ina wuninku" Najwa ta ganeta, Abdulmajeed ya amsa gaisuwan, ta kalli Ziyada tace "baku ganeni ba ko?" Abdulmajeed yace "kanwar Nura Kurma" sukayi daria, tace "Well, ashe zaku ganeni" karban Ayshatu Yesmin tayi daga hannun Ziyada tace "Wow, Allah ya sa Alheri" Zaid dauke da expression na tausayi, yasan Naeela na sonshi, ya san har yanzu tana sonshi yace"Naeela, how have you been?" ta dan murmusa tace "Good, i can see you are good also" ya gyada mata kai yace "Are you?" tace "Married? No banyi aure ba, amma zanyi dana koma Nigeria next month" Zaid ya saukar da ajiyam zuciya da yaji zatayi aure yace" Allah ya sa Alheri, kar ki manta ki gayyaceni in lokaci yayi tace "InshaAllah" ta kalli Ziyada tace "Your son is very brave, tell him about his Aunt Na'ilah in ya girma" murmushi Ziyada ta mata tace "InshaAllah" Sallama ta musu ta juya ta tafi.

Zaid duk yayi wani iri, be son Naeela, be taba sonta ba, amma yaji tausayinta, ya san ta so shi, jikinshi yayi sanyi ya kalli Najwa da ke zaune, yace "Baby je kamo Sadam kafin ya kara gaba" ta tashi ta chapkoshi, Ziyada ta lura da Zaid, ko kadan bata so taga ya shiga damu tayi tunanin sashi daria Mikewa tayi ta isa inda yake zaune, ta dagoshi, tace "kaga dai my Forever ka bar cema Matar YaMaji Baby, tun ina kauda kai, ina kawaici, kai baka gani ko? Har yanzu baka fasa ce mata Baby ba ko?" murmushi ya sakar mata yace"Ita fa yar baby ce in ba kya so sai a ce mata yarinya, ke kuma kece Babe, the one and only one Babe, My Forever, My Pure Heart" Abdulmajeed ya tashi da sauri hannunshi rike da Ayshatu Yesmin yace "No, No, ka kira matarka da ko wane suna banda PureHeart, i'm the originator of that name, nikuma kadai ke da lasisin amfani da sunan" Zaid ya dago kai yace "ko dadi ma, MyForever, an bar cema wata Baby, yarinya zaa dina ce mata, you are my one and only one Babe, and i love you".

Najwa tace "Meri Jaan, sharesu, their jealous of us, Tumase pyar kharta hoon" Zaid yace "oho dai bamu san me kikace ba, Abdulmajeed yace "wanda ta fada dominshi ya sani, au tumase bahoot pyar kharta hoon PureHeart"..

Armstrong da ke tsaye yana kallonsu yace "Group Picture?" Zaid yace "Oh Yes Arm" ya karbe Ayshatu Yesmin daga hannun Abdulmajeed yace "Zo nan Mamana"Abdulmajeed ya dauki Sadam, tare da rungumo Najwa ta gefe, itama Ziyada ta rankwafo wurin Zaid, Arm ya dinga daukansu Hotuna.

Bayan Shekara Uku

SADAM AUDU MEMORIAL ORPHANAGE HOUSE KADUNA
Walima Uku akeyi a SAMOH, na daya Walimar saukar Kurannin wasu daga cikin yan gidan Marayun SAMOH, na biyu kuma Walimar aurar da Mata 50 da Maza 50 da akayi wanda aka Gina Compound Houses guda 20, wanda Abdulmajeed yayi , inda Maauratan zasu zauna. Na uku kuma Walimar Karamma da Award of excellence da aka ba Gatan Marayu na Biyu wanda Gwamntin k'asa ta bashi.
Taron ya kunshi Manyan mutane daga sassa daban daban, wanda suka zo karamma Gatan Marayu na biyu, Alhaji Zaid farinciki ne lullube a fuskanshi, Mahaifanshi duk sun hallara, yanuwa da abokan Arziki duk sun zo tayashi murna.
Jawabin minti 45 Zaid yayi akan marayu, da wanda ake yaddasu don an samesu ta wata hanya, daga karshe ya rufe taro da ba wa mutane shawara kan Marayu, su tainakesu, su kuma jasu a Jiki don su ma 'Ya'yane..
Kabbara kawai kakeji inda manya da yara ke fadin "ALLAH YA JI K'AN GATAN MARAYU NA FARKO. YA JA KWANAN GATAN MARAYU NA BIYU, YA RAYA GATAN MARAYU NA UKU" haka sukayi ta maimaitawa kamar wak'a. Har taro ya watse kowa na ta sambarka.
***
Washegari Yan Kano suka koma Kano, Abdulmajeed da Iyalanshi suka koma Abuja inda Najwa na aji na k'arshe a matakin jami'a.
Abdulmajeed ya zama wani babba wanda ake damawa dashi a kasa gabaki daya, duk wani kwangila da ya kunshi Ginegine ko wani abu makamancin haka shi keyi, duk shekara sai ya kai Mahaifanshi Hajji don sauke farali, in akace Mahaifa ana nufin dukansu Biyar,
Ko da zaayi taron nan Abdulmajeed ya ba Zaid gudunmuwar miliyan Goma, ba wai don Zaid din baya dashi ba, aa don shima yana kwadayin ladan, sai dai muce Allah ya bada lada Yayan Gatan Marayu.

A kaduna a ka bar Zaid da iyalanshi, sun dawo Nan Main House din Marigayi Alhaji Sadam da ke Mando, Gidan da babanshi ya fara kawoshi kafin yasa suka koma PH, inda zasu dan kwana biyu, saboda ta gama University, , a cewarshi yana son yaronshi ya girma a nan, ya nuna mishi legacy din Marigayi kakanshi.

Wurin karfe 5, Sadam na bacci a dakinshi, Zaid ya shigo cikin shiga irin ta leburori masu aikin gidan zuwa dakin Ziyada kamar mara gaskia, zatayi magana ya sa mata hannu a baki alamun tayi shiru, a hankali yake magana "kin taba hawa Kekenapep?" ta gyada kai alamun eh, yace "kina so ki kara hawa?" ta daga kai sama, yace "badda kama zanyi, sabida yau nayi mafarkin na hau keke napep, and ina so mafarkina ya zama gaskia, for once in my life, ina so in fita ba tare da an bini ba" itama a hankali tace "ta ya zaka fita, kasan Faisal ya sa tight security" tsaki yayi yace "zo muje" faken idanuwa sukayi suka bi dakin masu aiki dake baya, Hijab din H-Jidda ta gani a saman igiya, ta daura da zanin jgonees itama ta bada kama, sukayi kama da masu aiki, yayi gaba tana binshi a baya, kansu a k'asa don kar a ganesu, har ta gaban Faisal suka wuce yana waya, har sun kusa gate hankalin Faisal ya isa kan wani me tafiyan Oganshi, ya dan latse wayar ya fara dan binsu a baya yace "kai, waye nan ku tsaya, kai ke ku tsaya" Zaid na jin haka ya kamo hannun Ziyada ya jata da gudu, Faisal na ganin haka ya zaro ido yace "Oga ne, kar ku barshi a fita close the Gates" Zaid na gudu hannunshi rike da na ziyada yace "in baka bude min ba ka bar aiki a gidan nan" Maigadi na jin haka ya wangale Gate, Zaid da Ziyada suka fita suna Daria da gudu, Faisal na binsu a baya don kar ya rasu wasu securities kuma suka bi bayansu a Mota.
Gudu suke sosai, Ziyada ta gaji ta fara haki ta ci burki tace "wallahi na gaji, sai kace barayi" a haka Faisal suka tarar dasu yace "Haba Oga, ina zaka haka? Look at how you are dressed" Zaid yayi tsaki, ya kawar da kai gefe, Ziyada tace "Keke Napep wai yake son hawa" Faisal yace "shine ka bamu wahala?" ya karasa bakin Titi ya tsaida Keke Napep, yace "Oya ku shiga" Zaid da Ziyada suka shiga, Faisal yace da Me Napep "Mu zagaya Kaduna" Me Napep ya ja Napep dinshi, Faisal suka bi bayansu a Mota.
Ziyada ta lek'a tace "Suna binmu" Zaid yayi daria yace "duk kece kikaja aka kama mu, da ni kadai ne da basu kamani ba" Ziyada tace "Hello Mr, kaima fa ka gaji, ji nayi kana nishi samasama kamar zaka shide, saboda kar a kamani nayi sneaking da Gatan Marayu shiyasa na tsaya" rungumota yayi yace "Wa ya isa ya kamaki? Kin uwar marayu" Mai Napep ya kallesu ta mirror a baiyane yace "Allahu Akbar, yau gani ga Gatan Marayu, Kakata ta yanke saa" Zaid da Ziyada suka sa Daria.

*ALHAMDULILAH TAMMAT BI HAMDULLAH*

Alhamdulilah Alhamdulilah Alhamdulilah
Allah kuskuren da nayi a cikin wannan rubutun nawa Allah ka yafe min, na tuba, Allah ka sa ayi amfani da abubuwan dake daidai a labarin nan, wanda nayi kure Allah ka bamu ikon wasti dashi.

*DonAllah Don Girmansa Kar ayi min Document din wannan labari, hakkina ne, duk wanda yayi ana iya mana hukunci dashi ranar gobe k'iyama, donAllah a kiyayye*

*Kamar sunan Novel din nan A DADE ANA YI, AN KO DADE ANA YI, AMMA KUN HAKURI, HAR DAI HUTU AKA JE AMMA KUNA TARE DANI, RASHIN UPDATE DA WURI, YI MIN UZURIN DA KUKE YI, ba abunda zance muku illah Nagode Nagode*

*ZAUREN BIEBEE ISA, KU SANI I LOVE EACH AND EVERY SINGLE ONE OF YOU WITH EVERY FIBRE OF MY BEING, BIEBEE BA KOWA BACE IN BA KU* *A BIG SHOUTOUT TO ZBI ADMINS#1love*

*Lubna Sufyan, Aynarh Dimples, My Muskeeteers, kunsan sai hali yazo daya ake abota ai? Yeah right we are of the same feathers and we flock together, these two are my people, like you dont know me if you dont know they are my ROD, ILYSVM.*

*WATTPADIANS, MY DIEHARDFREAKINGFANS EVER SINCE DAY ONE, THANKYOU FOR TAKING YOUR TIME TO VOTE AND COMMENT ON EVERY SINGLE LINE, I APPRECIATE EACH AND EVERY SINGLE ONE OF YOU, AND ILOVE Y'LLS*

*Bibiliciousfreakingfans a duk inda kuke Wallahi banda abunda zance muku illa na rok'i Allah Allah ya hada mu a gidan Aljanna Firdausi Ameen*.

ALLAH YA HADAMU DA DUKKAN ALHERINSA (Amin )

#1love
#ADAY
#Bibiliciousfreakingfans
#anatare
#bissalam
#nagode

Biebee Isa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.