Complete Hausa Novels

Arman Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Arman_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 3 of 4

Page 3.

A hankali ya miƙe, tare da daura baƙar Alƙyabba mai dan saukin nauyi a jikinshi, tare da ƙara gyara Rawanin kanshi, sai yy fito A Ahmad Sudeis sak.

cikin Kamala da natsuwa yake tafiya, yaba ta ƙara baza kamshin turarem Huge boss da, ya kama mishi jiki sosai dan har ko bai sa ba, to zaki ji kamshi a jikinshi.

yana Zikirin maraice ya fito daga bedroom din, zuwa palo, kasantuwar yana da Alwala yasa bai tsaya yin wata ba, ya nufi hanyar fita, a ƙafarshi yy shiga tattaki zuwa Masallacin da yake faron Masarautar in da anan kowa dan cikin Ahlin masarautar yake gabatar da Sallarshi.

yana tafe yana zikirinshi, har ya ƙarasa Masallacin, gaba daya Jama'ar da suke bakin Masallacin suka miƙe, tare da fara mimmiƙa mishi hannu, suna gaiswa, wani ɗan tsoho ne yace "Yah Shehin Malamin mu ka guji Ƙasarmu , bayan lokaci mai dan tsawo da ka bar nan sai a cikin Talabijin muke ganin ka, fatan dai komai lafiya?, Ya Mai martaba Abdul-azeez Arman Maleeq Sarki da jiki?", ya fada yana dunƙule hannayeshin.

karo na farko da tunda ya shigo cikin Masarautar da yy amfani da tattausar murya mai dadin Sauraro yy tsohon magana a hankali cikin rashin son maganarshi, ganin lokacin Sallah na shigewa Yasa ya nufi cikin Masallaci duk mara mishi baya suka yi suna Addu'ar Samun Sauƙin wa Abdul-azeez Arman Maleeq Sarki
, gurin Liman ya tsaya tare da kabbara Sallah cikin zazzaƙar muryarshi, gaba daya garin sai yy tsitttttt ana saurarar sautin karatunshi.

Masallacin kuwa kowa ya natsu, zukatansu gaba daya sun narke da jin Muryarshi da suka dauki tsawon wattanni basu ji ba, haka har Aka ƙarasa Sallah, gyara zamanshi yy, tare da nannade ƙafafunshi ya juya gurin dubban jama'ar gurin, wanda bb wanda ya fita duk suna zaune, suna jiran karatunsa.

Manyan Littatafan Addini ya dauka, dauka tare da fara koyae da su, cikin harshen fulatanci in yy da hausa yy da fulatanci yy da turanci, dan kusan rabin mutansn basa jin hausa, wasu kuma basu ciks fahimtar fulataccin ba, kasantuwar garin ya haɗa ƙabila biyu, hausa da fulani.

har lokacin Isha yy yana zaune yana koyar da su, sai da A kayi Sallar Isha kafin ya mike zuwa cikin gida, bakinshi yana ambaton sunan Allah,haka ya ratsa dukkan parts din da suke gidan har ya isa nashi part din,yana shiga ya zauna a palo tare da lumshe idanunshi, da suke dauke da tsananin gajiya , da barci.

bai fi 10minutes da zama ba, aka turo ƙofar Pallon, bai ɗago da idanunshi ba har wanda ya shigo ya iso tsakiyar palon, bb ko Sallama haka ta tsaya mishi a ka, a hankali ya fara bude idanunshi har ya saukesu akan Jadda da take tsaye.

mayar da idanunshi yy ya rufe, san dama yasan wani kayan sai Amale, cikin zazzaƙar muryarshi yace "ke baki iya Sallama ba ?, ko ke Arniya ce ?", ya fada cikin rashin damuwar cewae Ita Jaddar Babbar mace ce dan A kalla zata iya yin 95 a shekaru,sai dai yarda ta zubar da girmanta, sa boda yar da take babbar da batasan girmanta ba, ta tsaneshi bata son shi, bata kaunar Mahaifinshi da Mahaifiyarshi Da Yan uwanshi kullum neman abun da zai cutar da su take nema.

wani kallo ta mishi tare da cewa "ai kasan ni dangin Maimoon ne Uwarka sune basa Sallah dan Ubanka", ta fada cikin harzuƙa...

taɓe bakinshi yy bai ce mata komai ba, ita kuwa haushin rashin kulatan da yy yasa ta fice a faɗace tana zazzaga mishi zagi, sai da ta bar gurin kafin ya miƙe, ya nufi hanyar Upstairs dinshi, yana zuwa ya tura ƙofar ya shiga, bai zauna a na dayan ba sai ya shige chan na biyun, bathroom ya shiga yy wanka tare da dauro Alwala ya fito, Shafa'i da Wuturi yy, yy Addu'o'i da karatun Al-qur'ani, kusan 11pm yana karatub cikin muryarshi mai dadi kafin ya miƙe daga in da yake.

gefen bed ya zauna, tare da dan daura hannunshi akan cikinshi, ya lumshe idanunshu, fuskarshi ya dan yamutsa tare da dan shagwaɓeta, kaɗan irin na Shagwaɓaɓɓun da in suka samu wuri to zasu zuba shagwaɓa, a hankali ya miƙe ya nufi fridge din da ke kusa da bed din.

budewa yy , tare da fitar da peak milk mai sanyi sosai, tare da wata gorar zuma mai kyau, cup ya dauka ya daurayo, ya dawo tsakiyar carpet din da yake walale bakin bed din shi,zuba madarar yy ya sanya zuɓa, tare da sanya Spoon ya fara jujjuyawa sai da ya tabbatar ya haɗe jikinshi.

kafin ya dauka da Bissimillah..!, dauke a bakinshi ya kafa kanshi, sai da ya shanye tasss kafin ya ajiye cup din, sanyayyiyar gyatsa ya saki tare da lumshe idanunshi.

gefe ya mayar da cup din da gwangwanin ya, matsa ya jingina kanshi da jikin bed din yy shiru, idanunshi a lumshe kamar msi barci, a zahirin gaskiya kuwa ba barcin yake ba,tunanin rayuwa kawai yake..

A hankali guraren 1 ya miƙe daga zaunan da yake, ya nufi bathroom, alwala ya ƙara daurowa, yana fitowa ya sanya wata lafiyayyiyar Dubai Jallabiya mai masifar kyau black da tayi asalin fito jishi da tsantsae farin fatarshi.

gurin pray met dinshi ya matsa, tare da kabbara Sallah, cikin zazzaƙar muryarshi ya ringa rairo karatun Al-qur'ani, har guraren 4 sai da aka fara kiran Sallah Subhi kafin, ya tsagaita ya koma gefe yana karatu da Tasbihi 4:30am ya miƙe , Sabon Wanka da Alwala yy, tare da chanja kaya, ya nufo hanyar waje.

Shi daya ya fara takawa daga cikin Masarautar zuwa Masallaci , a hankali yake tafiya, bakinshi kuma har lokacin bai gushe da ambaton sunayen Allah ba da Addu'o'i tare da Tasbhi , haka har ya fita daga part dinshi, ya fara ratsawa ta cikin masarautar da bb kowa, bb motsin kowa, sai sanyayyiyar Iska Asuba da take kaɗawa, wadda take dauke da ni'imomi da wani yalwataccen nishaɗi, iska ce mai sanyaya zuciya, da sanya ruhi cikin natsuwa, iska ce mai dauke da iskar hadari wanda ya gangamu garin yy baƙiƙƙirin kamar za'a kece da ruwa.

haka yake tafiya cikin rashin tsoro, har ya ƙarasa Masallacin da bb kowa a ciki, A hankali ya ƙarasa cikin Masallacin, sai da ya dudduba komai kafin ya fito, tsayawa yy daga dan gaba cikin rumfar Masallacin, ya kauɗa kiran Sallah cikin sanyayyiyar muryarshi mai dadin gaske.

wadda tayi sanadiyar tashin kusan dukkan Al-ummar Masarautar tashi daga barcin da suke yi, gaba dayansu zuciyarsu tayi wani irin taushi jikimsu duk ya saki, kwaÉ—a kiran Sallarshi na biyu ne yy Sanadiyar tashin duk wani mai gigga-giggan masu Jinnun da suke cikin Masarautar, dan dama aje ne, duk lokacin da zai sauka masarautar, yy kiran Sallah to , duk wani mai gigga-giggan Aljannu da suke cikin Masarautar sun tashi.

cikin Azama gaba daya Ahlin Masarautar maza gaba dayansu suka yo Masallaci domin gabatar da Sallah Subhi , kafin kace Kwabo Masallacin da bb kowa ya cika damkam da Mutane, wanda cikarsu ma har tayi yawa, hakan zai shaida maka ba mutane ne kawai ba, cikin NishaÉ—in da ya tsinci zuciyarshi a cikinshi, ya fara karatuh Al-qur'ani cikin Surarul Maryam, wanda gaba daya dadin Surar da Daddin Muryarsa yasa illahirin Aljannu , Mutane , Dabbobin da suke cikin gidan suka yi tsiiiittttt suna saurararshi, hatta da iskar Hadarin da take kadawa da karfi sai ta daina kaÉ—awa da karfin, sai sanyayyyiyae iska da take ratsa ko ina, har sai da ya idar da Sallah, gaba daya wata iriyar iska mai karfi ta fara kaÉ—awa.

kan kace wani abu ruwa ya fara dan sauka a hankali, duk da haka sai da yy musu karatu sosai kafin a tashi, shine last din fita daga Massalacin sai da ya rufe kafin, ya fara tafiya cikin natsuwa .

lokacin 6am tayi, a hankali yake tafiya yana sauke numfashi, sai da ya kusan shiga cikin part dinshi, kafin ruwan ya fara sauka sosai kamar da bakin kwarya, har sai da yasa Shehi ya dan kara takun tafiyarshi da yake yi, duk kuma da haka cikin natsuwa yake tafiya,har ya ƙarasa.

palon ƙasa ya zauna, yana zama wata Babbar mace da zata iya kai wa 60years fara ta fito daga wata hanya fuskarta washe da murmushi, cikin dan farin cikin da ya mamaye gaba daya fuskarta da zuciyarta tace "Assalamu alaika...!",a hankali ya bude idanunshi,jin muryar da ta daki dodon kunnenshi.

wani murmushi da ya kusa kasheni ya sakar mata, kafin ta mayar da kamilalliyae fuskarshi kamar yarda take yace "Wa'alaikissalama...!", ya fada cikin sanyayyiyar muryarshi, idanunshi yy ƙasa da su kafin ya dan murya zoben Zinarin da yake cikin hannunshi da yake fitar da wani kyalli na musamman.

cikin bada girma da rissinawa, tace "Barka da Asuba Shehi..!", a hankali ya furta "Uhmmm Coffee..!", ya fada a hankali ba tare da yace komai ba , miƙewa tayi tare da cewa "bari na haɗa maka" tana fada ta bar gurin shi kuwa ya lumshe idanunshi.

bata dauki wani lokaci mai yawa ba ya dawo hannunta daure da ƙaramin tray mai dauke da wani flask ƙarami, da cups da tea spoon sai sugar, dan tasan zalla ake haɗs mishi shi yake aa sugar da kanshi.

Stool ta jawo ta ajiye gabanshi, kafin ta dan rusunar da kanta tace "Shehi an gama", tana fada ta matsa chan ta zauna, kan kujera ta zauna, tana dan kallonshi,shi kuwa a hankali ya bude idanunshi, tare da dan rankwafawa, ya dauki cup din ya dan tsiyayi rabin cup ya zuba Sugar tea spoon huÉ—u, tare da fara dan gaurayaww har ta narke, kafin ya matsa gefe, da Bissimillah ya fara dan sipping dinshi har ya shanye tass, ya ajiye cup din.

A hankali ya dan kalleta da idanunshu, yace "Ngd ..."', ya fada yana dan mayar da kanshi akan kujerar, jinjina kai tayi ba tare da tayi magana ba.

Dan Jim sai ga wanu kyakyawan matashin Sarauyi ya shigo cikin palon, cikin dan murmushi yace ''Barka da safiya Shehi . barka da safiya Umma Jakadiya", murmushi tayi tare da cewa "barka Zayn-Maleek . fatan kun sauka lpy ?", dan shiru yy tare da cewa "Qlau Umma", jinjina kanta tayi.

kallon Shehi Arman_Maleeq , Zayn-Maleeq yy tare da cewa "Yaa Shehi komai fa ya gama kammala. kayan suna wajen Masarauta zuwa Anjima za'a shigo da su." shiru Arman_Maleeq yy bai cewa Zayn_Maleeq komai ba...

daga karshe ma miƙewa yy ya haye sama, duk binshi da kallo suka yi, kafin Zayn_maleeq ya koma inda ya tashi, tare fara haɗa Coffee sai da ya gama ya kallin Umma Jakadiya yace "Umma An jima Shehi zai raba kayan Azumi, dan wannan karon ba zamu jima ba zamu koma,na ji kuma kamar Ammie tace a taho da ke ", ya fada yana surɓar Coffeen, murmushu tayi tare da cewa "Zayn_Maleeq baki abin magana, Allah ya kai mu, " dariya yy tare da cewa "Su Umma za'a hau jirgi a tafi Madina", dariya itama tayi cikin sabo da irin rahar Zayn_maleeq tace "Oh Zayn_maleeq baka gajiya. abin da ba zuwana na farko bane wannan, bari na tashu na shige", ta fada tana miƙewa..

******

Gaba daya kusan Drs Biyar ne a kanta bayan Nurses dukkansu sun rufa a kanta, suna dubata, dan gaba daya numfashinta daukewa yy , yana sama da ƙasa, sai shasheƙa take, gaba daya jijiyoyin jikinta sun fito, jikinta ya dauki wani rawa.

Gaba daya Drs din su fara sarewa da lamarin Yarinyar, cikin lokaci dan kaÉ—an zata birkice , sai kuma jikin ya dai-daita, yanzu ne abun ya fi ko yaushe gaba daya, ta birkice sun kasa yarda zasuyi da ita.

Dr Aslam wanda ya fara daukarta , ya fito yana sharce zufa idanunshi sunyi jaaazir, hatta kayan jikinshi sun jiƙe da zufa, Office dinshi ya shiga, ya zauna ya dafe kanshi...

sai kuma ya É—ago kan tare, da daukar wayarshi. lallatsawa ya shiga yi kafin ya karata a kunnenshi.

sautin ring din Wayar Shehi ne ya fara tashi cikin bedroom din nashi, lokacin 9am ,a hankali ya dan mirgina da Addu'ar tashi daga barci cikin bakinshi, ya miƙa hannunshi, ya dauku wayar, sai da ya duba sunan mai kiran kafin yy picking call din ya ƙara a kunnenshi.

Zallar tashin hankalin da ya ji a cikin muryar Dr din ne yasa ya dan muskuta ya gyara zamanshi,cikin gaggawa yace "Shehi a gaggauta fitar da Yarinyar nan domin yi mata dashen nan,dan jikin gaba daya ya rikice bb sauƙi gaba daya, numfashinta ma baya fita, gaskiya tana cikin hali, in da hali ayi duk abun da za'ayi a yau din nan zuwa gobe a fitar da ita,"sauke numfashi yy .

kafin yace "akwai abokina da yake irin wannan .......

Wannan littafin na kuɗi ne , game buƙata zai iya tuntuɓata ta number na kamar haka.

07033371851

DAGA TASKAR ƳAR LELE🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️
[2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼

*DAGA ALƘALAMIN*

ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️

SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA SADIYYA ABBAKAR MARU (ƳAR GATAN ROYAL STAR🌹🌹)

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.