Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Ba_Sonta_Nake_Ba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 1 of 2
Compiled By Umar Dalha Funtua.
Copied By Ummee Yusuf.
[8/31, 6:05 PM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAKE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
_A story about love and sacrifice._
_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_
_*From The Fantastic Writer of*_
```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```
*_And now_*
*_💃ðŸ»NBA SONTA NAKE BA💃ðŸ»
*âœâœ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶Ãt̶̶є αs̶̶s̶̶Ãd̶̶Ãσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єÃv̶̶є n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶Ãc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶Ãv̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✠*,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ Ãt̶̶ w̶̶Ãl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶.*
*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana gwiwa a wajen rubutu._
*BA SONTA NAKE BA* littafi ne daya kunshi darrusa na yau da kullum,ina rokon Allah kaman yanda na fara lafiya yasa na gama lafiya.
Da fatan zaku bani hadin kai kaman yanda kuka saba.
ØÙŽØ¯Ù‘َثَنَا ÙŠÙŽØÙ’ÙŠÙŽÙ‰ بْن٠يَØÙ’ÙŠÙŽÙ‰ التَّمÙيمÙىّ٠وَأَبÙÙˆ بَكْر٠بْن٠أَبÙÙ‰ شَيْبَةَ ÙˆÙŽÙ…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù Ø¨Ù’Ù†Ù Ø§Ù„Ù’Ø¹ÙŽÙ„Ø§ÙŽØ¡Ù Ø§Ù„Ù’Ù‡ÙŽÙ…Ù’Ø¯ÙŽØ§Ù†Ùىّ٠جَمÙيعًا عَنْ أَبÙÙ‰ Ù…ÙØ¹ÙŽØ§ÙˆÙيَةَ - وَاللَّÙْظ٠لÙÙŠÙŽØÙ’ÙŠÙŽÙ‰ أَخْبَرَنَا أَبÙÙˆ Ù…ÙØ¹ÙŽØ§ÙˆÙيَةَ - عَن٠الأَعْمَش٠عَنْ Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ عَنْ عَلْقَمَةَ قَالَ ÙƒÙنْت٠أَمْشÙÙ‰ مَعَ عَبْد٠اللَّه٠بÙÙ…Ùنًى ÙÙŽÙ„ÙŽÙ‚ÙÙŠÙŽÙ‡Ù Ø¹ÙØ«Ù’مَان٠Ùَقَامَ Ù…ÙŽØ¹ÙŽÙ‡Ù ÙŠÙØÙŽØ¯Ù‘ÙØ«ÙÙ‡Ù Ùَقَالَ Ù„ÙŽÙ‡Ù Ø¹ÙØ«Ù’مَان٠يَا أَبَا عَبْد٠الرَّØÙ’مَن٠أَلاَ Ù†ÙØ²ÙŽÙˆÙ‘ÙØ¬ÙÙƒÙŽ جَارÙيَةً شَابَّةً لَعَلَّهَا ØªÙØ°ÙŽÙƒÙ‘ÙØ±ÙÙƒÙŽ بَعْضَ مَا مَضَى Ù…Ùنْ زَمَانÙÙƒÙŽ. قَالَ Ùَقَالَ عَبْد٠اللَّه٠لَئÙنْ Ù‚Ùلْتَ ذَاكَ لَقَدْ قَالَ لَنَا رَسÙول٠اللَّه٠-صلى الله عليه وسلم- « يَا مَعْشَرَ الشَّبَاب٠مَن٠اسْتَطَاعَ Ù…ÙنْكÙم٠الْبَاءَةَ Ùَلْيَتَزَوَّجْ ÙÙŽØ¥Ùنَّه٠أَغَضّ٠لÙلْبَصَر٠وَأَØÙ’صَن٠لÙلْÙَرْج٠وَمَنْ لَمْ ÙŠÙŽØ³Ù’ØªÙŽØ·ÙØ¹Ù’ ÙÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙŠÙ’Ù‡Ù Ø¨ÙØ§Ù„صَّوْم٠ÙÙŽØ¥ÙÙ†Ù‘ÙŽÙ‡Ù Ù„ÙŽÙ‡Ù ÙˆÙØ¬ÙŽØ§Ø¡ÙŒ ».
*It was narrated that `Alqamah said: "I was walking with Abdullah in Mina when he was met by Uthman. He stood and talked with him and Uthman said to him: `O Abu Abdur-ur-Rahman, shall we not marry you to a young girl who can remind you of the times past?` Abdullah said, `If that is what you are telling me, (let me tell you that) the Messenger of Allah (s.a.w) said to us: O young men, whoever among you can afford it, let him get married, for it is more effective in lowering the gaze and guarding one`s chastity. And whoever cannot afford it should fast, for it will be a shield for him."*
Sahih Muslim
*BISMILLAHI RAHMANIR RAHIM*
________Hmmmmm bansan ta ina zan fara baku labarin na da yake cukuikuiye ba *BA SON TA NAKE BA* wannan Kalmar da na saba ji kenan a gidan mu har zuwa gidan aure na, bari dai in fara muku daga d'an farko yanda zaku fi fahimta.
Suna na Fatima. Amma Inna ta na kira na da Zareefa a halin yanzu shekaru na basu fi 10 zuwa 11 ba muna shirye-shiryen rubuta common entrance a makarantan mu na boko sai dai yau tunda na shigo kuka nake sosai saboda cin mutuncin da akayi min yau har yayi yawa duk da ba yau aka fara min ba sai dai na yau d'in ya tsaya min a rai.
Uniforms aka zo dasu ana rabawa daga gwarzon Governor mu professor Babagana Umara Zullum, harda jaka wadda ya kunshi note books, tex books crayon pen da sauran tarkacen da d'alibi zai bukata gefe d'aya kuma ga sandal da socks amma aka tsallake ni wai dan ban biya 200 na PTA ba duk da kasancewar nafi kowa bukatan wa'yan nan kayan domin uniform d'ina ya gama yagalgalewa.
Basa tab'a ganewa Inna ta ina zata samu gudan 200 ta bani in kawo musu Ita da kyar take samo 30 da safe ta bani 20 in sayi alale wajan Maman Dije dake gidan mu 10 kuma ta bani a matsayin kud'in tara, toh a wannan halin 200 ba karamin kud'i bane a wajan mu.
Kudin taran ma in na zo dashi sai in rasa abun saya dashi, gashi kiri-kiri ana mana girki a makaranta a rabawa kowa banda ni da ban san me na tare musu ba, bakin jinin Malamai prefect harda monitor nake dashi akan wannan 200 da bana kawowa yasa duk suke jin haushi na, ina ji ina gani za'a tsallake ni a hanani abincin nan wanda nake masa kallon kaman naman kaza suke ci sai randa suka ga dama suke bani bani, duk ranan da na samu ci nake kaman in had'a da hannu na.
Abinci ne da ake rabawa ko kwatankwacin sa babu a gidan mu, dan wata ran alale mai kwai da hanta ake rabawa wata ran kuma jallof d'in doya ko macroni ko kuma na shinkafa da wake yaji manja, toh ina mu ina cin wannan kayan dad'in a wannan gidan namu na yawa.
Abban mu matan shi 3, dan haka in gari ya waye kowa shi zai nemawa cinsa da 'ya'yan sa abinda zai ci babu ruwan Baban mu da d'aukan nauyin ahalin da Allah ya bashi duk ranan da Allah ya bashi zai sayo masara ko dawa a nika dayawa a rinka tuwo da daddare da safe da rana kuma kowa yaji da kan shi dan haka duk yayuna da kanne na wanda muke uba d'aya da cousins d'ina duk tallah suke dan rufin asiri amma ni Inna ta bata yarda da tallah ba duk da ni kad'ai ce wajan ta tana iya kokarin ta wajan ganin ta sauke duk wani nauyi daya rataya akan ta dai-dai karfin ta shiyasa kaf gidan mu babu masu zuwa boko ko islamiya sai ni kad'ai wanda 'yan gidan mu sukewa lak'abi da iyayi ne sai dare kuma muke zuwa makarantan Allo gaba d'ayan mu amma banda 'yan matan da suke tsayawa zance abin su.
Kona dawo makaranta wata rana babu abinda zanci in Inna bata samu wankau tayi ba sai dai ta tura ni gidan su da yake makotaka da namu inci duk abinda ya sauwaka a wajan kakata kasancewar suma kaman gidan namu suke babu wadata sai dai su basu da yawa kaman gidan mu,ranan da ta samu kud'in wankau kuma ta kan bani hamsin in sayi garau-garau nan wajan Gwaggo Aisha ta d'an yarfa min a roba dan mugunta ko mai da yajin kirki bata zuba min kuma in na fita waje na saya ya zama abin magana da habaice-habaice shiyasa ko zan fita saya a waje Inna ta ke hanani.
*BA SON TA NAKE BA* shine kullum Kalmar da Baban mu yake fad'awa Inna ta in wani abu ya faru a cikin gida kuma kayan takaici a gaban kowa yake fad'a mata hakan sauran matan gida suyi ta shewa ana kara habaice-habaice tun bani da wayo har nayi wayo na gane me hakan ke nufi kuma a bakin matan gidan mu na tsinta wai Kakana Abban Inna ta tsohon soja ne in ba'a biya su fensho ba wajan Baban mu yake neman rance har kudin suka taru ya kai Kakana ba zai iya biya ba wanda yasa dole ya bashi Inna ta shiyasa ko kad'an bamu isa mu d'aga murya kaman kowa a gidan ba,Inna ta in ba wani abu take ba kullum tana cikin d'akin ta dan matan duk sun had'e mata kai har yaran su duk raini suke mata sai wajan matan kanin Baban mu Maman Dije take samun sauki dan babu ruwanta da hargitsin gidan mu sai kishiyarta itama tana shiga cikin sauran matan Baban mu tana taya su wulakanta Inna ta.
Haka na fito daga cikin makarantan ina kukana na karin takaicin ma 'yar silifas da nake lallab'awa kuma nake shan bulalan rashin sandal akai ina zuwa bakin gate ya tsinke, ban tsaya neman leda dan gyarawa ba na rike a hannu na nufi titi ido rufe na manta da akwai motoci kan titin burina kawai in ganni a gida.
Karan takawan brick ne ya dawo dani hayyaci na, ganin mota ya nufo ni gadan-gadan yasa na rasa yanda zanyi saboda firgita nan na durkushe ina jiran ta Allah ta kasance min.
Motan daya ja brick Allah ya taimake ni bai kad'e ni ba amma motan bayan shi sai da ya fasa mishi danger, shima na bayan shi ya buga mishi a takaice dai motoci kusan 5 sukayi hatsari duk a dalilina, kuma duk abinda ake ina nan durkushen ban mike ba.
Wani wanda motan shi yafi na sauran bugawa ya fito a zuciye ya janyo ni yana bala'i yana zagina ya d'aga hannu zai yarfa min mari, ihu na yi na rufe fuska ta da d'ayan hannuna ina jiran saukan marin amma na ji shiru ina bud'e idona naga ashe mutane ne suka rike shi suna bashi hakuri, ina jin ya sake min hannu na kama hanyan gida da gudu dama tsakanin makarantan mu da gidan babu wani nisa sosai.
Ban iya tsayawa a ko ina ba saboda zafin rana da yake kona min kafa ina shigowa Hajara na fita da katon tire da aka jera mata robobi da aka zuba garau-garau hamsin hamsin a ciki, ni dai ban san ya akayi ba kawai sai gani nayi munyi karo kayan kan ta sun zube kamin kice kwabo almajirai sun fara wawaso nima ganin haka na wawasushi roba 2 na kama ci dama na kwaso yunwa ta na fitan hankali.
Ihu Hajara ta fasa tana "Wayyoo Gwaggo zo ki gani zo kiga abinda Zareefa tayi min" jin an ambaci suna na yasa matan gidan da yaran su lekowa dukan su, ni kuwa ko a jikina ina gefe sai zabga loma nake yau na samu shinkafa da wake daya ji mai da yaji har roba 2.
Salati manyan suka fara suna bina da kallo yanda baki na yayi nasha-nasha da mai,Gwaggo Aisha da fitowar ta kenan tace" kan uba ke Hajara meke faruwa ya akayi kika min b'arin abinci haka?"
"Wallahi Gwaggo kin gan ta nan Zareefa ce ina fita ta shigo a guje ta ture ni har nayi barin, kuma tun kamin almajirai su zo ita ta fara wawason min abinci" Hajara ta karasa tana harara ta yanda nake ta sud'e roba dan ban san ma sunayi ba sam.
Wani maka da Gwaggo ta kai min a gadon baya ban san lokacin da na saki roban na gatsare tare da fasa ihun azaba ba, wuyan matattacen uniform d'ina ta kama ta jani zuwa ciki tana" lalle na yarda wannan 'ya ta gado mugunta, hasada da tsiya yo banda tsiya yanda kuke ke da uwar ki baku da allura a cikin d'akin shine ta koya miki yanda zaki na yi min barna kina jawo min asara??
Ke Bintu koki fito wallahi kabo na ba zaiyi ciwon kai ba duk inda zaki shiga ki fita sai kin bani kudina yanzu kuma wallahi ba sai anjima ba, ki fito na ce ".
Kallon yanda wuyan uniform d'ina yake kara yagewa yasa nace" Gwaggo ki sake min uniform d'ina kinga kina kara......" Ban samu karasawa ba sakamakon buge min baki da tayi tana huci tace" inifon din banza inifon din wofi ke iskanci uwar taki take koya miki ko boko shegiya yarinya duk wani gantali kin iya wai an likawa boko da baida baki"
"Ni ai abin nasu dariya yake sakani haka masu bokon suke ko akan su aka fara oho, dubi kiga ko takarda d'aya bata dashi balle fensir,ko da uwar me take rubutun?" Cewar Inna Asabe.
Inna ta duk tana jinsu amma ko lekowa bata yi ba balle ta tanka musu, hayaniya sosai ya kaure a gidan mu harda mokota masu zugi sai yi suke harda masu cewa a gaban su ma abin ya faru, dole yasa Inna ta fitowa daga d'aki jin abin yaki ci yaki cinyewa.
"Yauwa daddawa uwar zaman d'aki dole ai yau ki fito azo a biyani kud'ina naira dubu daya da dari biyu ciff wallahi ko biyar d'ina ba zaiyi ciwo ba".
Dariya suka fara suna " keko Aisha ina wannan taga har dubu da dari biyu sai dai in 'yar zata sai da ta biya ki" ko kuma kije wajan tsohon soja" wani tsohon soja sai dai ayi sata" ire-iren kalamai da suke jifan Inna ta dashi kenan.
Kaman yanda ta saba bata kula kowa ba ta koma cikin d'akin ta sai gata ta fito da dubu d'aya da dari biyu ciff da Gwaggo Aisha ta ambata ta mika mata babu kunya ta sake min riga ta karb'e kudin tana lissafi tana mamakin ina Inna ta ta samu wannan kud'i ita da burin ta yau sai ta wulakan tamu yanda taga dama amma cikin ikon Allah ta biya.
Duk watsewa suka yi cike da mamaki wasu ko cewa suke dama bar raina mutum baka san sirrin sa ba.
Ana cika min rigata na shigo d'aki ina kallon wuyan rigata na ce, "Inna dubi fa yanda ta maida min wuyan rigata gobe ya zanyi in tafi makaranta?"
Inna da ta had'a rai sosai ta ce, "ba wuyan riga ya kamata kiyiwa kuka ba, gobe kika ce za'a rufe karb'an kud'in common entrance ko?"
Gyad'a mata kai nayi ina cire kayana.
"Toh kud'in da nayi wata 3 da wani abu ina tara miki na common entrance d'in su na bada a maimakon abincin mutane da kika zubda, gobe ma in kin taso daga makaranta kada ki rinka kula da gaban ki".
Yawan comments yawan typing.
[8/31, 6:05 PM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
_A story about love and sacrifice._
_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_
_*From The Fantastic Writer of*_
```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
*_And now_*
*_💃ðŸ»UWANI💃ðŸ»
*âœâœ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶Ãt̶̶є αs̶̶s̶̶Ãd̶̶Ãσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єÃv̶̶є n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶Ãc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶Ãv̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✠*,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ Ãt̶̶ w̶̶Ãl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶.*
*Addu'a Ga Wanda ka zage shi:*
Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce;
اَللَّهÙÙ…ÙŽÙ‘ Ùَأَيـما Ù…ÙØ¤Ù’Ù…Ùن٠سَبَبْتÙÙ‡Ù Ùَاجْعَلْ ذَلÙÙƒÙŽ Ù„ÙŽÙ‡Ù Ù‚ÙØ±Ù’بَةً Ø¥Ùلَيْكَ يَوْمَ الْقÙيَامَةÙ.
Allahumma fa'ayyuma mu'minin sababtuhu, faj'al zalika lahu kurbatan ilayka yawmal qiyamati.
Ya Allah! Duk wnai mumini da na zage shi, to ka sanya wannan ya zamanto sababi gare shi na samun kusanci zuwa gare Ka ranar kiyama.
*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._
*2*
Kasa cire rigan nayi na zaro ido waje ina kallon Innara na ce," Inna kud'in common entrance d'in kika basu?"
"Ya kike son inyi? Kin san halin Aisha sarai a gidan in ta fara fitina zata kai awa goma tana yi ba tare da ta gaji ba,ni kuwa kin san ba iyawa zanyi ba gwara in bata a rabu lafiya gobe ma idan zaki shigo gida kada ki natsu " Inna kenan ta bani amsa.
Zama nayi da rigan a wuyan na ina hawaye na ce," shikenan za'ayi banda ni kenan,ko yau ina kallo akayi ta rabon abubuwa a makaranta ni ban samu komai ba akan 200 balle 1500 nasan gobe ko class ba za'a barni in shiga ba".
"Haka Allah ya kaddara ba zaki rubuta ba a wannan shekaran amma kiyi hakuri zuwa shekara mai zuwa ko kuma muyi addu'an Allah ya kawo wata hanyan,kinji ko?" Inna ta fad'a min cikin rarrashi.
Goge hawayen fuskan ta nayi na tashi na cigaba da cire uniform d'in na ba tare da na kara cewa komai ba.
"Ki d'auki hamsin cikin d'ari ukun daya rage kije ki sayi wani abin kici" cewar Inna.
Dariya na fara kyakyalewa da shi harda rike ciki sai da nayi mai isa ta sannan na ce," ai inna ciki na kaman zai fashe saboda koshi, dan lokacin da Hajara tayi b'ari almajirai suka fara wawaso nima roba 2 na wawashe na cinye tas abina Gwaggo Aisha data ji haushi kinji yanda ta zuba min dundu a baya Wallahi ko jin zafi ma banyi ba".
Cikin tsuke fuska Inna ta ce," wai ya akayi kika yi musu b'ari? Kullum inayi miki fad'an ki natsu amma ba kya ji ko?"
Daina dariyan nayi sannan nayi kalan tausayi na fara bata labarin abinda ya faru a makaranta har zuwa yanda mukayi karo da Hajara,ajiyar zuciya Inna ta sauke tana mai jin tausayin na ta ce," hakuri zakiyi Zareefa insha Allah wata rana sai labari,karatu kuma da yardan Allah zakiyi shi".
Gyad'a kai kawai nayi na fita yin alwala zahar a lokacin duk yaran gidan anyi musu abin sana'a duk sun fita talla,ina idar da sallah na fara shirin islamiya shi kam cikin dokin zuwa nake shirin na kasancewar a can bana takura kaman boko.
Akwai wani Malamin mu da yake d'aukar mu Qur'an shi ya tsaya minsosai sabo kokarin na dan har kudin wata 500 shi yake biya min domin kullum dai-dai nake kawo hadda ta yanzu haka mun bawa izufi 30 baya.
Ina gama shirin na nayiwa Innata sallama na tafi.
Ina fita Inna ta kwaso uniform dana cire ta hau wanke min da sauran Omo da ta rage jiya,tanayi tana jin su suna ta haice-habaicen su ta gama ta shige d'aki ta rabu dasu.
Mun taso a islamiya ni da kawayen na muka nufi gida muna d'an wasan su na yara,muna zuwa dai-dai gidan mu na fara jin muryan Baban mu yana ta masifa kaman zai ari baki.
Dariya sauran yaran suka fara har suna lekowa ta rububben ginin daya zagaye gidan.
Jiki a sanyaye na nufi cikin gidan namu dan nasan yanda Baba yake d'aga muryan nan nasan da inna ta yake,muryan Gwaggo Aisha naji tana kara zuga Baba da fad'in karya da gaskiya.
"Toh ai Mallam dan ma baka ga irin rashin kunyan da yarinyan nan tayi min a waje ba,inda zaka san da gayya ta b'arar da kayan sana'a shine,itace farkon daka wawa sannan sauran almajirai suka bi bayanta.
Koda yake b'ata baki na nake ina gaya maka abinda ya faru na san babu wani hukuncin da zaka d'auka tunda 'yar amayar ka ce abin sonka".
A fusace Baba ya juyo kanta yana," wannan wani irin maganan banza kike min matar da *Ba sonta nake ba* aka lika min ita dole yasa na karb'a dan kar inyi asaran kud'i na,amma wallahi Aisha kin cuce ni"..
Gwaggo Aisha ta saki shewa dama Kalmar da take son ji kenan.
Baba ya cigaba da fad'an shi inda yake cewa," duk kin bi kin b'ata yarinya bata ganin kowa da darajan a gidan nan da anyi magana kice wai boko take sai kace ki d'in bokon kikayi aikin banza kawai zata zo ta same ni a gidan sai jikin ta ya gaya mata"
Yana juyowa muka had'a ido ina can makure karshen bango ,aiko baiyi wata-wata ba ya nufo ni zai sake min wannan rankwashin sa nan da sai yasa kullum na saki fitsari a wando.
A guje nayi d'akin mu na shige kamin ya kama ni sanin cewa in ba wani babban dalili ba baya shigowa,cikin sa'a kuwa bai shigon ba ya tsaya a tsakar gida yana cigaba da fad'an,sam na daina jin me yake cewa domin ganin Inna ta na kuka abinda ban tab'a gani ba kenan tun tasowa ta dan komai akayi mata a gidan ko Baban mu ko matan gidan sai dai tayi murmushin mai ciwo tace akwai Allah.
Toh tana furta wannan kalman duk yanda za'ayi da ita ba zata kuma tankawa ba na sha tambayan ta me yasa itama ba zata ke rama cin fuska da ake mata ba sai dai tayi wannan murmushin nata mai ciwo ta ce," bakomai Zareefa akwai Allah" daga nan kuma ba zata kara cewa komai ba.
Zuwa nayi har gaban ta na durkusa a gaban ta tare da d'aura hannu na kan guiwoyin ta na ce," Inna kuka kike,meya same ki?" Duk na jero mata wayan nan tambayoyi a lokaci guda.
Murmushin nan nata mai ciwo tayi min kana ta ce," babu komai ba kuka nake ba wani abu ne ya shiga ido na".
Ba dan na yarda ba nayi shiru nasan ko abinda ake mata a gidan nan dole tayi ta kuka kullum,komawa gefe nayi na zauna ina kallon ta tana dinke min wuyan uniform d'ina daya yage bata kuma yarda ta zubar da hawaye ba.
Da washe gari da safe bayan na sayo alale na naci Inna ta bani 200 a cikin kudin daya saura ta ce in kai makarantan nima a bani bani sabon uniform d'in inya so ko shekara mai zuwa sai in zana jarrabawan.
Cikin matukar farinciki na nufi makaranta yau nima za'a bani kyautan kayan makaranta kaman sauran d'alibai.
Direct office d'in principal na wuce ina jin kaina yau kaman bani ba,bayan na gaishe shi na bashi kud'in na ce ni jiya ban samu daman zuwa ba shiyasa ban samu komai na rabo ba.
Tambayan shekaru na yayi na fad'a mishi ya ko duba ya ciro uniform sabo dal ya miko min,murna fal jikina na karb'a amma sai na kasa tafiya ina jiran jaka da sauran tarkace.
Ganin na ki tafiya ya ce," me kike jira kuma?" Kasa nayi da kaina na ce," Sir su jaka da takardu suma ban samu ba".
"Okay toh sai gobe ko anjima dan suna store,ya suna ki kuma a wani class kike?"
"Suna na Fatima Hassan,kuma ina class 6A" na bashi amsa.
"Toh kije anjima zan sa akai miki" cike da farinciki na juya na koma ajin mu feeling proud.
A wajan assembly akayi announcing cewa duk wanda bai biya kud'in common entrance ba ya koma gida dan zuwa nan da awa 2 za'a fara kuma ba barin mu za'ayi mu shiga ba,nan take murna ta ya koma ciki.
Jiki a mace na kama hanyan gida dan nasan zaman nawa bashi da amfani,ina tafiya ina hawaye saboda na kwallafa rai na akan jarrabawan,shikenan inaji ina gani mates d'ina zasu wuce ni.
Ina tafiya cikin tafiya naji horn a kusa dani ,matsawa gefe na karayi maimakon ya wuce sai naga ya tsaya kusa dani yana kallo na ya ce," kanwata meya same ki kike kuka akan titi?"
Kallon shi na tsaya yi d'an kyakkyawa dashi duk da ba fari bane.
"Kiyi magana mana kanwa ta?"ya katse ni.
"Kud'in common entrance ake nema shine aka kore ni dan ban biya ba" na bashi amsa sabon hawaye na bin kunci na.
"Oh stop crying,kiyi shiru muje makarantan naku in gani" yace yana fitowa daga cikin motan shi.
Tsayawa nayi kallon shi ba tare da na motsa ba, murmushi shimfid'e a fuskar shi ya zagayo inda nake tsaye ya rankafo da kan sa kusa dani ya ce," me kike tunani ?"
"Inna ta zata min fad'a ta hana ni magana da wanda ban sani ba" nace ina kara komawa baya.
"Kada ki damu ni Yayan kine muje zan miki bayani kin ji?" Gyad'a mishi kai nayi muka koma makaranta dama banyi nisa ba.
Office d'in principal muka tafi bayan sun gaisa ya mishi bayanin cewa shi Yaya nane yazo biya min kud'in common entrance,ni dai ban ce komai ba sai bin su da nake da ido,a take ya cire kud'i d'ari biyar- biyar sabbi fil ya biya muka fito ya ce," kije class kuma kiyi kokari sosai kinji kanwata?"
Murmushi ne ya kwace min na gyad'a kai na tare da rugawa zuwa aji.
[8/31, 6:05 PM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
_A story about love and sacrifice._
_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_
_*From The Fantastic Writer of*_
```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
*_And now_*
*_💃ðŸ»UBA SONTA NAKE BA💃ðŸ»
*âœâœ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶Ãt̶̶є αs̶̶s̶̶Ãd̶̶Ãσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єÃv̶̶є n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶Ãc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶Ãv̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✠*,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ Ãt̶̶ w̶̶Ãl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶.*
*Abin Da Musulmi Zai ce idan aka yabe Shi:*
اَللَّهÙÙ…ÙŽÙ‘ لاَ ØªÙØ¤ÙŽØ§Ø®ÙذْنÙÙŠ بÙمَا ÙŠÙŽÙ‚ÙولÙونَ، وَاغْÙÙØ±Ù’ Ù„ÙÙŠ مَا لاَ يَعْلَمÙونَ (وَاجْعَلْنÙÙŠ خَيْرًا Ù…Ùمَّا يَظÙÙ†Ùّونَ)
Allahumma la tu'akhizni bima yakuluna waghfir lee ma la ya'alamun, (waj alne khayran mimma yazunnun).
Ya Allah! Kar Ka rike ni da abin da suke fada, Ka gafarta mini abin dab a su sani ba, Ka sanya ni fiye da yadda suke zato.
*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._
*3*
Koda na tafi class naga kowa harkan gaban shi yake kasancewar sai zuwa nan da awa 1 za'a fara jarrabawar, dan haka kawai sai na wuce bayan gida na canza sabon uniform nawa, na sanin cewar daga yau na gama amfani dashi dama Inna tasa na karb'a ne kan cewa zan ƙara wata shekarar amma Allah ya taimake ni ya kawo wannan mutumin da yake cewa shi Yaya nane.
Kayan ba ƙaramin kyau suka yi ba, sun zauna sosai a jikina dama gani ba za'a kira ni mai jiki ba kuma ba za'a kira ni da sirirya ba,ga fata ta irin mai tsadan nan ce, wato chocolate colour wanda yayiwa round face na kyau,bani da dogon hanci can amma inada daidai gwargwado sannan manyan idanu na da d'an ƙaramin baki na su suke sa mutane suke min kallon wata kyakkyawa,wajan gashi ma dai babu laifi dan ina dashi ba laifi.
A bola na watsar da tsohon uniform d'in nawa dan inada yakinin in aka bawa wani ko goge-goge ba zaiyi dasu ba,na kama hanyan class d'in mu sai na zama abin kallo ga sauran d'aliban wasu na min dariya wasun kuma na cewa sun min kyau,ni dai ban kula kowa ba nayi wucewa ta class d'in mu.
Nan ma bata canza zani ba dan wasu har tsokana ta suke,kala bance musu ba sai harkan gaba na nake zuciya ta fari kal zan rubuta jarrabawa tare da 'yan uwana.
Bayan wani lokaci malamai suka shigo raba mana paper, nan kowa ya natsu bayan sun gama raba mana kowa ya fara rubutu sai naga ashe abun ba wuya ba kaman yanda na tsorata da shi bane a farko,cikin kankanin lokaci na kammala na fito abu na ina mai jin farinciki a rai na.
Da daddaya kowa ke fitowa bayan mun gama fitowa aka raba mana abinci mai d'an karan dad'i jallof na shinkafa harda naman kaza da bobo.
Kin cin nawa nayi na kama hanyan gida da abinci na,ina tafiya ina ta dube-dube ko zan kara ganin bawan Allah nan amma ko mai kamanin sa ban gani ba har na iso gida.
Duk 'yan matan gidan mu yau suna nan basu fita tallah dan azahar batayi ba sai dai kowacce suna bakin murhu da uwayen su suna aikin kayan sana'ar su sai yara mazan ne da suka fita sai da pure water.
D'akin mu na wuce direct sanin cewa Inna ta tana ciki ko lura da kallon tsana da Gwaggo Aisha ke auna min banyi ba nayi sallama na shiga d'akin mu.
Inna ta na zaune da sabuwar multi na hula a hannun ta tana tsakawa ,da sauri na ida shigowa ina cewa," laa Inna hula kika fara,yaushe kika koya ko dama can kin iya?" Na jero mata tambayoyin nan duk lokaci d'aya cikin zak'uwa.
Murmushi shimfid'e a fuskar ta tace," kinga yanda sabuwar uniform d'in ya miki kyau kuwa,kinga har shekara mai zuwa zakiyi amfani da kayanki hankali kwance".
Zama nayi ina ajiye takeaway da bobo na hannu na, nace mata," ai Inna bana bukatan uniform d'in hasalima daga yau amfanin shi ya kare domin dani aka zana jarrabawan".
"Dake aka zana sun tausaya ne suka bar miki ko kuwa?"ta tambaya fuskarta d'auke da farinciki mai cakude da mamaki.
"Ko kad'an basu ji tausayi na ba Inna,kora tama sukayi har na fito daga makaranta zan dawo gida...." Nan na bata labarin abinda ya faru tsakani na da wanda ya ce shi Yaya nane.
Maimakon inga tana farinciki sai naga ta tsuke fuska ta fara min fad'an da kada in sake yarda da wani kan titi wanda ban sani ba ko ya bani abu in karb'a,a irin haka suke maida yara doya su tafi dasu suyi tsafi dasu ko kuma a yanke kan su.
Tsoro sosai ya kama ni nayi ta zare ido ina ganin na tsallake rijiya da baya ashe,nan na bata hakuri tare da alkawarin bani ba wanda ban sani ba nan gaba.
Daga nan hira muka zauna yi da Inna ta bayan na bud'e mana takeaway nace muci tare,kallon abincin tsaya yi kana tace,"yanzu dama irin wannan abincin ake raba muku harda naman kaza?"
Dariya na kyakyale dashi sannan nace," Inna baki ga harda bobo na ba?"
"Ikon Allah tunda nake ban tab'a jin labarin governor mai son talakawan shi haka ba sai akan bawan Allah nan,Allah ya kiyaye mana shi" cewar Inna .
Da "Ameen na amsa sannan nace mata muci mana,amma taki ci d'an tab'awa kawai tayi ta bar min kaya na anan ne take gaya min ashe 'yar wata makociyar mu mai suna Ya'ana ita ta koya mata d'inkin hula,shikenan ta huta da zaman banza inta gama ance ana saya da kud'i da d'an yawa,murna nayi tayi muma mun samu sana'a da zamu rinka samun kud'i kaman sauran 'yan gidan mu.
Tun daga wannan rana na mayar da hankali na kan makaranta islamiya da nake in kuma safiya ce Inna ta kan tura ni gidan kakanni na saboda gudun rigimar 'yan gidan mu sai lokacin islamiya yayi sai in dawo in shirya inyi wucewa ta domin Gwaggo Aisha tafi kowa iya tuggu kuma Baban mu sosai yake jin maganan ta in fact itace 'yar gaban goshin shi ba dan komai ba sai dan tafi sauran matan shi kud'i kuma tana bashi kud'i shiyasa yake ji da ita sosai.
Maganan shiga secondary school mun ajiye ta a gefe kan cewa sai inna ta dinka hula 2 ko 3 sai ta had'a kud'in ayi min komai dashi.
Cikin ikon Allah satin hulan 4 Inna ta kammala shi baiyi kyau irin na kwararre ba amma da yake cikin tsafta ta dinka shi babu datti ko kad'an a jiki sai ya zama abin sha'awa.
Ya'ana wacce ta koya mata itama ta gama nata zata kai sayarwa Inna tace muje tare sai ta sayar a bani kud'in kasancewar ita zata wuce gidan kakanni ta daga can kuma zata kwana 2 kamin ta dawo.
Bayan ta shirya ta biyo min muka tafi can London ciki wai can sun fi sayan hula da daraja, dubu da dari biyar aka sayi na inna ta ita kuma Ya'ana dubu tara aka sayi nata da saboda ita nata tangaran ne.
A leda baki ya'ana ta kulle min kud'in ta saka ni a napep na zuwa anguwan mu ita kuma ta wuce,muna zuwa kusa da layin mu suka sauke ni suka wuce.
Har nazo kusa da layin mu na had'u da wani mutum yace min," ke ana sadaka a wacan kwanan" kamin in bashi amsa wasu yaran su 4 suka zo wucewa ya fad'a musu ba musu suka bi hanyan daya nuna nuna musu,ganin sun bi hanyan yasa nima na bisu a guje muna shan kwanan ashe mutumin yana bin mu sai muryan shi muka ji yana cewa," kai ku tsaya in akwai abu a hannun ku,ku kawo in ajiye muku kar ya fad'i wajan karb'an sadakan".
Gaba d'aya mu muka mika mishi duk kud'add'en hannun mu da alamu suma sauran yaran aiken su akayi,yana karb'a yace mana ga gidan can mu shiga shi yana jiran mu anan.
Ga gudu muka shiga gidan da sunan karb'an sadaka amma me sai aka ce mana ai ba anan akeyi ba,wata da zata girme mu a ciki tana jin haka ta fita da gudu muka mara mata baya amma muna fita muka nemi mutumin nan sama ko kasa muka rasa shi,kuka ko wannen mu ya fara dan sai yanzu muka gane cewa ashe b'arawo ne yayi mana dabara ya sace mana kud'add'en mu.
Gefen titi na samu nayi zama ta ina kuka na kasa komawa gida in naje me zan cewa Inna ta bayan kwanaki tayi min fad'a akan irin haka sai gashi na maimaita,bayan haka hulan nan yanda ta dage tayi ta d'inka shi ba dare ba rana dan ta samu saka ni a secondary school amma sai in koma ince mata wani ya min dabara ya kwace? gaskiya ba zan iya komawa ba.
Ina zaune ina kuka na d'aya daga cikin yaran da shima an sace mishi kud'in yazo ya zauna kusa dani muka cigaba abin mu,kaman daga sama naji ance," kanwata yauma kukan kike?"
Da sauri na d'aga kaina dan ganin waye sai naga wannan bawan Allah daya biya min kud'in jarrabawa ne hannun shi rike da bottle water inaga a shagon kusa damu ya saya ga mutane a wajan suna ta shiga da fita babu wanda ya kula mu sai shi da yazo yanzu.
Kin kula shi nayi na d'auke kaina ina goge hawayen ido na.
"Kai meya same ku kuka zauna anan kuke kuka?"ya tambayi yaron kusa dani.
Shi kuwa kama jira yake ya fad'a mishi duk abinda ya faru nan ya tambayi shi nawa ne kud'in?.
"Dari uku ne akace in sayo taliya da mai da maggi" ya bashi amsa.
Dari biyar ya ciro a aljihu usual sabo dal ya bawa yaron,cike da murna yaron ya karb'a yana godiya ya ruga da gudu ya tafi shagon kusa damu ya sayi kayan yanda ya fad'a ya dawo mishi da canjin shi,amma sai yaki karb'a yace ya tafi ya bar mishi.
Murna fal ranshi ya kama hanyan gida da gudu ya bar mu a wajan,ganin ban bi yaron ba yace min," ba tare kuke bane?" Jiki a mace na girgiza kaina saboda na zata yaron yana amsan kudin zai zama doya kaman yanda inna ta ta fad'a sai naga ba haka bane lafiya lau yayi sayayyar shi ya tafi gida.
"Ke kuma nawa ya sace miki?" Muryan shi ya katse min tunanin da nake.
"Kud'in hulan Inna ta ya karb'e gaba d'aya" na bashi amsa.
"Stop crying kanwata kinji,gashi karb'i ki kai mata".
Kallon kud'in na tsaya yi ina tunanin in karb'a ko a'a?
"Karb'a mana ki goge hawayen ki" saka hannu 2 nayi na karb'a cikin sanyin murya nace," nagode!"
Girgiza min kai yayi ya ce," kada ki damu tashi ki tafi gida".
Da azama na tastashi nayi gidan mu ba tare da nasan nawa ya bani ba.
A gida kuwa Inna duk ta damu tana tunanin me yasa na dad'e haka,tana ganina ta sauke ajiyan zuciya ta ce," zareefa me yasa kika dad'e haka?"
Banyi kasa a guiwa ba na kwashe duk abinda ya faru na gaya mata,karban kud'in tayi ta kirga taga dubu uku ciff,fincikoni tayi da karfin tsiya na fad'i akan simintin d'akin na bud'i baki zanyi ihu ta ce kada na kuskura inyi mata ihu anan dole na had'iye kukana ina zaro ido saboda ganin Inna ta ta fusata yau sosai.
" Wato ke ba kya jin magana ko zareefa duk abinda na gaya miki ta bayan kunnen ki suka wuce ko,baki san ki kama kan ki a matsayin ki na ya mace ba duk ko wani d'an iska ya baki kud'i karb'a kike yau kuma harda bin wani, Inna ilahi wa inna ilahi rajiun!!!
Toh tunda kunnen kashi gare ki yau zanyi maganin ki wallahi" ta karasa tare da murd'e min kunne.
Sosai ranan inna tayi min abinda tunda na san kaina bata tab'a yi min ba daga baya tayi min nasiha sosai mai ratsa jiki.
Tun daga wannan rana nayi hankali ya kasance babu ruwana da duk abinda zai had'a ni da wanda ban sani ba sosai na kama kaina.
Kullum Baba inya shigo gida Gwaggo Aisha itace zatayi ta dawainiya dashi dan ko Maman su Hafsa bata samu wannan matsayi a wajan shi ba,shi irin mazan nan ne da mace in zata rike shi tayi mai komai toh dad'i zaiji kwata-kwata bashi da zuciya d'aukan nauyin iyali da Allah ya d'aura mishi shiyasa gidan namu kullum sai kara hargitsewa yake.
Maman su Hafsa abin na damun ta sai dai babu yanda ta iya tayi-tayi amma ta kasa kamo Gwaggo Aisha dan tafi ta samu nesa ba kusa ba.
Ranan wani juma'a daya kasance girkin inna ta ne kuma a ranan munyi sa'a Baba ya kawo mana masara kusan kwano 10 ya ce a nik'a tunda babu garin tuwo.
Maimakon manyan gidan su kai sai suka ce ba zasu kai ba tunda ba girkin iyayen su bane,shikenan sukayi zaman su babu wanda ya ce musu wani abu.
Dole yasa wheelbarrow inna ta aro ta saka min a ciki ta ce in kai, ina turawa da kyar na kama hanya na fita a gida ga kuma inda zan kai nikan da d'an tazara da gidan mu.
Inna ta ana cewa tana da girki a gidan ne amma baba baya shigowa d'akin ta kaman yanda yake shiga sauran d'akin matan shi kuma baya cin abincin ta,na sha jin yana cewa nima Allah ne ya kaddara sai na taka duniya amma har yau yana jin takaicin wannan abin.
Na isa lafiya sannan nabi layi har aka zo kai na aka nik'a min mutumin shiya taimaka ya mayar min cikin wheelbarrown na kama hanyan dawowa gida.
Ina cikin turawa jikina duk gumi ban san taya wannan yaron ya shiga gaba na ba da keken sa da alamu ma dan koyo ne dan da kyar ma in ya kaini shekaru,duk yanda naso kaucewa amma abin bai yiwu ba saboda nik'an da nauyi kamin kace me dani dashi duk muka zube a wajan tare da kurkurjewa buhun nik'a na kuma sai cikin kwata da yake kusa damu.
Hannu 2 na d'aura a kai na rusa ihu ina gari na dan ko zafin kurjewan na daina ji saboda nasan in na koma gida babu garin nan wallahi Baban mu zai iya babbake ni da raina.
Sosai nake kuka kaman raina ya fita mutane sun taru suna mana sannu ko jin su bana yi har yaron ya d'auki keken shi ya tafi babu wanda ya hana shi kasancewar karami ne babu abinda zai iya yi.
"Oh not again yauma kuka take,meya same ta?"naji muryan shi kaman daga sama.
"Karo sukayi da me keke nik'an ta ya fad'a kwata" wani yaro ya bashi amsa yana nuna mishi buhun da aka ciro a kwata wanda ko akuyoyi ba zasu iya cin garin da yake ciki balle mutum.
Baice komai ba ya koma ya motan shi ya wuce,ajiyar zuciya nayi da Allah yasa bai ce zai ban wani abu ba yau,mutane suna bani bakin in tashi in tafi gida amma kirmitsitsi naki motsawa balle su saka ran zan tashi.
Bayan kaman mint 5 na kara jin muryan shi yana cewa," ga wannan tashi in ajiye ki a gidan ku".
Kallon inda yake nayi naga buhun shinkafa da wasu kwalaye harda jerrican mai ana saka mishi a boot din mota,kaman wanda aka jona da remote na tashi jiki na na b'ari na fara tura wheelbarrow na da gudu nayi hanyan gida na bar shi tsaye anan.
Ana gama saka masa kayan ya tambaya ko akwai wanda ya san gidan mu anan?
Wani yaro yayi caraf yace ya san gidan mu gashi can babu nisa sosai daga nan.
Motan shi ya shiga tare da cewa yaron yazo ya raka shi,ba musu yaron ya shiga suka bi baya na.
[8/31, 6:05 PM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
_A story about love and sacrifice._
_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_
_*From The Fantastic Writer of*_
```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
*_And now_*
*_BA SONTA NAKE BA_*
*_4_*
*âœâœ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶Ãt̶̶є αs̶̶s̶̶Ãd̶̶Ãσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єÃv̶̶є n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶Ãc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶Ãv̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✠*,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ Ãt̶̶ w̶̶Ãl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶.*
*Addu'ar Tsayuwa a Kan Dutsen Safa da Na Marwa*
Jabir, Allah ya yarda da shi ya ce, yayin da yake siffanta hajjin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; yayin da ya kusanto dutsen Safa sai ya karanta:
Ø¥ÙÙ†ÙŽÙ‘ الصَّÙَا وَالْمَرْوَةَ Ù…Ùنْ Ø´ÙŽØ¹ÙŽØ§Ø¦ÙØ±Ù اللهÙ.
أَبْدَأ٠بÙمَا بَدَأَ الله٠بÙÙ‡Ù.
Bers Safa: Innas safa wal marwata min sha'a'irillah
Abda'u bima bada'al lahu bihi.
Hakika Dutdsen Safa da na Marwa suna daga cikin alamomin da Allah Ya sanya (na addininsa)".
Ina farawa da abin da Allah ya fara da shi.
Sannan ya fara da Dutsen Safa, ya hau shi har sai da ya hango dakin Allah, sai ya fuskanci alkibla, ya kadaita Allah, (ya yi hailala), ya girmama shi (ya yi kabbara) ya ce;
الله٠أَكْبرÙ! الله٠أَكْبرÙ! الله٠أَكْبرÙ!
Allahu akbar. Allahu akbar. Allahu akbar.
Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma.
لاَ Ø¥ÙÙ„ÙŽÙ‡ÙŽ Ø¥Ùلاَّ Ø§Ù„Ù„Ù‡ÙØŒ اَلله٠أَكْبَرْ، لاَ Ø¥ÙÙ„ÙŽÙ‡ÙŽ Ø¥Ùلاَّ الله٠وَØÙ’دَه٠لاَ شَرÙيكَ Ù„ÙŽÙ‡ÙØŒ لَه٠الْمÙلْك٠وَلَه٠الْØÙŽÙ…ْد٠وَهÙÙˆÙŽ عَلَى ÙƒÙÙ„ÙÙ‘ شَيْء٠قَدÙيرٌ، لاَ Ø¥ÙÙ„ÙŽÙ‡ÙŽ Ø¥Ùلاَّ الله٠وَØÙ’دَه٠أَنْجَزَ ÙˆÙŽØ¹Ù’Ø¯ÙŽÙ‡ÙØŒ وَنَصَرَ عَبْدÙÙ‡ÙØŒ وَهَزَمَ اْلأَØÙ’زَاب٠وَØÙ’دَهÙ.
Bers la Ka'aba: La ilha illallahu, allahu akbar, La ilaha illal lahu wahdahu la sharika lahu, lahul mulku wa lahul hamdu, wa huwa ala kulli shay'in kadirun. La ilaha illal lahu wahdahu. Anjaza wa'adahu, wa nasara abdahu, wa hazamal ahzaba wahdahu.
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Mulki ya tabbata a gare shi, kuma yabo ya tabbata a gare Shi; kuma Shi Mai iko ne a kan komai. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai. Allah ya gaskata alkawarinsa, Ya taimaki bawansa, Ya ruguza rundunonin kafirai Shi kadai.
Ya karanta wannan zikiri sau uku, yana yin addu'a bayan kowace marra. Da ya hau Dutsen Marwa ma ya yi kamar yadda ya yi a kan Dutsen Safa.
*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._
*_4_*
Ina isowa kofar gidan mu shima sun iso abinka da mota,ina ganin motan nayi jifa da wheelbarrow a nan bakin k'ofar gidan mu na shiga ciki da gudu ban tsaya a ko ina ba sai d'akin mu a d'akin ma a bayan k'ofa na b'uya ina lek'e.
Inna da tun shigowa ta take kallo na fuska d'aure ta ce," wa kika tsokono a wajan da kika shigo min a guce haka?"
Ban iya bata amsa ba sai zare ido da nake zuciya ta na cigaba da bugawa, Inna zata kara min magana muka ji muryan yaron daya rako mutumin nan ya ce,"wai ana neman zareefa".
Wani kallo Inna tabi ni dashi sannan ta dubi yaron ta ce," yana ina?" Yana nan k'ofan gidan nan" yana gama bata amsa ya juya ya tafi abinsa.
"Waye shi kuma me kika masa ya biyo ki har gida?"
"Sh...shine wan...wanda ya biya min kud'in jarrabawa" na bata amsa.
"Shine ya biyo ki har gida,ko dai da wani abu daban?" Shiru nayi na kasa bata amsa sai zare ido da nake saboda ban manta abinda tayi min akan shi ba.
Hijabinta da yake gefenta ta saka ta fita dan taji me yake tafe dashi,a tsakar gida ta tarar da 'yan gidan mu kwan su da kwarkwatan su suna tsatsaye suna k'us-k'us.
Suna ganin ta suka fara yi da karfi wasun su na cewa k'ila sata nayi mishi,wasu kuwa cewa suke asirin mu ne ya tonu k'ila yana cikin mazan da nake bi,tunda dama cewa suke karatun karuwanci nake.
Inna ta bata kula kowa ba ta fito 'yar rub'abb'en zauren gidan mu da niyyan yi mishi iyaka dani domin ta gane fad'an da tayi min kwanaki shi ya firgita ni haka.
Katuwar mota da ta gani ana sauke kayan abinci a ciki kaman za'a bud'e 'yar karamar shago yasa ta tsaya cak tana kallon d'an matashin saurayin da ba zai haura shekaru 21 zuwa 22 ba yana danna wata laftatiyiyar waya a hannun shi.
Inna sai yayi mata kwarjini ta kasa karasa fitan balle tayi mishi magana,shine dai daya gaji da danne-danne shi ya d'ago da kai karaf suka had'a ido da Inna ta,asalin kamanin ta na d'auko shiyasa yana ganinta ya gane ta.
Wayar nashi ya mayar aljihun rigan shaddar shi lafiyayya blue ya karaso gaban ta cikin sauri ya duka har k'asa ya fara gaishe ta,fuska a had'e ta amsa kana ta ce," lafiya kake neman zareefa,ko kuma akwai wani abinda kake nema daga gare ta,dan ta bani labarin duk abinda ta faru tsakanin ku kuma shine yau ka biyo ta har gida"?
Girgiza mata kai ya fara wasu waye na taruwa a idon shi ya ce," ba haka bane Aunty kada ki min mummunan fahimta saboda ni ba nufi na kenan ba,domin duk had'uwa da muke da ita Allah ne yake had'a mu,lokacin da na gan ta a hanyan makaranta na fito zan tafi wajan aiki ne na gan ta tana kuka sai na biyu kuma na tsaya siyan ruwa a gefen hanya ne na ganta ita da wani yaro suna zaune a gefen titi suna kuka,and still yau shima gefen kwata na ganta zaune tana kukan garin ta ya fad'a kwata mutane duk sun zagaye ta ana taje gida ta fad'a amma taki tashi saboda wai Baban ta ba zai bar ta duk taji ciwo amma ko jin zafin bata yi.
Ni suna na Abdulbasit kuma ni maraya ne da tunda na taso ban san kowa nawa ba,banida kowa akan titi nake rayuwata cikin yunwa,kunci da kuma kad'aici sai daga baya na samu wani bawan Allah ya tallafawa rayuwata har kika ganni haka sannan shiyasa na tsani inga karamin yaro yana kuka domin yana tuna min da lokacin kuruciya ta kuma duk yanda zanyi sai na san yanda zanyi in share mishi hawaye sannan hankali na zai kwanta.
Ba ita kad'ai nakewa haka suna dayawa Aunty bana son kowa ya sha wahalan da nasha a baya amma in har hakan ya b'ata miki dan Allah ina neman alfarman ki yafe min".
Inna da jikinta duk ya gama yin sanyi sai ta kasa furta komai saima jin ba dad'i da tayi kan yi mishi mummunan zato.
"Ga wannan kayan abincin a saka su ciki Aunty sannan a bawa Baba hakuri kada ya dake ta tsautsayi ne " taji ya yanke mata tunani.
Tulin kayan abincin ta kalla ido a waje ta girgiza mishi kai,"ta ce a'a ka tafi da kayan ka mun gode Baban ta kuwa zanyi mishi bayani zai fahimta kuma...."
Katse ta yayi cikin sauri ya ce,"haba Aunty ba'a maida hannun kyauta baya,sannan ni ina farincikin na samu ahali da zan iya nunawa a ko ina amma kika ce haka? Sannan hakan na nunawa baki karb'e ni a matsayin d'an uwa ba,ina neman alfarman ki rike ni a wannan a matsayin inji ya ake ji in mutum yana da ahali".
Wannan furucin da yayi saida yasa Inna hawaye,gyad'a mishi kai ta iya yi domin ta tabbata tana bud'e bakin ta kuka ne zai kufce mata saboda tsananin tausayi daya bata, shima cike da farinciki ya mike yana share hawayen idon shi ya ce,"nagode Aunty Allah ya saka da alkhairi zan tafi sai bayan kwana 2 zan rink'a zuwa mu gaisa".
Bai jira cewar Inna ba ya fad'a motan shi sai da yayi ribas sannan ya kira wani yaro ya bashi kud'i masu yawa ya ce ya kaiwa Inna ta,yaja motan shi ya fita a layin namu.
Inna tana tsaye ta rasa ta ina zata fara tab'a kayan sai ga yaron da aka bawa kud'in yazo gaban ta ya mik'a mata kud'in ya ce," wai gashi inji wancan mai motan ya ce in baki"
Wani yawu ta had'iye da kyar hannun ta na rawa ta karb'i kud'in a ranta tana ayyana anya wannan bawan Allah abinda ya fad'a gaskiya ne kuwa? Nan wani sashi na zuciyar ta ya ce mata tunda take bata tab'a cutar da wani ko tabi wani da mugun kulli ba insha Allah in ma da wata manufar yazo Allah ba zai bashi sa'a ba.
Da wannan kwarin guiwan ta samu ta kira wasu matasa da suke zaune gefe tace su taimaka mata su shigar mata da kayan abincin ciki,ba musu suka fara jidan kayan domin suna ganin girman ta sosai.
Su Gwaggo Aisha baki da hanci suka bud'e suna kallon kayan da ake wucewa dashi d'akin mu,bakin ya mutu murus sun rasa abin fad'a,nima ina nan a bayan k'ofa duk na had'a zufa naga a nata shigowa da kayan suna jerawa a gefe har suka gama suka fita ban fito daga mab'uya na ba dan haka basu san da mutum a d'akin ba.
Suna gama shigo da kayan Inna ta basu 500 cikin kud'in hannun ta tace su raba,cikin farinciki suka karb'a tare da yi mata godiya suka koma wajan zaman su,hannayyen ta cikin hijabi ta shigo dan haka babu wanda yaga abinda ke hannun ta.
"Hmmmm kun ga ikon Allah ko 'yan gidan nan gaskiya ta fito fili ga ribar boko nan mun gani yarinya 'yar k'arama an koya mata bin maza har gida ake biyo ta,Allah yayi mana tsari ya kare mana 'ya'ya".cewar Gwaggo Aisha kenan cike da hasada.
Suma sauran kaman jira suke suka fara nasu kowa na fad'an albarkacin bakin shi, Inna ko kallon inda suke ba tayi ba ta shigo d'aki ta cire hijabin jikin ta tare da zama dab'as kan simintin d'akin mu dako leda babu tana kallon kayan zuciyar ta na bugawa,kud'in hannun ta ta shiga kirgawa taga dubu goma ne cif ta ajiye a gefe.
Hango ni tayi a bayan k'ofa ina lek'en ta tace," ba zaki fito bane ko sai nazo na same ki" cikin sauri na fito ina goge gumin jikina,kallon tausayi tabi ni dashi ta san Allah bai bata haihuwa dayawa ba amma alhamdullilahi tana alfahari dani domin jumm'ar da zatayi kyau tun daga laraba ake gane ta.
Na zata zatayi min fad'a ko ta ce wani abu akai amma naji tayi shiru bata ce komai ba sai tagumi data zuba tana yawan ajiyan zuciya,da taga zaman ba zaiyi mata ba ta mik'e ta saka hijabi tare da yi min gargad'in kada in fita koda k'ofar d'aki ne kuma kar in kula kowa duk abinda zasu ce min.
Bata jira amsa ta ba ta fita daga gidan zuwa gidan su wato gidan kakanni na da muke makotaka dasu,da sallama ta shiga.
Kakata Ya Jalo da suke kira da Maa tana soya gyad'a na sayarwa ta amsa tana mata sannu da zuwa,bata gama suyar ba ta sauke gyad'an ta taso sanin cewa in taga kafar Inna ta a gida da dalili ne ya kawo ta duk da kasancewar muna makota basu bata daman zuwa gida any how ba.
"Bintu komai da kike gani na duniya mai wucewa ne sannan kowa yayi hakuri zai ga riba a gaba dan haka bana son kina sawa kan ki damuwa ko kad'an ki cigaba da hakuri wata rana sai labari" cewar kaka ta kenan ganin damuwa karara a fuskan Inna ta,dama haka take mata kullum koda tazo da damuwar ta bata bari ta fad'a sai dai tayi mata nasiha tare da kwantar mata da hankali ta koma gida.
"Nagode Maa Allah ya kara girma amma ba matsalan gida ne ya kawo ni ba akan Zareefa ne...." nan ta kwashe labarin Abdulbasit tun farko har zuwa yau da yazo ya tafi.
Shiru kaka tayi tana tunani kaman na second 20 can ta d'ago ta ce," a yanda na fahimci maganan nan yaron nan bashi da aibu da gasken sa taimakon yake yi in da bashi da gaskiya a yanda kika ce yana da kud'i nan ba zai tsaya yi miki wannan dogon bayanin ba balle ya gaya miki asalin sa,in kuma da yana da niyyan cutar da ita da tuni ya cutar da ita dan haka ki kwantar da hankalin ki Allah ne ya dubi zuciyar ki ya kawo wanda zai taimake ku ke da 'yar ki cikin ruwan sanyi".
Cike da gamsuwa maganan mahaifiyarta ta ciro kud'in ta bawa Maa dubu uku a ciki amma taki karb'a ta ce," ki bar shi ki had'a dana wajan naki ki saka Zareefa makarantan gaba kaman yanda kika ce".
"Maa akwai saura ai zasu isa ki karb'i wannan d'in ki saka albarka" cewar Inna kenan.
Dubu 1 kawai ta zara a ciki ta mayar mata da sauran tare da cewa," Allah ya sanya albarka".
Sun d'an tab'a hira kad'an sannan tayi mata sallama zuciyar ta fari kal ta dawo gida.
D'ari biyar ta cire ta bani a cikin kud'in tace inje in sayo naman miya harda kayan miya,cike da murna na fita a guje yau za'a dafa shinkafa a gidan mu kuma harda nama abinda ada sai sallah yake faruwa.
Ina dawowa Inna ta fito ta hura wuta ta fara girki nan da nan ko k'amshin miyan ta ya cika gidan, Inna Asabe ce ta fara mita," oh in da ranka zaka sha kallo yanzu fisabillilahi wannan abinci da aka samu ta haramtaccen hanya shi za'a girkawa 'ya'yan mu su shi?" Ta karasa maganan tana kallon gwaggo Aisha ko zata ce wani abu.
"Hmmm ni yara na ba zasu ci ba dama kowa ya san ni ba irin ku bace ina da abinda zasu ci nan wata ko 3 ne koda ace bana sana'a dan haka ku kuka sani" Gwaggo Aisha ta fad'i haka tana yiwa karamar 'yar ta da muke sa'anni da juna kitso wato Jameela.
"Ke kuwa daga magana sai ki wani dawo kaina kina wani cika baki,meye naki bamu sani ba wallahi mun san inda Hajara take zuwa tallah da abinda yake tafiya wallahi duk mun sani, a toh kada a cika mana baki kuma ba'a karya kusa da gida" Inna Asabe take mayarwa Gwaggo Aisha magana cikin fushi dan taji haushin maganan da ta yab'a mata.
Nan fa fad'a ya kaure ba abinda kake ji sai ifacce-ifaccen su suna zagin juna tare da tonon asiri kala-kala, sai Maman Dije ce da ta gaji da hayaniyar tasu tazo ta shiga tsakanin su sukayi shiru.
Inna ta dai tana gefe tana aikin ta ko inda suke bata kalla balle tayi gigin raba su domin ta sha gwadawa a baya sai fad'an ya dawo kan ta data fahimce su sai ta kama kanta ta koma gefe ta zama 'yar kallo.
Ana kiran sallah magariba Inna ta gama girkin ta duk da taji sun ce ba zasu ci ba amma haka ta nemo kwanukan kowa ta zuzzuba musu ta bani na kaiwa ko wacce d'akin ta suka bini da zagi da tsinuwa kuma wai inzo in d'auke tsiyar mu amma nayi musu kunnen uwar shegu domin Inna taja kunne na kan ina ajiye musu in juya in basa ci su bawa almajirai amma ni kar in d'auko.
Sai bayan sallah isha'i Baban mu ya shigo dama ko girkin Inna tane baya shigowa d'akin mu bare yaci abincin mu dan haka Inna tana jin muryan shi tace in d'auki abincin shi in kai mishi.
"Na'am" na cewa Inna ba tare da na shirya ba jin tace wai in kaiwa Baba abinci,sai naji abin wani banbara kwai.
"Ki kaiwa babanku abincin shi nace" ta kara maimaita min,amsawa nayi na d'auki tiren abincin da Inna ta d'aura kwanon tuwo daban miya ma daba sai kofin silver mai murfi da ta zuba ruwan randa mai sanyi.
A tsorace na nufi d'akin nashi ina jan k'afa dan na san karamin aikin shine ya koro ni da abincin,ba yanda na iya haka na karasa bakin k'ofan d'akin cikin rawan murya nayi sallama,da yake tsanan da yake min bana wasa bane nan da nan ya gane murya ta cikin tsawa ya ce," uwar me kike nema a nan?"
"Inna tace ta ce in kawo abinci" na bashi amsa cike da fargaba.
"Ita Bintu dan yau ta haukace shine zata aiko ki kawo min jagwalgwalo,kafin in kirga uku ki bar nan ko kuma in na tashi wallahi...." Ai ban bari ya karasa ba na jiyo cikin sauri Allah ya taimake ni babu kowa a tsakar gidan dan haka babu wanda ya ganni na shige d'akin mu.
Inna murmushi tayi ganin na dawo da abincin ta ce," koro ki yayi ko?" Gyad'a mata kai kawai nayi bata kara cewa komai ba ta sauke min tiren akaina ta zuba mana namu muka fara ci abin mu.
Saida naji ciki na barazan fashewa sannan na hakura da tura shinkafa da jan miyan da nake na kwashe kwanukan na fitar sai ga sauran yaran ma suna fitowa da nasu kwanukan suna ta tsid'e hannu su da iyayen su suka ce ba zasu ci ba.
Ina dariya na koma d'aki nake bawa Inna ta labari ta kwab'e ni kan bata son surutu in nemi waje in kwanta,ba musu kuwa na kwanta kan shimfid'a ta cikin abinda bai kai minti biyar ba bacci yayi gaba dani.
Da washe gari da sassafe Innata da ta tashi hura wuta tayi ta d'aura abin karyawa duka gidan abinda tun tasowa ta ban tab'a ganin anayi ba, spaghetti ta dafa mana harda kifin gongoni da take d'ibawa su kakata kayan a nan data bud'e wani kwali taga duka shine a ciki.
Kamshin girkin yauma ya cika ko Ina har ta gama, tana gamawa ta samu tire ta zuzzubawa yaran gidan ta ce duk su zauna su karya iyayen su kuma a kwano ta zuba na kai musu suna ta cika da batsewa bakinciki kaman su mutu.
Baban mu yazo fita kaman yanda ya saba yaga yara suna ta kai loman taliya baji ba gani wasun su kuma suna kokawa akan kifin da yake ciki.
"Kai uban wa ya baku abinci da sassafen nan kuke mana hayaniya a gida" Baba ya tambaya yana kara matsowa kusa dan tabbatar da abinda idon shi ya gani gaskiya ne ko akasinta .
"Innar Zareefa ce ta bamu" cewar Ibrahim d'an gidan Inna Asabe.
"Jiya ma shinkafa da miya ta zuba mana harda nama" shima musa d'an gidan Gwaggo Aisha ya kara akai.
Cike da mamaki Baban mu ya ce," ita Bintun ce tayi girki harda nama?" Yana magana ne yana kallon k'ofar d'akin mu.
Fasa fitan yayi ya koma d'akin shi yana tunanin ta ina zai fara rarrashin Inna ta zuba mishi wannan kayan dad'in shima.
[8/31, 6:05 PM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
_A story about love and sacrifice._
_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_
_*From The Fantastic Writer of*_
```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```
*_And now_*
*_BA SONTA NAKE BA_*
*âœâœ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶Ãt̶̶є αs̶̶s̶̶Ãd̶̶Ãσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єÃv̶̶є n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶Ãc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶Ãv̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✠*,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ Ãt̶̶ w̶̶Ãl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶.*
Yin Kabbara tare Da Kowace Tsakuwa Yayin Jifan Jamra.
Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana yin kabbara tare da kowace tgsakuwa idan ya jefi jamrori uku. Sannan sai ya yi gaba kadan ya yi addu'a yana mai fuskantar alkibla, ya daga hannayensa biyu yayin addu'ar. Yana yin haka ne bayan jifan Jamra ta farko da ta biyu. Amma bayan jamratul Akaba (jamra ta karshe), sai ya yi jifan kawai, ya yi kabbara tare da kowace tsakuwa, sannan ya tafi; ba ya tsayawa ya yi addu'a a wajenta.
*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._
*5*
Baba ya kasa zama yayi a d'aki sai safa da marwa yake,sai yayi kaman zai kira wani kuma sai ya fasa can dai yaja wani dogon tsaki shi kad'ai yana," in banda b'atawa kaina lokaci nake ba ita Bintun yaushe har tayi wani abin kanta zan tsinka kaina gaban yarinya k'arama" yana magana ne shi kad'ai tare da neman hanyan fita.
Ta gefen ido yake kallon yaran da suke ta buduri da taliyarsu bakin nan duk mai yasa kai ya fice.
Yana fita teburin mai shayi ya tafi kaman yanda ya saba ya bayar da naira d'ari yace a bashi shayi empty na naira ashirin da bredi na hamsin,ana bashi canji akwai mai kosai a gefen mai shayin itama ya sayi na talatin a wajan ta ya samu waje a rumfar mai shayin ya fara karyawa.
A da in yana cin wannan had'in ji yake kaman mai cin kaza amma yau sai yaji babu taste sam sai tuno taliyan nan daya sha mai da kifin gongoni yake,kaman dole haka ya rinka cuccusawa har ya gama ya tashi ba dan dad'i ba.
A gida kuwa muna gama karyawa da Inna ta tace mu shirya ta kaini makaranta kada wani abu yazo ya fad'awa kud'in,
Muna gama shiryawa muka kama hanyan ainihin makarantan mu na da wato *YERWA PRACTICE* akwai jss a ciki daga 1 zuwa 3, cikin ikon Allah komai yazo mana da sauki ba kaman yanda Inna ta zata ba domin kud'in registration da kud'in PTA duka dubu biyu suka karb'a,daga nan uniform,takalmi,jaka,takardu duk kyauta aka bani kuma principal yace gobe in fara zuwa domin har an fara karatu.
Cike da farinciki muka kama hanyan gida, a hanya sai da mukayi 'yan cefanen mu da kud'in hannun mu sai dubu uku ya rage muka dawo da kaya niki-niki a hannu.
Gwaggo Aisha tana yiwa Hajara fad'a a tsakar gida kasancewar Inna Asabe ma ta fita,tana ganin mu tayi shiru sai rarraba ido take alaman basu da gaskiya,mu dai bamu bi ta kan su ba muka wuce d'aki suka bi ledojin hannun mu da kallo.
Muryan Gwaggo Aisha ya cika gidan tana yiwa Hajara masifan me take bata fito ta tafi tallah ba gashi har azahar tayi,na fito da buta a hannu na dan zagawa makewayi muka had'a ido da Gwaggo Aisha ta gallah min wata muguwar harara,niko dan in cusa mata bakinciki sai nayi mata dariya dama in ina son kullar da ita haka nake yi.
Ai kuwa ta hau yanda ya kamata ta hau zagina harda Inna ta da bata san wainar da ake toyawa ba,ni kuwa ko a jikina na shige bayan gidan na kama ruwa na fito tsakar gidan na fara alwala ita kuma bata fasa zagin nawa ba,dana lura bata da niyyan dainawa nayi mata gwalo amma sai na fake da cewa Jameela da take kusa da ita tayi min nima na rama.
Ban gama wanke d'ayan kafa na ba naga ta rarumo murfin tukunya da yake kusa da ita ta jefi ni dashi, Allah ya taimake ni kamin ya karaso na gauce nayi d'akin mu da gudu ina dariya.
Had'iye dariyan nawa nayi ganin fuskar Inna ta babu alaman wasa ta ce," wai ke wace irin yarinya ce Zareefa,ban hana ki kula su ba ko akwai sa'ar ki a ciki,bayan haka duk matan Baban kine saboda babu abokin wasan ki a cikin su tsakanin ki dasu shine girmamawa".
Jiki a sanyaye na ce ," kiyi hakuri Inna ba zan sake ba dama ni bada ita nake ba nida Jameela ne"
"Naji ki kiyaye bana son neman magana" ban kara cewa komai ba na fara sallah na a zuciya ta kuwa banga zan kyale ta ba in ta min wannan shegen kallon tunda ba wani laifi nayi mata ba.
Da yamma Inna ta fito tayi tuwan ta na shinkafa da miyan yakuwa da yaji biscuit bone da wadacaccen gyad'an miya, jin yauma kamshi ya cika gidan yara suka fara tsallen murna suna," yauma Innar Zareefa zatayi mana kayan dad'i" iyayen su na hantaran su amma basu fasa ba.
Yauma d'aki nabi su da abincin ba wanda ya kalle ni balle inji sun ce basa cin abincin da aka same ta ta haramtaccen hanya.
Da wuri yau Baban mu ya dawo gida tare da tsammanin an girka kayan dad'i irin na d'azu,yana saka kafa a gidan kamshin abincin ya mishi maraba wanda sai da ya had'iye yawu yana bin tsakar gidan da kallo,yaji tsit kaman babu kowa a gidan saboda kowacce tana d'aki da yaran ta suna kwasan gara.
Da gangan ya d'aga murya wai dan Inna taji ta aiko mishi nashi ya hau fad'an an watsar da kaya a hanya amma aka rasa wanda zai kula shi.
Yana nan tsaye yanayi Ibrahim d'an gidan Inna Asabe ya fito da kwanukan da suka ci abinci yana kokuwa da kashi tare da tand'e yatsu.
"Kai zo nan,zo ka kwashe kayan nan" ya yafito Ibrahim da hannu yazo yasa hannu ya kwashi kwanuka guda biyu da suke gefe har ya juya zai tafi ya rike shi murya kasa-kssa ya ce," kai yauma Bintun ce tayi girkin" gyad'a mishi kai Kai yayi dan santin kashin ya hana shi magana.
Maida hankalin shi yayi kan d'akin mu da muka sauke d'an yalolon labulen mu, juyawa yayi ya shiga d'akin shi ya zauna jiran ko yauma za'a kawo mishi.
Ya kai kusan rabin awa zaune yana kallon k'ofa amma ko motsin mutum bai jiba balle yaga mutum,tsaki yaja a karo na ba adadi ya mike ya fito tsakar gida tare da kama hanyan waje,bukutin roba na Maman Dije da yake ajiye a gefe akai ya sauke haushin sa sannan ya fita,ji kake kararass ya fashe sakamakon harbi daya kaiwa bucket din da k'afa.
Fita yayi yana ta zage-zage shi kad'ai dole ne yasan yanda zaiyi ya shawo kan Inna ta kamin girkin ta ya zagayo.
Da washe gari ba girkin Inna ta bane d'an haka indomine ta girka min na karya dashi ta bani talatin kud'in tara na fita makaranta cikin tsantsan farinciki domin haka naga sauran yara ake musu nima yau anyi min.
Sosai a ranan na mayar da hankali na nayi karatu tsabani da,karfe d'aya dai-dai aka tashe mu na kama hanyan gida.
Tun daga zaure na fara jin muryan Gwaggo Aisha tana zagina tare da aibata ni ga dukkan alamu kuma Baban mu take fad'awa,a jikin bango na makure naki karasowa sanin halin Baban mu ya kware a rankwashi.
"Munafuka daina kallo na da shegun idanunki kaman na mujiya" cewar Gwaggo Aisha tare da aika min mugun kallo.
"Ke Aisha ba kya kula da lokacin daya kamata ki tari mutum da magana,ni yanzu a gajiye na shigo hutu nake nema" yana gama fad'a kuwa yayi hanyan d'akin shi ya shige ya bar Gwaggo Aisha baki bud'e.
Kuyi manage ba yawa
*Albishirinku mata masu son kamshi da gyara ga dama ta samu zamu fara classes na koyar da turaren wuta kala-kala humra shima in different colors dilke gyaran amarya man gashi nd lots more kada ko yarda a baki labarai akan 500 kacal zaki zama pro na kan ki, duk mai bukata ta tuntubi wannan no 08172724281 sai mun ji ku*.
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
_A story about love and sacrifice._
_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_
_*From The Fantastic Writer of*_
```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```
*_And now_*
*_BA SONTA NAKE BA_*
*âœâœ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶Ãt̶̶є αs̶̶s̶̶Ãd̶̶Ãσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єÃv̶̶є n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶Ãc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶Ãv̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✠*,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ Ãt̶̶ w̶̶Ãl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶.*
*Addu'a Idan Mutum Ya ga wani abu mai ban Mamaki, ko na farin ciki*
Ø³ÙØ¨Ù’ØÙŽØ§Ù†ÙŽ Ø§Ù„Ù„Ù‡Ù!
Subhanal-lah!.
Tsarki ya tabbata ga Allah.
الله٠أَكْبرÙ!
Allahu akbar
Allah ne mafi girma.
*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._
*6*
Yanda Gwaggo Aisha ta bud'e baki ta kasa rufewa saboda mamaki kowa a wajan sai da ya wangale baki muka bi Baba da kallo har ya shige d'akin shi abin sa ko waigowa baiyi ba.
Wata wawiyar Ajiyar zuciya na sauke na samun tsira daga rankawshin Baba, kasancewar a tarihin rayuwa ta yau shine karo na farko da Gwaggo Aisha ta kawo kara ta yaki fad'a ko kuma duka na dan haka cikin jin dad'i fuska ta d'auke da murmushi na wuce d'akin mu.
"Ni kikewa dariya dan uban ki,toh ba dani kike ba da lusarar uwar ki kike " cewar Gwaggo Aisha cikin matukar fushi.
"Ni wallahi Inna banyi mata magana" na fad'awa Inna cikin marairaicewa saboda ganin irin kallon da take bi na dashi.
Kwafa kawai tayi ta cigaba da d'inkin hular ta da take,cire uniform na nayi na saka kayana na gida har mukayi sallah Gwaggo Aisha nata bala'in ta babu wanda ya kula ta sai can Inna Asabe ta saka baki.
"Kema dai Aisha akwai ki da son surutu,kullum Mallam yana biye miki ya zane 'yar nan amma dan yau kad'ai ya fad'i haka kika tashi hankalin ki,ya kamata ki mishi uzuri ki...."
"Eh lallai Asabe kike kowa kin samu kaina har ni kika kalla kike cewa ina son surutu saboda wuyan ki yayi k'wari, ba surutu nayi ba uban surutu nayi sai inji bugu ga uwa ta nan" tana yi tana kara matsowa kusa da Inna Asabe wai tana jiran taji bugu.
"Hmmm Allah ya tsari gatari da saran shuka kema kin san inda kika baro ta bani ba" cewar Inna Asabe tana kawar da kai gefe.
Wannan kalaman sun fi k'ona mata rai akan na farkon nan da nan taci d'amara da d'an kwallin kanta suka fara zagin juna,har baka jin me suke cewa tsabar ihun da suke.
Cikin tab'e baki na kai loman abinci na baki na kalli Inna da hankalin ta yake kan hular ta naja tsaki na ce," ni wallahi ihun nan ya ishe ni har ciwon kai na fara ji".
"Ina ruwan ki da ihun su ko akan ki suke" da sauri na girgiza mata kai.
"Toh kiyi abinda yake gaban ki" da kai na amsa ina jin haushin su suna da daman suyi ta zagin mu son ran su suyi mana abinda suka ga dama amma ko da wasa ita Inna ba zata bar mutum ko d'an gulman su yayi yaji dad'i ba.
Basu fasa ba sai da suka tsinci muryan Baba yana magana," ni ban tab'a ganin fitina irin wannan ba,mutum ba shida daman hutawa a gidan shi saboda bala'in ku,mtswww sai ku cinye kan ku na bar muku gidan tunda zama nawa ne ba kwa so" yana gama maganan shi yasa kai ya fice.
Duk takaici ya gama rufe shi dama ya dawo gida ne ko zai samu d'an abin sakawa a bakin salati amma hakan ya gagara saima kara mishi tension da sukayi.
Majalisan nasu babu dad'i yau yana gani kowa ya sayi abu kiri-kiri suke hana shi dan yau ba shida ko ta sayan soyayyiyar gyad'a ne.
Inna Asabe ita ta hakura taja tsaki ta shige d'akin ta ya bar Gwaggo Aisha na cewa taji tsoro da ta tsaya mana taga yanda zatayi da ita.
************
Haka rayuwar gidan mu ya cigaba da tafiya babu wani canji saima kullum kara gaba yake na yanda suke mana a gidan,shi kuwa Baba bayan wancan girkin Inna daya fita yanzu tayi kusan girki uku amma ya rasa taya zaiyi ya shawo kan ta a rinka cin dad'in nan dashi.
Kullum in Inna tace da girki tun daga zaure zaka fara shak'an k'amshi mai saka yawu tsinkewa,haka Baban duk magariba zai dawo yayi ta b'uda hanci yana shak'an wannan kamshin yana," ikon Allah wai yau Bintu ce ke irin wannan girke-girke a gidan nan,da zan samu shawo kanta har na aljihu zan samu kashh Allah kawo hanya" haka zai zauna yayi ta sumbatu shi kad'ai kuma kullum cikin tsammanin zai ganni da tiren abinci yake.
Kusan sati na 2 kenan a makaranta hankali na kwance nake zuwa, Alhamdullilahi karatun ma yana shiga k'wanya ta sosai tsab'anin da,ko assignment aka bamu da kaina nake yi in na dawo gida.
Makaranta yayi min dad'i sosai dan yanzu har k'awaye gare ni,na murmure nayi kyau na k'ara haske abina yo kullum sai naci nayi nak abina,wani lokacin na saka Inna ta zubo min abinci na in tafi dashi makaranta kasancewar yanzu banda mu cikin way'an da ake rabawa abincin makaranta daga primary 6 ne zuwa kasa mu kuwa yanzu muna j.s.s1.
Abdulbasit tun ranan daya tafi bai k'ara dawowa ba yau kusan sati uku kenan,kayan abincin mu sun fara d'an yi k'asa kad'an saboda yawanci Inna in tayi girki ko ba ranan girkin ta bane sai ta zubawa k'ananan yaran gidan sun ci,albarkacin wannan abincin da suke samu sun daina mata rashin kunya ko iyayen su sun nemi suyi kememe suke k'i.
Ko aike zatayi in ni ina makaranta har rige-rigen karb'a suke suyi mata hankali kwance.
Ranan wani asabar bayan sallah la'asar ina zaune a d'akin mu ina duba English textbook na kasancewar yau babu islamiya ana auren wani Malamin mu Inna kuma tana gefe tana ninke mana kayan mu data wanke muka ji sallaman wani yaro a k'ofar d'akin mu Inna ta amsa tana tambayan waye ne,ya amsa mata da shine Alai gana yaron Yakura dama wani ne a mota yake k'iran zareefa a waje.
Kallon Inna nayi da sauri zuciya ta tana bugawa kaman ta fito ina jiran inji tayi min fad'a amma naji tace inje mu gaisa ince itama tana gaishe shi amma kada na dad'e.
Ni dai mamaki ya hana ni tashi dan sam bata tab'a gaya min yanda sukayi dashi ba dan haka ban san komai akai ba.
"Wai bada ke nake magana ba" ta fad'a a d'an tsawa ce tana ajiye kayan hannun ta, jiki a mace na tashi na saka hijabi na na fita, tsakar gidan mu babu kowa sai k'ananan yara da suke wasa iyayen su sun tafi biki can gaba da layin mu.
K'ananan kaya ne a jikin shi yau wandon jeans baki da riga t shirt fari sol sai takalmin sa shima baki yana tsaye hannayen shi duka biyu cikin aljihun wandon shi.
Ina fitowa muka had'a ido ya sake min murmushin sa mai kyau ni kuwa had'a rai nayi ina turo baki na tsaya d'an nesa dashi kad'an.
"K'anwata babu gaisuwa ne?" Ya tambaya yana murmushin.
Cikin turo baki na ce," ina wuni" bana buka rik'e kayan ki tunda sai da na rok'a". Yace Shiru nayi bance mishi komai ba.
"Bud'e seat d'in baya yayi ya ciro wasu manyan shopping bags guda uku yace biyu nawa d'aya kuma in bawa Aunty wai yana sauri ne shiyasa ba zai samu su gaisa ba kuma in bata hakuri yayi tafiya ne shiyasa taji shi shiru.
Ido na cike da hawaye na ce," in na karb'a fad'a Inna ta zata min kuma aini ban san Auntyn naka ba ta ina zan kai mata" na karasa hawaye na zubo min.
Murmushi yayi yana ," cry cry Baby,ke sam ba kya gajiya da kuka ne?" Nan ma ban kula shi ba ya cigaba," ammm Innar ki babu abinda zata miki saboda last time da nazo ita ta yarda in dinga zuwa muna gaisawa nd Aunty na kuma ba kowa bace Innar kice".
Sai a lokacin naji hankali na ya kwanta duk da dai ban yarda da abinda ya fad'a ba.
"Ki shiga gida ina jiran ki anan in tayi miki fad'an sai ki dawo min da kayan,kin ji ko?" Yace min ganin har yanzu ban yarda da maganan shi ba.qa
Da toh na amsa mishi na d'auki kayan da kyar saboda nauyin su na shiga gida zuciya ta cike da fargaban me Inna zata ce.
Kayan na ajiye ina kallon idon ta bayan na shigo da sallama ta amsa min.
"Har ya tafi?" Naji ta tambaye ni.
Da eh na amsa sannan na fad'a mata abinda yace sai banga wani tashin hankali akan fuskar ta ba saima cewa da tayi tana amsa gaisuwan shi.
Cire hijabin nayi na koma kan takardu na na cigaba da abinda nake ba tare da nabi ta kan kayan da na shigo dasu ba.
Sai da Inna ta gama abinda takeyi sannan ta bud'e jakan daya ce nata ne, turmin zani masu kyau guda 2 da lace guda d'aya sai kuma dubu ashirin a k'asan kayan ta gani.
Shiru Inna tayi tana kallon kayan cikin wani yanayi na damuwa da tsoro,ita in ba dan Maa tace mata bakomai ba data taka mishi brick.
A hankali kuma ta jawo nawan ta bud'e shima 'yar kantuna ne masu tsananin kyau da d'aukan hankali kusan su biyar riga da skirt biyu sai dogagen riguna biyu da kuma riga da wando irin wanda rigan yake sauk'owa har guiwa shi kuma guda d'aya da katon baby na a k'asan.
Shima ta dad'e shiru tana nazari sanna ta bud'e na karshen, roban ice cream manya biyu da sauran tarkacen su biscuit da chocolates sai kaji gassasu har biyu suma a kulle a ciki.
Yanzu kam tagumi ta zuba tana tunani anya akwai wanda zaiyi maka haka saboda Allah babu komai a zuciyar sa, zamani ya lalace dole tayi shakkan wannan al'amari.
Sanin gidan babu kowa yasa tace inje in kira mata Maman Dije ince tazo yanzu dan Allah.
Matan k'anin Baban mu ne,tun fil azal a wajenta Inna ta ke samun sauki dan ita babu ruwata da haukan su sai kishiyarta ce bakin su d'aya dasu Inna Asabe.
Batayi nawa ko gardama ba muka taho tare amma sai Inna ta ta dakatar dani shiga d'akin tace inje inyi wasa zasuyi magana.
Ina jin haka ni kuwa na fice daga gidan zuwa gidan kakata nayi zama na acan.
Inna tun daga farkon had'uwa ta da Abdulbasit har zuwa yau ta bata labari tare da fad'a mata abinda Maa tace da kuma yanda ita hankalin ta yaki kwanciya akan lamarin,dubu ashirin fa banda sauran sayayya da yayi gaskiya abin abun dubawa ne.
Bayan d'an nazari itama exactly kusan abinda Maa ta fad'a shi ta fad'a mata tare da cewa ta rike Allah ta kuma rike addu'a insha Allah babu abinda zai faru.
Godiya Inna tayi mata tare diban mata kayan makulashen tace ta bawa yara karb'a tayi tana godiya ta koma b'angaren su.
Ban dawo gida ba sai da Inna tasa aka kira ni sannan na dawo nan ma kayan makulashen ta d'ibarwa Maa tare da dubu uku tace in kai mata ince Abdulbasit ne yazo yau.
Karb'a nayi na fita ina maimaita sunan a raina wai Abdulbasit ni dai ban tab'a jin suna haka ba sai yau.
Maa kin karb'an kud'in duka tayi dubu d'aya ta d'auka tayi godiya na komawa Inna da kud'in ta karb'a tana zata je anjima da daddare da kanta wajan ta.
Kayan makulashen Inna ta bani, ice cream d'in nayi ta sharba dan ya min mugun dad'i sosai duk da rabi da kwata sun narke amma abinka da baka tab'a sha ba sai naji kaman madara empty nake sha,sai da ya kare muka ci kazar mu mukayi nak abin mu ranan ko girkin dare ba muyi ba.
Sai bayan sallah magariba sannan Inna ta nuna min kayan da Abdulbasit ya kawo min, aiko kaman in haukace saboda murna kayakin da ban tab'a tsammanin zan mallaka sai gasu har kala biyar duka nawa ni kad'ai harda Baby na.
Da kyar na samu nayi bacci a ranan saboda murna ina rungume da Babyn nawa nayi bacci a ranan.
Da washe gari da safe na fito ina share kofar d'akin mu naga Jameela ta fito dasu ledan alale da sob'o ta ajiye a wajan wanke-wanke tana kallon ido na tana murmushi irin su jiya sun ci kayan dad'in biki.
Ban kula ta ba sai da na kwashe sharan da nayi sannan na shiga d'aki nima na fito da robobin ice cream da kuma takardan naman kaza da muka ci harda warwarewa yanda za'a ga kasusuwan cikin sannan na ajiye a wajan wanke-wanke nima inayi mata murmushi na koma d'aki karb'o omo da zanyi mana wanke-wanken.
Da na karb'o omo sai da na d'auko Baby na na fito ina danna madannin jikin ta fara wak'an larabci,ina fitowa na tarar da Gwaggo Aisha tana leken inda na ajiye kwanukan mu.
Dariya nayi na ajiye Baby na a gefe na fara wanke-wanke na hankali kwance,ina jin Gwaggo Aisha tana jan tsaki tare da cewa," karyar banza bayan mun san komai me za'a nuna mana. Tana magana ne tare da shigewa d'akin ta sai dai tana shiga naji suna rigima da Jameela wai a saya mata irin Baby na,tun tana rarrashi naji an kai mata maka ta tsala ihu tayi waje da gudu.
Ko a ido ka kalli babyn ka san mai tsada ce shiyasa tayi mata haka domin bata da kud'in sayan shi.
Ranan muna zaune a d'aki bayan magariba ana gobe Inna zata karb'i girki muka ji muryan wani abokin Baban mu yazo yana ta masifa kan wai Baban ya ranci kud'in shi naira dubu biyu bai biya ba, ashe tun bayan la'asar Baba yake gida ya kasa fita majalisa saboda bashin da ake bin shi bamu sani ba.
Abu kamar wasa fitinan yayi girma dan ana ta bashi hakuri yace babu inda zai je sai Baba ya biya shi kud'in sa yau kusan wata 2 kenan ana abu d'aya kuma shi ya gaji da yanda Baba ke cewa yau ko gobe.
Jakar kayanta Inna ta bud'e ta ciro dubu biyun tace min in kaiwa Baban mu,karb'a nayi na fito kai mishi ba dan raina yaso ba saboda shima baya tausayin mu baya nuna kulawa gare mu sai sauran 'yan gidan shiyasa nima banga dalilin da yasa zamu tausaya mishi ba.
Sai dai ina zuwa saida na tausaya mishi,yana rab'e jikin k'ofan shi yayi abin tausayi shi kuwa mai bashi sai ci mishi mutunci yake, ga kanin Baban mu da muke kira da baffa shima sai hakurin yake badawa amma a banza
Ina zuwa kusa dashi na tab'a shi ya d'ago ya kalle ni da idon shi daya canza kala, mika mishi kud'in nayi na ce," gashi inji Inna tace ka biya su kud'in.
Baba kasa karb'an kud'in yayi ya tsaya kallo na haka sauran matan ma suka tsaya kallon kallo.
*Albishirinku mata masu son kamshi da gyara ga dama ta samu zamu fara classes na koyar da turaren wuta kala-kala humra shima in different colors dilke gyaran amarya man gashi nd lots more kada ko yarda a baki labarai akan 300 kacal zaki zama pro na kan ki, duk mai bukata ta tuntubi wannan no 08172724281 sai mun ji ku*.
[9/3, 9:06 PM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
_A story about love and sacrifice._
_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_
_*From The Fantastic Writer of*_
```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```
*_And now_*
*_BA SONTA NAKE BA_*
*âœâœ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶Ãt̶̶є αs̶̶s̶̶Ãd̶̶Ãσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єÃv̶̶є n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶Ãc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶Ãv̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✠*,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ Ãt̶̶ w̶̶Ãl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶.*
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
ØÙŽØ¯Ù‘َثَنَا سَعÙيد٠بْن٠مَنْصÙÙˆØ±Ù ÙˆÙŽÙ‚ÙØªÙŽÙŠÙ’بَة٠بْن٠سَعÙيد٠وَأَبÙÙˆ كَامÙل٠الْجَØÙ’دَرÙيّ٠وَاللَّÙÙ’Ø¸Ù Ù„ÙØ³ÙŽØ¹Ùيد٠قَالÙوا ØÙŽØ¯Ù‘َثَنَا أَبÙÙˆ عَوَانَةَ عَنْ سÙمَاك٠بْن٠ØÙŽØ±Ù’ب٠عَنْ Ù…ÙØµÙ’عَب٠بْن٠سَعْد٠قَالَ دَخَلَ عَبْد٠اللَّه٠بْن٠عÙمَرَ عَلَى Ø§Ø¨Ù’Ù†Ù Ø¹ÙŽØ§Ù…ÙØ±Ù يَعÙودÙÙ‡Ù ÙˆÙŽÙ‡ÙÙˆÙŽ مَرÙيضٌ Ùَقَالَ أَلَا تَدْعÙÙˆ اللَّهَ Ù„ÙÙŠ يَا ابْنَ عÙمَرَ؟ قَالَ Ø¥ÙنّÙÙŠ Ø³ÙŽÙ…ÙØ¹Ù’ت٠رَسÙولَ اللَّه٠صَلَّى اللَّه٠عَلَيْه٠وَسَلَّمَ ÙŠÙŽÙ‚Ùول٠لَا تÙقْبَل٠صَلَاةٌ Ø¨ÙØºÙŽÙŠÙ’ر٠طÙÙ‡Ùور٠وَلَا صَدَقَةٌ Ù…Ùنْ غÙÙ„Ùول٠وَكÙنْتَ عَلَى الْبَصْرَةÙ.
*It was narrated from Simak bin Harb, that Mus`ab bin Sa`d said: "`Abdullah bin `Umar came to visit Ibn `Amir when he was sick and he said: `Won`t you supplicate to Allah for me, O Ibn `Umar?` He said: `I heard the Messenger of Allah (s.a.w) say: "No Salat is accepted without Wudu` (purification), and no charity (is accepted) that comes from Ghulul," and you were the governor of Al-Basrah."`*
[ Sahih Muslim ]
*7*
Baban mu jikin sane yayi sanyi sosai, wai Bintu ce ta biya mishi bashi. Bayan duk abubuwa da yayi mata basu da misali bayan wa'yan da ya fifita duk suna tsaye babu wanda yayi gigin biya mishi alhalin suna dashi, more especially 'yar gaban goshin sa wato Gwaggo Aisha, ga Baffan mu duk suna wajen taya zai iya kallon idon ta nan gaba?.
"Amma Mallam Hassan ka cika mugu azzalumi,wato yanzu a baka kud'in da zaka biya ni shine ka rike ka maida ni d'an iska wato inyi in gama ko? Allah ma yasa a gaba na aka aiko da kud'in da shikenan sai ka cigaba da raina min hankali kana cewa babu" yana banbani ya matso kusa da Baban mu ya kwace kud'in a hannun sa ya fita yana," Allah ya so ka Mallam".
Da ido kowa ya bi bayan shi har ya ida ficewa, bai san cewa mamaki ne daya cakud'u da mutuwar jiki su suka hana shi bayar da kudin ba, bai kara kallon kowa a wajan ba ya koma d'akin shi ya zauna a bakin gado tare da rafka uban tagumi yana tunanin ta yayane zai shawo kan Bintu yaci dad'i kuma ya samu na kashewa, dubu biyu fa?.
Can shi kad'a ya saki murmushin jin dad'i alamun ya samu mafita kenan.
A waje kuwa Baban mu yana shiga d'akin sa Baffan mu shima ya bar wajan yana tab'e baki dan bai ga dalilin da zai saka ya biya mishi bashi ba, da ace wannan kud'in yayi amfani dasu wajan ciyar da iyalin shine zai iya biya amma tunda kansa kad'ai ya sani bai san hakkin daya rataya akan sa ba shi ya sani yaje can ya karata.
"Allah sarki Bintu Allah dai yasa ba mugun halin kema kika fara kaman sauran matan ba saboda mugun halin d'an uwana duk shi ya jefa iyalin shi cikin halaka" yana magana ne tare da shigewa b'angaren shi.
Gwaggo Aisha da Inna Asabe duk sun kasa barin wajen suna tsaye a wajan kaman wanda aka dasa su kowacce da irin tunanin da take a zuciyar ta saboda Abin ya mugun daure musu kai sosai ita da duk gidan itace wacce bata dashi amma yanzu ta dara kowa a gidan.
Gwaggo Aisha fargaban ta d'aya shine kada Inna tazo ta kwace mata matsayi a wajan Baban mu domin ta san halin shi tsab zai iya juya mata baya dama saboda tafi kowa kud'i a gidan yake fifita ta, kai dole ne tayi wani abu akai dan ba zata tab'a zuba ido Inna ta ta kwace mata ba.
Da washe gari ina dawo daga makaranta a nesa na hango motan Abdulbasit a k'ofar gidan mu, aiko da gudu na karaso wajan motan cike da murna dan yanzu na daina tsoro tunda Innata da kanta take cewa inje mu gaisa bayan haka ga kayan dad'i da kullum in zai zo yake kawo min, yana zaune a ciki motan amma kafafun shi a waje hankalin shi yana kan wayar shi ban san me yake dan dannawa ba.
"Sannu da zuwa Yaya na" na fad'a da d'an karfi bayan na karasa kusa dashi,a d'an razane ya d'ago sai kuma ya saki murmushin sa mai kyau da baya barin fuskan sa.
"Har kin tsorata ni saura kad'an in ruga da gudu" ya ce yana dariya.
Nima dariyan na kyakyale dashi sannan na ce," toh ya zakayi da motan ka in ka gudu ka barta?"
"Sai in bar miki ita ki rink'a zuwa makaranta dashi" toh ai ban iya yanda ake tukawa ba" na fad'a a shagwab'e.
"Kada ki damu zan koya miki, kije ki cewa Aunty zan shigo mu gaisa".
Da toh na amsa sannan na juya na shige gida da sauri na, su Hajara duk sun tafi tallah iyayen nasu ma ban gan su ba da alamu duk sun fita.
Inna tana k'ofar d'aki tana shara na shigo da sallama ta amsa tana yi min sannu da zuwa,ciki na shige na ajiye jaka ta sannan na kara fitowa na ce mata," Inna Yaya yazo yana waje yace zai shigo ku gaisa".
"Ciki nan zai shigo yace?" Ta tambaya da alamun tsoro da damuwa akan fuskan ta, gyad'a mata kai nayi ina kallon duk yanda ta zama wani iri.
"Toh ya shigo" ta ce tana komawa d'aki ni kuma na fita waje na sanar dashi kan ya shigo, a bakin k'ofan d'aki muka tadda Inna zaune cikin tagumi amma tana ganin mu ta saki ran ta tana mishi sannu da zuwa.
Kallon gidan namu yake tare da nazarin sa,har k'asa ya duka suka gaisa da Inna a mutunce tare da bata hakurin rashin zuwan sa akai-akai kaman yanda yayi mata alkawari, nuna mishi tayi babu komai kana ta d'aura dayi mishi godiya tare da addu'oin gamawa da duniya lafiya.
Cikin jin dad'i yake amsawa da Ameen sannan ya mike yace zai wuce dai-dai lokacin kuma iska mai karfi ya d'aga d'an yalolon labulen mu karaf idon sa sai a d'akin mu da ko arzikin leda babu sai siminti dasu ghana must gon mu a gefe.
Tare muka fito dashi har zuwa wajan motan sa ya ciro manyan jakuna na shopping daya saba kawo mana ya mik'a min sannan ya kara da kud'i masu yawa yace in bawa Inna ince ta sayi carpet na tsakar d'aki dasu gado.
Cikin tsananin murna na dawo cikin gida da kaya niki-niki sannan na nunawa Inna kud'in daya bata tare da fad'a mata abinda yace tayi dasu.
Karb'a Inna tayi ta ajiye gefe ba tace komai ba dan yanzu zuciyar ta ta fara amincewa dashi sannan ta fara sabawa da lamarin sa.
Ni kuwa duk na k'ogu ta bud'e kayan domin na san duk tsaraba nane a ciki, tana bud'ewa kuwa sune ice cream da sauran kayan dad'i sai kaza gasassu biyu,ice cream na na d'auka na koma gefe na fara sha domin ni yafi min kaza sau dubu.
Da washe gari Inna ta sayo mana carpet d'in mu maroon mai d'an karan kyau harda katifan mu da sabon labule, murna a waje na ba'a magana muma munyi katifa kaman sauran 'yan gidan mu, a ranan da kyar Inna ta kirani waje domin tarewa nayi akan katifan.
A wannan rana mun ga hasada kiri-kiri a wajan matan gidan mu, Gwaggo Aisha tafi kowa shiga tashin hankali sai zage-zage take babu wanda ya kula ta sai 'yan koron tane suke taya ta.
Babu abinda zan cewa Allah sai Alhamdullilahi saboda rayuwar mu ta canza sosai yanzu muci mai kyau mu sha mai kyau mu kwanta a waje mai kyau hatta suturar da muke sakawa ya canza albarkacin Abdulbasit.
Mu muna nan zaune zuciya d'aya ashe bamu sani ba Gwaggo Aisha ta saka ana tayi mata bincike ta ina muke samun kud'i har rayuwar mu ta canza muka zama zara a cikin su.
Bata sha wahalan samun cewa wani saurayi mai kud'i ne yake taimaka mana ba, daga wannan rana ta saka ido sosai tana jiran zuwan shi,cikin ikon Allah duk lokacin da zai zo bata nan sai dai taji labarin yau yazo ya tafi.
A wannan lokacin Gwaggo Aisha duk yawon ta daina fita muka ga tayi a gida take wuni haka Hajara ma ta daina zuwa tallah kullum suna gida,ni na d'auka cewa sun daina tallah ne ashe wai ta gaji da kullum sai ta dawo daga gantalin ta taji cewa yazo har ya tafi shiyasa suka daina fita kullum hanya suke kallo suna jiran zuwan shi.
Sun kai kwana biyar da shiga kullen nasu Abdulbasit yazo yanzu mun saba sosai ni dashi dan har tambaya ta yake abubuwa da nake so, ni kuwa in kirgo mishi in zai dawo ya kawo min.
Ranan ma haka ya kawo min sautu da nayi mishi na kayan kwalliya shi kuma ya sayo min masu tsadan gaske kaman wata budurwa da kuma kayan makulashe daya zame masa jiki kullum zai zo sai ya kawo min, bayan ya gama zolaya ta na gama kuka na muka shirya na kwashi kayana na zan shiga ciki bayan nima na saba kullum in yazo sai na zolaye shi da in d'an b'uda murya ince," sannu da zuwa Yaya naaa".
Sai ya juyo a d'an razane yace," kin tsorata ni zaki sa in fita a guce" sai inyi ta kyalkyalan dariya.
A zaure na tarar da Hajara tana tsaye sai lek'e take ta sha kwalliyan ta na 'yan tallah fuska ya sha make up har yayi over.
Tana gani na ta had'a rai ta tsaya ni kuwa da hankali na na kuruciya ban kawo komai a raina ba nayi shigewa ta ciki, tana ganin na shiga ta fito da saurin ta zuwa wajan shi domin har ya shiga motan shi ya tayar saura yaja.
"Assalamu alaikum barka da war haka ya kyakkyawan d'an saurayi".
Fasa jan motan yayi ya tsaya kallon ta da wani irin fuska sannan ya ce," meke tafe dake?".
Juya ido tayi mishi irin na jan hankalin nan sannan ta ce," haba yanzu har sai nayi maka bayanin abinda yake tafe dani,me budurwa zata nema a wajan saurayi? Koda yake bari in fito in fad'a maka yanda zaka gane.
Naga kana wahalar da kanka akan wancan 'yar karamar yarinya, bayan gani na had'a duk abinda kake nema zan saka ka farinciki domin babu abinda zaka nema a waje na ka rasa" ta karasa tana kara matsowa jikin motan tana girgiza mishi kirji.
Kallon takaici da kyama ya bita dashi sannan ya ce," pls matsa min ka jikin mota kada kisa min k'azanta a jiki".
Kasa matsawa tayi ta tsaya da idanuwa a waje tana kallon shi dan tunda take ba'a tab'a ci mata mutunci haka ba duk yanda taci kwalliya nan yace wai zata shafawa motan shi k'azanta , a firgice ta koma baya jin ya fisgi motan da matukar gudu saura kad'an ya take mata k'afa ya tafi ya bar ta a wajan.
Da hawaye shame-shame ta shigo gida tun daga bakin kofa ta fara ihu tana magana," ni Gwaggo wallahi baki ga wulakaci......" Da hannu Gwaggo Aisha tayi mata alama da tayi shiru, kama hannun ta tayi suka shige d'aki.
A kwana a tashi ba wuya a wajan Allah dan yanzu har munyi exam na third term muna hutu in mun koma kuma zamu shiga j.s.s 2.
Ranan nan muna wasa a k'ofar gida da kawaye na 'yan mak'otan mu naga Baban mu yana dawo wa gida ban kula ba dan shima ba kulanin yake ba kuma ya tsani in kula shi dan ma yanzu da sauki naga ya rage tsana da yake nuna min.
Bulala naga ya d'auka yayi kaina gadan-gadan zai zane ni bansan hawa ba ban san sauk'a ba, da gudu na kwasa nayi cikin gida ban tsaya a tsakar gidan ba na wuce d'akin mu sanin cewa baya tab'a biyo ni, Inna tana raba gasassun kaji da Abdulbasit ya kawo na fad'a d'akin ina haki.
Inna barin abinda take tayi ta kama min fad'an waye na tsokono zan fad'o mata d'aki haka?
"Inna wallahi ba tsokana nayi ba muna wasa ne sai naga Baban mu....." Had'iye sauran maganan nayi ganin Baban ya d'aga labule ya shigo, bani ba har Inna sai da ta zaro ido tana kallon shi da matukar mamaki.
"Ke yanzu Bintu haka ake tarbiyan 'ya mace yarinya ta fara girma amma ki bar ta tana wasa a waje sai kace namiji" yana maganan ne idon shi na yawo a d'akin har ya sauk'a kan kajin da suke gaban inna, mukut ya had'iye yawu tare da tsura musu ido shiri.
"Toh Mallam ayi hakuri insha Allah za'a kiyaye gaba" tana gama fad'an haka ta ture tiren da kajin suke ciki gefe tare da rufewa da wani tiren.
*Albishirinku mata masu son kamshi da gyara ga dama ta samu zamu fara classes na koyar da turaren wuta kala-kala humra shima in different colors dilke gyaran amarya man gashi nd lots more kada ko yarda a baki labarai akan 300 kacal zaki zama pro na kan ki, duk mai bukata ta tuntubi wannan no 08172724281 sai mun ji ku*.
[9/8, 5:01 PM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
_A story about love and sacrifice._
_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_
_*From The Fantastic Writer of*_
```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```
*_And now_*
*_BA SONTA NAKE BA_*
*âœâœ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶Ãt̶̶є αs̶̶s̶̶Ãd̶̶Ãσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єÃv̶̶є n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶Ãc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶Ãv̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✠*,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ Ãt̶̶ w̶̶Ãl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶.*
*Abin da ake fada idan za a yanka dabba, ko za a soke ta.*
Ø¨ÙØ³Ù’م٠الله٠والله٠أَكْبَر٠اللَّهÙÙ…ÙŽÙ‘ Ù…Ùنْكَ ولَكَ اللَّهÙÙ…ÙŽÙ‘ تَقَبَّلْ Ù…ÙÙ†Ùّي.
Bismil-lah wallahu akbar, allahumma minka walak, allahumma taqabbal minnee.
Da sunan Allah, kuma Allah ne Mafi Girma. Ya Allah! (wannan dabba) daga gare Ka take, kuma mallakarka ce. Ya Allah! Ka karba daga gare ni.
*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._
*8*
Karasa shigowa d'akin Baba yayi tare da yiwa kan shi masauki kan katifan mu yana kallon rufaffen tiren ya ce," haba Bintu yanzu iya abinda zaki ce kenan, Fateema ta fara girma sai da saka ido sosai fa".
Cike da mamakin furucin sa ta ce," naji Mallam za'a kiyaye gaba insha Allah" a zuciyar ta kuwa bata daina mamakin wannan sabon al'amarin ba domin ita dai tunda take a gidan bata tab'a ganin ya damu da 'ya'yan matan shi da yake so ba balle 'yar ta da kullum sai ya tsaya a tsakar gida yace ba son su yake ba
shiru ne ya biyo baya a d'akin,ni ina can bayan Inna ta saboda tsoron bulala duk da ya ajiye ta tuntuni naki fitowa, ita kuma Inna al'ajabin me ya zaunar dashi har yanzu a d'akin take gashi tana so ta gama rabon kazan in kaiwa wayan da take bawa kullum.
Mun kai minti kusan ashirin muna zaune shiru babu mai magana shi ya gaji da zaman kurame da muke ya d'an gyara zama yana kallon tiren ta gefen ido ya ce," naga kaman aiki kike Bintu dana shigo ko, toh ki karasa abin ki mana, in ta nine babu matsala Wallahi".
"Haba Mallam ba haka bane na riga da na gama ne shiyasa". Ta amsa mishi.
"Kin gama, me kika gama?" Ya tambaya tare da kafe tiren da ido.
"Rabo nake kuma na gama saura in bawa Zareefa ta kai" Inna ta amsa mishi cikin k'osawa da zaman nashi a d'akin.
"Toh su waye kuma zaki aikawa?"
"Maman Dije da Maa saboda sunyi yawa ga Zareefa ba ci take ba shiyasa nake aika musu".
"Ikon Allah amma Bintu kina da abin mamaki, ya za'ayi ki aikawa wasu alhalin ga 'yan gida nan, ko kin manta da nine?"
Cike da takaicin halin sa ta girgiza mishi kai sannan ta d'auko wani d'an gutsuri kad'an ta mika mishi jiki na rawa ya karb'a ya fara ci yana," kai amma Bintu baki da dama yanzu haka kike cin dad'i kuma ki manta uban 'yar ki?"
Ita yanzu inna halin nashi tsoro ya fara bata ya za'ayi kana magidanci mai iyali baka damu da ka samu ka kawo musu ba sai dai in ka gani a wajan su jiki na rawa ka karb'a, dubi yanda yanzu jiki na rawa yake neman a bashi kaza bai damu da tambayan a ina kika samu ba, sata ko maita ko karuwanci duk kiyi in dai zaki bashi to kece ma 'yar gaban goshin sa.
"Dama da yunwa na shigo kin ganni nan har wani juwa nake gani, Allah yasa da akwai abinci d'akin nan" yace yana faman tsid'e yatsu.
Girgiza kai Inna tayi sannan ta ce," babu abinci Mallam ba muyi girki ba sai...."
"Inna ki bashi nawa da kika ajiye min yaci dan ni nasha ice cream ba zan ci ba". Na katsewa Inna hanzari.
"Yauwa 'yar albarka, Allah sarki yarinya mai tausayin Baban ta" Abba yace cikin jin dad'i yana washe baki.
Inna tsuke fuska tayi tana jin kaman ta kamo ni tayi ta kirb'a sai yau ya san dasu a gidan a baya in ta aika mishi abinci kora ta yake hmmmm sai yau, ba dan taso ba ta tashi ta d'auko mishi hadaddiyar warmer sabuwa da ta sayo mana muke zuba abincin mu a ciki ta ajiye a gaban shi.
Cikin sauri Baba ya bud'e warmer, ba shiri ya lumshe ido saboda kamshi mai dad'i daya bugi hancin sa, yana bud'e ido sai da ya had'iye wani yawu ganin shinkafa da miyar kaza , ko ruwan wanke hannu bai nema ba ya tsoma hannu ya fara aikawa cikin sa hannu baka hannu kwarya.
Ni kuwa duk dad'i ya cika ni yau muma Baban mu ya shigo d'akin mu kaman sauran 'yan gida har yaci abincin mu tsab'anin Inna da duk zaman shi a d'akin namu ya takura ta saboda bata saba ba kuma ta san ba wai matsayin ta da yake kiran ta dashi a baya ba son ta yake bane ya canza a'a sai dan kwad'ayin abin hannun ta wanda ita kuwa ba zata so ya shiga jikin ta b sam..
Yana cikin cin abincin naje inda Inna take ajiye min juices da bobo
na d'auko mishi orange juice na ajiye a gaban shi.
"Ikon Allah shi kuma menene wannan 'yar albarka?" Ya tambaya cikin matukar farinciki.
"Lemon kwali ne Baba" na bashi amsa nima cikin jin dad'in sabon sunan da yake kira na dashi.
Balle murfin yayi ya kafa kai ya fara sha bai sauke ba sai da ya kusan shanyewa sannan ya ajiye yana tsid'e baki ya ce," wai..wai...wai.... Ikon Allah wai lemon kwali kika ce ko?" Ya kara tambaya bayan ya d'auko katon chicken breast a cikin abincin ya fara figa.
Ina dariya na amsa mishi da " eh Baba" Inna dai ko kallon mu batayi ta cika tayi fam jira kawo take ya fita tayi magani na.
Baba bai bar d'akin ba sai da ya gama cinye abincin harda lashe warmer sannan ya mike yana kallo na ya ce," 'yar albarka kada ki manta da Baban ki, ki rinka tunawa dani in kin samu kayan dad'i kinji ko?" Cikin jin dad'i na amsa mishi sannan yayiwa Inna sallama ya fita.
Yana fita muka ji muryan Gwaggo Aisha tana shewa ta ce," ahaiyye nanaye yau me nake gani jama'a kuzo ku tayani duba ko dai ido na ne yake min gizo?"
"Ba gizo idon ki yake miki ba nine nan Mallam Hassan kuma daga d'akin Bintu na fito ko kina da magana ne?" Baba ya b'ata amsa yana cire nama daya mak'ale mishi a hakori.
A yanzu yana dai-dai daya b'ata da kowa a gidan in dai akan Bintu ne, haba yaushe rabon daya ci kaza ko shinkafa da miya ita in banda aukin shinkafa da wake me take bawa mutum ko naira d'ari ko d'ari biyu amma ga Bintu kwanaki bashin dubu biyu ta biya mishi a take,gaskiya dole ne ma ya mak'ale a wajan ta.
Yana gama bata amsa yasa kai ya fice abinsa ya bar Gwaggo Aisha da ihu tana," aikin banza aikin wofi wato ta nan kika biyo dad'in abin kowa ya san dai sunan ki a gidan nan ba sonta nake ba, shine dai sunan ki".
Inna tana jinta bata tanka ba saima kamo ni da tayi zata daka akan abinda nayi Allah ya taimake ni ya jefo Maman Dije ta kwace ni tare da nuna mata kada tayi haka saboda koma ya yake ba'a tab'a canzawa tuwo suna ba, duk abinda zasuyi suyi tsakanin su amma kada ta sakani a ciki.
Da wannan nasihan Maman Dije na tsira ba'a jibge ni ba.
Tun daga wannan rana Baba ya maida d'akin mu wajan hiran sa duk da yanda Inna take tsuke fuska baya damun sa in dai zai shigo ya samu abin tab'awa, ni kuwa duk dad'i ya cika ni yanzu Baba na shigo mana kuma ya daina hantara ta saima sabon suna daya lika min wai 'yar albarka.
Inna kuwa duk rawan kafar da yake yi akan mu ba wani burge ta yake ba domin ta san dan abinda yake samu shiyasa har yake ihu da 'yar lelen shi wato Gwaggo Aisha, ta ina ma zata manta abubuwa da yayi mata na shekara da shekaru dad'in bakin sa na lokaci kad'an d'in nan ba zai tab'a goge tabo dake cikin zuciyar ta ba.
Abin takaici ma har yau bai tab'a yunkurin tambayan ina Inna ta ya take samun kud'i da har take wayan nan abubuwan ba, kuma wani ikon Allah bai tab'a had'uwa da Abdulbasit ba dan haka bai san daga inda muke samun kud'i ba.
Tsakani na da Abdulbasit kuwa wani shakuwa ne na ban mamaki ya shiga tsakanin mu ada yana kaiwa sati ko fiye kamin yazo gidan mu amma yanzu baya iyawa dan ana kwana 2 zai zo mu sha hiran mu yana sai dai mafi yawan hiran tsokana ta yake wai ya ganni da saurayi da sauran su ni kuwa insha kuka na in more daga baya kuma mu shirya abin mu ya tafi.
Rayuwa yanzu tayi mana dad'i sosai dan bamu da maraba da masu kud'i tunda duk abinda masu kud'in suke ci suke sha suke sakawa muma haka ni da Inna ta duk mun murmure harda d'an kumatu mukayi.
Gwaggo Aisha da Inna Asabe kuwa duk hankalin su a tashe yake ba ma kaman Gwaggo Aisha dan kiri-kiri ta rasa matsayin ta ya koma kan Inna tayi duk abubuwa da zatayi amma duk a banza dan gwara da yana d'an sauraron ta amma tunda ya shigo d'akin mu ranan ya tarar da Inna tana kirga kud'i sun kai kusan dubu hamsin a hannun ta tun daga wannan rana ya kara haukacewa kasancewar ko shi da yake d'a namiji bai tab'a rike irin wannan kud'i ba.
Ganin duk ya rikice yasa Inna ta bashi dubu biyar a ciki a ranan kaman yayi mata sujada haka ya kwantar da murya yana mata godiya.
Daga wannan ranan mulkin gidan ya koma hannun Inna ta dan Baban mu ya zama kaman wani bawan ta duk abinda tace baya musu balle ya karyata ta cin mutuncin kowa yake a gidan saboda mu.
.
Mun koma makaranta mun shiga jss 2 cikin farincikin sabon uniform da Abdulbasit ya d'inka min dasu sabon jaka da sauran kayan amfani na makaranta, tsab dani na koma kowa ma sai sha'awa ta yake masu tsokana ta da kuma yanzu sune suke bi na wai suna sona da k'awance.
Na biye musu nima duk abinda na kai makaranta na kayan kwalama ina basu ko in sun ce in saya musu wani abu bana kyashin saya musu amma fa ba wai na manta abinda suka min bane sai dai na barwa Allah ne.
A kwana a tashi ba wuya a wajan Allah dan yanzu muna jss 3 komai na alamun girman 'ya mace duk sun bayyana a tare da ni kyawu na ya fito sosai, shakuwa da yake tsanani na da Yaya na ya rikid'e ya koma zallan soyayya, dan sosai yake nuna min abinda ke cikin zuciyar shi tun ina had'awa da kuruciya har ni da kaina na fahimci na fad'a son Yaya na sosai kullum zai zo mu sha hiran mu da kyar zai daure ya tafi, daya ga hakan ma ba zai wadatar dashi ba ya sayo min dankareriyar waya ta wanda kullum ya kasance muna cikin communicating.
Wannan waya da Yaya na ya saya min gaba d'aya ya d'agawa Gwaggo Aisha da Hajara hankali harda Jameela wacce take ganin sa'anni muke da ita.
Ban san ko ta yaya abin ya kasance ba sai dai gani nayi itama wani mai mota yana zuwa wajan ta hira, daga ranan da mai motan ya fara zuwa a ranan ta sallami duk sauran samarin ta dan dukan su babu mai mota a cikin su dama lallab'a su take.
Tun daga wannan rana su Gwaggo Aisha suka fara d'aga murya a gidan komin kankantar abinda ya kawo mata sai an fito tsakar gida ana maimaitawa ana yi mana iyayi a gida, mu dai ko a jikin mu amma Inna Asabe duk ta damu dan tana da 'ya Hasiya kuma sa'ar Hajara ce, Allah ya jarabce ta da bakin jini babu wanda ya tab'a zuwa wajan ta .
Yawanci Yaya na in zai zo wajena sai bayan la'asar yake zuwa kuma Baba baya zuwa gida a wannan lokacin amma a yau bayan azahar yazo saboda wai zaiyi tafiya amma ba dad'ewa zaiyi ba gobe zai dawo, muna cikin hira na hango Baba ya nufo gida sai gyara binjimar jikin sa yake, dum naji zuciya ta ta buga dan daga ni har Inna ta bama son Baba ya had'u da yaya na dan zai iya tafka abin kunya dan shi ba damuwar shi bane.
Motan yabi da ido ya gan mu tsaye a gefe kaina a kasa dan bana son yayi min magana amma banyi nasara ba.
Yana gani na ya nufo inda muke cikin sauri yana," a'a 'yar albarka kece anan?"
Kamin in bashi amsa Yaya na ya durkusa har kasa ya fara gaishe shi, cikin washe baki yake amsawa yana bin katuwar motan shi da kallo .
*Albishirinku mata masu son kamshi da gyara ga dama ta samu zamu fara classes na koyar da turaren wuta kala-kala humra shima in different colors dilke gyaran amarya man gashi nd lots more kada ko yarda a baki labarai akan 300 kacal zaki zama pro na kan ki, duk mai bukata ta tuntubi wannan no 08172724281 sai mun ji ku*.
[9/17, 9:01 PM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚 🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
_A story about love and sacrifice._
_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_
_*From The Fantastic Writer of*_
```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```
*_And now_*
*_BA SONTA NAKE BA_*
*âœâœ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶Ãt̶̶є αs̶̶s̶̶Ãd̶̶Ãσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єÃv̶̶є n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶Ãc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶Ãv̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✠*,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ Ãt̶̶ w̶̶Ãl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶.*
*Addu'ar Wanda Ya ji Tsoron Faruwar Wani Abu Mummuna saboda Kambun Baka*
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Idan dayanku ya ga wani abu da ya kayatar da shi ga dan uwansa, ko ga kansa, ko ga dukiyarsa, to ya roki Allah ya sanya albarka gare shi; domin kambun baka gaskiya ne.
*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._
*Kuyi hakuri kunji ni shiru kwana biyu kun san jiki da jini sai a hankali amma yanzu Alhmdllh naji sauki, wayan da suka kira da wayan da suka turo sakonni duk ina godiya da kulawar ku Allah ya bar kauna.
Nagode sosai*😘😘😘
*9*
"Lafiya lau yaro.... lafiya lau" Baba ya amsa yana had'iyar yawu yana kara karewa motan kallo, ni dai sanin zai kwafsa min yasa ko d'ago kaina na kasa yi bare mu had'a ido da shi.
Yayana kuwa yana gama gaishe shi bai d'ago daga tsugunen ba yayi kasa da kai yana jiran Baba ya bar wajan, Baba ba dan yaso ba yaja kafa zuwa cikin gida yaso ya samu wani abu wajan mai tsallen motan nan, amma ba komai bari yaje wajan Bintu zai ji ko wanene shi d'in.
Wata b'oyayyen ajiyan zuciya na sauke ganin ya wuce gida salin-alin ba tare da yayi wani abu daya tsinka ni ba, nabi bayan shi da kallo kaman yanda shima Yaya na yabi sa da kallo sai faman gyara mayattacen binjimar sa ta tshohuwar shaddar sa fara ce amma saboda tsufa har ta koma ruwan toka .
"Allah sarki Allah baiyi zamu had'u da Baba ba duk shekaru nan ba sai yau" naji Yaya na ya katse min tunanin da nake.
Murmushi nayi ina gyada kaina.
"Amma nima ban kyauta ba da ban tab'a tambayan shi ba all this while,wallahi yanzu dana gan shi sai naji ban kyauta ba sam" ya kara fad'a cikin damuwa sosai.
"Laa! Kada ka damu Allah ne baiyi zaku had'u ba tun farkon amma yanzu daya so ba gashi kun had'u ba" na bashi amsa ina murmushi.
Shiru kawai yayi dan shi a tunanin shi rashi da iyali ne yayiwa Baban yawa shiyasa ya zama haka bai san cewa duk wani yanayi da hali da mutum zai gan shi a ciki shi ya jefa kan sa ba.
Har muka gama hiran mu a ranan yana cigaba da nuna min rashin jin dad'in sa ni kuma ina nuna masa ba komai da zai tafi dubu ashirin ya bani wai in bawa Inna ta ajiye min in case wai ko goben ba zai samu dawowa ba, na nuna mishi muna da komai ba sai ya bani kud'i ba amma yaki karb'a saima shopping bags daya maida farilla wajan kawo min su ya lodo min kusan su 3 yana complain wai dole ya nemawa inna fridge ko dan saboda rana irin ta yau, kasancewar na saba kullum sai ya kawo min ice cream na sha toh gashi gobe baya nan da Inna tana da fridge sai ya sayo dayawa a saka min a ciki ko na kwana nawa ne.
Amma tunda ya bani 'yan canji a hannu in naga ba zan iya hakura ba sai inje today's ko sidis in sayo abina in sha tunda na saba sha.
Ni dariya nayi ta masa ganin duk ya damu akan wai kawai ba zan sha ice cream gobe ba, in ba dan ba dan ba a da ina na san wani ice cream a rayuwa ta, dan gobe kad'ai ban sha ba me zai same ni, bai kyale ni.ba sai da nayi masa alkawarin zan je in sayo a today's d'in sannan ya hakura mukayi sallama ya tafi tare da bani hakurin inda zai tafi babu service dan haka ba zamu waya kaman yanda muka saba ba.
Haka ya wuce duk sai naji na damu domin sosai na saba kullum sai naji muryan shi nake iya bacci yanzu haka muryan sa shi ke tada ni a bacci.
A tsakar gida na tarar da Gwaggo Aisha da wata 'yar figaggiyar kaza guda d'aya ta saka a tire ta d'auko sharb'eb'iyar wuka sai faman kacan canawa take tana ta hura hanci,ni dariya ta bani ban ma kalli inda suke ba nayi shegewa ta d'akin mu anan na iske Baba yana zaune yana zaman jiran in shigo yaji karin bayani dan duk yanda yaso ji Inna kin bashi had'in kai tayi saboda ta san ba dan Allah yake neman sanin ba.
"'Yar albarka har kin shigo kenan"
"Eh Baba sannu da hutawa" na amsa ina ajiye kayan hannu na kusa da Inna amma kud'in yana hannu na cikin hijabina.
Ko kallon kayan Inna taki yi ta cigaba da d'inkin hulan ta hankali kwance, gefe na samu na zauna shima Baba zama ya gyara yana jiran Inna ta bud'e yaga menene a ciki amma ta basar, can daya gaji da zama ya ce," 'yar albarka me kika shigo mana dashi ne?"
"Kayan dad'i ne Baba na" na bashi da murmushi akan fuska ta ina kallon Inna ta gefen ido da take harara ta.
"A'a toh...toh... Wato Bintu yau kuma rashin kirkin ne ya tashi muna ji muna gani zaki hana mu kayan dad'i?" Cewar Baba cikin raha, Inna dai bata ce k'ala ba ta cigaba da d'inkin hulan ta.
"Mu kam bama zuciya kuma ba inda zamu je sai mun ci kayan dad'i ko 'yar albarka?"
Dariya nayi ina kallon Inna da tayi kicin-kicin da fuska dan ita al'amarin Baban mu sosai yake bata takaici da haushi, ya za'ayi ace wai kana ganin 'yar da ka haifa ta shigo da kaya masu yawa haka kuma kasan daga hannun saurayi ta samu, baka damu da binciken waye shi ko kuma ya akayi ya bata ko meye tsakanin su ba, saima jiki na b'ari kake son handame abinda ta kawo koma menene kai ba damuwar ka bane.
Cike da takaici halin sa da surutan sa daya ishe ta, ta bud'e d'ayan jakan da ta riga ta gane tambarin su kasancewar kullum ana kawowa, ba tare da ta lura da ko kaza nawa ne a ciki ba ta d'auko guda d'aya ta saka mishi a wata leda da babban roban juice d'aya duk ta had'a ta mik'a mishi .
Ba batun fushi ko zuciya yasa hannu yana washe baki ya amsa har zai fita na tsaida shi nima na jawo d'ayan jakan sanin cewa nawa shi saboda kullum aka kawo Inna bata tab'awa tarkacen kayan zaki na ne a ciki, roban ice cream babba dasu chocolate dasu snacks ne a ciki nima na cika mishi leda na mika masa harda dubu biyar na saka masa a kasan ledan bayan na faki idon Inna.
Ai Baba yanda kasan yayi hauka haka ya koma saboda murna dan akan idon shi na had'aa mishi kud'in yayin da Inna kuma hankalin ta yana kan hulan ta saboda dukkan mu haushi muke bata.
Fita yayi yana baza babban rigan shi, zai wuce Gwaggo Aisha ta tare shi da cinyar kaza a hannu cike da jin kai ta ce," Mallam tsaya ka saka albarka kaga 'yar ka Hajara Allah yayi ta samu saurayi mai mota, shine daga zuwa zance ya kawo mata gashasshiyar kaza na rabawa yara shine nace bari kai ma in kawo maka ka saka albarka".
"Amma Aisha kike kowa? Wallahi kin matukar raina ni, ni zaki tara ki tsamma wannan abu sai kace kin samu wani kwadayayye ko maye, toh tsaya kiji ni na fi karfin wannan abin naki mai kama da cinyar fara.
Dubi kiga inda ake cin arziki da kaza kuma aka san darajan miji ba watsatsu irin ku ba" yana magana yana nad'e hannun babban rigan sa nan manyan ledojin suka bayyana.
" Kinga wannan dakwaliyar kaza ce ta gidan gona da taji gashin inji ga lemon roba mai dad'in gaske, sannan kinga nan kuma kayan makulashe ne da sai in rantse da Allah ko wuka aka d'aura miki baki tab'a ganin irin su ba balle ki san sunan su, bayan nan kalli kasan kiga" yace yana nuna mata kud'in kasan ledan sannan ya mike tare da mai da komai cikin ledan ya cigaba da masifa," na dai gaya miki kada ki kara tare ni da maganan banza ko ranki yayi mugun b'aci ba abinda kika iya sai shegen surutu tsiya " nan ya shige d'akin shi ya bar Gwaggo Aisha da mataceccen jiki.
Tabbas sai sun sake shiri babba ma kuwa dan bata tab'a sanin haka Bintu tayi nisa ba,gaskiya dole ne ta nemi shawaran aminiyar ta dan samun mafita ko kuma suna ji suna gani wankin hula zai kai su dare.
Dariyan yaran gida ne ya dawo da ita hayyacin ta, sun had'a kai kusan su biyar suna mata dariyan yanda Baba ya bar ta da cinyar kaza a hannu, bata kula kowa a cikin su ba ta shige d'akin ta dan ji tayi gaba d'aya jikin ta ya mutu.
A d'aki kuwa Baba yana fita Inna har ta juyo da niyyan yi min fad'a dramar su da Gwaggo Aisha ya dakatar da ita, bayan sun gama ya wuce ya bar ta na ce," haba Inna ta, me yasa kike fushi haka yanzu fa kin zama 'yar lele a gidan Mallam".
Waje na fice da gudu da roban ice cream d'ina d'aya a hannu ina dariya ganin Inna ta shiga neman abinda zata buga min a kusa da ita bata samu ba.
Ciki na shiga b'angaren su Dije muka zauna sha muna hiran Yaya ina bata labarin yanda yau muka rabu da juna dan kawai zaiyi tafiyan kwana d'aya.
"Hmmmm gaskiya ke kam Zareefa Allah ya baki, ki ga yanda yake mutuwan son ki kuma yake nuna kulawa yake tarairayan ki, a gidan ku ma ya kula dake haka ina ga ya aure ki ya killa ce ki a gidan sa abin ba magana". Cewar Dije kenan.
"Allah gaskiya soyayya akwai dad'i Dije, kin san yanda nake jin sa a cikin raina kuwa? Allah ya nuna min ranan auren mu" duka Dije ta kai min a gadon baya na tana dariya tace.
"Shegiya Zareefa har nawa kike da zaki zauna kina maganan aure?" Murkud'a mata baki nayi ina ," eh d'in kema ai shirin yi miki ake nan da shekara d'aya idan munyi sauk'a, toh nima ina gama secondary shekaru biyu da rabi suka rage za'ayi mana ni da Yaya naaa" na karasa ina rungume hannye na biyu a kirji na tare da rufe ido nayi baya kaman zan fad'i Dije ta taro ni tana tafa hannu ta ce," ke yarinyan nan haka kika zama baki tafasa ba zaki kone mana mu shiga uku?"
"Wai da kike fad'an haka shekaru nawa kika bani da kike ta cika baki tun d'azu , ina biyu ne kawai harda wani ........ zaki kone mu shiga uku" na fad'a cikin kwaikwayon muryan ta, ta kai min duka na goje haka muka cigaba da shan ice cream muna hiran mu cikin raha..
Dije itace babban 'ya a wajan Maman Dije ta bani kusan shekaru biyu amma hakan bai hana mu zama kawaye ba domin yaran gidan dukan su iyayen su sun hana su wasa dani tun muna yara dan haka babu wani shakuwa ta 'yan uwan taka tsakanin na dasu sai dai kallon kallo.
Ba Yaya na kad'ai ba nima na shiga damuwa sosai na rashin sa a kusa da ni, cikin kwana biyu da yayi baya nan duk sai na zama kaman ba ni ba abinda yafi tayar mun da hankali rashin samun sa a waya, duk da ya gaya min inda zai tafi ba service amma hakan bai hana ni kwana da waya a hannu ina gwadawa ba, Inna tana ankare dani amma bata ce min cikan ki akai ba.
A ranan da ya cika na uku ne kiran shi ya shigo min yana fara ringing na d'aga cikin d'auki na ce," wayyoo Yaya naaa"
"Na'am k'anwa taaaa" shima yaja kaman yanda nake jan nashi.
Dariya muka sanya dukkan mu sai da mukayi mai isar mu kaman sabobbin kamu sannan ya ce," na kusan shigowa gari k'anwa ta, insha Allah gobe war haka muna tare"
Tsalle na daka da wayan a kunne na na ce," yessss Alhamdullilahi Allah ya shigo da ku lafiya Yaya na" da Ameen ya amsa sannan ya katse kiran.
Dije da take gefe tana min dariya tare da min signal ga Maman su a kusa inyi a hankali ko kula ta banyi ba, ita kuma Maman Dije murmushi kawai tayi tana girgiza kai ta shige kitchen d'in ta ta kyale mu tana mamakin wai yarinya kamata da iya soyayya, hmmm duniya kenan in da ran ka zaka sha kallo.
Zama nayi tare da rafka tagumi ina tunanin ya kamata nima ko sau d'aya ne in kyautata mishi yanda yake kyautata min kullum ko ba komai shima zai ji na damu da shi.
"Ke kuma lafiya, ba yanzu naga kina murnan masoyi zai dawo ba kuma inga kin zabga tagumi kina tunani kaman wacce akaiwa mutuwa?" Cewar Dije kenan.
"Dije kawai so nake inyi wani abu da zai faranta ran Yaya na tunda bai tab'a tafiya ba shiyasa nake son inyi wani abu na tarban shi".
"Gaskiya kinyi tunani mai kyau Zareefa in dai akwai kud'i a hannun ki ni zan taya ki ko abinci ne kiyi mishi".
Cikin jin dad'i na amsa mata da akwai kud'i a waje na, nan da nan muka tsara yanda zamuyi da abinda zamu girka masa.
Da washe gari tare muka je kasuwa muka sayo doya da nama sai kwai creast d'aya da mai muka dawo, gidan Maa muka kai kayan da muka sayo da taimakon Dije mukayi mishi yam balls da kwai cikin kwai da yake shine sana'an da suke ta kware sosai, Maa kuma tayi mana dambun nama mai dad'in gaske.
'Yan kulolli da Inna ta fara min tarun su nan gidan Maa na fito da set d'aya muka zuzzuba a ciki muka shirya a cikin tiren plastic mai kyau shima cikin kayan tarun muka d'auko.
"Kinga yanda kayan nan sukayi kyau kuwa kuma sunyi dad'i da zamu had'a da kunun aya mai sanyi zai fi tafiya" Dije ta kawo sabon shawara nima ba b'ata lokaci na amince sanin yanda shima Dije ta kware da yin sa shima suna sayarwa amma a lokacin zafi.
Da yake mu biyu ne bamu b'ata lokaci ba shima muka had'a ta muka zuba jug na glass haddade muka saka kankara, ni sai a ranan ma nasan na san cewa Inna tayi min taru dayawa haka, sai da muka gama tsab sannan muka wuce gida dan inyi wanka in shirya ita kuma Dije zata fita sana'a ta.
Sai da na shigo Inna ta rutsa ni da tambayoyi ina naje tun dazu?
Na amsa mata da ina gidan Maa tace karya nake bata yarda ba ta kira yaro ina gani ta tura gidan Maa dan a tambayo mata ni dai na shige wanka dan ina gudun kada Yaya na ya dawo ban shirya ba.
Ko da na fito daga wankan bata kuma kula ni ba da alama an tambayo mata Maa,sai da nayi sallah naci ado na da riga da skirt na lace pure cotton dark blue ya sha adon flowers pink, sosai kayan suka min kyau domin Yaya na ya iya zab'en kayan da zasu yi min kyau.
Inna duk tana kallon sabon falli da nake bata min magana ba sai da na gama sannan ta zaunar da ni ta fara min nasiha kan rike mutunci na na 'ya mace a duk inda nake, duk da ta amince da Abdulbasit amma tace kada in kuskura in bar shi ya rike min ko da hannu nane tunda shi ba muharrami na bane kuma ba aure na yayi ba, in ko na bari hakan ta kasance toh tabbas ciki ne zai bayyana a tare da ni wanda har jikokina zan barwa wannan bakin fenti.
Sosai Inna tayi min nasiha daya kashe min jiki ba shiri na fad'a mata duk abinda mukayi a gidan Maa, nan tace ai ba wani abu bane kyautatawa wanda yake kyautata maka,kar inji komai in dan wannan ne ko yaushe na tashi yi inyi anan gida bai sai naje gidan Maa ba.
Cikin jin dad'in fahimta da tayi muka zauna muna hira cikin dabara ta cigaba da wayar min kai akan zaman duniya da kalubalen da yawanci 'yan mata ke fuskan ta wajan kwad'ayi da bin maza kuma daki-daki suke shiga kaina, kiran wayan Yaya na ne ya katse mana hiran na saka hijabi na fito.
Center kofan gidan mu yake kallo fuskar shi d'auke da murmushi na musamman, yana gani na ya kara fad'ad'a murmushi nasa cikin sabon takun da na koya saboda shi na karaso gaban shi sai dai ina zuwa na b'ata fuska ta.
Cikin d'an damuwa yake tambaya ta me ya faru kuma nake b'ata fuska?
"Ba kai bane yau baka kallon waya na fito balle in tsorata ka yanda na saba" na bashi amsa a shagwab'e.
Dariya yayi yana shafa gashin kansa da hannun sa ya ce," ayi min afuwa k'anwa ta yau d'in ne nayi missing d'inki dayawa shiyasa na kasa hakuri har ki ban tsoro"
"Nima nayi missing d'inka sosai Yaya naaa"
"Ina son ki k'anwa ta"
Rufe fuska ta nayi ina dariya kasa-kasa sannan na bashi amsa da ," nima ina son ka Yaya naaa".
A take na bud'e fuska ta tunawa da nayi da abincin da na had'aa mishi a gidan Maa.
"Dan Allah bani minti biyu ina zuwa" ban jira amsar shi ba nayi gaba na kira Bakura wani yaron makotan mu muka tafi tare na d'aura mishi tiren akai ni kuma na d'auko jug d'in muka dawo wajan shi.
Tunda muka fito yake kallo na da mamaki har muka iso bai iya d'auke idan shi daga kaina ba,
"Ban san a ina zan ajiye maka ka ci ba,ko zaure zan saka maka tabarma?"
Girgiza kai yayi tare da nuna min motan shi, ban musa ba yayi gaba muka bi bayan shi ya bud'e seat na bayan motan ya karb'i tiren akan yaron ya saka a ciki sannan ya min nuni da in shiga ciki nima.
Sororo nayi da jug a hannu na kasa shiga kasancewar ban tab'a shiga motan shi ba kuma ga nasiha da Inna ta min d'azu, sai da ya shiga ya zauna ya ganni nan tsaye banida niyyan shiga.
Kara cewa in shiga yayi nayi shiru ni ban shiga ba kuma ban tafi ba sai raba ido nake nan ya fahimci cewa tsoro nake,sai da ya nuna min cewa tunda ban yarda da shi duk shekaru da muka d'auka tare in d'auke abinci na baya ci.
Ganin kaman ran shi ya b'aci yasa na d'an dosana duwawu na kad'an na zauna, yana murmushi yace toh in bud'e yaga me na dafa mishi mai dad'i.
Ina bubude mishi ya ce," iyye lalle k'anwa ta an girma,ke kika girka min ko Inna ce?"
*Albishirinku mata masu son kamshi da gyara ga dama ta samu zamu fara classes na koyar da turaren wuta kala-kala humra shima in different colors dilke gyaran amarya man gashi nd lots more kada ko yarda a baki labarai akan 300 kacal zaki zama pro na kan ki, duk mai bukata ta tuntubi wannan no 08172724281 sai mun ji ku*.
[9/23, 4:26 AM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
_A story about love and sacrifice._
_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_
_*From The Fantastic Writer of*_
```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```
*_And now_*
*_BA SONTA NAKE BA_*
*âœâœ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶Ãt̶̶є αs̶̶s̶̶Ãd̶̶Ãσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єÃv̶̶є n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶Ãc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶Ãv̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✠*,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ Ãt̶̶ w̶̶Ãl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶.*
*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._
*Addu'ar Cin Abinci*
Idan mutum zai ci abinci sai ya ce;
Ø¨ÙØ³Ù’م٠اللهÙ.
Bismi l-lahi.
Da sunan Allah
Idan ya manta to sai ya ce (yayin da ya tuna)
Ø¨ÙØ³Ù’م٠الله٠ÙÙÙŠ أَوَّلÙÙ‡Ù ÙˆÙŽØ¢Ø®ÙØ±ÙÙ‡Ù.
Bismi l-lahi fi awwalihi wa akhirihi.
Da sunan Allah a farkonsa da karshensa.
Wanda Allah ya azurta shi da abinci ya ci, to ya ce;
اللّهÙÙ…ÙŽÙ‘ بارÙكْ لَنَا ÙÙيه٠وَأَطْعÙمْنا خَيْراً Ù…ÙنْهÙ.
Allahumma barik lana feehi wa-at'imna khayran minh.
Ya Allah! Ka sanya mana albarka a cikinsa, kuma Ka ciyar da mu wanda ya fi shi alheri.
Wanda kuma Allah ya azurta shi da madara ya sha, to ya ce;
اللّهÙÙ…ÙŽÙ‘ بارÙكْ لَنَا ÙÙÙŠÙ‡Ù ÙˆÙŽØ²ÙØ¯Ù’نا Ù…ÙنْهÙ.
Allahumma barik lana feehi wazidna minh.
Ya Allah! Ka sanya mana albarka a cikinta, kuma Ka kara mana ita (madarar)
*10*
Rufe fuska ta nayi da hijabi na ina dariya ba tare da nayi magana ba,shima dariyan yayi ya d'auki yam ball d'aya ya kai baki ya gutsura ya fara taunawa har da lumshe ido wai dad'i ya kawo sauran baki na cikin sauri na kawar da kai na duk kunya ya gama mamaye ni.
Yaci ba laifi dambun naman da kunun ayan ne dai yace su kam gida zai tafi dasu sunyi dad'i sosai ya kara da cewa duk ranan da zai zo toh ya daina cin abinci anan zan rink'a mishi yana ci, koda ya gama muka sha hiran mu yauma kaman kada ya tafi haka nake ji amma haka muka hakura da zai tafi wani babban jaka ya bani yace in bawa Baban mu sannan muma ya bamu namu tsaraban mu nida Inna ya tafi.
Sai da na nemi taimakon wasu yaran sannan muka shiga da kayan cikin gida Gwaggo Aisha da sauran 'yan koron ta suka bini da harara wanda ban san ma sunayi ba.
"Ni ba wai bana son yayiwa Mallam alkhairi bane ba a'a yanzu Baban ku yazo yaga wannan tulin kayan da sunan nashi, gaba zai iya neman gidan yaron yace zai je maula ya zubar miki da mutunci gaba d'aya" Inna ke fad'an haka bayan na nuna mata jakan da Yaya na yace na Baban mu ne.
Shiru nayi ina tunanin maganan dan na san gaskiya Inna ta fad'a, zuwa can na fara murmushi ni kad'ai saboda na samo mana mafita.
"Inna in kin bashi kayan kice mishi a hukuma Yaya na yake aiki, kinsan yanda Baba yake tsoron hukuma na tabbata daga wannan rana ba zai yarda su had'a hanya ba balle har ya roke shi" na karasa ina dariya sosai dan na tuna yanda Baba yake bala'in tsoron su ban san kome yasa b ba.
Dariya Inna kanta tayi bata kuma ce min komai ba nima ban kara magana ba na kwashi tulin kayan da Yaya na ya kawo min da sunan tsaraba na fara jerawa cikin babban trolleyn kaya na.
Bayan sallah magariba Baba ya shigo d'akin mu ina gama mishi sannu da zuwa na wuce wajan Dije abina na basu waje wanda sam Inna bata san hakan domin ina barin wajan zai fara kokarin canza salon hiran nasu dan haka ba b'ata lokaci ta d'auko jakar kayan tsarabar shi ta ajiye a gaban shi ta koma can nesa dashi ta zauna.
Fara bud'e jakan kayan yayi yana mitan wai Inna ta maida shi dodo da zaran sun kasance su 2 a waje d'aya sai ta koma can gefe.........
Kasa magana Baba yayi saima jikin sa daya fara b'ari ya zaro ido yana kallon jakan in shock kawai, Inna da ta watsar da lamarin sa tana wasu sabgogin ta bata san halin daya shiga ba sai da ta juyo, a tsorace ta mike ta nufo shi tana," Mallam lafiya meya faru?"
Bai motsa ba kuma bai bata amsa ba sai da ta saka hannun ta a kafadar shi ta jijigashi da karfi tana," Mallam.... Mallam..." Sai a wannan lokaci ya firgita yaja dogon numfashi ya d'ago da kai yana kallon ta ba tare da yace komai.
"Kamin magana mana Mallam meya faru nace?"
Ajiyar zuciya yaja ya sauke kusan sau uku sannan ya ce," Bintu wayan nan kayan masu tsada kuma masu yawan da nake gani duka nawa ne kika ce?"
Ajiyan zuciyar itama Inna ta sauke jin cewa ashe wai kayan ne suka firgita shi ta koma wajan zaman ta ta zauna sannan ta amsa mishi da nashi d'in ne.
Firfito da manyan shaddodi da suke ciki ya fara bakin sa kuwa kaman gonan auduga sai da ya fito da guda shida suka kare sai takalma suma masu kyau guda 2 da huluna mu had'u a banki guda 2 da kud'in d'inki a kasa dubu hamsin.
Suma ne kawai Baban mu baiyi ba a wannan rana ya rasa ya zaiyi da rayuwar sa ya d'aga wannan kaya ya kalla sai ya d'aga wancan ga kud'in kuwa ya rike a hannu gam ya kasa ajiyewa kaman wani ne zai kwace mishi.
"Bintu.... Bintu Allah yayi miki albarka yanzu wannan duka a dalilin 'yar albarka na samu dama ai wannan yaron kana ganin shi kaga dan albarka shima, ko ba shi bane na gan su tare kwanakin baya?" Ya tambaya yana ta washe baki.
"Shine mana ma'aikacin hukuma ne ai, ni ko soja tace min ne ko d'an sanda, na manta dai" Inna ta bashi amsa ta kauda kai kada dariya ya sub'uce mata ganin yanda nan da nan Baba fuskar shi ta canza ya koma kalan fargaba da tsoro.
"Oho ashe hukuma ne, toh yayi kyau madallah da har ina cewa in naga ya dawo zanje in mishi godiya kuma muna gaisawa ashe yafi karfina". Baba ya fad'a bakin shi na rawa.
Inna had'iye dariyar ta tayi ta juyo tana kallon shi can ta ce," haba Mallam wani irin magana ne wannan, uhum sirikin naka shine yafi karfin ka?"
"Kema dai Bintu da son jan zance kike kin san bana shan inuwa d'aya da hukuma, Allah yajikan Baban ki ai ta nan ya rinjaye ni nayi ta bashi kud'i mudin in ya tambaya ko a wani waje sai naje na ciwo bashi na kawo mishi duk da shi na san yayi ritaya amma nake tsoron sa balle wanda yake saurayi mai jini a jika?
Hmmm ke dai kawai ki cewa 'yar albarka ta mik'a godiya ta a wajan sa".
"Toh shikenan Mallam zan fad'a mata" Inna ta bashi amsa.
Tun daga wannan rana Baban mu shima ya koma d'an gaye daga ya canza wannan sai ya cire wancan har a majalisan su yanzu shi yake mulki kowa so yake ya zama makusancin shi, maimakon kud'in nan daya samu ya juya su a kasuwanci suyi albarka ya rike gidan sa kaman kowani magidanci saima lalacin nasa ya karu d'an masarar da yake sayowa ma yanzu ya daina ba abinda ya shafe shi da lamarin cikin gida illa ya d'au wanka ya shigo d'akin mu yayi breakfast ya tura kud'i a aljihu yayi ficewar shi.
Aike kuwa Yaya na bai daina yi mishi na kaya dana kud'in duk bayan kwana bibbiyu yake aikowa, ranan da ya rasa na kashewa kuwa ni yake tambaya in bashi dan ya san ko ya tambayi Inna ba bashi zatayi ba.
Wahalar da muke ciki yanzu ya dawo kan Inna Asabe dan itace mai yara dayawa a gidan ga babu abinci babu jari balle ta daurawa yara sana'a, kananan yaran ta kullum a d'akin mu suke cin abinci.
Rannan Gwaggo Aisha bata gida Inna ta fito ta kawo mata rabin bugu na shinkafa da kuma carton na taliya sannan ta bata dubu goma tace tayi jari ita mai yara kanana zama haka ba zai yiwu ba.
Kuka wiwi ranan Inna Asabe tasa tana Inna ta yafe mata abubuwan da tayi mata a baya gashi wacce ta biyewa sukayi mata rashin mutunci yanzu babu ruwan ta da ita koda zasu wuni su kwana basu ci ba kuma basu sha ba ko a kwalar rigar ta sai wacce suka wulakanta itace yau ta mutumta ta haka?
Inna Asabe tun daga wannan rana ta samu abinyi itama kuma tun daga wannan rana ta fita harkan gwaggo Aisha tsakanin ta da Inna ta kuma sai mutunta juna.
**********************************
*Rubby private school* makaranta ce mai matukar tsada ta 'ya'yan masu kud'i ko manyan 'yan kasuwa, anan Yaya na ya nemo min gurbin karatu na fara fita ss1 abina kuma ya ajiye min mai napep da yake zuwa ya kaini kullum da safe kuma ya d'auko ni in an tashi, wata nayi kuma ya biya shi kud'in sa.
Maryam Alhaji idris itace seat mate d'ina tun ranan mu na farko da had'uwa muka kulla k'awance da ita domin Allah ya had'a jini mu sosai.
Kasancewar Maryam tana kusa dani yasa al'amarin makarantan yazo min da sauki, sosai take taimaka min kana ganin ta kaga wayayyiyar yarinya 'yar gayu tsabanin mu namu wayewar kauyenci ne a wajan su.
Ba'a magana da hausa sai turanci a makarantan abinda ya fara bani matsala kenan sannan kuma in ana koyarwa shima sai turanci ko kad'an basa d'an sirka hausa yanda irin mu zamu fahimta sai dai in an gama koyarwa Maryam ta kara wayar min da kai.
Term d'aya kawai mukayi na canza nayi wayewan 'yan gayu ga turanci ya fara zama a bakina domin makarantan ba wasa.
A wannan lokaci ne kuma aka saka bikin Hajara da Alhaji data samu ,wata biyu kawai aka saka Gwaggo Aisha sai habaice-habaice take 'yar ta zata je gidan hutu gidan kud'in halal bana yankan kai ba, wai kud'in Yaya nane na yankan kai.
Suna ta shirye-shiryen bikin su mu kuma muna shirye-shiryen walimar saukar mu a islamiya dan haka kona dawo daga makaranta banida lokacin zama sai na islamiya dan hadda muke kuma abinda ya rage mana bai fi izu biyar ba gashi har kuma date d'in da aka saka na saukan ya kusa shiyasa muka bada himma sosai, a yanda aka saka date d'in in anyi bikin Hajara da sati zamuyi walimar namu.
A boye Gwaggo Aisha filin ta na gado ta sayar tayiwa Hajara kayan d'aki dashi wai 'yar ta zata shiga babban gida kada su raina ta, ba laifi kaya kam sunyi kyau dan a bakin Dije nake jin wai Italian bed 'yan dubu dari uku ta saya mata da kujeru dubu dari da hamsin, Allah ya sanya alkhairi nayi na shi a wajan toh me zance ? Nida anko ma sunce kada na kuskura inyi na bikin d'akin su.
Ina gani su jamila suna ta rawan kai a shiga a fita sai shirye-shirye take itama wai zatayi nata shagalin daban dan haka ankon ma nata kala daban ne da k'awayen ta.
Ana saura sati d'aya gidan mu ya fara cika da baki 'yan uwan Baban mu da nasu Gwaggo Aisha ga hayaniya ga rashin zaman lafiya saboda kullum sai an raba fad'a, ba shiri na tattara kaya na zuwa gidan Maa ko zan samu natsuwa in ida hadda ta kuma a zuciya ta na kuduri sai sun gama bikin su zan koma gida.
Ana gobe daurin aure da yamma Yaya na yazo amma ya kasa parker motan shi inda ya saba saboda jama'a sunyi yawa anata shiga da fice sai gaba da gidan Maa yayi sannan ya kira ni a waya na fito wajan shi.
"Meke faruwa a gidan naku ne naga jama'a haka?" Ya tambaya ko gaisuwan kirki ba muyi ba.
Turo baki nayi ina mai jin haushi dan duk wanda zai min zancen auren nan haushi yake bani tayaya za'a ce wai ana biki a gidan ku amma ace wai an hana ka yin anko wani irin kiyayyane, me nayi musu da zafi haka??
Ina aiyana haka a raina naji hawaye ya zubo min wanda ya tayar da hankalin Yaya na ya shiga tambaya ta meya faru cikin damuwa.
Maimakon in bashi amsa sai na fashe mishi da kuka tsakani da Allah, nan ya kara ricewa yana tambaya ta amma na kasa magana sai shassheka nake.
Da kyar nayi shiru shima sai da naga hawaye a idon shi ba shiri na had'iye kukana na fara goge hawaye na da hijab.
Sai da muka natsu sannan ya ce," in ba so kike zuciyata ta buga ba kanwa ta ki gaya min meya faru??"
Cikin kara turo baki na ce," Auren Hajara za'ayi gobe"
Wacece kuma Hajara?"
"Yaya tace wacce a baya in kazo zaga ganta tana wucewa da abincin sayarwa"
Nan da nan ko ya gane ta na cigaba," yar Gwaggo Aisha ce kuma itace babba a gidan mu dan ni ba yar d'akin su bace suka ce kada inyi ankon auren" na karasa wasu sabbin hawaye na bin kunci na dama abin yana cina a rai sai yau na samu daman amayarwa.
Kallo na ya tsaya yi with expiration a fuskan shi, can ya girgiza kai ya ce," tunda can suke miki haka ko sai da auren yazo suka fara??" Ya tambaya fuskar sa na fallasa bacin rai da yake ciki.
"Tun muna kanana na taso naga haka ware ni suke suna hana 'ya'yan su wasa dani, ni kad'ai nake al'amura na, nake wasa na kaman mayya in Dije bata nan.
Shiru yayi na wasu dakiku sannan ya fara magana," dama bai kamata kiyi ankon su ba saboda kin fi su class shiyasa suke miki haka kuma ina so ki kwashe kayan ki zuwa gidan ku yanzu auren gidan ku ne dole dake za'ayi.
Zan kawo miki kayan da zaki saka a bikin zuwa dare nd...."
"Ba sai ka kawo min kaya ba ina da wayan da ban saka dayawa cikin wayan daka kawo min kuma ni ba zan je biki...."
" I don't care about that zan kawo kayan anjima kuma dake za'ayi bikin" yana gama fad'an haka ya fad'a motan shi ya fita a guje.
Da ido na bi shi ina jinjina girman irin son da yake min ko kad'an baya son gani na cikin damuwa.
"Allah sarki Yaya na Allah ya bar mu tare" nace na juya zuwa gidan Maa raina fess dan aiwatar da abinda ya saka ni.
*Albishirinku mata masu son kamshi da gyara ga dama ta samu zamu fara classes na koyar da turaren wuta kala-kala humra shima in different colors dilke gyaran amarya man gashi nd lots more kada ko yarda a baki labarai akan 300 kacal zaki zama pro na kan ki, duk mai bukata ta tuntubi wannan no 08172724281 sai mun ji ku*.
[9/30, 2:28 PM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
_A story about love and sacrifice._
_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_
_*From The Fantastic Writer of*_
```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```
*_And now_*
*_BA SONTA NAKE BA_*
*âœâœ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶Ãt̶̶є αs̶̶s̶̶Ãd̶̶Ãσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єÃv̶̶є n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶Ãc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶Ãv̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✠*,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ Ãt̶̶ w̶̶Ãl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶.*
*Addu'a Idan Mutum Ya yi fushi.*
أَعÙÙˆØ°Ù Ø¨ÙØ§Ù„له٠مÙÙ†ÙŽ الشَّيْطَان٠الرَّجÙيمÙ.
A'oothu billahi minash-shaytanir-rajeem.
Ina neman tsarin Allah daga shaidan tsinanne.
*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._
Duk da kin ki fad'a min sunan ki hakan ba zai hana ni nuna miki farinciki tare da godiya ta a gare ki ba,naga kyauta na yaba nagode Allah ya bar kauna wallahi ina kaunar ku fiye da yanda kuke zato ina kuma alfahari daku.
Lots of luv 😘😘😘ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜
*11*
Inna tana tsakar gida tana taya su aikace-aikace duk da habaice-habaice da suke bin ta dashi bai dame ta sai gani na tayi nazo na wuce ciki da jakan kaya na.
Na shiga d'aki ban dad'e ba Inna ta biyo ni tana," har kin gama shanye yajin da kika daka ne? Ai na zata zaki yi wata kina sha kamin ya kare ki dawo sai kuma ya kare da wuri".
Turo baki nayi tare da marairaice fuska na ce," Allah sarki Inna ni ina can ina ta kewar ki shiyasa na kasa zama na dawo amma ke ko kewa ta ba kiyi ba".
"Wani abun dai ya dawo dake ba kewa ta " Inna ta fad'a tana shirin ficewa.
"Shikenan tunda baki yarda ba amma a ina zan iya zaman sati ban gan ki ba inna taaaa" naja zancen ina murmushi,karasa ficewa tayi bata kuma kula ni ba.
Kwanciya ta nayi nima a d'aki ina chatting da Maryam ban kuma lek'a waje ba, ina jin su a waje anata mayar da zance wai ashe yau akwai dinner da angon yace za'ayi da farko sai kuma wata 'yar uwar sa tazo da yamma tace an fasa dinnern saboda wata kanwar Maman su tayi hatsari a hanyan ta na zuwa bikin.
Gyara kwanciya ta nayi ina ko akwai dinner ma wa zai je, can ta matse musu nace a zuciya ta tare da jan dogon tsaki ni kad'ai.
Kusan isha'i sai ga wayan Yaya na yace yana waje, Inna har yanzu tana cikin mutane dan haka banyi mata magana ba na fita wajan sa, yana tsaye a inda ya saba tsayuwar yasha gayun sa kaman yanda ya saba sai zuba kamshi yake.
"Naji dad'i da naga kin dawo gida kaman yanda na umarce ki" yace yana kallon karamin gyalen da nayi rolling dan kullum in zan fito wajan shi hijab nake sakawa sai yau nasa gyalen saboda dare ne kuma bai tab'a zuwa wajena da daddare ba sai yau.
" Allah kada ya kawo ranan da zaka bani umarni in kasa bi, ka wuce duk wani matsayi na duniya da ka sani a waje na, u re my every thing". Na fad'a mishi cikin shaukin kaunar sa da yake d'iba ta.
Murmushin nan nashi mai sanyi ya kara fad'ad'awa yana kallon na ya ce," nagode kanwata amma bake ya kamata ki fad'i wannan Kalmar ba sai ni domin na kasance maraya banida kowa kece kika zama dangina kika zama kanwata sannan above all kika zama masoyiya ta kin ga kuwa nine zance miki u re my everything".
Kasa cewa komai nayi sai murmushi da nake saboda kalaman shi sun kara narkar min da zuciya ji nake ba zan iya rayuwa babu shi ba.
"Wannan gyalen yayi matukar yi miki kyau amma ki daina saka shi in zaki fita ki cigaba da saka hijabi yanda kika saba " ya katse min tunani na.
"Insha Allah Yaya na " na amsa mishi ina sunkuyar da kaina kasa.
Wata katuwar jaka ya d'auko a seat d'in bayan motan shi ya mik'a min ya ce," ga kayan da nake son ki saka gobe ,zan zo kaman da karfe goma sha biyu dan kai ki beauty saloon make sure kin shirya before inzo"
Na bud'i baki da niyyan godiya ya katse ni ki shiga gida sai nazo " gyad'a kai nayi ina murmushi na juya na shiga gida.
Da ni da Inna ta duk saka kayan mukayi a gaba muna kallo cike da mamaki, wani haddaden gown ne light blue adon da akayi a jiki ma ya isa mutum kallo sannan ga wani karamin box da yake d'auke da wani tsiririn sarka mai d'an karan kyau da d'an kunnen shi wanda Inna tace tabbas gold ne sai kuma takalmi mai tudu da pos d'in sa suma ko makaho ya shafa su yasan naira tasha kashi wajan sayan ta.
"Wannan hidima anya batayi yawa ba, yau kuma harda zinare?" Inna ke fad'in haka cike da jimami.
" Yaya ne fa Inna meye abin damuwa saboda ya saya min kaya, ai ya riga ya saba yi " nace hankali na kwance kuma tsakani na da Allah na fad'a.
Shiru kawai Inna tayi ba tare da ta kara cewa wani abu ba kasancewar ta gane in banda tarin kuruciya babu komai a cikin kaina, abu d'aya yake sanyaya mata zuciya shine yanda bata sakaci wajan tsayuwar dare kuma duk a kaina.
A baya bata damu da lamarin Yaya na sosai ba kaman da yanzu na girma, duk da cikin hikima irin tasu ta manya tana jin yanda muke tsakani na da shi ko hannu na bai tab'a tab'awa ba.
Addu'an Allah yayi jagora ya tsare daga duk abin ki tayi ta tashi a wajan ni kuwa cikin zak'uwa da zumud'i na jawo kayan na fara kallo saboda dazu idon Inna ya hana in sake in kalla da kyau har na kosa goben tayi in saka kaya na.
Da washe gari da hayaniyan mutane muka tashi gidan mu ya cika ba masakar tsinke gaba d'aya sai naji na takura dan da naje da niyyan shiga bayan gida da gudu na dawo ina kakarin amai saboda yanda mutane suka b'ata shi, ba shiri na samu 'yar karamar jaka ta na had'a duk wasu abubuwa da zan bukata na zuba a ciki na wuce gidan Maa bayan na fad'awa Inna a can zan shirya sai in dawo.
Ko da na je gidan Maa itama bata zauna ba gidan namu ta tafi aka bar ni kad'ai a nan Inna ta aiko min da abincin safe da akayi na d'aurin aure,da yake safe ne sai na kasa ci na fito na samu yaro a waje na aike shi wajan mai shayi ya had'o min breakfast na nayi na kwanta bacci ni ban tashi ba sai kusan sha d'aya .
Ina shirin shiga wanka naga an ajiye min wani abincin bayan na safe, Allah sarki Inna ta na san wannan duk aikin ta ne, ban ci abincin ba sai bayan na fito daga wanka.
Lotion kawai na shafa na saka kayan da Yaya na ya kawo min jiya da daddare, aiko ya zauna das a jikina kaman an gwada ni irin gown d'in nan da bayan yafi gaba tsayi wani sarka da d'an kunnen kira Dubai data sayo min a baya shi nayi amfani da shi dan gold din Inna b'oye shi tayi tace ba zanyi amfani da shi ba,ko minti goma banyi da gama shiryawa ba kiran Yaya na ya shigo waya ta hijabi na d'aura akan kayan na fito.
Yau manyan kaya ne a jikin sa tsab'anin da ya murza hulan Ahaiyye a kan sa ya matukar kyau sai zuba kamshi yake.
"Yaya naaa ka gan ka kuwa kayi kyau sosai sai kace kai ne angon" na ce mishi ina dariya.
Murmushin sa mai sanyi ya yi min sannan ya ce" hmmm ke ba?"
"Ni me?" Na tambaye shi ina turo baki.
"Ke kanwa tace na ce".
"Kanwa only?" Na kara tambaya ina fiddo da ido waje.
"Baki kyauta min ba kin ki fad'a min auren nan in time balle in kawowa Baba wani abin kirki shiyasa na ki zuwa daurin auren,amma ki min magana da shi in bashi hakuri da gudumuwa na ko kad'an ne". Ya ce saboda kawar da wancan maganan da muka fara.
Gyad'a kai kawai nayi na juya ina dan dariya tun kamin inga draman da zai faru tsakanin Baba da Yaya na.
Allah yasa a hanya muka had'u da shi yana dawowa gida da yake ba a kofar gidan mu aka d'aura auren ba a can wani masallaci dake kan kwanan layin mu, yanzu haka suna tare da wasu 'yan uwan sa da sauran abokan shi ne a wajan bayan mutane sun watse.
"A'a 'yar albarka ke ce, ina zuwa kuma?"
"Baba dama wajan ka zan je, ummm...hmmmm wannan d'in nan da yake aiko maka da kaya shine ya zo yana so wai ku gaisa kuma ya baka hakuri da gudumuwan sa" na karasa kai na a kasa saboda kunya.
"Wai wannan mai zuwa wajan ki nan?" Ya tambaya yana zaro ido.
Danne dariyar daya taso min nayi ina gyad'a mishi kai.
"Toh meye sai mun gaisa da shi,naga a baya ke yake bawa ki kawo min ba yau ma ya baki d'in mana".
"Baba nima ban san dalilin da yake son ku gaisa ba yau amma tunda ya bukata kila yana da wani dalilin" na fad'a ina kallon yanda naga duk hankalin Baba ya tashi kaman ba yanzu na gan shi cikin annashuwa ba.
"Ki ce ya zo nan ya same ni ina jiran sa a nan " .
"Toh Baba" na ce tare da juyawa na koma wajan Yaya na sannan na fad'a mishi sakon Baba.
Naso bin shi inga yanda zasu kare da Baba sai kuma naga rashin cancantan hakan na tsaya jiran shi.
A nesa Baba ya hango shi yana zuwa yana saka wayar shi a aljihu wanda shi kuma Baba kallon bindinga sak ya yiwa wayan, nan da nan ko zuciyar Baba ta fara zillo kaman zata fito.
Cikin matukar sauri ya juya ya fara tafiya kaman zai kifa ya nufi masallaci inda ya bar mutanen shi suna jiran shi, yana cikin tafiyan kuma wani tunani ya fad'o mishi ya canza hanya zuwa bayan layin mu.
Yaya na yana zuwa wajan ya ga wayam bai ga kowa ba kaman zai koma kuma ya fasa ya karasa har bakin masallacin aka ce mishi baya nan, haka ya hakura ya dawo ya ce bai gan sa.
A hanyan mu na zuwa saloon sai murmushi nake dokawa ina hana dariya ta fitowa na san Baba k'in tsayawa yayi saboda tsoro.
Babban wani tsadadden saloon ya kai ni a west end wanda ba abinda basa yi na gyara da kamshi har da lalle, gefe naga Yaya na ya kira wata da alama ita ce babban su a wajan ban san me suka tattauna ba naga ya bata kud'i masu yawa ya fita, nan da nan suka shiga hidima da ni har da su drinks da snacks suka kawo min.
Ba b'ata lokaci suka warware yalwantaccen gashi na suka wanke suka gyara shi nan da nan kuwa ya kara kyau sai d'aukan ido yake, wanke min kafa suka yi a wani abin wanke kafa ni dai ban tab'a gani ba sai ranan,fara ce na su ma sun gyara sannan suka yaryad'a min lalle mai ja da baki.
Light makeup suka yiwa fuska ta daya kara fito da ainihin kyawu na, wani haddaden net mai kauri da yayi matching da kayan jiki na suka d'auko a shagon nasu suka nad'a min shi in a unique way.
Fad'an irin kyan da nayi ma b'ata lokaci ne dan sai in rantse da Allah ban tab'a sanin ina da irin wannan kyau ba sai yau, sai kallon kai na nake a madubi, su ma 'yan wajan sai yaba kyau na suke.
Da zan fita na fara kokarin saka hijabi na, 'yan wajan ne suka min caa wai kar in saka daurin net d'in zai lalace tun ban isa gidan auren ba,tunda a mota muka zo in tafi a haka.
Ba dan naso ba na fito a cikin saloon d'in ina takawa a hankali kaman mai tausayin kasa saboda tudun takalmin kafa na har na iso bakin motan Yaya na bai sani ba kasancewar ya kwantar da seat ya kwanta da earpiece a kunnen shi ban san me yake saurara ba.
Bud'e kofan motan nayi na shiga na zauna kamshin turare na shi ya isar da sakon isowa ta a gare shi ya bud'e ido ya sauke su a fuska ta da nima shi nake kallon, mun dad'e muna kallon juna daga baya nice na sauke nawa idon kasa ina d'an murmushi.
Ina jiyo shi sai da ya sauke ajiyan zuciya har sau uku sannan ya tashi ya zauna tare da gyara kujeran, ya juyo ya kara kallo na kaman zai ce wani abu kuma ya fasa ya tada mota muka kama hanyan gida,har muka iso babu wanda ya yi magana.
Yana yin parking na ce," nagode Yaya naaa zan shiga ciki sai anjima".
Har na bud'e kofan na fita bai amsa min ba na fara tafiya, nayi kaman taku uku naji muryan shi ya ce," Zareefa...."
Da matukar mamaki na juyo dan jin suna na a bakin shi yau.
" Kinyi matukar kyau....,kyan da baki ba zai iya furawa ba, amma dan Allah in muna tare ki rinka saka hijabin ki" yana gama maganan shi yaja motan shi ya tafi.
A hankali na juya zuwa cikin gida ina murmushi da mamakin me yasa yake yawan cewa in saka hijabi ba.
Ina saka kafa gidan mu ido ya dawo kai na kowa ni yake kallo da gudu Dije ta zo ta rungume ni cikin ankon da suka hana ni yi sai naga ashe da a lokacin ma naga ankon ba sai sun hana ni ba da kaina zance ba nayi.
Can b'angaren su taja ni muka tafi tana in bata labari meye sirrin?
A nan muka zauna ina bata labarin saloon d'in da muka je na fara jin sautin kid'a daga waje.
Da mamaki na ce", kaman kid'a nake ji?"
"Eh dama naji Hajara da kawayen ta zasu kawo DJ tun shekaran jiya suke zancen Ina ga shi d'in ne suka kawo" Dije ta bani amsa.
"Taso muje mu gani...taso muje" cewar Dije tana jan hannun na .
Muna zuwa kofar gida muka ga Amarya da kawayen ta suna ta rawa, jan hannu na Dije ta fara wai muma mu shiga nace mata ta shiga ina zuwa.
Ina daga gefe ina kallo kawai naga mutane sun rufu a kai na suna min liki, maza da mata amma mazan sun fi yawa na rasa ta ina ma suka zo dan ni dai ban san su ba.
Neman shiga gida nake amma sun tare ko Ina ba hanyan wucewa daga cikin matan naji wata tana ", ke Hindu ki zo ga Amarya nan kiyi mata liki"
Da mamaki na d'ago na kalle ta na ce", ni fa kanwar Amaryar ce ga Amaryan can" na karasa ina nuna musu inda Hajara da kawayen ta sukayi sororo suna kallon mu.
"Eh ga Amaryar can wannan kanwar ta ce " wata kanwar Gwaggo Aisha ta fad'a tana harara ta.
Jiki a tsabule suka juya ga Amaryan su suna kallon ta har taji ta muzan ta, ni dai ban san ya suka kare ba na shige cikin gida na bar su.
Da daddare bayan an kai Amarya gidan ta Dije tazo d'akin mu a lokacin ina kwance ina chatting da Yaya na.
"Zo...zo...zo muje ki sha labari zo muje" ta ce tana jan hannu na ina ta tsaya in ajiye waya amma ina haka taja ni muka tafi bangaren su.
"Mijin Hajara da ake cewa mai kud'i ne ashe karya ne,kin ga gidan nata gidan yawa mutane sun fi shida a ciki ga d'akin nata ya yiwa kayan ta kad'an ke abun b dad'in gani wallahi.
Ina matar da ta zo tace ita 'yar uwar sa ce tayi magana a kan an fasa dinner ashe gidan haya ce ta had'a su".
*Albishirinku mata masu son kamshi da gyara ga dama ta samu zamu fara classes na koyar da turaren wuta kala-kala humra shima in different colors dilke gyaran amarya man gashi nd lots more kada ko yarda a baki labarai akan 300 kacal zaki zama pro na kan ki, duk mai bukata ta tuntubi wannan no 08172724281 sai mun ji ku*
[10/10, 7:42 PM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
_A story about love and sacrifice._
_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_
_*From The Fantastic Writer of*_
```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```
*_And now_*
*_BA SONTA NAKE BA_*
*âœâœ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶Ãt̶̶є αs̶̶s̶̶Ãd̶̶Ãσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єÃv̶̶є n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶Ãc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶Ãv̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✠*,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ Ãt̶̶ w̶̶Ãl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶.*
*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. 👇
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._
*12*
Bangane ba Hajara me kike nufi wai?" Na tambayi Hajara cike da rud'u.
Kamo hannu na tayi muka zauna a bakin k'ofar d'akin su sannan ta fara magana," hmmmm duk abinda Alhaji Khalid mai gidan gona ya fad'a a gidan nan ashe zuki ta malle ne sunan shi haladu kuma sana'ar sa kuma bawa dabbobi abinci a gidan gonan Alhaji Mukhtar dake Sabon layi".
Samun kaina nayi da matukar jin haushin sa sannan ga tausayin 'yar uwata daya rufe ni lokaci guda,cikin wani irin yanayi nace", amma Allah ya isan Hajara makaryaci kawai in bashi da kud'in menene amfanin shirga mata wannan karyan? Allah sarki Hajara ko wani halin take ciki yanzu?"
"Lalle Zareefa kin bani mamaki meye naki na wani zakewa haka, wallahi kada ma kiji tausayin ta ita ta jawowa kan ta ko ince su suka jawo dan harda uwar ta su ala dole dake zasu yi gasa, chab ni wallahi ko kad'an bata bani tausayi ba hasali ma dariya ta nayi ta sha, a mota ina ta tunanin yanda Gwaggo Aisha zatayi in taji wanga batu" ta karasa cikin shekiyanci tana dariya.
Girgiza kai na nayi hawaye na taruwa a ido na, na ce mata," Dije kenan taya ba zan tausaya mata ba ko kin manta cewa 'yar uwata ce jini d'aya yake yawo a cikin jikin mu"
"Na sani mana amma ba kya ganin yanda suka saka ki a gaba su da iyayen su sun hana ki sakat ke da mahaifiyar ki tun muna kanana har zuwa girman mu"
"Koma menene Dije su d'in 'yan uwa na ne, jini d'aya yake yawo a jikin mu daurewa kawai nake ina share su amma ina kaunar su har cikin raina ina kuma sha'awa in ga mun had'a kan mu kaman sauran 'yan uwa"
Hawayen da ya zubo min na share na mike na kama hanyan bangaren mu itama Dije ko motsi kasawa tayi dan maganganu na sun kashe mata jiki,ko da na shiga d'akin mu na samu Inna zaune gefen gado ta rafka tagumi da alamu itama taji zancen kenan.
"Tun d'azu ake kiran wayan ki" ta ce min ba tare da ta sauke tagumin ba saboda wannan al'amari ya bata mamaki da tsoro samarin yanzu mayaudara ne kuma macuta ne, in banda cuta kazo da wata siffa da suna dan a baka mata me yasa ba zai zo a yanda yake ba? Ko da yake Maman Dije ta ce wai sun riga sun nunawa duniya cewa in ba mai kud'i ba akai kasuwa shine yasa shi zuwa da wannan siffa.
Ajiyar zuciya ta sauke wanda sai da na juya na kalle ta dama rply na tex nake rubutawa 'yar ajin mu a islamiya ta kira bana kusa shine ta min tex tana min tuni kan abubuwa da muka shirya na walimar mu.
"Inna lafiya kuwa na gan ki haka?" Na tambaya.
"Hmmmm ba komai je ki wanke min hijabi na da da yake cikin bukiti a waje" da toh na amsa na fita wankin.
Ina fara wankin naga Gwaggo Aisha sun shigo da kannen ta 2 duk sunyi wujiga-wujiga ko kallon inda nake ba suyi ba suka wuce, a zuciya ta na ce," chab Gwaggo Aisha ana cikin tashin hankali tunda bata harare ni ko ta tsaya ta zage ni ba, lalle yau tana cikin matsala, d'aki suka shige suna neman mafita.
Har gari ya waye ba'a cimma abu d'aya ba sai shige da fice suke, sun samu Baban mu da maganan yace toh me zai mata, ta riga da ta fita a hannun sa lafiya dan haka sauran ya rage musu ita da mijin ta.
Gwaggo Aisha takaici ya hana ta sauran sauran bayanin nashi tayi ficewar ta, ta rasa ina zata kai kukan ta a share mata hawaye, babban burin ta shine a raba auren domin jiya da daddare ita da kannen ta daga gidan Hajaran suke suka ja mata kunnen kada ta yarda ta bashi kan ta duk rintsi duk wuya dan gobe-goben za'a raba auren nasu sai gashi har sha biyu ta kusa babu alamun nasara ko kad'an.
Gwaggo Aisha bata gama shiga tashin hankali ba sai da d'ayan kanwar ta da ta tura gidan Hajara dan a dubo mata lafiyr ta ta dawo da mummunan labarin cewa Haladu yayi nasaran kusantan Hajara jina-jina suka same ta abun babu kyan gani ko taimaka mata bai tsaya ba ya tsallake ta yayi tafiyar shi.
"Yanzu fisabillilahi duk fad'an da muka yi mata sai da ta sakewa wannan mayaudarin jiki ya gama da ita?" Gwaggo Aisha ke tambaya tana goge hawaye da gefe zanin ta.
"Ba laifin ta ba ne shi mijin ne tantiri, ta bamu labarin komai cewa da ta fara mishi taurin kai shine d'aure ta a jikin gado yayi abinda ya ga dama da ita wai bata isa ta hana shi more kud'in sa ba" 'yar uwar ta ta bata amsa.
"Amma wannan yaro anyi tsinanne Allah ya isa tsakani da shi, ina zan shiga da wannan abin kunyan, kayyah " yanzu kam kuka Gwaggo Aisha take tsakani da Allah tana tunanin tayaya zata kalli idon 'yan gidan bayan duk abubuwa da tayi musu wai ita 'yar ta zata auri mai mota.
"Mama kada ki tada hankalin ki domin nayi miki alkawarin saka ki farinciki, ba zan tab'a kula kowa ba kuma ba zan auri talaka ba sai mai kud'i" Jamila ke fad'an haka da take sauraron su tun d'azu ba tare da sun sani ba,d UK kallon juna suka tsaya yi babu wanda ya iya bata amsa sai dai ita Gwaggo Aisha ido ta zuba mata tana nazari tare da hasko yiwuwa da nasara a cikin abinda ta fad'a domin Jameela tafi Hajara kyau da tsarin jiki nesa ba kusa ba.
Haka akayi wannan wunin a tsaye babu wanda ya lek'a gidan Amarya wasu ma saboda bakinciki a ranan suka koma inda suka fito shiyasa gidan namu ya zama shiru kaman ba biki ake ba.
Bayan kwana 2 da bikin Hajara Yaya na yazo da rana bayan azahar cikin kananan kaya wandon kaman na sojoji sai bakin t shirt da bakin glass sosai yayi kyau, muna hira a kofar gidan mu yana tambaya ta me da me nake bukata a walimar saukar mu? Ni kuma ina ce mishi bana bukatan komai duk abinda ake bukata mun gama shirya su.
A wannan lokacin ashe Baba yana gida ya dawo saboda wata bukatar shi lokacin da yazo Yaya na bai zo ba yana ciki ya zo dan haka bai san da zuwan shi ba,yana d'aki Gwaggo Aisha tabi shi tana magiya akan yayi wani abu akan al'amarin Hajara a raba auren domin muddin tana raye ba zata tab'a barin auran nan ya dad'e ba.
Bata san duk haushi ya cika shi ba tazo ta ishe shi da surutu alhalin shi in ya tuna tsoro ya hana shi gaisawa da Yaya na da yanzu yana cikin kud'i yanzu gashi bashi da kud'i a hannu, tsaki yaja yana bin ta da mugun kallo ya ce," ke Aisha wai wace irin mace ce ke da zaran kin ga mutum ya shigo gida sai ki bi shi da korafin ki na banza da na wofi yarinya tana gidan mijin ta shine kike neman wai ni uban ta inje in fito da ita wannan wani irin rashin kan gado ne, toh ba dani ba wallahi kije can ki gama haukan ki kada ki kara tunkara ta da wannan iya shegen ko kuma ranki yayi mugun b'aci". Yana gama maganan shi ya mike a fusace zai fita ya juyo ya ce," ba sai kin kara gani na a gidan ba balle ki zo ki takura ni"
Fita yayi rai a b'ace yana ta masifa shi yasa kai zai fita da sauri ya koma baya yana tunanin anya idon shi dai-dai ya nuna mishi kuwa?
Kara lek'a kan shi waje yayi yaga dai da gaske ne Yaya na ya gani fuska a murtuke wai shi ala dole yayi fushi me yasa ban fad'a mishi maganan saukar namu ya d'auki nauyin komai na ba nayi da kai na.
"Innalillahi wa inna ilahi rajiun wai shi wannan yaro banda bala'i irin nasu na sojoji meya kawo shi da rana tsaka yana muzurai sai kace anyi mishi dole" Baba ke fad'in haka bayan ya koma cikin zaure ya manne da bango wai duk dan kada Yaya na ya gan shi.
Da kyar na shawo kan sa ya daina fushin muka ci gaba da hiran mu cikin annashuwa da shaukin soyayya, abinda bamu sani ba ashe Baba yana nan mak'ale a zaure yana jiran tafiyan Yaya na ya samu shima ya tafi majalisa, yaki komawa cikin gida kuma saboda rigimar su da Gwaggo Aisha kada taga ya koma ta mishi dariya.
A takaice mun kai good 1 hour sannan mukayi sallama ya wuce ni kuma na shigo gida cikin farinciki hannu na d'auke da sayayyar da yayi min.
Ina shigowa zaure saura kad'an in zubar da kayan hannu na saboda firgita ganin mutum manne a jikin bango yana goge zufa, sai da na tabbatar Baban mu ne sannan na samu natsuwa amma kuma mamaki da tambaya fal cikin zuciya ta me kuma yau Baba yake a nan ?
Hanyan fita ya nufa yana masifa kallon inda nake bai yi ba hakan ko ya kara saka ni cikin konkonto, a yanda nasan Baba da son dad'i amma yau ko kulanin baiyi ba bayan ga shopping bags a hannu na, juyawa nayi da niyyan shiga gida naji muryan Baban mu yana," wallahi Allah yau yaron nan ya cuce ni, in banda ina gudun abin kunya cikin anguwa kada a ce ga Mallam Hassan can yana fad'a da sirikin sa ba Allah da na nuna mishi ko ni waye, Aikin banza wa zai yiwa barazana har kofar gida har da wani sako kayan sojoji toh sai me...?"
Dariya na tintsire da shi har da dukawa sai yanzu na gane me Baba yake a zaure, da kyar na tashi na kwashi kayana zuwa cikin gida.
Bayan kwana 2 akayi bikin saukar mu a islamiyar mu wanda ya tara duban jama'a ciki kuwa har da Yaya na sai dangin Inna a 'yan gidan mu Inna Asabe ce kad'ai ta tafi dan Gwaggo Aisha cewa tayi karatun karuwanci dama nake shine yau kuma za'a je party toh ba da ita ba.
Bajintar da Yaya na yayi ba a cewa komai kayan rabo kala-kala ya kawo aka raba harda na malamai suma nasu daban ga gifts nima daya kwaso min ba zasu lissafi ba duk da haka cewa yake komai ya min gani yake bai yi ba saboda sauke Al' Qurani mai girma ba abin wasa bane.
A islamiyar ma na samu kyauta daban-daban saboda hazaka ta daga karshe taro ya watse bayan mun sha pics saboda tarihi.
*************************
Wato ka mai da ni mutuniyar banza a gidan nan saboda ban isa in fada kaji ba ko, fisabillilahi ka kyauwa kan ka kenan?"cewar wata 'yar dattijuwa mai kamala da kyau da haiba wacce ba zata haura shekaru hamsin ba.
Wani kyakkyawan saurayi ne zaune a gaban ta shi take takewa fad'a amma shiru yayi kan shi a kasa yana kallon lallausan rug da yake malale a katafaren parlour nasu wanda kallo daya zaka mishi ka kira shi da aljannan duniya domin babu ne kawai babu a ciki, just ku hasaso shi a cikin zuciyar ku domin in nace zan tsaya zayyano muku tsari da kyan gidan sai mu kusan cika novel din bamu gama ba
Duk da kan shi a kasa yake bai hana ni hango dogon hancin sa ba ga sajen sa baki wuluk na lallausan gashin sa sun kewaye fuskar shi, gashin kan sa kuwa kaman na larabawa saboda laushi da tsantsi sai dai yayi mata wani aski wanda an kwashe daga gefe-gefe da keya sai tsakiya da ta gaba ne da gashi kana ganin gashin ka san ya sha gyara da kulawa wajan mai shi.
"Zafar... Wai ba da kai nake magana ba ka min shiru" wannan kyakkyawar dattijuwar ta fad'a cikin tsawa.
Wanda ta kira da Zafar ya d'ago kai masha Allah ashe da kan sa yake kasa ban ga komai ba sai yanzu.
Zafar fari tas irin farin nan mai yellow yana da dogon hanci wanda ya kawata kyakkyawan fuskan shi ga maidaicin bakin sa mai d'auke da jajayen lips sun kara fiddo ainihin kyan fuskar sa, idon sa kuma kaman mai jin bacci suke a takaice Zafar ya had'u iya had'uwa sai dai ya kasance d'an shan minti ne kasancewar shi d'a tilo ga multi millionaire.
A shagwab'e ya d'ago da kai yana d'an tale baki kaman d'an karamin yaro alhalin ya kai shekaru ashirin da takwas yana kallon mahaifiyar tashi da lumsassun idon shi da baturai sukewa lak'abi da sexy eyes ya ce," wai ya kuke so inyi ne Mom for god sake ni komai nayi kice bai yi ba, look at dis " yace yana nuna mata gashin kan sa sannan ya cigaba.
"Wats wrong with it nayi wancan kunce baiyi ba nayi wannan ma kice baiyi ba then which 1 do u want me to do?" Ya karasa yana watsa hannayen sa cikin iska.
Wacce ya kira da Mom ido kawai ta zuba mishi ta kasa cewa komai domin lamarin tilon dan nata ya fara bata tsoro a ce d'an da ka haifa shi zai rink'a mayar maka da magana haka, babu wanda yake shaka a gidan sai Abban shi, sanin haka yasa ta cewa," ok haka kace ko? Kaje kayi duk abinda kake so amma kafin ka fita inayi maka albishir da gobe Abban ka zai taso daga Portugal zuwa gida sai ka tanadi bayanin da zakayi mishi in ya ga askin naka".
A rikice ya dawo kusa da ita, da ya kai har tsakiyan parlour da niyyan komawa part d'in shi yana zuwa ya zauna a gaban ta tare da d'aura hannayen shi duka 2 kan guiwoyin ta ya ce," na san ko Abba ya dawo my sweet Mom zata kare ni kaman yanda ta saba ko Mommy naaaa just once daga wannan shikenan ba zan kara ba I promise shima wannan dan zamu yi bachelor's eve na Musaddiq ne shiyasa".
Murmushi tayi tana shafa gashin kan nashi ta ce," promise.. promise dai wanda ban san sau nawa aka yi min su ba remember jiya me kace?"
Dafe goshin sa yayi yana d'an tuno yanda yake mata in taki yi mishi abu, zai fara yi mata ta dakatar dashi tana," bana son wannan shagwab'an naka jeka let me think about it"
"Yesss.... dats my sweet Mom" yace yana d'an tsalle a gaban ta sannan ya fita da gudu yana dariya, itama dariyan take a zuciyar ta kuwa tana blaming kan ta da duk abinda Zafar yake itace sila domin a koda yaushe itace mai kare shi wajan Abban sa in yayi wani laifi, ita da kan ta bata jin dad'in abinda take wasu lokutan amma ya zata yi shine fa kad'ai kwan ta a duniya dan ma Allah ya tsare baya wasu mugayen dabi'un na 'yan zamani shi dai bar shi da zuwa parties da kula 'yan mata sai kuma son swagger.
*Albishirinku mata masu son kamshi da gyara ga dama ta samu zamu fara classes na koyar da turaren wuta kala-kala humra shima in different colors dilke gyaran amarya man gashi nd lots more kada ko yarda a baki labarai akan 300 kacal zaki zama pro na kan ki, duk mai bukata ta tuntubi wannan no 08172724281 sai mun ji ku*.
[1/26, 7:04 AM] Golden Pen Writer's Assoc: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
_A story about love and sacrifice._
_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_
_*From The Fantastic Writer of*_
```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```
*_And now_*
*_BA SONTA NAKE BA_*
*13*
✠*✠G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* âœâœ
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶Ãt̶̶є αs̶̶s̶̶Ãd̶̶Ãσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єÃv̶̶є n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶Ãc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶Ãv̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✠*,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ Ãt̶̶ w̶̶Ãl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*13*
Yana fitowa daga parlourn Mommy shi fara'an fuskar sa ta d'auke lokaci daya dif kaman wutan NEPA sai ma wani shan kamshi da yake wanda ya kara fiddo da kyan sa, a nan na fahimci wato babu mai ganin wannan fara'ar tashi sai mahaifiyar sa.
Wani haÉ—aÉ—É—en madaidaicin flat house ne dake gefensa na mahaifan sa, ya nufa ko kula masu aiki da suke gaida shi baiyi ba ya shige abin sa.
"Dude ka san I have been waiting for you amma ka wani shanya ni, tun dazun su Sabeer suka dame ni da waya wai kowa ya hallara sai mu ake jira" cewar wani guy dake zaune kan sofa shima kana ganin shi kaga classic guy saidai ko rabin kyan Zafar bai kai ba.
Ko inda yake Zafar bai kalla ba ya wuce bedroom d'in sa da yaji royal bed fari kal,komai na d'akin farare ne hatta da curtains tsab'a parlour kuma komai na ciki royal blue ne, bai tsaya cikin bedroom d'in ba ya fad'a bathroom domin yin wanka.
Girgiza kai Sadiq yayi ganin Zafar yaki kula shi ya wuce ciki in da sabo yaci a ce ya saba kam duk da cikin abokan sa jinin su yafi had'uwa da Sadiq d'in kuma tare suka taso tun suna kanana har zuwa girman su babu abinda ya tab'a raba su ko a makaranta.
Baban Sadiq yana da wadata shima amma ko rabin kudin su Zafar bashi dashi, saboda aminitar dake tsakanin su 2 yasa iyayen su maza da mata kulla zumunci sannan Baban Zafar shi yake biya Sadiq kud'in makaranta ganin cewa shine farincikin d'an su.
Zafar yana da fara'a sosai da wasa da dariya amma fa sai ga Mommy sa dan ko shi Sadiq da suke tare shekara da shekaru bai cika ganin dariyar sa ba sai jifa-jifa wanda shima in mutum ya bibiya toh yaga abin mugunta ya sami shi Sadiq d'in anan zaki ga dariyar sa harda rike ciki.
Zafar yana da wani hali ko kuma ince buri, ya raina 'yan matan mu na gida kwata-kwata basa burge shi a cewar sa bai ga abin so ba a tare dasu ba, 'ya'yan masu kud'i da masu fad'a aji na cikin kasar nan babu wacce bata kawo mishi kokon barar soyayyar ta ba duk yayi watsi dasu dan ko kallo basu ishe shi ba,sai dai in zasu tafi party wanda sai da chick ake zuwa toh shine zai kula ki shima da ya fito shikenan amfanin ki ya kare amma hakan ma farinciki wacce ta samu wannan daman take ko ba komai ta samu na canza status kenan tana sham kamshi cikin kawayen ta.
Wannan halin nashi yasa mutane da yawa suke mishi kallon mai neman mata alhalin ba haka yake ba.
Murya... Ya d'aga cikin k'osawa da zaman jira da yake ya ce " man wai me hakane, sai b'ata mana time kake pls ka fito mu tafi ba party zuwa da beb bane in dan wannan kake ja mana...…"
Ganin ya fito yasa ya had'iye sauran maganan shi yana bin shi da kallo ko makiyin shi ne bai isa ya kushe shi ba, toh duk iya dai bin kwakwafin mutum babu abin kushewa a halittar sa dan ko dama aka bashi aka ce yayi kan sa iya kar sa kenan.
Ya matukar had'u cikin dark blue polo shirt da wandon jeans baki sosai kayan sun matukar dacewa da farar fatar shi sai canvas dark blue dake kafar shi sai zuba kamshin tsadaddun perfumes din shi yake kasancewar sa mai son kamshi shiyasa baya amfani da turare daya kusan 4 ko 5 yake amfani dasu at a time dan haka ba zaka tab'a bambamce kamshin da yake ba.
Yana gyara agogon Rolex dake hannun shi ba tare da ya kalli inda sadiq yake zaune ba yace,' muje"
Girgiza kai kawai yayi ya mike yabi bayan shi dan har ya fita basu tsaya b'ata lokaci ba suka fad'a wata sport car d'in sa suka fice daga gidan.
********************
Gidan mu dai yana nan yanda kuka san shi babu abinda ya canza cikin zamtakewar da muke, cikin shekaru 2 da suka shud'e sai dan abinda ba za'a rasa ba, muna final year a makaranta sai shirye-shirye rubuta waec muke hankali kwance.
In ka san ni a shekaru 2 da suka wuce ba lalle ne ka gane ni yanzu ba na canza matuka na kara wayewa ga girman jiki dana kara sosai ,kyau na kuwa ba'a magana duk inda na wuce sai an dad'e ana magana ta wasu ko cewa suke wai ni balarabiya ce,ko a makaranta na sha raba musu musu cewar ba abinda ya had'a ni da larabawa ni asalin hausa Fulani ce amma wasu basa yarda sai dai suce b'oyewa nake bana son asan gaskiya.
Godiya sun tabbata ga Allah mahallacin komai da kowa sannan ga mutane 2 na cikin rayuwa ta wanda a dalilin su na zama abinda na zama wato Yaya na da besty na Maryam, dukan su 2 sun taka muhimmiyar rawa a rayuwa ta.
Yaya na shine gata na shine abin alfahari na ba dan shi ba da ban kai wannan matsayin da nake ba, sai Maryam ita ta kasance kaman roll model na domin komai na 'yan gayu ita ta koya min na fito cikin 'yan mata masu aji, dalilin Maryam da ta nace muka shiga wani catering school da sai da muka shafe watan ni sannan aka yaye mu yanzu ba wani nau'in girki da ban iya ba da snacks da drinks kala-kala, mostly in Yaya na zai zo sai nayi mishi.
Auren Yayan Maryam shi muka saka a gaba da za'ayi nan da wata 3 masu zuwa,sosai muke zuba tsare-tsaren mu dan so muke muke mu fita daban cikin 'yan biki.
Soyayyar mu da Yaya na kuwa sai abinda ya karu domin a kullum kaman kara wutan son junan ake a cikin zukatan mu tun Inna tana d'ari-d'ari har ta saduda ta tabbatar son so yake min lokaci kawai ake jira da zaran na kammala secondary school na za'a saka mana rana, tsakani na dashi ban san wa yafi zumud'i ba kullum cikin kirga kwanaki muke na zuwan lokacin.
Tsakanin su da Baba kuwa 😂😂 babu abinda ya canza dan Baba baya tab'a yarda su had'u duk yanda Yaya na ya kai ga son su gana amma yaki yarda kowani lokaci akwai excuse da zai nemo ya bada dan kaurace had'uwan nasu.
Dije anyi auren ta kusan wata biyar da suka wuce ta auri mijin ta mai suna Bala ba mai arziki bane amma akwai wadatar zuci da rufin asiri, ko bikin ma kowa sai son barka yake kasancewar anyi komai cikin tsari.
Hajara tana gida an kawo ta wanka satin da ya wuce bayan ta haifi d'a ba rai sakamakon yawan dukan da take sha wajan mijin nata ga yunwa da yake barin ta dashi sai dai Gwaggo Aisha tayi musu aike na kayan abincin domin yanzu tana samu ko sana'a ta daina yi duka bukatun ta Jameela ta d'auke mata su sakamakon samari masu kud'i da ta samu amma fa a cewar Gwaggo Aisha kenan dan ni dai ban tab'a ganin wani yazo kofar gidan mu neman ta da sunan zance ba sai dai inga taci kwalliya cikin matsattsun kaya ta fita kan zata je gidan kawaye in anyi sa'a ta dawo cikin dare ta kwana a gida wata rana kuma sai tayi kwana biyu bata dawo gidan ba, ta goge ta kara haske da kyau duk da hasken na shago ne.
Dawainiya kula da Yayar ta ma itace ta d'auka babu abinda ta rage ta dashi shi kuwa mijin tunda aka kawo ta gida bai kara bi ta kansu ba balle yazo ya duba ta ko yayi musu aike, wannan dalilin yasa Gwaggo Aisha d'aukan alwashin 'yar ta ta gama auren shi ko uban wa yayi mishi tsaye ta gama auren shi kenan.
Hura hanci da d'aukan kai da Gwaggo Aisha take a cikin gida sai wanda ya gani Inna Asabe take kula ta wani lokacin suyi tayi dan Inna ta kam ko iskar daya d'ebo ta bai ishe kallo ba.
Sosai take kokari na son ta burge Baban mu dan ta dawo da matsayin ta na da amma hakan ta bai cimma ruwa ba kasancewar Baban mu gaba d'aya hankalin shi ya dawo kan Inna ta domin ita komai zata yi mishi ko ta bashi bata yi mishi gori tsabanin Gwaggo Aisha da sai ta tsaya a tsakar gida take mishi terere kowa yana ji yana gani hakan yasa Baban fifita Inna fiye da kowa a gidan ita kuma Gwaggo Aisha wannan dalilin yasa tace asiri Inna tayi mishi kuma ko zata tafi tsirara sai ta karya shi.
*Albishirinku mata masu son kamshi da gyara ga dama ta samu zamu fara classes na koyar da turaren wuta kala-kala humra shima in different colors dilke gyaran amarya man gashi nd lots more kada ko yarda a baki labarai akan 300 kacal zaki zama pro na kan ki, duk mai bukata ta tuntubi wannan no 08172724281 sai mun ji ku*.
[1/26, 7:06 AM] Golden Pen Writer's Assoc: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
_A story about love and sacrifice._
_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_
*14*
_*From The Fantastic Writer of*_
```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```
*_And now_*
*_BA SONTA NAKE BA_*
✠*✠G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* âœâœ
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶Ãt̶̶є αs̶̶s̶̶Ãd̶̶Ãσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єÃv̶̶є n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶Ãc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶Ãv̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✠*,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ Ãt̶̶ w̶̶Ãl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶.*
*Addu'ar Mash'arul Haram*
Jabir, Allah ya yarda da shi, ya ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya hau taguwarsa mai suna Al-Kaswa har ya zo Mash'arul haram, sai ya fuskanci alkibla ya yi addu'a ga Allah, ya yi kabbara, ya yi hailala, ya kadaita Allah. Bai gushe ba a tsaye yana addu'a har sai da gari ya waye sosai, sannan ya dauki hanya kafin rana ta fito.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*14*
Gwaggo Aisha tana riƙe da ƙudirinta a zuciyarta na sai ta warware asirin da Inna tayi wa Baba ta maida hankalin shi kanta tayi mulkin ta a gidan son ranta saidai rashin kud'i shi yake kawo mata cikas dan Jameela ta kwana 2 bata dawo gida ba amma ta kudirta tana dawowa zata karb'a a hannunta taje ta gabatar.
Bayan kwana 2 Jameela ta dawo daga yawonta ba b'ata lokaci ta same ta da zancen ta bata dubu ashirin zata je gwaza wajan wani gawurtaccen boka da kawarta lantana ta bata labari dan yayi mata maganin Inna.
Ba musu balle bata lokaci Jameela ta cake mata dubu ashirin da biyar tace tasha ruwa da dubu biyar d'in,in so samu ne zata so ta had'a da ni a shafa min bakin jini ko d'an yankan kai daya makale min zai guje ni su ga ta tsiya . (hmmm wai Yayana take nufi.)
"Jameela wallahi kaman kin shiga zuciyata daman ita da kinibabbiyar uwarta duk shine takamarsu, kin ga in ya rabu da ita shikenan kowa ya huta tabbas hakan zamuyi zan fad'awa bokan ya shafa mata bakin jini da ko wani namiji sai ya guje ta muga ta tsiya".
Dariya Jameela ta kwashe da shi har suna tafawa da uwarta kaman wasu kawayen juna sannan tace"shiyasa nake son ki ummata".
Gwaggo Aisha ta bud'i baki zatayi magana suka ji muryan Hajara tana cewa "haba Umma wannan wani irin rayuwa ce,wayan nan bayin Allah babu ruwan su damu suna zaune da kowa agidan nan da zuciya d'aya amma ku burin ku shine ku cutar dasu ya kamata mu d'auki darasi ko akan abinda ya faru dani ga Jameela ta saka yawon karuwanci a gaba kina gan............"
Buge mata baki da akayi shi ya hana ta karasa maganan da tayi niyyan fad'a musu,hannu tasa ta dafe bakin ta daya fara mata zugi tana bin binsu da kallo idon ta cike da hawaye su kuma suna aikin aika mata muguwar harara
"Hajara ni kike gayawa magana akan wata banza can, ni mahaifiyar ki?" Gwaggo Aisha ke yiwa Hajara tsawa tana nuna kan ta da yatsa.
Gyad'a kai tayi kana tace "Ko da yake ba laifin ki bane ina ganin harda ke suka had'a suka tsafe dole sai na tashi tsaye ko kuma Bintu ta kaini ta baro,in banda aikin asiri tayaya zaki kira 'yar uwar ki wacce ta d'auki nauyin kulawa dake da wannan suna,. Kai jama'a kaji tsoron mutum Allah ya isa Bintu ki jira kiga yanda Allah zai wulakanta ki". Ta karasa cikin wani irin d'acin rai da tsantsan tsana.
Jameela da har ta fara jin haushin 'yar uwar ta amma jin abinda mahaifiyar su ta fad'a yasa taji ta huce ashe ba yin ta bane itama asirce ta sukayi, haba abin da mamaki a ce wai Hajara ke kare mu bayan a baya ta san yanda tafi kowa tsanan mu.
Da washe gari da sassafe Gwaggo Aisha ta fita tasha dan tafiya Gwaza domin cika nufin su akan mu.
**************************
A cikin wani tsadadden Hotel Zafar yayi parking motan na shi ba tare da ya cewa Sadiq ci kan ba ya kwashi wayoyin shi tare da bud'e murfin motan ya fita.
Fitowa shima Sadiq d'in yayi suka nufi hall da ake partyn tun kamin ka shiga zaka ji cool music na tashi ga wajan ya matukar tsaruwa komai cikin tsari da aji akayi shi.
Angon yana ganin su ya karaso da sauri ya tare su fuskar shi cike da farinciki, ricewa wajan yayi da hayaniyan zuwan nashi, ya d'an sake fuska kad'an yana amsa gaisuwan abokan shi bayan ya zauna a mazaunin shi.
Hankali kwance aka fara party shima Zafar ya saki ran shi sosai akayi shagali dashi tsab'anin wasu parties da yake guduwa saboda 'yan mata masu takura mishi amma wannan har aka tashi yana nan dan babu mace ko d'aya .
Yau tunda na tashi sai shirye-shiryen zuwan Yaya na nake saboda yau kwanan shi kusan 3 kenan baya gari yayi tafiyan nan nashi da na tsana dan yanzu sosai wannan tafiyan nashi yake bani haushi ko wani sati sai ya ciri tafiya har ta kai ina yawan fad'a mishi kan wallahi in munyi aure babu inda zai tafi ya barni kafa ta kafar shi ko kuma ya daina tafiyar gaba d'aya, dariya kawai zai min a duk lokacin da na fad'i haka baya ce min komai.
Tun kamin sha biyu tayi na gama girkin da zanyi mishi harda su drinks na adana su na shiga wanka,ko da na fito azahar tayi,alwala nayi na tada sallah.
Light makeup nayiwa fuska sannan na kama kalaba da Inna tayi min da ribon dan gashi na baya kitsuwa sam.
Riga da skirt na wani material peach color na saka kayan sun zauna a jikina duk da ba wani matse ni suka yi ba,ban saka hijabi ba rolling kawai nayi da gyalen mai d'an fad'i sannan nabi jikina da turaruka kusan kala hud'u amma duk masu sanyi ne wanda sai ka zo kusa dani kamin kaji kamshin sa.
Ina gama shiryawa kiran sa na shigowa cikin tsantsan farinciki da zumud'i na daga cikin tsigar shagwab'a da zallan so na ce" Yaya naaaaa"
Ina jin shi ya sauke nannauyen ajiyan zuciya ya kasa magana sai can ya samu daman cewa " pls Baby ki fito mana in gan ki ko zan samu natsuwa I'm damn missing you "
Dariya na kyakyale dashi tare da make kafad'a kaman yana gani na nace" ni fushi nake da kai dan haka ko gobe ba zaka ganni ba ina gama fad'a na kashe wayan gaba d'aya ina mishi dariyan muguta.
Dariya shima yayi yana girgiza kai ya san fad'a kawai nayi ko baiga fuskata ba ya san na fishi zumud'i.
Na share kusan minti 15 sannan na d'auki karamin basket dana shirya mishi abinci a ciki na fita, fuskata a d'aure tam na fito tsab'anin da, da nake fitowa daga gida kuma ko kad'an naki yarda mu had'a ido dashi.
Ciki-ciki nayi mishi sallama ina kawar da kaina gefe ni a dole ina fushi, amsa sallaman yayi da murmushi akan fuskar shi yana leka fuskata, cikin tsigan tsokana yace"wannan duk fushin ni kad'ai akewa,ban san me zai biyo baya ba in nace miki gobe da safe zan koma wajan aiki."
A wani dame na juyo ina kallon shi da ido duk a waje hannu na na dama kuma dafe da kirji na.
Dariya ya kwashe da shi har yana rike ciki ganin yanda duk na rikice lokaci 1 yace "nima na rama munyi one-one kenan,ba ni kika shanya ba har na minti 15 ba".
Kukan shagwaba na saka mishi har da bubbuga kafa a kasa rarrashi na ya fara tare da cewa inyi hakuri ya daina da kyar ya samu na daina kukan shagwaban na gabatar mishi da abincin da nayi mishi, asual yaci sosai har da santi kaman yanda ya saba yace yayi missing d'in abinci na.
"Kaine kake ja mana lokaci da kaso da anyi komai ya wuce abinci kuma sai ka ture" nace ina hararrar shi ta kasan ido.
Murmushi kawai yayi ba tare da ya tanka ba, ni dai kwana 2 nan wannan abin nashi yana damu na sai dai ban nuna mishi ba a duk lokacin da zanyi maganan auren mu ba zai tab'a ce min komai ba.
Haka yau ma na daure zuciya ta mukayi hirar mu da zai tafi ya kwaso tsaraba ta harda na 1su Inna da Baban mu ya bani sannan mukayi sallama ya wuce.
Karfe tara da kusan rabi sannan su Gwaggo Aisha suka d'auki hanyan Gwaza bayan sojoji sun tabbatar musu da hanya lafiya babu wani abin tsoro,shiru motan nasu kake ji tunda suka bar gari suka shigo cikin jeji kaman babu kowa a ciki sai karan engine motan, mafi yawan mutane dake ciki sai addu'an Allah ya sauke su lfy suke banda Gwaggo Aisha data rufe ido tana ayyana yanda zata taka kowa a gidan son ran ta sannan ta shimfid'a mulkin ta har yafi na baya.
Kiiiiiiiii karan kama buriki da taji da karfin gaske shi yasa ta bud'e ido a firgice tana dube-dube, salati da taji 'yan motan suka fara yasa ta kalli gaban ta ba shiri.
Kululuuuu taji cikin ta ya bada wani kara a take taji guduwa na son zubo mata hannaye duka 2 ta d'aura akai ta zunduma ihu tana " wayyoo Allah na shiga uku yau me zan gani haka ni shatu?"
Mutane ne sun kai kusan su hamsin fuskar su a rufe kowanne d'auke da bindiga su tare gaban motan nasu sai muzurai suke.
Kowa na cikin motan jikin shi sai karkarwa yake masu kuka nayi masu addu'a nayi Gwaggo Aisha kuwa sai ihu take zunduma musu iya karfin ta gaba d'aya ta fita hayyacin ta yau ga ita ga boko haram.
A fusace wani daga cikin su ya d'aga AK47 din dake hannun shi ya fara harbin sama ba shiri kowa yayi tsit, Gwaggo Aisha ko harda sake fitsari saban rud'ewa da firgita da tayi.
Su kaman 5 suka matso gaban motan suka bud'e kofan motan suka ce kowa ya fito kuma duk wanda ya musu wani rawan kai ko kuma taurin kai yanzu zasu aika shi barza'u.
Tsimi-tsimi duk suka fito matan su da mazan su aka saka sukayi layi , su kuma sauka rabu kashi-kashi wasu suka tsaya nan dasu Gwaggo Aisha wasu kuma suka tafi taro sauran motoci masu wucewa.
"Kowa ya kawo kudin da yake jikin shi da wayan ku gaba daya" cewar wani a cikin su gashi da babban murya kana jin hausan zaka san koya yayi.
Layi sukayi suna jefa kud'add'e da wayoyin su a cikin wani katon kyale da suka shimfid'a a k'asa.
Suna gama zuba duk abinda suka mallaka babban cikin su wato Amir din su yace musu saura suturan jikin su duk su ciro su kawo suma ba mata ba maza.
Kallon kallo suka fara a tsakanin su dan basu fahimci me suke nufi ba.
"Ku cire kayan ku duka ku zuba su anan nace" ya kara daka musu tsawa daya kara hargitsa su suka kama karkarwa amma babu wanda yayi yunkurin cirewa.
Tau kake ji suka d'auke wani saurayi da bindiga babu wani nisa tsakanin shi da Gwaggo Aisha.
Kaman kiftawan ido suka fara rige rigen cire kayan jikin su, aka kwashe duka aka zuba su cikin wani buhu sannan suka umarci driver da su shiga mota su koma cikin Maiduguri a haka.
[1/26, 7:06 AM] Golden Pen Writer's Assoc: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
_A story about love and sacrifice._
_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_
*15*
_*From The Fantastic Writer of*_
```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```
*_And now_*
*_BA SONTA NAKE BA_*
✠*✠G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* âœâœ
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶Ãt̶̶є αs̶̶s̶̶Ãd̶̶Ãσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єÃv̶̶є n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶Ãc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶Ãv̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✠*,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ Ãt̶̶ w̶̶Ãl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*15*
Shiru cikin motan kaman ba wani mai rai a ciki sai muryan mata da suke kuka kasa-kasa saboda kukanta su da akai babu mai kallon d'an uwan sa duk sun takure waje d'aya suna tunanin tayaya zasu shiga gari a haka? Ita kuma Gwaggo Aisha tana ganin kaman kaifin asirin Inna shi ya hana ta zuwa ga wannan mashahurin bokan har 'yan ta'addan suka samu daman yi mata aika-aika.
A wani kauye driver ya tsaya Allah ya sa akwai wani tsumamun riga da ya maida duster yana goge-goge dashi a cikin motan, shi ya saka ya fita ya karasa cikin kauyen yayi musu bayanin halin da suke ciki, nan da nan mai garin yasa aka hado musu suturu na maza da mata ya kai musu dan ba karamin tausaya musu sukayi ba.
Koda ya kai musu kayan kowa ya d'auka ya suturta jikin sa sannan suka mike hanya zuwa cikin gari.
Azahar dai-dai suka shigo driver ya zubar da kowa nan cikin tasha ya kama gaban shi, Gwaggo Aisha da kyar taja kafafun ta da har yanzu rawa suke saboda firgita ta fito ta samu adaidaita sahu zuwa gida duk da ta san bata da ko sisi a hannu.
A hanya ji take kaman kada taje gida ta wuce ko gidan 'yan uwan ta ko zata samu canza suturan dake jikin ta wai kada su Inna su raina ta, canza akalan tafiyan tayi daga gidan mu zuwa gidan kanwar ta.
Da yake duk tafiyar su d'aya da kanwar nata da taji abinda ya faru da Gwaggo Aisha maimakon ta nutsar da ita ko ta d'aura ta kan hanya saima kara zuga ta da ta rinka yi harda cewa ta samu kudi ta kara komawa, kuma kar ta kuskura ta nuna gazawar ta har sai ta kawo karshen Inna ta.
Da wayan nan kalaman nata ta kara karfafa mata guiwa, sai bayan sallahn magriba ta dawo gida hankalin ta kwance kaman babu abinda ya faru, anyi sa'a Jameela tana gida cikin murna ta tarbe ta kannuwan ta duk sun zaku da son jin daddadan labarin yanda sukayi da boka, Hajara tana yi mata sannu da zuwa ta fice ta bar musu d'akin tare da nema musu shiriya daga rabbi.
"Umma wannan wani irin magana ne haka kike cewa ko kuma dai sabon rainin hankali da kika zo dashi kenan?" Muryan Jameela ke tashi daga cikin dakin nasu cikin tsawa kaman ba da mahaifiyar ta take magana ba.
"Na lura tunda nace ki daina sana'a zanyi miki komai kika koyi wasa da kud'i saboda baki sha wahalan neman su ba, toh wallahi nima daga rana rin ta yau na daina baki kud'i na sai dai ki koma yin sanar ki dan ba zan iya ba" ta karashe tana harare-harare ita kad'ai.
Gwaggo Aisha kin kula ta tayi ta shige can d'aki ta rabu da ita domin ta lura asirin ta take son tonawa gaban kishiyoyi wanda ba zata tab'a bata daman hakan ba duk da kwanan nan alamun karara sun fara bayyana cewa Jameela ta fara tab'a shaye-shaye.
Hajara kam tana gefe tana sauraron su bata da daman saka.
baki Gwaggo Aisha ta hau kan ta da bala'i, Jameela ta gama suratan ta tayi ficewar ta.
Bata bawa kowa labarin abinda ya same su a hanya ba ta had'iye kayan ta amma ta kudiri aniyar neman kud'i tukuru domin ta samu tara kud'i ta koma wajan bokan ta.
Ko sati bai kai ba muka ga ta fara sana'ar ta na abinci kaman yanda ta saba sai dai banbancin yanzu almajiri keyi mata tallah saboda bata da yara kanana yanzu.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya wata rana dad'i wata rana kuma akasin ta, sai dai mu kam babu abinda ya canza a soyayyar mu sai ma karuwa da yake a ko wani dakika cikin zukatan mu.
Cikin ikon Allah yau muka gama waec d'in mu muka fito cikin farinciki muna taya juna murna tare da fatan Allah yasa mu fito da sakamako mai kyau, IV muka shiga rabawa kawayen mu na dinnern auren yayan Maryam Shamsuddeen wanda za'ayi sati mai zuwa.
"Yaushe zaki zo gidan mu muje saloon tunda shine kad'ai ya rage mana cikin shirye-shiryen bikin?" Maryam ke tambaya ta bayan mun fito daga makaranta.
"Toh uwar zumud'i in kin manta let me remind u auren fa saura sati". Nace ina aika mata da hararan wasa.
Dariya tayi sosai sannan ta ce" nafi ki sanin cewa saura sati kuma ai ba cewa nayi muje yau ba ko?"
"A toh ai na zata tsabar zumud'i yasa kin d'auka yau ne auren,ni ya kamata inyi wannan rawan kafar kin ga munyi waec d'in mu Allah yasa kada Baba yace sai anyi neco za'ayi bikin mu da Yaya na ayi mana yanzu wallahi in lokacin yin neco yayi sai ya rako ni muzo tare ina yi mishi 'yar...."
Duka da Maryam ta d'ad'a min a baya shi ya hana ni karasa magana ta, ina sosa wajan nace" ke me yasa kin cika mugun ta ne?"
"Ke ko kunya ba kya ji, bari in yi hanzarin zuwa gidan ku in fad'awa Inna tayi saurin aurar dake kada ....."
"Da kin taimaka min kuwa dan Allah zo muje ki gaya mata yanzu " nace in riko hannun ta.
Warce hannun ta tayi tana" Allah ya shirye ki Zareefa". Mukayi dariya dukan mu.
A nan mukayi sallama ta shiga motan su da driver yake jiran ta nima na shiga a daidaita da yake zuwa d'auko kuma ya kawo ni makaranta kullum kaman yanda Yaya na ya tsara.
Tun daga wannan rana bamu kara had'uwa da Maryam ba suna can hidima tayi musu yawa amma kowacce rana sai munyi waya kuma tana neman inje in taya ta wasu abubuwa sai dai kwata-kwata bana cikin natsuwa kasancewar Yaya na yau kusan kwanan shi 5 kenan da yin tafiya amma shiru bai dawo ba kuma wayar shi bata shiga balle inji lafiyar shi.
Wannan dalilin yasa bani da kwanciyar hankali sam shiyasa na kasa zuwa gidan su Maryam d'in, haka kawai kuma nake jin yawan fad'uwar gaba har na kasa daurewa na fad'awa Inna tace min inyi ta addu'a ba abinda zai faru.
A haka na daure nake dan al'amura na har ta kai gobe ne dinner gidan su Maryam kuma tun safe ta matsa min da waya kan yau bata son wani excuse lalle inzo da safe dan akwai abubuwan da zamuyi, ba dan ina so ba na amsa mata da toh kawai na katse waya ta dan rashin jin labarin Yaya na ya sanya bana jin dad'in duniya sam.
Da washe gari ma Inna ce ta matsa min akan in tafi tun safen tunda haka ta bukata ko akwai ayyuka da zan kama musu itama tana zuwa anjima kad'an,dole na na shirya nayi mata sallama na fita.
***********************
Tun jiya yaje tsadadden saloon da yake zuwa aka aske mishi gashin da ya tara kuma akayiwa askin zamani, sanin cewa in Abba shi ya gani ba zaiyi mishi da sauki ba , ko da yaji Abban nashi ya dawo duk daukin son ganin shi da yake sai da ya d'auko natsuwa da jarumta sannan ya nufi part din iyayen nasa cikin fargaban kada yayi mishi maganan aure.
A parlour ya tadda su zaune suna hira Abba na shan fruit salad da Momy ta had'a mishi da kan ta.
Kusa da kafafun shi ya karasa ya zauna tare da d'aura kan sa akan cinyan Abba ya kwantar, cikin tsantsan kaunar tilon d'an nashi ya hannu yana shafa kan a hankali fuskar shi d'auke da murmushi yana matukar son d'an nashi sai dai wasu halayan da ya kwaso marasa kyau ya d'aurawa kan shi yasa basa shiri, ganin sa cikin shigar kamala kad'ai yau yasa shi farinciki.
Babban burin shi yanzu shine yaga d'an nashi yayi aure ko zai natsu ya daina abinda baya so sannan shima girma ya fara zuwa mishi yana bukatan hutu yana son d'aura shi kan d'inbin dukiyar shi da shi kan shi bai san iyakar su ba.
Cikin girmamawa yayiwa Abban nashi barka da zuwa shima ya amsa cikin kulawa, zama ya gyara ya d'auki spoon d'in da Abba shi ke shan fruit shima ya fara sha yana kai na farko baki ya lumshe ido yace" Mom ji yanda wannan fruits din yayi dad'i amma ni in nace ki min ba yayin dad'i haka".
Mom tana dariya tace" kayi aure matar ka zata yi maka wanda yafi wannan dad'i".
Ras yaji gaban shi ya fad'i meya kai shi fad'in haka gashi har an tabo zancen da baya so ayi ta agaban Abba, shima dariyan yayi da son kawar da zancen yace" yauwa Mom abokinaboki na shamsuddeen nan da kike ta yabon shi kullum gobe ne fa auren shi anjima kad'an ma zan je dinnern kuma dasu Sadiq....."
"Aikin kenan zuwa dinnern wasu amma kai baka tab'a tunanin kaima kayi settling down, ko har yanzu kana tsamanin yaro kake komawa?" Abba ya katse musu zancen cikin daure fuska da zaka san ran shi a bace yake.
"Anyway duk ma laifi na ne da na zuba maka ido ina kallon ka da sunan ina jiran ka kawo min matar da kake so da kan ka,but tunda baka fahimta ba let me make my self clear, kwana 3..... Wallahi kwana 3 kacal na baka in baka fito da wacce kake so ba kauye zan je in samo maka mata cikin 'ya'yan dangi, in kuma ka d'auka wasa nake maka ka jira kwana 3 ka gani" Abba yana gama maganan shi ya mike fuuu ya bar musu parlon.
Cikin wata irin murya mai cike da tashin hankali ya rarrafo gaban Mom ya fara magana" Mom pls ki bashi hakuri wallahi ni banida wacce nake so a yanzu dan Allah ya kara min lokaci wallahi zan kawo ta har nan ku gan ta".
"Wannan karon nima babu hannu na a ciki saboda ka kai Abban ka makura sannan ni kaina ina son ganin auren ka ko dan jikoki su cika mana gida, so count me out of this" itama tana gamawa tabi bayan mijin ta suka bar Zafar cikin fargaba da tashin hankali.
[1/26, 7:06 AM] Golden Pen Writer's Assoc: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
_A story about love and sacrifice._
_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_
_*From The Fantastic Writer of*_
```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```
*_And now_*
*_BA SONTA NAKE BA_*
✠*✠G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* âœâœ
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶Ãt̶̶є αs̶̶s̶̶Ãd̶̶Ãσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єÃv̶̶є n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶Ãc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶Ãv̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✠*,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ Ãt̶̶ w̶̶Ãl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αÃn̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*16*
Zafar ya kai kusan 30 mins a zaune wajan sai share gumi yake duk da sanyin A.c dake parlor amma bai hana shi jikewa da gumi ba, ta ina ma shi zai nemo mata cikin kwana 3 kacal, shi fa ya raina 'yan mata 9ija kuma koda yayi karatu abroad bai samu wacce ta kwanta mishi a rai har yace zai iya auren ta ba.
Ringing d'in waya ne ya dawo da shi hayyacin sa amma ya kasa d'aga hannu ya d'auki wayan balle ya amsa,sai da akayi mishi 2 missed calls a na 3 ne ya d'auki wayan ya kai kunne yayi shiru.
"Zafar kana ina ne baka karaso ba, tun d'azu Shamsuddeen ya dame ni da na kira ka wai har an kusan tafiya hall" muryan Sadiq yaji cikin wayan yana magana, bai iya bashi amsa ba ya cire wayan daga kunnen shi ya mike a hankali ya fara tafiya cikin kasaita daya zame mishi jiki.