Complete Hausa Novels

Ba Sonta Nake Ba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Ba_Sonta_Nake_Ba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 2 of 2

Part d'in shi ya shiga bai tsaya a parlour ba ya wuce bedroom ya fad'a kan makeken gadon shi da a kalla zai lashe mutane 7 ba tare da wani takura ba, tunani kawai yake tayi dan komai na duniyan ya fice a ran sa bare zuwa bikin nan, bai dad'e da kwanciya ba d'ayan wayan shi ya fara ringing shima kaman ba zai d'aga amma ya daure ba tare da ya lura da sunan mai kiran ba ya amsa wayan, muryan ango Shamsuddeen yaji yana mishi magana.

"Haba Zafar yanzu ka kyauta min kenan, har an fara shagalin biki na baka ciki?"

"No Shams it's...., No just ba zan iya zuwa ba saboda wani dalili nd......"

"Dan Allah mana kada kace haka please ko minti 2 ne Zafar we really need u here ,pls I'm begging..."

"Stop that mana sai ka roke ni ne zan zo bikin ka, aiko saboda Sadiq zan zo ko yanzun ma wani issue ne yake son shige min gaba but gani ni nan zuwa tunda kace ko minti 2 then I will come sai dai ba zan dad'e ba" yana gama fad'in haka ya katse wayan tare da mikewa zuwa bathroom.

Can b'angaren su Ango kuma sadiq yana kallon Shamsuddeen daya gama waya yace" ya zai zo d'in?"

Gyad'a kai shamsuddeen yayi yana murmushi suka cigaba da shirin su.

******"""""*******

Tunda nazo gidan bikin na daure zuciya ta ake ta hidima da ni sai kai komo muke, cikin wannan yanayin ban fasa trying number Yaya na ba sai dai amsar daya ce a kashe har a wayan Maryam na gwada wai ko daga layi na ne a natan ma switch off ake ta maimaita min, bayan munyi sallahn la'asar Maryam ta takura min muka tafi saloon inda akayi mana gyaran gashi lalle sannan aka mana kwalliyan mu.

Muna dawowa daga saloon muka saka ankon mu na material Les dark blue da tie milk color sosai kayan suka zauna a jiki na, nayi wani kyau ina haske sai ka zata nice ma Amaryan , Maryam itama tayi kyau sosai abinta,

Lokaci yanayi mutane suka fara tafiya ga motoci birjik sai wanda ka zaba zaka shiga wasu kuma a nasu suke tafiya, duk yanda Maryam tayi min nasiha kan in saki raina cikin jama'a in kwantar da hankalin na Yaya na yana lafiya amma na kasa.

Ko da muka isa ma banyi wani abu ba na nemi waje na zauna kan wani table da babu kowa saboda ina bukatan kad'aici na fad'a duniyar tunani anya Yaya na lafiyan shi kuwa Allah yasa haka Allah ya kare min shi duk inda yake Ameen.

Haka na cigaba da tunanin shi ina yi mishi addu'a Allah ya kare shi yasa yana cikin koshin lafiya tare da kokuwa da hawaye cikin ido na da suke ta bara zanan zasu fito ina maida su ciki.

****************

A hankali yake takun sa cikin natsuwa da kasaita ya nufi wata bakar latest Honda wanda zai fita dashi, tsab yake kaman wani basarake yayi matukar kyau cikin half jamfa na wani arnanen voile milk color mai duhu wanda ya kara haska farar fatan sa, bai saka hula ba,gashin kan shi da sajen shi sun sha gyara sun kwanta lub sai sheki suke sai kamshin tsaddaun perfumes d'in shi yake, bai yiwa iyayen nashi sallama ba ya fad'a motan shi yaja ya tafi.

Sowan abokan sa sosai ke tashi a lokacin da ya iso na murnan zuwan nashi dan wasu sun fidda ran cewa zai zo, bai biye musu ba hannu kawai ya d'aga musu ya wuce ya samu waje ya zauna yana auna maganan Abban shi wai shi zai had'a shi aure da 'yar kauye shida na birnin ma basa burge shi in aka aura mishi ita ko Ina zai kai ta, oho.

Yana cikin zancen zuci yaji an dafa mishi kafad'a a dan razane ya d'ago yaga Sadiq ne tsaye a kan shi yana mishi murmushi yace " lafiya kake kuwa tun d'azu ina tsaye s kan ka ina maka magana baka ji ba har sai da na tab'a ka, kuma baka je kun gaisa da Shams din ba kazo ka zauna kai kad'ai".

Zafar kallon shi kawai yayi ya d'auke kai ba tare da yace mishi ci kan ka ba kuma bashi da niyyan tankawan.

A zuciye Sadiq ya mike zai bar wajan yana fad'in " d'an rainin hankali kada Allah yasa kayi maganan ai dama ka saba wulakanta mutane...".

Caraf yaji Zafar ya riko hannun shi ta baya tare da dawo da shi baya fuska a had'e yace" seat"

Ba musu Sadiq ya koma ya zauna yana mai nazarin yanayin Zafar d'in ,duk da bai cika faran-faram da mutane ba amma yaga tarin damuwa da tashin hankali a tare da shi kasancewar shine mafi kusanci dashi bayan iyayen shi.

"Wats wrong u look so disturbed?" Sadiq ya tambaya cikin kulawa.

Hannun shi duka 2 ya d'aura a goshi yana murzawa kaman ba zai amsa ba can kuma yace" ina cikin damuwa Sadiq kasan yau Abba ya dawo da naje...."

"But naga kayi aski ai ko an bashi labarin kaje wani party ne?" Sadiq ya tambaya yana dariya.

"Shut up just shut up it'ss not a joke ina gaya maka damuwa na nd u e making fun of me" Zafar ya katse shi a hasale.

"I'm sorry sorry pls I don't mean it naga kawai shine matsalan ka da Abba most time" cikin rarrashi da kwanantar da murya Sadiq yake magana yaga da gaske abokin nashi ya fusata.

"In wannan ne da sauki kaima kasan ba zai dame ni ba cos I'm used to it " sai da ya sarara yana had'iyen zuciya alaman abinda zai fad'a ya mishi zafi yace "can u imagine abba ya bani 3 days wai in kawo matar da zan aura ko ya had'a ni da 'yar kauye".

Dariya Sadiq ya kwashe da shi harda rike ciki yace" kai nagodewa Abba yayi min maganin ka Wallahi ba ka raina 'yan matan Nigeria gaba d'aya ba, shikenan anyi maka mai kankat waya ga Zafar da village girl.

Kasan me on ur wedding day ko kuma on ur dinner with d village girl nine zan....."

A fusace Zafar ya mike ya koma wani table ya bar Sadiq na kwasan dariyan mugunta, yana zaune a wajan sai saka da warwara yake na yanda zai zillewa auren da Abba keso ya lik'a mishi idon shi ya sauk'a a kaina da nake zaune a gefe ni kad'ai kai na a sunkuye kan waya ta sai neman layin Yaya na nake da bata shiga.

Ido ya zuba min ko kiftawa baya yi harda tagumi yayi kana ganin shi kasan yayi zurfi cikin nazari ni kuma ban san wainar da ake toyawa ba.

Tab'a shi da akayi ya dawo dashi daga dogon tunani daya tafi ya juya yaga Sadiq ne, gira daya ya d'aga mishi yana murmushi yace " da alama dai Abba ba zai had'a ka da village girl ba".

Cikin sauri shima ya amsa yana" yes I won't let dat happen Sadiq, look at dat girl Sadiq" yace tare da kallon inda nake zaune, bin wajan da kallo Sadiq yayi kamin yace" yes na ganta tun a can nake kallon yanda ka tsare 'yar mutane da ido, so finally Zafar got d love of his life,love at first sight huh"

Buge mishi kafad'a Zafar yayi yana hararan shi yace " dallah can who told u I love her kaima ka san abinda ba zai tab'a yiyuwa bane *BA SONTA NAKE BA*. I just have plan on her dat will free me from Abba".

Masu tambayan karshen Uwani ku kara hakuri shima zan cigaba nan bada dad'ewa ba.
[1/26, 7:06 AM] Golden Pen Writer's Assoc: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*17*

Komawa yayi ya zauna bayan ya tsurawa Zafar ido sannan yace" ban gane me kake nufi ba, *ba sonta kake ba* pls ka warware min ka saka ni a duhu" cewar Sadiq kenan.

Ajiyan zuciya ya sauke mai nauyi irin ya samu relief d'in nan yace" well ba wani abu bane just zan kai ta a matsayin wacce zan aura wajan Abba in akayi auren shikenan I'm a free man ba mai takura min akan rashin aure in tayi 1 or 2 month sai in sallame ta, that's all".

"What!! " Sadiq ya fad'a cikin zare ido sannan ya cigaba "Zafar me kake nufi da cewa zaka aure ta bayan wata d'aya ko biyu ka sallame ta, rayuwar 'yar mutane zaka lalata saboda cikan burin ka, haba my friend kada ka zama mai son kan ka mana wannan abinda kake yunkurin yi kuskure ne Babba".

Wani kallo Zafar ya watsa mishi na irin ka raina ni nan ya kawar da kan shi gefe kaman ba zai tanka ba ya bud'i baki yace " did u expect har wani abu zai shiga tsakani na da ita ne?

Zata amsa sunan mata tane a idon duniya but a zahiran ce ba haka bane kaima kasan irin wa'yan nan yaran ko kallo basu ishe ni ba balle ace zan so irin su ko kayi tunanin ni Zafar zan had'a shimfid'a da ita" ya fad'i hakan yana yatsina fuska kaman yaga kashi, shi dai Sadiq bai katse shi ba illa zuba mishi ido da yayi yana sauraron shi.

"Zanyi hakan ne kawai dan samowa kai na mafita dan haka stop dreaming cos ni *Ba sonta nake ba* as I said earlier" ya karasa fuskar shi d'auke da sansayan murmushi.

Har yanzu Sadiq ya kasa samun kalma ko d'aya da zaiyi amfani da shi ya gane abinda yake babban kuskure ne, shi kuwa hankali kwance ya zuba min ido yana kare min kallo a lokacin Maryam tana tsaye a kaina kan lalle sai mun shiga cikin masu rawa muyiwa Ya Shamsuddeen liki amma nace mata ba zan shiga zan koma gida saboda zazzab'i da naji yana son rufe ni.

Bata yarda ba sai da ta d'aura hannun ta kan goshi na taji zafi rau, a take taja kujera dake opposite da nawa ta zauna fuskarta d'auke da dumbin damuwa ta kama hannu na tace" Zareefa pls ki kwantar da hankalin ki nasan damuwa da kika saka a ranki shi ya haifar miki da zazzab'in nan,addu'a ya kamata muyi tayi Allah ya dawo dashi lafiya" duk cikin sanyin murya da tsigan lallashi take maganan.

Cikin son sakani dariya tace " ke nifa nafi ki damuwa Yayan mu ya dawo musha biki kin ga da bikin ku ne da muna can high table ba nan ba"

Ta koyi nasara dan murmushin da ban shirya ba ya tsubuce min tare da hawayen da nake shanye su tun d'azu, Maryam ba zata tab'a ganewa ba ni kad'ai ce na san yanda nake ji a cikin zuciya ta.

Rarrashi na Maryam ta fara da kyar ta samu nayi shiru ina ajiyan zuciya duk su Zafar suna kallon mu daga inda suke zaune, mikewa nayi ina gyara head tie dake kaina nace mata " zan tafi Maryam dan Allah kada ranki ya b'aci yanzu haka har na fara jin sanyi yana son rufe ni".

"No babu komai muje in raka ki but tayaya zaki tafi bayan baki da lafiya?" Maryam ta tambaya cikin kulawa.

Zan iya kada kiji komai" na bata amsa ina dafa kaina da nake jin kaman ya fashe.

"Thats d right time " cewar Zafar tare da shuran car keys d'in shi akan table , ba tare da ya juyo ba ya cewa Sadiq" zo muje".

Biyo shi Sadiq d'in yayi yana son yaga mai zai yi da yake cewa wannan shine right time, can gefen wasu flowers ya samu ya tsaya bayan ya fito daga cikin hall, Sadiq shima gefen shi ya samu ya tsaya.

Ko minti 3 basu yi da tsayuwa ba muka fito muma daga cikin ina tafiya a hankali ,har muka iso inda suke ni ban san da mutane a wajan ba naji muryan Maryam tana " Ya Sadiq ina wuni ku"

Sadiq d'in ne kad'ai ya amsa da " lafiya lau Maryam ya kuka fito lafiya kuwa?"

"Wallahi k'awa tace bata da lafiya shine na rako ta zata tafi gida"

"Subhallah Allah ya bata lafiya, amma ba zata iya driving a wannan yanayin ba ko da driver tazo?" Sadiq ya kara tambaya.

"No zan rakata bakin hanya ta hau napep ne".

"Allah ya bata lafiya" yace tare da kallon Zafar daya d'auke kan shi kaman baya jin me suke cewa alhalin duk hankalin shi yana kan mu.

Zungurin Sadiq yayi tare da yi mishi magana da ido, cikin sauri Sadiq yabi bayan mu ya tsaida mu yace " nan anguwan abin hawa yana wahala bari mu sauke ta tunda muma fita zamuyi"

Cikin farinciki Maryam ta fara musu godiya tare da jan hannu na zuwa wajan wata mota daya bud'e mana, da ido nakewa Maryam nuni da ba zan shiga motan su ba ita kuma ta min nuni da babu komai 'yan gida ne, rashin karfin jiki da hajijiya da nake ji ya bata daman tusa ni a bayan motan ta rufe tana d'aga mana hannu.

Kwantar da kaina nayi a jikin seat d'in tare da lumshe ido na fara shak'an wani fitinannen kamshi da ban tab'a ji ba a rayuwa ta, ina ji motan ya fara tafiya amma na kasa bud'e ido na can naji Sadiq d'in yana tambaya ta wani anguwan zasu sauke ni? Sai da naji a jiki na alaman ana kallo na ban damu da in bud'e ba saboda nasan sunan anguwan mu da na fad'a ne ya bashi mamaki kasancewar duka gidajen talakawa ne a anguwan.

"Sai ki nuna mana inda zamu bi mun shigo anguwan naku" muryan Sadiq ya katse min tunani, a hankali na bud'e ido sannan na nuna mishi hanya da zamu bi can nesa da gidan mu nace ya sauke ni anan.

Parking yayi daga gefe na bude kofan na sauka sauka a hankali cikin muryana mai sanyi da baya fita sosai nace " nagode jazakallahu khairan" na kama hanyan gida ina layi,da ido Sadiq ya rakani har na shige ciki.

Gyaran murya Zafar yayi wanda ya dawo da hankalin Sadiq ya juyo yana kallon shi yace" sai ka gaya min ma'anan kawo ta gida sannan dan wulakaci kaja baki kayi shiru na tabbata bata san mu 2 muka kawo ta ba.

"Mu tafi Mallam ba wai ka kama min tambayoyi ba" Zafar yace hankalin sa na kan wayan shi, girgiza kai kawai Sadiq yayi yaja motan suka fita daga layin dan wannan halin abokin nashi ya ci ace ya saba.

Da kyar na kai kaina d'akin mu na zube a gefen Inna da take kwance a kan gado,a firgice ta tashi zaune saboda ta fara bacci kuma bata ji shigowa ta ba.

"Wani irin rashin hankali ne wannan zaki shigo min d'aki ba sallama sannan kuma ki fad'o min a ka sai kace wata 'yar maye, ko daga wajan bikin kika koyo ne..." Shasshekan kuka na da taji shiya dakatar da ita daga fad'an da take min cikin fargaba ta d'ago ni ta fara dudduba jikin na tana tambaya ta meya faru???

"Inna Yaya na yau kusan sati da yin tafiya amma har yanzu babu labarin shi ga wayar shi bata shiga, Inna tsoro nake ji anya yana lafiya kuwa? Yaya na ba zai tab'a mantawa dani ba har na tsawon sati ba tare da yaji lafiya ta ba Inna kin..." Rufe min baki da Inna tayi da hannun ta yasa nayi shiru ina kallon ta hawaye na bin fuska ta.

"Babu abinda ya same shi insha Allah yana cikin koshin lafiya,bana son kina sawa kanki damuwa dayawa ki bari zuwa gobe da safe sai mu san yanda zamu bullowa lamarin" duk cikin rarrashi take min magana hannun ta kuma na kaina tana shafa gashina daya sha gyara ya kwanta yayi lub.

Jin ina sauke ajiyan zuciya kuma numfashi na fita d'aya-daya yasa ta gane nayi bacci, gyara min kwanciya tayi tare da zuba tagumi ta zauna tunani yanda zata bullowa wannan al'amarin domin babu abinda yake d'aga mata hankali kaman ganin tilon 'yar ta cikin tashin hankali, balle ma wannan na soyayya.

Kusan raba dare Inna tayi kan sallaya tana nafilfilu tare da kai kukan ta wajan Rabbi izzatti ya shiga lamuran 'yar ta ya zaba min abinda yafi alkhairi.

Koda gari ya waye da kyar na tashi daga kan gado nayi sallah na kara komawa na kudundune cikin bargo ina rawan dari saboda sabon zazzab'i da ciwon kai daya tsanan ta min, cikin matukar damuwa Inna ta had'a min tea mai kauri ta lallab'a ni na sha kad'an sannan ta b'allo paracetamol 2 ta bani tace in sha zuwa azahar in babu sauki sai mu tafi asibiti.

Cikin ikon Allah ina kwanciya bacci mai nauyi yayi gaba dani sakamakon jiya ban samu ishasshen bacci ba, gaba d'aya fita daga d'akin Inna tayi wai kada tayi wani babban motsi ta katse min bacci anan ta cigaba da ayyukan ta cikin dauriya.

Kaman a cikin mafarki naji waya ta tana ringing, da kyar na bud'e ido na da suka min matukar nauyi.

A zabure na tashi na zauna ganin sunan da na gani yana yawo kan screen d'ina, a hanzarce na d'aga kiran na kai kunne na kamin ya min magana na fashe mishi da matukar kuka kaman zan shid'e.

"Ki fito ina waje" yace min cikin wata murya da ban san shi da ita ba, amma duk da haka ban tsaya b'ata lokaci ba na diro daga kan gado dama da hijabin da nayi sallah asuba a jikina na kwanta dan haka takalmi kawai na zura na fito kofar gida ko lura da Inna dake tsakar gida banyi ba burina shine inje in saka shi a idanu na ko zanji sanyi a cikin raina.

Inda ya saba parking anan na gan shi tsaye ya juyawa kofar gidan mu baya haka kawai sai naji jikina yayi sanyi sosai a haka naja kafa na isa inda yake cikin murya na daya dashe saboda kuka da nasha nayi mishi sallama.

Amsawa yayi yana juyowa muka fuskanci juna, kasa tsaida hawayen ido na nayi ina kallon fuskar shi mai sanyaya min rai nace" barka da zuwa Yaya na aikin ne ya rike haka, wannan karon ka dad'e sosai har ya saka ni cikin matukar damuwa ga number ka bata shiga".

"Lafiya lau mana, hmmm kema dai Zareefa meye abin damuwa anan kin san in nayi tafiya bana saka miki ranan dawowa balle kice har kwanakin sun wuce ban dawo ba sannan tun a baya na gaya miki wajan babu network shiyasa bana iya kira ko a kira ni". Ya bani amsa hankali kwance.

Amsar yasa duk naji wani iri amma na daure tare da share hawayen fuska ta da gefen hijabi na ina sakin mishi murmushin da nasan yana saka shi farinciki nace" hmm ka gama komai ka yanzu dan wallahi in akayi mana aure ba zan yarda kana tafiya kana bari na ba
kafar ka kafata".

Sun glasses na fuskan shi ya gyara yana kallo na ta ciki yace" Zareefa kenan kin ga matsalar ki kenan wanda yasa nake ganin ba zamu iya zama inuwa d'aya ba".

Rass-rass naji zuciyata ta wani irin bugawa da har sai da na kai hannu na kan tsaitin wajan ido a waje nake kallon shi dan na rasa bakin magana, can dai nayi dariya kad'an ganin bai kara ce min komai ba nace " Allah Yaya na ka bar min irin wannan wasan zaka saka zuciya ta bugawa wallahi".

"Wasa!! Wasa fa kika ce, u see kina da matsaloli dayawa a rayuwar ki da in mutum ya duba koya auna ba zai fara ma kusantar inda kike balle maganan aure ya shiga tsakani, ke ko irin kunyan nan da aka san mace dashi baki da ita kullum maganan ki d'aya aure-aure mtsw..." Yaja dogon tsaki yana kawar da kai gefe kaman yaga abin kyama.

Ko kifta idona na kasa yi balle in iya cewa wani abu kawai ji nake wasa yake min jira nake in ga ya juyo yace min wasa yake amma ko kallon inda nake bai kara yiba.

Murya na rawa da son kara tabbatarwa kai na ba mafarki nake ba nace" Yaya na kaine kuwa ,nice fa kanwar ka Zareefa".

"Zareefa my foot me mutum zaiyi da macen da bata kamun kai, tunda can daure zuciya ta nake tare da saka ran zaki canza wata rana sai dai da alamu nayi kuskure dan abin naki kara gaba yake.

Pls ki bar nan in daina ganin ki ko zuciya ta zatayi sanyi saboda yanzu ko ganin ki nayi zuciya tafasa yake, dama abinda ya kawo ni kofar gidan ku kenan kada ki kara kira na a waya cos I don't have time for cheap girls like u". Yace yana min wani kallon tsana.

Wani irin kuka na fashe da shi na juya zuwa cikin gida da gudun tsiya har bana iya ganin gaba na, saura kad'an in mangaje Baban mu da yazo fita yayi sauri ya bani hanya na wuce shi zuwa cikin gida ko waiwayowa banyi ba duk da kira na da yake ta faman yi.

A masifance yace" wani d'an kwal uban ne ya tab'a ki a anguwan nan, bari inje in gani duk wanda na gani mai raba ni dashi sai Allah" ya faman gyara babban rigan shi ya nufi hanyan fita.

Da sauri ya dawo da baya yana zare ido tare da dafa kirji yace" wai-wai dama da wannan hukuman ne?????
[1/26, 7:08 AM] Golden Pen Writer's Assoc: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*19*

"Masha Allah an gode ranka ya dad'e har zaku tafi kenan?" Su Zafar suka tsinkayi muryan Baban mu a bayan su, wani malalacin murmushi yayi sannan ya juyo yana yiwa Sadiq signal da ido.

"Eh Baba zamu wuce tunda jikin nata da sauki sai mun kara dawowa" Sadiq ya bashi amsa ya juya zuwa ga motan nasu.

Zafar gaban Baban mu ya dawo ya tsugunna yana wani sunkuyar da kai kaman mutumin Kwarai yace" nagodewa Allah daya had'a ni da kai Baba, dama na dad'e ina son muyi magana amma ta ki hadani da kai".

"A'a ranka ya dad'e ni kuma gani na abu ne mai sauki me kake bukata?" Baba ya amsa jiki na rawa.

Sai da ya d'an sosa keya alamun yana jin nauyin abinda zai ce yace" Abba ne yake son su zo ayi maganan aure na da ita, shine nace bari in fara fad'a maka in ka amince sai su zo" wannan karan Baba rasa inda zai saka ran sa yaji dad'i yayi ji yake kaman ya kurma ihun murna sai dai ba hali cikin sauri har muryan shi na rawa yace" kai amma yaro yaro ne meye na wani sai an tambaye ni, bayan babu inda zan je kullum ina gida. Ko yau suke so su zo ina jiran su kaji?".

"Toh Baba nagode, mu zamu tafi" yace tare da mikewa ya kara ciro wasu bundles d'in ya zubar da su a gaban Baba sannan ya mike har suka fita daga compound d'in Baba bai dawo daga suman ganin makudan kud'ad'e daya tafi ba.

Sun hau kan hanya ba tare da Sadiq ya kalle shi ba yace " Zafar it's wrong, it's totally wrong".

"And who are you to say so?" Zafar ya tambaye sh yana kara cin magani, Sadiq bai kara ce mishi uffan ba sai ma kara maida hankalin shi da yayi kan tukin da yake.

A nan asibiti kuwa Gwaggo Aisha kasa zaune ta kasa tsaye sai jujjuya ido take wai me yake shirin faruwa ne, bata gama da wancan ba kuma ace ga wani ya bullo? Ita abinda yafi d'aga mata hankali shine ita 'yan matan ta basa samun masu kud'i sai ni, shi wannan kam bayan mai kud'in ne kuma gashi balarabe.

"Wallahi ba zata tsabu ba wai bindiga a ruwa wannan karan sai ta raba ni da komai na jin dad'in rayuwa ko da duk abinda ta mallaka zasu kare ba zata tab'a zuba ido Bintu da 'yar ta su kasance fiye da ita da yaran ta ba.

Kaman wacce aka tsikare ta da allura muka ga zuruf ta mike fuuu tayi waje kaman wata kububuwa,da ido kowa ya bi ta dan tunda su Zafar suka fita babu wanda yayi magana cikin d'akin kowa da kalan tunanin da yake a cikin zuciyar shi.

Tashin hankali da Gwaggo Aisha ta tarar a waje yasa taji kaman ta kurma ihu dan bakinciki, akan idon ta Zafar ya yiwa Baba kyautan makudan kud'ad'e suka shiga mota su dashi kad'ai ta kalla ta san cewa kud'in sa ya wuce duka tunanin ta.

Ganin Baban mu ya hangame baki ya kasa dawowa hayyacin sa tunda yaga ruwan kud'i ya kara tunzura ta, ta taho a fusace ta cikin d'aga murya tace "kai Mallam meye haka?" sai a sannan yaja doguwar ajiyan zuciya ya juyo ya kalle ta,ba tare da yace mata ci kanki ba ya kwashi kud'add'en sa yayi gaba abin shi.

Sosai Gwaggo Aisha ta shak'a wato ya mai da ita mahaukaciya ko? Zasu gani zata nuna musu ainihin true colors d'in ta zasu san da ita suke zancen, sai matsayin ta na da ya dawo ta cigaba da mulkan gidan baki d'aya.

Bayan fitan Gwaggo Aisha Inna abu da Hajara suka mike sukayi mana sallama tare da yi min Allah kara sauki suka fita, cikin sauri Inna tabi bayan su dan basu kud'in mota d'akin ya kasance daga ni sai Maryam da Maa da ta juya mana baya ta kwanta da alamu dai tayi bacci.

"Ni fa na kasa yarda Yaya na zai min haka, saboda yana matukar so na Maryam wallahi yana so na" na karasa ina fashewa da sabon kuka.

Gyad'a kai kawai Maryam ta iya yi min tana share hawaye itama saboda ta shiga duhu sosai a yanda muke matukar son junan mu ace ya juya min baya lokaci d'aya, tabbas babban al'amari ne zai iya raba mu , addu'an ta Allah ya daidaita tsakanin mu.

"Kiyi hakuri Zareefa ko wani tsanani yana tare da sauki, mu cigaba da addu'a insha Allah komai zai daidaita" ban iya bata amsa ba sai kuka da nake ina jin zuciya ta na min wani irin suya.

"Hmmm ni ban san su Ya Sadiq me ya kawo su nan ba abin ya daure min kai" cikin sauri na d'ago da kaina ina duban ta dama tambayoyin dake cin raina kenan su waye su, kuma menene dalilin zuwan su har asibiti duba ni ba dan ni dai ban san su ba.

"Ai na zata wajan ki suka zo " na fad'a da dashassiyar murya ta.

Girgiza kai ta shiga yi kana tace " ko d'aya, na shirya ina shirin zuwa duba ki kiran Ya Sadiq ya shigo bayan na d'aga mun gaisa yake tambaya ta labarin ki shine fa nace mishi nima yanzu zan zo duba ki anyi admitting d'in ki a Kanem Hospital, sai naji yace suma gasu nan zuwa in sun iso zai kira waya ta in shigo da su. Ni dai da toh na bi shi ina mamakin ya akayi ya samu number ta".

Ido kawai na zuba mata ina sauraron ta itama tace haka toh ni kuma in ce me kenan.

"D'ayan kuma shine Zafar Baban shi multi millionaire ne maybe ma zaki san shi sunan shi....."

Saurin katse ta nayi nace" bana bukatan ji koma shi d'an wanene wannan damuwar shi ce nima ki bar ni inji da nawa damuwar".

Shigowan Inna yasa muka bar zancen ta cigaba da bani baki, cikin dabara ta zubo min pepper soup na kayan cikin rago da ta kawo min naci ba laifi da yake tana ta Jana da hiran Yaya na sai gashi na d'an ware muna hira.

Sai kusan azahar sannan Maryam tayi mana sallama ta tafi, a takaice sai da nayi kwana 2 a asibiti sannan aka sallame mu.

Cikin kwanaki 3 nan da nayi a asibiti kullum ido na yana kan hanya wai ko zanga Yaya na yazo duba ni yace min wasa yake amma shiru kuma kullum cikin gwada layi shi nake amma ko sau d'aya bai tab'a shiga ba.

Cikin kwanaki 3 nan da mukayi a asibiti abubuwa da yawa sun faru cikin su kuwa yanda Zafar ya bi ya shiga jikin Baban mu yayi amfani da son abin duniya na Baban mu ya saye shi tsaf har yayi mishi alkawarin bani da wani miji a duniya sai shi, hakan kuwa ba karamin dad'i yayi mishi ba dan ya san yanzu bashi da matsala ta ko Ina .

Da yamma muka dawo gida nan da nan gidan ya cika da makota da basu samu daman zuwa asibiti duba ni ba suka shigo suna min ya jiki, har mutanen suka watse Gwaggo Aisha bata shigo ba dama rabon ta da asibitin tun ranan da suka je duba ni dukkan su daga nan bamu kara ganin ta ba sai Inna Asabe ce mai zuwa ita da Hajara, Jameela kam tunda aka kwa tar dani bamu ga keyar ta ba balle kuma yanzu kila ma bata gidan ta fita wannan gantalin nata.

Zafar da Sadiq sai da suka kusan samun tsab'ani a kaina wai lalle sai Sadiq yazo ya same ni ya min bayanin auren shi kuma yace ba da shi ba wannan dan wallahi in ya kuskura ya turo shi wajena ce mishi zaiyi sona yake kaman rayuwar shi shiyasa ya turo shi in taimaka inji tausayin shi in aure shi.

Wannan magana da Sadiq yayi ba karamin tunzura Zafar yayi ba wai kaman shi za'a ce wai k'aramar yarinya mara class mara kyau wacce yake ganin in ba dan takurar Abban shi ba ko a mai wanke-wanke gidan shi ba zai d'auke ni ba balle ace wai sona yake Allah ya kiyaye.

Cikin fushi yaja motan shi yayi hanyan gidan mu dan dole ayi ta ta kare saboda yau ne deadline da Abban shi ya bashi, shi kuma Sadiq yayi hakane dan yaje da kan shi saboda gaba yake jiye mishi amma shi sam baya gani.

Ina zaune kan sallaya dana idar da sallah isha'i nayi zuru ina tunanin ta yaya zan iya rayuwa ba tare da Yaya na ba, shine komai nawa na taso da soyayyar sa cikin jinin jikina duk wata rayuwa da shi na tsara yanzu rana tsaka ace ya rabu dani, to ya zanyi da rayuwata?

Muryan kani na Ibrahim naji yana cewa Inna ta daya tarar a waje wai ana sallama da Zareefa.

Ban tsaya jin me Inna tace mishi ba na fita da sauri kaman zan had'a da gudu, a zuciya ta ina haba na sani mana shima ba zai iya rayuwa babu ni ba na san dama wasa yake min.

Murmushin dana fito da shi a fuska tace ta b'ace bat ganin wanda ban tab'a zato ba tsaye a kofar gidan mu.
[1/26, 7:08 AM] Golden Pen Writer's Assoc: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*19 & 20*

Ina fitowa na ga ya ajiye motan sa a inda ya saba ajiyewa yana sanye da kaftani na farar shadda ya d'aura waya a kunne yana magana, farinciki naji kamar ya kashe ni Yayana ya dawo gare ni wayyoo ni.

Da gudu na ƙarasa ta bayan shi saboda farinciki ya rufe min ido nayi abinda ban tab'a yi ba wato ina zuwa banyi wata-wata ba na rungume shi ta baya ina sauke tagwayen ajiyan zuciya cikin muryan kuka na fara magana ;

" Yaya naaaaa ni na san ba zaka iya ba dole zaka dawo gare ni i know u truly love me idon ka kad'ai nake kallo in gane hakan"". Cak ya tsaya ya kasa juyowa kuma ya daina wayan mun kusan minti 1 a haka ya juyo tare da banbare ni a jikin shi ya watsar a gefe yace;

"Yuck how disgusting baki da hankali ne daga gani na zaki wani zo kiyi huging na haka ko ance miki irin samarin nan naki ne marasa kan gado?" Yanayi yana watsa min wani kallon kaskanci, muryan da naji kad'ai yasa gaba na fad'uwa dan wannan dai ba muryan Yaya na bane amma kuma na san mai muryan sai dai a sani na da tunani na babu abinda zai kawo shi gidan mu.

Cikin fargaba na d'aga ido na dan tabbatarwa kai na cewa bashi bane, amma me ina dagowa idona sai cikin nashi da yake aiko min da munanan sakonni.

D'auke nawa idon nayi cikin second d'aya ganin wanda ban tab'a zato balle tsamani ba a kofar gidan mu, na had'iye wani bushashan yawu da ya tsaya min a makoshi sai yanzu na lura da yanayin shigar sa tsayin sa fatan jikin sa komai daban dana Yaya na.

Kara d'agowa nayi naga yana min wani kallo kaman yaga kashi , cike da jin haushin kaina kama hanya zan shiga gida garin murnanan zuwan Yaya bada kaina.

Gaba na yasha yana wani kumbura fuska kaman ni na jawo shi gidan namu yace;

"Nasan yanzu gurgun tunanin ki ya baki cewa wajan ki nazo ko? well I don't have much time but to say I have a contract with you"

"Contract!?" Naji baki na ya furta cikin mamaki ba tare da na shirya ba, shi kuwa murmushin gefen baki yayi yana like father like daughter" shi a zaton sa duk son abin duniya yasa na amsa mishi lokaci d'aya bai san cewa mamaki ne ya kama ni ba.

"Yeah contract marriage kuma if possible ba zai wuce 1 to 2 months ba zakiyi tafiyan ki nd zan iya baki daga 100 millions zuwa sama kuma kada ki d'auka wai zaman ma'auran gaske zamuyi, no zanyi haka ne kawai dan in fita daga mess d'in da Abba na yake son jefa ni ciki" a garance ya cigaba da tambaya ta nawa zai bani.

Juyowa nayi ina fuskar shi da kyau duk da ina jin yanda zuciya ta take bugawa kaman ya fito saboda tsaban kwarjini da yayi min dan sosai yake cika min ido amma dole ne in nuna mishi mu mata daraja ne damu kud'i bai isa ya saye mu ba.

"Hmmm ikon Allah , naji ni mai gurguwar tunani ce, kai kuma wannan tunanin naka me zan kira ta dashi miskini ko nakashasshe?

"Anyway bari in fada maka ko duniya da abinda yake ciki zaka mallaka min toh ni Zareefa na fi karfin wannan kazami ko haramtaccen rayuwa da kazo min dashi sai dai ka kara gaba kila ka samu wata gantalalliya da zata amince maka amma ba ni ba"

Ina gama maganata na rab'a ta gefen shi zan wuce zuwa cikin gida naji an finciko ni ta baya tare da d'aga hannu zai yarfa min mari kuma ya fasa ya dungule hannun ya kaiwa iska naushi yace;

Damn u ! Who do u think u re ? Da har zaki bud'i baki ki fad'a min magana son ranki, I don't blame you baki san wanene ni ba da ko wuka aka d'aura miki a wuya u will not have d guts to do it.

Kada gani na a kofar gidan ku yasa ki d'auki kan ki kaman wata mace u re nothing yes I mean nothing, ba duniya da abinda suke ciki zan bayar ba amma Baban ki yace min ko gobe inzo zai d'aura min aure dake nazo nan na fad'a miki ne cus na san ba lalle bane su fad'a miki irin auren da zakiyi but for now at least kin san irin auren da zakiyi, as for me I don't have time for cheap girls like u".

Yana gama maganan shi fad'a motan shi yaja shi a d'ari ya fita daga layin mu tare da bad'e ni da kurar motan ya tafi abin shi.

Ni kuwa ko kafata na kasa d'agawa a wajan ba wai maganganun shi ne suka b'ata min rai ba illa sunan Baban mu daya ambata a cikin maganan shi ya jefa ni cikin tashin hankali mara misaltuwa.

Na san Baban mu tun ina k'arama akan kud'in Baban mu ba abinda ba zai aikata ba koda akan dubu d'ari ne zai amince balle yaji million d'ari, " Na shiga uku" nace hawaye na ambaliya a fuskata.

Nafi minti 5 tsaye a wajan ina hawaye sannan na goge fuska ta da hijabi na,naja kafafu na da sukayi min nauyi zuwa cikin gida.

Allah ya so ni babu kowa a tsakar gidan duk suna d'akunan su sai hayaniyar su daya cika ko Ina kai tsaye na wuce d'akin mu, da sallama na shiga d'akin ban tadda Inna ba ina zaton ta zaga bayi ne.

Ban tsaya bata lokaci ba na haye gado na kwanta ko hijabin dake jikina ban cire ba gudun kada Inna tazo ta same ni cikin sabon tashin hankali dan ban san wani bayani zanyi mata ba.

Tunani na zurfafa a ciki na yanda rayuwa take neman juya min baya ina 'yar k'arama ta koda yake Allah ba bawan sa da baya jarabta babba ko karami mace ko namiji, ni na san ina cikin jarrabawan ubangiji nane, yau na dawo daga asibiti wanda tashin hankali yaja min kwanciya can kuma gashi yanzu ga wata fitinan da kwanciya asibitin ma ba zai min maganin ta ba.

Ina ji Inna ta shigo tana min magana nayi likimo kaman mai bacci saboda bana son ta tambaye ni waye yazo, jin wanene ko meya zo dashi babu abinda zai kara mata illah tashin hankali.

Addu'oin bacci tayi ta shafa nima ta shafa min ta kwanta a gefe na taja mana bargo ba tafi 15 mins da kwanciya ba naji tayi bacci, a zuciya ta nace Allah sarki Inna ta dana fad'a miki halin da nake ciki yanzu na tabbata da baki samu daman runtsawa ba.

Har karfe d'ayan dare tayi ido na babu alamun bacci, cikin tsand'a na sauka daga kan gadon na fita na d'auro alwala na fara kai kuka na ga Rabbil Izzatti shine kad'ai madogara na.

****************

Zafar har ya isa gida zuciyar shi bai bar tafasa ba har kaman shi wannan yarinyan zata dubi cikin idon shi ta fad'a mishi abinda taga dama " bull shit" yace yana dukan stairin shi da karfi kaman shi ya mishi lafin.

Yana zuwa gida kai tsaye part d'in iyayen shi ya wuce, a kofan parlour ya tsaya ya gyara fuskan shi kaman he is in good mood saboda baya so su fahimci halin da yake ciki.

Da sallama ya shiga parlour suna zaune suna kallon wa'azi a Sunna TV da Sheikh Aminu Daurawa da yake , amsa mishi sukayi duka ya karaso ya zauna kan lallausan rug dake parlour ya gaishe su suka amsa mishi cikin kulawa daga nan yaja bakin shi yayi shiru shima ya maida hankalin shi kan wa'azin.

Kusan mint 10 wa'azin ya kare dama yazo karshe , remote Abban shi ya d'auka ya rage volume d'in TV sannan ya kalli inda Zafar yake zaune yace;

"Ina ta zuba ido ka kawo min wacce kake so kaman yanda mukayi magana tun kwanaki 3 da suka wuce amma na jika shiru, so yau ne deadline d'in kuma dole ne in cika alkawari na dana d'auka na samo maka mata a cikin 'ya'yan dangi".

"Kayi min afuwa Abba yanzu haka abinda nazo fad'a maka kenan na tarar kuna kallon wa'azi shiyasa na jira ku gama sai muyi magana" ya amsa yana wani sussunne kai.

"Okay sai yau kaga dama kazo min da zancen??

Hmm toh bakin alkalami ya bushe gobe zanje duk wacce tayi min itace matar ka insha Allah" Abba ya karasa hankalin sa kwance.

A rikice Zafar ya d'ago da kai ya rarrafo gaban Abba ya fara magana duk a rikice" Abba wallahi ba wai nayi biris da maganan ka bane na zata kace in kawo ta yau ne shiyasa nayi shiru, please Mom kisa baki wallahi maganan da nazo dashi yanzu kenan please Abba".

"Alhaji kayi mishi afuwa tunda bai fahimci abinda kake nufi ba sai yanzu ". Cewar Mom kenan da duk har yanayin ta ya canza.

"Hum kuma daina b'ata bakin ku kema kin san in nayi magana d'aya bana canza ta".

"Abba na sani wallahi na sani amma dan Allah kayi hakuri ba dan hali na ba" ya cigaba da magiya shida Mom Abba yana jin su bai kula su har sai da ya wana su son ran shi sannan ya ce;

"Ya isa haka naji sai ka kiyaye next time 'yar waye ne ka samo mana??"

Harshan sa har hard'ewa yake wajan bada amsa " sunan ta Zareefa a garin nan take 'yar Mallam....."

"Mallam kuma Zafar ?" Mom ta katse shi fuskar ta d'auke da matsanacin damuwa.

Kamin ya bata amsa Abba ya karb'e da cewa" ke yakewa bayani da zaki katse shi?

Meye laifi a auren 'yar Mallam, so kike kiji yace 'yar Alhaji ko 'yar governor or what?" Ya karasa fuskar shi na nuna bacin rai.

Cikin kwantar da murya Mom ta shiga bashi bashi hakuri bai amsa ba illa mikewa da yayi ya wuce sama tare da cewa Zafar ya biyo shi.

***********

Gwaggo Aisha da kawar ta Lantana suna tattaunawa cikin farinciki a cikin motar haya suna dawowa daga kauyen Manguno inda aka kai ta wajan wani boka.

Cikin annashuwa ta ce" gaskiya Lantana na jinjina miki dama kin san irin wajan nan.amma kika barni ina ta shan wahala kan kananan kwarin nan?"

Cikin fariya Lantana tayi wani dariya ta amsa da " A'i kenan ai ba nan kad'ai na sani ba wajaje dayawa na sani kin san duniyan nan sai da dan shige-shigen nan zaki kwacin kanki kuma ki wuce rainin miji ko kishiya.

Kin gan ni nan wallahi Mallam Ado sai abinda nace a gidan sa yake babu wanda ya isa ya tsallake magana ta har matan shi da yaran su".

"Kai kawata kina wuta ina bin ki da fetir har kinsa na fara hangowa ina juya Bintu da wannan fitsararriyar 'yar ta" cewar Gwaggo Aisha cikin jin dad'i.

"Ke dai kibi duk sharud'a daya kindaya miki kiga aiki da cikawa kasancewar aikin shi kaman yankan wuka yake.

"Ai dole ne in bi sharud'an nashi" da wannan tattaunawan har suka iso gida.

Sai bayan karfe 3 bacci yayi nasaran sace ni nan kan sallayan, kiran sallah farko Inna ta farka ta ganni kwance kan sallaya bata tashe ni ba tayi alwala ta fara nata nafilfilu kasan zuciyar ta kuwa tana mamakin kwanciya ta a nan.

Sai da aka fara sallah a sauran masallatai sannan ta tashe ni na fita nayi alwala nazo na kabbara sallah, ko azkar kasawa nayi saboda baccin dake cin ido na kara bingirewa nayi na cigaba abina anan Inna ta fahimci bacci bai ishe ni ba jiya cikin tausaya min ta kama 'yan aiyukan ta nan cikin d'akin ba tare da ta fita ba, bata kawo komai a zuciyan ta ba duk a zaton ta ban dawo dai-dai daga shock na rabuwa da Yaya na ba.

A wannan Gwaggo Aisha tayi bine-binne ta a mashigar kitchen d'in mu ta saka kujera a k'ofar d'akin ta tana jira mu fito mu tsallaka kaman yanda bokan ta yace.

Cikin ikon Allah Inna itama baccin ta koma tunda babu wani abu na azo a gani da zatayi, cikin bacci muka ji kaman ana tonon abu cikin k'asa, ko motsi banyi ba amma na farka sai Inna tace tayi karfin halin fitowa jin muryan maza kuma bakin murya ya cika gidan.

Maza tayani sun kai su biyar kowanne da abu a hannun shi yana tono Baban mu na tsaye daga gefe , kamin Inna ta bud'i baki tayi tambayi me yake faruwa suka ji muryan Gwaggo Aisha tana" kai! Kai!! Ku dakata me kukeyi haka?"

Duk suka juyo suna kallon ta duk ta had'a zufa sai wurwurga ido take, Baba ne ya bata amsa da " meye naki na ihu haka sai kace gidan ki ake tono,

Toh gini zanyi zan canza ginin gidan nan ya zama na zamani".....
[1/26, 7:12 AM] Golden Pen Writer's Assoc: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*21&22*

"Haba Mallam ba zaka bari mu d'an kimtsa ba gyara da sassafe haka?" Gwaggo Aisha ke fad'an haka cikin matukar tashin hankalin gani za'a saka ta wahalan banza.

"Wani irin kimtsawa sai kace daga kofar ki aka fara, ki bari in aka zo kofar ki sai ki kawo korafin naki" Baban mu ya amsa a dakile.

"Ni ba wani abu nake nufi ba naga safiya ce kuma ai ko ita Bintun zata so a bar ta ta d'aura abin karyawa ita da 'yar ta, ko ba haka ba Bintu?" A zuciyar ta kuwa tana ta addu'an Allah yasa Inna ta amince da abinda ta fad'a a fasa tonon sai bayan mun shiga kitchen d'in mu munyi girki, kamin nan mun sallake abubuwan da ta binne shiyasa dama ta zab'i binnewa a kofar kitchen d'in mu sanin ba wanda zai taka wajan sai mu.

"A'a in ta nine bakomai suyi aikin su, ba zamu rasa yanda zamuyi ba, wannan ai abin farinciki ne kuma cigaba ne muma zamu zama 'yan gayu" Inna ta amsa tana dariya sauran mutane da suke wajan suma dariyan sukayi suka cigaba da aikin su ba tare da sun lura da halin da sun lura da halin da Gwaggo Aisha ta shiga ba.

Afujajjan ta shiga d'akinta sai safa da marwa take duk ta had'a zufa ta kasa zama sai neman hanyar da zata dakatar dasu take amma kasan zuciyar ta kuwa gargad'i take mata na kar ta tsauwala har ta tonawa kanta asiri cikin mutane, da wannan shawaran ta nemi waje ta zauna sai karkad'a kafa take tana sharce gumi,Hajara tana ankare da ita amma taki tanka mata.

Ni kuwa tunda naji Baba yace ginin zamani za'a yiwa gidan mu na kasa ko daga yatsa na sannan kuma na tabbatar da zancen bawan Allah nan na jiya gaskiya ne kenan in ba haka ba ina Baba yaga kud'in ginin zamani,

"Ya Allah ka dube ni ka fidda ni cikin wannan fitinan" nace cikin raina.

Basuyi wani nisa ba suka fara tono tsirkullen Gwaggo Aisha, cikin mamaki suka tsaya cirko-cirko suna kare musu kallo an rasa mai magana cikin su.

"Mu cigaba da aikin mu mana" cewar d'aya daga cikin su.

"Kaman yaya mu cigaba bayan wannan abubuwa da muka tono,kamata yayi a sanarwa mai gidan sai ya san matakin da zai d'auka" nan duk sukayi na'am da shawaran nan suka tura karamin cikin su kiran Baba.

"Innalillahi wa inna ilahi rajiun" shine Kalmar da Inna ta samu daman maimaitawa fitowar ta kenan daga bayan gida taga sun tara tsirkullen a gefe suna ta tattaunawa akai.

Kasa wucewa tayi tana mamakin me ya kawo layu da guraye kofan kitchen d'in ta, fargaba fal a zuciyar ta na kada ace itace ta binne su,har Baba iso wajan tana tsaye sai ambaton sunan Allah take.

"Wannan ai ba wani abin tada hankali bane, ta yiwu tun na kakanin mune sune zasu iya ajiye irin wayan nan abubuwan su jima haka kasa haka" cewar Baba kenan cikin rashin d'aukan abin da muhimanci.

"A'a wayanan tsurkullen basu dad'e a kasa ba ta, da gani kwananan aka binne su" cewar d'aya daga cikin su.

"Matsalaha daya ne shine a k'ona su kurmus in ma mai shi da wata manufa ya binne toh zai zo da sauki"

Inna da jikin ta yayi sanyi sosai barin ma irin kallon tuhuma da taga Baba na aiko mata da shi yasa duk taji ba dad'i, tana jin anyi maganan konawa yasa cikin sauri ta wuce d'aki ta d'auko ashana a cikin drowern d'aki inda take ajiyewa in ta sayo kwali.

Kamin ta fito har sun tara su a gefe sun zuba kalanzir suna neman ashana, Baban mu ta mikawa ta koma gefe ta tsaya babu b'ata lokaci wanda ya karba ya ketta ashana bayan yayi addu'oi nan da nan kuwa wuta ya kama ya fara ci bakin hayaki na tashi a jiki kaman ana kona taya.

A d'akin Gwaggo Aisha kuwa tunda aka cinnawa layun nata wuta ta fara ganin d'akin na juya mata ga wani zafi-zafi da take ji a jikin ta kaman ana hura mata wuta, tun tana iya daurewa har abin yafi karfin ta ta fara ihu tana birgima a tsakiyar d'aki.

Sharewa nayi kaman banji ba dan nima ina fama da nawa matsololin inda zan samu daman ihun nima da nayi ko zanji sauki cikin raina.

Tsaki naja ina mikewa tsaye da d'an sauran kuzarin daya rage min na fita saboda yanda naji ihun yaki tsayawa kuma kana ji kasan wanda yake yana cikin mamuyacin hali.

Kus-kus na tarar masu aikin nayi ban kula su ba nayi wucewa ta zuwa d'akin Gwaggo Aisha da zan iya kirga shiga ta ciki tunda aka haife ni.

Da gudu na karasa nima ina kokarin rike ta kaman yanda naga Inna da Hajara sukayi Inna sai tofa mata addu'oi take, ban tsaya b'ata lokaci ba nima na fara taya ta muka cigaba da tofa mata har ta daina birgima sai jikin ta da yake rawa sosai, tuni Baban mu ya fice abin shi zuwa d'akin shi ya bar mu da ita.

Mun Kai good 30 mins muna yi mata sannan ta dawo hayyacin ta sai ajiyan zuciya take a kai- akai hawaye na bin gefen fuskan ta amma koda wasa bata bud'e ido ba, ganin taji sauki yasa Inna mikewa tacewa Hajara ta lullub'a mata abin rufuwa da alamu ta samu bacci, amsawa tayi da toh tare da mana godiya muka fito zuwa d'akin mu Inna bata zauna ba ta d'auki dubu d'aya ta bawa Ibrahim kan ya sayo mana abin karyawa a waje.

Tunda ta bada sakon ta dawo d'aki ta zauna shiru na san shirun nata baya rasa nasaba da abinda ya faru a safiyar yau, ba Inna da take shekaru ba ko ni nan na fahimci abinda ya faru da Kuma musababbin ta.

Allah sarki Inna ta kamin ka samu mai irin zuciyar ta a wannan zamnin sai an tona, tsab ta gane komai amma taje tayi mata addu'a, da wata ce sai dai ta mutu ko nice nan Yasin ko kurar da ya debo ki ba zan kallah balle har in nema miki waraka barin ki zanyi ki girbi abinda kika shuka.

Shi kuwa Baban mu akwai shi da kyaluwa ba kasafai kake gane mishi ba in ba harkan kud'i bane, ko ya fahinmci abinda ya faru ko bai fahimta ba oho.

*************

A b'angaren Zafar kuma yau cikin farinciki ya tashi ko ba komai ya ragewa kan shi tention da kuma fad'an Abban shi, ba komai yake kara mishi nishad'i ba kaman in ya tuno da hiran shi da Abban shi jiya a kaina.

Murmushi ya kara saki lokacin da ya tuna Abba shi yace" ina matukar alfahari da kai ka birge ni sosai da ka tashi neman aure baka nema cikin 'ya'yan masu kud'i ba ka nema a irin gidan da nake son in samu sirka,

Naji dad'i da baka bi halin mahaifiyar ka ba na wajan kin talaka, da mai kud'i da talaka duka Allah ne yayi mu saboda hikimomin shi ba yayi hakan bane dan baya son su ba.

Ina son ka auna da kanka ka gani a nan ne zaka gane hikiman ubangiji da nake fad'a maka, misali ace duniyan gaba d'aya babu talaka ya kake ganin zai kasance ko kuma ace duka talakawa ne babu mai kud'i, ka fahimta?" Ya tambaya yana kallon yanda ya natsu yana sauraron shi.

Gyad'a kai Zafar yayi a hankali kan shi a kasa da sai yanzu da Abba ya fad'a mishi ya gane dole talaka yana bukatan mai kud'i haka Kuma mai kud'i yana bukatan talaka a rayuwar shi.

Muryan Abba yaji ya cigaba da magana " babu wanda yafi wani sai wanda ya mutu ya samu aljanna, kana nan duniya kana taka mutum saboda kai kana da shi shi kuma talaka baka sani ba kila a wajan Allah yafi ka daraja, dan haka ka cigaba da rike mutane da kyakkyawan zuciya zaka ga amfanin haka duniya da kiyama".

Shi dai Zafar duk mamaki ya hana shi sakat yaushe rabon da su zauna da Abban shi har suyi magana mai tsayi cikin lumana haka, tun kafin zuwan sa abroad karatu, tunda ya dawo da sabbin halayen sa na shan minti kuwa suka daina shan inuwa d'aya tare.

"Kana da kud'i a account d'inka?" Ya karajin muryan Abba ya katse mishi zancen zuci yake.

"Eh akwai Abba ba za'a rasa ba" ya amsa a sanyaye kaman mutumin kirki.

"Ok bari zuwa anjima ko gobe zanyi maka transfer ko kad'an ne kada sirkata ta nemi wani abu kace mata babu" yace yana dariya.

Shima dariyan yayi yana kara sadda Kai kasa.

Cikin wani irin kwarin guiwa ya nufi part d'in iyayen nashi bayan yayi wanka ya sha gayun shi kaman kullum sai kamshin tsadaddaun turaruka yake, tsab'anin da in Abba yana gari da kyar yake iya zuwa saboda ya san in yaje ma ba zasu kwashe da dad'i ba.

Da sallama ya shiga parlour amma babu kowa sai masu aiki da suke kai kawo, kowa na aikin da yake gaban shi, zama yayi kan d'aya daga cikin royal cussion d'in da suka lamushe kusan set 2 ya d'auki remote yana canza channel zuwa aljazeera sports yaji motsin saukowan su.

Ajiye remote d'in yayi ya mike tsaye ya tarbe su basu tsaya anan ba direct dinning suka wuce kowa yaja kujera ya zauna banda Mom da sai da tayi serving din su sannan ta zauna suka fara cin abinci

Basu dad'e da farawa ba Zafar yaga alert na zunzurutun kud'i har 10 million cikin tsananin murna bai san lokacin daya durkusa jiki na rawa har kasa ya fara godiya yana" Abba naga sako nagode Allah ya kara girma da nisan kwana" ba dan komai ba Abba yafi shekara rabon shi daya bashi kud'i sai dai Mom ce ke bashi a cewar shi ba zai bashi kudin shi yaje yana shashanci dasu ba.

Abba kuma ya kalli Mom da take bin tilon d'an nata da kallon mamaki yace" da fatan kin fahimci abinda nake nuna miki kika kasa fahimta kinga tun kamin ayi auren ta fara canza mana shi ina ga Kuma anyi auren?"

"Oh yanzu duk sun d'auka wannan village girl d'in ce ta canza ni..."

Muryan Mom yaji tana cewa" na fahimta Alhaji ya tabbatar da alkhairi"

"Ameen Ameen addu'an ki yake bukata dama, Kai kuma a yau d'in nan ka cewa 'yar Mallam gobe zamu je mu tsaida magana da Baban ta"

Murmushi da bai shirya bane ya kwace mishi jin sunan da Abba ya kira ni dashi wai 'yar Mallam.

"Ja'iri ji duk wannan washe bakin dan nace gobe zamu je ne, ina ga inda aka daura auren Kuma ya zakayi?"

Dariya yayi kawai yana ficewa ya nufi part d'in shi yana kara dariyan sunan da kuma na Abban shi da yake ganin auren soyayya zaiyi bai san auren contract zaiyi ba.

Direct bedroom d'in shi ya wuce yana cigaba da dariyan shi yayi dialing no Sadiq , saida ya gama ringing kamn zai katse sannan ya daga yana cewa " meye ya faru??"

" Hey Ni ba fad'a yasa na kira ka ba, I just called dan in fad'a maka gobe Abba zai je nema min auren 'Yar Mallam" ya karasa yana dariyan da sai da yasa Sadiq ya cire wayan a kunnen shi ya kalli screen d'in ya kara tabbatarwa eh zafard'in ne sannan ya mayar kunnen shi.

"Wacece da wannan sunan ko cikin relatives d'in ka na kauyen ne aka samo maka wata". Sadiq ya tambaya.

"God for bid, bakin ka ya sari d'anyan kashi mugu kawai meya had'a ni da 'yar kauye, wannan village girl da kuka had'a ni da ita mana Abba ne ya saka mata wannan funny name d'in koda yake it suits her" ya karasa yana kara saka dariya dan d more zai fad'i sunan d more yake saka shi dariya.

"Ikon Allah, amma ban san Kai cikakken d'an rainin wayo bane sai yau, yarinyan da ta sace maka zuciya at first sight shine zaka ce mu muka nemo maka ita?"

"Damn it wai har sai yaushe zaka fahimta ni *BA SONTA NAKE BA* kuma kafi kowa sanin why I will marry her amma ba zaka daina fad'a min rubbish ba, anyway phone no ta nake nema in fad'a mata sakon Abba" yana kawo nan a zancen shi katse kiran yayi jifa da wayan kan gadon shima yabi shi ya kwanta ringine yana huci shi ala dole an b'ata mishi rai.

Ko minti 5 baiyi da kwanciyar ba yaji karan shigowan sako wayan shi, sai da yaja tsaki sannan ya bude sakon ba dan komai ba sai dan yaga daga Sadiq ne.

Number kad'ai ya gani babu rubutu hakan ya tabbatar mishi da number na daya nema ne ya turo mishi, sai da ya fara saving sannan ya kira ni lokacin muna zaune da Inna tana had'a min tea dan tace inzo mu karya nace bana jin yunwa, shine ta shiga had'a min wai ko shi kad'ai in sha.

Inaji har tagama ringing ban d'auka ba ganin sabon no ce, kara kira yayi Inna ta dakata da had'a shayin tace min " Wai ke ba wayar ki ake kira bane?"

"Inna sabon number ce babu suna" na amsa mata a sanyaye.

"Ko ba suna ai zaki daga kiji ko waye ko?" Inna ta sake fad'a min.

Koda na juya da niyan daukawa naji ya katse dan haka banyi magana ba nayi shiru Inna ma bata kara cewa komai ba ta cigaba da had'a min.

Miko min tayi bayan ta gama harda 🍞 tace in gusura ko kad'an amma na ce mata sai anjima, sama-sama itama ta karya bata ci wani abu dayawa ba ta ture gefe duk gani na cikin rashin walwala yana hana ta sukuni itama.

Gwaggo Aisha sai bayan fitan mu da kusan minti goma ta tashi ta zauna tana goge fuskan ta da hijabin da Hajara ta lullub'a mata ba hawayen amma duk ta jike da zufa.

Harara ta zabgawa Hajara da take ta jera mata sannu tayi kana tace" ke dai Allah yayi magulmaciya da kinibibi in banda gulma waye yace ki gaiyato min wacan manufukar matan can da 'yarta fitinanniyan nan?"

Baki a hangame hajara take kallon ta tace " haba Umma in baki gode musu ba ba zaki tsine musu ba, ihu fa kike tayi kina birgima kan an k'ona abinda kika binne dan su cutu ita da yarta amma matan nan ta zauna tana tofa miki addu'oi ita da yarta har kika samu lafiya, mutane nawa ne a gidan nan babu Wanda yazo kan ki sai su hatta Baba ma tafiyan shi yayi ya bar ki....."

"Ki min shiru wawuya kawai mai fifita uwar wasu kan uwar ta koda yake ba laifin ki bane duk asirce ku tayi Kuma wallahi ba zan saduda ba sai na warware duka mugun kulli da tayi a cikin gidan harda Baban naku..."

Shiru tayi tana wur-wurga ido kaman me neman wani abu, a zabure ta mike tana " kan bala'i in na yarda shigiya nake" tana gama magana ta fice fuuu zuwa tsakar gida.

Cikin daga murya ta fara magana" ina kake ka fito shanyayye kawai wallahi na gaji da rashin adalci da kake nuna min a cikin gidan dole ne ayi abu d'aya ehe"

"Ke Wai wace irin dakikiya ce mara hankali meya faru da zaki zo tsakar gida kinawa mutane ihu" cewar Abba kenan daya tsaya daga nesa yana kallon ta.

"Eh dole ka kira ni da sunaye da kaga dama Amma kada ka manta ko rigar sakawa na kirki baka da ita lokacin da na aure ka sai yau dan ka samu abu zaka wukanta ni, ace Wai gini zakayi a gidan baka fara ta kaina ba nida nake uwargidan ka sai wancan jamammiyar matar taka".

"Kinga dakikancin ki da nake fad'a ko, in kika ga abu tambaya ya kama kiyi ba Wai kiyi tayiwa mutane ihu ba, toh kudin daga hannun mijin da zai auri yar albarka ya fito kinga kuwa dole afara gyara mata b'angaren ta tunda auren ma ba zai fi wata d'aya ba".

Ras-rass naji zuciyata ya tsinke duk da na san da zancen amma jinta a bakin Baban mu yafi daga min hankali, a zabure Inna ta mike tana girgiza kai tana magana " ba zai yiwu ba wa zai aurawa 'yata ba tare dasani na ba,ba zan yarda da wannan cin fuskan ba zan iya jure ko wani irin cin mutunci amma banda kan 'yata ba"
[1/26, 7:12 AM] Golden Pen Writer's Assoc: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*23&24*

"Na sha had'iye wulaƙanci da cin fuska daga wajan sa da matan shi, amma wallahi kada wani yace zai tab'a min ke anan ne zasu ga fushi na". Tana magana ne a wannan lokacin tare da saka hijabinta ta kama hanyan waje.

Da gudu nima na miƙe ina kwala mata kira akan kada ta fita wajan nasu amma ina har ta fice daga d'akin, bakin gado na koma na zauna dabas ina jin zuciya ta na suya tsanar bawan Allah nan na ninkuwa a cikin ta ba dan komai ba sai dan yanda naga tashin hankali da bacin rai shimfud'e akan fuskan ta wanda zan iya cewa tunda aka haife ni ban tab'a ganin koda kwatancin shi a tare da ita ba.

Gata kuma ta fita sa-in-sa da Baban mu da Gwaggo Aisha shima wannan ban tab'a ganin Inna ta kula kowa ba a gidan,koda kuwa me zasu ce mata ko suyi mata bata tankawa kowa sai dai ta shige d'aki tayi zaman ta,nice dai a baya nake dan kula su kasancewa ta bana iya wuce tayi in dai na fad'a ne sannan kuma na tsani wulakanci da raini wanda duk Gwaggo Aisha tayi degree akan su.

Sosai take min fad'a kaman ta doke ni akan kula su da nayi amma yau itace dakanta ta fita yau; " Innalillahi wa inna ilahi raji'un" na zauna maimaitawa ina kuka, wannan wani irin mutum ne shi tunda ya shigo rayuwa ta komai kara cakub'ewa suke " I hate that ugly creature" nace ina Kara fashewa da sabon kuka.

Naci kuka na na more sai dai ga mamaki na banji motsin Inna ta a tsakar gidan ba balle inji muryan ta, Baban mu ma na daina jin muryar sa sai Gwaggo Aisha da take ta ihun ta ita kad'ai.

Shirun da naji yayi yawa ne yasa na mike a hankali na l'eka waje bayan na yaye labule kad'an, tsakar gidan babu kowa da alamu Gwaggo Aisha tayi ta gaji ta koma ciki sai masu aiki da suke ta aikin su sai kanne na da suke wasa a gefe,toh ina Inna ta ta tafi???

Ras-ras naji zuciyata ta harba da karfi kar dai yaji Inna tayi, abinda tunda akayi mata aure bata tab'a yi ba.

Cikin mutuwar jiki na koma d'aki na zauna ina tsiyayan hawaye masu zafin gaske, ban jima da zama ba naji waya ta ta fara ringing ko juyowa banyi ba balle in sa ran zanyi answering, haka ya gama ihun sa ya daina.

Kwanciya ta nayi akan gado ina rokon Allah yasa ba yajin tayi ba cos I can't imagine myself in dis house without my inna, wayance ta fara ringing Kuma cikin gajiyawa na d'auka ina kallon no data kasance special in ban manta ba kaman d'azu dashi aka jera min 2 missed calls.

Saura kad'an ya katse na daga kai kunne na nayi shiru ba tare da nayi magana ba, shiru naji shi wanda ya Kiran ma yayi bashida niyyan magana,mun kusan minti 2 a haka ina shirin cire wayan a kunne na kaman yana kallo na yace;

"Who do you think you are? Da har zaki dinga ignoring calls na, be very careful with whom you are dealing with or akwai lokacin da yana zuwa da zakiyi regretting duk abubuwa da kike".

Yawu mai d'aci na had'iye da ya makale min a makokoro ina sauraran bakaken kalaman sa da suka fi wuta zafi, sarai na gane muryan nashi wanda kullum in yana magana zaki jita cike da isa da kasaita.

Bai san cewe nima a wuya nake ba tunda har ya zama shine silan fara fitan Inna a gidan auren ta da sunan yaji, tsab zan juya mishi duk rashin mutunci da nake dauke dashhi dama nima ba tayar baya bace.

Muryan shi ce ta maido ni hankali na naji yana cewa; " 'yar Mallam kada kice wai saboda na damu da kene nake ta jera miki kira haka, nooo ko daya I just want you to tell Mallam Abbana zasu zo anjima". Kit naji ya katse kiran ba tare da ya jira yaji me zance ba.

" 'yar Mallam!! " Na maimaita sunan a fili "kunbu in na yarda shegiya nake nice 'yar Mallam din, wallahi sai na koyawa dan raini nan hankali ni har akwai wanda zai takale ni in kyale shi never".

Tsakani da Allah na zage ina masifata ni kad'ai kaman yana gaba na, danna mishi kira nayi ina jiran ya daga nima in rama amma har ya katse bai daga ba, ban hakura ba sai da na jera mishi missed calls 5 bai daga ba, cillar da wayan nayi na fashe da kuka sosai dan jin zuciya ta nake kaman ta fashe da ban samu na rama ba dama can ina da wannan halin tun ina karama na taso da abuna, cikin 'yan gidan mu babba ko karami ya tab'a ni sai na rama hankali na yake kwanciya, har duka Inna ta sha yi min akan in daina amma na kasa saboda a jini na yake. Wannan dalilin yana daya daga cikin dalilan da Gwaggo Aisha take min zazzafan tsana.

Inna kuwa tana fita a d'aki bata ko kalli inda Baba da Gwaggo Aisha suke ba ta fice zuwa gidan su, suma dai basu lura da ita ba duk hankalin su yana kan fad'an da suke.

A tsakar gida ta samu Maa da kanwar ta wacce suke kira da Ya ma'aji suna hiran su na 'yan uwan taka gwanin sha'awa, da sallama ta shiga sai dai bata tsaya taji amsawar sun ba ta shige d'akin Maa.

Da ido duk suka bita har ta shige cikin d'aki ba tare da ta tsaya wajan su ba kaman yanda ta saba ba ko kuma ince yanda ya kamata ba, Ya ma'aji ta dubi yayar ta tace" Yaya da alamau yarinyan nan tana cikin damuwa,dubi yanda ta shigo gidan nan hankali tashe, ni wallahi wannan kaddararren auren nata da kina jin shawara ta da tuni ta rabu da shi haba yarinya tana 'yar karamar ta amma kullum cikin tashi hankali take dubi yanda duk ta motsare,ga fitinan miji gana kishiyoyi da wanne zata ji" ta karasa da matukar fushi a fuskarta domin ita halin ta daban dasu Maa fad'a ne da ita sosai ga rashin hakuri.

Murmushi mai sanyi Maa tayi mata tana girgiza kai tace "kai ma'aji akwai ki da daukan abu da zafi baki san halin yaran yanzu ba abu bai kai ya kawo ba zasu d'auke shi da zafi........".

"A'a Yaya kada ki raina hankalin ta na tabbata ko ke da kika fimu sanyin hali aka ki gidan nan nata zasu kure ki,bari inje inji meya faru" tace tana mikewa tare da nufan d'akin da Inna take ciki.

A kan carpet da yake shimfid'e a tsakar dakin ta samu Inna ta had'a kai da giwa tana kuka kasa kasa.

Dafa ta Ya ma'aji tayi yasa ta d'ago da kai suka had'a ido tayi mata murmushi ita kuma kukan ta kara fashewa da shi cikin muryan kuka ta fara magana"Ya ma'aji ku ceci Zareefa dan Allah ku cece ta ni na yarda suyi min duk abinda suke so amma dan Allah su kyale ta tayi rayuwa mai yanci da farin ciki, yarinya ce k'arama bata san rayuwa ba dan Allah kada su jefa rayuwar ta cikin.........."

"Ya isa haka ya isa, ki natsu ba abinda zai faru da Zareefa muna tare da ke kuma Allah yana tare da mu dan haka ki kwantar da hankalin ki, ki min bayanin me yake faruwa?. Ya ma'aji ta katse Inna da take magana cikin fitan hankali.

"Wai aure zaiyi mata kuma ni baiyi shawara dani ba ban san waye zai bawa ba,kawai yau da safe ya shigo da masu gini wai zai canza ginin gidan zuwa na zamani kuma yana so ayi da wuri kuma a bangare na aka fara saboda auren wai ba zai wuce wata d'aya ba. ni abinda yake bani tsoro na san halin shi in game da kud'i ne komai zai iya yi......."

"Ba 'yar sa bace ko saida ta zaiyi ina ruwanki " suka ji muryan Maa a bakin k'ofa wacce da alamu ta dad'e tsaye a wajan,duk kallon ta suka tsaya yi har ta shigo ta samu waje ta zauna tana fuskantar Inna.

"Kin bani mamaki Bintu da har zaki tada hanklin ki kiyi abinda baki tab'a yi ba wato kawo karan miji, yanzu da kika kwashi kafa kika zo min gida menene a zuciyar ki ko so kike ni in kira shi ince bashi da daman zabawa 'yarsa mijin aurex ko kin manta addinin musulunci ne ya koyar da hakan...."

"Maa na sani wallahi na sani amma kema kin san halin shi zai iya yin komai akan kud'i, sannan ya kamata ya shawarce ni ya fad'a min abinda yake faruwa ba wai inji maganan ta sama ba" Inna ke fad'an haka cikin wani irin murya mai nuna tsananin halin da take ciki.

"Menene halin sa Bint? koma wani irin hali ne dashi ba zai tab'a cutar da Yar cikin sa kuma maganan shawara da kike so yayi dake, wani shawarwan zaiyi bayan ke kan ki a karkashin sa kike.

Tashi ki koma d'akin ki ki cigaba da ibadan ki cikin kwanciyar hankali kaman yanda kika saba sannan kija yarinyan nan a jikin ki,ki kwantar mata da hankali kiyi mata tuni da duk wanda yayiwa iyayen sa biyayya to tabbas zai ga alkhairi a cikin rayuwar sa, kada ki kuma yin abinda zai tashi hankalin ta, duk halin da zata shiga in fana ganin ki a kusa da ita zata ji sanyi,

Sannan ke kuma ki bita da addu'oin zaman lafiya da farinciki Mai daurewa ya tabbata a gidan ta, insha Allah sai ts samu fiye da yanda muke hasashe".

Inna share hawayen ta take wasu na zubowa bata son musu da mahaifiyar ta amma ta san halin Baban mu sai shi, mikewa tayi da niyyan komawa Ya Maaji da bata da hakuri ga zafin zuciya ta bud'i baki da nufin zatace wani abu Maa tayi saurin dakatar da ita ta hanyan daga mata hannnu, kawar da kai gefe tayi tana cize lebe na haushin an hana ta magana.

"Ya Maaji na tafi ki gaida su Bayuram,Maa na gode Allah ya saka da alkhairi ya baki nisan kwana insha Allah zanyi kaman yanda kika ce" Inna ke fad'an haka tana gyara hijhabi dake jikinta.

Ya Maaji da duk takaici ya hana ta saka baki cikin maganan nasu da taga Inna ta juya zata tafi tayi yunkurin magana nan ma Maa bata bata dama ba ta kara daga mata hannu alaman tayi shiru.

Shirun tayi tana kallon Inna har ta fice sannan ta dawo da hankalin ta kan 'yar uwar ta tace " haba yaya yanzu sanyin halin naki ya kai kija baki kiyi shiru a cuci 'yar jikar ki guda d'aya tilo, ni dai wallahi tafiya ta zanyi ba zan zauna bakinciki ya kashe ni ba"

Hijabinta ta shura tayi hanyan waje, Maa tana ta kwala mata kira bata yarda ta juyo ba balle ta amsa, Dan murmushi Maa tayi tana girgiza kai tare da mata addu'a Allah ya rage mata wannan zafin zuciyan.

Lokacin da ta dawo bacci ya d'an sace ni ban san ma ta dawo ba sai cikin bacci naji kaman kuka harda shashheka, a hankali na bud'e ido na dan tabbatarwa, bayan ta na gani tana ta kuka tsakanin da Allah wanda tun tasowa ta banga ko kwatanci sa tayi ba.

Tausayi da kaunar tane naji yana bin ko ina a cikin jinin jikina saboda na san duk a kaina ta tada hanklin ta kan auren da taji Baba yace zai min, banida zab'i dole in kwantar da hankali in nuna mata babu komai ta wajena ko zata samu natsuwa, wannan dalilin yasa naki fad'a mata tun farko kenan amma ba yanda zanyi dole ne ta sani.

D'an motsi nayi yanda zata ji, aiko nan da nan ta shiga share hawayen sannan ta d'an juyo sai taga ido na a rufe, bakin gado tazo ta zauna tana shafa min gashin kaina, jin ta daina kuka yasa na bud'e ido na kaman yanzu ne na tashi daga baccin.

Murmushi ta sakar min tace " bacci kika koma kenan?" Gyad'a kai na nayi nima ina maida mata martanin murmushin.

Ina ta jira inji ko zata min maganan auren amma naji tayi shiru sai jana take da hira tana bani labaran ban dariya, nima dan in kwantar mata da hankali yasa na saki raina nayi ta dariya amma can kasan raina cike ya tab da damuwa.

Bayan sallah magarib sai ga Abban Zafar da tawagar sa a kofar gidan mu Kuma sun taki sa'a Baba yana nan bai tafi ko ina ba, Baba duk ya rikice ya susuce ganin manyan masu kud'in garin maiduguri a kofar gidan sa kuma da sunan sun zo had'a zuri'a dashi.

Makotan mu biyu ya kira sannan ya kira Baban Dije wanda zance shi ya jagoranci komai ya hana Baban mu gudun kada ya kwafsa ko ya saki layi, hakan da yayi ya taimaka kuwa dan shi Abban Zafar tunda yaji ance Mallam ya zata Baban Mallamin ne da gaske.

Wata 2 ciff aka saka na biki mu aka rabu cikin mutunci bayan sun sauke carton carton na minti da chewing gum da goro na rabawa yan uwa, Abba yaja Baba gefe ya bashi check na wasu kud'ad'e kan yayi hidimar biki da gida sannan ya d'aura da basa bukatan a kaini koda cokali guda d'aya su zasu tanada min komai su kawai surka suke bukata.

Murna da Baba yake ji kaman ya daka tsalle amma ganin yanda Baban Dije ya kama kai yake musu magana shima hakan ya kwaikwaya har yayi mishi sallama ya shiga mota driver yaja suka tafi.

Muna zaune sai gani mukayi anata shigowa da kwalaye kaman za'a bud'e shago, kowa kallon kayan yake tare da neman karin bayani sai dai babu mai bamu, sai da aka gama shigowa da kayan tass sannan Baba ya shigo yana jan banban rigan shi a kasa cikin d'aga murya ya fara magana yanda kowa na gidan zai ji.

"Allahu yayi Allahu yayi!!! Ina kuke mutanen gidan nan kowa ya fito yaga abin arziki daya same mu, kayan saka rana ne na 'yar albarka, wata 2 kacal iyayen ango suka ce a saka dan suna bukatan ayi auren da wuri.

Ba wayan nan kayan kawai ba har takardan karb'an kud'i na banki sirikin nata ya bani sannan yace basa bukatan mu kai ta koda cokali su zasuyi mata komai...."

"Aaaaaaayyyyyyiiirrrrrrrr!!! Inna Asabe ce ta rangad'a wannan gud'a cikin farinciki tace" Masha Allah 'ya tayi goshi duk abubuwa daka lissafo duk na saka rana ne ina ga Allah ya nuna mana ranan auren ba magana....."

"Aikin banza aikin wofi kowa yaga dama zaiyi ai tunda abin shige-shige ne" Gwaggo Aisha ta katse ta, Inna Asabe dai bata kula ta sai shewa suke da Allah ya sanya albarka suke da Mama Dije.

Tashin hankali sosai na shiga da ganin kayan da muka maganan Baba duk da na san da zancen, kokarin dannewa nake saboda kada in karawa Inna tashin hankali amma na kasa daurewa,kuka na fashe dashi sosai har jikina yana rawa na shiga d'aki da gudu na fad'a kan gado ina mai cigaba da kuka mai tsuma zuciyan mai sauraro.

.
Jiki a sanyaye Inna ta biyo baya na ta zauna a gefena ta kura min ido itama idon ta na cikowa da hawaye amma ta hana su zubowa, tana rayawa a ranta inama zata iya dakatar da wannan auren da tuni ta dakatar da wanne zan ji cikin lokaci d'aya na had'u da jarrabawan rayuwa ga rad'ad'in rabuwa da Yaya na bai bar ni ba ace kuma ga auren da bamu san daga ina ya fito ba.

Sai dai bata da zab'i dole ne ta karfafa min guiwa inyiwa mahaifina biyayya kaman yanda itama tayiwa nata mahaifin, gyara zama tayi tana gyaran murya sannan ta fara magana cikin rarrashi" wani lokacin kuka bashi ne waraka ba ga matsaloli na rayuwar mu ba,sai dai mu kanji sauki da rad'ad'in da zuciyoyin mu suka tsinci kan su a ciki dan haka ba zan hana ki kuka ba kiyi Zareefa kema ko zaki ji sauki.

A al'adance da kuma addinin musulunci ya bawa mahaifi daman zab'awa 'yar shi miji daya ga ya dace da ita bi ma'ana ya yarda da addinin shi da kuma tarbiyan shi dan haka kada kiyiwa mahaifin ki mummunan fahimta domin ba zai tab'a Kai ki inda zaki wulakan ta ba kuma albarkacin biyayya da kikayi mana Allah zai saka miki da mafi alkhairi ko kuma da abinda baki tab'a zato ba balle tsammani.

Abu d'aya da nake son ki tuna wannan auren ko dan Abdulbasit ya kamata ki rike shi da hannu bibbiyu saboda na san duk inda yake zai ji cewa za'a miki aure,kn ga kuwa kin nuna mishi zaki iha rayuwa ko babu shi sannan zai fahimci cewa kina da masoya ba shi kad'ai ne gare ki ba".

Tun ina kuka kasa-kasa har na daina nayi shiru ina sauraron kalaman Inna, ya zanyi dole ne inyi biyayya in aure shi tunda ya biyo ta hannun Baba, baya ga haka in nace bana son shi waye nake dashi a yanzu, wanda na taso da son shi tun ban san kaina ba ya guje ni ya watsa min kasa a ido I don't have choice rather than accept this man domin na gama soyayya a rayuwata zuciya ta ta rufe kofa tayi ban kwana da soyayya harb abada.

Sanyi sosai Inna taji a ranta na ganin kalamanta sunyi tasiri a kaina har na daina kukan sai ajiyan zuciya da nake akai-akai, matsowa nayi jikin ta sosai tare da d'aura kaina a kan cinyar ta na saka hannaye na duka biyu na rungumo kwankwason ta, itama tasa hannu ta dama tana shafa min gashin kaina na fara magana a hankali kaman mai rad'a.

" Inna ku iyaye nane biyayya a gare ku ya zama wajibi a gare ni, kukan da kika ga inayi ba dan auren da Baba yace zai min bane kawai na tuna da Yaya nane" na karasa wasu sabbin hawayen na zubo min na tausayin kai na, na fad'i haka ne dan in kwantarwa Inna hankali ba wai da gaske ba.

Cikin jin dad'in kalamai na Inna ta kara rungumo ni jikin ta tana shafa kaina tare saka min albarka da addu'oin gamawa da duniya lafiya.

******************

A kwana a tashi babu wuya a wajan Rabbi Izzati, mun cinye wata d'aya cikin watanni 2 da aka saka na bikina kuma gini da Baban mu yake yayi nisa sa dan har an gamawa Inna bangaren ta,2 bedroom da babban parlour sai kitchen da store sosai ginin yayi kyau, yanzu bangaren Inna Asabe da Gwaggo Aisha ake yi.

Maryam ta dage sai rawan kai take akan bikin ni bata san haushi ma take bani ba, duk wasu frnds d'in mu na makaranta ta sanar dasu sai shirye-shiryen su suke ni dai na kawao na mujiya na zuba musu.

A bangaren Zafar ma hakan take dan shi cewa yayi babu wani biki da zaayi sai ranan da zai auri love of his life sannan zasu sha bukukuwa ba biki bama.

Sadiq ne yace bai isa ba dole ne su sha biki in ya tashi yin wancan yayi abinda ya ga dama, yaso yayi jayayya amma ganin yanda Abba da Mom suka dage suna shirye-shiryen auren yasa yaja bakin shi yayyi shiru tare da zuba musu ido ya san in har zai cigaba da nuna halin ko in kula asirin shi zai iya tonuwa.

Akwai wata mata daga sudan take ta kware wajan gyaran amare Inna ta nemo kuma wai dole sai kaje gidan ta da farko ta ganki sannan zata duba gyaran daya dace da fatar ki,sun gama magana da Inna saura wai ta tura ni ta ganni, ba dan naso ba Inna tasa na kira Maryam a waya kan tazo ta rakani.

Da washe gari kuwa tazo muka tafi gidan nata da yake can Shokari, koda muka je gidan ta cike yake da matan aure harda sabin amare ana tayi musu aiki dan harda 'yan mata masu taya ta tana biyan su.

Tarba na musamman akay mana a babban parlour ta inda take sauke bakin ta na musamman,bamu dad'e da zama ba tazo wajan mu bayan mun gaishe ta cikin girmamawa itama ta amsa mana cikin kulawa sannan ta fara aikin ta wato rubuta duk kayakin da zasu dace da fatana da kuma gashi na sannan ta sallame kan cewa sai next week zan fara zuwa, godiya mukayi mata muka fito zuwa gida.

A gajiye tibis muka dawo kasancewar Anguwan nata da nisa sosai da namu, mun shigo layin mu kenan wata had'add'iyar mota baka wuluk tazo zata fita mu Kuma muna shiga kaman ance min dago kanki ina d'agawa na tsaya cak tare da dafe kirji na da hannu biyu ina zaro ido waje duk at da same time bakina na rawa nace " YAYA NAAA..."
[1/26, 7:14 AM] Golden Pen Writer's Assoc: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*25&26*

Yanda ka san statue haka na tsaya ko motsi na kasa yi sai motan nabi da kallo da idanuwana kaman zasu zazzago kasa ga kuma zuciya ta na ta lugude kaman zai faso kirji na ya fito.

" What's wrong with you Zareefa daga ganin mota sai kice ga Yayan ki, ke duk wulakanci da mutumin nan yayi miki ashe baki cire shi a ranki ba har kina tunanin zai dawo gare ki Kuma ga dukkan alamu zaki karb'e shi da hannu bibbiyu kenan...."

"Maryam shi na gani fa ba imagination bane" na katse ta da muryar tausayi.

"What ever, zo muje ga Inna can da kaya a hannu zata shiga gida muje mu taimaka mata ba wannan surutu mara kan gado ba" tana magana ne tare da jan hannu na muka fara tafiya ina waiwayen baya ko zan ga motan zai dawo amma har muka shiga gida banga ko kalar motan ba, kamin mu karasa Inna har ta riga mu shiga gida.

A parlour muka iske ta zaune tana kallo babu lodin kaya da muka ga ta shigo dasu, zama mukayi muma anan Maryam tana yi mata bayqni akan zuwan mu gidan mai gyaran amma hankalin ta yana kai na ganin nayi shiru na zama wani iri ba kaman yanda muka fita ba.

"Ke kuma lafiyan ki kuwa ana magana kinyi wani zuru dake?" Kaina na mayar kasa ina kokuwa da hawayen da naji suna son zubowa, harara Maryam ta b'alla min tana muskudawa sannan ta bawa Inna amsa.

"Kyale ta Inna ni takaici ma ya hanani kula ta, muna shigowa layin nan wai kawai dan taga mota ya wuce kin ga yanda ta daskare waje d'aya wai taga wannan mayaudarin da kyar fa naja ta muka biyo bayan ki lokacin kina shiga gida ga kaya a hannun ki nace muzo mu taya ki".

"Ban san meyasa taki sakawa ranta dangana ba ko kin manta aure zakiyi, haka zaki je gida wani kina wanna shirmen da shashanci? Ki kama kanki daga irin haka na gaya miki" Inna take dad'in haka cikin fushi ba tare da ta bawa Maryam amsar tambayar ta ba, nima hakuri na shiga bata ina cewa na daina ba zan sake ba Maryam tana taya ni sai da muka ga ta sauko sannan muka bari.

Bayan mun huta mun ci abincin da Inna ta ajiye mana sannan Maryam ta wuce gida tare da cewa sai munyi waya.

Tun daga wannan rana suka kara kaimin shirye-shirye da suke Inna ta ta zama busy sosai these days sai fita sayayya suke da Maman Dije wata rana Kuma da Inna Asabe, Gwaggo Aisha ce dai ko kallo basu ishe ta saima yad'a habaice-habaice da take.

A haka satin da matan tace zan fara zuwa gyara ya zagayo na fara zuwa wajan gyaran a motan su Maryam wanda Mamanta ce ta d'auki nauyin hakan kullum driver zai zo ya d'auke ni in mun gama zuwa yamma kuma waya kawai zanyi yaje ya maido ni gida kasancewar tace ba'a son ina shiga rana saboda zai maida aikin baya.

***************

A gidan su Zafar suma ba karamin shiri suke ba abinka da masu kud'i an gyara mana gidan da zamu zauna duk da sabon gini ne sai da suka Kara da d'an gyare gyare,kayan da za'a saka na cikin wannan gida Abban Zafar ne yayi order su daga kasar waje haka ma kayan lefe na suma duk a kasar waje suka had'o su, shi dai yana gefe yana kallon su yana jin ina zai iya hana su ko kuma inama zai iya fad'a musu gaskiya cewa auren da zaiyi temporary ce ba permanent ba su daina kashe kud'in su amma hakan ba mai yiwuwa bane dan yayi Imani Abban shi yaji abinda ya shirya suna iya batawa na har abada.

Sadiq kuwa in ka ganshi zaka zata shine angon kan yanda ya kasa ya tsare komai yana tafiya daidai, baya ko neman shawaran Zafar yake abinsa shi kad'ai ko Kuma suyi da sauran friends d'in su saboda ko ya nema baram-baram suke rabuwa dan haka suma suka ajiye shi a gefe suke abinda ya dace.

Ana saura kwana goma bikin duk an gama komai a gidan nasu had'a dasu cards da kayan da zamu saka na duk event d'in sun kammala sai bikin kawai suke jira.

Da yamma Mom ta kira shi a waya kan ya same ta a part d'in su, amsawa yayi da toh dama ba wani abu yake ba dan haka ya mike ya fita zuwa amsa kiran nata.

A parlour ya iske su kusan su biyar da Aunty's d'insa wasu ta bangaren Mom wasu kuma ta bangaren Abba sun baza uban kaya a gaban su suna ta kallo.

Gaishe su yayi ya koma gefe ya zauna yana yan dane-dane da wayar shi.

"Ya kuma zaka zauna a nesa, oya come closer kayan amaryar ka ne zo ka duba in akwai abinda baiyi ba sai a canza ko" Mom tace mishi hakan.

" No Mom ba sai na duba ba duk abinda kukayi daidai ne" yace yana kara gyara zama alamun bashida niyyan motsawa bare tashi.

"Kema dai Yaya da son jan magana kike, wannan lefen nayi Imani ko gidan governor zamu iya kaiwa without fargaba balle Kuma wannan 'yar talakawan" cewar wata kanwar Mom da suke kira da Aunty Hauwa dama tana takaicin Zafar daya tashi aure bai nema a cikin 'yan uwa ba yaje ya jajib'o musu 'yar talakawa.

"Hmmmmm" Mom tace tana tabe baki alamun maganan yayi mata dad'i.

"Ai babu zancen duk abinda akayi dadidai ne kai kafi mu sanin matar ka da abinda take so da Kuma abinda zaiyi mata kyau dan haka kazo ka duba nace maka" Aunty Falmata ke fad'in haka babu alamun wasa kan fuskar ta.

Da yake ya san halin ta bata da sauki sam kusan halin su d'aya da Abban shi shiyasa yake matukar shakkar ta, ba musu ya taso yazo ya tsugunna gaban kayan ya fara dubawa kaman da gaske bayan kawai d'agawa yake yana ajiyewa ,su Kuma kannen Mom da ita kanta sai tab'e baki suke na jin takaicin wai sai ya duba.

Yana yi yana kallon ta ta gefen ido ganin hankalin ta baya kan shi ya mike ya dawo gabanta ya zauna cikin natsuwa yace " na duba su duk sunyi kyau sosai Baawa".

Murmushin jin dad'i tayi tana ajiye wayar ta a gefe sannan ta maido da hankalin ta gare shi ta fara magana tace" yanzu abinda ya rage ga kayan da zatayi amfani dasu a events na bikin ku naka da nata duk suna wajan mahaifiyar ka it's a small gift from me".

Mom da taji kaman tayi kuka dan haushi dama niyyan ta in har ba tayi magana ba ta tafi ba zata aika min su ba, cikin dauriya tace" eh gasu nan Son, zoka duba Baawar ka ta sayo muku latest designs na birgewa".

Karasawa yayi zuwa inda Mom take nuna mishi ya zauna ya bud'e had'add'un trollys d'in da wani cool suits mai d'an karan kyau ya fara arba wanda kana gani ba sai an fad'a maka kasan mai tsada ne, cikin farinciki ya cigaba da duba su d'aya bayan d'aya ko wani event da kayan da zai saka har zuwa ranar daurin aure kuma kowanne da takalmi da wrist watch d'in shi, godiya ya fara yi mata cikin jin dad'i dan kayan sun burge shi sosai.

"I'm glad u like it, sai dai ka manta baka duba na amarya ba" ta amsa mishi itama cikin farinciki, sai da ta fad'a ya tuna da wata amarya, bashi da wani zab'in illa kirkiro murmushi tare da bud'e first 1 dake kusa shi.

Sai da yaji numfashin shi ya d'an d'auke na second biyar da yayi arba da wata gown na Indian material sai walwali da d'aukan ido yake ya had'u har ya gaji da had'uwan, daurewa yayi ya cigaba da duba kayan Wanda gaba d'aya anko ne da nashi sai dai a tunanin shi wayan nan zasu fi nashi tsada tunda su kowanne ga jewelry da takalmi da jakan shi.

Tun yana kirkiro murmushi na kar a gane halin da yake ciki har zuciyar shi ta rinjaye shi fuskar shi ya nuna abinda ke cikin zuciyar shi, Baawa da hankalin ta yana kan shi tana jiran taga yayi ta murnan ganin irin kayan da ta hadawa amaryan shi sai taga tsab'anin haka fuskan duk a murtuke yake duba su.

Cikin sanyin jiki ta fara mishi magana" da alamu dai Zafar kayan amaryar nan basuyi maka ba ko?"

" Haba Baawa wad'an nan kayan ko makaho ya shafa su ya san sunyi matukar kyau, abinda yasa kika gan ni haka jikina ne yayi sanyi ban san wani kalamai zanyi amfani dasu ba wajan gode miki domin kayan sun burge ni sosai" yabata amsa yana gyara mood da kawata fuskar shi da yalwataccen murmushi.

"Menene a nan da har kake fad'in haka Son, ko ka manta kai d'in gudan jini nane?"

Girgiza mata kan sa da yake kasa yayi ya cigaba da murmushin dole.

"Good yanzu abinda nake so da ksi shine kada ka bar kayan anan ka kai su can bangaren ka ko zuwa dare sai ka kai mata ko?"

"Toh Aunty mun gode Allah ya saka da alkhairi" yace mata.

"Ameen my son Allah ya nuna mana ranan lafiya mu sha biki" tace tana d'an dariya 'yar uwar ta Hadiza na taya ta dan su Mom sun bar musu parlorn tuntuni.

Maida boxes d'in yayi ya rufe ya kira masu aiki suka taya shi d'auka yayi musu sallama ya fita, a parlour shi suka ajiye suka fita shi kuma ya nemi waje ya zauna yana ta jan tsaki dan shi raini ne baya so da girman shi da komai wai shi za'a aika wajan 'yar yarinyan ga Sadeeq ma jiya yazo mishi da rainin hankali wai shi zai kai mata invitation cards shi kuma yace in ba zai Kai da kan shi ba ya zubar dasu a bola shi Kuma ya watsar mishi akan gado yace ga bolan nan, da gudu ya bi shi ya fita yana mishi dariyan mugunta.

"D'an iska zamu had'u ai sai na koya mishi hankali" yace shi kad'ai kaman wani sabon kamu.

Ni kuma gyaran nan da akayi min na kwana 2 ya karamin masifan kyau kaman an canza min fata ta saboda yanda ya kara laushi da tsantsi ga kamshi na musamman da yake tashi jikina.

Da daddare bayan mun idar da sallah isha'i Inna ta kawo min wani had'i da akayi na madara tace in shanye in bata kofin ta, karb'a nayi na shanye na saboda ta zata auren gaskiya zanyi take b'ata kud'in ta bata san auren wata 2 ko uku bane.

Lafiyayyan abinci ta zubo min shima tace in cinye dan kwanakin nan abinci masu gina jiki take bani Kuma shine ya bada gudumuwar hana rama ta bayyana a idon mutane, ina cikin tsakurar abincin ina sauraron wa'azi da sheikh Aminu daurawa da yake akan rayuwa a tashan sunna tv,o sosai wa'azin ya saukar min da natsuwa domin kaman dani yake yi.

Sallaman yaron makocin mu da yayi yasa na dago da kai na tare da amsa mishi kasancewar ni. kad'ai ce a parlour Inna tana kitchen.

"Wai ana kiran ki inji wani mai mota a waje".

Rasss shine sautin da naji zuciyata ya bada, na kasa bashi amsa saima zuciya ta daya tafi tunani waye zai kasance kenan,Yaya na ko d'an rainin hankali nan ne?

Koma wanene ina daidai da shi, kamin in samu amsan da zan bashi naji muryan Inna a kaina tana " baki ji bane ana kiran ki kikayiwa mutane shiru ko duk salon wulakanci ne haka, wato duk maganganun dana gaya miki ta bayan kunne suke wucewa ko?"

Kamin in bata amsa ta cewa yaron yaje yace tana zuwa, shi kuwa ya amsa da toh ya fita abinsa.

Itama kitchen ta koma ba tare da ta kara kallon inda nake ba, hannu nasa na goge hawayen da suka zubo min sannnan na mike na d'auki hijabi na dake kan kujera na saka na kama hanyan fita nima.

Har na kai hannu zan bud'e kofa naji muryan Inna a bayana tace" ki tabbatar kin shigo dashi parlour baki na Baban ku kada ki bar shi a waje kuma in kun shigo ki zo ki kai mishi ruwa".

Da toh na amsa na fita, ina jan kafa har na fita waje na tsaya a kofar gidan mu da yanzu ya koma gate, na kusan minti uku tsaye a wajan ina kallon motan banida niyyan karasawa, shima kuma ko fitowa bai da niyyan yi balle in saka ran zai fito.

Tunawa da yanda naga Inna ta b'ata ran ta d'azu yasa na fara takawa a hankali kaman mai tsoron kasan har na isa jikin motan na tsaya.

Sauke glass d'in motan yayi yana min kallon up nd down fuskar shi d'auke da wannan shu'umin murmushin sa na gefen baki " 'yar Mallam Ni kike jira in je in same ki kenan, baki san cewa duk zuwan da zaki ga nayi nan dalili yake kawo Ni ba wai dan kin isa ba...."

"Kaman yanda nima dalili ne yake sakani fitowa ba dan kana gaba na" na katse shi nima ba tare da na bari ya gama ba.

"Really!!! I like ur courage, ki cigaba but ki rike a ran ki cewa zaki gane kuskuren ki when we are together under the same roof" yace har yana wani cize lebe.

Kaina na kawar gefe ina son bashi amsa amma abinda nake hangowa a nesa damu kuma cikin d'an duhu shiya d'auke min hankali har na kasa kula shi, shima ganin hankalin na baya tare dani yasa ya fito tare da sauke kayan da ya kawo ya kira yara da suke wasan su a gefe yace su shigar min dashi cikin gida.

Shiga motan shi yayi ya tayar yayi revise, karan motan shi da naji shiya da na mayar da hankali na kan motan ba tare da ya kara ko kallon inda nake ba yaja motan shi ya tafi na raka shi da ido, sai da ya kusan b'ace min sannan na dawo da ido na wajan dana d'auke sai dai Kuma yanzun naga wayam babu kowa a wajan sai duhu da ya kara mamaye wajan.

Dafe Kai na nayi da naji yana juya min saboda tsananin ciwo da yake min , da kyar naja kafafu na da suka min nauyi na nufi gida ina mai mamakin ya akayi Inga mutum kuma lokaci d'aya kuma ya b'ace, ko dan na kasa cire shi a raina shiyasa yake min gizo.
[6/16, 9:15 PM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*26&27*

Haka na shigo ciki hannuna dafe da kaina, ragwajab na zube akan kujera ina lumshe ido ba tare da na lura da kayan da aka shigo da su ba Inna ta saka su a gaba tana aikin kallo.

"Ban san yaushe kika samo wannan halin na rashin ji ba Zareefa, yanzu duk maganan da na gaya miki amma babu wanda kika d'auka kika bar bawan Allah nan a waje ko balle ki kai mishi ruwan sha?"

Ban iya bata amsa ba sai goge hawaye da suka ki tsayawa nake dan na san ba lalle ne ta amince da abin da zan fad'a ba kasancewar bata san komai akai ba, nima kallon kayan da ban san daga ina suka zo ba nake domin ko za'a yanka ni ba zan iya cewa shi ne ya kawo su ba.

"Kai jama'a wannan lodin kaya daya kawo su kuma na menene, uhum harda su gwalagwalai kuma da alamu na fitan biki ne ko?" Na tsinkayi muryar Inna ta katse min zancen zucin da nake.

Bani da mafitar da ta wuce na amsa mata da " eh " tunda yanzu na fahimci daga ina kayan suka fito.

"Toh Masha Allah amma hidiman nasu yayi yawa bana so gaskiya ki gaya mishi su rage hakan nan kinji?" Nan ma dai gyad'a mata kan nayi ina mamakin dukiya da aka narkar wajan sayan kayan nan.

Nan na kwanta kan kujera duk abin duniya ya ishe ni na rasa ya zanyi da rayuwata, ban tab'a kawowa a raina zan shiga cikin irin tashin hankalin makamancin wannan ba

A kwana a tashi babu wuya wajan Allah dan yau shine karshen gyaran fata da ake min sai lalle da aka shiga yarfa min na jan lalle gwanin sha'awa taso a yi min kitso nace mata bana so ta bar min gashi na haka, ba dan taso ba ta kyale ni suka maida hankali kan lallen.

Sai bayan sallah isha'i muka samu daman komawa gida ta d'eba min wasu kayan gyaran tace in rinka yi a gida tunda auren saura kwana 3, karb'a kawai nayi na amsa mata da toh amma ba dan ina da niyyan yi ba.

A kofar gida suka sauke ni Maryam bata shiga ba saboda dare yayi suka wuce tana ta santin lallen da akayi mata wai yayi kyau, ni dai ban iya biye mata na juya zuwa gida abina kasancewar na kwaso gajiya.

Mutane na gani cike a cikin gidan mu ana ta cece kuce kuma kana jin maganan kasan kaman fad'a ake , d'an d'aga kai na nayi naga matan gidan mu ne harda makota, ban kara gigin d'aga kai na ba na wuce b'angaren mu tunda banga Inna ta a wajan ba.

A parlour na samu Inna da 'yan uwan ta zaune sun saka kaya a gaba suna maida abinda ya faru duk fuskan su babu dad'i sai ita Inna ce ba zaka gane mataa ba.

Zama nayi a kasa kan carpet na fara gaishe su d'aya bayan d'aya duk suka amsa min fuska sake, muna gama gaisawa na wuce kitchen neman ruwan sha anan ma wasu kayan abinci na gani gari guda.

Ina cikin shan ruwa ne naji Ya Maaji tana magana cikin b'acin rai wanda ya sani maida hankali kan zancen nasu I really want to know what happened.

"Ni dai idan kun san ba zaku canza halin ku ba wallahi karshen ta ba dani za'a yi bikin nan ba, haba wannan wacce irin rayuwa ce ayi ta cutan ka ana kunsa maka bakinciki amma ka kasa ramawa, wa za'a nunawa hakurin muma ai muna da itan matsalsr idan yayi yawa sai a maida ki kwandon shara yanda kowa ya kwaso nashi kan ki zai juye".

"Gaskiya ne hakurin Bintu yayi yawa sosai har ta doke Yaya wajan sanyin hali, amma wannan zalincin ne dai ba zamu bari ba dole ne a d'auki mataki saboda gaba" cewar Aunty Batool.

"Kina ji fa ita Bintun da bakin ta yanzu take cewa ba yau ta fara yi ba wai ranan da aka fara musu gini an ga wasu layu wanda aka kona ita kuma a take ta fara iface-iface wani babban abin takaici wai ita da Zareefa su sukayi mata addu'a har ta samu lafiya...."

"Har ta samu kafan komawa wajan bokan ta zaki ce Batool, in ba dan Allah ya takaita wannan yaro Ibrahim ya ganta yazo ya fad'a ba, da shikenan auren nan ya fasu amma da yake bata da kunya bakin ta bai mutu ba ana magana tana mayarwa" fad'in Ya Maaji.

"Ban ki ta naku ba nima ba wai kuma fad'an ne ban iya ba, amma abinda nake son in tuna muku duk wanda ya rike Allah in ba wani ikon sa ba babu abinda zai same ka, ku duba mana sau 2 tayi yunkurin cutar da mu Allah yana mayar mata da abin ta.

Ban so kuka kula ta ba, jibi yanda asirin ta ya tonu cikin bainar jama'a wannan ma ya ishe ta ishara, mu kuma bama gajiya da d'aga hannayen mu sama insha Allah, Allah zai kare mu" Inna ta basu amsa cikin sanyin murya babu wacce ta kara cewa kala da alamu maganganun ta ya kashe musu jiki.

"Innalillahi wa Inna ilahi raji'un" shi kawai nake ta maimaitawa tare da sulalewa na zauna dabas kan tiles na kitchen d'in, cikin tashin hankali amma ni kam Ibrahim bai kyauta min ba da yazo ya fad'a har aka dakatar da ita, ina ma tayi nasaran sake binnewa da shikenan na fita daga wannan cakwakiyar matsalan.

"Gata da hassada da ya gama bin jinin jikin ta dubi yanda ta fito wai tana nuna adawar ta a zahiri kan kayan cin-cin da aka kawo" naji muryan Aunty Fatima tana magana cikin d'acin rai.

Sai ana na fahimci ashe kayan da na gani kayan cin-cin ne kenan, shikenan yanzu da gaske ake aure za'a yi min, auren ma da wanda bai san daraja ta ba?

Hawaye sai rige-rigen saukowa suke banyi yunkurin hana su ba na bar su suna kwarara domin yana rage min rad'ad'in dake cikin zuciya ta.

Muryan Inna naji tana kwala min kira ba shiri na mike daga zaunen da nayi ina share hawaye na na fito duk suka bini da kallon tausayi .

"Me kike yi a kitchen d'in tun d'azu" ta jeho min tambaya,

"Ruwa na sha " na amsa mata cikin murya kuka, kan kace me kuma hawaye suka fara kwaranya.

"Daga tambayan ki shine zaki fara min kuka? Bari in tashi inyi miki abinda zakiyi kukan da hujja" Inna ke fad'an haka tana shirin mikewa, da gudu nayi d'aki na maida kofa na rufe ina jin su Ya Maaji suna mata fad'an kada ta kuskura ta tab'a ni ta bar ni inyi kuka na, ban ji karshen maganan su nayi shirin kwanciya na kwanta abina.

Da washe gari ga mamakina ashe duk basu tafi ba anan suka kwana sai ya Maaji da ta kwana gidan Maa, da rana ya fara yi sai ga gidan mu ya fara cika da 'yan uwa ashe wai yau ake cin-cin ni dai ganin sun fara yawa na wuce bangaren su Maman Dije saboda kowacce ta ganni sai ta kira ni da sunan amarya basu san hakan kona min rai yake ba shiyasa na gwammace in tattara in bar musu gidan su kara ta.

Kamin in wuce naji sun fara sa-in-sa da 'yan uwan Baba da suka zo cewar su zasuyi, su Aunty Batool kuma suka ce anyi magana da professional bakers su zasuyi kasancewar komai ya zama na zamani ita kuma Gwaggo Hinde ta fara masifa wai ai zagin su akayi a fakaice meye basu iya ba da za'a ce zasu kira wasu suyi dama sun raina su.

Wucewa ta nayi abina ban san ya suka kare ba, ina can b'angaren su Dije Ni kad'ai duk abin duniya ya ishe ni zuwan su Maryam da sauran 'yan class d'in mu yasa naji d'an dama-dama.

Kusan azahar Dije ma ta iso da yaron ta da yayi wayo gidan ya gama kacamewa saboda surutun ta, hatta Hajara nan tazo tana d'an kqma jiki tana baya-baya saboda abinda ya faru jiya, sai da naja ta da wasa sannan ta saki jiki suka cigaba hayaniyar su Jameela ce dai ban san ina take ba domin yanzu abin nata kullum kara muni yake dan sai tafi sati bata gida kuma koda ta dawo to a buge take dawowa ta zama cikakkiyar 'yar kwaya.

Muna nan a b'angaren Maman Dije Har dare a lokacin mafi yawancin 'yan matan sun wuce Dije ma ta tafi sai Maryam da Hajara ne kad'ai suke tare da ni amma itama Maryam d'in shirin tafiyan take wai sai gobe zata taho gaba d'aya ba zata koma ba sai an gama bikin.

Har bakin gate muka raka ta nida Hajara inda driver gidan su yake jiran ta, ta shiga yaja suka tafi mu Kuma muka koma cikin gida, Hajara har tana shirin shiga kofan su na tsaida ta nace " Dan Allah Hajara muje mu kwana tare a d'aki na kin ga har yanzu da sauran mutane a b'angaren mu".

"Kina ganin babu matsala?" Tambayan da ta jeho min kenan idon ta na cikowa da kwalla.

"Wani matsala kuma ko kin manta ke'yar uwa tace" na bata amsa tare da jan hannun ta muka wuce, a parlorn muka tadda su Ya Maaji sun baje suna rarraba snacks da akayi da wayan da aka bayar akayi cikin different containers wai suna rarraba su.

Za'a cire na gidan su Ango da wanda za'a rabawa baki sai kuma w so hg6xhanda za'a rage min "wai" atoh dole ince wai dan ni har yanzu na kasa gaskata aure na ake.

Hajara duk ta kasa sakin jikin ta akan abinda ya faru jiya ga ya ma'aji sai binta da kallon banza take,ganin haka yasa na jata zuwa d'aki da yake mallaki na a yanzu, tunda muka shiga naga jikin ta ya kara sanyi sai bin d'akin da ido take alaman d'akin yayi mata kyau dan sai ince zan iya kira shigowan ta d'akin mu tun kamin ayi mana wannan ginin.

A bakin gado nace ta zauna ni kuma ina shiga bayi nayi wanka tare da dauro alwala na fito na fara shirin bacci,duk tana zaune a inda na bar ta"tashi kema ki watsa ruwa zaki fi jin dad'in baccin" nace mata ina saka kayan bacci na ba musu ta mike ta shiga kamin ta fito na fitar mata da rigan bacci sannan na haye gado na kwanta,ko da ta fito ta mayar da kayan jikin ta nace ta canza tare da nuna mata kayan da na fitar mata.

Ba zan iya cewa nayi bacci ko banyi ba a wannan daren saboda zanyi kaman bacci ya fige ni kuma duk juyi da Hajara tayi ina ji,ni dai gani nan har aka kira sallahn farko na tashi nayi alwala na fara nafila har aka kira na sallahn asuba mukayi tun da sanyin safiya mutane suka fara hidiman gaban su gidan ya d'auki hayaniya na ana shirin biki a gidan da gaske.

Breakfast da aka kawo mana ban iya cin komai illah tea dana sha kawai nayi wanka muka koma can b'angaren Maman Dije a lokacin 'yan uwan sun fara cika gidan na kusa da nesa

'Yan mata da muke mates duk wajan mu suka zo suka dasa sabon hira sunayi suna ta tsokananta amma na kasa kula kowa cikin su sai yake da nake binsu dashi.

Kusan 12 rana sai ga masu decor sun zo wai daga gidan su Ango aka turo su suyi decoration na wajan da za'ayi wushe-wushe.

Duk yanda nayi gudun kitso bai yiwu ba dan Maa ce da kanta ta turo wata mata tace in zauna a min kitso,dole na na zauna aka yaryad'a min kitson KELEYASKU.

Ba karamin kara fito dani kitson yayi ba, da yake step 2 akayi min wasu ta baya wasu Kuma ta gaba,na gaban nan ya sauk'o min har kan kirjina na baya kuma har gadon bayana kowa na wajan sai santi kitson suke,bayan sallah la'asar wasu masu make-up kusan su 4 wai suma daga can aka turo su harda photographer da masu video coverage kan kace kabo duk sun fara abinda ya kawo su,kamin ayi sallahn magriba naga 'yan mata sunyi wanka kowacce ta fito cikin ankon ta na atamfa mai tabarma da Maryam ta jagoranta sukayi.

Nima ina yin sallah aka tilasta ni nayi wanka ina fitowa masu make-up din suka rufu kaina kowacce tana baza fasaharta,cikin lokaci kankani na fito kaman wata tauraruwa ni kaina kasa daina kallon kaina nayi ta cikin mirror.

Maryam ce ta d'auko min akwati da kayan da zan saka suke ciki,ashe kowanne sun manna sunan event din da zan saka a jiki,ban tab'a gani ba duk da boxes d'ina a d'akina suke ko dan basa gaba nane oho.

Wani atampa ce da ban san sunan ta ba amma kana gani kasan kud'in ta ba na wasa bane anyi mishi d'inkin GUMJE KANURI daya sha aikin stones kaman ba gobe sai Kuma laffaya wacce zata shiga da kayan shima duk ya Sha adon stones sai Kuma jewelry na d'anyen gold.

Ba zan iya misalta muku irin kyan da nayi ba ku dai kawai ku hasaso da kan ku.

Fito dani waje akayi nan bakin gate din mu inda yasha decorations dada fararen fitulu kaman rana, su Maryam na min jagora Aunty Fatima na bin mu da turarrn wuta har zuwa inda aka tanada wai wajan zaman mu ni da shi suka zaunar dani wai ana jiran zuwan ango.

Ni dariyar suma nake a zuciya ta da suke saka ran wannan d'an rainin hankalin ne zai zo nan lalle suna da babban aiki.

Kaman daga sama naji gud'a da kid'an GANGA KURA ana shelan isowan ango da jama'arsa, tun daga nesa na hango shi cikin wasu dankareriyar shadda wanda yayi shige da kayan jikina wato sky blue.

Tun kamin ya karaso naji zuciya ta nata bugawa kaman ya fito Dan na San halin shi ban san yau Kuma da me yazo ba.
[6/16, 9:16 PM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*28&29*

Duk kamshin turaren wuta da yake wajan dana sauran mutane sai da wannan mayen kamshin nashi ya cika wajan,Kara sadda kaina kasa nayi ban kara gigin d'agawa ba tunda na d'aga na farko zuciya ta kuwa kaman zai faso kirji na ya fito haka nake ji tsabar bugu da yake.

Ba komai ya saka ni shiga wannan halin ba sai dan sanin halin sa na wulakanci da disgi, ina gudun kada ya gwada su a nan a gaban kowa ba abinda na tsana a rayuwata kaman mutum ya wulakanta ni ko ya disgani a bayyanar jama'a.

Ina cikin zancen zuci naji alamun mutum a kaina d'aga ido da zanyi na ga shine ya rankwafo da kan sa daidai fuska na yana sake min wannan shu'umin murmushi nasa yana kallon na, ni d'in ma shi nake kallo ya bala'in kara had'uwa cikin light blue shadda shi ga hula da ya saka itama light blue ce ba zan iya kwatanta muku yanda yayi kyau ba just imagined him.

Na shagala da kallon shi naji yana dariya kasa-kasa yace " please da baki wahalar da kan ki wajan wannan abubuwa da kika shafa ba domin kara miki muni sukayi" ya karasa da kara sautin dariyar shi sannan ya zauna a gefe na inda aka tanada domin zaman shi.

Hawaye naji sun cika min ido amma ban bar su sun zubo ba, I knew it na san dole ne ya shimfid'a min wulakanci son ran shi wai kara min muni sukayi ko ina ruwan shi da kwalliya ta.

Kuma abin takaicin salon da yayi amfani dashi ya min maganan zaka d'auka hiran soyayya muke sai wani narke ido yake dan haka abin ya birge mutane sukayi ta mana hoto a wannan yanayin .

Kawar da kai na nayi gefe ina jin kaman in tashi in gaggaura mishi maruka amma na danne zuciya ta ina hasaso yanda zaman namu zaya kaya nida shi.

Ina cikin zancen zuci naji wannan mayen kamshin nashi ya kara cika min hanci wanda yake kara tabbbar min da kusancin namu ya karu, ban juyo ba balle inga wace irin zama mukayi da shi.

A zabure na juyo ina kallon shi da ido na duk a waje sakamakon jin hannun shi a cikin nawa, muna had'a ido ya sake min wannan killer smile d'in nan nashi da in yayi babu alkhairi a cikin ta

Aiko kamin in tantance me yake faruwa naji ya fara murza min hannu cikin kwarewa da cin zali da mugunta, a take naji kaman in saki fitsari a wajan amma da yake nima ba baya ba wajan iya basar da abu dan haka na basar kaman ba ni yakewa wannan muguntan ba.

Cikin abokan shi wasu suka zo suna mu fito muyi rawa amma kememe yaki ko matsawa balle ya tashi , da suka ga bashi da niyyan tashi duk suka rufu kan mu tare da fara mana barin kud'i kaman basu san zafin su harda wasu cousins d'in shi 'yan mata da naga suna yi min wani kallon kasa-kasa ko me suke nufi oho dan ni Yayan nasu ma bai ishe ni kallo ba balle su.

A cikin gida kuma iyaye na sun yiwa nashi tarba na mutunci sannan aka fara wasu events na al'ada game da wushe-wushen, dama wushe means welcome da yaren kanuri so they are welcoming them to our family wato an zama family d'aya kenan suma sun bada kayyaki na al'ada da ake bayarwa sannan su Inna ma sun mayar musu da wasu kayan suma.

Sun d'auki lokaci mai tsawo sannan suka gama nasu a cikin gida suka fito gaba d'ayan su harda nawa iyayen, wata mata ce cikin 'yan uwan sa naga ta nufo mu kai tsaye tana murmushi tace " wannan wani irin Ango ne da ba zai cashe ba a ranar bikini sa?"

Turo baki yayi kaman wani karamin yaro sannan ya bata amsa " Baawa ni ban iya rawa ba Kuma..." Mugun kallo da yaga ta watsa mishi yasa ya mike babu shiri da hannu na a cikin nasa wanda yanzu nake ji kaman ba a jiki na yake ba tsaban mugunta da yasha.

A yanda ya mike ya tabbatar min da yana matukar shakkan matar nan jibi yanda ya mike babu shiri, a raina ina ashe duk wannan muzuran nashi na banza ne tunda da wanda yake. tsoro har haka.

Yanda kika san statues haka muka tsaya musu kikam ba wanda yake da yunkurin yin motsi balle a je ga zancen rawa, iyaye na da nashi suka fure ruf sai barin naira suke mana.

Ni dai duk mamaki ya ishe ni a raina yanda suke zubar da kud'i kaman basu san zafin su ba, a zuciya ta nace ina Gwaggo Aisha Mai cewa Yaya na d'an yankan kai ne tazo taga wayanan da ko ni kaina zan iya kiran su da hakan dan barnan kud'in yayi yawa.

Ana cikin filin Sadeeq yazo ya fara mishi magana a kunne wanda yaja hankali shi ya saki hannu na ba tare da ya sani ba, ban san me suka tattauna ba sai dai naga yana murmushi ya juyo zai kara rike min hannu kan zamu koma mazaunin mu nayi azamar janyewa nayi gaba yabi baya na har muka zauna basu daina mana liki ba.

Sai wajan sha d'ayan dare sannan taron ya tashi suka shiga motocin su suka tafi mu kuma muka koma cikin gida muka bar masu decor da tattare wajan.

Muna shiga ban tsaya a ko ina ba sai bathroom na samu ruwa mai d'umi sosai nayi wanka tare da gasa hannu na da nake jin sa kaman ba a jiki na yake ba dan tsabar jin zali daya sha.

Ina fitowa a wanka naji su Maryam da sauran cousins d'ina da muke mates sun zo taya ni kwana suna ta yaba mugun da basu san halin shi ba.

"Wow kai Zareefa tayi babban sa'an samun hadadden miji mai iya love ga kyau ga naira ohh so romantic" cewar Zainab tana zama kusa da Maryam.

"Allah ya samu a danshin ta abun yana bala'in burge ni samun classic miji haka" inji Hanan.

"Ni abinda yafi birge tunda ya iso yake makale da hannun ta kaman za'a kwace mishi ita" Hauwa ta katse ta.

Kallon hannun nawa nayi wanda ya koma jajawur saboda azaba su kuma a haukan su suna yabawa sun zata zallar soyayya ce, cike da jin haushin su na juya musu baya tare da jan duvet na rufe har kaina, ina jin su suka cigaba da suratan su daga baya suka hakura suka kwanta bacci.

Basu dad'e da kwanciya ba duk sukayi baccin su hankali kwance, tashi nayi na zauna ina kallon su cikin sha'awa ni da nake jin ido na a bushe babu alaman d'igon bacci, ba yau kad'ai ba tunda maganan auren nan ya tabbata na rabu da bacci mai dad'i dan sai in d'auki lokaci Mai tsawo ban runtsa ba, ko kuma na samu baccin ya kwashe ni daren yana rabawa rabi sai in farka kuma wani lokacin ya tafi kenan wani lokacin kuma sai kusan asuba zai kara sace ni.

Yanzu ma da naji kwanciyar ya ishe ni na shiga bayi nayi alwala nazo na tada sallah tare da neman agaji wajan ubangiji na.

A b'angaren su Zafar kuwa yan uwan Abba cikin farinciki da Kuma yaba yanda iyaye na suka karrama su suka isa gida yayin da yan uwan Mom sai tab'e baki suke wai ya rasa inda zai nemo aure sai a wannan gida kaman akurkin kaji.

Shi kuwa Zafar ko bai kula kowa ba ya shige part din shi ya kulle kan shi a ciki dan kowa ma haushi yake bashi, duk yanda abokanen shi suka so su gan shi bai yiwu suka wuce.

********************
Hausawa sun ce rana bata karya sai dai uwar d'iya taji kunya, toh hakane ya kasance a yau asabar itace ranar daurin auren kaman yanda naji suke fad'a kuma nake gani a yanzu duka gidan ya kaceme da hayaniya kowa sai hidiman gaban shi yake, masu gyaran gida nayi masu girke-girke nayi masu wanka ma nayi.

Ni kuwa ina can kuryan d'aki abin duniya duk ya ishe ni ganin cewa fa da gaske ne auren nawa za'a daura maimakon na tsinci kaina cikin farinciki kaman kowace amarya sai dai ni a bakinciki na tsinci kai na dumu-dumu ga kewan Yaya na da ya dawo min sabo fil, na san da aure na da shine da nafi kowa farinciki a rayuwa amma sai gashi yau da wanda bai sona bai san daraja ta ba za'a had'i ni aure.dashi wace irin rayuwa zan shiga???

Kuka naji mai tsanani ya taho min na tausayin kai na, mikewa nayi ba tare da na kula 'yan mata da suke ta hayaniyar su ba na shiga
bathroom dan in samu sukunin yin kuka na ko zan ji saukin rad'ad'in da zuciya ke min.

Zama nayi dirshan a ciki na kama kuka kaman rai na zai fita ji nake kaman rayuwa ta tazo karshe ji nake shikenan nayi ban kwana da farinciki a rayuwa ta ji nake kaman na yanki ticket na shiga kunci na har abada.

Ban san iya adadin lokaci da na d'auka a bathroom d'in ba sai knocking da naji ana yi a kofan yasa na d'an tsagaita kukan tare da maida hankali na kan mai bugawan.

"Zo ki bud'e kofan nan Zareefa" naji muryan Inna daga waje, goge hawaye na na shiga na nufi kofan na bud'e tare da komawa gefe kai na a kasa naki yarda mu had'a ido da ita, shigowa tayi ciki tana bin fuska ta da kallo.

"Rufe kan ki kikayi kina kuka ko?" Ta tambaye ni still tana karantar yanayi na ta maida kofan ta rufe, maimakon in bata amsa fad'awa nayi jikinta ina mai kara rushewa da kuka mai tsuma zuciyan mai sauraro balle ita da take mahaifiya a gare ni.

Rungume tayi itama tana kokuwa da nata hawayen dan kada su zubo da kyar tayi nasaran maida su sannan ta dago ni tana share min hawayen fuska ta tanayi wasu na kara zubowa.

Murmushi d'auke a fuskata ta take kallo na sannan ta fara magana " toh menene abin kuka anan kuma uhum? Yakin matan kenan muma haka aka rabo mu da gidajen zuwa inda bamu saba kuma muka d'auki hakuri da juriya muka saba kema hakuri zaki yi wata rana sai labari.

Aure bautan ubangiji ne a gare mu mata shine kuma mafi saukin hanyan shiga aljanna in min bi Allah kuma kika yiwa mijin ki biyayya kaman yanda Allah ya umarce da muyi toh tabbas zaki rabauta, miji a duk yanda kike tunani a musulunci ya wuce nan miji babban jigo ne a rayuwar 'ya mace tunda da zaran an kai mace d'akin mijin ta shikenan komai nata ya koma hannun shi ko iyayen ta basu da iko a kanta ko kad'an misali koda mutuwa akace nayi in yace ba zaki zo jana'iza ta ba dole ne kiyi hakuri ki zauna kiyiwa mijin ki biyayya...."

A razane na dago jajayen ido na da kuka ya rina ina kallon ta ina son yin magana amma na kasa sai baki na da yake ta karkarwa.

Gyad'a min Kai tayi tana mai cigaba da murmushin " irin wannan biyayyan ake son mace tayi a gidan mijin ta, nasan yanda kike ji na san abinda kike tunani amma ina mai baki shawara a matsayi na na mahaifiyar ki, ki cigaba da hakuri kiyiwa mahaifin ki biyayya insha Allah gaba ba mu ba ke da kan ki sai kinfi mu alfahari da wannan aure zan cigaba da yi muku addu'a insha Allah komai zai dai-dai ta .

Yanzu kiyi wanka ki fito ga masu miki kwalliya suna jiran ki a d'aki" tana fad'an haka ta wuce ta fita ta ja min kofa bata tsaya a ko ina ba sai bathroom din ta,ta fashe da kukan da take ta dannewa tun d'azu " ya Allah ka taimake ta ka kare ta kada ta fuskaci irin rayuwar da nayi a cikin gida na ya Allah ka sanyawa rayuwar auren ta albarka".

Haka ta cigaba da kukan ta tana sumbatu domin a kullum daurewa kawai take ace a aurar da 'yarka ga wanda baka san daga inda yake ba balle ayi bincike a san halin shi babban tashin hankalin ta shine bata da daman cewa komai akai saboda mahaifiyarta ta gargad'e ta tun farko, amma ba zata daina fad'awa Allah ba ya bani ribar biyayyan da nayi musu.

Da kyar ta rarrashi kan ta ta daina kukan ta fito jin hayaniya na kara yawa alamun mutane suna karuwa kenan.

Ko da ta fito sai ta aro jarumta ta daurawa wanda take dashi a baya ta cigaba gaggaisawa da yan uwa da abokan arziki amma taki yarda ta kalli gefen da Maa take balle su had'a ido ta fahinmci tayi kuka, sai dai bata sani ba ta makaro domin Maa ta riga da ta gane halin da take ciki, murmushi kawai tayi tana yaba jarumtar 'yar tata.

Bayan fitan Inna daga bayin sabon babin kuka na bud'e inayi ina mai tausayin kaina ta yaya zan iya yin biyyan nan da Inna take Fadi ga wannan azzalumin? Da kyar na rarrashi kaina na daina kukan na fara wankan sanadiyan takura ni dasu Maryam suka yi.

Koda na fito na kasa kallon kowa a d'akin sai kan stool na gaban mirror naja na zauna kai na a kasa ba dan komai ba sai dan bana son yawan magana, su kuma masu make-up suna ganin na fito suka iso dan yin aikin su, ban hana su ba kuma banyi musu gardama ba suka fara min sai dai yau light make up sukayi min amma duk da haka ba karamin kyau nayi ba, Maryam da jikin ta duk yayi sanyi ganin yanayi na ta d'auko musu trolley da aka saka kayan da zan saka yau da safe ta kawo musu.

Su suka taimaka min na shirya cinkin wata expensive lace fari sol dashi yasha diamond stones, ni dai tunda nake a rayuwata ko labarin irin lace din ban tab'a ji ba balle gani, headtie na wani yadi mai sheki suka nad'a min shima fari ne sai set na dan kunne da sarka harda zoben shi na pure diamond suka saka min.

Ba zan iya kwatanta muku yanda ni Zareefa nayi kyau a wannan rana ba just imagine it urself sai dai ko kad'an babu abinda ya burge ni a ciki in na tuna sabon rayuwan kunci da zan shiga ma sai inji kuka na neman kwace min.

Kawaye na suma sun fito cikin wani hadadden atamfa da sukayi anko kowacce sai zuba kamshi da haske suke zubawa ana jiran su angwaye su karaso dan karfe goma sha d'aya ne daurin auren.

A can gidan su Zafar suma haka suka tashi da shirye-shiryen gaske ba irin na jiya ba dan Baawa jiya bayan dawowar su daga gidan mu ta kai karan su Mom akan yaja musu kunne kada su zubar mishi da kima gidan surukai, aiko bata ji da dad'i ba wajan Abba dan sosai ya nuna mata b'acin ran shi sannan yaja mata kunne tayiwa 'yan uwanta magana kowacce ta kama kanta in ko ba zasu kama ba kofa a bud'e take duk su watse bayan son harkan k'ananan mutane, dole ta nuna tayi nadama a gaban shi da alkawarin babu wata b'araka da zata taso daga gare su sannan ya kyale ta ta koma ciki cike da tsana ta.

Sadeeq shine yazo ya tada Zafar daga bacci dan har tara saura yana kwance yana bacci cikin kwanciyar hankali abin shi, ya shirya tsaf cikin hadaddiyar shaddar shi ash color sai kamshi yake zubawa kaman shine angon,Koda ya farkan ma fad'a sukayi tayi shida Sadeeq din kan me yasa zai tashe shi yana cikin baccin shi mai dad'i.

Ganin yana son yaja hankali sauran abokanen su da suke parlour yasa shi yayi shiru yace toh yayi laifi kuma ya amsa ya tashi yayi wanka ya shirya ga Abba da sauran abokan su suna jiran shi su tafi wajan daurin auren.

Jin ya ambaci sunan Abba yasa ya mike Yana kumbure-kumbure kaman karamin yaro ya shige bathroom d'in shi dan yin wankan, dariya Sadeeq yayi sai da yayi Mai isar sa sannan ya ciro mishi kayan da aka tanada mishi domin d'aurin auren.

Sadeeq shiya taya shi shiryawa sunayi suna fad'a shi dai Sadeeq dariya yake ta mishi ganin yanda yake turo baki kaman wani karamin karamin yaro mai shagwab'a.

Farar dok ce mai matukar tsada yasa mai d'aukan ido yasha aikin hannu wato (gatau) hula takalmi duk farare ne wrist watch na hannun shi shima na pure diamond ne sai kamshi na musamman yake kana ganin shi kaga haddaen ango, suna gamawa suka fito parlour inda abokan sa suke jiran sa.

Yana fitowa ihu suka fara suna mishi kirari saura na tsokanan shi dan sake fuska yayi ya dan biye musu suka tab'a wasa sannan suka raka shi wajan Mom.

Tsakar gidan babu mutane sosai dan haka basu sha wahalan karasawa cikin ba , parlour Mom a cike yake ana ta hidima suna ganin shi wata mai murya ta saki wani irin gud'a da ya cika gidan nan da nan sukayi kan shi ana ta wasa da dariya da kyar ya samu ya karasa sama d'akin Mom, tana zaune cikin kawayen ta da 'yan uwan ta suna hira.

Ido ta zuba mishi har ya karaso ciki zuciyar ta kuwa kaman farar takarda yau Allah ya nuna mata auren tilon d'an ta.

Albarka suka yi ta saka mishi bayan ya suguna har kasa ya gaida su, Mom harda hawayen farinciki dan yau babbar rana ce mai babban tarihi a rayuwata.

Kiran da Abba yayi mishi ne yasa shi mikewa ya fita ya tarar da tawagar Abba har sun fara tafiya, ba b'ata lokaci shima ya shiga cikin abokan sa suka kama hanya.

Akwai wani babban masallacin juma'a a bakin layin mu kuma a nan ne za'a d'aura auren, so duk a can wajan layin sukayi parking wasu ma ko wajan parking din basu samu ba saboda yawan motocin dan haka wasu suka fara shigowa cikin layin namu Dan samun wajan parking.

Masallacin kan shi ma har yayiwa mutane kad'an wasu basu samu shiga ba ko ina ka duba taron al'umma ne, in wanda bai sani ba yazo yaga taron zai zata auren 'yar babban mai kud'i ake ba ko dan siyasa ba 'yar Mallam Hassan ba.

Baba yau in ka ganshi kaman yayi hauka saboda farinciki harda su governor a daurin auren 'yar shi harda manyan kusoshi na gomnati ,ba'a tsaya b'ata lokaci ba aka daura aure na da Zafar kan sadaki naira million 2.

Muryan maroki da ya fara shelan d'aurin auren har cikin gudan mu a lokacin ina tsakar gida cikin mutane dan Inna ta saka ni fitowa waje gaida 'yan uwan Baban mu, a take wajen ya kacame masu farinciki suka fara masu bakinciki ma nayi, ni kuwa ji nayi kaman an saka ni a cikin kankara haka naji jiki na yayi wani bala'in sanyi tare da zazzab'i mai zafin gaske ba shiri na nufi bangaren mu kamin na karasa d'aki na har na fara rawan sanyi ina shiga na kwanta na lullub'a da bargo ina hawaye a haka Aunty Batool tazo ta same ni cikin rarrashi tayi min nasiyan yadda da kaddara sannan ta bani magani na sha bata bar d'akin ba sai da taga bacci mai nauyi ya d'auke ni sannan taja min kofa ta fita.

Anan d'aura aure su Abban Zafar gaba daya suka wuce reception da Abba ya had'a a nan cikin gidan shi, su Zafar ma bayan shi suka bi duk yanda Sadeeq yayi dashi akan su tsaya ya d'anyi pics tare dani saboda tarihi yaki ya shiga mota suma suka rufa mishi baya.

Sai yamma naji d'an karfin jiki na aka kara canza min kwalliya zuwa walima cikin abaya da Inna ta siya min saboda walimar ba'a dad'e da farwa ba yan gidan su Zafar suka kawo lefe na da ya kusan haukata mutanen gidan mu dana anguwan baki d'aya, nima a yanda naji Maryam tana lissafowa ban tab'a jin labarin irin su ba.

Bayan an gama cece-kucen ganin lefen suma suka shiga cikin mu akayi walimar dasu inda Mallama Falmata Zanna ta wa'azantar kan biyayyan aure ko Inna ce tace tayi hakan oho, sai kusan magariba taro ya watse bayan anyi rabon manyan jakkuna masu d'auke da Al'quran ma daidaici sai sallaya da hijabi,nayi mamakin yaushe Inna ta shirya haka ko dan ban maida hankali ga bikin bane ban sani ba.

Basu bar ni nayi alwalan magriba sai da nayi wanka da ruwan turare sannan nayi alwala na fito nayi sallah ina kuka ganin cewa dai da gaske suke dan sai shirye-shiryen kai ni suke shirya ni sukayi cikin atampa super mai ratstsin silver a jiki , d'an kunne da sarka da suka saka min suma duk silver ne sannan suka nad'a min laffaya mai masifan kyau shima silver color aka fito dani wajan su Inna da yan uwan ta.

Nasiha suka fara min kan hakuri d'aya bayan d'aya Inna ta dai tana gefe tana kallon yanda nake kuka kaman raina ya fita, Maa ce ta katse ta tace itama tace wani abu mana.

Murmushi mai ciwo tayi muryar ta na rawa tace" me zancen Maa da ku baku fad'a ba, ni sai dai inyi mata addu'a Allah yaa...." Kukan da take rikewa ne ya kwace mata ta tashi cikin sauri tayi d'akin ta, kara kuka na nayi na mike zan bita suka rike ni ina musu magiya da roko amma basu saurare ni suka sada ni da d'akin Abba yana zaune shi kad'ai sai washe baki yake.

"Sai ku fita ku d'an bamu guri ni da 'yata ko" yace musu bayan sun zaunar dani a tsakiyar parlour shi, Aunty Batool har ta tsaya da nufin gasa mishi magana Aunty Fatima ta mata alama da ido da tayi shiru kawai su fita, ba dan ta so ba suka fita tana mitan wai dama ya san ni 'yar sace?

Suna fita ya juyo gaba daya gare ni yana kara washe baki yace " ke kuma in banda kuruciya menene abin kuka anan, Allah ya azurta ki da samun irin wannan mijin da babu kamar sa duk maiduguri yaushe kuka hadu dashi amma ga yanda ya sauya mana rayuwa baki d'ayan mu,

Wannan ai abin alfahari ne a gare mu ba ki saki baki kina kuka ba d'aurin auren ki har da gomna fa suka zo" ya karasa feeling very proud Yana gyara Zama.

"Abinda nake so dake shine kada kice zaki manta da gida dan kin samu daula ya kamata ki san yanda zaki rinka tatso wasu abubuwa daga gare shi kina aiko mana ai kin gane abinda nake nufi" ya karasa tare da zuba min ido gyad'a mishi kai nayi hawayen takaici na zubo min dan ni da yace su Aunty's dina su fita na zata zai min nasiya ko kuma ya rarrashe ni kan auren da ya d'aura min ashe shi tunanin shi daban, wai yaushe ne Baban mu zai canza?? Na jehowa kai na tambayan da babu mai bani amsa.

D'aga murya yayi ya kira su Aunty Fatima suka zo suka fita dani direct sai mota suka sakani suna ta zabga guda Aunty Fatima da Aunty Batool su suka sakani a tsakiya suna hirar su anan naji cewa wai Gwaggo Aisha da taji labarin taron d'aurin auren ta yanki jiki ta fad'i yanzu haka tana asbiti ba lafiya.

Har muka karasa gidan Zafar da ya amsa sunan shi gida ko ince Aljannar duniya dake can bolori lay out hawaye bai kara zubo min saboda mamakin halin Baban mu dana Gwaggo Aisha.

A maidaicin compound din gidan da fitilu da flowers suka ma ado drivern yayi parking ,Aunty Fatima dake zaune a gefe na dama ita ta fara fita sannan ta kama hannu na tace in fito da kafar dama, hakan kuwa nayi na fito kaina a kasa dan rabin fuskata a rufe yake tana rike da hannu na har entrance din parlour nan ma cewa tayi inyi Bismillah sannan in shiga da kafar dama.

Ni dai tafiya kawai nake ban san inda nake jefa kafa ta ba har naji mun shigo wani d'aki kuma naji an zaunar dani akan wani tattausan gado, sai a lokacin naji sabon kuka ya zo min na fara ina rike a jikin Aunty na, sauran yan rakiyan kuwa suka bazama duba gidan suna ta santi tare da yaba kayan d'aki da Inna ta min wanda ni ban san ma yaushe akayi su ba kasancewar naji Baba na cewa ba za'a min komai ba dan sun ce basa bukata komai daga gare mu.

Allah sarki Inna ta na san tayi hakan ne dan samo min martaba da Kuma daga gare su, bamu fi minti talatin da zuwa ba naga sun fara shirin tafiya dinner nima kara shirya ni sukayi cikin wani Indian material mai dan karan tsada da kyau, net suka saka min a tsakiyan kai suka kama da pin ana ganin kitson da aka min na gaba sai suka saka min sarkan kai wanda yazo min har goshi sarkan set ne da dan kunne da sarkan wuya da warwaro masu bada sauti mai dad'i.

Kamin su gama min duk sun tafi sai Maryam da wasu cousins dina 2 su suka tsaya Jira na da kuma Aunty Fatima har bakin wata arniyar mota da ko sunan ta ban sani ba suka rako ni tare da bud'e min kofa na shiga, ina jira inga ta shigo kaman dazu sai naga ta mayar da kofan ta rufe suka nufi wasu motoci guda 2 daya a gaban mu yake daya kuma a baya ya kasance sun saka mu a tsakiya.

Har motan ya fara tafiya naji motsi a gefe na a firgice na juya dan a zato na Ni kad'ai ce a cikin motan sai ganin mutum nayi a kishind'e kaman wani basarake yana latsa waya ko kallon inda nake baiyi ba, ni kuwa kasa d'auke ido nayi a kansa ganin sa cikin arniyar suit ko dan ban tab'a ganin ya saka bane sai naga ya masifan yi mishi kyau,

"Bana son kauyanci ki daina kallo na da wayan nan idanun naki" naji muryan shi ya katse ni.

Cike da jin haushin kaina na murkud'a mishi baki nace " da wani idon kasan ana kallon ka..." Ko rufe baki na banyi ba naji ya dalle min baki da yatsan shi a take naji hawaye sun cika min ido dan ba karya naji zafi sosai, a zuciya ta naja masa Allah ya isa cikin kwando na cigaba da murza lebe na can dai na kasa hakura dan abin na cizo na a rai ace kullum shi yake ha'in ta na ni bana ramawa.

Cike da tsiwa nima na bud'i baki zan rama naji mutumin da yake gaban motan yana ce mishi mun iso, bari yayiwa sauran magana su zo yace, kamin ma ya rufe baki su Sadeeq suka zagaye motan tare da bud'e mana, shi ya fara fitowa sannan ya zagaya ta bangare na ya kama hannu na ya fito dani yana wani murmushi kaman ba shine ya gama cin zalina yanzu ba.

"Come on wifey walk gently" yace min cikin wani murya da ban san shi da ita ba, a zuciya ta nace lalle wannan ya cika dan drama toh bai sani ba gidan ta yazo.

Cike da yanga da fari nima na amsa mishi da " yes husby".

A dan zabure ya juya ya kalle ni na second 5 ya d'auke kai yana murmushi, tafiya cikin hall din muka fara su Maryam suna watsa mana wasu abubuwa masu kyalli gefe daya kuma turaren wuta Hamra take bin mu da shi a baya.

Hannun mu sakale dana juna kaman masoyan gaske har muka karasa wajan zaman mu, tunda muka shigo mc ya saki wakan bikin da Ali jita ya rera mana mai taken Zareefa ta Zafar.

Sai da kowa ya zauna aka natsu sannan Mc ya fara gabatar da event cikin burgewa da wayewa, da aka nemi abokin ango ya bada tarihin ango Sadeeq ne ya fito ya bayar sannan Maryam ta bada nawa,daga nan aka bukaci mu fito mu yanka 🍰 kaman ince ba zan fito ba amma sanin duk abinda ya wakana anan zai je kunnen Inna yasa na fito muka tsaya a gaban tangamamen cake wanda ya kusan tsayin mu after d count of 3 muka yanka a tare, cikin wani salo ya gutsuro cake din ya saka min a baki da gangan na had'a da yatsun shi 2 na dalla mishi cizo wanda har ya saka shi saurin janye hannun shi yana yarfewa.

Dariya na tintsere dashi cikin tsananin farincikin nima na rama muguntan da yayi min, suma yan hall din dariya suke su a tunanin su wata salon soyayya ce haka.

Ina kallon shi sai harara ta yake ta kasan ido yana jiran in bashi shima ya rama bai san cewa na gama gano shi ba.

Maimakon in gutsuro cake din in bashi a baki sai lakato shi nayi a yatsana na shafa mishi a hanci nan ma dariyan yan hall din suka kwashe da shi ni kuwa ganin ya harzuka kaman ya shake ni yasa na juya da sauri zan bar wajan, har nayi step 2 naji anyi sama dani.

Tafi da ihu sosai ne ya cika hall din wanda ya ankarar da Zafar inda muke yayi saurin ajiye ni dan idon shi ya rufe burin shi ya min muguntan da nan gaba in muka had'a hanya da kaina zan gudu, lakace min hanci yayi yana yaken da yafi kuka ciwo, ni kuwa harda yi mishi gwalo muka koma wajan zaman mu raina fari tass yayin da shi kuma yake jin kaman ya had'iye zuciya ta mutu saboda haushi.

Ali jita shi ya baza basirar sa a wajan anyi rawa an cashe anyi barin nairori harda daloli , anci an sha sannan mun samu gift ba adadi zuwa 10 aka tashi kowa yayi inda ya fito, a mota daya muka dawo da kawaye na nayi musu karyan zai sallami abokan sa basu san guduwa nayi ba dan in na shiga mota daya dashi ban san kalan muguntan da zai min ba.

Muna zuwa gidan Aunty Batool ta had'a min ruwan turare ta sani a gaba nayi wanka ta shirya ni cikin wani dogon riga na material pink ta min light make-up ta zaunar da ni akan gado bayan ta min barin humra kala kala a jikina ta lulluba min katon gyale sannan ta zauna a gefe na ta kama hannu na duka 2 cikin nata tace;

"Toh Zareefa ni zan tafi sai gobe zamu dawo zan kara maimaita miki kiyi hakuri kiyi hakuri sannan...." Aunty dan Allah kadaki tafi ki bar ni mu kwana tare dan Allah Aunty" nace ina kokrin rushewa da sabon kuka.

"Kada ki kuskura hawayen nan su zubo shikenan naji zan kwana anan bari inje in rufo mana kofa sai mu kwanta ko" ta karasa cikin rarrashi.

Ajiyan zuciya mai nauyi na sauke ina gyad'a mata kai ta mike ta fita tare da bar min jakar ta a d'akin.

Toh fans yanzu aka fara wasan koyaya zaman ma'auratan nan zai kasance ??

Sai ku biyo ni a next page, sai kuna hakuri kwananan I'm so busy .
[6/16, 9:18 PM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*30&31*

Ina zaune da jakan Aunty sai baza ido nake in ga ta dawo amma shiru ko alaman motsi bana ji balle muryan mutum, gidan yayi wani irin shiru na ban mamaki, cike matsanacin tsoro da ya kamani lokaci guda na mike jiki na tsuma na nufi bakin kofa na bud'e na l'eko ina kyautata zaton parlour ne nan amma tashin hankali da nake ciki bai bar ni na tantance ba.

Muryata na rawa alaman kuka na iya kufce min a ko wani lokaci na bud'i baki na kwala mata, shiru kake ji babu wanda ya amsa ga dukkan yanayin gidan ma ni kad'ai ce a ciki, da gudu na koma d'akin da na fito na maida kofa na rufe harda murza key da na gani a jiki na haye gado da kayan jikina ko mayafi ban cire ba naja bargo na gudundune har Kai na saboda tsoro na fashe da kuka yanzu shikenan ya tabbata an min aure kuma da wannan mugun sannan gida d'aya zamu zauna, shikenan na shiga uku na sai yanda rayuwa tayi dani.

Tun ina kuka ina sake-sake har baccin wahala ya d'auke ni ba tare da na sani ba dama ga gajiyar biki ga rashin bacci su suka had'e min waje guda sai ajiyan zuciya nake a cikin baccin alamun na ci kuka na koshi.

Zafar kuwa tunda taro ya tashi duk hankalin sa yana kai na burin shi d'aya ne shine mu keben ce ya ci mutunci na sai zuba sauri yake mu shiga mota wani abokin shi da yazo bikin tun daga turkey ya tsaida shi yana mishi jawabin gobe jirgin karfe shida zasu bi su koma so ba lalle ne su had'u ba dan sun san a wannan lokaci yana can rungume da amarya ana shan soyayya, nan suka shiga yi mishi tsiya irin ta abokanen ango ya biye su ba dan yana so ba sai dan kawai kada su zargi wani abu yasa ya d'an b'ata lokaci har muka wuce bai sani ba.

Ya sha takaici kaman ba gobe da ya neme ni ya rasa, a bakin sauran mutane da basu gama wucewa yaji cewa mun wuce da 'yan uwana, minti biyu bai kara ba yace shima ya kamata ya tafi yayiwa wayan da zasu bi flight d'in safe Allah ya kiyaye hanya ya juya ko kula masu tsokanan shi wai zai gudu gida wajan amaryan shi,ko waiwayowa bai yi ba balle ya tanka shi dai burin shi ya same ni a wannan gida da babu kowa ya rama abinda nayi mishi.

Da kyar ya yarda Sadiq da wani abokin su mai suna Shu'aib suka mishi rakiya, a cikin motan ma bai tsira ba Shu'aib sai takalan sa yake Sadeeq na musu dariya.

A suya spot dake baga road Sadeeq ya tsaya ya saya musu manyan kaji 2 da drinks suka kama hanya, shi dai Zafar sai tab'e baki yake yana mamakin Sadeeq daya dage har da sayan kajin Amarci ko uban wa yace mishi wani abu zai shiga tsakin mu oho.

A bakin gate ya sauka yace musu ya gode ba sai sun bishi ciki ba

"Dama ni na san ksud'in banza ake mana gashi dai idon mu ya gane mana" cewar Sadeeq kenan yana bud'e murya dan Zafar da ya kusa shiga ciki yaji hannun sa d'auke da ledodin da sukayi shopping d'in.

Mai gadi na zaune har ya fara gyanyadi yaji tura karamin kofa na jikin gate d'in, cikin sauri ya mike yana yi mishi barka da zuwa.

Tsayawa yayi suka gaisa cikin mutunci sannan ya wuce ciki shi kuma ya kulle gate d'in tare da shigewa makwancin sa, murya can ciki yayi sallama ya shigo parlour ba shiri ya lumshe ido yana shakan daddadan kamshin turaren wuta da Aunty ta saka kamin ta tafi, ya kai good 5 seconds yana shakan kamshin sannan ya bud'e ido yana bin ko ina da kallo yanda aka jera komai cikin tsari gwanin burgewa.

Tab'e baki yayi ya kama tafiya ciki yana da shi Abba ya bawa kud'in nan yaki ya bada order furnitures masu tsadan nan dan da farko shi aka ce ya zab'a min da gangan ya zab'i wasu bakake wai tunda painting gidan masu haske ne wayan nan sune zasu haska.

Abba bai kara kula shi ba ya zab'o wayan nan da aka jera a parlorn, Kai tsaye inda ya san nan ne b'angare na ya nufa ya bud'e kofa kamshi days tarar a nan yafi na farkon, madaidaicin parlour nawa yabi da ido yanda komai aka shirya shi cikin kwarewa da wayewa babu tarkace dayawa amma komai ka gani a ciki classic nd expensive ne.

Sosai parlour ya tafi da imanin shi yana tunanin yaushe Abba ya sayo wayan nan dan shi dai a gaban shi akayi ordern komai, toh meye ma damuwar shi da zai damu kqn shi sai ya san ta ina suka zo kayan.

Cikin sauri ya karasa kofar bedroom da nake ciki ya murd'a handle d'in yaji ta a garkame gam kara murd'awa yayi yana jijjiga kofar wai ko zan zo in bud'e ni kuwa Ina can ina ta sharar bacci na ban san ma yana yi ba.

Tsaki yayi tayi yana cizon yatsa da takaicin kulle kofa da nayi,nan da nan wani tunani ya fad'o mishi ai ba za'a rasa spare keys na ko wani kofa ba, cikin sauri ya juya da nufin zuwa d'akin shi ya duba har yayi steps 2 zuwa 3 ya tsaya cak sakamakon wani abu daya fad'o mishi a rai.

Kar dai ace na rufe d'aki nane saboda ina tunain zai shigo min as ango??

Hmmm inko haka ne ba zai bud'e ba balle in saka ran cewa wani abu ya kawo shi, God forbid ba zai tab'a abinda wannan kucakar zata raina shi ba, dangwaran da ledan hannun shi yayi a bakin kofan ya juya ya nufi nashi d'akin .

Tun a parlour shi ya fara kunce necktie dake wuyan shi da maballan suit din shi a haka ya karasa cikin bedroom ya gama cire kayan ya shiga bathroom, wanka yayi da expensive liquid soaps da kamshin su ya cika gidan gaba d'aya bai dad'e ba ya fito sama-sama ya shafa d'an 🧴 a jikin shi ya saka white pyjamas d'in shi masu taushin gaske ya bi lafiyar gado.

Tsaki yaja shi kad'ai yana kara Jan bargo ya lullub'e jikin shi da kyau yana mai jin haushin kan shi na kawo irin wannan tunanin a ran shi,wai da auren gaske yayi da yana can tare da amaryan shi " Allah ya sauwake 'yar Mallam ce fa Kuma ka aure ta ne dan gujewa Abba ko ba haka ba?" Ya tambayi kan shi yana lumshe ido saboda ya fara jin bacci " Anya zan iya bari tayi min wata 2 a gida? she have to leave within a month kamin nan na samu d love of my life".

Tun yana suratai wa kan shi har bacci mai dad'i yayi awon gaba dashi.

Hankali kwance na sha bacci na ban tashi ba har sai da naji ana kiraye-kirayen sallah duk da naji na kwanta shiru ina jiran inji Inna ta leko ta tashe ni amma shiru, ganin kila zamu makara yasa na tashi a raina ina mamakin lafiya kuwa yau Inna bata tashi ba.

Da Addu'an tashi daga bacci na tashi zaune ina murza ido, a firgice na mike tsaye ganin Ashe ba a d'aki na da na sani na kwana ba domin Ina kallon komai tar dan ban kashe wutan d'akin ba na kwanta haka saboda tsoro.

A hankali na fara bin d'akin da akace nawa ne da kallo tare da mamakin irin dukiyar da aka narkar a ciki, ba komai ya saka ni mamaki ba sai dan jiya naji suna ambatar cewa Inna ce tayi min kayan d'aki.

Kara kallon wannan Royal set maroon da sirkin baki nayi sai sheki suke kaman an shafa musu mai ko kuma ince kaman da glass akayi su yanda suke walwali da d'aukan ido, ko turaren wuta,humra,kulacham da sauran su da aka jera min a cikin tangamemen show glass abin kallo ne dan kwalaben kad'ai sunyi jarin wani.

Jiki a mace naja kafafu na cikin bathroom nan d'in ma tsayawa nayi ina kare mishi kallo yanda komai na ciki fari ne kal kuma duk na zamani da kyar na gane wasu abubuwan na had'a ruwan zafi nayi wanka dan jiya tsoro ya hana ni yi, alwala ta na d'auro bayan na gama wankan na fito.

Aunty Fatima duk ta nuna min yanda suka ajiye min kaya na duk da ba'a kawo min lefen ba na gidan mu ne da Inna tayi min, wata atamfa doguwar riga na saka wanda ya sha dinki mai kyau kuma cif na cika shi, abin sallah na shimfid'a na saka hijabi na kabbara sallah.

Ban tashi a kan abin sallah ba sai kusan 6:40 domin sai da nayi azkar na safe na d'an yi karatun Qur'an sannan na mike na cire hijab na ninke su da sallaya na ajiye gefe, shafa shaffafen tommy na da yake kaman babu hanji nayi jin yana kukan yunwa dan ni kaina na manta yaushe rabo na da abinci, da fa auren gaske nayi ko kuma da Yaya na na aura I know he will pampered me yana rarrashi yana bani a baki ba zai tab'a bari in kwanta da yunwa ba, but dubi wannan mugun ko irin Kazan amarci da naji ana bada labari bai kawo ba.

A take Kuma wani sashin zuciya ta ya kwab'e ni da cewa ta ina zan sammaci wani kazan amarci daga gare shi bayan ya jadda min dalilin aure na da yayi kuma baya gajiya da nanata min ba so na yake ba.

"Hmmm" kawai nace a raina tare da niyyan neman abinda zan ci, kaman mai tsoron kada wani abu ya kamata na bud'e kofa na leka naga wata fitinanniyar parlour na da ya kusan saka numfashi na barin jikina.

"Masha Allah " nake ta maimaitawa da jinjinawa Inna, yanda parlour nan ya tsaru koma wanene kai dole ne ya burge ka ba'a cika mashi tarkace dayawa ba but yanda aka jera komai a position din shi sai ya fito da kyan parlorn cushions labulaye duk kalan su daya wato peach nd milk color ne sai tangamemen plasma da sauran abubuwan kallo suma wajan su d'aya, abinda da yafi birge ni wasu manyan flower vase da aka ajiye a kowani angle shima ya bada ma'ana.

Tafiya na farayi zuciya ta na dukan 3-3 dan ina tsoron had'uwa da wannan dodon, ina bud'e kofa wani parlour na kara gani har yafi nawa komai I mean girma da dukiya da aka zuba a ciki baya lissafuwa shi kuma nan komai na cikin sa brown nd white ne.

Nan ma da naga kallon ba zai fishe ni ba na fara duba kofofi da na gani a cikin parlour dan neman kitchen na san anyi min gara ba na wasa ba so ko indomie ne in samu in dafa in sakawa cikin nan nawa da nake ji sai kara ya mutsewa yake.

Babu tunanin komai kai tsaye na nufi wata kofa da hankali na ya kwanta dashi na bud'e, wani sanyi da wannan sassayan kamshin sa suka min maraba da sauri na waro ido ganin inda na kawo kaina, a can tsakiyan tanfatsetsen gadon shi na hango shi kwance yana baccin sa cikin kwanciyar hankali dan bai san ma na shigo ba a hankali na mayar da kofan na rufe kaman yanda na samu na juya cikin sauri na koma inda na fito domin har naji na daina jin yunwan.

In ba dan Allah ya taimake ni yana bacci ba wani bayani zanyi mishi na kare kaina, da shikenan sai yace biyo shi nayi.

Ido na rufe sai sauri nake buri na in shige d'aki na naji nayi tuntube da abu a gefen kofata, tsayawa nayi Ina kallo tambarin jikin ledan ba sai an fad'a min ba na gane kajin amarcin ya kawo min amma banida darajan da za'a miko min hannu da hannu shine ya dangwarar min ita anan?

A zuciye nayi ciki tare da banko kofa Ina huci ni kad'ai lalle ya cika d'an rainin hankali, nima ban d'auka kaman yanda ya ajiye abin shi haka zai dawo ya d'auka sai dai yunwar ta kashe ni.

Na kusan minti 30 zaune sai tsaki nake ta jerawa saboda takaicin da ciki na ke bani na kasa hakurin yunwan ni kuwa nace sai dai in mutu ban cin kazar da aka dangwar min.

Jiki na rawa ya fara na kai last stage da ba zan iya jurewa ba kuma,tashi na kara yi ina tafiya da kyar tare da addu'an Allah yasa bai fito ya d'auke ba dan na lura in na zauna yunwar ta kashe ni ba matsalar shi bace Inna ta akayiwa asara.

Ina bud'ewa kuwa naga tana nan ajiye kaman yanda na barta, wawurar ta nayi na koma ciki da sauri bayan na maida kofa na rufe, ban iya karasawa cikin bedroom din ba a nan parlorn na zauna jiki na rawa na dauki goran yogurt na kafa kai ban sauke ba sai da na shanye tas sannan na ajiye roban Ina ajiyan zuciya.

Kullin kajin na warware shima na fara ci hannu baka hannu kwarya, ban sarara ba sai da naji nayi kat sannan na ture su gefe na jingina da jikin kujera sai sakin ajiyan zuciya nake amma kuma can kasan zuciya ta kuma haushin kaina nake ji da na kasa hakuri na ci wannan kayan shikenan ya samu hanyan cewa ni kwad'ayayyiya ce na san kad'an daga cikin halin sa kenan.

Tashi nayi na tattara su na kai su cikin frdge da na gani cikin parlour na saka duk wai dan Kar ya shigo ya gani na ci, hmmm in banda abu na a Ina ma zai ganni ai duk hanyan da zan kaucewa had'uwa ta da shi zanyi har lokaci da ya d'iba yayi ya sallame ni in kama gaba na.

Da wannan kwarin guiwan na shiga bathroom na wanko hannyaye na yafa veil karami a kaina na fito parlour na zauna akan sofa tare da cigaba da nazarin rayuwata tun daga kuruciya zuwa yau.

Tun yanzu na kogu lokacin da ya d'iba yayi ya sallame ni makaranta zan shiga abuna inyi karatu mai zurfi in cika buri na, na zamewa Inna farinciki kuma abin alfahari.

Ban san lokaci ya tafi sosai ba nayi zurfi cikin tunani naji muryan mace na sallama.

Firgigit na dawo hayyaci na tare da tashi zaune na amsa sallaman tare da aro 'yar fara'a na yafawa fuska ta Ina kallon kyakkyawan yarinya da ba zata wuce age mate na ba hannun ta rike da wani hadadden basket mai dan girma da warmers masu kyau a ciki, nuni nayi mata da wajan zama nace ta zauna.

Ba musu ta zauna ta fara gaishe ni jin abun nayi bambara kwai wai ni za'a gaisar, amsawa nayi Ina tambayan ta mutanen gida tace min suna lafiya.

Miko min basket din hannun ta tayi tare da cewa " suna na Yasmin ni cousin sister ce ga Ya Zafar, mama na da Abban shi 'yan d'aki d'aya ne yanzu ma ita tace in kawo muku wannan breakfast din sannan akwai sakon da tace a bashi".

D'an murmushi nayi nace " Allah sarki yayi kyau".

D'aukan basket nayi na kai kan dinning table na jajjera warmers din na dawo na zauna kusa da ita da ko motsawa bata yi ba a inda na bar ta ba, I'm feeling nervous dan ban san wani irin hira zamuyi ba.

"Pls kiyi mishi magana zan tafi dan ance kada in dad'e" naji muryan ta ya katse ni.

"Toh" kawai na iya ce mata na mike Ina d'aga kafa da kyar zuciya ta kuwa kaman ya fasa kirjina ya fito, me zan ce mishi tayaya ma zan iya shiga d'akin wannan masifaffen?.

Na fi minti biyar tsaye a bakin kofan amma na rasa tayaya zanyi sallama ko kwankwasawa ba mamaki ma in ya ganni kofan d'akin shi yayi min wata fassarar, ganin babu sarki sai Allah yasa na daure na kwankwasa kofan amma a hankali kaman mai tsoron kada a jita.

Nayi knocking kusan sau 3 amma banji alamun motsin mutum ba, hakan yasa na bud'e a hankali na leka naga babu kowa sai sanyin ac daya had'u da kamshin sa ya bada wani yanayi mai ni'imar gaske, lumshe ido na nayi Ina kara bud'e kofofin hanci na Ina shakan kamshin naji bud'e kofa wanda ya haddasa min bud'e ido ba shiri.

Shine ya fito daga bathoom d'in shi daure da towel alamun daga wanka yake ya rike waya da hannu daya d'ayan kuma rike da karamin towel yana goge kirjin shi da ya wadatu da yalwataccen gashi mai taushi da d'aukan ido.

Zafar da sai yanzu ya lura da mutum a d'akin shi ya bini da kallon mamaki yana watsa min harara , ganin nayi nisa hankali na baya tare da shi ,tsawa ya daka min yana tambaya ta uban me na shigo yi a d'akin shi? .

A zabure na d'auke ido na akan shi tare da sauke kaina kasa ina mai jin haushin Kai na, how comes har nayi haka na tambayi kaina, shikenan ya gama raina ni na gama zubar da aji na a gaban shi dama ba wani girma na yake gani ba.

Ban iya yi mishi magana ba Kuma na kasa juyawa in koma inda na fito, kaman daga sama naji hannun shi mai d'an danshi ruwa akan hannu na, cikin kid'ima na d'aga kai na ina kallon shi da idanuwa na da suka fiffito kaman zasu fad'o kasa.

Murmushin gefen baki ya min yana kashe min ido daya yace " irin wannan kallon haka 'yar Mallam kaman zaki cinye ni , wato kin ga well builded body ko baki san cewa kwalele kike kallo ba"

"But let me help you ki d'an rage zafi na San abinda ya shigo dake kenan" yana gama fad'an haka naji ya d'aura hannu na kan lallausan gashin kirjin shi yana bina da naughty look harda karkata kai gefe d'aya.

Yanda kika san an d'aura min hannu kan wayan wuta tsirara haka naji wani irin shocking tun daga tsakiyar kai na zuwa tafin kafa ta, ba shiri na janye hannu na da karfin gaske jiki na rawa na fice a d'akin da gudu Ina jin dariyan mugunta da yake min.
[6/16, 9:18 PM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*32&33*

Zama nayi a inda na tashi ina daidaita natsuwata tare da kakolo murmushi dole na yabawa fuskata amma kuma sai na gaza furta mata komai,toh mema zance mata dan haka shiru nayi na cigaba da wasa 'yan yatsun hannuna.

" Yana zuwa ne?naji muryar ta ya katse mana zaman kurame da muke duk da ita naga alamun irin mai surutu ce sai dai rashin samun fuskata yasa tayi shiru itama".

"Eh......yana....yana shiryawa ne?na amsa mata a rarrabe.

Shi kuma ina barin d'akin shi sai da yaci dariya ya more sannan ya juya ya cigaba da shirin shi yana aiyana yanda zaiyi magani na inji tsoron shi sosai dan jiya a wajan dinner nan yaga rashin tsoro a idona.

Munfi minti 20 a zaune da yasmeen shiru sai dai itace mai kokarin kawo hira wanda ni amsa ta baya wuce ehh ko a'a.

Cikin wata maroon danyan shadda ya fito hatta da hular kan shi maroon ce kayan san matukar fito da shi ya haska farar fatan sa yana gyara agogo hannun sa ya fito bai ko kalli inda muke ba yayi hanyan fita koda yake na lura bai san muna parlour ba, yasmeen ce tayi saurin dakatar da shi ta hanyan gaishe shi.

Fara'a kwance saman fuskan shi ya dawo baya tare da amsawa a yana tambayan ta ya Baawa take?.

"Tana lafiya ita ta aiko ni in kawo muku breakfast kuma tace in fad'a maka tana son ganin ka a gidan mu yau d'in nan kuma da wuri".

"Allah sarki Ba'awa muna godiya baby ki tayani godiya mana" yace yana min wani kallo da yasa naji zuciya ta harba da karfin gaske cikin in ina na amsa da "ai tun dazu nayi sai dai in kara".

"Toh ni zan tafi sai ka shigo,amaryan yayan mu na tafi sai na juyo" tace tana mikewa da fuskar ta cike da fara'a ,mik'ewa nima nayi Ina amsa mata na biyo su da niyyan d'an taka mata nace " toh sai na ganta ta gaida mutanen gida,muna cikin magana da ita naji kaman daga sama anyi kissing d'in goshina,ba shiri na tsaya cak na kasa d'aga kafa balle inci faba da tafiyan saboda wani irin kasala daya sauko min lokaci d'aya na juya ina kallon shi cikin tsananin mamaki.

"Babyna sai na dawo ki kulan mun da kan ki kinji?"yana magana ne yana satan kallon yasmeen ta gefen ido yaga ta d'auke kai tana murmushi kasa-kasa,shima murmushin yayi, yayi gaba abin shi ko ba komai ya cire mata tantama daya gani d'azu shimfid'e a fuskar ta ko dan yanayin da da taga yazo fita bai nema ni bane oho.

Har suka fita ina nan tsaye kaman an dasa ni,da kyar na koma kan kujera na zauna ina kara mamakin halaiyan wannan mutumin mai halin hawainiya yana iya canzawa a duk lokacin da yayi niyya.

Misalin eleven kawaye na da sauran 'yan uwa suka fara zuwa nan da nan gidan ya cika da hayaniya 'yan mata baka jin na wani,nima ganin su yasa na wassake tare da rage damuwa mukayi ta hiran mu.

A can gidan mu kuwa da gaske Gwaggo Aisha ta kwana a asibiti amma da sauki ta tashi sai dai jin labarin irin gidan da aka kai ni da kuma labarin lefe na da Hajara ta kai mata ya kara birkita yanayin ta mata da suka zo da washe gari saboda yini yawancin sunje duba jikin nata dan babu wanda yasan takamaiman dalilin ciwon nata.

A gidan mu aka kawo mana abincin rana da akayi na yini kuma aka kai gidan su Zafar kaman yanda al'adar Maiduguri yake,daga baya kuma su aunties na da sauran jama'a sukayi ta zuwa ganin gida suna saka albarka,sai yamma likis suka fara watsewa.

Bayan magariba gidan yayi tsit duk sun watse sai na jiki da suka tsaya dan kimtsa gidan, bayan sun gama da gidan nima shirya ni sukayi cikin wani haddaden less pink mai adon stones sannan suma sukayi haraman tafiya,sabon babu kuka na bud'e inayi musu magiya ko mutum d'aya ne ya tsaya tare da ni mu kwana.

Dabara suka min suka tafi suka bar ni kaman wata mayya,tsoro duk ya cika ni na rasa me yake min dad'i komawa d'aki nayi na murza key kaman jiya nayi kwanciya ta nayi shiru ina jin matsaneciyar kewar Inna ta ji nake kaman na kai shekara ban saka ta a idona ba,wani b'angare na zuciya ta yana raya min in tashi in gudu in bar gidan in koma gidan mu.

Wasi- wasin da yayin yawa yasa na d'auko wayata da su Maryam suka zo min da shi na fara kallon pics da videos na biki da suka turo min, ai kuwa duk sai ya d'auke min hankali na shagala nayi ina ta kallo ina murmushi wani wajan inyi dariya saboda babu wanda zai kalle mu ba zaice masoyan gaske bane,tun ina kallo har bacci yayi gaba da ni ban sani ba.

Zafar bai dawo gidan ba sai past eleven saboda wai baya son ya shigo da wuri mu had'u dan ya lura da cewa kai na yana hayaki so gwara ya rabu da ni in lokacin da ya d'iba yayi mu rabu.

Kwana na 3 a wannan gida ban kara saka shi a ido ba in fact bana jin motsin mutum ma ni kad'ai nake rayuwa ta, tun ina d'ari-da'ri har na saki jikina ina sha'ani na,bana fitowa babban parlour a cikin b'angare na nake rayuwa ta bana fita ko Ina babu ruwa na da ya gidan yake yana bukatan shara ko goge-goge.

Yau da rana ina kwance a parlour na ina kallo naji ina kwad'ayin cin wani abu daffafe dan tunda aka yi yini rabon da inci abinci sai snacks da aka yi min nake ci in hada tea in sha ko in kora da juice.

Tight legins ne a jikina da rigan shi har iya guiwa amma bashi da hannu,rigan yellow ne da adon baki a jikin sai wandon shima baki ne ribbon yellow nayi amfani dashi na tufke gashina da ya zubo min har baya.

Ina sauraron favorite track a waya na , yanzu da nayi shirin shiga kitchen sai na saka earpiece a kunne na na fito abina ina mai bin wakan ina d'an rausayawa .

A wannan lokaci Zafar na zaune a parlour Abba ya bashi wani aiki yana taya shi yi a cewar sa ya fara da kad'an kad'an a gidan kamin ya fara fita office completely.

Ni kuma ban san da wani a cikin parlour ba na fito abina ina rausayawa nayi hanyan kitchen,da ido ya bini har na kulle zuciyar shi na ingiza shi cewar lalle wuyana ya isa yanka in shigo in same shi a zaune amma ko arzikin kallo bai samu ba balle in gaishe shi,ya lura kyale nin nan da yayi ya kara fand'arar dani dubi parlourn nan kaman ba mutum a cikin gidan.

A fusace ya mike yabi bayana zuwa cikin kitchen d'in ya same ni ina wanke set d'in tukane dana fito dasu zanyi amfani dasu.

"Keh" yace a d'an tsawa ce amma da yake earpiece ne a kunne na ban ji komai ba saima kara bin wakan nake ina rausayawa shi kuma ya zata duk salon raini ne wannan yasa bai tsaya tunanin komai ya shigo a fusace ya janyo ni ta baya.

Ni kuma da ban san da mutum a gidan ba balle in san da shigowar shi yasa na firgita sosai na rufe ido na na fara ihu iya karfina ina jero duk addu'a da yazo bakina "keep ur mouth shout my friend"naji muryan shi yana daka min tsawa da karfin gaske da yake earpiece din ya fita a kunne tar naji muryan nashi,a take na waro ido na waje ina kallon shi da fuska ta duk hawaye.

"Stop staring at me,da idon ki kaman na mayya.wato ke wuyan ki yayi kwarin har zaki taka ki wuce ni ba tare da kin gaishe ni ba"da sauri na girgiza kai na hawaye na zab'o min,sannan ya kara da cewa"and look at this house for god sake ace wai da mace a ciki ko'ina dirt ko kina jira inzo in share miki ne?"nan ma cikin sauri na girgiza kai na.

Kasa nayi da kai na tare da dana sanin fitowa da nayi da ban fito ba da ban hadu da wannan mugun ba.

"Baki iya gaisun ba ko?" Naji muryan shi cikin kunne na, murya ta na rawa na gai da shi ba tare da na dago Kai na ba.

Maimakon ya amsa sai yace " haka ake gaida na gaba, ina tsaye kina tsaye common kneel down and greet my friend".

Kuka na Kara fashewa da shi na takaici na durkusa nace " Ina kwana" still bai amsa min ba ya gyara tsayuwar shi da kyau yana wannan murmushin sa da na tsana dan duk lokacin da yayi shi babu alkhairi sai zallar mugunta.

"Zan kindaya miki sharud'a wanda dole ne ki bisu kamin lokacin ki yayi in sallame ki, na farko ya zama miki dole ko wani wani safiya kizo ki gaida ni, na 2 kuma kada ki kuskura ki bar gidan nan da datti dole ne ki rinka sharewa kina mopping din ko ina nd last thing kina girki kuma duk abinda na lissafo su make sure kinyi su before 8 am in ko kika tsab'a ko daya daga cikin su hmmmm" yace yana taune leb'en shi na kasa.

Ban iya bashi amsan komai ba kaina dai yana kasa har yanzu hawaye basu dai na zubo min, murmushi yake ran shi fari kal yana jin wani irin nishad'i ganin ina hawaye duk ya wanke mishi takaicin sa na daren dinner.

"Tashi ki gyara gidan yanzu ki tabbatar kin share kinyi mopping na ko ina kuma in har kikayi su any how zaki Kara repeating ne so its left for u" yana gama fad'a yayi gaba yana dariya cikin ranshi tare da kisisima yanda zai ci uba na cikin ruwan sanyi.

Tashi nayi daga tsugunen dana gaji da yin ta dan kasa tashi nayi daga farko ina tunanin ta ina zan fara, ganin dai babu mafita yasa na fito da vacuum cleaner da na gani a cikin kwalin sa na daidaita shi na fito dashi parlour dan in jona in fara sharan kaman yanda ya umarta.

Tun kamin in karasa wajan socket din ya daga min tsawa daya firgita ni na tsaya sororo Ina kallon shi " samun waje kenan wato baki da hannu kenan ko a gidan ku da wannan kike shara ?" Ya fad'a yana nuna min vacuum din da hannu.

Shiru nayi ban amsa ba kuma ban juya ba sai zuciya ta dake min zafi wai a gidan mu dashi nake amfani?

"Ki maida shi ki d'auko tsintiya ki share dashi right now" kala ban ce mishi ba na juya zuwa kitchen din na ajiye shi na d'auko tsintiya na fito na fara sharan bana ko kallon inda yake.

Ajiye pen din hannun shi yayi ya kwanta yana kallo na yana Kara jin nishad'i gani na cikin hawaye, da gangan ya kirkiro atishawa yayi kusan guda 3 sannan yace wai da gangan nake sharo mishi da kura har ya saka shi yin atishawa.

"Kina sharewa a hankali in kika sa na kara yi zan nuna miki true colour na" kaman in kurma ihu nake ji saboda takaici wani kura ne a parlour nan da za'a ce har ya saka mutum atishawa kawai dai salon wulakancin sa ne wannan na sani.

Ban kula shi na gama sharan ko Ina da mopping duk yana zaune ko motsawa baiyi ba, baya na duk ciwo yake min da yake ban saba aiki haka ba har zan wuce d'aki yace in dawo in d'aura girkin yanzu.

Cikin gunguni na wuce kitchen ina shiga na fara ja mishi Allah ya isa " wannan ai zallinci ne haka kawai ya sani sharan da tunda aka haife ni ban tab'a yin irin shi ba tunda gidan mu dai kowa b'angare shi yake sharewa amma dan mugunta yasa inyi wannan uban aikin, dani yake wallahi sai na rama" duk ni kad'ai nake ta masifa ta ina fere dankalin turawa dana gani an zuba su a cikin store.

Patatos omllet nayi na zubo mishi a plate na d'aura a kan tray na plastic mai dan Karan kyau na saka mishi spoon na fito dashi zuwa inda yake zaune kaman wani sarki na duka har kasa na ajiye mishi, wani abin takaici da wannan bawan Allah ya min yanda kika san kashi na ajiye mishi haka ya tsaya kallon abincin.

A kyamace ya d'auki spoon din ya sakuro kaman mai tsakuran kashi ya kai bakin shi, dama ina kallon shi ta gefen ido saboda inga wani reaction zaiyi domin na san karyan mutum ya kushe girki na koda banyi catering school ba Inna ta ba baya bace wajan girki, alaman mamaki na gani karara akan fuskar shi lokacin da abincin ya shiga bakin shi amma tsaban iyayi furzar da abincin yayi yana yamutsa fuska yace " meye wannan, tambayan ki nake meye wannan is this what u called food , muguwa wato so kike inci in mutu Allah kad'ai ya san abinda kika zuba a cik tsaban muguntai, common kwashe kayan ki nd leave my sight"

Duk a masifance yake min maganan , rai na kara baki yayi na rasa me zancen ko inyi mishi da zan huce nayi, kawai tattara kayana nayi na koma kitchen ban kula shi ba.

"What a mess" ina cikin had'a nawa abincin naji ihun shi daya kara firgita ni kamin in san me yake faruwa na gan shi a fusace a bakin kofan yace;

" lalle kin cika Yar rainin hankali ki gyara ko ina amma ki kasa gyara min d'aki?" Ya karasa yana zubo min ido tare da tare kofan kitchen din.

"Baka ce min harda d'akin ka ba shiyasa ban shiga ba".

"Oh sai na gaya miki sannan zaki gyara ko d'akin nawa ba acikin gidan yake ba?" Kamin in samu amsan bashi ya cigaba "wuce ki gyara min yanzu plus my bathroom"

Rufe plate din nayi nazo zan wuce na zata zai bar min kofan in fita ne sai naga matsawa kad'an yayi yace in wuce,ban san lokacin da na daga kai na kalle shi ba naga ya wqni kankantar da Lulu eyes din shi yana kallo na.

" Toh... Z...an ...wuce" nace mishi murya ta na rawa.

Na hana ki wucewa ne?" Ya tambaya Yana kara gyara tsayuwar shi, girgiza kai na kawai nayi ina maida shi kasa, da hannu ya min alama da inzo in wuce.

Tafiya na fara yi kaman wacce take tsoron taka kqsa ba dan komai ba sai dan sanin in zan wuce sai jikina ya gogi nashi, karkata jiki na nayi sosai yanda ba zai hadu da nashi ba, na ko yi sa'a dan ko bai hadun ba har na kusa fita naga ya saka hannuwan shi duka 2 ya tare kofan ya zama banida daman fita Kuma banida daman komawa ciki.

"Ni kike guduwa da wani kazamin jikin ki, ni banyi kyaman zaki had'a jikina da naki ba sai kece zakiyi?" Jikin na karkarwa kawai yake tsaban tsoro ban tab'a samun kusanci da d'a namiji kaman haka ba sai yau so ban san ya zan kwatanta muku halin da na shiga ba a wannan likacin.

Sai da yaga ya gama tsoratani sannan ya bani hanya, haba kaman in kifa haka na fara sauri na shiga d'akin na maida kofa na rufe na jingina a jikin kofan ina maida numfashi, sai da na dawo hayyaci na sannan na tsaya kallon d'akin ko ina fes yake a gyara kaman d'akin mace sai kamshi ke tashi, ajiyar zuciya nayi na wuce bathroom din shima dai fes yake.

Haka dai na had'a ruwan omo da hypo na goge ko ina na bayin nan ya kara kyalli da walwali, sai da na tabbatar komai yayi na bude kofa na fito.

A razane na koma baya ganin shi tsaye a bakin kofan daga shi sai dogon wando ya cire rigan jikin shi, rab'awa nayi na wuce shi Kuma ya shigah har zai rufe kofa naji shi yana cewa in tabbatar na gama gyaran d'akin ya fito.

Da toh na amsa mishi yana shiga na fara gyara mishi gado da jera pillows sannan na fara mopping din d'akin inda babu carpet, har na gama zan fita wata zuciyar ta zuga ni da yanzu shikenan ba abinda zanyi in rama yaci bulus kenan??

Bakin kofan bathroom din na dawo hankali na zubar da ruwan omo kad'an yanda ba zai iya ganewa ba na fita da sauri ina addu'an Allah yasa ya taka wajan da na huta takaici da ya guma min yau.

Jikin kofan na d'aura kunne na na tsaya jiran fitowan shi, aiko ban dad'e da tsayuwa ba naji karan fad'uwa muryan shi da karfi yace " ouch my back" haba da gudu na koma daki Ina dariyan mugunta raina fari kal.
[6/16, 9:19 PM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*35&36*

Zaune take kan sallaya da carbi a hannunta tana ja a hankali tare da kurawa waje d'aya ido,kallo d'aya zaka mata ka gane tana cikin damuwa kullum cikin wannan yanayi take tunda aka fitar dani daga gidan sai dai in damuwar yayi mata yawa,sai tayi nafila tana kai kukanta wajan mai kowa mai komai kan Allah ya bamu zaman lafiya mai d'aurewa.

'Yan biki duk sun watse tun ranan yini saboda an riga da an daina zaman bakwai sai dai gobe ne satin auran kuma a goben uwa take zuwa ganin d'akin 'yar ta amma ita tana ganin ba zata je ba hakan zai fi mata kwanciya hankali bata son taje ta ganni cikin wani yanayi ko kuma cikin tashin hankali hakan zai tsaya mata a rai ya hana ta sukuni, ta yanke shawaran zamanta a gida ta bini da addu'oi samun zaman lafiya.

Tana cikin zancen zuci baba yayi sallama ya shigo,sallamar nashi ne ya katse ta ta juyo tana kallon shi tare da amsawa a hankali tana bin shi da kallo yanda ya sauya zaka ce wani hamshakin mai kud'i ne,duk mamaki ya cika ta dan zata iya cewa tunda bikin nan yazo sai yau ta saka shi a ido saboda taga bashi da niyyan yin komai ya zauna akan abinda Abban Zafar yace na cewa kada suyi min komai su zasu yin min.

A lokacin ta nemi su zauna suyi magana ta fahimta bai kamata su sake musu komai ba kaman wacce bata da gata koda kayan d'aki daya ne ya kamata suyi min gudun gori watarana amma yaki sauraronta sam,wai tunda sunce abari a bari kawai itama tunda ta lura da takun shi ta fita harkan shi tayi duk abinda Allah ya hore mata dana 'yan uwa da abokan arziki cikin ikon Allah kuma asiri ya rufu.

Zama yayi a kan kujera ya d'auki remote ya kara volume na TV data rage,kaman ta share shi sai kuma taga koma yaya ne shine gaba da ita,tashi tayi ta kowa mishi ruwan sanyi da snacks na biki ta ajiye a gaban shi ta gaida shi tana zama a gefen shi.

Amsawa yayi sannan ya d'an sha ruwan da ta kawo mishi yana kare mata kallo yana murmushi yace"kinga yanda kika dawo kaman kece Amaryar gaya min menene sirrin?" murmushi kad'an tayi bata ce komai ba wai yau ita yake fad'awa haka ya manta duk munanan kalamai da yake furta mata da kuma aurar dani ga wanda ba son sa nake ba..........

"Tunanin 'yar albarka kike ne ,nima nan kullum sai nayi tunanin ta a raina toh ya za'ayi dole ne kiyi hakuri kuma kiyi murna tunda tana gidan hutu" yace yana gyara zama

"Yauwa ni abinda ya kawo ni daban, kin gan ni nan wallahi bikin nan ya cinye min duka kud'ad'en hannu na shine nace bari inzo ki bani wani abu na san 'yar ki na aiko miki tunda maganan da nayi ta jaddada mata kenan daren da za'a Kai ta gidan ta cewa kada ta kuskura ta zauna shiru duk dabarun da zatayi tayi ta rinka turo mana gida mu rinka shan maikon tare, in ma bata turo ba na san tana kan tarawa ne kema na san ki adana balle kuma kin samu makudan kud'i a bikin nan d'an gutsoro min rabo kamin 'yar albarka ta aiko mana" ya karasa yana washe baki.

Takaici ne ya kawowa Inna har wuya ya hana ta magana tir da mai irin halin sa irin nasihar da yayiwa 'yarsa da zata shiga gidan miji kenan, wai har sai yaushe zai canza sai yaushe ne zai gane gaskiya?

" Abin haushi ma kin ga banida number sirkin nawa ai da kai tsaye zan Kira shi muyi magana ta fah....." Cikin sauri Inna ta katse shi tana " haba Mallam yin hakan ba girman mu bane zai iya raina mu ka bari tunda dai ka fad'awa ita Zareefan zata aiko su ne da zaran ta samu"

"Ji wani zance wai ba girman mu bane, yo wani girma talaka yake da ita in banda abinki menene a ciki dan Mai kud'i ya raina talaka."

" Babu komai ba komai bane Amma ka bari in an kwana 2 da kaina zan karb'o maka numbern nashi a wajan ta kaga daga nan zaka iya magana dashi kai tsaye a duk lokacin da kake so" tana gama dad'in haka ta mike zuwa cikin bedroom dinta ta d'auko mishi bunch na dubu daya wato dubu dari kenan ta kawo mishi.

"Ka rike wannan zuwa wani lokacin ko?"

" Ai shiyasa nake son ki ke d'in ta daban ce" yace yana ta washe baki ya mike ya fice daga parlour ba tare da ya jira amsar ta ba.

Dabas Inna ta koma ta zauna tana nazari inko hakane tana da aiki babba a gaban ta ba zata tab'a bari ya zubar min da kima a gidan miji ba dole ta mike tsaye akan shi sannan ta dage da addu'a Allah ya shirye shi ya gane gaskiya.

***********************

Tundaga wannan rana ban kara ganin kowa a gidan da sunan ziyara ba daga ni sai shi, duk aikin da yace inyi kullum da sassafe nake yi kamin ya fito na tsabtace ko ina na saka turaren wuta abincin sa kuwa bana fashi ina ajiye mishi a kan table in koma d'aki in kulle kaina duk da akwai lokacin da ya same ni yace in daina ajiye mishi wannan jagwalgwalo na dan yafi karfin ci kullum masu aiki yake bawa, ban kula shi ba na cigaba da ajiyewa dan jiki na ya bani shi yake cinyewa ya fake da masu aiki, d'akin shi ne dai ban kara gigin lekawa ba balle ince zan share.

Duk wannan kokarin da nake bai hanawa in 'yan rashin mutuncin nashi suka motsa ya sauke su a kaina, ina dai daurewa bana nuna mishi rauni na sai na koma daki nake cin kuka na in more duk rayuwar gidan ya ishe ni.

Yau tunda na farka nake ta murna saboda a yau za'ayi yinin bakwai kuma a gidan nan za'a yi shi kaman yanda al'ada yake, babban farinciki na harda Inna za'a zo shima iyayen shi zasu zo a hadu gaba daya asan juna a kara karfafa zumunci.

Irin gyaran da nayiwa gidan yau na musamman ne tun 7:30 na shirya cikin wata hadaddiyar shadda ta blue dinkin doguwar riga yasha zubi har kasa, duk da ban iya wani d'aurin kirki ba na kokarta nayi yanda zan iya kuma cikin ikon Allah yayi kyau sosai sai na kara zama Amarya sak, duk d'auki ya hana ni sukuni sai kallon time nake ina jin lokaci baya tafiya, ina zaune ina ta kallon agogo naji an murd'a handle din kofan parlour cike da murna da d'auki na mike na tafi da gudu dan in rungume duk wacce ta fara zuwa, da gudu na kwasa nayi kofan sai dai kamin in karasa naja wani wawan briki na tsaya a tsoroce tare da mayar da kai na kasa.

Shiru banji yayi min magana ba Kuma banji alamun ya tafi ba, ina ta ayyanawa a rai na kila ya tafi ne in ba tafiya yayi ba me zai tsayar dashi anan? Hakan da na saka a raina yasa na dago da kaina karaf ido na a cikin nashi yana min wani kallo da ni dai ban san fassaran shi ba, mayar da kai nayi na shiga gulman shi a zuciya ta mutum sai shegen fadin ran tsiya da iyayi....

"Meye na gaya miki last time akan gidan nan?" Muryan shi ya katse min gulman shi da nake.

"Kace in rika share gidan nan kullum...."

"And then?" Ya katse ni tun kamin in karasa.

"Ina yi kuma harda girki" daki na fa?" Ya kara katse ni.

Harga Allah bai zata da gangan na zubar da ruwa ya fad'i ba a wancan ranan Kuma yaji dad'in gyaran da nayi mishi shiyasa ya biyo ni, ni kuma a tunani na ya sani shiyasa naki shiga d'akin kada ya kama ni na San halin shi na cin zali.

"Kayi hakuri zan rinka gyarawa " na bashi amsa cikin sanyin murya.

"Better " yace tare da juyawa ya fita nabi shi da ido har ya b'ace min dan yayi min masifan kyau cikin riga armless da wando 3 quater duka farare ne tass anr rubuta Gucci da manyan harufa da bakin fenti a gaban rigan mutum yana ganin well builded body shi a zahiri ga gashi kwance luf a fatan jikin shi kaman wani balarabe.

Kofan na rufe na dawo na zauna jiki na duk a mace me yasa kwanan man nake jin wannan yanayin in muna zaune waje daya kuma duk abinda yake yanzu birge ni yake ba kaman da danake jin haushin shi ba.

9:00 am dot Yasmeen da kannen ta 2 suka zo cikin farinciki na taro su bamu zauna a babban parlour ba naja zuwa nawa muka zauna naja karamin kanin ta da ba zai wuce 7 years ba ina tambayan shi ya sunan shi? Dan Allah ya daura min son k'ananan yara ko dan babu a d'akin mu ne oho.

"Muhsin " ya amsa min da karamin muryan shi mai dad'i, murmushi nayi nace " sunan ka mai dad'i".

"Aunty Amarya kin gan mu da sassafe ko, wlh muhsin ne ya takura mana tunda ya farka daga bacci yana ta kuka shi lalle sai an kawo shi nan shine fa da ya ishi Momy da fitina tace muzo kamin ta karaso" Yasmeen ta katse ni da murmushi a fuskar ta..

"Ni ai Muhsin ya burge ni ina zaune ni kad'ai kaman mayya gashi na samu abokanen hira, kema kince zaki dawo ban Kara ganin kafar ki ba tun ranan da kika fice daga gidan nan" na bata amsa ina dan dariya.

"Cab ai Momy ce ta hani ni zuwa wai zan zo in takura ku" ta karasa itama tana dariyan.

Kawar da wannan maganan nayi na kawo wata hirar daban nake tambayar ta ya matakin karatun ta yake, ta amsa min da zata rubuta jamb tayi joining next year, naga ashe matakin mu daya da ita a karatu.

*****************

Tun goma da rabi na safe gidan mu ya fara tara mutane amma na jiki sun zo ne dan raka Inna taga gida na, su Aunty's dina sune farko-farkon zuwa amma Inna tace musu babu inda zata je bata shirya zuwa a yau ba sai wani lokacin.

Ba yanda ba suyi da ita ba tace su suje kawai ta riga ta shirya duk kayayyakin da zasu kai min kaman su kayen lefe na da sauran kayan da ba'a samu kaiwa a ranan bikin ba, Aunty Batul cewa tayi shikenan tayi zaman ta tunda hankalin ta yaki kwanciya da zuwan nata.

Ita kuma Aunty Fatima bata yiwa kowa magana cikin su ba ta fita a gidan zuwa gidan Yar uwar su wato Maa ta same ta zaune cikin shirin tafiya su kawai take jira, tana ganin Aunty Fatima ta mike tana nad'a latfayan ta tace " aini tun d'azu ku nake jira sai yanzu Bintun ta gama ne?"

"Bintu fa cewa tayi babu inda zata je wai sai dai mu muje..." Ban gane babu inda zata je ba, zuwan uwa taga gidan 'yar ta ranan bakwai ai al'ada ce da ta kafu tuntuni balle tace akan ta za'a fara, maza wuce kice mata ta fito yanzu kuzo mu tafi".Maa ta katse ta a zafafe.

Ba musu Aunty Fatima ta juya zuwa gidan mu dama zuwa tayi ta fad'awa Maa ta san ita kad'ai ce zata iya saka ta zuwa ko bata so.

Masu rakiya duk sunyi jigum jin cewa uwar Amarya ba zata je ba Aunty Fatima ta shigo taja ta gefe tace mata maza ta shirya inji Maa su tafi, ba yanda ta iya haka ta shirya suka kama hanya a motoci kusan 3 da aka aiko musu daga gidan su Zafar.

Ni kuwa hira sosai muka Sha da yasmeen Wanda yawanci labarin Yayan ta take bani kan yanda yake tsoron Abban shi Kuma hakan baya hana shi tsula tsiyar shi Mom tana rufa mishi asiri, sosai nake ta shan dariya harda rike ciki bamu tsagaita ba saida su Maryam suka zo sannan ta bar labarin nashi muka shiga wata daban.

Sai bayan azahar su Inna suka iso baki na ya kasa rufuwa da gudu na fad'a jikin ta na kenkeme ta ina hawayen farinciki, ajiyar zuciya Inna take ta saukewa akai akai na kwanciyar hankali dan bata ga alamun tashin hankali a tare da ni ba.

Sai a lokacin ta samu kwanciyar hankali ganin gida tana ta jero min addu'oi a zuciya na samun farinciki mai daurewa a gidan mijina, duk wani abu na tarban baki maman Yasmeen ta aiko mana har manyan kuloli na abinci dan haka bamu nemi komai ba aka shiga serving din baki mu dai muna can ciki muna ta hayaniyar mu.

A daidai wannan lokacin Momyn Zafar da gayyar ta suka iso ,sai huhhura hanci suke suna kallon mutane a d'age su Inna basu kula su suka karbe su da hannu 2 har ana ce musu ga wajan Zama budan bakin wata daga cikin su tace;

"Yau naga ikon Allah mu da gidan dan mu wasu bare ke kokarin nuna mana iko" ta karasa harda rike haba irin abin ya bata mamakin nan, Aunty Batul da bata da hakuri kaman gudawa ta yunkura zata basu amsa Inna da take kusa da ita tayi saurin rike hannun ta Maa da suke zaune opposite da ita ta girgiza mata kai alaman kada tayi magana.

Haka ta koma ta zauna tana ta girgiza kafa bala'i na cinta, su Kuma sai da suka gama dariyar su na wulakanci sannan suka nemi waje suka zauna suna zama cikin ikon Allah ko sai ga Maman Yasmeen da wasu mata 3sunyi sallama sun shigo da fara'ar su a take fuskar Momyn Zafar da mutanen ta ya kuntata dan basuyi tsammanin zuwan ta a wannan lokacin ba sun so su gama tsula tsiyar su kamin ta iso ba dan wai suna tsoron ta ba sai dan sun san duk abinda da sukayi zaije kunnen Abba kuma bata manta warning din da yayi mata ba akan bikin ba.

A mutunce suka gaggaisa dasu Maman Yasmeen har suna tambayan ina 'yar su take basu ganta ba , Aunty Fatima ce ta shiga ta fito dani bayan ta nada min laffaya ta kara bulbule ni da humra.

A kunyace Kuma kaina a kasa na gaishe su suka amsa da kulawa banda su Momyn Zafar da suke amsawa kaman anyi musu dole ko masu ciwon baki, ina gama gaishe su ko minti 1 ban kara ba na koma ciki daman gaba daya a takure nake jina a wajan.

Zuwan Baawa duk ya rusawa Momy badget kuma zaman su a inuwa daya babu riba dan haka suka mike da niyyan tafiya Baawan taso tsaida su amma suka ki tsayawa suka Kara wuta, suma ba wani jimawa sukayi ba suka ce zasu tafi aka rabu cikin mutunci.

Karfe 3 su Inna suma sukayi haraman tafiya suka saka ni a gaba da nasihu sosai masu ratsa jiki sannan suka tafi suka bar ni ina ta kuka, su Maryam dasu Yasmeen suna ta bani baki suka taya ni gyara gidan sannan suma suka wuce suka bar ni.
[6/16, 9:20 PM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*37&38*

A hanyar su ta komawa gida sauran mata suna ta hira da santin gida na amma banda Inna da tayi jigum duk abin duniya ya ishe ta dama shiyasa bata son zuwa Maa ta tilasta mata dole tazo gashi ta ga abinda ya tayar mata da hankalin, alamu ya nuna cewa ni da Zafar babu matsala a zamanta kewar mu amma mahaifiyar shi itace babbar kalubele a cikin rayuwar aure na.

Duk yanda miji ya Kai ga son matar shi in har dangin shi basa kaunar ta toh fa babu zaman lafiya balle ace mahaifiyar shi ce sukutum bata son ta ai babu kwanciyar hankali, ajiyan zuciya ta sauke mai nauyi har Maa da take kusa da ita ta dago suka had'a ido, alama tayi mata da ido cewa kada ta tada hankalin ta sai sunje gida zasu nemi mafita.

Wani ajiyan zuciyan ta sauke tana mai lumshe idanun ta alamun ta fahimta, a bakin kasuwa mafi yawancin matan suka sauka kowacce zata nemi motan da zai Kai ta Anguwan ta sai su Inna, Maa, Maman Dije dasu Inna Asabe sune kad'ai aka karasa dasu kofar gida.

Maa bata shiga gidan mu ba ta wuce gidan ta su kuma suka shigo gida, a tsakar gida suka iske Gwaggo Aisha tana wanke wani abinta cikin bucket, sallama kawai sukayi kowacce ta wuce bangaren ta ba tare da sun tanka mata ba domin habaice-habaice take tana bin su da harara wai kwadayi yasa suka bi Inna, ita kuwa har duniya ta nad'e bata ga abinda zai sa tabi ta ba dan har abada a matar cushe matar biyan bashin take kallon ta.

Wankin ta bari tana cizon yatsa dan ba haka taso ba taso koda Maman Dije ce ta tsaya acikin su ta tanka mata sanin halin ta na bata barin ta kwana sai dai yau harda itan suka ki kulatan.

"Ai duk hanyan da zan bi sai nabi naga bayan ki Bintu baki isa kiyi walwala ba muddin ina numfashi a doron kasa sai nabi na kuntata rayuwar ku keda wancan kod'add'iyar 'yar taki" tana magana ne da dukan karsashi dake zuciyar ta fuskarta kuwa na nuna zata iya aikata koda kisa ne dan cimma burin ta.

Hajara da shigowar ta kenan gidan tana tsaye a bakin gate kuma tana jin duk kalaman da mahaifiyar ta take furtawa akan mu, hawaye take na tausayi mahaifiyar tasu kan rayuwar da ta zabarwa kanta kullum cikin addu'an neman shiriya take mata amma da alamu tayi nisa sai a hankali, hawayen fuskarta ta goge tsab tana ayyanawa dole ne tayi wani abu na dakatar da duka Shirin ta in ba haka ba ta san halin mahaifiyar ta zata iya aikata komai da ta fada koma fima.

Bayan ta tabi zuwa cikin parlour su da ko carpet din arziki babu, da tsaki ta shigo maimakon sallama ta zauna a kasa tana kara jan tsakin da karfi yanda zata ji tayi magana.

" Ke kuma lafiya zaki zo ki saka mutane a gaba kina ta jan tsaki kaman wata tsaka?" Gwaggo Aisaha ta tambaya tana mata wani mugun kallo dan harda ita cikin wayan da take jin haushin su kan ko kad'an bata son taji anyi maganan mu balle a fad'i laifin mu.

"Umma ki taimake ni zuciya ta zata buga, wannan kyakkyawan mijin da gida kaman aljannar duniya dani ya dace ba wannan kod'add'iyar yariyan ba" ta karasa tana kara b'ata fuska kaman zata fashe da kuka.

A mamakince Gwaggo ta juyo tana kallon ta fuskarta d'auke da alamun tambaya tace " wai maganan wa kike min kuma wwni gida?"

Sai da Hajara ta tab'e baki kaman abinda zata fad'a har cikin ran ta ne tace " hmmm maganan wannan kod'add'iyar yariyan mana 'yar gidan Bintu".

Cikin wani irin sauri tazo gaban Hajaran ta zauna tare da kamo hannayen ta duka 2 ta rike cikin nata fuskarta cike da tsansan farinciki tace " Hajara da gaske kike ?"

"Gyad'a kai tayi ta kwakulu hawaye tace" Umma kin gan shi kuwa kaman wani balarabe ga gidan ma yanda kika San a kasar waje kike, ni dai gaskiya ki taimaka in kwace su duka a hannun ta" ta karasa tana goge hawayen ta

"Alhamdulillahi!!! Allah nagode maka wannan mugun asiri da matar cushen tayi miki ya karye Hajara ta ta dawo gare ni" tace tana rungume ta harda kwallan farinciki a idon Gwaggo.

"Asiri gaskiya ce ni shaida ce tunda gashi nagani akan 'yata mafi soyuwa a gare ni amma kiri-kiri aka raba mu ba kya son a ambaci sunan su koda da wasa da mutum ya tab'a su gwara mutum ya shararawa uwar ki mari goma" Gwwggo ke fadin haka cikin kuka dan da gaske take farinciki dawowar tan domin tun ada baya itace abokiyar shawarar ta daga baya Kuma da ta gane gaskiya sai taja baya da ita.

Ta dad'e tana da burin yin wasu abubuwa da dama akai na da Inna ta amma ta rasa dawa zasu had'a Kai suyi domin Jameela kullum bata gida koda ta dawon ma a buge take shigowa.

"Kinga yanzu 'yar uwar ki halin da ta zabarwa kanta kenan bana ma samun ganin ta sai bayan satika ko kwanaki koda na ganta ma ba a cikin hayyacin ta take shigo min ba sai cikin maye dama kece kad'ai kika rage min ta raba mu da mugun asirin ta sai dai ta Allah ba tata ba gashi komai ya karye Alhamdulillahi" ta karasa cikin tsantasan farinciki da ta dad'e bata ganta a ciki ba.

Mayar hawayen idon ta tayi na tausayin mahaifiyar tasu sannan ta maye gurbin da murmushi tace " toh yanzu meye abin yi Umma?"

"Tun kwanaki Lantana ta min alkawarin kaini wajan wani boka da aikin shi yake kaman kaifin wuka, dama rashin ki a kusa dani yasa na bar maganan amma tunda komai ya warware zanyi mata magana mu tafi cikin kwanakin nan komai da suka mallaka sai ya dawo gare mu ".

***************

Shiru gidan kake ji kaman ba shine dazu take cike da mutane ba, duk sai naji babu dad'i Ina nan zaune a inda suka bar ni na kurawa tv da yake ta karaji shi kad'ai ido kaman kallon nake amma kuma hankali na ba anan yake ba ya tafi ga tunanin haka rayuwa ta zata kasance zama da wanda bai san daraja ta ba wanda yasha fada min da bakin sa ba sona yake ba, tunda aka kawo ni gidan nan ban abu wai shi farinciki ba ina dai zaune ne kawai in mun hadu banda mugunta ba abinda yake shiga tsakani na dashi.

A da nima haushi yake bani kuma in yayi min muguntan bana samun kwanciyar hankali har sai na rama amma a kwanakin nan ban san me yasa ba ko me yayi burge ni yake maimakon inji haushin sa, in yana zaune a parlor ko yana cin abinci nakan buya inyi ta kallon shi tunda ya min iyaka da inda yake yace kada in kuskura in zauna inda yake, so must time ko ina parlour in ya shigo zan tattara in koma nawa inyi ta leken shi wani lokacin nakan ji haushin kaina tare da tambayan toh me hakan yake nufi amma babu mai bani amsa.

Wani abin takaici ko cikin dare na tashi wani lokacin na kan leka d'akin shi,ina iya hango shi yana baccin shi cikin kwanciyar hankali, cikin d'an hasken dim light dake bari na gefen gadon shi ba na sanin ko minti nawa nake a wajan all I is ina dadewa sannan in koma in kwanta

Sallamar shi cikin azzakar muryan shi naji ya daki kunne na duk da ciki-ciki yayi ta dan na san baiyi tsammanin da mutum ba a parlorn ba, kasa amsawa nayi saima bin shi nayi da kallo har ya shige , yayi min matukar kyau cikin wani lallausan yadi maroon da ya saka anyi mata dinkin zamani irin iya cinyan nan kan shi babu hula sai bakin gashin kan sa dake sheki yana d'aukan ido.

Kara fitowa yayi sai dai wannan karon ya cire rigan sai farin vest ne a jikin shi murdadden jikin sa a wake, hannun shi d'auke da laptop yana duba wani abu gaba daya hankalin sa yana kai, ni kuma ina nan tsaye yanda ya barni na kasa motsawa a wajan duk da naga inda nake yake nufowa amma na kasa matsawa ina kallon yanda shima vest din ta zauna a jikin shi, wato shi komai ya saka sai tayi mishi kyau.......

Ina cikin zancen zuci naji mutum ya fad'o min mukayi baya tare kan kujera dake bayana ya kasance yayi min rumfa da faffadan kirjin shi, wani irin yanayi da ban tab'a tsintan kaina a ciki ba yau naji ni a ciki ganl kamshin jikin shi da kuma d'umin jikin sa da suka had'u suka bada wani yanayi na musamman, lumshe ido na nayi Ina addu'an Allah yasa mu dauwama cikin wannan yanayin Mai wuyar fassara.

Cikin wani irin zafin nama ya d'aga ni tare da hamb'are ni gefe na fad'i kasa dole na waro idanu na dana lumshe na sauke su a kan shi, kaman wanda ya tab'a Kashi haka yake ta kakkab'e jikin sa yana watso min mugun kallo kaman idanun shi zasu zubo kasa.

"Wannan kuma wani sabon iskanci kika fito dashi kizo ki tare min hanya kawai dan wannan kazamin jikin naki ya rab'i nawa, how dare you tayaya ma zakiyi irin wannan tunanin ko ban fad'a miki matsayin ki ba kamin ma ki shigo" ya karsa yana zaro min ido waje cikin sauri nayi kasa da nawa domin na razana.

"Wallahi kika kara bin hanyan da nake bi sai nayi mugun tsab'a miki da alamu ina raga miki dayawa shiyasa har kika samu daman baza kolin ki yanda kike so" still ni dai bance mishi komai ba sai kallon shi da nake ta kasan ido cos duk yanda naso hana kaina kallon shi na gagara.

D'aukan laptop dinsa yayi ya dudduba yaga tana nan lafiyan ta qalau babu abinda ya same ta, Kara saka kafa yayi ya hamb'are ni yana " get out of my sight da idon ki kaman na mayu a wajan ana magana kin zuba min su kaman zaki cinye ni".

Tashi nayi ba tare da nace mishi kala ba na wuce kitchen na hado mishi drinks da abinci na kawo na ajiye mishi na wuce daki ina jiwo muryan shi yana in dawo in kwashe jagwalgwalo na ko waiwayowa banyi ba balle yasa ran zan dawo in kwashe.

A bakin gado na zauna a hankali Ina mai lumshe ido tare sakin kayataccen murmushi ni kad'ai yanayin da muka kasance yanzu Yana min gizo a ido, kwanciya nayi rigingine ina kallon pop saman d'akin with a blushing face sai juyi nake akan gadon.

Zaune na tashi ina yamutsa fuska ni kad'ai tare da tambayan kai na what's wrong with me? Na rasa mai bani amsa nayi nayi ko zan samu haske amma ban samu ba, tagumi na zuba kawai na zauna shiru can naji zuciya ta na azalzala ta kan in leka inga ko yana cin abincin?

Cikin sand'a na iso bakin kofan na leka ta bulin makulli, laptop din naga ya ture gefe yana ta kwasan gara harda lumshe ido alamun abincin yana mishi dad'i, rufe baki nayi da tafin hannuna kada dariyan da nake rikewa ya fito fili ya ji ni.

Ina kallon shi ya cinye abincin tas ya kora da juice sannan ya tattara kayan ka Kai su kitchen yazo ya zauna ya cigaba da aikin da yake yi a laptop din, ni ko sai da naga ya gyara komai ya zauna sannan na fito nayi hanyan kitchen ba tare da na kalli inda yake ba .

Da ido ya bini har na shige yana tunanin me zai fad'a wanda zai kare kan shi kan cewa ba shine yaci abincin ba, har na fito bai samu wata gamshasshiyar magana da zai gaya min in gamsu ba.

Tafiya nake a hankali ina kallon shi da alaman tambaya akan fuskata na waye ya cinye abincin?

Cikin kame-kame ya fara magaa " hey look don't think negative dan ko yunwa zata kashe ni banga abinda zai saka inci wancan jagwalgwalon ba I just gave it to the driver suka cinye ya dawo da...." Kasa karasawa yayi ya tsaya kallon yanda nake ta gyad'a mishi kai tare da murmushin rainin hankali.

"Meye kika wani zuba min ido kina dariya kaman wanda ke miki karya?". Saurin girgiza kai na nayi Ina danne dariya da yake son kufce min.

A fusace ya tashi yayi kaina yana " dariya kike min ni zaki maida mahaukaci?"

Aiko Ina ganin ya mike na kwasa a guce ina sakin dariyan da na danne na shige bangare na gudu ban tsaya a parlour ba na wuce daki na fad'a kan gado Ina dariya sosai .

Shima daya biyo ni da gudu bai san lokacin da ya saki murmushi har hakoran sa suka fito ba ya girgiza kai yana " lallai yarinya nan ta fara raina ni".

Nagode da addu'oin ku Allah ya bar zumunci nd Alhmdlh jiki na yayi sauki sosai .
[6/16, 9:21 PM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Assalamu alaikum yan uwa da fatan munyi sallah lafiya, Allah ya karb'i ibadun mu ya nuna mana na gaba Ameeen.

*39&40*

"kada abinda kika gani ya tayar miki da hankali domin matan masu kud'in nan haka suke sun fi son 'ya'yan su su auri 'ya'yan masu kud'i kamar su, bakomai yasa kika ga tana mana wannan kallon ba sai dan sanin mu talakwa ne.

Idan muka cigaba da yi musu addu'a sannan kuma ita Zareefa zata iya samo soyayya surukan ta wajan dagewa da kyautata musu tare da yi musu zallar biyayya" Maa ce take fad'awa Inna cikin kwantar mata da hankali.

"Hmmmm hakane Maa har hankali na ya kwanta da tunda na dawo na kasa sukuni domin na san yanda wannan matsalar take" Inna ta amsawa mahafiyar ta cikin sanyin murya..

" Ki kara kwantar da hankalin ki saboda mun yarda da tarbiyan da muka bata ba zata tab'a yin abinda zai b'ata sunan ta ko na gidan ku ba" Maa ta kara tabbatar mata nan dai ta daura da shawarwari da hira masu sanyaya zuciya sai ga Inna da tazo mata wani cikin damuwa da sanyi jiki ta ware suna ta hira harda kyalkyalan dariya.

Bayan kwana 2 Gwwggo Aisha ta had'a duk wasu 'yan kud'ad'e da suke hannun ta tare da sayar da wasu kayayyakin ta saboda ta samu isassun kud'in zuwa wajan boka, dama haka take duk tabi ta sayar da abinda take dasu dan ko dakin Inna Asabe yafi nata kyan gani domin ita ta fawwalawa Allah lamarin ta ta rungumi sana'an ta kuma alhmdlh tana samu daidai gwargwado domin tana sayan kayan daki da kadan kadan tana gyara dakin ta.

Sun je wajan bokan ita da lantana da yake can jejin Goshe ko tsoro basa ji na yanda hanyoyin maiduguri suka lalace, sunyi sa'a sun same shi ya basu magani amma yace a abinci za'a zuba mishi na kwana 3 in dai har yaci abincin toh zai min wani irin tsana da bashi da iyaka ya min koran kare a gidan shi.

Wani kullin maganin ya Kara miko musu yace shi wannan kuma a turare zasu saka Hajara ta rinka shafawa a duk lokacin da zata je kusa da shi , in har ya shaki kamshin toh shikenan an wuce gurin zata zama itace mace kad'ai a rayuwar shi ko uwar shi ba zai kara tuna ta ba.

Cikin tsananin farincikin samun nasara ta dawo gida ta labartawa Hajara yanda sukayi da boka, nan kuwa ta hau murna kaman da gaske harda su rawanta wai ta kusa samun miji balarabe.

***************

Kaman yanda ya saba kullum sai yaje ya gaida iyayen nashi yauma ya isa gidan nasu akan lokaci domin ya samu Abban shi a gida bai fita ba, cikin girmamawa ya isa gare shi ya zauna wajan kafafun shi sannan ya gaishe shi yana daura kan shi kan kafar Abba.

Cike da so da kaunar tilon d'an nashi ya amsa yana mai shafa gashin kan shi, dan yanzu sosai suke shiri ba kaman da ba da kullum suke cikin rigima kan hallayyar shi ganin yayi auren yasa yake ganin ya natsu sosai.

"Ina 'yata tana lafiya ko?" Abba ya tambaya bayan ya amsa gaisuwan nashi.

"Tana nan lafiya Abba tace ma in gaishe ku" ya bashi amsa yana wani tsunne Kai kaman da gaske.

"A'a ni gaisuwan nan ta ishe ni hakan nan tunda taki zuwa mu ganta koda yake bata da laifi kai ne kake mana rowan ta ko Hajiya?" Ya karasa yana maida hankalin sa kan Mom da take saukowa yanzu.

Sai da ta tab'e baki ganin dukkan su basa kallon ta sannan ta kirkiro murmushi tare da karasawa gare su ta zauna kusa da Abban tana mai cewa " babu batun rowa ririta amaryar sa yake" ta karasa tana dariya kaman da gaske.

Dariyan suma sukayi suka cigaba da hiran su har zuwa wani lokaci sannan ya mike yace zai tafi

"Ya maganan da mukayi da kai sai yaushe zaka fara fitowa office?" Abba ya dakatar da shi.

"Sai nan da 2 months" yace yana sosa keya, dariya suka mishi Abba yana " ja'iri wata 2 ai kaman kwana 2 ne yanzu zai zo ya wuce, amma ka tabbatar ka kawo min 'yata mun gaisa".

Mom da duk haushi ya cika ta na me yasa Abba yake son gani na ta bud'i baki zatayi magana yayi saurin dakatar da ita wajan daga mata hannu ba dan taso ba tayi shiru tana gani har Zafar din ya fice zuciyar shi fari tass dama abinda yasa yace sai bayan wata 2 zai fara aiki kamin nan ya gama da chapter na ya Zama free man zaiyi abinda yake so.

Ni kuwa bayan wannan incident daya faru tsakanin mu wanda ya kasa barin kwakwalwata bamu kara zama waje daya dashi ba sai dai da naji motsin shi zan l'eko in kare mishi kallo sometimes yana cin abinci sometimes kuma yana wannan danne- dannen shi a laptop, ni dai har yau ban san me yasa bana gajia da kallon shi ba.

Yau tunda na tashi na gama aiki na zauna ina duba wani littafin Hadisi cikin litattafai na islamiya, wannan mayen kamshin nashi shi ya fara min sallama, wani irin zillo zuciya ta yayi kaman zai fad'o kasa jin wannan sassayan muryan yana cewa " ki shirya anjima da daddare zamu je ki gaida su Abba, nd saura in muka je kada ki kama kan ki kije kiyi ta musu kauyanci ki da kika saba kiga yanda zan tsaba miki ".

Maimakon inji haushi ni dariya ma ya bani dan haka ban san lokacin da na saki wani kayataccen murmushi ba, wai nice zanyi mishi kauyanci ko ce mishi akayi daga kauye nake oho.

Cike da takaici yake kallon yanda na sunkuyar da kai kasa ina murmushi, shifa wannan sabon dabi'a da na samu haushi yake bashi da duk abinda zaiyi min ko ya fad'a min baya bani haushi balle in nuna ko inyi kuka, in ya ganni ina kuka wani dad'i yake ji na musamman amma da yanzu bana nuna jin haushi sai yaji duk haushi ya kara cika shi.

Cike da tsana ta ya hamb'are ya fice yana" duk abinda za'a mata sai ta zauna tanawa mutane dariya, mayya kawai ni dai ba zaki cinye ni ba" yana magana yana mai ficewa daga parlourn.

Tashi nayi na karkad'e jikina still murmushin bai bar fuskata ba wai nice mayya hmmmm.

Tunda yace zamu je gaida iyayen shi duk sai na kasa zaune na kasa tsaye ina tunanin me zan kai musu da zan burge su, abinka da masu kud'in nan ba komai zaka musu kayi gwanin ta ba.

Duk tunani na ya tsaya ne kan girki, toh in banda girkin me nake dashi da zan kai musu, kitchen na shiga nayi tsaye ina tunanin what should I cook? Wai meye nawa da zan takura kai na kan sai na musu gwanin ta kwana 2 nan mantawa da nake cewa auren temporary nake zai iya sallama ta at any time tunda yanzu mun bawa wata d'aya baya, saurin kawar da wannan tunanin nayi saboda yanzu na tsani in tuno da hakan a cikin raina.

Tunani na ya tsaya ne kan inyi musu abincin gargajiya maybe zasu fi son ci, ina da garin ndalayi da aka had'o min cikin gara ban tab'a amfani da shi ba,yau shi na d'auko na daura tukunya mai dan girma da ruwa dai-dai yanda nake so.

Kamin ruwan ya tafasa na gyara kayan miyana na daura miyan a gefe, miyar kubewa danya da yaji zallar naman rago sannan na tuka tuwo bayan na wadata ruwan daya tafasa da man gyad'a, sabuwar warmers da ban tab'a amfani da su ba na ciro na zuba abincin a ciki bayan nayi malmala masu kyau sannan na Kara bin man su da man shanu na rufe.

Ganin akwai sauran time yasa nayi samosa da meat 🥧 suma nayi package din su a wasu containers masu kyau, duk na jera su a cikin yalwataccen basket sannan na lullub'e saman da tumakasa mai kyau na fito da shi kan dinning sannan na wuce dan shiryawa.

Cikin atamfa super fari tas da adon flowers blue na shirya kaina na zauna na dan yi make-up dina sama-sama harda kashe d'auri duk da Ina jin ana kiraye-kirayen sallah magarib ban dakata ba saboda ina fashin sallah, jewelries da na saka duka pure gold ne hakan sai ya kara haskani nayi kyau sosai abina .

Sai da na gama kwalliya na sannan na tuna ashe ban ci abincin ba, fitowa nayi kitchen na zuba rabo na a plate shima na zuba mishi komai da nayi harda su snacks din dan a tunani na ba lalle bane yaci abincin gargajiyan da na girka.

Ina cikin cin abinci na naji motsin ya shigo Kuma na tabbata yana dinning yana kwasan gara sai dai shegen girman kan shi yasa ba zai tab'a admitting cewa yana ci ba sai dai yace masu gadi yake bawa.

Muryan shi ne ya katse ni yana in fito mu tafi, sai da na kara shafe jikina da humra mai dad'in kamshi na yafa mayafi blue mai dan girma na saka takalmi flat shima blue da poss din sa wanda wayata ce kawai a ciki sannan na fito hannu na dayan d'auke da plate din da na gama cin abinci, a tsaye na same shi shima ya shirya cikin kananan kaya riga ash color da wandon jeans fari sol.

Ta gefen ido na kalli kan table din ga mamaki na tass ya cinye abincin ko tab'a su snacks din baiyi ba, fasa shiga kitchen din nayi na tsaya na tattara kan table din na wuce dasu Ina kallon shi ta gefen ido dariya na cina ganin yanda ya wani tsare gida wai shi ala dole ba shine yaci ba.

Naso in tsaya in wanke plates da muka bata sai dai gudun masifan shi yasa na bari kan sai mun dawo, koda na fito shi har ya fice nima ban tsaya b'ata lokaci ba na d'auki basket da na jera abincin a ciki nabi bayan shi, a dan tsorace na isa ga motan da yake ciki duk da kasan zuciya ta cike yake da farincikin yau zan fita in ga gari dan tunda aka shigo dani cikin gidan nan ko bakin gate ban tab'a lekawa ba.

Koda na iso bakin motan sai nayi tsaye na rasa ya zanyi in shiga kada in shiga baya yace na maida shi driver sannan ina gudun shiga gaba yace na raina shi, shahada nayi na bude gidan gaban na shiga ganin ko inda nake bai kalla ba saima mayar da kan shi da yayi yana duba wani abu a cikin locker, sai da na zauna sannan na mayar da murfin na rufe tare da neman inda zan ajiye basket d'in.

Basket d'in hannu nawa yabi da kallo kaman zaiyi magana ko me ya tuna oho naga kuma ya mayar da kanshi gefe tare da jan motan muka fita a gidan ba tare da ya Kara kallo na ba.

Shiru cikin motan kaman babu mutane a ciki har muka iso wani tangamemen gida wanda ko ta waje kasan masu gidan sun jiku da naira, horn d'aya kawai yayi sai ga mai gadi ya taho da gudu ya zuge mana gate muka kutsa kai cikin hadadden gidan, baki sake nake bin gidan da kallo ashe da gaskiyan shi da yake cewa kada na mishi kyauyanci.

Talle min baki dana sake yayi da yatsa yana harara ta yace" wato baki yarda da abinda na gaya miki ba ko?" Yace yana jefa min mugun kallo, b'ata fuska nayi ina shafa baki na dan ba karya naji zafi sosai.

Bai bi ta kaina ba saima bud'e motan da yayi ya fita abin shi, shiri na saita natsuwa ta na bud'e murfin motan nabi bayan shi ganin yana son bace min, tun kamin mu karasa ma'aikatan gidan nasu suke ta durkusawa har kasa suna kawo mana gaisuwa amma maimakon ya tsaya ya amsa gaisuwan cikin mutunci sai dai kawai inga ya daga musu hannu ya wuce abinshi a zuciya ta nace wato shi ko ina yake sai ya nuna wannan girman kan nashi.

Wata mata ce ta karaso gaba na cikin sauri zata karb'i basket din hannu na nace mata ta bar shi amma ta nace sai na bata,ni kuwa ganin zata kusan sa'a da Inna ta yasa naki sake mata, dago kan da zanyi naga ashe bai shiga ba ni yake jira wani mugun kallo ya watsa min mai kama da warning yasa na sake mata basket d'in babu shiri na karaso inda yake jira na.

Hannayen mu ya tsarke waje d'aya sannan yayi sallama muka shiga cikin parlorn ,ashe abin kallon na ciki banga komai ba, ban san yanda zan kwatanta muku ba amma gidan yafi gaban had'uwa da kyar na shanye kauyanci na wannan karon na daina kalle-kalle na kalli gaba na, a can tsakiyan parlour Abba ne da Mom zaune kan wani lallausan rug sun saka warmers a gaba da alamu abinci suke shirin ci muka zo.

Abba fuskar shi d'auke da fara'a ta musamman yake amsa sallaman yayin da Mom Kuma baka gane yanayin da take ciki gata nan dai fuskan nan nata ba yabo ba fallasa, sau d'aya kawai na dago daga nan ban kara gigin d'agawa ba saboda kunya duk ya gama lullub'e ni yanda muka shigo hannun mu sarke nayi ta kiciniyan kwacewa amma bai bani daman hakan ba.

Kusa da Mom matan nan ta duka har kasa ta ajiye basket din sannan ta fice, sai da muka zo tsakiyan parlorn sannan ya sake min hannu ya karasa kusa da Abban shi ya zauna yana zuba musu shagwaba kaman karamin yaro suna biye mishi.

Ni dai daga dan nesa dasu na tsugunna Kai na a kasa na fara gaishe su, cike da kulawa Abba ya amsa yana in karaso kusa Mom in zauna mana ya zan zauna a nesa sai kace wata bakuwa,cike da jin nauyin su na matso na zauna ina Kara gaishe ta ganin bata wani amsa min ba.

Sama-sama ta amsa min tana kokarin fara serving din mijin ta amma sai ya dakatar da ita yana mai cewa " dakata mana da zuba abincin nan, ga surkuwar mu ta kawo mana kayan dad'i shi ya kamata muci yau ki maida naki gefe sai wata rana" ya karasa suna dariya shida Zafar ni dai murmushi kawai nayi na kasa dago da kai.

Yake kawai Mum tayi tare da maida warmers din ta rufe zuciyar ta na kuna ta yaya zata kwashi lokaci tayi mishi girki amma wai dan yaga nawa yace ba zai ci ba, bata musa shi ba ta jawo basket din ta fara cire warmers da suke ciki , tana bud'ewa kuwa kamshi duk ya cika parlorn na girkin dana man shanu.

Ranta duk babu dad'i haka ta zuba mishi abincin ta ajiye a gaban shi tana shirin rufe su yace mata " ya zaki rufe baki diba ba?"

" Zan diba ba rufewa nake ba" ta bashi amsa ta jawo plate gaban ta ta zuba malmala kwaya d'aya tak ta zuba miya kaman bata so ko mai kyankyamin abincin ta kai baki a ba zata sai da ta lumshe ido, dan abincin yayi mata wani irin dad'i domin batayi tsammanin zata ji abincin haka a tunanin ta tunda ni 'yar talakawa ce ban iya komai ba.

Zafar da yake kallon duk drama dake faruwa ya saki murmushi domin shi shaida ne in ta girki ne bani da ta 2, Abba sai santi yake ta zubawa wai ya akayi na san yana son abincin gargajiya, ashe wai dole su daina ganin Zafar wajan neman abinci a gida bayan cika baki da yayi ta musu a baya ko mata 4 be dashi abincin Mom d'in shi kad'ai zai ci.

Mom tana ji bata ce uffan ba koda suka gama Abba cewa a ajiye mishi snacks din nashi ne shi kad'ai, Mom sai tabe baki take tare da jin haushi Abba yana tsinka su a gaban wannan jinjirar yana abu kaman bai tab'a cin abinci mai dadi ba, ni kuwa duk farincikin ya lullube ni ganin yanda Abba yake ta yabon girki na dan ni nayi ne kawai banyi zaton zasu ci ba balle in samu irin wannan yabon.

Tattare kayan Mom ta fara Nima nayi saurin mikewa dan in taimaka mata amma cikin tsare gida tace in bar su, duk sai naji jiki na yayi wani irin sanyi na kasa komawa in zaunan, muryan Abba naji yana min magana yace " zo nan ki zauna daughter akwai hirar mu ta musamman dake" ya karasa yana nuna min gefen sa da hannu.

Da kyar na ja kafafu na zauna a inda ya nuna min yayi kasa da murya yace " kyale uwar nan taku haka take bata son in tana aikin mijin ta wani ya saka hannu wai ladan ta zai ragu shiyasa bata barin masu aiki suyi sai ita da kan ta" ban san lokacin da murmushi ya kwace min ba dan salon da yayi maganan dole ne yasa mutum dariya.

Zafar dake d'ayan gefen shima dariyan yayi dan ko shi baiji dad'in abinda Mom din nashi tayi ba amma yanzu daya ga Abba yana min barkwanci sai yaji hankalin shi ya kwanta kuma yaji dadi har cikin ran shi.

Wani envelope mai dan girma da yake kan kujeran bayan shi ya d'auko ya miko min yace " ga wannan tukuici ne daga gare ni kan yanda kika bada gudumawa wannan stubborned son nawa ya koma gentle boy".

Kasa karb'a nayi sai bin foldern nake da ido ina imagining what could be inside? Zafaar da yake sauraron mu ya b'ata fuska cikin shagwaba yace" Abba pls mana".

"Kwarai hakane my daughter ki karb'a Mana" yace ganin na kasa karb'a, hannu na rawa na saka na amsa tare da cewa " nagode Abba Allah ya kara girma da daukaka" Ameen my daughter" ya amsa min cikin jin dad'in addu'an da nayi mishi.

Muna cikin haka Mom ta dawo ta zauna hankalin ta da imanin ta duk suna kan abinda ke hannu na wondering ya akayi yazo hannu na, ganin irin kallon da take min yasa Abba ya maimaita mata abinda ya faru tare da ce mata " saura kema ya kamata ki kawo taki gudumawar"

Dama ance in talaka ya rabe ka in ba kayi sa'a ba toh kaima sai ka talauce, if not ya zaayî ya d'auko takardun company shi na buga ledodi dugurungum ya bada kyautan shi ma yar mitsitsiyar yarinya? Duk a cikin zuciyar ta take wannan maganan amma a zahiri kuma sai ta kirkiro murmushi tace" lalle Alhaji kana ji da wannan surkuwar tamu sai dai ai ko ni ban kara komai ba nakan ma ya wadatar kyautan company fa ai ya wuce wasa" ta karasa zuciyar ta na suya.

"Company? Ni Zareefa aka bawa kyautan company?" Na tambayi kaina da kaina hawaye na kokarin zubo min amma na shanye ina kara kasa da kai.

" Ga complimentary card dina daughter duk private numbers dina suna jiki a duk lokacin da yayi miki ba daidai ba ko kina bukatan wani abu kada kiji nauyi ki Kira ni Kai tsaye ki fad'a min kinji ko?"

Yanzu Kam sai da hawayen yayi nasaran zubo min nayi saurin saka gefen gyale na goge na saka hannu na amsa kamin in samu bakin magana naji muryan Mom da ta kasa hakuri tace " kaima dai Alhaji sai kace kaga wani alamun rashin zaman lafiya a tare dasu ko Kuma wacce bata da iya..."

Wani kallon ki shiga hankalin ki da Abba yayi mata yasa ta had'iye sauran zancen nata tare da kawar da kai gefe, saida ya maye fuskar shi da murmushi sannan yace " ta riga da ta shigo wannan family dan haka muma iyayen tane ko kin manta ita zata haifo mana magajin gidan nan a gaba?"

A razane take kallon Abban Jin wannan furucin da yayi me yake nufi kenan, duk shekarun da ta b'ata tare da shi ya tashi a tutan babu? Lallai ko sai ta kara tsayawa da kafafun ta ko ayi mata tsakiyar da ba ruwa. Amma a zahiri sai ta gyara fuskarta da nemo aron murmushi da ya tsaya mata a iya leb'e tace " hakane Alhaji Allah ya kara bud'i".

Gaba d'ayan su suka amsa da "Ameen " daga nan Abba da Zafar ne kad'ai suka cigaba da hiran su game da business daya yake taya shi a gida ,zuwa kusan karfe 10 Zafar yace zamu tafi Abba yana ta saka mana albarka ita kuma Mom cewa kawai mu gaida da gida.

Ga mamaki na har muka shiga mota bai kara hantara ta ba saima murmushi da yake ta faman sakewa shi kad'ai yana tukin sa cikin kwanciyar hankali ni kuma zuciya ta tana wani waje daban Ina rike da complementary card din Abba ina ayyana abubuwa da yawa a raina.
[6/16, 9:22 PM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

*INNALILLAHI Wa INNA ILAIHI RAJI'UN
Muna taya 'yar uwar mu PRINCESS FATIMA MAZADU na babban rashi da tayi wato yayan ta HRH. ALH ABUBAKAR MUHAMMAD KWAIRANGA ( SARKIN FUNAKAYE) UBANGIJI ALLAH ya jikan shi da rahama yasa mutuwa hutu ce a gare shi AMEEEN*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*41&42*

Bakomai ne yake raina ba sai yanda zan rama zalunci da yayi min, domin na yarda da maganan Yesmin da take fada min na cewa yana matukar tsoron Abban shi saboda nima gauce yanzu ba jiyau ba, ya wani natsu sai abubuwan mutanen kirki yake alhali kuwa mugu ne na bugawa a jarida.

Har muka karaso gida ko ci kan ki bai kara ce min ba nima na share shi na wuce d'aki na, kayan jiki na na fara ragewa sannan na shiga na watsa ruwa na fito nayi shirin bacci na kwanta amma sai na kasa samun baccin, tunanin wannan company da Abba ya bani shi ya fad'o min a rai toh ni ya zanyi da companyn nan? kawai bari in bari in an kwana 2 sai in fad'awa Inna inji me zata ce.

Lumshe ido nayi da niyyan bacci haka kawai Yaya na ya fad'o min a rai, ko a wni hali yake ciki, ko meyasa ya guje ni??

Tunanin hakan da nayi yasa na fara hawaye sosai harda shasshek'a dan ji nayi abin ya dawo min sabo fil zuciya ta sai kuna yake, duk halin da nake ciki a yanzu shine sila da bai guje ni ba da wannan mugun ko kallo na ba zai samu daman yi ba balle har in shigo gidan shi.

A wannan dare da kyar na samu bacci ya d'auke ni mai cike da mafarkai kala-kala.

Ko dana farka da safiyan nan sai naji duk raina a cunkushe yake fuskata babu walwala sam, iya d'aki da parlor na kawai na share nayi kwaciya ta ko kitchen banida niyyan lekawa balle inyi batun girki.

Zuwa kaman karfe 10 naji yunwa na neman hallaka ni dole yasa na fito main parlour na had'a tea mai kauri akan dining na d'auki mug d'ina da niyyan komawa d'aki naga mutum a zaune yana waya ko kallon inda yake banyi ba nayi wucewa ta na bar shi baki bud'e cike da mamakin abinda nayi yake bi na da kallo har na shige.

"Toh wai me ya hau kan yarinyan nan yau? Zaman da nayi anan ya kusa 1 hr ina jiran inga ta girka wani abu in samu inyi breakfast in fita shine taki yin komai saima tea da ta had'a ta wuce ko gaishe ni batayi ba, ko dai ta gane bana iya cin abincin kowa yanzu sai nata?" Zafar kenan shi kad'ai yana sumbatun sa a cikin ran shi.

Zuruf ya mike yana cewa naga kwana 2 yana d'an sake min shiyasa na fara kawo mishi raini bari ya shiga ya gyara min zama, yana maganan ne tare da nufan d'aki na.

Hankali kwance nake sipping tea na naga mutum ya shigo min babu sallama sai wani had'a fuska yake wai shi ala dole zai tsoratani.

"Ke tsaban kin raina mutane shine har zaki shigo ki fita ba zaki gaida mutane ba?" Ya fad'a cikin tsawa.

Sai da na turo baki na dan kalle shi na watsar nace" ni dai banga mutane ba,mutum daya na gani a parlorn".

Mamakin da yake fuskar shi kasa boyuwa yayi yana bina da wani irin kallo, had'iye abin shi yayi ya Kara wani tsare gida yace" ohk in ma mutum dayan kika gani ba zaki gaida shi ba kenan, nd what do you mean by ki shiga daki ki zauna shan tea sauran mutanen gidan ba zakiyi musu girki bane?"

Sai da na kuma kurban tea na hankali kwance sannan na bashi amsa " I don't feel like cooking today"

"What!! Ni kike fad'awa u don't feel like cooking, kin ga ina bin ki a hankali shiyasa ko jira ni ina zuwa zaki min bayanin yanda ya dace" yana fad'an haka ya fuce fuuu kaman zai tashi sama, tab'e baki nayi na raka shi da ido wai ni zai rainawa hankali wai mutanen gidan me zasu ci, yace min dai me zai ci?.

No Abba da tun jiya nayi saving a wayata na kira na saka a handsfree na ajiye kusa da ni muna gaisawa Ina karasa shan shayi na daya rage ya shigo dakin a zafaffe da belt a hannun shi har zai bud'i baki yayi magana jin muryan Abban shi yasa yayi tsit yana zare ido, kallon up nd down na mishi ina murmushi Abba yace" da fatan kin tashi lafiya my daughter"

Kara kwantar da murya nayi sannan na amsa mishi da" yau na tashi da jiri da amai da zazzab'i Abba ko tashi bana iya yi shine na nemi alfarman ba zan iya shiga kitchen ba yau amma yake ta min fad'a"

"Mene! Yana ina, ki bashi wayar in yana kusa" Abba ya karasa a d'an zafaffe.

Ina kif-kifta ido kaman da gaske nace " gashi nan Abba" tare da mika mishi wayan, sai a lokacin ya dawo hayyacin sa ya saka hannu ya karb'a yana min mugun kallo, ni kuwa ko a jikina saima murmushin mugunta dana bi shi da ita.

"Assalamu alaikum Abba barka da safiya" yace cikin sanyin murya.

" Wa'alaikum salam son me nake ji haka kada ka kasance cikin mazan da basa kyautatawa iyalin su mana kayi koyi da manzan Allah dan ya kasance mai kyautatawa iyalan sa,ko kaga haka muke da Momyn ka?" Bai iya bude ya bashi amsa sai girgiza kai da yayi kaman yana gaban Abban.

"Kada in kuma jin irin haka try to be a good husband ok, nd get something for her tayi breakfast". Insha Allah Abba" ya amsa cikin sanyin murya sannan ya katse kiran.

Ina jira inga ko zai hau kaina da wannan masifan nashi amma ga mamamki na sai ajiye min wayan yayi ba tare da yace komai ba ya fita daga dakin, murmushin nasara nayi tare da gyra kwanciya ta kan kujera na d'auko wayata na shiga watsApp.

Bayan fitan shi kaman da minti 30 sai gashi ya kara shigowa da sallama da wasu shopping bags a hannun shi ya ajiye min harda na pharmacy a ciki da alamu magani ya sayo.

"Ga breakfast dinki da drugs ki sha bayan kin gama nd pls next time in baki da lafiya let me know" yana gama magana ya fita, ni abin ma sai naji shi wani bambarakwai wai yau Zafar ne yake min magana a nitse babu tsawa harda wani pls? Hmmm tab na yarda da maganan Yasmin da tace yana bala'in tsoron Abban shi daga waya sau 1 har ya sauya.

But sai nake jin kaman ban kyauta ba da na had'a shi da mahaifin shi har yayi mishi fad'a, wani bangare na zuciya ta na kara ingizani cewa sai me ai shima lokacin da yake takura ni bai tausaya min ba.

Bud'e ledan eatary nayi naga manyan package na take away guda 2 na farko cike da chips da kwai sai na biyun kuma cike yake da pepped chicken sai kamshi suke ba b'ata lokaci na d'iba na fara ci ina zuba santi,sai da nayi nak sannan na tattara sauran na kai kitchen ban gan shi a parlorn ba ban kuma bi ta kan shi ba nazo na cigaba da charting na.

******************

Washe garin ranan da suka dawo daga wajan boka Gwaggo Aisha tasa Hajara wanka da sassafe ta shirya wai ta taho gida na su fara aiwatar da kudurin su tunda wuri, bata musa mata ba ta shirya tsab tayi kwalliyar ta cikin doguwar rigar ta na atampa daya amshe ta sosai,tana bari tayi breakfast kamin ta fita amma ta hana ta tace in azo nan gidana taci.

Haka ta fito wajan 8 da wani abu ba tayi nisa da gidan namu ba ta samu kwata ta jefa maganin a ciki tayi wucewar ta, bata son zuwa gidan da sassafe haka ta san duk yanda akayi kila ko farkawa daga bacci bamuyi ba, tunda ta shigo anguwan da nake ta fara jan kafa dan bata san kowa a anguwan ba da ta shiga ta dan ja lokaci har sai Zafar din ya fita kamin ta shigo.

Dole haka ta karaso kofar gidan tayi knocking mai gadi yazo ya bud'e mata kofan ta shigo daga ciki sannan ta gaishe shi cikin girmamawa da yake ya dan manyan ta, amsa mata yayi cikin kulawa kasancewar yaji dad'in yanda ta gaida shin.

"Dan Allah Baba masu gidan sun tashi kuwa?" Ta tambaya shi lokacin yana shirin komawa dakin shi.

"Gaskiya bana jin sun tashi dan sai kusan goma sannan muke kin motsin farkawan su" ya amsa mata.

" Toh dan Allah zan zauna a nan kamin su farka" tace tana nuna mishi wasu kujerun roba da suke can gefe cikin furanni.

"Toh toh shikenan ki zauna sai sun fito" yace yana shigewa dakin shi, karasawa tayi ga kujerun ta zauna tana ajiyar zuciya samun relief ta ciro wayar ta daga cikin jaka ta fara game dan ya rage mata zaman kad'aici, ya ko taimaka matan dan bata san lokacin da taja a wajan zaune ba hankalin ta duk yana kan wayan taji saukan ruwa kaman daga sama a jiki ta, a firgice ta mike tana " innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" a masifance ta juyo da niyyan ciwa wanda yayi mata wannan danyen aikin mutunci sai dai tana jiyowa idanun su suka sarke dana juna shima ya taho da niyyan bata hakuri saboda sam bai kula cewa da mutum a zaune a wajan ba domin kullum yazo haka zaiyi aikin shi ya koma ba tare da yaga wani na gidan ba gwara shi Zafar din sukan had'u wasu lokutan.

Da kyar ya samu bakin bata hakuri cikin sanyin muryan shi da ya zame masa jiki, sai a lokacin Hajaran ta dawo hayyacin ta ta janye idon ta akan shi a kunyace tare da ce mishi babu komai.

Ajiye tiwon hannun shi da yake bawa flowers ruwa dashi yayi cikin sauri ya koma can inda ya ajiye kayan shi wajan Baba mai gadi ya d'auko wani babban handkie ya dawo duk tana tsaye tana bin shi da ido yazo ya goge mata ruwan da ya jika kujera da take kai sannan ya dube ta wannan karon fuskar shi d'auke da murmushi yace " ki zauna Hajiya kiyi hakuri wallahi ban lura da mutum a wajan bane d z an kullum Ina zuwa aiki ban tab'a cin karo da wani a nan zaune ba shiyasa".

Zama tayi a hankali itama fuskar ta d'auke da murmushin tace " kada ka damu na san ba da gangan kayi ba, nima na zauna a nan ne kamin masu gidan su farka daga bacci, ba matsala ka cigaba da aikin ka nagode".

" Toh Hajiya nima nagode" yace yana komawa kan aikin shi sai dai tunda ya fara hankalin shi gaba daya yana kan ta haka itama ta kasa natsuwa hankalin ta kacokan yana kan shi sai kallon shi take ta kasan ido dan ba laifi shima kyakkyawa ne gashi da hasken sa dan yafi ta haske sosai.

Suna had'a ido sai su sakarwa juna murmushi a haka har ya kammala aikin shi ya dawo wajan ta yana ko ya taya ta zama ne tunda har yanzu da sauran lokaci, bata musa ba ta bashi dama ya zauna sai gashi suna hira kaman sun dad'e da sanin juna kamin Zafar ya fita har sunyi exchange na phone number tsakanin su.

Zafar ya fito zuwa gaishe da iyayen shi kaman yanda ya saba ya shiga mota ya wuce su sun ga fitowan shi Amma shi sam hankalin shi bai Kai kan su ba yaja motan shi ya fita bayan mai gadi ya bud'e mishi gate.

Koda Zafar ya fita sai da suka kara kusan minti 20 tare kamin su rabu ta samu daman shigowa cikin gidan a lokacin ni kuma na gama breakfast nazo nayi kwanciya ta naji salkamar ta, cikin ihun murna na fito na rungume ta zan iya cewa bayan yinin bakwai da akayi sai yau wani nawa yazo min dan haka cike da farincikin na tarbe ta ina tambayan ta Inna ta da mutanen gida tace min duk suna lafiya.

Bayan gama gaishe-gaishe na gabatar mata da sauran abincin da na rage ta fara ci muna hira cikin tsananin farincikin da kewar juna.

Shi kuwa Zafar tunda ya tafi gidan su hankalin shi na kaina dan ya kasa sakin jiki suyi hira kaman yanda suka saba, bini-bini sai kallon agogo yake har Abban shi ya gano shi yace" ya kamata ka tashi ka koma gida son dan my daughter tana bukatan kulawar ka musamman a halin da take ciki yanzu".

"Wani hali take ciki kuma?" Mom da tundazu taki saka baki a hiran nasu ta tambaya a d'an rikice.

"Ke kuwa ai zaki fimu sanin halin da take ciki tunda ke macece, yau ta tashi bata da lafiya wai tana fama da jiri da ciwon kai kinga alamun ciki sun bayyana a tare da ita amma fa a nawa hasasshen kenan ko kunje asibiti?" Abba ya amsa mata da wadatattacen murmushi saman fuskar shi yana kallon Zafar daya duke kai shima yana murmushin tare da girgizawa Abba kan shi.

"Ja'iri ji wani murmushi dan Allah Hajiya yaran yanzu da shegen son 'ya'ya suke" ya karasa yana dungure mishi Kai.

Mom da tayi suman zaune ko jin abinda yake fad'a ba tayi ba har yayi musu sallama ya fita ya bar ta baki bud'e.

Anan Kuma nida 'yar uwata sai hira muke zubawa yanda tun daga kofar shigowa zaka ji hayaniyar mu ba dan komai ba sai na labarin sabon saurayi da tayi na gidan mu take tana yayi mata amma tana gudun kada yaji ta tab'a aure da haihuwa ya guje ta...

Ni kuwa ina kara karfafa mata giwan cewa babu wanda zai kalle ta yace ta tab'a aure balle har ace ta haihu, muna cikin haka Zafar ya dawo gidan jiki a sanyaye amma tunda ya fara jiyo murya ta cike da nishadi muna hira yasa ya shigo da karfin shi, sallama yayi ya tsaya daga bakin kofa fuskar shi d'auke da tsantsan farincikin samu na a haka da yayi, bude min hannuwa yayi alamun inzo gare shi har zan watsa masa harara na tuna cewa ashe fa in a gaban mutane ne drama muke yi hakan yasa banyi musu ba na taso cikin wani yauki da ban san na iya shi ba na nufe shi tare da kashe da wani sexy smile.

Kafe ni yayi da ido ko kiftawa ba yayi yi har na iso gaban shi kaman zan shiga jikin shi sai na zille ina dariya nace" ga Yaya ta nan ku gaisa"

Shafa suman kan shi yayi da hannnu daya dayan hannun kuma yasa ya rike min hannu sannan ya kai duban shi ga Hajara da duk kunyan abinda ke faruwa ya rufe ta yace " babbar Yaya barka da zuwa" har da d'an risinawa kaman da gaske, cikin jin nauyi Hajara ta amsa suka gaisa duk yana rike da hannu na.

"Zo muje ki had'a min ruwan wanka wifey" yace yana kokarin jan hannu na zuwa parlor, tirjewa na fara kokarin yi tare da nuna mishi nayi bakuwa zan zauna wajan ta ya tafi kawai banyi aune ba naji ya d'aga ni cak in a bridal style yayi waje dani.

" Naji dadi sosai da nazo na same ki cikin koshin lafiya" yace yana bin ko ina na jiki na da kallo ,muna karasa fitowa parlorn na watsa mishi harara tare da kokarin sauka a jikin shi nace " Mallam kana over acting fa sauke ni dan Allah sai kace da wanda yake ganin mu a nan".

Cikin wani yanayi na sanyin jiki ya sauke ni kamin yace min wani abu na bar shi nan tsaye na shige kitchen nemawa Yaya ta abinda zata ci da rana , jiki a mace ya koma ya zauna tare da dafa kan shi tsakanin jiya da yau din nan bai san me yake damun shi he feels a different person.
[6/16, 9:22 PM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*43&44*

A wannan rana a nan parlourn ya yini kaman an dasa shi yana zaune sai kurb'an ruwa yake duk inda zan wuce kuwa sai yayi ta bina da ido kaman ya samu tv, ni dai ko kallo bai ishe ni ba dan yau wani tashen rashin mutunci nake ji dashi.

Sallah azahar kad'ai naga ya fita yayi a masallaci ya dawo a lokacin ni Kuma fitowa ta kenan daga kitchen hannu na d'auke da wani tray mai d'an girma da na d'aura kayan dad'i dana girkawa 'yar uwata, wuce shi nayi zuwa parlona inda na bar Hajara zaune tana kallo,nan tsakiyar parlour na ajiye na fita na had'o drinks masu sanyi a fridge na kara wucewa ta.

Ya d'an jima zaune wai ko zan dawo in kawo mishi rabon shi yaji shiru, murmushi yayi kawai tare da kad'a kai ya d'auki makullin mota ya fita ba jimawa sai gashi nan ya dawo da kaya niki-niki a hannu leda d'aya tak ya ajiye a parlorn ya wuce da sauran parlona ya same mu mun fara cin abincin muna hiran mu, ajiye kayan hannun sa yayi ya d'an kalle ni yace " pls ga kada ki manta da drugs d'in ki in kin gama cin abincin ki sha sannan ga fruits suma ki sha zaki ji dad'in bakin ki" gyad'a mishi kai kawai nayi ya juya ya fita yana waiwaye na.

"Zareefa gaskiya kinyi dacen miji nagari a wannan zamani da maza ba abinda suka iya sai wulakanta matan auren su, amma ki ga yanda yake tarairayen ki" cewar Hajara kenan, murmushi kawai nayi mata ba tere da na bata amsa ba na fara bud'e ledan fruits d'in a raina ina baki san waye shi bane har kike yabon sa.

A can main parlour kuwa Zafar zaune ya saka fried rice nd chicken daya sayo dan yaci amma ya kasa kwata-kwata bai fi spoon 3 yayi ba yaji abincin ya fita ran shi, tsaki yaja yana hararan inda muke bai san ya akayi haka ta faru ba daya saba da cin abinci na har baya iya cin wani abincin wani.

Kara kallon abincin yayi gashi dai so color full ya sha veggies amma sam bai ji wani taste ba a bakin shi,tattre su yayi ya ajiye a gefe ya sha fruits d'in daga baya duk ya kwashe su ya mikawa Baba mai gadi.

Har kusan la'asar muna tare da Hajara sannan tace zata koma amma zatayi kwana 2 a jere tana zuwa saboda akwai wani waje da Gwaggo Aisha take Aiken ta ita kuma bata son zuwa shiyasa zata rinka zuwa nan as ta tafi inda ta aike ta, ni kuwa cikin murna da jin dad'in zan samu mai taya ni hira har na kwana 2 na amsa mata da ina jiranta tazo da wuri.

Duk sauran kayan ciye-ciye da Zafar ya kawo ita na tarawa nace ta kaiwa su Ibrahim, ta amsa tana ta godiya na rako ta har bakin kofan main parlorn ta tafi.

Tana zuwa gida ta tarar da Gwaggo Aisha a tsakar gida tana jiran ta, ganin ta da manyan ledoji yasa ta fara washe baki domin taga alamun nasara a aikin bokan ta.

"Ya kika dad'e haka Hajara, kin gan ni nan tun d'azu nake zaman jiran ki" ta fad'a cikin d'aga murya yanda sauran 'yan gidan zasu ji.

Cikin kara fad'ad'a farar ta ta karaso gaban ta tare da ajiye kayan hannun ta murya kasa-kasa tace" gashi nan yace in kawo gida yana gaishe ki".

Wani irin shewa Gwaggo Aisha ta saka tana dariya tace" wannan duka yace ki kawo min lalle sirkin nawa ba wasa" murmushi kawai Hajara tayi ta shige ciki ta bar ta a nan sai bud'e su take d'aya bayan d'aya tana kara bud'a murya tana yabon kayan tare da yad'a habaici.

Dare nayi suna zaune suna hira da Gwaggo Aishan wayan ta ya fara ringing ganin number sabon saurayin ta ne yasa ta d'aga tana murmushi bayan sun gaisa yake ce mata bata ma tambayi sunan shi ba, nan itama tace ai ba sai ta tambaya ba shi ya kamata ya fad'a mata nan yace mata sunan shi Amadu.

Tashi tayi zuwa bedroom d'in su ganin Gwaggo Aisha ta ishe ta da waye ya kira ko Zafar ne? Da kai kawai ta amsa mata ta karasa shigewa daki ta barta tana ta murna.

*****************************

Da daddarem ma kin girkin girka komai nayi na kwanta Ina kallon wani series da nake matukar so a zee world ya shigo min da sallama na amsa mishi ciki-ciki kaman yanda shima ya min, tsaye yayi kaman me son cewa wani abu ko me neman wani abu ni dai bance mishi kala ba na mayar da hankali na kan tv.

"Ya jikin naki?" Naji muryan sa kaman daga sama.

" Na warke" na bashi amsa ba tare da na kalli inda yake ba.

Bai kara cewa komai ba ya fita nabi bayan shi da harara, a raina ina wa zai kara kula ka kaci zalin shi ko ka mishi mugunta da ka saba.

Shirin bacci na nayi bayan na gama kallon, na sha bacci cikin kwanciyar hankali sab'anin Zafar daya kwana cikin wani yanayi da shi kan shi ba zai ce ga inda ya dosa ba shi dai kawai so yake ya zauna kusa da ni ko kuma inda zai samu yayi ta kallo na, tun yana d'aukan abin da sauki har ya fara jin haushin kanshi wai me yasa ya damu da wani lamura nane? in ya kalle ni uban me zan bashi illa ma in b'ata mishi rai da sabon rashin kunya da na samo, bayan wannan ma tun lokacin da ya d'auke ni ya fito dani parlor jiki na da nashi da ya had'u yake kewar d'umin jiki na tare da kamshin jikina mai sanyi da tsayawa a rai sai dai dole ya matse gudun kada raini ya shiga tsakanin mu.

Ya san bakomai yasa ya damu da lamurana ba maybe tausayi na da ya fara jine kawai dan yaji bani da lafiya, " hakane ma" ya furta a sarari yana mai kara bawa kanshi karfin guiwa da kyar dai ya samu bacci yayi nasaran sace shi a wannan daren.

Da washe gari na tashi da sauki dan wannan nauyin da zuciya ta yayi jiya yayi sauki hakan ne ya bani daman fara aiyuka na kaman yanda na saba, bayan na gama share ko ina tass na gyara sannan na shiga wanka ban dad'e ba na fito light make-up nayiwa fuskata na shirya kaina cikin English wears riga da skirt pink color anyi mishi ado da flowers blue hakan yasa na yane kai na da blue vail, kayan bai wani matse ni ba amma ya zauna das a jikina ya min kyau sosai.

Zagewa nayi ina girki sanin cewa Hajara zata iya zuwa at any moment,kayan dad'i nake dafawa dan haka gidan ya cika da kamshi masu dad'in shaka,kamshin nan shi ya fito da Zafar daga d'akin shi sai bud'e hanci yake yana lumshe ido tsohon yunwar shi ta jiya na dawowa sabo fil.

Kofar kitchen d'in yazo ya tsaya yana kallon yanda nake aiki gaba daya hankalina yana kan aiki ban san ma da zuwan shi ba,shi kuma controlling d'in kan shi yake akan abinda zuciyar shi take ingiza shi ya aikata dan ji yake kaman yaje ya rungume ni yaji wannan d'umin jikin nawa da wannan daddadan kamshin mai sanyaya zuciya amma ya daure yayi gyaran murya Wanda ya d'an firgitani na juyo a d'an razane na ganshi tsaye cikin kayan baccin sa farare kal da alamu tashin sa kenan ko wanka baiyi ba.

Kaman ana min dole nace mishi" Ina kwana" saboda ganin babu wasa a fuskar shi, maimakon ya amsa min sai cewa yayi " ki tabbata kinyi da rabon masu aiki tunda kin samu lafiya" sai da na turo baki sannan na bashi amsa da cewa " ni bada su nayi ba dan Hajara zata zone shiyasa nayi girkin".

Kara had'a fuska yayi yace" try anything stupid and see"Yana gama fada ya juya ya fita ba tare da ya jira amsa ta ba, " zaka gani kuwa ai ka daina cin abinci na a gidan nan tunda kai d'an wulakanci ne"nace ina cigaba da aiki na.

Bayan kaman 30 minutes na kammala komai na jera su kan try na fito na wuce parlour na ba tare da nabi ta kan shi da na gan shi zaune a main parlour ba, shirya su nayi anan tsakiyar parlour na tare da kara saka turaren wuta na dawo inda na shirya kayan abincin kenan sai gashi nan ya shigo da fuska kaman an aiko mishi da sakon mutuwa.

"Ina na masu aikin da na gaya miki?"
"Banyi dasu ba na amsa mishi ina kara gyara zamana a gaban warmers d'in, bai saurare ni ba direct kai tsaye ya karasa shigowa da niyyan zai d'auke warmer d'aya, cikin azama na kai hannaye na duka biyu na rungume su a kirjina tare da turo baki ina " ni wallahi ka bar min kayana".

Bai saurare ni ba yana zuwa yasa hannu ya d'agani cid'ak kaman wata karamar yarinya zai ajiye ni a gefe na rike shi gam ina "wallahi ba zaka d'auka min ba ni banyi da rabon ka ai na san cewa kai kake cinyewa ba wasu masu aiki da kake bawa".

Yanayin yanda na cukuikuye shi na rike sai ya haifar mishi da kasala kuma dama abinda tun jiya zuciyar shi ta kwad'aitu da shi kenan,da gangan yayi fara kiciniyan kwace kan shi ni kuma ina kara rike shi akan ba zai d'auka ba kan kace me kokuwa ya kaure tsakanin mu anan yayi amfani da wannan daman hannayen sa babu inda basu je ba a jiki na, ni kuma a hauka na ban kawo komai a raina ba na zata duk cikin kokarin kwace kan shi yake a hannu na.

Sallaman Hajara ne yasaka shi saki na cikin sauri ya tashi itama Hajara cikin sauri tayi hanyan parlour dan tunanin ta wani abu daban ya bata, murmushin mugunta shimfid'e a fuskar shi yace " ga tsaraba nan kin tari yayar ki dashi,sai ki san bayanin da zaki mata "sai a lokacin na fahimci abinda ya faru duk sai naji kunya ya rufe ni me ko zan cewa Hajara ai babu abinda zan fada in wanke kaina,dafe kaina nayi cike da takaicin abinda ya faru tare da dana sanin me yasa na biye shi dana sani da barin shi nayi ya d'auki abinda yake so.

Plate ya d'auka ya bud'e warmers d'in ya d'ebi abinda yake so ya fita abin shi ba tare da na sani ba domin nayi nisa cikin tunani,ita kuma Hajara bata tsaya a main parlour ba direct fita tayi ta zauna a inda ta zauna jiya tare da dafe kai duk Gwaggo Aisha taja mata wannan abin kunyan asuban fari ta taso ta kan ta shirya tazo kada ya fita aikin su ya koma baya.

Hankalin shi kwance yaci abincin sa yana ta sakin murmushi shi kad'ai kaman wani sabon kamu,he really enjoys what happened between us now, fitowa nayi main parlour ganin zaman ba zai fice ni ba .

Wani tukikin bakin ciki ne naji ya tokare min wuya ganin yana ci min abinci,duddubawa nayi ko zanga Hajara amma ko alamarta ban gani ba.

Komawa nayi cikin Ina ta kumbura saboda haushi na san kila ta koma gida shikenan ya rusa mana budget ina ta murna yau ma zamu yini muna shan hiran mu sai gashi ko gaisawa bamuyi ba ya kore ta.

Zaman ta kaman da 15 minutes sai ga Amadu yazo yin aikin sa, maimakon yayi aikin suka bige da hirar su cike da son junan su har Zafar yazo ya wuce da mota bai gama aikin ba ganin sa ne yasa ya maida hankali kan aikin sa,tana zaune ya kammala itama ta mike tace zata koma gida tare suka fito ya rako ta har gida sannan suka rabu cike da kewan juna.

Baba Yana zaune a majalisar shi tare da 'yan maula daya samu yana d'an miko musu da na cefane,daga nesa suka hango motocin sojoji har guda 2 sun nufo su, Baba Yana ganin su cikin sa ya murd'a ya mike jiki na b'ari yace "yau kuma me ya kawo wa'yan nan azzaluman cikin anguwan nan" yana magana ne yana nufan hanyan gida amma ko ten step baiyi ba motocin suka karaso tun kamin motan ya tsaya suka fara durowa daga ciki tare d'aga musu tsawa "kada wanda ya motsa daga nan".

Cak Baba ya tsaya yana tsiyayen gumi duk ya firgice.

"Waye Mallam Hassan a cikin ku?" Suka tambaya.

A tare mutanen wajan suka nuna baban mu da yake tsaye yana karkarwa.

"Kai ne Mallam Hassan ?" Kai kawai Baba ya iya gyad'a musu.

" Common my friend oya! oya! shiga mota mu tafi"wani daga cikin motan ya fad'a, wasu guda hud'u nufo shi fuska a murtuke babu alaman sun tab'a koda murmushi balle dariya, hannu Baba ya shimfid'a yana kokarin rokon su tare da basu hakuri , d'ayan ya d'aga katon bindigan hannun shi yace yana musu gardama wallahi zasu harbe shi a wajan su wuce kuma sun harbe banza.

Gudu-gudu Baba ya nufi wata bakar mota da sai yanzu ya lura da ita suka hankad'a shi ciki babu b'ata lokaci suka fice daga anguwan da matukar gudu.

" Allah ya kiyaye mu da basu d'ubi kowa daga cikin mu ba sai shi kad'ai suka nema" inji wani dattajo cikin 'yan zaaman majalisan.

"Ni dama wannan kud'i na Mallam Hassan akwai ayar tambaya ace mutum yayi kud'i lokaci d'aya"? Wani ma ya kara nashi.

" Ai ko yanda suka ciko motoci saboda shi kad'ai kuma kun san abin azimun ne"

" Kunga yanzu ba lokacin wannan bane mu watse kamin su canza ra'ayi su dawo su had'a da mu"

fad'an hakan ke da wuya duk suka watse cikin abinda bai fi kiftawar ido ba, nan da nan labari ya cika anguwa cewa sojoji sun kama Baba sun tafi dashi.
[12/14/2021, 7:54 AM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*45&46*

A guje Ibrahim ya shigo gida har yana fad'uwa kasa Inna da take tsakar gida ta nufo shi tare da d'aga shi tana karkad'e mishi jiki tace " toh d'an tsokana wa ka tsokano ya biyo ka, ka shigo a guje haka?"

Yana haki irin na alamun ya sha gudu yace yana nuna mata kofan waje " Baba ne..... Baba ne sojoji suka tafi dashi".

"Wani Baban kuma Ibrahim"?" Ta tambaya cikin rashin fahimta.

"Baban mu, Baban mu na gidan nan" ya amsa mata tare da fara kuka.

Salati Inna ta fara tana tafa hannu cikin tashin hankali murya na rawa ta d'aga murya tana " kuna ina matan gidan ku fito dan Allah kuji abinda yaron nan yake fad'a"

Inna Asabe ce ta fito da gudu har tana tuntube bakin ta d'auke da salati itama nan suka kacame dasu da sauran yaran suna ta cacekuce dan sun rasa ta ina zasu fara kasancewar kowa ya san harkan sojoji wuyan sha'ani ne dashi a nan maiduguri.

Duk hayaniyar nan daya cika gidan mu har makota sun shigo 'yan jin gulma da da masoyan gaske ana ta jajantawa amma gwaggo Aisha bata leko ba balle asan tana gidan ko bata nan a wannan yanayin Baban Dije ya shigo shima hankali tashe amma ganin su Inna a wannan yanayin yasa yayi kokarin boye nashi tashin hankalin ya shiga kwantar musu da hankali kan cewa kada su tada hankalin su su bi komai a sannu insha Allah Baba zai dawo gida tunda ko makiyin sa zai bada shaida akan sa baya aikata wani mummunan abu shi dai bar shi da son kud'i.

Da wannan bayanan ya samu suka d'an natsu kowacce ta koma daki makota kuma suka koma gudajen su da addu'an Allah ya sauwaka.

Hankali tashe Hajara tayi sallama ta shiga cikin gida dan saukowan ta kenan daga napep 'yan suka tare ta da mummunan labarin nan, ganin babu kowa a tsakar gidan yasa ta nufi d'akin su tana kwad'awa Gwaggo Aisha kira kaman zata tsaga gidan amma bata ji muryan ta amsa mata ba, a zaton ta bata gidan ta fita ko sun fita da sauran matan gidan.

Turus tayi fuskarta cike da al'ajabi ganin mahaifiyar nata kishingid'e tana cin gyad'a mai gishiri hankali kwance, d'ago kai tayi ta kalle ta sannan tace meya faru kike ta kwala min kira kaman zaki tsaga gidan nan ko dai yauma kin zo min da labari me dad'i ne?"

Had'iye mamakinta tayi tace umma ni ba dan wannan nake kiran ki ba yanzu ina saukowa a napep naji ana ta kananan maganganu a anguwa wai sojoji har mota 2 sun zo sun tafi da Baban mu?"

Tab'e baki tayi tare da watsa gyad'an hannun ta a baki ta fara taunawa tana hararan ta tace" toh sai akayi me ko ni na aike shi yin mummunan aikin da zasu kama shin, kema kin san Baban ku da shegen son kud'i kinga kuwa wani ta'asan yaje yayi musu, tsuntsun da yaja ruwa shi ruwan zai doka".

Tunda ta fara magana Hajara take kallon ta cike da takaicin abinda take fad'a wai Baban mu ne mayen kud'i, toh ita fa in banda ance laifi tudu ne yanzu bata ganin laifin munanan ayyuka da take sai na Baban mu wanda ta tabbata da wata akasa dan bai aikata abinda mutane suke cewa ba.

"Ke ina tambayan ki kin min shiru, nace dai yauma aikin ya tafi yanda ya kamata ko?" Ta katse ta cikin tsawa.

Gyad'a mata kai kwai tayi dan wani malolon bakinciki ne yazo ya tokare mata wuya, washe hakora tayi cike da farin ciki tana ," Alhamdulillah hankali na ya kwanta amma ya ban ganki da kaya irin na jiya ba, saboda na saka rai zaki kawo mana kayan dad'i ko girki ban daura ba na zauna jiran ki".

Daki kawai ta nufa ta san in ta tsaya takaici ne zai kashe ta, saida ta kusan shiga daki sannan tace mata " mahaifiyar shi ta kira shi ya tafi"

"Uwar shi? Dan uwar shi ta kira sai ya tafi ya bar ki, lalle muna da sauran aiki a gaban mu dole ne mu raba shi da ita in ba haka ba zata kawo mana barazana cikin aikin mu".ta fad'a a masifance ita dai Hajara bata kara kula ta ba ta ida shigewa ta bar ta da kumfan baki.

***************************

Tunda Hajara ta tafi ban kara jin motsin sa ba ina ciki duk haushi ya ishe ni sai kunci nake ni kad'ai, koda naga zaman kuncin ba zai fishe ni ba fitowa nayi na kama dan aikace-aikace na ko zan ragewa kaina damuwa, cikin ikon Allah ko Ina farawa na mance da abinda ya faru.

Kitchen na shiga na had'a kayan da b'ata ina wankewa naji a jiki na alamun ana kallo na da sauri na waiwaya na gan shi tsaye yana karewa baya na kallo, yana ganin na juyo ya basar yayi kaman yanzu ne zuwan shi, karasa shigowa yayi cikin kitchen din ya bud'e fridge ya d'auko malt mai sanyi ya koma bakin kitchen din ya bud'e ya fara sha.

Ban kara juyowa ba amma ji nake kaman na juya nayi ta kallon shi dan ba karamin kyau yayi min ba, kama gulman shi nayi a cikin zuciya ta ina mutum kaman wani aljani ko wani Kaya ya saka sai yayi mishi kyau dubi dai singlet ne da 3 quater a jikin shi amma sai ya zama kaman wani dressing yayi na gani na fad'a ga kamshin sa kuwa duk inda zai je kamin ya isa kamshin ya riga shi isowa haka kuma ko ya tafi zai dad'e a wajan.

Ta kasan ido na kara kallon shi yana tsaye a inda yake bai motsa ba gashi ni kuma na gama wanke-wanken ina son fita amma na rasa yanda zanyi saboda duk ya tare hanya yayi bake-bake babu wajan wucewa ni kuwa bana son yi mishi magana dan har yanzu haushin shi nake ji.

Wasu ayyukan na shiga kirkira wai ko zai gaji ya bar hanyan amma saima gani nayi ya gyra tsayuwar shi ya jingina da kitchen cabinet din ya cigaba da kurb'an malt din yana kara tsare ni da ido, gajiya nayi da kirkire kirkiren nayi shahada na nufo kofan wai ko in yaga nayi niyyan fitan zai bani hanya amma ga mamakina ko motsawa baiyi ba balle ya matsa.

"Zan wuce" nace ba tare da na kalle shi ba.

"waya hana ki wucewa?" Yace shima yana wani d'aure fuska " naga ka tare hanya ne"...

Dan matsawa yayi gefe ya bar wani karamin hanya,ta gefen ido na kalle shi naga har yanzu yana rike da malt din a rai na ina mamakin wani irin kurb'a ce yake mata tun dazu ace bai kare ba, sauke ido na nayi cikin sauri nazo zan wuce amma sai yasa hannun shi na dama ya tare hanya.

Dawowa nayi da baya zan koma kitchen d'in nan ma ya jefar da empty tin na malt din ya kara tare min hanya ya zamto ina tsakiya hannayen shi ya zuba min wayan idon shi mai rikitar dani, cikin azama nayi kasa da nawa idon dan ba zan iya jure kallon nashi ba.

"Da kike wani neman guduwa cinye ki zanyi?" Ya tambaya cikin wani irin murya da ban san yana da ita ba, ban iya bashi amsa ba na kara yin kasa da kaina, ina jin yanda zuciya ta take zillo kaman zata fito saboda kusancin namu yayi yawa.

"Hmmm na gane duka gulma ne u just want me to repeat what we did in d morning" yace yana bina da wani irin killer smile.

Cikin zaro ido na d'ago kai na da niyyan yi mishi masifan sharri daya lak'a min amma mukut na had'iye kaya na saima zaro ido da nashiga yi sakamon tattausan bakin shi da naji akan nawa.

Kiciniyar kwace kaina nake amma bai bani daman hakan ba, sai kara manne min yake tun inada karfin kokuwa har karfi na ya kare wani irin kasala na sauko min tare da hawaye kaman an bud'e famfo.

Jin hannuwan shi sun fara min yawo a jiki yasa na tattara sauran courage daya rage min na ture shi ya kuwa tafi da baya har yana bigewa da cabinet din bayan shi ni dai ban juyo ba balle in san halin da yake ciki na fad'a daki tare da rufo kofa na jingina ina maida numfashi.

"Ouch " yace yana rike bayan shi inda ya bugun ya shafawa yana murmushi tare da jin kaman ya bini ,shi dai wannan sabon jaraba daya same shi a kaina bai tab'a shiga irin wannan yanayin ba dan ko lokacin da yake karatu a kasar waje ga dai mata birjik suna yawo half nacked wasu har tallahn kan su suke kawo mishi amma koda wasa bai tab'a jin kwatancin abinda yake ji game dani ba akan su.

"Why! Why her?" Ya furta can kasan makoshi ganin babu mai bashi amsa yasa ya koma cikin parlour ya zauna ya dafe kai yana neman mafita.

Na dad'e jingine da jikin kofan ido na rufe ina wani irin murmushi da yake fitowa daga karkashin zuciya ta, me ya faru tsakanin mu yanzu? Na tambayi kaina.

"He just kissed me" nacewa kaina ina rufe fuskata da tafin hannaye na duka biyu ina kara fad'ad'a murmushin da nake saboda ina ayyanawa a raina cewa yana sona, yes yana sona in ba haka babu abinda zai saka yayi kissing na.

"BA SONKI NAKE BA, ZAN AURE KI NE DAN IN KAUCEWA AUREN DA ABBA NA YAKE SON YI MIN....."

Hannuwana na saka na toshe kunnuwa na dasu saboda yanda nake jin wa'yan nan munanan kalamai suna min amsa kuwwa a kunne na kaman an kawo loudspeaker saitin kunne na ana min magana dashi.

Girgiza kai na na fara yi Ina hawaye kada in yaudari kaina Zafar ba zai tab'a so na ba yasha furta min haka da bakin sa sannan ya tabbatar min da ba zai tab'a sona ba zai sake ni ne in time din alkawarin mu yayi.

Na tabbata yanzun ma haka take kawai ya tsiro da wata dabara ce yanda zai yaudare ni ya gama dani kamin mu rabu , dole ne inyi taka tsantsan domin tsira da mutunci na duk da yanzu ni da Kai na na fahimci na fada son shi ba na wasa ba kuwa.

Bedroom na wuce jiki a mace na zauna bakin gado hawaye na suna kara speed din gudun su inayi ina jin haushin kaina ko meye abin damuwa da wanda bai damu da Kai ba, na kan shiga mummunan tashin hankali in na tuna cewa zai iya rabuwa dani a koda yaushe dan ji nake kaman ba zan iya rayuwa babu shi ba.

Sai da naci kuka na koshi sannan na mike na shiga wanka, na dad'e a sosai ina wankan sannan na fito d'aure da towel wanda ko cinya ta bai ida rufewa ba tsefaffen gashin kaina da na wanke ya kwanto baya na ruwa na tsiyaya, direct mirror na nufa na ja stool na zauna tare da jona hand dryer na fara busar da gashi na.

Sai da ya fara bushewa na ajiye dryer na dauko mayukan gashi na shafa sannan na taje na saka rebon na tufke in pony tail kokarin kunche towel na fara domin inji dad'in shafa mai kaman wani abu yace juya baya ina juyawa muka had'a ido da mutum zaune akan gado na ya tsura min ido kaman zai cinye ni d'anye.

A zabure na mike da gudu zuwa bayi naga shima ya mike zai bini , haba kaman walkiya na shige na mayar da kofa na kulle harda murza key zuciya ta na harbawa da sauri-sauri.

Knocking ya fara yi a hankali yana " pls ki bude Zareefa ba abinda zanyi miki magana nake so muyi kinji?" Naji muryan shi cikin sanyin yana roko na.

Girgiza kai na kawai nake girgizawa kaman yana gani na baki na ya kasa furta komai dan na riga na gano abinda yake nufi ni kuma ba zan tab'a bari yayi min wayo ba haka kawai.

"Zareefa pls listen to me dan Allah ki bud'e kinji?" Nan ma shirun nayi mishi na kasa gaskata kunnuwa na wai yau wannan dan girman kan ne yake roko na harda sassauta murya jin suna na a bakin shi yasa naji kaman in fito inje gare shi saboda ban tab'a jin dad'in sunan nawa ba kaman a bakin shi.

Sai zuciya ta na kara gargadi na akan kar na biye shi duk salon yaudara be, hmmm maza kenan gaskiya sun kware a yaudara ina ma da gaske ya sauko ne muyi zaman mu.

Hakan da na saka a raina naji sabon kuka ya zo min anan na durkushe inayi ina jinsa yana ta min magiya da knocking amma ban amsa mishi ba har ya gaji ya bar wajan.

********************

Baban mu koda suka saka shi a wannan bakar mota sai da suka rufe mishi ido da wani bakin kyalle sannan suka d'auki hanya a cikin motan ma duk da idon shi a rufe yake amma sai rokon su yake yana basu hakuri, bige mishi baki da wani daga cikin sojojin yayi da gindin bindiga yasa Baba yin shiru bai kara yin koda tari ba balle ya Kara gigin magana sai faman tare jinin da yake zuba a bakin shi yake yana jin zugin tsakiyar kan shi.

Sunyi tafiya mai d'an nisa sannnan yaji sun tsaya duk suka fito shima fito dashi sukayi suna Jan shi dan har yanzu basu bud'e mishi idanun nashi ba.

Sunyi tafi mai nisa yana ta jin iface-ifacen mutane da hayaniya kala-kala har yaji sun iso wani waje shiru babu wani motsi balle muryan mutum, nan sun yi tafiya sosai sannan yaji sun tsaya a wani waje yana ji suka bud'e wani kofan karfe suka ingiza shi ciki sannan suka kunce mishi ido kamin ya dawo daidai yaji sun rufe kofan ta waje.

Wajen baki kirin take ko tafin hannun shi baya iya gani balle ya san a ina yake, shiru yayi ya zauna cikin wani yanayi mai wuyan fassara shi dai ya san shida fita a cikin wannan duhun sai ta Allah.
[12/14/2021, 7:54 AM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*49&50*

Yawo ya dinga yi a motan nashi yaki komawa gida saboda shine zaman lafiyan shi gashi bai san waye kuma zai tunkara da maganan nan yaji sauki ba shi Sadeeq da ya san sirrin shi ma bai bashi goyon baya ba to ina zai je?

A wani karamin masallaci daya gani ya tsaya yayi sallahn mariba da aka kira bai tashi ba yana nan yana kai kukan shi ga Allah kan yaye mishi wannan sabon al'amari da yake ji game da ni, gashi a dalilin baya iya controlling kan shi har raini ya fara shiga tsakanin mu, ji yanda d'azu na tsaya ina mishi tsawa for god sake this village girl? Yace cikin ran shi.

Jiki a mace ya fito daga masallacin tare da addu'an Allah ya amsa mishi addu'oin da yayi, mota ya shiga maimakon yayi hanyan gidan shi direct hanyan main house d'in su ya mika horn d'aya kawai yayi mai gadi yazo ya bud'e mishi gate ya kutsa kai cikin gidan nasu.

Abba da Mom suna zaune a tsakiyar parlour da alamu basu dad'e da gama cin abinci ba domin ya tarar Mom sai aikin had'a kayan da suka b'ata take, kusa da Abba ya zauna tare da daura kan shi akan kafadan Abba sannan ya fara gaishe su.

Mom ma dakatawa tayi da aikin da take ta amsa mishi cikin kulawa sannan ta kwashi kayan tayi hanyan kitchen, Abba na ganin Mom ta bar wajan ya juyo ga tilon dan nashi da kyau yana shafa kan shi yace " ya akayi ne son naga duk yanayin ka ya canza?"

Salon da Abba yayi amfani dashi yayi mishi magana yasa yaji hawaye na taruwa a idon shi amma ya shanye tare da kakaro murmushi ya daura kan fuskar shi yace" bakomai Abba"

"Ni mahaifin ka ne Zafar na san yanayin kana cikin damuwa da kuma na farinciki, ba zan tilasta maka sai naji abinda yake damunka ba but ka sani in aka ce maka kana da iyali dole sai kayi hakuri da kai zuciya nesa domin mata da kake gani akwai su da rauni manzon Allah yace da kashin hakarkari aka hallice su, kaga kuwa a lankwashe suke in kace zaka mikar da karfin tsiya sai dai ka karya so kabi komai a sannu. Kaji ko?" Abba ya karasa yana shafa gashin kan shi.

Murmushi yayi yana gyadawa Abba kai dan ya san Abba bai san matsalar da take damun shi bane, yanda ya fahimci abin daban ne, a haka Mom ta dawo ta same su ta zauna akan kujeran dake opposite da inda suke zaune idonta akan su tace" me Baba da yaro suke tattaunawa ne?"

" Shagwab'a ke damun yaron naki, kin riga da kin shagwab'a shi tun farko gashi ya girma harda iyali bai san ya girma ba" Abba ya amsa mata yana dungure kan Zafar.

Hannu ta mika mishi tana " come here my boy ai yaro baya girma a gaban maman shi" da rarrafe ya karasa wajan kafan ta ya zauna tare da daura kan shi akan guiwar ta.

"Yi shagwab'ar ka yanda kake so d'ana ko akwai wani abu da kake bukata ne?" Rungume kafaun nata yayi ya girgiza mata kai, dariya ta saka tana "lalle yau yan shagwab'an na kusa kuwa".

Abba ma dariyan yayi suka fara consoling d'in d'an nasu tare da yi mishi hira mai dad'i har ya wassake ya fara dariya harda kyakyatawa, damuwan dake ran shi kusan kashi 70 ya ragu sai kusan karfe tara sannan yace zai tafi gida yayi musu sallama ya fito ya shiga motan shi ya nufi gida.

Yana nufo gida damuwar shi da yaji ya d'an ragu yaji ya dawo sabo , ji yayi kaman ya fasa shiga gidan ya koma amma haka nan ya daure ya shiga saboda ya san rashin shigan ba shine mafita ba, koda yayi parking ya d'an dad'e zaune a cikin motan tare da daura kan shi jikin staryn yana neman mafita.

Ya jima a haka sannan ya hakura ya mike jiki ba kwari ya nufi cikin gida.

Ni kuwa tunda ya fita nake kuka wanda nima ban san dalilin shi ba amma can kasan zuciya ta soyayyar shi ce dankare a ciki yana dawainiya dani hakan yasa kowani irin hali ya shiga sai naji dumbin tausayin shi tare da jin zan iya taimaka mishi ta kowani hali dan ya samu farinciki.

Sabon yanayin da nake ganin shi ciki yana matukar damuna duk da wani b'angare na zuciya ta yana tunasar dani cewa yaudara ce sai nake kokarin karyatawa, har aka Kira sallah mariba bai dawo ba.

Ina zaune akan sallaya bayan na idar da sallah magriba ina jiran inji shigowan shi amma shiru gaba daya hankalina yayi kan shi domin ko lokacin da muke 'yar tsama dashi ya kan shigo da yamma sai bayan anyi sallah sannan in zai fitan ma ya kara fitan, gaba daya hankalina yana kan shi na kasa natsuwa I was so restless sai kallon agogo nake.

Jin an fara kiran sallahn isha'i yasa na tashi nayi sallah harda shafa'i da wutri but na kasa mikewa wa akan sallaya sai kara kallon agogo nake Ina jin kaman in fita in nemo shi zuciya ta sai kara ingizani take akan in sassauta muyi zaman mu tunda abinda nake buri kenan nima tunda shima duk girman kanshi ya sauke yana bi na harda roko.

Gajiya nayi da zaman na tashi na shiga wanka Ina fitowa na kama shirn bacci riga da wando na saka na wani yadi mai tsanti rigan da botira a gaban, gashi na kuwa tattare su nayi parking a tsakiyan kai na shafa humra na da aka ce min sai zan kwanta in rinka shafawa, na kuwa bulbulawa shi a jikina domin nima sosai kamshin sa da sanyin sa take tsaya min a rai.

Wutan d'akin na kashe na bar dim light bayan na hau gado ina ta sake-sake a zuciya ta har bacci yayi nasaran sace ni.

Zafar a nutse ya shigo gidan without making any noise ya shige d'akin shi ya rufe kofa ya zauna akan couch dake d'akin na wani lokaci yana tunanin anya yayi abinda yaji zuciyar shi take ingiza shi yi ko Kuma ya bari yabi komai a sannu?.

Haka ya hakura ya tashi ya shiga wanka ba tare da ya tsaida wani mataki da zai d'auka ba, wanka yayi with his bath gels masu bala'in kamshi ya fito ya shirya cikin singlet da boxers sabbi Kuma farare kal ya fesa body perfumes sannan ya shige cikin bargo tare da fatan Allah yasa yayi bacci da wuri ko zuciyar shi zata huta da wannan sabon al'amarin.

Rage karfin Ac yayi dan wani sanyi yake ji duk da yana cikin bargo, figigit ya bud'e idon shi domin yana lumshe ido da niyan bacci fuskata ya fara cin karo dashi ina dariya.

Tashi yayi zaune ya saka hannun sa cikin lallausan gashin kan shi Yana yamutsawa tare da rutse idon da karfin gaske domin yanda yake jin wani abu yana fisgar shi, yama rasa ya zaiyi da rayuwar shi.

Ya kai good 40 mins a haka tsam ya mike kaman wqnda aka tsikare shi da allura ya fita, kai tsaye d'aki na ya nufo dan a yanda yake jin shin nan gwara ayi ta ta kare dan in ya cigaba da zama a haka kila zuciyar shi ce zata buga.

A hankali ya turo kofan ya shigo yana tafiya a hankali cikin hasken dim light da ban kashe ba,yana hango ni cikin bargo da alamu bacci nake a hankali ya karaso ya tsaya ta wajan fuskana yana kare min kallo yanda nake bacci na cikin kwanciyar wanda shi ya gagare shi cikin kwana 2 nan.

Durkusawa yayi a gaban gadon yana mai cigaba da kallon fuskata kaman mai neman wani abu akai, wani masifan kyau yaga ina yi mishi ya fara kallo tundaga goshina da kananan gashi ke kwance kaman na jarirai har zuwa kan ido na da eye lashes suke a mike kaman wacce ta Kara da na kanti, hanci na da yayiwa fuskata kyau shima yabi da kallo ji yake kaman ya lashe ni.

Cak idon shi ya tsaya kan tsukakken lips d'ina da suke pink gwanin sha'awa bai san lokacin da ya duka a hankali ya min light kiss ba ganin na dan motsa yasa ya dan ja baya kad'an ya tsaya na wasu seconds yana kallo na yana jin yanda zuciyar shi take ingiza shi kan ya hau gadon ya rungumo ni ya saka ni a jikin sa.

Samun kanshi yayi da zagayawa ya haura kan gadon ta dayan side d'in a hankali kaman mai tsoron gadon.

Cikin tsanda ya daga bargon ya shiga ya lulluba shima yana kallon baya na so yake ya manna ni a jikin shi amma yana gudun kada in farka in kore shi yasa ya kwanta shiru yana sauke ajiyan zuciyan samun relief na ya kasance kusa dani.

Sai dai me ko cikakken minti 2 baiyi ba wannan fitinannen kamshin ya fara ruguza mishi lissafi ya fara manta a ina yake shi dai burin shi ya jini a jikin shi yana shak'an wannan daddadn kamshin mai tada hankalin ko wani lafiyayyen namiji daya shaka.

Cikin fitan hayyaci ya fara shashhafa duk inda hannu shi ya kai a jikina tare da kissing duk inda bakin shi ya kai yana shinshina ni kaman wani maye, cikin bacci na rinka jin bak'on al'amari mai rikitarwa da farko na zata a mafarki ne dan haka gyara kwanciya nayi na bashi access mai kyau yanda zai ji dad'in sarrafani.

Shi kuwa ganin haka yasa ya kara kaimi dan ya zata ido na 2, kwanciya da na gyara yasa botiran gaban riga na wasu suka bud'e har ana iya hango farin fatan jiki na da kuma kirji na a sarari, wani irin wahalallen numfashi yaja ya sauke yana kare musu kallo , damka da yayi musu na fitan hankali yasa na bud'e ido na babu shiri.

Mutum na gani mak'ale dani sai wasu abubuwa take min wanda suka girmi tunani na, kara na saka na ture shi da dukkan karfi na sannan na wani irin hansulowa na koma can karshen gado na kankame jikina Ina karkarwa tare da hawaye da suka fara ambaliya kaman an bud'e famfo.

Rub da ciki ya kwanta yana maida numfashi kaman wanda yake jinya idon shi kuwa a kulle suke gam, bai min magana ba nima banyi mishi ba sai kuka na da nake yanzu harda shasshek'a, munfi minti 5 a haka sannan ya yunkura da kyar ya tashi zaune ya d'ago idanun shi da sukayi wani masifan ja yana kallo na sannan ya bud'i baki da kyar ya fara magana da muryan shi da bata fita sosai.

"Meye haka wai, ya kamata ki tsaya ki nutsu muyi magana yau kwana nawa Ina binki muyi magana amma kin ki sauraro na at least ya kamata ki bani dama ko?" Ya dan yi shiru yana jiran in bashi amsa yaga ko dagowa banyi ba balle in bashi amsa hakan yasa ya cigaba da magana.

"Na san abinda nake miki kwana 2 nan baya cikin agreement d'in da mukayi tun farko, but ba yanda zanyi ne saboda its beyond my control , abinda nake ji akan ki ban tab'a jin shi akan kowacce mace ba anytime I feel like..... Huuuh no need to explain everything to you" yace yana shafa goshin shi.

" But abinda nake so dake just name any amount da kike ganin zai miki ni Kuma nayi miki alkawari zan ninka miki duk abinda kika bukata, just once ki yarda in kasance dake sau d'aya tak kawai besides ba zina muka aikata ba kin ga time da mukayi alkawari ya kusa I can let u go sai in nemi luv of my life, so ya kika ce?"

Tunda ya fara magana na tsaida kukana thinking of Allah ya amsa addu'an na hasashe na ya zama gaskiya kan shima ya fara sona, sai dai me kalaman sa na karshe su suka kusa tarwatsa min zuciya, dama nima yaudaran kai na nake tayaya mutumin da ya sha nanata min baya so na zai soni rana tsaka?......

Gutun hawaye da suke fuska ta na goge ina kallon shi da murmushi akan fuska nace " do you think I'm that so cheap da har kake ganin kana da dukiyan da zaka bani dan kasancewa dani...... Ni ZAREEFA" girgiza kai na nayi ina hana hawaye na zubowa na cigaba " a duk fad'in duniyan nan babu mai wannan dukiyar da har zai iya sayan martaba ta kaima sanin kan kane ko auren Baba nane ya tilasta ba wai wani abin hannun ka yasa na amince maka ba.

Mutum daya yake da wannan daman shine masoyi na mai sona tsakani da Allah ba wai sura ta ko sha'awa ta ba dan haka this should be the last time da zaka shigo min d'aki cikin dare or try something stupid with me and see wallahi zan kira Abba in sanar mishi duk abinda ya faru tun daga farkon auren har zuwa yau".

" Shut up just shut up ke har kin isa ki bani rules in my own house' who do you think you are?" Ya katse ni cikin tsawa da har saida na firgita na d'an ja baya.

"Ni zaki kalla kiyiwa maganan wani katon banza da aure na akan ki, how dear u?" Yace yana zaro min ido yana huci kaman zai buge ni.

Nuna ni da yatsa yayi cikin dacin rai kaman zai ce wani abu kuma naga yayi hanyan waje fuuu tare da banko min kofa kaman zai b'alla ta, dabas na zauna kan rug dake shimfid'e gaban gadon ina mai fashewa da kuka mai cin rai shikenan ni kuma haka tawa kaddarar take daga wanda ya gudu ya barni da syayyar sa sai kuma mai gasa min aya a hannu saboda skyayyar sa, a yau na gama tabbatarwa Zafar ba zai tab'a Sona ba kaman yanda ya sha fad'a min.

Kaico na inama zai iya sona koda rabin yanda nake son shi ne da na more rayuwa amma da alamu banida sa'a a rayuwa haka zan mutu ina dokon soyayyar shi a zuciya ta.

Da kyar naja jiki na zuwa kan gadon na cigaba da kuka na , shima tunda ya fita a d'aki na yake hawaye dan wani irin kuna yaji zuciyar shi nayi mishi zai iya ratsewa da Allah ba'a tab'a fad'a mishi kalma mai d'aci da k'ona zuciya irin wannan ba.

Da auren nashi akai na har nake iya kallon tsaban idon shi in mishi maganan wani katon banza can, wani wawan naushi ya kaiwa bango kaman shine yayi mishi laifin yana cigaba da hawayen takaici.

A wannan daren babu wanda yayi wani baccin kirki tsakanin mu kowa da abinda yake tunani har gari ya waye.

************************

A b'angaren Baban mu kuwa tunda suka had'a shi da ruwan sanyin nan sukayi tafiyar su suka bar shi cikin azaba tun yana sanin inda hankalin yake har ya suma ya zama bai san a Ina ma yake ba, sai bayan awa daya sannan ruwan ya daina zuba sannan suka kunna wata na'ura Mai feso mishi da zafi, nan da nan d'akin ya kuma d'aukan zafi wanda ya haddasawa Baba farkawa babu shiri.

Sunayan Allah yake ta ambata yana jin shi kaman a cikin wuta yake ya rasa ta inda zafin yake shigowa shi dai bai ga wuta a d'akin ba.

Wata murya yaji ya cika wajan ana " ka shirya gaya mana gaskiya ko har yanzu baka horu ba"

" Wallahi zan fad'a...zan fad'i duk abinda kuke son ji dan girman Allah ku cire daga zafin nan kome kuke so zanyi muku na rantse muku..." Baba ya amsa musu cikin tsananin azaba.

Wani irin dariya yaji an kece dashi sannan kaman da wasa yaji zafin yana raguwa zuwa kaman minti goma yaji zafin ya ragu sosai, haske suka Kara kunnawa yanzu ma daidai wajan shine kad'ai hasken ya tsaya baya iya ganin su sai haske da yake jin yana saka idon shi zugi da rad'ad'i, mutum daya yaga ya ratso ta cikin wani glass sannan ya shigo inda yake amma idon sanye da wani bakin glass hannun shi rike da bakin kyalle yana zuwa kusa da Baba ya d'aure mishi idon sa sannan ya finciko hannun shi ya fara Jan shi suka fara tafiya.

Saida sukayi mai nisa sannan yaji an ingiza shi ya Fad'i kasa daga bays suka kunce mishi idon, farko ma hasken rana ne ya fara dallaro mishi ido yayi sauri ya runtse idon tsawa da yaji an daka mishi yasa ya bud'e ido babu shiri yana rarraba ido duk da yanda yake jin zafin ranan har cikin kwakwalwan shi.

Manyan sojoji ne sun kai su goma zaune akan kujera da wani table a gaban su, gefen su kuwa hagu da dama duk wasu sojojin ne rike da bindigu sunyi layi-layi.

"Ka shirya gaya mana komai Mallam Hassan?" Daya daga cikin mayan sojojin ya tambaya yana kallon Baba da yake durkushe a gaban su kan shi a kasa kaman mai neman gafara, cikin rawan jiki yace " wallahi Allah zan fad'a muku ...Allah zan sanar muku da duk abinda kuke son sani ".

Gyad'a kai sukayi gaba dayan su cike da gamsuwa " yace toh menene shirn ku na gaba?"

Mukut Baba ya had'iye wani bushasshan yawu na fargaba da ya tsaya mishi a makoshi ya bud'i baki yace" Shirin mu na gaba shine........".

Tofa me Baban ZAREEFA yake shirin dad's🤭🤭🤭🤭
[12/14/2021, 7:54 AM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*47&48*

Bai san adadin lokaci da ya b'ata a cikin duhun nan ba yana nan dai zaune ne kawai amma ba zai iya cewa dare ne ko rana ne ba, addu'oi kuwa babu wanda baiyi ba yana son yin sallah amma rashin sanin inda gabar yake da kuma rashin ruwan alwala yasa ya hakura.

Zuwa wani lokaci ya tuna dai ko azahar ba'ayi ba suka kawo shi nan dan haka ya tashi yayi taimama da d'an kasa- kasa daya samu ya kabbara sallah, azahar,la'asar da magarib ya sallata ya sallame saboda tashin hankali da yake ciki ko yunwa baya.

Haushin karnuka da yake jine ya san cewa dare yayi nisa sosai bai tsaya b'ata lokaci ba ya kawo sallah isha'i da 'yan nafilfilu ya raya daren ko gyangyad'i baiyi ba balle bacci, rabon da Baba yayi nafilan dare shi da kan shi ya manta balle Kuma wani.

Da washe gari yana zaune makoshin shi duk ya bushe saboda kishi yaji an dallaro mishi fitila a ido wanda ya haddasa mishi rintse idanun nashi babu shiri har wani radadi yaji idon na mishi ko dan ya kwana a cikin duhun ne oho.

"Oga he don wake up" yaji wani kakkausar murya daga wajan ana magana,tafiya ya fara ji na mutane da bai san adadin su ba sun nufo inda yake a tsorace ya mike tsaye jikin sa na karkarwa yana jiran yaga ta ina zasu bullo dan har yanzu bakin shi da suka buge yana nan a kumbure har fuskan shi.

Cak yaji kafan ya d'auke lokaci daya amma baya iya ganin su kasancewar har yanzu hasken daidai fuskan shi yake wajan su kuma duhu.

"Kai ne Mallam Hassan ko?" Yaji an daka mishi tsawa, jikin shi na cigaba da bari ya gyad'a musu kai.

"Open ur mouth and answer me my friend, nace kaine Mallam Hassan?"

Duk da bai fahimci turancin da akayi mishi ba amma cikin sauri ya amsa da " nine...nine Mallam Hassan ranka ya dad'e".

" Good bana son gardama ko taurin kai ka gaya mana menene next target d'in ku me kuke shirin aikatawa a gaba?" Yaji wani murya daban ya tambaye shi cikin gurb'ataccen hausar shi.

Cikin rashi fahimta yake kallon inda yake jiwo muryan su duk da baya iya ganin su dan kwata-kwata bai gane inda zancen nasu ya dosa ba.

"Ka bamu amsa ba wai ka tsaya zare Mana ido ko kuma kana so mubi da kai yanda muka bi da partner ka" wani cikin su ya kara daka mishi tsawa, Baba duk ya rud'e ya rasa inda zai saka ran shi yaji dad'i sannan ko kad'an bai fahimci tambayan nasu balle ya basu amsa kaman yanda suka bukata illah jikin shi da yayi ta b'ari kaman an jona mishi shocking.

"Dole yayi mana taurin kai oga saboda babu wani criminal da za'a kawo ya amsa laifin shi cikin sauki but zamu bi dashi yanda muka bi da sauran.

Step 1" yaji wani murya daban har yana amsa kuwwa, kalle-kalle ya fara yi a matukar tsorace kamin ya ankara yaji ruwan sanyi harda kankara suna zubowa daga sama daga inda yake tsaye nan da nan yaji wani irin sanyi da tunda yake bai taba jin irin shi ba ya rufe shi a take ya fara rawan sanyi hakoran shi na had'uwa da juna.

"Ka huta cikin sanyin ka in ka shirya mana bayani zamu dawo" wani yace suka juya suka bar Baba cikin rawan sanyi yana son tsaida su amma ya gagara bud'e baki balle magana ya fito, yana ji yana gani suka tafi tun yana jin sawun kafan su har ya daina ji.

******************

A gidan mu kuwa babu wanda yayi baccin kirki saboda tashin hankali domin ganin har dare babu Baba babu labarin shi, masu nafila nayi masu addu'oi nayi in ka cire gwaggo Aisha da tasha baccin ta harda minshari, koda gari ya waye Baban Dije da wasu 'yan uwan Baban mu suka fita bin baracks ko Allah zai sa su dace su sami inda aka kai Baba.

Bayan tafiyan su babban tukunya Inna ta daura a tsakar gida na abincin sadaka da tayi niyya tun cikin dare sanin cewa sadaka yana maganin masifa, Inna Asabe tana gani ta fito ta kama mata suka fara aikin tare. A can dakin Gwaggo Aisha kuma drama ce ta kaure tsakanin su ita da Hajara kan cewa wai lalle sai ta fita tazo gidana sun kammala aikin su da suka fara ita Kuma Hajara tace babu inda zata je ta bar ta taji da tashin hankali na rashin Baban mu.

"Ke me yasa baki da wayo a rayuwar ki ne, ban san yaushe zakiyi hankali ba Hajara wani uban ne har kike kumfan baki akan sa, tunda aka haife ki meya tab'a tsinanana miki a matsayin sa na uba a gare ki , ina ni din nan da kika raina nice nake fad'i tashi har kuka taso.

Wannan aikin da nake dan waye nake yin shi dan ke da 'yan uwan kine ku samu rayuwa mai kyau koda bayan raina amma kike shirin watsa min kasa a ido, waye wata Bintu da za'a ce ita ce mai abu a gidan nan tazo tana d'aga mana hanci, hanyan da tabi ta hau muma shi zamu bi mu hau domin kowa ya san asiri sukayi har wannan d'an masu kud'in nan ya aure ta, in zaki farka daga wannan baccin naki ki farka ki kalli abinda duniya take ciki ba wai ki tsaya yin shirme ba"

Goge hawayan da suka cika mata ido Hajara tayi ta juyo tana kallon ta da kyau tace " Umma duk halin da baba na ya shiga dole ya dame ni tunda mahaifi na ne shi kuma a kowani hali yake ina son shi dan shine yayi sillan zuwana duniya kuma ina matukar alfahari dashi, sannan maganan Inna da kike cewa asiri tayiwa mijin Zareefa kema kin fad'a ne kawai amma kin san da asiri yana tasiri da kin dad'e da zama millionaire saboda haka babu inda zan je har sai naga mahaifi na ya dawo LAFIYA". Tana karasa maganar ta ta fice a dakin zuwa wajan su Inna ta kama musu suka cigaba da aikin tare.

Tagumi Gwaggo Aisha ta zuba tana kallon Hajara har ta gama ficewa daga dakin sannan ta sauke ajiyar zuciya tace " Ina murnan asirin ya sake ta ashe da sauran aiki a gaba na dole in kara d'aura d'amara yaki da wannan algungumar".

Hajara bata san ma tana yi ba suna can suna aikin su da sauran mutanen gida, jalof rice sukayi lafiyayye Inna ta saka yaran gida kiran almajirai suzo su karb'i sadakan abincin nan da nan kuwa suka cika gidan har da ma wayan da ba almajirai ba aka rarraba musu abincin suna karb'a bakin su d'auke da addu'a.

Su Baban Dije sai yamma likis suka dawo a gajiye ba tare da wata nasara ba , giwa Barack da 3-3 Barack suka je suka sha wahalan banza dan ko bakin gate ba'a bar su sun wuce ba sun dai wuni suna zagaye bakin gate d'in daga baya ma da kyar suka kwaci kan su a wajan sojojin bakin gate dan cewa sukayi basu yarda dasu ba.

Jikin kowa kara sanyi yayi jin babu wani labari gashi duk cikin zuri'ar mu babu wani mai kud'i balle mai mulki da zai tsaya mana wajan neman inda yake balle ayi maganan fito dashi.

"Gaskiya talauci baiyi ba, Inna ko za'a fad'awa Zareefa ne ko mijin ta zai iya taimaka mana a fito da Baba" cewar Hajara kenan tana share hawayen fuskarta.

"Kul kada inji wani yayi wannan gurguwan tunanin a cikin ku yaushe akayi mata auren da har irin maganan nan zai je kunnen mijinta, insha Allah zamu samu inda yake kuci gaba da addu'a, musamman ke Bintu kinyi tunani mai kyau da kikayi abinci kika sadakar hakan nada kyau sosai domin sadaka tana maganin musifa" Baban Dije ya karasa fada tare da wucewa bangaren shi.

Kowa haka ya watse cike da jimami tare da karfafa zukatan juna kan cewa za'a gan shin a cigaba da addu'a, har a wannan lokaci Gwaggo Aisha bata fito ba tana ciki tana jin mutane Hajara da ta shiga bata ma kalli inda take ba tayi wucewar ta uwar d'akar su itama Gwaggo Aishan bata ce mata ci kan ki ba dan a cewar ta sai ta tashi tsaye har yanzu asirin da Inna tayi mata bai gama sakin ta ba.

*******************

Zafar ya dad'e a dakina zaune a bakin gado yana dafe da kan shi da hannuwa duka 2 ji kaman yayi ta ihu ko zaiji saukin abinda yake damun shi dan ji yake zuciyar shi kaman zata fashe saboda azabar son kasancewa dani, ko da ba zai tab'a ni ba mu zauna waje d'aya yayi ta kallo na ma ya wadatar dashi.

"Ya Allah na roke ka yaye min wannan fitinan ko zan ji sauki a rayuwata" yace yana kara kallon kofan bathroom d'in, shi kan shi bai san adadin lokaci daya bata a zaune ba ya hakura ya fita ganin bani da niyyan fitowa.

Duk abinda yake ina kallon shi ta b'ulin mukulli sai dai banji abinda yake cewa kuma ko kad'an ba banji wani abu na tausayin shi a cikin rai na ba dan nasan ba abinda namiji ba zaiyi ba saboda cikar burin shi.

Ina ganin ya fita daga d'akin nima na fito na murza key a kofa ta na jingina a jikin kofan Ina sauke numfashi tare da lumshe ido sauran hawaye da suka mak'ale min suka samu nasaran zubowa, Allah ya sani soyayyar shi na wahal dani amma dole in kare kaina ba zan bari yayi nasara ba.

Shiryawa nayi cikin riga da skirt na wani material light blue ya min kyau sosai banyi wani kwalliya ba illah kwalli dana zira sai powder da wet lips, ina son fita amma ina gudun kada mu kara had'uwa da shi yasa nayi zama na a cikin d'akin ina chart dasu Maryam ina ce mata nayi fushi tunda taki zuwa inda nake tana bani hakuri wai zata zo kwanan nan.

Kiran sallah azahar ne ya tada ni daga kwancen da nake na shiga bathroom na d'auro alwala nazo na kabbara sallah, cikin natsuwa na idar na zauna nayi addu'oi na dan haka kawai nake ta jin gabana yana yawan fad'uwa.

Ganin zaman ba zai yiwu ba yasa na fito ina leka parlorn kaman wata barauniya cikin sa'a kuwa naga baya nan cikin sauri na shiga kitchen abubuwa dana girka dazu na had'a na mikawa Baba mai gadi bayan na zurmuka dogon hijabi na har kasa sannan na fita na bashi na dawo ciki.

Sabon girki na d'aura ba dan Ina jin yunwa ba sai dan farantawa Zafar har cikin raina ina jin dad'in yanda yake son abinci na.

Lafiyayyen white macroni da coslow nayi wanda ya wadatu da veggies sai kamshi yake, sabon warmer da ban tab'a amfani dashi ba na d'auko na zuba rabon shi na kara mishi da carrot juice na jajajjefa ice block a ciki na rufe tare da jera su akan maidaicin tray sannan na fito dashi kan dinning na shirya su a lokacin har an fara kiran sallah la'asar da alamu kuma har yanzu bai shigo gidan ba.

Komawa nayi ciki nayi alwala nayi sallah , sai a lokacin naji cikina yana kukan yunwa dan tun safe babu wani abin kirki daya shiga ciki na, fita nayi na zubo abincin a plate na dawo parlour na kunna kallo na fara ci ko rabi ban ci ba naji sallaman shi da wannan sabuwar muryan shi mai sanyi ba kaman da ba da sai yaga dama yake sallaman ko zai min magana cikin tsawa yake min.

Sanin muhimmancin sallaman a musulunci yasa na ansa ba tare da na kalle shi ba duk da zuciya ta tana kwad'ayin hakan amma na fuske naci gaba da cin abinci na.

"Kina fitowa main parlour muna ci tare mana , manzon Allah yace yafi albarka" yace bayan ya gama kare min kallo.

Sai a lokacin na d'ago na mishi kallon da baifi second 2 ba na d'auke kaina sannan nace " tun farkon shigowa ta gidan nan abinda na saba dashi kenan ,in ka manta ne in tuna maka cikin yarjejeniyan da mukayi na kamin wata 3 ya cika mu rabu kowa rayuwar shi zaiyi babu ruwan wani da wani so y all this?" Nace ina kara tsuke fuska ta da kyau.

Shiru yayi kaman bai ji abinda nace ba domin bashi da niyyan bani amsa nima kuwa ban damu ba na bawa iska ajiyr shi, ya kusan minti 2 a tsaye sannan ya fita sanyayaye, tab'e baki na nayi na cigaba da cin abinci na a zuciya ta Ina bari dai ai gwara da na tuna mishi yasan cewa ban manta ba balle ya cigaba da yi min wayo.

Kaina tsaye na fito yanzu babu wani tsoro irin na d'azu ga mamaki na yana zaune na gan shi akan dining ya saka abincin a gaba ya kasa ci yana dafe da kanshi da hannaye duka kana ganin shi kasan yana cikin damuwa, jin motsina yasa d'ago da kai yana bina da ido nazo na wuce kitchen ina jin wani iri a raina.

Jiki a sanyaye na ajiye plate d'in hannu na ina fuszar da iska a baki na, juyowan da zanyi naji nayi karo da mutum a firgice naja baya Ina zuba mishi harara domin na d'auki alkawarin ba zan tab'a bari yaudarar shi yayi tasiri a kaina ba.

"Meye haka ne Mallam, dan girman Allah ka daina bibiyata ka barni in sha iska" na fad'a a fusace ina kara jan jiki na baya.

Cikin muryar shi mai rauni ya fara magana " No I just want to..." Ban tsaya na saurare shi ba nabi ta gefen shi na wuce abina.

Ina shiga ciki na dafe zuciya ta da take bugawa kaman ya fito nayi Ina lumshe ido na zauna dabas tare da tunanin mokomata.

"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un!!! Yake maimaitawa tare da jingina da jikin bango ya runtse ido , inama inama.... inama zai iya yayewa kan shi wannan damuwa da yake ji inama zai iya kyale ni kaman da, shi ba wani abu ba so yake kawai muyi magana na fahimtan juna amma naki bashi had'in kai, dole ne ya nemi mafita kamin wani abun ya same shi.

Fita yayi gaba daya daga gidan kaman d'azu dan gwara in baya gida ya kan ji sauki akan ya zauna dani karkashin rufi d'aya, gidan su Saddeq ya nufa kaman yanda ya saba kwana 2 nan kuma ko yaje baya iya gaya mishi abinda yake damun shi sai dai ya samu waje ya zauna ya zubawa waje d'aya ido duk kuwa yanda Saddeq zaiyi dashi ba zai ce kala ba sai dai in yaji da zaman ya tashi ya tafi abin shi.

A parking lot na gidan ya ajiye motan shi ya wuce part d'in Sadeeq kai tsaye sanin yana gida dan yaga motan shi a parking space, babu kowa a karamin parlorn nashi sai TV da yake ta aiki shi kad'ai.

Kan kujera ya samu ya kwanta tare da lumshe ido yana tunanin halin da yake ciki, Sadeeq ne ya fito a cikin bedroom d'in shi da waya a kunne yana waya da wani daga shi sai boxers da singlet alamun bai dad'e da shigowa cikin gidan ba.

Saura kiris wayan shi ya Fad'i saboda tsoratan da yayi na ganin mutum cikin parlour shi ba tare da yaji koda motsin shigowan shi ba, cike da takaici ya nufo shi ganin cewa Zafar ne ya shure shi da kafa yana" wallahi kai banza ne ,wani irin iskanci ne haka zaka shigo min babu ko sallama" .

Bud'e idon shi da sukayi ja ya zuba mishi ba tare da yace mishi komai ba na second 10 sannan ya maida kayan shi ya rufe, zama akan handle din kujeran Sadeeq yayi yana sauke numfashi dan babu karya ya san abokin nashi yana cikin matsala kwana 2 nan.

"Haba Zafar me yayi zafi ne haka kake neman saka kan ka a damuwa, ni dai a iya sani na ban san abinda zai saka a irin wannan yanayin ba tunda ba abinda ka rasa tun tasowar mu, please calm down and tell me what is going on?" Yace mishi cikin rarrashi.

Shiru yayi bai bud'e idon ba Kuma baiyi magana ba tun Sadeeq na sa ran zaice wani abu har ya cire saboda ganin shirun yayi yawa , yana shirin mikewa yaji ya bud'i baki cikin sanyin murya yace " na rasa ya zanyi ban tab'a tsintan kaina a cikin irin wannan yanayin ba".

Zama Sadeeq ya gyara tare da bashi dukkan attention d'in shi jin yanda yake magana so calm kaman ba Zafar da ya sani a baya ba.

"A kullum so nake in zauna a inda take inyi ta kallon ta dan idanuna basa taba gajiya da kallonta, jiki na da gangan jiki na basu da wani buri da ya wuce su ji dumin jikin ta, hanci na kullum cikin kishirwan kamshin jikin ta yake haka kuma kunnuwa na basa tab'a gajiyawa da jin zazzakar muryan ta.................. Hmmmmmm" yaja dogon numfashi sannan ya cigaba " but ba yanda banyi da ita ba ta tsaya ta saurare ko zamu samu mafita amma taki ta bani dama". Ya karasa tare da bud'e idon shi dake cike da damuwa ya zubawa Sadeeq dake jifan shi da wani kallo dan duk a zaton shi zancen wata macen yake bani ba.

"Hmmmm wacece haka kuma ?" Sadeeq ya tambaya cikin halin ko in kula.

Lumshe idon ya karayi sannan ya amsa mishi da " ZAREEFA...."

Waro ido Sadeeq yayi fuskar shi na nuna zallan farincikin da yake ciki yace " shegen gari kace ciwon sone yake dawainiya da kai mana kazo kana wani langwab'e min kwana 2" ya karasa yana kecewa da dariyan shakiyanci

A matukar zabure Zafar ya mike yana watsa mishi mugun kallo yace " dan na gaya maka damuwata ba shi zai baka lasisin yi min wulakanci ba, kafi kowa sanin babu macen da take gaba na balle akai ga ace ni Zafar zan so ta talk less of dis village girl".

Wani dariyan Sadeeq ya Kara sakawa yana nuna shi da yatsa yace " see you, wai babu macen da take gaban ka ko, sai kace ba yanzu ka gama ce min ( jikina da gangan jiki na basu da wani burin daya wuce suji dumin jikin ta) in ba so ba menene?". Ya karasa yana kwaikwayon muryan shi.

A matukar fusace ya mike tsaye yana " BA SONTA NAKE BA kuma I will never do that na san kawai Ina samun wannan nagetive feelings d'in kasancewa I have never been with a woman before Kuma muna zaune gida d'aya shi ya kawo haka, I can pay her any amount she need to be with her just once tunda akwai igiyan aure a tsakanin mu ban aikata zina ba".

" Kai da kake kyankyamin mata baka yarda ko party ne kaje dasu shine yau kake cewa ko nawa ne zaka bata dan ka kasance da ita ko sau d'aya ne, yaro yaro ne ni tunda kace min zaka iya auren ta tun a lokacin na san there is something special about her in your heart da kaima baka san da shi ba, but for now ya kamata ka sani cewa ka riga da kayi nisa a cikin son ta....."

" Enough of this bullsheet Sadeeq kada ka kara tara ta da wannan banzan maganan, ba son ta nake ba I repeat myself ba sonta nake ba....." Ya fad'a a tsawace tare da ficewa fuuu cikin fushi kaman zai tashi sama, dariya Sadeeq yayi yana " zaka dawo ne ka same ni yaro".
[12/14/2021, 7:54 AM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*51&52*

A gidan mu Inna ta cigaba dafa abincin sadaka suna rabarwa , Inna Asabe da Hajara suna taya ta kullum sai dai har yau Gwaggo Aisha bata ce ci kan mu ba ko Kuma ta fito su jajantawa juna game da kame Baba da akayi , kullum tana d'aki ko motsinta ba'a cika ji ba.

Ta d'auki fushi da Hajara sosai kan taki yarda su karasa aikin da suka fara akan Zafar ga kuma aikin abincin sadaka da take taimakawa su Inna ya kara tunzura ta shiyasa ko kallon inda take bata yi, itama Hajaran share ta tayi domin tana cike da takaicin halin ko in kula da take nunawa akan halin da Baban mu yake ciki dan haka kowa tsabgar gaban shi yake.

Jameela kuwa yau ta kai kusan wata bata leka gida ba sannan babu wanda ya san inda take kuma babu wanda ya damu da ya neme ta ko dan sun saba ganin haka sai ranan da taga dama take dawowa gida.

Yauma su Inna suna cikin aikin su sai gata ta shigo cikin maye kaman yanda ta saba, ko sallama batayi ba ta fad'o musu cikin gida tana layi.

Cak ta tsaya tana bin su da kallo baki bud'e cikin murya irin na 'yan maye tace " wato biki ma kuke a gidan nan shine babu wanda ya fad'a min, da ban zo na iske ba shikenan sai kuyi ya wuce ni ko? Ala dole kun mayar dani saniyar ware...."

Tab'e baki Hajara tayi ta cigaba da aikin ta ba tare da ta kara kallon inda take ba sai kanwar Baban mu Gwaggo Hinde da suka iso yau da safe ta bata amsa da " kaji min ja'irar yarinya a gidan uban wa aka ganki da za'a fada miki abinda yake faruwa a gidan, keda kika saka yawo a gaba da shaye-shaye toh uban ku sojoji suka tafi da shi yau kwana 2 bamu san ina suka kai shi ba....."

Ga mamakin su dariya suka ga ta kyalkyale dashi harda rike ciki, saida tayi mai isar ta sannan tace " dan Allah ku kaini wajan sojojin nan in basu tukuicin abinda sukayi koda round d'aya-d'aya ne, wallahi sun matukar birge ni su Baba ana can ana girban abinda aka shuka.

Ke kuma Inna ya kamata kifi kowa murnan wannan al'amarin ko dan cin kashin da yayi akan ki amma dan rashin zuciya shine wai harda ke ake addu'an fitowan shi, Allah yasa ya dauwama acan su gana mishi irin azaban da yayi ta gana mana tun tasowar mu" Tana kaiwa nan tayi hanyan d'akin su tana cigaba da wasu suratai da ita kanta bata san ma'anar su ba.

Da ido duk suka raka ta har ta shige sannan kanwar Baban mu tace " toh Allah ya shirya mana zuri'a" da ameen suka amsa mata suka cigaba da aikin da yake gaban su.

Gwaggo Aisha ce ta tare ta cike da farinciki dan duk abinda ya faru akan idon ta akayi shi domin tana tsaye ta jikin windown ta tana kallon su.

"Allah miki albarka jameela ta kece kad'ai kika biyo halina a cikin ku, inama ace baki b'ata kan ki da shaye-shaye nan ba da kin cika duk wasu buruka na da 'yar uwar ki ta kasa cika min" cewar Gwaggo Aisha.

Cikin muryar ta na 'yan maye tace " ke wai umma meyasa ba'a hiran arziki dake ne, kina wani zancen shaye-shaye ki sani ko kece kika tab'a ba zaki iya rayuwa ba sai da shi,kin san nishadi'i da ake samu kuwa in ansha......" Ta karasa harda lumshe ido alamun abinda ta fad'a har cikin zuciyar ta haka take Gwaggo Aisha kuwa kallon takaici ta bita dashi ba tare da iya cewa uffan ba.

**********************

"Kai kar ka b'ata mana lokaci ko a kara mayar da kai inda aka fito da Kai ne?" D'aya daga cikin manyan sojojin da ya fara fusata da inda-indan Baba ya daka mishi tsawa.

"A'a zan fad'a wallahi....wallahi zan fad'a ranka ya dad'e" Baba ya amsa cikin sauri.

"No ka bari a kawo d'ayan partner shi d'in zaifi sai suyi mana bayani gaba ki d'aya" cewar babban cikin su, ba musu wasu 2 daga cikin kananan sojojin suka juya zuwa wani b'angare dake can nesa dasu shi kuwa Baba har a wannan lokacin kan shi a kasa yake ya kasa d'agowa sai had'a zufa da yake kaman ana mishi wanka.

Bayan kaman minti goma yaji dawowar su tare da ingiza wani ya zube a kusa dashi har yana bige baba da yayi tangal-tangal kaman zai fad'i da kyar ya samu yayi gaining balance din shi ya zauna amma har yanzu bai d'ago ba balle yaga waye aka kawo.

" Kai d'ago ka dubi mutumin gefen ka nan" Baba yaji an daka tsawa amma duk da yaji muyar da akayi maganan sai bayi saurin d'agowa ba domin duk a zaton shi da wanda aka kawo yanzu suke, a babu zato balle tsammani yaji saukan gindin bindiga a gadon bayan shi har sai da ya kwanta saboda azaba " how dare you ana yi maka magana kana jin mutane". Yaji wanda ya buga mishi bindigan ya yace yana huci.

"kuyi hakuri ranka ya dad'e wallahi ban san dani kuke ba " ya amsa daga kwancen sai jujjuya kai yake na azaba da yake jin tana ratsa har kwakwalwan shi.

Wani irin shure shi yaji an kara yi da kafa har sai da ya mirgina gefe cikin wani irin babban murya yaji ance " kana kwance kake bawa oga amsa, sit properly my friend" yaji an kara daka mishi tsawa.

Duk da ba jin turancin yake ba amma sarai ya gane me yake nufi dan haka cikin dauriya ya yunkura ya tashi zaune yana b'ata fuska alaman har yanzu yana jin zafi, a hankali kaman mai tsoro ya kalli gefen shi mutum ya gani fuska a kumbure da kayar ma ake iya kallon kwayar idon shi.

Duk wannan kallon cikin second 5 yayi su ya sauke kan shi kasa ba tare da yace wani abu ba.

"Ka san shi ?" Yaji babban cikin su ya tamabya, Baba bakin shi har rawa yake wajan bashi amsa dan har yanzu yana jin zugin da bayan ke mishi " ban san shi ba ranka ya dad'e"

" No enough don't hit him " babban nasu ya dakatar da wanda ya dago bindigar shi domin kara kwad'a mishi .

"Ka gaya mana gaskiya bana son kana b'ata mana lokaci ka gan mu nan muna da abinda zamuyi muka tsaya anan muna binka a hankali ko in kana so in barka dasu su tambaye ka toh....."

" A'a wallahi Allah ranka ya dad'e ban san shi ba hasalima ban tab'a ganin shi ba. Baba ya amsa har yana katse shi jin cewar za'a bar shi da masu zallan muguntan nan.

"Nd you gaya mana gaskiya kace shine shugaban nan naku amma yace bai sanka ba " ya tambaya tare da maida hankali shi kan d'ayan mutumin da aka kawo shi yanzu, cikin dashassiyar muryan shi da bata fita sosai na alaman yaci wuya a hannun su ba na wasa ba yace " shine shigaban mu Mallam Hassan"

A zabure Baba ya d'ago da kan shi ya zubawa mutumin nan ido da yace shine shigwaban su kuma sai yake jin kaman ya tab'a sanin mai muryan, murmushi mai kama da kuka ya sakewa Baba da kumburarren fuskan shi ganin yanda ya zuba mishi ido yace;

"Baka gane ni ba ko Mallam Hassan? nine Abdulbasit yaron ka mafi kusanci da kai cikin yaranka wanda har kayi alkawarin bani Yar ka Zareefa da aure ka tuna, kana mamakin ya akayi suka kama ni bayan tarin makamai da ka bamu toh sun kama ni ne a hanyan mu na kaduna da ka saka mu muyi kidnapping minister man fetur ashe ba securities d'in shi da muka saya bane suka rako shi wasu sabi ne daban Kuma suma dan rashin amana basu gaya mana ba sai clashin mukayi dasu, munyi yunkurin guduwa sauran Allah ya basu sa'a sun gudu sai nine kad'ai suka kama sanadiyan harbi da suka min a kafan dama " ya karasa yana nuna mishi kafan shi na dama da yake a kumbure ya sha daurin bandage.

"Kayi hakuri wahala yasa na fad'a musu sunan ka da inda za'a same ka , yanzu ma tambaya suke menene Shirin mu na gaba shine nace baka fad'a mana har sai zamu fita aiki kake fad'a mana abinda zamuyi" yana gama magana ya sunkuyar da kai kasa alamun he is sorry for what happened.

Baki bud'e kawai Baba ke kallon shi ya kasa gaskata abinda yake faruwa kaman a mafarki ko Shirin film, tsoro, mamaki, firgici yasa ya kasa furta komai sai kallon wanda ya kira kan shi da Abdulbasit yake dan haka ko kad'an bai ji abinda babban sojojin yace ba sai gani yayi an had'a su waje d'aya an ingiza su zuwa wani babban d'aki sai dai wannan karan ba cikin duhu bane an bar su da haske , suna fita suka kulle su ta waje aka bar su su kad'ai.

********************

Ina farkawa da safe bayan na idar da sallah ban iya tsayawa nayi azkar d'ina da kyau saboda wani irin bacci da ya cika min ido har wani yaji-yaji yake min, nan na bingire kan sallayan ko hijabi na ban cire ba bacci mai dad'i yayi awon gaba dani.

A bangaren Zafar kuwa ko da safen ma kasa komawa baccin yayi zuciyar shi har yanzu zafi take mishi akan abinda ya faru tsakanin mu, sosai abin yake mishi zafi kuma yana jin dole ne ya koya min hankali but tayaya? Shine abinda yafi damun shi ya rasa ta yanda zaiyi ya hukunta ni.

Dik wani hanya da yake ganin ya cancanta yabi ya hukunta ni sai ya ga ba zai iya ba saboda zan cutu ta hakan sannan deep down him kuma baya son ma ya d'auki matakin saima hanyan da zai bi ya rarrashe ni yake nema dan shi kad'ai yasan abinda yake ji game dani.

Sai kusan karfe goma na farka ina mamakin irin baccin da nayi ban b'ata lokaci ba na cire hijabin jikina na nad'e sallayan na ajiye su a mazaunin su na gyara daki da parlour na tsab sannan na shiga nayi wanka da brush na fito da yake na san na sakawa kofa ta key shiyasa cikin kwanciyar hankali na shirya cikin riga da skirt na less light blue daya ji aikin stone sai walkiya suke.

D'an kwalliya nayi tare da d'aura d'an kwlin na fesa turare sannan na nufo kofa zuciya ta na bugawa ban san had'uwa ta dashi ya zata kasance ba yau, parlour na na fito na bud'e kofan main parlour ina leke ganin babu kowa yasa na fito abina kai tsaye nayi kitchen Dan yunwa na fara ji sosai.

Turus nayi a bakin kitchen d'in ganin Zafar a gaban coffee machine yana hadawa, jin motsina yasa ya juyo muna had'a ido na tsuke fuska ina shirin d'auke nawa idon ga mamaki na wani sasssayan murmushi ya jefo min wanda kana gani daga kasan zuciyar shi take.

Saura kiris in zubda ajina da nake kokarin karewa agaban shi domin a take naji notinan kai na sun kunce saboda ban tab'a ganin yayi irin wannan murmushin ba tunda na san shi shiyasa a take naji gaba daya jikina yayi lakwas.

Daurewa nayi na wuce shi zuwa wajan fridge na ciro kwai 3 da niyan soyawa sai ji nayi yana " ba sai kin sha wahalan soyawa ba, I have already made breakfast for you" yace yana nuna min wani hadadden tray mai d'auke da wani plate a rufe, d'auke kaina nayi na cigaba da fito da kayayyakin da nake bukata wajan girkin da nayi niyya.

Wuka na d'auko zan yanka albasa naji karaf ya rike min hannu wani mugun kallo na watsa mishi ina mishi kallon meye haka, shi kuwa marairaice fuska yayi harda wani langwab'e kai irin pls din nan.

Kwace hannu na nayi ba tare da nace mishi kala ba nayi hanyan parlour, saida yayi murmushi sannan ya biyo ni da tryn akan kujera ya same ni zaune na dafe goshi na da hannun dama dan na rasa abinyi ajiyewa yayi a gaba na ya koma kitchen din ya fito da mugs guda 2 da ya had'a coffee a ciki ya ajiye suma a gaba na sannan ya durkusa Yana leka fuskata.

"I'm very sorry for what happened yesterday dan Allah kiyi hakuri na miki alkawari hakan ba zai kara faruwa ba ki bar komai ya wuce let's be friends for the rest of the time we will spend 2geda" yace cikin sanyin murya.

Ban iya d'agowa ba nayi shiru ina sauraron shi dan na rasa a wani mizani zan auna maganganun nashi, dan sun dan sanyayya min jiki kamin in samu abin cewa waya ta da na bari a kitchen ya d'auki kara, kamin in mike har shi ya rigani mikewa kitchen din naga ya koma sai gashi ya dawo da waya ta a hannu ba tare da yayi magana ba ya miko min..

Ajiyar zuciya na sauke bayan na gama maganar shi a zuciya ta na cewa ba girki da d'auko waya zai rinka yi ba ko menene zaiyi ba zai tab'a cin nasara a kaina ba tunda na riga da na gane manufarsa a kaina.

Hannu na saka na karb'a daidai wayar ya katse duba sunan nayi naga Dije ce babu bata lokaci na kira ta kaman kuwa jira take bugu daya kawai ta d'aga cikin ihu tace " kaji matan mayan Alhazawa basa d'aukan kira sai dai su kira mutum".

Murmushi kawai nayi dan yanda yake zaune kusa dani yana jin abinda muke cewa ba zan iya sakewa inyi magana yanda raina take so ba nace " Dije ba kya rabo da zolaya ya kike?"

" Lafiya lau Zareefa ya muka ji da wannan iftila'in daya fad'awa Baba ku?" Ta amsa min cikin sanyi.

" Wani iftila'i kuma Dije?" Nima na tambaye ta cikin rashin fahimta.

"Ke kuma akwai ki da wani zance, wani iftila'i kuwa banda wanda sojoji suka tafi da Baban ku"

" Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un!!! Kawai nake iya maimaitawa cikin mugun tashin hankali da ban tab'a tsintan kaina a ciki ba, Baban mu a hannun sojoji toh meya faru meyasa babu wanda ya gaya min a gida.

Kuka na fashe da Ina" Baban mu sojoji suka kama Dije tun yaushe , meyasa babu wanda ya fad'a min"

Cikin rashin jin dad'in kotobarar da tayi dan ita duk a zaton ta na sani shiyasa ta kira ta min jaje dan duk zuwanta gidan mu bata gani na ashe ban ma ji ba, maimakon ta bani amsa kawai sai ta katse kiran.

Cikin tashin hankali na kara Kiran ta amma sai naji wai switch off, jefer da wayan nayi ina kara fashewa da kuka na kama jeka ka dawo a tsakar parlour na rasa ina zan saka raina inji sanyi.

Kafadata naji ya riko ta baya tare da juyo dani muna fuskantan juna ya saka hannu ya share min hawayen da suke ambaliya a fuska na wasu na zubowa yace" shhhh ya isa haka kada ki sakawa kan ki ciwon kai, naji duk abinda aka fad'a miki a waya kada ki tashi hankalin ki kina da ni duk inda sojojin suka kai Baba nayi Miki alkawarin ni zan tsaya har sai naga ya fito".

Kallon shi kawai nake kaman yau na fara ganin shi murna zanyi akan abinda ya fad'a ko akasin ta, duk bayan maganganun da ya fad'a min jiya why zai cigaba da nuna min kulawa haka?

"Komai maza zasu iya yi dan cimma burin su " zuciya na ta kwab'e ni kamin in samu amsan bashi ya katse da " shhhhh kada kice komai kije ki d'auko hijabin ki mu tafi gidan ku muji ya maganan take"...

Ban San lokacin da murmushi ya subuce min na farincikin zanje gidan mu cikin matukar jin dad'i nace " thank you Ya Zafar....."

Nagode da soyayyar ku gare da wannan novel Allah ya bar kauna, nima ina muku fatan alkhairi my fans.
[12/14/2021, 7:54 AM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*43&44*

Shiru motan ya d'auka babu mai magana a cikin mu sai dai yana tuki amma duk hankalin shi a kaina yake, ni kuma na maida kaina gefe ina kallon titi lokaci-lokaci na kan share hawaye da suke zubo min na kasa dannewa sai tunanin halin da Baban mu yake ciki nake, toh meya aikata haka da har sojoji suka tafi dashi...

Sojoji bama police ba, Baba da ko police ya gani duk sai ya gigice balle ace yana barracks na sojoji ya Allah ya fitar da shi cikin sauki, duk a zuciyata nake ta wasi-wasin nan har muka iso kofar gidan mu cikin azama na fara kokarin bud'e kofan in fita naji ashe ya saka lock.

Juyowa nayi na watsa mishi wani kallo da yake nufin menene haka? Bai nuna fushi ko b'acin rai ba yace " calm down pls ki bi komai a sannu insha Allah ba abinda zai samu Baban mu I promised u this, in kin shiga ciki pls ki min iso wajan kanin Baban inji ta ina zan fara" yana karasa maganan shi yayi unlocking d'in kofan jiki a mace na bud'e na fita.

Ina fitowa Kuma sai naji kaman in d'iba da gudu in shiga ciki nake ji amma na daure banyi gudun ma sai uban sauri da nayi ta zubawa na tura gate din na shiga daga can na hango Inna ta da Inna Asabe suna ta kiciniya da murhun itace a tsakar gida zasu daura abincin sadaka, ai ban san lokacin da na kwasa da gudu na isa gare su sai kawai Inna ji tayi an fad'o mata akai .

A zabure ta juyo muka had'a ido sai washe baki nake dan farincikin da nake ciki bai zai tab'a misaltuwa ba, itama cikin farincikin ta rungume ni fuskarta d'auke da zallan murnan gani na cikin koshin lafiya ga wani dan haske da na kara kana gani kasan ina cikin hutu.

"Zareefa kece haka sulum bako waya?" Inna Asabe tace tana kallon mu cikin farinciki itama, sai a sannan na fashe da kuka sosai jin ta ambaci sunan waya nace " yanzu Baban mu yana cikin wannan halin shine babu wanda ya kira ni dan a gaya min?"

"Baban ku karami shi ya hana a gaya miki sanin cewa ba zaki tab'a kwantar da hankalin ki ba dole kice zaki fito shi kuma baya son fitowan naki saboda ko cikakken wata 3 baki yi a d'akin ki ba" Inna Asabe ce ta bani amsa a daidai wannan lokaci kuma Baban mu karami da Zafar suka shigo tare da sallama.

Amsawa su Inna sukayi suna gyara lullub'in jikin su ya durkusa har kasa ya fara gaishe su kai a k'asa, amsawa sukayi suma kawunan nasu a kasa sun kasa kallon shi a zuciya ta na fara gulman shi ina dube shi yanda yake ta tsunne kai kaman da gaske.

Suna gama gaisawa Baban mu karami yaja shi zuwa b'angaren Baban mu da yake a rufe ya bud'e suka shige ciki, bayan wucewar su Inna ta ture ni daga jikin ta tana " ke Kam ban san ranan da zakiyi hankali ba ya zaku taho tare da mutum ki shigo ki bar shi a waje ba tare kinyi mishi iso ba?"

Baki na turo mata na shagwab'a zanyi magana ta nuna min hanyan ciki tare da had'e fuska, banyi gardama ba na juya zan shiga kenan naji muryan Hajara cikin ihu ta ambaci suna na nima na juyo cikin murna ina amsa mata da d'an karfi ta taho cikin sauri muka rungume juna sannan muka shige ciki su Inna kuma suka cigaba da aikin su.

A can b'angaren Baban mu kuma koda suka shiga Zafar zubewa ya karayi a k'asa ya fara gaida shi cikin sauri Baban mu karami ya dakatar dashi yana haba ya zauna akan kujera mana ai sun riga sun gaisa a waje.

Tashi yayi ya zauna amma bai hau kan kujeran ba ya sunkuyar da kai yana sauraron Baban Dije daya fara koro mishi bayanin yanda al'amarin ya faru da irin wahalhalun da suka sha amma ko takamaimai inda yake basu sani ba balle akai ga maganan fito dashi.

"Tun farko da na samu labari da ba zai kai har war haka a hannun su ba kasan wani lokacin mutane suna yiwa mutum cune su Kuma ba zasu bi diddigi ba su kama mutum su jefa cikin barracks d'in su shikenan in mutum bashida gata sai a nemi labarin shima a rasa but insha Allah akwai abokina da mukayi karatu tare a abroad Baban shi Marshal ne zanyi mishi magana in Allah ya yarda komai zai zo karshe" .

Cike da farinciki Baban mu karami ya fara mishi godiya amma ya dakatar dashi yana " haba nima ai Baba nane dan bana son Abba na yaji labarin ne saboda wasu dalilai amma da waya kawai zaiyi ba tare da mutum yaje ba zasu sako shi".

Nan ma Baban Dije gyad'a mishi Kai yake cike da gamsuwa da bayanin nashi domin karshen ta in Abban Zafar d'in yaji wannan labarin babu dad'i ko dan kare mutuncin sa hakan yana da kyau, sai yaji Zafar d'in ya kara birge shi .

Sun dan kara tattaunawa sannan yace zai tafi wajan friend din nashi duk yanda sukayi zai zo musu da labari kamin nan nima zai barni anan sai in ya dawo sai mu koma tare, har bakin gate ya rako shi sannan suka rabu.

Ni kuma muna parlour Inna da ya sha gyara sai kamshin turaren wutan sandal yake nake ce ma Hajara " ni dai nayi fushi tunda irin wannan abu ya faru ace harda ke wajan masu boye min, ba dan Dije ta Kira ni tayi min jaje ba Ina can ban san me yake faruwa ba aiko ba abinda zan iya yi zan taya shi da addu'a".

" Ke ni tunda abun ya faru da washe gari naso a fad'a miki ko dan mijin ki kila zai iya yin wani abu amma Baban Dije ya hana kuma yayi gargadi kan kada a kuskura a gaya miki wai yaushe aka miki aure " Hajara ta tari numfashi na.

Haka muka yini muna ta hiran mu da Hajara a parlour Inna har kusan Azhar sannan Maa da yan uwan Baba da suke gidan ta suka shigo nan suma suka hau murnan zuwa na daga baya kuma muka jajantawa juna aka zauna ana maida abinda ya faru har wannan lokaci Gwaggo Aisha tana ciki bata leko ba duk da hayaniyan mutane da ya cika gidan dan harda makota duk sun shisshigo.

Kasa hakuri nayi na sassauta murya na tambayi Hajara ko ina take? Ita kuwa cewa tayi ta fita anguwa tunda sassafe ta boye min, ni kuwa abin ya bani mamaki ace ana cikin wannabe halin har ta iya zuwa anguwa.

Zafar tun a mota ya kira abokin shi mai suna Hamis kan yana Ina?

"Ina gida " ya amsa mishi bai bari ya Kara cewa wani abu ba ya katse kiran tare da yin hanyan Pori dan a wannan anguwan yake da zama, tafiyan kusan minti 40 ya kawo shi kofar gidan Hamis horn d'aya kawai yayi mai gadi ya bud'e mishi gate ya shigo hadadden gidan daya qawatu da flowers kana ganin gidan kasan shima ya taka kasa .

Parking yayi a wadatattacen parking space na gidan ya fito ya nufi cikin gidan cikin takun katsaita da ya zama jikin shi, door bell d'in ya danna ko second 30 ba'ayi ba aka bud'e kofan wani matashin saurayi da ba zai wuce sa'an shi ya bayyana a gaban shi yana murmushi yace " wai da gaske kake dama zaka zo, ni wallahi ban d'auki abin ma da gaske ba sai da gan ka da idona" ya karasa yana bashi hanya .

Shiga yayi ciki bakin shi d'auke da sallama bai kula abinda Hamis d'in yake ce mishi ba, shima Hamis d'in murmushi yayi yabi bayan shi bayan ya rufe kofan, anan hadadden parlour nashi suka iske kyakkyawar matar shi da cute kids d'in su mace da namiji sun baza toys a tsakiyan parlorn suna ta wasa abin su gwanin sha'awa.

Gaishe shi sukayi da kanuri ya amsa musu yana musu murmushi maman su ma gaishe shi tayi sannan ta tattara kayan wasan yaran tayi ta kai su d'akin su sannan ta had'o drinks ta kawo wa Zafar ta shige ciki.

Gaisawar su ta abokai sukayi Hamis na kara tsokan shi amma bai tanka ba ya shiga yi mishi bayanin abinda yake tafe da shi.

"Hahhh dama na sani haka kawai ba zaka tuna dani har ka kawo min ziyara ba saida dalili" nan ma bai ce mishi uffan ba sai ma kara daure fuska daya karayi dan ya riga ya san dole sai Hamis ya mishi iskanci kamin ya saurare shi.

Haka ko ya karaci neman maganan shi Zafar bai kula shi ba daga baya kuma ya koma serious suka fara magana akan abinda ya kai Zafar d'in gidan sa.

"Ban san me yasa ba yanzu duniya ta lalace da zallan mugunta, mu talakwan ma kenan da ace wani mai mulki ne yayi hakan sai ace dan Allah ya bashi saurauta yake taka mutane.

"Mutum ya san shi kad'ai ya shuka tsiyar shi amma in yaga abun zai rufta dashi sai ya nemo wanda a baya yake jin haushin sa ko kuma Wanda ya tsaya mishi a rai ya mishi cune , baiji ba kuma bai gani ba za'a je dashi a rufe shi, wani shikenan mai kara jin labarin shi saboda bashida gata ko kuma a kashe shi gaba d'aya a shafe labarin shi amma insha Allah zamu samo bakin zaren tashi muje barracks d'in su Dady muji kasancewar shi baya yarda da zalinci kuma baya yarda ayi a gaban shi sai dai in a rashin sani, shiyasa ko wani case in ya shigo hannun shi sai yayi bincike sosai kaman wani police kamin ya yarda a yanke hukunci" ya karasa yana mikewa tsaye yana kwalawa matar shi kira.

Fitowa tayi da sauri tana karasa daurin dan kwalin ta yace mata "zamu d'an fita ne da Zafar "

D'an Bata fuska tayi alamun bata ji dad'in hakan ba cikin lallashi yace " don't worry I will not stay long yanzu zan dawo".

fuska ta sake tana murmushi tace " shikenan my love sai kun dawo Allah ya tsare" da Ameen" ya amsa Yana kissing goshin ta sannan ya juyo ya kalli Zafar da ya tsaya musu kallon sha'awa yana ji inama haka zaman mu yake a gida.

Maimalari barracks suka nufa bayan sun fito suna hirar su jefi-jefi a cikin motan har suka iso bakin gate da sojoji suke birjik suna binciken ababen hawa da zasu shiga ciki, suna duba motan su ganin Hamis ne yasa suka basu hanya suka wuce, haka sukayi ta wuce gates sun kai 4 kamin su shigo ainihin inda office d'in Baban Hamis yake...

Basu karasa ciki ba saida akayi musu iso sannan suka shiga katon office d'in nashi daya k'awatu da kayan alatu sai kamshi da sanyin ac ke tashi, da murmushi ya tare su yana daga ina suke haka yana nuna musu wajan zama.

Zama sukayi a inda ya umarce su sannan suka gaishe shi ya amsa kamin su fara koro mishi bayanin suka ji knock a kofan office d'in wani soja ne ya bud'e ya shigo da wasu files a hannun shi ya kame a gaban shi tare da salute sannan ya ajiye files d'in kan makeken table dake gaban su ya kara salute ya fita.

Jawo files d'in yayi ya fara duba su a tsanake yace " uhum ina jin ku ".

Hamis shi ya korowa Baban shi bayanin da Zafar ya mishi tsab ba ragi ba kari, shi Kuma Zafar shiru yayi har ya gama fad'a mishi komai amma bai dago ya kalle su ba ya cigaba da duba files na gaban shi har zuwa wani lokaci mai dan tsawo sannan ya ajiye su a gefe ya d'ago ya zubawa Zafar ido yace " menene sunan nasa kuma yaushe hakan ta faru?"

" Mallam Hassan sunan shi kuma yau kwana 3 da kama shin".

Gyad'a Kai yayi cike da gamsuwa yace" muna da similar case da wanda ka fad'an nan amma shi ba yanda ba muyi dashi ya gaya mana gaskiya ba yaki cewa komai , so mun had'a su waje d'aya sannan an saka musu cctv camera a d'akin da suke dan mun san dole sai sunyi magana a tsakanin su".

Duk shiru sukayi suna sauraron shi ya koma ya jingin da kujeran da yake kai yana jujjuya da shi yace " wannan files d'in ma na bayanan su ne bari mu tabbatar da abu d'aya zuwa gobe sai in neme ku ko?"yace yana duban su.

Godiya sosai Zafar yayi mishi sannan sukayi mishi sallama suka shiga mota suka kama hanyan gidan Hamis sai dai bai shiga ciki ba a bakin gate d'in gidan shi Zafar ya sauke shi da yake a motan shi suka tafi shima ya nufo gidan mu .

A can barracks din kuwa bayan fitan su Zafar Baban shi ya kira wayan da suke aikin tare kan su same shi a office d'in shi, ba'a d'auki lokaci mai tsawo ba suka taho su 3 kowanne su sai da ya fara mika gaisuwan shi gare shi wanda hakan yana nuna cewa shine babban su, gyad'a Kai yayi tare da yi musu alaman da hannu kan su zauna ba musu suka nemi waje suka zauna .

"These are files about those people case yanzu sergeant Ibrahim ya kawo min su " yace yana ciro wata 'yar karamar memory card a cikin gidan ta ya saka a system dake gaban shi yayi wasu latse-latse sai ga shi ya fara nunawa ta can gefe kaman tv dukan su kuwa suka maida hankali kan screen d'in ga su Baba sun fito b'aro-baro a jiki suna zaune da kumburarrun fuskokin su.

Shiru ranan da aka Kai su basuyi wani magana mai mahimmanci ba sai da washe gari da yamma sannan suka zo inda suka ga sun fara magana a tskanin su..

" Wai kai har yanzu saboda dakikancin ka baka gane ni bane bayan duk bayanin da nayi maka?" Cewar wanda ya kira kan shi da Abulbasit ma Baban mu.

Murmushin takaici Baba yayi mishi yace" in nagane ka da ban gane ka ba duka d'aya ne tunda har ka iya min irin wannan kazafin ka kawo ni nan, ban san me nayi maka ba kake son ganin baya na......"

Dariya da Abdul basit ya kece dashi shi ya hana Baba karasa maganan da yayi niyya ya zuba mishi ido kawai yana bin shi da ido dan shi bai ga abin dariya a cikin wannan halin da suke ciki ba.

"Bani kad'ai ba kayiwa ba hatta iyalan gidan ka sun matukar cutu da mugun halayyarka, tayaya Allah zai baka mata da yaya ka mayar dasu abin wulakancin ka, ko abinci baka basu sun ci ba balle aje ga wasu abubuwan rayuwar na yau da kullum.

Ko a yanda na shigo rayuwar Zareefa na d'auki nauyin karatun ta da sauran su amma a matsayin ka na mahaifin ta da Allah ya daura maka alhakin kiwon su baka tab'a damuwa ka san wanene ni ko kuma ka damu ka san a ina suke samun kudin ba saima nuna zalamarka da kwad'ayin ka akan abinda suke samu , farkon zuwa na da niyyan cutar da ita nazo domin kuwa mai gida na yana safaran yara kanana sai dai yanda naga rayuwar da take ciki da kuma yanda mahaifiyar ta ta nuna min ita ba mai son abin duniya bace duk da talaucin da suke ciki, ba karamin burge ni tayi ba sannan ta goge bakin niyya dake zuciya ta Allah ya darsa min tausayin su a raina tun daga wannan rana nake taimaka musu da zuciya daya.

Ni maraya ne na taso banida kowa Kuma wannan rashin gatan shi ya jefa ni a halin da na tsinci kaina a ciki, ni dai na taso na ganni Ina garari a gari ban san kowa nawa ba cikin yawon da nake Allah ya had'a ni da Emeka shi ya kasance uwa da uba a gare ni ya saka ni makaranta kasancewar shi Christan bai sa ya canza min suna ko addini na ba hakan ya sa nima na rike shi da hannu 2 inayi mishi biyayya kaman shi ya haife ni" dago kai yayi yaga Baba ya zuba mishi ido yana sauraron yayi lakwas da alamu jikn shi ya fara sanyi.

Kara sauke kan shi yayi ya cigaba " duk wani mugun aiki Emeka nayi kuma tun muna kanana ya bamu horo kan irin aiyuka da yake yi kasancewar muna dayawa Kuma dukan 'yan arewa ne babu kabilan shi ko d'aya a ciki, yana tura mu munayi mishi safaran kwayoyi cikin kasar nan sannan ga kidnapping na yara ana mishi safaran su kasashen waje Kuma muyi kidnapping na manyan mutane ko masu kudi muyi demanding kud'i masu uban yawa a wajan su daga baya in ya samu kud'in sai ya sake su su tafi amma wayan da suka mishi taurin kai kuma sawa yake a kashe su, a yanzu kam da Boko Haram suka yawaita yin b'arnan su shima sai ya saje dasu dan sai ya tura mutanen shi kauye guda a kashe iyayen ya kwashi yaran da yan matan ya tura su kasar da yake turawa a aiko mishi da kudin sa.

Wasu hawaye masu zafi da suka zubo mishi yasa hannu ya d'auke tare da sauke ajiyar zuciya yace" duk cikin mu yaran shi Emeka yafi ji dani saboda kwazo na akan aiki dan babu aiki da zai bani a samu kuskure ko tangard'a a ciki sai dai kash had'uwa ta da ZAREEFA ya fara canza ni banida burin da ya wuce kyautata mata da saka ta farinciki tun tana karama , a lokacin da ta fara girma sai wannan tausayin da nake mata ya rikid'a ya koma so , I so much love her har Ina ji a jikina in ban aure ta ba rayuwa ta ba zai tab'a daidaita ba.

A lokacin da na maida hankali na kan soyayya a lokacin kuma ya zama nayi sanyi a wajan aiki,duk aiki da Emeka zai bani sai an samu kuskure tun abin baya damun shi har ya fara damun sa kasancewar ya lura hankalin nawa ne sam baya tare dasu , a sirrance yasa aka fara bincike a kaina kan me yake d'auke min hankali har nake wasa da aikina haka, cikin kwana 2 aka kawo mishi rahoton soyayya nake da wata ta karbe min hankali har an saka mana rana auren ta zanyi.

Sosai hankalin Emeka ya tashi dan ko shi baiyi aure ba saboda aikin namu hana bukatan sirri shiyasa ya jingine batun aure a gefe sai dai in ya bushi iska ya kan shigo cikin gari ya kama hotel ya hole da yan matan da yake so, dan haka yasa a ran shi dole ne ya dakatar dani tun kamin in rusa mishi tsari.

Anan ya neme ni cikin lumana yake ce min in rabu da yarinya nan babu aure balle soyayya a cikin tsarin kungiyar mu ko na ga wani a cikin mu da mata? Sosai kalaman shi suka tada min hankali tayaya zan rabu da Zareefa yarinyan dana rayu da soyayyar ta tsawon shekaru kusan 7 yace min in rabu da ita?

Ban tab'a yi mishi musu ba balle gardama amma a ranan shafawa ido na toka nayi nace babu abinda zai saka in rabu da ita koda kuwa zan fita a kungiyar ne, sosai hankalin Emeka ya tashi yayi ta rarrashi na amma na nuna sam abinda yake so ba zai tab'a yiwa ba, gsnin da gaske nake Kuma rarrashi ba zai saka in canza ra'ayina ba yasa ya fito min a ainihin suffar shi da yake boyewa a gaban mu wato d'an kungiyar sirri ne shi yana yaye wata kofa sai ga kayan tsafin sa kalala sun bayyana a gaban mu , Yana fara wasu kalmomin tsafi sai ga wata yarinya ta bayyana tana tafiya a cikin kasuwa, wata wuka ya ciro ya daba a kirjin yarinyan nan sai ga jini ya fara zubowa cikin kwaryan tsafin amma a zahiri mutane sai gani sukayi ta dafe kirji ta yanki jiki ta fad'i mutane suka taru akanta ana neman ba'asi.

Juyowa yayi ya kalle ni yana murmushi yace ya umarce ni da in rabu da ita a yau din nan ba sai gobe ba ko kuma ya halaka ta, tunda na san kaina a cikin duniyan nan ban taba shiga rud'ani da tashin hankali irin wannan ranan ba jikina har karkarwa yake na shiga bashi hakuri akan kar ya kashe ta nayi mishi alkawari a yau zan rabu da ita.

Shine naje a wannan ranan nayi mata munanan kalamai duk dan taji na fita ranta , koda muka rabu ta shiga gida kasa tafiya nayi har Innar ta ta fito ta same ni a Lokacin kuka nake kaman karamin yaro sosai ta shiga tashin hankali take tambaya ta me yake faruwa nan nace mata rayuwata da nata duk na cikin hadari muddin in ya kasance muna tare saboda wasu dalilai daban dana lissafo mata yanda zata fahimta kuma Allah cikin ikon shi ta gamsun sannan na bar kofar gidan.

A zahiri na rabu da ita amma kuma a bad'ini ina tareda ita ko wani motsin ku akan ido na yake, na kasance kaman mutum mutumi komai na duniya ya fita akaina rayuwa ba Zareefa is like living in a hell, shiyasa lokacin bikin ta na kawo maka gudumawa ta akan ayi mata kayan d'aki na kece raini sanin gidan masu kudi za'a Kai ta amma dan mugunta irin naka ka cinye kudin kaki yi mata sai daga baya naji labarin shine na bawa mahaifiyar ta akayi mata duk abinda ya dace, wannan abinda kayi ya Kara harzuka ni dama ina neman hanyan dazan d'auki fansa akan ka shiyasa na fara ambaton sunanka da aka kama ni.

Shi kuma mai gidan mu na dad'e da d'aukan alwashin sai na d'auki fansa akan shi in tarwatsa rayuwar shi kaman yanda ya tarwatsa nawa shiyasa daya bani kud'i in sayi securities d'in Minister nayi zagaye na dawo ban saye su ba kaman yanda ya bukata, ni naso suka kamani dan ko harbin da kake gani a kafana ni na harbi kaina kawai dan a kama ni kuma nayi abinda ya tabbatarwa sauran yaran da muka zo tare na mutu na san iyanzu Emeka ya d'auka na mutu ".
[12/14/2021, 7:54 AM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Wannan page din naku ne masoya na kuyi yanda ku ka ga dama dashi, ina mika godiyata gare ku kan yanda kuka nuna min kauna ba abinda zance sai dai nayi muku fatan dacewa da duniya da kiyama ina matukar alfahari daku a duk inda kuke kan jajircewan ku sai da kuka sa na dawo online, Allah ya bar kauna bounch of love*.

*58&59*

A baya na kulla ce shi naji na tsane shi saboda duk halin da na tsinci kaina a baya shi nake daurawa laifin domin da bai guje ni ba da ban fad'a cikin tashin hankali da nake ciki ba, saidai wannan bayanai da naji yanzu ya ruguza min lissafi yasa naji zuciyata ta karye tausayin sa duk ya cika ni na irin rayuwar daya taso a ciki da kuma halin da maraici ya jefa shi a ciki.

Kuka sosai nake kaman raina zai fita yasa hankalin kowa na parlour ya koma kaina suka shiga bani baki dan sun san irin shakuwar da yake tsakanin mu dole ne inyi kuka.

Sai a lokacin Gwaggo Aisha ta kai duban ta gare ni a zabure tayi baya tana kare min kallo tun daga kan kayan jikina har tsarka da d'an kunne da na saka, sosai hankalin ta yayi kololuwar tashi irin rayuwar da take burin ganin yayan ta a ciki shine na samu.

Bayan an jajantawa juna Baban Dije yace mu fita a bar Baba ya huta, duk muna shirin fitowa sai ga jameela kaman an jefo ta ta fad'o d'akin tana layi, ganin mutane cike da parlour yasa ta fara bin kowa da kallo har idon ta fad'a kan Baban mu da yake kwance shima yana kallon ta, for the first time yaji zuciyar shi ta kuntata da yanayin da yaga 'yar cikin sa ta zama sanadiyan rashin kulawar shi gare mu.

Zaro ido tayi harda dafe kirji da murya ta yan maye tace " lah Baba dama basu kashe ka ba suka bar ka a raye har ka dawo gida...."

" Ke baki da hankali ne mahaifin naki kike fad'awa irin wayan nan kalamai” Gwaggo Aisha ta daka mata tsawa ta hana ta karasa maganar da tayi niyyan fad'a.

Kyalkyalewa da dariya tayi tana nuna uwar tata da hannu tace kai Umma bayan kece kika fara d'au......."

Fincike hannun ta da taji uwar nata tayi yasa bata karasa abinda tayi niyyan fad'a ba tabi bayan mahaifiyarta da take Jan ta kaman ta kife suka fita a d'akin duk muka bi su da ido kowa da abinda yake sakawa a zuciyar shi, Hajara kuwa duk kunya ya rufe ta ta kasa kallon 'yan d'akin.

Ajiyar zuciya Baban Dije ya sauke tare da furta " Allah ya kyauta, yanzu kowa ya fita a bar Yaya ya huta...." Bai gama rufe bakin shi ba kowa ya mike ana kara mishi Allah ya sauwake sannan muka fita tare da ja mishi kofa.

Maimakon Baba yayi baccin kaman yanda akace sai dai kunan da zuciya shi keyi ya hana shi jin rad'ad'in da jikin nashi ke mishi balle har yaji wani abu wai shi bacci, yanzu wannan 'yar cikin sace a haka har take mishi fatan mutuwa saboda abinda yayi musu. Tabbas ba zai taba ganin laifin kowa a cikin mu ba domin ya cancanci fiye da haka ma dama duk wanda Bai bi hanyar da Allah yace yabi ba dole zai ga sakamakon abinda ya aikata tun kamin akai ga zuwa kiyama.

Sai dai shi a yanzu babu abinda zaice sai ALHMDLLH ga Rabbil Izzatti daya ankarar dashi halin da ya jefa kan shi da iyalan sa amma ta ina zai fara gyara wannan babban barna da yayi???

Kuka sosai Baba yayi kaman karamin yaro Yana yi yana kara godewa Allah har la'asar tayi bai samu ya runtsa ba.

Gwaggo Aisha bata saki hannun Jameela ba sai da ta kai ta can cikin d'aki Dan ko a parlour basu tsaya ba, watsar da ita tayi a tsakar d'akin tayi taga-taga kaman zata fad'i da kyar ta samu courage ta tsaya tana auna mata harara tace" wai ke Umma meye haka ina cikin magana zaki wani jawo ni ki kawo ni nan kaman wacce ta fad'i ba daidai ba"

" Eh dole kice haka mana kina can kina kokarin tona min asiri cikin makiyana, ba zaki bari komai kike son cewa ki fad'a min a d'aki ba" gwaggo Aisha ta bata amsa itama tana mata mugun kallon.

"Ni ina ruwana duk inda naga dama zanyi magana ta kuma babu wanda ya isa ya hana ni, gobe zan dawo in karasa abinda nayi niyyan fad'a sai na fad'a wallahi" tace tana mai juyawa ta kama hanyar fita.

Cikin sauri gwaggo Aisha ta riko ta tare da fara rarrashinta kada tayi hakan domin ta san halin Jameela tsab zata aikata abinda yafi hakan ma tunda ba tsoron kowa take ji ba, da kyar ta rarrashe ta harda bata 200 kan ta bar maganan sannan ta hakura ta fita abinta cike da murnan ta samu na cakewa.

Duk yanda nake kuka Inna bata kula ni ba wucewa tayi ciki ta kama aikin gabanta, a nan parlour na zube kan kujera na cigaba da kuka na a wannan lokaci babu abinda nake so kaman in sanya shi a ido na domin akwai maganganu dayawa da nake son muyi dashi amma tayaya zan samu daman ganin shi waye zai kai ni???

Zafar gida ya wuce direct sai huci yake shi kad'ai a mota dan sosai kukan Zareefa ya tsaya mishi a rai shaid'an kuwa sai kimtsa mishi yake kan cewa kukan rabuwa da masoyin ta take, tsaki yaja tare da dukan staring da karfi Yana " da aure na akan ta take wannan kukan rabuwa da b'arawon ko kidnapper ko? Hmmmmm I will show her" yace yana dannawa mai gadi horn kaman zai cire mishi kunne.

Da gudu yazo ya bud'e gate d'in yana mishi barka da zuwa, ko kallon inda yake Zafar baiyi ba balle ya amsa mishi saima jan motan yayi dagudu kaman zai bi ta kan shi Allah ya bashi sa'a ya kauce cikin zafin nama yabi motan da kallo yana mamakin yau me ya b'ata ran mai gidan nashi haka ya shigo cikin fushi haka??

Ko parking d'in kirki baiyi ba ya fito cikin wani takun da zai tabbatar maka da ran shi a matukar b'ace yake ya nufi kofan parlour ya shiga ya kama safa da marwa shi kad'ai " na san yanzu Allah Allah take in sake ta dan ta samu komawa gare shi ko??" Ya tabayi kanshi.

Toh kai meye naka a ciki in ta koma gare shi ko ka manta ba son ta kake ba? Yaji zuciyar shi tana tuna mishi abinda ya manta " yes ba son ta nake ba but dole she should mind her business kamin in sa......" Yay shiru yana jin girman furucin da yake shirin furtawa kuma yana ganin abune da ba zai yiwu ba.

Jagwab ya zube akan kujera tare da dafe kan shi da hannu 2 yana mayar da numfashi dan ya rasa kalan tunanin da zaiyi.

Sai da yayi sallah la'asar sannan yaji zuciyar shi tana mishi sanyi kad'an-kad'an sakamakon tunanin da yayi na cewa yanzu fushi ba nashi bane dole yabi komai a hankali domin babu abinda fushin zaiyi saima kara jagula al'amura, sabon wanka yayi ya canza shigar sa zuwa shadda gezner armyn color d'inkin zamani kayan sun zauna sosai a jikin shi sai maiko yake amma bai saka hula ba sai lallausan gashin kan shi daya sha gyara yana d'aukan ido.

Cikin takun sa na cikakken namiji mai ji da class ya fito ya nufi motan shi bayan yayiwa kanshi wanka da turarukam shi masu dad'in kamshi, bai tsaya b'ata lokaci ba ya nufi gidan mu yana kara tausan zuciyar shi kan ya kau da idon shi kan duk yanayin da ya gan Ni a ciki saboda wannan kidnapper.

Ni kuwa a gida sai da Inna ta nuna min jan ido sannan na had'iye sauran kuka na ba dan raina yana so ba, nasiha tare da fad'a tayi min sosai akan kada In kuskura in kara nuna damuwa ta akan wani d'a namiji bayan miji na hakan zai iya haifar da babban matsala balle shi da kowa ya san munyi soyayya a baya.

Shiru nayi ina sauraron ta ba tare da nayi magana ba domin duk abinda zan fad'a ba lalle ne ta gane ba, ni ba kukan rabuwa da shi nake ba kawai dai ina kukan tausayin sa ne da kuma halin da yake ciki yanzu wanda nasan da kyar in za'a mishi sassauci a kotu, koma menene Allah yasa ayi mishi saukin.

Bayan munyi sallah la'asar muka ji sallaman Zafar a nan bakin parlour Inna, cikin azama Inna ta amsa tana gyara hijabin dake jikin ta dama bata cire ba ni kuwa ina kan sallaya ina ta rokon Allah ya fitar da Yaya na, sai da Inna tace mishi ya shigo sannan ya shigo kan shi a kasa kamshin turaren shi duk ya cika parlour.

A nitse ya kara gaishe ta ta amsa mishi tare da yi mishi sannu da zuwa ya amsa yana tambayan ya jikin Baba ta amsa da sauki ta tashi ta fita zuwa d'akin Baba dan dubawa ko ya tashi.

"Let's go home" yace yana leken fuskata dan naki dagowa in kalle shi duk da ina jin yanda Inna ta zungure ni da kafa kamin ta fita sarai na gane nufin ta cewa in gaishe shi amma sai nayi kaman ban fahimci me take nufi ba na watsar dashi, " hello " yace yana shafa min gefen fuskata.

Cikin sauri nayi baya dan ban san lokacin da ya iso gaba na ba sai jifa na yake da tsadadden murmushin sa mai kara mishi kyau, Ni bai san duk haushin sa nake ji ba kan me yasa ya dawo yanzu dan nafi son in kai dare kamin ya dawo.

"Let's go home Baby yanda zan ji dad'in rarrashin ki kinga nan gidan Inna ne I will not be comfortable to do....."

"Ni ban nemi rarrashin ka ba pls leave me alone" na katse shi sabin hawaye na taruwa a ido na, zai kara yin magana muka ji muryan Inna tana sallama cikin sauri ya koma inda yake zaune da farko nima nayi saurin share hawayen fuskata tare da fara magana bayan na amsa sallamn Inna kaman tun farko hira muke.

"Eh ai tunda muka fito Baba yake ta bacci ban kara komawa wajan shi ba" na karashe da murmushi a fuskata, shima murmushin ya min yana kara tsunne kai ganin Inna ta shigo.

"Muje mu kara duba jikin nashi sai mu wuce gidan tunda kince kina son mu isa da wuri" yace da d'an muryan da Inna zata iya jinsa domin da ta shigo direct tayi hanyan d'akin ta ba tare da ta kalli inda muke ba, takaici naji ya cika min ciki Ni yaushe nace zan tafi har yake min sharrrin wai ina son mu isa da wuri?" kanne min ido 1 yayi yana dariya kasa-kasa, Ni ko baki na murkuda mishi ina hararran shi ta gefen ido.

Nuna kan shi yayi da yatsa yana kallo na alamun dashi nake, maimakon in bashi amsa sai kara murkuda bakin nayi murmushi yayi tare da cizon lip d'in shi na kasa, duk abinda muke akan idon Inna da take hango mu daga can cikin d'akin ta zuciyar ta fari ka ganin ma kwantar da hankalina.

"Zareefa"! Naji muryan Inna tana kwala min Kira, amsawa nayi tare da nufan d'akin nata cikin natsuwa.

"Ki tashi ku tafi kada dare yayi muku, ku biya kuyiwa Baban ku sallama sannan ku wuce" tace min lokacin da na karaso inda take zaune a bakin gadon ta.

B'ata fuska nayi kaman zanyi kuka na bud'i baki zanyi magana ta katse ni da " bana son jin komai wuce ku tafi".

Dole na fito ina kara b'ata fuska alaman saura kiris in fashe,yana ganin na fito shima ya mike yazo kusa dani ya durkusa kasa yayi mata sallama ta amsa da mu gaida gida, fuuu na fice na bar shi a baya zuwa sashen Baban mu na same shi zaune akan sallaya da carbi a hannun shi yana ja, kallon mamaki na bishi dashi wai yau Baba ne da carbi?.

Da sauri na shanye mamaki na tare da dukawa kasa muka fara gaishe a tare da Zafar da shima shigowar shi kenan, amsa mana yayi da kulawa kaman ba Baban mu da na sani ba a baya daga nan godiya ya kara yiwa Zafar shi kuwa yana kara tsunne kai yana babu komai saboda kunya wasu kalaman Baban ke bashi.

Abin mamaki dai baya karewa a duniya dan Baban mu ne ya maida hankalin shi kan mu kacokan yana mana nasiha akan hakuri da zaman duniya sannan yace mu tashi mu tafi gida kada dare yayi mana.

Godiya muka mishi muka mike muka fito ni duk jikina yayi sanyi akan yanda Baban mu ya dawo lalle ba karamin wuya ya sha a hannun su ba daya canza farat daya.

Shi ya bude min motan na shiga na zauna sannan shima ya zagaya ya shiga ya zauna yana kallon yanda na dawo so cool, marairaice fuska yayi kaman zaiyi kuka yace " Allah sarki ni,i na rasa ya zanyi komai nayi banyi daidai ba"

Ban san lokacin da nayi murmushi har hakorana suka bayyana saboda salon da yayi amfani dashi yayi maganan dole yasa mutum dariya, dariyan shima yqyi ganin ya saka ni murmushi sannan ya ja motan muka hau hanya.
[12/14/2021, 7:54 AM] Golden Pen Writers Associ: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Wannan page din naki ne rahama lawal Umar ( ummu Farhan ) kiyi yanda kike so dashi ,alkhairin Allah ya isa gare ki a duk inda kike nagode da soyayyar gare ni Allah ya bar zumunci Ameen*

*Sorry last page nayi mistake wajan saka number maimakon 54&55 , na saka 44 &45.

*56&57*

Baba gaba d'aya jikin shi a mace yake da jin bayanan Abdulbasit tabbas ya tafka kuskure ko Kuma yace yana cikin b'ata, son duniya da sharrin shaid'an ya kai shi ga aikata duk abinda yayi sai dai komai rubutattace ne a kundin kaddara wanda ba makawa sai ya samu mai shi, in da ya kasance mai kulawa da iyalin sa da duk haka bata faru ba.

"Na san ba zan kai labari ba dan kashe ni zasuyi kuma nima hakan nake fata domin tunda na rabu da Zareefa ban tab'a jin dad'in rayuwata daidai na second d'aya ba, nayi jinya a boye ba tare da kowa ya sani ba da naje asbiti doctor yace na kamu da ciwon zuciya mai tsanani , shiyasa na kudiri aniyar ganin bayan Emaka kamin in karasa 'yan kwanaki da suka rage min" Abdulbasit ya karasa da fashewa da kuka da bai samu daman yi ba duk watanin nan.

Hawaye da suka zubo mishi Baba ya share zaiyi magana Baban Hamis ya kashe system d'in shi ya juyo yana facing abokanen aikin shi da duk suma labarin ya girgiza su kaman yanda ya girgiza shi shima sai dai kowannen su ya shanye abin sa a rai ba zaka tab'a fahimtar komai akan fuskokin su ba.

Gyaran murya yayi sannan ya fara magana" duk da komai ya bayyana Ina son shi wannan Abdulbasit d'in ya amsa laifin shi da bakin shi sannan yayi jagora inda za'a samu gang d'in nasu gaba d'aya" babu wani ja suka nuna gamsuwar su kan hukucin da ya yanke bayan dan tattaunawa da sukayi suka wuce offices d'in su.

Zafar bai masu isowa gidan mu ba sai da ya tsaya yayi sallahn azahar ya tsaya a wani shopping mall yayi sayayyan kayan masurufi masu yawan gaske sannan ya karaso gida.

A waje yanzun ma yayi parking din motan shi ya samu yara a kofar gidan suna jiran a gama abincin sadaka a raba musu yace su shigar da kayan cikin gida nan da nan ko suka fara shigowa da sayayyan da yayi zuwa tsakar gida suna ajiyewa, Inna da fitowar ta kenan daga wanka tana neman Ibrahim ya fara kiran masu karban sakadan tayi arba dasu suna ta shigowa da kaya suna jibgewa hayaniyar su duk ya cika gidan.

Cike da mamaki tabi su da kallo kamin ta tambaya Ibrahim da shigowar shi kenan rungume da carton na indomie yace " Innan Zareefa mijin Zareefa ne yace mu shigo da kayan nan kuma yace wai ta fito su tafi".

Cizon yatsa Gwaggo Aisha da take leke ta window tayi tana jin bakinciki da takaici ya kume ta dole ne tayi maganin Inna ta shiyasa take ta d'agawa mutane hanci a gidan ita wai 'yar ta na auran mai kudi, Hajara da shigowan ta kenan zata wuce ciki ta ga yanda take rike da labule tana kallon yaran fuskarta kuwa kaman anyi gobara sai cizon d'an yatsa take, kain ta girgiza kawai tayi wucewar ta ciki tana mata addu'an shiriya ta barta anan tsaye tana faman leke .

Na fito daga bathroom d'in daki na kenan fuskata na d'igan ruwan alwala da nayi murmushi nake sosai ina jin kaman babu inda na tafi iya watanin nan kaman bacci nayi na tashi haka nake ji domin komai na dakina yana nan tsab ba abinda ya canza kaman lokacin da nake nan.

Kara fad'ad'a murmushi na nayi ganin Inna zaune a bakin gadon tana jiran fitowa na kamin in samu daman yi mata magana tace " kina idar da sallah ki fito ku tafi yazo yana jiran ki a waje" a take farar dake fuskata ya kau na kwab'e shi kuwa kaman zanyi kuka saboda ko kad'an ban saka ran tafiya yanzu ba na zata sai dare zai dawo.

"Bana son shashanci kiyi sallah ki fito nace sannan kada ki yarda in kara dawowa dakin nan baki fito ba kema kin san sauran" cewar Inna kenan tana barin d'akin, hawayen da suka zubo min na share tare da karasowa ciki na shimfid'a abin sallah na fara sanin halin Inna in ta shigo ba zatayi min da dad'i ba.

Har na idar da sallah ban daina hawaye ba dan ko kad'an bana son tafiyan, dole na na fito parlorn Ina sharar kwalla na samu Inna zaune da wani babban leda kusa da ita tace in shiga d'akin ta muyi sallama dasu Maa, jiki ba kwari na shiga na same ta harda 'yan uwan Baba duk sun idar da sallah kowacce rike da carbi suna lazimi.

Har kasa na zauna dan niyyan yi musu sallaman amma na kasa furta komai sai hawaye na da suka karu, dariya suka fara min wai Inna ta shagwab'ani dayawa daga baya kuma suka shiga yi min nasiha kan in kara hakuri domin zaman gidan miji saida hakuri, ba gidan miji ba duniyar kanta in kana son kaji dad'in ta toh sai da hakuri da kauda kai.

Tun ina kuka har na daina saboda yanda suka kashe min jiki daga nan suka ce in tashi in tafi yana Jira na, tashi nayi na fito Inna tana nan a inda na barta, miko min ledan tayi tace to in tafi mu gaida gida maimakon in karb'a kuka na saka mata ina sai naci abinci domin nayi missing girkin ta.

Kala bata ce min ba sai ganin ta nayi da wani madaidaicin warmer ta zubo min abincin sadaka da sukayi tace in naje gidana inci kuma in biya wajan sauran matan gidan inyi musu sallama, dole na karb'a na fito Inna Asabe ita na fara yiwa sallama sai maman Dije ban shiga wajan Gwaggo Aisha ba kasancewar Hajara tace min ta tafi anguwa, a kofar d'akin su na tsaya dan muyi sallama amma sai ta karb'i kayan hannu na ta fara taka min tare muka fito bakin gate.

Ta window Gwaggo Aisha take leken mu har muka fita bakinciki kuwa kaman ta had'ye zuciya ta mutu take ji wato na shiga ko Ina nayi musu sallama ita da na raina shine ban shiga mata ba ? Koda yake ta san Inna ce ta kitsa min hakan , ita kuma Hajara dan rashin zuciya ina kanwar bayan ta shine harda karban kayan hannu na tayi min rakiya.

Yana ganin fitowan mu yayi saurin bud'e min kofan mota dama yana tsaye a jikin motan ne, gaishe shi Hajara tayi tare da saka min kayan a mota sannan tayi min waving ta koma cikin gida.

Tsaye nayi ina kumbura fuska da tura baki gaba dan gaba d'aya haushi shi nake ji na me yasa bai barni na kai dare a gidan mu ba, fuskar shi d'auke da fara'a yace " shigo mu tafi mana 'yan mata na?"

Ko kallon shi banyi ba na shiga ina jin haushin sunan daya kira ni dashi wai 'yan matan shi ko ta ina na zama 'yan matan shi oho, rufe min kofan yayi ya zagaya ya shiga mazaunin driver yayi reverse muka kama hanya har sannan naki kallon side d'in da yake kacokan na maida hankali na kan hanya shi kuwa sai juyowa yake yana kallo na .

A wani restaurant ya tsaya yana kallo na nima jin mun tsaya kuma bamu kai gida ba yasa na juyo na dubi side d'in shi caraf ido na cikin nashi ya wani kashe min ido tare da daga gira daya alaman ya dai? Kawar da kaina nayi ina kara turo baki , da san irin wannan kallon yake min da ban juyo ba na kalli inda yake ba dan sosai ya kashe min jiki da salon shi.

"I will be right back wifey" yace min cikin wani husky voice sannan ya fice na bi shi da ido har ya shige ciki, ajiyar zuciya na sauke mai karfi ina kara jin son shi na ninkuwa a zuciya ta " how I wishh......." Nace Ina lumshe ido tare da fad'awa duniyar tunani har ban san lokacin da ya dawo ba sai lallausan tafin hannun shi da naji akan fuskata yana shafawa a hankali yasa na bud'e ido na a zabure ina watsa mishi mugun kallo d'an dariya yayi yana d'aga hannun shi sama alaman surrender.

"Tunanin me kike haka da har ba kiji shigowana ba" yace yana juyowa gaba d'aya shi gare ni bance mishi komai ba na sunkuyar da kai na kasa hawayen da ban san na menene ba suka fara sauko min.

"Ohh shiitt me yasa kike min asaran hawayen ki masu tsada da darajan nan, in maganan Baba ne I promised you babu abinda zai same shi kuma soon zai dawo gida pls ki kwantar da hankalin ki kinji " yace yana miko min tissue .

Banyi gardama ba na karb'a na goge ido na tare da gyad'a mishi kai a hankali, ajiyar zuciya ya sauke yana "good girl" sannan yayiwa motan key muka mike hanyan gida, koda muka iso gida ya hana ni d'aukan kayan yayi shi ya shigo mana dasu duka har parlour na ya kawo min kayan sannan ya ce in fito muci abinci.

"Ni na koshi "nace ina cire hijabin jikina tare da nemawa kaina wajan zama, marairaice fuska yayi yana kallo na can kuma sai ya zauna kusa dani yace " haka mukayi da ke, i thought mun riga da munyi solving komai before mu fita, meyasa kike son maida mu baya pls ki bar komai ya wuce kinji we are now good friends uhum?" Ya karasa cikin rarrashi ya kama hannu na ya mikar dani muka fito, bai saki hannu na ba kaman yanda nima na kasa yi mishi musu har muka isa dinning.

Kujera yaja min na zauna sannan shima yaja ya zauna ya fara firfito da kayan kwalama da ya sayo mana a restaurant " zabi abinda zaki my babe" yace yana turo min su gaba na.

Tsam na mike ba tare da na bashi amsa ko na kalli tullin abincin da ya turo min ba na wuce ciki abina, da kallo ya bini zuciyar shi na mishi wani irin share shi da nake yi, kasa tab'a komai yayi shima ya ture su gefe ya zuba tagumi yana zurfafa tunanin ta ina zai b'ullo min ya shawo kaina, yaga na dawo da warmer da Inna ta zubo min abincin a ciki na ajiye sanna na zauna ina kokarin bud'ewa .

"Wow ashe kayan dad'i kika kawo mana daga gida" yace yana kallon yanda na cika plate d'ina kuma bani da niyyan zuba mishi, amma jin yanda yayi maganan cikin natsuwa da danganta gidan mu da masu yasa shima na zuba mishi na tura gaban shi ba tare mun had'a ido dashi ba.

Kara jawo plate din yayi gaban shi ya saka spoon ya cika da jallof din shinkafan da yayi shar dashi da tarin nama a ciki kaman ba abinncin sadaka ba ya kai bakin shi a take ya lumshe yana " hmmmm ashe a wajan Momyn mu kika koyi daddadn girki nan, sai dai ita nata yafi naki sau goma kullum Ina santin naki ashe ga original din nan naki photo copy ne".

Ban san lokacin da na d'ago kai muka kalle shi ba fuskata d'auke da murmushin jin dad'in yanda ya yabi Inna ta for the first time naji ya burge ni ban san lokacin da na fara bashi labarin yanda yan gidan mu suke santin girkin ta kullum manya da yara duka.

Cikin jin dad'in yanda na saki jiki muna labari dashi ya rinka ja na yana yabon gidan mu daya lura shine abinda nafi so kuma yake sakani farinciki, sai gashi mun cinye abincin tas harda karawa da fruit sauran kayan kuma na Kai kitchen na ada na su.

Har dare muna tare yana cigaba da jana a jiki babu laifi nima na sake sosai tare mukayi kallo na kawo mana su alewan madara dasu gulli shiwa da Inna ta had'a min acikin ledan dana taho dashi harda su tsumi a ciki sai dai su can cikin drower na bud'e na adana su cos ban san amfanin su a yanzu ba ,har zuwa goman dare muna tare sannan na mishi sai da safe na shige d'aki na bar shi zaune yana jin kaman ya biyo ni mu kwana tare amma ya daure shima yayi d'akin shi yana ganin nesa tazo kusa tunda har ya gano abinda yake saka ni farinciki lokaci d'aya.

Da washe gari haka na taso cikin walwala dan kasncewar mu tare jiya yasa na rage damuwan da yake zuciya ta sosai, kitchen na shiga na fara nema mana abu mai sauki da zamu yi breakfast dashi bayan na gama kimtsa gidan tsab sai kamshin turaren wuta yake tashi ta ko Ina.

Na gama komai cikin kankanin lokaci na jujjuye su a warmers ina cikin juye tea da na dafa da kayan kamshi a flaks naji numfashin mutum dab dani a tsorace na juyo saura kiris ruwan shayin ya zube a kafana yayi saurin tarowa ya rike yana " hey be care full zaki kona wannan kyakkyawan kafan naki ki min asara" bance mishi komai ba sai zamewa da nayi na bar mishi shayin na koma gefe shi kuma ya cigaba da juyewan.

"Ina kwana " nace mishi a hankali Ina kallon kasa.

"Da fatan princess d'in Inna ta tashi lafiya" yace yana murmushi.

Nima murmushin nayi jin ya Kira ni da princess d'in Inna, d'aukan tryn dana jera kayan Karin a kai ya fita zuwa dinning fuskar shi d'auke da zallan farincikin ya samu logo na.

A wajan cin abincin ma haka yayi ta ja na da hira wai abincin Inna na jiya yafi dad'i wai ko dai zamu koma kai mata kwanon mu kullum tana zubo mana abinci, dariya nayi sosai dan ba karamin dariya maganan nashi ya bani ba.

Sai da muka gama yace min in shirya muje gidan mu in ya ajiye ni zasu wuce barrack da Baban mu yake da Baban Dije saboda yau da safen nan aka kira shi kan suje by 12.

Cikin azama kuwa na koma d'aki na fad'a bayi dan yin wanka zuciya ta cike murnan yauma zan ga Inna ta, ban b'ata lokaci ba na fito cikin shirina da nayi da wata atamfa super golden da adon fari a jiki shiyasa mayafi, takalmi da jaka da na riko duk suka zama farare, d'an kunne da sarka da na saka suma white pure gold ne dan haka ba karamin kyau nayi ba.

A parlour na tadda Zafar da shima kaman had'in baki ya saka wata tsadaddiyar shaddar shi fari sol da hula kindai da akayi da zare Mai golden da fari, takalman shi da agogon hannun shi suma duka farare ne sosai muka shagala da kallon juna kowa na yaba kyan da d'an uwan shi yayi a zuciya.

Da kyar na samu na janye ido na daga kan shi na mayar kasa Ina wasa da gefen mayafina naji muryan shi" let's go" yace bayan ya sauke nauyayyen ajiyan zuciya.

Gaba yayi nabi shi a baya zuwa inda motocin gidan suke ya bud'e min wata sport car fari na shiga na zauna sannan shima ya zagaya ya shiga yaja muka kama hanyan gidan mu, cike da nishad'i yake tukin sai murmushi yake ta sakewa shi kad'ai nima yau ban juya kaina gefe ba amma Kuma ba shi nake kallo ba ta kasan ido nake kalon shi.

A kafar gidan mu yayi parking Baban Dije da kawun su 2 da suka zo dama suna tsaye suna jiran zuwan shi, zan bud'e kofa in fita naji yauma a kulle a shagwab'e na juyo ina kallon shi tsabanin jiya da nake aika mishi da mugun kallo.

D'an dariya yayi yana d'aga min gira d'aya yace " in ba dan nayi locked ba da haka zaki fita ki bar ni babu sallama" turo baki nayi na d'auke kaina toh wani irin sallama ne da sai ya wani rufe kofa, bakin nawa da yake matukar birge shi zubawa ido yana ji Ina ma Ina ma.....

Jin shiru bai min magana ba kuma bai bud'e min kofan ba yasa na d'ago muka had'a ido alaman kiss ya min da bakin shi sannan ya min blowing yace " take care of yourself for me princess" duk kunya sai ya rufe ni na rasa yanda zanyi shi Kuma sai murmushi da naji yayi mai sauti sannan ya bud'e mana Lock d'in motan , shiya fara fitowa sannan nima na fito ganin iyayen nawa yasa na Kara jin sabon kunyan kaman kasa ya bud'e in shiga haka nake ji sabida dadewa da mukayi a mota kada suyi mata wata fassara.

Har kasa ya duka ya fara gaishe su nima na zagayo na durkusa na hau gaishe su cike da kunya, cike da kulawa duk suka amsa sannan ni na wuce cikin gida su kuma daga nan barrack suka wuce amsa Kiran Baban Hamis.

Da yake an san da zuwan su babu wani shamaki ko dogon bincike aka bar su suka wuce, direct office d'in shi wani sojan yayi musu jagora suka samu gaba d'ayan su da abokan aikin shi suna jiran isowan su.

Bayan gaishe-gaishe Baban Hamis yayi musu bayanin Baban mu bashida laifin komai hasalima shi wanda suka kama da wani dalilin shi daban wajan yi mishi wannan sharri, nan duk suka hau hamdala daga baya kuma aka kunna musu video da suka d'auka ta cctv camera suka kalla, duk mamaki ya cika su Baban Dije jin wai Abdulbasit yayan Zareefa shine yayiwa baba wannan d'anyen aiki, gaskiya ba zaka tab'a shaid'an mutum ba jibi yanda wannan mutumin yake komai kaman na Allah ne shi ashe mugu ne na bugawa a jarida?.

"Tun jiya mun saka shi Abdulbasit d'in gaba ya kai ma'aikatan mu mab'oyan gang d'in nasu dake can dajin mafa Kuma Alhmdlh Allah ya basu sa'an cafke su duka yanxu haka duk suna hannun mu zamu tura su Abuja inda za'a yanke musu hukunci" cewan Baban Hamis kenan, nan ma kara godewa Allah sukayi sannan suka gode mishi shi kuwa Zafar taf ya cika saura kiris ya fashe dan lokacin an tafi d'auko musu Baba suke maida labarin irin soyayyan da mukayi yayan nawa.

Suna zaune a wajan aka shigo da Baba da ko mikewa baya iyayi jikin sa kuwa duka ba kyan gani saboda kumburin da yayi hatta fuskan shima a kumbure yake, da gudu Baban Dije ya taro shi dan suna zuwa tsakiyar office d'in suka sake shi suka juya abin su.

Duk kan shi sukayi suna yi mishi sannu , Baban Hamis hakuri suka basu tare da cewa zasu iya tafiya dashi ,haka suka fito dashi suna rirrike dashi suka saka shi a mota direct wani private hospital dake nan wulari area Zafar ya kai Baba, nan da nan kuwa suka karbe shi su fara mishi treatment su kuma suka fita masallaci dake nan cikin asibitin yin sallah azahar.

Koda suka dawo rigima suka tarar tsakanin Baba da likitocin sunce dole ne su bashi gado yayi kwana 2 har yaji kwarin jikin sa shi kuma ya ce sam bai san zancen ba shi gida zai tafi, su Baban Dije suma sun saka baki amma fa Baba ya kafe kan cewa ba zai zauna ba.

Zafar ne yace a bar shi su tafi gidan in yaso zai d'auko doctor ya rinka zuwa yana duba shi kullum, su Baban Dije sun gamsu da bayanin Zafar dan haka ba b'ata lokacin suka saka shi a mota sai gida.

A gida kuwa dana shiga na iske kowa na cikin farinciki kaman Baban ya dawo duk yan uwa sun taru ana taya juna murna na samun labarin sa da akayi sai sakawa Zafar albarka suke da addu'oin gama wa da duniya lafiya.

La'asar dai-dai mukaji muryan su Ibrahim suna ihun murna ga Baba ga Baba, har rigen-rigen fitowa muke a tsakar gida muka gan su suna kokarin wucewa dashi d'akin shi.

Duk sai murnan mu ya koma ciki ganin yanayin shi kad'ai ya tabbatar mana ba karamin wahala ya sha a hannun su ba, rufa musu baya mukayi jiki a sanyayaye suka kwantar dashi a parlour shi nan kowa ya shiga yi mishi sannu ans barka da arziki.

Gwaggo Aisha da tunda abin nan ya faru bata tab'a shiga cikin mutane ayi jaje da ita ba sai kawai ganin ta mukayi sulum ta fado parlour harda kukan munafurci wai ai tunda aka kama shi ta shiga halwa tana addu'a bata fito ba sai yau da taji labarin fitowan shi.

Cike da mamakin karya da ta sambad'o kowa yake kallon ta amma babu wanda yace mata wani abu sai Baban Dije da ya shiga mayar mana labarin yanda baba ya shiga hannun sojoji dalilin Yaya na Abdulbasit.

Jagwab na koma ta zauna dabas tare da fashewa da kuka sosai , na tausayin Yaya na Allah sarki ashe ba abinda nake tunani bane ashe babban sadaukarwa yayi da soyayyar mu dan ya ceci rayuwata , ina ma zan iya ganin shi yanzu ina ma ina ma..........

Zafar kuwa zuciya da kishi me ya d'ebe shi ya bar mana parlour ba tare da kowa ya lura dashi ba dan a tunanin shi kukan rabuwa dashi nake yi.....

[2/23, 8:12 AM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*60&61*

Tunda muka d'auki hanya motan ya d'auki shiru babu mai magana cikin mu,kaina a kasa ina wasa da yatsun hannu na, shine dai yana tukin hankalin shi yana kaina sai juyowa yake yana kallo na dan baya so mu zauna shiru in har muna tare.

Tunawa yayi da babu abinda yake sakani farinciki da nishafld'i kaman hiran 'ya gidan mu yasa yace;

"yau baki kawo mana kayan dad'i a wajan Momy ba ko?" Yace yana d'an dube-dube ta wajan kafa na, ban san lokacin da murmushi ya tsubuce min ba na d'an kalle shi naga shima ni d'in yake kallo ya wani narkar da fuskar shi kaman yaro mai ji da shawgwab'a, sauke nawa idon nayi cikin sauri jin yanda zuciyata ta harba da karfi sabon kaunar shi na bin jikina nace;

"Ban kawo komai ba kasan muna can muna ta murnan dawowan Baba shiyasa Babu wanda ya mayar da hankali wajan yin wani abu a gidan dama naso sai dare ka dawo na san Inna zata yiwa Baba special amma shine ka dawo da wuri...." Nima na karashe cikin shawgwab'a da ya kara tafiya da imanin shi.

"Ohhh Soo sorryy my babe ban san cewa kina bukatan kaiwa dare ba ai da ban zo yanzu ba nd kema da naki laifin why not ki Kira ni ki fad'a min time d'in da kike son zuwa na" yace min cikin muryan lallqshi.

Ban bashi amsa ba amma har cikin raina naji dadin maganan shi, haka ya rinka jana da hira har muka iso gida shi ya bud'e min kofan motan muka shiga ciki ni dai sai kallon shi nake ta kasan ido ina mamakin sauyawan shi.

A parlour ya zube Yana" gosshh I'm tired" murmushi nayi na wuce ciki ina ce mishi "sai kace da kafa ka dawo gida?"

"Babu maraba 'yan mata na zo ki dafa mana abinci kalan na Momyn mu, I'm damned hungry" yace min cikin d'an d'aga murya yanda zan iya jiyo shi, ban bashi amsa ba sai dariya da nayi na ajiye su jakana na fito zuwa kitchen.

Tunanin me zan dafa mana mai sauki na tsaya yi sai gashi ya fad'o kitchen d'in yana " pls ina abincin nan da kika tab'a yiwa su Abba irin shi, kiyi mana shi dan Allah".

Zaro ido nayi nace " kai tuwon ndalayi.... wallahi akwai wahala fa" na karasa cikin shawgwab'an da ya kara zautar dashi domin yana bala'in son yaga ina yin hakan sai dai ba ko yaushe yake nasaran gani ba.

"Alright just cool anything else you want since daga hannun ki ya fito na san it will be delicious" yace cikon sanyi da kasala da suka sauko mishi lokaci d'aya, ni kuwa na zata saboda nace ba zan girka choice d'in shi bane ya zama haka cikin sauri nace " no shi zan girka mana saboda nima it's my favorite amma akwai sharad'i in ka aminci?"

Sai da ya jingina da fridge d'in dake bayan shi sannan yace " wani irin sharad'i ne haka?" Ya karasa yana aika min da wani irin kallo da ya haddasa min dauke ido na daga kan shi babu shiri.

" Tare zamuyi zaka taya ni aikin " nace ina dariya, nad'e hannun rigan shi ya fara yana " dame zan taimaka miki?"

"Laaaaa! Wasa fa nake maka kaje ka zauna yanzu zan gama insha Allah" nace masa ina cigaba da dariya.

"No ai tunda kika fad'a hakan toh tabbas tare zamuyi, ki bani ko albasa da tomatoes in yanka miki".

"Albasa akwai zafi fa ba zaka iya ba" na kara ce mishi . " No don't worry just give me" yace yana kara gyara tsayuwan shi a jikin kitchen cabinet d'in, ban musa mishi ba na dauko albasan daidai yanda nake bukata da wuka da chopping board na ajiye mishi sannan na juya na kama aikina.

Jan hanci da yake akai akai yasa na juya na kalle shi, ban san lokacin da na tuntsire da dariya ba harda dukawa kasa ganin Zafar da hawaye shame shame kuma bai fasa yankawan ba.

Shi kuwa tsayawa yayi yana kallo na wani abu yana tsirga mishi a zuciyar mai kama da nishald'i nishad'i farinciki farinciki dan bai tab'a gani na ina dariya haka ba, ashe in ina dariya nafi kyau, inko hakane zai kara d'aura dantse wajan ganin ya sanya ni cikin dariya kullum.

Yana kallo na tare da cigaba da yanka albasan shi fuskar shi cike da annuri mai kayatarwa, "ouchhh" yace yana jefar da wukan sakamakon yanke yatsan shi da yayi abinka da lafiyayye nan da nan sai ga jini kaman an bud'e tap, had'iye dariyan nayi babu shiri na taso da gudu na kama hannun.shi da yake yarfewa mukayi wajan sink na bud'e tap na saka hannun shi a kasan ruwan yana wankewa sai sannu nake jera mishi.

"Kaga abinda nake gudu ko? Gashi ka yanke yatsanka ji yanda jini yake zuba " nace ina kokarin d'aure inda ya yanke da farin handkie saboda jinin ya tsaya, shi kuwa kawai kallon fuskana da yake mai dauke da damuwa kaman in fashe da kuka haka nake ji.

Ganin zan dago yasa ya fuske yana " ai ba wani abu bane dan mutum yana aiki ya yanke a kitchen, it's normal ai" a'a ni dai nagode kaje ka huta" nace ina karbe wukan daga hannun sa.

"Ok toh ki bani wani aikin" yace min bashida niyyan fita ko kadan " hmmmm " kawai nace na cigaba da girki na, shi kuwa kememe yaki fita yana nan tare da ni duk abinda na kama zanyi sai ya saka hannu wai shima sai yayi har tuka tuwon ndalayi shima saida yasa hannu, duk yanda naso daurewa in rabu dashi kasawa nayi na rinka dariyan sa.

A haka muka karasa aikin yana ta min shirme kala kala ina shan dariya na, tare muka jera abinci akan dining sannan na wuce daki na bar shi domin magariba ya gabato, wanka na fara yi sannan na d'aura alwala na fito na shimfida abin sallah na kabbara sallahn magariba jin har an fara a wasu masallatai.

Ban fito parlour ba bayan na idar da sallahn na cigaba da da addu'oina har aka kira Isha'i shima nayi sannan na mike tare da cire hijabin dake jikina na ninke na ajiye a wardrobe,ina kan ninke sallaya wannan fitinannen kamshin sa mai saka natsuwa ya fara min sallama sannan naji muryan shi mai cike da natsuwaa yayi sallama.

Amsawa nayi tare da ajiye sallaya a mazaunin shi " fito muci abincin mana ni yunwa nake ji" yace yana shafa cikin sa, murmushi nayi ina kallon yanda kananan kaya da ya saka ya matukar kara fito da kyan sa da alamu shima wankan yayi.

Gyada kaina kawai nayi muka fito, shi ya ja min kujera na zauna sannan shima yaja na kusa dani ya zauna ba bata lokaci na fara serving d'in shi zan zuba nawa ya rike min hannu wai in bar wannan d'in ma ai ya ishe mu.

Kallon shi na tsaya yi cike da mamakin ta yaya zan iya cin abinci tare da shi? Ganin irin kallon da yake min yasa na sauke nawa idon nayi shiru, Bismillah ya min ya d'auki loman farko ya kai bakin shi

"Hmmmmmm delicious wow..." Yace yana wani lumshe ido ya juyo yana tauna abincin da yake bakin shi cikin wani salo mai burgewa " jinjina ga Innar mu, gaskiya da za'a bud'e eatery ana saida girkin ta na tabbata people will go crazy" yace yana kara kai wani loman bakin shi ni dai sai bakin nashi nake kallo ina jin farinciki yanda yaba min Inna ta.

"Open ur mouth girl kiji yanda yake nasan sai kin fin santi " yace yana nufan bakina da spoon d'in da ya debo abincin, Bai tsaya jirana ba ya kai abincin direct cikin ikon Allah ban iya musa mishi ba na bud'e bakin ya juye min abincin.

Tsatsare ni da ido yayi yana kanne min ido d'aya yace" ya kika ji? Nasan tunda kika fara girkin nan ba kiyi testing ba". Murmushi kawai nayi ina taunawa a hankali.

Haka ya rinjaye ni da wasa da dariya muka cinye abincin dana zuba mishi malmala 2 har ya kara mana ban ankara da irin lodin da nayi ba sai da naji ciki na yana barazanan fashewa sannan na cire hannu na ina cewa na koshi.

"Haba dai nida nake Shirin kara mana zaki ce kin koshi?" Yace yana min wani kallon kasan ido wanda yake kara dagula min lissafi akan shi, girgiza kai nayi da wuri ina mai mikewa a wajan tare da fara tattara kayan da muka bata na kai kitchen na wanke su na ajiye komai a mazaunin shi sannan na fito a lokacin shima ya tashi a kan dinning d'in ya koma parlour yana kallo

.

Zuwa nayi zan wuce ciki yace min in zo in zauna mana muyi kallo ko hira in daina zama ni kad'ai a d'aki, samun kaina nayi da kasa musa mishi na dawo na zauna kusa dashi da yake yana zaune ne akan kujera 3 seats.

Mbc2 yake kallo ana haska wani film gashi nan shi ba advanture ba shi ba horror ba amma sai shegen dad'i,ni kuwa in akwai abinda na tsana shine horror film amma saboda dadin da ya min na kasa tashi a wajan muka kalla har zuwa karshe duk da a lokacin kaman kace min aaarr in fita a guce.

Ganin dare baiyi nisa ba ya mayar da tashan zuwa mbc Bollywood yana ai ya san nafi son Indian films ba Ni kad'ai ba most haka mata muke, murmushi kawai nayi ba tare da na musa mishi ba dan na san gaskiya ya fad'a ina bala'in son kollon duk abinda ya shafi India.

Raaz shine film d'in da suke haskawa a wannan daren yayi bala'in dad'i amma akan fatalwa akayi film d'in ga d'an banzan tsoro gaba daya tsigar jikina sai mikewa suke saboda ina masifan tsoron abinda ya danganci fatalwa ji nake kaman gaske ko hiran naji anyi dare nayi zan ta tuno da labarin in kasa bacci wani lokacin sai na koma dakin Inna nake samun bacci

Bamu gama kallo ba sai wajan 12:30 , duk a tsure nake ina tunanin ya zanyi bacci yau? Haka na daure nayi mishi sai da safe na wuce d'aki na ina ta waige-waige duk da ga hasken fitulun d'akin kaman rana amma ji nake zan ga gilmawan wani abu, wankan ma a gurguje nayi shi na fito nazo gaban mirror da lalume na kwashi turaruka na koma bakin wardrobe sannan na bud'e ido na wai duk ji nake in na kalli madubi a wannan lokacin zan ga wani abin tsoro.

Rigan bacci na saka irin mai guda biyun nan na cikin karami ne mai hannun shimi ga tsayin shi bai wuce guiwa ba
sai na saman shi da yake dogo har kasa da dogon hannu sai dai gaban a bud'e yake sai igiya ta tsakiya da mutum zai daure in ya saka, turarukan na feffesa na dawo kan gadon na kwanta da tsoro fal a raina bayan na ajiye dogon rigan baccin a gefena na jawo bargo na rufu sannan na fara addu'oin ina ta shafawa a jikina.

Kasa kashe wutan d'akin nayi na lumshe ido da sunan bacci amma sai na kasa baccin sai films din suke ta dawo min kaman yanzu nake kallon,wani motsi motsi kunnuwa na suka fara jiyo min ta gefen gado, cikin hanzari na jawo bargon na rufe har kaina tare da kara rutse ido na da karfin gaske ina karanto duk addu'an da yazo bakina.

Bargon da yake tab'a ni ji nayi kaman mutum ne yake min tafiyan tsutsa da mugun gudu na wacalar da bargon na mike jikina na bari, dakin na tsaya kallo kaman me neman wani abu tsaban na saka tsoron a raina har golmawan inuwan mutum na gani, ban san lokacin da na kurma ihu da dukkan karfina ba na manne a jikin bango jikina na kara bari gumi sai tsiyaya yake a jikina.

A bangaren Zafar kuwa zuciyar shi fes ya shiga dakin shi ya hau cire kaya, yana gama cirewa ya fad'a bathroom dan yin wanka yana imagining ina ma muna tare da ba abinda zai hana muyi wankan tare.

"Sannu bata hana zuwa" yace yana lashe lips d'in shi na kasa tare da rarrashin kan shi cewa ya kara hakuri tunda har na fara sakin jki dashi mun kusan zama abu 1. Koda ya fito daga wankan singlet da boxer farare kal ya saka yabi jikin shi da turarukan shi masu kamshin gaske sannan ya kara karfin Ac yana shirin hawa gado yaji razqnannen ihu da na sake.

A guje ya fito bayan yayi wurgi da remote din hannun shi ya banko kofan d'akin ya shigo can ya hango ni manne da gini duk na fita hayyacina in banda karkarwa da gumi ba abinda jiki na yake, da gudu ya karaso wajena yana tambayana meya faru?.

Ina jin muryan shi na juyo na fad'a jikin shi tare da kankame shi ina cigaba da kukana, shi kuwa sai da yayi suman kusan ten seconds sannan ya dawo hayyacin shi,hannayen shi duka 2 ya saka ya kara manna ni ajikin sa yana aikin sauke tagwayen ajiyan zuciya yana jinsa a wata duniya daban, da kyar ya samu ya had'iye wani busahhen yawu daya tokare mishi makokoro sannan ya samu bakin magana.

"M.....meyaaa.. faru...? Yace yana hada kalmomin da kyar.

"Ni tsoro nake ji ina ta jin motsi a dakin nan kuma na san fatawa ne irin na film din da muka kalla dazu ne ta biyo ni" nace cike da kuruciya.

Wani irin dad'i ne ya lullube Zafar yaji kama ya daka tsalle dan yaga zallan kuruciya a magana ta kuma ya samu hanyan da zai kara samun kusanci dani.

"Ya Salam baby, kin san all these ghost stories are real? Shiyasa ban so mu kalla ba but saboda naga kina so muka kalla just kiyi addu'a ki kwanta ba abinda zai faru" yace min yana karamto duk addu'a da yazo bakin shi kan ince mu kwana tare ko in bishi dakin shi.

Saurin rike mishi singlet nayi ganin zai zame ya fita ya bar ni " Dan Allah kada ka fita ka bar ni Dan Allah".

Wani munafikin murmushi ya saki ya sake dawowa baya yana kara kire ni da kyau yana godewa Allah da yasa muka kalli horror films d'in nan. " Shhhh it's okay gani nan babu inda zan je, muje ki kwanta I'm with you".

Sake shi nayi na juya a hankali na fara tafiya zuwa bakin gado shi kuwa yabi kafafuna da suke waje da kallo yana had'iyen yawu, zama yayi gefen gadon yana kare min kallo dan duka rabin kirjina a waje yake.yana ganin zan bud'e ido ya dauke kan shi da wuri Yana " toh kina nufin Ni kwanan zaune zanyi kenan?" With much hope din nace ya hau gado ya kwanta.

"Akwai bargo a cikin wardrobe ka dauka sai ka shimfida ka kwanta a nan" nace mishi ina nuna mishi kasa gaban gadon.

"Kuut" yace da karfi harda zaro ido kaman wanda yaga abin tsoro " Amma wannan yarinya kin raina min wayo ki saka ni gadin ki sannan kice Wai in kwanta a kasa ke kuma akan gado? U re not serious" yace yana mikewa a fusace kaman gaske.

Cikin sauri na rike hannun shi idona na cikowa da hawaye nace " kayi hakuri pls kada ka tafi zo ka kwanta toh " wani murmushin gefen.baki ya saki ganin hakar sa na neman cika da ruwa.

"No ba matsala ki kwanta abin ki let me go to my room dan ban fiye son sharing room da mutum ba" yace yana kara tsuke fuska.

Matsawa baya na fara yi da sauri nace "zo ka kwanta pls kada kayi fushi kaji?" Bai ce min kala ba sai dai ya juyo a yangan ce yadawo da baya ya zauna tare da ayyana abubuwa dayawa a ran shi.
[2/23, 8:12 AM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*.

*62&63*

Jan bargon nayi na rufe har kaina ina jin sanyi a raina tunda ina jin motsin mutum kusa dani, shi kuwa a É—osane ya kwanta irin shi a dole alfarma yake min alhalin a zuciyar shi kuwa ji yake kaman ya taka rawa.

Kamshin sa duk ya hana ni sukuni ya cika min hanci sai wani natsuwa yake sauko min na musamman,shima ta b'angaren shi hakan yake kamshin turaruka da nayi amfani dasu masu sanyin duk sun dagula mishi lissafi ji yake kaman ya matso jikina ya rungume ni yayi maganin abinda ke damun sa,wani ɓangaren na zuciyar tayi saurin kwabar sa kan ya bi komai a sannu.

Muna nan kwance shiru kusan awa 1 amma babu wanda yayi bacci a cikin mu kuma babu wanda ya motsa,wata dabara ce ta fad'o mishi a rai nan da nan ya fara sake numfashi da d'an karfi alaman yayi bacci kenan.juyowa nayi a hankali na fuskance shi da yake ya juya min baya bana ganin fuskar shi sai yalwataccen gashin sa baki sidik da yake kwance na zubawa ido ina jin kaman in kai hannu na in shafa.

Dakin nabi da ido ganin ya kashe wuta mai hsken dim light kawai ya bari sai naji duk tsoro ya fara rufe ni, matsowa nayi kusa dashi ina "Zafar! Zafar!! "Cikin murya kasa-kasa ya basar dani yayi kaman da gaske baccin yake harda hadawa da minsharin karya wanda ya kara tsorata ni.

Kusa dashi na matsa sosai kaman zan shige jikin shi har yana jin d'umin numfashi na na sauka a wuyan shi,nan da nan kuwa yaji ya kara rasa natsuwan shi har ya kasa daurewa ya juyo idon shi a rufe amma ya daura min hannun sa na dama a konkoso na ya kara manne ni da jikinsa duk wai a cikin yana bacci yake.

Banyi gigin raba jikina da nashi ba saima kara gyara kwanciya ta da nayi saboda sai yanzu na samu natsuwan yin bacci, aiko ban kai minti goma ba bacci mai dad'in gaske yayi gaba dani na bar Zafar mai baccin karya yana karewa fuskana kallo kaman yau ya fara kallo na.

Tun daga kan giran idona ya fara kallo zuwa hancina haka yayi ta yawo da idn shi akan fuskata mai neman wani abu, da kyar yayi nasaran tsaida idanun nashi kan d'an mitsitsin baki na da yake dauke mishi hankali kullum, fuskar shi ya kawo dab da nawa ya hade goshin mu wuri daya yana goga min hancin sa akan hancina, da sauri ya dauke fuskar shi yayi baya kadan tare da rufe ido ganin nayi motsi ya zata farkawa zanyi.

Murmushi ya sake yana dawo da fuska shi wajan shi na da ganin na cigaba da bacci na cikin kwanciyar hankali, brushing lips d'in shi yayi akan nawa tare da lumshe ido jin taushin labban nawa har kwanyan shi.

Wani irin farinciki ya tsinci kanshi a ciki yana jim inama mu dauwama a haka, kasa hakura yayi saida ya kama lip dina na kasa ya dan tsostsa with his eyes closed.gyara min kwanciya yayi a jikinsa yasa hannayen shi duka 2 ya rungume ni tsam a jikinsa ya lumshe ido with the hope ko bacci zai iya daukan shi saboda yanda yake jin d'umin jikina da Kuma yanda yake jin kirjina ya hadu da nashi duk sai yaji ya shiga da nasani.

Haka yayi ta fama da kyar ya samu bacci ya dauke shi wuraren asuba. da washe gari a makare muka tashi ni dad'in bacci ya hana ni farkawa da wuri yayin da shi kuma rashin baccin da wuri yasa ya makara. 6:20am shi ya fara farkawa cike da farincikin we slept together,ya tsaya kallon innocent face dina da nake bacci na peacefully sai yaga kaman nafi kyau a haka.

Light kiss ya manna min a goshi yana murmushi sannan ya had'a fuska ya fara magana kaman gaske" ke Zareefa!! Ya haka? Daga taimako ga yanda kika wani kanainaye ni kika haye min jiki, amma da nine nayi miki haka sai kice da wata manufa nayi miki ko?"

Shiru nayi naki in motsa balle in bashi amsa duk kunya ya lullube ni dan gaba daya a jikin sa nake kwance, dariya kawai yayi ya cire ni a jikinsa yayi hanyan fita yana " in kin gama likimon sai ki tashi kiyi sallah, kin sa mun makara har na rasa sallah jam'i " ina jin shi amma ban tanka ba har sai da na tabbatar da ya fita sannan na mike na shiga bathroom domin yin alwala.

************************

Gidan mu yanzu ya zama kaman bashi ba ko ina shiru hatta da yaran gida sun canza kasancewar canjin da baba yazo dashi gidan, kullum da safe ya kan tara su Inna a parlour shi ya nemi gafaran su akan yanda suka zauna ada na yanda bai damu da sauke nauyin da Allah ya daura mishi ba sannan ya kanyi alkawarin canji a zamanta kewar su Kuma yana bukatan hadin kan su domin babu abinda zai tafi daidai sai sun bashi hadin kai .

Inna ta da Inna Assbe su kanyi mishi alkawarin bashi dukkan hadin kai da yake bukata yayin da ita kuma Gwaggo Aisha takan tabe baki ta dauke kai saboda ita wannan tsarin kwata kwata bai mata ba, tafi jin dad'in rayuwar gidan mu na da yanda kowa yake kara zube kayi duk abinda kake so babu mai hana ka musamman ita da take taka duk wanda take son takawa a gidan ta kwana lafiya.

Kananan yaran gida duk yasa an saka su a islamiya da boko cikin ikon Allah sun natsu tare da maida hankalin su ga karatu, maganan tallah Kuma babu shi dan ya dade da soke ta wanda hakan sam Bai yiwa Gwaggo Aisha dad'i ba.

Da farko taso tada masifa a tsakar gida kaman yanda ta saba yi shekara da shekaru, sai dai nan da nan Baba ya taka mata biriki ta hanyan da bata tab'a tsammani ba.

Kiran su yayi parlour shi ya zaunar dasu sannan ya fara magana;

"Ina son ku bani hankalin ku gaba dayan ku kuma ku fahimce ni Dan daga rana irin ta yau bana son inga kun daurawa ko wani yaro tallah a gidan nan,ina son ku bani hadin kai su samu tarbiya da karatu da suka rasa a baya.a kullum sai naji kaman in zubda hawaye in na tuna yanda gidan yake a baya sannan bana gajiya da naiman yafiya ku akan...."

"A'a dakata mallam akan me zaka ce ba zamu daurawa yara abin sana'a ba sai dai mu zauna kara zube babu sana'a, kana wai su je boko da isamiya ko menene?" Gwaggo Aisha ta katse shi a hasale tana kumbure kumbure cikin fushi shi kuwa ido ya zuba mata ganin hakan kuwa yasa ta cigaba da masifarta.

"Ni dama na rasa gane kan ka tunda ka dawo daga barikin sojojin nan duk ka canza ka zama sabon mutum, da farko ina tantaman abinda zuciyata take raya min game da hakan amma yanzu na gaskata tabbas Mallam wajan dukan nan da sukayi maka sun daki kan ka har ya jawo maka tabin hankali. Toh wallahi ni dai ba zan dauka ba tun wuri ka canza shawaran na fad'a maka ehe" ta karasa cikin fushi.

Baba kuwa murmushi kawai yayi ya a kada kai ya tabbata da ace a can baya ne ta fad'a mishi wannan kalmar ta tabin hankali, da ya nuna mata haukan amma a yanzu kam yafi karfin wannan.

Cikin natsuwa da ta fara zama jikin shi yace" ba shawara nake baku ba Aisha wannan umarni ne a matsayina na uban yaran kuma miji a gare ku".

"Hmmmm su miji manya ni dai na gaya maka wannan umarnin naka ka bawa saunayen matan naka amma banda ni domin babu abinda zai hana ni yin sana'a" Gwaggo Aisha ta mayar mishi da martani cikin gadara.

Zaiyi magana Inna tayi saurin cewa" toh Masha Allah Mallam munji dad'in wannan hukuncin naka insha Allah zaka same mu masu cika umarnin kane a kowani lokaci, su kuma yaran Allah yayi musu jagora ya basu ilimi mai amfani".

"Ameeen " ya amsa can kasan makoshi lumshe ido yayi cikin jin dad'in kalaman nata tare da jin takaicin kan shi ta yanda ya wulkanta mace mai daraja haka a baya.

"Insha Allahu kuwa Mallam ba zamuyi wasa da wannan daman da muka dade muna nema ba, zamu tsaya tsayin daka har sai sun samu ilimi mai inganci" cewar Inna Asabe domin ita har ga Allah taji dadi sosai saboda ta dade tana sha'awan taga yaran ta suna karatu kaman kowa sai dai rashin wadata da kuma rashin samun kula daga wajan mahaifin su yasa ta hakura.

"Kaji munafuka mara zuciya, ke dama tun ba yau na lura baki san ina yake miki ciwo ba.in banda shashanci harda wani cewa wai irin daman kin dade kina jira, toh kin samu amma ni kam babu uban da ya isa ya hana daurawa yayana abin sana'a".cewar Gwaggo Aisha tana watsawa Inna Asabe mugun kallo.

"Babu uban da ya isa kika ce ko? Toh tsaya kiji yara dai nawa ne Kuma daga yau ba zasu kara yin wani abu mai kama da tallah ba sannan duk wacce ta daurawa d'ana tallah a bakin aurenta. Zaku iya tafiya" Baba ya karasa a d'an hasale tare da kwaciya abin shi ya juya musu baya.

Inna ta da Inna Asabe godiya suka mishi suka fito suka bar Gwaggo Aisha da shock ya daskarar da ita saboda ta kasa yarda wannan kalmar daga bakin Baba ya fito, da kyar ta samu ta mike zuciyar ta cike da kudirin sai ta nemi bokan da zaiyi mata maganin su duka.

Wannan kalman da Baba ya furta shi ya kawo mana zaman lafiya a gidan mu saboda sosai take kaunar Baban.mu gashi bata son rabuwa da yyaran ta, dama Inna Asabe da Inna ta basu da matsala.

******************

Kasa fitowa nayi da washe gari bayan nayi sallah da azkar kara kwanciya ta nayi saboda gaba daya wani irin kunyan shi naji nake ji in na tuna yanda muka kwana,shi kuwa Zafar a bangaren shi cikin zallan farinciki da nishad'i yayi wanka sannan yayi alwala yayi sallah yana ganin yanzu nesa tazo kusa tunda har Allah yayi muka kwana daki daya kan gado daya Kuma manne da juna.

Kasa komawa gado yayi ya fito bayan ya shirya kanshi cikin wani red sports wear ya shiga kitchen yana son yayi wani abinda da zai birge ni sai dai kash babu wani abin kirki da ya iya daya wuce dafa ruwan zafi.

Wani tunani daya fad'o mishi yasa ya koma dakin shi cikin sauri ya dauko wayan shi tare da shiga Google yayi searching yanda ake soya chips nd fried egg, nan da nan suka turo mishi da recipe su step by step.

Cikin natsuwa kuwa ya fara bi duk yanda sukayi da yake ma video ne, common chips and fried egg sai da ya kwashe good 1 hr sannan ya kammala ya dafa ruwan tea a gefe ya shirya komai kan dinning sannan ya koma bedroom din shi tare da sake wanka but this time yaci gayu sosai cikin riga longs sleeves fari kal da wandon jeans baki,kan nan nashi yasha gyara sai sheki yake sun kwanta lub gwanin sha'awa ya kara da wanka da turarukan shi masu d'an karan kamshi sannan ya fito parlour ya tsaya yana mamakin meya hana ni fitowa har yanzu da a baya ne war haka na fito har na gama aiki na.

Tunanin ya shiga yaga lafiya ya fara amma wani sashi na zuciyar shi tana ya kara jira kadan ko zan fito, dakin nawa ya nufo kai tsaye dan yafi yarda daya shigo ya ganni domin tabbarwa.

Ni kuwa a lokacin da na kwanta bacci mai nauyin gaske ne yayi awon gaba dani ba tare dana shirya mishi ba,sai bayan karfe takwas na safe tukun na farka.cikin mamakin irin nauyin baccin nawa na diro daga kan gadon na fad'a bathroom dan yin wanka.

A gurguce nayi wankan ina tunanin me zan girka mana mai sauki saboda naga lokaci ya tafi maybe zai fita da wuri, ina fitowa daga wankan mai kawai na shafa a lallausan fata na sannan na saka wani straight gown red colour bai wani kama min jiki ba amma ya zauna min cib gwanin sha'awa.gashina Kuma cikin hula shima red mai adon stones na saka tare da shafa humra masu kamshi na nufi hanyan fita cikin sauri dan shirin nawa duk a gaggauce nayi su.

A daidai wannan lokaci shima Zafar ya shigo parlor na ganin babu motsina anan yasa ya nufi bedroom din na Kai tsaye, ya mika hannu da niyyan budewa na bud'e yaga na bud'e saura kiris muyi gware nayi baya da sauri cikin jin nauyi na gaishe shi ba tare da na yarda mun had'a ido da shi ba duk da yanda idanuwa na suka kwadaitu da ganin nashi.

"Morning princess da fatan kin tashi lafiya" ya amsa min yana neman ya saka kwayan idon shi cikin nawa amma Bai samu daman hakan ba.

"Wow u look beautiful as always" yace tare da rike min hannu ya cigaba " come let's go nd see what I got for you" yace ya fara jana muka fito bai tsaya a ko ina ba sai dinning room, shi ya ja min kujera na zauna sannan shima yaja na kusa dani ya zauna.

"Yau nayi mana girki saboda naga kina bacci shiyasa ban tashe ki, hope you will like it" ya karasa yana kashe ni da killer smile dayasa nayi saurin sadda kai na kasa.

Bud'e warmer mai dauke da soyayyen chips yayi ya fara serving din mu a plate daya, duk sai danne dariyar da take cikina nake kada ya fito fili ganin yanda ya dage Yana zuba mana abinci alhalin na san babu abinda ya iya, a cikin zuciya ta kuwa cewa nake yau zanci jagwalgwalo kenan.

Duk da sai da yayi testing ya tabbatar babu miskila kamin ya kawo ni amma cikin fargaba ya saka fork ya debo abincin ya kawo bakina, banyi musu ba na bud'e baki na ya juye min ga mamakina sai naji normal sai dai kwan ne mai yaso ya danyi yawa amma shima babu laifi yayi.

Taunawa nake a hankali shi Kuma kurawa dan karamin bakin nawa ido yayi har ya tafi wani duniyan sai magana ta ne ya dawo dashi " woww ❤️ yaushe ka iya girki haka" nace mishi fuskata cike da fara'a.

"A wajan ki na iya, Nima sai na koyi yin girki irin na Innan mu" ya bani amsa.

Murmushi mai kama da dariya ne ya kwace min zuciyata na jin dad'in yanda yake yaba min Inna ta, sosai muka ci abincin yana ta jana da hira har ban san lokacin da na sake ba.

Bayan mun gama breakfast ne Kuma ya mike kaman yanda ya saba duk safiya ya tafi gaida iyayen shi ni Kuma na gyara dinning table din na kwashe kayan da muka bata na kai kitchen da niyan wanke su, abinda na gani a kitchen d'in yasa saura kiris in zubar da kayan hannu na.
[2/23, 8:12 AM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*.

*64&65*

Innalillahi kawai nake maimatawa a zuciyata ganin yanda ya mayar min da kitchen up side down, saboda soya dankali da kwai gaba daya ya hargisa kitchen d'in ko ina kaya ne a warwatse ga b'awon dankalin da ya b'are suma zube a k'asa.

Karasa shiga kitchen d'in nayi na ajiye kayan hannu na sannan na fara gyarawa ina yi ina maganan zuci" ina ma ace kulawar da yake bani da kuma soyayya da yake nuna min da gaske ne, dan ni kam kullum soyayyar shi ƙaruwa take a zuciyata sai dai nasan abin da yasa yake wannan draman dan ya samu jiki na ne, kuma na san yana samu ni kuma na gama yawo domin lokacin da ya d'ibawa auren mu ya kusa cika".

Ras-ras naji zuciyata tana bugawa, fargaban rabuwa da shi ce cike da zuciyar, ina ma zamu kasance ne har abada, domin a yanzu bani da burin daya wuce in ganmu tare ya kasance muna tare na har abada, bani da burin daya wuce in jini a jikin sa. A kullum shauƙin son kasancewa dashi ninkuwa yake a zuciyata da gangan jikina sosai nake kai zuciyata nesa wajan ganin banyi wani abin a gaban shi ba, dan in yana wani abin ji nake kaman in had'iye shi in huta.

maganan zuci da nake yasa ban san lokaci ya d'an tafi ba, ganin sha biyu ya d'an gota yasa na daura mana abincin rana, abu mara nauyi na girka mana sannan na fito na kimtsa parlor duk da ba wani datti yayi ba na share nayi mopping sannan na kunna coal na zuba turaren wuta na zallan itacen sandal.

Nan da nan ko gidan ya d'auki kamshi mai sanyaya zuciya, abincin da na gama kwashe mana cikin warmers na jera mana su kan dinning sannan na shiga wanka ganin ko ina yayi kal dashi, saida na kusan minti talatin ina wankan sannan na fito.

Zama nayi agan mirror nabi jikina da lotions masu kyau da kamshi, light make up nayiwa fuskata domin ni ba ma'abociyar son kwalliya dayawa bane.lungu da tsako na jikina nabi da body spray masu sanyin kamshi da sanyaya zuciya.

A gaban sip d'ina na tsaya ina karewa kayayyakina da suke a jere kallo ina tunanin wani kaya zan saka, cikin dube duben da nake ido na ya sauka kan wani english gown black color tsayin shi da kadan ya wuce guiwa ta sai adon stones da red flowers da akayiwa gaban rigan daya kara mishi kyau.duk da ban taba saka irin kayan tunda nazo gidan ba amma haka nan zuciya ta ta kwadaitu da saka kayan.

Ina sakawa kuwa yayi min cip na cika kayan ya lafe a jikina ya fito mun da shape d'ina sosai kayan ya min wani irin kyau nida kaina na san na canza,tsayawa nayi ina karewa kaina kallo sai naji sha'awan shafa lipstick a labba na

Red lipstick na shafa a labban nawa nan da nan ko ya kara haskani ko dan ni ba ma'abociyar lipstick bace oho.

Hijabi na zura na kabbara sallahn azahar jin har an fara sallah a wasu masallatan anguuwan.

Shi kuwa Zafar yana fita gidan su ya wuce kai tsaye ba tare da ya biya wani wajan ba,yana fitowa a motan shi bayan ya daidaita parking d'in shi ya hango Abba na saukowa daga steps d'in fitowa a parlour su cikin haraman fita hannun shi rike da 'yar brief case.

Da sauri Zafar ya karasa gare shi cikin natsuwa da ta fara zame mishi jiki ya rusuna ya gaida Abban shi, shima cikin jin dad'in canjin tilon d'an nashi ya amsa yana tambayan shi lafiya ta.

Cikin dan jin kunya ya amsa da " tana nan lafiya lau tana gaishe ku".

"Muna amsawa, daga gida kake ko"?
"Eh Abba naga kaman fita zakayi?"ya tambayi Abban yana kallon jakan hannun shi.

"Tafiyar gaggawa ce ta same ni zuwa kasar Germany, munyi order wasu kaya aka samu akasin da dole sai naje da kaina. Wayanan nan abubuwan kai ya kamata kayi su ko Kuma ka fara taya ni da wasu harkokin ne amma ban san meyasa baka son aiki ba sai zaman banza" Abba ya bashi amsa a d'an kausashe.

Murmushi yayi Yana sosa keya tare da fara in ina " ammm ummm Abba na kusa karban business din ka dawo gida ka huta da sweetie ka " duka Abba ya kaiwa keyar shi yana dariya tare da cewa " ja'irin yaro kana son maida ni kakan ka ko ganin babu su kusa da kai ko?"

Shima dariyan yayi ya nufi cikin parlour da gudu cikin nishad'i yace "safe trip Abba". Driver da tundazu yake jiran su gama tattauna tsakanin uba da d'an sa ya nufo Abban da saurin shi ya karbi jakan hannun Abban ya wuce gaba Abba na bin shi a baya har zuwa inda ya fito da motan da zai kai shi airport dashi,bayan motan ya bud'e mishi ya shiga ya zauna sannan ya ajiye jakan a gefen Abban sannan ya rufe murfin motan sannan shima cikin sauri ya zagaya ya bud'e mazaunin driver ya tada motan tare da nufo gate da mai gadi ya dade da wangale musu gate suna fita ya kama hanyan airport.

Shi kuwa Zafar da sallama a bakin shi ya shiga parlour amma bai samu Mom a nan ba sai masu aiki, direct sama ya hau zuwa dakin ta yayi sallama ya tura kofan ya shiga.

Amsawa Mom tayi tare da juyowa daga gyara gaban dressing mirror ta da take yi tana mishi sannu da zuwa.

Karasa shigowa yayi ya zauna kusa da kafar ta ya fara zuba mata shawgwab'a kaman yanda ya saba itama tana biye shi, " ga breakfast a dinning room if u re hungry" tace mishi tana shafa mishi gashin kan sa.

"Haba Mom I'm a married man fa now how comes ba zanyi breakfast ba har zuwa wannan lokacin" ya bata amsa cikin turo baki kaman karamin yaro, kamin tabashi amsa cikin sauri ya daura hannayen shi duka 2 kan guiwa ta yace" Momy guess What"?

Dan dariya tayi tana " just tell me what is going on kaima ka san I'm not good at guessing" shima dariyan yayi yace " yau ni na girka mana breakfast a gida".

Cikin mamaki Momy tace " bangane kai ka girka breakfast ba".

Gyara zaman shi yayi ya fara cewa "yes Mom yau ni na shiga kitchen tana ma bacci na girka mana breakfast chips nd fried eggs nd tea" ya karasa so excited.

Zuciyar Momy na bugawa ta kara tambayan shi" kai da ko ruwan zafi baka iya tafasawa ba ya akayi har ka soya dankali da kwai?"

"Google " ya bata amsa kai tsaye kuma cikin kwarin guiwa.

Kai ta jinjina ta tafi duniyan tunani dole nema ta tashi tsaye kamin komai ya ida juye mata, ita fa shiyasa tun farko bata maraba da wannan auren domin talaka in Bai iya samun wuri ba balle Kuma ni yar malamai.shikenan iyaye na sun asirce mata yaro da mijinta ma baki daya duka-duka yaushe akayi auren amma gashi duk mun saye zuciyar su,l Abba yayi min kyauntan company nd yanzu Kuma tilon d'an nata yazo yana fad'a mata Wai ya girkawa yar yarinya karama abinci abinda duk tsawon shekaru da sukayi tare ko sha'awan shiga kitchen d'in bai tab'a nuna mata ba?.

Tayi nisa da bata jin yanda Zafar ya dage yana mata bayani dalla-dalla ta yanda yabi yayi girkin shi cikin sauki, tab'a ta da yayi ne ya dawo da ita hayyacin ta.

"Na'am me kace boy?"

"Let me sleep kadan " yace yana hamma ya hau gadon ta ya kwanta, da ido kawai tabi shi tana tunanin abin yi

Sai kusan karfe daya ya tashi daga baccin bai tsaya bata lokaci ba ya shiga bathroom yayi alwalan azahar ya fito yayi mata sallama zai wuce gida daga masallaci, tana ce mishi ya tsaya yayi lunch before ya wuce shi kuma yace mata " no zanje gida in ci na san by now ta gama mana delicious tana jirana".ya fita abin shi

Ajiye serving spoon dake hannun ta tare da rafka tagumi da hannu 2 zuciya na kuna.

Ina idar da sallah na fito main parlour shima a lokacin yayi sallama ya shigo muna had'a ido ledan daya sayo mana fruits ya tsubuce a hannun shi suka zube a kasa, ido ya zuba min kaman ya cinye ni domin tunda muke bai tab'a gani na cikin irin wannan shigan ba ga hot red lipstick dana shafa ya bala'in tsotse mishi ruwan kai.

Hannu ya ware min alamun he needs a hug, cikin wani irin taku da ban san na iya shi ba na nufo shi.gyara tsayuwan shi yayi yana jiran in karaso, ina zuwa dab da shi har kamashin turaruka na sun fara ruda shi maimakon in fad'a jikin shi yanda yake tsamani sai gani yayi na durkusa na fara rattare fruits da ya zubar ina maida su cikin ledar.

Pls kuyi hkr kuyi manage da wannan.
[2/23, 8:16 AM] Ummee Yusuf: 🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*.

*64&65*

Innalillahi kawai nake maimatawa a zuciyata ganin yanda ya mayar min da kitchen up side down, saboda soya dankali da kwai gaba daya ya hargisa kitchen d'in ko ina kaya ne a warwatse ga b'awon dankalin da ya b'are suma zube a k'asa.

Karasa shiga kitchen d'in nayi na ajiye kayan hannu na sannan na fara gyarawa ina yi ina maganan zuci" ina ma ace kulawar da yake bani da kuma soyayya da yake nuna min da gaske ne, dan ni kam kullum soyayyar shi ƙaruwa take a zuciyata sai dai nasan abin da yasa yake wannan draman dan ya samu jiki na ne, kuma na san yana samu ni kuma na gama yawo domin lokacin da ya d'ibawa auren mu ya kusa cika".

Ras-ras naji zuciyata tana bugawa, fargaban rabuwa da shi ce cike da zuciyar, ina ma zamu kasance ne har abada, domin a yanzu bani da burin daya wuce in ganmu tare ya kasance muna tare na har abada, bani da burin daya wuce in jini a jikin sa. A kullum shauƙin son kasancewa dashi ninkuwa yake a zuciyata da gangan jikina sosai nake kai zuciyata nesa wajan ganin banyi wani abin a gaban shi ba, dan in yana wani abin ji nake kaman in had'iye shi in huta.

maganan zuci da nake yasa ban san lokaci ya d'an tafi ba, ganin sha biyu ya d'an gota yasa na daura mana abincin rana, abu mara nauyi na girka mana sannan na fito na kimtsa parlor duk da ba wani datti yayi ba na share nayi mopping sannan na kunna coal na zuba turaren wuta na zallan itacen sandal.

Nan da nan ko gidan ya d'auki kamshi mai sanyaya zuciya, abincin da na gama kwashe mana cikin warmers na jera mana su kan dinning sannan na shiga wanka ganin ko ina yayi kal dashi, saida na kusan minti talatin ina wankan sannan na fito.

Zama nayi agan mirror nabi jikina da lotions masu kyau da kamshi, light make up nayiwa fuskata domin ni ba ma'abociyar son kwalliya dayawa bane.lungu da tsako na jikina nabi da body spray masu sanyin kamshi da sanyaya zuciya.

A gaban sip d'ina na tsaya ina karewa kayayyakina da suke a jere kallo ina tunanin wani kaya zan saka, cikin dube duben da nake ido na ya sauka kan wani english gown black color tsayin shi da kadan ya wuce guiwa ta sai adon stones da red flowers da akayiwa gaban rigan daya kara mishi kyau.duk da ban taba saka irin kayan tunda nazo gidan ba amma haka nan zuciya ta ta kwadaitu da saka kayan.

Ina sakawa kuwa yayi min cip na cika kayan ya lafe a jikina ya fito mun da shape d'ina sosai kayan ya min wani irin kyau nida kaina na san na canza,tsayawa nayi ina karewa kaina kallo sai naji sha'awan shafa lipstick a labba na

Red lipstick na shafa a labban nawa nan da nan ko ya kara haskani ko dan ni ba ma'abociyar lipstick bace oho.

Hijabi na zura na kabbara sallahn azahar jin har an fara sallah a wasu masallatan anguuwan.

Shi kuwa Zafar yana fita gidan su ya wuce kai tsaye ba tare da ya biya wani wajan ba,yana fitowa a motan shi bayan ya daidaita parking d'in shi ya hango Abba na saukowa daga steps d'in fitowa a parlour su cikin haraman fita hannun shi rike da 'yar brief case.

Da sauri Zafar ya karasa gare shi cikin natsuwa da ta fara zame mishi jiki ya rusuna ya gaida Abban shi, shima cikin jin dad'in canjin tilon d'an nashi ya amsa yana tambayan shi lafiya ta.

Cikin dan jin kunya ya amsa da " tana nan lafiya lau tana gaishe ku".

"Muna amsawa, daga gida kake ko"?
"Eh Abba naga kaman fita zakayi?"ya tambayi Abban yana kallon jakan hannun shi.

"Tafiyar gaggawa ce ta same ni zuwa kasar Germany, munyi order wasu kaya aka samu akasin da dole sai naje da kaina. Wayanan nan abubuwan kai ya kamata kayi su ko Kuma ka fara taya ni da wasu harkokin ne amma ban san meyasa baka son aiki ba sai zaman banza" Abba ya bashi amsa a d'an kausashe.

Murmushi yayi Yana sosa keya tare da fara in ina " ammm ummm Abba na kusa karban business din ka dawo gida ka huta da sweetie ka " duka Abba ya kaiwa keyar shi yana dariya tare da cewa " ja'irin yaro kana son maida ni kakan ka ko ganin babu su kusa da kai ko?"

Shima dariyan yayi ya nufi cikin parlour da gudu cikin nishad'i yace "safe trip Abba". Driver da tundazu yake jiran su gama tattauna tsakanin uba da d'an sa ya nufo Abban da saurin shi ya karbi jakan hannun Abban ya wuce gaba Abba na bin shi a baya har zuwa inda ya fito da motan da zai kai shi airport dashi,bayan motan ya bud'e mishi ya shiga ya zauna sannan ya ajiye jakan a gefen Abban sannan ya rufe murfin motan sannan shima cikin sauri ya zagaya ya bud'e mazaunin driver ya tada motan tare da nufo gate da mai gadi ya dade da wangale musu gate suna fita ya kama hanyan airport.

Shi kuwa Zafar da sallama a bakin shi ya shiga parlour amma bai samu Mom a nan ba sai masu aiki, direct sama ya hau zuwa dakin ta yayi sallama ya tura kofan ya shiga.

Amsawa Mom tayi tare da juyowa daga gyara gaban dressing mirror ta da take yi tana mishi sannu da zuwa.

Karasa shigowa yayi ya zauna kusa da kafar ta ya fara zuba mata shawgwab'a kaman yanda ya saba itama tana biye shi, " ga breakfast a dinning room if u re hungry" tace mishi tana shafa mishi gashin kan sa.

"Haba Mom I'm a married man fa now how comes ba zanyi breakfast ba har zuwa wannan lokacin" ya bata amsa cikin turo baki kaman karamin yaro, kamin tabashi amsa cikin sauri ya daura hannayen shi duka 2 kan guiwa ta yace" Momy guess What"?

Dan dariya tayi tana " just tell me what is going on kaima ka san I'm not good at guessing" shima dariyan yayi yace " yau ni na girka mana breakfast a gida".

Cikin mamaki Momy tace " bangane kai ka girka breakfast ba".

Gyara zaman shi yayi ya fara cewa "yes Mom yau ni na shiga kitchen tana ma bacci na girka mana breakfast chips nd fried eggs nd tea" ya karasa so excited.

Zuciyar Momy na bugawa ta kara tambayan shi" kai da ko ruwan zafi baka iya tafasawa ba ya akayi har ka soya dankali da kwai?"

"Google " ya bata amsa kai tsaye kuma cikin kwarin guiwa.

Kai ta jinjina ta tafi duniyan tunani dole nema ta tashi tsaye kamin komai ya ida juye mata, ita fa shiyasa tun farko bata maraba da wannan auren domin talaka in Bai iya samun wuri ba balle Kuma ni yar malamai.shikenan iyaye na sun asirce mata yaro da mijinta ma baki daya duka-duka yaushe akayi auren amma gashi duk mun saye zuciyar su,l Abba yayi min kyauntan company nd yanzu Kuma tilon d'an nata yazo yana fad'a mata Wai ya girkawa yar yarinya karama abinci abinda duk tsawon shekaru da sukayi tare ko sha'awan shiga kitchen d'in bai tab'a nuna mata ba?.

Tayi nisa da bata jin yanda Zafar ya dage yana mata bayani dalla-dalla ta yanda yabi yayi girkin shi cikin sauki, tab'a ta da yayi ne ya dawo da ita hayyacin ta.

"Na'am me kace boy?"

"Let me sleep kadan " yace yana hamma ya hau gadon ta ya kwanta, da ido kawai tabi shi tana tunanin abin yi

Sai kusan karfe daya ya tashi daga baccin bai tsaya bata lokaci ba ya shiga bathroom yayi alwalan azahar ya fito yayi mata sallama zai wuce gida daga masallaci, tana ce mishi ya tsaya yayi lunch before ya wuce shi kuma yace mata " no zanje gida in ci na san by now ta gama mana delicious tana jirana".ya fita abin shi

Ajiye serving spoon dake hannun ta tare da rafka tagumi da hannu 2 zuciya na kuna.

Ina idar da sallah na fito main parlour shima a lokacin yayi sallama ya shigo muna had'a ido ledan daya sayo mana fruits ya tsubuce a hannun shi suka zube a kasa, ido ya zuba min kaman ya cinye ni domin tunda muke bai tab'a gani na cikin irin wannan shigan ba ga hot red lipstick dana shafa ya bala'in tsotse mishi ruwan kai.

Hannu ya ware min alamun he needs a hug, cikin wani irin taku da ban san na iya shi ba na nufo shi.gyara tsayuwan shi yayi yana jiran in karaso, ina zuwa dab da shi har kamashin turaruka na sun fara ruda shi maimakon in fad'a jikin shi yanda yake tsamani sai gani yayi na durkusa na fara rattare fruits da ya zubar ina maida su cikin ledar.

Pls kuyi hkr kuyi manage da wannan.
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹
🦚
*BA SONTA NAkE BA*
🦚
🦚🌹
🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹
🦚🌹🦚🌹🦚🌹🦚🌹

_A story about love and sacrifice._

_Written by_ *UMMEE YUSUF*
_(Maman Yusuf)_

_*From The Fantastic Writer of*_

```FARHAT```
```KAMACE```
```UKUBAR KISHIYATA```
```UMMU~SALMA```
```UWANI```

*_And now_*

*_BA SONTA NAKE BA_*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*.

*66&67*

Kallon santala-santalan kafafuna yake tare da ayyana abubuwa da yawa a ran shi, har na gama kwashe kayan marmarin da ya zubar bai sani ba saboda yayi nisa a tunani. Hannun shi da na riƙe shiya dawo da shi hayyacin sa ba tare da musu ko gardama ba ya fara bina da zuwa cikin parlourn kaman yanda na buƙata, ban tsaya a cikin parlourn ba sai a dinning area.

Kujera na ja mishi dan ya zauna kaman yanda yake min, maimakon ya zauna sai ido ya zuba min yana ta zuba wannan tsadadden murmushin shi mai tsayawa a rai.

Kawar da fuskata gefe nayi nima ina wani boyayyen murmushi sannan na dawo da duba na gare shi,da ido nayi mishi alaman daya zauna mana sai a lokacin ya lura da inda muke.nan ma bai musa ba ya zauna ni Kuma kayan daya sayo na wuce kitchen dasu na wanke na yanka mana a plate sauran Kuma na saka su a fridge,na dauki wanda na yanka mana na fito.

Ina fitowa muka had'a ido da alamu tunda na shiga idon shi anan yake har na fito, ajiye plate din nayi akan table sannan naja kujeran kusa da shi na zauna tare da fara zuba mana abincin a plate daya kaman yanda naga yake yi.

"Ina su Abba da Mom?" Na tambaya ina cigaba da aikin da nake, sai a nan ya samu bakin magana cikin washe hakora ya bani amsa" suna nan lafiya amma Abba yayi tafiya yau sai Mom ce kad'ai muka sha hira da ita har nake bata labarin yau da safe ni nayi mana breakfast bata yarda ba kasanewar tun taso wata ta san babu abinda na tsana kaman shiga kitchen".

Ajiye spoon din dake hannu na nayi ina jin babu dad'i a raina how could he tell her such things,na san iyayen mu na yanzu ba mamaki ta fara nagetive thinking balle ma Momy da nake ganin tsana ta a cikin idon ta.

"I think daga yau Zaki fara koya min wannan delicious da Innar mu ta koya miki" naji muryan shi ya katse min tunanin da nake, murmushi yake nayi ina " kada ka damu da koyan girki bayan kana namiji, girki ai aikin mata ne".

Dariya ya fara tare da debo abincin ya nufi baki na dashi nima babu musu na bud'e mishi baki ya zuba min na fara taunawa a nitse tare da zuba mishi kyawawan idanuwa na ina jin kaman in rungume shi dan wani matsacin soyayyar shi nake jin na kara ninkuwa a cikin zuciya ta.

Shima dariyan nashi ya tsayar tare da kurawa baki na ido yana kallon yanda nake motsa su a hankali, ji yake kaman ya kamo su yayi ta tsotsa amma babu hali.duk mancewa da cin abincin mukayi kowa ya tafi duniyan tunani wanda har ya abinda yake ran shi ya ingiza shi without any thoughts ya fara motso da fuskar shi zuwa nawa domin cikawa zuciyar shi muradin ta.

D'umin numfashin sa daya sauka akan fuskata shiya dawo da ni hayyacina cikin azama nayi saurin yin baya da tawa fuskar da saura kadan ya hadu da tashi, sai a lokacin ya ankara da abinda yake faruwa.cikin waskewa ya d'an had'a rai yana" ke tsaya abu nagani zan cire miki a saman ido kar ya shiga miki cikin idon" komo da fuskata nayi kaman yanda muke d'azu numfashin shi na cigaba da sauka akan fuskata daya sanya ni tsintan kaina cikin wani yanayi mara misaltuwa daya wajabta min lumshe idanu na hoping for mu tabbata a haka.

Fuskar nawa ya kurawa ido yana jin wani sabon yanayi a tare da shi,how he wish he could suck dis pink lips right now Amma babu halin yi, sai da yayi da gaske sannan ya aro jarumta ya saka hannun shi na dama ya dan goge min saman idon a sunan ya cire min sannan yaja baya nima sai a lokacin na samu daman bud'e ido na.

Haka dai a shirarance muka ci abincin da ko rabi bamu ci ba muka bari anan dining din ya hau bani labarin makarantan su muna ta kwasan dariya kaman ba Zafar din nan mai ji da kan shi ba.bamu tashi a wajan ba sai da aka Kira sallan la'asar,shi ya taimaka min muka kwashe kayan da muka bata zuwa kitchen na tsaya wanke su shi Kuma yayi alwalan ya fita masallaci.nima sai da nagama wanke-wanke na kintsa kitchen d'in sannan na wuce daki nayi alwala nayi sallahn.

Koda na idar kasa tashi a wajan nazauna tunanin rayuwar aure na, ina tuna yanda a sch ake labarin yanda daren farko yake kasancewa da yanda miji yake bawa matar shi kulawa a wannan daren,a lokacin da Yayana kawai nake imagining amma gashi cikin ikon Allah ashe ba shi bane mijina,ashe abinda nake ji akan shi ba so bane shakuwace kawai dan sai yanzu na san asalin menene so.sai dai kash wanda nake son bana gaban shi asalima auren manufa yayi dani.

Shima Zafar ana idar da sallah bai wani jima ba ya dawo gida dan yanzu in ba dole ba baya son abinda zai saka yayi nesa dani,yafi son mu kasance tare a kowani lokaci.sallamar da yayi shiya dawo dani daga duniyan tunani dana lula amsa mishi nayi ina kakalo murmushi don boye yar damuwa dake kan fuskata.

Karasa shigowa dakin yayi yazauna a bakin gado na abinda bai tab'a yi ba kenan dan haka da kallo na bishi zuciya ta na min sanyi duk da na san fake love ne Amma ina matukar jin dadi in yana nuna min kulawa komin kankantarsa.

"Kar dai sai yanzu ki kayi sallah?" Ya tambaya yana kallo yanda nake ninke doguwar hijabi na sallah dana cire,ban bashi amsa ba sai da na ajiye shi a mazaunin shi sannan na juyo na dawo kusa dashi na zauna a gefen shi sannan nace" a'a tundazu na idar ban dai tashi daga wajan da nayi sallah bane...." Kallon da yake bina dashi yasa na hadiye sauran maganan nayi mishi alama da hannu wato "ya dai".

"I'm just thinking ne ko Abba ya isa lafiya gashi bai kirani ba ko za kira shine ban sani ba" ya fadi hakan cikin waskewa,duk da na gane amma nima sai na basar nace" kana da no shi na kasar daya tafi ne?"

"Roaming no shi yake a duk kasar daya tafi,so baya canza sim in yayi tafiya" ya bani amsa yana ciro wayar shi daga aljihun rigan sa ya shiga neman layin Abban cikin sa'a kuwa sai gashi ya shiga ya fara ringing, yana gab da katsewa ya daga cikin murya dake nuna zallar gajiya ya amsa sallaman da yake mishi.

Bayan sun gaisa yayi mishi ya hanya yake tambaya ta ya nake, wayar ya daura min a kunne ba tare daya amsa tambayar ba yana min alama da ido da in mishi magana.sallama nima na mishi ya amsa muka gaisa daga nan ya dauke wayan daga kunne na ya daura a nashi suka cigaba da magana,kokarin mikewa na fara yi ganin hirar tasu ba mai karewa bane amma ya dakatar dani ta hanyan rike min hannu.

Hannuna daya rike na kalla sannan na kalle shi naga shi hankalin shi gaba daya yana kan wayan da suke yi da mahaifin shi,shagala nayi da kallon shi yanda yake magana cikin natsuwa da wannan tsadadden murmushun akan fuskan shi, he is looking damned cute dan ever b4.sam ban san lokacin da suka gama wayan ba har ya juyo shima ya zuba min nashi idon sai ya lura hankali na yayi nisa cikin tunani.

Bai ce min komai ba sai murza hannu na da yake cikin nashi daya fara shiya dawo dani hayyacina,cikin sauri na kwace hannun nawa tare da dauke Kai ina dan murmushi kunyan kamani ina kallon shi, dan dariya mara sauti yayi yana" ina zaki je kuma bayan na shigo tayaki hira?"

"Kitchen zan shiga naga har 5:30 ta gota" na amsa ina kallon gefe dan har yanzu ban gama warwarewa daga kunyan kamani da yayi ina kallon shi ba.

"Me Kuma zakiyi a kitchen d'in?" Ban san lokacin da na juyo ba jin tambayar daya min kaman bai san meye kalmar kitchen d'in yake mufi ba,dauke kaina nayi ganin har yanzu idon shi a kaina suke.

"Girki zan daura" na bashi amsa a takaice.

"No yau ki huta ba sai kin dafa komai ba we re having our dinner outside today dan haka ki huta yau".

"Toh" nace kawai ina jin dad'in cewa zamu fitan da yayi,nan ya zauna muna dan hira jefi-jefi har aka Kira sallah magarib.tashi yayi ya shiga bathroom dina dan yin alwala na bishi da kallo hankali tashe saboda na shanya su panties dasu bra dana wanke dazu ban kwashe ba dan koda na shiga alwalan la'asar basu gama bushewa ba,aiko kaman in tashi in kamo shi nake ji sai dai babu dama.

"Shikenan ya gama gane min sirri" nace kaman zan fashe da kuka.shi kuwa yana shiga bathroom din sai da ya lumshe ido saboda kamshin sabulai da nake wanka duk sun kama bathroom din ga Kuma turaren wuta da nake sakawa shima, tsayawa yayi Yana karewa bathroom din kallo kasancewar yau shine karon farko daya fara shiga, gashi nan fes komai a kimtse a bushe. Har ya fara takawa zuwa gaban sink da niyyan yin alwala karaf idon shi ya sauka kan shanya da nayi kaman Wanda aka sakawa magnet ana jan shi zuwa gare su haka ya karasa yana kallon su kaman bai taba ganin abu makamancin su ba.
.

Hannu yasa yana duba size d'in cikin mamaki ya sake tare da toshe baki yana dariya" wai dama haka yarinyan nan take ban tab'a gani ba,koda yake suna cikin kaya tayaya zan gane" duk shi kad'ai yake surutan sa a bayin yana mamakin ya akayi bai sani ba all this while,can kuma ya tuna ashe fa ko eye pencil bai saya an saka a lefe na ba,sai yaji Kuma babu dad'i " all this are fake zan hado mata nawa da kaina" yace yana nufan sink din ya fara alwala murmushi bai bar fuskan shi ba.

Ni Kuma ina zaune ne kawai amma gaba daya hankali na baya tare da ni I was thinking maybe yana can yana kalle min sirri shiyasa ya dade,ina cikin maganan zucin sai gashi ya bud'e kofa ya fito.wani irin kallo daya min yasa na dauke Kai na da sauri ina jin kaman in fashe da kuka saboda tsab na fahimci ma'anar kallon " kiyi sallah sai ki shirya ba zan shigo ba sai bayan sallah Isha'i" gyada kaina kawai nayi ba tare da na kalle shi ba.

Dariya ya fara kasa-kasa ya fita na raka shi da harara sannan na tashi ina ta mita na shiga bayin nima,sai da na kwashe shanya na sannan nayi alwalan na fito na shimfida abin sallah na fara sallah ta cikin natsuwa.
..

Ban tashi akan sallayan ba sai da nayi sallahn Isha'i da shafa'i da wutiri sannan na shiga wanka,ban wani jima ba kasancewan yace zamu fita,koda na fito ban tsaya dogon kwalliya ba kawai mai na shafa sai powder da kwalli sai wet lips dana gogawa lebe na duk da haka ba karamin kyau nayi ba.parking d'in gashi na nayi na saka ribon na daure su ya koma kaman a cuci maza.

Tashi nayi daga nan zuwa wardrobe ina duba kayan da zan saka, akan wani Turkish gown light blue ido na ya tsaya ba wata-wata na fito dashi ya sha stones work tun daga sama har kasa na saka kayan nayi rolling da gyalen, gaban mirrna dawo na fara shafa humra na mai dad'in kanshi sai gashi nan ya shigo bakin shi dauke da sallama.

Numfashi na kusan tsayawa yayi na wucin gadi kamin ya dawo daidai ina tasbihi ma Allah da yayi wannan kyakyawan haliita da nake gani a gaba na,sosai yayi wani mahaukacin kyau cikin sabon shiga na wani yadi mai taushin gaske d'inkin half jampa kan shi babu hula sai gashinsa daya gyara sai sheki yake.wani abin mamaki kaman hadin baki shima yadin nashi light blue ne sai kamshi yake zubawa.

Ashe shima ta wajan shi abin haka yake dan ba karamin kyau na mishi.ba da kyar ya samu ya tattaro kuzarin sa yace" muje ko"

Tashi kawai nayi nazo zan wuce naji Yana" ba dai a haka zaki fita ba?" Kallon jikina nayi ina neman makusa amma ban gani a raina ina mitan shi komai sai yayiwa mutane iyayi.

"Pls wear ur hijab,tayaya zamu fita a haka mutane su kalle min ke" yace min a d'an kausashe, juyawa kawai nayi zuwa gaban wardrobe na jawo wani hijab ba tare da nasan wani kala bane na fara warwarewa cikin fushi.ban san lokacin da ya zo ba kawai Jin mutum nayi a bayana daf sosai har kirjin sa da bayana sun hadu,kan shi ya daura a gefen wuya na numfashi sa na sauka a gefen wuya na.ban san lokacin da na lumshe idona ba saboda wani irin yanayi da na tsinci kaina a ciki.

Kwace hijabin hannu na da yayi yasa na bud'e ido na sai gani nayi ya ciro wata dark blue irin mai hannun nan ya ajiye na hannu na sannan ya juyo dani ya warware ya fara kokuwan saka min,hannu na kawo da niyyan taimaka mishi ya saka min cikin sauri da sauran fushin sa ya kwabar da hannu na Wanda saida na kwabe fuska dan babu karya naji zafi.

Yana gama saka min yaga wani sihirtacaccen kyau da Kamala sun bayyana kaman yanda yakewa kowace mace data saka hijabi,ajiyar zuciya yayi tare da jawo hannuna muka fito yana aiyyanawa a ran shi cewa dole sai ya nemo min nikaf a gaba.

Har muka fito compound bai sake min hannun ba kuma bai ce min kala ba, wata mota baka dake pake a gefe ya nufa dani ya bud'e gaban motan ya sanya ni a ciki ya.rufe sannan shima ya zagayo ya bud'e mazaunin driver ya shiga ya zauna yayiwa motan key mai gadi ya bud'e mana get muka fita.

Tsit cikin motan baka jin komai sai kira'ar sheikh Sa'ad al ghamdi dake tashi cikin suratul Nisa'i, munyi tafiya mai nisa ba tare da mun kula juna ba domin dukkan mu cikin fushi muka fito amma sauraron kira'ar nan ya saukar mana da natsuwa duk muka rinka sauke ajiyar zuciya akai-akai.

D'an satan kallon inda yake nayi cikin rashin sa'a ashe shima ni d'in yaje kallo, wani sasssanyan murmushi mai kara min natsuwa ya aika min nima ban san lokacin da na mayar mishi da martani ba.

Dayan hannun shi ya miko ya rike min hannu yana murzawa a hankali yana tuki da dayan hannun, haka ya cigaba da tuki muna sauraron kira'ar har muka iso wani hadadden restaurant dake by pass.da alamu sabon waje ne dan ni ko sunan ban taba ji ba.

Shiya bud'e min mota na fito ya kulle motan sannan ya rike hannu na muka shiga ciki,duk inda muka wuce mutane sai sun bimu da ido suke dan ba karamin kyau da dacewa da juna mukayi ba.

Bamu tsaya cikin mutane ba VIP naga muka wuce, Kuma shi yafi ko ina tsaruwa sannan babu mutane, wani table dake can gefe muka nufa yaja min kujera na zauna sannan shima yaja ya zauna ya fito da wayan shi yana daddanawa cikin basarwa.hakan da yayi ba karamin kyau ya mishi ba,muna zaune a haka wata waitress mai kama balarabiya tazo table d'in mu ta tsaya tana tambaya me muke bukata tare da miko mana menu.

Zafar duk da hankalin shi yana kan wayan shi hannu ya mika ya karba ba tare da ya dago ba balle ya san ya take,nima dai ban dago na kalle ta ba wajan nake bi da kallo domin ya tafi da imani na sosai. Ina daga ido naga ta kafe Zafar da ido kaman ta lashe shi har wani murmushi take ta jerowa ba tare da ta san tana yi ba.

Ras naji zuciya ta tayi wani mugun harbawa ina jin wani zafi na taso min a zuciya dan ji nayi kaman in tashi in shako ta,cikin rashin sa'a kuwa ta juyo muka had'a ido wani banzan kallo mai cike da gargadi na aika mata ina Jin wajan ma ya fara fita kaina sai dai ganin shi Zafar din bai san ma tana yi ba yasa na dan ji sanyi a raina.

"Fried rice and chicken with couslow" muka ji muryan shi ba tare da ya dago ba ya fad'a yana mika mata menu su,cikin sauri ta karba ta bar wajan mu dan kawo mana abinda yace.

Ajiye wayan nashi yayi ya dago ya kalle ni yace" ko wajan bai miki bane naga kinyi shiru"..

D'an turo baki nayi cikin jin haushin kallon shi da tayi nace" sun cika kallo dayawa".

Murmushi mai sauti yayi yana"ki fito fili kice kina kishin wata ta kalle ni".

Sai a lokacin na tuno katobar da nayi dan haka cikin tsare gida nace kishin meye kuma zanyi,wani ne da zai fita naga yana ta kallo na".a take murmushin fuskar shi ta bace lokaci daya yana "meyasa baki gaya min ba a lokacin".

Kamin in bashi amsa waitress d'in ta kawo abinda yayi order ta fara jejjera mana su.

Tana gama jerawa ta juya ta bar wajan ba tare da ta kara gigin hada ido da mu ba,tana tafiya naji yace" meyasa baki gaya min ba?"

"Saboda naga ya fita ne shiyasa"kwafa yayi ba tare da ya kara magana ba ya ture dayan plate d'in gefe yasa min spoon a cikin plate na gaban shi yace min " let's eat".

D'an satan kallon mutane dake wuri nayi naga kowa harkan gaban shi yake dan haka banyi magana na dauki spoon d'in muka fara cin abincin ina mita a zuciya ta kan a wajan ma dan iyayi irin nashi a plate daya zamu ci abincin.

Bai fi spoon 4 yayi ba ya dauki tissue ya goge bakin shi, spoon d'in da ya ajiye nabi da kallo kamin inyi magana ya riga ni yace" it's not tasty at all, Ni tunda na saba da girkin ki bana iya cin abincin ko ina wlh".

Wani dad'i ne ya ratsa ni dan inko abinda ya fad'a haka take to tabbas na kusa mallakan shi,ajiye spoon d'in nayi nima ina " toh mu koma gida mana in samo maka abinda zaka ci".

"No dare yayi yanzu,amma tashi muje "yace yana mikewa nima mikewan nayi saida yazo ta waje na ya rike min hannu sannan ya saka musu kud'in su a cikin bill da suka kawo mana muka fito ,yanzu ma shi ya bud'e min mota na shiga ya rufe sannan ya zagaya shima ya shiga ya tada mota muka fito bamu zo gida direct ba sai da ya tsaya a suya sppt ya saya mana dasu ice cream sannan muka dawo gida.

A nan tsakiyan parlour muka zauna kan rug muka ci naman sosai dan suyan yayi mana dad'i,ice cream kam ni kad'ai ce na sha Zafar cewa yayi baya sha.tattara sauran naman da ice cream d'in nayi na kai kitchen naman na saka su a fridge koda na dawo ban tarar da shi a parlour ba ya shiga dakin shi.

Nima dakin nawa na wuce direct bathroom na fad'a nayi brush na watsa ruwa sharp-sharp na fito,gaban mirror naje bayan na goge ruwan jiki na shafa lotion sama-sama sannan nabi lungu da tsako na jikina da humra mai sanyin kamshi.

Normal rigan bacci na saka amma bashi da wani tsaho dan da kadan ya wuce guiwa na, hawa gado nayi na kwanta ina tunanin yinin mu na yau.Zafar ya canza sosai wanda kullum nake tunanin ko dai ya fara sona ne? Wata zuciyar Kuma kwabata take tana tunanin furucin sa akaina.

Zafar kuwa shima bayan ya gama shirin sa na bacci ya kwanta sai yaji duk kwanciyar bata mishi ba so yake ya gan shi kusa dani mu kwanta irin na jiya.

Zurum ya mike kaman Wanda ya tuna wani abu bedroom sleepers d'in shi ya saka ya fito a hankali yana tsand'a har ya iso kofan parlour ya tura ya shiga ya d'an saurara jin shiru babu motsi ya tabbatar mishi da cewa na gama shirin kwanciya na kwanta.

Sai da ya kara matsowa kusa da kofan bedroom d'ina sannan ya fara yin motsi da abubuwa can Kuma ya kunna kukan mage a wayar shi ya d'an yi kukan sannan ya fice da sauri ya koma nashi dakin ya kwanta yaja bargo ya lullub'a yana dariya tare da fatan Allah yasa tarkon da ya d'ana ya kama mishi tsuntsu gasasshiya.

Ni kuwa a lokacin har na lumshe ido ina jiran bacci ya dauke ni amma na fara jin motsi a parlour na,nan da nan na tsure dan ya tuno min da horror film da na kalla sannan ina matukar tsoron mage a rayuwa ta.karkarwa jikina ya fara lokacin da naji kukan mage da gaske ne kuka na fara ina karanto duk ayoyi da addu'oi da suka zo bakina na ja bargo na rufe har kaina.

Lokacin da na daina jin kukan magen na fito da kaina a hankali ina dube-dube a cikin dakin ganin babu komai yasa na sauko a hankali cikin tsand'a na fito parlour shima na leka banga komai ba amma kofan parlour a bud'e take bàyan ina da tabacin na kulle.

Ai ban san lokacin da na fita a guje ba jikina na kara daukan karkarwan ban tsaya a ko ina ba sai dakin Zafar da yake baccin karya.

"Finally" yace can kasan makoshi Yana murmushiin jin dad'i,kamin ya ankara sai ji yayi na fado kan shi tare da kankame shi cikin tashin hankali da tsoro Ina "mage mage Zafar a parlour na,I don't like cats ina matukar tsoron su nace ina kara shigewa cikin jikin.

Da kyar ya samu ya fusgo numfashin sa daya bar jikim sa na wucin gadi,hannu 2 yasa ya kara mana ni da jikin shi yaja bargo ya rufa mana yana shasshafa ni da sauri-sauri dan gaba daya notin kan shi ya kwance babu abinda yake gani ko yake ji a halin da yake ciki sai na cikar burin shi bai taba shiga hali na bukatuwa kaman yau ba.

Nima duk da ina Jin bakon al'amari a tare da ni firgita da nayi bai barni na dawo normal ba,shima ganin ban hana shi ba ya fara aika min da sakonni da zafi-zafi cikin fitan hayyaci.

Ban ankara ba naji yana kokarin zame min riga cikin sauri na rike mishi hannu ina girgiza mishi kai,da kyar na iya bud'e baki na nace" kayi hakuri ba muyi haka cikin yarjejeniyar mu ba"

Idanun shi da suka canza kala ya watso min, cikin azama nayi kasa da nawa har yanzu jikina bai bar rawa ba sai da ya min kallon kysan 30 seconds sannan ya janye idon nashi a fuskata ya dawo dashi kan kirjina da ban saka komai a ciki ba kawai rigan bacci na zura,da yake rigan mai mannewa a jiki ne ana iya ganin su freely.

Yawu ya hadiye da kyar tare da maida kallon shi kan fuskata yace" na san da wannan just ki bar abinda ya wuce ya wuce pls, yanzu mu fuskanci gaba".

Dan Satan kallon shi nati naga har yanzu idon shi a kaina suke na sauke nawan ina" ba zai yiwu ba Zafar abubuwa nawa ka fad'a min kamin auren wanda kace ba zasu taba canzawa ba" na karasa ina addu'an Allah yasa yace ta janye kalaman nashi.

*I'm very sorry I always keep u people waiting,Dan Allah kuyi min afuwa wlh na fiku son inga mun kammala littafin nan Amman hakan Bai yiwu ba,ina ganin korafin ku a groups har da pc insha Allah zaku rinka jina a duk lokacin da na samu sarari*.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.