Rijiya Gaba Dubu Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Rijiya Gaba Dubu Part 2 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 1 of 1
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 1
Da isar saiyaru cikin gidan kurkukun bayan ya wuce kofofi goma sha daya sai ya wuce kai tsaye izuwa dakin tuhuma yana ta murmushin mugunta,da isar sa kofar dakin sai masu gadin dakin suka rusuna suka gaishe shi,ko kallon su bai yi ba ya daka musu tsawa yace Maza ku budemini kofar da sauri na shiga,cikin hanzari daya daga cikin masu gadin yasa kuba ya bude kofar ya kunna kai,ashe wadannan masu gadin duk na bogi ne acikin shigar kayan dakaru suna daga cikin dakaru guda ashirin din da Imhal suka zaba domin su taimaka musu wajen samun nasarar guduwa daga kurkukun.Da shigar saiyaru cikin dakin sai yayi arba da Zauwadu zaune akan kujerar da aka saba dora masu laifi an daure hannayensa da kafafunsa da sarkoki ga badakare daya a tsaye akansa yana dukansa da kulki har ya fasa masa baki da hanci jini na suba.koda ganin haka sai saiyaru ya bushe da dariyar mugunta sannan ya dubi badakaren yace dakata haka yanzu kuma nine zanyi masa tawa azabar,ya kai Zauwadu kayi sani cewa yau ne ajalinka zai tabbata a hannnuna tunda har ka karya dokata ka sake haddasa fada tsakanin fursunoni,hakika yau gawrka rabon kifayen dake cikin teku ne.yana gama fadin haka sai ya daga kulkinsa ya nufi Zauwadu da nufin ya buga masa a kansa,ba zato ba tsammani sai kawai wannan badakaren dake tsaye ya shammaci saiyaru ya maka masa kulki akan kunnensa na hagu,take saiyaru ya sulalae kasa sumamme.Koda saiyaru ya farfado sai ya tsinci kansa a zaune akan kujera wacce ake dora fursunoni idan za a yi musu azaba an daure hannayensa da kafafunsa ta baya,Imhal da Zauwadu na tsaye akansa sanye da kayan dakaru,shi dai Zauwadu kayan saiyaru ya sanya sannan ya sanyawa saiyaru nasa na fursunoni.Koda saiyaru yaga haka sai ya tuntsire da dariyar mugunta kuma ya turbune fuska yace kun bata lokacinku a banza domin baku isa ku iya guduwa daga cikin gidan nan ba,nan gidan mutuwa ne gidan da babu wani fursuna da ya isa ya tsira da rayuwarsa koda kun gudu sai an kamo ku an dawo daku idan ma sanyin teku da halittun cikinsa basu hallaka ku ba.Koda gama fadin haka sai saiyaru yaci gaba da kyalkyala dariyar mugunta,cikin fushi Zauwadu ya daga katon kulkin nan na saiyaru ya maka masa shi a ka,take kan saiyaru ya fashe har kwakwalwarsa tayi fallatsi,koda suka ga saiyaru ya mutu sai Imhal ya dubi Zauwadu yace to fa yanzu duk nasarar mu tana hannunka duk yadda za a yi kada ka kuskura ka bari a gane cewa kai ba saiyaru banen,hatta muryarka sai ka karyar da ita irin ta saiyaru tunda daman can kuna kama da juna a fuska da yanayin jiki.Zauwadu ya risina ga Imhal yace yakai abokina kuma shugabana a wannan gida na darul maut,ina mai tabbatar maka cewa baza a taba samun wata matsala ba daga gareni sai dai daga sauran yan'uwanmu fursunoni guda ashirin wadanda muka janyo cikin wannan aiki,ni dai alkawari daya nakeso kayi mini,koda jin haka sai mamaki ya kama Imhal yace wane alkawari kakeso nayi maka?koda jin wannan tambaya sai Zauwadu ya sanya hannu acikin aljihunsa ya dauko wata sarka ta dinare ya damkawa Imhal a hannunsa yace,Wannan sarka ce ta matata wacce muke tsananin son juna fiye da hangen mai hange,a ranar da aka daura aurenmu da ita acikin birnin kisra dakarun sarki Gurzalu suka zo su dubu uku suka rufeni da masifaffen duka har sai da suka sumar dani,ina ji ina gani aka Rabani da amaryata SUHAILA aka sa mini sarka a wuyana,hannayena da kafafuna aka tafi dani suhaila tana kuka da ihu.Wannan shine asalin rabuwata da suhaila yau tsawon shekaru ashirin da bakwai kenan,suhaila na raye ko ta mutu ban saniba.ina son duk sanda ka dawo cikin birnin kisra komai dadewa ka nemi suhaila a unguwar Sharkas ka bata wannan sarka idan har na rasa rayuwata a kokarin guduwarmu daga nan,idan kuma na tsira da rayuwata to zan karbi sarkata domin nayiwa suhaila alkawarin cewar indai ina raye komai daren dadewa sai na dawo gareta ,amma idan ta ga an kawo mata sarkarta to bana raye.Koda Zauwadu yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubo masa,Al'amarin da ya karya zuciyar Imhal kenan shima yaji ya kamu da tausayin Zauwadu har kwalla t acika masa idanu,nan take dai suka fito daga cikin dakin tuhuma Imhal ya sanya sarkar suhaila a cikin aljihunsa suka kullo kofar dakin ,masu gadin dakin mutum biyu suka rufa musu baya.
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 2
Duk ta inda su Zauwadu suka zo wucewa sai ka ga ana gaishe su sabo da ana zaton saiyaru ne,hatta muryar Zauwadu ta amsa gaisuwar sai ta zama iri daya sak da ta saiyaru,su kansu su Imhal sai da suka cika da tsananin mamaki bisa yadda suka ji Zauwadu ya iya mayar da muryar tasa haka,haka dai suka cigaba da tafiya har suka iso dakin da ake ajiye gawarwakin fursunonin mutum hudu da suka mutu a sanadiyyar fadan da akayi a dakin cin abinci,kawai sai Zauwadu ya bada umarni a debo gawarwakin a dora su akan amalanke domin a futar dasu gaba daya daga gidan a watsa a teku,nan take kuwa dakaru suka cika wannan umarni daya bayan daya fursunonin nan guda ashirin abokan aikin su Imhal suka dinga shigowa cikinsu suna take musu baya.dama su duka sunyi shigar dakarun gidan kurkukun,haka dai su Imhal suka cigaba da tafiya acikin kurkukun suna tura amalanken gawa ana bude musu kofofi,duk inda suka zo da zarar anga saiyaru akan gaba sai kaga anbude musu kofa da sauri har suka shige ta cikin kofofi goma sha biyu na kurkukun kuma duk kofar da suka fita sai an mai da ita an rufe.
Suna fitowa daga cikin kofa ta karshe sai suka yi arba da dandazon dakarun dake tsaron gidan kurkukun,a gefe daya kuma ga jirgin ruwa da ma'aikatan kurkukun ke shiga idan zasu je karbo abinci ko wani kaya acikin birnin kisra.Su dai masu gadin kurkukun dakaru ne kimanin guda dubu arba'in,kuma ko yaushe acikin shirin yaki suke dauke da muggan makamai,koda suka yi arba da juna tsakanin su Imhal da masu gadin sai aka tsaya ana kallon-kallo,in ba don ma shugaban dakarun ya hango saiyaru akan gaba ba da tuni ya baiwa yaran nasa umarni su afka musu.
Cikin karamar murya Imhal ya matso daf da Zauwadu yace dashi kada ka kuskura ka matsa kusa da dakarun can,domin sai shugabansu ya gane cewa kai ba saiyaru bane,daga nan zaka yi musu magana ka gaya musu cewa zamu tafi watsa gawar fursunoni ne teku.Koda jin wannan umarni sai Zauwadu ya daga murya ya dubi shugaban dakaru yace ya kai Murwatu kayi sani cewa yau an samu mutuwar fursunoni har guda hudu,sabo da haka ina son ku bani jirgi na zuba su a ciki sai na isa tsakiyar teku sannan na zubar dasu domin na tabbatar da cewa sun zama abincin kifayen ruwa.Koda jin wannan batu sai Murwatu ya turbune fuska ya dakawa saiyaru tsawa yace,Kai saiyaru sabo dame yau zaka zo mana da sauyin yanayin aiki? A aikin tarihin gidan nan tsawon shekaru arba'in da kafuwarsa ba a taba yin hakan ba,duk fursunan da ya mutu daga nan ake jefa gawarsa cikin tekun,idan baza ku iya jefa gawarwakin ba daga nan to fa sai dai ku hakura ku koma da gawarwakin ku,duk wanda yayi wani yunkuri cikin ku kuwa zamu far masa.
Koda jin wannan batu sai hankalin su Imhal ya dugunzuma ,suka rasa abinda ke musu dadi domin ga dukkan alamu sun sha wahalar banza kenan bisa duk irin kokarin da sukayi suka samu nasarar fitowa har kofar karshe ta gidan kurkukun DARUL MAUT.
Cikin tsananin damuwa da karayar zuciya Zauwadu ya dubi Imhal yace ya kai abokina yanzu mene abin yi?Imhal yace Bamu da abin yi face mu yaki su Marwatu ko mu ko su!
Cikin firgici Zauwadu yace Baka da hankali ne,ta yaya mu ashirin da biyu zamu iya yakar dakaru dubu arba'in?
Imhal yace bamu da wani zabi wanda ya wuce hakan,ko dai mu yake su ko kuma mu jefa kanmu acikin tekun nan mu hallaka shine kadai gatan da zamu yiwa kanmu,ya kai abokina kai sani cewa faduwar gaba asarar namiji ce,yau ne za muyi yaki da dukkan karfinmu na jiki da karfin zukatanmu,ko mutuwa mukayi mun bar abin fadi.Ko kuwa ka zabi ka koma cikin darul maut a cigaba dq gana maka azaba har ka mutu tunda kasan cewa ko kadan baza ayi mana sassauci ba tunda mun kashe saiyaru?koda Zauwadu da sauran fursunonin suka ji wannan batu sai nan take suka ji dukkan tsoro ya kau daga cikin zukatan su.
AYI MIN AFUWA ZAN CI GABA
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA3
Lokaci guda su duka suka daga kulakensu,sannan suka ruga izuwa kan dandazon dakarun suna masu kurma uban ihu,ai kuwa suma wadan nan dakaru su dubu arba'in sai suka zare takubban su suka ruga gare su.ana haduwa aka kacame da azababben yaki. a kofar gidan na darul maut.Kaico hakika idan mutum yaga mutuwa muraran to fa sai inda karfinsa ya kare,duk da cewar su Imhal yan kalilan ne a cikin wadannan dakaru sai gashi suna ragargazarsu don duk inda suka sa gaban su sai dai kag maza na zubewa kasa alokacin da jini ke feshi da fantsama,kuma ihun mazaje da karafkiyar karafa ta cika dodon kunne.Koda aka samu dakika dari biyu ana wannan gumurzun sai labari ya sauya sabo da sarkin yawa yafi sarkin karfi,nan fa dakaru suka fara samun nasarar saran jikin fursunonin nan,jikinsu na darewa suna ihu amma sabo da naci gami da taurin rai sunki su fadi kasa,a hakan suke cigaba da yaki.Sai dai kaga jikin fursuna yayi kaca-kaca da sara da suka tamkar yayi wanka a kogin jini amma shima bai fasa ragargazar maza ba,wani lokaci ma har faduwa suke kasa sakamakon jiri dake dibarsu amma sai kaga suna mikewa tsaye suna cigaba da yakin.
Koda shugaban dakarun ya ga ana ta ragargazar yaransa kuma ya kasa fahimtar bangaren dake samun nasara a tsakanin mutum ashirin da biyu kacal da kuma mutum dubu arba'in sai ya fusata ainun ya kutsa cikin fursunonin nan da karfin tsiya cikin tsananin kwarewar yaki ya dinga fillewa fursunonin kawuna suna zubewa kasa matattu.
Kafin Zauwadu da Imhal su ankara da abinda yake faruwa tuni ya kshe musu mutane goma sha biyu ya zamana cewa saura goma kacal,koda Imhal ya juyo yaga gawarwakin jama'arsu a kasa a lokacin da gaba daya jikinsa ya rine da jinin dakarun da ya kashe sai ya kwarara uban ihu ya kara kaimi yana mai cigaba da sara da suka cikin tsananin zafin nama mara misaltuwa sai gashi yana yiwa dakarun mummunar barna.
Shima Zauwadu da yaga Imhal ya kara zage damtse sai shima yayi koyi dashi suka haukace suna ta daukar rayuka,Koda shugaban dakaru Murwatu yaga haka sai ya daka tsalle sama kamar an cilla shi daga cikin kibiya ya dira a gaban Zauwadu ya tare shi suka ruguntsume da azababben yaki.
Wohoho! idan tsagwaron karfi ya hadu da kwarewa akwai tashin hankali,kai koda ga dan kallo ma cikin firgici da tashin hankali zai iya kallon wannan gumurzun.Sai da Marwatu da Zauwadu suka shafe dakiku masu yawa suna kaiwa juna mugayen hare-hare na sara da suka basu samu nasarar komai ba.
A wannan lokaci kuwa Imhal ya samu nasarar bazar da dakaru dubu ashirin a kas,ragowar dubu ashirin din ma sun razana dashi ainun sun fara ja da baya duk da cewa wasun su ya sassare su amma sabo da naci sun ki hakura dada yi masa kawanya suke domin suyi masa rubdugu
A bangaren Marwatu da zauwadu kuwa,lokacin da suka fafata ainun suka ga babu wata nasara sai suka ja da baya sukayi cirko-cirko suna haki da kallon juna kamar wadan su zakaru,kowannensu na tunanin irin dabarar da zai sauya don ya samu nasara akan abokin yakinsa.kamar hadin baki suka zare takubbansu suka daga sama lokaci guda suka rugu izuwa kan juna suna kururuwa,koda ya rage saura bai fi taku uku ba su hadu sai kowannensu ya daka tsalle sama suka kaiwa juna mummunan hari.Cikin sa'a Murwatu ya sokawa Zauwadu takobi a kahon zuciyarsa,shi kuwa Zauwadu ya soka masa a gefen cikin sa,suka rikito kasa a matukar galabaice jini na zuba a jikin su.
Zauwadu ya baje a kasa wanwar ya kasa tashi yana aman jini da karkarwar jiki,shi kuwa Marwatu sai ya mike tsaye ya yage rigar jikinsa ya daure raunin cikin nasa don tsaida zubar jini.
TO AYI MUN AFUWA ZAN CIGABA IDAN NA HUTA
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 4
Koda ya dubi Zauwadu yaga yana kakarin mutuwa kuma ya waiga yaga shima Imhal ya fara gajiya ainun tsabar naci ne da tsananin juriya yasa yake cigaba da yakin sai ya bushe da dariyar farin ciki ya dubi zauwadu yace Ai babu yadda za ayi ku samu nasarar guduwa daga nan har ku tsira da rayuwarku,shekaru arba'in baya haka muke gadin gidan nan ku duka sai kun zama gawa,saura Imhal shi kadai a tsaye shima kuma yanzun nan zan koma na gama dashi kamar yadda na gama dakai.
Koda jin wannan batu sai hawayen bakin ciki ya zubowa zauwadu ya dubi gawarwakin 'yan uwansu fursunoni dake kwance a kasa,kawai sai ya yunkura cikin matukar karfin hali ya bushe da dariya ya dubi marwatu yace,Tabbas mutuwa zanyi amma ko ba komai na jagoranci fursunoni mun karya alkadarin gidannan tunda gashi har mun samu nasarar fitowa daga cikinsa alhali babu fursunan da ya taba fitowa,ko ba komai kai marwatu zan mutu na barka da tabon yankan takobina a cikinka.
Gama fadin haka keda wuya sai suka ji karar bude kofofin kurkukun guda goma sha biyu gami da gudun sawaye alamar cewa dakarun da ke cikin gidan sun faarga da mutuwar shugabansu saiyaru wanda aka bar gawarsa a dakin tuhuma don haka fitowa za suyi waje su kawowa su marwatu dauki.
Koda Imhal ya jiyo sautin gudun dakarun daga cikin kurkukun sai ya zabura ya falfalo da azababben gudu izuwa inda su marwatu suke ya buda dakarun nasa da karfin tsiya yana saransu da banke su kai kace tamkar bai taba gajiya ba ko kuma a sannan kuma a sannanne ma ya fara yakin.
Kafin marwatu ya juya ya tari Imhal tuni Imhal ya dako tsalle a sama ya doki gadon bayansa,sabo da karfin dukan sai da marwatu yayi tsalle sama ya bar kan tsuburin gaba daya ya fada cikin tekun,koda ganin haka sai ragowar dakarun nasa gaba daya suka ruga zuwa bakin tekun domin su ceto rayuwar marwatu.
Damar da Imhal ya samu kenan ya sunkuya ya dauki zauwadu ya saba shi ae kafada ya ruga da baya izuwa inda jirgin ruwa yake ya daka tsalle ya dirga acikin jirgin ruwan ya warbar da zauwadu a ciki sannan yasa takobinsa ya sare igiyar da ta daure jirgin,aikuwa sai igiyar ruwa ta kada jirgi sai gaba.
a dai dai wannan lokaci ne dakarun cikin kurkukun suka karaso kofar gidan a guje suna da yawa kuma a sannan ne aka tsamo marwatu daga cikin tekun aka dawo dashi kan tsibirin.
Koda marwatu ya kyalla ido ya hango su Imhal acikin jirgi nesa kadan da tsibirin sai ya kwarara uban ihu yace A ruga a debo karnukan gidan,nan take kuwa aka je aka debo karnukan,Marwatu da karnukan tare da wadansu dakaru kimanin mutum dari biyu suka shiga wani jirgin dabam suka bi bayan jirgin Imhal.
TO JAMA'A AYI MIN AFUWA IDAN NA HUTA ZAN CIGABA.
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 5
Lokacin da Imhal yaga igiyar ruwa ta kada jirginsu yayi gaba sa ya dawo inda ya warbar da Zauwadu ya iske shi yana ta kakarik mutuwa bai mutu ba,Imhal ya durkusa daf dashi ya kama hannayensa ya rike a lokacin da hawaye ya zubo masa ya dube shi yace "Haba ya kai abokina,sabo dame zaka tafi ka barni alhalin gashi mun sami nasarar guduwa daga kurkukun darul maut?" koda jin wannan batu sai Zauwadu yayi kakin jini ya tofar sannan ya dubi Imhal cikin karfin hali yace"ya kai abokina ina mai farin ciki da ya zamana cewa kai kadai ka tsira da rayuwarka daga cikin mu ba don komai ba sai don nasan cewa ka samu damar da zaka cika alkawarin dake tsakanin mu, duk ranar da ka riski matata suhailat ka bata labari irin rayuwar da mukayi a cikin kurkukun darul maut da yadda ka zama babban abokina kuma masoyina alhalin da farko mun kasance makiyan juna,ka sanar da ita yadda akayi muka samu nasarar guduwa daga wannan masifaffen kurkuku har izuwa sanda ajalina ya riskeni,ya kai Imhal idan kayimin haka ka gama yimin komai,kuma cikin kabarina zanyi bacci acikin kwanciyar hankali batare da bakin ciki ko nadamar komai ba,sabo da ko ba komai matata tasan cewa na mutu a filin daga a matsayin gwarzon jarumi,ka sani cewa ba wani laifi nayi baaka kawoni kurkukun darul maut face kawai na hana dakarun sarki Gurzalu zalunci a watavrana sanda suka shigo cikin gari suka kashe wani attajiri suka kwashe dukiyar gidansa kaf,suna shirin kashe iyalinsa ne na afka musu na ragargaje su suka gudu,nan take na taimaki iyalan attajirin na kaisu tashar jirgin ruwa suka hau jirgi suka bar garin gaba daya,tun daga wannan rana sarki Gurzalu ya dinga farauta ta ina buya har izuwa ranar da tsautsayi yasa aka zo aka kamani ranar da na auri suhaila" kodaZauwadu yazo nan a zancen sa sai yayi wa Imhal murmushin karshe sannan idanunsa suka kafe gaba daya jikinsa ya sandare ya zama gawa.Koda ganin haka sai Imhal ya kwanta akan gawar zauwadu ya rungumeta yana mai fashewa da matsanancin kukan bakin ciki kamar ba zai taba dainawa ba, sai da Imhal yayi kuka har ya gaji barci ya dauke shi bai sai ba,a lokacin da igiyar ruwa ta ci gqba da kada jirgin acikin teku yayi ta tafiya ba sassauci.
TO JAMA'A ZAN CIGABA IDAN NA HUTA
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 6
Al'amarin su marwatu kuwa,wadan da suka hawo wani jirgin tare da mugayen karnuka kimanin guda arba'in sai suka nemi jirgin su Imhal suka rasa a cikin tekun domin ya bace musu sakamakon iskar da ta ie kadawa mai karfin gaske ce gami da hazon da ake yi mai duhun gaske,amma sai suka cigaba da tuka jirgin nasu a haka,sai da suka kwana uku suna tafiya a cikin teku sannan suka iso bakin gaba a wata sakaliyar safiya,ai kuwa suna isowa suka yi kicibis da jrgin su Imhal a gefen tekun,cikin hanzari murwatu yasa aka saki wadan nan karnuka suka ruga izuwa cikin jirgin Imhal suna nemansa suna shinshine-shinshine,A lokacin ne murwatu da dakarunsa suka iso gaban jirgin suka caje cikinsa kaf amma basu ga Imhal ba sai alamar jinin zauwadu da ya zuba a kasa wanda har ya bushe,Kawai sai marwatu ya dago kai ya dubi dakarunsa yace Duk yanda akayi Imhal yana nan cikin dajin nan bai yi nisa ba amma abokinsa zauwadu ya mutu domin babu mutumin da zai zubar da jini mai yawa haka ya rayu,yanzuzamu bazama cikin wannan daji duk inda Imhal yake sai mun riske shi mun kashe shi,sai na cire kansa na tafi dashi izuwa darul maut domin sauran fursunonin gaba daya su gani ya zama gargadi a gare su don kada wani yace zai kara yunkurin gudu anan gaba,kuma nasan cewa sai sarki Gurzalu ya daukaka ni ya bani dukiya mai yawan gaske sakamakon wannan gagarumin aiki da zanyi kai inda hali ma a araye nake so na kamo Imhal domin na mayar dashi cikin darul maut mu sake tsare shi sabo da sarki ya fi son su sake haduwa a gasar jarumtaka wacce za ayi a birnin misra nan da cikar kwana goma sha daya,maza ku saki karnukan nan subi sawun Imhal domin suna iya jin kamshin mutum komai tazarar da ya basu kuma suna da karfin gudun da bai isa ya tsere musu ba.Koda jin wannan umarni sai dakarun dake rike da karnukan suka sake su suka sake rugawa izuwa cikin dajin suna masu haushi da falfala azababben gudu su marwatu suka bi bayan karnukan da gudu.Marwatu na cikin yin gudu sai raunin da ke gefen cikinsa ya motsa yaji wani azababben zafi da zugi ya shige shi,bai san sanda ya fadi a kasa ba,nan da na dakaru suka yanyame shi,koda ya kwaye rigarsa sai yaga ashe dinkin raunin ne ya farke,cikin tsananin takaici marwatu ya kwarara uban ihu ya dubi dakarun yace Maza ku tafi farautar Imhal kada ku dawo nan sai tare dashi,nan take kuwa suka bi bayan karnukansu da gudu shi kuwa marwatu sai ya bude jakar guzurinsa ya dauko zare da allura gami da garin magani domin ya sake gyara rauninsa.
Al,amarin Imhal kuwa,a ranar da jirgin ya kawo shi gabar teku sai ya dauko gawar zauwadu ya fito da ita daga cikin jirgin ya nausa da ita izuwa cikin daji,sai da yayi tafiya mai nisa ya iso gaban wani katon dutse sannan ya sauke gawar ya haka kabari ya binne ta.A sannan ne ya kurawa kabarin idanu yana tuno duk abubuwan da suka faru a baya tsakaninsa da zauwadu a cikin darul maut,kawai sai hawaye ya fara zubo masa,yana cikin wannan hali ne ya jiyo sautin haushin karnukan nan na darul maut,da yake yasan irin haushin nasu kuma ya san tsananin gudunsu da irin mugun horon da aka basu sai hankalinsa ya dugunzuma ainun,kawai sai ya mike tsaye zumbur! ya falfala da azababben gudu izuwa cikin dajin.
Imhal ya dage iya karfinsa da iyawarsa har yana tashi sama yana shallake duwatsu da karyayyun bishiyoyi da suka fadi kasa amma koda ya waigo sai ya hango wadan nan karnukan suna neman cimmasa sai kawai ya kara kaimin gudun,Ba zato ba tsammani sai yaga wani katon rami mai tsananin zurfi a gabansa,kafin ya iya sarrafa kansa ya cije sai karfin gudun nasa ya rinjaye shi ya fada cikin ramin yana mai kurma uban ihu.
TO AYI MIN AFUWA IDAN NA HUTA ZAN CIGABA
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 7
Sa'ar da yayi kawai kawai kasan ramin cibiya ce ta ruwan teku amma yana tsunduma a cikin ruwan sai kansa ya bugu da wani dutse ya sume.
Su kuwa karnukan suna isowa bakin ramin sukayi tirjiya suka fara haushi,sautin haushin nasu ya cika dajin gaba daya,wanda hakan ne ya janyo hankalin dakarun Marwatu suka rugo sashin da suke jin haushin cikin matsanancin gudu,suna cikin gudun ne suka hango karnukan sun kewaye wani rami suna ta haushi,don haka suka kara azama don nufar inda ramin yake.
Lokacin da dakarun marwatu suka iso bakin ramin wanda Imhal ya fada sai suka iske karnuka a tsaye a wajen suna ta haushi sai suka leka kasan ramin,ai kuwa sai suka hango Imhal a kwance akan ruwa kuma ruwan yana tafiya dashi ko motsi bayayi kamar gawa.
Cikin gaggawa wasu daga cikinsu suka gangara kasan ramin suka shiga cikin ruwan suka tsamo Imhal,suna fitowa dashi sai suka ga yana numfashi don haka sai suka yi sauri suka turmushe shi suka daure hannayensa da kafafunsa da sarkoki sabo da sun san cewa in har ya farfado baza su iya kamashi ba.
Nan take suka daure shi suka kai shi can inda Marwatu yake zaune,da zuwan su suka iske Marwatu a kishingide ya gama dinke raunin dake cikinsa ya saka magani,koda Marwatu yaga dakarunsa sun dawo dauke da Imhal a daure cikin sarka sai ya kamu da tsananin farin ciki mara misaltuwa ya mike tsaye zumbur!ya kwarara uban ihu irin wanda manyan barade ke yi afilin yaki yayinda suka samu nasara akan abokin gabar su,kawai sai yasa aka warbar da Imhal gefe daya a kasa aka kyale shi har sai da ya farfado daga suman da yayi.
Koda Imhal ya bude idon sa yayi arbuna da marwatu zaune a gabansa yana yi masa murmushin mugunta sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya yunkura da nufin ya gudu amma sai ya kasa sakamakon sarkokin da suka daure kafafuwansa da hannayensa
AYIMIN AFUWA ZAN CIGABA
TO AYIMIN AFUWA ZA CIGABA IDAN NA HUTA
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA8
Nan take yaji wani irin bakin ciki ya lullube shi,ya ayyana a ransa cewar da ma ya mutu a kokarin wannan guduwa da yayi daga kurkukun Darul maut da ya fiye masa alheri.
Kawai sai yaji marwatu ya bushe da dariyar mugunta yana mai nuna shi da yatsa,daga can sai marwatu ya fara yiwa kansa kirari yana cewa Nine sa gudu maganin ki gudu,kuma nine sarkin darul maut mai RIJIYA GABA DUBU,ya kai wannan takadarin jarumi,kayi Sani cewa inda ba muyi nasarar kamoka ba da sai Na kashe kaina sabo da Kaine kadai jarumin da ya karya alkadarina,ya sami nasarar guduwa daga kurkukun darul maut Wanda Na shafe shekara da shekaru INA gadinsa,ban taba samun rauni ba a rayuwata sai wannan karon don haka idan muka koma darul maut sai Na dandana maka azabar da bantaba dandanawa wani fursuna ba sai Na shigar da kai RIJIYA ta azaba mai GABA DUBU.Koda gama fadin haka sai marwatu ya mike tsaye yaje inda jarumi Imhal yake zaune ya shammace shi ya gabza masa wawan naushi a fuska ,nan take Imhal ya sulale a kasa sumamme.
lokacin da Imhal ya farfado sai ya tsinci kansa a cikin jirgin ruwa ga marwatu da dakarunsa sun kewaye shi,yana daga kansa sama ya dubi gabas sai ya hango kurkukun Darul maut a nesa da su kadan,jirgin Na tafiya acikin teku,al'amarin da ya jefa Imhal acikin bakin ciki kenan a cikin zuciyarsa yace Yanzu mene ne amfanin wannan yunkurin guduwar da nayi?wai shin menene dalilin da yasa bai kashe kansa ba ya huta da wannan bakin ciki?yana cikin wannan tunanin zuci ne jirgin nasu ya I so kofar kurkukun Darul maut,nan take aka tsaida jirgi ya tsaya cak! sannan dakaru suka kama Imhal suka tashe shi tsaye aka fitar dashi daga cikin jirgin ,shi kuwa marwatu bai fita daga cikin jirgin ruwan ba sai ya dubi dakarun da suke rike da Imhal yace dasu Kada Ku kaishi bangaren dakin fursunoni Ku kaishi dakin RIJIYA GABA DUBU Ku daure shi a jikin bango da sarkoki Ku barshi a haka,kuma kada a bashi ruwa ko abinci har sai Na dawo,
Zanci GABA in Na huta
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA9
Na tafi gidan Sarki domin inyi masa albishir bisa nasarar kamo Imhal da mukayi,koda gama fadin haka sai marwatu ya juya ya umarci masu tukin jirgin da su juya akalar jirgin su nufi cikin gari,ba tare da gardamar komai ba kuwa suka bi umarninsa suka juya jirgin suka kama hanya akan ruwa.
Su kuwa dakaru sai suka shigar da jarumi Imhal cikin kurkukun,suna shigewa aka mai da kofar Gidan aka rufe,tayi kara mai karfi tamkar an kulle kofar birnin gaba daya,yayin da aka zo wucewa da jarumi Imhal ta bangaren dakunan fursunoni suka kyalla I do suka hango shi sai suka kama ihu da shewa suna yi masa tafi da jinjina sabo da kasancewarshi fursuna Na farko da ya taba samun nasarar guduwa kuma ya tsira da rayuwarsa.Koda fursunoni suka ga an nufi dakin RIJIYA GABA DUBU da Imhal sai gaba dayan su jikin su yayi sanyi suka kamu da tsananin tausayinsa,ba komaine ya haddasa hakan ba face sanin cewar duk mutumin da aka shigar dashi cikin
ayya frnds ayimin afuwa wlh fefar littafin ta tsakiya banganta ba amma bari nayi wani postn din Na cigaba yanzu
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 11
Koda Imhal yazo nan a zancensa sa aljani Sautil makatur ya bushe da dariyar mugunta a karo Na biyu yace, Sai kayi kokari ka fita daga nan din cikin hayyacinka yadda zaka iya bude idanunka ka kalli maharbi Imzanu. Koda gama fadin haka sai aljani Sautil makatur ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba acikin dakin,nan fa Imhal yaci gaba da jin tsananin zogi da radadin Harbin da kunamun nan suke masa har ya dinga jin kamar ya yanke duk wadan nan kurajen na jikinsa wadan da suka duri ruwa, gashi kuma a wannan lokacin yunwa da kishirwa sun addabe shi sai birgima yake yi a kasa yana mutsu- mutsu,kai komai rashin tausayin mutum idan yaga Imhal acikin wannan hali dole ya tausaya masa, haka dai Imhal ya kasance acikin wannan hali har sai da dare ya raba sannan aka bude kofar dakin RIJIYA GABA DUBU aka shigo aka baiwa Imhal wani irin ruwa mai tururin zafi acikin kwarya,Hakika masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce, Wanda yake cikin ruwa ko takobi aka mika masa kamawa zai yi, domin ana mikawa Imhal wannan ruwa a lokacin da yake fama da kishi sai kawai ya karbi kwaryar ya kafa a bakinsa ya fara kwankada duk da cewar ruwan yana kona masa harshe kuma yana mugun war I sannan bashi da dadin dandano,shi dai kawai burinsa ya jika makogwaronsa ya kawar da kishirwar da ta addabe shi. Hakika rashin Sani yafi dare duhu! Inda Imhal yasan abinda sai biyo baya da bazai sha wannan ruwan ba,gwara ya gwammace kishirwa ta zama ajalinsa domin yana gama shan ruwan da kamar dakika daya sai cikinsa ya murde matuka ya kama ciwo yaji kamar ana daddatsa hanjin cikinsa,bai San sanda yaci gaba da birgima ba a kasa yana rusa ihu,idanunsa kuwa suka kumburo sukayi bulu-bulu kamar zasu fado kasa.
Ayi min afuwa zanci gaba idan na huta
RIJIYA GABA DUBU 2 CIGABA 12
Kurajen dake jikinsa kuwa sai suka cigaba da tsananin zogi suna kara kumbura, Daga can kuma sai Kurajen suka dinga fashewa da Kansu suna zubar da jini gami da wani irin mugunyar ruwa mai doyi, nan take kurajen Na gama fashewa gaba daya sai ya sume, bai sake farfadowa ba sai da sanyin asuba ya buga.A sannan ne aka sake bude kofar dakin aka kawo masa abinci loma daya da ruwa mukurwa uku acikin wani Dan karamin kofin kasa, Haka dai aka cigaba da ganawa Imhal azaba kullum, daga cikin azabobin da aka tanada na cikin RIJIYA GABA DUBU, har tsawon kwana goma sha hudu ya zamana cewa ya rame matuka ya lalace kuma ko ina a jikinsa duk ciwuka ne babu kyan gani,hatta fuskarsa ma sai da tayi muni amma duk wannan tsananin azaba da yunwar da ake yi masa horo da su bash sa ya mutu ba.
A Ranar kwana na goma sha hudu ne da sassafe aka bude dakin RIJIYA GABA DUBU aka fito da jarumi Imhal a cikin matukar galabaice tamkar an dauko tsumma domin ko kadan babu kuzari a jikinsa da kyar ma yake iya taka sawayensa, da yawa daga cikin fursunonin Gidan ma da aka zo za a wuce dashi ta gabansu kasa shaida shi suka yi saboda yadda kamanninsa suka sauya da kuma yadda ya rame matuka, Koda fursunoni suka shaida shi sai suka kamu da tsananin tausayinsa harma wasu suka zubar masa da hawaye, nan dai aka fitar da Imhal daga cikin kurkukun gaba daya aka saka shi acikin jirgin ruwa a daddaure cikin sarkoki, kai kace wani katon goggon biri aka kamo, kuma suma dakaru DUBU ne suka kewaye shi acikin jirgin ruwan don kada yayi wani yunkuri na guduwa, nan take aka nufi Gidan sarautar birnin kisra da wannan jirgin ruwan,Wannan shine abinda ya faru da jarumi Imhal bayan ya gudu daga kurkukun Darul maut an kamo shi ansake dawo da shi.
Al'amarin shugaban dakarun kurkukun Darul maut kuwa, wato sadauki Marwatu, lokacin da yaga sun dawo da jarumi Imhal kurkukun cikin nasara sai ya tafi izuwa gidan Sarki Gurzalu yana mai tsananin farin ciki.
tayi min afuwa zan cigaba idan Na huta
RIJIYA GABA DUBU 2 CIGABA 13
Da Isar sa gidan sarautar kuwa aka yi masa iso a wajen Sarki, take Sarki yayi masa izini ya shiga har cikin turakarsa inda ya iske shi tare da matarsa Muzaina a zaune acikin farin ciki da nishadi suna ciye-ciye da shaye-shaye, da isowar Marwatu kusa da kujerar da su Sarki suke zaune sai ya zube kasa kamar zai yi masa sujada ya kwashi gaisuwa sannan ya dago kai da nufin yayi bayani amma sai Sarki Gurzalu ya daga masa hannu yana mai yi masa muni da yayi shiru,Sarki Gurzalu ya mike tsaye ya tako har gaban Marwatu ya kama kafadun sa ya tashe shi tsaye sannan ya dube shi fuskarsa cike da annuri yace, ya kai Marwatu kayi sani cewa a iya tsawon aikin da kake yi mini a kurkukun Darul maut baka taba yi mini aiki mai kyau ba kamar wannan na kamo jarumi Imhal, domin inda ya samu nasarar tserewa da ya karya alkadarinmu gaba daya,kuma da ya rusa tarihin da mahaifina ya kafa akan kurkukun Darul maut, tabbas sakamakon da zai biyo bayanka shine mutuwa, to amma yanzu da ka samu nasarar kamo shi na baka kyautar dinare dubu dari biyar gami da nayi mata da maza guda dubu, sannan kuma na baka gidan gona ta na birnin Saihur, Koda Marwatu yaji wannan bushara sai ya dimauce ya sake zubewa kasa yana sumbatar kafar Sarki yana mai yin godiya, Sarki Gurzalu ya bushe da dariyar murna yace, Tashi ka tafi abinka ya kai Marwatu, domin ka kamo min zakin da idan ya balle daga daji zai iya hallakani ya kawar da dukkan zuri'ata ta yanzu, Nan take Marwatu yayi sallama da Sarki ya mike tsaye da nufin ya juya ya fita,sai matar Sarki Gurzalu ta kirawo sunansa ya waigo sannan ta dube shi tace, Ya kai Marwatu kayi sani cewa nayi maka matukar farin ciki matuka da kasa aka kai wannan babban makiyi namu dakin RIJIYA GABA DUBU na kurkukun Darul maut, lallai acigaba da yi masa azabobin cikin RIJIYA GABA DUBU har tsawon kwanaki goma sha hudun nan kafin as tafi da shi birnin misra inda Sarki zai kashe shi a gaban miliyoyin jama'a a lokacin GASAR JARUMTA, Koda Muzaina tazo nan a zancen ta sai Marwatu ya risina yace,Angama ya shugabata sannan ya juya ya fice daga cikin turakar.
zan cigaba idan na huta
RIJIYA GABA DUBU 2 CIGABA 14
Faruwar hakan ke da wuya sai ga wata tsaleliyar budurwa ta kunno kai cikin turakar, Hakika wannan budurwa ta cika dari a fagen kyau domin sau tari idan ta fito cikin gari bata wucewa tabar mutane lafiya dole sai kaga hadari na faruwa, domin Wanda ke kan jaki ko doki zai bangaje masu tafiya a kasa bai sani ba,wadanda ke dauke da kaya a Kansu zasu saki kayan su zube bash sani ba,Kai bama maza ba hatta 'yan uwanta mata idan suka yi arba da ita sai kaga sun Wangame baki suna dalalar da yawu basu sani ba,sabo da tsabar kyawunta da burgesu da take yi,Ba wata bace wannan budurwa face Gimbiya LAMIRAT 'ya guda daya JAL! a wajen Sarki Gurzalu, A duniya babu abinda Sarki Gurzalu yake so dama da Gimbiya LAMIRAT, ba don komai yake tsananin sonta ba sai saboda halayenta sun zo iri daya da NASA,wato ko kadan lamirat bata son talakawa kuma sannan bata da imani da tausayi ko kadan,Laifi kankani bawa ko baiwa za su yi mata tasa a gaba musu azaba mai tsanani ko kuma tasa a sare musu hannaye, idan ma ranta ya baci sosai da kanta zata zare takobi ta sare musu kai,Gimbiya lamirat ta gado mahaifinta Sarki Gurzalu a tsananin Mark da iya yaki sannan tana taba samun tsananta gaba akan makiyi, domin idan tasa shi a gaba sai taga bayansa, Bisa wannan dalili ne take yiwa 'ya'yan sarakai da 'ya'yan attajirai na birnin matukar kwarjini suke tsoron tunkararta da batun soyayya ko aure, Ita da Kanta Gimbiya lamirat ta dauke alkawarin baza ta auri wani namiji ba face Wanda ya fita bata,karfin damtse kuma ya cinye gasar jarumtaka ta nahiyar akan mahaifinta tunda mahaifinta shine ke rike da kambun gasar sama da shekaru ashirin ankasa samun Wanda zai karbe daga hannunsa.
Lokacin da Gimbiya LAMIRAT ta shigo cikin turakar Sarki Gurzalu ta iske shi tare da mahaifiyarta Muzainat a zaune cikin farin ciki bayan taba fitar sadauki Marwatu sai ta karasa garesu cikin tsananin murna ta fada kan kirjin Sarki Gurzalu ta rungume shi tana mai cewa, Ya kai Abbana ina mai tayaka murna da aka samu nasarar kamo wannan babban makiyin namu bayan ya gudu daga kurkukun Darul maut kayi sani cewa naso ace ka bani dama naje har Darul maut na kashe wannan makiyi namu da hannu na domin ko sunan sa bana so naji an ambata bare kuma na ganshi da idanu na".
To zan cigaba idan na huta
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 15
Koda jin wannan batu sai Sarki Gurzalu ya bushe da dariya yana mai janye jikinsa daga cikin na LAMIRAT sannan ya tsuke bakinsa ga barin yin dariyar ya dubeta cikin nutsuwa yace,yake 'yata rabin jikina ki kara hakuri daga nan zuwa ranar da zamu hadu da wannan babban makiyi namu a filin gasar JARUMTA ta misra, zaki ga yadda zanyi masa kisan gillah ta hanyar yi masa mugayen sare-sare da takobi na,lallai sai na daddatsa shi kamar yadda ake daddatsa nama a mahauta, yanzu zan sanar daku wani babban sirri Wanda baku sani ba ke da mahaifiyarki, Ku sani cewa wannan jarumi Imhal Wanda nake so nayi gasar KAMBUN JARUMTA dashi ba wani bane face Dan marigayi Sarki Imhal na kasar nan Wanda na kashe shi na hau karagar mulkin da karfin tsiya,idan ban kashe wannan yaro yanzu ba nan gaba sai ya kashe ni ya karbi karagar mulkin sa,duk naga wannan al'amari ne a cikin madubin tsafi na bisa bincike da nayi a jiya da daddare. Koda Sarki Gurzalu yazo nan a zancen sa sai hankalin Gimbiya lamirat da mahaifiyarta ya dugunzuma ainun suka rasa abinda yake musu dadi,cikin alamun tsananin damuwa lamirat tace,Ai kuwa tunda haka ne yanzun nan zan he kurkukun Darul maut na kashe jarumi Imhal da hannu na in ba haka ba ina cikin zulumi da fargaba tunda nace Ka kashe makashinka karfin ya samu damar kashe ka,Koda gama fadin haka sai Gimbiya lamirat ta mike tsaye da nufin ta fice daga cikin turakar amma sai Sarki Gurzalu yayi wuf ya ruko hannun ta yana murmushi ya dubeta yace,Haba yake 'yata ai kin sani cewa duk irin kiyayyarki da Imhal bata kai tawa ba amma sai gashi nayi hakuri ina jiran lokaci ya cika Wanda ya dace da zan kashe wannan yaro, kin sani cewa dake zanyi wannan tafiya izuwa birnin misra a gabanki zan kashe wannan yaro, abinda nake so dake shine, lallai ki danne kiyayyarki ga Imhal a yayin wannan tafiya tamu, kada ki kuskura ki sanar dashi cewa nine na kashe mahaifinsa da dukkan zuri'arsa domin idan ya gano hakan burina na kashe shi a filin gasar JARUMTA ba zai cika ba,Koda Sarki Gurzalu yazo nan a zancen sa sai zuciyar Gimbiya lamirat tayi Dan sanyi ta dube shi tace ,shikenan ya kai Abbana zan cigaba da hakuri har izuwa wannan rana amma fa ka sani cewa ba zan iya danne zuciya ta ba akan nunawa Imhal kiyayya gami da cin zarafin sa da azabtar dashi kafin mu isa birnin misra, Sarki Gurzalu yace A a bana son ki taba lafiyarsa domin ina so ya murmure kafin mu isa can din ramar dake jikin sa ta bace kuma ya samu isasshiyar lafiya don kada mutane suga cewar da nakasasshe zanyi wannan gasa, Koda jin wannan batu sai Gimbiya lamirat ta ciza yatsanta cikin tsananin takaici domin ba haka taso ba,tabbas taci buri ta kara azabtar da Imhal ainun bayan da ma ya Sha azabar RIJIYA GABA DUBU. wannan shine abinda ya faru a gidan Sarki Gurzalu kafin cikar kwanaki goma Sha hudun da za a fito da Imhal daga cikin kurkukun Darul maut.
To jama'a ayi min afuwa zan cigaba idan na dawo,jiya na dawo gida amma gobe zan sake komawa ina fatan za ayi min uzuri.
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 16
Al'amarin Jarumi Imhal kuwa bayan Angama yi masa wannan azaba ta kwanaki goma Sha hudu da kayan masifun dake cikin RIJIYA GABA DUBU an fito dashi an kai shi gidan sarautar sarki Gurzalu a matukar galabaice kuma a daddaure cikin sarka sai aka watsar da shi a cikin rana yayi ta gasuwa a cikin harabar gidan sarautar har tsawon kimanin sa'a guda sannan sarki Gurzalu tare da 'yarsa Gimbiya LAMIRAT suka fito Daga cikin gidan sarautar a cikin gagarumar shigar yaki gami da kimtsawar tafiya, tun daga nesa Gimbiya LAMIRAT ta kurawa Jarumi Imhal idanu Wanda ke kwance a kasa magashiyan ya jike sharkaf da gumi yana faman nishi kamar Wanda ransa zai fita. duka da cewar Imhal ya rame matuka amma surar jikinsa irin ta manyan sadaukai tana nan kuma babu abinda ya taba lafiyar kyakkyawar fuskarsa, koda tayi arba dashi a karon farko sai taji zuciyar ta ta buga da karfin gaske kuma ta kasa sanin dalilin haka, Yayin da sarki Gurzalu da Gimbiya lamirat suka iso akan jarumi Imhal suka tsaya sai sarki gurzalu ya sa kafarsa ya dunguri wani ciwo dake hakarkarin Imhal,Imhal yayi Dan ihu sakamakon mugun zafin da ya ji, shi kuma sarki gurzalu sai ya dube shi ya bushe da dariya yace Ya kai yaro, ka sani masu iya magana suna cewa, Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya,Yau gashi ranar yin gasar mu ta JARUMTA ta so kamar yadda na shaida maka, ko da gama fadin haka sai sarki ya kirawo wadansu hadimansa yace, Ku dauki wannan fursunan kuje kuyi masa wanka kuma a kirawo likita na yayi masa magani sannan a bashi kayan yaki yasa azo dashi bakin kafar gari inda za muyi wannan tafiya tare dashi, Koda gama fadin haka sai wadannan hadimai suka ciccibi Imhal suka tafi dashi dakaru kimanin guda dubu na kewaye da su don tabbatar da tsaro, saboda kar Imhal yayi yunkurin guduwa duk da cewar yana daure cikin sarkoki, Bayan an tafi da jarumi Imhal ne sarki gurzalu ya juyo ya dubi Gimbiya Lamirat yace, amma fa kin bani mamaki, wai shin duk ina zafin zuciyar taki ya tafi ne alhalin ga babban makiyin namu a gabanki amma ko dukan sa ba kiyi ba bare kiyi masa azaba ko wulakancin da kike furucin za kiyi masa, koda jin wannan batu sai lamirat tayi dan guntun murmushi tace,ya kai Abbana na sani cewa bana cin zalina ba ramamme ko nakasasshe, na fison na zalunci lafiyayyen mutum Wanda ko yaya na taba shi zai ji mugun ciwo amma ba ragowar mutuwa ba,Koda jin haka sai sarki gurzalu ya bushe da dariyar farin ciki yace Dakyau 'yata hakika barewa bata gudu danta yayi rarrafe, lallai yanzu na gamsu cewar kin gaje ni kuma ko a bayan raina nasan zaki iya tafiyar da mulki kamar yadda nake tafiyar da shi. to jama'a idan na huta zan cigaba.
RIJIYA GABA DUBU 2 CIGABA 17
Koda gama fadin hakan sai sarki ya kama hannun Gimbiya lamirat ya na ta suka tafi izuwa can kofar gidan sarautar inda aka ajiye keken dokin da za su hau don tafiya birnin Misra kuma ga dakaru masu yawan gaske sun kewaye keken dokin gaba da baya, kuibi-kuibi, wadanda zasu yi musu rakiya, kamar yadda sarki gurzalu ya bayar da umarni haka akayi, wato sai da aka yiwa Imhal wanka aka sa masa magani a jikin raunikansa sannan aka kawo abinci mai rai da lafiya aka bashi yaci yasha ya koshi,daga nan kuma aka sanya masa kayan yaki a jikinsa, amma maimakon a dama masa makami sai aka sake zuba masa sarkoki aka daure shi aka kawo shi cikin tawagar sarki da zata tafi birnin misra, nan take aka sanya Imhal acikin wani akurki Wanda dawakai ke Jansa aka kulleshi a ciki, sannan aka dunguma gaba daya aka fice daga cikin birnin gaba daya.
Tsakanin birnin kisra da misra tafiya ce ta sa'a bakwai don haka fun safe aka fara wannan tafiya ba a iso birnin kisra ba sai da rana ta take, kai tsaye tawagar sarki gurzalu ta nufi gidan sarautar sarki Taiyara don haka sai ya shirya ya fito ya tare su cikin tsananin murna, nan take aka shigar da Gimbiya lamirat da mahaifiyarta izuwa inda iyalan sarki Taiyara suke, shi kuwa jarumi Imhal sai aka kai shi cikin wani daki mai kama da kurkuku aka kulleshi, Sarki gurzalu da sarki Taiyara kuwa sai suka shige izuwa turakar sarki Taiyara inda suka zauna aka kawo musu abinci da aka Sha har da giya suka ci suka Sha suka yi tatul suna ta kyalkyala dariya, daga can sai sarki Taiyara ya numfasa ya dubi sarki gurzalu yace, Ya kai tsohon abokina jarumin jarumai na wannan nahiyar, wai shin bana da wanne guzuri kazo mana da shi ne?ka sani cewa duk shekara Kaine kake lashe gasar nan don haka babu sabon wani al'amari Wanda zai sa mu samu kudade masu yawa tunda kowa ya San cewa kaine zakaran gasar, yayin da sarki taryan yazo nan a zancen sa sai sarki gurzalu ya bushe da dariya sannan yace, Kwantar da hankalin ka ya kai abokina kayi sani cewar nazo mana da wani gwarzon jarumi wanda zai burge yan kallo kuma nine kadai zan iya gamawa da shi, kafin na kara dashi zan bashi dama yayi wasa kamar sau shida, ina mai tabbatar maka da cewar a ranar da yayi wasan farko labarinsa zai bazu a ko ina, kuma kashegarin da zai sake wasa sai filin gasar ya cika ya batse da yan kallo don haka kafin ranar da zamu kafsa ni da shi ba kananan kudin shiga zamu samu ba.
to zan cigaba idan na huta
RIJIYA GABA DUBU 2 CIGABA 18
Wannan karon har dukkanin sarakunan da ke nahiyar nan sai sun zo sun kalli wasan karshe, domin suga yadda zata kaya, Yau baza ayi wasa ko guda daya ba sai gobe saboda ina son jarumin nawa ya huta sosai ya samu karfin jikinsa, Koda sarki gurzalu yazo nan a zancen sa sai sarki taryan ya bushe da dariya sannan yace, Ya kai abokina nifa duk wannan labarin da na bani naji sane kamar tatsuniya, duk da cewar banga wannan jarumi ba da kazo dashi nasan nawa jarumin sadauki Darwaz ya fishi komai da komai, don haka a goben da safe ina son Darwaz da jarumin naka su kara.Koda jin wannan batu sai sarki gurzalu ya sake bushewa da dariya yace Ai shikenan, dama masu salon magana sun ce sai an gwada akan San na kwarai.
Sarki Taryan yana da 'ya' guda daya wata kyakkyawar budurwa ta kwatance mai suna Shumaira, Shumaira da Lamirat sun kasance kawayen juna tun suna yara kanana saboda abotar dake tsananin iyayensu, don haka suma sun shaku ainun, Wani abin mamaki shine, ko kadan ra'ayinsu baizo daya ba,domin ita Gimbiya Shumaira tana da tsananin tausayi, sabanin lamirat wadda ta kasance Mara imani ga zalunci, hakan bata sa sun kasa shakuwa da kaunar juna ba,amma suna yawan samun sabani domin ako yaushe Shumaira tana matsawa lamirat akan ta daina zaluntar talakawa da masu rauni, wani lokacin ma idan suka samu sabani, sai su kwana uku basa magana da juna,kuma su daina kwana a waje daya da con abinci tare.
Gimbiya Shumaira na zaune a cikin turakar ta sai ga Gimbiya lamirat ta shigo, Koda ta dago kai suka yi arba da juna sai Shumaira ta Mike zumbur! ta ruga gareta cikin tsananin farin ciki suka rungume juna,Shumaira ta janye jikinta daga cikin nata suka fuskanci juna sannan tace,Ai tun jiya nake zuba ido naga kun iso amma sai naji shiru tunda dai shekara ta zagayo, Lamirat tayi murmushi tace Ai mun kara kwana daya ne akan lokacin da muka saba tasowa, saboda wannan karon mun taho da wani gagarumin jarumi, wanda za a samu kudade da yawa a dalilin sa,Koda jin wannan batu sai mamaki ya Kama Gimbiya Shumaira tace, Haba ya ke kawata yanzu Ashe har za a iya samun wani jarumi wanda zai burge mutane a wannan nahiyar tamu sama da mahaifina ki?Lamirat tayi murmushi tace,Ai bana nufin yafi mahaifina JARUMTA, amma dai zai taka muhimmiyar rawa a wannan gasa da za ayi ta bana,kuma ina tabbatar miki da cewar inba mahaifin nawa ba babu wanda zai iya kaishi kasa a wannan gasa, Shumaira ta girgiza kai tace Yake kawata kin sani cewa ban taba zuwa kallon wannan gasa ba saboda ko kadan bana son naga jini yana zuba, bana son naga ana kashe mutane a aikin banza, amma wannan karon naji zuciyata tana son taga wannan bakon jarumi wanda kika zo mini da labarin sa don haka indai zai yi wasa gobe zan fita filin gasar na kalle shi don kawai naga iyakar jarumtakar tasa da kike kodawa, Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube Gimbiya lamirat saboda ta dade tana son ta dinga Jan Shumaira suna fita kallon wannan gasa tare amma taki tsawon shekara da shekaru, Tabbas lamirat tayi mamaki da taji Yau dare daya Shumaira ta amince zata fita kallon wannan gasa.
to jama'a sai na huta zan Dora
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 19
A daren wannan rana kuwa aka yi ta shela birni da kauye cewar sarki gurzalu yazo da wani sabon gwarzon jarumi kuma ansa cacar kudi akan sa cewar duk jarumin da ya kai shi kasa za a bashi dinare miliyan daya,kuma sannan zai yi wasan farko a gobe da safe tare da sadauki Darwaz na birnin misra, Koda wannan labari ya bazu sai gari ya rude da kace nace ana mamaki, attajirai kuwa suka yi ta shirya cacar kudi a tsananin su kowa na zabar gwaninsa a tsananin jarumi Imhal da sadauki Darwaz, Jama'ar gari kuwa mata da maza yara da manya kowa ya dinga dokin gari ya waye yaje ya biya kudin shiga filin gasa domin ya ga irin gumurzun da za ayi tsananin wadannan manyan jarumai.
Kai! tun kafin ma gari ya waye filin gasar ya cika makil ya zamana cewar har akan katanga mutane ne a zaune, duk inda mutum ya duba baya ganin komai sai kawunan bil'adama, babu wani guri da yayi saura sai na sarakuna da manyan attajirai, sune kadai basu iso ba,sai kuma jaruman da za suyi gasar, wato jarumi Imhal da sadauki Darwaz.
Sadauki Darwaz wani narkeken katon mutum ne mai girman gaske wato mai kirar mutanen farko, Darwaz ya kasance shahararren gwarzon mayaki mai tarwatsa maza a filin daga,A ranar da suka fara yin gasar kambun JARUMTA shi da sarki gurzalu, dakyar shi sarki gurzalu ya samu nasarar kaishi kasa,don har sai da ya yanki sarki gurzalu sau biyu bayan sun shafe sa a daya da rabi suna bakin yamutsi, daga wannan lokaci basu sake haduwa ba kawo I yanzu, kuma har gobe ta ciki na ciki, domin kowannensu yayi matukar bakin ciki bisa yadda gumurzun nasu ya kasance saboda sun Sha bakar wuya sun zubar da jini, wannan karon da sadauki Darwaz yaji cewar jarumin da zai kafsa dashi, sarki gurzalu ne yazo dashi sai yaci mugun burin daukar fansa a kansa ya kudurce a ransa cewar a gaban sarki gurzalu zai yiwa jarumin kisan gillah.
Sai da gari yayi haske sosai sannan jama'a suka ji anfara buga tambura ana busa algaita da sarewa alamar cewa sarakuna zasu fito daga cikin gidan sarautar, nan take gaba daya jama'ar dake filin gasar suka mimmike tsaye don girmamawa, Fadawan sarki taryan da manyan attajiran kasar suka fara shigowa cikin filin gasar, sannan sai ga sarki taryan, sarki gurzalu, Gimbiya lamirat da gimbiya Shumaira sun shigo,dakaru da kuyangi na take musu baya har suka iso wajen da aka tanadar musu mai dauke da kujeru na alfarma,Koda jama'ar gari suka ga Gimbiya Shumaira ta fito kallon wannan gasa sai suka cika da matukar mamaki, nan dai su sarki taryan da su Shumaira suka isa mazauninsu suka zazzauna.
Al'amarin jarumi Imhal kuwa, tun a jiya bayan anyi masa wanka, ansa masa magani ajikin raunikan jikinsa, kuma an bashi abinci na alfarma ya cika cikin sa sai ya nutsu sosai ya dawo cikin hayyacinsa inda ya fada cikin kogin tunanin abubuwan da suka faru a baya.
to jama'a zan cigaba idan na huta.
RIJIYA GABA DUBU2 CIGABA 20
Babu abinda ya fara fado masa a rai face irin tsananin azabar da aka gana masa a bakin RIJIYA GABA DUBU ta tsawon kwana goma Sha hudu, A tsawon kwanakin azabar gobe tafi ta jiya, haka akai ta azabtar dashi babu sassauci, azabar farko itace wadda kunamun nan suka fito suka yi ta cizon sa,kashegari kuwa macizai ne suka fito suka yi ta saran sa,haka abin ya cigaba da wakana, wata ran ya ga dodanni suyi ta dukansa suna tamola dashi. Koda jarumi Imhal ya gama tuno wannan masifaffiyar wahala da ya Sha acikin RIJIYA GABA DUBU wacce ke cikin kurkukun darul maut, sai ya takarkare ya kwarara uban ihu,Ihun nasa ya cika gidan sarautar gaba daya, har sai da dakaru masu yawa suka rugo izuwa kofar dakin da yake,Koda suka leka suka gan shi a kwance a kasa kuma a daure ga kofar dakin a kulle sai hankalin su ya kwanta, sabo da dama can an gargade su matuka akan cewar kada su kuskura su bari ya tsere, idan kuwa ya gudu a bakacin ransu su duka.
Gama tunani ke da wuya sai ya kamu da tsananin bakin ciki ya fashe da matsanancin kuka, A karshe ya kudiri aniyar cewa komai rintsi da tsanani sai ya jure duk irin bala in dake gaban sa domin ya tsira da rayuwarsa, ya koma gidan kurkukun darul maut ya ruguje shi kuma ya kone wannan RIJIYA ta gaba dubu domin a daina azabtar da al umma,Bayan nan kuma yayi alkawarin cewar sai ya koma gidan Likiciya Zumaira domin ya dauke tsoho imzanu su gudu izuwa wata nahiyar daban inda da sannu zai cigaba da bincike domin ya gano asalin iyayensa da danginsa, haka dai Imhal yayi ta sakar zuci har dare ya raba bai sani ba sannan bacci ya kawo masa mamayar ba zato,
Kashe gari kuwa da safe aka sake kawo masa abinci da abin Sha mai rai da lafiya ya kimtsa cikin sa,sai bayan ya huta sosai sannan aka zo aka bude dakin aka fito dashi a daure cikin sarkoki, aka nufi filin gasar JARUMTA dashi.
koda aka iso filin gasar da jarumi Imhal a daddaure cikin sarka, da jama'a suka yi arba dashi sai filin gaba daya ya rude da shewa gami da tafi.
zan cigaba
RIJIYA GABA DUBU 2 CIGABA 21
Gimbiya lamirat da Shumaira na hango shi sai su duka suka mike tsaye, suka kura masa idanu domin a wannan rana kyawunsa da siffar jarumtakarsa sun bayyana a fili muraran,ita dai Gimbiya Shumaira nan take taji ta kamu da tsananin kaunar sa,bata ma San sanda ta kama yin murmushi ba a gareshi, ita kuwa Gimbiya lamirat sai kawai taji zuciyar ta taci gaba da bugawa da karfi, bugawar da bata San dalilin ta ba,shin kiyayya ce ko soyayya ta janyo hakan? amsar da ta kasa baiwa Kanta kenan.
Koda aka kawo jarumi Imhal tsakiyar filin gasar wanda sama da dakaru dubu dari ne suka kewaye shi rike da makamai don tabbatar da tsaro harma da wadanda suka dana kibiyoyi akan baka, kawai jira suke suga wani yayi ba dai dai ba yasha ruwan kibbau, aka kwancewa jarumi Imhal dukkanin sarkokin da ke jikinsa sannan aka bashi takobi da garkuwa ya rike, nan fa Imhal ya fara waige-waige da dube-dube domin ya ga abokin gwaninsa, amma bai ga kowa ba,Alokacin ne sarki taryan ya bushe da dariyar mugunta ya dubi sarki gurzalu yace,Yanzu wannan Dan jarumin ne lake tunanin zai iya karawa da gwarzo na abin alfahari na?Sarki gurzalu yace,Ai a inda babu kasa nan ake gardamar kokawa, ina naka jarumin ya fito su kara mu gani,Koda jin haka sai sarki taryan ya daga kai ya dubi wani barde,take barden ya daga wata katuwar gudumar danko ya daki wani katon bandiri, karar bandirin ta cika birnin gaba daya da amsa kuwwa, Faruwar hakan ke da wuya aka bude wata katuwar kofa, sai ga sadauki Darwaz ya fito cikin shigar yaki rike da takobi da garkuwa, Tunda Imhal yazo duniya bai taba ganin mutum mai tsananin tsawo, kauri, da murdewar jiki ba irin ta sadauki Darwaz, nan take zuciyar Imhal ta karaya ya fara tunanin cewa, ai bazai iya ba da wannan katon domin da sadauki Darwaz ya karaso ya tsaya daf da shi sai ya zama Dan mitsitsi akansa kamar an ajiye dantsako a gaban shirwa, tun kafin a bayar da umarnin a fara gasar sai Darwaz yasa hannu daya ya make Imhal, saboda karfin dukan sai da Imhal ya yi tsalle sama yaje ya gwaru da karfen da aka kewaye filin gasar ya fado kasa Tim!yana aman jini,Koda Faruwar hakan sai filin gasar ya rude da shewar jama'a, Attajiran da suka shiga cacar kudi da sadauki Darwaz suka kama murna suna ihu da tsalle domin suna ganin cewar lallai jarumin sune zai lashe gasar su kwashi tsabar kudi, shima sarki taryan sai ya kama kyalkyala dariyar mugunta, ita kuwa Gimbiya Shumaira sai hankalin ta ya dugunzuma ta rude ainun ta kamu da tsananin tausayin Imhal, har kwalla ta cika mata idanu.
Ba zato ba tsammani sai aka ga jarumi Imhal ya mike tsaye zumbur! ya ruga da gudu izuwa kan sadauki Darwaz sun ruguntsume da azababben yaki suna masu kaiwa junan su SARA DA SUKA cikin tsananin zafin nama da juriya da bajinta ta ban al'ajabi.
WAYE ZAI SAMU NASARAR WANNAN GASA TSAKANIN JARUMI IMHAL DA SADAUKI DARWAZ? SHIN SARKI GURZALU ZAI SAMU NASARAR KASHE JARUMI IMHAL YA LASHE GASAR KAMBUN JARUMTA? SHIN IMHAL ZAI CIKA BURINSA NA RUGUJE KURKUKUN DARUL MAUT DA KONE RIJIYA GABA DUBU?YAUSHE NE IMHAL ZAI KOMA BIRNIN MISRA YA SAKE SADUWA DA TSOHO IMZANU KUMA YA SAN 'YAR UWAR MAHAIFIYARSA LIKICIYA MUZAIRA? Mu hadu a littafin RIJIYA GABA DUBU 3 don jin cigaban wannan kasaitaccen labari.
to jama'a zan Dan huta kafin Ku jini a cikin na uku