Trending Hausa Novels

Tame Gari Littafi Na Daya Complete Hausa Novels

Reading file: Tame Gari Complete.txt

Chapter 2 of 5

part din sajida zaune suka sameta sanye cikin riga da wando three quater sai wata 'yar mitsitsiyar riga wadda da kadan ta rufe cibiyarta kanta yasha qananan kitso jikin nan sai kamshi ke tashi sajida bata da kyau kwarai amma akwai wanka domin irin matan nan ne masu son komai suga sune a farko shiyasa komai nata yake kan gaba ko cikin friends dinta

da fara'arta ta tarbesu amma ta rasa dalili tun ranar da ta tambayi habeeb meye alaqar su da dije ya fada mata da ganinta da tayi gurin dinner taji sam bata ra'ayinta ko da ta ganta yanzu gabanta saida ya fadi amma sbd halinta na 'yan duniya kuma goggiyar 'yan boko yasata sakin fuska nan ta karbi dije hannu bibbiyu abinci me rai da motsi takawowa dije inda ta bude ciki taci t koshi dan dama yunwa takeji tunda dawowarta kenan daga skull mami ta tunkudota nan ba laifi amaryar habeeb ta iya girki amma dai gaskiya basu dace ba cewar dije dan wannan ai kusan sa'arsa ce

sun dan taba hira kafin suka tashi suka koma part din yusrah inda suna shiga yusra ta shige ciki tace ma dije tana zuwa miqewa tayi itama ta shiga toilet din dake parlour ta dauro alwala tazo tayi sallar la'asar

bayan ta idar ne ta koma kan kujera ta kama kallon wani film da ake haskawa a bollywood film din yatafi da hankalinta hakan yasa sam bataji tsayuwar mota a gidan ba illa jin sallamarshi kawai da taji yayi

amsawa tayi ga mamakinta shima din cikin sakin fuska ya shiga fadin ah ah mutanen kauye yaushe aka dawo?

kallon mamaki tayi masa tare da fadin shekaran jiya

to an dawo lfy?

lfy qalau suna gaisheku

hmmm muna amsawa

ok bari na shiga ciki in dan watsa ruwa

shiru tayu bata bashi amsa ba a ranta tace kinga dije anya kuwa bazaki tashi ki gudu ba ba mamaki mutanen nan shirya yankaki suka yi dan kin san dai ko giyar wake kika sha bamai yimiki dariya irin wannan amma da ganin yadda suka miki kin san da mugunta a zuciyarsu dan haka tunda qafafunki ki tashi ki fece kafin a karya miki su miqewa tayi ta nufi qofa harta daga labulen ta tsinkayi muryar yusra na fadin ina kuma zaki?

am dama zan tafi ne tunda ya dawo

cikin hade rai tace mamy bata fada miki cewar sai kinyi kwana biyu zaki koma ba

zaro ido tayi tare da fadin kwana biyu fa a nan gidan?

eh ko bazaki zauna ba?

to amma ai ban taho da kaya ba kuma ma skull dina fa?

iyeeeh lallai yarinya wato skull dinki da yaushe kika fara bokon yau she ma ministry tasan da zamanki shine zaki fadamun makaranta to bari ma kiji da ke kin dauka abinda kikamin kisha a banza wlh duk duniya bawanda ya isa ya hana inci ubanki ba duka ba zagi amma zaman prison zakiyi a gidan nan na tsawon kwana biyu cikin awa biyu kika barar min da burin danaci a bikina toh ke cikin kwana biyu sai duk wanda ya ganki ya tausaya miki dan haka kada ki kuskura ki fita a gidan nan dan dama an sanar da me gadi kada yabari ki fita

kirjin dije fa ya shiga lugude inda takeji kamar ta arta bata san tanadin da sukai mata ba tasan ma makaman yakin su sunfi nata dan haka ta yunkura da niyyar artawa taji ya riketa haba classic lady ina zaki kuma ai kinzo gida kuma sai jibi ya fada tare da hade rai mutsu mutsun kwacewa takeyi inda ya riqe hannun da karfi riqo bana wasa ba hakan yasata sakin qara don jinda tayi yana barazanar ballata wurgi yayi da ita gefen kujera inda saida kanta ya dan bugu kafin ya dauketa da wani wawan marin dayasa ta ganin star wata qarar ta saki yayi saurin aza hannunshi a saman bakin shi alamar tayi mishi shuru

kasa shirun tayi inda nan ya shiga fyadarta yusra na gefe tana dariyar mugunta saida ya gama canzawa dije hallitar fata abinka da fari duk jikin sai yayi ja yayi rudu rudu kafin ya kyaleta ya zauna yana maida numfashi

cikin daurewar fuska yace dan uwarki ubanwa yasa kiyi min abinda kikaimin

shiru tayi in banda shasshekekar kuka ba abinda takeyi da alama dije akwai zuciya

yusar ce ta taso cikin daga murya dan uwarki ba magana akeyi miki ba ta karasa maganar cikin daka tsawa

uwarki ce😠

sukaji ta ce 🙊

cikin zaro ido kusan a tare suka fadi

me kikace

cikin jan kuka da majina tace cewa nayu uwarki ce kuma wlh tunda kuka taba mana godiyarmu duk sai kunci ubanku

kallon kallo aka shiga yi shi naseer yana nazari da tunanin rainin hankalin yarinya itako yusra ta tuna da yadda suka kwashe kwanakin baya amma kuma kai ai da gani wannan ba irin wadan can bace dan haka a hasale tayo kan dije da niyyar dukanta wata irin zabura dije tayi kayo cikin yusra ganin da yusra tayi dije tayo kanta yasata sakin ihu tayi bayan naseer

ke ni zaki yiwa iskanci cewar naseer wlh zan babbala ki

itako dije ko'a jikknta ta nufosu tana qara barw baki miqa hannu yayi da niyyar riqota aikuwa tayi caraf da hannun a bakinta ta dankara masa cizo kuma gam ta rike hannun qara ya saki wadda tasa yusra saurin barin gurin ta ruga da gudu tayi bayan kujera duk yadda yaso ta saki hannun ki tayi saida taga jini yana bin yatsansa besan sadda yakai mata mangari ba aikuwa zafin da taji ne yasata tashi ta dane bayansa ta shiga yakushinsa tako ina baji ba gani cizo duk ta dabaibayeshi ga azabar da hannunsa keyi ga jini nabin yatsan dan ta dauke mai fatar koma cinyewa tayi oho waya sani

duk yadda yaso yaraba dije da jikknsa abu ya faskara gashj tana kuka tana yakushinsa duk ta damalmale masa jiki ta hada masa jini da majina cikkn daga murya ya kira sunan yusra sakamakon wani dankareren cizon da dije ta mallara masa a kunne hakan yasa shi finci kota da iya qarfinsa ta fada kan kujerar da yusra ta labe a bayanta riqe da waya jikinta na makyarkyata tana son yin kira takasa nemo number ma ido biyu sukayi da dije aikuwa ta kwalla wata qara wadda duk gidan ya amsa kanta dije tayi ta cakumeta aikuwa yusra memakon ta tabuka wani abun sai kawai ta bude baki ta shiga kurma ihu nan ko dije ta fara caskala ta itama harda rabon nata cizon a kumatu

ganin tana shirin kashe masa mata yayo kanta ai kafin ya qaraso ta saki dije ta qara nufarsa ba shiri shima ya juya dan ko kadan bazai so ta qara dane shi ba yarinya kamar mayya sai shan jini takeyi

habeeb na zaune a parlour shida sajida suka tsinkayi ihun yusrah da sauri suka taso suka nufo part din suna zuwa suka shiga kokarin budewa dan lokacin da naseer ya kamo dije da niyyar duka yusrah ce harda rufe kofa dan haka suka shiga bugawa yana fadin nasir nasir lfy bude mana

yusra ce ta nufi kofar danta bude dije tasha gabanta tanata kada kai tana bude baki naseer ko nacan yasa tissue yanata qoqarin goge jinin dake bin hannunsa da bayan kunnansa fuskarsa kuwa tuni duk ta hade tayi burdin burdin dan tasha yakushi

da dabara yasamu ya qaraso ya bude kofar

ya salam meya faru haka naganku a wannan yanayin ?

kafin yabada amsa yaji kukan dije daga cikin parlourn

leqawa yayi aikuwa ya ganta ta fara jifa da duk abinda ke falon tanayi tana kuka

tambayar nasir yayi meke faruwa nan ya sanar masa dalili

gurin dije ya nufa inda take kokarin jefo da wani fishers dishuis ya riqeta gam tare da hadata da jikinsa ya rungume ta tsam ya shiga yi mata addu'o'i a kunne

dije na jinsa tayi luf tare da qara gyara kwanciyar kanta a kirjinsa dukansu sai suka tsinci kansu cikin yanayi me wuyar fassarawa dije kam sai sauke ajiyar zuciya takeyi tare da qara shakar daddadan kamshi turaren dake jikinshi har take taji wani bacci na shirin kwasheta

jin shirun da sukayi ne yasa naseer leqowa dan duk su yusra da sajida gayyar tsorone hakan yasa suka kame a waje

yanayin daya gansu ciki duba da yadda yaga habeeb ya wani rufe ido bakinsa saitin kunnen dije gashi kuma ita ta wani lafe a jikinshi

duk radadin da ilahirin jikinshi keyi mishi sai yaji ya dena ji yayin da yaji zuciyarsa tayi masa wani irin zafi dan me zai rungumeta haka to me hakan ke nufi

jin shirun da matan sukayi ne yasa su dan shirin leqowa dan da alama abun ya lafa tunda sunji shiru aikuwa suna leqowa idon su yasauka akan abinda naseer ya kurewa gani

daram dammmmmm gaban sajida yayi dubs da yadda taga mijinta rungume da wata mace bata san lokacin datayi kansu ba tana zuwa tajanye dije daga jikinsa dije najin an jata tayi saurin qara langabewa ta zube a gurin

shi kuwa bude idonsa yayi a hankali ai kuwa ya saukesu cikin na sajida data kafeshi da ido ckin tuhuma waigawa yayi ya kalli inda dije ta sheme kafin ya maida dubansa ga naseer yace sai ku maidata gida tunda kun rama

yana gama fadar haka ya juya ya fice a dole sajida ta bishi itama............

*vote*
*comment*
*with 08066364077*

*Alqalamin khady*✍
[16/12, 11:41] ‪+234 806 493 3819‬: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀

TA ME GARI

1⃣5⃣

team dijeee kuna qarawa wutar nan fetur sai dai fa kuma hmmm a dai yi shuru yanzu muci gaba da gashi

ga masu tambayar littafin daga farko masu kirana da masu yimin mgn ta pc pls ku taimaka ku dinga tambaya a group dina in baki ciki kiyi min magana zan tura link kiyi join nasan mutan gidana akwai karrama bako da kin tambaya zasu hau tururuwar tura miki dan akwai su da karamci 👍

ina mugu mugun ji daku member's na khadeeja fans novels😘

******

ita kam yusra ko ta kan dije dake kwance bata qara biba ta lallaba ta shige daki shima naseer din binta yayi inda ba shiri dole ya dauki emergency care box suka nufi part din habeeb yayi musu dressing kafin suka dawo ind take kwance har yanzu tana nan yadda suka barta itako dije bacci ne ma yadauketa a gurin sai sauke ajiyar zuciya takeyi cikin baccin

koda suka shigo suka risketa a hakan naseer ya kalli yusra yace ke jeki tasheta ta tafi gida

wani kallo tayi masa kafin tace kai ka tasheta mana

ah ah naga dai ai ke yafi cancanta daki tasheta tunda ke kika sa aka kawo miki ita

hmm lallai to ai sai kayi duba cikin ni dakai wayafi wani shan jiki kaga kenan wanda yafi wahala shine yafi matsuwa da a barshi ya huta ni zaka danawa tarko inje in tabata tayimin yadda ta yi maka ka ganka kuwa?ta fada tare da sakin dariya

kulewa naseer yayi kafin yace ban ganni ba amma na ganki ki duba gefen bakinki da kuma kumatunki ga dankwalelen cycle nan an zana miki na musamman dan haka ki wuce kije ki tasheta ta bar gidan nan ina zaman zamana ke da mamy kunja an rudamin jiki yanzu ta ina zan doshi zuba ruwa duk yarinya tabi ta yage mutane sai kace kura nk ina zargin ma a garin nan akwai damusoshi alamu sun nuna cikinsu ta girma ga kuma 'ya'yan aljanu nidai wannan yarinyar ba qaramar jaraba baba malam ya jefo mana ba

kaga ni wlh duk ba wannan ba yanzu dai ka samo min maganin da zansha wlh ji nakeyi fuskata duk ta daure

hararar ta yayi kafin yace toh duk azabar da kk ji bata kai ya wadda nake ji ba

suna tsaka da maganar dije tayi juyi tare da yin miqa alamar zata tashi

da gudu suka kwasa suna rige rigen shiga daki wajen shiga dakin ma yusra ta riga shiga inda tana shiga dai dai naseer ya kawo kai danya kutsa ai kuwa ji kk yi bamm tare da wani sauti qummmm goshinsa ya daki qofar ko zafin daya ji baibi ta kai ba ya danna qofar ya qarasa sa key din kafin ya jingina bayansa da kofar suka shiga maida numfashi kamar wadanda suka yi gudu ko wani aikin wahala

jin goshinsa yayi kololo ne yasashi sa hannu ya taba yaji zafi kuwa kallon yusra yayi dake zaune gefen gado tana mayar da numfashi kafin yace kinga maza ki kira mamy ta turo a kwashi yarinyar nan

da sauri ko ta dauki wayarsa ta shiga kiran layin mamy

tana dagawa yusra tace yauwa mamy pls ki turo a dauki yarinyar nsn pls

jin hakan da mamy tayi yasata fadin baku kuka ce a barta tayi kwana biyu ba meye kuma na cewa ta dawo yau ko har kun gama huce fushin naku ne?

ai gara kawai ta tafi din inba haka ba...fizge wayar naseer yayi tare da fadin hello mamy

au kana kusa ashe ya akayi ne naji kunce a turo a dauketa yau ince ko kaci ubanta dai ko

yasan halin mamy inya fada mata abinda ya faru zata iya sasu daukar wani matakin shi kuma a nashi tunanin ya lura duk lokacin da ya yima yarinyar wani abu toh sai yaga shi yafi cutuwa qara maimaita tambayar tayi hakan ya katse mishi tunanin dayake yi ko baka jina?

tun yaushe ma ai ba qaramar lallasata nayi ba i hp dai daddy ma baya nan dan ban son ya ganta a wannan yanayin gashi kuma yusra kinsan ta da rigima tace lallai saita koma yau dan wai kada inyi kisan kai ganin yadda na lugwiguita mata jiki

ah to indai haka ne gara ta dawo din dan daddy'n ku yana nan kada kuma ya ganta yace meya sameta ta fada mishi gaskiya kasan shi fa akan yarinyar nan kamar wanda aka sihirce dan haka inaga kawai ku barta ta qara kwana kafin nan ta dan murmure sai ta dawo bayan ya tafi ni kuma in barje nawa haushin

no mamy ai duk hukuncin daya kamata ayi mata zan gama yi mata kedai barni da ita kawai amma dai ki turo a dauketa din kawai

tunda kun matsa dai to ka kawota mana kaga ma saika san abinda zaka fadima daddy'n naku ka fadi wani laifin tayi ka hukuntata

nikam yadda nake din nan ina zan iya fita ki ganni ya fada a zuciyarsa

ya naji kayi shuru

naga ne zaiyi wuya in samu lokaci dan inada meeting karfe 8 din nan na dare gashi zai daukemu lokaci kuma kinga ni inama zan sami time har inkawo ta kawai dai ki turo din inya so kisan me zaki fadawa daddy inya ganta ko kuma kawai ma ki hana haduwar ta so

ok to hakan yayi bani yusra

mika mata wayar yayi suka qara magana ta kashe wayar

******

shi kuwa habeeb ba qaramin fama yasha ba kafin sajida ta fahimceshi saida yasha aikin rarrashi tare da fada mata kalaman da suka kwantar mata da hankali kafin suka koma normal

****

ita ko dije koda ta farka ganin wai hartayi baccin gaske daga na qarya ganin yadda suka kwasa da gudu dazun duk tana kallonsu jin duk jikinta na ciwo ga kuma fatarta data tashi inda naseer ya daketa tunawa da abinda tayi musu kuma yasata sakin dariya tare da fadi a fili ta furta wlh tunda kuka yimin haka sau kun sani wato ni kuka kawo ga jaka kuyita dimata har kwana biyu hhhhhh bakusan dije bane na gwada muku kalata ta fuskar rahma kunki fahimta yanzu aka fara game din let's see who's d winner between us dakin dake pacing dinta ta nufa koda ta shiga hakan ya nuna mata bedroom din yusra ne dan haka kanta tsaye ta nufi toilet din dakin heater ta kunna har ruwan yayi dumi kafin ta fara yin wanka tanayi tana wash tare da matsar kwalla tana kuma ayyana irin fansar da zata dauka akan su

niko nace dije banda kuma kisan kai 🤣

ta jima sosai kafin ta gama ta dauro alwala tana fitowa ta bude wardrope ta shiga neman kaya sai kace dakinta tasan duk kayan yusra sun mata yawa duk da ba wai sosai ba dan haka ta shiga neman ko doguwar riga ce cikin sa'a ta samu kasancewar rigar nada madauri saitayi mata dai dai bayan tayi sallah ta fito farlon inda ta hango mutan gidan nata zuro kai ta qofa suna leqe

duk tana lura dasu ta share su ta zo parlour ta zauna tare da dora kafa daya kan daya ta shiga tunanin meya kamata tayi musu ne ma

ba ta jima ba ta tsinkayi bugub qofar falon tare da sallama kwarai ta dau murya ta baba habu driver ce amsawa tayi tare da fadin ana zuwa

su kuwa mutan gidan sunaji aka fara takaddama nasir yace yusra ta fita ita tace shi ya fita kowa yaqi fitowa cikin hasala yace wlh dai kinji kunya wai wannan 'yar mitsitsiyar yarinyar tasa ki kasa fita dan tsoro

mun dai ji kunya ni da kai idan kai ka kirani babba akanta amma akanmu fa nida ita ai kaine kai kuma yakamata ka fita ka sallameta tunda kaine me gidan ni kam bazan je ba dan ko yanzu ban gama jin zafin ciwon jikina ba haka kawai yarinya ta zo ta qaramin wani ciwon kana gani ma dan raini harda samin kaya ni inka fita ma kaja mata kunne ta ciremin kaya wlh ko inzo inci mata uwa

bude qofar gayi tare da fadin zo ki je da kanki ki fada mata zuwa da kai ai yafi sako maza zo ya fada yana me nuna mata hanya

wlh ba inda zani dan ba sunana saratu ba zan iya zuciya in shake yarinya har saita mutu kaga ko maganin kada ayi kar a fara wuce ka sallameta tabar min gida

yaso ya qara magana amma ya qyale yasan halin yusra akwai rai ni gara ya koma mata nasir din kada taga damar sa

cikin hade rai ya fito tare da nufo inda dije ke zaune

ko kallonta beyi ba ya wuceta ya nufi qofar falon bayan ya bude suka gaisa da baba habu kafin yace bari ya kira dijen ta fito su tafi

yana shirin shiga sukayi kacibis da ita

ke maza inda abinda zaki dauka dauko ki wuce gida

to tace tare da rabashi ta wuce

a ranshi yace wannan duk wanda ya aureki ya aurarwa kansa masifa da kudinsa

bakin mota ta nufa shi kuma yana ganin haka ya koma ciki

tana qarasawa bakin motar ta dubi baba habu tace

baba dan Allah inda hali aromin wayarka in kira daddy

mika mata yayi yana washe baki bayan ya matso number Alhajin

flashing tayi inda daddy na zaune yana cin abinci yaga shigowar kiran habu driver kuma yasan ya tafi dauko khadija hajiya ta fada masa dan haka yssan ba mamaki akwai magana shiyasa ya yi dialling number

muryar dije yaji dan haka cikin sauri yace lfy diyata?

lfy qalau daddy dama naga baba ne yazo daukata kuma ni gaskiya daman um....dama...kinga fadi kawai kanki tsaye khadija me kk bukata

dama cewa zanyi munyi magana ne da Aunty yusra da ita matar yaya habeeb shine suka ce in dawo nan da zama toh shine nace su fada maka wai bazasu iya ba shine nace ni bari na fada maka

dadi daddy yaji dan haka cikin sakin fuska yace kaji su to ai wannan ba matsala bane duk dayane ai naji dadi kwarai

to nagode daddy gobe abawa baba habu yakawomin unifoam dina zan wuce school in mun taso sai in biyo in dauki kayana

toh badamuwa Allah yayi muku albarka

ameen daddy ta kashe wayar tare da miqawa baba habu tace ya tafi kawai

ita ko ta juya ta koma cikin gidan

tana shiga falon ta tarar da su zaune jin bude kofar suka jiyo suna ganin dije kusan a tare suka furta lfy?me kika dawo yi kuma

bata tamka musu ba saita fara kokarin zama saida ta zauna kafin tace naji kunce kuna son nayi muku kwana biyu ne shine nace bari in zauna din yafi kada in tafi kuga rashin kyautawata ko mamy tayi fada

mun shiga uku🙆‍♀

🤣🤣

*vote*
*comments*
*with 08066364077*

*Alqalamin khady✍*
🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*TA ME GARI*

1⃣6⃣

*ina neman afuwan mutane pls dan Allah ku dinga min adalci nasan masoya basa yawa kuma daukaka daga Allah take ina iyakar kokarina wajen ganin na faranta ran kowacce a cikin masoya na idan kun tambayeni littafin daga farko ko wani page din ban tura muku ba kuyi min uzuri kun san jiki da jini kuma inada abin yi amma nake sadaukar da lokacina dan nishadin ku duk wadda take son littafin tayi magana group nasan zata samu pls afuwan dan Allah na kuma gode da soyayyarku gareni Allah ya bar kauna ya qara zumunci*

***

kut......in kin isa Allah ya tsinen ai wlh bazan zauna da 'yar jagaliya a gidana ba cewar yusra ta fada tana huci

shima nasir cikin hade rai yace ke ina wasa dake ne ?wlh tun muna mu kadai ki tashi ki tafi gida waye zai yadda ibola ta zauna masa a gida har kwana biyu ko ki tashi wlh ko in babbala ki a kwasheki a kaiki

gani sukayi ta miqe yusra da dama tun tuni ta miqe tsaye ta riqe kugu ganin dije tayo kanta yasata kwasa da gudu tayi bayan naseer wanda shima ganin dijen ta miqe ya danji wani abu a zuciyarsa amma fa gara ya nuna mata shima namiji ne dan haka saiya dake ya tsaya yana fadin ke yusra meye haka ban son iskanci

saida ta qaraso gabansa kafin ta kalleshi ido cikin ido shiko kawar da kai yayi domin shi in yana kallon idonta sai yaga kamar idon mage bare yanzu daya qara tabbatarwa kansa yarinyar nan ruwa biyu ce wato mutum aljan😂dan haka be son hada ido da ita kada yaje ko maguzawan ne akanta arnan farko su nuna masa basu san hasken addini ba

tsinkayar muryarta yayi tana fadin

haba yayana yanzu kawai dan nace zan kwana biyu gidan ka kk korata bayan kuma tun farko ku kuka nemi da in zo inyi kwana biyu a wajenku ai ko ba komai nayi muku haka dan zumunci amma tunda bakwaso shikenan

jin kalaman datayi yasashi sauke a jiyar zuciya domin yasan yanzu zata ce zata tafi amma me ?

sai ji yayi tace tunda na fuskanci baka son in zauna gidanku hakan na nufin tun yanzu zumuncinmu zai samu rauni kuma nasan megari bazaiji dadi ba bare iyayenmu dan haka na yanke shawarar zamana a gidan nan har sai ranar da nayi aure

😳

me?

la'ilahaillah anta subahanaka inni kuntu minazalimin

a'uzubillahi minasshaidanir rajim

ka manta baka hada da ayatul kursiyyu ba

cewar yusra dake bayan naseer wanda keta kwarara addu'o'i kawai dan dije tace zata zauna a gidansu

itako dije dariya ma abin yabata cikin zuciyarta tace ikon Allah sai kallo

ganin yaki yin shuru banda ruwan dala'ilai ba abinda yakeyi hakan yasa dije fadin haba ya naseer meye naga kanata addu'a ko wani abun ne yafaru ?

kinga khadija dan girman Allah da ma'aikinsa na rokeki ki taimaka ki koma gida kinji

to wai sbd me?

ta tamvaya

yasan sha'anin jinni be zama lallai yarinyar tasan meta aikata musu ba kuma baya son tasani dindan haka saiya waske yace kawai kinga mamy nada hawan jini ga shi ma yau mura take fama da ita matsananciya ina ma zargin limoniya gareta kinga gara kije ki zauna kusa da ita nasan zaki taimaka mata da wasu abubuwan

hakane kam yakamata in koma

yauwa qanwata ya fada a dan raunane

yusrah ma harda gyada kai tare da fadin wlh kam gara kije dan tayi kewarki

toh shikenan ta fada tare da fadin

ni zan wuce toh saida safe

Allah ya tsare ya kiyaye a sauka lfy

qofar falon ta nufa har ta isa sai kuma ta tsaya ta juyo yake sukayi mata tare da wiving din hannu ita wlh dariya ma suka bata dan haka saida ta dara tare da fadin

lah ya naseer meya sameku ne a fuska kaida aunty yusra naga duk kunji ciwo

saurin kallon juna sukayi kafin daga baya suka hada baki wajen fadin Accident

subahanallah accident kuma?da kura ko kuma da kare dan wannan ai naga ciwon kamar bada mota ko wani qarfe akayi shi ba ko

da biri mukayi fada naseer ya fada yana yashe baki

.biri kuma a ina?

ai da yake akwai shi a nan gidan toh shine ina masa wasa ya yakusheni yusra ma haka

.wow gaskiya wlh har kunsa nafasa tafiya sbd wlh ina son biri dama

.wayyyoooo 🤣

dan girman Allah ki tafi kawai gobe zan kawo miki shi

ah ah nidai ina son ganinshi wlh

ai nasa an kasheshi

what ?

kisa fa?

akan me?

.sabd yaji mana ciwo har haka saina lura gaba gaba zai iya daukar rai ma

amma ko wannan biri sai kace ba dan nigeria ba

ah ah dan boko haram ne

au dama dabbobi ma suna zama 'yan ta'adda

ai.....kaga dan Allah ka barta ta tafi dare yanayi kuma gashi taxi zata shiga Allah ya kaiki lfy sister cewar yusrah dake tahowa danta dan tura dije

au ni kinga ma fa na manta wlh aunty ashe fa baba habu ya tafi ko yanzu ya zanyi to ni dije ta fada tare da rike haba

.akwai abinyi kawai kinga bari nadauko miki kudi kishiga taxi tunda baki da su ko

ah ah barsu kawai inaga inada su a jakata zasu isheni zuwa gida

to a gaida su daddy zasu ji tace tana qoqarin fita

tana ficewa kuwa yusra ta rufe qofar tare da sauke ajiyar zuciya haka shima naseer din

bakin gate ta nufa gurin me gadin gidan inda ta samu guri tazauna suka shiga hira kamar sun san juna tun da can gumi fa ta hadu da anka nan kayan zance ya hadu sukaita zubawa kuwa kafin daga baya taji qarar mota a waje koda suka leqa baba habu ta gani da kayanta a akwati kin kim kim musa me gadi ne ya karbi kayan tace ya tafi kawai nan ya juya ya musu saida safe

ganin dare nayi ne yasata miqewa tare da fadin toh baba musa zan shiga ciki saida safe ko

toh hajiya mu kwana lfy

Allah yasa ta fada tare da jan trolly dinta

harta nufi part din su yusrah kuma saita fasa ta tsaya ta danyi jimm kafin ta juya akalarta zuwa part din su habeeb tana zuwa ta shiga knoking a hankali a daidai wannan lokacin suna zaune suna hira tare da dan taba kallo jin ana buga kofar yasa shi fadin waye a hankali

shiru tayi sai da ya qara maimaitawa kafin tace nice

jin muryar mace yasa sajida saurin miqewa ta nufi kofar tana fadin kece wa?

khadija!!

bude qofar tayi sukayi ido hudu da dije inda gaban sajida ya yanke yafadi ganinta da tayi da jaka dirkekiya

lfy ?

ta tambayeta cikin dan hade rai

kallonta dije tayi ganin yadda tayi mata tambayar yasata itama hade nata ran kafin tace lfy lau mana ta karasa maganar tana me kutsa kai palon

sai yanzu ya dago ya dubesu shima ganin dije da jaka yasashi mamaki tare da fadin ke lfy naganki da jaka haka kamar me shirin barin gari

guri ta samu ta zauna tare da fadin lfy lau wlh nadauka daddy ya kiraka yayi maka bayani ai shine yace in zauna inyi kwana biyu anan nama shirya zan tafi sai gashi yasa an aikomin da kaya na toh da zanje part din ya naseer sai naga kaine babba kada kaga ban kyauta ba gara in zauna anan ko

hmmm haka

tunda yace haka be qara fadin komai ba illa juyawa da yayi ya kalli sajida dake tsaye kikam ta zuba musu ido maida kallonsa yayi ga tv din itama sajida ganin haka yasata samun guri tazauna dan nesa dashi

sun jima a haka banda karar tv babu abinda kk ji a falon itako dije duk jikinta ciwo yake mata gashi tana jin yunwa ga bacci data fara ji

gyaran murya tayi kafin tace am yaya nace ba

kallonta ya juyi yayi jin yadda take son yin magana dashi lallai ma yarinyar nan yafada a ranshi

itako ko'a jikinta tace wai azumi kukeyi ne a gidan nan?

cikin rashin fahimtar magsnarta yace kamar ya ban gane ba kina nufin na nafila ko me?

ah ah na dare nake nufi naga ne ko ruwa ba'a bani ba ga yunwa da nakeji kamar hanjina zai tsinke toh naga kada inyi nauyin baki tunda ni bana azumin gara a in magantu kada in cuci kaina

binta yayi da kallo wanda tarasa na meye shi kanshi ya kasa tantancewa ko kala be ceba taga ya miqe tare da daukar wayarsa ya nufi dakinsa

ganin hakan datayi yasata fadin to ko masauki a tausaya a bani ai ko tunda abincin bazai samu ba nazo gidan economic masu auna ci da ciyar da wani

rasa me zai ce yayi kaji yarinya sai kace irin kurege shi sam be son yawan magana bare wasa dan haka cikin dan hade rai yace ki tambayi matar gidan mana ai itace da gidan yana gama fadar hakan ya shige daki

sajida data tsaya kallon ikon Allah tare da nazari inda daga karshe taji dadin yadda habeeb din yai sannan tasaki ranta tare da fadin oh khadija baki abin magana ga gajen haquri tashi muje in nuna miki inda zaki sauka

ok ta fada tare da mikewa dakinta dayan takaita inda tace ta zauna a kawo mata abinci

ah ah ni ai a gidan nan nafi qarfin a kawomin kice dai in tashi in dibarwa kaina kawai in hidimtawa kaina kada kizo inga laifinki kin san hausawa sunce mu dangin miji ba'a iya mana

kallonta sajida tayi tare da nazarin yarinyar wannan yarinyar fitinanniya ce ta qarshe amma zanyi maganinki ta fada a ranta........

naso inyi muku yafiv haka amma kaina ciwo yakeyi bacci😚

*vote*
*comments*[3/14, 9:18 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀

TA ME GARI

1⃣7⃣

nayi adungure na wulwula na heqo na mazgo gaisuwa ta tare da jinjina ga dukkan masoya ta me gari tare da jinjinar ban girma ga members na khadija. fans novels 1 da khadija fans novels 2 ina ganin comments dinku gaskiya kuna yin dije da yawa 😘

miqewa tayi ta tabi bayan sajida wadda ke ganin ikon Allah ganin da gaske take bin nata zatayi yasata juyowa tare da fadin

haba qanwarmu ai kya tsaya inyi dawainiya dake ko iya na yau ne ko a matsayinki na bakuwa kamar yadda kk fada

dakatawa dije tayi tare da fadin ah ah matar yaya bawai fa wani dalili yasa nace ki bari in nemawa kaina d'a'amin ba kawai sai dan kin san iyawa mutum sai Allah kuma gashi naga bakisan da zuwana ba kada in saki wahala kije kawai ki kula da mijinki dan naga alamar ke yake jira bakin ciki ya cika masa zuciya kije ki rarrasheshi

kallonta sajida tayi tare da fadin wane irin bakin ciki kuma ?

ah bakin cikin zuwana mana shin wai be baki labarin abinda ke tsakaninmu ba?

dammmm gaban sajida ya fadi cikin karfin hali tace meye tsakanin kun ?

ah lallai da sauran ku tunda har yanzu be fada miki ainihin sahihin abinda ya hadani dashi ba

zuciyar sajida fa tafara cunkushewa jin yarinyar na ambatar wai alaqa tsakaninta da habeeb shin me hakan ke nufi?wace alaqa ce kuma?to ko dai ya so yarinyar ne ?kai no habeeb dake son babbar mace wadda ta iya tattali irinta me zaiyi da wannan berar wadda inba kayan fitina da jaraba ba ba abinda ta ginu akai dan haka cikin dan hade rai tace ai ke yakamata ki sanar min alaqar ba shi ba

kallonta dije tayi ta nazarci matar tun dazu ta karance ta akwai kishi dan haka saita kiyasta a ranta kawai inta yi mata wani rashin kyautarwa wlh ta hakan zata azabtar da ita

itako sajida haushin yarinyar ta tsinci kanta da ji dan sai yanzu ma taga meye dalilinta na tsayawa ta biye mata yarinyar da bata wuce sa'ar kausar ba autar su dan haka saita sa kai da niyyar ficewa daga dakin muryar dije taji na fadin

.yauwa Aunty jeki bashi haquri ni bawani dadewa zanyi ba zan koma gida amma dan Allah a dan taimaka a qara yawan abincin gidan kar ayi la'akari da girman mutum shi ci ba'a nan yake ba kada ki ganni siririya wlh rainon kauye ce dan haka a taimaka kada a tauye ma cikina hakkinsa kuma kada ki manta kice masa ya baki labarin zuwansu qauye last

ko ta kanta sajida bata bi ba tasa kai ta fice itama ta fito sajida na kokarin shiga dakinta ta tsinkayi muryar dije na fadin

aunty inane madafa?

kamar ya ?

ashe fa matar yaya 'yar gayu ce na manta wlh

i mean kitchen?

nuni sajida tayi mata da hannu inda tai shigewarta daki

tana shiga dije ta kwashe da dariya tare da qarasawa kitchen din ruwan tea kawai ta hada tasha dan duk jikinta ciwo yakeyi har yanzu musamman gurin da nasir ya riqeta a nan ta shanye shayin ta gama ta koma masaukinta tare da bude jakarta ba kayan bacci ciki dan haka ta kwanta abinta a haka da kayan yusra🤣

tana shiga dakin ta sameshi gaban mirrow yana fesa body spray a dan hade rai ta qarasa ta karba ta shiga fesa masa duk yana lura da yanayinta kasancewar ta mace me iya tattali da soyayya sajida ta waye kwarai ta san hanyoyin mallakar miji cikin sauki ba boka ba mallam tasan kissa kala kala hakan yasa ta mamaye zuciyar habeeb domin shi dama dan son rayuwa ne kuma saiya samu me tarairayarsa duk yadda yake da jin kai da miskilanci to fa a gaban sajida tamkar yaron goye yake kuma yana iyajin zai iya mata komai a rayuwa dan haka koda yaga yanayinta yasan akwai damuwa damuwar kuma bazata wuce akan zuwan dije ba dan yasan sajida akwai kishi dan haka saida yabari sun gama shirin kwanciya kafin ya jawota jikinsa cikin salon tasa soyayyar ya shiga fadin

what's wrong with my princess ?

uhmm ?

shuru tayi kafin zuwa can yaji tace

mece sahihiyar alaqarka da khadija?

cike da mamakin tambayar datayi mishi yace kamar ya ban fahimta ba inaga ai kinfi kowa sanin matsayinta a gurinmu ko?

hmmm amma ai tace in tambayeka ainihin sahihiyar alaqar dake tsakaninku wai a kauye shine nake son jin ko akwai wata a qasa ne

murmushi yayi a zuciyarsa tare da fadin lallai yarinyar nan bala'i ce ko ince annoba ifritu wato tayi nazarin hallayar sajida harta zurma ta ita kuma duk da girmanta da shekarunta ta kasa fahimta wannan akwai shegiyar yarinya wato so takeyi ya bata labarin abinda tayi musu a qauye abinda ya barshi a sirri baya fatan matarsa tasan abin kunyar daya faru shine take son fallaso shi ai wlh gobe korata zaiyi gidan nasir suje can su karata tunda su sun saba wristilling da ita

jin yayi shuru ne yasata fadin kayi shuru baka bani amsa ba

oh baby matsala wlh wlh kinji na rantse miki wlh babu wata alaqa tsakanin mu in ba matsayinta na qanwa garemu ba ke ni wlh banma santa ba sai zuwan da mukayi time din da muka dawo nigeria daga nan tsohon nan ya hadomu da ita shine silar zamanta a gidanmu so banda wannan alaqar banga wata ba amma ban san dalilinki na tambayata ba

hmm ai dole in tamvaya ganin yadda kayi mata dazu a gidan naseer kuma gashi yanzu ta dawo nan amm.......shiiiiiii ya fada tare da dora yatsan shi a saman lips dinta haba baby ya kk son maidani baya ne me kk tunani namijin dake da mace kamarki shine zai iya hango wata to kisani wlh inda ana ciro zuciya to dana ciro mikitawa kinga yadda nake sonki nake ji dake ke wlh ni ko wacce mace kallon 'yan daudu nake musu kuma ma in zaki hadani da wata ina laifin ma ki hadani da ta kwarai saiki hadani da hambirin hayam wlh kin cuce ni kin san yadda na tsani yarinyar ma kuwa wlh sbd daddy yasa nake raga mata kuma bana son raini shiyasa kika ga ban. fiya shiga shirgin kowa ba sai naki ke kadai keda habeeb kisawa ranki ko'a lahira bazan miki kishiya ba bare gidan duniya da sai naga wadda taimin zan aura dai ko ? to duk ba wadda tayimin sai fadimatuz zahra'u sajida,batula,Aliya,kamila,sharifa,zakiyya.....zai ci gaba ta katse shi ta hanyar mannewa da jikinshi tare da aika masa da rikitattun sakonnin da suka sa ya kasa qarasa wa ya shiga maida martani ita ko ta dage wajen ganin ta biyashi tukwicin kalamansa masu tsadar gaske a wajenta nan suka lula duniyar masoya

Asuba ta gari

*******

ana kiran sallar asuba a kunnen dije koda ta farka tayi sallah ta yi addu'ointa kamar yadda ta saba kafin daga baya ta miqe ta afka kitchen break fast me rai da motsi ta hada sannan ta jera saman dinning kafin ta koma daki wanka tayi tare da shiryawa cikin unifoam dinta sannan ta fito saman dinning ta nufa ta fara karyawa amma bataji alamar mutan gidan sun shirya fitowa ba gashi har kusan 7:15 sai da ta gama karyawa tsaf kafin ta miqe ta nufi dakin dataga sun shiga jiya

kwankwasawa ta shiga yi

ya akayi ne waye ?

taji muryar sajida na fadi

au to bakuwar gidan ce naga shuru ne me gidan be fito masallaci ba shine nace bara in sanar muku ana shirin tada sallah ya gaggauta koya samu jam'i don kin san sallah in rana ta fito ba kyau gara a yita da duhun asuba

bude qofar sajida tayi tare da kallon dije jin abinda ta fada mata wato dai so takeyi tace basa tashin asuba kenan shine ta fada a fakai ce ganin ta cikin shirin makaranta yasata fadin to tasalla munji mun tashi ai a bari mu gama kimtsawa sai mu fito ko?

ah ah in dan ta dije anty ku koma bacci nidai kiramin me gidan a sallameni in tafi naga zan makara

gyaran murya yayi daga bayan sajida shirye yake tsaf cikin kayan suit ash colour sunyi masa kyau matuqa cikin hade rai yace lfy nake jin hayaniya

lfy qalau yaya dama zuwa nsyi ince na shirya zan tafi school

toh a dawo lfy

to wa zai kaini?

au dama baki taho da me kaiki din ba yayi maganar yana me fitowa a dakin sajida ta biyo shi suka nufi waje inda suka bar dije tsaye da sakin baki

ganin da gaske fita zasuyi gashi dai bataga ya karya ba oh yanzu nagane ta fada a zuciyarta wato sbd ni aka ki yin abin kari a gidan nan hhhhh tayi dariya kadan ashe kuwa akwai kura dan wlh ko da bala'i sai naci na qoshi tana ta sambatun ta har suka fice bata sani ba saida taji alamar rufe kofar kafin ta juya a hankali tabi bayansu

.direct gurin motar sa ya nufa yana zuwa ya bude mazauninsa ya shiga inda yabar murfin bude sajida ta tsaya riqe da murfin suna maganar su ta masoya

tana fitowa ko ta kansu bata bi ba ta nufi part din nasir ta shiga kwankwasawa

nasir da suke tsaye suma suna bankwaba da juna yaji ana buga kofa yayi saurin sakin yusra ya nufi kofar yana fadin sai mun dawo dan yana kyautata zaton habeeb ne dan ya fada masa in zai wuce asibiti zai wuce dashi dan yanason yaga likitan fata dan yadda kura ta yayyageshi🤣a cewarsa

yana bude kofa sukayi ido biyu da dije

.besan lokacin daya furta

la'ilahailla anta subahanaka inni kuntu minazzalimin

lfy me ya kawoki da sassafen nan ?

ganin yadda yayi yasa dije kusan sakin fitsari dan dariyar data guntse

yusra da tana dab da shiga daki taji yayi wannan addu'a yasata dawowa dan taga meya gani aikuwa itama na ganin dije tace ya salam meye kuma kika manta ai da kin fadawa mamy ta kira waya ai sai a aika miki shi

ai badaga gida nake ba anan na kwana

cikin hada baki sua ce a ina din?

a gidan y habeeb

sauke ajiyar zuciya sukayi kusan a tare kafin nasir yace

Alhmdllh qanwarmu sarkin hankali ai gara da kk kwana a can ni yanzu ma kinga abuja zamu tafi ni da yusra dan haka basai kin zo mana sallama ba in zaki tafi ki gaisheda su mamy tsarabar ki insha Allah daban take in mun dawo yana fadar haka ya juya ya koma suka kullo kofa harda sa key

dariya dije tasa kafin ta gaji ta mike ta nufo inda su habeeb suke wadanda duk abinda ke faruwa suna kallo sai dai basu san me suke fada ba sun dai ga komawar nasir da dariyar da dije tayi

tana qarasowa bata ce qala ba ta bude murfin baya ta shige ta qame ta kalli window

cike da mamaki a fuskar kowannensu sajida ta bude baki zatayi magana ya dakatar da ita ta hanyar daga hannu kafin cikin hade rai ya juya yace

ke dan ubanki bakida hankali ne meye na shiga motar mutane uban waye drivern ki?

cikin marairaice fuska tace kayi haquri yaya wlh dama tsayuwar da mukayi da yaya nasir ne yace in fada maka wai daddy yace ka ajiyeni a school daga can zan wuce gida ma nafasa zaman

jin ta ambaci tafiya yasa sajida saurin fadin ai kawai ba komai sweety ka ajiyeta din inaga shi nasir din yafasa fitar tunda kaga ya koma watakil dan yaga za'a fita da jerry dinsa ce

jin sarauniya tayi magana yasashi fadin ok kawai

sallama sukayi inda ya fita daga gidan be ko bi takan naseer ba

kasancewar yasan school din tasu direct can ya nufa da ita yana tsayawa ta bude ta fita tare da fadin saina dawo yaya

.ki dawo ina?

gidan ka mana ai ni naga wuri .........

*Alqalamin khady*✍
[3/14, 9:34 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*TA ME GARI*

NA
khadeeja usman

1⃣8⃣

*ina matuqar godiya da addu'arku gareni Alhmdllh nasami sauki tare da kuzari da karsashin ci gaba da suburbudo da sambado tare da sheko muku ta me gari uwar mazga hakika kuna dadamin qwarin gwiwa ta yadda nake jin zan iya yini zungur ina muku typing amma sbd halin yanayi zan bawa kaina haquri inyi muku na 'dan lokaci zakufi jin dadin sa😂*

tana gama fadar haka ta juya ta shige makaranta ta barshi da sakin baki inda ya shiga fadi a fili wlh bazan yadda ki zauna min a gida ba bari kawai in kira daddy ince masa ki koma can kuma sai yace kai nasan halin yarinyar nan yanzu haka bazata koma bs kawai fadamin tayi dan inyi haushi sbd ta mayar dani kare hmm zanyi maganinta haka yayita tuki yana sambatu da masifar ba gaira ba dalili har ya isa asibitinsu yana zuwa ba jimawa ya fara aiki

itako dije tana shiga cikin makaranta direct office din principal ta wuce ta sanar dashi daga yanzu a dinga biyawa daukarta da motar makaranta ta fada musu inda ta koma dayake dama a cikin bill din makarantar harda kudin transport suke hadawa sai dai in ka so kasa a kawo danka amma su ba ruwansu shi yasa koda dije ta fada ba'a samu matsala ba

tana fitowa ta nufi class nan suka hade dasu rufaida aka shiga hira kafin malami ya shigo suka fara lesson

****

Amarya kenan kin ganki kuwa yadda kika canza kinyi wani kyau dake kamar wata black american

dariya sajida tayi kafin tace ke laila wlh banda sharri

wlh ba maganar sharri fadamin meye sirrin ne me habeeb ke baki

kulawa da soyayya ta fada tare da yin fari da ido

shegiya qawata kodai to har an sama mana baby ne

baby fa kika ce tun yanzu ?ai sai mun shekara kafin inyi ciki ke yadda habeeb yake dan son rayuwa yanzu in nayi ciki ai sai a hankali shima kanshi yafi son mu huta ai

tafawa sukayi tare da fadin kusha sha'aninku bird loves naso inga habeeb ranar aurenku inga bakin nan sai gashi ina malesia na tsinkayi lbrn bikin gashi ba halin in dawo sbd wani uzuri

.hakane kam Allah be nufa dake za'ayi ba yanzu gashi kinzo har gida ai bari in tashi in sama miki abinci ko me kike so ta tambayeta tana qoqarin miqewa

komai ma kin san ni banida zabi

ok ta fada tare da kokarin miqewa ta shiga kitchen

da sallamarta ta shiga falon inda ta iske laila hakimce da remote tana canza tasha batare data juyo ba ta amsa sallamar har saida ta ji dije nayi mata ina yini kafin ta maido da dubanta gun

wani kallo tabi dije dashi ta amsa gaisuwar a yatsine ko ba'a fada mata ba tasan wannan qanwar habeeb ce domin kuwa tana kallonta ta hango kamar su sai dai kawai ta fi shi haske dan ita fara ce sosai hmm tab di lallai akwai aiki wato har an fara kawo 'yan leken asiri lallai sajida batada hankali ita ina zata yadda da a kawo mata wata dangin miji ai ko kawowa za'ayi gara a ce ta dauko a danginta balle wannan yarinyar da gani idonta feke yake

tund dije ta lura da kallon da matar ke binta dashi taga kuma ta lula duniyar tunani kawai saita qarawa wutar ta mai tayi shigewarta dakin data kwana jiya

laila na tsaka da tunani sajida ta fito hannunta dauke da jallop din makaroni daya sha kayan vegetables da busashshen kifi sai kamshi yakeyi

qarasowa tayi kusa da ita taja mata dan qaramin center table din dake gefen kujera ta ajiye mata abincin tare da komawa ta qaro mata ruwa da lemo ta na ajiyewa ta zauna ita kuma laila ta sauke gwouron numfashi tare da fara cin abincin

saida ta gama tsab kafin ta kalli sajida tace

qawata wani abu nagani a gidanki daya dagamin hankali

.cikin razana sajida tace me kk gani ?

wata yarinya nagani yanzu ta dawo da alama kanwar mijinki ce naga daga makaranta ta dawo sajida ina tunaninki ina iliminki da wayewarki suka tafi tun yaushe aka daina yayin 'yar zaman daki wannan budurwar yarinyar ai kawota kawai akayi ta hanaku sakewa inba haka ba su dai ba ci suka rasa ba ba sha ba bare ace sun takura ne suka kawota nan dan haka wlh kisan abinyi ke banda ma uwarsu daya ubansu daya ai da sai ince ko kawota ma akayi ta gama gane miki sirri karshe ta aure miki miji

rasssss gaban sajida ya fadi tare da nazarin maganar laila

ganin yadda duk yanayinta ya fara canzawa yasa laila qara dogon sharhi aikuwa nan sajida ta fada mata tsakanin habeeb da dije da dangantakarsu ai kuwa nan laila ta dinga kwarara wa sajida ruwan zuga tare da fadi mata illar zama da dangin miji dan mijinki na babba sai a kawota nan a kaita gidan naseer mana nan sajida ta fada mata yadda suka kwashe dasu naseer

tab iskancin banza ajanun banza aljanun wofi mu za'a gwadawa aljani ni danayi gadonsu dari ba daya ne akan kakata data mutu suka dawo kaina dan dama tun tanada rai munfi da ita shiyasa koda ta mutu suka ce ni suke so wlh duk qaryar rashin mutunci takeyi yarinya qarama da kicifi tun yanzu

ganin yadda laila ta dage tanata zazzaga masifa ne yasa sajida fara lallaminta domin da alama akwai aljanun fa a nan dan yadda ta fara daga murya

itako dije tunda ta shiga daki tayi wanka ta canza kaya ta nufo falon domin nemawa kanta da'amin inji ta saita tsinkayi maganar da laila keyi saida ta gama ji tsab har takai lokacin da sajida ke rarrashinta babu wanda ya lura da fitowarta direct kitchen ta nufa tana shiga ta shiga gyara duk wani abu da sajida ta bata tare da dora nata girkin kasancewar kitchen din rufe yake hakan yasa basuji kamshin girkin ba bare kuma girkin na mugaye ne dama dirka dirkan kulolin data gani ta dauka ta juye a ciki shinkafa ce fara sai miya datayi leqowa tayi falon inda ta gansu laila har yanzu tanata ma sajida famfo qara lababawa tayi ta dauko abincin cikin sanda ta ajiye saman dinning din kafin ta koma kitchen din ta gyara sji fes kamar ba'ayi amfani dashi ba

kafin ta kuma lababawowa ta shige dakinta tare da mayar da unifaom dinta sannan ta fito da rarrafe ta zagaya bayan kujera ta labe

jin kamar qofa tayi motsi yasa su saurin waigawa sajida da zuciyarta ke kusa dan sai ysnzu ma ta tuna da yarinyar cewa tayi gida zata tafi to uban me ya dawo da ita bari ta tashi taci uwarta kawai inya so ta kadata ta koma gidan su nasir suje can su qaraci gayyar rashin hankalinsu can inma kashe su aljanun zasuyi su kashe su sai me nan ta miqe laila ta dafa mata baya suka nufi dakin suna zuwa suka tura qofar ga. mamakinsu bakowa toilet sajida ta nufa ta shiga fadin ke khadija !! khadija!!

jin shuru yasata tura qofar ta leqa bakowa cike da mamaki ta juyo ta dubi laila tace kika cemun ta dawo kuma?

ban gane nace miki ta dawo ba to karya zanyi miki ko me?

ta fada cikin hade rai

to kuma gashi bata nan duk da nasan munyi magana da habeen da safe cewa gida zata wuce

toh nidai naga yarinya ta shigo kuma da unifaom fara ce siririya ko

tabbas itace amma ai muna falon ko dai kafin in fito ta fice baki lura ba

wlh ba wani fita datayi dan tana shigowa kina fitowa sai dai in wani salon munafircin ne na qannen miji kinga irin abinda nake fada miki ba nan fa suka shiga neman dije gani duk sun leqa basu ganta ba yasa sajida fara zargin kodai aljanun laila ne suka fada mata qarya gashi ba damar tace ah ah tasan halin laila yanzu sai su hau sama ganin basu ganta ba duka cike da mamaki suka fito suna tunanin ina ta shiga

itako dije tun shigarsu dakin ta miqe ta koma kitchen nan ta hau safa da marwa na shirya kaya a saman dinning duk wani ruwa da kalar lemo saida ta hada a gurin saisa ya cika tab da kayan ciye ciye kafin tayi saurin fita zuwa qofar falon ta cake tana jiransu fito

tana daga tsaye taji alamar sun dawo falon dan haka ta turo kofar ta shigo da sallamarta tare da nuna alamun gajiya a tare da ita

kallonta suka shiga yi musamman laila da taga yadda ta shigo din itako sajida ta shiga karyata maganar laila dan duk wanda yaga dije a wannan lokacin yasan dawowarta kenan basu gama tunanin na sukaji dije ta buga tsalle tare da fadin

yehhhh dan dunga yaushe kuka karaso bayan saida nace ku bari mu taho tare ashe kun sato hanya kun taho lah ashe akuyatu ta fanshe ni dan tayi muku girki

dukansu juyawa sukayi suka kalli inda take magana
ganin gima giman kuloli ga dinning din cike da kaya yasa sajida sakin qara tare da nufar bayan kujera dan ta buya itama laila ta mara mata baya

habeeb ne ya shigo dauke da sallama a bakinsa inda yana shigowa yaga dije tsaye na fadin

aunty laila taso ga dan kutungayya wannan aljanin dake saki yawan munafurci yana son ku gaisa

da kyar ya mayar da
kofar ya rufe inda ya saki baki yana kallon sajida data leqo kai jiki na karkarwa

ganin hakan da yayi yasa shi fahimtar yarinyar nan ce yanzu hska tayi musu wani abun dan yasan iskancinta ai kuwa yau saita ci ubanta daga yau bazata qara ba nufarta yayi gadan gadan da niyyar cafkarta ya nadeta kawai sai gani yayi tayi gurin dinning tana fadin kada ki damu darwanatu ai kowa zai ci abincin nan waya isa kiyi girki aki ci duk ds nasan duk kayan 'yan gidan ne

ah ah kada ku damu basai kun kawo naku ba ku barmu da namu kalar

kutttt habeeb ya hadiyi wani yawu dan sai yanzu yakai dubansa ga saman dinning dinsu wanda yaga dirka dirkan kuloli ga kuma kayan ciye ciye nan tab akai dubansa yakai ga sajida wadda ya zuwa yanzu banda rawa ba abinda jikinta keyi cikin rada ya shiga tambayarta abinda ya faru hankali ta fada mishi duk abinda tasani da yadda laila ta fada mata dawowar dije da kuma yadda ta duba basu ganta ba

jin murysr dije sukayi na fadin ah ah ai basai kun dauko su ba dukansu yanzu zasu taho muci gaba daya ai kada ku damu dukansu na jin haka suka juya da niyyar kwasa da gudu amma me? kafin su kai ga fita suna rige rige da gwara kawuna dije tayi caraf ta riqe habeeb wani ihu ya saki dan in baku manta ba na fada muku habeeb akwai tsoro

dariya dije takeyi iya yinta ta kuma riqe habeeb wanda ya kama ihu iya yinsa tare da karanta ayatul kursiyyu a fili naseer da yusra ne suka fito daga part dinsu jin ihun naseer ganin laila da sajida sun rukunkume juna suna rawar dari a bakin falon yasasu qarasawa tare da tambayarsu lfy duk sun kasa magana inda naseer yayi ta maza shida musa me gadi da shima ya karasso yanzu jin ihun me gidan suna shiga suka ga dije zaune dirshan a gaban habeeb ta riqe masa maka kam tana dariya harda kwalla shiko ya bude baki yana ihu da addu'a naseer yasan kwanan zancen dan haka ya kasa qarasawa sai musa ne ya qarasa koda ya isa nan ya tsugunna ya fara bawa dije haquri domin yasan wannan aikin na jinni ne

kallon sa tayi tace nice dai dijen da ka sani ga dai aljanun can akan dinning suna walima

kallon gurin duk sukayi suka ga abinda ke kai kowa yafara zufa yana neman hanyar fecewa inda habeeb najin muryar musa ya shiga magiyar yace ta sakeshi

zan sakeka amma su dan dukununu sunce yau sai mun tayasu murnar zagayowar haihuwar dan autan su dan haka dole kowa na gidan nan ya zo yaci abin cin can

nan aka shiga kallon kallo su kuwa matan na waje tuni suka sheqa pary din yusra suka kulle inda sajida ta dubi laila tace kin gani ko gashi nan harda irin na kanki sunzo min gida ina zaman zamana gashi kinsa sun kawo ziyara kin san suna binki meyasa kika zomin bayan kin san ni dul lamarin iska tsoronshi nakeyi

cikin kuka laila tace wlh ni banida aljanu ki dena jamin jaraba kada suji su dafemin

ina na kan naki dari ba dayan ?

ai sun barni tun da aka yayeni wayyo ni wlh gida zan tafi tunda abin harya kai haka baxan kara zuwa gidanki ba ashe har uwar aljanu kk aje a gida

duk kansu tsorace suke sunata kukan nadama wai🤣

su kuwa mazan nacan dije fa tace sai kowa yaci abincin nan kafin su dan dukununu su bar gidan nan jin in ba'aci bazasu tafi ba yasa habeeb saurin amsa duk zasu ci shidai tunda ta sakeshi

a gaba tasasu suka nufi dinning inda musa jikinsa ke bala'in rawa hakama naseer suna qarasawa sukaja kujera da niyyar zama dije ce ta da karfi tace ya naseer ka jefar da tunguji ba ruwana

da sauri ya ja da baya tare da kwalla kara habeeb da yake kokarin zama ji yayi tace shikenan ya zauna akan iya tsibbanatu qara yayi tare da zamewa qasa ji kakeyi kwal ya kwale da gefen table din yayin da qugunsa yayi qara.......

*Alqalamin khady*

TA ME GARI

na
khadeeja usman

1⃣9⃣

naji rokonku masoya amma kuyi haquri bazan iya yi muku typing sau biyu a rana ba ku tuna fa dukanmu matane munada uzuri a gabanmu karantawa ba wahala cikin qanqanin lokaci zaka gama amma typing akwai wahala ina son nishadinku shiyasa na ke bada lokacina nake muku typing fatana kuyi haquri mu qarasa da yadda muka fara idan nasami dama zan iya yi muku fiye da biyun ma a rana

wata azaba yaji amma ba halin yin ihu ya zuwa yanzu dan duk a rude yake ganin yanayin da duk suke ciki yasa dije cewa

lah sannunku kunga fa yanzu sun fara fushi gara ku tashi a gaggauta walimar nan su kama gabansu kaga dan dukununu kuyu haquri ku debo naku kujerun ku basu wannan su zauna ta fada tare da qara gyara zaman kujerun gurin

cikinsu duk wanda ka kalli fuskarsa kasan kadan yake jira ace arrr ya arta dan haka cikin himma suka fara qoqarin zama a dan dosane

itama dijen zama tayi ta kame guri daya tare da fadin toh ku zuzxuba mana arwanatu

😳 sukayi sunata raba idanu jin ta ambaci a zuba abincin kowanne yana kissima yadda zai kwashi wannan girkin na aljanu itako dije ta kame tana kallon kowa a ranta banda dariya ba abinda takeyi

can kuma sai ta miqe zumbur kamar wadda ta tuna wani abun suma miqewar sukayi dan su yanzu duk wani motsin yarinyar tsoro yake basu ganin duk sun miqe ne suma yasata fadin ina kuma zakuje?

binki zamuyi cewar naseer da kyar

ai nima ba tafiya zanyi ba zanje ne na kirawo matanku suzo su taya autaress murna suma

yauwa Alhmdllh dan Allah kirawo su din

cewar habeeb da ya zuwa yanzu ya dora laifin faruwar komai akan sajida dan a bayanin data masa ya fuskanci bakuwarta ce silar komai

toh ku koma ku zauna mana in kirasu

duk komawa sukayi suka zauna inda ita kuma tasa kai ta fice a falon ta nufi part din su yusrah dan tasan suna can

tana fita naseer ya kalli habeeb cikin marairaicewar fuska kamar zaiyi kuka yace bros nifa wlh lamarin yarinyar nan tsoro yake bani wannan wace irin masifa ce tunda muka fara ganin yarinyar nan bamu taba wanyewa lfy ba wannan ai ita ce da tauraruwa me wutsiya gani yayi habeeb da musa nata mishi alama daya yi shuru sai daga baya ya fahimci me suke nufi ganin musa nayi masa nuni da saman dinning hannu yasa da sauri ya kama bakinsa kamar qaramin yaro suka shiga raba ido🤣

tana zuwa part din ta shiga kwankwasawa laila da sajida da suke jiran tsammanin warabbuka sukayi saurin nufo kofar dan sun san yazuwa yanzu komai ya kamalla barin ma laila data matsu tabar gidan dan ita yusra ta shige daki ta kulle kanta ta shiga kiran wayar mamy amma bata daga ba

da sauri sajida ta bude kofar batare da tambayar waye ba aikuwa sukayi ido biyu da dije da gudu ta nufi ciki inda suka fara rige rigen tserewa ita da laila amma dije ta shigo tana fadin meye haka aunty ?

jin tace Aunty kuma cikin muryarta ya dan sa sajida tsayawa amma ita kam laila tayi bayan kujera tanata rarrafawa dan ta samu ts fece

jiki na rawa sajida ta tattaro karfin halin daya rage mata tace ya...ya...akayi ina su habeeb

kallonta dije tayi kafin tace ban gane ina su yaya habeeb ba gasu can a part dinki yayi baki yace in fada miki wai in kin gama gudun tsoron kizo ku gaisa

kuri tayi tana kallon dije jin cewar har habeeb yace ta zo yasata yin tunanin komai ya zama normal ba mamaki malamai ya kirawo ai gara ayiwa gidan addu'a gaba daya da alama komai ya lafa dan taga yarinyar ta warware dan haka cikin dan qarfin hali ta maze tace toh jeki ina zuwa

ok ta fada tare da fadin ina Aunty yusrah itama yakamata taje a gaisa da ita dan bakin daga family dinmu ne na qauye

toh bari na kirata tana ciki cewar sajida data juya ta nufi dakin da yusra ta kulle tana zuwa ta shiga buga qofar yusra dake can bayan gado manne da waya ta qanqame jiki tanata faman kiran wayar mamy wadda sai yanzu ta samu ta dauka tana dagawa kuwa yusra ta shiga fadin pls mamy kizo ki taimakemu wlh jaraba da annoba kika kawo mana ashe cikin kwana daya datayi a cikin biyun da kkk ce tasa kowa yasan da zamanta mamy pls n'd pls kizo ki dauketa ta koma gidan ni nayafe mata duniya da lahira

jin da mamy tayi yusra na kuka yasata fadin calm dawn mana yusrah ki ci ubanta mana karfinki tafi ko kuwa shi naseer din tafi qarfinshi ne iye

bazaki gane ba mamy duk yadda na fada miki nidai dan girman Allah kizo ki dauketa

.to amma ai naji tace wa daddy'n ku ku kukace ta zauna tayi muku kwana biyu dan haka ma nabar maganar dawowar tata

wlh mamy na rantse da Allah bani bace wall.....kinga ya isa wai meya ke faruwa ne kk kuka haka dukanki takeyi ko yankar naman jikinki

wlh mamy ni gara ma ta dakeni da masifar da nake gani nidai mamy kizo ki dauketa dan Allah suna tsaka da maganar ta tsinkayi bugun kofa aikuwa ta fashe da kuka tare da fadin kin ji ta ko mamy dan Allah kiyi sauri kixo

jin haka da mamy tayi yasata saurin kashe wayar ta miqe dan ta sanar da daddy su taho

jin taki budewa ne yasa sajida yi mata magana saida taji muryar sajida kafin ta bude tana leqo kai tace ya ake ciki

dan juyawa sajida tayi bayanta taga dije bata hangota nan ta sanar da yusra sakon da dije ta sanar mata

tab wlh ba inda zani

ah to ni ina ruwana kiyi zamanki kin san dai ba mamaki malamai ne suka zo daga kauyensu dan inaga sun san da zaman lalurar ta inaga shiyasa sukayi addu'a muma gara muje kar abin ya shafe mu bayan sun tafi tunda abin har yakai ga ana min girki da walima a gida ai ni nafi kowa shiga uku

sun dan jajja kafin yusra ta yadda ta fito da kyar laila ta fito a bayan kujera suka bi bayan dije kamar abin magani amma ganin ko'a jikinta yasa su yadda da almatsutsan sun sauka ya zuwa yanzu

koda suka qarasa part din nan aka shiga kallon kallo kowa ya kasa shiga sai da dije ta juyo ta kalle su tace ya haka ku shiga mana

laila ce tace ah ah ni daga nan ma wucewa zanyi ki mikomin jakata da takalmi in kin shiga Allah ya bada zaman lfy

ai wlh baki isaba sai dai ki shiga ki dauka in kin matsu

wace matsuwa nayi ai ba dole a mota fa nike kinga bari in tafi a haka na turo daga baya a karbar min

dije ce ta kalleta tace haba aunty ta ya zaki shiga mota a haka ba takalmi me yayi zafi haka ?

ai ni sai yanzu na tuna ma ashe bada takalmi nazo ba suna mota har jakar

sakin baki sajida tayi tana kallon laila da duk ta birkice kamar ba itace daxu ke ruwan bala'I ba dan haka cikin quluwa tace ah ah tsirara kika shigo gidan ba takalmi ne kadai baki zo dashi ba amma ai karki manta mukullin motar na ciki ko?

innalillahi wa'inna ilaihir raji'un cewar laila a fili

ba yadda ta iya dole suka tura qofar suka shiga suna shiga suka hangi mazan tsaye kamar ace arr su arta ita ko dije suna shiga ta mayar da qofa ta rufe tare da fadin sannunku da zuwa ku qarasa ayi walimar daku ku kadai ake jira

nan fa guri ya hautsine zasu sa ihu tace lah aunty kada kuyi ihu wlh kunayi zasu sa bakinku ya qara girma

nan fa jikin kowa yahau makyar kyata kasancewar dinning din kujeru takwas ne nan tajawa kowa daya ya zauna duk wanda ka kalla matsar kwalla yakeyi inda duk suka dubi kayan dake gurin wanda suka kalli kwalbar carbont din dake gurin gaba daya sai idanunsu yake musu gizo suke ganin kamar jini ne🤣 kunji fa sharri😜

bude kular tayi ta leqa 'yar mitsitsiyar shinkafar dake can kasan kular ta hango dan dama fa iya wadda zata iya ci kawai ta dafa jaraba ce tasata zubawa cikin wannan kular

lahhhh amma ko baku kyauta ba akuyatu ai bani kadai nace muku ku ragemun ba suma fa duk zasuci irin girkin ku amma shine kuka rage iya cikina ta fada tare da dan hararar kujerar daba kowa

jin ta ambaci an cinye abinci sai ita kadai aka ragewa yasa kowannensu hamdala a zuciyarsa juyowa tayi ta kallesu taga duk sun kafeta da ido dariya taso kwace mata amma ta danne tace toh kunga har sun gama cin nasu abincin kunyi jinkiri amma ai ga kayan drinks nan kuci ni bari inci wanda suka ragemin din nan ta shiga kokarin zuba shinkafar harta gama ta fara ci cikinsu ba wanda ya motsa bare ya dauki wani abun

shi kam musa ji yakeyi dazai samu dama da inya fece bamai sake ganinsa tunda aikin gadin ba dole bane

itakam dije tanata cin abincin ta hankali kwance su kuwa sai muzurai sukeyi

sai da ta gama tasha ruwa kafin ta juyo ta kallesu tace sunce tunda baku cin irin wannan bari su kawo muku irin nasu

da sauri aka shiga rubibin daukar abin ci inda saboda tsabar sharri habeeb daya dauki apple wai jinta yayi kamar goribar data bushe wai kawai dan ta aljanu ce🤣

kowa a gurin yana shan abu kamar magani kuma yana kuka itako dije sai surutun ta takeyi ita kadai hakan ke qara firgita su sukuwa suka shiga 'yammatan hawaye

su mamy na qarasowa suka shiga yin horn jin shuru ba'a bude ba yasa habu fitowa ya bude gate din da kanshi ya shiga da motar

mamy cikin tashin hankali ta bude murfin motar ta fito ita da daddy wanda suka nufi part din da basu san ko na waye a ciki ba suka shiga bugawa

jin ana buga kofar da dan karfi ga alamar magana yasa su naseer qara rudewa dan duk a tunanisu ko abincin da suka ki cine abubuwan suka gayyato wasu

dan haka suka qara kidimewa tare da qoqarin tura duk abinda ke hannunsu baki

dije ce ta miqe ta nufo kofar a ranta tana fadin wane me tsautsayin ne kuma

tana bude qofar taga su daddy mamy na qoqarin tureta ta shiga tana fadin suna ina?me kk yi musu jin muryar mamy ne yasa yusra da su naseer bude murya suka sa kuka.......

*kai kai naso inci gaba amma....*

*vote*
*comments*
*with 08066364077*

*Alqalamin khady*✍
[3/14, 9:42 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*TA ME GARI*

NA
Khadija usman

2⃣0⃣

*A gaskiya mutane basuyi mana adalci ba duk da nasan masu qarancin ilimi da tunani ne sukayi abinda sukayi kowa fa da ra'ayinsa duk wadda taga bazata iya novels kyauta ba ra'ayinta ne ban kuma ga laifinta ba haka mu da mukaga zamuyi kyauta muma ra'ayinmu ne dan haka bai kamata ayita magana daya ba har takai ga anyi mana rubdugu ana zagin iyayenmu gaba daya dan girman Allah ina rokonku ku dinga mana adalci reader's ku duba irin wahala da westing time din da muke yi duk dan mu faranta muku ina rokon afuwar duk wanda magana ta ta batawa rai🙏*

cikin rudewa da tashin hankali mamy ke fadin ya salam me zan gani haka me yake faruwa ta fada tare da qarasawa cikin falon ta nufi inda su yusra suke

daddy ne ya shigo shima inda dije na ganinsa ta shiga yimasa sannu da zuwa cikin nuna farin cikin ganinshi ta fara fadin oyoyo daddy gwamma da kuka zo wlh kunzo a dai dai sai ayi tare daku

daddy ne ya dubi sauran mutane yaga yadda fuskokin su suke amma kuma yaga dije qalau da alamun farin ciki a tare da ita ga kuma mamy data azalzaleshi cewar ba lfy gidan yaran ya taso suje dan haka ya juya ya kalli inda mamy take tana tambayar yusra dake ta kuka me ke faruwa

caraf dije tayi tace ai wlh daddy ban san haka nake da farin jini ba sai yau kai wlh naga soyayya kasan fa yau na cika shekara goma sha bakwai to ni nama manta sai dazu na tuna shine nake fadawa yaya shine fa yace wai dole sai anyi qaramar walima toh shine fa aka dan hada kayan sha wai kafin su shiryamin bikin birthday din wai shine fa Aunty yusra tace bata yadda ba a gidan ta za'a shirya party din shine itama aunty sajida tace ah ah sai dai ayi anan toh shine fa aketa rigimar yanxu haka ashe har kun samu labari

duk qamewa sukayi jin abinda dije ta karkace baki tana fadi yayin da yusra ta tsaida kukanta dan bataga amfanin yinsa ba ya zuwa yanzu kutmelesi lallai wannan yarinyar kashesu zatayi kawai

itako mamy jin abinda dije tace ya qara bata ranta wato ma har rigima yaranta keyi dan kawai su shiryama wannan me kama da mutanen boyen party lallai ma wato dai inta fahimta saude da yunusa ba qaramin shiri sukayi ba kafin su turo yarinyar nan duba da yadda komai yake tafiya game da yarinyar daga kan daddy yanzu har gashi yaranta ma zasu fara dawainiya da ita kamar ba su ne suke nuna tsanar yarinyar ba a fili a bar ma tasu to matansu fa ji yusra yanda take kuka ashe ma akan wannan ne take cewa ta zo yarinyar zata kashe su to sbd kawai ba'ayi iskancin tuna ranar haihuwar bane a gidan su ko kuwa? lallai yazama dole ta dauki mataki dan wannan yarinyar daga ganinta ba alkhairi bace

daddy ne yace kai amma yaran nan kun fiya shiririta wlh kai yanzu habeeb harda kai da girmanka akayi wannan abin dakai habeeb da tun dazu yayi zugum yanata raba ido sbd tsoron Allah yayi masa yawa yama rasa gane inda batun ya dosa sai da ya ji muryar daddy na fadin wlh dai in an girma asan an girma yanzu dai kun ajiye iyali dukanku ba yara bane yanzu gashi ina zaman zmana kun tasoni akan wani shirme naku

dukansu shuru sukayi suka shiga rarraba idanu domin kuwa ba halin suce qarya ne ba haka bane aljanun dake wurin suyi kulin kulifita dasu suce sun qaryata uwar dakinsu dan haka kowa ya shiga mirgina kai da raba ido ita kam laila fatanta bai wuce ta bar gidan ba

dije ce ta katse wa kowa tunanisa inda tace cikin 'yar shagwaba daddy ku taso kuma ayi daku

ah ah ni bada ni ba cewar daddy wannan aikin ku ne na yara a dai bani ruwa ya isheni

miqewa dije tayi ta dauko masa gorar ruwa ta dauki cup ta zuba masa inda ya karba yana kaiwa baki da niyyar sha yaji naseer na fadin kada kasha daddy pls

sauke kofin yayi kafin yace sbd me ?

kafin ya bashi amsa dije tace sbd tunanisa akwai sanyi ne to babu wani sanyi ka dauka ka fini son daddy din ne dazan bashi ruwan dazai cutar dashi kaga ya naseer wlh ba ruwana idan ka hadu da fushin......hmmm bari dai inyi shuru ta qarasa maganar tare da kashe masa ido tana dariya kasa kasa

ganin yadda tayi ne yasashi yin gum da bakinsa mamy dake gefe duk tana lura da yadda komai ke faruwa ganin hakan yasata sakin ranta tare da fadin

oh wato daddy'n ku kadai kuka sani ni ko tayi ma ba'aminba to ba damuwa godiya nake

ah ah mamy wlh ba haka bane cewar habeeb munga kamar a koshe kike ba kya buqata

au dama ana gane mutum ya qoshi da ruwa kenan?

ah ah no ba haka bane barii inje in kawo miki wani ya fada yana qoqarin mikewa duk tana hankalce dashi hakan yasa ta shiga nazarin tabbas akwai abinda ke faruwa boye mata sukayi dole ne kuma ta bincika dan haka saita maxe tare da fadin no shi wannan ba nasha bane

ai duk sunyi expire cewar sajida dasai yanzu tayi magana tun shigowarsu duk mamy ta karanci halin da kowa ke ciki

expire kuma duk kayan gurin

eh wlh habeeb ya fada da sauri

musa ne ya mike tare da fadin to ni fa zan koma bakin aiki wanda a ransa ya ayyana yana fita hada kayansa zaiyi yayi kauye bai ko jira amsar kowa ba yasa kai ya fita aikuwa yana fita dije tabi bayansa yana gab da shiga daki yaji ta kira sunansa aikuwa da gudu ya afka dakin be ko tsaya rufewa ba jiki na rawa daga labulen dakin tayi ta tsaya daga waje kafin ta dan leqo kanta tace nasan ya zuwa yanzu so kk yi ka bar gidan nan ko to wlh kasake ka bar aiki a gidan nan ko kasa kafarka ka fita sainasa inna arwanatu ta shanye mun qafafunka da hannaye inga ta inda zaka moru inka musa ka tafi din tana gama fadar hakan ta juya ta koma cikin gida musa kuwa kuka ya shiga yi harda sharbar majina ganin hakan bazai fishsheshi ba ya miqe ya dauki buta ya daura alwala ya samu guri ya zauna a cewarsa gara ya dinga zama cikin tsarki da alwala shina kariya ce nan ya shiga karanta ayatul kursiyyu

tana shiga ta tarar da daddy ya mike yana fadin tafiya zaiyi dan ita mamy tace ya wuce sai anyi murnar da ita jiki na rawa laila ma ta miqe ta dibi kayanta dan tasami hanyar kubuta ba wanda taiwa sallama ta fice

daddy har yakai bakin kofa ya tsinkayi muryar habeeb na fadin am daddy dama maganar khadija ne

dakatawa daddy yayi tare da juyowa dauke da murmushi akan fuskar sa yace ai kada ka damu tayimin bayanin komai nan da can ai duk dayane

da sauri habeeb yace daddy baka fahimceni bane ina nufin batun....caraf dije tace wai batun zuwa makaranta ta ai nayima principal bayani kada ka damu nace a dinga zuwa daukata

da sauri naseer yace a dinga zuwa daukarki kamar ya?

eh ai kasancewar na dawo nan da zama shine naga ba sai anyi wahalar daukar min driver ba kawai su dinga daukata da motar ina

gidan wa kk dawo da zama suka fada da bayyanar tashin hankalin maganarta a fuskokinsu har suna hada baki

sai dai in gidan naseer cewar habeeb

ah ah gidanka dai

naka dai

jin suna neman kwafsa mata yasa ta fadin kai brothers meye haka in dai dan nice kada ku bata ranku ina gidan kowa zan iya yini nan in kwana can ko kuma in dinga kwana daddaya ko bibbiyu dan haka daddy kada ka damu bari in bika in kwaso sauran kayana daya kamata tana gama fadar haka ta fice tayi wajen mota daddy kuwa juyawa yayi yace to sarakan rigima ni ba ruwana gata nan ta raba muku rigima ai
yasa kai ya fici yabarsu duk da bugun zuciya

mamy da duk abinda akeyi bata ce qala ba saida daddy ya fita kafin ta kalle su tace su zauna kowa ya zauna ta dan jima kafin tafara magana tace ina son sanin abinda ke faruwa a gidan nan tsakanin jiya da yau dan idona ya ganmun wasu ina son qarin bayani dukansu suka shiga rattaba mata bayani kuwa

jinjina kai ta shiga yi tare da naxari zuwa can ta nisa tace idan na fahimta wannan yarinyar annoba ce kenan a gida na nasan aninda zanyi badai tace zata dawo nan ba da zama to yau zan fada muku abinda zakuyi mata tasan ta dawo da zaman kamar yadda ta buqata nan ta shiga yi musu bayanin tare da fada musu matakinda zasu dauka dazai sa sai dije ta koma kauye da qafarta ta fada tare dayin kwafa ta miqe tayi musu sallama ta fito su habeeb suka biyota inda ta shiga motar habeeb danya maidata gida

itako dije koda sukataho ita da daddy ta sanar dashi tana son yasai mata waya koda qarama ce dan su dinga gaisawa tunda yanzu sun danyi nisa ba musu kuwa suka shiga wani shagon saida waya ya siya mata qarama dai dai ita a cewarsa saita gama secondry kafin yasai mata babba harda layi yasai mata kafin suka wuce gida suna zuwa kuwa ta shiga hada kayanta baseera tayi kewar rabuwarsu amma ta tausayawa su habeeb da zasu zauna da dije

komai nata saida ta hada tsab aka loda a mota ta ta shiga ita da habu driver ta nufi gidan su habeeb....... ...........

*wlh drmar nan fa yanzu aka fara kudai ku biyoni*

*Alqalamin khady*✍[3/14, 9:45 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*TA ME GARI*

NA
Khadija usman

2⃣1⃣

*A gaskiya banida bakin da zan gode muku masoya ta me gari a duk inda kk ina matuqar alfahari daku ngd sosai Allah ya qara qauna da zumunci luv u all😘*

suna qarasawa gidan habu ya shiga fito mata da kayanta inda ta tsaya tunanin to ina zata dosa gidan habeeb ko na naseer ?kai gidan ya habeeb ya kamata in fara zama tukun musa sai sim sim yakeyi tare da ladabi dashi aka dinga jidi kayan dije zuwa qofar part din habeeb kasancrwar magariba tayi yasa suna gama ajiye mata kayan suka juya shida habu dan yin sallah ita ko dije ta shiga knoking ta jima tana bugawa amma shiru kk ji ba'a bude ba tun dije nayin bugun marmari harta koma yin na qarfi amma still shuru jin ba ada niyyar budewa yasata juyawa ta nufi part din naseer canma bugun ta shiga yi still ba wanda ya bude ta jima anan din ma nan fa ran 'yammata ya fara baci wato ni zasuyi wa haka ko? to ko basa nan ne ta fada a zuciyarta tabbas da alama basa dan da suna nan tasan bazasu ki budewa ba kodan abinda ya faru dazu da wannan tunanin ta nemi guri ta zauna jin ana sallar magariba yasata miqewa ta nufi bakin gate gurin musa ta dauki buta tayi alwala bata ko tambayeshi mutanen gidan na ciki ba ta koma can gefe ta shimfida dankwalinta ta tada sallah

tana tayarwa taji ana danna horn musa ya bude habeeb ne ya shigo aikuwa yana gama parking ya fito ya nufi part dinsa a kofar yaga kayan dije murmushi ya sake tare da fiddo wayarsa ya kira sajida tana dagawa yace zo ki bude nadawo zuwa can sai gata ta bude masa ya shiga suka mayar da kofa suka rufe

saida ta idar da sallarta a nutse kafin ta miqe ta nufi part din ta kuma bugawa shima still banza akayi da ita ta gaji da bugu sannan ta nufi gun musa take tambayarshi ko matan gidan basa nan ne nan yake shaida mata duk suna ciki zamewa tayi ta zauna a ranta tace au wato ni za'ayiwa wulakanci dan na nuna ina son zama hhhh tayi dariya kadan kafin tace yaseen zaku san kunyi min haka nasan duk dan in koma gida ne to wlh ko kasheni zakuyi ba inda zani shi dai musa nashi ido dan yanzu hirar ma dayake yi da ita ji yayi bazai iyaba dan haka yana kallon ta tanata dariya ita kadai be ce kala ba zuwa can ma ya shige dakinsa ya banko bayan ya rufe gate din kamar yadda ya saba

ita ko dije ko 'a jikinta saima tunanin data shiga yi na inda ya kamata ta kwana ta jima zaune a gurin har aka kira sallar isha'i ta miqe tayi kafin ta kuma zama tana neman mafita zuwa can ta miqe ta nufi gurin kayanta jakarta ta zuge ta fito da wayar da daddy ya siya mata gashi bata sata carji amma ai da akwai na ciki bari ta kunna ta yi amfani da ita haka to wai ma uwar me zakiyi da ita din ta fadawa kanta a hasale (niko nace su dije za'a huce haushi akan waya ne) ba kaiii ya salam ta fada a fili nan ta shiga kakkanta sauran kayan tana jansu gefe guda harta gama duk ranta a bace yake kawai tuna irin saqar rashin mtuncin da zatayi musu tasan sun shirya mata hakan ne dukansu an fada musu ita tana jin tsorone wlh nan zata kwana tasan kafin gari ya waye ta yi mafarkin irin abinda zata musu da wannan tunanin ta shiga neman abinda zata shimfida ta kwanta ganin bazata samu ba yasata dauko dankwalayenta da siket dinta dan batada zani ta shiga shimfidawa har ya danyi tudu yadda zata kwanta hijab babba ta dauka ta kwanta ta rufe ko ina na jikinta

*niko nace haba dije sai kace mayya ki koma gida mana*🤣

****"

su kuwa su naseer shawarar mamy suka dauka ita tace suyi mata hakan tasan idan taga basu bude ba dole ta koma gida ai dan haka duk bugun da takeyi suna jinta sun san itace dan tun zuwansu da habu sun ganta itama sajida habeeb cewa yayi ta bari inya dawo zai kirata saita bude masa kawai dan haka duk sun saki jiki ya zuwa yanzu dije ta koma dan sun san dai duk ifritancin ta bazata kwana farfajiyar gidan nan ba ita kadai koda kuwa ita ce aljanar da kanta

***

dije fa dare yayi baccin nan fa ba dadi dan sanyin kasan tiles din ga kuma sauro duk da ta rufe ko ina na jikinta amma sai ta ji kamar suna bula hijabin suna cizonta ga kukansu daya dameta duk ta rasa abinyi oh ni dije na shiga uku ta fada tana me sosa qafarta dataji kamar sauro ya cije ta wlh da da inda zan samu turmi na rantse da Allah da saina dauko shi cikin daren nan na shiga daka koda shinkafa ce inya so kowa kada ya rintsa ta kiyasta kalolin mugunta a ranta sunkai kala hamsin a haka tayita saka da warwara tana ja musu Allah ya isa tare da tunanin me zatayi musu gobe ta huce kuma wlh ko da bala'i saita kwana cikin gidan nan tanata wannan saqar zucin bacci ya kwasheta har akayi sallah bata sani ba sai da sanyin asuba ya kadata kafin ta tashi taga gari har yayi haske salati tayi tare da miqa ta miqe ta nufi dakin musa tana zuwa ta tarar da buta bakin kofar dauka tayi tazagaya cikin flower tayi fitsari kafin ta dawo tayi alwala sai da tayi sallah ta fara shirin zuwa school duk da yunwar da take ji gashi ko wanka batayi ba jiya da dare bare kuma yanzu haka dai ta kimtsa dan tana gudun makara kasancewar yanzu suna S.S.3 ne suna ta shirye shiryen fara S.S.C.E gashi kuma dama dije bata wasa da karatu duk iskancinta dan haka ta shirya ta kankanta kayanta a gefe harta ta juya da niyyar tafiya kuma sai ta tsaya jimmm

dariya naga tayi kafin ta juya ta koma gurin ta nemi guri ta zauna ta shiga fadin wlh na ma fasa zuwa school din in na tafi ai nabar baya da kura kenan hhhhh ta saki dariya kafin naga ta miqe ta ciro waayarta ta kunna time ta duba taga 7:10 dan haka tasan duk inda masu gidan suke ya zuwa yanzu sunata shirye shiryen zuwa office dan haka ta miqe ta shiga zagaye a gidan ko me take nema ohoo

ta jima tana zagaye gidan kafin daga baya ta taga wata igiiya daure daga bayan dakinda alama ta shanya ce dan haka ta je ta fara kokari. kuntowa

tasha wuya kafin ta kunce ai kuwa tana zuwa ta shiga dariya tare da nazarin ta ina zata fara

qofar ta kalla aikuwa nan ta shiga neman salon da zatayi qaramar jakarta ta bude ta dauko kifiyar tsifa nan ta shiga turawa guri. mukullin ta jima tana malqwayawa hada cije baki kuwa har saida taji wani abu yayi 'yar qara kafin ta zare kibiyar wadda ita kanta dan wahalar da aka bata saida ta malkwaye danma irin me kwarin nan ce ta kusa saida ta tabbatar ta gama lalata inda makuli zai iya shiga kafin ta fara neman dabarar daure kofar wata irin dauri tayima kofar na fitar hankali wanda ita kanta in ance ta fadi ta inda ta fara bazata iya ba tana gamawa ta koma part din naseer shima yadda tayiwa habeeb din haka tayi musu duk ta hada zufa sai da ta kammala kafi. ta tsaya ta riqe kugu ta shiga fadin yau sai inga yadda zaku bi ku fito wlh sai kun san na kwana a waje naga me zuwa ya bude ku ta fada tana haki kamar me shirin yin dambe

****

su kuwa dukansu suna ciki suna shiri dan yau sunada meeting da zasuyi dan haka sukayi waya akan kowa ya shirya cikin lokaci sam sun manta ma da wata aba dijeee

*da babu gara ba dadi manage pls*

*Alqalamin khady✍*
[3/14, 9:48 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀

TA ME GARI

NA
khadeeja usman

2⃣2⃣

kai kai kai gaskiya na fuskanci mutane ma sunfi son dije dani zan fa koma 'yar adawarta dan na fuskanci hmmmm bari dai kawai nayi shuru

bazan gaji da nuna farin cikina ga daukakin masoya tame gari ba a kullum ina ganin sakonni tare da kira ban san adadi ba ngd da addu'oinku gareni ina matuqar sonku tare da ji daku

****

luv birds suna manne da juna suna sallama an rako miji suna qarasawa bakin qofar falon sajida aka shige gaba ana kwarkwasa aka zira key dan a bude ji tayi yaqi shiga shiko habeeb dayake ganin kamar tana hakan ne dan qara salon jan hankalinsa yasashi fadin pls baby aimun afuwa a barni haka kin san sauri nakeyi

cike da salo wai ita irin baby din nan tace wlh ba haka bane sweety key din ne yaqi shiga ban san dalili ba

qarasawa yayi ya karbi key din ya shiga zurawa ganin da gaske fa yaqi shiga yasa shi qara azama amma still dai haka

haka ma a bangaren su naseer suna can suna kokawar bude qofa amma taqi buduwa

dije na tsaye tana jin ki..ki..ki ..ki anata dannar kofa jin sun jima sunayi tasan ya zuwa yanzu duk sun wahala ransu ya baci dan haka ta qarasa jikin qofar tare da kwankwasawa da sauri habeeb yace waye ?dan ya matsu ya fita

ni ce nan cewar dije

hasbunallahu wa'nimala wakeel ya fada a fili wannan jaraba har ina wato yarinyar nan dawowa tayi kenan kamar tasan meyake fada a zuciyarsa sai ji yayi tace

ina nan dama ba inda naje anan na kwana badai ni kuka sa na kwana a waje ba to naji ni na kwana a waje cikin duhu da sanyi da sauro to ku kuma ku yini cikin haske da A.C ga fanka ba sauro bare kuda kuzauna kuyita kallon juna ta qarashe maganarta tare da yin dariya tace wlh kuma naga wanda zai bude ku muddin ina nan a haka zaku tabbata ni naji ina nan zan dinga kwana a nan waje ku kuma kuyi zamanku cikin gidanku ai yafi

jikin window suka dawo habeeb yayi slide dinsa tare da leqowa yafara mata magana cikin bacin rai dan ya zuwa yanzu yafara tunzura da lamarin yarinyar gara kawai yafara cin ubanta inya so kome zai faru ya faru ba aljanu ba ko kukar bulukiya ce akanta be shafeshi ba

keeee dan ubanki ni sa'an wasanki ne ya fada yana me nunata da yatsa ta ciki

ah ah kai ba sa'an wasana bane dan inaga lokacin da aka haifeni ma kai ka zama saurayi da ace ma anyi auren wuri da an ajje kamata

kai ya fada tare da dukan qarfen dake tsakiyar jikin window wlh idan baki zo kin bude qofar nan ba wlh wlh kinji na rantse sainayi miki abinda iyayenki bazasu gane ki ba dan zan manta da komai inci uwarki

yatsina fuska tayi tare da fadin iyayenmu bazasu gane mu ba dai dan yaseen sai dai a qona gidan nan ta fada tare da juyawa ta nufi part din su naseer wai ta leqo su suma

tana zuwa suma ta kwankwasa suma haka ta rattaba musu bayani sai dai sabanin habeeb shi naseer hakuri ya shiga bata tare da rokon ta budesu ya shiga sanar mata meeting garesu kuma wlh in basu halarta ba zasu sami matsala

tunani tayi taga ko ba komai bai kamata tayi musu haka ba coz wannan fannin da ban amma kuma sai dai naseer yafi habeeb dan shi ya karaya da wuri ya bada kai bori ya hau dan haka nan ta shiga kici kicin kunce igiyar amma ta kasa tana tsaka da haka ta hango habeeb ya nufo gurin da take gadan gadan cike da mamakin yadda akayi ya fito ta kwasa a guje tayi hanyar gate ya so binta amma ya kasa dan shi bazai iya gudu ba sam duba da yadda yaga ta zura a guje kamar iska na qara mata gudun

kwafa yayi tare da qarasawa bakin kofar su habeeb da suma suke ta leqe ta window kamar maguna cikin dan zafi yace kai kuma dayalla malam saika bude ta kitchen ka fito sam naseer ya ma manta da wata qofa ta baya ta cikin kitchen sai yanzu sim sim ya juya ya nemo key din ya bude ya fito yana fiwo ko kallonsa habeeb beyi ba ya juya ya nufi bakin motarshi shima ganin hakan yasa be tamka mishi ba ya shiga tashi motar shima suka fita

ita ko dije cikin sa'a tana fitowa daga gidan ta ga motar makarantar su aikuwa ta afka aka wulla da ita

***

sam yarasa mafita game da lamarin dije yarinyar da gani kasan batada lfy duba da yanayin kiriniyarta da fitina gashi yanzu inya ce ta koma gida daddy zaiga kamar da wani abu ko ma yaga laifin mamy duba da yadda mamy ke nuna kin dangin daddy to yanzu meye mafita? yana tsaka da wannan tunanin naseer ya turo kofar office din tare da sallama

amsawa yayi tare da yi masa nuni daya zauna suyi magana

zaman yayi duk da shima yana son suyi magana dashi dan ita ta kawo shi amma bari ya fara jin tashi

bayani ya shiga koro mishi akan dije nan yake tambayarshi meye mafita ,?

wlh nima maganar dana zo da ita kenan gaskiya ya ksmata asan abinyi ni a ganina tunda dai yarinyar nan irin naci ce dangin laquwa kawai mu haqura ta zauna din kamar yadda ta nuna ta na son zaman tare damu sai dai mu kiyaye bata mata rai tare da duk wani abinda mukasan zai sa sabani tsakaninmu tunda dai kaga ita dangin ifritai ce da an tabata sai mutum yaji jiki mu samu mu gagganda mu aurar da ita cikin qankanin lokaci dan na fuskanci batada wani wayo kaga saimu dan sami wani galmashuran mu hadata dashi mu lallabata cikin salama a rabu lfy

Ajiyar zuciya habeeb ya sauke tare da fadin to ai duk ba wannan ba a ina zata zauna ? dan ni gaskiya zamanta zai kawomin matsala da sweety na duba da yadda yarinyar ke da rawar kai ita kuma sweety na ga kishi kuma ma ni bana son harkar hayaniya wlh ni ko kallon yarinyar nayi gabana faduwa yakeyi kada taje taci gaba da gayyato aljanun nan suna watanda da kayan gidana dan kaga ko na jiya fa maimakon suzo da nasu to nawa fa duk suka nakasa

jimmmmm naseer yayi ya shiga nazarin maganar habeeb lallai fa akwai matsala to ammaai ko su aljanun in ka lallabasu basa cutarwa a cewarsa

dan haka ya nisa yace wannan ba matsala bane saita zauna inda nake ko?

Alright indai kaga ba wata matsala ai shikenan amma wlh yarinyar nan ko yau dana kamata inaga saina kusa kasheta

dariya naseer yayi yace ka kusa kasheta ita kuma ta kasheka gaba daya ba ko kuma tasa ka kukan.....bari dai nayi shuru ya fada yana rufe baki tare da dariya qasa qasa

to dadin abin dai kowa yanada abin fadi

gaskiya ne amma na wani yafi na wani ba naseer ya fada yana qoqarin miqewa dan tafiya shima miqewar yayi yana fadin na sa an kira me gyaran doors din nan inaga ya zuwa yanzu an gyara

ok ya fada tare da sa kai suka fice gaba daya

*****

itako dije sam ta manta ma da tsiyar data shuka sai da aka kusa tashinsu ta tuna dan haka ta shiga tunanin mafita kawai in koma gida ince wa daddy nafasa zaman nan shi yafi min alkhairi dan wlh wannan me siffar mugun dawan ya rikeni kwanana ga kare yaje ma yayimin rauni a zo aurena a ragemin farashi

to wai ke dije yaushe kika fara tsoro ne kece fa uwar mazga jahannama ga fasinja dije Annoba fitinatu cewar wani bangare na zuciyarta

ke banza da ne nake amsa wannan sunan amma yanzu tunda na fara shan ruwan alwalar la,asar naji nafara sanyi ita kadai take ta surutunta a zuciyarta har aka tashi ta shiga motar komawa gida jikinta a sanyaye

ta jima zaune a unguwar nesa da gidan taki shiga kamar abin dole danma suna ci suna koshi a makarantar amma da yau taci ubanta da yunwa duk da tunanin matakin da habeeb zai dauka a kanta ya hanata sakewa taci abincin

*niko nake su dije anyi laushi ne*😂

tana nan zaune har magariba ta gabato ta hango dawowar su habeeb nan ta shiga neman mafita zuwa can kuwa ta saki murmushi dan tunawa da tayi da wata dabara

qafar wandonta ta shiga nadewa duka biyu zuwa gwiwa ta bubbuda qafafu ta gyara saiti shi kuwa musa ya wangale gate motocin na shiga yayin da matan masu gidan kowacce ta fito dan tarbar mijinta anci kwalliya dan tarbar miji suna gama shigewa musa ya fara qoqarin maida gate aikuwa dije ta kwaso a guje ta nufo ciki yana gaf da ida rufewa ta afko kamar an jefota tana fadin ku gudu gasu nan ku gudu ku gudu ai musa be ko tsaya qarasa turawa ba ya afka dakinsa ya banko ji kake garam

su kuwa mata anata kwarkwasa sun nufo parking space inda mazajensu suka parka suna qoqarin fitowa sukaga ahigowar dije na fadin ku gudu gasu nan ganin yadda take a sukwane yasa naseer da yusra kwasa suma a guje inda sajida ta juya itama da niyyar guduwar shims habeeb haka ji kakeyi kummmm kawunansu ya hadu yayin da hancin habeeb ya fashe jini ya fara biyowa itako sajida bakinta ya bige shima har da jini amma ko ta kan juna basu bi ba suka shiga rige rigen tserewa yayin da ita uwar gayyar tuni ta shige parlor ta tsaya tana mayar sa numfashi a wannan yanayin suka shigo suna kokarin danna kofar da aka gyara dazu suka aa key nan habeeb ya sunkuya tare da safe kai jin jini na bin gefen hancinshi ita ko sajida sai yanzu taji zafi kamar kada ta taba aikuwa taji baki yayi suntum dan da nan jambakin datasa ya hade da jini da maiko abin saiya qarawa bakinta style 😂

sun jima haka kowa na mayar da numfashi kafin dije ta dago ta dubi sajida taga yadda lokaci daya halittar bakinta ta sauya aikuwa duk yadda taso hadiye dariyarta kasawa tayi sai da ta dara dariyar da takeyi ne yasa habeeb dagowa dan tambayarta me takewa dariya ai kuwa shima yayi tozali da bakin sajida da ya samu qarin armashin kwalliya.....

*wayyo cikina*
😂😂😂🤣🤣🤣
*na kasa qarasawa*

*

*Alqalamin khady*✍
[3/14, 9:52 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀

TA ME GARI

NA
khadija usman

2⃣3⃣

shi kanshi duk yadda yaso ya maze kasawa yayi duba da yadda yaga bakin sajida lokaci daya ya koma kamar na jaba sam yama manta da ciwon nashi nan shima ya shiga dariya

sajida kuwa ta zubawa sarautar Allah ido ganin duk su biyun shi da dije sai babbaka dariya sukeyi hakan yasa tayi tsammanin ko abinda ya biyo dijen ne ya shige jikinsu dan haka saita fara ja baya tana neman hanyar shafcewa

cikin dariyar harda rike ciki ya nunata da yatsa ya na fadin kin ganki kuwa sweety kin kalli yadda bakinki ya koma kuwa ?

tabawa tayi da hannunta taji yayi suntum sai yanzu na fuskanci meyake yiwa dariya itako dije cikin dariyar ta juya kallonta ga habeeb tace wlh yaya kaima bakaga hancinka ba har ya malkwade shafawa yayi shima ya danji zafi sai yanzu ya dan nutsu kafin ya rike kansa ya samu guri ya zauna tunawa da yayi da gudun da suka sheko to ko uban me ya koro yarinyar oho

cikin wannan yanayin ya dago da kyar yace ke su waye suka biyo ki ne?

tsayar da dariyar tayi kafin tace ba fa wasu bane qawaye na ne na skull shine mukace ayi rige rigen zuwa gida to shine fa na sheqo a guje.......

dukansu sakin baki sukayi suna kallonta inda zuciyar su ta shiga sama da kasa kowannensu yama rasa abin cewa tana gama fadar haka kuwa ta juya tayi cikin daki tana dariya

dukansu sun kasa magana sajida da ya zuwa yanzu takejin kamar ta shake yarinyar ta mutu kowa ya huta takeji wannan jaraba har ina yanzu duk wannan gudun famfalakin data sa su ashe shirmenta ne na banza da wofi dama ga haushinta da take ji tun safe tama rasa hukuncin daya kamata tayi mata

haka shima habeeb ransa ya gama dagulewa wato ma duk wannan gudun data sa su ashe kawai na iskanci ne yanzu dubi yadda ta mayar masa da bakin mata tamkar na jaba duk soyayyar da aka kwadaita masa yau amma yarinyar nan tayi masa bakin cikinta tunda ta yaya zai fuskanci wannan bakin na sajida a haka

itama sajida a nata bangaren hakan take domin yau ta kudiri aniyar shayar da shi soyayya ta musamman amma sai gashi wannan matsiyaciyar yarinyar ta bata masu shiri ji yadda hancin mijinta ya wani maude abin haushin ma ga gobe yusuf zai zo da matarsa yanzu haka zasu zo su gansu sun canza kamanni kai wannan yarinyar Allah ya hadata da marurun rayuwa wannan jaraba har ina ga yadda ta kwaso a guje wlh ita ta dauka ma 'yan boko haram ne suka shigo anguwar ashe wai shirmenta ne gashi dai ta zama budurwa amma ba hankali tana tsaka da wannan tunanin taji muryar habeeb cikin dariya yana fadin sweety duk tunanina ne hakan ya fada yana me qara kunshe dariya iya kuluwa ta kulu amma itama data kalleshi taga yadda hancinsa ya wani bude yayi dirimm dashi ai saita fara dariyar itama ganin tana kallonsa tana dariya yaga yadda bakinta yakeyi shima sai dariya

haka suka dinga yi sam sun manta da dije wadda tun da ta shiga daki itama ta zube ta fara tata dariyar ganin yadda lokaci daya halittar mutan gidan ta canza gashi ta kubuta daga hukuncin laifin dazu sai da tayi me isarta ta miqe ta shiga toilet tayi wanka ta canza kaya kafin ta fito falon

koda ta fito bata iske kowa falon ba da alama sun shige ciki dan haka kai tsaye ta bude kofar ta fita ta shiga jido kayanta tana kaiwa dakin datake kwana

sai da ta gama tsab kafin ta duba saman dinning taga an shirya shi tsaf da abinci mai rai da motsi komawa tayi tayi sallar magrib inda ta zauna tana karatun kur'ani har aka kira isha'i tayi kafin ta miqe ta fito falon bata iske kowa ba nan ma da alama masu gidan basu da niyyar fitowa dan haka ta zauna ta fara harraka abincinta sai da taci ta koshi sannan ta kai plates din data bata kitchen ta dauraye su kafin ta koma falon ta zauna kenan kuma saita mike ta fice daga part din gaba daya

su kuwa masu gidan suna can cikin daki zazzabi ne ya rufe sajida yayin dashi ma gwaskan kansa ke masa ciwo ko yunwar ma ba ji sukeyi ba dan sajida ta rasa bakin cin abincin ji takeyi ya zuwa yanzu kamar bakinta ba'a fuskarta yake ba dan haka da kyar sukayi sallah suka kwanta aka shiga zaman kurame

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.