Taura Biyu Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Taura Biyu Mamuhgee.txt
Chapter 3 of 5
Cigaba yayi da cewa,
Ayshah inason abokina sosai sbd shine sanadin danake cikin rufin asiri nida mamana da qannena harma nake karatu sbd shine yake biyamana komai.
Cikeda tsoro da mamakin Jin hausa ra'dam a bakinsa ta 'dago ta kallesa batareda tabude baki tayi magana ba.
Murmushi yayi kafin yacigaba da cewa,
Ayshah akwai abinda nakamu da tsananin so tun farkon ganina da abin Amma yau an wayi gari Nik na tsananin son abin fiyeda tunaninsa wandashi bai gama gano hakanba..
Saidai nayiwa kaina alqawarin bar Masa abinnan natafiyata..
Kallonsa tayi cikin mamakin yanda yake fa'da Mata abinda bai shafeta.
Miqewa yayi tareda juyowa ya kalleta yace,
Goodbye ayshah duk da nasan destiny will bring us together again.
Wucewa yayi tabisa da kallo akaro na farko dataji kamar wani alamari nashirin faruwa da ita saidai abinda batasaniba Mai da'dine ko Mara da'di.
Harya 6ace Mata Bata daina kallonsa ba kamar daga sama saitaji antoshe Mata baki da qyalle an 'dauketa tareda turata cikin mota akabar makarantar da ita.
Fitowa yayi mota jiki a sanyaye saiyaga wayam Bata gurin yana 'daga Kai saiga fitar motarsu mujahid makarantar da mugun gudu.
Komawa motarsa yayi yabi bayansu a guje kaman zai tashi sama da motar.
Hanyar wajen gari suka nufa batareda sun lurada Yana biyeda suba suka gangara cikin dajin ka'dan saiga wani qaramin flat Mai kyau sukayi parking suka fito Shahid ne riqeda ita har lokacin bakinta a toshe niqaf dinta ma tuni yacire acikin motar Wanda tuni kyakkyawar fuskarta ta qara rura mugun nufinsu gareta.
Fixgo mujahid yayi tareda 'daga hannu ya sharara Masa Mari yayi baya Yana yarfe hannu tareda sakin qaramar qara sbd xafin da hannunsa yaji alhalin shiyayi Marin Dan baita6a duka ko marin wani ba bare yaji zafi haka.
Daria suka sheqe da ita suna kallon yanda yake yarfe hannu Shahid yakallesa a 'dage yace,
You see Mama's boy you can't do anything like a man so stop acting like child and leave.
Hasala yayi ya qara 'daga hannu zai Mari Shahid mujahid yariqe Masa hannu tareda sharara Masa wani lafiyayyan Marin dayasashi qwalla qara tareda zubewa qasa yana riqe kumatunsa.
Kallonsa tayi tareda rintse idanuwanta hawayenta naci gabada gangarowa sbd tasanda bayada wani qarfinda zai taimaketa.
Ganin hawayenta yasashi miqewa cikin 'yar jarumta ya Sha gabansu yazamto ita tana bayansa yakallesu da idonsa dasukai jajir sbd azaba yace,
If you don't want to end your lives behind bars let us go.
Wata dariyar suka Kuma sheqewa da ita kafin mujahid yafara rufesa da duka Nan take hancinsa da goshinsa yafara jini gashi ko ka'dan baida kuzarin ramawa.
Lilis sukai Masa suka koma yimasa dariya ganin so yake yatashi yakasa.
Ahankali sautin kukanta yafara fita ta juya Masa baya tafara rero kukanta.
Duqowa Shahid yayi yakalli yanda yake Nishi yace,
Stop being stubborn and leave quickly okay lover boy.
Miqewa yayi a daddafe hannunsa riqeda gefen cikinsa dake ciwo sosai ya nufi motarsa.
Saurin juyowa tayi zuciyarta na karyewa ganin tafiya zaiyi ya barta dasu mujahid 'din.
Kallonta yayi yaji duk jikinsa yayi sanyi sbd tun yanxu yafara gane bai cancancetaba tunda har yakasa samun qarfin ku6utarda ita.
Motarsa ya shiga daqyar ya iya Zama ya tada ita yayi ribas ahankali.
Saiti yayi dasu ya taho a guje yayo kansu a gigice sukabar gurin yadaki motarsu yayi saurin fitowa tareda bu'de Mata seat din gaba ganin tatsaya kallonsa ya'daga hannunsa yakamo nata yasakata cikin motar sukabar gurin da gudu.
Tunda yakamo hannunta shi take kallo ko qyaftawa Bata iyayi..
Did he take all this risks to save me from them..
Daf dazasu Isa cikin gari taga ahankali yafara rage gudu saikuma ya gangara ya tsaya tareda zubewa jikin sitirin motar a sume.
A gigice takallesa takalli waje taga hadari ya ha'du sosai har anfara yayyafi alamun saukowar ruwan.
Fitowa motar tayi hankalinta duk atashe saikuma ga ruwan sama sun 6arke masu qarfi sosai.
Bata damu da qarfin ruwanba ta tsaya bakin titi neman taimako Amma Sam Babu alamar mota bare tasaran samun taimako ga ruwan tuni sunyi Mata jagaf.
Dawowa motar tayi taga shima kusan duk ya jiqe sbd glass 'din dake sauke.
Wata muguwar rawar sanyi taga jikinsa nayi sbd ruwan dasuka dakesa Nan take wahala ta canxashi taga yanda ruwan ke dukansa Yana Jan numfashin wahala gashi Sam takasa iya tada glass 'din motar Sai kawai ta fito tazagayo bakin windon dayake ta tsaya ta tare Masa ruwan na dukanta jikinta na rawar sanyi amma bazata iya bari ruwan yaci gaba da dukansa ba.
Kusan awa 'daya da rabi ana ruwan kafin suka tsagaita zuwa time 'din daqyar take iya bu'de idonta sbd sanyi da mugun zazza6i Mai qarfi.
Bu'de idanuwansa yayi daqyar ya kalleta yaji wata muguwar zazzafar soyayyarta na sake shigarsa ahankali ya tashi zaune jikinsa na rawar sanyi ya fito tareda kamota daidai lokacinda take qoqarin zubewa yasaka cikin mota tareda kwantarda ita ya tayar da glass ya kunna 'dumi.
Ahankali ya 'daga wayarsa yakira wayar Murphy akashe kafin yakira mum 'dinsa yafada Mata inda yake murya na rawa.
Fuskantar juna sukai ya qura Mata ido Yana qoqarin yaqar tsananin ciwo da zazzan zazza6in dayakeji.
Rintse idanuwanta tayi sbd Bata iya cigaba da kallonsa ko jure nasa kallon.
Ahankali ya bu'de baki cikin qaramin sauti yace,
I love you ayeeshah.
Bu'de idanuwanta tayi da sauri hawaye na taruwa acikinsu...
Kafin yakuma yunqurin wata maganar aka qwanqwasa glass din motar.
Shiyayi qarfin halin 'dagowa yaga wani mutum da wata tsohuwar bus ya juyo ya kalleta yaga idanuwanta a rufe hawaye na tsiyayo da qarfi.
Cikin sanyin murya ya kalli mutumin yace,
Awuce da ita cikin gari.
'dagowa tayi takallesa ya lumshe Mata idanu ta bu'de motar ahankali ta Fice jikinta a sanyaye zuciyarta na tsananta duka tashiga bus din suka wuce..
Harsun fara tafiya tajuyo takalli motarsa saita rintse idanu wasu sabin hawaye masu zafi suka gangaro mata.
Mamuhđź’‹
_dont forget to follow, vote and comments_
[7/12, 7:40 AM] ‪+234 902 378 7901‬: *_MAMUH GEEE_*
_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida...._
_Viawattpad@mamuhgee_
*15&16*
Kodasu mum suka iso gurin ya Dade da fita haytacinsa Dan dama Yana daurewane gaban ayshah sbd kar abin kunyar yayi Masa yawa anyi Masa duka gabanta Kuma ya ciwo yayi Masa rigis gabanta.
Hankali tashe mum tasa akai asibiti dashi bayan ankira police sun fara bincike agurin Dan ga alamar duka Nan ajikin 'dan nata.
Kodata Isa gida kasa tu6ewa tayi ta shige qarshen gado ta zauna tareda takurewa tana kuka ahankali sbd zazzafan baqon alamarin dataji yana shiga tareda Kama kowace kusurwar jijiyar dake aiki cikin zuciyarta.
Zazza6i ne Mai qarfi itama yakamata Nan take Wanda yasa hankalinsu husna tashi Amma ta hanasu fadawa iyayensu.
Kwananta 'daya da yini tana fama da zazza6i da rashin sukunin zuciya.
Gudun zargi da tambaya yasa tashirya tacigaba da zuwa makaranta.
Koda ya farfado kansa ciwo yake sosai Amma haka ya nunawa mum 'dinsa yaji sauqi dole aka sallamesu duk da mura yake sosai sbd dukan da ruwa sukai Masa.
Lumshe ido yayi Yana tunano ko awane Hali ayshah take ita data fisa Shan dukan ruwan.
A daddafe yayi kwana biyu agidan mum na jinyarsa a kwana na ukun ya shirya yace yaji sauqi makaranta zashi.
Kallon mamaki mum tayi Masa tace,
Sweetheart you're not fully recovered... you're still weak.,,I can see it in your eyes.
Atishawa Mai qarfi yayi tareda saka farin lallausan handkerchief ya tare hancinsa kafin ya 'dago ya kalleta da lazy eyes dinsa yace,
Mum I'm fine.,,I promise.
Cikin kulawa da yar damuwa tace,
Ok my sweet boy,,but please take care..
Yes mum,,,,yace tareda 'daukar wayarsa da key 'din sabuwar motarsa ya sauko ya fice batareda ya tsaya bawa Davina amsar Murphy datake tambayarsa ba Dan shima nemansa yake Amma haryanzu wayarsa Bata zuwa.
Duk inda yake sakaran zai ganta ya Duba bai gantaba Nan take yaji jikinsa yafarayin sanyi..
Tunda yafara nemanta tagansa tayi saurin 6oyewa bayan wata mota tana kallonsa zuciyarta a sanyaye Amma hakanan taji dadin ganinsa yaji sauqi duk da dai tana iya ganin baida wani kuzari.
Tundaga ranar tafara 6oye Masa duk da baqaramin tirsasa zuciyarta takeba gurin aikata hakan.
Tun mum 'dinsa na 'daukar abin wasa saigata hankalinta yayi mugun tashi sbd wata irin damuwa da muguwar Rama data sako Nik 'din agaba sbd rashin ganin ayshar gashi yakasa samun ko wane information akanta.
Sam shida kansa baisan son da yake Mata yakai hakaba Sai yanzu..
Iya bincike da lallashi mum tayi Masa yafa'da Mata damuwarsa Amma yaqi.
Yau tun 6 na safe yatafi makarantar kosu mum basusan da fitarsaba..
Bakin bus stop ya Parker motarsa zuciyarsa sanyaya da damuwar dayake ciki game da ita Dan yau jiyake kozai kwana ya yini agurin saiya ganta zai iya samun sukunin masifar da zuciyarsa take ciki.
Ahankali bacci ya 'daukesa sbd rashin baccin dayake fama dashi na kwanakin.
A kunne yabar motar sbd Ac.
Sai 10 ta iso makarantar ana ajesu busstop ta fito ta nufi hanyarta cikin sanyin jiki sbd rashin kuzarin da itama take fama dashi.
Kamar daga sama ta hangosa kwance Yana bacci cikin motar yayi matuqar ramewa saitaji zuciyarta na neman karyewa tayi saurin juyawa tabar gurin.
Qarfe biyar na yamma ta gama lectures ta fito a galabaice sbd ranar azumi take..
Cak ta tsaya sakamakon ganin har lokacin Yana gurin saidai wannan time 'din yafito jingine yake jikin motarsa yayi wani irin fadawa sbd yunwa da wahala Amma yaqi tafiya.
Kamar ance ya juyo Sai kawai idonsa yashiga cikin nata yayi saurin miqewa tsaye daidai Yana kallonta amarairaice.
Dakewa tayi ta matso tareda ra6asa ta wuce tashige bus tareda sunkuyar da kanta Dan karma su hada ido.
Binta yayi da lazy eyes 'dinsa suna taruwa da ruwa sbd tunanin qila wani laifi yayi Mata.
Matsowa yayi da sauri zai shiga bus 'din cikin tsautsayi yaron direban motar ya turesa sbd already motan yacika ya fa'di qasa cikin ruwan saman dake taruwa awurin Nan take kayansa da jikinsa ya lalace bai tsaya dubawaba ya miqe da sauri zaikuma matsowa aka tada motar sukabar gurin.
Motarsa yashiga da sauri yabi bayansu saigasu har anguwar su ayshah 'din.
Tana fitowa motar tagansa Yana qoqarin parking ya fito.
Saurin wucewa tayi batareda takuma kallon inda yakeba.
Biyota yayi da gudu batareda ya tsaya kashe motarsa ba..,,
Sauri ta qara gabanta na tsananta fa'duwa daf da zata shiga kwanar layinsu saiga ya Umar...
Wata mummunar fa'duwa gabanta yayi ta saci kallon bayanta taga Sai zubo sauri yake Dan ya iso wurinta ta rintse ido zuciyarta na tsinkewa da tausayinsa.
Kallonta ya Umar 'din yayi Yana son karanto firgicin daya gani tattare da ita.
Kamar ance ya Duba bayanta saiya hangosa Yana zubo sauri tareda tsalle Yana qoqarin fa'duwa sbd agwagi dasuka biyosa Sai tsalle yakeye Yana kallota karta 6ace Masa.
Kallonta Umar 'din yayi cikeda zargi kafin yayi Mata alamar ta wuce da ido.
Sum sum ta wuce Amma saita kasa shigewa konar ta juyo.
Manyan agwagin dasuka fi girma Umar ya 'dauka tareda jefa Masa cikin baqin ciki da takaicin ganinsa.
Baya yayi da sauri cikin tsoron agwagin cikin rashin sa'a Ashe yakai kwata sai gashi zaune cikinta.
Batareda 6ata lokaci ba ya yunquro yataso har lokacin idonsa nakan kwanar datake la6e tana kallonsa.
Qoqarin wucewa yake cikin takaici Umar ya fixgosa tareda wurgar dashi ya nunasa da yatsa cikin xafi yace,,
Zanbarka yau katafi Amma wlh duk nakuma ganin wannan kafirar fuskar taka cikin anguwar Nan saina yanka maka ita da kwalba..
Juyawa yayi zai wuce tayi saurin barin gurin tayi gida da sauri zuciyarta na wani irin nauyi.
Mamuhđź’‹
_dont forget to follow, vote and comments_
*_MAMUH GEEE_*
_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida...._
_Viawattpad@mamuhgee_
*17&18*
koda Nik Yakoma gida ya tsaya gaban mirror yakalli kansa saiyaji hawaye sun ciko idanuwansa..
Tubewa yayi ya jefo kayan qasa ta windown dakinsa ya fa'da toilet yayo wanka Banda zazza6in wuya Babu abinda yakeji.
A daddafe ya saka kayan bacci black yashige bargo ya kwanta jikinsa na rawar sanyin zazza6i..
Qarfe Tara mum tashigo dakinsa Finn na biyeda ita tana ganin yanda yake shaking cikin bargo ta qaraso da sauri tana Kiran sunan Jesus..
Tallafosa tayi taji jikinsa da mugun zafi ta kalli Finn cikin tashin hankali tace,
quickly call Dr Finn.
Fiddo wayarsa yayi daga aljihu ya latsa Kiran Dr cikin gaggawa.
Shigewa yayi jikin mum 'dinsa yana fiddo numfashi ahankali cikin azaba yace,
Mum I'm fine,, it's just a fever,,I will get better soon there's no need to call the Dr....
Cikin karyewar murya kamar zatayi kuka tace,
Quite.. you're not fine my love and it's not a normal fever,, you're hiding something from me,,I can feel it.
Lumshe idanuwa yayi cikin sanyin murya qasa qasa yace,
Mum,,,,mum..i.i..I'm in love....I love someone.
Wat""""tafa'da da qarfi tareda kallon fuskarsa cikin rashin Jin dadi tareda rashin na'am da zancen cikin damuwa tace,
You can't be in love my boy,, you're too young for that and I ca....
Katseta yayi cikin sanyin murya da cewa,
I love her so very much mum,,,I can't even imagine my life now without her mum...mum..I really want her for myself,i love her mum..I madly love h....
Rungumesa tayi cikin tausayinsa sbd dukkanin alamu sun nuna Mata baqaramin so yakewa kowaceceba..
Share Masa hawaye tayi tana adduar Allah yasa ko wacece kada tayi amfani da wannan zazzafar soyayyar da Nik yake Mata ta cutatar Mata da yaro.
Kwanansa biyu Yana zazza6i Mai zafi ko qasa baya iya saukowa bare ya fita,,
Mum dinsa kuwa hutu ta dauka Dan bawa 'dan lelenta kulawa hakama 'yan uwansa wannan karon dukkaninsu sun matuqar tausaya Masa sbd yayi matuqar sanyi kamar ba Nik ba danko irin muguwar sakuwar dayake acikin gidan ta rage kullum Yana kwance.
Duk iya yanda take danne damuwarta saidata bayyana a jikinta sbd ramar datayi su husna sunyi faman tambayar harsun gaji Amma alamarin bamai kar6uwa bane ko a zuciyarta bare fa'duwa.
Kwananta biyu kotaje makaranta Bata gane komai sbd dukkanin nutsuwarta ta tarwatse Wanda Sam takasa samun kuzari ko qarfin tattarota.
Ahaka take lalla6awa har tsawon kwana biyu.
Yau Bata samu bus da wuri ba shiyasa tayi yammacin dawowa gida,,
Ahankali take tafiya cikin nutsuwa duk da kwanakin nutsuwarta rawa take,,
Daf dazata shiga kwanar layin gidansu taga su ya Umar taredasu Yaya abbakar kusan su shida kowanne da abun duka jikinsu har rawa yake bama Kamar ya Umar 'din da idanuwansa yafi nakowa rufewa da 6acin Rai.
Mummunar fa'duwa gabanta yayi tai saurin sunkuyar da Kai cikin tsananin fargaba..
Kallonta ya abbakar yayi cikin 'daga murya yace,
Meyasa kikai yamma sosai yau?
A sanyaye tace,
Bansamu bus bane yau da wuri.
Shikenan maza wuce gida.
Wucewa tayi a hankali gabanta na tsananta fa'duwa,,
kaman daga sama saitaji ya Umar cikin zafi Yana cewa,,
Duk inda yake Yana guraren Nan sbd da idona nagansa Yana tambayar yara Kuma na tabbatarda akwai abinda yake qullawa.
Cak ta tsaya sbd qafuwanta dasuka 'dau rawa..
Taji ya sani yace,
Wlh Nima yau nayi ido hu'du da shegen kafirin Nan saina karairaya Masa qafafuwa Dan ya koyi tsaya matsayinsa.
Yawu ta ha'diye da qarfi jikinta na rawa sbd fahimtar datayi kenan Nik nacikin layin,,Kuma ta tabbatarda ita yake nema....
Juyowa tayi takalli mugayen gororin dake hannunsu taji hankalinta yayi mummunan tashi Dan tasan duka 'daya za'ayiwa Nik da wannan bazai qara sanin inda kansa yakeba.
'daga kai tayi cikin bugawar zuciya Sai gasa ta hangosa kusada wata qaramar matsatsiyar kwana Yana tahowa..
Wani mumman yawun tashin hankali ta ha'diye tareda juyowa takalli su ya Umar taga ba 6angaren suke kallo ba Amma gaf sukeda juyowa..
Cikin wani irin zafin naman dabatasan tanadashiba tayi saurin Isa gabansa daidai ya Umar ya juyo kawai saita janyosa cikin kwanar da qarfi Saida ya fa'do jikinta.
Wani irin kallo yake Mata cikin Jin da'din ganinta qayataccen murmushi na fita a fuskarsa..
Ahankali takallesa qwayar idanuwansu ta ha'du tai qasa dakanta gabanta na fa'duwa cikin sanyi da laushin muryar tace,
Why are you doing this?
Yana kallon cikin idonta yace,
Because I love you..
Kalmar ta daketa matuqa ta rintse idanuwanta cikin sanyi tace,
It's impossible...so please stop following me...yo don't know wat trouble you're getting your self into..
Cikeda sonta daya rufe Masa ido yace,
I'm ready to face anything for your love..
Girgixa Masa Kai tayi idonta na gangaro da hawaye tace,
We can never be together can't you get it,,,,we are from a different rel....
Shihhhh yafa'da tareda matsota sosai Yana kallon idanuwanta da lazy eyes 'dinsa murya qasa yace,
I'm ready to be like you if that's will b the only way for me to get you..,to be with you...
I love you ayeeshah..
Stop please''''''tafada da 'dan qarfi kuka na qwace Mata..
Kaman zaiyi kuka shima murya na rawa yace,
I love you ayeeshah,,, even if I wanted to get it out of my head I can't...
Muryoyinsu ya abbakar taji suna kusanto gurin tayi saurin 'dagowa ta kallesa cikin kuka tace,
Please go from here,, leave please...
Gyara tsayuwa yayi Yana kallon hawayenta dake ta6a zuciyarsa yace,
I'm not leaving until you tell me why you are so worried like this...
and this tears???'''yafada Yana kallon yanda hawayen ke gangarowa..
Karkace Kai yayi cikin son tabbatarda abinda yake zargi murya na rawa yace,
Ayeeshah,,,do you have any feelings for me too???
Rintse ido tayi cikin qaguwa tace,,
No please go...
Jada baya yayi yace,
No I won't go anywhere...
Matsowa tayi cikin magiya da kuka tace,
They will beat you black and blue... please pls leave.
Kusantota yayi sosai har numfashinsu na ha'duwa Yana kallon cikin idanuwanta da lazy eyes 'dinsa dasuka cikada hawaye yace,
Idan har dukan dazasumin zaisa natabbatarda you love me too then so be it..
Zan jira suzo.
Kuka tasaki ahankali hartana ciccika Nan take jikinsa ya 'dau rawa cikin hawaye yace,
Am sorry my love,,,I know I'm being stubborn but I can't help it because *i love you*......
Kalmar data shiga kunnensu ya Umar kenan daidai lokacinda suka kawo gurin.
Mamuhđź’‹
_dont forget to follow, vote and comment_
*_MAMUH GEEE_*
_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida...._
_Viawattpad@mamuhgee_
*19&20*
Zafin zuciya da bugawar zuciya ne suka mugun tasowa ya Umar ya rintse idanuwansa Dan Daman tuni ya fara zargin ayi hakan tun kallonda yaga Nik 'din yayi Mata a station lokacin....
Rufewa idanuwansa sukayi ya qarasa gurin zuciyarsa na tafasa bai tsaya komaiba ya 'daga qaqqarfan hannunsa ya shararawa Nik wani gigitaccen Mari saiga jini ya 6alle ta hancinsa...
Saukar wani mugun zafi taji a zuciyarta tayi saurin rintse ido ta bu'de hawaye suka gangaro Mata ta 'dago a cikin karaya ta kallesa saitaga ko motsi yaqi yi ita ya qurawa lazy eyes 'dinsa dasukai ja sbd azabar Mari ko qyaftawa bayayi...
Fixgota taji anyi da qarfi ta 'dago jajayen you takalli ya Umar 'din ta bu'de baki zatayi magana a zuciye ya mare bakin da qarfi...
Durqushewa tayi qasa cikin azaba Amma tabbas azabar da zuciyarta ke ciki taci wannan 'dan Marin..
'dagowa tayi idanuwan Nik suka sauka kan 'dan jinin daya fito gefen bakinta sbd Marin yayi saurin zubewa gabanta jikinsa na rawa hawaye na taruwa idonsa murya na rawa yace,
You're hurt ayeeshah....
Ya 'daga hannu ya nufi inda jinin yake.....
Cikin zafi ya Umar ya riqe hannun tareda mur'dewa su ya abbakar kuwa Nan suka rufesa da duka.
Rintse idanuwa tayi hawaye na tsiyaya akaro na farko dataji wata mummunar qiyayyar ya Umar tana shiga tareda Huda duk wasu jijiyoyin dake aiki acikin jinin ajikinta.
Miqewa tayi batareda tajuyoba takalli irin dukan dasuke Masa ta fara tafiya cikin damuwa tabar gurin.
'dakinsu ta nufa direct batareda ta leqa ko inaba ta gaida iyayensu kaman yanda tasaba.
Kodata shiga su husna basa 'dakin suna 6angaren mama sakina Dan can sukafi Zama a irin wannan time 'din..
Zubewa tayi bayan qofa tareda sakin wani irin kuka ahankali tana dafe zuciyarta datakejin kaman xata tarwatse...
Hayaniyace ta kaure cikin gidan Nan take tani kowa na fitowa sbd hayaniyarsu ya Umar hardai shi da muryarsa tafi tashi cikin 6acin Rai...
Tanajin an ambaci kafiri ta lumshe idanuwa hawayenta na tsananta zuciyarta na da'da karyewa sbd batasan mummunan halinda suka sako Nik acikiba...
Da daddare bayan tayi sallah Bata tashi kan sallayarba anan ta qudundune sbd damuwa da zazza6in datakeji mai tsanani...
Nuratu ce tashigo 'dakin jiki a sanyaye ta zauna kusada ita takalleta murya asanyaye tace,
Anty ayshah su baba malam na Kira..
'dagowa tayi takalli nuratu da jajayen idanuwanta a sanyaye tace,
Sun kashesa ko nuratu?
Girgixa Kai nuratu tayi cikin tausayin 'yar uwarta tace,
Aa,,,,amma dai abun yayi Muni...
Kuka tasaki ahankali zuciyarta naci gabada tsananin zafi..
Anty ayshah da gaske soyayya kuke?
Batareda ta 'dagoba cikin kukan ta girgixa Kai...
Kafin ta miqe cikin sanyin jiki ta fito 'dakin ta nufi babban palon baba malam Dan tasan yanxu kowa nacan ya halarta..
Kanta a qasa tashiga tareda rakubewa ta zauna qasa..
So 'daya ta 'dago taga yanda kowa ke Mata kallon 6acin rai,qyama da tuhuma..tayi saurin qasa da kanta Tana danne hawayenta.
Cikin 'daurwar fuska da zafi baba alhaji yace,
Ayshah meye ha'dinki da wannan arnen.
Cikin sanyi da nutsuwa tace,
Babu komai..
A hasale babanta yace,
To meyasa ya biyoki yau harkuka ke6e?
Lumshe ido tayi ta bu'de sbd akaro na farko kenan dazatayi qarya murya a tausashe tace,
Nazo wucewa ne Sai muka ha'du shine yakeson tambayana nace bazan tsayaba.
Sake zaburowa baba alhaji yayi yace,
To su Umar sunce sun gani sonki shi yaron yakeyi.
Girgixa Kai tayi tace,
Ni banta6a sanin wannan ba hasalima yaza'ayima ta yiyu tsakanin ni dashi ba yare 'daya ba,
Ba addini 'daya ba..
Sai lokacin baba malam yayi gyaran murya sbd anxo gurinda yakeso Kuma yayi na'am da abinda ta fa'dan ya kalleta yace,
Ayshah???
Na'am'''tace a sanyaye batareda ta 'dagoba yace,
Na yarda dake nasan bazaki iya ta6a sa6a Mana ba ko take doka da umarnin mu Dan haka ga garga'di da umarni Mai qarfi,,,,daga yau ko hanyar dayabi karki Kuma kallo bare har wata magana ta hadaku harma afara Kuma irin wannan zargin Dan ni ko maganar wani kafiri banaso acikin zuri'ata bare har irin wannan mummunar zancen ya tabbata..
'dago Kai tayi ta kallesa tareda cewa,
To baba insha allah.
Miqewa tayi ta bar palon ahankali ya Umar yabita da kallon tuhuma danshi yana ganin abubuwa da dama datake 6oyewa Amma saiyasa ta bayyanasu da kanta agaban kowa na gidan.
Koda wasa dama batai gangancin tunanin bacci zaizo Mata ba hakanan ta kwana cikin tunanin wane Hali Nik yake ciki.
Koda gari ya waye taje gaida umminta saitaji duk jikinta ya da'da sanyi sbd ganin ga dukkan alamu ma umminta na cikin tunani da fargabar Kar zancen jiya ya tabbata.
Gaida ummin tayi cikin sanyi tareda kallon nuratu dake Mata kallon tausayi tana gaisheta.
Amsawa tayi tareda kallon ummi tace,
Ummi zan tafi makaranta..
Cikin kulawa da sanyin jiki ummin tace,
Ayshah Dan Allah karki bari zuciya takaiki ga Dana sani da muguwar rayuwa.
Hawaye taji sun taho Mata Dan tasan saidai Kuma wani ceto daga Allah Dan Mai Sha tarigada Tasha.
Zama tayi tareda kar6ar cup 'din kunun tsamiyar da ummin ke miqo Mata ta kar6a badan zata iya sha ba saidan kadata kuma bawa ummin damar wata damuwar.
Abbanta ne yashigo tareda sallama ta sunkuyar dakai ta gaidasa cikin sanyin murya..
Amsawa yayi kadaran kadahan kafin ya zauna kan tabarmar kusada ummin Yana cewa,
Ki qara kiyayewa sbd gudun jawo fitina da tashin hankali tareda 6acin suna acikin zuriar gidan nan Dan yanxu ina amfanin irin hakan tunda shi yaron sun Masa mummunan duka sun barosa can kangon gidan bayan layi sbd......
Wata mummunar sarqewa tayi tafara tari Mai qarfi sbd gigitar da zancen baban yasata.
Saurin miqa Mata ruwa nuratu tayi tana Mata sannu..,
Baba da ummi kuwa kallo suka bita dashi fa'duwar gabansu na tsanantuwa .
Miqewa tayi ahankali tace,
Na tafi..
Allah tsare ummi tace a gajerance baba kuwa ko amsa Mata baisamu yiba sbd damuwa da fargaba.
Bakin titi ta tsaya cikin zurfin tunanin rashin sanin abin yi....
Kusan Rabin Rabin awa tashare bakin titin Dan Sam zuciyarta taqi barinta tafiya...
Juyawa tayi ta canza hanya zuwa bayan layin gidansu.
Bakin wani kangon gida ta tsaya da kusanma anmaidasa bola sbd dadewar da'akayi ba'a cigaba da gininsaba.
Jujjuyawa tayi taga Babu mutane sosai agurin saitayi saurin shigewa gabanta na tsananta fa'duwa Dan jikinta har rawa yake.
Cak ta tsaya tareda zubewa qasa ba shiri...
Kwance yake baisan inda kansa yakeba cikin jini duk gabaki 'daya kamannunsa sun canxa da sbd duka da wahala.
Da rarrafe ta qarasa gurinsa tareda tallafosa jikinta ta fashe da kuka Mai qarfi tana Kiran sunansa.
Kuka take sosai kamar ranta zai fita Dan tabbas batasan sonsa yayiwa zuciyarta mugun kamuba Sai yanxu data gansa cikin wannan mummunan halin....
Jin tayi kamar ya motsa tayi saurin 'dagowa suka ha'da ido sabbin hawaye suka gangaro Mata ta fara girgixa Kai cikin kuka tace,
Why....why...why Nik,,,,why did you choose to make me suffer by seeing you like this????
Duk da a wahalce yake danko hannunsa bai iya motsawa Amma ganinta yakawo farin ciki sosai acikin ransa barema dayaga halinda tashiga ganinsa haka..
Wani mugun yunqurin amai yayi saiga jini na fitowa ta bakinsa..
Zaro manyan idanuwanta dasukai ja tayi takalli jinin takuma maida kallonta kansa taga Yana numfashi sama sama
Da gudu ta fito tareda mantawa da wani tsoron Kar aganta tasamo taxi itada mai taxi 'din suka sakasa mota..
Baya tazauna taredashi duk da numfashinsa zuwa time 'din yakusa 'daukewa...
Damqe hannunta yayi cikin nasa hawayen wahala na gangaro Masa murya qasan maqoshi yafada Mata sunan asibitin dazata kaisa.
Shihhhhhhhh don't talk pls""""''''''tace Masa qasa qasa cikin kunnensa tareda qara damqe hannunsa tanajin zafi da ra'dadin ciwonsa na shiga zuciyarta.
Asibitin daya fa'da can takaisa suna zuwa akai emergency dashi Dr naganinsa yayi saurin zare farin glass 'dinsa cikin tashin hankali da mamaki yace,
Oh my God,,Nik ne wanna ai...
Fitowa yayi tareda kallon nurse 'din data biyosa yace,,,
Waya kawo patient 'din dake ciki?
Ada sauri ta nuna Masa ayshah dake zaune ta sunkuyar dakai sbd kukanta dayaqi tsayawa Dan yanda taga hankalin nurses 'din dasuka kar6esa ya tashi tasan ba qaramin Hali Nik 'din yake ciki ba.
Qarasowa gabanta Dr yayi tareda kallonta dakyau kafin cikin mamaki yace,
Kece Kika kawo Nik?
Kai ta 'daga da sauri cikin tsoron Mai zaice yasamu Nik 'din.
Kallon tuhuma yakuma jifanta dashi kafin yace,
Ina muma 'dinsa da....
Bata Bari ya qarasaba cikin fargaba tace,
Please Dr kafadamin idan zaiji sauqi..
Yes zai zamu sauqi but....
Ok Dr ngd Amma Dan Allah idan kanada number mum 'dinsa kafa'da Mata.
Share hawayenta tayi tajuya batareda tabari yakuma wata magana ba.
Kwance take nurse 'din da'aka 'dauko Mata tun Daren jiya Dan kulada ita tana zare Mata drip 'din dake hannunta har lokacin idanuwanta dasukai mummunar kumbura Basu daina zubar da hawayeba..
Finn ne akusada ita ya kwantarda kanta kan kafa'darsa Yana shafa kanta alamar rarrashi.
Mr Aiden ma daya iso da safen zaune yake kusada ita Davina na zaune kusadashi tashige jikinsa...
Dukkaninsu kallo 'daya zakayi musu kasan mummunan alamarine yasamesu Mai kamada mutuwa.
Waya Mr Aiden ya Kuma 'dagawa akaro na ba adadi yakuma Kiran police yayi Koda akwai wani update Amma still Babu.
Wayar mum ce tafara ringing Amma ko qyafta idanuwanta batayiba bare ta motsa...
Finn ne yayi qarfin halin 'dauka tareda saka loudspeaker...
Gabaki 'dayansu atare suka zabura Jin abinda Dr yafada mum kuwa tuni takai qofa jiri na 'dan 'dibarta Amma batajin zata iya jira.
Da sauri Finn ya riqota suka 'dunguma mota gabaki 'daya Sai asibitin.
Tashin farko da mum taga halinda Nik 'dinta ke ciki Sai ganin sukayi ta yanke jiki Saida dadinsu yayi saurin riqota ta fashe da kuka tana kallon yanda Nik dinta ke numfashi cikin azaba da wahala duk da har lokacin tashiba.
Saidata shaqi kukanta kafin ta miqe Finn ya Kama hannunta suka nufi office 'din Dr suka bar dad da Davina a room 'din.
Dogon bayani Dr yayi musu akan Yana tunanin mummunan dukane akayiwa Nik 'din Wanda harya ja Masa internal bleeding Dan qila andaki kansa.
Share hawayenta tayi ta Kuma kallon Dr tace,
Where did you find him I mean who brought him here?
It was a lady,,, she was all covered by.....I think she's a Muslim.
Tafasa zuciyar mum tafara Nan take 6acin ranta da baqin cikinta suka danne damuwar dayake ciki...
Miqewa tayi tareda kallon Finn dashima yacika yayi fam dajin cewar ninja lady ce tayiwa Nik wannan mummunan aikin.
Kallon Finn tayi bayan sunbar office 'din cikin tuquqin da zuciyarta keyi tace,
I want them to pay double for wat they've done to my poor darling boy...make them cry and regret their lives.
Yes mum""""yafada Yana fiddo wayarsa aljihu Dan making call.
Da daddare ya farka Nan dukkanin familyn suka kewayesa suna basa kulawa cikin so da qauna musamman mum da kamar tayi ihu takeji duk ya motsa taga ya rintse Ido alamar azaba.
Da daddare bayan Finn da Dad 'dinsa sun taimaka Masa yayi wanka ya saka kayan bacci ya kwanta mum ta lullu6esa ya lumshe idanu alamar bacci duk suka fito Dan tafiya gida.
Lumshe idanuwansa yayi tareda sakin murmushin da iyakacinsa zuciya ya tuno baby face da fararen idanuwanta lokacinda take kuka tana Kiran sunansa.
Ahankali cikin maqoshinsa yace'
I love you my sweet ninja lady...
Washe gari ma data fito kasa wucewa makaranta tayi saita samu kanta dabin umarnin zuciyarta ta nufi asibiti gabanta na tsananta fa'duwa Amma ba yanda ta iya Dan batajin zata iya Kai yamma batareda taga halinda yake ciki ba..
Baba alhaji da baba shehu tareda Yaya Ahmad da Yaya abbakar ne suka dawo daga gurin wani taron fatawa...
Daf dazasu Kai anguwarsu wata baqar mota Tasha gaban taxi 'din dasuke ciki kafin suyi want motsi qartin maza majiya qarf suka fito da bindigogi suka tasa qeyoyinsu baba alhaji dayaso gardama aka 'dibesa wani mummunan Marin dayasashi ha'diye maganar dayaso yi sukabar gurin da mugun speed.
Kodata isa asibitin Kai tsaye emergency ta nufa cikin sauqi saiga 'daya daga nurses 'din dasuka kar6esa a jiyan ta tareta cikin sanyin murya ta tambayeta room 'din dayake.
Nuna Mata tayi ta nufi 'dakin gabanta na tsananin bugawa.
Nesa ka'dan da 'dakin ta tsaya tareda qurawa qofar 'dakin ido tana qoqarin controlling matsuwarta tason ganinsa.
nurses biyu taga sun fito 'dakin mace da namiji tayi saurin qarasawa ta tare macen cikin sanyi tace,
Please patient 'din dake ciki yaji sauqi kuwa?
Kallon up and down tayi Mata kafin tace,
Eh Amma dai yanxu mun Hana kowa shiga gurinsa har family 'din sbd munason yasamu isashen hutu.
Bin bayan nurse 'din tayi da kallo bayan ta wuce tana tunanin kenan ba kowa a 'dakin.
For the first time taji wani farin ciki bayan tsawon lokaci..
'dakin ta dosa gabanta nacigaba da fa'duwa.
Tsayawa tayi bakin qofa tareda rintse ido tasaki numfashi ahankali tareda tattaro Yar nutsuwa ta tura qofar ahankali.
Cak ta tsaya sbd idanuwanta dasuka sauka cikin nasa Yana kwance ya qurawa qofar Ido kamar Daman yasan itace zata shigo..
Tashi zaune yayi batareda ya 'dauke idanuwansa cikin nataba..
Har ya iso gabanta Bata motsaba sbd garkuwar jikinta da idanuwansa suka kaririya..
Hannunta ya riqo ya jawota ciki ya rufe qofar har time 'din batayi wani qwaqwaran motsiba.
Zaunar da ita yayi bakin gadonsa tareda durqusawa gabanta idonsa cikin nata yace,
Ayeeshah did you came to hia see?
'daga Masa Kai tayi sbd batada kuzarin magana..
Wani qayataccen Murmushi yasaki harsaida haqoransa suka bayyana ka'dan..
Tasowa yayi ya zauna kusada ita yakai bakinsa saitin kunnenta da wata kasalalliyar murya yace,
Did you love me ayeeshah?
Shiru tayi tareda sunkuyar dakai qasa.
Murmushi yakuma saki yace,
Please talk to me ayeeshah..
Juyarda Kai tayi still batace qalaba.
Murmushi yayi tareda zubewa qasa ya riqe kansa Yana juye juye cikin tsananin azaba.
A ki'dime ta sauko gabansa tana Kiran sunansa cikin tashin hankali da tsoro Amma saitaga Yana qara mimmiqewa saikuma yayi dif ba alamar numfashi ataredashi.
Kansa ta rungumo batareda tasaniba tafara kuka tareda Kiran sunansa...
_*I love you Nik*_,,,pls wake up..
_*I love you so very much*_.....
Miqewa tayi da sauri Dan kirawo Dr taji anriqo hannunta tayi saurin juyowa sukai Ido biyu Yana sakar Mata wani hot smiling...
Kallon mamaki take Masa da sauran guntayen hawayenta Dan tagano da gangan yayi hakan Dan ta fa'di abinda yake son ji..
Wata fitinanniyar kunyace ta rufeta tayi saurin juya Masa baya tana sauke numfashi ahankali...
Zagayowa yayi tareda matsota sosai danshi Sam bai 'dauki hakan komai ba...
Matsota sosai yayi jikin bango tareda duqo da fuskarsa daf da Tata har numfashinsa na mugun ha'duwa ya 'daga hannu ahankali ya cire Mata niqaf tai saurin rintse ido... fuskarta na bayyana wani sahirtaccen murmushin daya Kuma tafiya dashi.
Bakinsa yakai daidai kunnenta cikin wata kasalalliyar murya yace,,
You finally said it my love...
Sake tamke idanuwanta tayi sbd Jin kalar muryar dayayi amfani da ita ba qaramin shigarta tayiba.
Kallon dogayen eye lashes 'dinta yayi yace,
Will you marry me ayeeshah...
'daga Masa Kai tayi ahankali sbd tuni ta manta da wani banbancin yare da addininsu.
Su baba alhaji kuwa wani qaton gida aka kaisu suna shiga aka 'daddauresu tareda jiqasu tsaf da ruwan qanqara kafin aka fara jibgarsu baji ba gani.
Mamuhđź’‹
*_MAMUH GEEE_*
_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida...._
_Viawattpad@mamuhgee_
*21*
Tsayawa Finn yayi akansu Yana kallonsu cikin wulaqanci ganin har lokacin da sauransu ya juyo ya kalli tiger yayi Masa alama da ido...
Kallon yaransa tiger yayi Sai aka Kuma 'debo ruwan qanqanra a qaton bucket aka Kuma jiqasu tareda cigaba da dukansu..
Iya dakuwa Kam sun daku bama kamarsu Yaya abbakar dasuke samari anfi dukansu duk da dai Suma su baban ba a raga musu ba...
Sake kallonsu Finn yayi yaga sun bugu yasaki murmushin qeta tareda fiddo wayarsa ya 'daukesu yaturawa mum kafin yakirata yace ta duba..
Dariyar Jin da'di tayi lokacinda taga hoton takira tace a kaisu inda aka 'daukosu a watsar..
Zamewa tayi daga rumfar dayayi Mata takoma bakin gado ta zauna kanta a qasa tana kallon dogayen fingers dinta..
Dawowa yayi kusada ita ya zauna shima ya qurawa hannun nata ido..
Ayshah please lets get married before informing our families about us...
'dagowa tayi ahankali takallesa ta kawar da idonta kafin ahankali tace,
No Nik...I can't marry you without my family's approval.. besides that I'm Muslim you're Chris.....
Katseta yayi da cewa,
I'm ready to convert my love....I want to become Muslim too...
Kallonsa tayi idonta na cikowa da hawaye sabuwar soyayyarsa na qara shigarta sbd ganin yanda idonsa ya rufe bayako tuna masifar dake gabansu ta dukkanin 6angaren biyu...Dan tasan gidansu sun gwammace ta mutu dasu barta dashi..
I love you ayeeshah...
Juyarda Kai tayi tareda sakin 6oyayyen murmushi..
Fira yafara yi mata ahankali Yana Bata lbarinsa saidai tayi murmushi kawai batareda tayi maganaba.
Mantawa suka da komai da kowa Saida sukaji knocking tayi saurin miqewa tsaye gabanta na fa'duwa jikinta na rawa..
Kallonta yayi tareda sakin qaramin murmushin daya bayyana white teeths 'dinsa qasa qasa yace,
Wait hia...
Qofar ya 6ude ahankali saiyaga nurse ce yasaki ajiyar zuciya ahankali tareda juyowa ya kalli yanda ayshan tayi zuru duk saiyaji tabasa tausayi ya matso kusada ita yakai bakinsa saitin kunnenta zaiyi magana tayi saurin zillewa ta Fice 'dakin da sauri tana Jin farin ciki na shigarta tako ina.
Shafa kansa yayi tareda kwantawa a gado Yana Jin farin ciki Mara misaltuwa.
Tundaga nesa ta hango qofar gidansu da kamar mutane gabanta yayi fa'duwa ta qarasa a darare..
Su Yaya sani dasu babanta ne ke qoqarin shigardasu baba alhaji cikin gida dukkaninsu ba kyan gani kawunansu da fuskokinsu a kumbure da jini a kayansu..
Yawu ta ha'diye daqyar tashigo gidan Nan ta tararda kowa hankalinsa a tashe su husna ma harda kuka ganin mummunar aika aikar da akayiwa su baban.
Sosai itama hankalinta ya tashi Dan koba'a fa'daba tasan wannan aikin mum ne..
Har dare gidan ba da'di Dan kowa na cikin jimami da baqin ciki..itadai Bata kosanyin wani qwaqwaran motsi sbd tsoron Mai zai biyo baya.
Har akai kwana biyu ba'ai zancen komaiba kan al'amarin Kuma tun ranar Bata fitaba sbd tsoro da fargabar abinda zai biyo baya duk da ba qaramin tausar zuciyarta takeyiba akan son sanin ya jikinsa yakeba..
Yau kwana hudu da afkuwar tsautsayin su baba..
Matuqar zafi gidan kusan kowa ya 'dauka musamman matasan gidan wannan karon ko baba malam ya 'dau zafi matuqa....
Shiyasa ya tarasu yau kowada kowa..
Gyara Zama yayi tareda kallon ayshah murya a karsashe yace,
Ayshah Kinga abinda wa'innan mutanen sukayi Mana ko?
Shiru tayi gabanta na bubbugawa da sauri..