Complete Hausa Novels

Abdulmalik Bobo Complete Hausa Novel

Reading file: Abdulmalik_Bobo_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 4 of 4

_Shafin nakune Biebie, Sawwama & Mrs Amaan gaisuwa da fatan alkairi agareku._
Luv u so much.😘

5⃣7⃣

*_8:30am_* Nawal tasakama Safna kuka ita wajen momynta zataje.
Ita kanta Safna abin mamaki yake bata Dan ganin har tara saura Rahma bata fitoba, kota manta Nawal zataje makarantane?, dukda dai bobo yace mata batada lfy, amma yakamata ace tafito aii, jitai ranta yakuma 6aci, wata zuciyarta ta ce, "idan kin kwantar da hankalinki aii bobon yakusa zama naki gabad'aya.......
Nawal ta girgizata, aunty naje wajen papa na tambayesa momyna.
Safna tad'aga mata kai alamar eh.

Bugun k'ofarne yasakashi farkawa, bobo yaja d'an tsaki sannan ya yunk'ura yatashi da k'yar, sakkowa yayi daga gadon yanufi k'ofar, wayene yay maganar dad'an haushi.
Nawal ta ce, " papa nice.
K'ofar yabud'e mata tashigo sannan yamaida yarufe.
Papa ina momyna take?.
Bobo yanuna mata gado da hannu, da gudu taje ta haye Rahma dake barci, momyna zan makara a school kitashi ki shiryani, kuma yunwa nakeji.
Bobo yad'an zaro ido Shifa yama manta yau akwai aiki.
Baby ya haka? Kosai kin tada momyn nakine?.
Rahma tabud'e idonta ahankali, ganin Nawal akanta yasa ta yunk'ura ta tashi zaune, Nawal kin tashi?.
Eh momy tund'azu natashi nake nemanki momy yunwa nakeji, kuma ba'amin wankan tafiya school ba.
Bobo dake tsaye yana kallonsu cikeda sha'awa yakamo hannun Nawal yana fad'in kinga kibar momynki batada lfy kinji, makaranta kuma tunda yau juma'a ki hak'ura kawai dankin makara Tara saurafa.
Kai Nawal tad'aga MASA, tamaida kallonta ga Rahma, momy kanki keyin ciwo?.
Murmushi Rahma tayi tareda satar kallon bobo, ta ce, "kaina keyin ciwo amma na warke.
Momy sorry, Nawal tafad'a kamar zatayi kuka.
Murmushi Rahma tayi tareda jawo Nawal jikinta ta rungume, karki damu babyna nawarke aii, tashi muje namiki wanka.....
Bobo yakatseta dafad'in no kwanta ki huta bara namata wankan, itada safna saina saukesu gidan Appa suje suwuni.
Da Sauri Rahma tad'ago tana kallonsa, ta kwa6e fuska tamkar zatayi kuka, cikin muryar shagwa6a ta ce, " nifa?."
Zama yayi kusada ita yakamo hannunta yarik'e anasa, kinga kibarsu sutafi tunda bakida lfy, Nima bazan dad'e awajen aikinba zandawo gida muyi zamnmu.
Nidai ALLAH inason zuwa kumafa ni lfy ta k'alau, Rahma tayi maganar tana hawaye.
Murmushi yayi yashare mata hawayen, itadai Nawal tana kallonsu, ganin papanta na sharema momyn ta hawaye itama tasa hannu tana goge mata, ta ce, "papa".
Bobo ya ce, " Na'am.
Papa kabar momy taje itama kaga tana kuka.
Shafa kan Nawal yayi tareda fad'in baby aina barta, kutashi Ku shirya idan mukaje can saimuyi breakfast.
Sakkowa sukayi, Nawal ta ce, "momy muyi wanka a bathroom d'in papa.
A'a baby muje namu.
Bobo ya ce, " saboda kina guduna.
Ahankali yayi maganar yanda Nawal bazatajiba, Dan yakula yanzu dole su iya bakinsu agaban parrot d'innan.
Babu yanda Rahma ta iya dole suka Shiga bayinsa, bobo yabi Rahma da kallo Dan ganin yanda take tafiya dad'an d'ingishi.

Acikin 'yan mintuna suka gama shiryawa tsaf harda Safna, fitowarsu falo babu dad'ewa saiga bobo yafito cikin ash colour na shadda d'inkin zamani yayi k'yau sosai, Safna tashagala da kallonsa kuwa, jitake tamkar ta rungumeshi amma babu damar hakan.
Rahma tanufi kichin danta rufe k'ofa, bobo yabita da kallo dantayi MASA k'yau dukda dogon hijjabine har k'asa ajikinta, tafito tanufosu safna ta ce, "waike lfyarki kuwa kike tafiya haka?.
Cak Rahma tatsaya amma takasa cewa komai, bobo dake latsa waya yad'ago yakalli Rahma sannan ya maida kallonsa ga Safna ya ce, " bana fad'amiki batada lfy ba.
Okey namantafa, Safna tayi maganar cikeda rainin wayau, Dan ita bata yarda Rahma batada lfy ba.
Bobo ya maido kallonsa ga Rahma my cute badai haka babynki zata Fita babu d'ankwaliba?.
Rahma takalli Nawal dake zaune akujera tana wasa da filoliwa ta ce, "nabata gyale bansan INA ta ajiyeba, Nawal ina mayafinki?.
Nawal tad'ago tana kallonta, ta turo baki ta ce, " momy nibanason gyalen Nafi k'yau ahaka.
Tsawa bobo yadaka mata zakitashi ki d'akko kosaina zanekine?.
Da Sauri Nawal tamik'e zatayi kuka, Rahma tarik'e hannunta kinka fad'amin bakison wancanne na canja miki wani?.
Kai Nawal tad'aga mata tana satar kallon baban ta.
Bobo ya harareta Yakama hangar Fita dama Safna tafita, to kinga bisu naje nad'akko miki.
Bobo yak'arasa ga mota yabud'e yashiga, wuf Safna tabud'e gaban itama tashige, k'ala baice da itaba saima k'ok'arin tada motar dayakeyi, Nawal tabud'e baya tashiga tana satar kallonsa Dan bataso yadaketa.
Babu dad'ewa saiga Rahma tafito da farin siririn gyale ahannunta, takulle k'ofar falon tanufosu, tunda ta taho ioon bobo na kanta jiyake wata k'aunarta nak'ara ratsashi, ga wani k'yau na musamman dayaga yau tak'ara masa.
Koda tak'araso taga Safna agaban motar batako kallesuba takama k'ofar baya zata shiga.
Bobo ya ce, "dawo gaba.
Kallonsa Rahma tayi, yanda yaymaganar babu wasa afuskarsa kuma ba ita yake kalloba, a ranta ta ce, " to a INA zan zauna?, afili kuma saitayi shiru tana kallonsa.
Ya ce, "bakijini baneba?.
Ta ce, " naji amma a INA zan zauna?, badan Nawal dake motarba dasai yafad'i abinda zai saka Safna FASA binsu amma ALLAH ya taimaketa bazai iya kowace maganaba agaban d'iyarsa.
Duk abinda ke faruwa Safna nagaban mota ta kacire kamar motar mijinta.
Bobo yawatsama Rahma wani kallo, muryarsa cikeda gargad'i ya ce, "madam kina 6atamin lokacifa kuma kinsan office zanje."
K'ofar Rahma takama tabud'e Safna tad'ago ta kalleta suka kalli juna, badai ta ce, "komaiba amma fuskarta tanuna alamar bak'inciki.
Rahma tadaure ta ce, "aunty kifito kikoma baya Dan ALLAH.
Cikin masifa Safna tabud'e Baki zatayiwa Rahma magana, saidai kuma komi tatuna saita FASA ta fito, tad'an bangaje Rahma tabud'e baya tashiga.
Itama Rahman gaban tashiga.
Bobo yagirgiza kai kawai dama yayima Rahman hakane danyafi son taringa takwatarma kanta 'yanci awajen Safna.

Ahankali yake tuk'in tamkar bayaso, wayarsace tafara wringing, yad'auka yana fad'in malam miye nawani kirana da farar Safiya?.
Dariya ammar yayi, ya ce, "ho d'an duniya basaika nunamin ka girmaba aii.
Shima bobo dariya yayi ya ce, " ALLAH Ammar bakada mutumci, yanzu nan nine kakecema sai yanzu na girma?.
Hhhhhh eh mana, kaima Kasan hakane.
Bakomai zan rama, yanzudai miye na kirana?.
Dama zan tambayrkane ko kana office?.
Kabari kawai wlhy namakara, yanzudai INA hanyar zuwa gidan Appa, amma daganan office d'in zan wuce.
OK to kabiyo tanan mana idan bakada wani uzuri.
Kai nifa Kasan banason zuwa office d'inka, wannan masu bak'ak'en kayan daka wani baza suyita kallon mutum.
Hhhhh toka had'une shiyyasa suke kallonka, Inda basu sankabama bazasu barka ganinaba ehe, ato bara nayi zamana Idan kamatsu kazo office kasameni.
Hhhhhh to yi hak'uri na Ammi kodayake yanzu kazama na Rahma.
Dariya bobo yayi ya yanke wayar, baikai ga ajiyewaba kiran Ya Sulaiman yashigo, yad'aga suka gaisa.
Bobo ya ce, "yaya dama wlhy INA niyyar kiranka, magani nake buk'ata.
Maganinmi bobo?.
Ummm saidai Nazo, inafata kana asibiti.
Eh, amma kai kana ina?.
Gani zanje gaidasu ammi, OK nima yanzu nabar gidan babu dad'ewa nida ya ishaq da Hamza.
Ayya tosaina shigo.
Okey, ina jiranka.

Bayan ya ajiye wayar yakalli Rahma kad'ain ya kauda kai, murya k'asa k'asa ya ce, " gara naje na k'ar6o miki magani wannan tafiyar taki tadawo daidai, damma kinki hak'ura ne amma yanzu haka zakije gidan Ammi kina tafiyar 'yan kaciy......
Bai k'arasaba yay saurin rufe bakinsa da hannunsa yana dariya.
Rahma taturo baki gaba, yakuma kallonta yashek'e da dariya.
Ba Rahmaba har Safna da Nawal saida suka kallesa, suna had'a ido da Safna ta madubi ya gimtse fuska.
Aranta ta ce, ''zakazo hannune malam.
Itakam Rahma ta ce, "mugu d'an masa sai ALLAH yasakamin aii.
Da hakadai suka k'arasa gidan AMMI.

Safna da Nawal suka fice, Rahma na niyyar fita bobo ya kulle motar, juyowa tayi tana kallonsa shima ita yake kallon, ya ce, "yadai 'yammata namiki k'yaune?.
Kauda idonta tayi daga kansa, ta ce, " Dan ALLAH kabud'emin.
Aidama zan bud'e miki, sonake nacemiki kiyi k'ok'ari koyaya kid'an gyara tafiyarki inba sokike kowa yasan miya faruba.
Kallonsa tasakeyi, saikuma tayi k'asa da kai tana turo baki gaba, nifa wlhy zafi nakeji awajen.
Shiyyasa nace ai kiyi zamanki sai gobe amma kikak'i, amma babu damuwa bara na kar6o miki magani wajen ya sulaiman, yanzudai muje ciki, amma idan kinje kiyi kwanciyarki ki huta kinji.
Batace komaiba takama k'ofa zata bud'e yarik'o hannunta haba tawan ko sallama babu?.
Tokai bazaka shigaba?.
Jawota jikinsa yayi yana fad'in zan shiga mana, amma ai bazan dad'e ba, k'ok'arin saka k'wayar idonsa yake anata itakuma tak'i basa dama, saima talumshe idanunta gaba d'aya, wani murmushi yayi Wanda har tanajin sautinsa, jin bakinsa kan nata yaskata saurin zabura, amma ina tamakaro yarigada yayi nasarar cafkar harshenta.

Na ce, "humm bara nakoma daga waje najiraku."

Ak'alla sunkai minti biyar sannan naga Rahma tayi saurin fitowa tana murmushi, shima bobo yafito yana dariya, gaba tayi abinta hartana had'awa dad'an gudu, bin bayanta yayi yana fad'in matsoraciya kawai.
Ak'ofar falo tatsaya ta daidaita nutsuwarta sannan tashiga.
Gaba d'aya yaran suka taso suka tareta, itama tahad'asu tarungume tana dariya, Rahma akwai San yara shiyyasa duk inda taje saikaga yara suna sonta.
Bobo yana shigowa suka saketa suka nufeshi, zama Rahma tayi suka gaisa da su aunty Rasheeda, aunty ummy, aunty sameera, khairiyya da khursiyyama suka gaisa.
Bobo yak'araso shima suka gaisa su aunty Rasheeda suna tsokanarshi, Rahma dai mik'ewa tayi tanufi d'akin Ammi itada khairiyya.
Bobo ya ce, "ALLAH idan baku daina matsaminba saina saka mazanku sun k'ara aure.
Da sauri aunty Sameera ta ce, " a'a Abdulmaleek wlhy nikam nabari yi hak'uri, tashi yayi yana murmushi ya ce, "waiku mata miyasa kuke tsoron kishiyane?.
Aunty Rasheeda ta ce, " jeka katambayi Rahma, d'akin Ammi yanufa yana fad'in ai ita bata tsoron kishiya.
Dariya suka saka gabad'aya shikuma yashige d'akin Ammi da sallama.

Ammi ta ce, "a'a mukarram d'ina kaine?.
Wlhy nine Ammi wad'ancan 'ya'yan naki duksunbi sun rainani, nakusa daina musu dariya.
Dariya Ammi tayi ta ce, " kunfi k'asa aii.
Shima dariyar yayi sannan yagaida Ammi cikin girmamawa, yanayi yana satar kallon Rahma dake zaune kusada Ammi suna ware wasu kaya itada khairiyya.
Ya ce, "Ammi yunwa nakejifa.
Kallonsa Ammi tayi tana dariya, haba mukarram aii gwauro aka sani da zama da yunwa, murmushi yayi shima, ya CE, " Ammi nima tawa matarce babu lfy."
Ayya, Ammi tafad'a tana kallon Rahma, nima tunda tashigo nake kallonta duk naganta sukuku babu walwala sosai, ga idonta sund'an kumbura, mike damunta?.
Sosa kansa yayi yana fad'in em...em.. Ammi zazza6ine.
Dariya Ammi tayi ta ce, " mukarram magana da in ina kamar mara gsky.
No Ammi inada gsky kawai inaso natuna sunan zazza6inne.
To ALLAH yabata lfy kunje asibitine?, a'a ammi jiya da daddare zazza6in yasameta, dama yanzu zanbiya tawajen ya sulaiman na kar6o mata magani.
Okey to Aida tayi zamanta agida tahuta ko.
babu yanda banyi da ita tazaunaba amma fir tak'i wai itadai saitazo, yayi maganar yana kallon Rahma.
Tana jinsu amma tashare kamar batasan zancen da akeba, Ammi ta ce, "khairiyya jeki had'omusu break fast ko, suma su Safna haka.
To Ammi khairiyya tafad'a tana mik'ewa.

Ammi da bobo suna 'Yar hirarsu khairiyya takawo break fast, bobo yalangyare wai saidai Ammi tayi feeding d'insa.
Rahma tad'ago ta kalleshi saiya yimata gwalo, Ammi na kallonsa, danhaka tayi murmushi had'eda girgiza kai, koba komai tasan d'anta yasamu farinciki daga matar tasa,.
Rahma d'auke idonta tayi daga kansa tana d'an murmushi, aranta ta ce, " Indai ta6arace kaganta salo salo ga daddyn Nawal, wani abunma idan yayi saiya baka dariya wlhy.
Ammi kam dakanta tabama bobo abincin yaci, saida yak'oshi sannan yamik'e, AMMI bara nad'anje office naga mike tafiya.
To ALLAH yabada sa'a yatsareka babana.
Amin ammina.
Ya kalli Rahma, ya ce, "my cute nawuce.
ALLAH yabata kunya amma saita dake ta ce, " ALLAH yabada sa'a, ameen yafad'a yana fita, idon ammi kawai yahanashi mata kiss.
Afaloma yamusu sallama yafice.
Da sauri Safna ta tashi tabi bayansa..................

*_luv you oll_*
*_(((S))).......2017_*
[11/12, 2:57 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•{🅱🅾🅱🅾}•_

*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*

5⃣8⃣

Bobo dabaisan Safna nabinsa abayaba yabud'e mota yashiga, harya tada motar yaji ana kwankwasa masa gilas.
Sauke gilas d'in yayi ahankali Dan atunaninsa Rahma ce kosu khursiyya, had'e fuska yayi Dan ganin safnace, baice komaiba ya kauda kai daga kallonta.
Rik'e k'ugu tayi tanamai jifansa da shu'umin kallo, cikin narkewar murya ta ce, "haba my jaan wai miyasa kakeson wulak'antanine?, aiko bakomai ance kaso mai sonka, yanzu Dan ALLAH abinda kamin agaban Rahma d'azun yadace?.
Tsaki yaja tareda yatsine fuska tamkar Wanda yaga kashi, ya ce, "ke awa? dabazan miki abu agaban Rahma ba?.
Ya nunata da d'anyatsa wlhy kifita hanyata, karki yarda kibari na nunamiki asalin colour d'ina, ina d'aga miki k'afane saboda 'Yar uwarki, amma zakisha mamaki idan kikacigaba da bibiyata.......
Kafin ta ce, " wani Abu yaja motarsa yafice, dama tuni mai gadi yabud'e masa gate.
Hawaye suka kwararo afuskar safna, wani d'an lungu tasamu dagacan baya ta zauna, saida tad'anyi kuka sannan tad'auki waya takira baseera, bata d'agaba takuma kira nanma haka, ajiye wayar tayi tazabga tagumi cikeda damuwa.

Su Rahma suna ciki basusan bikin da akeba, bayan sungama ware kayan da ammi tasakasu suka dawo falo wajen sauran 'yan uwansu suna hira, saidai hankalin Rahma yana kan tunanin ina aunty Safna?, gashi batason tashi Dan gudun karsu fahimci halin datake ciki, tasan ko kowa bai tanka tafiyartaba sai aunty Rasheeda tayi magana, Dan tun d'azu take binta da kallo, itakam idan antambayeta batasan amsar dazata bayarba.

Da sauri Safna ta kalli wayarta ganin Baseera CE yasa tad'auka da hanzari, ko gaisuwa bata tsaya sunyiba ta ce, ''kekam baseera ina kika Shiga haka inata kiranki tun d'azun?.
Safna muna lectures ne, kinsan ba'a d'agama sir hamza waya idan yana lecture, waimi yahanaki zuwa school yaune?.
Wlhy babu komai hakanan naji banason zuwa.
Lallai kinyi wauta Dan wlhy sir hamza yayi test yanzu.
Ke babu damuwa aii ina gidansu, kinsan ankusa bikin k'annenesu nextweek, to muna gidan ana shirye².
Hummm ALLAH yasa yad'aga miki k'afa to, Dan wlhy ya CE........
Da sauri Safna ta katse baseera kenifa bawannan bane damuwata, nakirakine muyi magana.
To inajinki baseera tayi maganar tana zama kusada zeenat data fita harkarsu tuntuni dantaga sunyi nisa basa jin kira, idanma zasuyi k'ulle k'ullensu basaya akusada ita.
Safna ta ce, "baseera wlhy inacikin matsala."
Matsala kuma kamar ya?.
Safana tafara zayyanama baseera abinda yafaru tundaga Daren jiya da motarta ta lalace harzuwa abinda bobo yamata yanzunnan.
Jinjina kai baseera tayi sannan tad'an kalli zeenat dake karatu amma hankalinta na Kansu kuma tanajin duk abinda safna ke fad'ama baseera awaya, baseera ta ce, "lallai safna bakida wayo wlhy, keyanzun harya sakaki dafa ruwan zafin Gaza Rahma amma ki Gaza ganewa?, kumafa k'uru k'uru yafito yace miki Rahma tagirma amma duk Baki ganeba.
Safna tad'an ta6e baki baseera ban... bangane kema mikike nufiba aii.
Tsaki baseera taja tana fad'in aikin banza, asheke zaman banzama kikeyi agidan, ayanzukam kid'auka bobo yamiki nisa wlhy dankuwa adaren jiya ya angwance kenan.....
Agaban safna yafad'i cikin masifa ta ce, " baseera karki k'ara 6atamin rai kema banason fatan tsiya, taredakefa malam da'u yacemana yaturomusu aljani dazai hana ya kusanceta.
Baki baseera ta ta6e ta ce, "wannan zancekam yazama labari tunda bobo ya aikata hakan ajiya, saidai kuma kujira result d'in ciki.
Kuka wuy wuy safna tasaka tana kuran tashiga uku bobo yaci amanarta itakam rayuwarta tazo k'arshe garama tamutu ta huta.
Tsaki baseera tayi tareda yanke wayar tana fad'in 'Yar wahala keni nagaji da matsalolinki, wlhy da bobon zaice yana sona nimafa sonshi nakeyi harma nafiki Dana kula yamin nisa saina hakura, amma nakula ke kinkasa ganewa *_" ANNABI"_* yafaku, haba Dan ALLAH ayi mutum da tosashshiyar basira, idanma bakisaniba kisani dagani har malam da'un cin k'ud'inki kawai Mukeyi babu wani aiki dayake miki Dan tun farko yafad'amin komai wlhy, ya ce, "kwata kwata babu aure tsakaninki da bobo Dan bazaima sokiba.
Zeenat tayi galala tana kallon baseera wadda da alama tamanta tana wajen shiyyasa taketa sakin zance babu (,) babu (.).
Ganinfa da gsk tamanta tana wajen yasaka zeenat zungurar ta baseera kinsan mikike fad'a kuwa?.
Figigit baseera ta kalleta saikuma tafara Kame kame au.. au.. Ummm zeenat dama kina nan?, Dan ALLAH kinji minake fad'a?, pls kirufamin asiri maganarnan tatsaya dagani saike Dan ALLAH, kitaimakeni Zeenat wlhy su6utar bakice.
Girgiza kai kawai zeenat tayi tamik'e tabar mata wajen Dan wlhy yau bak'aramin tsoro baseerar tabataba, lallai maganar Sajna gsky CE datace *_wata k'awar tafi guba_*, itakam yau ta shaida akan baseera, idan bata mantaba baseera CE tasaka safna ahanyar bin malami da bokaye, amma Ashe tanacan tahad'a baki da bokayen sunacin dunduniyar safnar, ALLAH ma ya k'ara, aiduk Wanda baiji bariba yaji hoho, babu irin nasihar da bataima safna ba amma tak'i saurarenta daga Bayama daina mata magana tayi wai bata k'aunarta, toga baseerar datake d'auka tana k'aunarta d'in nan tajefata arami mai zurfi kuma mai duhu, aii duk Wanda yagagara yima iyayensa biyayya to yanatareda gamon wahala, to ita baseera CE gamon wahalarta kuwa.
Ganin baseera tanufota yasakata saurin yin gaba.
Da gudu baseera tacimmata kuwa.

A6angaren Safna kuwa baseera tana Yanke wayar tAk'ara sautin kukanta, tama rasa wane irin sambatu zatayi?, amma jitake Duk duniya babu Wanda ta tsana kamar Rahma arayuwarta, jitake zata iya kashe Rahma wlhy, afili ta ce, "wlhy natsaneki Rahma, natsaneki tsana irin wadda banta6ama wani mahalukiba, Rahma kin cuceni kedasu Ya Shaheed munafukai kawai, duk bakwa sona nimakuwa natsaneku bana sonku harma ya munnir d'in dasu ummi dukna tsaneku, kuka take Rurus da sambatu.

Zeenat Dan ALLAH ki saurareni pls.
Mizaisa na saurareki baseera?, aini yanzu kinfi k'arfina wlhy, keba k'awar rayuwa bace, tunda har kika iya cin amanar safna data d'auki sirrinta Dana gidansu tabaki duka, tonikam sai yaya kenan?, ALLAH abin tsoro kema baseera dole aji tsoron kaidinki, kecefa kika jefa rayuwar Safna a halinnan amma Ashe kina gefe kina cin dunduniyarta, haba baseera miye ribarki Dan ALLAH?, tundaga sanda iyayen safna sukace sun mata miji kika Shiga kika fita kika kanainaye rayuwarta, kin hana afad'a mata gsky bare ta fahimta, saboda son zuciya irin naku yanzu kun koma danku 6ata rayuwar auren k'anwarta, haba baseera kashe aurefa ba abin wasa bane, *_"ALLAH ne ya halatta aure da saki, amma shikanshi bayason sakin aure, duk sanda igiyar aure ta katse sai al'arshin ubangiji ta girgiza saboda kad'uwa, shaitan yakanyi farinciki awannan rana saboda yaraba aure, shin kuma kunaso kuzama daga jerin shaid'anu?."_*
Wlhy kuji tsoron ALLAH kutuba tun kuna da dama, idan kuka bari damarku ta su6uce kunci amanar kanku, kutuba tuba na gsky ALLAH zai iya yafe muku *_"domin shi gafurun rahimunne, kuma maji6incin al'amuran bayine."_*, kuma godema ALLAH daya fargar daku da wuri Dan yana sonku da rahmarsane.
Tunda zeenat tafara maganar baseera kuka takeyi, tabbas ta tafka babban kuskure kuma sharrin shaid'anne, wlhy tayi nadamar halayenta, tarik'o hannun zeenat tana hawaye ngd sosai zeenat kin tunatar dani abinda ban saniba kuma ngd wlhy kinsamu ladana Dan nayi nadamar abinda na aikata, kuma daga yanzu insha ALLAHU zan tuba, zan samu Safna na warware mata dukkan k'ulli, amma inaso ki taimakamin da nuna mata hanya itama, Dan inaso yanda natuba na dawo hanya itama ta tuba ta gyara kodan mugudu tare mu tsira tare.
Jinjina kai zeenat tayi tana murmushi had'eda sharema baseera hawayenta, karki damu 'Yar uwa ngd Nima dakika fahimceni kika kuma gane abinda nake nufi, ALLAH ya yafe mana gabad'aya ya kar6i tubanmu, ALLAH yasa mufi k'arfin zuciyarmu, ina fata yanda kika fahimta da wuri ALLAH yasa Safnama ta fahimta d'in.
Ameen zeenat ngd.
Karki damu muje Dan sir koba hakabane,😜 yakusa Shiga mana, muje muk'arasa lecture d'in muwuce gida.
Jinjina kai baseera tayi tana murmushi suka kama hannun juna suka nufi holl.

😁 _wlhy abinda yaburgeni kuma yamin dad'i masu karatu, ALLAH yasa safna itama ta fahimta kamar yanda baseera tagane kuma ta tuba.🙏🏻ameen._

Su Rahma duk suna kichin suna aikin soya cincin d'in gara, amma jitake zazza6i yana neman rufeta, ga k'asanta yana mata zafi har yanzu ko motsi bata sonyi ma, Ammi dake kallonta tun d'azun ta ce, "Rahma yaya dai?.
Murmushi yak'e Rahma tayi ta ce, " babu komai Ammi."
Aunty Sameera ta ce, "kai Rahma bakida lfy gsky, tun d'azun nima ina lura dake, aunty Rasheeda ta ce, " wlhy nima nakula tundama tashigo batada walwala kamarma tana d'ingishi, kokinji ciwo ak'afarne?.
Shiru Rahma tayi kanta ak'asa, jitake duk kunya ta isheta, itakam bobo yaja mata, yanzu hakama kowa yagane abinda yafaru........
Ammi CE ta katse mata tunani dafad'in tashi muje kisha magani.
Ahankali Rahma tamik'e tana duk'ar da kai, duk sukai mata sannu amma banda safna, azuciyarta ma sai tsinema Rahma takeyi.
Kama hannun ta Ammi tayi suka nufi d'akinta, ta zaunar da ita abakin gado sannan itama ta zauna tana fuskantarta, kallonta take cikeda nazari, ita kam Rahma kanta na k'asa tana wasa da zobenta.
Rahma kodai fad'a kukayi keda mukarram d'in?.
Girgiza kai Rahma tayi ta ce, "a'a Ammi bamuyi fad'aba."
To mike damunki?.
Ammi babu komaifa k'afatace kemin ciwo, shuru Ammi takumayi tana kallonta, zuwa can ta ce, "fad'uwa kikayine?, a'a, to ciwo kikaji kenan?.
Eh, Rahma tafad'a cikeda kunya, ga hawaye suncika idonta taf, bata fata ammi tasake tambayarta wani Abu kuma bayan wannan Dan batasan mizataceba kuma.
Ammi ma batasake cewa komaiba Dan sai yanzu tafahimci komai, amma tayi mamakin hak'urin mukarram dahar ya iya barin Rahma har zuwa yanzun, dawani yagaya mata bazata yardaba, amma gashi tagani da idonta, koda yake tasan duk cikin 'yayanta babu Wanda yakai mukarram kawaici saidai zuciya da masifar tsiya.
Bayi tashiga tahad'a ruwa mai zafi tareda magunguna masu k'au cikin wad'anda takema su khairiyya gyara, fitowa tayi tana fad'in Rahma taso kigani.
Rahma tamik'e tamkar wata muna fuka tanufi Inda ammi take tsaye, bayi ammi tanuna mata da hannu, kishiga ruwa na nan aroba kicire kayanki saiki shiga ruwan, amma saikin daure Dan yanada d'an zafi, idan yahuce kikuma Tarar wani ga maganin nan ajiye aroba saiki kuma shiga kinji, shima saiya huce insha ALLAHU k'afar zata daina ciwo sannu, nima idan k'afata na ciwo dashi nake amfani.
Sanyi Rahma taji aranta Dan duk tunaninta Ammi taganene, amma dataji tace itama dashi take amfani idan tana ciwon k'afa saitaji dad'i, risinawa tayi Tanama Ammi godiya.
Ammi tayi murmushi tana fad'in aii babu godiya tsakaninmu Rahma, kud'inma 'ya'yanane, matsayinku d'aya dasu mukarram araina.
Murmushi Rahma tayi tashige bayi tanamai jin k'aunar tsohuwar aranta, itama jinta take tamkar umminsu.

Ammi tana niyyar fita saiga ya hamza da bobo sunshigo d'akin da sallama.
Baya ammi takoma tana musu sannu, suka gaisheta sannan suka zauna abakin gado, shi boboma kwanciya yayi, Ammi ma zamatayi saman kujerar d'akin tareda jawo k'atuwar ledar dasu bobo suka ajiye, miye kuma anan?.
Ammi d'unkunanmune wlhy muka amso cewar bobo dake kwance male male agado.
Ammi tayi murmushi a alallai manyan yayye sun shirya, harkun kama d'inkinku ahannu?.
Ya hamza yay dariya to Ammi aigara haka, inba hakan mukayiba aiki cud'e mana zaiyi, Dan kinga daga yau babu hutu, sauk'inma banida lectures gaba d'aya satin nan, boboma nashi mai sauk'ine tunda zai iya d'aukar Hutu, ya sulaiman da ya ishaq nedai babu dama.
Hakane amma aii ansamu sauk'i tunda gaku, ALLAH dai yayi muku albarka.
Ameen Ammin mu.
Ammi appa bai dawoba?.
Eh bai shigoba, k'ila yau a can zaiyi sallar juma'a Dan yacemin sunada meeting.
Okey nima bara naje gida nayi wanka to kafin su ya ishaq su taso.
To shikenan saika dawo.
Bobo ya ce, "saika dawoto, bara nayi barci kona minti30 ne, plz idan kadawo katadani.
Humm ALLAH ya shiryaka kaikam, to kana nufin bazakayi wankan masallaciba?.
Ah zanyi mana, nikasan inada kaya anan gidan, to Dana tashi zand'an watsa ruwa na shirya, kafinma ad'akko yara school amusu wanka ashiryasu aina d'an huta.
Dariya ya hamza da Ammi sukayi, ya hamza ya ce, " Ammi wannan autan naki bansan yaushe zaisan yagirmaba?.
Bobo ya ce, "babu wani auta, kana ina ammi ta tureni daga sannan kujerar ta d'ora hibba.
Yanda yay maganar cikin shagwa6a yasaka Ammi da ya hamza yin dariya, ya hamza yafice yana fad'in bara na dawo sai azauna shari'a.
Ammi ma mik'ewa tayi tafice zuwa kichin tana dariya.

Bobo yagyara kwanciyarsa yana murmushi, arayuwarsa yanason rayuwar irinta gidansu, Inda ace hakane akowane gida toda zuminci bai lalaceba, ALLAH yak'arama amminsu da Appa tsawon kwana.

Na ce, " ameen.

Lumshe idanu yayi dansonyin barci, baisan Rahma tana d'akinba.
Itakam tanad'anjin hirarsu sama sama, daga baya taji shiru duk zatonta sunfita gaba d'aya.
Tamik'e daga cikin ruwan da ammi tahad'a mata Dan har ya huce, wani takuma had'awa kamar yanda ammi ta umarceta, tasake shiga, nanma takai minti 15 aciki ruwan yana ratsata, yanzukam taji dad'i sosai, harma jitake wajen yabar zafi, wanka tayi kawai tafito.
K'arar bud'e k'ofarne yasaka bobo bud'e ido ahankali ya sauke akan Rahma.
Sosai yakuma bud'ewa Dan yayi mamakin ganinta, dama tana band'aki tun d'azun amma tayi muk'us kamar babu kowa?.
Shiru yayi bai motsaba Dan yakula batama gansaba.
Aiko Da gsk Rahma bata kula dashiba, tasa k'aramin tawul tatsane jikinta, jinta take wasai yanzun kamar iska zata d'auketa, kujerar madubi taja ta zauna tana mai fad'in kai ALLAH yabiyaki Ammi, Ammi uwa tagari, dabadankeba k'ilan saina had'a sati ina fama dazafin wajennan Dan wlhy ciwo yakemin, ALLAH yak'aramiki tsawon Rai Amminmu Dan zuciyata kullum k'ara k'aunarki takeyi wlhy.
Murmushi bobo yasaki danjin furucin Rahma ga mahaifiyarsu, jiyayi sonta yak'ara nunkuwa azuciyarsa.
Itadai hidimar shafa manta takeyi harda yaye yawul Dan ko kad'an hankalinta baikai akanshiba, tsaf tagama sannan tad'an gyara fuskarta dukda bawata kwalliyar kirki tayiba amma tayi k'yau.
Kayan su data d'akko ta d'auka tasaka, tayi d'as cikin siket da rigar na farin material mai d'igo d'igon bak'i.
Bobo dai yana kwance yana kallon ta cikeda k'auna, baimasan sanda yafurta woow my cite kinyi k'yau.
Arazane Rahma tajuyo tana kallonsa, tako wage baki zata tsala ihu Dan ita azatonta aljanine yay shigar siffar bobo yazo mata.
Da sauri bobo yajawota yarufe mata baki da lallausan tafin hannunsa...............

*_luv you oll_*
*_(((S))).......2017_*
[11/12, 2:58 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•{🅱🅾🅱🅾}•_

*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*

*_duk Wanda yasake d'aukar number ta yay amafani da'ita ta hanyar dabata daceba, dasakani a group d'in banza, ko turomin sak'on banza ta PC ALLAH ya Isa ban yafeba, nabarsa da ALLAH shine zai sakamin, tunda nayi magana harna gaji ank'i bari._*
😭😭😭😭😭😭

5⃣9⃣

"K!, 'yammata karki taramin mutane mana, bobo yay maganar yana mai matse Rahma ajikinsa.
Sotake ta kwace kanta amma yak'i bata damar haka, ganinfa kamar da gsk atsorace take dashi yahad'e bakinsu waje d'aya, wata sassanyar ajiyar zuciya Rahma tasaki saidai har yanzun jikinta baibar k'yarmaba, saima k'aruwa dayayi Dan ayanzun ta shaid'a lallai bobone, to amma baya gudun Ammi tashigo tagansu?, kokuma wani daga cikin matan yayyensa.
Mintsininsa take amma yak'i sakinta, dole tahak'ura tazubama sarautar ALLAH ido wadda ta girma ta d'aukaka, daga kiss yafara kauce hanya, ayanzukam bazata iya jurewaba musaman idan ta tuno da azabar datasha adaren jiya wadda har safiyar yau wajen namata rad'ad'i, iya k'arfinta take turesa amma mutumin naku ko gazau sak'wanni kawai yakai son isarwa cikin nuna k'warewa.
Hawayene suka fara zurara akumatun Rahma Dan ayanzu kam batada wata hanyar ku6ta saidai kuka dan shikad'aine yarage mata.........
Da gudu khairiyya da khursiyya suka shigo d'akin suna kwala kiran aunty Rahma! Aunty Rahm.........
Suduka maganar tamak'ale amak'oshi Dan ganin abinda yafi k'arfinsu.
Shima da sauri bobo yabar abinda yakeyi yad'ago, yayinda Rahma ALLAH yabata nasarar mik'ewa daga jikinsa.
Bobo ya k'ank'ance idonsa dasukayi jaa yana kallonsu khairiyya dasukayi tsuru², yasan tabbas idan yayi magana saiya fallasa asirin muryarsa, to amma bazai iya k'yale yarannanba.
Rahma tara6a tagefensu khursiyya zata fice yace karki fita.
Cak tatsaya cikeda mamakin wannan k'arfin hali irinnasa.
shikam kallonsa yamaida akansu khairiyya ya ce, "ku bakuda hankali Baku iya sallamabane idan zaku shiga waje?.
Yaya wlhy bamusan kana nanba munzata ita kad'aice Dan ALLAH kayi hak'uri bazamu sakeba.
Le6ensa yacije yama rasa mizaice musu, tsaki kawai yayi dallah kutashimin kai shashashu, haka za a kaiku gidan miji kunama mutane shirme.
Da sauri sukayi waje, suna fita khursiyya tarufe bakinta da hannu ta shek'e da dariya, itama khairiyya dariyar tasaka, suka tafa suna cigaba da dariyarsu, saidai sukayi mai isarsu sannan khairiyya ta ce, " kai ya bobo an iya mazuran rashin gsky, nakulafa yama rasa mizaice manane shine ya koromu, dariya suka kama tuntsurewa da ita.
Khursiyya ta ce, "yar uwa yau naga ruwan soyayya, dama irinsu ya Abdulmaleek akwai iya soyayya, amma akwai dai mazuran tsiya, badan karyaci ubanaba wlhy saina koma naga mi akeyi yanzu.
Idanu khairiyya tazaro ta ce, " tabd'i wlhy badaniba, kingama tafiyata baza'a kaini gidan miji da karyayyar k'afaba, haka kawai su sunacin tasu soyayyar da allura ni akaima mijina jiyya yakasa nunamin.
Rahma dake bayansu ta ce, "ALLAH ya shiryaku wlhy.
Da sauri suka juyo ganin Rahma yasasu nufowa gareta harsuna 'Yar rigerigen tambayarta ya aikayi tafito?.
Hararar wasa tamusu ta ce, saiya fito yaritsaku wlhy.
Da sauri suka bar wajen itakuma tabi bayansu tana murmushi.

Tundaga wannan lokacin Rahma bata sake bari sun had'a hanya da bobo ba har dare lokacin tafiyarsu yayi.
Bansan miya faruba Ammi tace safna tayi zamanta anan danta tayata wasu ayyukan.
Ina kallon bobo yayi wani murmushi mugunta, Rahma dai batace komaiba, Safna kam jitayi tamkar tafasa ihu Dan Bak'inciki.
Rahma ta ce, "ina Nawal mutafi.
Kinga d'iyata kuyi tafiyarku tunda weekend za'a shiga kuma dukan yaran nan za'a barsu.
Jiki a sanyaye Rahma ta ce, " to Ammi saida safe.
ALLAH yakaimu d'iyata kinji.
Tunda suka fita bobo yake wata 'Yar dariyar mugunta k'asa² itadai Rahma batace dashi k'alaba saidai jikinta duk yayi sanyi.
Da kansa yabud'e mata motar tashiga, shima yazagaya yashiga, har suka fice daga gidan baikuma cewa k'alaba, bayan yahau babban titi yana tuk'i ahankali yad'an juyo ya kalleta ya ce, "matsoraciya har an hau network d'in tsoronne?.
Shiru tamasa kamar batajiba, murmushi yayi yasaka hannunsa d'aya yakamo nata yana murzawa, d'ayan kuma yana tuk'i dashi, batace masa komaiba bakuma ta hanashi abinda yakeyiba.
Wai baza'amin maganaba ne my cute?.
Idanunta tad'ago ta kalleshi ganin hankalinsa nakan titi yasa takauda kai, miye kuma kike kallona?, bobo yay maganar har yanzu idanunsa atiti.
Nifa ban kallekaba, Rahma tafad'ad'a kamar zatayi kuka.
Humyim yarinya zaki maganane, ainasan hanyar dazansaki maganar bara mu Isa gida dai kigani.
Gaban Rahma ne yafad'i, saikawai hawaye yafarabin kumatunta, aranta ta ce, " wlhy ka k'aramin irinna jiya mutuwa zanyi.
Karya kwana yayi yashiga layin gidansu, anguwar shiru babu kowa sai haushin karnuka, yay hon mai gadi yabud'e masa gate bayan sun gaisa yashige ciki damotar.
Yana tsayawa ko kashewa bata tsaya yayiba tayi wuf tafice, sauri sauri gudu gudu tashige ciki bayan tabud'e k'ofar falon, kafin yak'araso harta shige d'aki ta kulle kanta.
Tabama bobo dariya danhaka yashige d'akinsa yana wata 'Yar dariya.
Tana Shiga d'akin tadafe k'irji tanama kanta dariya, wata zuciyarta ta ce, "kai Rahma akwai tsoro?, yo badole naji tsoroba, wlhy nabari mutuminnan idani zaiyi, afili tayi maganar Tanana kanta dariya.
Wanka ta shiga bayan tagama ta d'auro alwala tafito, shirin barci tayi sannan tahau abin sallah tayi shafa'i da wutiri, tayi addu'ointa tamik'e, aranta tana fad'in yaudai ba'a nemi shayin k'addaraba.
Gado tahaye ta kwanta hankalinta kwance taja bargo ta lullu6a.

Shimadai bobo yana Shiga d'akinsa wankan yashiga, yay shirin barci tsaf, duk abinda yakasance al'adarsa yagudamar sannan yajawo laptop akahau aikin k'a ida.
Har wajen k'arfe d'aya yana gaban laptop sai biyu saura yad'ago yana kallon agogon dake d'akin, mik'a yayi tareda hamma, yarufe laptop d'in yamik'e, dirowar gefen gado yabud'e ya d'au key da wayoyinsa yakashe fitilar d'akin yafice.
d'akin Rahma yanufa yasandai yanzu tayi barci, ahankali yabud'e k'ofar yashiga yamaida yarufe, kallonta yayi kwance akan gado ta k'udindine abargo, aransa ya ce, " yarinyar nan sai abarki, gakida bargo na gsky mai laushi kin 6uge da shiga bargon bogi.
Wayoyinsa yazube adurowar gefen gadon yahau yakwanta ahankali, bargon ya janye yashige ciki tareda rungumeta a faffad'an k'irjinsa mai yalwar k'amshin turare.
Ahankali yasauke ajiyar zuciya tareda lumshe idanu, Alhmdllh yafad'a azuciyarsa.
Rahma kam dabatasan yanayiba takuma gyara kwanciyarta sosai a k'irjinsa, ahankali tarink'a sauke numfashi mai d'umi ak'irjinnasa.
K'ara lumshe idanu yayi yana mai lashe la66ansa da k'yar ya iya control d'in Kansa yay barci.

_washe gari_
Da asuba Rahma tariga bobo farkawa, jinta kamar ajikin wani Abu yasakata saurin bud'e idanu, ganin bobo yasakata zare k'yawawan idanunta, aranta ta ce, "to yaushe yashigone?, mutum tamkar aljani?, k'yak'yk'yawar fuskarsa tazubama idanu, aranta ta ce, " mutumin nan akwai sirrin k'yau, babu Abu mafi d'aukar hankalinta ajikin bobo kamar Sajensa, tanason sajensa sosai danya k'awata sirrin k'yawun fuskarta, ahankali talumshe idanunta tareda kai hannu bisa k'yakykyawar fuskarsa tana shafa sajensa daya kwanta luf luf yanata tashin k'amshi mai dad'i kamar yanzun yasaka masa turaren.
Tunda tafara shafa masa fuska yafarka, ta k'asan ido yake kallonta, aransa ya ce, "ALLAH yabani magulmaciyar mata, anasona ana kaiwa kasuwa, Rahma tajanye hannunta tana murmushi Dan duk zatonta bai tashiba, k'ok'arin zare jikinta tafara daga NASA, jin haka yasa bobo k'ara rungumota, acikin kunnenta ya ce, " guduwa zakiyi kibarni?.
Shiru tayi wai ita a adole barci takeyi, ya ce, "humm nizakima pretending? Bayan kingama shafemin fuska kina shauk'i?.
Rahma ta cusa kanta ak'irjinsa tana dariya k'asa k'asa, shima dariyar yayi ya ce, " oh ni dama matana ta iya gulmar soyayya saikace matar k'auye?.
Itadai luf tayi ajikinsa Dan kunya.
Jin ana kiran assalatu yasashi yunk'urawa yatashi da ita ajikinsa, to madam pretending tashi muyi sallah.
Zame jikinta tayi daga nasa batareda tad'ago ta kalleshiba, shimadai mik'ewa tayi yashiga bayinta ya d'auro alwala, Inda take ya iso yana gyara hannun rigarsa daya nannad'e saboda alwala, sunkuyowa yayi yasumbaci kumatunta sannan yafice yana fad'in saina dawo.
Batace komaiba saidai tasaci kallonsa tagefen ido tana murmushi, yana fita tatashi itama Dan d'auro alwala.
Saida yaje d'akinsa ya canja kayan barcinsa zuwa doguwar Riga sannan yafice masallaci.

Saida gari yayi haske sannan bobo yadawo, lokacin Rahma ma tana zaune akan sallaya tana addu'a bayan ta k'arasa karatun alkur'ani.
Zama yayi suka shafa addu'ar tare.
Kan Rahma ak'asa ta ce, ''ina kwana?."
Bazan amsaba saikin kalleni.
Murmushi tayi tareda rufe idanunta da tafin hannu, kamata yayi yamik'ar tareda zare hijjabin sannan yajata suka zauna a bakin gadon, my cute wai ita wannan kunyar bazata raguba haka?, nafa rage kusan 60% acikinta amma ank'i nunamin hakan.
Murmushi tayi kawai batareda tace komaiba, ya ce, "idan kinaso nakaiki gidan Appa yau saikin kalleni, yafad'a yana tsura mata mayun idanunsa.
Ahankali tad'ago k'yawawan idanunta masu kasheshi ta sauke akansa, kallon ido cikin ido sukema juna, suduka sunshagala cikin shauk'in so, bobo yad'an lumshe idanunsa yabud'e ahankali, cikin muryarsa mai dad'i ya ce, " ina k'aunarki dayawa Rahma, tabbas da ubangiji bai sauya al'amuraba danayi asarar rashin kasancewarki matata, ALLAH na gode maka dakamin wannan k'yauta.
Rahma talumshe fararen idanunta, ta ce, "nice na cancanci gidema ALLAH ya *_Abdulmaleek_*, kaid'in namijine mai wahalar samu acikin maza, zanta godema ALLAH har k'arshen numfashina da kasancewarka mijina, Nawal d'iyata, tabbas kai alkairine ga rayuwata, hawaye yafara bin kumatunta na dad'i......
Ganin haka yasaka bobo fara bata Sumba ako ina najikinta, saida ya yamutsata San ransa, itakam dukda tsoron dake cikeda ruhinta haka tadake zuciyarta tana kar6ar sak'wanninsa.
Rungumeta yayi yana sauke numfashi asarek'e, muyi barci yafad'a ahankali yana gyara mata kwanciya.
Shiru tayi kamar tana barcin, shikam bobo mintuna kad'an barcin yay awon gaba dashi, ganin barcinsa yayi nisa tazare jikinta ahankali tamaida masa filo a madadinta.
Ficewa tayi domin had'amusu breakfast.
Cikin 'yan mintuna ta kammala komai ta gyara ko ina yad'auki k'amshi, abayinsa tayi wanka sannan tadawo d'akinta, mai tashafa tayi 'Yar kwalliya yau harda jambaki tasaka, aiko tayi k'yau tamkar kasaceta kagudu.
Siket dariga tasaka na atanfa fara da adon jajayen fulawoyi.
Masha ALLAH nafad'a araina Dan babu k'arya Rahma tahad'u.
Kum tad'auka tana taje kanta, wani d'an ruwa daya d'id'd'iga asaman gashin yafara tsalle harya sauka akan fuskar bobo.
Bud'e ido yayi ahankali yasauke akan Rahma dake tsaye agaban madubi tana faking d'in gashinta da jan ribom.
Lumshe ido yayi yabud'e yana murmushi aransa yace masha ALLAH.
Itakam dabatasan yanayiba tad'auk'i d'ankwali ta tayi d'auri mai k'yau na zamani, tad'auki 'yan kunne jajaye tasaka sannan takuma feshe jikinta da turarenta.
Juyowa tayi danufi fita saitaga idon bobo akanta, hannu tasa tarufe fuska tana 'Yar dariya, shima mik'ewa yayi zaune yana murmushi, yatako ahankali zuwa gabanta, hannunsa biyu yasaka yarik'o k'ugunta, muryarsa anarke ya ce, "beautiful Lady kinyi k'yau sosai, shine kikamin wayau ko?.
Girgiza masa kai tayi haryanzu hannunta nakan fuska.
Ya ce, " to bud'e fuskar naga kwalliyar tawa ko?, akunyace tacire hannunta, woow my beautiful wife kwalliya namiki k'yau amma bak'yasonyi, todaga yau haka nakeso aringa tsantsaramin wadda zata ringa hanani fita office.
Yabata dariya Dan haka tatuntsure da dariya, shima dariyar yayi tareda rungumeta, bayan sund'an sarara ya ce, "to muje nima kimin wankan.
Idanu tazaro waje ta ce, ''rufamin asiri."
Asirinki arufe yake aii, shima yafad'a yanad'an zaro ido kamar yanda tayi.
Murmushi yayi, shikuma yafita yana fad'in tom bara naje nayi my cute, amma next time bazan d'aga miki k'afaba.
Murmushi Rahma tayi tareda d'aga hannunta sama tana fad'in ALLAH ngd maka daka daidaita al'amurana alokacin dabanyi zatoba.
d'akin tahau gyarawa cikin lokaci k'alilan takammala takoma falo tazauna jiransa yafito.
Shima baid'auki lokaci mai tsawoba yafito cikin k'ananun kaya wando 3½ da k'aramar Riga tashan iska duk farare tas, yasaka Jan silifas ak'afarsa, sai zabga k'amshin turarensa yake na alfarma.
d'agowa tayi tana kallonsa, yasakar mata murmushi itama ta mayar masa tareda mik'ewa, a dinning suka yada zango, tazuba musa abincin tana k'ok'arin zuba nata yarik'e hannunta tareda mata magana da ido.
Zama tayi danta fahimci inda yadosa, indai tak'aice muku dakansa yabata abinci itama tana basa, haka sukaci suka k'oshi tagyara wajen suka dawo falo suka zube.
Rahma takalli bobo ta narke murya, wai bazamuje gidan AMMIN ba?.
Ido d'aya ya kanne mata, ya ce, "a'a yau zamu huta agida musha soyayyarmu my cute.
Baki taturo kamar wata bebyn roba.
Zamewa yayi yakwanta bisa kujera yana murmushi.
Sallamar da akayice takatsema bobo maganar dayayi niyyar yi......
Rahma ta amsa tana maida kallonta ga k'ofa, ta ce, " kushigo.
Zeenat da baseera suka shigo da sallama, mik'ewa Rahma tayi taje ta tarbosu cikin farincikin ganunsu, zeenat ta ce, "oh ni Autar ummy amare.
Hannu Rahma tasa tarufe fuska tana fad'in kai aunty zeenat, baseera ta ce, " Yar lukutar ummi kin k'ara kibafa, aunty baseera kema hadake ko?, Rahma tayi maganar cikeda shagwa6a.
Dariya sukayi tareda k'arasawa cikin falon, baseera da zeenat suka kalli juna Dan basuyi zaton bobo yana nanba.
Zama sukayi suna gaisheshi, baiko kallesuba ya amsa da lfy amma fuskarsa asake, mik'ewa yayi yana fad'in yakuke?.
Sukace lfy lau wlhy.
Fita yayi harabar gidan danya basu waje, dandanan Rahma tacika musu gaba da kayan ciye ciye, ta zauna suka gaisa.
Zeenat ta ce, "nibanji motsin mutuniyarba.
Wai aunty safna?.
Sukace eh.
Lah tana gidansu ya Abdulmaleek aii, a can takwana wlhy. Dama tunda naganku nasan zuwantane tunda Baku ta6a zuwaminba.
Dariya sukayi baseera ta ce, " a'a dama gunki mukazo ko zeenat, gyad'a kai zeenat tayi tana dariya.
Daganan hira sukashigayi, bayan kamar minti30 suka mik'e tareda alk'awarin suma zasu halarci bikinsu khairiyya d'in.
Godiya tamusu tarakosu har harabar gidan, bobo nasaman mota zaune, suka masa sallama sannan suka tafi.
Dirowa yayi daga saman motar idonsa akan Rahma, batayi auneba taji yad'auketa cak kamar jaririya yanufi cikin falon da ita.
Direta yayi saman doguwar kujera suna dariya, yakwanta tareda d'ora kansa saman cinyarta suna kallon juna, ya ce, "wad'an nanfa daga ina?.
K'awayen aunty Safna ne?.
Baice komaiba, saima ya kauda zancen da d'akko wani daban.................

*_"Dan ALLAH duk masoyina yamin addu'a acikin sallarsa, ALLAH yabiyamin buk'atata ta alkairi, yakuma azurtani da abundana nake buri na alkairi."_*
😭😭😭🙏🏻🙏🏻🙏🏻

*_luv you oll_*
*_(((S))).......2017_*
[11/12, 2:58 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•{🅱🅾🅱🅾}•_

*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*

*_duk Wanda yasake d'aukar number ta yay amafani da'ita ta hanyar dabata daceba, dasakani a group d'in banza, ko turomin sak'on banza ta PC ALLAH ya Isa ban yafeba, nabarsa da ALLAH shine zai sakamin, tunda nayi magana harna gaji ank'i bari._*
😭😭😭😭😭😭

6⃣0⃣

Wunin ranar gaba d'aya haka bobo da Rahma suka kasheshi asoyayya da tattalin juna, dukda Rahma tanad'anjin kunyar bobo har yanzu.
Ganin shiru basuzoba Ammi takira bobo tana tambayar ko jikin Rahmar ne har yanzu?.
Cikin Sosa kai na jin kunya ya ce, "a'a ammi taji sauk'i bamuzoba daine kawai, sai gobe idan ALLAH ya kaimu.
Murmushi Ammi tayi ta ce, " toshikenan ALLAH yakaimu goben tunda dai lfy Alhmdllh, ka gaishemin da ita
To Ammi zataji.
Rahma dake kwance ajikinkinsa ta ce, "ya Abdulmaleek ko kunya bakajiba Dan ALLAH.
Murmushi yayma tareda fad'in kunyar wa zanji?.
Ta Ammi mana.
Nanma murmushin yasakeyi batareda yace komaiba.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Shirye shiryen biki ya kankama sosai, hidima akeyi babu kama hannun yaro.
Rahma da bobo kan sai godiyar ALLAH, soyayyarsu suketa zubawa kamar babu gobe, amma dai baisake mata komaiba Dan yana tausayinta sosai, kuma bobo ba irin fitunannun mazan nan baneba, tattalikam tana shansa, azuciyarta har mamakin bobo takeyi Dan bata ta6a tunanin yanada sauk'i hakaba, ada tana masa kallon muskili masifaffe.
Amma yanzun data k'ara kusanci dashi saitaga Bahaka bane, dukda yanada fad'a amma sai anta6oshi yakeyi.

Safna kam abin duniya ya isheta, k'iri² Ammi tahanata komawa gidansu Rahma, kayantama ranar gabad'aya bobo yakawomata gidan Ammi, bak'aramin 6aci ranta yayiba dantasan wannan Duk shirin bobone.
Yau tunda safe take tsumayensa amma yak'i zuwa gidan kamar yanda yasaba, suna zaune itadasu khairiyya dake had'a kayansu saboda daga gobe shagalin biki zai fara.
Kad'an kad'an saita lek'a window d'akinsu khairiyyar Dan daganan ana hangen Wanda zaishigo gidan, ta kalli agogon hanunta tareda yin tsaki.
Khursiyya ta ce, "aunty safna lfy kuwa?.
Murmushin yak'e tayi tareda wayancewa ta ce, " wlhy ya Abdulmaleek nake jira sonake nakar6i sak'o awanjensa.
Su khairiyya basu kawo komaiba aransuba sukace ayya k'ila yanacan yana shan sharafin soyayarsama, kinsan su ya Abdulmaleek sai addu'a, k'ila kuma bazaizo gidanba saiya tashi daga aiki Dan wataran haka yakeyi.
Dammmmm safna taji gabanta yafad'i, azuciyarta ta ce, "soyayya kuma?, wani kululun bak'in ciki yatokare mata mak'oshi ta had'iyeshi dak'yar, zamewa tayi takwanta visa gadon su khursiyya tana sauk'e ajiyar zuciya wadda su bama sukulaba hankalinsu nakan rigima akan wani wandon jins dakowa ya ce, " yanaso sukahau kokawa, can ALLAH yabama khursiyya sa'ar kwacewa daga hannun khairiyya ta sambad'a da gudu zuwa waje.
Itama khairiyya ta take mata baya tana fad'in wlhy baki isaba saidai kowa yahak'ura mu badashi, daidai zasushiga d'akin Ammi bobo yashigo falon da sallama.
Sanye yake cikin suit blue, komai na jikinsa blue ne amma banda belt da takalmi dasuka kasance jajaye, dressing d'in bak'aramin feeting d'insa yayiba, masha ALLAH.
hannunsa yatura cikin aljihun wandonsa yajingina da kujera yana kallonsu khairiyya daketa zagaye falon batareda sunkula dashiba.
Ganinfa bamasu gansaba yasakashi daka musu tsawa, kai!!! Wane irin iskancine wannan?, zaku maida mana gida filin polo?.
Can suka tsaya suna mazurai, yacire hannunsa daga aljihu ya nunasu Ku nakula kafin kubar gidannan saina ta6a lfyar jikinku?, dannaga wani tashen iskanci kukeji yanzu?, to ubanmiye ya had'aku?!!.
suduka saida sukad'an razana da tsawar dayayi, sukad'anja baya khairiyya ta CE, "Yaya wandonefa nad'auka shine ta kwace tagudo.
Tsaki yayi ya ce, " wandon nawaye?.
Da Sauri khursiyya ta ce, "nawanefa, itama khairiyya ta CE, " Yaya k'arya takeyi nawanefa.
Kansa yadafe Dan suna Neman samasa ciwonkai ma wlhy...
Ammi tafito ta ce, "miya faru kuma tom and Jerry?.
Suduka suka nufi Ammi suna mata bayani.....
Hannu Ammi tad'aga musu ta ce, " ainagaya muku kubar sayen Abu guda d'aya saboda gudun irin wannan ranar to gashinan kun saya kuma yanzu bawaje d'aya zaku kasanceba sannan kowa yanaso.
Khairiyya tayi kwalkwal zatayi kuka, Ammi tafasan Nafi son wandon kuma nace ta d'auki rigar nitabani wandon amma tak'i yarda.
Hannu bobo yamik'a ya ce, "kubani wandon....
Jikin khirsiyya na Rawa tamik'a masa, yana kar6a ya haura saman Appa batareda yasake maganaba.
Khairiya tafara hawaye tana hararar khursiyya Ammi ta ce, " wlhy ALLAH yabaku sa'a kunsandai halin mukarram sarai ba bak'oku bane, idan darabon saiya zaneku kuna a amare kukuka sani, idan kunason kanku da arzik'in toku kama kanku danni babu ruwana wlhy, tana gama fad'a itama tahaye saman Appa.
Jiki asanyaye suka koma d'akinsu, Safna ta kallesu tana fad'in kukuma lfy INA wandon?.
Baki Khairiyya ta turo ta ce, "bataja ya Abdulmaleek ya kwaceba.
Zumbur safna tamik'e tana fad'in yazone?.
Basu tanka mataba Dan duk haushinsa ya ishesu.
Itama bata saurari amsa daga garesuba tafito falon, jin k'amshin turarensa daya tafi yabari yasakata murmushin jindad'i, tasan yanzu yana wajen iyayensa danhaka tafito harabar gidan.
Ganin motarsa yasakata k'ara sakin wani murmushin, bud'e gaban motar tayi tashige Dan bai kulleba.

Shikam yanayanacan gaban Appa suna magana.
Appa ya ce, "Mukarram tunda Alhaji sunusu dala yabada hak'uri miyasa bazaka hak'ura dakaishi koti ba, bakamar yanda kayi niyya tun farko ba?.
Appa idan na k'yaleshi to bansan mizaimin agaba ba, badan ALLAH ya tak'aita wahalabafa nasan yaransa zasu iya kashe Rahma da Nawal alokacin nan, Amma shine yanzu zai dawo yana 'Yar murya wai ayi hak'iri, naga da ko magana baya maka amma dayake yanzu yasan miya shirya shine zaizo yay maka dad'in baki akan kahanani kaisa kotu?.
Hakane mukarram amma ni aganina duk bak'in halin mutum idan yay nadamar kuskure dayayi to yanada k'ayau agafarta MASA tunda ALLAH ma muna MASA laifi kuma idan muka rok'eshi saiya yafe mana, amatsayina na mahaifinka INA rok'ama alhaji sunusi gafara agareka da iyalanka, daga nan idan yasake yunk'urin cutar dawani namu saika d'auki matakin daduk yadace bazan hanakaba saidai na taimaka maka akan hakan.
Shikenan Appa zan yafe MASA to amma Alhaji Abdurrazak fa?, na tabbata tare sukayi k'ulle k'ullen sacemin mata da 'ya.
Eh nasani Dan yafad'ami. Shinema yazugashi akan suyi hakan, to amma wani nacin arzik'in wani aii, to shima Alhaji Abdurrazak yaci arzik'in Alhaji sunusi.
Shikenan Appa zanfad'ama Ammar karsu tura maganar kotu dama sonake agama bikinnan sannan mushiga kotu, tunda hakane zan fad'a MASA najanye amma akwai shari'ar damukeyi da Alhaji Abdurrazak akan kisan Barrister Lawan Usman D/tofa, da ake zargin su suka saka akasheshi akan wata shari'a daya tsaya da lauyansu kuma yasamu nasara.
Ranar dayaje office d'ina danyimin gargad'i kuma yaso tabbatar min dahakan saidai bodyguard d'insa yak'atseshi.
Ajiyar zuciya APPA yasauke ya ce, "a'a wannan bazan hanakaba kam Dan waccan shari'ar daban wannan daban Dan haka saidai nace ALLAH yabaka Nasara, Yakuma k'ara kareka daga Sharrin mak'iya da azzalumai, ALLAH yamuku albarka kaida sauran 'yan uwanka.
Ammeen Appa, bobo da Ammi suka amsa.
Daganan wani zancan suka d'akko.
Bobo yakalli agogo tareda mik'ewa, Ammi Appa bara nashiga Office time na wuceawa kuma inada shari'a yau k'arfe 11:30.
To ALLAH yabada nasara jarumin babammu.
'Yar dariya yayi yana k'ok'arin fita, to kugaidamin inna da Baba Dan bazan samu shiga wajensuba nayi latti.
To zasuji idan sun fito.
Ficewa yayi da hanzari, abakin k'ofa yaci karo da Idris tareda ya sulaiman zasu shigo.
Tofa kukuma daga ina haka?, bobo yay maganar yana mik'amusu hannu, gaisawa sukayi cikin musabaha.
Ya sulaiman ya ce, "yanzu nashigo muka had'u da idris zashi gaida su Ammi.
Bobo ya maida kallonsa ga idris, ya karatu idris?.
Alhmdllh yaya komai normal munata fama.
To ALLAH ya taimaka, ni bara nawuce nayi latti.
To ALLAH ya tsare yabada sa'a.
Ameen ngd.
Ya sulaiman ya ce, " yauwa idan katashi kuma Kannada lokaci plss kad'an biyo ta asibiti dama inason ganinka.
Okey babu damuwa saina shigo.
Okey saina ganka shima ya sulaiman yafad'a suna nufar ciki shida idris, shikuma bobo yafito.

Motarsa yanufa hankali kwance yabud'e yashiga yana fad'in masha ALLAH yanzu kuma sai office.
Idan ka gama dani ko?........
Da sauri bobo yakalli gefensa dan son ganin waye?.
d'aure fuska yayi tareda fad'in miyasa kina shigarmin mota?, wama yabaki izinin shiga?.
Wani murmushi Safna tasaki tareda k'ara lafewa cikin kujerar tana shak'ar k'amshin mortar da turaren bobo, tayi far da idanunta tana kallon k'yak'yk'yawar fuskarsa, aibasai anbani izinin shiga motar mijina ba, tayi maganar tana d'an d'aga gira.
Kauda kansa yayi daga kanta tareda k'ara had'e fuska, ke banason k'aramin iskanci fitarmin amiota.
Safna ta marairaice fuska harda hawaye, cikin muryar kuka ta ce, "Dan ALLAH ka saurareni wlhy magana nazo muyi kuma mai muhimmancice.
d'agowa yayi yakalleta haryanzu fuskarsa ad'aure take, ganin tana kuka saikuma tabashi tausayi, bayason mutum yashiga damuwa akansa, yad'an huro iska daga bakinsa tareda kallon jan agogon fatar dake hannunsa 8:45, batareda ya kalletaba ya ce, " nabaki minti5 Dan inada abinyi.
Hawayen fuskarta ta share ta ce, "wlhy minti5 yamin kad'an pls ka k'aramin.
d'agowa yayi yad'an kalleta saikuma ya kauda kai, saidai ki hak'ura kuma saina taso daga aiki Dan yanzu haka nayi latti, so idan nadawo zanzo nan saiki sameni amma ki tabbata magarki tanada muhimmanci, kuma ki tabbata itace magana tak'arshe dazata shiga tsakaninmu daga ita kifita arayuwata, ina d'aga miki k'afane saboda banaso nazama silar rushewar zumincin iyayenmu, sannan bazan iya wulak'anta jinin Rahma ba, dan itama bata wulak'anta jininaba.
Batareda yasake kallontaba yatada motarsa, ya ce, " sai anjima.
Jiki a sanyaye Safna ta bud'e motar ta fito, hakan yayi daidai da fitowar ya sulaiman da idris.
Suduka cikin mamaki suke kallon Safna da kuma motar bobon.
Bobo dake kallonsu ya sulaiman ta madubi yad'anja tsaki, dama abinda yake gudu kenan, ganin ya sulaiman kamar yanufoshi yaja motar da sauri yabar gidan Dan bayason tambaya, musammanma akan safnar.
Cak ya sulaiman ya tsaya yabi motar da kallo har bobo yafice daga gidan, kallonsa yadawo dashi akan Safna dake ida share hawayenta.
Rissinawa tayi tana gaisheshi sannan tara6a ta gefensa zata wuce.
Jimana ya sulaiman yafad'i yana kallonta.
Safna tatsaya harya k'araso gabanta suna fuskantar juna, lfy kuwa mike faruwa?.
Babu komai safna tayi magana muryarta nad'an rawa, shiru ya sulaiman yay yana kallonta da nazarin yanayinta, yad'an gyara tsayuwarsa yana sauke numgashi, ya ce, "keba yayar Rahma bace?.
Yayartace, cewar Safna.
To amma miya had'aki da Abdulmaleek? har kike kuka?.
d'ago ido tayi ta kalleshi, bazata iya kallon idonsaba Dan yana mata kamada na bobo, tayi shiru batareda ta iya cewa komaiba.
Ganin bazatayi maganaba ya ce, " to shiga cikin....
Da sauri tawuce batareda ko juyowaba.
Shima binta yayi da kallo cikin mamakin miye tsakaninta da bobo?, bai zargi komaiba Dan yasan bobo dodon matane, bazai ta6a zarginsa da fasik'anciba, amma tabbas akwai wata ak'asa tunda har bobo yafice daga gidan Dan bayaso suyi magana.
Yabud'e motarsa yashiga zuciyarsa cike da waswasi, shima ficewa yayi da zummar zai tambayi bobo inhar sun had'u.

++++++++++
a6angaren bobo kam yana fita office yanufa kai tsaye.
Sakatariyarsa ta gaishesa cikeda salo kamar yanda ta saba, babu k'arya yau wankan bobo yakasheta, datanada dama har pic zata masa.
Turare tad'auka tafesa tareda k'ara kallon kanta amadubi, komai daidai, tagyara zaman siket d'in material d'inta da rigar, shima mayafin aka sake salon yafawa sannan. Tanufi office d'in.
Masinja Kamilu dake la6e yana kallonta Dan yasan dolene indai oga yashigo saitayi gyare gyarennan ya tuntsure da dariya yana fad'in kai iska na wahalar da maikayan kara, kedai awahala zaki k'are yarinya, mutum kamar wannan aii kasan matarsama abar kalloce, tomizai tsaya kallo ajikinki wannan karfata.
Itadai Sakatariya Madeena😂😜 dabatasan masija nayiba tanufi office d'in cikin takun k'asaita da salon yanga irinta d'aukar hankali.
Bobo na zaune akan kujerarsa ta alfarma yana rubuce rubuce sakatariya tayi sallama.
Bai d'agoba amma ya amsa mata, yad'ora dafad'in waye yazo nemana?.
Lissafa masa tafarayi daga k'arshe ta ce, "ad'arare sai Alhaji sunusi da la..
Tak'are maganar da in ina.
Dukda haka bai d'agoba sannan baice komaiba itakuma baice tatafiba.

Araina na ce, " mulki kenan."

Yakai kusan minti 4 yana rubuce rubucensa saida yagama sannan yad'ago yana linke takardar.
Mik'a mata yayi, tamatso tareda rissinawa takar6a.
Yamaida bayansa yakwantar ajikin kujerarsa yana d'an lilawa kad'an, idonsa akanta ya ce, ke yanzu dakikayi shigar mutunci bakijin kinfi kima a idon mutane ba?, amma da ko kunya bak'yaji kisakko kananun kaya kina tallar jikinki ga jama'ar gari da sunan wayewa, wannan ba wayewa bace shashancine, ki kama kanki sai miji nagari yaganki yasoki, shigar banza babu abinda yake jawomuku sai mazan banza suyita bibiyarku dankoba 'yan iskanbane tofa kallon 'yan iska irinsu suke muku, ki kiyaye banason shashanci.
Kaita gyad'a duk kuma sai jikinta yayi sanyi, ta ce, "sir ngd ALLAH yak'ara girma da d'aukaka yatsareka daga sharrin mak'iya.
To amin, ALLAH yasa mudace yafad'a yana d'agowa daga kwanciyar dayayi akujera, yanuna takardar hannunta, wannan takardar kibama Kamilu yakai office d'in Barrister Kamal Abubakar, yatsaya yakaranta yabasshi Reply yakawo min.
Okey sir madeena sakatariya yafad'a tanad'an rissinawa cikeda girmamawa.
Hartakai k'ofa tajuyo sir baka buk'atar wani Abu?.
Kai bobo ya girgiza mata yana jawo laptop d'insa daga cikin jakka.
Itama ficewa tayi tana fad'in OK sir.

Tana fita ta tararda Kamilu zaune akujerar dake gefen tebir d'inta, fuska ta had'e dantasan gulmace ta kawoshi.
Ilaikuwa kallonta yayi yana 'Yar dariya, madee ince dai yau andace oga ya k'yasa?.
Harararsa tayi tareda fad'in ban saniba magananne ni dalla kar6i oga ya ce, " ka kaima sir Kamal, kuma kajira yabaka Reply ka kawo masa.
Mik'ewa yayi yakar6i takardar, to madee bara naje nadawo muyi magana, tunda har yanzu oga yak'i k'yasawa nisaina taya.
Wata uwar harara tawatsa masa, kaidai shashashane Kamilu, yoko mazan duniya sun k'are aibanga abinda zanyi da sakaren namiji irinkaba.
Tab yarinya aii ba'a fuska ake gane sakaran namijiba.
Tsaki tayi tareda mik'ewa wlhy zanje nafad'ama oga baka tafiba.
Da sauri yawuce a'a Madeena rufamin asiri Dan ALLAH, wannan zakin faman yanzu saiya hau kaina aii.
raka bayansa tayi da harara, taja tsaki tazauna tana mita.

Bobo yakalli wayarsa dake wringing ganin Ammar yasashi d'aukar wayar da hanzari, gaisawa sukayi tareda tsokanar juna kamar yanda suka saba.
Bobo ya ce, "dama kobaka kiraniba zan kiraka.
To miya faru angon Rahma?.
Murmushi bobo yayi, ya ce, " so inaga anjima zanshigo gidan saimuyi magana atsanake yanzu time d'ina k'urarrene nanda 'yan mintuna kad'an zanshiga wata shari'a.
Okey babu damuwa to saina ganka, nima inada ganawa da Governor nanda minti 10.
Hummm mutumina kuna sha'aninkufa, idan kukayi wasa duk ad'aure zakuje lahira Dan daku ake mulkarmu ak'asarnan.
Dariya Ammar yayi ya ce, "masheranci aii kaima ad'auren zakaje indai hakane.
Can abakinka d'an fatan tsiya sai anjima.
Yanke wayar sukayi suduka suna dariya.
Harzai ajiye wayar saikuma yafasa yakira Rahma.
Tana zaune afalo ita kad'ai tana kallon wani India film, takalli wayarta dake wringing, ganin sunan dake a screen d'in yasakata murmushi, *_Nurulk'albee_*, d'auka tayi muryarta can k'asan mak'oshi tace amincin ALLAH ya tabbata agareka ya *_Nurulk'albee._*
Wata sassanyar ajiyar zuciya bobo yasauke, murya akasalance ya ce, " kema amincin ALLAH ya tabbata agareki my *_Nusfulhayat_*. Ina fata kina cikin k'oshin lafiya da kuzari?.
Alhmdllh sai godiyar ALLAH kam.
Wani k'asaitaccen murmushi yasaki Wanda hartanajin sautinsa akunnenta, ya ce, "nagodema ALLAH da kika kasance cikin k'oshin lfy, kinga kenan yau za'a kar6e ni 100/100 abani kulawa ta musamman awajen barci.
Kamar tana gabansa tafara buga k'afafu cikin shagwa6a ta ce, " nidai a'a wlhy inajin tsoro kuma har yanzu wajen akwai zafi.
Yanda take masa magana cikin shagwa6a yasaka jikinsa yin sanyi, k'ara lafewa yayi acikin kujerar yana shak'ar kamshin turarensa dana office d'in, yakuma narke murya can k'asan mak'oshi haba my Angel kedai kincika tsorone kawai, amma yau kwana hud'u ace haryau anajin zafi?, kodai ana gudunane?.
Hannu tasaka tarufe fuska wai ita kunya kamar tana gabansan, nidai Dan ALLAH kabarmin wannan maganar banaso.
'Yar sassanyar dariya yayi harda shashsheka wadda tasaka Rahma shagala tana saurarensa, ya ce, "shikenan idan nadawo gida zamuyi aii, kafinma nadawo kisaka d'iyarki tayi barci, ummuch💋 yamannama wayar kiss, batareda yajira amsartaba ya yanke Kiran.
Lumshe ido Rahma tayi tana murmushi, afili ta ce, ''kai maza sai'a barsu sudai ko kunya basaji?.
Shimadai a can murmushi yayi, yamik'e yana had'a takardu, yad'auki k'atuwar rigarsu ta lauyoyi tareda hular yarik'e sannan yad'akko siririn farin Gil's d'insa yasaka yafice domin gabatar da shari'a...............

*_luv you oll_*.
*_(((S))).........2017_*
[11/12, 2:58 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•{🅱🅾🅱🅾}•_

*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*

*_masu karatu bara namuku gulmar Xoxo da 'Yar ficika,😎 hummm Xoxo cedai Xoxo cedai da Yar Ficika, saimukaje gidan Hafsat Rano aka kawo mana gasashshiyar kaza da lemo🍗🍹🍾hummm ina gaya mukudai, shikenan dai shikenan dai, sai.....🙊um bara nayi shiru kar zarah Bukar da hajja sufad'a musu gobe su sassambad'i k'eyata alungu🏌, kekuma Rano saura kifad'a ehe♀😏._*
_😂luv you so much, my sweet sisters, Hafsat xoxo, Hafsat Rano, 'Yar Ficika & Zarah Bukar, hajjace, Ayusha ilyasu, gaisuwa agareku dafatan Alkairi._
😘😘😘😘😘👌🏼.

6⃣1⃣

*_5:12pm_* bobo yamik'e tareda harhad'a takardun dazai buk'ata agida, yacire laptop d'imsa daga caji yasaka a jakka, bayan yagama had'a komai yakashe kayan wutar office d'in sannan yad'auki rigarsa ta lauyoyi ya sak'ala ahannu, yarataya jakar aikinsa akafad'a yafito.
Da sauri Kamilu yataso yana fad'in oga kafito?.
Nafito kamilu, zan wuce gida kuma.
Kamilu ya washe baki tareda kar6ar key d'in hannun bobo ya kulle k'ofar, fitowa sukayi har wajen mota yarakishi, Dan tuni sakatariya Madeena tana gida, k'arfe hud'u da rabi yake sallamarta ita.
Saida yashiga motar sannan yad'ago yana kallon Kamilu, to kashigo muwuce mana Dan naga garin kamarma hadarine.
Dariya Kamilu yayi yabud'e mortar yashiga yana fad'in oga ai damunar tafara kankamane, nanda 'yan satittika zakaga ruwa yafara wadata.
Murmushi kawai bobo yayi danyasan surutun Kamilu baya k'arewa, ahankali yake Murza kan motar yana kuma sauraren karatun alkur'anin dake tashi amotar cikin k'ira'ar shriek Abdurrahaman sudes, har k'ofar gida yakai Kamilu yamik'a masa kud'i yana fad'in gashi asaima uwargida kaza.
Cikin washe baki Kamilu yakar6a yana godiya, wannan dalilin yanasakashi k'ara ganin kimar ogan nasu, kwatakwata bashida k'yankyamin talaka bare girmankai irinna alhazan birnin nan, gashida alkairi kullum baya gajiyawa.
Har bobo yafice daga anguwar Kamilu natsaye yana kallonsa, saida ya6acema ganinsa sannan yashiga gida cikeda farinciki.
Ganin hadarin nak'ara tasowa yasaka bobo k'ara gudun motarsa cikin 'yan mintuna k'alilan ya Isa gida, guri yasamu yay parking sannan yakwashi tarkacensa yanufi ciki, zuwa sannan anfara yayyafi.
Rahma tana kichin Dan k'ok'arin had'a abincin dare taji ana kwankwasa k'ofa, fitowa tayi da hanzari dakuma tunanin wanene haka? Acikin hadarinnan.
Batayi gaggawar bud'ewaba saida ta ce, "wayene?.
Jin haka yasa bobo niyyar tsokanarta, ya mak'e murya kamar mace ya ce, " nice hafsat Xoxo budurwar bobo.
Gabantane yafad'i gakuma wani k'ululn bak'inciki aranta, cikin masifa ta ce, "ai bayanan saiki koma sai sanda yadawo kizo.
Pls madam ki taimakeni ruwafa na jik'ani.
Yo ya kasheki mana, Rahma tafad'a ak'ufule tareda juyawarta kicin.
Magana yasakeyi yaji shiru, ga ruwa yafara jik'ashi, da Sauri yanufi baya yaduba ko k'ofar kichin abud'e take ta baya, yana turawa tabud'e, yashigo da hanzari Dan tasowar wata iska mai sanyi.
Da sauri Rahma tajuyo dansan ganin waye, ido tad'an zaro waje Dan mamaki, sannu dazuwa tayi maganar a cunkushe Dan tuna abundana yafaru yanzu tsakaninta da Xoxo.
Dariya tabashi danganin kishi k'uru k'uru kwance afuskarta, amma saiya gimtse ya ce, " yawwa.
K'arasowa tayi inda yake tsaye takar6i jakarsa da rigar, sai wani kakkauda kai takeyi.
Lfy kuwa?, naganki haka?.
Lfy lau tafad'a tana nufar cikin falo.
Binta yayi da kallo yana murmushi, zame rigar suit d'insa yayi danta d'an jike yaja kujerar dake kicind'in ya zauna yana cire takalminsa.
Rahma tadawo kichind'in ganinsa azaune yasata binsa da kallon mamaki, dukda yaji shigowarta amma bai d'agoba saida yagama cire takalmin yad'ora k'afarsa fara Sol Asama.
Rahma ta ce, "azuciyarta, hummm jik'afa kamar ba'a takata ak'asa........
Bobo yad'ago shima yana kallonta, nikam Nusfulhayat wana ganin ak'ofar falo tsaye kamar mace?.
Baki Rahma taturo gaba, ta kauda kanta gefe, nima bansaniba.
Ido yazaro waje bakisanibafa kikace?, datazo batayi Knocking bane?.
Hawayen datake mak'alewa suka zubo akumatunta, cikin shagwa6a ta ce, " bakai tazo nemaba, kuma ta ce, "budurwarkace ita.
Yaso ya shek'e da dariya amma saiya dake, yamik'e da Sauri yana fad'in amma kika barta awaje ruwa na dukanta, yanzunan cute sokike kifara korarmin 'yammatane?, kwasar takalmansa yayi ahannu yawuce cikin falon.
Rahma taduk'e kanta ajikin cabinet d'in kicin tana kuka.
Shikam bobo d'akinsa yanufa yana 'Yar dariyar farincikin ana kishinsa Ashe?, kayansa yacire yafad'a wanka.
Itakam Rahma saida taci kukanta ta more sannan tad'ago tacigaba da girkin, jitake dama batayi MASA girkinba, tsaf ta kammala komai tajere a dinning sannan tagyara kichind'in tsaf.
Dubanta takai ga agogon falon, ganin lokaci yayi nisa tanufi d'akinta ta tatada Nawal dake barci Dan magriba ta k'arato, hannunta taja zuwa bayi tawanke mata fuska sannan suka dawo falo tabata ruwa.......hummm ni shinema yau ko ruwan ba'a baniba bare akula dani, maganar bobo tadaki dodo kunnenta.
Da Sauri Nawal takwace hannunta taje tarungumeshi tana fad'in my papa oyoyo.
Shima d'aukarta yayi yad'aga sama, my baby INA kika shigane bangankiba?.
Papa barci nakeyi yanzu momyna ta tadani magriba tayi.
Oh 'yargatan momynta yafad'a yana sumbatar kumatun yarinyar.
Rahma dai tana tsaye tana kallonsu cikeda sha'awa, hannunsa yasa yakare fuskar Nawal sannan yad'agama Rahma gira, kauda kai tayi tanad'an murgud'a baki.
Ya ce, "Niko?.
Nidaifa banceba ehe, itama tafad'a kamar badashi takeba.
Murmushi yayi sannan yadire Nawal, baby sauka nasha ruwa tunda an hanani.
Da d'an gudu Rahma taje gaban firij tad'akko ruwa da cup takawo MASA.
Bobo yayi dariya tareda fad'in ashedai ana tsoron kishiya.
Gaba tayi tashige d'akinta tana tura baki, shikuma yazuba ruwa a cup yasha yana dariya.
Nawal ta CE, " papa yaushe zamu tafi gidan Ammi?, gobene bikinsu aunty khursiyya.
Saida ya shanye ruwan sannan ya ce, "jekiyi sallah idan nadawo masallaci zan sanar miki.
d'akin momynta tanufa shikuma yadoshi hanyar fita, yabud'e sannan yad'an lek'a, ruwa akeyi sosai Dan haka yahak'ura yajuya d'akin Rahma dansuyi jam'i.
Shigar tasa tayi daidai da fitowar Rahma daga bayi, da alama alwala tayi, baice da ita komaiba ya gyara shimfid'ar sallayar, itama ganin haka yasa tagane abinda yake nufi.
Yana gaba suna baya itada Nawal yajasu jam'in magriba.
Bayan sun idar Rahma ta d'akko alkur'ani tana koyama Nawal, shima yana zaune yana kallonsu cikeda jin dad'i, har lokacin sallar isha'i yayi suka mik'e domin gabatarwa.
Saida yamusu doguwar addu'a sannan kowa yamik'e suka fito falo.
Bobo yazube saman kujera yana fad'in wash ALLAH na, Nawal tazauna kusadashi my papa bakada lafiyane?.
A'a baby nagajine kawai....... ga abinci fa....Rahma takatse musu zancen tana kallonsu.
Fararen idanunsa yad'ago yana mata wani shu'umin kallo, ta kauda idonta daga kansa shima saiya ta6e baki.
Nawal tamik'e shikuma ya ce, "nidai nagaji bazan iya hawan dining ba.
Yanda yay maganar ashagwa6e saiyabama Rahma dariya, dinning tanifa tana murmushi, komai saida suka sakko dashi tsakkiyar falon.
Tana niyyar zuba abincin taji ya ce, " kihad'amana a filet d'aya kawai, batace k'alaba tacigaba da zuba abincinta, bayan tagama ta tatura gabansa.
Gyara zamansa kawai yayi yafara cin abincin atsanake, Rahma azuciyarta ta ce, "guy d'innan komai yahad'a, cin abincinsama abin kallone.
Hakadai suka gama cin abincin anutse, daganan aka koma kallo, Nawal najikin papanta kwance yana shafa kanta ahankali.
Tuni barci yad'auketa, yakalli Rahma dake kwance a 2sita tana game da wayarta, momyn Nawal zoki d'auketa tamin barci ajiki.
Mik'ewa Rahma tayi domin d'aukar Nawal amma saiya jawota ta zauna akusadashi, hannunta yarik'e gam sannan yashiga k'ok'arin janye Nawal daga jikinsa cikin dabara.
Rahma ta turo baki gaba, yatsu biyu yasa ya d'alli bakinta, da sauri tasaka hannunta awajen Dan zafi, cikin shagwa6a ta ce, " wayyo bakina.
Habawa yarinya nagafa kamar kinfara rainani, bobo yay maganar yana matseta ajikinsa.
Shinwai ni sa'ankine?.
Da sauri Rahma ta ce, "a'a dantaji zafin d'allar mata baki dayayi. Ya ce, " to miye kiketa wani kumbura fuska?, nifa babu komai kaina yake ciwone.
Ayya my Angel sorry, namiki kamu?.
Kai tad'aga masa alamar eh.
Ahankali ya kwantar da ita acinyarsa, maimakon yamata kamunkai saitaji bakinsa akan nata, tabud'e baki zatayi magana yasamu damar zira harshensa......

🚶🏻‍♀baya najuya musu karsuce nacika saka musu ido.
Saida aka d'auki tsawon lokaci sannan na juyo Dan inada tabbacin komai ya kammala.
Raham nagani tana cusa kanta acikin bobo suna dariya, da alama wani abun yafad'a mata taji kunya.
Ya ce, "kinga tashi muje mu kwanta, mik'ewa tayi cikin jin kunya, ta d'auki Nawal takai d'akinta, kayan barci ta canja mata itama ta canja, tana k'ok'arin hayewa gado saiga Bobo yashigo sanye cikin kayan barci shima.
Kallo d'aya tamasa ta kauda kai, shima baibi ta kantaba yamatsa kusada Nawal yamata kiss akumatu sannan yaja bargon yarufeta yana fad'in saida safe d'iyar albarka.
Itadai Rahma batace komaiba Dan harta kwanta agefen Nawal, jitayi anyi sama da ita, tafara wutsil wutsil da k'afafu wayyo ya Abdulmaleek kabarni barci nakeji, nidai yau bazanbar Nawal ita kad'aiba, pls kabarmu mu kwanta.
Bai sauraretaba har yakaita d'akinsa yadire agadon, tana k'ok'arin tashi yasa k'afa ya danneta, wayoyinsa yad'auka ya kashe sannan shima yahaye gadon yakwanta tareda jawota jikinsa.
Itakam tuni tafara kuka zuciyarta cike fal da tsoro, jin yafara mata abinda hankalinta bazai d'aukaba tafara kuka tana zame zame.
K'ara matseta yayi ajikinsa yana k'ara rud'a jikinta da sakwanni wad'anda sukeyin tasiri ajikinta da zuciyarta, amma kuzarinta na k'ok'arin turesu domin ku6tar kai.
Ina mutumin naku baiko saurara mataba Dan tuni jikinsa da ruhinsa sun Lula duniyar begen aika aikar dayakeyi, da zafifi yake aikamata sak'wannin soyayyarsa, kafin tafarga yad'auki hanyar mallakarta daga ita har zuciyarta Dan tuni itama tabada kai dukda d'unbin tsoro da fargaba dasuka kanainaye ilahinrin lungun da sak'on zuciyarta.

_Hummm masu karatu nima bara naja camryn 🚶🏻‍♀k'afafuna nanufi wajen angona kuma sarkina mamallakin zuciyarta da ruhina_ *_{Abdus'salam)_* d'ina adon zuciyata😘😂.

_washe gari_
Hummm yaukam na iso amakare Dan natarar har Rahma tagama tsaftace ko ina na gidan, takuma had'a breakfast mairai da lafiya.
Zaune na isakesu a dinning suna karyawa, Rahma da bobo dasun had'a ido saisu sakarma juna murmushi, bobo kam harda d'aga mata gira, takan kauda kai tana murmushi Dan gudun kar Nawal tafahimci wainar da suke toyawa.
Bayan sunci sun k'oshi suka mik'ewa tareda yin hamdala ga sarkin sarakuna mai k'yauta da k'ari.
Bobo yad'auki jakar aikinsa ya rataya, yaukam sanye yake cikin wani farin yadi mai laushi, Wanda akaima ado da bak'in zare, rigar dakad'an tawuce d'uwawunsa amma yayi d'as aciki kamar kazauna kayita kallonsa,
_Hummm karkuma ka kalla k'ilu tajawo bau, Rahma ta ce, "kana kalan mata miji🤥, my Xoxo ki kalleshi kad'an keda Rano_o😎.
Rahma tasakama Nawal jakarta abaya sannan tad'auki d'an kwandon abincinta suka fito, itama Rahma sanye take da shadda ruwan k'asa mai turuwa zani da Riga, tasaka farin hijjabi har k'asa Asama.
Saida suka fara sauke Nawal a school sannan Bobo yad'auki hanyar gidan Appa.
Juyowa yayi ya kalleta hayateena awajefa zan saukeki dannayi latti.
Itama kallonsa tayi sannan ta kalli agogon motar ta ce, " k'arfe 7:34am yanzu".
Eh nasani, sonake naje office dawuri yau, nayi duk aikin dazanyi zuwa 4 nadawo gida mukasance tare.
Hannu Rahma tasa tarufe fuska tana 'Yar dariya, ALLAH kana bani kunya.
Murmushi yayi idonsa atiti ya ce, "tom nadaina baki kunya Nusfulhayat d'ina mai kuka, yaya Dan ALLAH kabini ahankali, daddyn Nawal wlhy yauma a kwai zafi, wayyo ummina kizo ki cecen...........
Bata bari yak'arasaba tasaka MASA kukan shagwa6a.
Ohh sorry my cute nadaina fad'a, cikin dariyar shak'iyanci yay maganar.
Maigadi yabud'e masa gate yashiga, ko gama tsayawa da motar baiyiba tafice tayi cikin gida.
Binta kawai yayi da kallo yana murmushi, afili ya ce, "wato idan ka auri yarinya k'arama tana maka ta6ara kaima saika zama ta6ararre, ya shafa sajensa daya kwanta luf, yad'an lumshe ido yana fad'in ALLAH yak'arama ANNABI daraja da fadila da Wasila.
Rahma kin mallake *_Barrister Abdulmaleek Aliyu Abdulmaleek hamshak'i_* gaba d'ayansa da komai nasa, kin mantar dani damuwata gabad'aya, ya ALLAH kak'ara mana soyayyar juna, kakuma nisanta shaid'an daga garemu.

Na ce, " Ameen bobon Rahma.

Fitowa yay shima yanufi cikin gidan, babu kowa afalon sai kamshi dake tashi da sanyin AC.
Shiru yay atsaye yana nazarin gidan, sallamar Baba hansai mai Aiki yasakashi juyowa, ta ce, "a'a Alhaji kaine agidan.
Murmushi yamata sannan yarisina ya gaisheta, baba hansai masu gidan basu tashi bane?.
Khairiyya da khursiyya sun tashi tun d'azu, amma banga Ammi ba gsky.
Okey bara to nawuce office kawai saina dawo.
To Alhaji bazakaci komai bane?.
Ahhh baba nidanake da mata, ai tuni nafita agandu.
Dariyar jin dad'i baba hansai tayi, ta ce, " to madallah Alhaji, ina Nawal da mamanta?.
Nawal na makaranta, mamanta kam tana nan cikin tare mukazo, kud'i yazaro a aljihu yamik'a mata yafice.
Itakuwa tarakashi da k'yawawan addu'oi.

Rahma kam koda tashigo taga falon babu kowa saita wuce d'akinsu khursiyya, cikeda ihun murnar ganinta suka tashi suka ruk'unk'umeta, akan gado suka zube suna dariya.
Daga nan hira suka farayi.
fitar bobo badad'ewa safna tafito daga bayi, dama tana wanka sanda Rahma tashigo.
Rahma ta gaisheta, da k'yar ta amsa, itakam batabi takantaba Dan abunda su khairiyya suke nuna mata ya d'auke hankalinta.
Khursiyya ta ce, "aunty Rahma wai waya kawokine?."
Ya Abdulmaleek mana Rahma tafad'a tana dariya.
Kai yana ina?.
Inaga yakoma Dan yace dama bazai shigoba sauri yakeyi.
Ajiyar zuciya Safna ta sauke aranta ta ce, "yagama guje gujensa yazo yasameni daram.
Sudai su Khairiyya dabasusan tanayibama hirarsu suketa zugawa suna kwasar dariya kamar wasu k'awaye.................

*_💃🏻Taka rawar gani akalla kome kayi kanka duniyace, mai jimirin zama cikinta, shike zuga kansa d'an magori._*

(zancenka haka yake nura m inuwa😎).

*_luv u oll_*
*_(((S)))........2017_*
[11/12, 2:58 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
🅱🅾🅱🅾

*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*

*_yau gaisuwar da shafin duk nakune sister Fertymerh xarah & Nafi Anka, alkairin ALLAH yakai muku aduk inda kuke, bilyn Abdul na gaisheku tareda bobon Rahma._*
_I Luv you manya manya😘😂_
6⃣2⃣

Sai wajen k'arfe biyar su bobo suka dawo gidan, kamar had'in baki suka dawo kusan lokaci d'aya suduka hud'un, bayan kowa yafito daga motarsa suka gaisa cikeda k'aunar juna.
Ya Hamza ya ce, "lallai gida yafara kar6ar bak'i irin wannan hayaniya.
Dariya sukayi gabad'aya, ya ishaq ya ce, " tokumu k'arasa ciki..
Cikin falon suka nufa suna 'Yar hirarsu da dariya.

Na ce, "masha ALLAH, biki ya kankama Dan falon yad'an cika da bak'i wad'anda suka iso yau, ga hayaniyar yaransu ya ishaq daketa wasa da yara sa'anninisu bak'i.

Su bobo suka rissina suna kwasar gaisuwa, kowa kallonsu yake cikeda sha'awa, bayan gaisuwa aka ta6a 'Yar hira da tsokanar juna, shidai bobo banda murmushi babu abinda ya iya, dama haka yake ko tsokanarsa kakanni sukeyi iyakarsa murmushi, amma baya iya maida murtani, saidai 'yan uwansa idan suna kusa su kare masa.
Yanzuma wata 'Yar tsohuwa ke tsokanarsa, ta ce, " mai sunan Alhaji wai kaidai kana nan babu canji?, maganama wahala take maka bare dariya?.
Nanma murmishi kawai bobo yayi kamar yanda yasaba baice komaiba.
Ya sulaiman ya ce, "Hajiya iya aii maganar Abdulmaleek tsada gareta saikin saya da kud'i.
Yo sule mizanyi da maganarsa nikam barema na siya, wannan sai matarsa dai amma baniba.
Dariya suka saka gabad'aya falon.
Bobo Yakama gemunsa nagayu yana shafawa fuskarsa cikeda murmushi, ganin zasu saka rayuwarsa gaba yamik'e ya haye saman benen, aiko suka rakashi da dariya, ya ishaq ya ce, " Hajiya iya kinga kin koreshi?.
Isahaqa ai dankar yayi maganane yatashi, nibansan halinwa mai sunan Alhaji yakwasoba?, tunda nake ban ta6a ganin muskilin mutum irinsaba, mifa zan iya k'irga maganarsa mai tsawo danaji atsawon rayuwata, mutum kulum dund'un dunkum, sai murmushi shima idan ya gadamar yi.
Dariya aka sakeyi, su ya Hamza suka mik'e suna dariya, suma sama suka haura, cikin dariya da zolaya ya Hamza ke kiran Dund'un Dunkum! Kana inane?.
Bobo dake zaune kusada Ammi yaturo bak'i gaba, ammi kingansu ko?, wlhy nasan dani suke.
Murmushi Ammi tayi kafin tabashi Amsa su ya sulaiman suka shigo d'akin suna dariya dacigaba dakiran dund'un Dunkum.
Ya Hamza ya kalli bobo haba Dund'un Dunkum ya munata kira kaki amsa mana?.
Hararsu yayi cikin sigar wasa, ya ce, "halan faratun tsohurcan ce tafad'i sunan nan?.
Ammi dake k'unshe bak'i tana dariya ta rankwashi kan bobo, mukarram k'aniyarka wace faratun?..
Uhhhchch bobo yafad'a Dan zafi yana dafe kai, wayyo Ammi ALLAH da akwai zafi.
aidama dankaji zafin namaka tayi maganar tana k'ara kai masa wani rankwashin.
Da Sauri ya kauce, su ya ishaq suka saka dariya, gefe bobo Yakoma yana turo bak'i kamar wani k'aramin yaro, sai shafa Inda Ammi ta rankwasheshi yakeyi.
Sudai su ya hamza dariya suketa masa.
Ana cikin haka Appa yashigo d'akin da sallama, duk cikin dariya suka amsa harda ammi, Amma banda bobo dake gefe zaune ya shagwa6e fuska.
Tofa dariyarmi kuma akeyi uwa da 'yayanta?, Appa yafad'a yana zama abakin gadon Dan duk su ya Hamza suna ak'asan kafet ne zaune.
Bak'i bobo Yakuma turowa ya shagwa6e fuska kamar zaiyi kuka, Appa nifa sukema dariyarnan.
Kai kai kowa ya saurara, yazaku tasamin babana a gaba kuna dariya?, haba Ammi harda ke?. Babana zonan naji miya faru?..
Tasowa bobo yayi yazo yazauna kusada k'afafun Appa, yad'ora Kansa bisa cinyarsa, Appa yasaka hannu yana shafa kan bobon dayawani narke kamar yayayye.
Babana mikayi ake maka dariya haka?.
Appa ba Hajiya iya bace tacemin wai Dund'un Dunkum shine suka tasani gaba da dariya, ita kuma Ammi Dan nacema Hajiya iya 'Yar fara shine tarankwasar min kai, kumafa kaina harya fara ciwo.
Shima Appa sunan yabashi dariya wai Dund'un Dunkum, amma saiya gimtse saidai yayi murmushi, yacigaba da shafa kan bobo kaga mukarram d'ina barsu duksai na Rama maka, kowa saimun za6i suna sannan musaka masa.
d'agowa bobo yayi yana dariya shima, aii Appa harnama tanadi sunan dazan saka musu sai ranar deener zan fad'a idan za'a gabatar da manyan yayye yakare maganar dayimusu gwalo.
Appa yasaka dariyashida Ammi, sukam su ya ishaq kowa ya tsaya da dariyarsa suna hararar bobo Dan sun San zai iya aikatawa sarai.
Ya sulaiman ya ce, "haba bobon Ammi garadai kafad'a anan komai ya wuce.
Hum'im ban yarda da wayonba a can zan fad'a dankuji ehe.
Kaga sulaiman barsa yafad'a d'in , ALLAH yakaimu muma aisaimu fad'a, muce INA yayansu Amarya Dund'un Dunkum.
Appa ka gansuko?, bobo yay maganar cikeda shagwa6a.
Yanzunkam kowama saida yadara harsu aunty Rasheda dake k'ok'arin shigowa Dan gaida Appa, dama duk suna tsaye tun d'azun sunajin diramar family d'in, kowa sai kunshe bak'i take tana dariya dankar ajisu, zuwa yanzun sun kasa rik'eta Dan haka suka sheke da dariya suduka suna shigowa cikin d'akin.
Ya Hamza ya ce, "ALLAH bobo kaji kunya, wai yaushene zaka daina shagwa6ar nan takane?, Rahma kina fama gsky.
K'asa Rahma tayi da kanta tana dariya, Dan maganar ya Hamza tabata kunya.
Bobo ya kalli Rahma dake dariya tana to she bak'i da hannu, ba k'aramin birgesa tayiba.
Safna ma dai yau ba abarta abayaba Dan dariyar takeyi, ba k'aramin birgeta shagwa6aar bobo tayiba.
Saida aka tsagaita da dariya su Rahma suka gaida Appa, ya amsa fuskarsa wasai.
Mik'ewa su Aunty Sameera suka fara da zummar Fita su basu waje.
Appa ya ce, " a'a INA zakuje kuma?, kuzauna ayi hirar zumunci asamu ladan juna, komawa sukayi suka zazzaauna cikeda kunya da k'aunar sirikan nasu masu kamala da dattako.
Hira aka cigaba dayi cikin farinciki har aka kira sallar magriba kowa ya mik'e mazan suka wuce masallaci, sukuma kowa yayi alwala sukayi agida.

Basu dawoba saida akayi isha'i.
Safna dake la6e ajikin motoci tayi saurin rik'o rigar bobo.
Da Sauri yajuyo dansan ganin waye?, ganin Safna yasashi saurin zare ido, ya maida kallonsa gasu ya ishaq yaga babu Wanda yajuyo harma sun shige falo, hamdala yayi azuciyarsa dabasuga aika aikar da Safnar tayiba.
Juyowa yayi yana kallonta fuska a gimtse ya ce, "sakarmin Riga.
Babu musu tasaki Dan gizagon fuskarsa yabata tsoro, ta marairaice fuska kamar zatayi kuka ta ce, kacika "alk'awari.
Yagane mitake nufi amma dukda haka saiya yatsine fuska ya ce, " alk'awarin mi?, ke nifa kin addabawa rayuwata.
Safna ta marairaice fuska saiga hawaye sharrrr, ta ce, "bobo kana wulak'antani saboda ALLAH ya jarabceni da Sonka ko?, pls ka taimakeni ka taimaki rayuwata, wlhy sonka zai kasheni Abdulmaleek, bana iya barci, Sonka yana neman haddasa k'iyayya tsakanina da 'Yar uwata, Dan ALLAH karda kayadani Abdulmaleek wlhy Sonka zai halakani, inasonka INA Sonka fiyeda son dAnakema kaina..... Takasa k'arasawa saboda kuka dayaci k'arfinta.
Shikam tsayawa kawai yayi yana kallonta, zuwa yanzu tafara basa tausayi, jiyayi zuciyarsa tana shawartarsa daya taimaketa koda da nasihane k'ila tagane ta farka daga nannauyan barcin daya d'auketa.
Yad'an lumshe idanunsa yabud'e akanta, kinga tashi yafad'a cikin muryarsannan mai dad'i da amo.
Safna ta tashi tsaye tana share hawayen fuskarta.

A can ciki kuwa saida su ya sulaiman suka zauna sannan sukaga babu bobo.
A'a INA Abdulmaleek ya tsaya?, cewar ya ishaq.
Kasansa shida baba mai gadi yanzu haka yana can.
Ammi ta ce, "Rahma jeki kira mijinki yazo yaci abinci tukunna saiya tafi suyita hirar.
Akunyace Rahma tamik'e, zata fita Appa yafito shima daga d'akinsa, ya kallesu ya ce, " a'a INA mukarram d'in?.
Gashi can antafi kiransa wajen baba mai gadi.
To Aida kun k'yalesa babu dad'i suna hira kuma akatsesu, shima bazaiji dad'iba malam salen, daga yau kar a k'ara haka kunji?.
Insha ALLAHU Appa baza'a sakeba suka had'a baki wajen fad'a.

Rahma kam tana fita domin kiran bobo, harta kusa tsakkiyar gidan saita hango safna da bobo tsaye safna tana masa murmushi, badai ta hango fuskar bobo ba Dan ya juyasaiata baya, Dan haka batasan shi miyakeyiba, amma wata zuciyarta tana shaida mata shima murmushi yakeyima safna, tsayuwar sojan badakkare tayi, bata gama farfad'owaba ta hangosu sun nufi hanyar lambun gidan, jitai hawaye nabin kumatunta, yaukam abinda take zargi ya tabbata, inhar bobo da Safna ba soyayya sukeyiba a6oye mizaisasu ware kansu alambu kuma arin wannan lokacin?.
Ta share hawayenta tareda cije le6enta da k'arfi, juyawa tayi takoma cikin gidan, ta daure ta ce, "yana tareda baba suna hira awaje.
Appa ya ce, " kinga Rahma barsa kawai, idan sun gama yazo yaci abincin.
Jinjina kai tayi cikin ladabi ta ce, "to Appa."
Amma azuciyarta saitace aibama saiyaci abinciba soyayya zata k'osar dashi, d'akin su khairiya tashige tashiga bathroom tasha kukanta San ranta, zuciyarta sai tafarfasa takeyi Dan bak'in ciki, jitake gaba d'aya yau tatsani bobo dakomai nasa.
Haka tasha kukanta, bata fitoba saida taji aunty ummy na kwala mata kira tazo suci abinci, wanke fuskarta tayi tafito tana murmushin yak'e, ganinan aunty ummy wani abune yashigarmin ido shine nake cirewa.
Ayya sannu yafita ko?.
Eh ya fita aii ruwa naita sakawa.
To sannu, muje muci abinci ko.
To kawai tace mata suka fito falon k'asa inda kowa yake har Ammi, mazan ne kawai babu suna sama tareda Appa.
Aunty Sameera ta ce, "a'a INA safna wai?.
Da sauri Rahma ta ce, " tana waje tana waya, aii muci abincinmu kawai wannan ba yanzuba, idan tafara waya sai ALLAH.
Dariya sukayi gaba d'aya, aunty rasheeda ta ce, "wlhy kubarta ta soye abinta, itama muje musha biki, tunda tak'i bobon mu, madai gani ko guy d'in nata yafishine haka?.
Babu Wanda yace komai saidai anyi dariya, harda Rahma datayi na yak'e, tasan sarai habaici aunty Rasheeda tayima Safna, amma bataga laifintaba tunda itama ga aunty Safnar can suna cin dunduniyarta itada mijinta datad'auki so ta d'ora masa ayanzun.
Hakadai sukecin abincinsu, Rahma tanacine kawai badan dad'iba, amma jitake kamar tana cin magani.

Safna da bobo kam suna lambu zaune, bobo ya d'aure fuska kamar bai ta6a dariyaba Dan ganin yanda Safna takafeshi da idanu tamkar zata cinyeshi.
d'an tsaki yaja yana kauda kai daga kallinta, ke kinga inada abunyifa nazo nan nazauna, kuma matata banaso taduba bata ganniba Dan haka miye maganar taki?.
Dukda maganarsa ta 6atama safna rai, musamman dayace bayaso matarsa taduba taga bata nan amma saita danne ta matso hawaye tana shashshekar kuka.
Hannu ya d'aga mata, kinga ba kuka na tambayekiba fa malama.
Share hawayenta tayi, ta durkusa agabansa guywa ak'asa tana cigaba da hawaye, Abdulmaleek pls kasamo mana mafita, nidai nasan kaima kana sona, idan zaka iya daurewa wlhy ni bazan iya jurewa ba ka taimaki rayuwata karta salwanta akan sonka.
Wani murmushin mugunta bobo yayi, ya ce, "tabbas ina sonki amma so na 'yan uwantaka, irin Wanda nakema khursiyya da khairiyya.
So na gsky irin na soyayya da tsan tsan k'auna da begen juna, mai ratsa jijiya da ruhi da 6argo mutum d'aya tak nakemashi, itace Rahma, my Nusfulhayat d'ina, farin cikina uwar 'yayana, sarauniya mai sarautar dukkan zuciyata da duk abinda ke cikinta.
Safna kamar yanda na gaya miki wannan zaman shine zai zama zama na k'arshe tsakanina dake, kuma itace zata zama magana ta k'arshe tsakanina dake wadda ta danganci wannan, zan baki shawara kuma zan miki nasiha, idan kin d'auka kin huta, idan kin watsar ke wahala, nidai ALLAH yagani nafita hak'k'inki amatsayina na d'an uwanki musulmi.
Zamansa yagyara yana mai k'ara tattara nutsuwarsa waje d'aya.
Cikin murya mai nuna muhimmancin maganar dazaiyi ya ce, "Safna!.
d'agowa tayi tana kallonsa amma bata tankaba.

Ya ce, "Safna ina d'aga mini k'afane saboda darajar Rahma amma nakula ke bakisan zuruba.
Zan baki shawara ta k'arshe atafiyamu Dan inaso mugudu tare my tsira tare..............

*_Luv you oll._*
*_(((S)))......2017_*
[11/12, 2:58 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•{BoBo}•_

*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*

6⃣3⃣

Ina mai baki shawara amatsayina na mijin k'anwarki, ki nutsu kinemi miji kiyi aure kidaina wahalar da kanki akaina.
Amatsayinki na wadda tayi kuskure abaya yakamata kiyi zaman gyarashi yanzu, sannan ki d'auki sona dakike ik'irarin kinayi ki jefar dashi gefe ki tsarkake zuciyarki, ki daina biyema k'awayen banza suna sakaki a hanyar hallaka na bin bokaye.....
Cikin matuk'ar mamaki Safna take kallonsa, azuciyarta ta ce, "a ina yasan wannan?.
Kamar yasan tunanin datake yayd'an murmushi tareda jinjina kai, yacigaba da fad'in kina mamakin ina nasani ko? Humm hakan babu inda zai kaiki wlhy saidai kiyita komawa baya arayuwarki, Safna babu abinda ke cutar da rayuwarki sai son zuciya, to son zuciya kuma facin zuciyane.
Na tabbata ALLAH ya jarabceki da sonane saboda hakan yazamarma masu hali irinnaki ishara.
Da'ace su Abba basuda Rahma dasunji kunya awaccan ranar dakika nuna musu basu isaba, saboda k'ok'arin kunyatasu dakikayi akan dalilinki mara tushe.
Shin alokacin kinada tabbacin sake ganina?, kokuwa idan kin ganni kinada tabbacin zan kar6i soyayyarkine?, amma saboda son zuciya kika bijirema iyayenki akaina, wannan itace jarabawa tafarko dakika fara fad'uwa arayuwarki.
Safna iyayenmu sunfi kowa sonmu Dan haka bazasu cutar damuba, idan baki saniba zan fad'a miki ayau, tunda nake banta6a za6ar matar aureba da kaina.
Matata ta farko ma iyayenane suka za6amin, dukda banasonta amma nayima iyayena biyayya nakar6i k'yautarsu da hannu bibbiyu, biyayyar danamusu ban bijireba sainaci riba, daga ni'ima har Rahma sunzamemin alkairi arayuwata, wadda na tabbata da auren soyayya nayi bazanci riba hakaba, kema na tabbata dakinma iyayenki biyayya dakinyi gamon katar da abinda kikeso, amma kinga sakamakon da bijirewar taja miki yanzu, saidai sharri shaid'an dana zuciya sun danneki kin kasa ganewa bare kiyi nadama harki nemi afuwar iyayenki.
To inamai tabbatar miki idan baki gyaraba haka zakiyita fad'uwa ak'asa, ki k'are rayuwarki a bibiyar tamu rayuwar, gashi mukuma kullum farincikine ke k'ara baibaye rayuwarmu saboda albarkar iyaye dake bibiyarmu.
_amatsayinmu na 'Ya'ya wad'anda iyayenmu sukasha wahala wajen haihuwarmu, rainanmu, karatunmu, tarbiyyarmu, basa son kukanmu, kulada lafiyarmu daduk wani motsinmu, amma ayayin damuka girma muka mallaki hankalinkanmu lokacin daya kamata mu share hawayensu, amma sai suka nemi wata alfarma agaremu muka bijire musu, saboda mu muna ganin mun waye su mutanen Dane, mukuma 'ya'yan zamani wad'anda boko tagina, shin kuwa muna ganin ALLAH zai k'yalemu kuwa?, aganina babu abinda 'ya'ya zasuyi aduniya su biya iyayensu akan hidima da d'awauniyar dasukayi dasu suna k'anana._
Akwai inda zaka iya bijirema iyaye kaci riba, shine idan sunce kasa6ama ALLAH, wannankam ba'a yarda kamusu biyayyaba.
Idanfa ta gsky da tsarin addini za'abi, iyaye akace suza6ama 'Ya'ya mijin farko, idan kuma k'addara ta gifta hartayi zawarci to wannan tanada 'yancin za6ama kanta akaro na biyu tunda ta mallaki hankalin kanta.
Safna kije ki tsugguna ga iyayenki kinemi gafararsu na tabbata insha ALLAHU ko yayane saikinji sona yaragu azuciyarki.
Inhar iyaye na fushi dakai tom dolene kaita tsintar kanka cikin asara, bafa zaka sami sassauciba harsai sun janye fushinsu akanka, tokema ki gwada ki gani insha ALLAHU zaki dace.......

Shashshekar kukan Safna ne yakatsemasa dogon bayanin daya d'akko, d'ago k'yawawan idanunsa yayi yana kallonta, ya ce, "ba kuka zakiyiba inhar nasihata tashigeki, nadama zakiyi, kuma ki d'auki hanyar gyarawa.
Cikin shashshekar kuka safna ta ce, " duk abinda kafad'a gsky ne, amma wlhy akowane dak'ika na rayuwata k'ara sonka nakeyi, narasa yanda zanyi nacireka araina, ina sonka so bana wasaba.
Tabashi tausayi kwari da gsk, Dan haka cikin taushin murya ya ce, "kiyi hak'uri Safna, kimik'a lamarinki ga ALLAH shine zai taimakeki, na tabbata shaid'an nak'ara hura wutar sonane azuciyarki Dan kawai yaraba zumincin dake tsakaninki da 'Yar uwarki, Yakuma cigaba da 6atar dake acikin duhuwa kikasa rok'ar gafarar iyayenki bare harkici riba a rayuwarki.
Zan tayaki da addu'a ALLAH yacire miki sona azuciyarki kema yabaki miji nagari maisonki fiye da komai amadadina, nabaki kwana uku kije kiyi tunani kuma kiduk'ufa da addu'a Nina zan tayaki.
Jinjina kai Safna tayi cikin sanyin jiki, ga hawaye sha6e sha6e afuskarta, yazaro farin handky d'insa daga aljihu sai tashin k'amshi yake yabata.
Hannu biyu tasaka takar6a tareda fad'in ngd ya Abdulmaleek, ALLAH yabiyaka da mafificiyar nasara, yasakama rayuwarka da mafificin alkairi.
Jinjina mata kai yayi tareda lumshe idanunsa fuskarsa d'aukeda murmushi Wanda bata ta6a ganin irinsaba daga gareshi.
Itama mayar masa da murmushin tayi, tashare hawayenta da handky d'in.
Gaba tayi yana binta abaya gabad'aya saiyaji tabashi tausayi Dan baiyi tunanin zatayi sanyi dawuri hakaba.
Cak safna tatsaya tanabin mutanen Dake tsaye da kallo a harabar gidan d'aya bayan d'aya.
Da Rahma suka fara had'a ido, tunda take bata ta6a ganin 'Yar uwarta Rahma hakaba, ta tamke mata fuska tamau kamar batasan miye dariyaba arayuwarta, juyawa tayi da kallonta ga sauran saitaga ya ishaq da matarsa ya Sulaiman da mayarsa ya Hamza da matarsa, wannan ya tabbatar mata sunfitone dazummar tafiya k'ila anata Neman bobo, gaba d'ayansu takula kallon tuhuma da tsana suke mata, k'asa tayi dakanta idonta cikeda hawaye, batason su maidata ruwa, tanason kowa ya fahimceta kuma ya k'aunaceta, juyawa tayi ta kalli bobo, shikam hankalinsa kwance yake, Dan fuskarsa da murmushi ya ce, "oh kunata jirana ko?, bara nama su Ammi Sallama mu wuce.......
Baijira amsar kowa acikinsuba yayshige warsa falon.
Sum sum safna itama tayi yunk'un tafiya Dan tsorata da kallon tsana dasuke mata kuma harda 'Yar uwarta a ciki, da Sauri aunty Sameera tayi yunk'urin Tarar safna amma sai Yaya ishaq yad'aga mata hannu alamar tabarta.
Ganin haka yasaka safna saurin shigewa falon sukaci karo da bobo dake fitowa, kallonta yayi d'an murmushi ya ce, " karfa komai yadameki nida kaina zan warware musu k'ullin kinji.
Kanta ta d'aga Dan koba komai taji sanyi tunda bobo yafara nuna mata kulawa, saida safe tafad'a a sanyaye.
ALLAH yakaimu yay maganar yana fita, Itakuma tahaye sama zuciyarta na k'ara k'arfafata akan karta bari dalilin wasu tubanta ya ruguje.
Koda bobo yafito saiya Tatar ya ishaq nagaya musu karkowa yatada maganar sai bayan biki, suna ganinsa kowa yagyara tsayuwarsa kamar basa maganar komai.
Shima bai nuna musu yaji komaiba yabasu hannu sukayi musaBaha kowa yashiga motarsa, hannun Rahma Yakama saita fisge..
Cikin d'an mamaki yakalleta ta kauda kanta gefe, k'ara damk'ar hannunta yayi yatura amota, Duk abinda ke faruwa 'yan uwansa suna kallonsu amma babu Wanda yay yunk'urin yin magana.
Yana turata amotar yamaida yarufe, shima yazagaya yashiga suka fice kowa Yakama hanyar gidansa.
Tunda suka fice agidan Rahma tafara shashshekar kuka, baice da ita komaiba dukda kukan NATA na ta6a zuciyarsa, tsayawa yayi wajen wani gashin kaza yasaya sannan yadawo motar, gefen Rahma yakalla saiyaga tayi barci, girgiza kai kawai yayi yatada mortar yay gaba.
Bayan sun gaisa da maigadi yashiga cikin gidan yay fakin Inda yadace, baitadasuba sai kawai ya d'auki Nawal yakai cikin gidan, yadawo Yakuma d'aukar Rahma, yana tafiya yana kallon fuskarta daduk yayi jurwayen hawaye, lallausan murmushi yasaki ahankali ya ce, "my Nusfulhayat sarakan kishi, Ashe kema rigimammace?,...da wannan tunanin yakaita d'aki itama, yadawo yakwashi tarkacensa yay ciki.
Bai tadasuba amma cikin dabara yasauya musu kayansu zuwa na barci, yamik'e yanufi d'akinsa, shima wankan yayi sannan yazauna yaci naman ya k'oshi yad'ora da ruwa mai sanyi, yay hamdala ga ubangiji ya mik'e Yakoma d'akin Rahma.
Shima gadon yahaye yakwanta a bayanta tareda rungumeta, hannu yakai danufi shafa fuskarta amma amamakisa sai yaji hawaye sha6e² wasu na korar wasu.
Tashi yayi zaune ya kunna fitilar d'akin yana mai kallon fuskarta, yakai tsawon minti 6 ahaka, amma har sannan kukan takeyi kuma idonta arufe ruf.
gyarama Nawal kwanciya yayi, itakuma Rahma yad'auketa cak yay waje, duk abinda yakeyi tana jinsa amma tak'iyin koda motshin kwarai.
Koda ya direta asaman gado saiya kuma dawowa yakashema Nawal fitila yasake yimata addu'a, Yakoma Inda yabarta anan yatarar da ita, yagirgiza kai kawai yakashe fitilar tareda hayewa gadon.
Jawota yayi jikinsa yarungume, cikin taushin murya ya ce, "my Nusfulhayat!.
Shiru Rahma tayi kamarma batasan da wata halittaba awajen, yakira sunanta yakai so hud'u amma ko motsi batayiba, ajiyar zuciya ya sauke tareda k'ara k'ank'ameta ajikinsa yana aika mata da wasu sakwanni cikin nutsuwa da kwarewa.
K'arfin kukan Rahma ne yak'aru, tad'an fara mutsu mutsu ganin haka sai kawai ya manne bakinsa da NATA........

Hummm saida safenku bobo.

Washe gari tunda yadawo sallar asuba bai Tarar da Rahma ad'akin saba, yata6a k'ofar d'akinta yaji gam. Kyaleta yayi yatafi d'akinsa yakwanta.
Rahma kam tana zaune tana jinsa, saida taji shiru alamar yakoma d'akinsa sannan tafito tahau hidimar gyran gidan da had'a breakfast, fuskarta dukta kumbura saboda kukan datayi, yanzun haka tana aikinne babu ko d'igon walwala atattare da ita.
Bayan ta kammala aikin tsaf tayima Nawal wanka tamata shirin makaranta, itama wankan tashiga, batawani dad'eba tafito, 'Yar kwalliya tayi cikin atanfa zani da riga takama hannun Nawal suka fito falo.
Bayan sun hau dinning ta had'a musu breakfast, Nawal ta kalleta cikeda shagwa6a momyna ina papana?.
Kallonta Rahma tayi da zummar mata magana saiga bobo yafito cikin shigar gayun zamani ajin farko.
Dukda tana fushi dashi ita kanta saida ta yaba, kauda kanta tayi daga kallonsa, yad'an ta6e bakinsa afili ya ce, "gulma.
Tana jinsa kuma tasan da ita yake amma ta share kamar batasan yana yibama.
Sumbatar kumatun Nawal yayi, itama yabata nasa tayimasa, ta gaisheshi, fuskarsa cikeda murmushi ya amsa, yak'arasa inda Rahma take, muryarta can k'asa ta ce, " ina kwana?.
Bai amsaba saida ya sumbaci kumatunta, acikin kunnenta ya CE, "inafata kintashi lfy?, sarauniyar zuciyata.
Batako kalleshiba tacigaba da bama Nawal break abaki.
Shima baikuma cewa komaiba yad'auki cokali yasaka a abincin nasu yanaci, shayin gaban Rahma yajanyo yafara sha, yitayi kamar bata gansaba har suka kammala suka mik'e.
Yauma saida suka fara ajiye Nawal a school sannan yakaita gidan Appa, yanda tashareshi babu magana shima haka ya shareta, saidaifa idan yafaki idonta saiya kunshe baki yana dariyar mugunta, itadai batamasan yanayiba.
Agurguje ya gaisa da mutane yafice Dan zuwa office, bayaso ya had'u da yayyensa ko d'aya.
Gaba d'aya yinin Ranar haka Rahma tayisa sukuku babu walwala, kuma ko kad'an bata kula Safna bare shiga sabgarta.
Dukda Safna bataji dad'in hakaba amma taso ace Rahma ta fahimceta, saidai zatayi hak'uri har shi dakansa ya kwance kullin kamar yanda yagaya mata ajiya.
Ammi taso fuskantar wani Abu amma hidimar saukar bak'i ta d'auke hankalinta gabad'aya, saidai dukda haka saida ta tambayi Rahma gameda kumburin fuskarta, sai Rahman tace tayi zazza6ine jiya da daddare.
Ammi Tamata sannu dukda bata yarda da abinda taceba, amma tabar komai sai zuwa bayan biki.

*_4:15pm._* na yamma aka fara gudanar da kamu wanda ya k'awatar da jama'a, amare sunsha k'yau masha ALLAHU kamar kasacesu ka gudu, dangin angunan sunzo kuma suntaka rawar gani ta burgewa, taron yakasance na mata zallah Dan haka babu su bobo awajen bama su dawo daga aikiba.
Can na hango Rahma tasha k'yau cikin doguwar rigar material blue sun nad'a farin d'ankwali, ankone itada matan su ya Hamza, sunyi k'yau sosai dukda dai yau Rahma bata cika walwalaba amma tana iyakar k'ok'arinta Dan ganin tarage damuwar fuskarta.
Abinda yak'ara mata dad'ima shine zuwansu Basma da ihsan da aunty Ameera, Anty Naja'atu matar ya Muneer, aunty haleema matar ya Shaheed duk sunzo mata, ganinsu yasakata sakin jikinta tanamai jin dad'in ganinsu.
Alhmdllh kamu ya k'ayatar kuma antashi lfy kowa yakama gabansa.
Mutane basu ida barbajewaba su bobo suka dawo, rarraba ido yashigayi danson hango matarsa amma yakasa ganinta.
K'awayensu khairiyya sai fad'in kai guy d'innan ya had'u sukeyi, wau su khursiyya sumusu jagora wajensa.
Khursiyya ta ce, "Ku yanafa da mata wlhy kubari babu ruwana, wlhy ya Abdulmaleek d'an hayak'ine, idanma kuka cigaba da yawan kallonsa sai rankowa ya6aci awajennan Dan haka ku kama kanku.
Wata ta ce, " amma ba gidannan yakeba?, Dan ban sanshiba.
Dariya khairiyya tayi ta ce, "to k'arewar gidannanma shi muke bimawa, dagashi saimu.
Cikin mamaki sukace amma dai wasu sun rasu a tsakaninku?, kumafa mudai bamu sanshiba, kai 'yan biyu kuji tsoron Allah.
Hhhhhh lallai baku yardaba kenan?, to yagirmemu sosai Dan Ammi ta ce, " wajen ahekara 12 yabamu, bayan shi harma ta fiddarai da haihuwa saigamu mun wuntsilo, abinda yasa Baku sanshiba bashida hayaniyane, kuma bakowace sabga bace zaku ganshi aciki, shinefa wanda kukazo bikinsa wata biyar dasuka wuce baya.
Idanu suka zaro, Zainab kabeer ta ce, ''wlhy bamu ganeshiba kinsan da daddare muka Ganshi awajen deener, masha ALLAHU, ina matarsa?.
Tana nan bara zaku ganta aii.

Bobo dabaisan sunayiba yahaye saman mota yazauna Dan bayason shiga falon saboda duk matane, harabar gidan tad'anfi k'arancin mutane tunda an ragu, Taufiq babban d'an ya ishaq yakira, ya ce, "my son ina auntynka?.
Taufiq ya ce, "uncle aunty Rahma?.
Eh, ita.
Yanzu naganta itada heebba sunshiga falo.
Yauwa jeka kiramin ita to.
To uncle.
Babu dad'ewa saiga Taufiq yadawo ya ce, " uncle tana zuwa.
Okey my son, yanzu kuma sai ina?.
Uncle muna tarene nida abokaina.
Kaima gayyan kayo wajen taron mata?, maimakon kabari sai ranar d'aurin aure ko gobe wajen brother's Night.
Uncle aii duk zasuzo shima.
Dariya bobo yayi ya ce, "to na mata.
Shima Taufiq tafiya yayi wajen abokansa yana dariya.

Na ce, " masha ALLAHU yaron yafara zama saurayi, su bobo ankusa ajiye surukai, lol.

Yana zaune awajen yana latsa waya saiga Rahma tafito.
Kamshin turarenta kawai yaji yad'ago.
Kallo d'aya tamasa ta kauda kai.
Murmushi yayi yana kallonta, ya ce, "kai my Nusfulhayat kinyi k'yaufa, kamarma kece amaryar wlhy.
Ganin ta kauda kai ya ce, "madam har yanzu fishinne?.
Batace komaiba itadai, kuma fuskarta asake take gudun kar mutane su fahimci wani Abu.
Ya ce, " my Nusfulhayat yunwafa nakeji, gashi duk mata agidan nama rasa yanda zanyi.
Murmushi mugunta tayi ta ce, "ina Safnar tabaka abinci?, ko sak'one naje nafad'a mata?.
Kallonta yayi ido cikin ido, tai saurin kauda kanta Dan bazata juri kallon cikin idonsaba, shima murmusawa yayi ya ce, " idanma kinyi hakan ai babu laifi, yadiro daga saman motar, ki kaimin falon su inna munacan nidasu ya Sulaiman.
Baijira amsartaba yawuce............

*_"happy juma'at Mubarak."_*🙋🏼🙋🏼🙋🏼🙋🏼

*_luv u oll._*
*_(((S)))......2017_*
[11/12, 2:58 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•🅱🅾🅱🅾•_

*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*

_a *RASHIN SANI* nayi *AUREN K'ADDARA ko BIYAYYA,* mizan d'auketa?, *K'ANWAR UWACE ko KISHIYAR UWA?.* San zuciya yakawo sa6ani *NI DA AMINIYATA*, salon *NAWAFF* yasani fuskarntar *SABON AL'AMAREE*, *KUKAN KURCIYA JAWABINE* dan haka kugane *BAN SAKETA BA* masoyan *ABDUL-MALEEK BOBO* mukasance tare a *BABU SO, MIYA KAWO KISHI?!!!*._👌🏼
_wad'annan sune rukunin jerin books dani bilyn Abdul narubuta a social media._
Zaku iya samunsu a shafina kamar haka.👇🏻
https://mrsbilkisa.blogspot.com
*_sai kunje👌🏼._*
*_BAK'IN HAURE!_*
zaizone a sabuwar shekarar 2018 insha ALLAHU, karku bari ayi babu ku😘.

6⃣4⃣

Binsa tayi dakallo tana k'unk'unai, amma baijitaba Dan yayi gaba abinsa.
Safna tana dagacan saman kujera tana kallonsu, hawaye suka cika mata ido taisaurin saka handkyn daya bata jiya tagoge, ta Yanke shawara yau zatabi su Ameera sutafi gida, Dan inhar tana ganin bobo bata tunanin sonsa zai ragu azuciyarta barema ayi tunanin fita gaba d'aya, amma idan tayi nesa dashi k'ila taji sauk'in zuciyarta, Dan insha ALLAHU tayi tuba na gsky kenan.

Rahma tahad'a musu abincin Wanda dama tun d'azu ta tanada domin su, ihsan da Basma ne suka tayata d'auka zuwa 6angaren inna.
Duk sunacan harda Ammar dawasu mutum biyu dabata saniba, bayan sun ajiye suka gaidasu, idanun bobo nakan matarsa, itama tasaci kallonsa ganin idonsa akanta yasa ta kauda idonta tareda Jan hannun su ilham suka fice.

...........................÷
Bayan sallar isha'i su anty Hafsat sukace zasu wuce, Safna data gama had'a kayanta tamik'e itama, kallonta kawai Rahma takeyi amma batace komaiba, su dama su aunty Ameera tafad'a musu zata bisu Dan gidan yacika damutane kuma Rahma anan zata kwana itama, basu kawo komai aransuba sukace eh gara kawai tatafi gida.
Har harabar gidan tarakasu saida suka Shiga mota taga fitarsu sannan takoma ciki.
Amota Safna cikin dabara take share hawayenta, wata zuciyarta tana fad'a mata anya zata iya daurewa kuwa?, da sauri ta ce, "insha ALLAHU zan iya.

.+.+.+.+.+.
Tafiyarsu Safna babu dad'ewa sosai bobo yashigo falon, wasu kallo sukeyi wasukuwama harsun kwanta, yagaidasu sannan ya haura sama, afalo yatarar dasu zaune sunata kulla kayan rabo, zama yayi yana fad'in wai Kodai yau anan zamu kwanane?.
Kallonsa ammi tayi, ta ce, " nidama zaku barsu su kwanan Aida yafimin, idan bamu gamk'ullin nan yauba nasan zuwa gobe gidannan zai d'inke da mutane.
Kansa yashafa yana d'an murmushi Ammi sudai gama kawai saimu wuce ko zuwa 12 ne.
Hararsa Ammi tayi cikin wasa, ta CE, "fin k'arfi za'a nunamin akan 'ya'yana?.
A'a Ammi mu mun isane.
Hira sukaitayi har su ya ishaq suka shigo suka had'u gabad'aya sukayi k'ullin sannan kowa ya d'auki matarsa sukai gida.

Biki yacigaba da kankama cikin farin ciki, komai yana tafiya yanda yadace, washe gari da safe akayi k'unshi, zuwa yamma gida kam ya d'inke da bak'i na nesa Dana kusa, su Rahma kam aii ko ganinsu ba'ayi Duk sun zama busy, to barema su bobo manya manyan yayye.
Da daddre k'arfe takwas aka fara d'ibar mutane zuwa wajen brother's night dasu bobo suka shirya, abokansu sosai suka gayyato, taron 'yammata da samarine kawai saikuma irinsu bobo masu mata, amma babu yara bare tsofaffi.
Taro yak'ayatar kam masha ALLAH, amare da angwayensu ansha k'yau abin sai Wanda yagani, su bobo suntaka rawar gani irinta manyan yayye, ko INA yashiga yana mak'ale da matarsa abin zak'yk'yau da burgewa, 'yammata kam dayawa sun k'yasa, saidai ganinsa mak'ale da matarsa yakansa sushiga taitayinsu.
Alhmdllh dahaka taro yatashi lfy kowa Yakama gabansa.

_washe gari_
Aka d'aura auren khairiyya Aliyu Abdulmaleek hamshak'i da angonta Ahmad m sadiq, sai Khursiyya Aliyu Abdulmaleek hamshak'i da angonta Zaharadden usman Aliyu.
Masha ALLAH d'aurin aure yatara d'unbin jama'a nanesa Dana kusa 'yan siyasa da masu mulki, 'yan kasuwama ba'a barsu abayaba.
To khairiyya da khursiyya saimuce ALLAH yasanya alkairi yabada zaman lfy da zaman hak'uri.
Hummmm abun mamaki wai harda alhaji sunusi dala a 'yan d'aurin aure, (araina nace su alhaji sunusi anji yaji🌶🤣 ahanun bobonmu😎😂😜) aiko bobo sai antaya MASA kallon banza yakeyi.
Shidai baimasan yanayiba.

Bayan kammala d'aurin aure su bobo sukaima anguna jagora zuwa cikin gidan, shidasu Yaya ishaq duk wankan farar shadda sukayi, masha ALLAH daka gansu kaga 'yan uwa jini d'aya.
Har cikin falon suka Shiga anata gaisawa da 'yan uwa da abokan arzik'i, bakin anguna yak'i rufuwa hakama su ya sulaiman suna cikeda farin cikin yau k'annensu sunyi aure.
Tunda sukashigo falon bobo yaketa baza ido domin hango Nusfulhayat d'insa, rabonsa da ganinta tun jiya bayan sun dawo daga faty.
Ganin duk d'unbin taron Matan falon bai Gantaba har sama dasuka haura aka gaisa dasu ammi nanma bata nan baimaga Matan yayyensaba ko d'aya.
Sakkowa yayi yabarosu a can, wayarsa yaciro a aljihu yafara kiran number ta amma bata d'aukaba, yana nan tsaye yanad'an waige waige saiga Nasiba zata shige itada wasu 'yammata, Nasiba ta gaidashi ya bobo ina yini.
Juyowa yayi danson ganin wanene, oh Nasiba dama kinzo?.
Wlhy nazo jiya Yaya, tunda nazo bangankaba kaida ya sulaiman, amma naga ya hamza da ya ishaq.
Muna nan muma munyi busy ne da yawa, Dan ALLAH ko kin ganemin Rahma?.
Aunty Rahma, naganta anan baya itada umminta da Ammi dawasu mata, saidai ban saniba ko sun koma ciki.
Kai a'a bata ciki, amma ummi da Ammi nagansu aciki.
Okey bara na duba maka ita.
Ok thanks.

Gaba sukayi 'yammatan sukace kai Nasiba wannan guy d'infa?.
Dariya Nasiba tayi ta ce, "shima yayanmu ne.
Ya sunansa?, Dan munsan bobo ba sunan yanka bane.
Hhhhh kukam miye damuwarku da sunansa?, wannanfa ba irin mazannane masu sauk'in samuba, wlhy yanzuma bak'aramar sa'a mukayiba dahar yay doguwar magana......
Hangen Rahma datayi yasata cewa yauwa gama aunty Rahman can bara nakirata nadawo.
Basuce mata komaiba tanufi Rahma dake tsaye itada aunty Ummy hannunsu d'auke da fillatai masu yawa.
K'arasawa tayi wajensu da sallama, cikeda fara'a suka amsa mata, Nasiba ta ce, " aunty Rahma ya Abdulmaleek kam yana nemanki.
Rahma tad'an marairaice murya, wayyo ALLAHna shikuma Dan ALLAH mizan masa yanzu?.
Hararta aunty ummy tayi, takar6i fillatan hannunta tana fad'in zauna Jan aji wata ta k'yasa miki miji, kinga jeki ina nan ina jiranki.
Cikin kunya Rahma tajuya suka tafi itada Nasiba, Nasiba ta ce, "aunty Rahma ALLAH kirage kunyar nan, mazannanfa sunfison surunga ganinka ido atsaye kana basu kulawa, barema irinsu ya Abdulmaleek 'yan Hutu.
Itadai Rahma mirmushi kawai tayi amma batace komaiba.
Tunda suka dosa yake k'are mata kallo cikeda k'auna, kwalliyarta ta tafi dashi kwarai da gsk, sanye take cikin atanfa zani dariga, zanin Rafa siket yabi jikinta da k'yau kamar siket, kwalliyarta daidai misali tayi d'as da ita.......
Saida sukayi sallama sanan yadawo hayyacinsa, yay firgigita yana murmushi.
Nasiba ta ce, " to Yaya gata nan.
Yau Nasiba sannu da k'ok'ari.
Yauwa yaya Nasiba tafad'a tana juyawa cikeda jin dad'in yau ya bobo yamata doguwar magana.
Tana tafiya bobo yamatso daf da Rahma tamkar zai shige jikinta, baya tad'anja tana fad'in mutanefa na kallonka.
Baki yata6e yana fad'in ina ruwana dasu, nifa kema kad'ai nake gani awajen.
Fararen idanunta tajuya tana gyara tsayuwa, itafa haushinsa takeji idanma bai saniba.... K'yass k'yass taji ana d'aukar hoto, d'agowar nan dazatayi aka k'ara mata, Ammar tagani abayan bobo d'aukeda camera, bobo yay masa alamun jinjina sanan yamatsa Kusada ita aka d'aukesu tare, bata ankaraba taji hannayensa biyu bisa k'ugunta, da sauri tad'ago suka kalli juna aka d'auka, gira yad'aga mata.
Bak'aramar kunya abun yabataba Dan haka tajanye jikinta tamatsa gefe Dan kunya, ga mutane sai kallonsu sukeyi, wasu naganin sun dace, wasu kam kishi yahanasu ganin dacewar.
K'awayen Nasiba sikace kar dai itace matarsa?.
Dariya Nasiba tayi ta ce, "eh mana, aii itace yace na nemo MASA.
Kai ammafa itama ta had'u, amma yarinyace sosai yamata yawa, saidai kuma tamore sosai dasamun wananan miji na garari, wata acikin k'awayen Nasiba tafad'a tana kuma k'arema Rahma da bobo kallo da Ammar keta kestasu hotuna.
Ana cikin haka amarema suka fito dasu ya Hamza aka cigaba da hituna harda sauran jama'ar wajen, bobodai duk inda zaka gansa yana manne da Rahma, ita dai duk kunya ta isheta, haka aka gama hituna hardasu Ammi da umminta Dan itama tunda safe tana gidan.
Haka aka cigaba da gudanar da biki awanan yini Alhmdlh kowa kagansa yana tareda walwalarsa.

*_6:30pm_* d'unbin jama'a suka raka amare d'akunansu, sundai sha kuka tamkar zasu shid'e, Ammi ma tasha kuka sosai na rabuwa da 'yan autocinta wad'anda suka kasance su kad'ai mata.
Appa da yayyensu duk sun musu fad'a yanda yadace, hakama dangin uwa Dana uba kowa yamusu daganan aka kwashesu sai gidajensu, Anfara kai khairiyya tunda itace hassana, sanan akai husaina khursiyya.
Bayan kamar awa d'aya 'yankai amare suka dawo kowa yafara shirin tafiya dinner da anguna suka shirya.
*_8:30pm_* aka fara tururuwar tafiya wajen dinner faty d'in data tara d'unbin jama'a na 6angare uku Dan had'ewa akayi domin sauk'ak'ama mutane wahala.
Masha ALLAH amare sunsha k'yau kamar babu gobe, sunyi kwalliya cikin kaya iri d'aya, farin material doguwar Riga, annad'e musu kawuna da golden d'in gwaggwaro, idan kagansuma saika Gaza ganesu abin sai Wanda yagani.
Can nahango su Xoxo su Deejerh kakus, su Sa'adatu sa'ad, zulaihat, mamn haneep, mamn sultan, Maryam zuntu, miss Ayush, deexerh, hawwa, kai idanfa naita lissafosu saina cika muku page d'in taf dasunayen masu karatu, ammafa har wad'anda ban ambataba na k'yallosu awajen.
Har Anfara gudanar da shagali hankalin amare atashe Dan basuga walk'iyar kod'aya daga cikin yayensuba bare matansu, amma yaran duk dangi sunzo dasu, su Nawal ma suna tare dasu daga kai amarya ba'a koma dasuba.
Tsayuwa wasu motoci yasakani gwalo idanu dansan ganin suwaye acikine?.
😳tofa masu karatu manyan yayyene.
Hummm tuwon girma miyarsa nama muka fad'a nida Maman ussy, sai baza ido muke muga wankansu.
Chaiiii!, namuku na IBO, wankafa aka d'auka iya wanka awajennan dankuwa kowa yahad'e cikin shiga ta alfarma shida matarsa, ya ishaq ya sulaiman ya Hamza, oga bobo duk sanye suke cikin wasu dakakkun shaddoji milk colour, sunsha d'inki 'yan ubansu, komai najikinsu iri d'ayane, takalmi hula agogo kai komaidai.
Suma su aunty Rasheeda Anty sameera Anty ummy, Rahma sanye suke cikin less milk da d'igon Silva, sun nad'a d'aurin d'ankwali kalar Silva, suma komai nasu iri d'ayane, cikin hall d'in taron suka dosa kowa rik'eda hannun matarsa, shigowarsu kallo Yakoma sama, kowa yabawa yake azuciyarsa, guri na musamman da aka ware musu suka zauna.
Kai yanzu ran khairiyya da khursiyya yay fes.
Dagananfa al'amura aka fara gudanarwa cikin farinciki.
Awajen lik'i kam manyan yayye sun ajiye tarihi suda matansu, abindai saimuce sambarka.
Dahakadai taro yatashi lfy, anguna sukad'auki amarensu suka maida gida, suma su bobo kowa gidan Appa yamaida matarsa Dan yauma anan zasu kwana.
Washe gari aka gudanar da walima dawuri Dan 'yan nesa su sami damar tafiya.
To dagadai yau biki yatashi, zuwa dare kuma gidan yarage hayaniya Dan mutane duksun ragu.
Sai bayan isha'i su Rahma suka bar gidan amare, kowa mijinta yaje yad'auketa sai gida.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Washe garima dai su Rahma saida suka koma gidan Ammi, suka gyara duk Inda aka 6ata suda 'yan aiki, duk kuma abinda aka aro aka maida.
Sudai su bobo kowa Yakoma kan aikinsa, hakama yara duksun koma makaranta, sai dare kowa yazo yakwashi iyalinsa, daganan kuma sai juma'a kowa ya huta.
Ammi da Appa sai sakamusu albarka sukeyi da jinjinama k'ok'arinsu, sun taimaka an rufama juna asiri anyi angama lfy cikeda farinciki.
Babu abinda kake ganin afuskar 'ya'yan na Appa da matansu sai murmushin jin dad'i.
Dahakadai kowa yay gida.

*_Safna.............._*

🤔🤔🤔🤔🤔✍🏿✍🏿

*_luv you oll_*
*_(((S)))........2017_*
[11/12, 2:59 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•🅱🅾🅱🅾•_

*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*

6⃣5⃣

_wai masu karatu ina Safna?._

ALLAH sarki rayuwa, duk wanan shagali da ruguntsumi da'ake fama Safna nacan tana fama da ciwo batareda kowa yasaniba.
Babu yanda Ummi batayi da itaba akan tashirya suje wajen bikin amma tak'i ta ce, "kanta namata ciwo.
Ummi bata d'auki zancen ciwon nata serious ba dantasan halin Safna sarai da d'orama kai ciwon k'arya idan batason yin Abu.
K'yaleta tayi ta cigaba da jerangiyar zuwa bikin, yayinda Safna ke jiyyar zuciya Dana ruhi, zuwa yanzu tayi ALLAH wadai damai hali irin nata yafi sau dubu, tabbas tagane illar bijirema iyaye dazama akan ra'ayin rik'au, idan tatuna ranar data tuburema iyayenta batason auren dasukayi shirin yimata takan tsani kanta dadukkan rayuwarta, lallai zuwa yanzu tagane sharri zuciya dana k'awa, Dan baseera ta taka rawar ganin wajen zurma rayuwarta ga halaka.
ALLAH sarki zeenat dama kin fad'amin zanyi nadama, amma na k'aryataki, nak'i yarda da zancenki lokacin Sharrin shaid'an Dana zuciya suna d'awauniya dani, sai yanzu nagane ke mai k'aunatace da gsy, kece k'awa abar alfahari agaren......tarushe dawani kuka maiban tausayi.
Da sauri ummi tak'araso gareta tana fad'in Safna lfy kuwa?.
Tashi tayi zaune da sauri tak'ank'ame ummi tana kuka, ummi wlhy nayi nadama, yanzu zan canja, dan ALLAH ki gafarceni keda abba dasu ya munner, wlhy nayi nadama bazan sakeba........
Takuma rushewa da kuka yayinda numfashinta ke sama yana k'asa, k'irjinta tadafe tana fad'in wash ummi zan mutu, ummi k'irjina zai fashe..
Arazane ummi take girgizata tana kwala kiran Safna! Safna!!, ke Safna!!!.
Ina Safna tayi nisa batajin kira, numfashinta yatsaya cak da aiki, afirgice ummi ta ce, " nashiga uku ni sa'adatu mizan gani haka?, wayar safna ta raruma jikinta sai rawa yake takira abba, yana d'agawa tafashe dakuka mai tsuma rai, abban shaheed ka taimakeni kada safna tamutu dan ALLAH.
SHIMA cikin mamaki ya ce, "safna kuma?, miyafaru da safnar?.
Abba Shaheed nidai kataho gida wlhy safna bata numfashi gabad'aya wayyo ALLAH na safna karki mutu, munyafemiki dan ALLAH karki tafi kibarni wayyo safna....
Surutai da sambatu kawai ummi ke zubawa.
Cikin lokaci k'alilan saiga abba da likita harda ya munnir, ai ganin Safna sharaf kamar gawa doctor ya ce, " sud'auketa kawai atafi asibiti, jikinta yawuce adubata agida.
Ya munnir yasa6eta batareda yabarima likita ya k'arasa fad'aba.
Agaggauce suka isa asibiti.
Taimakon gaggawa aka shiga bama safna wadda saidai abinda ALLAH yayi kawai, dan kwance take sharaf babu alamar numfashi.

Masu karatu nimafa atsorace nake😟, safna saidai wani abu ga ALLAH.

Su Abba sai safa da marwa sukeyi ak'ofar d'akin da'aka sakata, ummi kam banda hawaye babu abinda take shar6ewa, Abba da ya muneer sai hak'uri suke bata.

*................................*
Awanan lokacin kam Rahma nagida itada Nawal da direba yad'akko yanzu Daga school.
Bayan Tamata wanka sukadawo falo, Nawal nagefenta zaune tanacin abinci itakuma tana duba buks d'inta taga ko anbasu homework
Nawal ta ce, "momy!.
Na'am babyna, miya farune?.
Nawal tayi 'Yar dariya, momy auntynmu ce ta ce, " wai bankai mata kayan bikiba, shine nace gobe zan kaimata, aizaki bani nakai mata ko?.
Murmushi Rahma tayi tareda d'agamata kai, zan baki my sweety na insha ALLAH.
murna Nawal tafara, itakuma Rahma tana kallonta tana dariya.
Bayan takammala cin abincin ta koya mata homework, suna kammalawa suka fito harabar gidan suna shan iska, Nawal tanata wasanta cikin 'Yar motarta, ita kuma tana zaune tana karatun book awaya dansu Basma sun sakata groups na Novels.
Jin k'arar bud'e gate yasa tad'ago tana kallon hanyar gate d'in dukda basosai take hangowaba amma taga kamar motar bobo.
Agogon dake manne ahannunta ta kalla _4:15pm_ afili ta ce, "lfy kuwa Nurulk'albi?.
Bobo yay farking a inda yadace sanan yafito, sanye yake cikin k'ananun kaya, blue d'in wandon jins da farar Riga mai dogon hannu, yayi k'yau tamkar yanzu yay kwalliyar, jakar aikinsa yad'auka ya rataya sanan yakwashi wayoyinsa, harya nufi hanyar falon saiya jiyo dariyar Nawal da Rahma abaya.
Dawowa yayi yanufi inda yakejin dariyar.
Nawal naganinsa ta tashi da gudu ta taroshi, rungumeta yayi yanamai farincikin ganinta, ya ce, " baby ya school?.
Lfy lau papana.
Masha ALLAH, amma yau ba'aje islamiyyaba?.
Kanta ta d'aga.
Ya ce, "miyasa?.
Shiru tayi Dan tama manta abinda yasa yau bazasu islamiyarba.
Ganin haka yasaka bobo d'agowa yana kallon Rahma, sauke idonta tayi daga satar kallonsa, idonsa yalumshe yana murmushi, afili ya ce, " gulma.
Kallonsa tayi tana turo baki Dan tasan da ita yake, fuska akumbure ta ce, "sannu da zuwa".
Bakinsa yata6e ya ce, " bazan amsaba, aiba haka ake tarar mijiba.
Idanu tad'an zaro tana kuma satar kallon Nawal.
Shima Nasal d'in ya kalla saikuma yamaida kallonsa ga Rahma, gira yad'aga mata yana wani murmushin gefen baki.
Tashi tayi tak'araso gareshi, tamik'a hannu nufinta yabata jakarsa, maimakon yayi haka saiya mik'a mata kafad'arsa duka.
Nawal takuma kalla taga takoma wajen motarta, d'an kad'a idanunta tayi sanan tasaka hannu tazare jakar.
Bak'aramar kasala tasakarma boboba data kad'a idanunta, yalashe la66ansa sanan yamatso daf da ita ya manna mata kiss akumata.
Ja baya tayi da Sauri, harma taso bama bobo dariya saboda yanda ta razana kamar wani maciji ya ta6ata amma yadake.
Ra6awa tayi ta gefensa tawuce, binta yayi da kallo harta shige.
Yakalli Nawal daketa wasanta da mota, ya ce, "baby kijirani yanzu zanyi wanka nadawo.
To my papa, Nawal tayi maganar hankalinta awasa.
Ciki shima yanufa.
Yana shiga d'akinsa Rahma na niyyar fitowa, Ra6awa tayi tagefensa zata fice yay saurin shan gabanta, k'ara kaucewa tayi nanma ya tareta, tad'ago ido tana kallonsa saitaga fuskarsa ta canja yakomamata ainahin bobo nada data sani ada.
Jada baya yayi yajingina da k'ofar, ya hard'e hannayensa ak'irji yazuba mata mayun idanunsa, k'asa tayi dakanta gawani tsoro yana shigarta, jitai miyasama take masa haka?, kodan taga yanzu ya sake mata yana wasa da ita?.
Kallonta yake daga sama har k'asa, shifa ganin yakema tak'ara MASA k'yau da haske, yad'an lumshe idanunsa yabud'e, murya a tausashe ya ce, " Rahma!."
Kanta tad'ago ahankali tana kallonsa, ganin ya zuba mata idanunsa da awanan munafikin kallon NASA k'asa k'asa yasa tamaida idanunta tana wasa da zoben hannunta.
Yakuma fad'in Rahma!.
Na'am ta amsa kanta asunkuye kuma muryarta tana rawa.
Ya ce, "miyeni awajenki?.
Tambayarsa tabata mamaki Dan haka tad'ago tad'an kallesa ta maida kanta k'asa sanan ta ce, " mijinane.
Ajiyar zuciya ya sauke sanan ya warware hannayensa yatako ahankali zuwa gareta, jin k'amshin turarensa yak'ara kusantota yasakata rumtse idanu, nanma tsayawa yayi yana k'are mata kallo, saikuma yasaka hannunsa yad'ago ha6arta, kalleni yay maganar akasalance.
K'ara rumtse idonta tayi Dan bazata iya kallon nasaba.
Yakuma cewa My Nusfulhayat kalleni.
Girgiza MASA kai tayi alamar a'a.
Ya ce, "miyasa?.
Batace komaiba amma tagyara tsayuwarta.
Bobo Yakuma narke murya can kasa tamkar mai rad'a ya ce, ''kina fushi da mijinki ko?, saboda kina zarginsa dacin amanarki yakeyi?.
Hawaye suka ziraro daga idanunta, ahankali suke silalwo visa kumatunta, yad'an cije le6ensa yanamai k'ara tsura mata idanu.
Matsota yakumayi, yasak'alo d'ayan hannunsa kan k'ugunta, ahankali yad'ora bakinsa visa nata, cikin Sauri da rawar jiki tabud'e idanunta saidai tamakaro Dan haryayi nasarar zira harshensa aciki, kissing nata yake cikin kwarewa danuna zalama.
Itakam tun tana yunk'urin kwacewa harta hak'ura tamik'a wuya Dan tuni ga6o6in jikinta sun saki, da wanan damar yayi amfani wajan cud'anyata San ransa, ganin tsayuwa tana Neman gagararsu yad'auketa can sukayi gado.

🚶🏻‍♀sum sum nafito wajen Nawal.

Soyayya sosai Bobo yasha, saida nutsuwa tazo musu sanan Yakuma jawota jikinsa yarungume, muryarsa can k'asan mak'oshi ya ce, "Rahma da gsk kina zargin mijinki da cin amanarki?.
K'ara kwanciya tayi luf visa faffad'an k'irjinsa tana shak'ar daddad'an k'amshinsa, muryarta nad'an rawa ta ce, " nifa ba zarginka nakeyiba.
Ya ce, "to miyasa kike 6ata rai idan kinganni?, miyasa kuma Safna tatafi gida batareda nasaniba?.
Idonta ta rumtse tareda sauke sassanyar ajiyar zuciya, wlhy bani nakori aunty Safna ba, kuma bansan abinda akai mataba tatafi, nidai naganta da kaya kawai.
To miyasa baki hanata tafiyaba?, Ko kuma ki sanarmin?.
Inatsoron kartamin masifane, kuma gashi acikin mutane Muke.
Huci yafitar daga bakinsa, yasaka hannu ahankali yana shafa kanta, suduka sukayi shiru nad'an lokaci, jin shirunta yayi yawa yad'ago yalek'a fuskarta saiyaga barci yakwasheta.
Maida kansa yayi ya kwanta shima ya lumshe ido amma ba barci yakeyiba yafad'a duniyar tunanine kawai, tundaga randa Appa yay masa maganar auren Safna harzuwa canjamasa da akayi da Rahma, bikinsu, rayuwarsu tanesa nesa, har zuwa yau dasuka zama Abu guda, yad'anyi murmushi dantuna darun Rahma, yasan kishine kawai kecin zuciyarta, jiyayi yak'ara k'aunarta nikin baninkin, yad'ago ahankali yana kallon fuskarta, ahankali take sauke numgashi ak'irjin nasa, fusakarta tayi fayau gawani annuri namusamman datake fitarwa, shiru yayi yana sauraren yanda Nawal take buga k'ofa tana kiran momy! papa!.
Tashi yayi ahankali da Rahma ajikinsa, cikin hikima yazameta daga jikinsa ya kwantar da ita tareda kara mata filo, kafin yagyara mata kwanciyarma harta gyra kanta tareda jawo filo tarungume.
Murmushi yayi yana mai kallon k'yak'yk'yawar fuskarta, azuciyarsa ya ce, "ragguwa da anta6aki sai barci.
Jin Nawal takuma bugawa yamik'e yad'auki tawul yad'aurama k'ugunsa sanan yanufi k'ofar yabud'e.
Tana tsaye abakin k'ofar, ya ce, " baby miya faru?.
Papa ina momyna?.
Saida yajuya yakalli Rahma sanan yadawo da kallonsa kan Nawal, momynki tana aikine jeki kijirata afalo kinji d'iyar albarka.
Kanta ta jinjina, ta ce, ''papa nakalli cartoon?.
Eh babyna jeki saka MBC 3 kigani, muma yanzu zamu fito.
Tafiya tayi abinta tana murna, shima yamaida k'ofar yarufe harda saka key.
Bathroom yashiga yay wanka, dama Rahma tahad'a masa ruwan wanka, bayan yagama k'alk'ale k'alk'alensa yafito.
Kujerar madubi yaja yazauna, yana cikin shafa mai yaga Rahma yatashi afirgice tana sambatar aunty Safna! Aunty Safna!!, Dan ALLAH karki mutu, A'uzubillahi minashshaid'anirrajim!, sai jikinta ke rawa, da Sauri. Bobo yamik'e yaje yajata jikinsa yarungume, yana kiran my Nusfulhayat nutsu kinji, mafarki kikeyi ba gske bane, nutsu.
Hawaye tafara zirarwa, a'a my Nurulk'albi Dan ALLAH ka kaini na ganta, kacemin bata mutuba, wayyo aunty Safna karki tafi ki barni.........
Kafin tarufe baki wayar bobo tafara wringing, dak'yar tayarda ya janyeta daga jikinsa yatashi yad'auki wayar, gabansane yafad'i shima Dan ganin sunan ya Shaheed 6aro 6aro akan screen d'in wayarsa.
Haka kawai yasamu zuciyarsa dayin rawa, dakuma k'ok'arin gaskata mafarkin Rahma, shiyyasa ba'ason barcin la'asar yafad'a azuciyarsa yana kallonta.
Ganin kallon dayake mata saita sake fashewa da kuka, cikin muryar kuka ta ce, "yan gidammune ko?, namasan zasu fad'amin aunty Safna na tarasune kawai...... Tasaki kuka maiban tausayi da tsuma zuciyar mai saurare.
Kiran ya Shaheed ne yakuma shigowa, jiki a sanyaye yad'aga yakara akunne, muryar ya Shaheed kawai dayaji yasaka zuciyarsa karaya, bayan sungaisa ya Shaheed yasanarma bobo abinda nikaina banjiba.
Cikeda tashin hankali ya ce, "ya Shaheed gamunan zuwa, koda suka yanke wayar.. Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un kawai bobo ke iya ambata, Rahma tataso ta warce wayar, ganin sunan Wanda yakirashi yasakata fashewa da kuka, matsowayayi Kusada ita ya ce, " addu'a Safna take buk'ata yanzu agaremu Rahma, kinga tashi kiyi wanka muje.
Kasa tashi tayi, saishine ya d'auketa yakai bathroom yaymata wankan dakansa, dak'yar yasamu tayi wankan tsarki sanan suka fito, d'akinta yaje yad'akko mata wasu kayan, babu zancen shafa mai zirawa kawai tayi, shima yasaka doguwar riga kawai yakama hannunta suka fito.
Afalo suka d'auki Nawal sai gidansu Rahma.
Amotama sai kuka take, shima yakasa lallashinta Dan duk arud'e yake, tuk'i kawai yakeyi cikeda damuwa..............

🤔😭😭😭😭

*_"Hummm masu karatu akwai damuwafa, mikuke tunani gameda Safna??????."_*

*_Luv you oll_*
*_(((S)))........2017_*
[11/12, 2:59 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•🅱🅾🅱🅾•_

*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*

6⃣6⃣

Ganin yanufi wata hanya daban yasa Rahma tsura masa idanunta dasuka k'ank'ance saboda kuka, yana kallonta tagefen ido kuma yakula magana takesonyi amma takasa, shima bai iya cemata komaiba, gudu kawai yake shararawa, ganin sunshigo cikin asibitin Rahma takuma yarda mafarkinta ya tabbata, guri bobo yasamu yay fakin kowa yafito jiki a sanyaye, banda Nawal dabatasan wainar da'ake toyawaba, cikin asibitin suka shiga kowa da abinda yake sak'ama zuciyarsa, Rahma takan share hawaye lokaci lokaci.
A Reception suka tsaya bobo yakira ya shaheed.
Babu dad'ewa saigashi yazo, Rahma tana ganinsa tafad'a jikinsa tana kuka, cirota yayi daga jikinnasa yana fad'in haba Autar Ummi bakisan kin girma bane?, kinga share hawayenki kinji.
Cikin shashshekar kuka ta ce, ''yaya waye bashida lfy?.
Ya ce, "safna CE."
K'ara share hawayenta tayi ta ce, "yaya nasamma aunty Safna tarasu ko?.
Idanunsa yazaro ya CE, "haba auta wayace miki tarasu?, a'a tana nan da ranta har yanzudai tana tareda doctor's ne.
Ta share hawayenta tana kallonsa, to yaya miya sameta?.
Muma bamu saniba Rahma saidai idan likitoci sun fito muji.
To muje kokin manta bake kad'ai baceba?.
Ita saima yanzu ta tuna tare suke da bobo Dan haka takalli Inda yake tsaye rik'eda hannun Nawal dake kuka tunda taga Rahma na kuka.
Da sauri tazo taja Nawal jikinta ta rungumeta tana lallashi, bobo dai da ya Shaheed suna tsaye suna kallonsu.
Ganin abun bana k'are bane yasa bobo matsawa kusada ita ya CE, " yakamata mu k'arasa ko.
d'agowa tayi ta kalleshi saikuma takama hannun Nawal suka shiga ciki.
Acanma tana ganin su Abba taje tafad'a jikinsa tana kuka, dak'yar ya lallasheta tayi shiru, bayan sun gama gaggaisawa suma sukabi sahun 'yan zaman tagumi.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Har akayi sallar magriba likitoci nakan Safna, su bobo dasu Abba suka nufi masallacin cikin asibitin, sudai su ummi da matansu ya Shaheed duk suna nan zaune jigum jigum, Nawal kam tuni tayi barci, ummi taciro d'ankwalin kanta dayake yanada girma tabama Rahma ta ce, "ta Goya Nawal, amsa Rahma tayi tacika umarnin ummi, gama goyon babu dad'ewa saigasu ya Muneer sun dawo daga masallaci, hakan kuma yayi daidai dafitowar doctors d'in kowa yana yarce gumi, da Sauri kowa yanufesu yana tambayar halinda safna take ciki, duk zame jiki sukai suka gudu akabar doctor Kaleel kawai, kallonsu yayi d'aya bayan d'aya yana share gumi, ganin duk 'yan gidane ya sauke ajiyar zuciya, ya ce, " Alhmdllh munsami nasarar ceto ranta, yanzu haka tasamu barci, yanzuma za'a wuce da'ita d'akin Hutu danhaka Ku kwantar da hankalinku alhaji, komai yazo da sauk'i aii alhaji, sauran bayani kuma sai zuwa gobe idan ALLAH yakaimu.

Alhamdllh suka fad'a gaba d'aya, godiya sukaima doctor Kaleel sannan yawuce office d'insa.
Tafiyarsa babu dad'ewa aka gunguro Safna a d'an gadon marasa lfy, kwance take sharkaf tana barcin wahala, cikeda tausayi da addu'ar samun lafiya suka bita.
Zuwa yamzu fuskokin kowa garage damuwa bakamar d'azunba.
Bobo yamatso kusada Rahma ya ce, "My Nusfulhayat ki sauketa mana, aii yanzu Nawal tawuce goyo karkizo k'irjinki yana ciwo.
Girgiza MASA kai tayi ta ce, "bafa tada nauyi ALLAH.
YA munnir dake kusadasu yana jinsu ya ce, "aidama gida kuka tafi tunda anga yanda jikin NATA yake.
Abba ya ce, " gaskiyarka muneer, Abdulmaleek kutafi gida hakanan, kuma su Muneer kud'auki iyalanku Ku tafi gida saboda yara dakuka bari..
Rahma ta turo baki gaba cikin shagwa6a ta ce, "Abba nidai anan zan kwana gsky.
A'a auta bazai yuwuba, idan anbarki kin kwana anan mijinkifa, bobo yad'an shafa Kansa idonsa ak'asa ya ce, "Abba abarta ta kwana Indai Dan tanine babu wata matsala.
A'a a aiba hauka akeba Cewar ummi dake Harar Rahma.
Abba ya ce, "kutafi gida kinji auta, ALLAH yay muku albarka gaba d'aya, gobe idan ALLAH yakaimuma aii ranace ko.
Bobo ya ce, " to Abba bara muyi sallar isha'i, Dan komun tafi a hanya zata riskemu.
Eh gsky ne to kubari ayid'in.

Bayan sallar isha'i badan Rahma tasoba suka fito gaba d'aya harsu ya Shaheed da matansu domin tafiya gida.
Abba da ummi kad'ai aka bari a asibitin zasu kwana.
Har yanzun Nawal tana bayan Rahma agoye saida zasu Shiga mota bobo ya taimaka mata ta sauketa ya kwantar da ita a sit d'in baya sannan suka Shiga mota kowa yanufi gida.
Babu maima wani magana harsuka Shiga cikin gidan, bayan mai gadi yabud'e musu suka Shiga, bobo yay fakin suka fito, harzata d'auki Nawal ya ce, "tabari ya d'auketa, bata Musa masaba tabari ya d'auketa suka Shiga cikin gidan.
Har d'akinta yakai Nawal ya kwantar, ita kuma tashiga wanka.
Shima d'akinsa yanufa yacire doguwar rigarsa yasaka kayan barci, fitowa yayi yanufo dinning Dan yunwa yakeji.
Rahma tafito wanka ta rama sallolinta sannan tanufo falo domin d'aukar Abu.
Ganin bobo zaune a dinning yatuna mata dabaifa ci abinciba Ashe, jitayi yabata tausayi, tak'araso Inda yake tana fad'in sorry Nurilk'albi muntafi ko abinci bakaciba.
Murmushi yay mata ya ce, " karki damu o, kina arikicannan ta'inama zaki tuna da cikina.
Marairaice fuska tayi tamkar zatayi kuka, ta ce, "pls kamin afuwa.
Ayya my Nusfulhayat karki damu ai nasan bakiyi da niyyaba.
Itama murmushin tamasa.
Ya CE, " babynkifa?.
Tana barcinta har yanzu.
OK tom zoki zauna muci abinci, Nima yunwace ta addabeni shiyyasa ban nemekiba.
d'an yatsine fuska tayi tareda ta6a cikinta ta ce, "nikam na k'oshi."
Kamo hannunta yayi, yajawota ta zauna saman cinyarsa, shima hannunsa ya d'ora akan cikin nata yana shafawa ahankali, haba my Nusfulhayat kinaso ki haifamin babyna d'an k'aramine?, nifa k'atoto nakeso Wanda Nawal zata d'auka da k'yar.
Kallonsa tayi tad'an juya idonta dasuka kummbura saboda kuka, tasaka hannu tarufe fuskarta tana fad'in Nurulk'albe baby kuma?, a INA?.
Hannunta ya janye ya d'aga mata gira, ya ce, "acikinki mana.
Tad'an zaro ido tana tura baki gaba ta ce, " nidai kabar fad'a.
Ya ce, "miyasa?."
Since kanta tayi ak'irjinsa cikin sassanyar murya ta ce, "wlhy inajin kunya.
Tabashi dariya Dan haka yay murmushi mai sauti tareda d'agota yana fad'in Ashe kunyarnan har yanzu ban gama fiddataba?, shikenan nadaina tashi muci abincin.
Girgiza masa kai tayi.
Ya ce, " pls ko kad'an kici.
Yunk'urawa tayi zata tashi, ya maida ita ya zaunar, no yizamanki kawai.
Badan tana son cin abincinba ya matsa mata, dakansa yarink'a bata shima yanaci, tana zame zame damasa ta6aradai har sukaci da d'an yawa sannan suka mik'e, ya taimaka mata suka gyara wajen tsaf sannan kowa yanufi d'akinsa.
Harta kwanta ta rungume Nawal taji motsin shigiwarsa shima gadon yahawo, suka saka Nawal a tsakkiya, yamusu addu'a ya shafama kowa sannan yahad'asu yarungume sai barci..

Nima dai homajeep d'in k'afafuna naja natafi wajen my Abdul d'ina nabar Rahma Dana itama.😜

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Washe gari bayan sunyi breakfast Rahma tabisu, yasauke Nawal A school sannan suka nufi asibitin.
Har cikin yashiga shima, yatayata d'aukar kulolin kayan breakfast d'in Data had'o musu, ahanya suka had'uda Abba zai fita, suka rissina suka gaisheshi, cikeda fara'a ya amsa musu, Yakoma yimusu bangajiyar jiya, suma suka tambayeshi yamai jiki?, ya ce, "a dasau kam Dan tana nanma zaune yanzu haka.
Alhmdllh suka fad'a atare.
Ya ce, "kuk'arasa ciki to, nima zanje gidane na shirya nawuce kasuwa.
Saika dawo.

Da sallama suka shiga d'akin, Safna tana zaune akan gado tajingina bayanta da filo, hannunta manne da k'arin ruwa.
Ummi na zaune agefenta tana had'a shayi, d'agowa sukayi gaba d'aya suna amsa sallamar, Safna kallo d'aya tamusu ta kauda kanta.
Ummi ta tashi tareda turama bobo kukerar tace ya zauna.
A'a ummi kiyi zamanki, zanma wuce wajan aikine, rissinawa yayi ya gaidata da tambayar maijiki, ta ce, "jiki Alhmdllh tunda gata azaune hartana magana.
Ya ce, "ALLAH yak'ara sauk'i.
Ameen ummi tafad'a tana fita.
Rahma dake Kusada Safna tsaye tana tambayarta yajikin?, da k'yar ta amsata, Rahma dai bata kawo komai arantaba duk zatonta zafin ciwone.
Ummi nafita bobo ya kalli Safna, ya ce, " antynmu ya jikinki?.
d'ago manyan idanunta tayi ta kallesa, ahankali ta ce, "da sauk'i.
Ya ce, " ALLAH yak'ara sauk'i, yasa kaffarane.
Amin tafad'a a saman la66anta.
Shiru nawani d'an lokaci, bobo yakalli agogon hannunsa sannan yakalli Rahma, my Nusfulhayat bara nawuce ko, kinsan yau k'arfe 10 zamushiga shari'armu dasu Alhaji Abdurrazaq.
Itama kallonsa take tana d'an murmuahi ta ce, "to Nurulk'albi ubangiji ALLAH yabada nasara, yakuma d'oraka akansu.
Lumshe idanunsa yayi yana murmushi, ahankali yabud'e akanta ya ce, " ngd sosai da addu'arki gareni my Nusfulhayat.
Murmushi kawai tamasa batareda tace komaiba.
Yamatso daf da ita, bata ankaraba taji kiss akumatunta, d'an zaro ido tayi tana kallonsa, shikuma yad'aga mata gira sannan yamik'a mata kumatunsa wai tamasa kiss, hannu tasaka tarufe fuskarta tareda fad'in kai Nurulk'albi nidai a'a gsky.
Dariya yayi ya ce, " shikenan aii, ya kalli Safna da bak'incikin abinda sukeyi agabanta tamkarma sun manta da ita ya tokare mata mak'oshi.
Auntynmu ALLAH yak'ara lfy fa, bara natafi office time natafiya, sai dai ganinki yasa matana takasamin adawo lfy.
Murmushin yak'e Safna tayi Wanda duk Wanda yagani yasan tabbas na yak'ene, ta ce, "a'a nikam babu ruwana..
K'ofar yabud'e zai fita sannan yajuyo ya kalli Rahma yakashe mata ido d'aya yafice.
Murmushi Rahma tayi tana girgiza kai.
Safna tazame ta kwanta idanunta cikeda kwalla.
Ahaka ummi tashigo ta samesu, sai yanzu Rahma tasami damar gaida ummi.
Ummi takama hannu Rahma suka zauna ta ce, " autana ina d'iyar takine?.
Tana makaranta ummi, saida mukama ajiyeta sannan muka wuto nan, ALLAH sarki aii yarinyar tanada Shiga rai wlhy, gatada wayonta masha ALLAH.
aii ummi saima kin zauna da Nawal wlhy, yarinyar batada damuwa ko kad'an.....
Haka sukaita hirar Nawal, Safna tana kwance tana jinsu amma tayi shiru, da k'yar ma ummi tasata ta tashi tayi breakfast da kayan Rahma data kawo.
Ummi saiyabama girkin Rahma takeyi itakuma tanatajin dad'i, Safna dai batacemusu k'alaba har doctor yashigo yaduba jikinta yacire k'arin ruwan.
Fitar doctor babu dad'ewa saigasu ya muneer da matansu, suma basu dad'e dazuwaba saiga 'yan gidansu ya Kamal, harma dashi ya Kamal d'in, saikuma ga Appa Ammi da inna, nanfa akashiga gaishe gaishe datambayar mai jiki.
Zuwa azuhur asibin yacika da dangi, sunata tururuwar zuwa ganin Safnar, haka suka kasance da dangi, kowa yaga Rahma saita burgeshidantakuma yin bul bul da ita, ga wani k'yau da murjewa data k'ara na musamman.
Aunty yahanasu Maman Basma ma cewa tayi 'yata kodai nasamu jikane?, irin sannan k'yau haka?.
Hannu Rahma tasa tarufe fuskarta, aiko mutanen d'akin sukaita mata dariya, mamansu ihsan ta ce, "wlhy yaha nimadai tun d'azu nake kallonta, Abdulmaleek yarik'e mana ita da k'yau, ALLAH dai yak'ara baku zaman lfy.
Akace amin.
Duk firarnan da akeyi Safna jitake tamkar ta had'iyi zuciya tamutu, duk saima taji tatsani 'yan cikin d'akin.

Na ce, " Safna aiduk Wanda baiji bariba to zaiji hoho.😜

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Haka Safna tacigaba da jiyya kullum dangi na jerangiyar dubata, su ya ishaq dukansu sunzo da matansu suma, Rahma kullum acan take yini, bobo yakaita idan zayi aiki, idan kuma yataso yabiyo tanan su wuce gida.
Zuwan bobo asibitin bak'aramin tada hankalin Safna yakeyiba, duk sanda yazo saitayi kuka a6oye shiyyasa ta k'agarama a sallamesu su koma gida.
Cikin kuwa ikon ALLAH yau doctor yabasu sallama, ba k'aramin farinciki Safna tayiba Dan har fuskartama saida tanuna, to suma dangi kowa yayi farinciki damata addu'ar k'ara samun lafiya.
Haka suka rankaya suka fito domin tafiya gida, akuma daidai wannan lokacinne motar bobo tashigo asibitin, fitowa yayi ya iso garesu, yarissina yamik'a gaisuwa gasu ummi tareda fad'in lfy dai naga kun fito?.
Rahma ta ce, an sallamemu aii.
Murmushi yayi yana kallon safna, a lallai auntymu yau sai kwanan gida ko?.
Dariya akayi itakuma Safna tad'anyi murmushi.
Abba ya ce, "Rahma to kibi mijinki kuwuce gida ko.
Rahma ta marairaice fuska tamkar zatayi kuka, amma batace komaiba.
Dafata ummi tayi ta ce, " kije kinji autata ainasanki akwai biyayya.......
Bobo ya katse ummi da fad'in ummi ki barta kawai muje muyima auntynmu rakkiya har gida.
Kallonsa Rahma tayi tanaijin farinciki, haka suka rankaya suka tafi.
Bak'aramin farin ciki Rahma tashigaba data ganta yau agida, aiko haka taita yawo lungu da sak'o nagidan babu inda bata shigaba, itace har gidansu ya Kamal, sai bayan isha'i bobo yad'auketa suka tafi, dama Nawal tana gidansu Appa.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Rayuwa mai gudu da sauri, sakwanni sunata tafiya, mintuna sunata sauri, awoyi NATA gudu, akwana atashi babu wuya wajen ALLAH, Alhmdllh jikin safna yayi sauk'i sosai saidai abinda ba'a rasaba, shimadai jiyyar zuciyane narashin bobo.
Bayan sallamota ma Rahma tad'an zazzo ganinta dukda dai bata cika sake mataba amma bata damuba.............

*_luv you oll_*
*_(((S))).........2017_*
[11/12, 2:59 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•🅱🅾🅱🅾•_

*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*

*_"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ubangiji ALLAH ka gafartama mahaifiyar khadeeja Ahmad (kdeey), ALLAH ya yafemata Yakuma bada hak'urin rashinta, ALLAH ya albarkaci abinda tabari da mad'aukakiyar shiriya ameen🙏🏻😭"._*

6⃣7⃣

Kasancewar yau weekend bobo yana gida, yanzu ma haka yana kwance bisa gadonsa dagashi sai wando 3½ da t-shirt mara nauyi, gefensa Nawal ce kwance tana barci, sai Rahma dake d'an kai kawo atsakar d'akin tsakanin dirowa da gado, kayan bobo damai wanki yakawo take shiryawa, kad'an kad'an takan yamutse fuska da cije le6enta, bobo daketa binta da kallo tun d'azun danba k'aramin tafiya dashi dressing nata yayiba, sanye take da jins blue yasha adon duwatsu daga saman cinyarta saikuma Riga pink t-shirt ta mata, kanta babu d'ankwalli tadaiyi farking nasa da pink d'in ribom, gashin yaywani Tim atsakkiya saboda kasancewarsa roba roba, yad'an lumshe idonsa yana shak'ar kamshinta daya baza d'akin, dukkuma motsin datayi saiya bigi hancinsa.
Rahma dake gyara linkin wasu kaya ta ce, "oga me wannan kalonfa?.
d'an murmushi yayi yana k'ara gyara kwanciyarsa har yanzu idonsa akanta, murya akasalace ya ce, "my cute zokiji wata magana mana.
'Yar dariya tayi tareda nok'e kafad'a ta ce, " nak'i wayon, nakula yau sokake kawai mushiririce agidannan batareda nayi aikin komaiba, kallifa agogo har 12 tayi amma banshiga kicinba, mikakeso muci da rana?.
Wata Narkakkiyar dariya yayi sannan Yakuma juya kwanciyarsa zuwa gareta Dan yanzun takoma jikin dirowa.
Ya ce, "to aii Indai dan tanine yau kiwuni ajikina kina bani ni'imtaccen k'amshinki ina shak'a tareda jin d'umin lallausar fatarki sannan naringa kallon k'yawawan idanunnan naki fararen wad'anda sai antara mata dubu ake samun mace d'aya mai irinsa, hakan kawai ya wadatar dani kuma zai k'osar dani fiyeda abincin dazanci.
Yabama Rahma dariya, Dan haka dariya takeyimasa sosai harda wata shashsheka mai d'aukar hankali dakuma kashe jiki, aikodai idanma tarkone Rahma keson d'anawa to tayi kamu, Dan kuwa tuni bobo ya narke agadon yana binta da wani shu'umin kallo, itakam dariyarta tacigaba dayi batareda tasan tarkonta Yakama zaki ba, kayan dasuka rage ta ida kwashewa tasaka adirowa, ganin yana niyyar sakkowa daga gadon yasata fita ad'akin dad'an gudunta, dariya tabashi yazauna abakin gado yanayi.
Itakam kichin tanufa domin d'ora girkin rana, Abu naga tasamu tarufe hancinta sannan ta kunna gas, yau wajen kwana biyu kenan batason kamshin gas d'innman, idan zatayi girki saita to she hanci shima a daddafe take gamawa, yau kuma ga abun yana Neman had'e mata biyu Dan cikinta ciwo yakeyi yana daurewane kawai.
Ruwan shinkafa tafara d'orawa sannan tabud'e firij tad'ebo naman kaji zata wanke, wani wuntsilawa da cikinta yayi ya tilasta mata rik'e murfin firij d'in, tadafe cikinta jitake tamkar tafasa kuka.
Daidai nan bobo yashigo kichind'in da zummar tayata aikin dan dama duk weekend tare suke aikin gidan, haka zaita tayata tana hanashi, amma saiyace yana koyi da ANNABIN ALLAH ne, Dan wannan sunnace mai k'arfi, tun tanajin kunyar idan yana tayata suyi bak'i harma yanzu tasaba abin yazamemata jiki.
Ganin takifa kanta tayi shiru yasa bobo fad'in lfy kuwa my Nusfuhayat?.
Bata iya basa amsaba saidai tad'aga MASA hannu, da Sauri ya iso Inda take, tabaya ya rungumota yana k'ok'arin juyo da ita, aijitayi tamkarma yak'ara mata ciwonne, tai saurin k'adandaneshi tana fad'in wayyo ALLAHna dadyn Nawal cikina, wayyo kamar ana tsitstsinkamin hanjina, da Sauri yazame abinda tarufe hanci dashi, aiko tana shak'ar k'amshin gas d'in sai yunk'urin amai, da gudu ta fisge jikinta daga gareshi ta arce waje, shima take mata baya yayi.
Abayin dake falon taja birki amai tafara zazzagawa kamar zata amayar da kayan cikinga, bobo dukya rud'e yarik'eta sai sorry yake mata.
Saida tagama yataimaka mata tawanke jikinta shikuma ya wanke Inda ta 6ata, cak yad'auketa suka nufi falo, zaunar da ita yayi ajikinsa yana fad'in sorry my cute duk-ya rud'e tamkar zaiyi kuka, cikinne yak'ara murd'a mata takuma k'ank'amesa tana kuka.
Shima sosai ya tallafota jikinsa, tuni ya janye hannunta daga kan cikin ya maye gurbin wajen danasa yana shafawa ahankali, can azab ta isheta takuma k'ank'amesa tana ambatar sunan ALLAH, tare suka k'arashe da bobo Daka gansa kasan yana cikin damuwa.
Ganin abun NATA k'ara gaba ya ce, "my Nusfulhayat Kodai asibiti zamuje?.
Da Sauri ta girgiza MASA kai tana cije le6e, hawaye da gumi kam sun jik'e fuskarta sharkaf dukda da AC dake aiki a falon.
Hijjab d'inta datakan ajiye afalo Indai tasan k'ananun kayane ajikinta, gudun kar bak' yazo yasa takan ajiye, bobo yajawoshi yana share mata gumi da hawayen dasukaima fuskarta ado, wata damk'a data MASA yasakashi fad'in uchch my cute, ita batamasan yanayiba takanta take kawai, wayarsa yad'auka yakira ya sulaiman, ko gaisuwa bai tsaya sunyiba yafad'a MASA abinda ke faruwa, da Sauri shima ya sulaiman ya ce, "ganinan zuwa to.
Cikin mintuna k'alilan ya sulaiman ya iso gidan, har yanzu Rahma tana jikin bobo, kai tsaye cikin gidan ya sulaiman yashigo.
Bobo yad'auki hijjab d'inta yasakamata, hakan yayi daidai dashigowar ya sulaiman, basu tsaya ko gaisuwaba yashiga dubata, 'yan tambayoyi yafara mata wad'anda duk cikin kuka da zafin ciwo take amsa masa.
Ya sulaiman yabama bobo wata kwalba, Abdulmaleek kakaita tayo fitsari mugani.....
Aibaima bari ya sulaiman ya k'arasaba Yasureta sai bathroom d'in dake falon, fitsari tayi a 'Yar kwalbar sannan suka fito, nanmadai d'akkota yayi dukda tanata nok'e nok'e wai bataso yabarta zata iya da kanta, bai saurareta yasunkuceta suka fito.
Saman doguwar kujera ya direta sannan yamik'ama ya sulaiman kwalba.
Ya sulaiman yayi gwajin ciki, ganin abinda tsinken yanuna yad'ago yana fad'in Alhmdllh, fuskarsa cikeda murmushi.
Bobo dake binsa da kallon mamaki ya ce, "yaya lfy dai?.
Jinjina kai ya sulaiman yayi ya ce, "congratulations my lil bobo, Nawal tasamu k'ani ko k'anwa.
Rahma jitayi cikinta yak'ara juyawa Dan tsoro, shikam bobo Baki ya washe tareda d'aga hannu sama ya ce, "Alhmdllh ala kulli halin", yataso suka rungume juna shida ya sulaiman, ya sulaiman dai sai dariya yake masa.
Nandai yarubuta maganin dazata buk'ata sannan yamata allura wadda saida akasha fama tayarda akayi, sai sinne kai take Dan kunya tak'i yarda su had'a ido da bobo barema ya sulaiman.
Cikin mintuna kad'an barci ya d'auketa.
Ya sulaiman yakalli bobo, Abdulmaleek kamarfa k'auri nakeji.
Da Sauri bobo yamik'e yana fad'in ya ilahi wallahi na manta tad'ora girki.
Cikin hanzari ya sauke tukunyar datasaka ruwan zafin shinkafa harya k'one kamas shine tukunyar tafara k'auri.
Kashe gas d'in yayi yafito.
Ya sulaiman yamik'e, Abdulmaleek bara nawuce gida.
Kai yaya tun yanzu?, koma 'Yar hira bazaka tsaya ayiba?.
Dafa kafad'ar bobo yayi sorry bobon Ammi zanje wajen antynka kasan irin wannan ranarce kawai mukeda damar kasancewa da iyali.
Murmushi bobo yayi ya ce, " hakane kam yayana.
fita sukayi suna dariya, saida bobo yaga fitarsa sannan yadawo gida.
d'aukar Rahma yayi yamaida d'akinsa, shima yakwanta suka hau barci abinsu.

..................................
Haka rayuwar tacigaba datafiya, Rahma tanata shan laulayi Dan cikin NATA maisa laulayine, cikin 'yan kwanaki dukta rame, bakomai take iya Ciba, yanzu hakama tadaina girki Dan batason k'amshin gas ko kad'an, kullum daga gidan Ammi ake kawo musu abinci safe da yamma Dan darana tana gidan AMMI, idan zaitafi aiki saiya ajiyeta can, idan kuma yataso yabiya ya d'auketa, daga shi har Ammi tarairaya suke mata ta musamman tamkar zasu maidata ciki, Appa ma ba'a barsa abayaba, duk abinda Rahma tace tanaso saiya siyo mata shi, kamar yanzune za'a haifi jikan farko agidan, ita wani lokacinma har kunyar kanta takeji, amma yazatayi badasonta take sakasu wata wahalarba tsirface kawai irinta ciki.
Nawal kullum idan tadawo makaranta tana nane da Rahma, maganarta bata wuce yaushe zaki haifomana babyn momy?.
Rahma takanyi dariya tacemata bayanzuba da sauran lokaci.
Wata sa in takanyi dariya wataran kuma kuka ta ce, " itafa dawuri take so ahaifamusu sabon baby.
Idan Ammi ko bobo suna kusa ake diramar sukanyi musu dariya.......

..................................
Safna na kwance afalo ita kad'aice yau agidan, Abba yana kasuwa, ummi kuma tana gidan aunty yahanasu mamansu Basma, taje saka ranar auren Basma da akeyi yau.
TV take kallo amma bata fahimtar komai a film d'in dukda sonsa datakeyi tamkar mi.
Ta gyara kwanciyarta tareda kai dubanta ga hotonta itada Rahma sannan suna yara, sunyi matuk'ar k'yau duk sunyi murmushi, takuma kai dubanta gawani k'aton hoto Wanda yak'awatu da k'yau, kauda idanunta tayi tanamai share hawayen dake ziraro mata akumatu.
Dubana nakai ga hoton danson ganin suwaye ajiki?, hummm Rahma CE da bobonta sunyi masifar k'yau, hoton and'aukeshine aranar mother's day, tanasanye da bubu shikuma bobon suit, tad'anyi k'asa da kanta yayinda bobo ke kallonta yana murmushi, ya munner agefensu yana bama Rahma wani Abu.
Masha ALLAH nafad'a azuciyata danba k'aramin k'yau sukayiba, dolene Safna taji 6acinrai, tamayi k'arfin hali databar hoton Agalon, kodayake tana tsoron ummi ne kawai nasani.
Sallamar da ake kwad'awane yasakata mik'ewa tana tsaki, k'ofar tanufa tabud'e, ganinsu zeenat da baseera yasakata k'are tamke fuska, tayi hakane saboda baseera.
Basuji komaiba gameda canjawar tata Dan sunsan halin kayansu.
Cikin falon suka bita, kowa yanemi gurin zama batareda tabasu izinin hakanba.
Itama tsanar baseerar datayi bai hanata had'o musu abin motsa bakiba kamar yanda tasaba, koba komai aii harda mai k'aunarta Zeenat.
Zeenat takalleta cikeda tausayawa ta ce, "Safna yak'arin k'arfin jiki?.
gyara zamanta tayi ta ce, " da sauk'i Zeenat, aina warke.
Baseerama ta mata ya jiki, adak'ile ta amsa mata.
Zeenat takuma fad'in wlhy mu bamusan bakida lfy ba, mundai kwana biyu bakije school ba toshime mukace bara muzo muga ko lfy?, munshigo anguwar muka had'u da yaya kamal yake fad'a mana harma asibiti kika kwanta.
Safna tad'anyi murmushi wlhy kuwa zeenat har asibiti na kwanta yau kwana hud'u da sallamomu.
ALLAH yasa kaffarane.
Ameen.
Daga nanan sukayi shiru nad'an lokaci, Zeenat takatse shirun da d'akko zancen bobo.
Baki Safna ta ta6e saiga hawaye.
Arud'e zeenat da Baseera suka k'arasa gareta suna lallashi, dagananma har Zeenat ta zayyanemata yanda sukayi da Baseera a kwanankin baya, dakuma Nuna mata tayi nadama, itama suka Shiga mata nasiha da lallashinta da nunamata muhimmancin iyaye da had'arin bijire musu, baseera ta durk'usa har k'asa tana Neman gafarrar safna.
Ta ce, "tayafe mata, ALLAH ya yafemusu baki d'aya, daganan zeenat tak'ara musu nasiha itama, saikuma suka koma hira tamkar basune sukasha kuka yanzunba.
Anan suka wuni zubur suna k'ara kwantarma da Safna hankali dakuma k'ara bata shawarwarin yanda zata nemi gafarar iyayenta.
Saida ummi tadawo suka gaisa sannan suka tafi gida.

%%%
Da daddare bayan Abba yadawo suna zaune afalo shida ummi saiga ya Shaheed da ya munner.
Safna dake kwance ad'aki tamik'e tanufo falon Dan ganin ga dama tasamu na Neman gafarar iyayenta da 'yan uwanta.
Tunda tafito kowa yamaida kallonsa gareta, ganin tanata ra6e-ra6e Abba ya ce " safnata miya farune?."
Tana tsaye saiga hawaye suna zirara akumatunta, ya munner sarkin tausayi yatashi yaje yakamo hannunta, zaunar da ita yayi kusada k'afafun Abba.
Abba yadafa kanta yana fad'in haba safna mike damunkine wai a 'yan watanninnan?, kodai har yanzu jikinne mukoma asibiti?.
Kanta ta girgiza tana share hawaye, cikin shashshekar kuka ta ce, "Abba Dan ALLAH Ku yafemin Kozan samu sassaucin son Abdulmaleek dake son hallakani, wlhy Abba nayi nadamar abinda na aikata, nayi kuskuren bijiremuku akan abinda wayona bazai bani shiba, Abba narantse muku *_NAYI NADAMA_* (sabon buk d'in pertymerh xarah) Dan ALLAH Abba kujanye fushin dakukeyi dani kozan samu ubangijina yabar fushi dani.............nanta shiga basu labarin yanda akai tagane Abdulmaleek shine Wanda take so alokacin data bijire musu, tafad'a musu komai danganeda shawara da muguwar k'awa tabata, saidai ta6oye sunan kowacece kuma batafad'i zuwa gidan malami da bokayeba.......tarushe dakuma mai tsuma zuciyar mai sauraro.
Tabasu tausayi sosai Dan haka suka shiga lallashinta, Abba ya ce, " munyafe miki Safna domin kuwa ALLAH ya nuna miki kuskurenki tuntuni nadamace dai kika gagara yi saboda sharrin shaid'an, to ayanzunkam ki tabbatar kinyi tuba na gskya Wanda babu kome a aikata wani laifin makamancin haka.
Kanta tad'aga tana fad'in ngd Abba ALLAH yak'ara tsawon kwana da ikon cigaba da rik'emu, ta rarrafa gaban ummi tana kuka da Neman gafararta, ummi tajata jikinta tarungumeta, nayafemiki safna domin idan nace bazan yafemikiba bansan kuma wane irin gararin rayuwa zaki fad'aba nan gaba, nayafemiki ki kwantar da hankalinki kema ALLAH zai baki miji nagari domin Abdulmaleek yamik'e nisa ayanzu, shid'in mijin k'anwarkine.
Nanma kanta ta girgiza ta ce, "nahak'ura ummi tuntuni, saidai har yanzu inajin sonsa azuciyata, jinake tamkar kullum ana k'aramin sonsa, ummi ta6a k'irjina kiji, tayi maganar tana kamo hannun ummi tad'ora asaitin zuciyarta.
Ummi ta jinjina kai danjin bugun zuciyar Safna dake fita da k'arfi, tabata tausayi sosai, dama doctor Kaleel yafad'a musu zuciyarta tana barazanar kamuwa daciwo Ashe dalin son *_Abdulmaleek_* ne.
Lallashinta ummi taitayi da kwantar mata da hankali, suma su ya Shaheed da ya munner dukata rok'i gafararsu sunkuma gafartamata, tareda alak'awarin tayata da addu'a.
Nasiha sosai sukai mata mai ratsa jiki da jini.

Tundaga ranar Safna tazama wata shiru shiru amma har yanzu son bobo na nan mak'ayale da zuciyarta saidai Alhmdllh yaragu bakamar daba dayaso zame mata ciwo.
Yanzukam kulawa ta musamman iyayenta suke bata da k'arajanta ajikinsu, hakan nak'aramata kwanciyar hankali da k'aunarsu, haka rayuwar tacigaba da shurawa har ayau ranar wata juma'a da iyayenta sukazo mata dawata magana ta had'ata aure da yaya kamal, (Brr....kamal Abubakar, yayansu Ameera kuma abokin aikin bobo).................

*_luv you oll_*
*_(((S)))........2017_*
[11/12, 2:59 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•🅱🅾🅱🅾•_

*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*

*_"INA rok'on ubangiji yabada nasara a aikin daza'aima mahaifiyar mman Useey, ALLAH yabata lfy dadukkan d'aukacin 'yan uwa musulmai baki d'aya, ameen🙏🏻."_*

6⃣8⃣

Safna tak'ara k'asa da kanta amma bata iya crwa komaiba.
Abba ya kalli ummi itama kallonsa takeyi, ya Shaheed ya ce, "Safna ke muke saurare, shin akaro na biyu kin amince da auren Kamal?.
d'ago idanunta dake cikeda kwalla tayi, ahankali ta jinjina kanta, muryarta na rawa ta ce, " na amince iyayena, amma Dan ALLAH ina Neman wata alfarma agareku.
Abba yayi murmushi, kinemi kowace iron alfarma agaremu Safna, insha ALLAHU zamuyi miki inhar batafi k'arfinmuba.
Hawayen dasuka fara gangarowa visa kumatunta ta share, ta ce, ''Abba Dan ALLAH inhar ya Kamal baya sona to kuyi hak'uri kucanja min da wani, ahalin danake yanzun ina buk'atar mai sona dazai iya d'aukar duk wani Abu daga gareni kasancewar halin dana tsinci kaina acikj.
Gani nayi gabad'aya sunyi murmushi, ya muneer ya ce, "ki kwantar da hankalinki Safna, Kamal dakansa ya CE, " yana sonki, kuma shine ya tuntun6i iyayenmu da maganar, abinda yaragemiki kawai shine krma ki koyi sons a, kema kifara k'ok'arin fidda *_"ABDUL-MALEEK"_* daga cikin zuciyarki, ki koma yimasa kallon mijin k'anwarki kuma d'an uwanki.
Jin jina kanta tayi tana murmushi mai had'eda kuka, ummi tajawota ta rungume Rana saka mata albarka, suma su Abba fuskar kowa ka kalla saikaganta wasai cikeda farinciki.

Bak'aramin kuka Safna tashaba ayau, tasan yanzunkam bobo yamata nisa har abada, zeenat takira away a ta zayyane mata komai, shawara tak'ara bata tareda kwantar mata da hankali, nasiha sosai tamata mai ratsa jiki, hakanne yad'an k'ara rage mata damuwa.
Itama ummi tashigo takuma mata nasiha, zuwa yanzun hankalinta Yakima kwanciya, Dan koba komai kowa yana tausaya mata kuma yana lallashinta, zuwa yamma Kamal yazo gidan, jitayi tamkar tafasa ihu amma babu yanda zatayi haka tashirya tafito gurinshi.
Atsakar gida ta iskeshi visa farar kujerar roba, gakuma wata an ajiye kusadashi alamar tatace, sallamarta yasakashi d'agowa saga latsa wayarsa dayakeyi, murmushi yamata tareda amsa sallamar tata.
Tayi k'asa da kanta, gurin zama yanuna mata yana fad'in bismillah, Safna tad'an jawo kujerar bays sannan ta zauna, idonsa akanta ta ce, "ina yini.
Murmushi yayi sannan ya amsa, yad'anyi k'asa da muryarsa sannan ya ce, " nifa banason sanyin nan dakika kowa, Madison ganinki tamkar safnar da mai tsiwarnan darashin Baron kota kwana, solon sanyi na Rahma be amma ba Safna taba.
d'an murmushin yak'e tayi Wanda yafi kuka ciwo, wato had yanzu kowa nakuma nunamata Rahma tafita k'yawawan halaye kenan, kwallah suka cika mata ido amma tayi jarumtar hanasu sauna visa fuskarta.
Kamal yad'an tsura mata idanunsa zuciyarsa cikeda nazarinta, tabbas ya yards da maganar bobo Safna tanada k'yau idankuma aka Shiva lamarinta za'a iya canja mata rayuwarta Mara k'yau zuwa mai k'yau, insha ALLAHU zaiyi k'ok'ari wajen canjata d'in, tabbas ada yaso Rahma run tana k'aramarta domin k'yawawan halayrnta sine suka dunkareshi darashin yin sure da wuri yana jiranta, alokacin dayayi shirin mik'a buk'atarsa ga iyayensu said auren Safna yatashi cikin gaggawa, yayi shirurune had akamala biking Safna da bobo asannan sannan yakaowo maganrsa da Rahma, saidai kasha al'amura said sukayi uyin wahainiya Auden Yakima kan Rahma, yashiga bak'inciki da tashin hankali awannan lokacin harya kasa halartar taro ko d'aya data tarurrukan auren Rahma da bobo, bak'aramin yak'i da zuciyarsa yayiba wajen bats hak'uri harta hak'ura yacigaba da rayuwarsa Lamar da.
Awata rana saiga sak'on takarda masinjan bobo yakawo office d'insa, sak'9n takardar yana k'unshe da shawara data bobo akan yanemi auren Safna domin tanada 6oyayyun halayr Wanda saita samu mai jagorantarta akan hanya mai k'yau zasu fito.
Da farko bai d'auki maganar taxa serious ba, saidaga bays yazaina yay nazari sosai tareda k'arin k'arfin guywa da bobo kebasa aduk sands suka had'u, saikuma yaji yakamu Dawson Safna d'in, saidai kuma bayason tad'auki halin sanyi irinna Rahma Dan hakan zai iya jawowa son Rahma yaringa motsa NASA harya aikata wani Abu ga Safna a madadin Rahma, shikuma Sam bayason tagane yama ta6a son Rahma d'in a baya, wannan me yasa yamata magana akan komawarta safnarta taxa mai tsiwa...........
Jin yayi shiru gashikuma yadasa mata idanunsa ko k'yaftawa bayayi yasakata fad'in ya Kamal mikake tunani?.
Firgigit yayi yana murmushi, yagyara zamansa ya ce, "nayi zurfi akogin sonkine my Safna, INA data kema kin kar6eni amatsayin masoyi na had abada, inaso mutaru nidakr mushare hawayen juna my mantar da kanmu munta6a son wasu abaya, mutaru mugina sabuwar rayuwa maicike da abubuwan sha'awa ga al'umma.
Kallonsa tayi cikeda mamaki, asaninta ya Kamal baita6a budurwaba Dan bata ta6a jin hakan abakin kowaba, NASA daurewa tayi ta ce, " ya Kamal damage kata6a soyayya?.
d'an murmushin takaici yayi sannan ya ce, "nata6ayin makauniyar soyayya abaya domin ba'asan inayiba, wadda nayi Dan it a batasan nayiba harta su6ucemin, amma ayanzu kid'auka babu it a araina saike kad'ai kuma INA Neman taimakonki mutaru muk'ara karfin ginin soyayyar kodan mugudu tare my tsira tare, Safna nami alk'awarin share mini hawayenki inhar INA numfashi, kuma zan nuna mini soyayya da k'auna iya iyawata.
Hawayen dasuke zirara akumatunta ta share, cikin rawar murya ta ce, " ngd ya Kamal amma Dan ALLAH INA rok'onka kayi hak'uri daduk halin dazaka ganni had zuwa lokacin da komai zai daidaita mugina ni'imtacciyar rayuwa Lamar yanda kabuk'ata.
Murmushi yayi tareda mik'a mata hanky d'insa ya ce, "karki damu my sweery na, mijinki ya fahimceki kuma zaimiki dukkan uzuri kinji.
Kanta ta jinjina tana murmushi tareda share hawayenta da hanky d'insa, sunyi 'Yar hira duk akan yanda biking Nash zai kasance, sannan yamata sallama yatafi.........

.*.*.*.*.*.*.*.*..*.*.*.
Rahma kwance visa gadon Ammi tana sharar barci bayan tagama con d'anwaken filawa Wanda ayanzu yazame mata abinci akoda yaushe, haka take wuni barci tamkar kasa, saidai idan lokacin sallah yayi ammi ta taxa ita tanayi kuma wata sa in zata 6ingire akan sallayar, yanzu haka kosu bobo batasan sundawo saga masallacin juma'a bama.
Matansu ya ishaq gaba d'aya suna falo tareda yaransu, sai kuma wasu bak'i dangin Appa dasukazo musu bangajiyar biki dansu basu sami Samar zuwa bikinba.
Appa da ammi dasu bobo kam suna falon appa ana shari'a.
Su ya Hamza me suna kai maganar ganin bobo da Safna dasukayi ana jibi auren su khursiyya.
Shine appa yake kallon bobo cikeda alamar tambaya, Mukarram kafad'a mana gsky mike tsakaninka da ita?.
d'an cije le6ensa yayi cikeda 6acinrai, bai ta6a zaton 'yan uwansa zasu zargesa da wani mummunan abuba bare harsh kawo maganar ga mahaifansu, tuni idonsa yad'an sauya kala, duk said a ya kalli 'yan iwan NASA sannan yafara zayyane musu komai fake tsakaninsa da safna, tundaga farkon had'uwarsu had zuwa ganin dasuka masu aranar, yad'ora da fad'in saidai gsky kunbani mamaki Dan banta6a zaton zaku zargeni da Abu makamancin hakaba, raina ya6aci bazan 6oye mukuba, danni ko'a mafarki bazan ta6a zarginku da aikata Abu makamancin haka Mara k'yauba..
Gaba d'aya sai jikinsu kuma yay sanyi, sungane gsky basu k'yautaba, kosu kad'ai ya Isa sumasa maganar basai sunzo gaban iyayensuba, amma sumafa sunada hujjarsu nayin hakan.
Yunk'urawa bobo yayi yamik'e danufin barin wajen, da sauri ya Hamza dake kusadashi yaruk'o hannunsa, bai juyoba baikuma kwace hannun nasa saga rik'on Yaya Hamza ba.
Ganin haka Appa ya ce, ''mukarram dawo kazauna.
Itadai Ammi batace komaiba binsu kawai takeyi da kallo.
Baya bobo yadawo ya zauna danshi mutumne dabaya k'etare maganar iyayensa komaiba kuwa son dayakrma Abu sukace yabarsa to zai barsa, Duke kuma k'in dayakema Abu sukace yayi to zaiyi inhar bai sa6ama shari'aba, zan iya cewa wannan tarbiyyar yaran guidance gaba d'aya Dan kunsan halayensu d'ayane suduka.
Inda yakeda Yakima ya zauna, nasiha Appa yashiga yimusu, sannan yanunama kowa kuskurensa dagasu had bobon, gaba d'aya kuma said jikinsu yayi sanyi, ganin nayi suna mik'ama juna hannu suna musabaha, duk kuma suka bama bobo hak'uri daneman afuwarsa shima hak'urin yabasu saboda kasa fahimtarsu dayayi, saga nan hira mai dad'i sukacigaba day I kamar basuba, said a aka kira sallar la'asar sannan suka mik'e zuwa masallaci.

.....................→
Koda suka dawo masallaci sai duk suka zauna afalon k'asa har Appa.
Bobo dai daya wawwaiga yaga babu Nusfulhayat d'insa saiya mik'e, harya kama k'arfen benen zai haye Ammi ta ce, ''mukarram sai ina?."
Kunyace takamasa yad'an sosa kansa umm Ammi zand'an duba abune.
Ammi ta hararesa zakaje duba Abu kokuma zakaje tada Rahma me.
Dariya kowa yakeyi danganin yanda bobo ya Sosa k'eya alamar an harbo jirginsa.
Ammi ta ce, "to dawo kazauna, nibansan miyayake tsolemaka idoba idan Rahma tana barci saikayi yanda kayi katada it's, bayan kuma kasan barcin nata na lalurane.
Dawowa yayi yanad'an zum6ura baki, yaje Kusada k'afafun Appa ya zauna.
Kansa Appa yashafa yana murmushi ya ce, " babana yaushe ka koyi k'arya?.
Lah Appa bafa k'arya nayiba nafad'ane kawai ba daidaiba.
Nanma dariya sukayi, ya ishaq ya ce, "ALLAH ya shiryaka Abdulmaleek.
Amin babban Yaya bobo yafad'a yana dariya.
Rahma dake niyyar sakkowa takoma da baya, tun d'azu ta tashi tayi sallar la'asar, sanda bobo ke k'ok'arin hawowa it's kuma tana niyyar sakkowa, jin maganar da Ammi take masa yasata la6ewa, duk abinda ke faruwa itama tanaji tana dariya dagacan.
Kangado takoma tad'auki waya tana chatting abinta Dan tanajin kunyar fita falon k'asa.
Ganin lokaci yaja ammi ta ce, ''hibba taje ta tado Rahma.
Mik'ewa tayi tana fad'in to Ammi.

" araina na ce, "yarinyarnanfa tafara zama 'Yar budurwa, to yanzu tana samun kulawa yanda yakamata gasu ammi, ga karatu tanayi a tsadajjiyar makaranta, komai tasamu na fannin rayuwa itada iyayenta da yayanta Idris.

Akeance hibba ta tartar da ita tana chart, Rahma tad'ago tana kallonta da murmushi, itama hibba murmushi takeyi, ta ce, ''anty!, ammi ta ce, " kitashi hakanan lokacin sallah na k'urewa.
Mik'ewa Rahma tayi tana fad'in ainama tashi tuni nayi sallah muje kawai hibba.
Koda suka fito falon Rahma ta rissina tagaida Appa da Ammi, ta Haida su ya ishaq, idon bobonta na kanta, yitayi tamkar baya gansaba harta zauna sannan tad'an sack kallonsa, har yanzu shima ita take kallo, tad'an murgud'a masa baki, nuna kansa yayi waishi?. Saida tad'an faki ido sannan tamasa gwalo, kansa yagirgiza alamun zata gane kurenta idan tazo hannunsa.
Duk abinda sukeyi Appa na lura dash, murmushinsu na many a kawai yayi yana girgiza kai.

..............................°
Alhmdllh komai yana tafiya yanda yakamata, Rahma anata jan ciki, masha ALLAH tak'ara k'yau abinta, soyayyakam itada bobonta sai Wanda yagani, tarairayarta yake tamkar kwai acokali.
Ana cikin haka kuma aka saka bikin Safna da ya kamal wata d'aya kacal, za'a had'a bikinsu Dana Ameera, bak'aramar murna Rahma tayi dajin sannan labariba, haka taita rok'on bobo saiya kaita gidansu.
Aiko dolensa yakwasheta itada Nawal yakaisu suka wuni, lokacin dasuka Isa basu iske Safna agidanba yana gidan ya Shaheed, sai yamma tadawo ta iskesu, ta amshesu babu yabo babu fallasa, Rahma sarkin hak'uri kuwa farincikinta ta nunama Safna sosai, tareda fatan ALLAH yakaisu susha Niki.
Safna dai batace mata k'alaba harta k'araci murnarta tabarta.
Sai bayan isha'i Bobo yadawo yad'aukesu, safna har kuka tayi bayan tafiyarsu, dayansu ita bobo yazo d'aukafa, dayanzu itace d'auke da cikinsa, amma rashin biyayya ga iyaye yaja mata😭...............

*_kuyi hak'uri da wannan, wlhy 2page nayi typing amma yara suka gogemin bansaniba😭😭, dak'arma na ita sake wanan d'in ._*

*_luv you oll._*
*_(((S)))..........2017_*
[11/12, 2:59 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•🅱🅾🅱🅾•_

*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*

6⃣9⃣

*_BAYAN WATA →1_*

Bikin su safna ya kankama, anata hidima dakai kawo, yau takasance ranar kunshi suna tsakar gida itada Ameera da k'awayensu irinsu zeenat baseera da sauransu, masu k'unshine har uku sukema k'awayen amaren, saikuma Basma datakema Ameera da Safna harma angama ma Ameera yanzu safna akeyimawa, hira da barkwanci aketayi irinna taron k'awayen amarya.
Duba nakai ga fuskar safna, kadaran kadahan take, bata d'aureba sannan kuma bata saka baki cikin hira da dariyar k'awayen nasu.
Rahma ta fito daga cikin falon hannunta d'aukeda filet na d'anwake dayasha yaji, sanye take dajar atanfa zani da Riga, rigar fitet ce wannan yabama matashin cikinta damar fitowa d'as, bak'aramin k'yau cikin Yamataba, gashi yakaramata fari da 'yar k'iba masha ALLAH, ga atamfar takuma haska k'yawun halittar jikinta.
Da yawan 'yammatan wajen bak'aramin birgesu Rahma tayiba, taja kujera 'Yar tsigunno tazauna tana fad'in kai aunty Ameera k'unshinfa yabada ma'ana tafad'a tana k'ara lek'a k'afar.
Murmushi Ameera tayi ta ce, "da gsk auta?.
Wlhy kuwa yau duk kunfito amarenku keda aunty safna.
To mungode, ke sai yaushe za'a miki naki?.
Saita gama muku 'Yar wulak'ancin idan ta gadama, nikoma zan iya jure zaman?, Rahma tayi maganar tana hararar Basma.
Dariya Basma tayi ta ce, " karki damu uwar uku dolene namiki kodan ya Abdulmaleek yagani.
Rahma ta d'akama Basma duka a baya 'Yar fatan tsiya ukun lfy?, nama haifi d'ayan mana, saidai ke ALLAH yasa Ranar damuka kaiki ki samo mana biyar nasan Yaya Salman bazaiyi wasaba.
Basma dake shafa wajen da Rahma ta doketa ta ce, ''Mara kunya wlhy Rahma kin fetsare.
Dariya Rahma tayi tanacin d'anwakenta dayaji uban yaji sai faman sheeeee! Take da baki saboda zafin yajin, ta ce, "kibari zan fad'amiki yanda akayi na fetsare.
Anty Ameera ta ce, " ALLAH ya shiryeku yarannan, yanzufa Rahma saitace ta girmemu ko?.
Dariya duk 'yan wajen keyi, wata acikin 'yammatan amaren ta ce, "eh mana tunda tarigaku shiga daga cikin itace babba yanzu.
Dariya suka kuma shek'ewa da ita wasu harda tafawa.
Safna dai fuskarta tamau babu alamun annuri, dan ita hirar tasu ba burgeta takeyiba.
Wayar Rahma yafara Wringing, d'auka tayi tana murmushi, cikin wata sassanyar murya da kowa bayajinta awajen harsu Basma ta ce, ''Assalamu alaika ya Nurulk'albi.
Bobo dake zaune a office d'insa sanyin AC da k'amshin turarensa na ratsashi yalumshe idanunsa yana wani murmushi na musamman tamkar yana gabanta ya ce, " wa'alaikissalam my Nusfulhayat, ina fatan kina cikin nagarta da aminci da k'oshin lafiya keda babyna?.
Murmushi mai sauti Rahma tayi cikin salonta ta ce, "Normal Muke, kaima muna fatan kasancewarka cikin kuzari da jarumta irin na ma'aikacin kwarai mai k'ok'arin kare hak'in al'ummarsa?.
Alhmdllh my Nusfulhayat duk abinda kike hasashe agareni ALLAH yasaukar da ni'imarsa agareni musamman dakika kasance mai yawan tunatar dani waye ni akowane dak'ik'a na rayuwata.
Masha ALLAH Rahma tafad'a murya anarke.
K'ara lumshe idanunsa yayi dak'ara lafewa cikin kujerar yanad'an lilakansa akujerarsa alamun yanajin dad'in yanayi da hirar dasukeyi, ya ce, " mikikecine haka kiketa faman shan yaji?.
Dariya mai Narkar da zuciya Rahma tayi ta ce, ''canki mana."
Shiru bobo yayi yanad'an nazari, zuwa can ya ce, "tom saidaifa muyi da sharad'i?.
Hummm sharad'in mi?.
Idan na canka dai-dai to yaufa babu k'orafi awajen barci, dannaga wani guduna akeyi yanzu.
Dariya mugunta Rahma tayi ta ce, " nayarda Dan nasan bama canka zakayiba.
Shima dariyar yakeyi ya ce, "kardai ki cika baki.
Batace komaiba saidai tayi murmushi.
Shima shiru yayi yana tunanim mizaice?.
Rahma tayi gyaran murya.
Ai kamar ta zurgud'a masa allura ya ce, " d'anwake kikeci.
Shiru Rahma tayi, shikuma shirun datayi yabashi damar tuntsurewa da dariya yana fad'in naci gari, yarinya yau ki shirya babu d'aga k'afa.
Kukan shagwa6a Rahma tasaka masa tana fad'in itadai bata yardaba.
Dariya su Basma suka saka mata har bobo na jiyosu.
Safna kam tsaki taja ta na kauda kai.
Rahma tajuya baya danjin suna mata dariya, jin dariyar dayake mata shima yasa tadage akan bata yardabafa.
Shima dagacan cikin dariyar ya ce, "ahaf 'yammatana ai babu hanyar ku6ta, kima shirya tarbata Dana tashi daga office zanbiyo mutafi gida nasha Amarcina yanda yakamata.
Da sauri ta ce, " banida lfy fa.
Karki damu inada magani, yana gama fad'a ya Yanke wayar yana cigaba da mata dariyar mugunta.
Ameera tarik'e ha6a oni auta d'an koyamin shagwa6ar nan mana nima na iyata, Rahma tarufe fuskar tana dariya, Ameera ta ce, "yo ALLAH kanama mijinka wannan shagwa6ar ai babu inda zai fita, shiyyasa ya Abdulmaleek baya ganin kowa saike kad'ai.
Tashi Rahma tayi tabar wajen suna mata dariya.

K'arfe *_5:6pm_* bobo ya iso gidan, ak'ofar gida yatsaya yakira wayarta, alokacin Rahma ta na zaune kusada ummi tana zubamata shagwa6ar wai k'irjinta na ciwo, ummi tashafa kanta tana fad'in auta saidai hak'uri, ba'a Raba mai cikin da irin wad'annan k'ananun ciwuwwukan harsai anhaihu suke dainawa.
Baki tad'an turo sannan tazame ta kwantar da kanta bisa cinyar ummi.
Ummi ta ce, " sannu autana.
Kanta tad'aga cikin salon shagwa6a.
Dariya ummi tamata tana fad'in auta Abdulmaleek yana fama da wannan shagwa6ar taki, kekiyi Nawal tayi gakuma baby zaizo.
Hannu Rahma tasa tarufe fuskarta tana dariya.
Ana cikin haka kiran bobo yashigo, akunyace tad'auka tasa akunne batareda tayi maganaba.
Bobo ya ce, "kifito muwuce ina mota."
Cikin muryar kamar zatayi kuka ta ce, "wayyo ALLAH tun yamzu?.
Haba my Nusfulhayat gobe idan ALLAH yakaimufa zaki dawo, nima atausayamin mana.
Baki takuma zun6urowa tamkar zatayi kuka, shikuma dagacan ya ce, " inajiranki, ya Yanke wayar batareda yajira cewartaba.
Lalla6ata ummi tashigayi Dan taji wayar dasukayi, mik'ewa Rahma tayi tashirya tanatama ummi shagwa6a harda 'yan kwanlanta, tayima mutane sallama tafito, cikin mota ta iskeshi, koda yashiga sallama kawai tamasa ta zauna tajuya masa k'eya.
'Yar dariya kawai yayi yatada mota suka tafi, shima baice da ita k'alaba har sukayi nisa, tuk'insa kawai yakeyi yanabin karatun alkur'anin dake tashi amotar cikin suratul Nurr.
Itama Rahma tayi shiru tanabin karatun ahankali cikin k'ira'ar shiek Abdurrahman sudies, takula bobo yanason karatunsa.
Koda sukaje gida bata tsaya jiransaba tabud'e motar tafice abinta, binta yayi da kallo yana wani shu'umin murmushi, shima fitowa yayi yakwashi tarkacensa ya take mata baya.
Afalo ya isketa kwance akan 3sita, tana ganinsa tafara cije le6e.
Dariya tabashi Dan yasan sarai pretending ne datasaba masa a 'yan kwanakinnan, baisan miyasa yanzun batason yara6eta dasunan auratayyaba.
Yi yayi kamar bai gantaba yawuce d'akinsa, harya kai k'ofa ta ce, "wai Nurulk'albi yaushe zaka d'akko mana Nawal ne?, wlhy nayi kewarta gidan babu dad'i kuma.
Bakinsa yad'an ta6e cikin zolaya ya ce, " sai randa momynta tabar guduna, baki ta turo shikuma yashige d'akinsa yana murmushi.

Itama mik'ewa tayi tanufi d'akinta, suduka kowa wanka yashiga.
Bobo yana fitowa ya tsane jikinsa ya zira jallabiya yafito, d'akin Rahma yad'an lek'a, daga bakin k'ofa ya ce, "My Nusfulhayat natafi masallaci.
Kanta kawai tad'a masa tana cigaba da tsane ruwan jikinta, Dan fitowarta kenan daga wanka itama.

Bai shigoba sai bayan isha'i, tana zaune afalo daga ita sai wando na jins pink iya cinyarta tasaka best fara tas sai tashin k'amshi takeyi.
Kallo d'aya bobo yamata ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya, sannu tamasa, ya amsa yana lumshe idanunsa, d'akinsa yanufa, mintuna kad'an yafito dagashi sai gajeren wando da best, hannunsa d'aukeda laptop da wayoyinsa, zama yayi kusada ita yasaka hannu afilet d'in kayan marmari datake sha.
d'ago ido tayi tana kallonsa, yad'aga mata gira tareda kanne idonsa d'aya.
Kauda kai tayi gefe tana murmushi, zuwa can kuma ta ce, " Nurulk'albi serious ina kewar babyna fa.
Hannunsa na haggu yasa yatallafota zuwa jikinsa, yankan abarba yad'auka yasaka mata abaki, ya ce, "nima ina kewarta my cute amma haka zamu hak'ura tak'arasa hutunta a can, kullum k'orafin mama ba'a kaimata Nawal Hutu, shiyyasa wannan karon nace taje ta musu kwana biyu, tokuma gashi sun rik'e mana ita, d'azuma sunzo office d'ina itada musaddiq, kiyi hak'uri kinji, data kammala hutun zata dawo garemu, Nawal batada wata uwa aduniya sai ke kinji.
Kanta tad'aga tana masa murmushi, yacigaba dabata fruit d'in yana fad'in har andaina fushin?.
'Yar harararsa tayi cikin sigar wasa, ta ce, " aikasan bana iya fushi dakai Nurulk'albi, soyayyarka ta mamaye dukkan jikinna da 6argo ruhina da jinina, wad'an nan matakan tsaron daka gark'ame ilahirina jikina dasu basa Barin masarautar zuciyata dogon fushi dakai, inasonka dayawa bobona, har zuciyata tanayi tamkar zata faso daga k'irjina zuwa gareka musamman alokacin data nisanta da 'Yar uwarta.
My zumana kai namusamman ne, kai jarumine acikin jarumai, kai gwanine acikin gwanaye, kazama zaki acikinsu, tutar nagarta na hannunka kad'agama sauran maza saidai subika abaya kosunaso ko BASA so kuwa.....
Wani sanyin dad'ine yaratsa zuciya da 6argon bobo, yad'uki filet d'in kayan fruit d'in ya ajiye saman Santa tabir, k'ara matsota yayi jikinsa yashiga nuna mata zallar k'auna da zazzafar soyayya mai cikeda alfahari gaduk macen data sameta ga mijinta, sunkai rabin awa yana Abu d'aya, Rahma kam tana k'ara harhad'o hanyoyi da gudummawa na taimakonsa, sun lula basajinkira, gabansu kawai suke hange amma ba bayaba, saida suka nutse bisa tirbar soyayya kowa yakuma yarda da jarumtar nagartacciyar soyayya daga d'an uwan nasa sannan suka tsagaita tareda tsurama juna shu'umin kallo kowa na zubda kwallar farinciki da ni'imtaccen so tsaftatacce kuma gawurtacce.
Rungumeta Yakuma yi yana lashe dukkan hawayen dake zirara bisa kumatunta tareda shiryamata nutsatstsin kalamai masu nisan kiwo ga ballagazar mace.
Bayan ya sarara itama talashe nasa tas suna mai k'ara dulmiya cikin farinciki da nutsuwar kasancewa tare tamkar kowane ma'aurata dasuka kasance cikin inuwar aure.
Bayan shud'ewar mintuna kamar ashirin suka 6ararraje a tsakkiyar falon, Rahma najikin bobo kwance suduka idonsu nabisa laptop d'insa dayake danne-danne da'alama yana aikin daya shafi office ne, Dan gaba d'aya daga ita harshi sun maida nutsuwarsu ga abinda yakeyine..
Sunkai tsawon awa biyu ahaka kafin bobo yad'ago idonsa visa k'yak'yk'yawar fuskar Rahma dake barci tun d'azu.
Murmushi yayi yana fad'in kasa kenan, kedai yanzu ba'a hira dake, da amfara saiki 6ingire barci, aiko zama kitashine Dan yau bazan iya jurewaba.
Kwanciyarta ya gyara mata wai tak'ara samun barci kafin yagama, haka yacigaba da aikinsa lokacin-lokaci yakan kur6i lemon data ajiye masa.
Yaja lokacin mai tsawo yana aikinsa da Rahma lafe ajikinsa, zuwa can yad'aga kai yakalli agogo, d'an zare idanu yayi danganin shabiyu harta wuce, agurguje yak'arasa abinda yafara, ya rufe laptop d'in yad'auki Rahma zuwa d'akinsa, saida ya ajiyeta sannan yakoma d'akinta yad'akko mata kayan barci yakwashi tarkacensa yakoma.
Kayan barcin ya canja mata shima yasaka nasa sannan ya haye gadon, mugunta irinta bobo bai k'yaletaba saida ya tada ita ya raya sunna sananan.......😎.

______________________
Biki yayi biki, yau aka gudanar da kamu daya k'ayatar aharabar gidansu Safna, anhad'eshi gaba d'aya itada Ameera, komai ya k'ayatar damutane, zuwa gab da magriba aka tashi.
Daga nan ancigaba da gudanar dabiki su Rahma amarori k'irjin biki danma ciki namata cikas bata iya komai yanda yakamata.

Ahaka aka wayi gari yau asabar safiyar d'aurin aure, Kujiba-kujiba su Rahma aketa sha Dan annan takwana, dak'yar bobo ya yarda ta kwana saida Ammi ma tasaka baki sannan, aiko gidan Ammi ya kwana wai bazai kwana gidansu shi kad'aiba kewa ta isheshi, dariya Rahma taitayi masa shikuma yana hararta.

*_2:30pm_* dai-dai aka d'aura auren Safna bilal Basheer mai Gold & Kamal Abubakar Basheer, sai kuma Ameera Abubakar Basheer & Hafeez Lukman sa'eed.
d'aurin aurene daya Tara d'unbin al'ummar Annabi, Appa dasu ya Hamza ya ishaq ya sulaiman bobo Ammar Musaddiq idris duksun halarci taron d'aurin auren.

To saimuce ALLAH yasanya alkairi safna da Ameera da ya Kamal da hafeez, duk ALLAH yabaku juriyar zaman ibada da hak'uri Wanda akasan ma'aurata dashi.🤓

Bayan gama d'aurin aure su bobo abokan ango suka shigo tareda anguna domin d'aukar hotuna, bak'aramin tashin hankali Safna tashigaba da ganin bobo, jitake tamkar tad'ora hannu aka tarushe da ihu amma babu dama, sai satar kallonsa takeyi, shima yana kula dahakan shiyyasa yakoma can gefe nesa da inda take tsaye da k'awayenta.
Cikin ikon ALLAH ma saiga Rahma ta fito daga falon itadasu aunty ummy matansu ya Sulaiman, k'arsowa sukayi wajen suna gaisawa da angunan, Bobo yakamo hannun Rahma yana fad'in woow my Nusfulhayat kinyi k'yau, nakuma gode miki dakika saka gyale bakifito harabar gidanan hakaba.
Murmushi tamasa ta ce, "Murulk'albi na nasanka da kishi Dan haka zanyi k'ok'arin toshe duk wata hanyar da kishinka zai motsa.
Lumshe idanunsa yayi yana murmushi jin dad'in furucinta, zungurarsa ya Kamal yayi kai malam agabanfa jama'a kuke.
Dariya bobo yayi ya ce, "d'ansa ido miya kawo idonka kammu?, kabar amaryarka can kataho nan neman gulma, halan Ammar ne ya cinnoka Dan nasan yashahara sosai awannan 6angaren.
Ammar dake jinsu ya ce, " indai har na shahara tokuwa kai ka gawurta fitsararre.
Duka bobo yakai masa, Ammar yakauce yana fad'in abin kunya bobo agidan surukai saika nuna hali?.
Rahma dake dariya ta ce, "Nurulk'albi kabar Yaya Ammar zamu ramane.
Hakane my Nusfulhayat saiyazo gidanmu zamu tararmasa.
Dariya sosai ake musu, 'yammata dayawa sun k'yasa matasan samarin k'yawawa masu wadataccen ilimin addini Dana boko.
Dayawan 'yammatan wad'anda suka San labarin bobo abakin safna sukan tayata jimamin rasasa Dan babu k'arya guy d'in yahad'u tako ina, hotuna akayi kowa sotake taga tafito kusada bobo amma Rahma takasa ta tsare tana manne dashi ako ina ko 'Yar kunyar nan tata yau ta tureta gefe gudun kar wad'annan manyan 'yammatan dasuka FItA wayewar boko Suyi mata suruf bahana da Nurulk'albi d'inta.
Bak'aramin kishine ya turnuk'e safna ba, amma haka ta daure tadake akayi hotunan aka gama su bobo suka tafi.
Shagalin biki yacigaba da gudana acikin gida........... .

*_luv you oll_*
*_(((S)))........2017_*
[11/12, 2:59 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•🅱🅾🅱🅾•_

*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*

7⃣0⃣

Zuwa dare aka halarci dinner faty daya tara d'unbin al'umma, ita Ameera ankaita gidan mijinta tund'azu, dagacanma suka taho dinner d'in, safna kam sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu tunda angon d'an gidane.
Amare da angwaye kam sunsha k'yau matsa ALLAH, fuskokinsu duk cike suke da annuri da akasan amare da anguna nayi aranar bikinsu, balaifi awannan karonma safna tad'an saki jikinta.
Sai hange-hange da lek'e-lek'e nakeyi amma ban hangomuku Rahma da bobo ba saboda cikar da wajen yayi.
Sai awajen lik'i ALLAH yabani nasarar sauke idanuna kan Rahma da bobo dasuketa zubama su Safna lik'i, Rahma taci ado cikin less yellow riga da zani buba kamar d'inkin yarabawa, ta nad'e kanta da blue d'in d'ankwali sark'arta 'yan kunnenta dakomai blue ne, bobon tama sanye yake da shadda blue sai maik'o da d'aukar ido takeyi, shikam komai ajikinsa blue ne, sai kamshi suke zabgawa tamkar sune amarya da angon.
Tunda suka fara musu lik'in idanun safna da Kamal akansu kowa da abinda yake tunani, sukam sai zabga murmushi sukeyi hankalinsu kwance, ganin kud'in dasuke zazzagarwa mawak'i yafara wasasu tamkar sukad'aine a hall d'in taron.
Safna dai data kasa daurewa saida tayi kuka, kular da bobo yayi yasashi kama hannun Rahma sukabar wajen.
Inda sukeda suka koma suka zauna, awajen bada cake ma safna saida suka had'a ido da bobo, murmushi yamata kawai yana masu tafi, murmushi nasa ya sanyaya zuciyarta Dan haka itama tayi.

Araina na ce, "safna kinada aiki wlhy, yakamata kihak'ura hakanan.🤓

Rahma tanarke ajikin bobo tana yatsine fuska, tallafota yayi sosai zuwa jikinsa ya ce, " my Nusfulhayat ya dai?.
Shagwa6e fuska tayi, Nurulk'albi barci nakeji.
Idanunsa yad'anzaro waje, barci kuma?, bafa agama ba.
Takuma yatsine fuska nidai wlhy nagaji hayaniyarnan tama isheni.
Kingani ko, saidafa nace kiyi zamanki karkizo kikak'i, to gashinan tun ba'aje ko'inaba harkin gaji.
Tab, nazauna agida wata ta manne maka, inacan nikuma sagaga da baki.
Dariya tabashi amma saiya gimtse, yay nufin zolayarta, my cute nifa mijin mata hud'une, kumafa inada sha'awar k'ara aure.
Zame jikinta tayi daga nasa, amamakinsa saiyaga tamik'e zata bar wajen, da sauri yaruk'o hannunta yana fad'in sorry my hayatee wasa nakeyifa, dagake aii babu k'ari, dukda haka bata saurareshiba, su ya hamza dake kusadasu kowane da matarsa suka shiga musu dariya, Ammar ya ce, "karki yarda Rahma dad'in bakine kawai yanada budurwa.
Hararsa bobo yayi ya ce, ''tod'an had'i kuma tunzurata.......
Baijira cewar ammar ba yabi bayan Rahma da sauri Dan har takama hanyar barin hall d'in.
Su ya ishaq da mamansu sai dariya suke musu.
Da Anty yahanasu sukaci karo itama zata fita, a'a Rahma lfy ina zakije haka da sauri?.
Saurin saisaita kanta tayi, Anty wlhy nagaji barci nakeji.
Aidama rigimar kice tasa kikazo, mujeto nima gidan zani nagaji......
Dai-dainan bobo yak'araso yarissina yagaida aunty yaha, Anty yaha ta ce, "ko tare zaku tafine?.
d'an Sosa kansa yayi yana murmushi.
Dariya aunty yaha tayi tareda fad'in kaga koma kayi zamanka saimuwuce tare tunda nima gidan zani.
To shikenan Anty saida safe.
Har waje yarakasu, har suka tafi Rahma bata yarda sun had'a ido da bobo ba.
Dariya yayi bayan tafiyarsu ya ce, " humm my Nusfulhayat kishinki na burgeni da k'ara tsundumani a lodin k'aunarki.
Juyowa yayi zai koma, daidai zai Shiga sukayi karo dawata k'yak'yk'yawar budurwa, suduka kowa jadabaya yayi, sorry my guy, yarinyar tafad'a cikeda yanga.
d'aure fuskarsa yayi baice komaiba yara6a ta gefenta zai wuce.
Da sauri tasha gabansa tana fad'in pls jimana.
Tsayawa yayi yana kallonta saidai fuskarsa babu alamar yasan miye dariya, tamkar bashine yagama dariyaba yanzu.
Tagyara tsayuwarta tana wani far da idanu, ni sunana Anisa Ahmad Sa'eed, so atak'aice ana cemin neesa, k'anwace ga angon y Hafeez.
Wlhy tunjiya awajen launch kaketa birgeni bansamu damar maka magana bane sai yanzu, pls ina fata zaka kar6i tayina?, tayi maganar tana tsura masa ido da langa6ar da kanta gefe.
Yamutse fuska yayi yana mata wani kallon rainin wayo, baice da ita k'alaba yara6a tagefenta yawuce.
Binsa tayi da kallo tamkar zata FASA kuka dan bak'inciki, Dama saida Anty laura ta ce, "kartazo Dan daga ganinsa zaiyi Girman kai, kuma taga kamar yanada mata, amma tak'i azatonta kodan k'yawun da ALLAH yay mata dolene bobo ya saurareta saigashi ya bud'a mata k'asa a ido.
Jiki asanyaye takoma cikin hall d'in, amamakinta saita hangoshi yana dariya shidasu ammar, shagala tayi sosai tana kallonsa da addu'ar ALLAH ya mallaka mata bobo amatsayin miji.

" Araina na ce, "humm."

Dahakadai taro yatashi, ango Hafeez yad'auki amaryarsa Ameera suka tafi, shima ya kamal yad'akko safna sukayo gida, su bobo da sauran jama'a kowa yay gida.
Sanda suka iso tuni Rahma tayi barci a falon Abba dama a can takwana jiya.

Washe gari aka kai safna d'akinta itama bayan anyi walima.
Masha ALLAH gidan yayi k'yau, su ummi sunmata gata irina iyayen kwarai, kowa ya yaba kam saidai mak'iyi.
Tom daganan taro yatashi kowa Yakama gabansa, Raham ma bobo yazo ya d'auketa sukai gida abinsu.

_____________________
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, Rahma anata rainon ciki, suma su khairiyya da khursiyya an gamu, Dan jiya agidansu Rahma da Nawal suka wuni, sunjajje musu yawo, aiko bak'aramin farinciki sukayi da hakanba, suntarbi su Rahma tamkar su goyasu, ansha hira zuwa dare bobo yaje yad'akkosu.

Su safna amare anata shan amarci, sosai ya Kamal yake k'ok'ari wajen mantar da Ita bobo, rayuwa sukeyi mai dad'i, itama kuma tanata k'ok'arin faranta MASA dukda har yanzu idan son bobon yamotsa takansha kukanta a6oye, amma tana iya bakin k'ok'arinta danganin tacireshi azuciyarta.
Ameerama dai ba'a barsu abayaba sunata shan soyaya itada hafeez d'inta.

Sai masu gayya da aiki bobo da Rahmarsa soyayace tsantsa ake zubawa agidan cikeda kulawa da tarairayar juna, yanzukam sai abinda yay gaba wajen kulawar da bobo yake bata musammam da cikinta yashiga wata Tara na haihuwa, datace wash, zaice miya faru?, wani lokacin har tsokanarshi takeyi saita langa6e tana zuba shagwa6a, dataga yarud'e saita saka MASA dariya, yakace haba yarinya zan ramane baridai ki haihu.

Awannan tsakaninne yasamu nasarar shari'arsu da Alhaji abdurrazak, yanzu haka an Yanke musu hukuncin d'aurin rai da rai agidan yari, Dan ba wannane karo nafarko dasuka saka yaransu yin kisaba.
Mutane sai yabama k'ok'arin bobo sukeyi, yak'ara girma a idon al'uma, kowa k'ara k'aunarsa yakeyi Dason tarayya dashi, hakama iyayensa da 'yan uwansa kowa alfahari yakeyi dashi.
Gama sharia'ar babu dad'ewa yak'arasa ginin gidansu idiris harsunma koma amma ambarma ammi hibba kamar yanda ta buk'ata, babansu idris yayi murna yasakama bobo albarka harbabu adadi.

Su Rahma sunsha bikin Basma Wanda dak'yar bobo yabarta take zuwa saboda cikinta yatsufa sosai ga cikin yayi girma masha ALLAH.
Bayan kammala bikin da kwana biyu Ammi tazo hargida zata tafi da Rahma takoma gidansu Dan ta CE, "bata amince tabarsu sukad'ai agidaba ga haibuwa yau ko gobe.
Rahma dai tayi murna da haka amma bobo tamkar zaiyi kuka, daga k'arshema shima shirya kayansa yayi Yakoma gidan Appan, Ammi dai ta CE, " shiyya sani Rahma cedai bazata bayarba sainanda wata hud'u.
Idanu bobo yazaro yace ammi wata hud'ufa kikace?.
Eh Ashe kajini?, sainan da wata hud'u lokacin baby yayi kwari, d'iyata ta huta sosai.
Shiru yayi kamar zaiyi kuka.
ammi sai kunshe dariya take, Rahma dake zaune Nawal na matsa mata k'afafunta dasukeyin fishi, itakam kasa daurewa tayi ta tuntsure da dariya.
Hararta bobo yayi tareda yin kwafa yatashi yafita.
Saida yafita sannan ammi tayi dariya itama.
Da Appa yadawo tabashi labari shima dariya yayta k'yalk'yawltawa, ya ce, "wai da gsk shima yahad'o kaya yadawo nan gidan?.
Wlhy kuwa Appan ishaq karkaji wasa, yana nan tsohon d'akinsa kwance yanzu haka yana barci.
Appa ya ce, " kai mukarram kayan shirirta, shi koyaushe zai gane yagirma ne?. To ALLAH yak'ara had'a kawunansu shida ita dakuma sauran 'yan uwansa da matansu gabad'aya.
Amindai Ammi tafad'a cikeda farin ciki.
______________________
Rahma tana kwance itada Nawal akan gado, Ammi na zaune bisa sallaya tana addu'oi bayan ta idar da nafila datakanyi akowane tsakar dare, yanzu itama ad'akin take kwana saboda gudun kar Rahma tafarka da ciwo cikin dare.
Agogo Ammi takalla 2:54am, filo tajawo daga saman gadon ta ajiye akan sallayar tazame ta kwanta, barcine yakwasheta, akuma daidai lokacin Rahma tafarka dawani matsanancin ciwo, amma saboda jarumta irin tata takasa magana saidai cije le6e da hawaye daketa sharara.
Zuwa wani lokaci takasa daurewa, ahankali ta daddafa tasakko daga gadon tadawo k'asa ta duk'usa tareda d'ora kanta bisa gadon tana murk'ususu.
Abin tamkar wasa sai gaba gaba yakeyi, can taji bayanta da k'ugunta cikinta ko ina yarik'e, wani wahalallen kuka tasaki tana fad'in nashiga uku ummi zan mutu, wayyo bayana cikina k'irjina zasu cire........
Afirgice Ammi tafarka, ganin Rahma durkushe tana kuka Takuma rud'ewa, Rahma yadai?.
Ammi cikina, bayana, ko ina ciwo zan mutu Ammi kuyafemin.
Bazaki mutuba Rahma, runk'a addu'a, akid'ime ammi take maganar, ga waya a hannunta tana kiran bobo.....
Shima azaune yake, tun d'azun yafarka saboda mafarkin Rahma dayayi tana kuka dakiran sunansa, tund'azu yakeson ya lek'a d'akin yaganta amma yanajin kunyar had'uwa da ammi, ganin damuwa zata masa yawa yatashi yad'auro alwala yazo yay nafilfili yanzu haka yana zaunene yana karatun alkur'ani, ganin kiran ammi yasashi d'aga wayar da hanzari.......
Zumbur yamik'e danjin ammi tana fad'in yafita da mota gasu nan fitowa, Alkur'anin ya ajiye yafigi key yay waje da sauri, mota yaje yagyara fakin sannan yadawo ciki, afalo yagamu da Appa d'auke da Nawal zai kaima 'yan aiki ita, wuceshi yayi yatarbo Ammi dake rik'eda Rahma tanata kuka.
Aii baijira cewar Ammiba yad'auki Rahma gaba d'aya yay waje da ita, ammi kuma d'akinta takoma ta d'akko kayan daza'a buk'ata, cikin mintuna k'alilan Ammi da Appa suka fito, bayan Ammi tashiga Kusada Rahma, shikuma Appa yazauna Kusada bobo, a 360 bobo yaja motar sai asibitin ya sulaiman.
Koda suka isa cikin gaggawa aka kar6esu, dandanan doctor Fa'iza takar6i haihuwar Dan ya sulaiman akwai kunyar surukuta tsakaninsu.
Har zuwa 4:46 Rahma bata haihuba, anatadai shan tata6urza, aii bobo dayaga abin bana k'are bane sai kawai yadanna kai cikin d'akin, duk maganar da ya sulaiman yake masa bai saurareshiba.
Inda take kwance yak'arasa, tana ganinsa tafara mik'a masa hannu tana kuka dakiran sunansa, Nurulk'albi ka gafartamin zan mutu, wayyo ALLAH dadyn Nawal nima mutuwa zanyi kamar Anty Ni'ima.
Dukda arikice yake shima haka yake shafa kanta yana fad'in a'a My cute bazaki mutuba, insha ALLAHU lafiya zaki haihu........kafin tabashi amsa wani sabon ciwon yazo.
K'ank'ameshi tayi sosai tana wani wahalallalen nishi.
Aiko bobo yaji rik'onnan na Rahma, sai jije le6e yake shima kamar mai Nak'udar.
Cikin ikon ALLAH saiga jariri yafad'o yana tsayyara kuka, cikeda murna doctor Fa'iza ta ida ciroshi tana fad'in Alhmdllh, saikuma sabuwar nak'uda, mik'ama Nurse tayi jaririn takuma kar6ar sabon baby daya kunno kai.
Ai Rahma na sauke wannan kaya saitayi lakaf ajikin bobo.
Ahargitse yake kiran my Nusfulhayat!, my cute!, momyn Nawal!!.
Katseshi doctor Fa'iza tayi da fad'in sir babu abinda yasameta tana hutun wucin gadine.
Doctor Fa'iza bafata numfashi.
A'a yalla6ai tanayi kalli k'irjinta kagani, kallonkuwa yayi saiyaga tana sauke numfashi ahankali.
Dukda bai samu nutsuwa dukaba yaji dad'i, ko sauraren 'ya'yan baiyiba dukda yana cikin matsanancin farincikin zuwansu duniya, amma ta mamansu yakeyi yanzu, bayan shigewar mintuna Rahma tad'aga idanunta dasuka k'ank'ance tana kallon bobo, murmushi tamasa.
Cikin farinciki yarungumeta yana fad'in Alhmdllhi Alah kulli'halin, sai yanzu d'unbin farincikinsa yafito fili.
Tuni labari yakaigasu Ammi, anhaifi twins namiji da mace.
Dan dad'i Appa har rungume ammi yayi, ya sulaiman sai kauda kai yayi yana dariya.

Cikin 'yan mintuna aka gyara baby's da mamansu, bobo yad'akkosu yafito dasu wajensu ammi, bakinsa yak'i rufuwa yaukam.
Had rige-rigen d'aukarsu ake tsakanin ya sulaiman dasu Ammi.
'Yan gata sun iso duniya, yara masha ALLAHU basuda maraba da yayarsu Nawal, dakuma mahaifinsu Abdulmaleek bobo.
To saimuce ALLAH yaraya 'yan dugwuy-dugwuy iyalan baba.

Sai karfe 8pm sukabar asibitin, aka rankaya zuwa gidan Appa, zuwa sannan labari yabaje dangi, sanda suka Isa gidan Appa cike yake dasu anty rasheeda, har and'ora ruwan wanka.
Innar su hibba tayima Rahma cikakken wanka, tanata zille-zille da zame-zame har aka kammala, yarama anmusu, annad'esu cikin fararen kayan sanyi masu laushi sai barcinsu sukeyi.
Rahma tafito daga bayi Dan tuni inna tafito tabarta tana k'imtsa kanta.
Zama tayi tashafa mai tashirya tsaf cikin atanfa sabuwa dal, itakad'aice ad'akin mutane duk suna falon k'asa har jariran.
Abincin da Anty ummy ta ajiye mata tazauna taci, shayine mai kauri da farfesun 'yan ciki, saikuma soyayen dankali, citai kad'an sanan tahaye gadon ta kwanta sai barci, dama barcin bai ishetaba..............

*_luv you oll._*.
*_(((S)))........2017_*
[11/12, 3:00 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•🅱🅾🅱🅾•_

*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*

7⃣1⃣

Falon cike yake da dangi, bobo yashigo da sallama hannunsa d'auke da leda babba, gaisawa suka shigayi da mutanan falon anata masa barka, cikeda farinciki yake amsawa, mutane dayawa dabasa ganin dariyarsa yau har mamaki sukeyi yanda yaketa yak'e hakwara.
Ammi dake fitowa daga kichin ta ce, "yauwa mukarram kadawo?.
Eh ammi nadawo.
A'a yanaganka da 'Yar leda?, sauran Kayanfa?.
Mik'a mata ledar yayi yana fad'in wlhy naje zan sayo saina tadda ya ishaq awajen yana siya, shiyyasa najuya nasiyo wad'annan kuma.
Ayyo aiban saniba, to ina yayan naku yanzu?.
Acan nabaroshi, amma nasan yana hanyar zuwa shima.
To shikenan ALLAH yakawoshi lfy.
Ameen, Ammi ina Rahma d'in?.
Tana d'aki kwance tana barci, kasan jiya bawani barcin kirki tasamuba, kaima aii yakamata kaje kad'an kwanta kona awa biyu kasamu kayi.
Shafa kansa yayi yana murmushi, wlhy Ammi ni namafa daina jin barcin.
Dariya ammi tayi, lallaikam murnar zuwan kishiya da miji yasa idonka bushewa kenan?.
Dariya sosai bobo yakeyi, ya ce, " ammi aii k'yautar ALLAH daban take, wlhy ko'a mafarki banta6a zaton Rahma zata iya haihuwar yara biyuba yanda nake mata kallon yarinya karama.
Itama ammi dariyar tayi, mukarram aii ikon ALLAH kenan, Ubangiji mai hikimane, amma gsky koni bankawo Rahma tana d'auke da cikin yara biyu bane, ALLAH dai yarayasu akan turbar addinin islama.
Amin ammi, bara nalek'a Rahman kota tashi?.
To, ammafa Indai barci take karka tada ita kaji nagaya maka.
Karki damu ammi, bobo yay maganar yana haurawa sama.

Cikin barci Rahma taji ana shafa kanta, ahankali tamotsa, jin k'amshin turarensa yasakata bud'e idanunta ta sauke akansa.
Murmushi yamata murya a sanyaye ya ce, "my Nusfulhayat kin tashi?.
Kanta tad'an jin jina tana murmushi, yunk'urawa tayi zata tashi yataimaka mata, ta zauna sosai amma tana jingine ajikinsa, Nurulk'albi yaushe kashigo?.
Sumbatar kumatunta yayi idanunsa cikin nata ya ce, " tun d'azun ina zaune ina gadinki aii.
Tofa saikace wata sarauniya?.
Aikinfi sarauniya awajena Rahma, Ubangiji ALLAH yayimiki albarka, tabbas ke Alherice arayuwata, shigowarki Rayuwata kin yalwata alkairi mafi daraja agareni, inason yara sosai Rahma, inaso yara fiye dazaton mai tunani, saigashi tashi d'aya ALLAH ya albarkacemu da samun biyu, Rahma yanzu nine da yara har uku?, kai ALLAH na gode maka godiya Mara adadin kididdiga, lale dake yasanyin idaniyata.
Dad'i da farinciki duksun yalwatu afuskar Rahma, takuma narkewa ajikinsa, ngd my Nurulk'albi, ina rok'on ALLAH ya tsawaita rayuwarmu domin miyita bauta masa da kuma kasancewa tare har abada.
Ameen my cuty na.
Amma Dan ALLAH ina neman wata alfarma agareka.
Gyara zamasa yayi Yakuma jawota sosai ajikinsa ya rungumeta, kitambayi Duk abida kikeso agareni insha ALLAH zanmiki shi inhar bai sa6ama ALLAH ba.
Murmushi tamasa ta ce, "inason asakama macen sunan marigayiya aunty Ni'ima Dan ALLAH kamin wanan alfarmar, idan kamin haka zanyi farinciki sosai.
Tsura mata idanu yayi nawani d'an lokaci, har jikinta yafara sanyi ko bazai aminceba, amma saitaji ya rungumeta tsam yana bata Sumba takowane 6angare ajikinta.
Ammi dake tsaye tun d'azun tana kallonsu ta kauda kai tana murmushi, dama tabiyo bayansane danta tada Rahma tabama yaran nono, Dan sunfara kukan yunwa.
Jin maganar dasukeyi yasa tatsaya bata shigoba Dan batason katsesu saga farincikin dasuka tsinci kayinsu.
Saida bobo yagama bata hot kisses sanan yad'agota yana kallonta, ALLAH yamiki albarka shine abinda yaketa maimaitawa, cikin raunin murya ta ce, " my Zuma kayarda kenan?.
Jinjina mata kai kawai ya iyayi yana murmushi, ahankali ya ce, "Rahma nazama naki, kinrigada kin dabaibaiye komai daya shafi rayuwata, aduk duniya daga iyayena saike acikin jerin Abu mafi Girman muhimmanci a tafiyar rayuwata, sai kuma 'yan uwana wad'anda suka zama jigogi kuma matakan tsaro agareni, 'ya'yana sanyin idaniyata, ALLAH ngd maka daka yalwatani da wad'annan ni'imomi naka badan Nafi sauran bayiba kabank, badan nakasance mafificiba acikinsu, badan wayonaba, badan iyawataba, badan k'arfinaba ka yalwatani ka azurtani ka ni'imtani, ka suturtani, ka ingantani, ka d'aga darajata acikin bayinka, ya ALLAH yanda kamin wanan k'yauta aduniya ka Albarkaceni dasamun mafiyinta alahira....... Hawaye suka zuraro akumatunsa, Rahma tasa hannunta tana share masa.
Yacigaba da fad'in ya ALLAH karka jarabceni da kasancewa acikin masu butulci agareka, ya ALLAH karka jarabceni dagacikin masu sa6onka, ya ALLAH karka jarabceni daga cikin marasa godiya agareka, ya Ubangijin Al'arshi ma'abocin Rahma da gafara, ka gafartamin dukkan kurakuraina nida zuri'ata data musulmai baki d'aya, ya ubangijina kak'ara imani da tsoronka azuciyata, ya ubangijina katsare harshena daga sa6amaka komai ribar hakan agareni, ya Ubangijina ka tsare idanuna daga kallon haramun komai farincikin da hakan zai sakani, ya Ubangijina katsare k'afafuna daga zuwa inda haramun yake komai d'aukakar da hakan zata jamin, ya Ubangijina katsare gangarjikina, zancena, numfashina, furucina, daga afkawa tarkon shaid'an la'ananne nida dukkan zuri'ata data musulmai baki d'aya, ALLAH ka k'arama annabi daraja da fadila da Wasila, ALLAH yasa munacikin al'ummar da zaiyi alfahari damu muda zuri'armu baki d'aya, ALLAH yasa munacikin wad'anda zasu amsa kiran cetonsa awata rana mai cikeda rud'ani da hargitsi, ya ALLAH idan katashi d'aukarranmu kad'auka munacikin imani da tsoronka bacikin shagaltuwa da duniya da abinda ke cikintaba.
Ameeen Rahma tafad'a tana k'ank'amesa hawaye sharkaf da fuskarta saboda addu'ar mijin NATA ta ratsa dukkan sassan jikinta da 6argon jikinta.
Ammi ta share guntun hawayenta itama sannan tamusu sallama.
Da Sauri Rahma ta tashi daga ajikinsa tamatsa gefe kanta asunkuye saboda kunya.
Shima k'asa yayi da kai yana Susa k'eya.
Sunbama ammi dariya amma saita gimtse.
Fuskarta d'auke da murmushi ta ce, "Rahma kintashi?.
Kan Rahma akasa ta ce, " eh ammi natashi tund'azu.
Kodai mukarramne yatadaki?, dannasan halinsa sarai.
Girgiza kai tayi cikeda kunya tana murmushi.
Ammi tayi dariya, to tunda kintashi bara nakawosu ki basu abincinsu tun asuba yara basuci komaiba sai ruwan zam zam da Zuma aketa basu......
fita ammi tayi, bobo ya kalli Rahma baki bud'e, my cute wai kinanufin basuci komaiba yarannan harfa 12 tawuce?.
Shagwa6e fuska tayi Nurulk'albi wlhy ina gama wanka na kwanta saboda barci danakeji sosai.........
Kafin ya ce, "wani Abu Ammi tashigo d'auke da yaran ahannunta.
Bobo ya kar6i macen, saida yasumbaci goshinta sanan yamik'ama Rahma ita.
Cikeda kunyar Ammi ta kar6a Dan ita saima yanzu zata gansu tunda sukazo duniya, jitayi k'aunar yaranta tana ratsa dukkan sassan jikinta, Aranta Ta CE, " ALLAH sarki haka iyayenmu sukeji akanmu, ALLAH ka k'aramana k'aunar iyayenmu dakuma taimaka musu iya iyawa Dan bazamu iya biyansuba.....
Ganin tayi shiru ammi ta ce, "Rahma bata tasha mana.
Ajiyar zuciya Rahma tasauke, idanunta Akan k'yak'yk'yawar jaririyar daketa bud'e baki alamar tana Neman abinci, ga idanu kyar masha ALLAH, (Yaran yanzu haka ake haihuwarsu da wayensu, saidai fatan ALLAH yatsare manasu damu kanmmu).
Tana saka mata abaki yarinyar tafara sha, da sauri tacire tana fad'in wash da zafi.
Daga bobo har Ammi dariya suka saka mata, Ammi ta ce, "haka zaki daure kibasu, daga baya zaki daina jin zafin.
Tasowa bobo yayi yadawo Kusada Rahma, ita kunyama yabata ga Ammi a zaune kan kujerar madubi, bobo ya ce, " kinga kidaure mana, kokin manta wahalar jiya tafi wannan.
K'asa-k'asa yay maganar yanda ammi bazatajiba, ita tunima tad'auke kanta daga Kansu tana kallon baby boy d'inne Wanda take kallo amatsayin tarihi ya maimaita kansa, Dan tamkar bobo yana jariri haka take kallon yaron.
Rahma takuma sakama yarinyar, tana kamawa tacire tana yarfe hannu dafad'in shiiiii wlhy da zafifa.
Tabama bobo dariya amma awannan karon saiya dake, dakansa yasakama yarinyar akaro na uku, Rahma tarik'e hannunsa ga zafi ga kunyar Ammi data lilli6eta, kallon Ammi tayi sannan takalli bobo tamkar zatayi kuka, ammifa na kallonka Dan ALLAH kasaki zan bata da kaina.
Ammi shima ya kalla yana murmushi, to aii bamu Ammin takema kalloba, hankalinta nakan angonta sabo fil.
Dole Rahma tahak'ura har babyn tad'ansha amma sai matse baki takeyi da yarfe hannu harta sha da yawa.
Ammi takatsesu da fad'in to abarta haka shima maigida yasamu yasha.
Sosai kunya ta lilli6e Rahma, Ashe Ammi na kallonsu amma ta sharesu.
Ammi tamik'ama bobo Namijin, itakuma takar6i macen, akafad'a tasakata tana shafa bayanta danson tayi gyatsa.
Shikuma bobo yad'ora ma Rahma beby boy acinyarta, yanzuma haka yasaka masa shima abaki da kansa, Rahma nakukan zafi-zafi, ana cikin haka saisukaji sallama, ammi dake tsaye ta amsa, Safna tashigo cikin 'Yar fara'a, rissinawa tayi yagaida ammi, ammi ta amsa mata cikeda fara'a da tambayarta mai gidan?.
Yana nan lfy Ammi, Ashe ansamu k'aruwa?, ALLAH ya raya.
Ameen Safna, yaukam kunyi 'ya'ya gasunan masha ALLAH, ammi tafad'a tana mik'a mata baby gal dake hannunta.
K'ar6a Safna tayi cikeda sha'awar babyn.
Rahma ta ce, "Anty Safna sannu da zuwa, tana maganar tanad'an yarfa hannunta.
Dariya Safna tayi, ke lfyarki kuwa?..
Zafi wlhy, Dan ALLAH kabarshi haka Nurulk'albi wlhy yak'oshi.
Bobo yad'ago yanama Safna sannu dazuwa, ya ce, " wannan k'anwar taki akwai ragwantaka.
Zama Safna tayi abakin gadon tana dariya, Ammi tafice abinta dama.
Bobo yacirema babyn nono abaki yana dungure kan Rahma, raguwa kawai.
Eh naji babu komai koma miye kufad'a, anjima kuma saiku nemi abinci awajen jaruma.
Dariya bobo yayi ya ce, "koda k'arfin tuwo aii sai anbamu 'yammata.
Rahma ta ce, " shikenan k'arfinku yabaku to.
Kizuba ido mana zaki gani aii.
Safna dai dariya take musu, Dan yanzu Alhmdllh son bobo yaragu sosai azuciyarta saboda k'ok'arin da ya Kamal yakeyi wajen mantar da ita hakan.
Tal'ek'a fuskar baby boy dake hannun bobo, masha ALLAH yaran duk kai suka biyo kaida Nawal.
Cikeda farinciki ya ce, " ko auntynmu?.
Wlhy kuwa, Safna tafad'a tana dariya, ta kalli Rahma dake gefe tana jiyyar kanta, auta next time saiki haifa mana mai kama dake.
Idanu Rahma tazaro Anty safna ban fito daga magagin wannanba amma kike zancen wata, yanzu kam saidai ku.
Kallonta bobo yayi yana dariya, my Nusfulhayat aikema nanda next year nakeason ki k'ara haifo wasu biyun.
Narke fuska tayi tamkar zatayi kuka, Dan ALLAH my Zuma kudainamin fatannan wlhy akwai wahala.
Dariya safna da bobo suka saka mata..........adaidai nan kuma khursiyya da khairiyya suka shigo dagudunsu, rungume Rahma sukayi suna murna, suduka suka haye gadon khairiyya tazauna Kusada bobo tana amsar baby, itama khursiyya na hannun Safna ta amsa, sai dad'i sukeji sunata k'ank'ame yaran.
Khairiyya ta ce, "yaya, su ya Hamza suna kirankafa.
Mik'ewa yayi yana fad'in lah sunzo gidanne?.
Eh yanzu suka shigo suma.
Fita yayi yabarsu sunata hirarsu da dariya.
Safna sai kallon yaran takeyi cikeda sha'awa, dayanzu itace ta haifesu, dayanzu ita bobo yakema wanan tattalin, ya ALLAH kaciremin son bawan ALLAHnnan gaba d'aya, nima namaida hankalina ga mijina kodan tattalina dayakeyi.
Duk a zuciyarta takeyin maganar.

To nimadai na amsata da Ameen, Dan yanzu tausayi take bani.

_bayan kwana uku_
Aka kawo kayan barka, bobo yataka rawar gani, kayan sai sambarka a keyi, Appa da Ammi ma ba'a barsu abayaba suma da nasu, Rahma sai fad'in kayannan sunyi yawa takeyi, jitake k'aunar mijinta da 'yan uwansa nak'ara ratsata.

Haka akaci gaba da kar6ar bak'i yan barka har zuwa ranar suna.
Yara sunci sunansu, Namijin sunan Appa yaci, wato Aliyu haidar, macen kuma Ni'imatullah.
Za'a ringa cemusu Shareeff da Shareefa, to saimuce ALLAH yaraya Aliyu & Ni'imatullah.
'Yan uwan Aunty Ni'ima sunji dad'in wanan karamci daga Rahma, Appa ma sai albarka yake saka mata, hakama sauran dangi.
Suna yak'ayatar alhmdllh abin sai Wanda yagani, naga tarin masu karatu awanan suna masha ALLAH.
kwalliya kam Ranar Rahma tashata, kamar kasaceta ka gudu, awajen yin hotunama bobo sai yabawa yakeyi, shima yaci wankan shadda sai k'yalli da k'yawun haiba kefita agareshi.
K'yaututtuka kam sun samu bila adadin, gadon Ammi damk'am yake da kaya iri-iri.
Zuwa dare taro yatashi mutane kowa yakama gabansa, sai su Ammi kawai, da Rahma bobo Nawal hibba, Appa da 'yan aiki, saikuma shareeff da shareefa.
Bayan Rahma tafito wanka tashirya kanta cikin kayan barci.
Tana zaune ak'asa shayi takesha, yayinda Ammi takeyima Shareeff da shareefa shirin barci, Nawal da heeba suna zaune kan gado sai k'irga kayan jariran da aka samu sukeyi da turame.
Da sallama bobo yashigo d'akin shima sanye yake da kayan barci, zama yayi Kusada ammi yana fad'in Ammi shirin barci kukeyine?.
Shirin barci mukeyi mukarram, suma sun gaji yakamata su kwanta su huta ko.
Gsky ne ammi.
Mik'a masa Shareeff tayi tana cigaba da shirya shareefa, umm my sweet dady, yau kunsha hayaniya ko?........ Nawal ta ce, "papa!.
Na'am Mamana miya faru?.
Kaga kayasu baby's d'inmu dayawa.
Nagani kuwa, kunyi goshi, nawa kuka k'irga?.
Papa bamu gamaba'ai cewar hibba.
To kudage mugani nawa muka samu.
To papa.
Dubansa yamaida ga Rahma, ohni 'yammata dankina shan shayi saikiyita shama mutane k'amshi?.
Murmushi Rahma tayi ta ce, " aibanaso kace zakashane.
Ummyim aina ganoki, Ammi ALLAH nima yunwace takoroni nakasa kwanciyafa.
Dariya Ammi da Rahma sukayi, ammi ta ce, "Ashe da gskyar Rahma datak'i yimaka tayi.
Humm ammi kibarta aii zan rama.
Mik'a masa shareefa tayi, to rik'eta nasamo maka abinci.
Kar6arta yayi yana sumbatar kumatunta, my beauty na.
Rahma takallesu cikeda sha'awa, yanda yaketa wasa da yaransa abin birgewa.
Babu dad'ewa Ammi takawo masa abinci, ta d'auki yaran shikuma yasakko yanacin abincin, heeba da Nawal suka sakko suna murna dafad'a musu adadin kayan.
Sudai su Rahma sai dariya suke musu.
Ammi ta kwantar da yaran ad'an gadonsu sanan tafice wajen Appa.
Rahma takalli bobo daya ture filet d'in abinci, wai harka k'oshine?.
Alhmdllh my Nusfulhayat nak'oshi.
A dama bayunwar dakake fad'a kakejiba.
Haka kikacedai, amma kinsan ALLAH, tun safe damukayi break nidasu ya sulaiman bankuma samun nutsuwar zaman cin abinciba har awajen waleema, Ammar nata fama dani nazauna naci amma nakasa, lokacinma banajin yunwar saboda d'awainiyar mutane, kai my cute mutane sunmana halacci wlhy, yanda kikasan mun Tara taron bikifa, sandasu Ya ishaq sukace za'ayi walema kamar yanda akeyi duk sanda aka haihu canayi kawai abarsa tunda lokacin haihuwar Nawal anyi, Dan gani nake mutane bazasuzoba.
Amma suka dage sai sunyi, wai yanzuma yadace suyi tunda wanan ne karo nafarko da'aka haifa mana twins a family.
Saiga mutane tamkar anbusa k'aho.
Dariya Rahma tayi ta ce, "Zumana aikai mutumin muranene kowa zaiso halartar taronka, gakuma gayyar su ya Hamza.
Hakane my Nusfulhayat, kumafa Appa shima yayi tasa Walemar da safe.
Kai haba?.
Wlhy kuwa my cute.
Tab lallai mungodema ALLAH sosai, ALLAH yasakama mutane da alkairi dansuyi rawar gani, jibifa kayan da'aka Tara mana.
Nagani wlhy, ALLAH yabar zuminci dai.
Amin.
My Nusfulhayat yaushe kuma zamu koma gidanmu?, tunda angama suna.
Wata 'Yar dariya Rahma tayi tana hayewa gado, ta ce, " sai bayan arba'in.
Shima dariyar yayi danbai d'auki maganar tata serious ba, tashiyayi yana fad'in haba yarinya kima canja shawara dai, gaban gadonsu shareeff yaje yamusu kiss sanan yayma Nawal dasuke kwance agado idata hibba, Rahma dai duk tana kallonsa.
Gabanta ya iso ya durk'usa ak'asa yana kallonta, itama kallonsa takeyi, batayi auneba taji bakinsa cikin nata.
Kissing nata yake sosai danba k'adamar kewarta yayiba.
To itama daga gareta hakane, sosai ta taimakeshi suke faranta ran juna, jin tahowar Ammi d'akin yasaka Rahma saurin k'wace kanta, suduka duk maida numfashi sukeyi a wahale.
Ammi tashigo da sallama, kasa bobo yay da kansa Dan bayaso suhad'a ido da ammi, ya tabbata saita gane halin dayake ciki.
Ra6awa yayi tagefenta yafice kansa asunkuye, itadai Ammi ta kalleshi ta kalli Rahma dake kwance akan gado tayi luf ita adole barci takeyi.
Saida yakai gab dazai fita sanan ya ce, "Ammi saida safe.
ALLAH yakaimu Ammi tafad'a tana binsa da kallo harya ida ficewa.
Kallonta ta maida ga Rahma, ta ce, " kidai dage kibiye masa keda kikeda la6u6un jarirai, wannan dalilin yana d'aya daga cikin abinda yasa na maidoki gabana, dannasan halin mukarram ko kad'an bashida hak'uri akan abinda yakeso.
Rahma dai tayi luff kamar ruwa yacinyeta, sai fad'in take a zuciyarta My Zuma kabani kunya yau wayyo ALLAH na.
Ammi ta shige bayi tana cigaba dayima Rahma fad'a................😂

*_Luv you oll._*
*_(((S))).........2017_*
[11/12, 3:00 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•🅱🅾🅱🅾•_

*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*

7⃣2⃣

Alhmdllh abubuwa nata tafiya yanda yakamata, su Rahma harsunyi arba'in, yara sunyi 6ul-6ul dasu abin sha'awa da birgewa kamar subani, bak'aramin gyara Ammi takrma Rahma ba awanan zaman wanka, aiko ko ita kanta tasan taji gyara Dan fatarta tayi wani k'yau da laushi, kuma zammm takejin kanta.
Bobo nata fushi Dan yaso sukoma gidansu tuni, ammi ta ce, "saidai yakoma shikad'ai su Rahma dai ba yanzuba, wanan dalilinne yasashi fita harkar Rahma gaba d'aya, shi adole fushi yakeyi da'ita, daga gaisuwa babu abinda yake had'asu, saikuma yad'auki yaransa kokuma yazauna ad'akin yana musu wasa, ada Rahma tashiga damuwa da sauyin nasa, amma da Ammi ta zaunar da ita tana lallashinta da nuna mata itama tafita harkarsa da Kansa zai dawo gareta, daganan sai Rahma tasami nutsuwa, wani lokacinma har dariya yake bata idan yana shan k'amshi, musamman idan takamashi yana satar yimata kallonnan nasa k'asa-k'asa, dasun had'a ido saiya gimtse fuska, kokuma yakwashi yaran yabar mata d'akin.
Ita kanta ammi bobo yana bata dariya, data kasa daurewa har Appa tabama labari, shima yaci dariya ya ce, " babana na kaina.

Bayan kammala arba'in suka fara zaga dangi.
Gidansu tafara zuwa, bak'aramin farinciki Abba da ummi sukayiba daganin jikokinsu, anan tawuni sai dare oga yazo yad'aukesu abisa matsawar Appa, Dan ya ce, "dolene yakaita ko ina takeso.
Haka suke tafiya amotar babu mai tanka wani.
Washe gari kuma gidan ya ishaq sukaje suka yini saidare yaje yad'akkosu, daganan kullum akwai gidan dazasuje su yini, haka sukaita zaga dangi, sunje gidan ya sulaiman, gidan ya Hamza, gidan ya Shaheed, gidan ya muneer, gidan Ammar, gidan aunty yahanasu, gidansu marigayiya Ni'ima, gidan khairiya da khursiyya, gidan Ameera, gidan Basma, kai babu Inda basu zagaba, gidan Safna ne k'arshen zuwa, tabar gidan Safna k'arshene dantasamu suje weekend yakaita tunda safe tawuni sosai..
Aiko ayau Asabar suka Isa gidan, cikin farinciki Safna ta tarbesu, har mamaki Rahma tayi, sai nan-nan takeyi dasu, tamkar tagoyasu Rahma, cikin mutunci suka gaisa da bobo, Wanda shima canjawar safnar kebashi mamaki.
Itakam zuwa yanzun zuciyarta fes, kallon bobo takeyi amatsayin d'an uwa kuma mijin k'anwarta, bayan haihuwar Rahma tak'ara dukfa da addu'a, takuma k'ara Neman gafarar iyayenta, suka kuma k'ara jaddada mata sun yafe mata suna kuma k'ara tayata da addu'a ALLAH ya daidaita lamuranta.
Wad'annan abubuwanne suka taru suka k'ara taka rawar gani wajen inganta farincikita dakuma jin son bobo yafita fit azuciyarta, saidai tana ganin girmansa damasa soyayya irinta 'yan uwantaka tamkar su ya munner, soyayya mai tsafta kuma ingantacciya suke gudanarwa itada mijinta, wani bala'in sonsa takeji ayanzu haka, shima soyayya yake nuna mata irinta 'yangatan mata kamilallu, dankoba komai yana alfahari da safna, cif tazo MASA a cikakkiyar budurwa shiyya 6areta aleda, dama baita6a kallonta dawata illaba saita tsiwa.
Su Kansu Rahma da bobo yau sunsha kallo, danba kunya safna da ya Kamal suke narka soyayya agabansu.
Rahma taji dad'i sosai dataga 'Yar uwarta tak'ara kwantar da hankalinta, aiko yau sosai takejanta ajikinta, su shareefa kam ai tamkar ta lashesu Dan so da k'auna, wuni sukayi ahannunta, tad'auki wanan ta ajiye ta d'auki wannan, haka suka wuni cikin farinciki da k'ara k'aunar juna.

Su bobo na fita sallah Safna taja hannun Rahma suka shige k'uryar d'aki, magunguna tad'akko tabama Rahma, tanata mata bayanin yanda zatayi amfani dasu, Rahma tarufe fuska yana fad'in kai aunty Safna ALLAH kina bani kunya.
Dukan wasa Safna tayima Rahma, kai auta gulmarki tayi yawa wlhy, idan kina tareda ya Abdulmaleek aii idonki rufewa yakeyi amma saikina gabanmu kice wata kunyar gulma, dama sabodake na had'asu, jiyannan nakecema my heart yakaini gidan Ammi nakuma gano yarana, ya ce, "nabari sai ranar Sunday, to ashema kuma hanya, 'Yar uwa k'ara gyara kanki ya Abdulmaleek yaji zammm danya k'ara rik'e manake d'amm, safna tak'are maganar da d'agama Rahma gira, dariya suka saka harda tafawa tamkar wasu k'awaye, Rahma ta ce, " ALLAH yabarminke auntyna, suka kuma kashewa da dariya.

😂wayyo masu karatu dad'i tamkar yakasheni, nasan kumafa yau hakan take agareku musamman masoyan Safna, luv you so much safnarmu😘👍🏻.

Sosai tahad'a 'Yar k'anwar tata Dan acewarta batada kamarta aduk fad'in duniya, sukad'aine mata agidansu sukashe su rufe abinsu, hira sukayi sosai ad'akin harsu bobo suka dawo basu saniba.
Abubuwa sosai safna tahad'ama Rahma harda sabulai na gyaran fata, Rahma sai dad'i takeji da k'ara k'aunar 'Yar uwarta, yanzukam sunzama tamkar yanda take buri tun farko, saidai fatan ALLAH yak'ara had'a Kansu waje d'aya.

Sai bayan isha'i suka fito zasu tafi, shareef da shareefa suna hannun Safna da ya Kamal, Rahma tashiga Kusada bobo ta zauna sanan Safna taziro mata shareef da ledar kayanta, my sweet lil gasu karfa ki tsaya Sanya Dan da zafi-zafi ake dukan k'arfe, abinda Baki ganeba to naji kira.
To my aunty godiya nake sosai ALLAH yabar zuminci saikinzo d'in.
Bobo dake kallonsu sun burgeshi sosai, cikin zolaya ya ce, "auntynmu mi muka samune haka?.
Dariya Safna tayi ta ce, " k'anina abin sirrine aii.
Lalala yanzunan auntyna dake za'a had'eminkai?, Kamal zoka ganemin nan.
Dariya ya Kamal yayi idonsa akan safna, tad'aga MASA gira, shikuma yasakar mata lallausan murmushi, bobo ya ce, "Kamal sai magana akeyi agabana adunk'ule bana gane komaifa.
Cikin dariya ya Kamal ya ce, " kaikuma ga rashin hak'uri, aisaika kwantar da kai kaji Inda bakin zaren yake, kokuwa my Angel?.
A to my heart gaya MASA dai.
Rahma dai dariya take musu, bobo ya ce, "shikenan idan tayi wari aii maji, cikin dariya Rahma ta ce, " aibama zatayiba.
Dariya suka kwashe da ita su duka, safna takuma gwargwad'ama Rahma magana akunne suka kuma tafawa suna dariya.
Bobo ya ce, "Kamal bara kaga nagudu da my Nusfulhayat d'ina kafin matarka tak'ara zugemin ita.
Nanma dariya suka kumayi sosai, daganan sukayi sallama bobo yana mota suka tafi, zuciyar bobo k'al da farincikin Safna tasaki jikinta yanzun komai ya wuce, gashi sun had'e Kansu itada 'Yar uwarta, dama fatansa kenan akullum.
A can kuwa su bobo na tafiya safna ta narke ajikin ya Kamal wai saidai ya d'auketa bazata iya tafiyaba, dariya yayi ya ce, " my Angel kemafa shagwa6a66iyace tafad'a a ji, d'aukar kayansa yayi tamkar jaririya suka shige gidan suna dariya, asaman doguwar kujera ya sauketa suna cigaba da dariyarsu, cikinta yashafa yana fad'in Nima yaushe zaki bani nawa babyn my Noor?.
Ido d'aya safna takshe masa ta ce, "ayanzu hakama ina zaton kasamu, Dan kwanakin preod d'ina sun wuce kobaka lissafi?.
Cikin farinci ya k'ank'ameta yana fad'in kumafa hakane my Angel, soyayya mai tsafta kuma nagartacciya yashiga Nuna mata, safna ma tana bashi gudummawa saida suka soyu sanan suka tashi adarennan sukaje pharmacy, tsinken gwajin ciki suka siyo, aiko suna gwadawa sukaga tanada ciki, wayyo zokaga murna da farinciki awannan gidan, tun adaren suka fara bazama dangi.
Safna Rahma tafara kira wadda harsunje gidan tuni, tagama shirin barci kenan kiran safna yashigo, ta guntsa mata abin farincikin daya samesu bayan tafiyarsu, tsalle Rahma takeyi harta bama safna dariya, safna ta CE, " kai lil ya bobo nashan fama, har yanzu ana nan ana gwada halin k'uruciya.
Kai aunty nid'in?, Rahma tafad'a cikefa shagwa6a.
Eh mana.
Bubbuga k'afafu Rahma tafarayi ak'asa ita adole ba haka bane, bobo daya shigo yanzu yakwantar dasu Shareef yatsaya yana kallonta, suna had'a ido yakauda kai yana ta6e baki, shi adole ba kallonta yakeyiba, Ra6awa yayi tagefenta ya fice, Rahma tabishi da kallo yana turo baki gaba.
Bayan fitarsa Rahma ta ce, "wlhy Anty d'azun namanta muyi wata magana, tamkar zatayi kuka take maganar.
To inajinki auta miya farune?.
Zayyane mata abinda ke faruwa tsakaninta da bobo tayi.
Dariya safna tayi ta ce, " kema ki shareshi, kedai kita amfani da magungunan nan, na tabbata duk randa kuka koma gidanku yakashe amarci insha ALLAHU saiya dawo dakansa yana Neman shiri da lalla6arki, kuma zakice Nina fad'a miki.
To shikenan aunty na ngd ALLAH yabar zuminci ya saukeki lfy kema, ki Haifa mana yaranmu 'yan uku.
Kai auta rufamin asiri 'yan ukun lfy.
Dariya sukayi gaba d'aya, Rahma ta ce, "I luv you so much my sweet auntyna.
Luv you more my lil sisina, ALLAH yak'ara kauda shed'an atsakaninmu, Yakuma k'ara had'akanmu waje d'aya muzama taintsiya mad'aurinki d'aya, asuba tagari my heart yana jirana nabashi d'umin jikina, gwauruwa arungumi fillo lfy... d'if ta Yanke wayar, tabar Rahma da dariya.
Kai Anty safna ALLAH ya shiryaki, Nima aii nakusa tashi daga Layin gwagwaren, ALLAH INA k'ara godiya Daka daidaita mana komai cikin sauk'i, ALLAH ka k'ara ninka salatinka ga annabi Muhammad tsira da aminka su k'ara tabbata agareshi.
Sumbatar yaranta tayi ta tamusu addu'a dukda papansu yamusu, gado tahaye tamusu addu'a itada Nawal tareda rungume Nawal dake barci, itama ta sumbaci kumatunta, har yanzu zuciyarta yana k'ara k'aunarta tanajinta tamkar su Shareefa, bak'aramin tausayi yarinyar Take bataba saboda rashin uwa, amma tayi alkawarin zamema Nawal uwa har abada, bata fatan ranar dazatazo ta banbanta soyayyarta dasu shareeff.

*_BAYAN KWANA UKU_*
bayan kwana uku da zuwa gidan aunty Safna Ammi tashirya Rahma tsaf da shirin maidata d'akin mijinta, nasiha sosai Ammi da Appa sukai musu tareda fatan alkairi agaresu, sosai Rahma tasha kuka Dan ko babu komai tayi sabo da zama gidan sosai ayanzu, amma babu yanda ta iya.
Zuwa dare bobo yakwashesu sai gidan, ko a mota kuka Rahma taitayi, bobo yana kallonta amma baice da ita k'alaba.
Koda suka Isa gidan saitaga komai tsaf, angyara gidan sosai, wanka kawai tayima yaran tamusu shirin barci, Nawal na kwance bisa gado tanatama su shareef wasa, sosai yarinyar take k'aunar yaran, komai tasamu ta ce, "na Shareef da Shareefa ne.
Rahma dake tsaye agaban madubi tana shirin barci ta ce, " babyna bazakiyi barciba?, gobefa idan ALLAH ya kaimu akwai school.
Momy nidai bazanjeba zan zauna gidan taredasu Shareff.
A'a babyna to idan bakison zuwa makaranta suma idan sunyi girma aii bazasuje ba ko, ki kwanta kiyi barci abinki da antasoku bakina tareda suba.
To momy bara suyi barci sannan nayi.
Dariya kawai Rahma tayi batace komaiba.
Bobo dake tsaye abakin k'ofa yanajin hirarsu ya ida shigowa cikin d'akin, ta madubi Suka had'a ido da Rahma, batace komaiba haka shima bai tankaba yahaye gadon wajen yaransa.
Lalla6a kayansa yaytayi harsukai barci suduka ukun sanan yagyarama Nawal kwanciya, yamata addu'oin barci ya shafa mata, suma su Shareefa ya kwashesu zuwa d'akinsa, itadai Rahma da kallo kawai tabishi, ad'an gadonsu yasakasu yamusu addu'oi suma, Rahma na zaune abakin gado tana addu'oin barci danta k'udiri aniyar bazata bishi d'akinsaba.
Batayi auneba taji anyi sama da ita, ciccila k'afafunta takeyi tana fad'in wayyo dadyn Nawal Dan ALLAH kabarni ALLAH barci nakeji.
Bai sauraretaba yadireta agadonsa, ganin zata addabi kunnensa da surutu ya had'e bakinsu waje guda, zallar soyayya mai tsafta yashiga aika mata, hummm lallai bobo uayi missing d'in Nusfulhayat d'insa, itamafa mutuniyar taku muk'us kakeji, tuni tafara maida murtani........🤰🏻😜.
Hummmm yaukam ansha fama Dan sabon ango da amarya suka koma, ranar kam Rahma ta murzu ta shaida bobo yayi kewarta sosai Dan bai d'aga mata k'afaba har gabannin asuba ana Abu d'aya.
Washe garima dak'yar ta lala6ashi tatashi tahad'a musu breakfast.
Wankama tare sukayi, nanma saida suka kashe juna da soyaya sanan akayi wankan suka firo, ta shiryashi tsaf cikin shirin office, sanan ta tata Nawal itama tamata wankan shikuma yataimaka mata da shiryata, tayima su Shareefa suma duk shine yashiryasu.
Gaba d'aya suka d'unguma zuwa dinning shi yana d'aukeda shareef nawal tana d'aukeda shareefa, Rahma kuma tashiryama kowa breakfast agabansa sanan ta kar6i sharifa ahannun Nawal danta samu nutsuwar cin abinci.
Bayan gamawarsu yad'auki Nawal suka tafi, aka bar Rahma itadasu Shareefa kawai.....

Haka rayuwa taciga da tafiya musu wataran Zuma wataran mad'aci, yaransu sunata k'ara samun girma da kulawar iyayensu.
Soyayya kam Rahma da bobo ba'a cewa komai sai sambarka.
To ALLAH yacida 'yan bayan haka irinsu o e😂.......bandai fad'i sunaba bare ace nace😜🤸🏻‍♀.

*_"BAYAN WASU SHEKARU........_*

*_Luv you oll_*.
*_(((S)))........2017_*
[11/12, 3:00 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•🅱🅾🅱🅾•_

*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*

7⃣3⃣

*_BAYAN WASU SHEKARU...._*

Abubuwa sun faru da dama, ciki harda haihuwar Safna, tasamu d'iyarta mace wadda taci suna khadeeja, bayan ita takuma haihuwar Abubakar sadiq, yanzu haka tana goyon mace Asma'u.
Soyayaya itada ya Kamal d'inta ko sai abinda yay gaba, komai yawuce tamkarma bai faruba saidai tashin zance.
Su khairiyya da khursiyyama duk sun haihu, yanzu suma yaransu uku uku.
Anty Ameera ma yaranta biyu.
Hakama Basma tanada biyu.
Anyi Auren zeenat da baseera suma harda tsarabar ciki.
Itama ihsan k'anwar ya kamar ansha bikinta da musaddiq k'anin marigayiyya aunty Ni'ima, Wanda sun had'une ranar bikinsu Safna suka shirya Kansu.

*_bara nalek'a muku gidan bobo naga wace waina ake toyawa kuma._*🤓.

Tundaga harabar gidan naked'anjin hayaniyar yara, nak'arasa falon saina tadda Rahma kwance saman doguwar kujera idonta akan TV, gefe kuma Nawal ce zaune itada Shareeff da Shareefa tana koya musu homework, saikuma yara biyu dake fad'a duk maza wad'anda ak'alla zasukai shekara hud'u da kuma 5½, d'an shekara hud'unne Kebin d'an shekara Biyar suna zagaye falo yana fad'in nisaika bani abuna, nisaika bani abuna.
Nawal datazama 'yammata Dan ayanzu tana ss2 a Secondary ta ce, "Farhan wai bazaka bashiba, ALLAH natashi saikayi kuka, kabashi kazo kayi homewook d'inka.
Wanda aka kira Farhan ya ce, " yo Anty Nawal nawanefa shi kulum kulum saiyayta yima mutane rigimar banza sai anbashi Abu, yaje d'akin papa yad'akko NASA mana.....
Kafin Nawal tace wani Abu bobo yafito daga d'akinsa sanye cikin jallabiya fara da alama ma alwala yayo......ya ce, "a'a Farhan mike faruwane haka?, momy kina zaune kina kallonsu sunata faman fad'a idan wani yazame yafad'i yaji ciwo fa?.
Yatsina fuska Rahma tayi ta tashi zaune tana fad'in wlhy bazan iyaba Nurulk'albi, ni takaina nakeyi, idan nabiyema Farhan da Shureim gidanan wlhy sainamusu mugun duka, Dan ALLAH gobe idan ALLAH yakaimu ka kwashesu ka kaima Ammi weekend kokuma anty Safna nikam nahuta koda na kwana biyune.
Dariya tabashi da tausayi, tunda tasamu cikinnan yake bata wahala, hargashi yashiga wata na hud'u amma bata hutaba, yay saurin rik'o Shureim dake bin Farhan suna zagayashi, d'aukarsa yayi yana fad'in haba Abbana miyasa kakeda rigima?, yanzu kai ina naka jirgin yake?.
Papa nawafa baya tashi sama yanzun....... Papa wlhy k'arya yakeyi, d'akinkafa yakai ya 6oye jiya dadaddare ko Anty Nawal?.
Shareefa ce mai maganar tana Harar Shureim daketa turo baki gaba.
Kallonsa bobo yayi ya ce, " Abbana wai da gsk aunty Shareefa takeyi?.
Girgiza kai Shureim yayi alamar a'a ba gsky bane.
Farhan ya ce, "ALLAH papa da gsk Anty Shareefa takeyi d'akinka yakai ya ajiye.
Dire Shureim bobo yayi, Yakama hannun Shureim da Farhan kunga kuje kuyi alwala mutafi masallaci lokacin sallar la'asar yayi, Ya Shareeff atashi idan mundawo acigaba da homework d'in tunda babu islamiyya yau.
Mik'ewa Shareeff yayi, araina na ce, " like father like son, gaba d'aya yaron kamarsa d'aya da bobo sosai har d'an Karen muskilancin na bobone, idan baigadamaba sai agama wanan shaftar bazai sakama kowa bakiba, haka yake bashida hayaniya ko kad'an.
Rahma tabishi dakallo tana girgiza kai, miskili kafi mahaukaci ban haushi, wai yaronnan duk abinnan da akeyi bamu isheshi kalloba?.
Dariya bobo yayi ya ce, "k'yawun d'a.....
Rahma ta ce, " yagaji ubansa.
A to kingani, bashida lokacin yahaniyarku ne, baby kuma kutashi kuyi sallah.
To papa Nawal da Shareefa suka fad'a suna mik'ewa.
Nawal ta ce, "momy haryanzu bakijin yunwar?.
Wlhy babyna inajin yunwar amma bana sha'awar cin komai.
Langa6e kai Nawal tayi kamar zatayi kuka momy kidaina zama da yunwa dukfa kin rame.
Daga bobo har Rahma dariya sukayi, bobo ya ce, " to momy ba'aso ki ramefa kullum anfison ganinki Orobo.
Nanma dariya sukayi, Nawal ta ce, "momy bara nayi Sallah Nazo nadafa miki wani abun, to baby jekiyi.
Nawal nabarin wajen bobo yadasama Rahma mayun idanun nan nasa cikeda so da k'auna, my cute Kodai wajen ya Sulaiman zamu komane?, yakuma duba minke?.
Murmushin k'arfin hali Rahma tamasa, a'a Zumana bama saimun komaba, yanzu babu Inda kemin ciwo saidai kasala da d'acin baki.
To shikenan my Nusfulhayat, amma inaga wannan karon uku zaki Haifa mana shiyyasa cikinnan ke baki wahala da yawa, dama gashi kin huta dayawa ga Shureim da shekara hud'u aduniya.
Wayyo zumana dainamin fatannan, idanma ALLAH yasa na haifi mace ai hakama sun ishemu maza uku mata uku Alhmdllh.
Ido yad'an zaro tab my cute saura shidda kenan 12 nakesofa, kuma duk daga gareki.........
Kafin tabashi amsa su Shareeff suka fito kowa yayi alwala, bobo ya kalli Shareeff babana koma ka canja wanana wandon, koma ka saka dogon wando dai kokuma kasaka jallabiya.
Papa jallabiyoyina duk sunyi dattine.
Rahma ta ce, " ba saida nace jiya kad'akko Ashiru ya wankeba tunda zayyi wankin papanku.
Momy ALLAH nibanjiba.
Yaza'ayi kajini tunda kamaida kanka dud'um dunkum, mutum sai muskilanci.......
Bobo yakatsesu da fad'in to yanzudai kasaka dogon wando gayican za'a kabbara sallah.
Juyawa yayi mintuna kad'an yadawo suka tafi masallaci, Rahma ma tashi tayi tanufi d'aki Dan gabatar da sallah.
Hajara mai aiki tazo tagyara falon kafin su dawo, su Farhan sukuma 6atawa.

_____________________
Rahma kwance ajikin bobo, kasancewar yau weekend yana gida, ahankali yake shafa kanta tanad'an lumshe ido dansan yin barci amma k'iriniyarsu Farhan ta hanata.
Tajuya kwanciyarta tana d'anyin tsaki, bobo ya ce, "yayadai my Nusfulhayat?.
Yunk'urawa tayi ta tashi zaune tana turo Baki gaba, Dan ALLAH Nurulk'albi ka iza k'eyar yarancan islamiyya daga nan idan sun dawo suwuce gidan Ammi wlhy surutunsu na damuna, Nawal da Shareeff kawai nake buk'ata.
Dariyace taso kuccema bobo saboda yanda Rahma ke maganar kamar zata FASA kuka, daurewa yayi ya gimtse, ya ce, "kai my cute bak'aramin masifaffiya cikinnan yamaidakiba, da bakiyima yaranki fad'a ko Abu sukaimiki saidai kimusu nasiha da sakamusu albarka, amma yanzu dukkin canja. Miyasa?.
K'ara shagwa6e fuska tayi ALLAH banason hayaniya yanzu Nurulk'albi.
Amma indai Shareefa da Farhan da Shureim suna gidanan sai sun saka mutum ciwonkai.
To Shareeff fa?.
Wanana shi bashida damuwa shida Nawal.
'Yar dariya bobo yayi ya ce, " amma jiya kika gama cemasa dund'un dunkum ko?, Hajiya iya takawo muku Sara ALLAH dai yajik'anta.
Ameen, amma Kasan miskilancin Shareeff fa harso yake ya zarce naka, yaronnan bayason yima kowa magana agidanan, idanfa kaji yana doguwar hira to dakaine.
Lumshe idanunsa yayi yana murmushi , ya ce, "d'an gado kenan my cute saiya zarta....
Buga k'ofarne yasa bobo yin shiru batareda yak'arasaba.
Shurein ne yake kuka yana buga k'ofa da kiran papa! Momy!.
Tashi bobo yayi yaje yabud'e MASA k'ofa, Abbana miya farune?, Yayi maganar yana d'aukar Shureim dake sanye da kayan islamiyya.
Papa ya Shareeff ne idokeni a zuciya.
Kaikai azuciyafa Abbana?.
Eh, shureim yafad'a yana d'aga kai.
Fita bobo yayi dashi, Rahma dai dariya take musu, ta kwanta tana fad'in ALLAH yashiryaka Shureim a INA ake ganin zuciya dahar za'a doketa?.
A can kuma bobo ya iske Shareeff ad'akinsu yana had'a littatafansa na islamiyya acikin jakka.
yana ganin papansu ya yarissina yagaidashi cikeda girmamawa, Shareefa ma dake gyaran gadon su Shareeff d'in tazo tagaida papansu, suduka sanye suke da Uniform d'in islamiyya lemon green.
Bobo yazauna akujerar d'akin yana fad'in ina Farhan da Anty?.
Papa suna d'akinmu, wai Farhan ne baiga hularsaba.
To ina aka ajiye?.
Papa shiyya ajiye da kansa, waikuma ya manta.
ALLAH yasa aganta to.
Yaya Shareeff mi auta yamaka ka dukesa azuciya.
Dariya Shareefa takeyi, Shareeff kam murmushi yayi, araina na ce, "masha ALLAH yaronnan bashida maraba da bobo tako ina.
Papa littafina na Fiqhu ya yaga min, shiyyasa na rankwashi kansa, Dan yakiyaye a gaba, amma ni bandaki zuciyarsaba.
Shureim Ashe kaji laifi kayima Yaya shiyya ya hukuntaka.
Nawal da Farhan suka shigo da sallama, suma gaida dadynsu sukayi, ya amsa yana tambayar anga hular?.
Eh papa anganta, Ashe cikin kayan Shareefa yasaka.
Mik'ewa bobo yayi ya ce, " to kuyi sauri Ku k'arasa lokaci na k'ure muku.

Afalo ya iske Rahma tafito, a'a momy bakiyi barcinba?.
Hummm inani ina barci?, aii inaga saidai idan basawan gidan sun tafi islamiyya kuma.
Zama Kusada ita yayi yana dariya.
Mintuna kad'an duk yaran suka fito.
Duk suka gaida Rahma, murmushi tamusu tana amsawa, tareda tambayarsu sun tashi lfy?.
Kowa ya ce, ''lfy lau momy.
Baby anhad'a wanki waje guda ko?, basai ashiru yazo Yata jiraba.
Lah momy harma yafara wankewa, yaga akwai wuta shine yace bara yayi kafin su d'auke.
Amma yayi dabara, anhad'a da kayan nan na Farhan daya had'a musu daud'a agidan Abba ko?.
Eh duk nahad'a dasu.
To adawo lfy.
Suduka kowa yazo yasumbaci kumatun iyayensu, suma suka sus sumbacesu sanan aka fita ana fad'in sai andawo.
Ajiyar zuciya Rahma tayi ta ce, "kai gidan haryayi dad'i.
Dariya bobo yayi ya ce, "aizasu dawone.
Amma kafin sudawo nahuta.
Ya ce, " idan nabarkiba, yayi maganarne yana d'aga mata gira.
Murmushi tayi ta ce, "Zumana kafa girma.
Hhhh girma kuma?.
Eh mana, kallifa yaranka biyar, koyanzu aka aurar da Nawal zama zatayi ga Shareefa ma tana neman kamota atsawo, yarinyarnan ni bammasan inda takwaso jikinnanba?, sainagama kamar tafi Shareeff k'iba.
Zamewa bobo yayi yakwanta yad'ora kansa saman cinyarta, jikin ya Hamza takwaso aii kobaki kulaba?.
Kumafa hakane wlhy Nurulk'albi, da jikin jiddahn ya Sulaiman da jikin Shareefa, amma duk tsayonka suka kwaso, jiba Nawal da Zainab d'in ya ishaq harfa rankwafawa yarannan sukayi.
Wlhy hakane my cute, jiya danaje gidan ya ishaq naga Zainab cewa nayi kawai suna kammala Secondary amusu aure itada Nawal, ni idan tanima za'abi harda Sumayya yaran duk sun zangame fa.
To aii girman ne babu wahala, mustapha da Sageer gasunan subasuyi tsawoba bakuma su gajarceba har Shareeff naneman finsu tsawo, amma Ahmad da Kamal d'in ya hamzama duk kune, ALLAH dai yaraya manasu baki d'aya.
Ameen my cute, ALLAH ya saukeku lfy kuma, yafad'a yana shafa cikinta.
Murmushi tayi ta ce, " Ameen my zumana, kasan kuwa jiya muna waya da khairiyya takecewa tanason fita takasa saboda laulayi nace mata ainida ita babu maraba, da k'yar na iya zuwa sunan Basma, shine take dariya wai Anty Safna da khursiyya sunfimu dauriya, ranar bikin taufiq da heeba sai aiki sukeyi tamkar bamasu tsohon cikiba.
Dariya yayi ya ce, "dafa gsky khairiyya wlhy, wanan cikin duk yamaidake raguwa, amma cikin Shureim wasuma saida yafito sukasan kinada cikin aii.
Tab kaidai danba ajikinka yakebane, amma cikin Shureim ma nasha zaz6in rana, wata sa'infa kamar jira kana fita aiki su Nawal suka tafi makaranta sai zazza6i yarufeni, ga son jikin tsiya har k'agara nake kadawo najini kwance ajikinka.
Hhhhh mage kenan.
Wlhy asanan namafi mage, cikin Farhan nedai kam bansha wahalaba sosai da cikin daya zube bayan haihuwar su Shareeff, shi saidama nayi 6arin nasan inadashi kamanta.
Inafa zan manta my cute, kai ranar narud'e dayawa, dayanzu yaranmu shida ga na 7.
Dariya Rahma tayi ta ce, haka ALLAH ya tsara, wad'annanma daya bamu mungode masa, wasunacan suna nema basu samuba.
Hakane kuma my cute d'ina, ALLAH dai yaymiki albarka kinji.
Ameen Zumana tafad'a tana sumbatar kumatunsa.
Lumshe idanu yayi yana murmushi, ahankali yabud'e akanta, my cute tashi mutafi d'aki.
d'aki kuma Nurulk'albi?, mizami yo?.
Lada zamu samo mana, yad'aga mata gira, dariya sukayi gaba d'aya...

_____________________
Duk suna zaune afalo, Shareeff da Shareefa na game dasuka had'a da TV, Rahma tana gyarama Farhan kumba Dan gobe idan ALLAH yakaimu Monday, Nawal kam tana note, Shureim najikin bobo yana barci bayan angama masa gyaran k'umba.
Jisukayi ana kwankwasa k'ofa, suduka suka kalli k'ofa, bobo ya ce, "Shareeff tashi kaga waye.
To papa, Shareeff yamik'e tareda ajiye handle d'insa yanufi k'ofar yabud'e.
Kallon mutumin yake d'an kimanin shekara 40+, yarissina ya gaidashi.
Mutumin ya amsa cikeda murmushi yana k'arema Shareeff kallo, tabbas da ace d'an Adam yana komawa baya zuwa k'uruciya dayace bobone agabansa.
Ganin kallon da mutumin yake masa yasashi fad'in uncle kana Neman waye?.
Murmushi yayi ya ce, " yaro ina Neman mahaifinkane, Dan daga ganinka kai jinin *_Abdulmaleek bobo_* ne, babu inda ka banbanta dashi, yaro miye sunanka?.
Sunana Shareeff.
Masha ALLAHU d'ana Shareeff, kacema mahaifinka Haneeff Sunusi dala ne yake sallama dashi.
Jinjina kai Shareeff yayi yajuya domin isar da sak'o ga papansa.
Shareeff yanaga ka dad'e?, wayene?.
Papa ya ce, "sunansa Haneeff Sunusi dal.......
Aii kafin Shareeff yak'arasa Rahma da bobo duksun zaro ido waje, bobo yace cemasa yashigo.
Yakalli su Nawal yace kusaka hijjabanku, ak'idarsace wanan indai wani bak'o namiji zai shigo koda Ammar ne, ko 'ya'yan su ya ishaq to dolene su Shareefa su saka hijjabai, dama tuni Rahma tasaka nata..
Da sallama Haneeff yashigo, bobo ya amsa cikeda fara'a da mamakin canjawar haneeff, yazama babban mutum harda gemu,haneeff ya zauna cikeda fara'a yanabin yaran da kallo, masha ALLAH Abdulmaleek ka Tara zuri'a kam.
Dariya bobo yayi yabashi hannu suka gaisa, Rahma ma ta gaidashi, su Nawal kowa ya gaidashi, sannan suka tashi suka koma d'akinsu.
Dandanan Shareefa da Nawal suka cika masa gaba da kayan motsa baki.
Bobo ya ce, " haneeff dama zaka iya tunawa dani?.
Dariya Haneeff yayi ya ce, "Abdulmaleek kai basoyine dabaza'a manta dakaiba, kakafa tarihin dabazai gogu a duniyaba, tundaga lokacin Dana tsinci kaina gidan yari lokacin da abubuwa suka fara nisa, addini da ake koya mana ya hudani saina tabbata kai masoyine na hak'ik'a domun kataimaki rayuwata, k'ila dabaka saka ankamaniba har naje wannan gida da yanzu rayuwatama ta lalace, bazan mori komaiba, amma yanzu kalleni nazama babban malami acikin gidan, jiya jiya nafito amma nace tabbas sainazo na ganka, naje office d'inka sai akacemin aii tuni katashi, sunmin kwatancen office d'inka na yanzu, dakuma super market d'inka, to naje super market d'innne aka bani address d'in wannan sabon gidan naka, shine nazo.
ALLAH sarki haneeff kar ka damu kanka aii komai yawuce, ya bayan rabuwa?.
Sai godiyar ALLAH kam, ya iyalinka?.
Dariya bobo yayi ya ce, " gasunan lfy lau, haneeff yabama Rahma hak'uri daneman gafararta akan kamasu da mahaifinsa yasa akayi alokacin, yad'ora dafad'in nazo Neman yafiyarkune dakuma heebba Dan ancemin tana wajenka.
Hakane tana tareda mahaifanane, yanzu hakama tayi aure wata d'aya daya wuce.
Da sauri Haneeff ya ce, "wata aure?.
Yaron yayanane Taufiq d'an wajen Yaya ishaq.
Haneeff yashare hawayensa yana fad'in ALLAH sarki heebba ALLAH ba azzalumin sarki bane, ALLAH yabaku zaman lfy, Abdulmaleek Dan ALLAH ina rok'on alfarma kahad'ani damijinta danna rok'i gafararsu.
Wlhy babu damuwa haneeff zan had'aku, yaunema kawai baizo gidananba amma kullum saiyazo ya gaishemu, inagama yau wani uzurinne yahanashi.
ALLAH sarki.
Daganan hira sukayi, bobo yakirasu Nawal duk yanunama haneeff su.
Kaga wanan Nawal ce, itadai nasan bazaka mantataba, itace wadda aka kama tareda momynsu, saikuma 'yan biyu Aliyu da Ni'imatullah, muna kiransu Shareeff da Shareefa, sai kuma Muhammad Farhan, sai Bilal munakiransa Shureim gashinan yana barci.
Masha ALLAH ubangiji ALLAH ya rayamanasu akan turbar addini, yatsaresu daga sharrin shaid'am da gur6atattun abokai.
Ameen ya ALLAH, tokai kuma sai yaushe zakayi auren?...
Hummmm Abdul kenan, wacece zata yarda ta auri tsoho.
Kai habadai aii zama bazai yuwu hakaba, yakamata kayi aure, yakuwa Alhaji?.
Dad yana nan ciwo yahanashi komai, sai yawon asibiti, yanzu hakama daga wajensa nake, harma yace yananeman afuwarka abisa abinda yafaru abaya Dan ALLAH ka yafe masa.
Ayya wlhy komai ya wuce, aibansamma yadawo k'asarba, kwanaki munje muda Appa da ya ishaq da ya Suleiman da ya hamza dubashi, sanan yana tsaka da ciwon nasanma bai ganeniba.
Yanzu bara mushirya saikamana jagora mudubashi Dan ALLAH.
To shikenan.

Cikin 'yan mintuna suka shirya, gaba d'aya har yaran sukaje asibitin.
Bak'aramin tashin hankali su bobo suka shigaba da ganin Alhaji sunusi dala, dukya yamushe tamkar bashiba.
Yana kuka yana rok'on gafarar bobo dasu Rahma.
Bobo yace ya yafemasa.
Alkairi yamasa sosai sanan suka fito kiwazuciya cikeda k'arajin tsoron ALLAH.
Daganan gidan Taufiq sukaje haneeff yanemi gafarar heebba da Taufiq, duksun yafe masa.

Daga nan gidan Ammi suka biya suka gaishesu.
Amma da Appa tsofaffin kirki sunji dad'in zuwan 'yan jikokinsu, nan suka zauna akasha hira da dariya har yamma sanan sukaje gidansu Rahma nanma suka gaida ummi da Abba, suma sunji dad'in ganin 'yan jikokinsu, agidan Safna aka yada zango itama danata family abin sha'awa, sai dare suka dawo gida bayan bobo yabiya dasu shopping kowa takwaso abinda yakeso, suka dawo gida cikeda farinciki da k'aunarjuna.
Kowa d'akinsa yanufa danyin shirin barci.

Rahma na tsaye gaban madubi tana d'aure igiyar rigar barcinta bobo yashigo, tabaya ya rungumeta, yana dad'in amincin ALLAH ya tabbata agareki uwar 'ya'yana.
Juyowa tayi suna fuskantar juna, itama cikin kashe murya ta ce, "kaima amincin ALLAH ya tabbata agareka uban 'yayana.
Murmushi mai kashe zuciya bobo Yamata, yakuma manneta sosai ajikinsa, ya ce, " I luv you so much my Nusfulhayat.
Luv you more my Nurulk'albi na zumana.
d'aukarta yayi cak yahaye gado da'ita suka shiga nunama juna zallar k'auna maicikeda farinci na har abada, tamkar sunyi shekara basa tare.......

🚶🏻‍♀sum sum nafito domin nabarsu haka suma su shak'ata nima nahuta, masu karatu kuma Ku huta.

Tammat bi hamdullh.

*_luv you oll._*
*_(((S))).....2017_*
[11/12, 3:00 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•🅱🅾🅱🅾•_

*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*

7⃣4⃣

_Alhamdullahi Ala kulli halin, ina mik'a d'unbin godiyata ga ALLAH mad'aukakin sarki daya bani iko da damar kammala wanan littafi mai suna Abdulmaleek bobo, babu abinda zance da masoya saidai godiya domin kun nunamin d'unbin k'auna, ALLAH yabar zuminci ngd ngd ngd har babu adadi._

*_inad'anso naja hankalin masu karatu a wanan ga6ar._*

_bai k'yautu amatsayinka na Wanda ka6ata lokacinka harnawani tsawon lokaci kana bibiyar littafiba ace baka ammfani dakomaiba acikinsa, saidai kawai ka karanta kayi farinciki, ko tausayi, ko bak'in ciki ka kakka6esu anan katashi batareda kad'auki wani muhimmin abuba ka gwada wa rayuwarka Dan ganin amfaninsa, aganina indai hakane gara karka 6atama kanka lokaci waje karantawa kuwa._

*_ni yanzu ba alfahariba bana karanta littafi na 6ata lokaci na a banza, kumani babu ruwana ko yau kika fara rubutu to zan karanta littafinki, idan soyayace alittafin yak'unsa tofa saina d'auki wasu abubuwan nagwada ga mijina naga shin sunada amfani?, idankuwa wani abune sa6anin hakan tofa shima saina gwada, idan Wanda yakamata ka gudane to zan gujeshi kuwa, idan Wanda zai amfanenine bana sanya wajen yinsa, to kuma haka nake fata Ku kasance._*

_littafin Abdulmaleek yakunshi abubuwa dayawa, soyayya, muhimmancin biyayya ga iyaye, muhimmancin sanin hak'in 'ya'ya mata dakuma kwato musu hak'insu, musamman akan fad'e da ayanzu babu abinda ake cin mutuncinmu dashi kamar fad'e, awani fannin muma Matan munada laifi saboda shigar banza damukeyi dasunan wayewa, wani kuma lokacin ana cutar damune musaman ga k'anan yara wad'anda bazasu iya kare kansuba, kuma bayan an keta musu haddi basuda wani tsayayye dazai tsayama raayuwarsu bare k'wato musu hak'k'insu musamman idan 'ya'yan masu kud'ine suka aikata ta'asar, sai muhimmancin zuminci, littafin Abdulmaleek yanuna muku muhimmancin zuminci musamman idan kukayi dubi da family d'in Alhaji Aliyu Abdulmaleek hamshak'i abinsu abin birgewa da ban sha'awa, babu mummunar ak'idarnan irinta uwar miji ko uban miji ga surukansu, Rayuwar bobo abar alfaharice gakowane matashin saurayi Dan zaiso yakasance Jan wuya mai gasky da Kare hak'in d'an Adam, bobo bashida tsoro kuma bashida kwad'ayi shiyyasa yazama dodon azzalumai, ayanzukam samun irinsu bobo k'alilanne acikin al'umma, zakaga duk tarin dukiyar mutum hangen k'ari yakeyi takowacce hanya, saikuma k'awaye, idan bakayi gamo da k'awayen kwaraiba tuni za'a zirmaka karuguza tarbiyya da iyayenka suka dad's suna ginaka akai, Safna taso tafad'a wanan tarkon akan hud'ubar baseera, amma da taimakon zeenat tagane gsky harma baseerar, saikuma hak'uri duk rayuwar dababu hak'uri acikinta saika sameta cikeda damuwa, hak'uri babban jigone dake Jan zaren rayuwar d'an Adam, idan bakada hak'uri ibadar da ALLAH ya hallicceka Dan ita bama zakayiba, saboda rud'anin duniya mai shagaltar da bayi, da Rahma batayi hak'uriba da bata samu boboba, da Safna tayi hak'uri data samu abin Sonta bobo, amma tabijire aganinta iyayenta sun cutar da rayuwata, wanan matsalar tana taka rawa acikin al'umma, idan iyaye suka za6ama 'yayansu miji sai ace zasuyi musu auren dole, gsky hakan bai daceba mufa 'ya'ya yakamata mu runga tunawa da d'awainiyar da iyayenmu sukayi damu wadda bamuda abin biyansu duk duniyarnan, wannan biyayyar dazamu ringa musu itace me sakasu acikin farinciki da alfaharin sumafa sun haifa, idan har d'a bazai iya share hawayen iyayensaba alokacin dasuke kwaranya to aii banga amfanin haihuwaba kuwa Dan batayi ranaba, hattara 'ya'ya mugyara, fushin iyaye akanmmu babban masiface, kungadai halin hau da Safna tashiga Wanda koda wanan kad'ai aka barka kashiga taskun rayuwa._

_wasu sunsha fad'in na matsa rayuwar Safna dayawa, ba haka bane, inaso Ku gane muhimmancin iyaye da gujema fushinsu, Inda Safna tama iyayenta biyayya data samu abinda takeso alokacin dabatayi zatoba._

_Ku kalli rayuwar bobo mana, shifa namijine amma bai bijirema iyayensaba, dukan aurensa biyu za6insune, kuma idan kuka duba duk yaci ribar gamon katar da mata nagari, to albarkar iyaye ta taka rawar gani wajen samun haka agareshi._

_so masoyan Safna ina mai baku hak'uri sosai, muma muna k'aunarta, munsata a wanan fagenne Dan kugane kuskuren abinda tayi kuma Ku gyara, gamasu sha'awa kuma karsu aikata._

*_idan kuma kuka d'auki soyayyar bobo da Rahma kowacce mace zatayi fatan mijinta yanuna mata irin haka, to hattara samari saikuyi koyi danmu mata 'yanson soyayyane, wlhy ko mace bata sonka idan kanuna mata soyaya saitayi sanyi tamik'a wuya, mukuma mata bafa zuba ido zamuyiba, muma saimuna taimakawa danamu salon sannan za'a had'u agina ingattaciyar soyaya irinta aure._*

Bara nabarku haka, ina k'ara mik'o godiya agareku domun bazaku lissafuba saboda d'unbin yawan dakuke dashi wasuma ban sansuba, ngd sosai ALLAH yabar zuminci, group's da admins dukna gode ALLAH yabar k'auna, 'yan uwana writer's kuma ina mik'o godiya, ALLAH yabar zuminci da hak'uri da juna.

Narubuta wannan littafi tun a 2012 sanan ina amarya agidan my Abdul, ada sunan littafin *_ASHE MIJIN K'ANWATACE?._* daga baya namaida sunan *_ABDUL-MALEEK BOBO_* saboda rawar da bobo yataka a buk d'in, naga yadace sunan littafin yakoma haka.

Saimun had'u a books nagaba insha ALLAH, idan ALLAH Yabani iko kafin k'arewar shekarar 2017 zanyi cikon littafi na goma mai suna *_KARAYAR ARZIK'I_*.
Idan hakan bata samuba kuma sai a sabuwar shekara, zan fara da rubuta *_BAK'IN HAURE_* daganan kuma sai masu zuwa↓

*_KARAYAR ARZIK'I_*.
*_BALBELAH_*
*_BABU SO MIYA KAWO KISHI..... etc_*

Kukasance taredani har kullum.

Takucedai Bilkeesa ibraheem (bilyn Abdul.)

Marubuciyar.
*_→RASHIN SANI!_*
*_→AUREN K'ADDARA KO BIYAYYA?_*
*_→K'ANWAR UWACE KO KISHIYAR UWA?_*
*_→NI DA AMINIYATA!!_*
*_→NAWAFF!_*
*_→KUKAN KURCIYA...._*
*_→SABON AL'AMAREE!_*
*_→BAN SAKETA BA!_*
*_→ABDUL-MALEEK BOBO!!_*

*_K'ARAYAR ARZIK'I_* Coming soon👌🏼

Luv you more, har babu adadi😘😘😘😘😘❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤😄😄😄😄.

*_Bilyn Abdul ce👌🏼._*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.