Complete Hausa Novels

Abu Maleek Complete Hausa Novel

Reading file: Abu_Maleek_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 2 of 3

*Page 33-34*

Sai da mu sha hira sosai sannan Abbas ya baiwa Haidar biscuit da chocolat da ya sawo mashi,haka kawai naji kamar nayi zamana a can tare da É—an uwana.

Kallona Abbas yayi yace "ko ke ma a mayar da ke boarding ɗin ba ki san je ka ka dawo?"baki na turo na girgiza kaina,stop yayi gun mai gasa masara ya na mai fiddo waya ya kira Alhaji amman sam layin yaƙi shiga.

Kuɗi ya miƙa a zuba mashi masarar a leda,miƙo min ɗaya nayi da murna na karɓa na fara ci ina mamakin yadda aka yi su ke sayar da masara kamar wasu Hausawa.

Mu na shigowa gida na tsinkayi Raliya zaune kusan flowers ta na sunsunar su,baki na ɗan taɓe haka kawai naji matar ta fita raina sai ma haushinta da ni ke ji.

Fita nayi na kama hanyar da za ta sada ni da ƙofar shiga falo yayinda shi kuma Abbas ya zarce gun sanyin idaniyar shi,a Shagwaɓe ta faɗa jikin shi ta na shafar gemun shi "miss You dear"sai da yayi mata kiss a lips sannan "moi aussi tu me manques"masarar da ya sawo mata ya miƙa mata ta karɓa haɗi da komawa ta zauna.

Abbas na ƙoƙarin shiga falo appel d'urgence ya shigo mashi,a kiɗime ya nufi mota yayi mata key mai gadi ya buɗe mashi ko da ya hau titi gudu ya kawai ya ke shararawa.
Zuwan shi asibiti sai da ya girgiza,aiki suka fara yi mata sai dai abu ya cuttura doli ya fito ya kira number Noor ta Niger sai da ta kusa tsinkewa ya ɗaga bai bashi damar yin magana ya shiga ce mashi "urgence dan Allah in akwai jirgi mai zuwa ka dawo Innalillahi wa'inna iley raji'un Noor marâtre ce...."sai kuma ya kasa ƙarasawa saboda kuka a doli ya yanke kiran.

Ana shirin kiran sallah jirgin su Noor ya sauka ,direct asibitin ya wuce shi ma sai da ya girgiza yadda ya ga lokaci ɗaya yadda marâtre (uwar rainon su Abbas a gidan marayu)ta koma lokaci guda rabin fuskarta ya yashe yayinda ƙashin ƙafarta ya tsage zafin ciwon kuma ya so taɓa zuciyarta.

Cike da ƙwarewa Noor ya shiga yi mata aiki yayinda a doli aka canzawa fuskarta fasali,naman kanta kuma da ya fita a cinyar ta aka yanka aka yi ma dashe.

Ƙarfe biyun dare har da wasu mintinan sannan aka kammala yi mata aiki duka,cike da gajiya Noor ya shiga ɗakin da aka kwantar da Abbas tausayin abokin na shi ne ya ɗarsa ma shi doli ne ya girgiza domin marâtre tamkar uwa ta ke gare su tun tasowar su ba su san kowa ba sai ita.

Wanka yayi a nan cikin asibitin sannan ya samu tea ya sha,zugum yayi ya na tunanin Tirday irin borin da ta hau a kan zai tawo haka kawai yaji kukanta ya tsaya masa rai.

Ƙoƙarin hakiceta ya ke amman ina tayi katutu cikin zuciyar shi da kwanyar shi, da wannan tunanin barci ya ɗauke shi.
Washegari bayan ya dawo daga sallah asuba ya shiga ya duba Abbas ,jikin nashi kuwa yayi garas dama fargaba ce ta haifar mashi da ciwon.

Har ɗakin da aka kwantar da marâtre Noor ya kai shi,sharrr sai hawaye ganin yadda duk rabin jikinta ya ke naɗe da bandeji.
Ko da suka fito kallon shi Noor yayi yace "please kar ku bari Raliya ta san da haka saboda cikin jikinta"kai Abbas É—in ya girgiza yace "in shaa Allah ba zan sanar da ita ba kuma zan gayawa abokanan ta kar su sanar da ita"

Wuraren tara na safe asibiti ta cika da marayu wai sun zo ganin marâtre ,haƙuri Abbas ya fara basu sannan ya kwantar masu da hankali,sauran marâtres ɗin ne kawai aka bari suka shiga su ma ta glass ne suka hangeta na'ura sai aiki ta ke a jikinta doli suka zubar da ƙwalla.

Abbas kuwa ya na zuwa gida ya tarar da Raliya na sharɓar barci a falo yayinda Hadeeyatullah ke kitchen ta na girki, murmurshi yayi lokacin da ya leƙa ya ga ta dafe ƙugu ta na kallon yadda wanke ke tsuuu cikin mai.

Jin kamar mutum a kaina yasa na waigo, murmurshi nayi tare da yi mashi alama da ya shigo ya gani.Ƙarasawa yayi wanken da cikin mai na nuna mashi wani ƙato nayi mashi alama da shi ne sai wani ɗan matashi na mashi alama da falo wato Raliya ce sai wasu ƴan ƙanana kusan biyar na taɓa cikina haɗi da nuna falo alamun yaran da Raliya za ta haifa ne.

Dariya yayi jin shirme na,sai yace min "to ke ki na ina?"shiru nayi can sai na maƙe kafaɗa na girgiza mashi kai dungure ni yayi da goshi yace "to ke yara dozin za ki haifa min"cike da Shagwaɓa na shiga bubuga ƙafafu shi kuma ya na dariyaya ta.

***Bayan wata biyu

Sosai jikin marâtre yayi sauƙi sai dai har yanzu ba'a cire bandejen ba,a lokacin kuma tuni Raliya ta sani dan dubiya mu ka tai.
Yunwa ni ke ji amman sam Abbas ya hana ni cin abinci kuma ban san dalili ba,baki kawai ni ke turowa shi kuma ya zuba min ido ya na kallo.
Mu na nan zaune Raliya ta fito ita ma cikin shirinta,mota mu ka nufa ga mamakina sai na ga Raliya ta shiga seat É—in baya ni kuwa na shige gaba.
Ba mu zarce ko ina ba sai asibitin su,a cikin harabar asibitin na tsinkayi Dr Noor ya na saffa da marwa ya kasa zama ya kasa tsaye sai zagaye ya ke.

Tsayuwar motar mu ne ya sa shi yin tsaye cak ya ƙurawa Hadeeyatullah ido,wani irin tausayinta ya ke ji tun ɗaga ƙasan zuciyar shi.
Fuska Abbas ya tamke dan ya san dama za'a rina wai an saci zanen mahaukaciya,bai baiwa Noor damar tambaya ba gaisuwar da Raliya ta yiwa Noor ƙememe ya ƙi amsawa sai ni da ya kafe da ido.

Ciki mu ka shiga,gabana ne ya shiga bugawa da ƙarfi ganin Abbas ya fara cire min kaya yayinda Raliya ke gefe tayi zir haihuwar uwa ta ko pant babu a jikinta.

Ina ji ina gani Abbas ya cire min kaya,wani ƙyalle ya luluɓa min haka ma Raliya.
Wani ɗan matashin saurayi ya shigo ina kallo lokacin da ya yiwa Raliya allura da ƙashin baya,cikin kunne na Abbas ya raɗa min "ki kwantar da hankalin ki riga-kafi ne za'a yi maku yanzu zan maida ku gida kin ji ko?"kai na ɗaga dan har ga Allah maganar shi ta samu karɓuwa dan ba ƙaramin kwantawa hankalina yayi ba.

Ya na gama yi min allurar Abbas ya kwantar da ni sai a lokacin Noor ya shigo, dishidishi na fara gani ina jin lokacin da Noor ke cewa Raliya ta ɗaga hannunta ita kuma ta na cewa ta kasa ba ta iyawa to fah shikenan ban ƙara sanin abinda ke faruwa ba saboda barci mai kama da mutuwar da ya ɗauke ni.

Cikin ƙwarewa Noor ya fasa cikin Raliya daidai marar ta ya ciro baby ɗan wata uku da ƴan kwanaki tare da ɗaukar sa ya dasa shi cikin marar *HADEEYATULLAH*😭

Cikin mintinan da ba su wuce sha biyar ba aka gama komi tare da É—inke cikin aka naÉ—e shi da bandeji,É—ankin hutu duk aka kai su.
Noor ya dubi Abbas yace "yanzu hakan da kukayi kun yi adalci ne?ta yaya yarinya ƙarama za ta iya ɗaukar cikin da ba nata ba?"shiru Abbas yayi bai ce komi ba Allah na gani wannan ce kawai hanyar da zai sa su ma su ga ɗan cikin su.

Ko kafin Sallah azahar Raliya ta farka dan allurar da aka yi mata ba ta mutuwar jiki ba ce duka, Hadeeyatullah kuwa sai washegari.
Yunƙurawa nayi in tashi sai dai mi?azaba naji ga cikina doli na koma na kwanta ina hawaye nurs ce ta fita sai ga ta sun dawo ita da Abbas ....

*_35-36_*
Wani mutumi daya kafa bakinsa a hannun Julde, bayan ya finciki naman hannunta ne kuma ya kafa bakinsa ya shiga zuƙar jinin dake zuba ta jikin wajan daya cire naman wajan.

Zuciyar A.m ce ta buga da ƙarfi tare da wani irin harbawar daya sanya shi sanya hannunsa ya dafe tsakiyar goshinsa, tashin hankali ƙarara ya bayyana a saman fuskarsa.

"Innalillahi wa'inna ilaihir Arjun!" Shine kawa abinda yake fita daga ƙasan zuciyarsa tare da fitowa ta cikin bakinsa, yayinda wata ƙyakƙyawan zufa ta shiga yanko masa, jijiyoyin kansa suka shiga Miƙewa.

A hankali ya dinga jaa da baya, sai sauke Ajjiyar zuciya ya kamar wanda yayi tsere, bai taɓa ganin mutanan da suke cin naman mutum ko susha jinin mutum ƙarara a zahiri ra'ayin aini ba, sai yau, wanne kalar abu ne haka? Mene Amfanin shan jinin mutum? Waye wannan ɗin? Sune abubuwan da yake ta tunani a ransa amma babu amsa.

Wata kalar zabura yayi saboda tunawa da mutanan Birnin Bera, ƙara mai da idanunsa yayi kan mutumin daya dage yana shan jinin Julde, ba wasu sutturar arziƙi ne a jikinsa ba, sai wani jan bante daya sanya ya rufe al'aurar jikinsa, yayinda jikinsa yake baƙiƙirin.

A hankali ya juya ya shiga duba wajan, ga mamakin sa sai yaga babu kowa na dangane da mutanan Birnin Bera sai wannan mutumin hakan ya tabbatar masa cewa ƙwace wa yayi daga cikin Birnin Bera ya fasu jikin gari!.

Julde dake fidda wani kalar numfashi bakinta ya shiga fidda wata kalar Kumfa, mai yauƙi ga kuma yadda Jikinta ke ɓari kamar wacce take jijjiga, azabar data keji a cikin jijiyoyin dake Jikinta wacce jini ke gudana a cikinsu ɓata Lokaci ne, zuwa yanzu kam gaba ɗaya tunaninta ya fara sauyawa yayinda hancinta ya fara ɗauko mata wani kalar ƙamshi wanda bata taɓa jin maka mancin sa ba.

A sannu a hankali kuma ƙamshin data keji ya fara juyewa yana dawowa ƙarnin jini, da sauri kuma ta zabura tana ɗan buɗe bakinta yayinda ta ware idanunta akan A.m dake tsaye dukkan jikinsa yana ɓari tamkar wanda ake buga masa gangi.

Kwaɓe fuska yayi tare da marai-raice wa, ya ɗan langwaɓar da kansa gefe guda, saboda wani Irin kallo da yaga Julde ta nayi masa, wanda a zahiri shike Ganin hakan amma sam bata ganin komai kawai Ubangiji ne ya nufe ta da kallon saitin da yake tsaye.

Shiru Julde tayi saboda wani irin baƙon yanayi daya fara shigarta, yayinda gaba ɗaya ta kasa fahimtar komai, sosai taji zuciyarta na buƙatar wani abu, yayinda hancinta ke jiyo mata ƙamshin wani abu, wanda yake gigita mata lissafi,
A hankali kuma jijiyoyin jikinta suka fara saki, yayinda dukkan wani kuzarinta ta neme sa ta rasa, wani kalar numfashi take fesar wa yayinda take jan numfashi kuma da ƙyar.

A gigice Mutumin kuma ya cire bakinsa daga hannun Julde, yana wani irin gurnani, gaba É—aya bakinsa É—igar da jini yake,
Yana layi kuma ya janye jikinsa zuwa baya tare da Miƙewa tsaye, juyawar kuma da zaiyi ne idanunsa ya sauka akan Abu Maleek dake tsaye ya sunkuyar da kansa zuwa ƙasa.
Hangame bakinsa Mutumin yayi wanda zai iya bashi sunan (Arnan daji).
Kai tsaye kuma yana tan gaÉ—i da wata iriyar tafiya mai kama data Æ´an shaye-shaye,
Gaba É—aya bashi da kuzari saboda ya sha jini yayi bankas.

A.m kowa tuni jikinsa ya fara rawa, jijiyoyin kansa sun fito sunyi raɗa raɗa, yayinda gargasar jikinsa ta shiga mimmiƙewa, yana jin kansa na wani irin harba masa tamkar zai tsage gida biyu.

A hankali mutumin yake nufar A.m yana tafe yana buɗe bakinsa, alamar a wannan karan jinin Abu Maleek yake nema, kai tsaye kuma yana zuwa ya fara ƙoƙarin kaiwa A.m cafka.

Karyar da wuya Abu Maleek yayi kafin ya ɗan buɗe bakinsa Murya can ƙasa bata fita sosai yace.
"O'ohhhh"
A dai-dai lokacin ne kuma Mutumin ya ƙara buɗe bakinsa tare da kusanto A.m kafin ya ida sauke bakinsa a damtsan A.m,
Tuni Abu Maleek yayi ƙasa tare da ɗaukan wani ƙaton Dutse ya miƙe a hanzarce kai tsaye kuma ya sauke dotsen akan Mutumin,
Nan take ya tsulale a wajan jini na zuba ta tsakiyar kansa,
A hankali shima Abu Maleek ya sulale a wajan, wanda tuni ya manta da shiga É—aya duniyar tasa, hakan yasa gaba É—aya yaga samaniya na juya masa,
Yana ganin taurari na sakkowa zuwa dab da idanunsa,
Idanunsa a shiga Lumshe yayinda fatar jikinsa ta É—auki rawa sanadiyyar rawar da naman jikinsa yake,
Cikin rashin makama da kuma rashin sanin abinyi ya sanya tafin hannunsa dake fidda wani gumi ya manna a tsakiyar goshinsa, wanda ya kejin kamar zai rabe masa gida biyu, kunnuwansa kowa wani irin numfashi yake jiyowa wanda ya kasa tantance wanne kalar numfashi ne wannan É—in.

Ƙara cure jikinsa waje guda yayi tare fesar da numfashi, ya shiga taune leɓansa, yana jin wata azaba na fincikar jijiyar kansa, kafin a hankali ya fara saki wani sound mai kama da gurnani, gaba ɗaya jikinsa ɓari yake, sanyi da kuma iskar wajan haɗi da haraɓar dake kwance a wajan bai hana,
Wata wahalalliyar zufa keto masa ba, sosai ya keji samun kansa a cikin a zaba muddin juyewar tunaninsa ya tashi.
Zuro sweet tayi da idanunta, yayinda ta rakuɓe waje guda.

1hour left
Ya shiga sauke wani Numfashin wahala yana ɗan jujjuya kansa, dake sara Masa, duk da cewa yaji ciwon yayi ƙasa, amma hakan bai yana yaji kansa yayi masa nauyi sosai ba.

Bakinsa ɗauke kuma da salati ya shiga buɗe narkakkun gajiyayyun idanunsa, wanda sukai masa nauyi, kafin a hankali ya yunƙura ya miƙe tsaye baki ɗaya,
Sweet dake gefe na ganin hakan ta fara tsalle tana kaɗa jela, a sanyaye fuska a narke ya kalli sweet suna haɗa idanu ya kwaɓe mata fuska, irin I'm tired ɗin nan, a hankali ya sunkuya zai ɗauki sweet domin suci gaba da tafiya domin Allah yana kallo ya mance da batun Julde, baya Sweet tayi tare da juyawa ta kalli Inda Julde ke yashe, slowly ya juya idanunsa zuwa ga direction ɗin da Sweet take kallo.

Idanunsa ne suka sauka akan Julde wacce take kwace, farar fuskarta ya tsorawa idanu ganin yadda ta ƙara wani mugun haske, tai fari fatt da ita,
Langwaɓar da kansa gefe guda yayi yana ya mutsa fuska tare da marai-raice wa baki ɗaya kafin ya juya ya kalli sweet yace.

"Kin gani ko? I can't Sweet ni bazan iya ba gaskiya aita wahalar da mutum, ko uban me take a kwance kuma ohhhhoo??"

Ya ƙare maganar yana ƙara mirgina kansa gefe guda, tare da ƙoƙarin juyawa, cak kuma ya tsaya, saboda kansa da yaji ya sara take kuma ya fara tuna abinda ya faru, cikin sauri ya juya kanta tare da cilla idanunsa akan Julde wacce take fidda numfashin wahala,
"Yasubuhanallah!"
Shine abinda ya zo bakinsa, Shikenan ta harbu yaya zai yi kenan? Anya bazai barta a nan ba, tunda daman neman kai yake da ita?
Wata zuciyar kuma tace.

"A'a Jalaluldeen, wannan dukkan haƙƙin ta yana wuyanka, kula da lafiyarta, cinta, shanta, sutturar ta, Wheel ba ita tace tana sonka ba,
Sanda za'ai auran itama bata sani ba a yanzu dukkan abinda ya sameta you're the reason behind, dan haka ya zama dole ka kula da ita, domin ita É—in KYAUTAR ALLAH ce, KYAUTA CE DAGA ALLAH kare ranta kuma na nufin kare rayuka da dama wanda suke gab da salwanta"

Zuciyar ta ƙare maganar tana harba masa, tare da ƙara bashi umarnin zuwa ya taimake ta.

Kwaɓe fuska yay yana jan tsaki kafin ya kalli sweet yace.
"Sweet naje? I'm scared kada ta cijan na zama maye"
Karkaɗa jela sweet tayi, kafin tayi gaba zuwa wajan Julde taɓe baki Abu Maleek yayi yace.
"Uhm! Allah za muyi faÉ—a sweet, i don't know why kike son Fulani girl É—in nan"
Ya ƙare maganar yana riƙe ququnsa da dukkan hannayensa, kafin kuma walking slowly ya marawa sweet ɗin baya, yana zuwa ya durƙosa dai-dai kanta ya kallo ƙyakkyawar fuskarta mai kyau wacce ta kasance zagayayyiya (Oval shape).

Wani irin fisgar numfashi Julde taja lokacin taji ƙamshin mutum kusa da ita, a hankali kuma Jikinta ya fara rawa ta shiga ƙoƙarin tashi zaune tana buɗe baki,
Zare ido A.m yayi a ransa yake faÉ—in "Mayya!!" Zanyi maganinki yasin,ji yadda take buÉ—e mitsitsin baki ko small yatsana bai shiga"
Ya ƙare maganar yana sanya duguwar yatsarsa ya dungure mata kai.

Julde bata san mene yake ba, burinta kawai ta samu abinda hancinta yake jiyo masa ƙamshin sa,gane abinda take so ne yasa ya ɗan saki Murmushi ƙiri-ƙiri an mayar da ita mayyar ƙarfi da yaji.

Idanunsa ya juya kaɗan cikin Sa'a idanunsa ya sauka akan wani yadi, kafin yayi magana sweet ta ɗauko yadin da bakinta ta kawo masa, kanta ya shafa cikin ƙaunar magen tasa yace.
"Love You!"
Zama yayi sosai yana mai ya tsuna fuska shi gaba É—aya tsantsamin Julde yake,
bisa dole ya tattausan hannunsa ya É—an jawota gefensa tare da É—ura kanta a cinya,
idanunsa kuma ya mayar wajan ciwon ganin yadda yake zubar da jini,
wani irin zabura Julde tayi tayo kan Abu Maleek duk da bata gani,
unexpected abun ya zuwa A.m hakan yasa yayi baya tare da faÉ—uwa Julde kuma tabi jikinsa ta kwanta tana buÉ—e baki tare da neman inda zata ciza,
ganin hakan yasa Abu Maleek neman yadda zai ƙwaci kansa dan muddin ya bari ta cijesa ya gama aiki,
hannunsa ya buɗe baki kasancewar mai faffaɗan ƙirji yasa gaba ɗaya ta rufta cikin ƙirjin nata,
da sauri kuma ya sanya hannayensa yayi mata rumfa dasu,
Kokawa suka fara inda take ƙoƙarin ganin ta kama hannunsa yayinda yake sun ganin ya riƙe fuskarta baki ɗaya, shi Abin dry ya basa,
Ganin kuma tana ɓata masa Lokaci ne yasa ya ɗan haɗe fuska sosai tare dasa hannunsa a saman karan hancinta ya ja,
Wata ƙara ta saki saboda zafin da taji sai kuma ta kwaɓe fuska ba tare kuma da tace komai ba kamar wacce aka bawa umarnin tayi ƙasa da kanta zuwa ƙirjinsa, tare da sauke ajjiyar zuciya,
Tana mai ƙara mannewa a jikin nasa ba tare kuma data kai masa cizon ba.
Lumshe idanunsa yayi sosai yana jin yadda take saukar masa da gajiya, kafin kuma
Ya É—auki yadin ya shiga naÉ—e mata baki dashi, yana gamawa ya sauke numfashi tare faÉ—in.
"Ya Allahu Ya Rahamu"
Kana ya miƙe tsaye da ita a jikinsa tare da ɗan taɓe baki yana faɗin.

"Kawai aita wahalar dani, yarinya wallahi sai na rama, ƙwaffff"
Ya faɗa yana jan ƙwafa, kana ya cilla ta bayansa ya ɗauki sweet a hannunsa,
Ko takan nono da ruwan bai bi ba, ya kama hanya tare da suma tafiya, yayinda kuma Julde tai lubb a bayansa tana sauke ajjiyar zuciya da ƙarfi.

Yau ta kasance ranar juma'a, ranar da dukkan wanda yake Kanzaf bazai taɓa mancewa da ita ba, ranar data shiga tarin daga cikin ranakun tarihi, ranar da mutanan Kanzaf da mutanan da suke cikin Alaafi suka shiga cikin tashin hankali, tashin hankali mara fasaltuwa, ranar da Kanzaf ta zama kamar wani sansani na maƙabarta saboda Shiru da garin yayi baka jin motsin komai, Hatta tsuntsayen da suke shawagi kullum daga Cikin bishiyoyin Alaafin zuwa bishiyoyin Kanzaf yau babu su,
Sai wata dadɗar iska mai daɗi da kuma ratsa zuciya dake tashi, cikin ƙaramin lokaci kuma garin yayi duhu saboda tasuwar hadari daya haɗa da wata gagarumar iska mai ƙarfi.

Oumuu-Ayman ce tafe ita da Salimerh sun sanya Mai Babban ɗaki a tsakiya wacce Idanunta yayi jajurr, ga wani irin rawa da Jikinta yake, a haka suka nufi sashin King Tunde suna zuwa suka samu Queen Ayoola a kusa dashi riƙe da hannunsa sai kuka take, gefe guda kuma Otun da Agba Akin ne zaune suna masara addu'a tare dayi masa fifirta,
Daga can gefe guda sautin kukan Bola ne tashi a hankali, Zama Mai Babban É—aki tayi tare da kallon É—an nata, a hankali ta sanya dai-dai kunansa ta shiga karanta masa addu'a, ta nayi tana kalmar shadda,
Jin yadda Mai Babban É—aki take nanata Kalmar Shahada ne ya sanya Salimerh gigice wa, tare da sanya kuka tana faÉ—in.
"Innalillahi wa'inna ilaihir Arjun, Dad!! Dad!!"
Ganin yadda Salimerh ta gigice take neman ruɗa MALEEK dake kusa da King Tunde Muhammad Jalal daya riƙe hannunsa sosai yana jin tamkar Zakinsa ne kusa dashi,
Ya sanya Oumuu-Ayman ta riƙe Salimerh tare da rungome ta sosai, tana faɗin.
"Just pray for him, ita yake buƙata Salimerh"
Kuka Salimerh tasa tana rungome Oumuu-Ayman tare da faÉ—in.
"Oumuu!! Oumuu Dad!! I'm going to lose my Dad Oumuu, Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"
Sosai Oumuu-Ayman ta rungome Salimerh a jikinta, ganin tana neman ficewa daga cikin hayyacinta.
"In sha Allah, noting will happen to him sai abinda Ubangiji ya tsara Salimerh, just pray kiyi masa addu'a"
Ta ƙare maganar tana juyar da idanunta saboda hawayen daya cika mata idanu,
Da sauri Salimerh ta miƙe tana faɗin "Oumuu Zaki?? Shakiru, Sharefddeen, babu kowa Oumuu yaya za mu yi?"
Sai kuma ta juya da sauri ko ganin gabanta ba tayi yana fita, taci karo da Junaid tana ganin ta nufi inda yake, runtse idanunsa yayi saboda wani mugun mugun! Tausayinta da yaji, tana zuwa ta faɗa jikinsa tare da riƙesa sosai tana faɗin.
"Junaid, My Dad! Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un zan rasa farin ciki na Junaid yaya zanyi? Yaya Zaki zaiji idan ya dawo ya samu babu Dad? Wayyoooo Allah, Ubangiji ya dube mu, ka kawo mana sauƙi akan abinda yake shirin samu mun ba, Ubangiji ka dubi idanun mu ka tausaya mana ka barmu da mahaifin mu, shine jin daɗin mu, shine farin cikin mu, shine garkuwan mutanan Kanzaf, La'ilahaillahu Muhammadur Rasulullah S.A.W"
Ta ƙare maganar tana sakin kuka sosai, tare da riƙe Junaid, idanun Junaid yayi jaa sosai, a hankali ya sa hannunsa ya rungome ta a jikinsa yana so da ƙaunar ta na ƙara nunkuwa a zucyarsa, ga kuma wani tausayinta daya gama mamaye zucyarsa, a hankali ya shiga bubbuga bayanta tare da faɗin.
"It's okay My princess, In sha Allah Dad zai miƙe zaici gaba da zama damu, Kiyi masa addu'a please wifyna"
Ya ƙare maganar yana ɗan bubbuga bayanta, kafin ya janye ta daga Jikinsa, yana kama hannunta tsayawa tayi tana girgiza masa kai alamar ba zata shiga ciki ba.

Girgiza kai kawai yayi kana ya shiga ciki, yana barin wajan Salimerh ta nufi Part É—in ta, tana zuwa ta samu wayarta na ringing da sauri tai answering daga cikin wayar akace.
"We are on our way Ranki ya daÉ—e?"
Wasu zafafan hawaye ne suka sakkowa Salimerh kafin tace.
"Ina Zaki na?"
Daga cikin wayar akace "we're all together Maaahh!"
Jinjina kai tayi cikin tsananin farin ciki da kuma jin daÉ—in Dawowar JULALUDEEN TUNDE MUHAMMAD JALAL, kafin tace.
"Ka shigo ta ƙofar baya"
Daga cikin wayar aka amsa mata da "In sha Allah" kashe wayar tayi a sanyaye kuma tace "Allahamdulillah"

Oumuu-Ayman ce tsaye da Salimerh suna nan tsaye kuma suka hango motar na shigowa ta can ƙofar baya, wata Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Oumuu-Ayman ta sauke, yayinda wata nutsuwa ta sauka a zcyarta, tun bayan tafiyarsa bata da wata nutsuwa kullum cikin damuwa take,
A hankali motar take tafiya harta iso inda suke Oumuu-Ayman suke, a hankali kuma Oumuu-Ayman ta nufi back seat tare da sanya hannunta ta buɗe motar, Idanunsa dake lumshe ya ware a hankali tare da sauke su akan Oumuu, tashin hankali daya a cikin ƙwayar idanun ta ya sanya ya tsorawa mata narkakkun idanunsa,
Zame idanun ta tayi daga cikin idanunsa saboda kallon da taga yana bata, a hankali kuma idanun ta ya sauka akan Julde wacce take kwance bakinta a É—aure tana bacci juyawa tayi ta kalli Salimerh tace.
"Shiga ciki ina zuwa"
Tayi hakan ne kuma saboda bata son Kowa yaga Julde, hannunta ta miƙa wa Jalaluddeen alamar ya kama,
Ƙara ware idanunsa yayi a kanta kamar bazai magana ba dai kuma yace.
"Dad????"
Ya tambaya kai tsaye domin shine kawai ya faÉ—u masa, musamman yadda yaji ko'ina shiru hakan yasa jikinsa yayi sanyi,
Girgiza Kai tayi tace "Yana ciki, Zaki baƙuwa mukai?" ta ƙare maganar tana ƙara kallon Julde wacce taji nan take so da ƙaunar ta ya shiga zuciyarta, taɓe baki yayi tare fitowa daga cikin motar, yana fitowa daga motar sweet ta diro ita ba, ta shiga tsallan murna, har yayi gaba sai kuma ya tsaya tare dayin baya,
Cikin motar ya koma ya jawo Julde fuskarsa a É—aure kuma ya É—auki Julde a hannayensa kamar Jajiriya,
Kallonsa kawai Oumuu tayi tasan Abu Maleek bazai taɓa aikata abinda ba shike nan ba, hakan yasa bata zarginsa ko kaɗan,
Bayansa tafi kai tsaye kuma ya nufi wajan prvt bedroom yana zuwa ya cilla Julde ciki wacce tayi ɗan ƙara sai kuma taci gaba da bacci abinta,
Oumuu-Ayman dake bayansa sanin halinsa yasa tai masa shiru, tsayawa yayi tare da sanyawa Ƙofar passward, kana fuskarsa babu walwala ya kalli Oumuu-Ayman yace.
"Where's my Dad?? Ina Daddyna Oumuu??"
Idanunta ya kawo ruwa ganin haka yasa a gigice Abu Maleek yayi waje ta cikin ƙofar cikin family side ɗin ɗasu, kai tsaye kuma ya nufi Sashin King Tunde Muhammad Jalal, babu wanda bai mamakin dawowar Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal a wannan lokacin ba, yana zuwa ya amshi King Tunde Muhammad Jalal a hannun Mai Babban ɗaki tare da rungomesa, jikinsa na rawa tace.
"Dad! Dad!! Dad!!! Open your eyes please Daddy!!!!!!"
Ya faɗa yana Rungome Mahaifin nasa, wata ƙaƙƙarfar ajjiyar zuciya King Tunde ya sauke lokacin da yaji ɗumin jikin Zakin nasa, tare dajin sautin Muryar sa, bisa mamaki a kaga King Tunde na motsawa tare buɗe idanunsa ya riƙe hannun, Jalaluldeen ganin yadda bakinsa ke rawa yasa Abu Maleek sunkuyawa, ya ɗauka wata magana zai faɗa sai yaji yace.
"Allah yayi maka albarka, Allah yayi riƙo da hannayenka, Jalaluldeen ga Khaleluddeen nan, ga Zubaida nan, Oumuu-Ayman zata faɗa maka komai, zan tafi ciki farin ciki da kuma salama a Zuciyata, Zakina ka kula da kanka dan Allah ka sani ka girma ka daina wannan shagwaɓar, ka zauna cikin Kanzaf ka maye gurbina a Cikin Alaafi, kada ka yarda da kowa face Oumuu-Ayman, Mai Babban ɗaki Sai Zubaida, ko ƴan uwanka maza kada ka amince masu, akwai wani haske da zaizu a duk sanda ka kusance sa, za kaji faɗuwar gaba kada kaji tsoro wannan shi ne mahaɗin Wanda zai zame maka ɗan uwa wajan gudanar da Mulkin Kanzaf, Allah yayi maka albarka Zakina, Ka faɗawa Maminka ta na tafi cike da so da kuma kewarta a cikin zuciyata, kada ka Amincewa kowa Jalaluldeen kada ka yarda da kow......"
Wani irin tsayawa numfashin sa yayi wanda ya tilasta masa tsayawa da maganarsa, duk abinda yake faÉ—a babu wanda ya keji sai Abu Maleek, wani Daimond ring King Tunde Muhammad Jalal ya bawa Abu Maleek kafin yace.
"Duk yarinyar daka sanyawa wannan ring ɗin yayi mata dai-dai to itace farin cikin ka, itace mahaɗin rayuwarka kada ka sake ka wulaƙanta ta"
Tsayawa yay da maganar da ƙarfi kuma yace "La'ilahaillahu Muhammadur Rasulullah S.A.W"
Cak Numfashinsa ya tsaya, haka ma bugun zcyarsa ya tsaya da aiki, yayinda jikinsa gaba É—aya ya saki a jikin Abu Maleek, Salati Gaba É—aya suka sanya, Kafin wasu daga ciki suka sanya kuka,
Shikenan lokaci yayi tashin hankali sun gashi, gaba É—aya Alaafi ta hargitse banda ihu da yarda zani babu abinda mutane suke, Garin Benin ya É—auki sautin tamburan gidan sarautar wanda yake shaidawa mutane Tabbas Sarki kuma Mai Martaba, King Tunde Muhammad Jalal ya rasu!
Nan da nan aka shiga sanarwar gidan t.v da kuma Redio kafin Yamma tuni Garin Benin ya ɗauki tururuwar jama'a, Sarkin Kano, sarkin Katsina, manyan sarakuna shugaban ƙasa, da gwamnoni suka dira A Benin.
Yayinda kusan a tare jirgin Adams dana Shakiru, Sharefddeen sukai saukar ungulo,
Jalaluldeen kam yanayin daya shiga ba'a magana gaba ɗaya ya gigice bai taɓa ganin mutuwa haka ba, yau gashi mahaifin nasa ne ya rasu a saman cinyoyinsa, banda sakin ajjiyar zuciya babu abinda yake.
Sai washe gari da safe akai jana'izar King Tunde Muhammad Jalal jana'izar data tara mayan mutane ƙososhin ƙasa, da manyan malamai.

Abu Maleek na kwance a saman Royal bed ɗin sa sai Ajjiyar zuciya yake saukewa, tun jiya daya sanya mahaifinsa a gidansa na ƙarshe ya dawo part ɗinsa bai ƙara fitowa ba, ko ruwa bai sanyawa cikinsa, yana tunani abubuwa da yawa Mahaifinsa ya tafi ya bar shi da nauyi masu yawa nauyin da baya jin zai iya saukewa, baya jin zai iya zama Sarkin Benin ba zai iya da wannan tashin hankalin ba sam.
Juyawa yayi gaba É—aya baya jin daÉ—i duniyar, sosai yake neman mai rashinsa, da sauri kuma ya buÉ—e idanunsa saboda da tunawa da Julde yayi.
"You see ba?? Abinda nake gudu kenan yanzu idan ta mutu sai a É—ura laifin a kai na"
Ya ƙare maganar kallon sweet kafin ya miƙe tsaye kai tsaye kuma prvt bedroom ɗin daya sanyata ciki ya nufa, passward ɗin jikin ƙofar ya saka, kafin a hankali ya shiga yana rufe ƙofar, yana shiga ya fara jin ƙarar buge bugen da take a hankali ya buɗe sanyayyun gajiyayyun idanunsa kafin ya sauke a kanta, tana kwance saman lallausan carpet sai bige bige take saboda azabar data keji ga kuma maitar daya tasu mata.
Lumshe idanunsa yayi yace.
"Ya Allah!"
Ya faɗa yana sauke wata wahalalliyar ajjiyar zuciya ganin zata jima kanta ciwo ne ya sanya ya nufi inda take tare da durƙosa wa dai-dai inda take ya sanya tattausan hannunsa ya ɗaga ta cak ya dire saman bed ɗin, kafin ya zauna a gefen ta, cikin rashin Sa'a kuma ɗaurin dake bakinta ya zame,
Da wani irin sauri ta hantsila saman cinyar Abu Maleek kai tsaye kuma bakinta ya sauka a saman ƙirjin ta, da sauri ta buɗe bakinta zata sakar masa cizo wata tsawa Abu Maleek ya sakar mata wacce ta amsa duk sashin nasa, ba ita ba hatta shima sai daya tsorata da tsawar daya fito daga cikin bakinsa, wata zabura Julde tayi sosai tsawarta gigita mata lissafi, hakan ya sanya gaba ɗaya tayi baya zata faɗa ƙasa cikin zafin nama irin na ɗan Ball yasa ƙafa ya tarota tare cilli da ita zuwa baya kai tsaye ta dawo jikinsa, wani gigitaccen ihu Julde ta sanya ihun daya sanya cikin sauri Abu Maleek ya haɗe hannayensa tare da run.....

ABU MALEEK IS NOT FREE CONTACT TO SUBSCRIBE 08119237616

*_37-38_*
Rungome nata hannayen, ya zamana ya sanyata a tsakiyar jikinsa ba tare daya rungome ta ko kuma ya riƙe Jikinta ba.

Sassanyar Ajjiyar zuciya ya sauke, yana wani irin masifafan harbawa da zucyarsa yake masa,
Tsananin bugun da take masa ne yasa har yake É—an sauke ajjiyar zuciya da sauri da sauri.

A hankali yasa tongue ɗinsa tare datse laɓɓanta ya shiga taunawa, tare da gana masu azaba, a hankali ya fesar da wani zazzafan huci daga cikin bakinsa zuwa saman fuskarta wacce take dab da nasa fuskarsa, kasantuwar kusanci da suka samu da juna.

Narkakkun gajiyayyun idanunsa da suke a lumshe ya É—an buÉ—e yana mai ya motsa fuska saboda kansa daya sara masa,
Ga bugawar zuciyarsa data ƙaro fiye da baya, ba tare kuma daya san dalilin hakan ba.

Idanunsa ya sauke a saman fuskarta wacce take ɗauke da ruwan hawaye har lokacin kuma shassheƙar kuka take,
Tsawar da yayi mata ne kuma ya sanya ta firgita, wanda ya haddasa mata tsoransa Sosai.

Sosai take jin azaba a jikin a zaba a Jikinta, amma bata da ikon faɗa ko kuma samun abinda ta keso, ta san tayi kaɗan ya bata abinda take so ɗin a yanzu dole ne taja bakin tai Shiru tare da maida ƙwala marta.

A hankali ya shiga zareta daga jikinsa, jin hakan ne kuma yasa gaba ɗaya ta kwaɓe fuska ta fara buɗe baki zata sakar masa kuka.

Fuska ya É—an ya motse alamar gajiyawa, tare da É—ura yatsarsa guda a baki yace.

"Shittt!!"
Luff tayi a saman bed É—in yayinda ta buÉ—e bakinta ta shiga taunar lallausan bedsheet É—in dake saman bed É—in

Abu Maleek a hankali ya ƙara sauke ajjiyar zuciya cikin nutsuwa kuma ya fara taka ƙafafuwan sa a saman lallausan carpet ɗin dake kwance a tsakar bedroom ɗin.

Cikin takunsa na ƙasaita da kuma zallar izza ya nufi waje hannunsa duk biyun zube cikin aljihun wandonsa na long white jeans wanda ya ɗan tattare da can bakin wandon wajan sanya ƙafa.

A hankali kuma ya sanya hannunsa tare da ɗura shi saman handle ɗin ƙofar yaja a hankali yadda sautinsa bazai dame sa ba, shi kansa yanzu duk a razane yake, baya son wata ƙara ko ihu a saman kansa,
Walking slowly ya nufi ɗan ƙaramin part dake cikin side ɗin nasa, a hankali ya sanya kansa ciki, wani ƙawataccen Pharmacy ne wanda babu abinda babu a cikinsa, har wani ɗan ƙaramin gado na marasa lafiya.

Kayan da zai buƙata ya ɗauka kana ya fito daga cikin Pharmacy ɗin ya koma can side ɗin da take ciki.

A hankali ya tura ƙofar yana jin bugawar zuciyarsa na tsananta kamar zata tsaga ƙirjinsa ta fito haka ya kejin zuciyarsa, sam baya jin daɗin duniyar nan a dai-dai irin wannan lokaci, komai yayi masa zafi, da ace za'a amince kuma a lamunsa masa Tabbas da ana yin 40days na rasuwar Mahaifin su zaibi jirgi ya koma inda ya fito.

Tura ƙofar yayi a hankali kana ya zura kansa, tana jin motsin shigowar sa ta ɗan zabura, tare da cure Jikinta waje guda, cikin nutsuwa kuma ta sanya yatsarta a baki ta fara tsotsa tamkar ta samu lolipop.

Jingina bayansa yayi da jikin door É—in a hankali ya ware Manya kuma gajiyayyun Maraitattun idanunsa,
Wanda suka É—an janye kaÉ—an, saboda tension É—in da yake ciki ga kuma rashin bacci,
Uwa uba wata azababbiyar yunwa dake zaƙulan cikinsa, baya jin kuma zai iya kai wani abun bakinsa.

A hankali ya sauke wani sound tare da janye idanunsa daga kallon saman bedroom É—in da yake ya rufe su ruff,
Tamkar wanda yake Shirin yin Bacci sosai ya kejin wani irin acikin jikinsa yanayi mai wahalar fassaruwa,
Yanayin da bakinsa yayi kaÉ—an wajan furta sa.

Ji yake wani nauyi na musamman wanda baya jin zai iya sauke sa ya hau kansa, sosai yake jin kansa Tamkar wanda aka sanya igiya aka É—aure masa jikinsa,
Ga wani nauyi da kansa yay masa, nauyin kuma daya sauka a ƙasan jikinsa.

A hankali take tsotsar yatsarta wanda sautin tsotsar Derect yake tafiya cikin kunan Abu Maleek, al'amarin daya sanya tsigar jikinsa tashi kenan ta wani mimmiƙe,
A hankali kuma wani sihirtaccen sanyi ya fara kawowa fatar jikinsa farmaki kasantuwar buÉ—ewar kofufin jikinsa.

A sanyaye cikin gajiyawa kuma ya ƙara buɗe luntsumammun idanunsa wanda suka ƙara janyewa, kai tsaye kuma ba tare da wani shamaki ba ya sauke idanunsa a kanta.

Tana kwance luff saman bed É—in dai tsotsar yatsarta take tana sakin Ajjiyar zuciya, ga yadda Jikinta yake É—an rawa,
Alamar wahalar da take sha ya tsananta, a ko wanne lokaci tana iya samun kanta cikin wani hali nada ban.

A karo na barkatai ya ƙara sauke ajjiyar zuciya tare da jan numfashi mai wahala, Cikin nutsuwa haɗi da kamewa ya fara taka Fararan sahunsa a saman lallausan carpet ɗin dake malale saman tayals ɗin bedroom ɗin.

A haka yana tafe yana sauke ajjiyar zuciya akai akai ya ƙarasa inda take kwance,
Wata ƙaƙƙarfar ajjiyar zuciya Julde ta sanya tana mai ƙara kulle idanunta, yayinda zuciyarta take wani irin harbawa tare dayin wani tsalle tsalle kamar zata faso tsakiyar ƙirjinta ta fito,
Tsoransa ya bayyana ƙarara a saman fuskarta yayinda kuma a hankali take jin sanyi da kuma tarin nutsuwa na saukar mata a can ƙasan zuciyarta.

Abu Maleek shiru yayi a hankali yake yatsar da take tsotsa da idanu, ganin yadda yayi jaa, ya tattare waje guda, ga wani É—an janyewa da yayi, Amma a hakan ta dake sai tsotsa take ko mene ta keji a jikinsa ohhhu!!????
Ya tambaya a cikin ransa yana mai ɗan taɓe bakinsa.

Jin shiru kamar babu kowa cikin bedroom ɗin ne ya sanya Julde, kwaɓe fuska idanunta ya cika taff da hawaye, hawayen da suke nuna zallar buƙatar abinda take so ɗin,
Tayi ƙarya ta kwana da yunwa idan tace dai a yanzu abinda zuciya da kuma gangar Jikinta take buƙata zata samu,
Numfashi mai zafi taja saboda zazzafan zazzaɓi dake ƙoƙarin mamaye ilahirin gangar Jikinta, domin har wani ƙara taji ƙashi da ɓargwan Jikinta nayi,
A zabar datai mata yawa ne ya sanya a hankali hawayen dake cikin idanunta silaluwa zuwan gefen fuskarta, kafin a hankali ta shiga motsa bakinta dake rawa yana ɓari kamar laɓɓanta zasu fita, cikin tear out taja wahalallan numfashi tace.

"Ballowo!!!!!!!!!"
Ta faɗi sunan a sanyaye tana mai jan harafin O!!!! Ɗin saboda raunin da zuciyarta yayi, so take tace ya riƙeta a jikinsa ko ta samu sauƙi na azabar da take sha, amma ta kasan saboda tsoran abinda zai faɗa mata, ita gaba ɗaya Matsayin Madibbo ɗinta take jinsa, kawo Yanzu ma bata san cewa ita ɗin mata ce a garesa ba, to mutumin ba bata taɓa ganin ba, ko da ace ta kansa ba zata taɓa sanyawa ranta cewa zai so ta ba, bare harya aureta ya zauna da ita matsayin mata wacce take ƙarƙashin kulawar sa, it's difficult!!!.

Abu Maleek dake zaune kamar statue yana kallon yadda hawaye ke tsiyaya daga cikin idanunsa yaja numfashi ta ɗan ƙarfi tare da haɗiye wani Salivas ɗin cikin bakinsa, daga cikin zuciyarsa wani sound ne ke tashi dib dibb dibbb dibbbb!!!! Saboda kukanta har tsakiyan kansa ya kejinsa, ganin bata niyyar kuka ne yasa a hankali ya furzar da iska daga cikin bakinsa kafin cikin husky voice ɗin nan nashi mai sanyaya zuciyar mace ya ɗura yatsarsa a baki yace.

"Heyyyyyyhh!! Fulani girl be quite!!"
Ya faÉ—a ba taushashe cikin dakakkiyar muryarsa wacce take nuna cewa Tabbas ya dawo Abu Maleek É—insa ba wanda ta sani na cikin jeji ba,
Juyawa yayi gaba ɗaya da raguwar ƙarfin daya rage masa, ya ware wani ƙaramin drip daya ɗauko tare da saƙale sa a jikin wani ƙarfe,
ganin yadda take a kwancan ne yasa hannunsa guda biyun ya riƙe kafaɗun ta ya jata zuwa can sama,
Kana ya zauna a gefe shi kansa yasan cewa tana shan azaba haka kuma akwai abinda take buƙata,
yadai shareta ne saboda haushin auran da aka liƙa masa yake, he's not interested at all!.

Wrist É—inta ya kama tare da zuba masa,
da sauri ya É—auki wata siririyar igiya fara,
ya É—aure wrist É—in da kyau, nan take jijiyoyin hannunta suka firfito, Wata allura ya É—auka tare da fara gogawa a inda yake tunanin itace jijiyar ruwa.

Tsinin allura data jini ya sanya ta kwaɓe fuska tana ƙara narke masa, cikin siririyar muryarta mai Amo!!! Da amsa kowa a cikin kunan nan Abu Maleek tace.

"Mene zakai min Ballowo???"
Ta ƙare maganar hawaye na sauka idanunta duk da cewa bata gani
Amma ta Fahimci abinda yake shirin yi mata,
banza yay mata sai ma saurin nutsa allurar da yayi wacce ta lume cikin Jikinta, wani irin raunataccen kuka Julde ta sanya,
tare da sanya bakinta a dai-dai saitin lap É—insa ta sakar masa cizo!
Da sauri ya runtse idanunsa tana taune leɓansa tare da faɗin.

"Auchhhiii hyyyyyyyh!!"
Ya faɗa yana tsotsar laɓɓansa,
nan take gumi ya shiga tsastsafo wa daga saman goshinsa,
a hankali ya buɗe idanunsa tare da saukewa a saman fuskarta ƙuri tai masa da idanu a tunaninta wajan data ke kalla daban yake,
nan kowa Kallonta babu inda ya tsaya sai tsakiyar idanun Abu Maleek.

Ɗauke idanunsa yayi tare da taɓe idanunsa a cikin ransa yace..

"Munafuka, ji idanu kamar idanun babyn rubber!!"
Ya ƙare maganar zucin yana juya idanunsa kafin ya gama ɗaura mata drip ɗin,
Wata duguwar siririyar farar robber ya ɗauka, wacce Jikinta yake ɗauke da allura, can ƙasa kuma wani baki ne, a hankali yaja jikinsa kusa da ita tare ɗaga kanta wanda ya fara duhun tsastsafuwar gashi, ya ɗura saman pillow kafin kuma ya tsorawa ɗan mililin bakin nata idanu, ya tsuna fuska yayi domin duk ya gaji banda ceton rai da gudun faɗawar jahannama mene yayi masa zafi da wannan yarinyar, tattausan hannunsa yakai zuwa bakinta Ajjiyar zuciya ta sauke tana mai ɗan ƙara lafewa saman lallausan bedsheet ɗin dake saman bed ɗin, yatsarsa guda biyu ya sanya ɗaya a ƙasa ɗaya a sama ya buɗe bakinta, kana cikin sauri ya tura mata robber cikin bakinta, kakarin Amai ta fara hakan yasa bada tunanin komai ba ya mai da hannunsa ɗaya saman ƙirjinta ya shiga dannawa yana ƙara tura robbern cikin bakinta, yayinda idanunsa suke manne cikin wata na'ura har sai da robber ta shiga cikinta, kana ya tsaya.

A lokacin kam tuni Julde idanunta yana É—an yooo waje saboda azaba, sai ruwan hawaye dake zuwa daga cikin idanunta.

Abu Maleek allurar ya ɗauka a hankali ya fara saitawa da jijiyar hannunsa kana ya zura can ciki nan take jini ya fara fita daga jikinsa zuwa cikin Julde, domin sosai wannan mutumin ya shanye mata jinin Jikinta, kuma duk wannan fisge fisgen da take yasan cewa abinda take buƙata kenan wanda ko ita kanta bata san menene shi ba.

Wata ƙaƙƙarfar ajjiyar zuciya Julde ta shiga saukewa, yayinda tayi tsitt sai motsi take ta yatsun hannunta, wani daɗi da farin ciki ya lulluɓe mata zuciya, cikin Lokaci kaɗan kuma idanunta ya fara Lumshe wa saboda baccin daya kawowa idanunta ziyara!

Sauke numfashi Abu Maleek yayi yana mai jingina jikinsa da frame É—in gadon, Shiru yay yana sauraran sautin bugawar zuciyarsa ga kuma jinin jikinsa dake fita da gudu yana shiga Jikinta.

Almost 30minutes
Yana zaune idanunsa a lumshe tunani ne fal ransa a yanzu kuma tunanin ball ɗinsa ce ta faɗu masa, idanunsa ya buɗe a hankali tare da kai dubansa zuwa gare ta, tuni bacci ya ɗauke ta sai Ajjiyar zuciya take saukewa, hannunsa ya sanya ya zare allurar daga jikin hannunsa, yabar iya carnonar, kana ya miƙe tsaye.

Da sauri ya dafe bango saboda wani jiri daya É—ebe sa tamkar zai yarda shi, dai-dai-ta gudun drip É—in yayi kafin cikin nutsuwa da haibarsa haÉ—i da zallar izzar sa ya fara tafiya.

Ya fita ya maida ƙofar ya rufe tare da ƙara sanya mata passward, kai tsaye shashinsa ya koma idanunsa ya sauka akan sweet, wani sassanyar murmushi ya sauke yana shafa ƙwantaccen gashin ƙirjinsa, ciki lafiyayyiyar muryarsa mai daɗi.

"Wake up sweet!!"
Ya faɗa yana jan ƙafafuwanta, ƙara curewa waje guda tayi bisa dole ya barta domin ya fahimci itama ta gaji sosai, cije lips ɗinsa kawai yayi kana ya huce bathroom ɗinsa.

Wanka yayi sosai domin har lokacin jikinsa bai masa daɗi, duk wannan baƙin fenti sai daya fita, kafin yaji daɗi Fatar jikinsa har wani jaaa take, brush yayi sosai kana ya ɗauki handrayer ya gyara kansa...
Nan da nan ya fara wani sheƙi da ƙyalli kafin ya ɗauki wani siririn ribbon ya ɗaure gashin dashi, jelar ta ɗan sauka a bayan wasu kuma suka kwanta gaban goshinsa.

Fitowa yay daga cikin bathroom ɗin ya nufi gaban dressing mirror a sanyaye ya fara shirya kansa nan da nan ƙamshi turarensa ta cika cikin bedroom ɗin nasa.

Wasu Olivia von Halle silk robe ya sanya dark masu taushi da laushi, yana gamawa ya sanya wani Vally Slippers na maza masu gashi gashi, jikinsa na fidda wani dadɗan ƙamshi ya nufi parlonsa,
Yana zuwa Oumuu-Ayman na shigowa hannunta riƙe da tray, fuskarta ɗauke da Murmushi ganin Abu Maleek ya sauya ya ɗan kimtsa kansa,
Zama tayi gefensa tana faÉ—in.

"Zakina!!!"
Kwaɓe fuska yay yana langwaɓar da kansa gefe guda tare da narke mata cikin shagwaɓaɓɓiyar Murya yace.

"Oumuu na!!"
Ya ƙare maganar yana mannewa jikin lallausan kujerar da yake kai, yana ɗan sauke numfashin gajiya da kuma yunwar dake damunsa,
Kallonsa Oumuu-Ayman tayi kafin tace.

"Kayi breakfast?"
Ƙara narkewa yayi a jikin kujerar yana ɗan lumshe idanunsa tare da sauke nauyayyiyar ajjiyar zuciya kafin yace.

"Ba'a bani baaa"
Kallonsa tayi cike da tausayinsa wato bazai taɓa cewa a bashi abinci ba, indai ba mutum ne yayi niyya ya basa da kansa ba,
Sandwich da Bacon Egg and chee Read ta shiga buɗe masa, sai lafiyayyan kunun gyaɗa wanda yaji gyaɗa sai ƙamshi yake, mug ta ɗauka ta zuba masa kunan Gyaɗar tare da miƙa masa tace.

"Shanye wannan yanzu"
Marai-raice mata yayi yana sauke wani fitinan nan numfashi fuska a narke yace.

"Oumuu kiban, jikina babu ƙauri fa"
Ya faÉ—a yana buÉ—e idanunsa da suke a Lumshe, girgiza kai kawai Oumuu tayi mai hali baya fasawa, Kunun gyaÉ—ar ta shiga bashi yana sha yayinda yake É—an jan numfashi tare da Lumshe idanunsa saboda garÉ—in gyaÉ—ar da yayi masa daÉ—i a baki sosai, kafin ya shanye gumi ya gama yanko masa.

Bakinsa ya janye yana faÉ—in "Allahamdulillah! Allahamdulillah biii Ni'imatikaaaa Ya Arhaman rahimin"
Ya ƙare addu'ar yana kallon Oumuu-Ayman wacce take faɗin.

"Da saura ai"
Narkewa yay kamar zai kuka yana shafa cikinsa yace
"Allah Oumuu I'm full kuma sai nai tusbi na kasa buga ball"

"Anzo wajan"
Oumuu ta faɗa a ranta dan bata tunanin zai ƙara buga wata ball ya barta kenan duk da cewa itace mafarkinsa amma dole zai barta.

Tissue ta bashi ya goge bakinsa kafin ta miƙo maza zuma da bakilawa dasu Alkaki, babu abinda yaci sai Inibi ɗaya daya cira ya sanya a bakinsa, sanyin inibin da kuma ɗanɗanonsa suka game bakin Abu Maleek.

Ganin kallon da Oumuu take masa yasa shi tura bakinsa gaba kafin yace.

"What again Oumuu!! Allah ni kibar kallo na ina tsarguwa and kinfi kowa sanin bana son kallo ko?"

Jinjina kai tayi Alamar fahimta kafin taja numfashi tace.
"Who is she??"
Juya idanunsa yayi kafin ya zame gaba ɗaya ya kwanta saman kujerar tare da sanya kansa saman ciyar Oumuu wacce yayi missed nata sosai, domin ita ta sabar masa da hakan tun yana Ƙarami.
Yana rufe idanunsa yace.
"Wa????"
Hannu Oumuu ta sanya taja kunnansa da sauri ya riƙe yana faɗin.
"Auchhhiii Oumuu bafiiii fa"
Murmushi tayi masa kafin tace.
"I knew!, I'm talking about yarinyar da kazo da ita Zaki, who is she???"

Taɓe bakinsa yayi yana tsotsar laɓɓansa kafin ya lumshe idanunsa yace.

"I don't even know her Oumuu believe kinji???"
Kallon Mamaki tayi masa kafin tace.
"Stop laying Zaki Allah last question Wacece ita And mene ya sanya bakinta yake rufe??"

Ƙara gyara kwanciyar sa yayi a cinyar Oumuu, yana jin bacci na ɗaukarsa kafin yace.

"Oumuu ban ƙara fa, Allah ban san wannan Fulanin girl ɗin ba, Ahhhaaa ina Rugar Mahinjo da aka faɗa to a nan take then...."
Ya kwashe labarin komai ya faɗawa Oumuu ya ƙare maganar yana faɗin "Jikina ciwo har yanzu why za'a min bulala akan wannan Yarinyar Allah I'll never ever loving her, kai ni sweet ta fimin ita bana sonta Oumuu to me nayi masu ma??? Bulala talatin fa, Uhmmm ai kam hamsin nayiwa ɗayan I'm telling you na girma ina da ƙarfi ai"

Murmushi Oumuu-Ayman tayi mamaki da ta'ajjuji ya hana tayi magana, yayinda zuciyarta take raya mata wasu abubuwa da yawan gaske, Ajjiyar zuciya ta sauke kafin tace "Allahamdulillah!!"
Sai kuma tace.
"I see ka girma tunda kayi faÉ—a akan mace, ina tafan kuma farkon nasarar Zakina Jalaluldeen ce"
Turo baki yayi gaba yana kwaɓe fuska kafin yaja numfashi mai ɗan ƙarfi murya can ƙasa yace.
"Allah Oumuu bana sonta sai da ta zama Hadi.....

Abu Maleek isn't free contact to subscribe 08119237616

*_39-40_*
"Hadimata" ya faɗa yana mai ƙara gyara kwanciyar sa, a saman cinyar Oumuu-Ayman, a hankali kuma ya sauke tagwayen ajjiyar zuciya yana zuciyarsa na ɗan yin sanyi Saboda raɓuwa da jikin Oumuu-Ayman da yayi.

Murmushi kawai Oumuu-Ayman tayi tana jin wani irin abu nayi mata yawo a cikin zuciyarta, wani abu wanda bata taɓa jin irinsa ba.
Tsananin farin ciki da jin daÉ—in da yayi mata yawa ne ya sanya ta É—ura hannunta saman sumar kan Abu Maleek tana faÉ—in.

"Zaki, tayaya matarka zata zama Hadimar ka? Ko baka mayar da ita Hadimar ka ba, daman ai haƙƙin ta ne ta kula da kai, duk mene kake so zaka samu, for now Daman ya kamata ace kana da iyali wacce zaka kasance da ita, wacce zaka gaya mata damuwarka, wacce idan ka raɓeta zaka samu farin ciki, rayuwarka a yanzu tana buƙatar mace Jalaluldeen, me mata sukai maka ne da har baka son a haɗaka dasu? Koda ace sunyi maka abu mai dace ka ɗauki hukuncin yake mu'amala da su ba, rayuwa tana da sauƙi Zaki Yadda ka ɗauke ta a haka nan zata zo maka, why are publishing yourself? Mace na sanya nutsuwa a zuciyar na miji, mace kuma tana taka rawar akan DAI-DAI-TO-WAR halayyar namiji, Allah I'm telling the truth ya kamata ka nutsu ka san mene kake, accept your wife I'm sure wata rana zakai mamaki"

Idanunsa a lumshe yake yayinda yake sauraran dukkan abinda take faÉ—a masa, mai kama da tatsuniya, she never understand his fellings, ballai tasan abinda yake ransa kuma yake damunsa ba.

Shi kansa baya jin cewa akwai wata rana daza tazo ya amince da mace, komai na rayuwarsa yana tafiya ne bisa umarnin zuciyarsa, bai taɓa yin abu ance ba dai-dai bane, hakan yasa baya gane dai-dai da kuma ba dai-dai ba,
Rayuwa yake ta kaÉ—ai ce wacce kuma yake jin daÉ—in ta a yadda yake!

Ajjiyar zuciya ya sauke yana mai É—an Lumshe idanunsa dan baya jin zai amsa maganar ta Oumuu-Ayman dan bata da wani muhimmanci a garesa, rayuwarsa shi kaÉ—ai mugun daÉ—i take masa.

Kallon yadda ya rufe idanunsa tayi a hankali kuma numfashin sa ya fara sauka,
wanda yake fita da wani irin zafi,
Gane cewa ballai yayi magana ba domin duk abinda bashi da muhimmanci a garesa baya damun kansa dashi.

A hankali ta shafa lallausar sumar kansa tana jin so da kuma ƙaunar Jalaluldeen na ratsa zuciyarta,
yayinda tausayin rayuwarsa ya mamaye dukkan Zuciyarta,
lumshe idanunta tayi a hankali ta sauke ajjiyar zuciya yayinda wani kalar rauni ya cika mata zuciya, cikin tausasa murya mai É—auke da su da kuma kewa yace.

"Ya Allah! Ka bawanka ka kula dashi, ka sanya albarka a cikin rayuwarsa, Ya Rabbi ka kare rayuwarsa daga magauta, Allah ka sanya masa tawakkali a cikin zuciyarsa, Ubangiji ka sanya kada rauninsa ya bayyana ga maƙiyansa, Allah ka karesa daga cikin kariyarka, Allah ka bashi lafiya ka cire masa tsoron da mata suka dasawa zuciyarsa, Ya Allah ga bawanka Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal ka kula dashiiiii"

Ta ƙare maganar a raunace yayinda idanunta ya cika da hawaye, bata san mene zai je ya dawo ba, amma Tabbas Zuciyarta ta fara samun nutsuwa da kuma gamsu wa wacce bata san dalilin faruwar hakan ba.

Yadda Numfashinsa ke fita a hankali ne ya ɗan cure waje guda, tare da narke jikinsa a jikin Oumuu-Ayman yasa Oumuu fahimtar kewa da kuma ɗumin jikin uwa da yayi, Tabbas Abu Maleek yana buƙatar kulawa yana son kasancewa da Uwa mahaifiya wacce bai daɗe a wajanta.

Hannunta tasa a hankali ta shiga shafa sumar sa yayinda bakinta ke motsawa tana yin addu'a tare da tofa masa a tsakiyar kansa.

Duk da cewa bacci yake amma sosai yake jin daɗi da kuma sanyi a ransa sanadiyar addu'a da Oumuu take masa, wani irin kuzari da kuma ƙarfi ne suka sauka a saman gangar jikinsa, a haka yaci gaba da baccin daya daɗe bai ba, sai Ajjiyar zuciya yake saukewa akai akai!

Ganin yadda yake jin daɗin baccin ne yasa Oumuu gyara masa kwanciya tare da riƙe tafukan hannayensa, a haka suka kasance tare Abu Maleek sai sharar bacci yake.

Adams ne yake tafiya a hankali kansa a ƙasa, cikin nutsuwa da kamala kai tsaye sashin Mai Babban ɗaki ya nufa, bai shiga ba sai da Mai Babban ɗaki ta bada umarnin ya shiga.

Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga yana ɗan cilla idanunsa, a can ya hangota saman Ladduma hannunta riƙe da casbawa tana jaa.

Kallonsa tayi kafin tace.
"Lale! Da zuwa mijin tun shekaran jiya ban sanyaka a idanuna ba, lafiya dai?"

Kwallon e kawai yayi ba tare da yace koma ya nemi waje kusa da Mai Babban É—aki ya zauna, kafin a hankali ya dumeta da kyau yace.

"Matar irin wannan kyau haka, ko ni akaiwa??"
Ya faÉ—a yana sanya hannunsa tare da É—aukan Apple É—in dake gabanta a saman plate É—in dake É—auke da nau'in kayan lambu kala-kala.

A hankali yasa Apple É—in a bakinsa tare da gutsira kafin yace.
"Nikam Ina Oumuu ne?? 2days ban ganta ba"
Ya faɗa yana ƙara gutsirar Apple ɗin.

Jinjina kai Mai Babban É—aki tayi kafin tace.
"Kasan shalelenta ya dawo, tana can wajanta hala shine ya tsare ta ta son jikin nan nasa, kamar wannan magen tasa wacce yana nan tare da ita rai da rai kamar wata uwarsa"

Shiru Adams yayi bai ƙara magana ba, sai Apple ɗin da yake sha, ganin hakan yasa Mai Babban ɗaki sanya hannunta ta ajjiye plate ɗin fruits ɗin tana faɗin.

"A'a ya haka kuma?? Wannan sata ne ko kuma fashi?"
Kallonta yayi ya É—an sakin murmushi kafin yace.

"Da bindiga kika ganni hala? Sata kuma ai ba sata nayi ba, Allah ki ban ko naje na kwashe waccar zumar da kike masifar so"

Zare ido Mai Babban É—aki tayi kafin tace.

"Yau na kejin sabuwar masifa? A'a wallahi babu ruwan maza fice min, kada na sake ganin shuɗaɗɗiyar ƙafar nan taka"

Miƙewa tsaye Adams yayi kafin ya faki idanunta ya kwashe Apple ɗin gaba ɗaya na plate ɗin.
Yana É—auka Otun na shigowa ganin haka yasa Mai Babban É—aki sakin kuka tare da faÉ—in.

" Yawwa Otun tunda kai Ubansa ne ƙilan yaji maganarka, wallahi ko dai ya biyani ko kuma na kira masa Police, dan Allah wannan ba fashi bane, yanzu kai magana ace rikicin tsufa bane, gaba ɗaya kuɗaɗe ba shine yake kwashe su, to Fisabilillahi wannan ba sata bace? A'a wallahi bazan iya zama da ɓaruwa ba"

Ta ƙare maganar tana sakin kuka tare da ɗaukan wayarta tace.

"Wallahi babu ruwana da cewa kai jikana ne, yanzu zan sa akai ka bayan kanta"

Ta ƙare maganar tana danna wayarta, Otun dake tsaye ya nemi waje ya zauna kafin ya kalli Adams dake tsaye yana ɗan sakin murmushi yace.
"Aremo mai kai mata ne? Matar da ba lafiya ba....."

Da sauri Mai Babban É—aki ta katse Otun da faÉ—in.
"Muhammadur Rasulullah S.a.w na shiga Aljanna naƙi fitowa masifar da kake jawo min kenan? To wallahi sai dai kaga Junaidu a gadon Asibiti ba dai ni ba"
Ta ƙare maganar tana sakin kuka, Murmushi kawai Otun yayi domin ya fahimci tun lokacin rasuwar late King Tunde Muhammad Jalal Mai Babban ɗaki ta ƙara riki cewa, ga kuma shekaru dake a kanta kullum,
Gyara zama yayi yana faÉ—in.

"Kai Adams mene kayi mata ne har haka? Ko kuma kana son kwanan kanta ne?"
Ka faÉ—a Adams ya É—aga tare da watsar da hannu alamar "Ohhhhoo!!"
Kafin ya juya cikin izza yabar musu wajan yana sakin Murmushi.

Bayan fitarsa ne kuma Otun ya gyara zama sosai, cikin nutsuwa tare dayin ƙasa da murya yadda Mai Babban y zata fahimci abinda zai faɗa yace.

"Mai Babban É—aki daman magana nazo muyi ne, naga kuma dake kaÉ—ai ya dace nayi maganar shine ya sanya nace bari nazo wajanki"

Kallonsa Mai Babban ɗaki tayi, kafin ta ɗauke idanunta tana ɗan jan casbahar hannunta, gane cewa ba zatai magana bane yasa Otun ƙara yin ƙasa da murya yace.

"Kin san cewa sarauta bata jira..."
Da sauri ta katse sa da faÉ—in "Ai haba dai, bani da labari ai"
Ta faÉ—a tana É—an yi masa kallon gefe, jinjina kai kawai Otun yayi yana danne abinda yake ransa kafin ya É—ura da faÉ—in.

"Eh! Haka ne, Sarauta bata jira, koda ba za'a naɗa wani ba, ya dace a bawa wani riƙon ƙwarya domin hakan zai sanya Mutunan Kanzaf suji daɗi a ransu su gane cewa ko babu King Tunde Muhammad Jalal akwai wanda zai iya mulkarsu kuma yayi mulki irin na Murgayi"

Jinjina kai Mai Babban É—aki tayi tare da É—aukan glass É—in ta, ta sanya kamar ba zatai magana ba sai kuma tace.

"Au too! Yanzu na gane yanzu mene kake so ayi sarautar za'a naɗa ko kuma riƙon ƙwaryar??"
Ta faɗa tana ɗaukan sandar ta, tare da Miƙewa tsaye hakan ya sanya Otun sauke numfashi kana cikin jin daɗin fahimtar maganarsa da Mai Babban ɗaki tayi yace.

"A'a ko riƙon ƙwaryar ne sai a fara, kafin a duba wanda ya dace ya hau kan wannan kujerar, daman ko Agba Akin ko kuma ni naga duk mu manya ne zamu iya komai"

A hankali Mai Babban ɗaki ta fara tafiya zuwa cikin bathroom ɗin wanda aka ƙawata da kayan mure rayuwa, sai da taje bakin ƙofar shiga bedroom ɗin ta tsaya tace.

"Babu maganar riƙon ƙwarya, Sarauta za'a naɗa ana yin 40days ba kowa bane kuma King ɗin sai Zakina Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal, idan ka fita ka jamin ƙofar"

Tana faɗin hakan tayi cikin ɗaki tana surutu ƙasa ƙasa,
Wata harbawa zuciyar Otun tayi yana jin wani irin mai kama da damuwa ko kuma baƙin ciki yana mamaye dukkan kofufin zuciyarsa,
Cikin rashin kuzari da kuma juyawar da kansa yake ya miƙe tsaye tare da ficewa daga cikin sashin na Mai Babban ɗaki.

Mai Babban É—aki kowa na shiga Bedroom ladduma ta sanya tare da tayar da sallar zhur saboda jin masallacin Alaafi na tayar da sallah.

A hankali Abu Maleek yake taka ƙafafuwansa, fitowar sa kenan daga cikin Masjid, idanunsa ya lumshe yana sauraran abinda da Shakiru yake faɗa,
Kasancewar duk tare suka fito daga cikin Masjid É—in, Yana tsakiya Yayinda Shakiru ke gefensa sai kuma Sharefddeen dake gaba yayinda Adams yake baya.
Shakiru ne ya ƙara duban Adams dake baya yace
"Big bro Company's takalan man nan yana buƙatar sabbin ma'aikata, kuma ƙwararro duba da yadda muka samu sabbin disygner masu kyau da kuma ƙayatarwa"
Jinjina kai Adams yayi kafin yace.

"Kuyi magana da P.a mana Shakiru ka faɗa masa abinda ake buƙata, and why kake tambaya ma? Bayan kai ne Manager na Companyn"
Ya faÉ—a yana gyarawa zaman agogon hannunsa , Murmushi Shakiru yay kafin yace.
"Haka ne big bro daman na faɗa maka gane kada kazo kaga baƙin fuskoki a companyn, amma zanyi komai dani da P.a"

Ya faɗa yana duban Abu Maleek dake tafe a hankali yana sauraran dukkan abinda suke faɗa, bai san komai na daga kasuwanni ba, shiyasa bai fiya gane dukkan zan can da suke faɗa ba, ƙara Lumshe idanunsa yayi yana taune leɓansa saboda bugawar da zuciyarsa tayi,
Wani Murmushi Shakiru ya yi kafin ya dubi Adams yace.

"Ga Abu Maleek ko za'a fara ta kansa ne, domin ya rage zaman gidan hakan zai sa ya daina zama cikin kaÉ—ai ci da kuma samu kansa cikin damuwa"
Ya faɗa yana kallon Abu Maleek Sharefddeen dake gaba juyawa yayi ya kalli Jalaluldeen ganin yadda ya marai-raice fuska ne kuma tare da taɓe baki yasa kawai ya ɗauke kansa tare da shigewa cikin sashinsa, domin tuni sun Shigo cikin Makaken babban side ɗin Family na Alaafin.

Adams ya ɗaga kansa a hankali kuma ya sauke idanunsa akan bayan Abu Maleek dake tafiya kamar bai so, tafiya kuma mai cike da nutsuwa da kamala, sosai Abu Maleek ya kere su a girman jiki tsayi faɗi, uwa ba tarin haiba da kwarjini ga wani sahihin kyau mai ɗaukan hankali,babu abinda yafi ɗaukan hankali a jikin Abu Maleek sai jajayen laɓɓansa da kuma blue eyes ball ɗinsa, sai kuma ƙwantaccen gashin bayansa Wanda yake ɗaure da ribbon.

Ɗauke idanunsa yay ba tare daya ƙara kallon Abu Maleek ba ya dubi Shakiru da yake ƙare masu kallo yana son ya fahimci wani abu yaji Adams yace.

"Shakiru kayi abinda yake gabanka kawai, duk abinda kukai da P.a let me know!"
Ya faÉ—a yana É—an tsayawa ganin hakan yasa Shakiru tsayawa yace.
"In sha Allah big bro komai zai tafi cikin tsari"
Yana faɗin haka ya dubi Abu Maleek daya ɗan tsaya shima yana kallon sararin samaniya a hankali kuma yake tsotsar laɓɓansa da suke ɗauke da danshin ruwa yace.

"Our footballer ko magana babu yau?"
Abu Maleek yi yayi kamar baiji abinda Shakiru ya faɗa, yayi hakan ne e saboda baya son takura ko kaɗan, wajansa Shakiru ya ƙarasa yana faɗin.
"Ina fatan gwarzon mu yana lafiya, ya kuma ƙarin haƙurin mu?"

Gently Abu Maleek ya juyo tare da sauke tsumammun idanunsa akan Shakiru kafin ya É—an sauke ajjiyar zuciya yana dai-dai-ta tsaiwarsa, bakinsa ya shiga motsawa yana son dai-dai-ta kalaman da zai faÉ—awa Shakiru can kuma ya numfasa yace.

"Allahamdulillah bro"
Ya faÉ—a yana Lumshe idanunsa wanda suke nuna gajiyawa da maganar da yayi ga kuma tarin baccin dake idanunsa, domin har yanzu gajiya bata gama sakinsa, uwa ba kewa da rashin Dad É—insa dake damun zuciyarsa.

Murmushin Shakiru yay yana yin gaba tare da faÉ—in.
"Allah ya ƙara mana haƙuri da juriya"
Ya ƙare zan can yana shigewa cikin sashinsa shima, wajan ya rage daga Adams sai Jalaluldeen, cikin nutsuwa Abu Maleek ya ɗaga idanunsa tare da sauke kallonsa akan Yayan nasa, wanda ganinsa yake haifar masa da nutsuwa yake jin kamar Maminsa ya gani,
Shima Adams ɗin kallonsa yayi sosai, kallon da yake nuna zallar tsana da kuma ƙyamata,
Zuciyar Abu Maleek tayi rauni sosai a hankali ya langwaɓar da kansa gefe guda cikin nutsuwa kuma ya nufi wajan Adams yana zuwa ya faɗa jikinsa tare da ruggumesa yana sakin ajjiyar zuciya mai nauyi yayinda farin ciki ya lulluɓe zuciyarsa, muryarsa na rawa yace.

"I miss You so much Lovely bro"
Ya faɗa yana sakin tagwayen ajjiyar zuciya mai ɗan ƙarfi, Rungumesa Adams yayi kafin ya ɗura bakinsa akan kunnan Abu Maleek yace.

"Uhm ya tabbata kai ne ka sace Mami, duba da yadda baka damuwa da rashinta, na tsaneka Jalaluldeen tsana mai yawa, tsanar da ban taɓa yiwa wani ɗan adam ba, wallahi muddin baka dawo min da mahaifiya ta ba, uhm!!!!"
Ya ƙare maganar yana janye jikinsa daga jikin Abu Maleek kai tsaye shima ya nufi sashinsa

Runtse idanunsa Abu Maleek yayi yana jin tsallan da zuciyarsa tayi sosai kalaman Adams suka tsaya masa tashin hankali, tsoro da fargaba suka ratsa masa zuciya, lumshe idanunsa ya ƙarayi yana shaƙar iskar dake Kaɗawa a wajan, kafin yaja ƙafafuwansa ya nufi sashinsa, yana shiga kai tsaye bedroom ɗin sa ya shiga tare da murza key yama mance da batun wata Julde.

Kai tsaye Art room ɗinsa ya shiga ya ɗauki pencil da colours masu yawa, wani madaidaicin ɗaki ne, mai masifar kyau, wanda yake ɗauke da wasu ƙawatattun kujeru masu kyau wanda suka kasance na ƙarfe, sai wasu Flowers masu kyau wanda suke fidda wani dadɗan ƙamshi mai sanya nutsuwa da kasala a jiki.

Sai wata A.c mai bala'in bada sanyi a wajan, ka wani lallausan green ɗin carpet dake shimfiɗe a ƙaramin parlon dake cikin bedroom art ɗin, ga deep freezer dake gefe guda, sai ƙaramar plasma, ga wata ƙatuwar kwalba wanda aka cikata da kifaye masu kyau wanda kai tsaye ruwa yake saukar masu daga lambu.

Wani table ya jawo ya zuba pencil da colours ɗin a ciki, kafin a hankali ya nufi wata loker ya zaro wata farar carbon paper a ciki, yana ɗaukowa ya mannata a jikin wani ƙarfe da yake zanan jiki, kafin ya nufi deep freezer ɗin ya ɗauki fresh milk da lemon power horse energy masu sanyi ya ajjiye saman table ɗin, wata ƙaramar kujera ya ɗauko tare da zama kai ya ɗauki pencil ɗin bayan ya ɓalle murfin fresh milk ɗin ne ya ɗan kafa a bakinsa, saboda sanyin daya jine yasa ya lumshe idanunsa a hankali kuma ya manne hannunsa a saman paper ya fara zanan idanunsa a lumshe.

Wajan 20 minutes ya É—auka yana zaman still kuma idanunsa suna rufe, sanssanyar ajjiyar zuciya ya sauke bayan ya furzar da iska daga cikin bakinsa, slowly ya buÉ—e idanunsa tare da saukewa akan art É—in da yayi,
Da sauri yaja idanunsa ya Lumshe saboda zanan da yayi arba dashi, cije lips ɗinsa yay zuciyarsa cike da mamaki why kullum idan yayi zanan idanunta a rufe? Mene ya sanya kuma har yanzu ya kasa tantance photon Namiji ne ko kuma na mace? A kullum yayi zanan sai yaga kai babu gashi idanu a rufe, kirji kuma fal da brest kamar zasu tsaga ƙirjin su fito,
Ajjiyar zuciya ya sauke yana ƙara ware idanunsa akan laɓɓan wacce ya zana, kawo yanzu ya fara tunanin macace, duba da yadda laɓɓanta suke jajir gwanin sha'awa, amma irin laɓɓan tsiwa ne.

Lumshe idanunsa e a hankali ya ware laɓɓansa tare da cizon lips ɗinsa na ƙasa kamar zai kuka Murya a narke yace.

"Fitananniyyaaaa!!!"
Ya ƙare maganar yana jan harafin Yaaaa!!! Yana nan zaune har aka kira sallar Asar, gaba ɗaya baya jin daɗin fresh milk ɗin babu abinda yake son sha yanzu wanda ya huce Alcohol, Abar da aka sabar masa sa shanta tun yana Ƙarami.

A sanyaye ya miƙe ya koma bedroom ɗinsa yana zuwa ya samu sweet na shan madara kanta ya shafa yana faɗin "Sweet my love, my best friend"
Ya faɗa yana shigewa bathroom ya ɗaura alwala kai tsaye yabi ta ƙofar baya kasancewar yana sahun gaba yasa bai haɗu da ƴan uwansa ba, bayan an idar da sallah kuma zama yayi tare da lumshe idanunsa yana sauraran bugawar zuciyarsa.

Haka sallar magrib da Isshā duk haka yayi bai ƙara haɗuwa da kowa ba,
Ko Abinci bai tsaya ci ba ya shige cikin bedroom ɗinsa tare dayin wanka ya sanya wasu haɗaɗɗun nightwear Panjams masu santsi da taushi ya sanya bayan ya fesa parfume ne ya kwanta tare da jawo sweet ya rungome ya lulluɓe su da duvet mai laushi bayan ya ƙure gudun a.cn bedroom ɗin.

Washe gari
Tun 4:05 ya tashi saboda sautin kiran sallar farko na Subhi da yaji, jiki a sanyaye jike da kasala ya ware duvet É—in jikinsa kai tsaye bathroom ya nufa,
Yayi wanka ya wanke bakinsa tare da É—aura alwala,
Shirya kansa yayi cikin wata farar tattausan Male La Doublej Jallabiya mai gajeren Hannu, wata farar hula ya É—auka wacce ake cewa tashi kafiya naci irinta larabawa, a saman sumar kansa ya sanya hular wacce ta rufe masa sumar kan sauran gashin kansa kuma suka sauka saman wuyansa, kai tsaye masjid ya nufa bai dawo ba sai wajan 7:00

Yana dawowa ya shirya kansa cikin ƙana nan kaya masu kyau, wandon ya tsaya masa iya laps ɗinsa kamar dai kayan spots wear, gorar ruwa ya ɗauka mai sanyi kai tsaye gym part ɗinsa ya nufa, yana zuwa ya fara motsa jikinsa domin idan yace zai zauna haka tabbas damuwa da kuma rashin mahaifinsa sai iya tarwatsa zuciyarsa, haka ya dinga motsa jiki har wajan 10:30 sai zufa ce take karyo masa.

Tura ƙofar side ɗinsa yayi a hankali bakinsa ɗauke da gorar ruwa yana shan yayinda gumi ke yanko masa, ganin Oumuu-Ayman ne yasa ya ɗan ware idanunsa tare da kwaɓe fuska a sanyaye ya ƙarasa saman kujera yana sauke numfashi.

Murmushi Oumuu-Ayman tayi kafin tace.
"Wlcm Zaki"
Jinjina kai Abu Maleek yayi kafin yace.
"Barka da safiya Oumuu na"
Kallonsa tayi sosai ajjiyar zuciya ta sauke ganin babu abinda Abu Maleek ya bari na dan gane da kamannin Murgayi King Tunde Muhammad Jalal.

"Zaki Ya mai jiki?"
Zare idanunsa yayi kafin ya langwaɓar da kansa gefe guda cikin gajiyawa yace.
"Ayyah! Baga irinta ba, wallahi Oumuu na manta da ita tun shekaran jiya"

Murmushi kawai Oumuu-Ayman tayi kafin tace "Ni ina sane da ita, domin duk bayan wasu awanni sai nazu na gyara mata Jikinta na shafa mata mai a kanta, Allahamdulillah naga gashi ya lulluɓe kan nata, gwanin sha'awa wallahi"

Taɓe baki yayi ba tare da yace komai ba, gani yau bai tashi da ƴan son magana da ita bane yasa Oumuu bashi breakfast Pancakes and Syrup sai haɗin salad Wanda yaji da faffan ƙwai, da Tomato's With Onion kana masan Salad da caroot.
Yana gama ci ya shige bedroom ɗinsa, Miƙewa Oumuu tayi ta nufi bedroom ɗin da Julde ke ciki, tana kwance tana sauke numfashi goge mata Jikinta tayi ta bata madara tare da gyara mata sumar kanta daya feso da yawa Lokaci guda.
Kwaɓe fuska Julde tayi a hankali ta shiga motsa bakinta cikin Murya mai rauni tace.
"Ballowo!!"
Shiru Oumuu-Ayman tayi domin ta fahimci Julde Makauniya ce, amma sam bata Fahimci sunan "Ballowo" da take yawan faÉ—a.

After 7days
Bayan anyi sadakar bakwai ne aka fara shirin yin naÉ—i, gefen Abu Maleek kowa ya manta da batun Julde rabonsa da ita tun ranar daya bata jininsa tasha wajan kwana shida ko biyar kenan.
Yayinda kullume sai Oumuu ta gyarata kuma sosai Jikinta ya murje saboda zama waje guda, cima mai kyau ga kulawa, har lokacin kuma babu wanda yasan da zamanta a cikin Alaafi!.

4:40 dawowarsa kenan daga masjid yana sanye da wata Blue É—in Armless mai kyau, wacce ta É—an kamasa yayinda ya É—an zuge gaban rigar bayan shigowar sa cikin side É—in nasa,
Walking slowly yake shigowa cikin side É—in nasa, yayinda yake tafe yana É—an sauke ajjiyar zuciya saboda bugawar zuciyarsa take masa, wacce lokaci zuwa lokaci take masa,
Ya iso dab da bedroom ɗin da Julde ke ciki yaji Zuciyarsa ta harba da ƙarfin gaske da sauri ya runtse idanunsa tare da saurin faɗin.
"hasbunallah!"
Ya faɗa yana dafe ƙirjinsa, har ya ɗaga ƙafa sai huce kunnuwansa suka jiyo masa sautin Muryar ta, tare da buge bugen da take,
Golden eyes É—insa wanda suke fidda wani ruwa ruwa saboda tsabar farinsu,
Kamar zai tafi sai kuma ya nufi bedroom a ransa yana faÉ—in "O'ohhhh This Fulani girl..."
Hanunsa ya ɗura saman wajan passward ɗin yana rubutawa ƙofar ta buɗe, a hankali ya sanya ƙafarsa ciki yanayin kusantar ɗakin yanayin ƙaruwar bugun zcyarsa, can ya tsaya lokaci guda kuma yaja baya da sauri yana dafe ƙirjinsa saboda idanunsa da suka sauka akan......

Abu Maleek isn't free contact to subscribe 08119237616

*_41-42_*
Dugwayen ƙafafuwan ta, wanda suke farare tass har wani yellow suke saboda wani fari da tayi fatar ƙafafuwanta sunyi fresh, sunyi ɓulo ɓulo.

Ga wasu gargasa da sukai kwance a saman farar fatar jikin ƙafafuwan nata, sai ƙyalli suke saboda tsanani kulawar da Oumuu-Ayman take bawa Julde,
Sauyawa ta musamman tayi saboda zama waje guda, da kuma kulawar da Oumuu-Ayman take bata akai akai.

Ajjiyar zuciya ya sauke a hankali ya jingina bayansa da jikin door, yana ɗan sauke numfashin tare da jan Maraitattun idanunsa ya rufe su, a hankali yake fidda numfashi kuma yake shaƙa, almost 30seconds kafin cikin nutsuwa ya shiga ɗaga zara-zaran eyes lashes ɗinsa wanda suke kwance saman fatar idanunsa.

Kai tsaye kuma ya sauke idanunsa a saman fararan farcen yatsun ƙafafuwan ta, wanda akaiwa ado da wani red ɗin jan farce, hakan ya ƙara bayyanar da Zallar kyau da kuma tsarin kyawun yatsun nata.

Ƙuri yaywa yatsun ƙafar nata kamar mai Shirin neman wani abu, some seconds kuma ya shiga zame idanunsa yana ɗan taɓe bakinsa kamar wanda yaga kashi,
Teeths ɗinsa yasa ya datse jajayen laɓɓansa tare da fara tauna su, saboda wani irin harbawa da zucyarsa tayi masa da ƙarfi, al'amarin daya haddasa masa saurin runtse idanunsa yana furzar da iska daga cikin bakinsa.

A hankali kuma ya sanya tafin hannunsa da a kullum baya rabuwa da gumi ya manna a saitin wajan da yaji yafi harba masa a cikin ƙirjin nasa, kwaɓe fuska yay tare da langwaɓar da kansa gefe guda,
Cikin wata kasalalliyyar murya mai matuƙar sanyi ya ware laɓɓansa tare da faɗin.

"Uhm! Ya Hakkamu!!!"
Ya faÉ—a yana É—an juya da sauri zai bar cikin bedroom, domin ji yake idan yaci gaba da tsaiwa Tabbas zuciyarsa zata iya fitowa saboda a zabar bugawar da take masa.

Kamar daga sama yaji sautin Amon muryarta wacce take fita a hankali, Muryar da Amonta kawai zai sanya ka fahimci rauni da kuma halin buƙatuwa da mai muryar take ciki tana faɗin.

"Ballowo!!"
Shine abinda ta faɗa yayinda sautine Amon muryarta wajan faɗin wo!!!!! Ya ƙare a raunace kamar mai shirin fashewa da kuka.

Julde kam tun kafin ya shigo taji, Zuciyarta tayi sanyi a hankali kuma ta shiga bada sautin dib! dib!! dib!!! Sakamakon kusanta zuciyarta data Abu Maleek, shiru tayi kamar mai nazari a hankali kuma ta tsaya da buge bugen da take, yanayin yadda Jikinta ke ɓari da kuma bugawar zcyarta daya tsananta yasa ta fahimci Kallonta yake.

Ajjiyar zuciya ta sauke, a hankali kuma kunanta yaji sautin mutsawar gangar jikinsa alamar fita zai wannan dalili ya sanya ta kwaɓe fuska a hankali wasu sila sila hawaye suka ganganro daga cikin idanunta zuwa gefen fuskarta, kafin cikin muryarta mai ɗauke da zallar shagwaɓa ta ambaci sunan nasa.

Wannan dalili ya sanya Abu Maleek tsayawa ba tare daya juyawa ba, shi kam shagwaɓe fuska yayi kamar zai kuka,
Jin shiru yasa Julde fara sakin shassheƙar kuka yayinda da Jikinta yaci gaba da bugawa, tana shirin yin magana taji Muryar sa wacce ta sanya tayi saurin yin shiru da bakinta sai Ajjiyar zuciya take saukewa amma still Jikinta bai bar rawa ba.

Walking slowly ya fara taka ƙafafuwan sa a saman lallausan carpet ɗin bedroom ɗin, hannunsa duk biyun zube cikin aljihun wandon sa, cak ya tsaya saman kanta, Jin numfashinta a kusa da ita ne yasa,
Ta ƙara marai-raice fuska ta shiga ƙoƙarin Miƙewa zaune,
Ganin abinda take ne yasa ya ɗaga ƙafarsa guda ɗaya, tare da ɗurawa a saman hannunta ya danne.

Ƴar ƙara ta saki tana turo bakinta gaba kafin tace.
"Bafiiii fa Ballowo"
Juya idanunsa yayi sosai a ransa yake faÉ—in "wato Yarinyar nan komai nawa take kwaikwayo Uhm, Witch!"
Ya faɗa a ransa yana ƙara danna ƙafarsa dake saman hannunta.

Oumuu-Ayman ce ta turo ƙofar a hankali tare da shigowa bakinta ɗauke da sallama, tun kafin ta shigo ta san cewa yana ciki saboda ƴar danjar dake harbawa a bakin ƙofar alamar an shiga ciki.

Akan wani table ta ajjiye tray É—in hannunta, tare da juya ta nufi wajan Abu Maleek fuska É—aure take faÉ—in.
"A'a ya zaka zaki? Bafa na son cin zaki kaji ko?"
Ta faɗa tana zama gefen bed ɗin tare da sanya hannunta ta ture ƙafarsa amma ko motsi ƙafar ba tai ba,
Kallonsa tayi tace.
"Kaga kowa zan ɓata maka"
Zame ƙafarsa yayi a hankali tana sakin numfashi kana ya ɗan zauna a gefen Oumuu na dama, Murya can dai-dai kunnan Oumuu yadda Julde baza taji abinda yace ba yace.

"Oumuu na, yunwa taimakamin"
Ya faÉ—a yana narke mata fuska kamar yaron goye, banza tai masa duk tasan cewa lallai yunwar ya keji tunda har ya buÉ—e bakinsa yayi magana.

Oumuu-Ayman Julde ta kalla a hankali kuma ta sanya hannunta ta shafi lallausar baƙar sumar data yiwa kan Julde ƙawanya har wani tsayi tayi sosai, saboda mayukan da take shafawa kan bana wasa bane dalilin da yasa lokaci guda gashin ya Fito ya cika kan, yanzu kuma tsayi kawai yake.

Cikin kulawa Oumuu-Ayman tace
"Daughter Meke damun ki?"
Jin Muryar matar da kullum take zuwa wajanta ta bata abinci ta gyara mata jiki harda wanka some time, yasa ta ɗan juya fuskarta zuwa derection ɗin inda yake jiyo Muryar Oumuu, cikin Sa'a kowa juyayyun idanunta suka sauka akan Oumuu kafin ta kwaɓe fuska tana shirin yin kuka tace.

"Wala ko Damata'm"
Ma'ana ba abinda yake damuna, jinjina kai Oumuu-Ayman tayi kafin ta sanya hannunta ta ɗaga Julde tare da ɗan Rungome ta, kallon fuskarta tayi, Zallar kyau kawai take gani kyau na a salin gaske, yayinda kuma fuskar take mata kamanceceniya data wata, sai take gani kamar ta taɓa ganin fuskar Julde.

Jinta a jikin Oumuu-Ayman yasa ta lafe tana tura baki gaba tare da sakin Ajjiyar zuciya, Abu Maleek da bai san mene ake ba Wayarsa ya zaro ƙirar Iphone 13pro max ya fara latsawa, kai tsaye kuma team ɗinsu na Hala Madrid ya fara dubawa.

Oumuu-Ayman ce ta kallesa kafin tace.
"Zaki maza É—auko min tray É—in lunch É—in can"
Idanunsa ya ɗaga ya kalli Oumuu-Ayman ganin kallon da take masa ne, ya sanya shi karyar da wuya ba tare da yace komai ba, ya miƙe jiki a sanyaye ya nufi wajan tray ɗin a gefen Oumuu ya ajjiye kana shima ya zauna a gefenta yana mai ajjiye Wayarsa waje guda tare da zuba masu idanu.

A hankali kuma ya fara yawo da idanunsa akan shigar dake jikin Julde wasu, Applique logo detail T-shirt black color ce a Jikinta, wacce ta tsaya mata iya cinyoyinta, wuyan rigar nada faÉ—i sosai, gashi mai siririyar igiya ce, ga wani shape É—in Almakashi da wuyan rigar yake dashi, hakan ya sanya farar fatar wuyanta ta bayyana, har ana iya hangen saman tsayayyun brest É—inta.

Ƙasa yayi da idanunsa a hankali kuma ya sauke ganinsa akan shatin nipples ɗinta Wanda suka bayyana sosai, jin kansa ya sara da ƙarfi ne yasa a hankali ya janye idanunsa yana mai sauke ajjiyar zuciya tare da faɗin.

"Iskanci kawai,uhm!!"
Ya faɗa a cikin ransa, yana mai ɗan lafewa a jikin Oumuu-Ayman hakan yasa fuskarsa tayi farcing data Julde har yana iya shaƙar ƙamshin Jikinta dake fita a hankali yana kawowa hancinta, lumshe idanunsa yay yana ƙara narkewa jikin Oumuu-Ayman kafin a hankali cikin daddaɗar sautin Muryar sa yace.

"Oumuu ki matsar da ita daga jikin ki"
Ya faɗa yana ƙara kulle idanunsa saboda wani mahaukaciya sarawa da kansa yay masa,
Oumuu-Ayman Murmushi tayi kafin tace.

"Matsayinta É—aya dakai akai, Daughter sunana Oumuu-Ayman, Zaki kuma nace min Oumuu na!!"
Ta faɗa tana sanya spoon a cikin plate ɗin lunch ɗin me ɗauke da Amala and ogbono soup, sai how head Wanda yaji kayan ƙamshi hadda daddawa.

Julde dake shaƙar ƙamshin wani ƙamshin strowbeery dake fita daga cikin bakin Abu Maleek ta kwaɓe fuska tare da faɗin.

"Oumuu na, kin gansa ko?"
Ta faɗa tana ɗaga hannunta tare da saukewa a ƙirjin Oumuu wanda yay dai-dai da kusa da bakin Abu Maleek, Oumuu-Ayman ganin yadda Julde take kwaɓe fuska za tayi kuka tace.

"Me yayi maki?"
Oumuu-Ayman ta faɗa tana ɗebo Amala tare da kaiwa bakin Julde ƙaramin bakinta ta buɗe, wanda laɓɓan sukai jajirr Tamkar wacce ta shafa Lip balm saboda jan da sukai, a hankali ta fara cin abincin tana zare juyayyun idanunta hakan yasa Abu Maleek kwaɓe fuska.

"Oumuu na, kallo na yake fa"
Julde ta ƙara faɗa bayan ta cinye Amalan bakinta, Tuni Abu Maleek ya kulle idanunsa ba tare daya bari Oumuu-Ayman ta gansa ba.
Ganin Ba ita yake kallo ba yasa Oumuu-Ayman ƙara mata Abincin tana faɗin.

"Ba kallonki yake ba Daughter"
Oumuu-Ayman ta faɗa tana ƙara bata Abincin, lumshe idanunta kawai tayi domin a Jikinta ta kejin kallon da yake mata,
A hankali take cikin Abincin harta ƙoshi, koda Oumuu-Ayman ta bata naman kan saa ƙin ci tayi saboda rashin sabo,
Ruwa tasha mai sanyi a hankali ta sauke Ajjiyar zuciya tana ƙara riƙe ƙirjin Oumuu-Ayman kamar wani zai gudu da ita.

Abu Maleek da idanunsa yake a lumshe ya shiga buɗewa a hankali kana ya sauke idanunsa akan ɗan ƙaramin bakinta, wanda suke shanny sun ɗan tattare hakan yasa suka ƙara kyau.

Idanunsa ya janye kafin ya kalli Oumuu-Ayman murya dai-dai kunanta yace.
"Ki daina shafa mata jambaki ba kyau"
Ya faɗa yana Miƙewa daga jikin Oumuu-Ayman tare da ɗauke fresh milk ɗin da Oumuu-Ayman tazo dashi zata bawa Julde.

Da sauri Julde tace.
"Oumuu na ya tafi fa"
Kanta Oumuu ta shafa tace.
"Rabu dashi kinji Daughter na"
Marai-raice fuska Julde tayi tace.
"To ya sunansa shi?"
Jinjina kai Oumuu-Ayman tayi tana girmama Surutun Julde kafin ta bata amsa da.
"Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal, popular name Shine Abu Maleek Amma ke yayanki ne Kinji kina ce masa Yaya Jalal is better"

Shiru kawai Julde tayi, Oumuu kan ƙara gyara mata jiki tayi kana ta fita zuwa sashin ta, domin ta shirya ta amsa kiran Mai Babban ɗaki.

Abu Maleek kai tsaye flat ɗinsa ya nufa, a ƙawataccen parlon nasa ya samu sweet a saman kujera, gana ganinsa ta tashi da gudu ɗaukan ta yayi yana shafa bayanta, sai daya ƙara shan fresh milk ɗin kana ya zube saman kujera yana faɗin.

"Miss You so much sweet, sorry Kinji"
Ya faÉ—a yana kafawa sweet fresh milk É—in a baki sai da ta shanye tass Sannan ya cire yana yin baya tara da kwanciya, ba jimawa bacci ya É—auke sa, kiran Sallar Magrib ne ya tayar dashi, yana tashi kai tsaye cikin bedroom É—insa ya nufa yana ajjiye sweet tare da shigewa bathroom.

Yana shiga ya zame kayan jikinsa ya sanya jikin hanger, kansa ya sakarwa shower ruwa ya fara saukar masa, a hankali ya sauke idanunsa akan zanan ƙirjinsa zanan da har yanzu bai fahimci na mene ba, lumshe idanunsa yayi yana mai da idanunsa akan J ɗinsa wacce take kwance ko harbawa ba tayi bare yayi tunanin lafiyarta,
Zuwa yanzu kam baya damuwa yasan Ubangiji ne kaɗai yasan abinda yake ɓoye, idanunsa ya ɗauke kana ya kashe shower, ya fito sanye da bathrobe jikinsa na zubar da ruwa, ko mai bai shafa ba, sai parfume daya fesa kana ya ɗauki wata Muslim thobe jalabiya Maroon color mai kyau ga wani laushi da take dashi, yana sanyawa yasa Mon mule slippers, ta can ƙofar baya yabi zuwa Masjid.

Yana zuwa ana tayar da Sallah hakan yasa ya zamana yana layin baya, bayan an idar ne kuma ya zauna a haka sallar Isshā ta samesa, sai daya gabatar da ita kana ya nufi part ɗinsa.

Yana shiga Bedroom É—insa ya samu Wayarsa na haske, ganin mai kiran ne kuma yasa yayi answering tare da manna wayar a kunansa, tare da kwanciya a saman bed É—in sa.

Shiru yayi yana sauraran abinda mai kiran yake faÉ—a, "Uhm"
Kawai yace bayan ya gama sauraran komai kana ya kashe wayar, jin baya jin yunwa ne yasa yaci Apple da Inibi, kana ya shiga bathroom ya watsa ruwa.

Wasu fararan Tartan check print pyjama ya sanya kana ya fesa turare tare da cilla strowbeery mouth freshnerh a bakinsa, kai tsaye royal bed É—in sa ya nufa tare da jawo sweet ya rungome duvet yaja ya rufe masu jiki babu jimawa bacci ya É—auke sa.

Washe gari
Tun safe da Mai Babban É—aki ta kira Abu Maleek bai dawo part É—insa ba, yana can tare da ita da Oumuu-Ayman da kuma sauran Aremo.

Yanzu ma yana zaune bayan ya dawo daga masjid ya ɗan zauna kusa da Oumuu-Ayman yana jin kansa duk a takure, ga kuma kallon da Bola take masa, ga MALEEK dake jikinsa yasa, hakan yasa duk ya kejinsa a takure sarai Oumuu-Ayman tasan bai san yawan mutane da kallo, hakan yasa tai masa banza tana jin yadda zungurinta tare da riƙe mata hannu, sosai take son ya saba da ƴan uwansa, to mutumin da zai wakilci dubban jama'a ga baki ɗaya kenan.

Mai Babban É—aki ce ta É—an sakace bakinta saboda naman da taci tace.
"An zauna da Sarkin Fada, da kuma dukkan wanda suke da ruwa da tsaki a naÉ—in Sarautar sabon sarki"

A tare Adams da Shakiru haÉ—i da Otun suka É—aga idanunsa suka kalli Mai Babban É—aki, Sharefddeen da Junaid kam kowa Wayarsa yake dannawa, dan wannan shirgin baya gabansu.

Gyara zama Queen Ayoola tayi tana faÉ—in.
"Ma sha Allah, to wa aka tsayar matsayin wanda zai zama tsarki na huÉ—u a wannan gari na Benin wanda zai shugaban cin Al'ummar Kanzaf damu baki É—aya"

Sanin cewa idan Mai Babban É—aki na magana babu mai tankawa sai an bada damar Magana hakan yasa Kowa yay shiru,
Mai Babban É—aki dai-dai-ta zamanta tayi cikin halin daddako domin yau bata tashi da rikicin ba cikin kamewa tace.

"Queen Ayoola Femi Zaki iya fita waje"
Mai Babban É—aki ta faÉ—a in a don't care manner É—in nan, ba tare kuma data kalli Queen Ayoola É—in ba.

Murmushi kawai Queen Ayoola tayi tana mai danne abinda ta keji a ranta kafin ta miƙe tana gyara zaman Alƙyabbar jikinta ta ɗan durƙosa tare da faɗin.

"Allah ya huci zuciyar mai Kanzaf da Alaafi baki É—aya"
Ta faÉ—a tare dayin waje, tana fita Mai Babban É—aki tace.
"Nasan kowa ya matso yaji wanda yake shirin zama King? Akwai meeting da yamma so a nan kowa zaiji komai kowa zai iya tafiya"
Ta faÉ—a tana É—aukan Apple ta sanya a bakinta, É—aya bayan É—aya suka shiga barin É—akin.

Da sauri Abu Maleek ya yunƙura zai tashi Oumuu-Ayman tayi saurin riƙe hannunsa, hakan yasa ya ɗan kwaɓe fuska tare da faɗin.

"Oumuu na Please"
Ya faÉ—a yana karyar da wuya, Mai Babban É—aki ce ta kallesa tana Murmushin jin daÉ—i kafin tace.
"Oumuu-Ayman ja yaron ki kuyi gaba kada ya cika min É—aki da mita, kamar wanda yake zaune da wasu dodona"

Kwaɓe fuska yay tare da kallon Mai Babban ɗaki yace.
"Allah Grandma duk kin cika mutane da surutu,uhm!"
Ya faÉ—a yana tashi tsaye tare da cire Maleek dake jikinsa.
"Kai ka sani, kaci caka baki yanzu zan ce na sake ka"
Mai Babban ɗaki ta faɗa tana miƙewa tare da shafa kansa tace.

"Allah yayi maka albarka, Ubangiji yayi riƙo da hannayenka Jalaluldeen, Allah ya kare ka daga sharrin mutum da aljan, mugun ji da mugun ya kiyaye ka daga su Zakina"

Kallonta yayi tare da yin gaba, kamar bazai magana ba sai kuma yace.
"Ameen badan halinki ba"
Ya faÉ—a yana ficewa daga parlon nata, kana ya nufi ficewa daga part gaba É—aya, ganin haka yasa Maleek binsa da gudu yana faÉ—in.

"Bàami zan kwana wajanka Please"
Shiru Abu Maleek yayi ba tare da yace komai ba, Bola dake tsaye tai saurin faÉ—in.

"Abu Maleek"
Cak ya tsaya ba tare daya juya ya kalleta ba, domin tuni ya ɗauki Muryarta, ganin ya tsaya yasa Bola dawowa gabansa ta tsaya, da sauri yayi ƙasa da idanunsa, tare da zubawa yatsun ƙafar Maleek ido, ganin hatta ɗan cindon dake ƙaramin yatsar sa yaron na tashi, mai san mene yasa yake jin faɗuwar gaba da zarar Maleek ya raɓu dashi ba.

"Abu Maleek, sai yaushe zaka fara duba na a matsayin mace, macan ma matarka, ko ka manta da cewa niÉ—in matar kace?"

Maleek ne ya sanya kuka ganin mahaifiyar tasa tana kuka, ƙara riƙe hannun Abu Maleek yayi yana shigewa tsakanin ƙafafuwansa,
Shi dai shiru yayi still kuma kansa yana ƙasa, yana jin jijiyoyin kansa na Miƙewa.

"Ni fa macace kamar kowa, shin kana tunanin bazan so kasancewa dakai bane Abu Maleek? Ban san me nai maka ba haka kuma bana da laifi wajan kasancewa matarka, ko kuma kai ƙaddarar ce ba zaka iya amsa ba kamar yadda na amsa? Yeah nayi believe kowa akwai nayi destiny ɗin so mu ɗauka dani dakai haka ƙaddarar mu take, kuma ta haka tazo, bana da laifi haka kuma ɗana Maleek bashi da laifi amma mene ya sanya baka son buɗe idanu ka gamu ne? Dan Allah Jalaluldeen accept me as your wife please"

Ta ƙare maganar tana haɗe hannayenta alamar roƙo, kana ta saki kuka tana yowa gabansa a ƙoƙarin ta na son shigewa jikinsa,
Saurin yin baya Abu Maleek yayi Maleek dake ƙafafuwan Abu Maleek ya saki Kuka yana ƙara riƙe Abu Maleek duk ya gigice.

Runtse idanunsa Abu Maleek yayi yana jin wani jiri na ɗibansa, nan da nan numfashinsa ya fara sama, ya shiga fisgarsa da ƙyar, ga wani duhu daya fara gani a cikin idanunsa, da alama ciwon daya jima bai ba shine yake shirin tashi.

Bola da bata fahimci komai ba ta ƙara nufarsa a ɗan gigice ya sanya duk hannayensa a saman shoulder ɗinta tare da matsawa da ƙarfi, wanda ya sanya Bola saurin sakin ƙara kafin tai magana yayi saurin yin gefe da ita tare da yin gaba yana rufe hancinsa, saboda wani hayaƙi daya tawo kai tsaye ya shige hancinsa ba tare kuma da sanin daga inda hayaƙin yake ba.

Ihu Maleek ya sanya yana tafiya wajan Bola rungome sa tayi tana sakin kuka itama.

Abu Maleek a daddafe ya shige babban side ɗin sa wanda yafi na kowa girma kyau da kuma tsaruwa, da ƙyar yake jan ƙafafuwansa yana tafe yana fisgar numfashi, a haka ya buɗe ƙofar shigowa side ɗin kana ya nufi part ɗin da yake rayuwa ciki, yana zuwa parlon Oumuu-Ayman na ajjiye Julde a saman kujera 3seater, wacce ta taimaka mata tai wanka tai sallah tare da sauya kaya zuwa wata silk Falling rose pattern nightdress masu mafifafan kyau, wanda suka tsaya mata iya cinya, ga yadda manya manyan cinyoyinta da suke a waje sai ƙyalli suke saboda gyara, abin mamaki kuma kawo lokacin har yanzu Julde bata fara period ba, sai brest da Allah ya wadata dasu,
Ta ƙara fari tai fresh kamar ƙwayar ƙwai, ga pink ɗinta sunyi kyau tare dayin wani bala'in pink, sai wahala hula mai gashi da Oumuu ta sanya mata tafin ƙafarta sanye cikin Aquaholic Slippers, tai kyau sosai kamar ba Julde ba.

Oumuu na zaunar da ita ta juya da ɗan sauri saboda ƙarar buga ƙofar da taji, gabanta ne ya faɗi saboda ganin Abu Maleek dake shirin faɗuwa dukkan jikinsa rawa yake, idanunsa a Lumshe da sauri tayi wajansa, Julde kam ƙara zama tayi tana tsotsar yatsarta tana jin daɗin fito da ita da Oumuu tayi.

"Innalillahi wa'inna ilaihir Zaki na, mene ya sameka Sabunallahu! Zaki what happened to

you kai da waye? Waye ta tare ka? Me akace maka? Ina ke maka ciwo? Ko wani ya baka wani abu kaci ne???"
Ta ƙare tarin tambayoyin nata murya a raunace, hanunsa ta riƙe cikin fusgar Numfashin ya fara kokawa da laɓɓansa kafin ya samu zarafin furta.
"Asthma,, Inhaler!!!!! Oumuu!!!!!!"
Ya faɗa yana yin baya kai tsaye ya faɗa saman kujerar da Julde take kai, kansa ya sauka a ƙirjinta saboda tsayin da yayi mata, da wani irin sauri Oumuu tayi waje.
Wani irin galabaitaccen numfashi Abu Maleek yaja tare da juyar da kansa inda yake jiyo wani sihirtaccen ƙamshi da ɗumi na dukan fuskarsa, da wani irin sauri ya cusa fuskarsa a cikin ƙir.......

Abu Maleek isn't free contact to subscribe 08119237616

If you read for free🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️

*_43-44_*
Ƙirjinta inda yake jiyo wani ƙamshi da kuma ɗumi na fitowa ta ciki, wani irin wahalallan numfashi ya ja da ƙarfi, yayinda jikinsa ya tsananta ɓari, idanunsa sun jajir.

Tsananin a zaba da kuma fitar hayyaci da suka ratsa gangar jikinsa ya haddasa masa wani irin matsanancin ciwon kai, nan da nan kuma jijiyoyin kansa suka fito tare dayin raÉ—a raÉ—a a saman goshinsa.

Kawo lokacin tuni ya fara ficewa daga hayyacinsa, saboda sosai ya shaƙi hayaƙin da bai san daga inda ya fito ba, hakan ya haddasa wa Numfashinsa cushewa tare da dunƙulewa waje guda.

Jikinsa na rawa kamar mazari ya ƙara manna fuskarsa a tsakiyar ƙirjinta inda yake jin wani mugun daɗi idan yayi hakan, a hankali kuma ya miƙa hannunsa tare da kama na Julde wacce take zaune.

Tun lokacin da taji kansa a saman ƙirjinta taji zuciyarta ta buga da ƙarfi, yayinda taji wani abu mai kama da fargaba na saukar mata a Zuciyarta, tsoro da zullumin rashin abinda yake faruwa ya wanzu a saman fuskarta, kallo guda zakai mata kasan tayi matuƙar razana.

Ga wani a zabban hucin Numfashinsa wanda yake fita da ƙyar yake sauka sauka a saman ƙirjinta zuwa fuskarta,
Ajiyar zuciya duk su biyun suka sauke lokacin da Abu Maleek ya manna tafin hannunsa a saman tsakiyar lallausan hannunta wanda ya sha ado da wani red É—in lallai da Oumuu-Ayman ta É—aura mata a Æ´an yatsun.

Kasa magana tayi itama ta shiga fidda numfashi saboda ba ƙaramin nauyi yayi mata a Jikinta ba,
Musamman ƙirjinta da take jin kamar zai rabe gida biyu, saboda yadda ya sanya kansa da kuma tulin gashin kansa ya danne mata ƙirjinta,
Hakan ya haifar da É—an tsayawar nata numfashi itama ta shiga fidda dashi a hankali.

Shiru tayi tare da sauke ajjiyar zuciya yana ƙara sauraran yadda bugun Zuciyarsu ke bugawa a tare dib! dib!! dib!! Haka zuciyarsu ke buga in one time kuma very fast, yadda numfashin nasu ke fita a tare kuma yake haɗewa waje guda,
Zaka fahimci Tabbas su ɗin abu guda ne, amma rashin sani kowa yaƙi amsar ƙaddarar da tazo masa.

Matse tafin hannunta dake cikin nasa yayi dalilin tsayawar da yaji numfashin sa yayi, kafin ya zagayar da ɗaya Hannun nasa zuwa bayan ququnta ya ƙanƙame shi da ƙarfi kana yaja wani irin wahalallan numfashin daya sanya Julde sakin kuka tare kifa fuskarta a saman tashi ba tare data sani ba.

Abu Maleek kama duk yadda kake tunanin halin da yake ciki ɓata baki ne, dan ma yana trying control ɗin kansa ne, bakinsa ya buɗe zai magana amma ya kasa domin, he can't say what was in his heart ba,
he can't explain how pain he feel in his heart, and it's difficult Mutum ya fahimci halin da yake ciki sai shi kaÉ—ai da mahalicci, the pain is unexplainable.

Shiru kawai yayi bayan ya ƙara manna innocent face ɗinsa a cikin ƙirjinta by mistake kuma laɓɓansa suka sauka a gefen nippy ɗinta da suke cikin rigar baccin.

Da sauri Julde ta matse idanunta saboda jin yadda tsigar jikinta take mimmiƙewa, hakan yasa taji kamar wani abu ke mata yawo a jiki like kiyashi, All her life bata taɓa jin irin abun nan a Jikinta ba, hakan yasa ta ƙara sakin kuka.

A hankali kuma hawayenta ke sauka a saman fuskarsa hakan yasa ya fara fidda wani gigitaccen numfashi, cikin fitar hayyaci ya ware laɓɓansa da sauri cikin wata kalar Muryar wacce take nuna ciwon daya keji yayi worse da yawa yace.

"Ya Jabbaruuu!!"
Ya faɗa yana taune lips ɗinsa tare da ƙanƙame Julde sosai a jikinsa yana jin kamar ya shige Jikinta ya wuta.

Cikin tashin hankali Oumuu-Ayman ta fita daga cikin Sashin na Abu Maleek, kai tsaye kuma ta nufi nata sashin tana zuwa ta shige bedroom, tare da nufar wata ƙaramar box ta sanya hannunta a jikin box ɗin ta kawo wuta, tana sanya yatsarta jikin tampering ɗin box ɗin ta buɗe, cikin sauri ta fara duba Drugs ɗin ciki, cikin Sa'a ta samu Inhaler nasa.

Gaba É—aya a gigice take hakan yasa ko tsayawa rufe box É—in ba tai ba, ta fice daga cikin bedroom É—in, kai tsaye wajan flat É—in nata tayi, tana jin yadda Hadimarta take mata magana, amma ina hankalin ta na can kan Abu Maleek.

Wanda suran ciwon nasa ya É—imauta ta, da sassarfa ta nufi Abu Maleek flat, a hanya taci karo da Adams, wanda yake tafe yana latsa Wayarsa da alama yana wani abu mai muhimmanci ne.

Kallon Oumuu-Ayman yayi yaga ba yadda ya saba ganinta ba, duk da cewa baya sakin jikin yin magana da ita sai ta kama Amma ya danne zuciyarsa,
Tare da zame wayar kunansa ya nufi wajan Oumuu cikin tafiyar ƙasaita yana zuwa ya kalli hannun Oumuu-Ayman zaro ido, saboda kaɗuwa da yayi sakamakon ganin Inhaler Abu Maleek a hannunta, sai kuma yayi saurin ɗauke tunanin da yake a ransa yace.

"Oumuu-Ayman lafiya dai ko?"
Kallonsa tayi cikin damuwa kamar zatai kuka tace "Adams jikin É—an uwanka ya tashi"
"Ikon Allah" Shine kawai abinda Adams ya faÉ—a kafin yace.
"Tunda ya dawo yayi ne??"
Kai ta girgiza masa Idanunta na kawo hawaye, kowa da rauninsa amma ita Abu Maleek shi ne nata raunin kafin tace.

"A'a wallahi, ko ciwon kai bai ba, kawai yanzu ina parlonsa naga ya Shigo riƙe da ƙirjinsa ya rufe fuskarsa da tafin hannunsa, hakan yasa na fahimci halin da yake ciki, Adams ina jin tsoro ban sani ba ko har a Madrid yana tasar masa ko kuma yanzu ne, ɗan uwanka yana buƙatar ka Adams"

Ta faÉ—a hawayen idanunta na zuba, sosai Adams yayi mamaki, domin rabon da yaga Oumuu na kuka ya manta, har rasuwar King Tunde Muhammad Jalal babu wanda zai ce yaga zubar hawayenta, amma yanzu dalilin Abu Maleek tana sakin Kuka.

Kai kawai ya jinjina yabi bayan Oumuu da kallo, kamar zai huce sai kuma yabi bayan Oumuu-Ayman É—in just to see yadda jikin Abu Maleek É—in yake.

Kasancewar ƙofar shiga babban Parlon abuɗe take yasa Oumuu-Ayman kai tsaye ta shige ciki, tana shiga ta nufi inda suke sai a lokacin ta tuna da Julde, wacce ta zaunar da ita a wajan,
Kallon yadda Julde take kuka wiwi tayi,
duk Jikinta rawa yake, yayinda shi kuma yake riƙe da ita zuwa lokacin, ko ido baya iyawa buɗewa,
sai amon sautin Muryar kukanta kawai da yake jiyowa,
sai kuma wani duhu da yake gani a cikin ƙwayar idanunsa.

Oumuu-Ayman na zuwa ta zauna gefensu,
tare da ɓalle Murfin Inhaler,
har zata sanya ta É—auke Abu Maleek daga jikin Abu Maleek,
sai kuma ta sauke ajjiyar tare da kallon Julde a hankali tace.

"Dai na kuka Daughter maza sanya masa wanann a baki, bari na É—ura yatsarki a inda zaki dinga dannawa"
Ta faÉ—a tana É—urawa Julde Inhaler a tafin hannunta kafin ta É—ura hannunta a saman bakin Abu Maleek tare da saita bakin Inhaler a cikin bakinsa, sai da ta tabbatar komai ya dai-dai-ta sannan tace.

"Stop cry My Daughter, idan kina kuka zuciyarsa zafi take, maza fesa masa Inhaler he will be fine in sha Allah"

Ta ƙare maganar tana shafa kan Abu Maleek tare tsorawa fuskarsa idanu,
Julde da har yanzu bata san meke damunsa ba, haka kuma bata san matsayinta a wajansa ba, yasa tana jan ajjiyar zuciya Jikinta na É—an rawa ta danna yatsarta a inda Oumuu-Ayman ta É—ura mata,
Wata ƙaƙƙarfar ajjiyar zuciya Abu Maleek ya sauke lokacin da Inhaler ta ratsa cikin bakinsa,
da sauri kuma ya zame hannunsa da ququnta ya É—ura saman hannunta dake bakinta,
kafin ya saita hannunsa a wajan na Julde ya shiga danna Inhaler da sauri da sauri.

Turo baki Julde tayi tana kwaɓe fuska kamar zata ƙara sakin wani kukan tace.
"Oumuu bana iya ba? To mene yasa yake yi da kansa? Ko baya son nawa ne"
Girgiza kai Oumuu-Ayman tayi tana faÉ—in.
"Is not like that Daughter, yafi yi da sauri saboda ya samu sassauci daga ciwon da yake ciki, kiyi masa addu'a Kinji"

Adams dake tsaye bakin ƙofa ya kasa koda mutsi ne, saboda mamakin da yayi masa yawa, tun shigowar sa idanunsa ya sauka akan ƙyakkyawar Yarinyar,
Wacce kallo yayi mata yasan shekarunta basu huce 17yrs ba, gefe guda kuma tunda Idanun zuciyarsa suka kalli Julde yanayin bugawar zuciyarsa tasa ya sauya, daga wani abu na daban zuwa wani abu wanda yake jinsa kamar so!

A hankali ya ƙarasa shiga Parlon kafin yace.
"Yaya jikin nasa?"
Ya tambaya yana ƙara ware idanunsa akan Julde, wacce kyahun da tayi a cikin idanunsa ɓata baki,
Wacece ita? Mene ya kawota cikin Alaafi? Har Kuma cikin sashin na Abu Maleek sashin da ko shi bai fiya shigarsa ba, saboda matakan tsaron da suke jikin ko wacce ƙofa, something is feshin,
Oumuu-Ayman da tayi shiru tana kallon yadda Abu Maleek yake sauke numfashi a hankali, da alama ya fara jin sassauci daga ciwon da yake ciki,
Idanunta ta É—aga ta kalli Adams ganin Gaba É—aya idanunsa ba akanta yake ba yasa ta juya, sai a lokacin data tuna da Julde na wajan, a ranta tace.

"Shikenan batun ɓoyewa ya ƙare"
Mema ya sanya ta fito da ita ne, yanzu bata da wata mafita wacce zata kare kanta da kuma ƙaryar da zata shimfiɗa akan Julde, cikin basarwa tace.

"Allahamdulillah, naga ciwon ya fara sauka, taimakamin na kaisa Bedroom"
A hankali ya zame idanunsa yana mai dashi akan Abu Maleek, wanda gumi ya shiga feso masa jikinsa kuma duk ya saki,
Shikam tunda ya fara shaƙar Inhaler yaji numfashin nasa ya fara sauka a cikin huhunsa, hakan yasa ya ƙara narkewa jikin Julde yana shaƙar Inhaler yana shaƙar ƙamshin dake fita a ƙirjinta, yayinda har kawo lokacin hawayenta bai tsaya ba.

Miƙewa Oumuu-Ayman tayi tare da ƙoƙarin janye kan Abu Maleek dake ƙirjin Julde, da sauri Julde ta kwaɓe fuska hawaye na sakko mata tace.

"Oumuu zai gudu fa, kice kada ya sauka Kinji"
Ta ƙare maganar tana ƙaryar da wuya like yadda Abu Maleek ɗin keyi,
Ganin haka yasa Oumuu-Ayman faÉ—in.
"A'a Daughter, É—aki zan kaisa fa, naga bacci zaiyi"
Girgiza kai Julde tayi tace.
"A'a Oumuu ni kibarsa ba kinci bashi da Lafiya ba?"

Adams dake Kallonta yace
"to ba kya jin nauyi ne? Kalleki ba kuma ki kallesa"
Shiru tayi Saboda jin baƙuwar Murya da tayi sai kuma tace
"waye wannan É—in? Shima É—an ki ne?"
Oumuu-Ayman dake janye Abu Maleek tana miƙar dashi zaune tace.
"Eh, yayan Ballowo ki ne"
Washe baki tayi haƙuranta da sukai fari yanzu suka bayyana kafin tace.
"To amma dai kana magana ko? Ba Irin Ballowo ne ba kai? Nama san zakai magana ai ina jin hakan a jikina"

Shiru yayi mata sai fuskarta daya tsorawa idanu, kafin a hankali ya sauke idanunsa zuwa cikin idanunsa da yake masa tsananin kama da dana Abu Maleek har blue É—in ciki iri guda ne, bambancin kawai nata a É—an juye suke, sosai surutun ya birge Adams.

Abu Maleek kam cikin dauriya ya ɗan aro jarumta ya sanyawa kansa, duk da cewa har kawo lokacin bai ji dai-dai ba, amma ya ɗan samu relief daga azabar ciwon da yake ciki, bisa taimakon Oumuu-Ayman ya miƙe tsaye gaba ɗaya kuma ya narke a jikin nata, ita dai Oumuu-Ayman bata tsaya biyewa Adams ba taja Abu Maleek zuwa can part ɗin da yake amfani dashi a cikin flat nasa.

Bayan shigewar su ne, kuma Adams ya gyara tsaiwarsa cikin son jin sautin zazzaƙar Muryarta yace.
"Ke kuma magana kike so? Cai cai cai haka?"
Ya faÉ—a yana kalon tsarin surarta, jerarrun teeths É—inta ta buÉ—e tace.
"To ai kurma ne kawai yake shiru da bakinsa ko? To kai yaya sunanka?"
Murmushi yayi sosai yana shafa kai yace.
"You Are beautiful, i mean kina da kyau sosai"
Ya faÉ—a yana Kallonta kafin kuma ya ware idanunsa saboda abinda yaji tace na.

"Haka a Rugar mu wasu suke faÉ—a, amma kasan mene?"
Girgiza mata kai yayi domin a tunaninsa tana kallonsa, jin shiru ne yasa Julde tura yatsarta a baki tana fara tsotsa kuma ta zame tace.

"Ayyah! Nikam ai ban taɓa ganin kyau ɗina ba, kai ma kana da kyau ne kamar nawa?"
Ta faÉ—a lokacin da idanunta yayi rau rau, da mamaki Adams yake Kallonta kafin yace.

"Kamar ya?? Mene yasa baki kallon kyan naki?"
Yarfar da hannayenta tayi Alamar ohhhu!! Sai kuma tace.
"To ai bana gani, nifa Makauniya ce, kai ma bana ganinka, haka ban taɓa ganin Ballowo ba, har muka gama zama a cikin jeji"

Wani irin buÉ—e ido Adams yayi saboda kaÉ—uwa da al'ajabi gadai idanunta sosai a buÉ—e babu wata alama data nuna ita Makauniya ce, cikin mamaki yace.

"Wacece ke? Daga ina kike? Wane ya kawo ki nan É—in tunda ke Makauniya ce, And wanne jejie kike magana"
Ya jera mata tambayar yana ƙara buɗe ido
Baki Julde za buÉ—e zatai magana sai kuma Oumuu-Ayman ta katse ta da faÉ—in.

"Daughter lokacin sallar Isshā yayi maza zo muje kiyi, kici abinci ki kwanta kinji ko"
Da sauri Adams ya juya a zuciyarsa yana faÉ—in.

"Ƙwarƙwara da ita tafi mutanan gida sakewa, duk laifin Daddy ne daya bata dama mtwss!!!!"
Ya faɗi hakan a ransa yana ɗan jan siririn tsaki gefe guda kuma ya fice daga flat ɗin cike da so da kuma ƙaunar Yarinyar daku sunanta bai sani ba.

Ƙara narkewa jikin duvet ɗinsa Abu Maleek yayi yana jin wani iri sam ɗumin duvet ɗin bai gamsar dashi ba, duk da cewa a cikin halin ciwo yake amma ya fahimci ɗumin jikin Julde daban yake dana duvet ɗin, kuma har A.c Oumuu duk sai wani blue light ta bar masa,
Marai-raice fuska yayi yana taune leɓansa yana jin yadda kuma numfashin sa ke dai-dai-to wa, lumshe idanunsa yayi sai kuma ya saki tsaki saboda abinda yake masa gizo a cikin idanunsa,
A haka bacci ya É—auke sa.

Washe gari
4:10
Ya shiga motsa idanunsa Wanda sukai masa nauyi sosai, wani numfashi yaja cikin Sa'a kuma yaji Numfashinsa yayi nrml kamar ko yaushe, cukurkuɗewa yayi cikin duvet ɗin kafin ya miƙe zaune a hankali bakinsa ɗauke da addu'a,
Ya motsa fuska yayi jin yadda gaba ɗaya jikinsa yayi weak, lumshe idanunsa yay yana taune leɓansa da sauri kuma ya buɗe tunawa da ko sallar Isshā bai ba, jiki a sanyaye ya miƙe tsaye,
A hankali ya miƙa hannunsa ya kunna light ɗin bedroom ɗin, cikin nutsuwarsa da kamewa irinta masu sarauta ya nufi bathroom,
Ruwa mai É—an zafi ya sanya rabonsa da ruwan zafi kam har ya manta, bayan yayi wanka yayi brush ya É—aura alwala, handrayer,
Ya ɗauka sai kuma ya ajjiye yana langwaɓar da kansa gefe saboda gaba ɗaya bashi da wani kuzari.
Jikinsa yaja zuwa bedroom yana zuwa yaja stool ya zauna,
Wani cream ya shafa mai ƙamshi da laushi kana ya shafa wani Ginger Geminal Oil -hair bayan ya shafawa kan nasa mai ne ya ɗauki Luxury Beard Oil ya shafa a sajansa zuwa gemunsa, nan da nan ya ɗauki ƙamshi da kuma ƙyalli.

Wata lallausar White kaftan ya ɗauka mai gajeran hannu ya sanya bayan ya sanya pat da trouser, a hankali ya jawo wata ƙatuwar prayer mat ya shimfiɗa cikin nutsuwa kuma ya tayar da sallah, bayan ya idar ya zauna har lokacin sallar Subhi yayi jiki a matuƙar sayaye ya gabatar da sallar dan bazai iya zuwa Masjid ba, yana idarwa ya zame rigar jikinsa ya zauna da trouser nan na ɗewa yay cikin duvet nan take bacci ya ɗauke sa.

Gaba É—aya suna zaune saman dinning area kasancewar yau Friday ne, Salimerh dake shan coffee ta kalli Oumuu-Ayman tace.
"Oumuu-Ayman kwana biyu banga Zaki ba, ko kuma miskilanci nasa ne ya motsa a kanmu"

Girgiza kai Oumuu-Ayman tayi tana ajjiye spoon É—in hannunta tace.
"Kwana biyu baya jin daÉ—i Asthma É—insa ya tashi tun shekaran jiya"
A gigice Salimerh ta miƙe tana faɗin.
"Subuhanallah, amma Oumuu-Ayman mene yasa baki faÉ—a min na duba shi ba?"
Ta faÉ—a cikin tausayin yayan nata, Murmushi Mai Babban É—aki tayi tace.
"Ai da sauƙi nima yanzu naje dubasa yana ma bacci, kuma naga yau ɗin da safe har wajan tsuntsayen sa yaje, ƙila zuwa Yamma ya fito"

Ajjiyar zuciya Salimerh ta sauke sai yanzu hankalin ta ya kwanta, a hankali ta zauna ta fara cin abinci, a ranta kuma tana faÉ—in.
"Ka ƙara haƙuri, haƙiƙa azzalumai sun Cutar da rayuwarka, Amma komai yazo ƙarshe Lokaci kawai nake jira lokacin da gaskiya zata bayyana kanta"
Ta ƙare maganar zucin tana Miƙewa domin tafiya makaranta.
Queen Ayoola, Bola, Adams, Shakiru ba wanda yayi magana sai Sharefddeen da yace.

"Allah sarki Zakin Oumuu-Ayman our champion har yanzu Asthma bar barshi ba, Allah ya ƙara lafiya zan dubasa zuwa anjima"

Miƙewa Oumuu-Ayman tayi tana faɗin "Ameen ya rabbi, sai kazo"
Ta faÉ—i hakan ne kuma domin tasan Sharefddeen bashi da Matsala, da wani irin kallo Queen Ayoola tabi bayan Oumuu-Ayman dashi, Bola ce ta numfasa tace.

"Dan Allah Oumuu-Ayman na biyoki na dubasa??"
Ta ƙare maganar Zuciyarta a karye, Allah ya gani tana son mijinta ciwonsa kuma dole ya shafe ta, Kallonta Oumuu-Ayman tayi kafin tace.

"Yana bacci yanzu, amma yana tashi zan nema maki iso wajansa"
Ta faɗa tana yin gaba zuwa fita daga cikin baban flat ɗin family ɗin baki ta isa zuwan cikin asalin harabar Alaafi ɗin, nan da nan Barori da Fadawa suka shiga zubewa suna gaida ita, kasancewar ta ƙwaƙƙwarar late King bai sanya sun hana bata girma ba, domin soyayyarta ƙarara ta bayyana a fuskar Late King Tunde Muhammad Jalal hakan yasa Kowa na Alaafi yake girmama ta fiye da Asalin matarsa Queen Ayoola, Queen Roomana wannan mai gaba ɗaya ce,
So da ƙauna ko ina nuna mata yake.

Kai tsaye wajan Dawakai ta nufa fa, Sarkin Kilisa na ganinta ya miƙe tsaye yana zubewa tare da gaisar da ita, Murmushi tayi sosai kafin tace..
"Ina fatan ana kula da dawakan Jalaluldeen Tunde Muhammad??"
Cikin girmamawa yace.

"In sha Allah, kullum cikin hidimta masu ake sunyi kyau da kuzari sosai ai zaiji daÉ—in ganinsu"
Juyawa tayi ganin ba kowa yasa tace.
"Yaya Khaleluddeen yake? Fatan yana cikin ƙoshin lafiya?"
Ƙasa yayi da kansa yace.
"Ya shugabanta Khaleluddeen yana cikin ƙoshin lafiya, kamar yadda kika buƙaci na bawa matata ta kula dashi har zuwa lokacin da zaki buƙace sa"
Numfashi ta sauke cikin jin daÉ—i tace.
"Ma sha Allah, ina godiya kwarai sai na sake dawowa"
Ta faÉ—i haka tana juyawa, wajan Shanu ta nufa ta amshi Madara mai zafi wacce aka tasu a idanunta kana aka zuba mata zuma akai.

Kai tsaye flat É—in Abu Maleek ta nufa,
Fitowar sa kenan daga cikin part ɗin da yake kwana, yana sanye cikin wasu Sleeveless jersey tank top wacce take milk sai tracksuit trouser mai kyau shi kuma black, yana tafe a hankali saboda rashin kuzarin da har yanzu bai samu ba, hannunsa riƙe da Inibi yana sha, sai sweet dake hannunsa,
Kai tsaye babban Parlo ya nufa inda yake saka ran ganin Oumuu-Ayman yunwa yake ji sosai,
Yana fitowa ya buÉ—e baki yana faÉ—in.

"Oumuu! Oumuu!! Oumuu na fito yunwa ciki na please"
Ya faɗa yana lumshe idanunsa tare da zubewa a saman kujera yana ajjiye sweet, jin zuciyarta ta buga da ƙarfi ne yasa ya ɗan marai-raice fuska tare dasa hannu ya riƙe saitin wajan, mostin da yaji ne ya sanya ya buɗe idanunsa kai tsaye kuma idanunsa ya sauka akan Julde wacce take bacci a saman kujera ta juya tare dayin miƙa, gaba ɗaya tayi baya zata faɗi, hakan yasa ya miƙe yana jan tsaki tare da nufar inda take kafin ya ƙarasa yaji ta saki wata iriyar......

Abu Maleek isn't free contact to subscribe 08119237616
Kiji tsoran Allah🥰

*_45-46_*
Miƙa a hankali kuma ta sauke ajjiyar zuciya tare da mirginawa ta koma baccin ta, tana haɗe Jikinta waje guda saboda sanyin A.c, domin ko sanyin gari babu a flat ɗin na Abu Maleek ko ina a rufe yake.

Ganin ta gyara kwanciyar nata ne ya sanya shi yin baya tare da komawa saman kujera ya zauna, shiru yayi zuciyarsa fal tunani, ganin tunanin na son yi masa yawa ne ya sanya ya ɗauki remote ya kunna t.v, duk channel ɗin da yakai sai yaga suna love serious tsaki yaja murya can ƙasa yace.

"Uhm! Iskanci ko ina ba dole mutum ya lalace ba idan yana kallon wannan shirman"
Ya faÉ—a yana saurin sauya channel daga telemondo zuwa zee world, lumshe idanunsa yayi a hankali kana ya shiga sauke ajjiyar zuciya, kafin a hankali ya buÉ—e idanunsa tare da sauke ganinsa akan wani mutum dake fuskar t.v,
Yanayin shigarsa mutumin ya tabbatar da cewa sarki ne, ƙara ware idanunsa yayi sosai, ganin yadda yake zazzaga mazifa, yayinda matansa suke gefe da alama kuma shine da gaskiya.

Idanunsa ya mayar ƙasan t.v haka nan ya samu kansa da duba sunan film ɗin ganin an sanya Johda and akbar yasa ya tabbatar da cewa mijin shine Akbar matar kuma Johda amma sauran matan fa?? Jalaluldeen Muhammad Akbar ne ya zare ta kobin hannunsa lokacin daya samu labarin ɗan gidan Mahmanga wacce ya kewa kallon uwa ya shigo palace ɗin ya kashe masa babban amininsa kuma ɗan uwansa..

Haka Abu Maleek ya wanzu a parlon yana kallon Film ɗin Johda and akbar yana nan zaune har aka gama episode ɗin ranar aka tsaya a wajan da Akbar yake ƙona kujerar Sarauta saboda baƙin ciki da kuma tashin hankali, yace kujerar bata haifar masa da komai ba sai damuwa, ko burinsa yaga ya mallaki kujerar dan haka bata da wani Amfani shine ya sanya ya cilla mata huta.

Sauya channel yayi zuwa International channel wato (Aljazeera) Ajjiyar zuciya ya sauke tare dayin baya ya lafe saman kujerar tare da lumshe idanunsa,
Tunani ne fal ransa, haka nan kuma tunaninsa ya ƙara ta'azzara tunda ya kalli Johda and akbar, wato sarauta banzar abace, musamman yadda yaga palace ɗin su Akbar take, Masarauta iya Masarauta, amma kowa son zuciyarsa yake bi, mutane kaɗan ne masu tsoran Allah,
Ƙara fesar da iska yayi daga cikin bakinsa, wato zafin mulki sai ya sanya ka kashe ɗan uwanka?? wannan tunanin Shine a ransa kafin ya ja table ya ɗura fararan ƙafafuwansa yana jan tsaki a cikin ransa yace.

"Shima Akbar yayi haÉ—a ma, mata uku kamar wani maye, Queen Johda, Queen Rukayyah, Queen Salima"
Ya faÉ—a yana sanya hannunsa tare da shafa sajan fuskarsa yana É—an fidda numfashi kaÉ—an.

Oumuu-Ayman ce ta shigo cikin Babban Parlon hannunta riƙe da wata ƙwarya mai kyau anyi mata zanan tambarin sarautar, tunda ta shigo idanunta ya sauka a kansa yana zaune ya lumshe idanunsa tare miƙar da ƙafafuwansa a saman table,
Wajansa ta nufa tana sakin Murmushi tana zuwa ta ajjiye ƙwaryar hannun nata a saman wani table ɗin daban, kafin ta juya ta nufi cikin wani wanda da alama kitchen ne, plate ta ɗauka ta zuba masa alkali da bakilawa, sai kuma wani da zuba masa tarkacan fruits domin yau abincin Masarauta take son yaci.

Bayan ta gama jera masa komai a table É—in ne ta nemi waje kusa dashi ta zauna tare da faÉ—in.
"Zaki your breakfast is ready"
Idanunsa ya buÉ—e a hankali ya kalleta sai kuma ya É—auke idanunsa tare da kawar da abinda yake ransa, table É—in ya tsorawa idanu kafin da sauri ya kalli Oumuu-Ayman tare da faÉ—in.

"Oumuu what is this??? Nifa ba wannan ba"
Ya faɗa yana marai-raice fuska tare da langwaɓar da kansa gefe guda alamar shi ba'ai masa dai-dai ba,
Idanunta ta É—auke daga garesa bayan tayi masa wani irin kallo sai kuma tace.
"Abinda za kaci yau kenan, na tsara maka time table na duk abincin daza kaci, Breakfast, lunch, dinner, bayansu duk abinda aka baka ban yarda kaci ba"
Ware idanunsa yayi sosai kamar bazai magana ba sai kuma yayi baya yana faÉ—in..

"Gaskiya Ni bazan iya cin wannan abun ba, mene wannan abun a duƙunƙune kuma??"
Sosai abin ba ƙaramin mmki ya bata ba, musamman yadda taga yana narke fuska hakan ya tabbatar mata da gaskiyar abinda zuciyarsa yake faɗa,
Tana jin yadda yake mita tai masa banza haka ta bashi Alkalin tauna É—aya yayi yace shifa sam bazai ci ba,
Sai ma ya motsa fuska yayi tare da Miƙewa tsaye yana faɗin.

"Oumuu wannan ai a ciki zai tsaya kawai aiyi wani kamar maciji, uhm"
Ya faÉ—a yana shigewa cikin part É—insa kai tsaye kuma bathroom ya huce ya É—aura alwala jin ana kiran sallar zhur, bayan ya fito ne ya samu Oumuu zaune da Julde tana bata Abinci,
daga kallo ɗaya da yayi musu bai sake ba ya nufi ƙofar baya kai tsaye ya shige masjid.

Julde ta ɗan kwaɓe fuska tare da faɗin
"Oumuu to baya magana ne wai shi??"

Ta faɗa tana shagwaɓe wa, kamar zatai kuka.
Murmushin kawai Oumuu tayi domin ta daÉ—e da fahimtar Julde matan nan masu surutu, gashi kuma Ubangiji na neman haÉ—ata da miskilanci miji wanda gane masa sai addu'a.
Fresh milk ta bata tana faÉ—in.
"Yana magana mana,ba kiji muna hira dashi ba"
Rau rau haka idanunta suka kawi ruwa kafin ta tura baki gaba tace.

"Oumuu to ni mene yasa ba yayi min? Ko dan yaga bana gani ne, Allah Oumuu yanzu ji nake dama iduna zai buÉ—e naga Ballowo nasan ba wani kyau ne dashi ba"
Wani irin Murmushi Oumuu-Ayman tayi kafin ta ɗaga Idanunta a sanyaye ta kalli bakin ƙofa,
haɗa ido sukai da Abu Maleek wanda yake tsaye jinjine da ƙofa ya a harɗe hannayensa waje guda,
Kallon yadda ya haÉ—e fuska tayi waje guda kafin ta É—auke idanunta tana danne dariyar dake shirin kwace mata tace.

"Eh gaskiya bai cika wani kyau ba, gashi nan da manyan idanu,
da gashi har wuya kamar wani buzu,
sai tsayi da faÉ—i kamar basamude,
kai abinda zai wanda ya gani"
Oumuu-Ayman ta faÉ—a tana sakin wata lafiyayyiyar dariya mai ban sha'awa,
Abu Maleek kam cika yayi fam sai bakin yarinyar daya tsorawa idanu ko yawo bata haÉ—iya sai É—an ban zan surutu kamar ako.

Julde dake sauraran abinda Oumuu-Ayman take faÉ—a ne yasa ta karyar da wuya tace.
"Ayyah, kenan shi yasa baya magana? Oumuu Kice yana kulani mana"
Ta faÉ—a kamar zatai kuka,
Daga bayansu sukaji ance.
"Ni zan kulaki idan shi yaƙi, har labarai zanna baki ai"
Washe baki tayi fararan haƙuranta suka bayyana har wani haske suke fiddawa kafin tace.
"La!! Yayan Ranar ko Oumuu, shi kam yana da kirki"
Da mamaki Oumuu-Ayman ta juya tana kallon Adams mene ya sanya masu tsaron flat ɗin Abu Maleek suka basshi ya shigo? Idanunta ta ɗauke daga kallon Adams kana ta miƙe tsaye tare da shigewa bedroom ɗin da Julde take kwana,
Tayi hakan ne kuma domin ta haÉ—awa Julde ruwan haka, dalilin kuma hakan zai sanya ta janyeta daga wajan Adams.

Da idanu kawai Abu Maleek yake kallon É—an uwansa Adams da ita kanta Julde mamaki ya kamasa, ganin yadda Adams É—in yake ta jan Julde ta surutu,
Hakan nan yaji zuciyarsa babu daɗi ransa ya ɓaci ga wani mugun haushin yarinyar daya cika masa zuciya,
Mai makon ya shigo sai kawai ya fice tare da nufar Lambu.

Adams kam duk abinda Abu Maleek yana sane dashi, yana son ya Fahimci mene halaƙarsa da Yarinyar amma ya kasa fahimtar hakan, saboda yadda fuskar Abu Maleek take a ɗaure hakan yasa bai fahimci komai ba.

Gyara zama yayi idanunsa akan Julde yace.
"Uhm what's your name? I mean menene sunanki beauty?"
Shiru tayi sai kuma tace "Naji ƙamshin turaren Ballowo shi ne ya shigo?"
Ta faÉ—a tana narkar da fuska, da rashin fahimta yace.
"Ballowo?? Waye haka kuma?"
Cikin siririyar muryarta tace "Oumuu tace sunansa Jalaluldeen amma ana ce masa Abu Maleek to Shine Ballowo ai"
Shiru yayi yana nazari kafin ya É—an cije baki yace.
"Nagane, ba shi bane ƙamshin turarena kikaji"
Girgiza kai tayi Idanunta na kawo ruwa tace.
"Allah shi ne gashi nan naji zuciyata yana harbawa, kuma sai yazo waje kawai na kejin hakan"
Ta faɗa Idanunta cike da hawaye, wani abu mai ɗaci Adams ya haɗiye domin jiya kawai da yaga yarinyar tayiwa zuciyarsa mugun kamo, da ƙyar ya iya bacci daya rufe idanunsa ita yake kallo.

Ajjiyar zuciya ya sauke tare da faÉ—in "Ok Amma kina son idanunki su buÉ—e ko?"
Da sauri ta É—aga kai tace "Eh ko dan naga Ballowo ai"
Jinjina kai yayi yace "Ok zanwa Oumuu-Ayman magana za'a fita dake waje ayi maki aiki idanunki su buÉ—e"
Wani daɗi ne ya lulluɓe zuciyar Julde wanda ya sanya tayi ɗan tsalle a saman kujera hakan yasa brest ɗinta juyawa wanda suke a tsaye ƙam,
Cikin farin ciki tace "Dan Allah da gaske kake? Idanuna zai buÉ—e?"
Murmushi yayi mai sauti domin komai na Julde birgeshi suke kafin yace.
"Eh mana, amma kiyi min al'ƙawari"
Da sauri ta É—aga kanta tace "Nayi maka Allah tunda idanuna zasu buÉ—e"
Ɗan juya yayi sai kuma ya sauke numfashi ganin babu kowa ne yasa shi faɗin "Kimin Al'ƙawarin ba zaki taɓa auran Ballowo ɗinki ba?? Kimin Al'ƙawarin ba zaki taɓa son sa ba"
Shiru tayi a zahiri tasan kalmar Aure kuma tasan daman ai Ballowo É—inta bazai ce zai aureta ba, sannan bata san soyayya ba tana jinta dai a baki,
Ya take? Ya daÉ—in ta take duk bata sani ba, ganin tayi shiru yasa Adams faÉ—in.
"Ko baki son idanun naki ya buÉ—e ki fara gani kamar kowa beauty?"
A sanyaye tace "A'a ina so, kuma na baka al'ƙawari"
Wata lafiyayyiyar ajjiyar zuciya Adams ya sauke yana jin wani daÉ—i na ratsa masa zuciya kafin ya É—an ware idanunsa yace.
"Ok Yaya sunanki, Nima gaya min tunda Oumuu-Ayman ta faÉ—a maki nawa ko?"
Ji tayi Jikinta duk yayi sanyi ba tare da sanin dalilin faruwar hakan ba tace.
"Hawwa'u Julde"
Lumshe idanunsa yayi yana jin daɗin sunan nayi masa yawo a cikin ƙwaƙwalwarsa.

Oumuu-Ayman ce ta fito fuska a sake tace "Zo Daughter kiyi wanka ki Sallah ki kwanta ki huta"
Hannu Julde ta miƙawa Oumuu-Ayman haka ta miƙar da ita suka nufi ciki,
Gyara zama Adams yayi domin ya É—auki alwashin bazai bar gurin nan ba sai an faÉ—a masa Matsayin Julde a cikin Alaafi.

A hankali yake tafiya cike da nutsuwa da kamewa ga wata haiba da kwarjini daya mamaye ilahirin saman fuskarsa,
Yana tafe yana sauke numfashi tare da Ajjiyar zuciya a jajjere yana jin ransa na ƙara ɓaci,
Ga kuma gudun da zuciyarsa ta ƙara, a haka ya isa haɗaɗɗan Lambun nasa mai ɗauke da shukoki da furanni dabam dabam,
Ga kukan wasu tsuntsaye dake tashi a hankali yake saukar da nutsuwa kuma a zuciya,
Gusa da ƙoramar dage gudana a wajan ya ƙarasa, tare da zama a wajan wata duguwar kujera ta hutawa,
Jikin kujerar yabi ya ɗan kishin giɗa yana sauke ajjiyar zuciya tare da lumshe idanunsa, a hankali kuma ya zura ƙafafuwansa cikin ƙoramar,
Ya shiga wasa da ƙafafuwansa nasa yana jin daɗin sanyin ruwan nayi masa daɗi,
Wayarsa dake aljihu ce ta fara ƙara yana ji amma bai ko motsa ba, sai da akai wajan 5 miss call kafin ya zaro haɗaɗɗiyar wayar tasa,
Ganin sunan Salimerh yasa yayi answering call tare da sawa a speaker.

Daga can ɓangaren kowa Salimerh ce, zaune a cikin mota Dawowar ta daga makaranta kenan, har zata shiga ciki sai kuma ta tsaya tare da ɗaukan waya ta kira Abu Maleek ajjiyar zuciya ta sauke lokacin da taji ya ɗaga kiran.
Kafin a hankali ciki ƙasa da Murya yadda ba zata damesa ba tace.
"Fatan zaki yana cikin koshin lafiya?"
Ta faɗa tana ƙara gyara zama, sanin ba lallai yayi magana bane yasa ta faɗin.
"Zaki dan Allah dukkan abinda zai fito a hannun Mumy kada kaci, ko ruwa ta baka kada kasha"
Ta faÉ—a cikin raunin Murya.

Abu Maleek dake sauraranta ya É—an gyara kwanciyar sa yana ware idanunsa tare saukar da idanunsa a saman nunannun gauva wacce sukai manya gwanin sha'awa,
Kafin ya Fito da tongue ɗinsa ya shiga taune leɓansa tare da sauke ajjiyar zuciya yace.
"Uhm"
Ya faÉ—a cikin wani Emotional sound domin tun É—azo ya kejin jikinsa duk yayi weak.

Jin "Uhm" ɗin da yace ne yasa Salimerh fahimtar cewa ƙarin bayani ya keso cikin nutsuwa da kuma dadɗan kalami tace.
"I don't means anything Zaki, kowa da kalar zuciyarsa, Mumy mahaifiyata ce, amma kwanan na fahimci wasu muna nan abu a tare da ita, to dan Allah ka tayani tseratar da rayuwarka, idan kayi hakan zaka taimake ni ƙwarai wajan ganin nayi aikina ba tare da wani matsala ta faru ba, a yanzu hana da shaidar da zan nuna maka amma Tabbas ina zargin mahaifiyata akan abubuwan da suke faruwa a cikin Alaafin, Dan Allah Zaki daga nan har abada kada ka sake bawa Mumy dama a kanka, Kada ka sakar mata fuskar da zata baka wani abu tace kaci"

Ta ƙare maganar Muryarta na rawa kamar zatai kuka,
Tunda ta fara maganar yake sauraranta yake kuma fahimtar kalaman nata, amma tayaya Mumy zata cutar dashi? Baya tana bashi maganin damuwa a lokacin da zuciyarsa take masa ciwo? Wannan maganar ma ta sanya yaji yana ƙaunar zuwa wajan Mumy yaji idan zai samu abinda take basa.

Jin yayi shiru ne Kamar baya fahimta yasa Salimerh faÉ—in.
"Please Zaki saboda Allah ba danni ba"
Ganin tana shirin sauya masa lissafi yasa a É—an kasalance ya buÉ—e baki yace.
"Ok!"
Ya faÉ—i hakan yana kashe kiran nata,
Kafin a hankali ya miƙe jin ana sallar Asar, ko flat ɗin bai koma ba ya nufi Masjid.

Oumuu-Ayman ce ta kalli Adams tace.
"Me kace?"
Ta faÉ—a like batai understanding maganar tasa ba, bai damu ba domin shike nema a wajanta dan haka ya gyara zama yace.
"Wacece wannan Julden? Mene haÉ—in ta da Alaafi??"
Murmushi Oumuu-Ayman tayi tace.
"Ba kowa bace ita É—in face sabuwar Hadima wacce ake sanya ran zata zama Amintacciyar Hadimar sabon King"
Jinjina kai yayi cike da gamsuwa kafin yace.

"Zan Æ´antar da ita, domin naji kamar ina sonta Oumuu-Ayman, kuma zan fita da ita waje domin a gyara mata idanunta"
Kallonsa kawai Oumuu-Ayman tayi tana Miƙewa tsaye tace "To babu matsala za muyi magana da Mai Babban ɗaki, batun ƴantar da ita kuma baka da wannan damar Aremo Adams Tunde Muhammad Jalal"
Ta faɗi hakan tana shigewa bedroom ɗin Julde tana zuwa ta sameta har bacci ya ɗauke ta, Abu Maleek kam bai dawo cikin flat ɗin nasa ba sai bayan sallar Isshā domin daga Lambun nasa gidan gonarsa ya shige.

Yana dawowa wanka yayi ya shirya cikin wasu Maroon É—in Payjmas masu kyau, kana ya ja sweet ya rungome.

Washe gari
Da yamma a can bayan Masarauta cikin wani ƙaramin ɗaki wanda ciyayi ya lulluɓe, wata mata ce tsaye akan wata wata magidanciyar mace, wacce ta cure Jikinta wace guda, jikin nata sai ɓari yake kafin a hankali ta buɗe baki tace.
"Ban sani ba, ban san inda take ba, bana da Labarin komai akai, ki yarda dani"
Dariya matar dake kanta tayi kafin cikin fusata ta ɗaga hannu ta shararawa mai maganar mari tare dasa ƙafa ta danne mata ciki da ƙarfi kuma tace.

"Ohhh! Ba zaki faɗa ba? Munafuka ƙarya kike, babu wanda King Tunde Muhammad Jalal yake bashi amana yake faɗa masa sirrinsa kamar ke, Tabbas a wannan karan idan kikai gardama ba Iya kan ran King Tunde Muhammad Jalal zan tsaya, zan taɓa abu mafi suyiwa a Ranki, zan nakasta jikinki ko kuma na kawar dashi daga Duniyar baki ɗaya, wallahi billahi idan baki faɗa min inda TASWIRAR Masarautar nan take ba, zaki mamakin abinda zai aikatawa JALALULDEEN TUNDE MUHAMMAD JALAL"

A gigice matar ta riƙe ƙafar mai maganar tana faɗin.
"Duk abinda zaki aikata Kada ki taɓa Zaki, he's innocent Zaki ladama idan kikace a wannan karan zaki ƙara cutar dashi, ki rabu da Zaki ki rabu da King Tunde Muhammad Jalal duk abinda zaki ya tsaya iya kai na"
Ta faɗa tana sakin kuka, tare da ƙara riƙe ƙafar matar,
Wata dariyar matar tayi tana gyara tsawarta kafin tace..
"Au ashe fa maki da labari ko? Yanzu wajan 30days sa rasuwar King Tunde Muhammad Jalal kenan kinga Jalaluldeen kawai ya rage min idan har baki faÉ—a min inda zan samu taswirar da za'a iya fita da kaya a cikin Alaafi ba tare da kawo ya gani"
Cikin KaÉ—uwa da tashin hankali matar tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Mijina ya rasu??? Kin kashe min miji....,"
Katseta tayi da faÉ—in
"Uhm ba kiga komai ki zauna kada ki faÉ—a min Inda Taswirar take zuwa gobe zaki samu labarin mutuwar É—akin ki"
A gigice matar ta ɗaga Idanunta kana da ƙarfi tace "Zanan Taswirar yana ƙirjin Jalalu.....

😍👏🏻 Ayi weekend lafiya, mun kusa zuwa wajan daɗin kamar yadda na faɗa ba sauri nake ba, sannu a hankali za kuyi farin ciki...

Abu Maleek isn't free contact to subscribe 08119237616

*_47-48_*
"Ƙirjin Jalaluldeen" wata iriyar juyawa matar tayi tare da sauke idanunta akan wacce take gabanta tace "what!? Zanan Taswirar Alaafi a ƙirjin Abu Maleek? How can that be possible? Lallai Kunyi amfani da iliminku kun nuna min cewa ban iya komai ba, amma a wannan karan zan nuna maku cewa ban fito ba sai dana shirya, Tabbas zaku gane cewa ni murucin kan dutse ce"

Ta ƙare maganar tana sakin wani shu'umin e mai ɗauke da Zallar mugunta haɗi da mugun nufi a hankali kuma taja baya tare da neman wajan zama ta zauna saman kujera cikin nutsuwa da izza tace.

"Lallai kun raina ni, kuna da tabbacin cewa akwai mai farautar zanan Taswira wannan dalilin ya sanya kuka rasa inda zaku zana Taswirar sai jikin Abu Maleek? Well-done, what a great idea? Waye mai wannan tunanin tsakanin ko ukun nan?"
Shiru tayi tana kallon idanun matar dake gabanta wacce har zuwa lokacin bata daina kuka ba, saboda tashin hankali da take ciki, ga mutuwar King Tunde Muhammad Jalal data risketa a yanzu tayi mugun gigita mata lissafi, hakan yasa take kuka bil haƙƙi da dukkan Zuciyarta, tayi baƙi ta rame, saboda rashin saboda da kuma rashin Abinci wanda bata samun ishesshe ta sanya a cikinta.

Miƙewa Matar tayi tana gyara ƙyakkyawar sutturar dake Jikinta, cikin isarta tace.
"Any way kin taimaki rayuwar ɗan ki, da kuma kanki gaba ɗaya kuma idan ina da rai da lafiya wallahi sai naga ƙarshen Abu Maleek na maki wannan Al'ƙawarin"

A gigice Queen Roomana wacce kanta yake a ƙasa ta ɗaga Idanunta cikin sabon tashin hankalin daya shigeta take bin matar da kallo kafin a hankali ta sauke Ajjiyar zuciya cikin ranta take faɗin.

"Uhm Rashin sani yafi dare duhu, ina mai tabbatar maki da cewa duk ranar da kika yi gigin taɓa Zaki da niyyar samun zanan Taswirar nan ina mai tabbatar maki sai dai wata bake ba, duk yadda kike tunanin Alaafi ta huce haka, tsananin tsaro da kuma kariyarta basu taɓa bari ki samu abinda kike so ba, wannan dalilin ya sanya komai na Alaafi a shirye yake, koda kin kashe Abu Maleek kinyi banza domin ba iya jikinsa kaɗai wannan zanan Taswirar take ba"

Da sauri matar ta juya tana kallon Queen Roomana kafin ta nuna ta da hannu tace.
"Magana kikai? Did you just talk back at me Roomana???"

Girgiza kai kawai Queen Roomana tayi tana jin zuciyarta wani irin bugawa, tsoro da fargabar abinda zai samu Abu Maleek ya cika mata zuciya, so take tace ko sauya É—aya takk ta fita da ita taga Zakinta,Amma ina bata da wannan damar tasan har abada ita da Abu Maleek sai dai a darin Salam, domin zuciyarta ka gab da muguwa Abubuwa sun taro sun yi mata yawa a Zuciya.

Hawayen idanunta ta share ta kifa kanta a saman cinyoyinta a hankali ta shiga sauke ajjiyar zuciya,
Wani killer smile matar tayi kafin a hankali ta juya tare da fita daga cikin ɗan ƙaramin ɗakin.

Mutumin dake gadin wajan ne ya rusuna tare da gaisheta,kai kawai ta É—aga masa cikin iko haÉ—i da isa tace.

"Ka haɗa mata fruits ka bata, ka tabbatar tasha domin ina buƙatar ganin a raye saboda yanzu ne wasan zai fara, badai ta rusa min dukkan wani plans ɗina ba, Tabbas ni kuma zan sanya ɗan cikinta wanda take ji dashi ya kasheta da hannunsa Just watch and see"

Tana faÉ—in hakan tayi gaba Abinta, sa idanu kawai mai gadin ya bita a ransa yana jinjina rashin imani na matar.

A hankali ya fito daga cikin bathroom sanye da wani long white towel wanda ya sauka zuwa west ɗinsa, hannunsa riƙe da wani ƙaramin towel yana tsane ruwan dake zuba daga gashin kansa zuwa farar matar jikinsa.

Lumshe idanunsa yayi a hankali tare da jan wani reaction sound mai bayyana Æ´ar kasalar dake kwance a jikinsa,
Slowly kuma ya buÉ—e dugwayen eyes lashes masa wanda sukai wani kyau yalolo ruwa duk ya manne masu.

Stool yaja ya zauna tare da gyara zamansa sosai yay farcing mirror'n dake maƙale a jikin dressing mirror ɗin bedroom ɗinsa,
Cikin nutsuwa ya shiga shafawa jikinsa wani cream mai ƙamshi da laushi, kafin ya ɗauki handrayer ya gyara tsaftacciyyar sumar kansa, kana ya shafa mata Ginger Geminal Oil - hair kana ya ɗauki wani ribbon ya ɗaure sumar kan nasa daga ƙasa.
Body spray ya shafa a jikinsa kana ya nufi wajan wardrobe.

Wasu floral jacquard one button suit ya sanya, wanda suka kasance nevy blue ga wani taushi da suke dashi, sai wani Black Leather shoe daya sanyawa fararan ƙafafuwansa bayan ya sanya wata Black ɗin Safa,
Lumshe idanunsa yayi lokacin daya gama kimtsa kansa cikin tsaftatattun sutturar da sukai mugun mugun yi masa kyau,
Bayan ya kammala ne a kasalance yana cije laɓɓansa ya kwashi wayoyinsa tare da ɗaukan briefcase walking slowly ya fita zuwa babban Parlo.

Tun daga nesa idanunsa ya sauka akan Julde wacce take zaune a saman sofa, hannunta riƙe da Mug sai juya abu take da spoon da alama coffee ne, ya lura kwana biyu babban Parlon shi ne wajan shan iskar ta.

A kallon seconds 10 da yayi mata ya lura da kayan Jikinta taba sanye cikin Emilio pucci Silk kaftan dress, red colour ga wata siririyar necklace dake dugun wuyanta wacce ta ƙara haska farar fatar Jikinta, sai ƙafarta dake cikin Aquaholic Slippers ga gashin kan nan ya fito sosai ya kwanta har saman goshinta so ma sha Allah! Tayi kyau sosai Banda jajayen laɓɓanta babu abinda ke haske a fuskarta skin ɗinta kam sai glowing take.

Gajeren tsaki yana yana É—auke idanunsa, kafin ya mayar da Kallonsa ga Oumuu-Ayman dake faÉ—in.
"Tubarkalllah, Ma sha Allah! Zaki yau kuma ina zaka?"
Ya tsuna fuska yayi wanda hakan ya ƙara fito da ƙyallin sajan sa wanda yasha Luxury Beard Oil.
A hankali yaci gaba da tafiya ba tare da yayi magana ba yana zuwa bakin ƙofa kuma ya tsaya tare da kallon Oumuu-Ayman cikin serious tone voice yace.

"Oumuu-Ayman Kada wannan Yarinyar ta ƙara sanya wannan abin aljanun is totally haram"
Ya faÉ—a yana haÉ—a fuska domin zahirin abinda yake ransa kenan.

Murmushi kawai Oumuu-Ayman tayi domin tuni zuciyarta ta fara harshashen wani abu dake shirin faruwa soon kuma dalilin hakan komai zai zama dai-dai, numfashi taja kafin ta kalli Julde wacce tayi rau rau da idanu kamar zata saki kuka.

Domin tun fitowar ta taji Zuciyarta ta fara bugawa ga wani fargaba daya risketa, ƙasa kawai tayi da idanunta ba tare da ta faɗi abinda take shirin faɗa ba sai Ajjiyar zuciya kawai da take saukewa.

"Zaka daÉ—e idan ka fita?"
Shine tambayar da Oumuu-Ayman ta cilla masa ba tare data bi ta kan mitar da yake ba.
Lumshe idanunsa yay
Yana jin zcyarsa na tsananta bugu shiyasa gaba ɗaya kwana biyun nan ya ƙaura cewa zaman babban Parlon nasa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.