Aljanar Ruwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Aljanar_Ruwa_Ce_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 4 of 6
Part din amriya suka koma inda suka tasheta Tasha maganinda doctor Amina tace Tasha . Inda suka sata a gaba ta dunga durkan magunguna datayi order daga Niger
Suka turare ko ina na gidan bah abunda ke tashi sai kamshi. Tareda daukan breakfast dinta aunty amarya tace taci, amriya tace takoshi.
Hade rai aunty amarya tayi inda tasata agaba tafara feeding dinta da kanta.
Bayan fucewar doctor amina ta kwasheda dariyar mugunta tareda daukan wayanta tayi dialling number ,ringing biyu aka dauka.
Daga dayan bangaren mom tace you did a very good job zainab, murmushin mugunta tayi Tareda cire mask din datasa a fuskanta, Wanda yayi suffar doctor amina, zainab tace ai babu wacce tadace da kabir samada ni din nan.
Amma fah mom kin iya basaja, yanzu step 1 na kammalashi saura step 2, ina mai tabbatar miki cewa tanashan wannan magani toh bazata kara ganinta awanan duniyar bah saidai duniyan.
Mom ta kwashe da dariya tace hmm dama nafada mata Duk Wanda yashiga gonata toh baya futowa a Raye. Tunda tashiga gonata toh taruga data tona kabarinta, kuma bayan nagama da itah zan gama da sauran na mallaki zoben datake jidashi. Dukiya tazama tawa ni the devilish mother. Hhhahahaha ta kwashe da dariya mugunta.
Zainab tace amma kada ki cutar min da Kabir kinsan shine rayuwata, mom tace kada kidamu da wannan babu abunda zan masa .kinajina idan kinje gida jigsaws mahaifin ki usman cewa dole ya hallarci taro yau domin akwai muhimmiyar abu dazan fada.
Zainab tace toh uwar shedanu, ni kinga mah nagaji da kayan likitocin nan Allah, Allah nake na je gida na ciresu, zainab tace yauwa Mom kada kimanta kishafa mata wannan laya abayan tah idan tasha maganin
Kuma please kada kimanta maganin bita zaizai dakuma na mallaka dakika ce zaki bani yau a taro
Mom tace Duk wannan bah matsala bace kedai kawai ki hada Kai dani mu kashesu domin na zama shugaba a qungiya, idan mukagama toh koh kaina kikace na sare miki zanbaki.
Zainab tace banda dai cire kaii, sai anjima sai mun hadu a qungiya, Dan Allah ki kulamin da kabir Dina. Okay mom tace, tareda lashe wayan.
Tsaki taja tareda fadin bakuga komai bah wlh yanzu aka fara wannan yakin . Sainasa zaman duniyar nan ta gagari kowanne daga gidan nan.
Juyawarta keda wuya taga Ummi, fuskanta Duk shabe shabe da hawaye. Jikinta sai karkarwa yake,
Gaban Mom ne yafadi, inda tace kalisat yaushe kika shigo dakinan.
Tafada cikin faduwar gaba. Tafara nufan inda Ummi take,
Jada baya Ummi tafarayi tace kada... ki matso.. kusada.. Ni, tafada cikin sheshekar kuka.
Bantabah tunanin kina neman rayukan ahalin nan ruwa a jallo bah, Bantabah tunanin aka daga gareki bah.
Dama ke muguwa ce, Dama ke azzalumace Mara imani Mara tausayi, meye wannan ahalin suka rage ki dashi, mene kike bukata a duniyar nan da DAD baiyimiki bah.
Na tabbata soyayyar da yake miki batakai ta aunty amarya bah, amma aka kike so kikashe mana iyaye, sannan muma ki Gama da tamu rayuwar. Wace riba zakici kenen.
Me muka tare miki, meyasa saboda me, menene ribarki na aikata aka, tabbas ke macuciya ce, kuma tabbas ke kike cin naman mu batareda kin gasa bah.
Dafe kanta tayi Wanda yake mugun sarama mata tace, Meyasa, meyasa zai kasance kace zaki aikata aka, tabbas da labari aka bani koh wuyana za'a kama a yanke bazan taba yarda bah, amma nagani dakaina,
Aba Mom ta karashe maganar hawaye na bin kuncinta.
Hatta children da kika haifa baki Kyale bah wannan wace iriyar bakar zuciyace dake, tabbas idan aka ganki aka ga maciji toh afara kasheki kafun akashe macijin. Domin ke kinfi maciji illah.
Dan Allah koda zaki kashe kowa, meyasa zaki kashe amriya wane laifi ta aikata miki, yarinyarda babu ruwanta, meyasa zaki saka marainiyar Allah aciki,saboda mee, saboda mee.
Saboda itace ta Hana na kasheku tuntuni, zaro ido Ummi tayi tace kamar yaa kenen,
Kwarai mah kuwa, cewar mom, wannan yarinyar amriya ta taremun abubuwa da dama kujerarda za'a bani a qungiya tasaka aka fasa bani domin, ban cika alkawarin dana daukarwa qungiya bah.
Hatta kashe kabir da kwanakin baya dazanyi ita ta hana na kashe tah. Gashi yayi mugun tsananta amma Tana taimakarsa.
Kuma batareda yasan itace ta ceci rayuwarsa a teku bah, ita ta hanani kashe shi tun tuni, Domin shine farko a lissafi wadanda zankashe.
Tsuman tsaye Ummi tayi batareda ta iya furta wani kalmaba, tafara kukan bakinciki,
Tace Allah sarki amriya baiwar Allah dama ita ce yake tsaron rayukanmu agidanan takesa nata rayuwar a hadari. Wannan wace iriyar kyakyawar zuciyace da ita. Tabbas yahya Kabir baiyiwa amriya hadalci bah.
Tabbas wannan maganar bani kadaice zanji bah kowa na family saiya san Duk irin muganci dakike kullawa wannan family.
Direct hanyar waje tayi, shan gabanta Mom tayi Tareda sakin murmushin mugunta tace kina tunanin bayan kinsan sirrina zanbaki kifuta ne da ranki, toh imppossible.
Duk wanda yaruga daya San sirrina toh a ranar zai bakunci lahira, Dan aka, idan kinje Chan lahirar kya basu labari achan.
Rike kan Ummi tayi Tareda bugawa akan bango.
Kara ummi tasaka tana kokarin cetan rayuwata amma ina akan yagaza. Daukan katon kwalba mom tayi Tareda rotsa wa Ummi akai, faduwa tayi jini yafara zuba akanta.
Fasa ihuuuu
Salma dake kofan dakin Tana video Duk abunda Mom tafada akan ahalin dakuma abunda tayiwa Ummi, wani ihuun yakara fasawa, wayan datake video dashi ya sabule yafadi.
Kallon kasa tayi tanemi wayan ta rasa. Jikinta ne tafara karkarwa,
Kallonta Mom tayi tasaki murmushin mugunta tace yata salma kenen,.
Kokarin guduwa Salma keyi. Amma kafun tayi wani yunkuri ta chafko Salman.
Ihuun taimako salma tafasa inda mom tasa hannu ta buga mata baki,
Cikin sheshekar kuka tace Dan Allah mom kada ki kashe Ummi, ni yarki ce ki kasheni tunda kekika kawoni duniya amma Ummi wacce bataji bah batagani bah, kuma sannan yarinya ce, na roke ki, kirabuda itah ki kasheni please mom Tafada tana hada hannayenta guri daya, tareda fashewa da kuka.
Dariya Mom ta kwashe dashi tace ke yata ce bazan iya kasheki bah amma kuma idan takama don burina yacika babu Wanda bazan iya kashewa bah hatta kedinnan.
Amma for now bazan kasheki bah domin ke yata ce amma Ummi wannan confirm ne saina gamada rayuwarta.
Kuka salma takara fashewa dashi tace aba Mom Duk menene wannan Dan Allah ki kasheni ki rabuda ita, itama kamar yar ki fah take.
Allah ya kiyaye, wannan bah zata taba zama kamar yata bah, kinga kina batamin lck, kibarni na aiwatar da abunda zan aikata akanta. Daukan wuka tayi tanufi inda Ummi ke yashe cikin jini.
Durkushewa salma tayi Tareda rike kafar Mom tafara kuka Tana bata hakuri, amma koh kallo bata isheta bah, saima tureta datayi tafadi kanta yabuge bango.
Hawayene yafarabin gefen fuskan Ummi, cikin matsanci ciwo da radadi tace, mom na roke ki, na yarda ki kasheni amma Dan Allah kibari naga mahaifiyata, inason namata kallon karshe, inason na mata sallama kafun na mutu. Yanda ruhi na zaifi kwanciya.
Na rokeki dan Allah da manzonsa, kibari Nayi wa mahaifiyata Kallon karshe, nice mafi soyuwa agareta, idan kika kasheni batareda tayimin Kallon karshe bah nasan zata iya rasa rayuwanta,
Na rokeki, takarashe maganar hawaye nabin fuskanta, mom bata yi wata wata bah ta tsinka mata mari, tace wato na kyaleki kije kitonamin asiri bah impossible.
Daga wukan mom tayi zata soka mata.
Ummi tace tabbas karshenki bazaiyi kyau bah, tabbas zaki haduda fushin Allah,
Kin kashe rayuka bah adadi, sannan nima yanzu zaki kasheni, bkm ki kasheni bissmillah , rintse idanuwanta Ummi tayi Tareda yin Kalman sha'ada, hawaye na bin kuncinta.
Batareda guntun imani bah Mom ta chaka mata wukan, Kara ummi tasaki, daga nan kuma numfashinta ya tsarke, alamun babu numfashin tattareda ita.
Innalilahi wa innahilahi rajihun.
Ihuun Salma tasaki, Tareda yinkan Mom a fusace, shake mata wuya mom tayi tace indai har burina zai cika banki na kashe kowabah. Buga kan Salma tayi ajikin bango, hatake salma tafadi sumammiya.
Wajan wardrobe dinta tanufa, Tareda jan wardrobe din gefe, Hatake wani kofan ya baiyyana,
Maganganu naji tafarayi wanda nima bansan metace bah, ba'afi mintuna biyu bah kofan ya bude, tanufi inda gawan Ummi yake tajata Tareda jefata cikin wannan kofan,
Takuma daukan Salma tasakata aciki.
Hatake kofan yarufe kansa.
Azabure amriya ta tashi tareda kwallah uban ihuu dayasa gabadaya gidan ya amsa, sosai su nadira dake kusada itah suka tsorata. Tashi tayi Tareda nufa hanyar waje.
Shan gabanta kabir yayi yace ke ina zakije, menene aka, cikin zafin rai da baccin rai tace, ka matsa,
Kabir yace bazan matsaba dukana zakiyi, kallonshi tayi da brown eyes dinta Wanda suka Kara rinewa sukayi brown ta daka mai tsawa, Tareda tureshi a hassale,
Sosai hankalin kowa yatashi.
Mom kam jin karan amriya tayi uwa saukar aradu bah shiri tafara goge jini dake akasa. Tareda feshe ko ina da turare.
Ganin hanyar dakin Mom zataje ,yasa kabir janyo hannunta. Tareda rungumeta.
Ba shirt tafara kokarin cire jikinta daga nashi amma ta gaza, aka tacigaba da kokarin cire jikinta daga nashi amma tagaza, fashewa tayi da kuka, tana mai fadin ta kashesu wannnan azzalumar ta kashesu,
Aunty amarya tace wa aka kashe, sakinta Kabir yayi, suka ga tanufi dakin mom, babu bata lck suka bi bayanta,
Banka kofar amriya tayi, bah shiri Mom ta tashi, Tareda fadin yata amriya Lfy,
Kallon ta amriya tayi tace, menene suka aikata miki zaki kashesu, meyasa, sbd mee, meyasa zuciyarki tagama bushewa babu digon imani acikinta.
Kallonsu mom tayi ta fasheda kukan munafurci, tace yanzu ni amriya nice muguwa, mena miki, Duk irin soyayyar danake nunamiki amma shine kike kokarin yimin sharri.
Amriya tace bah sharri zanyi miki bah, indai akane toh kibari na chaje dakinan indai kinada gsk, rass gaban mom yafadi,
Fashewa takumayi da wani kukan tace yanzu kin mayarda ni makaryaciya kenen, Kabir kaji abunda matarka take fadamin koh, kanajinta kayi shiru, zuwa inda take yayi yace aba mom kada kidaga hankalinki nasan mah bazaki aikata aka bah, kinsan batada Lfy, shiyasa take magganganu.
Amriya tace Lfy yana kalau wannan azzalumar matar Tana neman rayuwanka ruwa a jallo, Tass, tass ya sharara mata mari.
Tareda nunata da Dan yatsa tace, kada ki kuskure kishiga tsanina da mahaifiyata, wato sokike ki hadamu koh, ke wace iriyar mahaukaciya ce.
Mahaifiyata zakiyiwa sharri toh ta Allah bata ki bah banza shashasha, Mara hankali
Dafe kuncinta tayi wanda hawaye suka Fara zarya akai, Tareda girgiza kanta,
Tafuce daga dakin, suma su Nadira suka rufa mata baya. sosai ran kowannensu baiji dadin marinda Kabir yayiwa amriya bah.
Kiyi hkr mom kinsan yarinyar sai a hankali kamar mai tabin kwakwalwa. Bkm kabir ainasani, Bb komi kaje kaci abinci kaji my son, OK mom, kuma kada ka manta ka rarrasheta.
Allah ya kiyaye Kabir yafada, murmushin mugunta mom tayi cikin ranta kuwa tace yanzu kaine nagaba a lissafina a Wanda zankashe.
Jin wayarsa yayi Tana ringing, sallama yayi wa mom Tareda fucewa daga dakin, ganin bakuwar number akan yasa yaki daukan waya, saida aka Kira wajan 10 miss call, ganin wanda ke kira bazai daina bah, ya dau wayan a fusace yace hello waye, waye yake addaban rayuwata da Kira.
Daga Dayan bangaren akace shin ina magana ne da Sir Kabir, kabir yace Eh nine ya akayi.
Dayan bangaren akace toh kazo kudauki gawar yar uwarka Ummi yana bakin titi, gabadaya police da likotoci dakuma yan jarida Sun zagaye wajan.
What Kabir yafada tareda mikewa tsaye yace gawar Ummi Kuma.
Jin aka yasa gabadayansu mikewa tsaye, gaban kowannensu yafadi.
馃ス馃ス馃ス馃槶馃槶馃槶馃槶馃槶
TOH FAN'S MUJE DAI ZUWA
COMMENT & SHARE PLEASE 馃檹馃檹馃檹
ALKALAMIN 馃枈锔忦ç…å©ç¬é¦ƒæžˆé””?
BABY ISHA 馃挒馃挒馃挒
2/28/24, 22:12 - AISHA M.B (Baby isha): Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE91
馃摎馃摎馃摎馃摎馃摎馃摎馃摎馃摎
馃î¡éˆ¥å¶æª§é””å¿¦ç…£æº¾â‚¬å¶æª§é””å¿¦ç…£æº¾â‚¬å¶æª§é””å¿¦ç…£æº¾â‚¬å¶æª§é””å¿¦ç…£æº¾â‚¬å¶æª§é””å¿¦ç…£æº¾â‚¬å¶æª§é””?
é¦ƒå¯ é¦ƒå¯ é¦ƒå¯
馃挮BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM 馃尮
ALJANAR RUWA CE 馃î¡éˆ¥å¶æª§é””忦煣滒煂? PAGE 3锔忊儯8锔忊儯鈻讹ç¬3锔忊儯9锔忊儯
WRITTEN & DIRECTEDé‰å¶ç¬ BY BABY ISHA 馃挒馃挒
-----------------------
fucewa amriya tayi tanufi dayan dakin,
Kabir jiyayi kamar ya hadiye zuciya ya mutu tsabar bakin ciki, yau karo na farko a rayuwarsa da wata ta Kalli kwayar idonsa tagayamai mgn .
Mamaki yashigayi yana mai fadin ni Kabir mace tagayamin mgn kuma Nayi shiru how is that possible. Tsaki taja Tareda fadin zatasan ta tabo kabir wlh.
Kwanciya yayi akan gado saiyaji gabadaya gadon mah babu dadin kwanciya, Tsaki yaja yatashi Tareda fucewa daga dakin yanufi, dakin da amirya tashiga.
Tura kofan yayi yace toh mai guri yazo mai taburma ya nadi.
Koh Kallon inda yake batayi bah saima kara gyara kwanciyanta datayi,
Gani tayi banza dashi akan yakara hassala shi yace ke bada ke nake bah koh bakiji bah, zoki fucemin daga daki,
Cikeda bakin ciki amirya ta tashi tace wai kai wane irin Dan takura ne, kace nabar maka wancan dakin nabaro Chan nadawo nan kai meyasa kawai burinka ka ga ka batamin rai. Aba Dan Allah wannan shirmen naka ya isheni, nagaji
Nabar maka wancan dakin na dawo nan kuma ka Kara biyoni yanzu kuma kanacemin wai in futa, toh wlh bazan futa bah.
Kabir yace nikike cewa bazaki futabah, shiru tamai ta koma kan gadon ta kwanta,
Shiru yayi yana mai hayyana irin rashin mutuncin dazai yiwa amriya, Chan gefen gadon yanufa, tareda daukan pillow sannan ya kwanta . Jan bargon yayi Tareda rufawa ajikinsa.
Ganin ya debe bargon gabadaya yasata, Jan bargon ta dunkuleshi ajikinta, ganinta kwashe bargo yasa shi kara Jan bargo. Aka suka dunga ja, amriya naja shima naja.
Daga karshe yasamu ya tureta tafadi akasa, tashi tayi, cikin jin aushi ta janye bargon gabadaya ta hada dashi kabir din, luuuu kabir yatafi sai ajikin amriya,
Faduwa sukayi, numfashi kowanne aicinsu na gogan najuna, rass gaban kowannensu yafadi, kabir kamm jin jikinshi yayi wani iri, sosai suke kallon juna bako kifta ido. Kamshi turaren amriya ne kabir yasaka Hatake yaji wani irin sanyi da shauki nashigarsa, a hankali yadunga lumshe ido, sosai kamshin turarenta ya burgesa.
Gyaran murya amirya tayi sai a lckn kabir yadawo hayyacinshi
Tashi kabir yayi yakoma kan gado sannan yayi aduar bacci ya kwanta, itama amirya aka ta tashi tanufi kan kujerar dake daki sannan ta kwanta akai. Bah shiri baccin barawo yayi hawan gaba da ita.
Juyawa kabir yayi yana fuskantar inda take, Kallonta yayi, yaga yadda gashin kanta ya sauko. Murmushi yayi sannan yajuya ya kwanta.
Washe gari da sassafe amriya ta tashi inda tadora abinci na breakfast , bayan ta gama ta hajiye akan dining, sannan ta zuba wasu a kuloli Wanda zata kaiwa su DAD dake asibity.
Futowa kabir yayi cikin kananun kaya, kayan Ba karamin kyau suka masa bah, kallonshi amirya tayi, cikin ranta tace bah laifi kyakyawa nee amma sai iya shegen jaraba.
Harde hannuwanta amriya tayi tace ina kwana, koh Kallon inda take beyiba, ya nufi dining ,
Zama yayi sannan yabude kulan wani kamshi ne ya daki hancin shi, ya mutse fuska kabir yayi yace menene wannan, amriya tabashi amsa dacewa mee idonka ya ganar maka,
Murmushin takaici yayi tareda janyosa ya Kama bakinta ya murda, kara amriya tasaki, saida yaga ta jigata sannan yasaki leben.
Kara rinewa lebenta yayi tace mugu kawai,
Kallon soya da Kwan data kawo mishi yayi yace wannan Ai shashanci nee , ina kika taba ganin anci abinci mai nauyi da sassafe,
Amriya tace bantaba gani bah toh akanka za'a Fara,
Kabir yace ni bazan ci wannan Abunba, murmushi amirya tayi tareda daukan kulan tarufeshi tasaka acikin basket tace abu yazo gidan sauki, yunwan CE bakaji dakanajin yunwan da ko tuwo nakawo maka zakaci.
Ni yanzu inaso zan kai wa su mami abinci Dan aka inason ka kaini asibity, Kallon bakida hankali kabir yamata yace,
Gsk yane wuyanki ya isa yanka, ni zakice nakaiki hospital Dan tsabar kin Raina min hankali, kuma kin rainani.
Amriya tace toh in baka kaini bah wazai kaini, Dan Allah kayi sauri kada mu makara, kabir yace bazan jee bah, idan kinso kitashi sama,
Hawaye ne yafara ciko mata a ido tace, yanzu ace mami Tana asibity DAD yana asibity ga aunty amarya da gradma, na tabbata tunjiya babu abunda suka saka abaki sbd jimamin mutuwan Ummi, abincin dazasu saka fah aikinsu zan Kai musu,
Yanzu Dan Allah ... Bata karasaba taji yace shikenen, shikenen, ya isa banason takura, shirya mutafi.
Cikeda farin ciki amirya tace, Ngd, kabir yace karki dauka sbd kince nakaiki zankaiki, zankaiki nee sbd mahaifina dakuma mami suna Chan,.
Ya mutse fuska amriya tayi cikin ranta kuwa tace shidai wannan bazai taba chanzawa bah.
Tashi yayi Tareda daukan car key, yanufi hanyar waje ganin akan yasata bin bayansa .
Daidai suma su nadira na futowa daga part dinsu, gaggaisawa sukayi, inda suma sukadau mota, body guard suka bude gate din gidan suka fuce saura su amriya, Wanda yazage sai jamata aji yakeyi .
Mom ce Tafuto daga part dinta idanuwanta sun kada sunyi jajir Duk Sun kumbura tsabar kuka.
Ganin aka yasa hankalin kabir tashi da sauri yanufi inda mom take yace, mom what happened, meyafaru kinsan banason na ganki cikin Damuwa please mom kifadamin menene.
Share hawayenta mom tayi tace kabir, meyasa mutane suka fiye zalinci, yanzu ace yarinya karama kamar Ummi asamu wani mara imani ya kasheta,
Na rokeka kabir tabbas kasaka agano Wanda yayi kisan nan sannan agano Wanda yasace min yarinya Tana kaiwanan ta fashe da kukan muna furci.
Rungumeta kabir yayi, yace insha Allah mom zansa agano ko waye yanzu aka yan sanda suna bincike akan case dinsu Ummi nee insha Allah kuma za'ayi nasaran gano kowaye.
Murmushin mugunta mom tayi tareda Kallon inda amriya take ta kesta mata ido daya, ran amriya ne yakai kololuwar bacci, cikin baccin rai tace, Dan Allah kazo mutafi kada mubarsu, sunajin yunwa basuci komai bah.
Sakin mom kabir yayi yace mom bara muje mudawo zamuje asibity. mom tace toh nima mutafi tare zanje.
Cikin fusata amriya tace Aa mukadai zamuje, babu inda zaki bimu.
Kabir yace me kike nufi, amirya tace aba kalb yanzu so kake muje ta dunga mana kuka , baka ga yadda fuskanta ya kumbura bah, baikamata muje da ita, bah sbd kada taje ta dunga kuka, itama mami tafara kuka,
Kaga gwanda ta zauna a gida zuwanta babu abunda zai tsanana mana, zuwa inda mom take amriya tayi tace,
Mom kije ki huta kisha magani ki kwanta sbd baikamata ace kina ganin abunda zai daga miki hankali sbd halinda kike ciki.
Kabir yace mom amriya tafadi gsk kije ki huta, zamuje mudawo da gawar a mata sutura akaita gidanta na gsk.
Fashewa da kuka mom tayi tace za'a kai Ummi gidanta na gsk shine baza a barni naga gawar yata bah, sbd mee,
Cikin jin haushi da kunan rai amriya ta daka mata tsawa, Tareda fadin bayan kinkasheta, wato baki gamsu ta mutu bah shine kikeso kibimu, idan bata mutu bah ki karasata achan tantiriya, azzaluma, mai bushashiyar zuciya.
MANAGE PAGE PLS 馃檹
COMMENT & SHARE 馃檹馃檹馃檹
ALKALAMINé‰å¶ç¬é‰å¶ç¬é‰å¶ç¬
BABY ISHA馃挒馃挒馃挒
2/28/24, 22:12 - AISHA M.B (Baby isha): Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE91
馃挮WRITER ASSOCIATION @@@@@@@@@@@馃挮
馃摎馃摎馃摎馃摎馃摎馃摎馃摎馃摎
馃î¡é¦ƒî¡é¦ƒî¡é¦ƒî¡é¦ƒî¡é¦ƒî¡é¦ƒî¡é¦ƒî¡
é¦ƒå¯ é¦ƒå¯ é¦ƒå¯ é¦ƒå¯ é¦ƒå¯ é¦ƒå¯
BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM 馃尮馃尮
ALJANAR RUWA CE 馃î¡éˆ¥å¶æª§é””忦煂å©ç…‚? PAGE 3锔忊儯9锔忊儯鈻讹ç¬4锔忊儯0锔忊儯
WRITTEN & DIRECTED é‰å¶ç¬ BY BABY ISHA 馃挒馃挒(AISHA M.B)
------------------------
Firgit mom ta tashi daga mafarkin da takeyi, gabanta ne yafadi tace, yakamata Nayi wani abu kada yarinyar nan ta tona Min asiri.
Tashi tayi tareda daukan mayafinta tanufi hanyar waje a daddafe Dan dukan da amriya tayi mata bah kadan bane.
Futowa tayi harabar gidan, Daidai lckn taga su amriya suna kokarin Shiga mota.
Kabir tafada da Dan karfi, juyowa kabir yayi yace, mom ina wuni , mom ta amsa da Lfy son, ina zakuje aka.
Kabeer yace wlh zamu kai wa su mami abinci nee, Tom kabeer muje koh nima inason naje natayata jaje,
Kabir yace Aa mom kizauna ki huta koh.
Mom tace hutun me zan Zaune yi, yata amriya kice masa Dan Allah yabarni naje.
Amriya tace mom keda Danki ni ina ruwana, dakin ne fah, kinga kinada Dama kimasa Mgn yaji.
Kabir ya harari amriya, sannan yace shikenen mom Tunda kince aka muje, bude mata kofan motan yayi, tashiga,
Inda amriya tatsaya tazuba ido koh zai bude mata itama.
Ganin bata Shiga motan bah yasa yace ke bazaki shigo bah ne koh mee, kinafah batamin lck, amriya tace toh ni bazaka bude min kofan bah,
Binta yayi da kallo yace, Mace daya tilo takk zan iya budewa kofa a duniyar nan, itace mahaifiyata, so idan kinga bazaki iya budewa bah toh, wa kanki, musaimu tafi,
Ya mutse fuska amriya tayi ta bude kofan motan tashiga, masu gadi ne suka wangale musu kofa suka fuce.
Tunda sukafara tafiya Ba wanda ya kulla Dan uwansa saima sake sake ds kowannensu yakeyi.
Direct hospital din suka nufa, ba'afi 20minutes bah suka isa wajan, parking yayi yafuto daga cikin motan sannan yabudewa mom kofa ta futo daga cikin motan.
Sanin cewar bazai bude mata kofa bah yasa itama ta futo daga cikin motan, tareda futowa da food flask din, direct cikin reception din suka Shiga.
Tarar dasu sukayi a zazzaune kowa yayi tagumi, gaishesu su kabir sukayi, su aunty amarya suka amsa batareda walwalah a fuskokin suba.
Amriya tace Yauwa ga abinci na dafa muku, barana siyo Ruwa, Gradma tace munkoshi wlh,
Hade rai amriya tayi tace wlh Baku isa bah, sai kunci, murmushi DAD yayi yace Tom shikenen, daukan daya daga cikin flask din amriya tayi tace barana kaiwa mami nata abinci nasan tanajin yunwa.
Dad yace mushiga tare, tunjiya rabona naga yar uwata. Tashi sukayi gabadaya sukashiga cikin room dinda mami take. Da sallama sukashiga, inda mami ta amsa kasa kasa.
Murmushi amriya tayi tace mami ga abinci nakawo miki, kici kinji, idanuwan mami ne ya cika da hawaye tace Aa amriya nakoshi, kibarni da tarun bakinciki, da kuncin da nake ciki.
Amriya tace aba mami, Dan Allah kidaina fadan aka, Allah yarabamu da bakinciki, Allah kada yakawo abunda bazai wuce bah., abunda yafaru yaruga daya yafaru, Allah yaruga daya kaddara cewar Ummi zata mutu batareda kinyi ido hudu da itah bah, ki share hawayenki mami , mu fauwala wa Allah komai,
Bai kamata ace kina kuka bah aduar ki take bukata bah kuka bah,
Mami tace yanzu shikenen Ummi ta rasu, batareda ansan wanda yakasheta bah, yanzu auta tah ta tafi kenen.
Amriya tace aba mami kin manta kinadani, na miki alkawari zan Maye gurbin Ummi acikin zuciyarki,
Kuma Allah yatona asirin wanda yayi wannan kisan nan bada dadewa bah, munafukai masu idon jemage, Tafada Tana Kallon mom takeyi fari da ido.
Mami tace Dan Allah inason naga gawar yata, DAD yace bazai yuhuba sbd anruga da ankaita gidanta na gsk.
Wasu hawayen ne suka Fara zubowa, Mom tace Allah sarki Ummi Allah yajikan ki da rahama, yamiki rahama yasa aljanna firdaus ce makomarki .
Gabadaya suka amsa da Amin
Maryam wato mami cewar mom sannan tace Dan Allah kici abinci kinji,abunda yafaru yaruga daya faru zaizai Allah ya kiyaye gaba.
nadira tace, mami please, taya hankalin mu zai kwanta idan muka ganki a wannan halin.
Share hawayenta mami tayi tace shikenen Naji zanci , Yauwa mami naa, yanzu baranaje na siyo ruwa, wanda zaku sha,
Khalid yace kibarshi nizanje, Amriya tace Aa kana min bakinciki zanje Aiken mami naa, bakasan nasamu lada koh
, murmushi gabadayansu sukayi ,Tana kaiwanan tafuce daga dakin. Murmushi Kabir yayi karo na farko da amriya ta burge shi.
Kallon kabir mami tayi tace kabir gsk kayi dacen mata, kariketa hannu bibbiyu, karike matarka kuzauna Lfy, yadda hakkinta bazai aukanka bah itama hakkinka bazai aukan ta bah kaji, wlh sa'ar mata, irin Mace kamar amriya, mai tausayi da amana dakuma taimako daidaiku nee, kaji koh, kabir yace insha Allah mami Ngd, kifara cin abincin kafun takawo ruwan. Barana je nadawo yana kaiwanan yafuce,
futan shi keda wuya suka ci karo da abbansu Khalid, gaisheshi kabir yayi, abba su Khalid Ya amsa .
Tareda fadin suna ciki kuwa, kabir yabashi amsa da cewar Eh suna ciki, OK tom shikenen Ngd. Kabir yace ya hkr, abba yace wlh Lfy Ngd.
Shiga dakin yayi da sallama a Bakinsa, inda su DAD suka amsa gaggaisawa sukayi, inda su DAD suka fuce suka basu guri.
Inda ake sayarda ruwa amriya tanufa inda mutanen wajan sai binta suke da kallo.
Sallama amriya tayi, inda mutanen wajan suka amsa,
Sannan tace abani ruwa na roba, mikamata mai ruwan yayi ta karba, Tana shirin budewa tasha taji Ihuun mutane suna fadin aka mota ,aka mota.
Juyawarda zatayi taji anfado mata ajiki, daka tawa amriya tayi ta dago da matar. Daga jikinta bayan amriya matar ta tsaya sannan matar tafara mgn cikin dashashiyar muryanta tace, kada kibari su kama ni Dan Allah nidin bah mahaukaciya bace.
Daya daga cikin likitocin yace, ke yarinya ki matsa daga wajan matar nan mahaukaciya cee, tanada cutar mantau .tsintar ta akayi acikin ruwa . Yanzu sacatery za'a kaita shine take guduwa.
Kallon idanuwan matar amriya tayi tace Wacece kee, hada idanuwa sukayi da matar Hatake hankalinta yatashi, tarike hannuwan amriya sannan tace kece, kece, tabbass kece.
Kokarin cire hannunta amriya tayi tace ni Kuma menayi, matar tace ke zaki kawo karshenta, ke zaki gamadasu, dole ki gama dasu babu inda zalinci ya Dore, dole hasan cewar jaruma ta baiyyana, kada kibarsu, kada kirabudasu, ki yakesu har sai inda karfinki yakare yata.
Kada kataba gazawa, yakamata ace asan cewar kin baiyyana, mai kawo karshen zalinci ta zo. Kitashi tsaye, kitada makamai ki yake su,
Taruke kafadar amriya tace kada kirabudasu na rokeki, ki kawo karshensu, tabbas zun debo ruwan dafa kansu, ki kashesu karki Kyale kowa. Tana kaiwanan matar tafadi summamiya , daukar matar sukayi suka feceda itah daga asibity.
sosai hankalin amriya yatashi ,jikinta yafara karkarwa. Karasowa kabir yayi ganin mutane sun taru aka yasa yaja hannun amriya suka bar wajan.
Bangaren su mami kuwa, Shiga ciki abba yayi yace sannu maryam ya jiki, sama sama, mami ta amsa.
Ajiyan zuciya abban su Khalid yayi yace, nasan nayimiki babban laifi, na tauye miki hakkinki a matsayinki na matata. Bansan dawane ido zan kalleki bah, tabbas na aikata kuskure kuma nagano kuskurena, Dan Allah na rokeki kiyafemin ki gafartamin,
Na miki alkawarin cewa akan bazata sake maimaita kansa bah, Dan jimm mami tayi tace naji nayafe maka, Dan Allah kafuta zan kwanta.
Aba maryam kenen haryanzu fushi kike dani, ki taimaka ki yafemin, wlh bada San raina nake aikata, abunda nake yamiki bah, koh kishiyarki mah tuntuni na Dade da sakinta, kawai namiki karyar cewar ta tafi wajan iyayenta Hutu nee.
Mami tace toh ni ina ruwana da ita Ai bah akaina take zaune bah. Kowa zamansa yakeyi.
Murmushi dad yayi yace, matata kenen, shikenen zan tsuguna Kuma na hada hannayena na rokeki Dan kisan da gsk nake
.
Kokarin tsugunawa yake, mami tayi Saurin mikewa tace Aa, ka rufamin asiri, sokake Allah yayi fushi dani, na yafe maka, toh idan mah ban yafe maka bah mezanyi, abunda yafaru yaruga daya faru, wlh na yafe maka duniya da lahira kuma.
Nice mah yakamata ace na nemi gafarar ka sbd magganganu dana fada maka Mara dadi, Dan Allah ka yafemin.
Abba yace aini babu abunda kukamin Kuma baki min laifin komai bah, akasari mah dalilin magganganu da kika fadamin yasa na gano kuskure naa, Dan aka na yafe miki. Murmushi mami tayi tace Alhmd ina mai godiya a gareka, abba yace nine yakamata na gode miki.
Jijigata Kabir yashigayi Ganin tafara futa a hayyacinta,yasa yanufi gida da itah batareda yanar dasu DAD bah, direct daki yakaita, Tareda zaunan da ita
yace ke meyasa meki, meyafaru, Rike hannunsa tayi wanda zoben tah ke sanye tayi, tareda saita Daidai saitin zuciyarta ta dora, zoben akai, wani irin nutsuwa ne yafara ziyartatta,
dauke hannunsa zaiyi ,yaji takara kankame hannun tace, kada kacire hannunta katsaya, tsyawa yayi yana Kallon ikon Allah, rintse idanuwanta tayi sukacigaba da Tsayuwa wajan harta samu nutsuwa.
Dagowa tayi tareda sakin hannunshi tace kayi hkr na Rike maka zobe batareda izininka bah, ka yafemin, Kallonta Kabir yayi yace, meyasa wancan matar naga tarike ki, meyasa kike yawan faduwa idan kinga abu ko Kuma idan an watsa miki RUWA. Meyake faruwa dake kifadamin gsk, yau inason kifuto ki gayamin asalin Wacece kee, meyasa Duk wannan, fadamin Wacece kee.
Dago idanuwanta tayi wanda hawaye sukara zarya akan fuskanta, tace ni be kowa bace bace mutum irinka.
Yes I know, amma inason insan dalilin dayasa kike faduwa just like that, koh ki tsuma, kokuma akasarin aka, waye yayi sanadiyan faruwan akan.
Share hawayen dake bin kuncinta tayi tace, KAINE SILA . ...........
é¦ƒæŒ®é¦ƒæŒ®é¦ƒæŒ®é¦ƒæŒ®é¦ƒæŒ®é¦ƒæŒ®é¦ƒå¯ é¦ƒå¯ é¦ƒî¡éˆ¥å¶æª§é””å¿¦ç…£æº¾â‚¬å¶æª§é””å¿¦ç…£æº¾â‚¬å¶æª§é””å¿¦ç…£æº¾â‚¬å¶æª§é””å¿¦ç…£æº¾â‚¬å¶æª§é””å¿¦ç…£æº¾â‚¬å¶æª§é””å¿¦ç…£æº¾â‚¬å¶æª§é””?
COMMENT & SHARE PLS 馃檹馃檹馃檹.
ALKALAMIN 馃枈锔忦ç…å©ç¬é¦ƒæžˆé””?
BABY ISHA 馃挒馃挒馃挒(AISHA M.B)
2/28/24, 22:12 - AISHA M.B (Baby isha): Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE91
ALJANAR RUWA CE 馃î¡éˆ¥å¶æª§é””忦煂å©ç…‚? PAGE 4锔忊儯0锔忊儯鈻讹ç¬4锔忊儯1锔忊儯
WRITTEN & DIRECTED é‰å¶ç¬ BY BABY ISHA 馃挒馃挒馃挒
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*é‰å¶ç¬
(J.W.A)
Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan 茩asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau茩i.é‰å¿¥ç¬
------------------------
Jin furucinta yayi kamar saukar aradu. Juyowa yayi ya da Kallon mamaki ya kalleta, ya ce "Kamar ya kenen? Ban fahimta ba."
'Dan jim Amriya tayi ta ce "Kwarai kuwa, kaine silan komai da yake faruwa da ni."
Kabir ya ce "Ni Kuma taya na zama sila? fad'amin ina jinki." ya karashe maganar fuskanshi a had'e.
Kallonshi tayi ta ce "Eh kaine, kuma har yau har gobe zan cigaba dafad'in kaine."
Kabir ya ce "Nifa ba abunda na tambaye ki kenen bah, tambaya ta itace tayaya ni nazama sila?" Ya fad'a tare da sunkuyar da kansa gefe.
"Amriya ta ce, ta yarda na ceci rayuwarka daga teku, wanda shine ta saka haryanzu ka kasance a Raye.."
A firgice ya juyo ya kalleta, da sauri ya mike idan ran kabir yakai dubu to ya 'baci ,ya ce "Harke kinkai kimin karya, wato kin samu labarin cewar wata ta ceci rayuwata, Kuma na kamu da sonta, wato saboda kinsan rauni na shine kike son kibi ta salon yaudara ki yaudareni, that can never be possible."
'Dago idanuwanta amriya tayi wanda suka kada sukayi jajir, ta ce "Dan Allah ka yarda dani , wlh ni ce na taimakeka, zobena ne a hannunka wanda ya su'buce ya fad'a hannunka, dan Allah ka bani zoben na koma duniyata, inba haka bah mutuwa zanyi na rokeka."
"Ya isa, wannan magganganu naki sun isheni haka, bana son na karajin komai daga bakin kii, sbd kin rainamin hankali shine zakice wai kece, toh duk wanda ya turo ki wajena domin ki zo ki yaudareni toh ki koma wajansa kice inji ni na ce hakan bazata taba faruwa bah impossible."
"Dan Allah ka saurareni, ka saurari abunda zancemaka, a halin yanzu ma rayuwarka dana Hosanna tana cikin hatsari, dan Allah kabani zobena domin na ceci wannan ahalin."
Kabir ya ce "A matsayinki nawa kenen? Ke wace? da zaki iya hana abunda zai faru, Kuma insha Allah babu wani abu dazai samu family nan, insha Allah duk wanda yake da mugun nufi akan wannan ahalin Allah ka mayar masa da niyarsa. wanda ba shine alkhairi bah agaremu.
Ke a matsayinki nawa zaki ce zaki taimake mu?"
Amriya ta ce," A matsayina na ALJANAR RUWA." Kallonta ya yi da sauritare da yi mata Kallon up and down, ya saki dariya saida yayi mai isarsa sannan yace "Ke ALJANAR RUWA, wow, Kuma kinaso na yarda dake."
"Hmmm toh bara kiji wlh, kada mah ki fara fad'an haka sbd nidin nan babu abunda nafi tsana a duniyar nan sama da amin magana aljanar ruwa, banaso, dan haka maza kafucemin daga d'aki."
Tashi Amriya tayi tana shirin nufan inda yake, dakatarda ita yayi da faè“·in "Kada ki kuskure wallahi, maza leave my room or else, I will show you my true colour.."
"Me yasa ba zaka yarda dani bane?" Ta k'arashe magana tare da fashewa da kuka.
Jin ana bubbuga k'ofa yasa tayi Saurin share hawayenta, tareda nufa hanyar d'akin, ta murda handle din k'ofa, tare da bud'ewa, fatima ce tsaye hannunta rike da flask ta ce "Gashi inji Mom ta ce na kawo muku, na rana ne, Kuma na sanar miki cewar su Mami sun koma Lagos."
"Toh" Amriya ta ce, Kallonta fatima tayi tace, "Amriya lafiya kuwa naga kamar kinyi kuka meyafaru?"
Kabir dake cikin d'aki ya tashi tare da nufa hanyar waje inda ya bangaje amriya ya wuce.
'Daga ta fatima ta yi ta ce, "Sannu Amriya, menene aka yake faruwa ki fad'amin, yau Kuma wane laifi kika masa?" fashewa Amriya ta yi da matsancin kuka ta ce "Allah sarki babu komi wlh."
Fatima ta ce "Toh amma me yasa kuke samun sa'bani kinga wlh Tunda su Docyor Amina da Aunty Amarya suka zo suka yi mana nasiha tun lckn nakeyi wa yaya Khalid biyayya. Kuma yanzu na koyawa kaina sonsa."
"Toh yanzu damai zamuji ga mutuwar Ummi, ga batar Salma da haryanzu jami'ai nemanta suke amma ace mutum bazai fauwala Allah komai bah? Ki k'ok'arta ki Rike mijinki hannu bibbiyu."
Kallonta Amriya ta yi tace "Tom insha Allah zan k'ok'arta, fatima dan Allah kinada abun rubutu.?"
Fatima ta ce "Eh ina dashi me zakiyi?"Amriya ta ce, "Abu zan rubuta ne, ki aramun." Kallon kan table Fatima tayi ta ce "Yauwa ga wani bairo nan mah kinga saiki rubuta duk abunda kikeso."
Wajan table din Fatima ta nufa tare da d'aukan bairo din ta mikawa Amriya, kar蓳a aAmirya tayi tare da yi mata godiya.
Daga bisani fatima ta fuce daga d'akin. Hajiye flask din abincin Amriya tayi, tareda goge Hawayen dake shirin zubo mata akan kuncinta.
Daki ta shige koh takan abincin bata bi bah, ta d'auki littafi, tafara rubutu.
Sai wajan karfe Tara 9:0 clock na dare Kabir ya shigo, tarar da ita yayi a Zaune tayi tagumi, tana ganin shi ta mike tare da fad'in "Sannu da zuwa, abinci ka yana kan dining." Koh takanta baibi bah, yanufi toilet tare da yin wanka ya futo yafara shafamai inda suman jikinshi suka kwanta sukayi luff gwanin sha'awa . Bayan yagama shafa mai ya mike tsaye tareda nufa kan gado zai kwanta.
Da sauri tace masa baka ci abinci bah fah, dan Allah kaci abinci kafun ka kwanta na safe mah baka ci bah yanzu bazaka ci bah."
Kallon ta yayi ya ce, "Ina ruwanki cikin ki konawa? me yasa wai ke kinfiye nacin jaraba, wannan mata aka auramin koh annoba?"
Banza kawai, kinga ki futo kifad'a idan saki kike bukata toh ko yanzu zan dambara miki shi, so please don't disturb my life. Ni zuwanki gidanan mah ba abunda yayi sai jawowa mutum mafisa da bala'i , banza kawai mai farar kafa."
Kukane yaci karfin Amriya, hawaye mai zafi suka fara bin kuncinta, ta ce n"Ni è“·in, ni ce mai farar kafa, nice masifa koh, Allah sarki, è“·an Adam butulu ne."
Bayan gwagwar maya da wahalar da nake sha a sanadiyan kawai domin na tseratar da rayuwarku, shine zaka cedani mai farar kafa, wannan wace iriyar rayuwa ce?" Dafa kanta ta yi wanda yake mugun saramata ta ce, "Tabbas na aikata kuskure, meyasa ban tsaya acikin ruwa bah ankashe ni? Meya futo dani ya Allah me yasa na ceci wannnan bawan Allah naka, meyasa banyi zamana bah?"
Da nasan zan kasance a raye ne dan kawai naga wannan bakar ranar, da nasani na tsaya an kasheni."
Kallonsa tayi tace "Ko dan ina zamane a gidanku yasa kake min irin wannan rashin mutuncin? kodan an aura min kai ba tareda nak'i bah, koh sbd Banida kowa nid'in marainiya ce yasa ka ke aibata ni kake zagina da zalunta tah yadda kakeso."
Sosai jikin kabir yayi sanyi inda yaji tausayinta yayi mugun kamashi, tashi yayi yanufi inda take a zaune yace "Kiyi ha茩uri, kinji nasan na aikata kuskure Kuma hakan bazata sake maimaita kanta bah."
Rungumeta yayi a jikinshi, inda itama ta rungumeshi, kallonta Kabir yayi yace yanzu kin yafemin, girgiza masa kai tayi tace "Eh, amma inason ka yarda da... " Shiiiiii yayi mata nuni da yatsanta. "please dan Allah kada kayi min zance d'azu abar maganan. Muje mu kwanta kohh, Yauwa kintuna min zamuje muyi alwala muyi sallah, yau ina son na sauke hakkin ki dake kaina. Koda yake mah ni na riga da nayi alwala sbd aka kije kiyi alwala."
Rasss gaban Amriya yafad'i, hanjjin cikinta suka kad'a, ta ce, Kamar ya?" Kesta mata ido daya yayi yace aikin gane abunda nake nufi ko saina futo na baiyyana kije dan Allah."
Mikewa Amriya tayi inda gabanta bai daina bugawa bah, shiga cikin toilet tayi, tace "Nashiga uku yanzu ya zanyi, so yake muyi mu amala na ma'aurata."
"Taya hakan zai yiwu a matsayina na ALJANAR RUWA, shikuma BIL adama, wannan bazaiyuba, dole ne nasan yadda zanyi na kawar masa da hankali."
Tap din ta kunna Tareda Dauro alwala, Tana gamawa Tafuto waje, Jikinta sanye da towel.
Kallonsa tayi taga ya sauya shiga, cikin jallabiya yana kan sallaya yana lazumi, saka kaya tayi tareda daukan hijabinta, tace "Nagama ma."
Tashi Kabir yayi inda, ya tada musu sallah, bayan sun idar da sallah, yayi musu addu'a, inda ya Rike goshinta yamusu aduan saduwa da iyayi.
Shaketa tayi jikin bango, Hatake matar tafadi, inda Mom taja gashin kanta, Kara matar ta saki, yana mai fadin "Ki rabu dani, muguwa, mara imani,
Me kikeso namiki, kin rabani da farinciki na, kin raba ni da d'ana, kusan shekaru 37.
Kin azabtar dani son ranki kin kulle ni a wannan dakin wajan shekara da shekaru. toh meya ra ge, kawai ki kasheni na huta.."
Dariya Mom ta kwashe da shi tace "Ke a tunaninki, narabaki da d'anki ne sbd kawai ina sonsa, toh barakiji, babu abunda nafi tsana a duniyar nan sama dashi, kuma saina ga bayansa tukunan hankalina zai kwanta ,Kuma keda barin d'akin nan har abada."
"Wallahi Allah yafi karfinki, insha Allah d'ana bazai mutu ta hannunki bah, wlh saidai shi yayi ajalinki, uuma ki sani matar d'ana tafi karfinki, kedin kinayi duk abunan ne kawai sbd abun duniya da ya rufe miki ido."
Itakuma haryanzu tana zaune ne a gidanan domin ta taimaka mana, kuma ita zata futo dani daga wannan bakin dakin dakika ajiyeni."
Mikewa mom tayi tace, "Tom shikenen basai in tana raye bah tukun zata taimkeki." fucewa mom tayi, tabar matar a tsaye. Tsugunawa matar tayi tareda fashewa da kuka, tace "Allah ka kawomin agaji.
Kasa wannan matar Ta gane gsk, kasaka ta gane hanya mai kyau.."
Washe gari da sassafe Amriya tanufi part dinsu DAD domin ta je ta gaishesu kamar yadda aka saba.
Tana cikin tafiya tafarajin kukan mutum, Juyawa tayi bataga kowabah, idanuwanta ne suka sauka akan k'ofan daki, Amriya tace "Wai Wacece wannan matar dake cikin wannan d'akin, kitchen tashiga tareda ebo abinci acikin plate, dakuma RUWA, tanufi dakin dashi.
Bud'e d'akin tayi yauma kamar, kwanaki dakin duhu nee, kuna futula tayi, ganin matan amriya tayi ta chunkushe waje daya.
Hajiye mata abinci Amriya tayi tace "Ga abinci kici nasan dacewa kinajin yunwa."
Mika mata abincin Amriya tayi, barar da abinci matar tayi tace,
"Bana bukata, ina bukatar yarona, dana kawai nake bukata."
Fashewa matar tayi da kuka tace "Inason naga dana koda Kallon karshene kafun na mutu."
Amirya tace Waye d'anki, fad'amin nikuma namiki alkawarin cewar zankawo miki shi
."
Matar tabawa amriya amsa da cewar mijinki Kabir shine d'ana na cikina."
Rass gaban Amriya ya bada, Amriya ta ce "Kenen Mom bah itace Mahaifiyar Kalb bah? hakan yana nufin cewa kece fatima wacce aunty amarya tafadamin cewa kinrasa d'anki daga bisani kika rasu?"
Matar tace, "茩warai kuwa ina raye ban mutuba, wannan azzalumar matan ita tadunga azabtar dani bah kakkautawa, ki taimaka kiceci rayuwar dana."
Amriya tace, "Tabbas yau è“·innan, zan tona mata asiri kowa saiyasan abunda ta shuka."
Tashi Amriya tayi tare da fucewa daga è“·akin tanufi dakin Mom , tarar da mom tayi a Zaune tana shan lemon kwalba, Kallonta Amriya tayi tace "Tabbas kin tabbatar min da cewa ke din makura ce a fannin zalinci.."
"Dama bake kika haifi Kalb bah, menene wannan ahalin suka aikata miki da har suka cancanci irin wannan mummunan sakayyar."
"Kin kashe Ummi wacce bataji bah, bata ganiba, kin batarda Salma wacce take ya ta cikinki, Ba iyasuba kinkashe mutane da Dama wanda bazasu irgu bah."
"Me yasa toh ki dakata aka, ya isa, yau zan tona miki asiri kowa yasani agidannan."murmushi mom tayi tace, "Nizaki tonawa asiri? to na fiki hatsabibanci, kafun ke kitona min asiri nizan fara tona naki."
'Daukan wukan dake kan table mom tayi ta yanki Jikinta dashi, tareda fasawa kanta kwalba, inda ta jefawa amriya wukan."
Faè“·uwa mom tayi kasa tareda fasa ihuu wanda yan gidan sukayo hanyar dakin.
Duk abunda Mom keyi Duk a idon Salma, amma babu halin futowa tafada sbd tana a kulle ne.
Bude kofa Kabir yayi, inda su nadira mah suka Iso gurin, Mamakine yakama kowannensu Ganin wuka a hannun amriya, ga mom rai a hannun Allah.
Direct wajan Mom kabir yanufa a firgice yace Mom meyafaru, Mom tace" Zata kasheni, ku taimakeni, kada kubari takasheni..
"
Kallon Amirya Kabir yayi, gaban Amriya ne ya fadi ganin idanuwansa sun kada sunyi jajir, tunda take bata taba ganin ranshi ya 'baci bah sai yau. Hatake yaji wani tsanan Amriya takara karuwa acikin zuciyarshi.
Tashi yayi tareda shake mata wuya yace , "Menene mahaifiyata ta miki kikeson kikashe ta dama ashe mashekiya aka auramin bansanibah?"
Kakari Amriya tafari , sakinta Kabir yayii , inda Amriya ta fara tari, idanuwanta suka ciciko da hawaye tace "Wallahi karya takemin sharri tayimin so take ace ni mashekiya ce."
Mom tace, "Kabir wlh bah karya nayi mata bah, Kuma abunda baka sanibah shine itace ta kashe Ummi sannan ta batar da Ummi sbd bataso na tona mata asiri yasata kokarin kasheni."
Zaro idanuwa gaba d'ayaba suka yi.
馃ス馃槶馃槶馃槶馃槶馃槶馃槶
Allah sarki amriya baiwar Allah koya zata kaya a nan gaba, mujedai zuwa. daga taku baby isha wato Aisha m.B.
COMMENT & SHARE PLS 馃檹馃檹馃檹
ALKALAMIN 馃枈锔忦ç…å©ç¬é¦ƒæžˆé””?
BABY ISHA 馃挒馃挒馃挒(AISHA M.B)
2/28/24, 22:12 - AISHA M.B (Baby isha): Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JYYV16dbYaX1dykLX7EE91
ALJANAR RUWA CE 馃î¡éˆ¥å¶æª§é””忦煂å©ç…‚? PAGE 4锔忊儯2锔忊儯鈻讹ç¬4锔忊儯3锔忊儯
WRITTEN & DIRECTED é‰å¶ç¬ BY BABY ISHA 馃挒馃挒馃挒 (AISHA M.B)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*é‰å¶ç¬
(J.W.A)
Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan 茩asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau茩i.é‰å¿¥ç¬
------------------------
Tass Amirya taji saukan mari a fuskanta, Dafe kuncinta tayi wanda ke mata zugi da radadi,
Kallon kabir tayi ta ce
"Meyasa zaka mare ni?
Saboda kawai na tsaya akan gaskiya, na tsaya, tsayin daka, domin cetan wannan Ahalin."
Shiruuuu, Nadira tafada da karfi, tareda fadin,
"Banyi tsanmmanin aka daga gareki bah Amriya, tabbas kin cutar damu, wane laifi muka Aikata miki? Shin mun taba cutar dake ne tun sanda kike Zaune a gidan nan, koh kuma mun taba tauye miki hakkinki, menene bamu miki bah, duda cewar bamusan ke Wacece bah, aka muka dauke ki kamar yar uwar mu, muka had'a kai muka zauna tare, amma kirasa da abunda zaki saka mana sai tsiya"
Kabir yace Toh a yau bah gobe bah zaki bar wannan gidan.
Dakatar dashi Aunty Amarya Tayi, tace Bai kamata ace kun yanke hukunci ba tareda, kunyi bincike bah, ku yanzu a Sanin ku da Amriya" ta taba yinkurin cutarda daya daga cikin wannan Ahalin? Dan Allah ku dunga bincike kafun yanke hukunci.
Share hawayen da ke shirin zubo mata tayi, tace naji na Amince cewar zantafi, amma Kuma dole a yau bah gobe bah, zan tona asirin wannan makirar" matar, Kallon Kabir Amriya tayi tace, wannan matar da kake Kira mahaifiya, kake bauta mata bah dare bah rana, toh itadin bah mahaifiyar kah bace bah, itadin basaja kawai takeyi, tana nuna cewar ita ta haifeka.
Fashewa" Mom tayi da kuka" tace, yau ni ake karya tawa agaban yayana, da mijina, Allah saiya saka min, Tunda ni na Haifi abuna bah wani bah.
Nuna mata hanyar futa yayi yace, futa daga nan, banason na kara sake hada ido dake, na tsaneki, tsana mafi muni, bantaba tsanan wata Mace a duniyar nan sama dake.
Ka mata Ai ace nasa aka ma min ke, Jami'ai su tafidake, amma bazan yi Akan bah saboda ni nasan darajar Mace, Dan aka fucemin daga gida,
Amriya tace Dan Allah ku saurareni, zanyi maka bayani, wannan bah itace mahaifiyar kah bah, mom itace ta kashe Ummi, takuma batarda Salma.
Rike hannunta yayi yanufi hanyar waje da itah, kokarin kwace kanta takeyi, amma Ya cutura,
Tsakiyan parlour ya nufa Tareda jefata akasa, faduwa Amriya tayi, inda kafanta ya gurde, wani azzababben" Kara tasaki,
Maza kifuta daga gidanan, yafada tareda, jefa mata pillow" a fuska. Yana mai fadin' wai waye ya turoki? Me kike bukata daga wannan family? Shin kudine koh, Dukiya, kokuma" turoki akayi ki kashe wannan Ahalin.
Tukunan mah Wacece?
Mikewa Amriya tayi daga kasan da take, ta Kalli Kabir" tace, nidin ALJANAR RUWA CE, daga teku na futo, Kuma nazo gidanan ne badan komai bah, Dan na karbi zobena da ta subuce tafada hannunka, na ceci rayuwarka batareda nasan ko waye kai bah,
Bantaba tunanin da abunda zaka sakamin ba kenen,
Rike kanshi Kabir yayi yace ALJANAR RUWA, Aljanar ruwa, kin isheni da wannan zance naki, kina tunanin, ni Kabir zan yarda da zancenki cewar ke ALJANAR RUWA CE. Toh ki tsaya kiji ni da kyau, wlh babu abunda nafi tsana da kyama a duniyar nan samada ALJANAR RUWA, su suka hallakar da kakana, bazan taba manta da wannan mumunan ranar bah,
dalilin aka yasa, naci alwashin cewa dole saina zama mai company kifi, don kawai nasamu aka mamun wadanda suka kashe kakana, Hmmm babu Wanda yasan asalin labarin, Dan aka, maza kifuta daga gidanan, Kokuma nasa a kulle min kee a magarkama.
Hada hannuwanta waje guda, Amriya tayi tace, "Naji basai ka yarda dani bah, amma Dan Allah ku yarda da maganata, da macuciya kuke rayuwa, wannan matar muguwa Ce, ita takashe Ummi, Dan Allah ku yarda dani. Gaskiya nake fada muku, ku taimaka ku ceci baiwar Allah dake dakin ......" Bata karasaba, taji Khalid yana Fadin tunda yace "kije, kitafi mana."
Mom dake bayansu tasaki murmushin mugunta, Tareda daukan ruwan dake cikin Glass Cup na kan dining table, ta watsa ma Amriya Ajiki.
Gurnani Amriya tafarayi, inda fatarta yafara sabulewa, faduwa kasa tayi, tana birgima, sosai tsoro da fargaba yakama ko wannensu,
A hankali, sufarta yafara chanzawa, har sufarta na ALJANAR RUWA ya bayyana.
Zaro ido gabadayansu, sukayi, kara su Khalid suka saki, inda gradma tafadi a wajan sumammiya.
Dafe kansa Kabir yayi wanda yakeji kamar, Hana buga masa guduma. Sadiq da Khalid da sauran yan dakin suka jaa da baya, banda Kabir dayayi zololo, yana Kallon tah.
Juyo da jelanta, na Aljanar ruwa tayi tace, "kwarai nidin ALJANAR RUWA CE, nafada maku cewar, nidin ALJANAR RUWA CE, amma kuka karyatani, toh yau na bayyana kaina"
Dama nace Duk ranar da akasan ni ALJANAR RUWA CE, toh zamana a gidan nan yakare. "A yaud'inan zan koma duniyata, banki bah kona mutu konayi rai."
Zan tafi, bazan sake dawowa bah, Hawaye ne, yafara bin kuncinta, share hawayenta tayi, da bayan hannunta, tacigaba da fadin, kiyafemin, Nayi muku karyar cewar, na manta abunda yafaru, kudin mutanen kwarai nee kun zauna dani,
batareda kunsan asalin Wacece ni bah, Kuma yau zaku rabudani, Dan kunsan asalin Wacece nii, ina godiya da irin kulawa da soyayya da kuka nuna min,
Allah yasaka muku da mafifi cin alkhairy.
Ni zantafi, zan koma inda nafuto, amma Kuma taya akan zata yiwu kenen batareda zobena bah, saidai na zauna, a duniyar ku, har sai sanda aka gindaya min cewar zan mutu, idan ban koma duniyata bah.
Kallon kabir tayi tace, nagode da irin wannan sakayyar. Kuma zaka dawo neman gafarata a gareka. Tana kaiwanan, halittar ta yadawo na mutane. Tashi tayi tanufi hanyar waje.
Dakata, taji Kabir yafada, juyowa tayi tace, meyafaru, Kabir yace kin manta baki karbi takardar sakin ki bah, kije na sakeki, saki daya.
Murmushi wanda yafi kuka ciwo Amriya tayi, tace, nagode sosai. Tana kaiwanan ta fuce daga gidan.
Sosai tausayin Amriya yakama su Aunty Amarya.
Direct wajan gradma da mom suka nufa Tareda .watsawa gradma RUWA, Hatake gradma ta farfado daga suman datayi, ririke kabir Tayi tace waiyyo, ku taimakeni, kabir yace aita ruga data yi tafiyarta,
Rike mom DAD yayi yanufi dakin shi da itah, domin yayi mata maganin ciwon dake kanta.
Tafiya Amriya keyi tana kuka, batareda tasan ko ina bah na layin,
Wani bishiya ta hango, akan yasa ta nufi inda bishiyar take tareda, zama a karkashin bishiyar,
Zama tayi, ta chunkushe waje guda, tana kuka, sheshekar kukan tane ya tashi wata mahaukaciya, dake kwance a wajan,
Tashi mahaukaciyar nan tayi, tanufi inda take,
Mahaukaciyar ta ce, "Kai wanene wannan, me yasa kike kuka."
Tausayin Amriya ne yakama wannan, mahaukaciyar, daga Amriya mahaukaciyar tayi, hada ido sukayi da mahaukaciyar, da sauri mahaukaciyar taja da baya. Tana fadin kece, kece,
"Tabbas kece, Kallonta Amriya tayi, tabbas ta gane wannan matar, itace na jiya wanda ta gani a asibity."
Cikeda tausayawa, Amriya tace,
"Kedin Wacece, waye ya mayarda ke aka, menene kika aikata, ke dama asali mahaukaciya ce?"
Tsugunawa mahaukaciyar tayi, tareda fashewa da kuka, tace,
"Dama ni mahaukaciya ce, bansaniba, Dama hauka nakeyi, shikenen Ashe Dama ni mahaukaciya ce, Dama Banida lafiya."
Rike hannunwanta, Amriya tayi tace, ki nutsu, kada kidamu zaki, zaki samu lafiya da yardar Allah.
"Zan warkar dake, zaki daina hauka, Kuma Duk wanda, tayi miki aka saita dandani kudarta."
Rike hannun matan Amirya tayi gamm, Tare da rintse idanuwanta, Hatake aka Fara wani iska, Tareda guguwa, wanda ya gauraye gabadaya ilahirin, wajan.
.
MANAGE PAGE PLS 馃檹馃檹
COMMENT & SHARE 馃檹
ALKALAMIN 馃枈锔忦ç…å©ç¬é¦ƒæžˆé””?
AISHA M.B (Baby isha)
2/28/24, 22:12 - AISHA M.B (Baby isha): https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
JAJIRTATTAU WRITER'S ASSOCIATION 馃枈锔?
(J.A.W)
Rubutu baiwa ce daga Allah,jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan kasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauk'ié‰å¿¥ç¬
ALJANAR RUWA CE 馃î¡éˆ¥å¶æª§é””忦煂å©ç…‚? PAGE 4锔忊儯3锔忊儯鈻讹ç¬4锔忊儯4锔忊儯.
WRITTEN & DIRECTED 馃枈锔? BY BABY ISHA馃挒馃挒 (AISHA M.B)
-----------------------
Jikin mahaukaciyar ne ya fara karkar wa, ta fara shure shure da kafafunta, lokaci daya matar ta kwallah kara wanda ya gauraye dajin.
Daga bisani Kuma tayi Tsit alamun ta tsuma. Kallon ta Amriya tayi, cike da tausaya wa, tace insha Allah zaki samu lafiya, babu wanda zai Kara Kiran ki mahaukaciya,
Tana gama fadin aka ta Mike tsaye Tareda jin ginar da matar a jikin bishiya, daga bisani Kuma tayi tafiyar ta.
Saida dare yayi sosai
matar ta farka daga baccin da takeyi, Kallon Jikinta tayi, taga gany'an yak'i da datti a jikin tah.
Salati tasa ka tana mai fadin, meya ke faruwa dani, menene wannan Kuma? Taya akayi nazo wajan nan. Tambayar data Shiga yi wa kanta kenen. Rike kanta tayi domin ta tuna sanadi yar tah fada wa cikin wannan yana yin, amma akan ya cutura. Ba yadda ta iya, aka tafara ciccire dattin dake jikin ta.
Kallon ko ina na jejin tayi, tace yanzu ta ina ne zan gane hanyar gida, haske ta hango daga Chan nesa, akan yasa ta karasa wajan domin ta nemi taimako".
Zuwan ta keda wuya" ta tarar da Amriya a Zaune a wajan tayi tagumi. Kallon ta matar tayi cikin far gaba da tsoro tace! Sannu baiwar Allah.
Dagowa Amriya tayi ta dora idanuwan ta akan matan. Ganin aka yasa Amriya Mike wa, tace laa kinsamu lafiya, yanzu zaki iya fada min wanda yayi miki wannan aika- aikan
Cikin rashin fahimta doct khadija tace! Kamar ya kenen, Dama kin San ni ne,
Amriya tace, Eh nice na warkar dake daga ciwon hauka da kike, inaso ki fada min Wanda yayi miki aka.
Dafe kanta doct khadija tayi, sai a lokacin ta fara, tuna abunda ya wakana a baya. Kallon Amriya tayi tace,
Wata azzaluma,Mara imani, wacce babu tsoron Allah koh ka d'an a zuciyar tah,Dan zuciyar tah a bushe take. Koh d'igon imani batadashi
Kallon ta Amriya tayi tace, koma Wacece wan nan baza ta taba kai mom rashin imani bah.
Doct khadija tace,wacece ke, meya kawo ki cikin jejin nan tsakar daren nan ,
Amriya tace wacce tayi sanadi yar ki fada wa wannan halin da kike ciki, toh nima itace ta kawo ni jejin nan, tayi amfani da makircin ta wajan kora ta daga gidan. Na tabbata matar nan saita gasa musu haya a hannu,saboda bana nan, Kuma tasa ka sun koreni, Tana nuna musu soyayya a fili, ba tareda sun San cewar azzaluma ce bah.
Doct khadija tace kina nufin Karima devilish mother, Amriya ta bata amsa da fadin kwarai kwarai ita,
Doct khadija tace kenen ke wace a wajan su. Kallon doct khadija Amriya tayi tace, nidin matar wanda take karyar cewar danta ne,
Doct khadija tace kenen kema kin san bah ita ta Haifi Kabir bah? Amriya ta bata amsa da cewar kwarai na sani.
Share hawayen da ke kokarin zubawa Amriya tayi, sannan tace kuma na daukar wa kaina alkawari cewa nida Kara dora kafana a wannan gidan har abada. Koda kuwa akan zaiyi silan ruguje war rayuwa ta, Dama lokaci kalilan ne ya rage mun a raye, kasan cewa ta Kuma ALJANAR RUWA, akan bazai sa na kara taimakon wannan ahalin bah.
Ajiyan zuciya doct khadija tayi tace, tabbas Dan Adam butulu ne, amma kada dalilin aka yasa ki k'i karasa ladar ki na taimakon wannan ahalin, da nice na samu damar da kika samu a wan nan gidan toh da tunan na tona asirin Karima, na bayyana gaskiyar da ke boye wajan shekara da shekaru. Amma ina akan bazai yuhu bah saboda, taruga ta hura musu wutan tsana ta a zuciyoyin su.
Dan Allah inaso ki koma gidan, ki karasa aikin ki, ke kika dace ace kin kammala wannan aikin bah wani bah, saboda kema ta sha feki.
Kwance yake akan makeken gadon sa, yana juyi.gabadaya ya kasa samun nutsuwan sa, tashi yayi, yafara Kai kawo a cikin dakin.
Zama yayi sannan ya dafa kansa yace, menene yake faruwa da ni ne, Meyasa na kasa samun nutsuwa tunda na Kori yarinyar nan. Kardai ta yimin asiri, back to sender, yafada yana shafa kansa.
Daukan wayar sa yayi, ya fara Kallon videos na shiek tijjani, aka ya ci gaba da kalla har aka zo kan wani video.
Playing yayi, yafara kalla, su Ummi ne da nadira wajan upstairs, suna cewa nadira taje, zata yi nasara, shikuma a lokacin sadiq ya kunno kai, Tana shirin fada wa kan kabir, tafada jikin Sadiq.
Dariya yasaki, yana mai fadin wai Dama aka nadira ta ke sona ban sani bah, Gashi Allah yaba ta, mafi alkhairy agare ta.
Next video ya kunna Tareda Kara volume, Amriya ce Zaune tana kuka inda su nadira sai rarrashin ta suke,
Amriya tace Dan Allah inason zanje na basa hakuri, kalisat tace ke haka zalunta Kuma kece da Bada hakuri,
Amriya tace kawai inason zan Bashi hakuri, dalili na mom ta wanka masa mari, da wane ido kike so ya kalle ni, wlh bana son naga abunda zai bata masa rai. Ta karasa maganar Tareda fashe wa da kuka.
Sosai yaji tausayin ta ya kama sa, shafa fuskan ta yayi,ta wayan yace, Allah sarki tabbas na sani cewa koda yaushe cikin kun Tata miki nake,
Baki taba roka ta wata alfarma na cika miki bah, tabbas nidin mugu ne Kuma mara imani, tabbas Nayi dana sani, kiyi hakuri ki yafe min.
Murmushi Aunty Amarya ta saki, babu Kalman da take furta wa sai Alhmadulillah, Alhmadulillah, abunda take ta Nana tawa kenen.
Share hawayenta Aunty Amarya tayi, san nan ta fara Kwan kwasa kofan dakin.
Saurin hajiye wajan yayi, yace, yes who's that at this late time. Aunty Amarya tace nice Kabir,
Kabir yace come in, Shiga ciki Aunty Amarya tayi, tare da samun guri, a gefen gado ta zauna.
Cikin rashin fahimta Amriya tace taya ta shafe ni, menene hadi na dasu, nima zobe na ne ya kai ni gidan, amma da babu abunda zaisa na futo duniyar mutane .asali mah ni na tsani Bil Adama saboda ya wanci su, basuda imani.
Dan aka babu abunda zai kara hada ni da wannan gidan, tunda na barta toh na barta kenen. Zobe na Kuma sai dai na mutu, amma nida gidan nan Ar abada.
Doct khadija tace, kada ki ce aka Amriya na sanki fiye da tunanin ki, a tunanin ki yau na fara Ganin ki, Aa na sanki shekara da shekaru.
Dan aka dole ki koma cikin wannan ahalin, saboda a nan zaki San asalin Wacece ke, menene sanadin fada warki wannan halin, taya ya kika zama wata jinsi da ban bana mutane bah, toh Duka tambayar ki, amsar ta itace wannan ahalin, sune zazu baki amsar tambayo yin ki.
Mikewa Amriya tayi a fusace tace, ni na ce inason Sanin wani abu game da rayuwa ta ne, bana bukata, domin ko na sani koh ban sani bah, lokaci kalilan ne ya rage min a duniya.
Kuma nidin ALJANAR RUWA CE, bah mutum bah, wato so kike na koma wannan ahalin da suka watsa min kasa a ido, akan baza ta taba faruwa bah, Dan aka idan zaki yi wani zance kiyi amma banda, koma wa tah cikin wannan ahalin.
Dan jimmm doct khadija tayi tace, nima a lokacin da, babu abunda ban fada bah, nace bazan kara koma wa wannan ahalin bah, amma nice yanzu nake rabar su, domin na ceto rayu kansu dake cikin hatsari.
Amirya tace wannan Kuma su ta shafa bani bah, tsakanin su ne wannan, su suka San laifin da suka yi har wannan matar take neman rayu kansu ruwa a jallo.
Doct khadija tace, ni kuma idan kika min wannan al farman, kika koma gidan, toh na miki alkawarin cewar,
Zan nuna miki mahaifiyar ki, juyowa Amriya tayi da sauri, tace kin San mahaifiya ta ne, nifa mahaiya ta! ta mutu, Kuma ita din ALJANAR RUWA CE bah BIL adama bah,
Murmushi doct khadija tayi tace, kwata kwata, mahaifiyar ki bata mutu bah, Kuma ita din bah ALJANAR RUWA bace, mutun ce kamar kowa.
Amriya tace kenen mahaiya ta, bah ALJANAR RUWA na ce, BIL adama ce, Kuma tana raye .
Toh Meyasa zata tafi ta barni wajan shekara da shekaru. Meyasa ta wulakan tar dani, bata ko ne mana, akan yana nufin kenen bata damu dani bah? Kokuwa akan yana nufin bata sona.
Doct khadija tace kada kiyi wa mahaifiyar ki gurguwar fahimta, asalima ita bata San kina raye bah, Kuma babu ranar da zata tashi ta fadi bata yi kuka akan ki bah.
Dan aka idan kika cika min alkawari wajan tona asirin Karima, toh tabbas zan kaiki wajan tah.
Share hawayen ta Amriya tayi tace, shikenen zan tafi, zan koma gidan badan komai bah Dan na cika miki muradin ki, amma daba Dan aka bah, da bazan Kara zuwa gidan bah.
Yauwa doct khadija tace, sa'anan ta ce shikenen yata Allah yadawo dake lafiya,
Mi kewa Amriya tayi, lokaci daya jiri ya di beta , da sauri doct khadija ta rike ta, Tareda zaunar da ita tace, meya faru,
Amriya tace wallahi ban sani bah ,tun dazu nake jin zuciya ta na tashi.
Kallon idanuwan Amriya doct khadija tayi tareda Kallon tafun hannunta, tace shin kin keda mijin ki, kun taba yin mu amala ta aure.
Cikin jin kunya, Amriya ta rufe fuskan ta da tafi hannun ta, tace, Eh sau daya ne.
Doct khadija tace kina cikin kunci, ga abun farin ciki ya riske ki, toh na taya ki murna kinada juna biyu,
Zaro ido Amriya tayi gaban ta yayi mummunan faduwa, tace juna biyu fa kika ce, nidin Kuma,
Kallon ta doct khadija tayi tace, me ya faru, kamata ai ace kina farin ciki, da irin wannan abun.
Amriya tace, bawai bana farin ciki bah, tunanina daya ne shine nasan Kalb bazai taba son Dan da zai futo daga kar kashi na bah.
Saboda nidin ALJANAR RUWA CE, Kuma babu abunda yafi tsana a duniyar nan sama Da jinsi na wato na Aljanar ruwa. Kuma ni ina matukar sonsa.
Yanzu Gashi lokaci da ya rage min a duniya kalilan ne. Doct khadija tace kada Ki taba sare wa akan abunda kike so ,dole da jajurce warki da Kuma adua, shine zaisa ki cimma burin ki wanda yake kyakyawa.
Bai ka mata ace ki shiga gidan cikin bakin ciki bah, ka mata ai ace kishiga cikin farin ciki da annashuwa,
Yanzu ki kwantar da hankalin ki, kije gidan cikin karfin gwiwa, Kuma ki fada masa cewar ki nada juna biyu,
Nasan tabbas bazai k'i ki bah. Maza ki tafi, ki Kara karfafa wa kanki gwiwa kada ki saduda tun,kije ki fuskan ce shi, nasan tabbas zai fahimta.
Godiya amriya tayi wa doct khadija, cikin farin ciki ta bar wajan. Tareda nufa hanyar gidan su Kabir.
Aunty amarya lafiya na ganki acikin wannan lokacin, murmushi Aunty Amarya tayi tace, kwarai kuwa lafiya,
Shawara nazo na baka, badan ko bana sonka bah, sai don soyayya da nake maka da Kuma, yan gidan nan.
Okay Tom ina jinki Aunty. Aunty Amarya tace , Kabir inason ka saura reni da kyau, inason fada maka abu dake cin rai na na wajan shekara da shekaru,
Kabir! Dago wa yayi ya kalle ta sannan yace na'am aunty, Aunty Amarya tace, ina son na fada maka cewar, Duk abunda Amriya ta fada dazu babu karya acikin ta, tabbas abunda ta fada gaskiya ne. Mom itace ta kashe Ummi Kuma.... Bata karasa bah taji yace,
Aba Aunty, aba Aunty, koda kowa zai biyi bayan aci dun duniyar mom ai bazaki ciba .
Na tabbatar miki da cewar karya Amriya tayi wa mom, so take ta hada mu nida mom dina, Kuma bata San Allah yafi karfin tah bah.
Murmushi Aunty Amarya tayi, sannan tace, Allah sarki Amriya baiwar Allah, kina taimako, kina sa rayuwar ki a hatsari amma basu San kina yi bah,
Kace ka tabbatar cewa karya Amriya take koh! Kabir yace yes of course, am 100% sure that, karya take yiwa mom.
Aunty Amarya tace tunda ka tabbatar, toh menene hujjar kah.
Kabir yace ni Banida hujja amma nasan mom can never do such thing, idan mah tayi ribar mee zata ci, Amriya kawai yar leken asiri ce, maybe wani ne ya turo ta gidan nan.
Wai kai Kabir Meyasa baza ka yi nadamar abunda kakeyi bah?
Saboda mahaifiya ta, ta tsaya min, Kuma Duk mahaifiyar da ta iya tsaya wa domin Kare rayuwan danta, babu wata ma'alukiya da zata iya cin galaba akan tah.
Kenen kana nufin Amriya bah mutuniyar kirki bace,
Dai dai lokacinda Amriya ta karaso cikin gidan. Jin muryar Kabir tayi, taji yace kwarai kuwa, Amriya bah mutuniyar kirki bace,
Chakk Amriya ta tsaya, Tareda jigina ajikin kofan Tana jin abunda yake fadin.
Kabir yace tunda yarinyar nan ta dora kafa fuwanta a gidan nan, toh tun lokacin masifa da baka'i suke ta faruwa, tabbas yarinyar nan bah mutuniyar arziki bace.
Da nafara dana sani abunda na aikata mata, amma shigowar ki yanzu, yasa na tuna da cewar tabbas mashekiya ce , muguwa Kuma, Mara imani. Baby macen da nafi tsana a duniyar nan sama Da itah. Na tsane ta, na tsane ta, tsana mafi muni, kinga Kare war Ta mah, bana son na kara hada ido hudu da ita, banason na Kara Ganin ta har abadan abada.
Hawaye ne suka Fara gangaro wa daga idanuwan Amriya, hannunta ne suka Fara Kar kar wa, kuka ne ke shirin subuce mata Saurin rufe bakin ta tayi, Tareda rintse idanuwanta jin zuciyar take kamar zata futo..
Tashi tayi daga jikin dakin, inda kuka ya ci karfinta.
Juyawa gabadayan su sukayi, inda Kabir yace waye a nan.
Saurin rufe bakin ta tayi, Tareda Saurin barin gidan.
bude kofan Kabir yayi yaga babu kowa, futowa Aunty Amarya tayi tace shikenen, ni zan wuce, ina fatan ka gane gaskiya. Tana kaiwa nan tayi fucewar tah.
Ya mutse fuska kabir yayi tareda rufe kofan ya koma kan gado ya kwanta.
Tafiya Amriya ta farayi batare da tana cikin hayyacin ta bah. Dafa kanta tayi wanda ke mugun Sara mata. Jiri ne yafara di banta, a daddafe ta karasa wajan junction. Tareda samun guri ta zauna.
Kallon kanta tayi, ta fashe da matsancin kuka mai cin rai.
Meyasa, Meyasa, wannan wace iri yar jarabbta ce, wannan wace iriyar bakar kaddara ce, Meyasa na ka sance a raye har yanzu. Dama na kasan ce a raye ne don kawai naga wannan ranar bakin ciki, ranar da bata da gobe.
Meyasa tun tuni ban mutu bah, na tsane ka Kabir, na tsane ka, bana son sake hada ido dakai, bana kaunar kah,
Kuma wannan ajiyar da ka bani, zan Adana tah har karshen rayuwa ta. Zan kula da abun ciki na har numfashi na, na karshe.
Tabbas zan Nisan ceka, kamar yadda ka bukata , bazaka sake haduwa da koh inuwa ta bah. Karuga da ka Gina min tsanan ka acikin zuciya ta. Rayuwa tah da komai nawa, nasa a hadari don kawai naga, baka cutu bah, amma akan baisa ka gani bah.
Ta karashe maganar tana mai fashewa da kuka, mai ratsa zuciya.
馃ス馃ス馃ス馃ス馃ス馃ス馃ス馃ス
COMMENT & SHARE PLS 馃檹馃檹馃檹
ALKALAMIN 馃枈锔忦ç…å©ç¬é¦ƒæžˆé””?
BABY ISHA 馃挒馃挒馃挒
(AISHA M.B)
2/28/24, 22:12 - AISHA M.B (Baby isha): https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
JAJIRTATTAU WRITER'S ASSOCIATION 馃枈锔?
(J.A.W)
Rubutu baiwa ce daga Allah,jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan kasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauk'ié‰å¿¥
ALJANAR RUWA CE PAGE 44?45
WRITTEN & DIRECTED BY BABY ISHA (AISHA M.B).
-----------------------------------------
Kallon wajan gidan Amriya tayi tace, ya Allah, kada ka kawo abunda zaisa na Kara sanya kafafuwa na acikin wannan gidan, insha Allah baza ka Kara ganina bah na har abada, har abadan abada.
Mike wa tayi, ta Fara tafiya, Chan cikin dajin wajan ta nufa ta tarar da doct khadija a Zaune, Kallon ta doct "khadija tayi cikin rudewa tace,
yata Amriya, me yafaru?, Meyasa kike kuka? shin Kabir ya Kara bata miki rai nee? tambayar da doct khadija ta Shiga yi wa Amriya kenen.
kuka Amriya ta Kara fashe wa dashin cikin, kuna da bakin ciki, tace doct khadija na aikata wani kuskure mara goguwa a rayuwa ta, wai shin yaushe kuka na da bakin ciki zai zo karshe,
Nayi dana sani futowa daga ruwa nazo duniyar mutane, Meyasa banyi za mana a ruwa bah, Kalb ne yayi sanadin futowa ta daga ruwa , abunda na futo karba daban, abunda na tarar daban, Meyasa
na tsane shi, banason sa, tunda aka yake so zaiga asalin tsana Daga Aljanar ruwa, wallahi, yanzu ji nake kamar na kashe shi nima na kashe kaina.
Saurin rufe mata baki doct khadija tayi tace, Aa Amriya kada ki Bari zuciyar ki ta kaiki nesa, kada ki Bari shedan ya rin jaye ki, komai yayi farko zaiyi karshe, ma hakuri mawada ci, idan kikayi hakuri zaki dace.
Amriya tace, hakuri na me, hakuri na nawa, wane hakuri ne nan banyi bah a wannan rayuwa, ya wulakan ta ni, yaci min mutunci, zagi ba dare bah rana, yace min kaskantaciya, Duka zagi Ba bu abunda baiyi bah.
toh fadamin shin Nayi hakuri koh banyi bah, na tabbata da wata ce bani bah, wallahi saita iya kaishi ga hallaka..
kinga Dan aka yaje na bar masa zoben, Dama rayuwa tah bata da amfani, Kuma cikin kwanan na zan mutu, kamar yadda gumurzu ya fadamin. inaso zanga abunda zan haifa a duniya kafun Allah ya dauki raina.
insha Allah babu abunda zai same ki cewar doct khadija, ta cigaba da fadin, kada kidamu, duda cewar Ahalin Muhammad sun tsane nii, saka makon sharrin da Karima ta min, amma akan bazai hana ni na je na bayyana musu gaskiya bah, dole Su san abunda Karima ta shuka.
Karima tayi min abubuwa da Dama Mara misaltuwa. ta raba ni da yan uwana, ta rabani da yar uwata mafi soyuwa a gareni, ta kashe min dana, Wanda iya shi Allah ubangiji ya bani, ta sanya na raba da da mahaifiyar sa, ta kuntata wa rayuwa ta.
tasa na aikata babban zunubi amma akan baisa ta rabu dani bah, dole ne na dauki mataki akan tah, shiru bazai yi magani bah, saidai abu ya Kara baci.
Amriya tace, Dan Allah inason kikaini wajan mahaifiyata, inason zan ganta.
Kallon ta doct khadija tayi tace, zan kaiki kamar yadda kika bukata amma yanzu lokacin kaiki baiyi bah, dole sai mun kashe wutar dake ci a gidan Muhammad kafun na kaiki,
Amriya tace bazan karya rantsuwa ta bah, nice miki bazan sake dora kafana akan wannan gidan bah.
murmushi doct khadija tayi tace, bazan ga laifin ki bah, saboda kina da hujja tayin akan, Kuma akan bazai sa naji bah dadi bah,
Amriya tace zan cigaba da zama na a nan dajin har sai lokacin da zan sauka lafiya. Aa Amriya" bai kama ta ki zauna a nan bah, kama ta Ai ace kin samu gida, Wanda za'a dunga kula dake.
ki tawo Tareda ni, zan kaiki gidan ka wata doct Amina, na tabbata zata kula dake harda abun cikin ki.
Aa doct khadija, ki barni na cigaba da zama a nan shine zai fiye min sauk'i, saboda idan ina cikin jama'a, zan dunga jin zuciya tah na kuna, inaso na zauna ni kadai.
Aa Amriya kiyi hakuri, ki tawo dani muje, Banaso na kaiki gida na, saboda har yanzu Karima bata San ina Raye bah, Kuma idan ta gano baza ta bar ni har ke bah, Dan aka ki tawo na kaiki gidan kawa ta Dan Allah.
shikenen, zanje amma da sharadi, Doct khadija tace inaji ko menene ki fadamin .
Amriya tace, zaki je gidan su Kalb, kamar mahaukaciya, Kuma sannan kice musu, mahaiyar Kalb Tana Raye, what doct khadija tace, Tana mai fadin kinsan ko me zanyi bazasu taba yarda bah, Amriya tace kawai kiyi abunda na fada miki .
shikenen, Doct khadija ta fada, Tareda fadin, zanje Kuma zan fada musu. insha Allah gobe goben nan.
ki taso muje gidan doct Amina,cewar doct khadija. Amriya tace, Aa ki Bari gobe. Tom shikenen, Allah ya kaimu goben.....
Washe gari da sassafe Amriya da doct khadija suka wuce gidan doct Amina.
Kwan kwasa gate din gidan sukayi, inda mai gadi ya bude musu Ganin doct khadija ce, yasa mai gadi ya bar su suka Shiga, yayi musu rakiya har wajan corridor din, parlour. Shiga ciki doct khadija tayi bakin ta rike da sallama.
Kabir inason muyi wata magana mai mahimman ci da Kai, dago kai Kabir yayi ya dora idanuwansa akan mom yace mom inajin ki.
mom ta cigaba da fadin, kasan wannan yarinyar kirkin wato zainab yar gidan Alhj usman, Kabir yace Eh nasan zainab, naga yarinyar Tana da tarbiya, Kuma tana da hankali, mezai hana ka aure ta domin d'aga darajar Ahalin mu.
Dan jimmm, Kabir yayi, yace naji dadin wannan Shawarar mom, amma am sorry to say, i can't marry zainab, she's not my type. bata Kai tsarar da zanso tah bah.
and mom as for me, inada wacce nake so, Kuma ni ban shirya yin wani aure bah yanzu gaskiya. Mom tace, shikenen Kabir, amma na Tambaye kah, shin tunda kake ka taba tambaya ta wani abu a duniyar nan, ban maka bah.
Duk abunda kake bukata shi nake maka amma, shine bazaka iya cika min wannan muradi nawa bah, shikenen bakomai, zaka iya taciya.
Dafe kansa kabir yayi yace, mom ki tambaye ni wani abu ko menene zanyi,.amma banda auren zainab.
mom tace, auren zainab shine muradina, inason ka aure ta, Dan Allah, ta Fada tana hada hannayen ta guri guda.
shikenen mom naji zan aure tah, cikeda farin cikin jin furucinsa, mom tace da gaske kake zaka aure ta. Kabir ya bata amsa da cewar da gaske nake zan aure tah, shikenen kinyi farin ciki koh, ya fada yana Murmushi, mom tace farin ciki mara misaltuwa mah.
yanzu inason yau kaje ka ganta a gidan su, kaji, Tom mom naji, farin cikin ki shine farin ciki na, banason na ga bacin ranki kwata kwata,
tashi yayi yace, zan tafi saina dawo, mom tace Allah ya dawo dakai lafiya. Kabir ya amsa da Ameen.
Kallon su Nadira Kalisat tayi, tace, kuna Ganin abunda aka yiwa Amriya yayi Daidai kuwa, Meyasa za'a yanke mata irin wannan tsatsauwar hukuncin.
Nadira tace, Meyasa ba za'a yanke mata bah, kokarin kashe mom fa tayi, Kuma ita ta kashe Ummi, kama ai ace an yanke mata hukuncin kisa.
fatima tace kwarai kuwa, amma saboda yahya Kabir yaji tausayin ta yace tayi tafiyar ta, mu mun rike ta da hannu bibbiyu., bamu taba yin kurin kashe ta bah.
kalisat tace dukkan ku, bakuda tunani , a ranar da abun ya faru,. naga mom da idanuna ta dauki ruwan dake kan dinning ta watsa wa Amriya.
Nadira tace toh Dan Mom ta watsa mata ruwa mene akan yake nufi, kalisat tace mom ta Daidai tah lokacin da Amriya ta keson fadar wata magana.
kinga akan yana nufin Mom tana da wani kulla kulla acikin ranta, Kuma akan yana nufin Amriya bah karya ta fada bah, gaskiya ne,
Fatima tace Aba Kalisat, Meyasa bakida tunani nee, wannan abunda kike fada, babu hankalin da zai daukeshi, koda kin fada babu Wanda zai yarda saboda, Mom baza ta taba aikata abunda zai cutar da wannan Ahalin bah bare Kuma y'ay'an tah.
Kalisat tace hakane, amma saina war ware abunda ya sanya kowa cikin duhu.
Nadira tace oho Ke kika sani, kya yi kya gama, amma Duk abunda zaki yi, daga karshe Mom itace da gaskiya Ba Amriya bah.
mikewa Kalisat tayi tace, aida yar uwarku ce bazakuBazakuce aka bah, amma kuma ni ina goyon bayanta, zan tsaya mata har sai inda karfina ya Kare, zan nuna mata cewar Tana yar uwa kuma wacce kuma zata tsaya mata tsayin daka, domin futo da gaskiya. Tana kaiwanan tayi fuce warta.
ikon Allah doct khadija nake gani aka a gida na, murmushi doct khadija tayi tace, Eh wallahi, hayyuka ne suka min yawa shiyasa kika ga bana zuwa office.
doct Amina tace wa nake gani aka kamar Amriya, gaishe ta Amriya tayi, amsawa doct Amina tayi da fadin lafiya kalau y'ata, ya mijin naki, da fatan yana cikin koshin lafiya.
Sosa Kai doct khadija tayi tace yana lafiya, Tareda fadin Amina inason mudanyi wata magana dake a sirrince, doct Amina tace, okay bah Damuwa,
Kallon
Amriya doct khadija tayi tace Amriya ki shiga daki kinji, Tom Amriya ta tace tareda mikewa tsaye, ta nufi cikin guest room.
komai da komai, daya faru doct khadija ta zayyane wa doct Amina, amma doct khadija bata ce mata Amriya ALJANAR RUWA CE bah.
Girgiza Kai Doct Amina tayi tace, Dan Adam ba'a iya masa, babu komI kawa ta, zan kular miki da ita har Dan cikin ta, kada kidamu itama ai tamkar y'ata take.
godiya doct khadija tayi wa Doct Amina, doct Amina tace Aba kawa tah ai a tsakanin mu babu godiya.
tashi doct khadija tayi tace, shikenen ni zan tafi, inaso zan kai wa yan uwana ziyara,
shikenen toh Allah ya kaiki lafiya cewar doct Amina, amma shin bazaki tsaya kici breakfast bah, Aa wlh na koshi. saina dawo tana kaiwa nan doct khadija tayi fucewar tah.
bayan fucewar doct khadija, doct Amina taTaShiga dakin da Amirya ta Shiga, Amriya na ganin ta ta Mike, Aa y'ata zauna mana cewar doct Amina.
me kike so kici zan dafa miki, Girgiza kanta Amriya tayi tace na koshi, wannan Kuma bazai yuwu bah, babu abunda kika ci fah amma shine kike cewa kin koshi, toh ki taso akwai abinci akan dining kitawo muje muci koh, sannan na baki magunguna kisha.
Amriya tace Aa na koshi, banajin yunwa, doct Amina tace toh shikenen nima bazan ci abinci bah,kowa ya zauna aka.
murmushi Amriya tayi hawaye na son zubo mata Saurin share su tayi tace shikenen, Doct Amina muje zanci .murmushin jin dadi doct Amina tayi tace Yauwa y'ata ko ke fah,
taso muje koh, bayan mungama cin abinci zan ce da babban dana yusuf ya kaiki shopping kiyi siyayya ,shima kidauke shi tamkar yayan ki kinji .
tashi sukayi suka nufi dining, inda suka tarar Abban yusuf da yusuf na Zaune, da alama su suke jira.
serving dinsu doct Amina tayi ,inda itama taja gefe ta ibi nata, suka Fara ci.
oh my God sir Kabir ne yau a gidan mu, Kuma wai yazo hira wajena, Tsaki Kabir yaja, yayi murmushin takaici yace, ke ni yanzu zan tafi, idan na tafi ki kira Mom kice mata bakya sona bazaki iya aurena, bah inba aka ranki ya baci.
zainab tace Aba masoyi yaushe kazo, da har zaka tafi, shikenen zan fada mata amma Dan Allah inason ka kaini shopping, yau ranar fah masoya nee Valentine day, ya Kama ta ace ka bani babbar kyauta,
toh nida ke naga Ba soyayya muke, bah Dan aka, ki kiyaye ni kinsan ni bah tsarar ki bane wallahi,
aba sir Kabir please, and please, Dan Allah, ke naji shikenen, zan jiraki a waje, wlh idan baki futo bah nan da 20second, tafiya zanyi, Dan bazai yu nazama, bawan ki bah tohh.
yana kaiwa nan yayi fucewar shi , Kai na rawa Zainab ta dauki gyale Dan karami wanda dashi gwanda babu.
futowa tayi ta Tarar dashi yana shirin tafiya, Saurin daka tar dashi tayi sannan ta Shiga cikin motan, yabar harabar gidan.
Yauwa Yusuf inason ka kaimin kanwar ka shopping, kaji, yusuf yace Ammi consider it done. ni naga shirya wa, ban dai sani koh kanwa ta taga ma shirya wa bah.
Amriya tace ni a shirye nake, bayan sun gama cin abinci, yusuf ya dau mukullin mota yayi hanyar waje, hijabi, Ammi ta bawa Amriya, saka wa Amriya tayi ta bi bayan yusuf, bude mata gaban mota, Yusuf yayi ta Shiga.
tareda barin harabar gidan. direct shopping mall, suka nufa, Daidai lokacin suma su kabir na isa wajan.
bude wa Amriya kofa yusuf yayi , futowa Amriya tayi daga cikin motan suka nufi cikin mall din.
Rike hannun kabir zainab tayi wafce hannun sa kabir yayi yace ,are you normal, kada ki karamin irin wannan abun in badan Mom bah Allah koh a matsayin yar aiki bazan iya daukan ki bah bare Kuma azo kan wai mata.
hakuri zainab ta Bashi inda suka Shiga wajan mall din.
inda ake saida kyaututuka suka nufa, gabadaya masoya sun cika wajan, kowa yana siyawa budurwarsa kyauta.
saida su yusuf suka gama siyayya sa'an nan suka nufi wajan saida gift, Yusuf yace kan wata yau fah ranar masoya nee bazaki siya wa masoyinki kyauta bah, Amirya tace bani da masoyi. yusuf tace toh muje ni na siya miki saina baki kyauta a matsayinki na kanwata,
Aa wallahi ka barshi, nagode, Yusuf yace no bazan yarda bah, wato kina k'in kyauta daga wajan yayan ki.
wajan da ake saida Valentine Gift yusuf ya nufa da Amriya.
wata kyauta Kabir ya dauko ya damka wa zainab, Cikeda farin ciki zainab ta rungume shi,a bai nan nasi. Daidai lokacin idanuwan Amriya suka sauka akan su Kabir.
Cikeda bakin ciki da takaici, Amriya tajawo yusuf tace inason mubar nan wajan, Dan Allah, yusuf yace why? baki ga wasu masoya bah sun rungume juna, Dan aka kawai ki bari na siya miki.
Saurin cire jikinshi kabir yayi daga na zainab yace, ke wace mahaukaciyar ce, taya zaki rungume ni a gaban jama'a.
bakida hankali ne, kayi hakuri, kaji my love.
Cikeda takaici Amriya ta dauke idanuwan ta daga kansu, ta Kalli yusuf tace, sweetheart, ni wannan nakeso tayi nuni da hannun ta,.
da sauri kabir ya juyo jin kamar yasan wannan muryar, hada ido sukayi da Amriya Hatake gaban shi ya fadi.
Amriya ta cigaba da fadin Sweet, wannan nake soo, yusuf yace kada kida mu, zan siya miki koma Wanne,
wani irin kishi ne ya turnuke zuciyan Kabir, nufan inda suke yayi tareda Jan hannun Amriya yace, waya baka izinin futa da matar wani, kaidin waye
ke Kuma ya fada yana Kallon Amriya, Dama Ashe ke yar iska ce, uban waye ya baki izinin futa da wani na mijin, Dama abunda ke faruwa kenen idan ka auri karuwa,
Tasssss Amriya ta tsinka wa Kabir mari.
zaro idanu jama'a wajan sukayi. nuna Kabir Amriya tayi da Dan yatsan ta tace...
.
COMMENT & SHARE PLS
KUYI HKR JIYA KUNJI SHIRU WLH WAYANA NE YASAMU MATSALA,
AMMA INSHA ALLAHU ZAN GYARA
ALKALAMIN AISHA M.B ( BABY ISHA)
BISSMILLAHI RAHAMANI RAHEEM
ALJANAR RUWA CE PAGE 45&46
WRITTEN & DIRECTED BY
AISHA M.B (BABY ISHA)
---------------------------------------
Cikin baccin rai Amriya tace, har kai waye, Da zaka zo ka neman cimin zarafi agaban jama'a, shin na taba ganin ka ne ,koh kaidin mijina ne, da zaka zo kana ci min mutunci,
Bansan ka bah, baka Sanin bah, toh ina ruwan ka dani, kazo da masoyiyar ka, nima nazo da nawa, shin akwai laifi ne aciki, toh ka sani, aure ce ta hada ni dakai , Kuma yanzu ta raba, Dan aka baka da iko akaina, baka San irin muguwar tsanan da nayi maka bah, tsanan da nayi maka koh ma'auni, bazai iya aunawa bah, Kuma kayi na farko, kayi na karshe. Kada koda gigi yasa ka kara aikata min aka, Dan wallahi, abunda zan maka bazaka jita da dadi bah.
Idanuwan "Kabir ne suka kada sukayi jajir! cikin zafin rai, yace ni kika mara, kin manta waye ni, Amriya tace taya zan iya manta da Kai, Dama ai mutum baya taba manta alhery da mutum ya masa, kai baka min alhery bah, aka sin aka mah, zalunta ta , kake yi,
Kallon shi tayi tace, tsaya wa ina magana da Kai bata lokaci ne, maida Kallon ta kan yusuf tayi tace, sweet, Dan Allah ka tawo mu bar wajan nan, naga yan hassada da k'eta, sun cika nan wajan,
Zuwa daf, da wajan zainab tayi tace, ke me kike da suna, wallahi, Kabir yafi karfin ki, kada ki sake kiyi wasa da wuta, domin kuwa idan ta fusata, baza ki ji da dadi bah.
Kallon "Zainab Amriya tayi tace, ke daka ta nan , ni bah sa'ar wasar ki bace, kije kifara ji da matsalan dake damunki, kafun ki kara fada wa a wata matsalan, wallahi, Duk abunda na miki toh ke kika siya da kudin ki.
Tsintar kansa kabir da yin shiru, Amriya na kaiwa nan, ta bar wajan, bin bayanta yusuf yayi,
Tsaki Kabir yaja, ganin kallo gabadaya ya koma kansa, fucewa shima yayi daga wajan, inda zainab ta bi bayan sa, Tana Kiran sunan sa.
Shiga cikin mota yayi, ya tada motan sannan da mugun gudu ya bar harabar wajan, zainab na Iso wa taga yabar mall din.
Tunda suka Fara tafiya babu Wanda ya ceda wani cikan ka, yusuf ne yayi karfin halin fadin, Meyasa kika tozarta Kabir a bainan jama'a, Kuma Meyasa kika ce ni masoyin ki ne, bayan Kuma ni bah masoyin ki bane.
Aba Amriya, Shifa mijin ki ne, bai ka mata ace kin masa irin wannan rashin mutunci bah, bai kamata mah ki mareshi bah, why Amriya, Why?
Dago fuskan ta tayi, wanda suka jiku da hawaye tace, Duk abunda Nayi masa shiya siya da kudinsa, ni menene bemin bah, zagi, Duka, babu abunda baiyi bah.
Tabbas bai kama ta ace na maresa, bah, amma meyasa zaice min karuwa? Kalman da na tsani akira ni dashi, ba iya ni kadai bah, koh wata macen da tasan daraja da kiman ta ta d'iya Mace , ba zata, so a kira ta da Kalman karuwa bah,
Yana min Duk abunda ya gada ma, banta rama wa bah, amma yau, yakai ni kololuwar makurar karshe, shiyasa na maresa, Kuma nasan akan bai dace bah, bai ka mata na mare sa bah, amma duk abunda na Mai shiya siya da kudin sa.