Trending Hausa Novels

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Asanadin_Makwabtaka_Part_3_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 3 of 4

cigaba da tafiya sukai Fauzyn ta k'ara cewa "amman dai suna bala'en kama da Ya Haisam wllh har k'irar jikin kawae bambancin kala ne, amman kin san mi, ni ina son Namiji haka banson wanda ya cika fari" harara Fatuu ta wurga mata tace da bata samu ba ko amman k'arya ne tace wai bata son Namiji fari, dariya Fauzy tay tace "Allah ya baki hak'uri matar fari maida wukar nima na fad'i ne kawai dana samu wanda nike so ni ina ruwana da wani fari ai ko Yellow ne in dai ina son shi auran shi zanyi"

"Yanzu ace yace yana son ki zaki so shi?" tambayarta Fauzyn tay wa, Fatun tace "shi wanccan d'an uwan Ya Haisam d'in" zaro ido Fauzy tay ta kai hannu ta ruk'e ha6a tace "tabbb kema dai da wani bahagon tunani kike wllh, ke yanzu ko wani yace maki wanccan zai so ni zaki yarda mutumin da daga gani zai yi izza ba kad'an ba, ai irin wanccan mutumin wllh matar shi ta bani don kuwa ba k'aramar wahalar shi zata sha ba don daga gani baza'a iya mashi cikin sauki ba, irin su komai akai masu ba'ai masu gwaninta" Fatuu dake dariya tace kawae ta bata amsa in ya ce yana son ta misali da aure zata iya auren shi, shiru Fauzy tay kaman mai nazari can tace "kinga don Allah mu bar Maganar nan abunda baka samu aka ce had'a shi da baka so don haka bai man ba" dariya sosae Fatuu ke yi tana fad'in Allah don bai ce yana son ta bane amman tasan tabbas zata so shi don ta fahimci ya yi mata, murmushi kawae Fauzyn tay zuciyarta na suffanto mata shi a ranta ta raya wannan ta ina ma zai iya wani son ta mima zai yi da ita, daidai lokacin suka iso part d'in da suke suka shiga.

Bayan sun shiga d'akin Toilet Fatuu ta wuce tayo Alwalar sallar isha, bayan ta gama hira suka dasa wadda yawanci duk akan Walimar gobe ce saida suka kai tsakar dare sannan Fatuu ta tashi don tafiya Fauzy tace ta kwana anan kawae mana tace ai gadon bazai ishe su ba tunda akwae wuri can bari taje kawae suka yi sallama dasu Haulat Fauzy ta rakota har waje kafin suka yi sallama ta koma. Washe gari Juma'a ana tashi aka fara shirye shiryen Walima ba kama hannun yaro masu aikin girki tuni sun fara dama tun jiya aka fara aikin nama banda shanun da Baffan Fatuu ya bada harda raguna da kaji aka yayyanka, Misalin k'arfe sha d'aya lokacin duk an gama breakfast Laila tasa Fatuu taje tayi wanka, da kanta taje d'akin Hajiya da yake nan aka kai akwatunan lefenta ta d'aukko mata kayan da zata saka wanda babbar Super ce ta had'u ba k'arya anyi mata straight skirt da riga half gown tare da sark'a da yankunan gold harda yan hannu da su jaka da takalmi da mayafi mahad'in kayan, bayan ta saka kayan Laila ta yi mata yar light make up kafin anjima wadda zata yi mata Bridal makeup d'in ta zo, da kanta ta d'aura mata kallabi abun sai dae ace Tubarkallah, nan fa aka hau yi mata hotuna bayan sun gama Laila ta kamata ta nufi d'akin Mom d'in su da ita, a parlor suka isketa da wasu mutane cikin yan uwan su da suka zo bikin Mom d'in na ganinta ta hau yi mata murmushi tace a kawota gefenta, bayan ta zauna ta gaishe da ita da sauran mutanen ana ta fad'in Ma sha Allah Amarya, mik'ewa Mom tayi ta kamo hannun Fatuu itama ta mik'e suka shiga cikin Bedroom harda Laila, wurin Hajiya Zainab ta kai ta, itama da murmushi ta tarbeta Mom ta sata ta zauna a bakin gado itama ta zauna a d'ayan gefen, gaida Hajiya Zainab d'in tayi da fara'a ta amsa ta yaba gayun nata tare da Addu'ar fatan Alkhairi Laila na amsawa daga baya ta kama hannun Fatun tace suje wurin Hajiya ta mik'e suka nufi hanyar fita idanun su Mom akan su, bayan sun fita Hajiya Zainab tace yarinyar nada kyau Mom dake murmushi tace sosae, part d'in Hajiya suka wuce bayan sun fito, duk suna zaune a parlor suna ta hira harda gwaggo suka shigo Laila tayi sallama duk suka maido idon su kan su suna amsa sallamar, gaishe da Mutanen parlon tay duk suka amsa, gefen Hajiya ta kai Fatun ta zaunar da ita tana murmushi tace "ga kishiyar ki na kawo kiga adon ta" d'an murmushi Hajiya tay ta ta6e baki tana kallon Fatuu da itama kallon ta take tana murmushi sai cewa tay ina ta wani yi kyau haka kamar an bad'a mata k'asa a fuskar, gaba d'aya yan d'akin sukai dariya suna fad'in duk kyaun nan da tayi wannan dai kishi ne ba wani abu ba Gwaggo dae sai murmushi take farinciki fal ranta ganin yadda Autarta ta fito sai kace d'iyar manyan mutane, gaishe da Hajiyar tayi bayan ta amsa ta juya kan sauran mutane ta gaishe da su da fara'a duk suka amsa suka hau yin Addu'oi Laila dasu Hajiya na amsawa daga baya suka bar part d'in, baya suka wuce inda su Haulat suke, lokacin da suka shiga cikin parlon su Yadikko dasu Yaya duk suna zaune suna yin kallo, wurin su Laila ta nufa duk suka maido idon su kanta suna washe baki, zama tayi akan kujera Fatuu ma ta zauna a gefen ta suka hau gaishe da ita, da fara'a ta amsa Yadikko ce tace "wannan kaman Amarya" sai lokacin Laila ta gane ashe basu gane Fatun ba tana yar dariya tace itace ta kawo masu suga gayun ta gaba d'aya suka k'ara washe baki suna fad'in ai su basu ganeta ba Fatuu dai sai murmushi take ta gaida su,Yadikko ce ta daddage ta rangad'a gwad'a sai ga su Mino sun fito da gudu ta nufo ta ai koda taga Fatuu da gudu ta koma cikin d'akin tana fad'in azo aga Adda Fatuu Amarya tayi kaman sarauniya, nan duk suka firfito harda su Aunty Mareeya Fanan ma na a d'akin su tafi zama a wurin su duk da a d'akin Laila ta sauka, nan fa aka shiga yabon gayun aka hau yin hotuna da ita Fanan tace ai yakamata a kawo photographer Saboda ayi hard copy na tarihi Laila tace zai zo sai anjima sunyi Magana yace na iPhone d'in ma lafiya lou zai wanke su tace Ok, bayan sun gama hotunan Laila ta k'ara kamo hannunta ta fito da ita, part d'in Haisam ta wuce da ita suka shiga ta baya, knocking k'opar tayi aka bata izinin shigowa ta tura, su biyar ne a zaune, Haisam, Sameer, Salim, Abbas sai wani abokin su d'an nan Abujar Na'eem, da murmushi Laila ta nufi cikin parlon idanun su gaba d'aya akanta banda Sameer da yake sanye da headphones da alama ma bai san ta shigo ba, tunda suka shigo idon Haisam na akan Fatuu suna ta sakar ma juna murmushi, gaishe su Laila tayi tace ga Amaryar su nan ta kawo masu su ga gayunta na farko duk suka maido idon su akan Fatuu, kunya ce ta kamata da sauri ta sunnar da kanta k'asa ta gaishe dasu Abbas ya shiga tsokanar ta, mik'ewa Haisam yay jikin shi sanye da k'ananun kaya basu dad'e da gama yin Breakfast ba, inda suke tsaye ya nufo yana zuwa ya kai hannu ya kamo Fatun kawai sai ya rungumeta gaba d'aya Abbas da Na'eem suka sa sowa shi dai Saleem murmushi yake, abunda su Abbas ke yi ne ya jawo hankalin Sameer ya d'ago ya kalle su Abbas ya fara masu Video, gaba d'aya wata irin kunya ce ta kama Fatuu ji take kaman ta nutse k'asa, kokarin d'ago da kanta ya fara yi ta kafe kan tak'i yarda ya d'ago ta, d'ukar da kan shi yay can k'asan mak'oshi ya furta tayi kyau sosae murya can k'asa tace don Allah kunya take ji ya fita da ita ya furta Ok, d'agota yay tak'i yarda ta kalli side d'in da su Abbas suke yace ma Laila suje yana ruk'e da Fatun yayi mata side hug suka nufi hanyar fita ta cikin parlon Sameer dake kallon su ya d'an ta6e baki da yanayin d'an murmushi akan fuskar shi, suna fitowa wayar Laila ta fara yin ringing tace masu tana zuwa pls ta d'an yi gaba tana amsa wayar, maido Fatun yay jikinshi ya rungumeta ta yadda suna kallon fuskar juna sai yamutsa mashi fuska take tana fad'in ita kunya take ji don Allah, yana murmushi idanun shi a d'an lumshe yace to mi yay mata da zai zama abun kunya da ido tay mashi nuni da rungume tan da yayi, ce mata yay wannan ba wani abu bane yake ma yan'uwan shi ma balle ita matar shi, sai faman tura mashi baki da ya sha jambaki take gaba d'aya hakan da take ya fara turning d'in shi on, kallon ta kawae yake tana mashi shagwabar kar wani ya gan su don Allah, slowly ya duk'ar da kan shi saitin nata ya kai bakin shi kunnanta ya rad'a mata magana, d'agowa yay ya d'age mata gira tace "Yaushe?" a hankali ya furta "after isha" shiru ta d'an yi kaman mai nazarin wani abu taji yace ko bata so da sauri ta girgiza mashi kai, Laila ce ta dawo wurin su tana murmushi da sauri Fatuu ta juyar da fuskar ta, ce ma Haisam d'in tayi ko ta barta a nan ne ba tare daya ce komai ba ya saki Fatun Laila ta kamo hannunta suka nufi sauka daga benen tana yi tana d'an waiwayen shi yana tsaye bai koma ba fuskar shi da d'an murmushi har suka sauka sannan ya koma ciki.

Lokacin da akai Sallar juma'a hidima ta kan kama bak'i yan Walima tuni sun fara zuwa, bayan an yi salla mai makeup tazo lokacin Fatuu na d'akin Laila ta shirya cikin dandatsetsen lace Swarovski d'an dubu d'aruruwa anyi mata d'inkin riga da skirt tasa su sark'ar diamond abun ba'a magana jikin Fatuu ya zama kud'i ko ince kud'ad'e, ba 6ata lokaci aka fara mata bridal Makeup d'in, tun ana cikin yi ake aikowa kiranta daga d'akin Mom don tazo a ganta, Laila ce ta kira Mom d'in nasu ta sanar mata ana mata kwalliya ne in aka gama zata kawo ta, Jama'a kuzo kuga Fatuu ya fillo don Allah ni Saboda kallon ta ma har saida Alk'alami na ya fad'i, abun sai dai ace Tubarakallah Ma sha Allah an k'ara jik'a kyau da ruwan Naira abun ba'a magana, Nan aka shiga yi mata hotuna harda su Video mai makeup d'in ma tana ta mata don ta d'aura a handles d'inta na social media gashi da yake Fatun a wayancenta take abun sai ya tsaru sosae, ana cikin yi Jidderh ta shigo tasha ankonta an mata yar Arzik'in Fitted gown (bana ce matsiyaciya ba😂) sosae d'inkin ya had'u an tsara shi da mix and match d'in ta fito a yar matan Abuja, ce ma Aunty Laila tayi Mom tace a kawo ta hakanan Friends d'inta ne zasu ganta, wani had'add'an gele mai shara shara ana ganin komai na jikin mutum baida girma sosae ta d'aukko ta yafa mata tasa takalma nasu tsini sosae hannun ta ruk'e da yar purse d'in su Laila ta kama hannunta suka tafi,

bayan sunje a parlor suka tsaya Mutanen ciki suka hau yabon gayun Amarya daga baya ta wuce da ita cikin Bedroom, duk k'awayen Mom ne a ciki wasu anko ne a jikin su na full embroidery har Hajiya Zainab ma da Mom ankon ne a jikin su anyi masu dogayen riguna sunyi kyau abun har ba'a magana, harda Hajiya Kubra ta Comment section a cikin su ashe itama mutuniyar First Lady ce tasha anko full embroidery, ciki Laila ta shiga da ita Jidderh ma na biye da su, bin su d'aya bayan d'aya ta shiga yi da Fatun suna ganinta tana gaishe dasu sai yabon kyaun ta suke nan aka shiga bata kyautar kud'i Laila na amsar mata harda wadda ta bata kyautar yan kunnan zinari ita dai Fatuu sai murmushi kawai take bakin ta ya mutu abun ya girmi tunanin ta, abun mata sai ya zama kamar gasa ma, ita Hajiya Zainab Account details d'in Fatun tace abata aka sa sowa ana mata kirari sai murmushi take daga baya aka kaita wurin Mom ta zaunar da ita kusa da ita a hankali Fatuu ta gaisheta tana murmushi tace "Ma sha Allah Daughter kin yi kyau" tace mata ta gode, bayan sun gama da nan Laila ta fito da ita suka nufi part d'in Hajiya daga nan kuma bayan sun fito baya suka nufa gaba d'aya rud'ewa su kai da ganin yadda Fatuu ta had'u, anan Laila ta barta ta tafi itama ta shirya don duk kusan kowa ya saka ankon shi kowa ka gani atamfar tayi mashi kyau daga bak'ak'en har fararen, sosae Fauzy da Mino suka yi kyau ita Fauzy fitted gown ce Mino kuma riga da skirt, su Aunty Mareeya da Feenah duk dogayen riguna aka masu styles masu kyau kalar na yan Abuja Fanan itama fitted gown aka mata sosae tayi kyau gashi a jikin atamfar akwae kalar gashinta, da Laila zata tafi ta bita don ayi mata makeup itama.

Da lokacin cin Abinci yayi a parlor aka shiga jerawa saman Dining tables an k'ara wasu guda ukku suma masu cin mutum sha biyu sai aka matsar da set guda na kujeru aka had'e su, Abinci ne kala daban daban sai wanda Mutun ke so sai kuma mutum ya ci ya ture nama kuwa ba don kar inyi k'arya ba sai ince duk tsoka tayi dunkulan hannun mutum in ma bata yi ba to ta kusa🤧 ga kaji Malam, drinks da ruwa su wannan kaman company d'in su ka zo ma, bayan an gama tsara wurin aka je aka sanar ma Mom da Aunty suka fito da Mutanensu aka zazzauna yan baya ma su Aunty Mareeya aka masu magana suka fito, yadikko bata son suje ai kauyanci hakan yasa taje tayi ma gwaggo magana kan in zai yiwu akawo masu nasu can gwaggon ta fahimceta tace to,

Table guda duk k'awayen Mom ne harda Hajiya Zainab Wani kuma Aunty ce da K'awayen ta wanda wasu k'awayen su ne gaba d'aya ita da Mom, a d'ayan table na ukku su Aunty Laila ne harda Amarya Fatuu da K'awayen su sai table na k'arshe nan su Aunty Mareeya suke harda Fanan da wasu yan uwan su yan Daura Ma'aikata nata Serving nasu abun gwanin burgewa kowa harkan gaban shi yake bai damu da yadda wani ke cin Abincin shi ba, a can cikin parlon ma a saman kujeru akwae mutane zazzaune suna cin Abincin, Haisam na part d'in shi da Abokan shi harda Najeeb da ya iso da daddare ya sauka a guest house d'in baban shi suma suna cin Abincin haka Nameer ma yana a part d'in shi da su Kawu Amadu da Tk da wasu Abokan shi, Senator ma na a part d'in shi da wasu Abokan shi da kuma yan uwan shi harda Baffan Fatuu dasu Ardo, sai da Baffan yayi masu hud'uba cikin hikima da zasu zo ya nuna masu abunda yakamata suyi don nan ba komai a ke masu ba sudai gyad'a kai ne nasu don yanzu mulkin ya koma kan Baffan Fatuu, duk wanda yazo sai Senator ya nuna masu dangin Amaryar sun gaisa, abun dai sai dae ace Ma sha Allah don Walima kam tayi Walima an ci an sha anyi hani'an kowa ka gani fuskar shi cike take da annuri bayan an gama aka hau yin hotuna gwaggo taje ta kira su Yadikko suka zo suma akayi hotunan da su, Fanan da kanta taje part d'in Haisam ta kira shi don ayi hotuna suka dawo dashi yana sanye da Farar shadda haka takalman shi da agogon shi duk farare ne yau dae Allah yayi an rufe kan da hula babbar rigar shi na ruk'e a hannun shi tare da Abbas suka fito shima yana sanye da riga da wando na farar shadda, idon Fatuu akan shi har suka k'araso wani irin dad'i take ji kaman ta kama yin rawa a yau ta k'ara jinjina girman Ubangiji ta k'ara gasgata Kalmar nan ta mahakurci mawadaci ne, bayan sun shigo Photographer yaci gaba da aiki, Mom da kanta ta kirawo Senator da Nameer don su zo ai hotuna dasu harda su Kawu Amadu su ka zo daga baya Senator d'in ya koma Saboda mutane d'aya baro, ana cikin hotunan Jidderh tazo wurin Fatuu tace mata ga bak'uwa Daddy yace akawo ta wurin ta, da farko Fatuu bata gane bak'uwar ba dake ta kallonta tana dariya hannunta ruk'e da yarinya da bazata wuce watanni ba, sai can da tay magana tace ma Fatun hala bata ganeta ba sannan Fatun ta d'an waro ido tace "Kaman Aunty Sadeeya?" tana dariya tace itace, mamaki ne ya kama Fatuu ganin k'anwar Khalid a wurin, hoton akayi masu tare bayan an gama ta nufi cikin parlon da ita suka zauna a saman 2 seater,

"Amman Aunty Sadeeya ya akai kika san da walimar nan har kika zo?" Fatuu ta tambaya da alamun mamaki akan fuskar ta, tana murmushi tace "tare da Dad muka zo shi ya kira ni ya sanar dani yace zamu zo dashi, ni da yake ina nan ina Aure ban fi shekara guda da watanni ba, gyad'a kai Fatuu tay tace Allah sarki,

"kin yi kyau sosae wllh kaman bake ba duk da dama kina da kyau an ma kin canza sosae kin k'ara girma kuma, na taya ki murna sosae Allah yasa Alkhairi ya baku zaman lafiya da zuriya d'ayyiba" Fatuu nata Murmushi ta amsa mata da Amin, shiru suka d'an yi dukkan su murmushi ne akan fuskar su can Fatuu ta tambaye ta Mom d'in su tace tana nan tama san zasu zo don sunyi waya take sanar mata tace ma ta kirata tayi mata Allah yasa Alkhairi, kai Fatun ta jinjina suka d'an k'ara yin shiru can Sadeeyar tace "baki tambayi Ya Khalid ba" har saida gaban Fatuu ya fad'i jin sunan Khalid, d'an murmushi tay a sanyaye tace ma Sadiyar yana ina,

"Yana nan yanzu a koma Yola acan yake aiki tare ma akayi bikin mu don bayan an fasa naku yayi nadama sosae, don har gwuiwa k'asa ya rok'i Dad kan ya bashi dama ta k'arshe kada a fasa Auren anan yake sanar mashi ai an ma d'aura maki Aure don haka ya hak'ura dake ba matar shi bace, aikuwa anan ya sume mashi abun ya kai shi ga kwanciya har gadon Asibiti, sosae yayi nadama wllh don akwae lokacin da muka zauna dashi yana k'walla yake fad'i man Allah ya jarabe shi da son ki sosae dama tunda ya gan ki matsayin wadda zai Aura yaji kin mashi gajan hak'uri yaja mashi amman yasan Allah ne ya kama shi, lokacin da aka zo neman Aure na shine Dad yayi mashi Maganar ya fito da wadda yake so tunda yasan bai rasa yan mata sai a had'a shine yace ma Dad d'in ya bar mashi komai ya nemo mashi kowacece zai Aura, farko Dad cewa yay ya fidda hannun shi akan shi saida Mom tay ta rok'on shi tana nuna mashi da gaske ya canza ba zai bashi kunya ba anan har take mashi Maganar wata k'anwar ki wai da akayi magana da suka je Dad d'in yace ai kuma shi ba K'aramin mutum bane ya riga yace a kyaleta tayi karatun ta yanzu bazai Koma ba yace a bashi ko ba don haka ba ma don abunda Ya Khalid d'in yay maki bazai nema mashi k'anwar ki ba, k'arshe dai wata d'iyar Abokin shi ya samo mashi Hafsat itama Secondary ta gama ba laifi tana da kyau itama bafullatana ce a cikin Yola suke shine akayi bikin mu tare, Yanzu suna acan Yola d'in yasa taci gaba da karatu tana nan ma da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe, gaba d'aya Ya Khalid ya canza ta sanadiyyar abunda ya faru, sosae yay sanyi duk wani hali mara kyau da kika sani ya bari wllh don ni bai 6oye man komai tun lokacin da yana cikin ciwon son ki ya maida ni kamar k'awar shi yay ta fad'i man damuwar shi in ta lallashin shi ina k'arfafa mashi gwuiwa yanzu haka shima yasan da zamu zo nan" idanun ta cike da k'walla ta k'arasa Maganar itama Fatuu sosae jikinta yayi sanyi zuciyar ta sai tunano mata abubuwan da suka faru tsakanin su take, Allah mai juya Al'amari a yadda yaso a kuma lokacin daya so da rabon ta silar hakan zata auri Haisam yanzu data k'i yarda kota yanke ta gudu da tayi ma kan ta, k'arshe rayuwarta ta wulakance ta kuma jefa iyayen ta a matsala, shiyasa ake son bawa ya rink'a yarda da k'addara mai kyau da mara kyau, duk abunda Allah yayi ma bawan shi mai kyau ne don yafi mu son kan mu, sau da yawa abubuwa marasa dad'i da suke faruwa damu wasu kan haifar da abubuwa masu dad'i agare mu matuk'ar zamu dogara da Allah muyi rik'o da yin Hak'uri, suna zaunen Laila ta zo tace mata Dad d'in su na nemanta tace to ta nuna mata Sadeeya tace bak'uwarta ce yar uwarsu ce a Adamawa tana aure anan, a mutunce suka gaisa harda tambayar ta Unguwar da take anan Abuja ta d'auki Baby d'inta, daga baya ta kira Jidderh ta had'a su tace a kaita d'akinta a bata Abinci kafin su dawo, part d'in Dad d'in suka wuce gaba d'aya parlon shi cike yake da Manyan Mutane masu tumbin Naira kama daga shahararrun masu kud'i zuwa masu Mulki, Laila ta shiga bin su da ita suna gaishe su suma dae har da kyautar kud'in suka mata daga baya Dad yace akawo ta wurin Alhaji Lawal dake a kusa dashi, a k'asa ta tsugunna ya kai hannu ya dafa Shoulder dinta da fara'a yace "Ma sha Allah Daughter, nayi matuk'ar farincikin yadda abu ya kasance, wannan aikin Albarkar da muke sa maki ne, matuk'ar zaka yi biyayya ga iyayen ka to kuwa rayuwar ka zata yi Albarka, Allah yasa Alkhairi ya baku zaman lafiya da zuria dayyiba yasa gidan zaman ki ne na har abada" Mutanen dake a kusa dashi sai amsawa da Amin suke harda wani abokin shi d'an Majalisa da suka zo tare, kasa jurewa Fatuu tay ta shiga yin hawaye komai daya faru a baya yana dawo mata, Envelope ya fiddo daga cikin Aljihun shi ya mik'a mata kawae sai ta fashe da kuka ya hau rarrashinta yana fad'in ai ba abun kuka bane, Senator dake ta murmushi yace "Kukan dad'i ne kasan shima yana sa ayi kuka" ya kalli Fatuu yace "Hakane ko Daughter?" A hankali ta d'aga mashi kai duk aka yi dariya daga baya Dad d'in yace ma Laila taje da ita.

Bayan sallar la'asar Nameer ya d'auki Mino suka fita Tk ma ya d'auki su Kawu Amadu da Kamalu suka shiga gari, Lokacin Laila tasa Fatuu ta canza shiga zuwa rantsatstsiyar shadda gray data sha ubansun aiki harda alkyabba aka d'aura mata lokacin Malamar da aka d'aukko zata yi Wa'azi wadda sananna ce ta zo, tuni an gyara main parlor d'in tsaf anan aka zazzauna Malamar itama a kan kujera ta zauna ta fara Wa'azin hannunta ruk'e da lasifika da ta karad'e ko ina, Wa'azi mai tsuma zuciya kan rayuwar Aure tayi, sai gab da sallar Magrib aka gama nan aka shiga rabon souvenirs abubuwa kala kala masu d'auke da sunan Haisam Ali Adamu Zakee da Fatima Muhammad Ardo, ba masu hotunansu cikin abubuwan da aka raba don Haisam d'in ya nuna bai so. Alhamdulillah Walima ta tashi lafiya abun dai sai san barka wllh, mun ci mun sha munyi hani'an yan Comment section an sha da ku da baku yi anko ba kun zo, kar ku manta gobe in Allah ya kai mu akwae Dinner itama kuma in ba anko ba shiga zaku yi ba ato😹.

Da daddare bayan isha gaba d'aya Su Fauzy bajewa sukai a parlor harda su Aunty Mareeya gaba d'ayan su dai yan part d'in ana hirar Walima cike da nishad'i, Wayar Fatuu dake hannun Fauzy had'e da tata ce ta fara ringing ta kai idonta kan screen d'in, ganin Haisam ne yasa ta mik'e don taje ta kai mata, har lokacin ankonta ne a jikinta rigar ta kamata kanta tayi d'aurin kallabi mai steps da akayi mata gashinta dake fake ya fito ta tsakiya ya bud'e sosae, sauri sauri gudu gudu ta nufi cikin gidan ganin kiran ya yanke ya kuma sake kira, hanyar d'akin Mom d'in su Haisam ta nufa don tun bayan da aka gama Wa'azi Fatun na can Mom tasa ta zauna Saboda masu son ganinta ba sai an ta nemota ba, tana zuwa daidai bakin corridor tana niyyar shiga da d'an gudu gudu kwatsam taci karo da Mutum wanda har saida tai taga taga tayo baya, ba arziki ta kai hannu ta dafe goshinta idanunta a rufe ta shiga fad'in "wayyo..wai...wai.wai...." A yadda taji sai kace ta bugi dutse, a hankali ta d'ago still hannun na a goshin slowly ta fara bud'e idanunta, koda tay arba da wanda tay karon ai ba shiri ta idasa bud'e idanun ta waro su, tsaye yake k'ik'am sai kace an dasa shi don koda sukai karon bai ko yi gezau ba, Sameer ne yana sanye da farin jeans da farar riga ta ciki sai aka d'aura Yellow a sama ma6allan ta a bud'e hakan ya bayyana ta cikin agogon hannunshi fara ce itama daga wurin glass d'in kan yana reflecting yellow sai k'afafun shi ma sanye suke da fararen takalma, daga wurin Mom d'in shi yake Hajiya Zainab data kira shi bayan ya fito ya d'aga waya yana magana sukai karon, gaba d'aya wayar shin da glass d'in shi daya ruk'o a hannu sun fad'i k'asa, bin shi da kallo Fauzy tay gabanta na wani irin Fad'uwa ganin mugun kallon da yake mata ya tamke fuska sosae, Murya na rawa tace "D...don Allah kayi hakuri bansan ka taho bane ina sauri ne zan kai waya ana kira" ta k'arasa tare da d'aga mashi wayar don ya gani, in bango ya tanka to shima ya tanka haka yanayin fuskar tashi ma bai canza ba, yan kame kame Fauzy ta shiga yi tana haka idanunta suka sauka akan Wayar shi da glass d'in dake yashe a k'asa, da sauri ta duk'a ta d'aukko su Allah yaso glass d'in bai yi komai ba, tana juya wayar zata mik'a mashi taga glass d'in yayi lafiyayyun tsaga har kusan hud'u, zaro ido tay ta bud'e baki gabanta ya shiga wani irin bugu, ganin reaction d'in fuskar ta yasa slowly ya kai idanun shi kan wayar idanunshi suka sauka akan glass d'in dake a tsattsage, wani irin kallo ya d'ago yana mata da sauri ta fara ja da baya tana yamutsa fuska daga d'an can gaban shi ta tsaya, kawai sai gani tay ya fara nufota, tana shirin k'ara ja baya cikin husky voice d'in shi ya furta "Stay where you are!!!" har saida cikinta ya yamutsa, a gabanta ya tsaya ya mik'a mata hannu da sauri ta mik'a mashi wayar ya k'i amsa ta bishi da ido cike da tashin hankali, a kausashe ya furta ta bashi glass hannunta har kerma yake ta mik'a mashi ya amsa, saka shi a idanun shi yayi bayan ya gama ya tsaida kallonshi akanta duk da bata ganin idanun, k'ara Mik'o mashi wayar tay murya na rawa tace don Allah yayi hak'uri wllh bada niyya bane, banza yay mata sai da ya mula sannan ya furta "ki biya shi!" Wani irin miyau Fauzy ta had'iya ko ba'a fad'i mata ba daga ganin wayar tasan mai tsada ce balle kuma daya kasance ga wanda ke rike da ita, da yake dare ne kowa ya gaji wasu kuma basu a gidan ba wasu mutane da ke shigowa wurin sai wanda ba'a rasa ba sun fito su kuma ba lalle su fahimci abunda ke wakana ba don daga yanayin su sai kaga kaman magana suke, Magiya taci gaba da yi mashi kan yayi hak'uri tana cewa tasan bazata iya biyan shi ba, ringing wayar ta fara yi ta kalli wayar kafin ta kalle shi tana kikkafta idanu, hannu ya mik'a ya amsa ya furta mata "ki biyo ni" daga haka ya juya, tsaye tay duk da taji abunda yace aikuwa ya juyo cikin daka tsawa tace "I told you to Follow me!!!" bin shi tay ya nufi hanyar fita daga cikin parlon, daidai gaban wata Mota da aka parker a gaban Entry Hall ya dakata itama ta tsaya daga d'an nesa dashi, dama wayar da ya taho yana yi umarni yake badawa na azo a d'auke shi suka yi karon, hannu ya kai ya bud'e kopar gaba, da kai yayi ma driver d'in alamun ya fito, bayan ya fito tsayawa yay daga gefe ya d'an russuna kai, ce mashi yay yaje zai driving da kan shi yayi mashi godiya ya juya, juyawa yay ya kalli Fauzy da tay tsuru tsuru a kausashe yace "come and get in to the car!" Nan take k'wallan da suka tarun mata a ido suka fara zubowa taci gaba da yi mashi magiya tana yayi hak'uri don Allah, kai ya jinjina ya d'an cize baki can cikin d'an d'aga murya yace "I don't allow anyone to argue with me! Ki shiga Mota else, yanzu zan sa aje a kulle ki!" yarfa hannu Fauzy ta shiga yi a hankali ta fara fad'in ta bani, matsawa ta fara yi a hankali tana tunkarar Motar, ganin yadda take tafiya ya k'ara ce mata kada tay wasting time nashi, tana niyyar bud'e k'opar baya ya galla mata wata muguwar harara ba shiri ta fasa bud'ewa da kan shi yay mata alamar taje ta shiga gaba ta zagaya tana kuka k'asa k'asa, saida ta shiga sannan ya kai hannu cikin aljihun jeans d'in shi ya fiddo wani farin hanky ya shimfid'a a saman seat d'in sannan ya shiga, bayan ya zauna da k'arfi ya rufo k'opar, dama Motar a kunne take aikuwa a tsiyace ya ja ta bayan yasha round d'in ya Mik'i hanyar Gate ya fuce............

*ASM 081*

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.........Suna fita daga cikin gidan suka hau hanya, hankalin Fauzy in yayi dubu to ya tashi tunanin ta ina zai kai ta kuma mi za'a mata, basu dad'e da hawa titi ba wayar Fatuu dake hannun Fauzy ta fara ringing, a hankali ta juya ta kalli Sameer da idon shi na akan titi yana driving, a d'arare takai hannu zata d'auka a kausashe taji yace "Don't pick it!" fasa d'agawar tay ta juya ta kalle shi fuskarta a yamutse har lokacin k'walla na zubo mata, wani kiran ne ya sake shigowa bayan wanccan ya yanke taji yace ta kashe wayan gaba daya, cikin muryar kuka tace "Don Allah ka bari in d'auka in fad'i mashi bana gidan, Ya Haisam ke kiran matar shi wayarta ce dama ita na taho in kai mawa Saboda yanata kira shine har na buge ka ban gani ba" banza yay mata yana ta driving d'in, saida kiran ya kusa yankewa ya bata umarnin ta d'aga, hannunta har d'an rawa yake tay picking kiran, tun kafin yace wani abu ta riga shi ce mashi k'awarta ce wayar na a hannunta kuma bata gida ya Furta Ok kawae daga haka ya katse kiran, tafiya suke ta faman yi a saman shimfidaddun titinun Abuja, tun Fauzy na yin k'walla tana kai hannu tana gogewa har ta saduda taci gaba da kallon hanya ta widescreen don glass d'in Motar blacktinted ne ba'a ganin waje sosae ta cikin su, saida suka d'auki kusan mintuna 30 sannan suka iso wata unguwa mai d'auke da had'add'un manyan gine gine ga fitilu ta ko'ina kaman da rana, yar tafiya sukai a kan titin Unguwar suka iso bakin wani katafaren gida da jami'an yan sanda guda biyu ke gadi kowannensu na rataye da bindinga a jikin shi, karya kan Motar yayi ya tunkari dank'areren gate d'in gidan da sauri su duka jami'an suka hau zuge gate din, bayan sun gama ya nufi shiga cikin gidan duk suka d'aga ma Motar hannu, ko horn baiyi masu ba balle ya tsaya ya shige ciki da Motar da gudu, babban parking space d'in gidan ya nufa bayan ya parker ya kashe Motar, sai lokacin ya juya ya kalli Fauzy tun bayan da suka fito ya furta mata "come out!" bud'e baki tay da niyyar yin Magana ya bud'e kopar ya fita, hannunta sai rawa yake ta bud'e kopar ta zuru k'afafunta dake sanye da takalma masu d'an tudu kafin ta k'arasa fitowa, hankali tashe take bin gidan da kallo wanda ba k'arya ya matuk'ar Had'uwa, ba wani mugun girma gidan gare shi ba kuma ba k'arami bane, bene ne hawa d'aya iya fentin gidan abun kallo ne don ya tsaru sosae, a harabar gidan akwae had'add'un Flowers su kan su an tsara shukar su gasu a gyare luf luf dasu, daga can gefe runfunan shak'atawa ne guda ukku kowacce na d'auke da k'ayatattun kujerun katako a zagaye da table, zagaye da runfunan akwae manyan shukokin Flowers harda irin Xmas tree da ake ma adon fitilu itama anyi mata hakan tana ta sakin haske kala daban daban haka sauran flowers d'in akwae masu reflecting hasken dogayen fitilun dake a wurare daban daban a cikin harabar gidan sun haske ko ina ta yadda ko allurar ka ta fad'i to zaka iya ganinta, a cikin hall d'in sama wata jigunannar katuwar fitilar sama ce mai adon sarkoki kai kace in mutum ya tsaya zata fad'o mashi,

Bayan ya rufe k'opar hanyar fita daga cikin parking space d'in ya nufa, har ya kusa fita ya dakata ya juya yana kallon Fauzy da tayi tsaye a bakin kopar Motar da ko rufeta bata yi ba sai zare ido take a iya fuskarta zaka fahimci ba K'aramin tashi hankalin ta yay ba, cikin d'an d'aga murya yace zata tsaya anan ne, yamutsa fuska tay ta fara kuka tana mashi magiyar don Allah yayi hak'uri, tsaye yay yana mata wani kallon rashin Arzik'i ta cikin glass d'in daya maida bayan daya fito daga cikin Motar, ganin zata 6ata mashi lokaci yasa shi ce mata ta tsaya anan za'a shigo da ita, jin haka yasa ba shiri ta biyo bayan shi don gaba d'aya a tsorace take, har ta fito cikin harabar ya dakata ya juyo hakan yasa itama ta tsaya, ce mata yay waye zai rufe mata kopar da sauri ta juya ta nufi komawa cikin parking space d'in tana yi tana waiwayen shi yana tsaye yana kallon ta, bayan ta rufo k'opar ta dawo ya juya yaci gaba da tafiyarshi mai cike da k'asaita, ganin ya kusa shiga cikin ginin gidan yasa ta k'ara saurin da take, a bakin dakakkar kopar shiga gidan dake a cikin entry hall ya tsaya saida Fauzy ta k'araso wurin ta tsaya daga d'an nesa dashi sannan ya kai hannu cikin d'ayan Aljihun jeans d'in shi wata farar wallet ya fiddo ya bud'eta, wani d'an card ya ciro ya kai shi jikin kopar cikin wani d'an rami dake kusa da handle d'inta, yana zura shi sai gashi tayi wata yar k'ara, zaro katin yayi ya maida shi a cikin wallet d'in sannan ya kai hannu jikin handle d'in ya tura k'opar ta bud'e, shiga yay ciki ya juyo yana kallon Fauzy, ganin irin kallon da yake mata yasa cikin fad'uwar gaba ta tunkari k'opar tana tafiya a d'arare aikuwa ya daka mata tsawa yace kar ta 6ata mashi lokaci baiwar Allah har saida ta firgita da sauri ta nufi ciki, matsawa yay gefe ta wuce ya kai hannu ya rufe k'opar aikuwa a firgice ta kalli kopar kafin ta maido kallon kanshi ta fashe da kuka mai sauti ta hau rok'on shi don Allah yayi hak'uri ya k'yaleta ta tafi, kai kace bada shi take ba ya shige cikin Corridor d'in da suka shigo, yana niyyar karya kwana ya dakata ya juyo yana kallon Fauzy dake ta kuka tayi tsaye a wurin hannunta d'aya ruk'e da kopar sai jan ta take amman sai kace tana jawo bango, jinjina kai yay yace mata in ta bari ya shige zata ga abunda zai same ta a wurin aikuwa tun kafin ya rufe baki da sauri ta nufo shi, bene ne a wurin shi kan shi abun kallo ne don ya tsaru tunda ga kan Matattakalar zuwa yadda akai design d'in shi ya wani markwad'a, da sauri da sauri take hawa saman shi har tana yin kamar zata fad'i tana yi tana waiwayen bayanta,

bayan ya haye a cikin wani Corridor ya tsaya cikin shi akwae flower vases masu kyau d'auke da kayatattun Flowers haka saman wurin akwae fitila mai kyau da tsari, kopopi ukku ne a wurin a gaban d'aya daga ciki ta bangaren hagu ya tsaya, hannu ya kai jikin kopar ya ta6a wani d'an circle na glass nan take k'opar tay wani d'an sauti alamar ta bud'e, tura ta yay ya shiga ya tsaya daga bakin kopar yana kallon Fauzy da tay fiki fiki duk ta firgice gata daga ita sai rigar jikinta ko gyale babu, "Come in" ya fad'a tare da yi mata nuni da kai, yamutsa fuska ta fara yi k'walla suka cigaba da zubowa ba tare data matsa daga inda take ba, hak'uri ta fara bashi kawae sai ya saki kopar yace mata ta bari ta rufe, a rud'e ta kutsa kai ciki bayan ta shiga kopar ta maida kanta ta rufe, Ya Allah kai mana Arziki mai Amfani shine abunda na furta, had'add'an parlor ne daya amsa sunan parlon masu Arziki sosae, komai na cikin shi fari da golden ne tun daga kan kujerun, labulaye, carpet, hatta fitilun cikin shi fari da golden ne kai kace da gold akai adon wasu abubuwan, sam parlon baida hayaniya komae tsaf tsaf sai ni'imtaccen sanyi mai had'e da daddad'an k'amshi ke tashi, a yanayin parlon kai kace mutane basu rayuwa a cikin shi yadda fararen abubuwan suke K'al da su, tsaye tay a bakin kopar duk da halin da take ciki sai da ta bi parlon da kallo fuskarta duk hawaye, cikin parlon ya shiga a saman farin c-table shima da adon golden ya d'aura wallet da wayar shi, hannu ya kai ya cire glass d'in Fuskar shi shima ya aje a wurin, saida ya d'an juyo ya kalleta suka had'a ido kafin ya juya walking majestically ya nufi hanyar wani Corridor ta bi bayan shi da kallo har ya shige, lokacin ta samu damar k'ara bin ko'ina na cikin Parlon da kallo baki a d'an bud'e, bai d'auki lokaci sosae ba ya fito ya cire yellow rigar ta sama sai farar ta ciki da ta kama jikin shi kirar k'arfin shi ta bayyana ya cire takalman k'afafun shi ya sanyo wasu bak'ak'en slippers masu d'an tudu, da sauri Fauzy ta maida idanunta cikin Corridor d'in jin sautin tafiya, yana fitowa suka had'a ido ya wani k'ara tamke fuskar da sauri ta maida idon gefe gabanta na bugawa da k'arfi da k'arfi, cikin parlon ya shigo ya nufi inda fridge yake a can gefe, bud'ewa yay bayan yaje gaban shi Fauzy ta kai idon ta wurin, hannu ya kai ciki ya fiddo wata k'atuwar bak'ar kwalba an nad'e saman marfinta da wata leda mai k'yalli haka ma a jikinta akwae takarda mai d'auke da rubutu zagaye da ita, d'aurata yay a saman fridge d'in ya k'ara kai hannu ciki ya d'aukko tumbler, bayan ya rufe fridge d'in ya kai d'ayan hannun shi ya d'aukko kwalbar tana ganin zai juyo da sauri ta kauda idonta daga barin kallon shi, cikin parlon ya dawo ya nufi kujera ya d'aura abunda ya d'aukko kafin ya kai hannu ya jawo c-table d'in gab da kujerar, d'aukar kwalbar da cup d'in yay ya d'aura su a saman table d'in kafin ya zauna ya kai hannu ya d'aukko kwalbar ya kaita baki yana cizge ledar da aka nad'e bakin ta, sakin baki Fauzy tay tana kallon shi cike da Al'ajabi don ita a saninta irin wannan kwalbar ta giya ce, lokacin daya gama bud'ewa ya fara tsiyayawa a cikin cup d'in wani irin harbawa zuciyar Fauzy ta shiga yin don kuwa ganin kalar abunda ya zuba a cikin cup d'in ta tabbatar ma kanta da giya ce, kaman rabi ya zuba bayan ya rufe kwalbar ya d'auka ya kai baki ya fara sipping a hankali, yana cikin sha yayi mata kallon k'asan ido da sauri ta sunnar da kanta k'asa gaban ta na cigaba da fad'uwa, yana cikin sha ya kai hannu kan table d'in ya d'aukko remote da ke a saman shi daga d'an can gefe ya kunna Tv, bayan ta kama ya shiga caccanza channel ya kamo wadda yake so sannan yaci gaba da shan lemun d'ayan hannunshi ruk'e da remote d'in ya d'aura kafa d'aya akan d'aya idon shi akan Tv yana kallo, fara gajiya da tsayuwar Fauzy tay daurewa kawai take don k'afafunta har sun fara mata zafi sai wuwwurga ido take sai ta kalle shi sai kuma ta kalli Tv shi kam gaba d'aya ya maida hankalin shi akan Tv ko kallonta bai yi sai kace ma ya manta da ita a wurin, sun d'auki lokaci a haka gaba d'aya Fauzy ta gaji da tsayuwar har k'afafunta sun fara mata zunga sai kallon shi take tana yamutsa fuska tare da kikkafta idanunta da suka cika da kwalla, matsawa ta d'an k'ara yi gaba kad'an cikin rawar murya tace "Don girman Allah kayi hak'uri ka k'yale ni in tafi, nasan ana can anata nema na wllh" da alama dae bango take ma magana don kuwa sipping d'in lemun shi da ya k'ara zubawa kawai yake, kuka Fauzy tasa sosae mai sauti sai lokacin ya juyo yana mata wani kallo, cigaba da magiya tay mashi tana nuni da hannuwan ta, janye idon shi yay daga kan ta ya ci gaba da kallon shi, bayan ya gama shanye abun cikin cup d'in d'aura cup d'in yayi saman table, tsam ya mik'e ya nufo cikin parlon ganin inda take yake nufowa yasa ta zaro ido ta fara ja da baya gabanta na wani irin bugu tamkar ana mata luguden ta6are, cigaba da tunkararta yay tana ja da baya can ta juya a rud'e ta kama k'opa ta fara jijjiga handle d'in a K'ok'arin ta nata bud'e tana yi tana waiwayen shi duk ta gigice ba kamar da take ganin giya ce ya gama sha, tana haka ya cimmata kokarin bi ta gefe ta ruga tay ya kai duka hannuwan shi ya dafe kopar ta yadda ya sakata a tsakiyar su yay mata rumfa, gaba d'aya jikinta 6ari yake har bakinta sai numfashi take da k'arfi tunda take a rayuwarta bata taba shiga firgici irin wannan ba, ko lokacin da aka sanar Mata Mujaheed yayi Aure batai irin wannan firgicewar ba Saboda sumewa tay lokacin yanzu kuwa bata fatan ma ta sume d'in, gaba d'aya ganin shi take a buge yake hakan yake k'ara tada mata hankali, kafeta da ido yay yana mata wani matsiyacin kallo sai kerma bakinta ke yi tama kasa cewa komai, wayarta ce da har lokacin tana ruk'e a hannunta tare da ta Fatuu ta fara ringing da sauri ta kai idonta kan screen d'in ganin Aunty Mareeya ce me kiran yasa a kid'ime ta fara k'ok'arin d'auka don ta sanar mata halin da take ciki kwatsam taji ya kawo hannu ya buge wayar ta fad'i k'asa ta daki tiles, daga jin sautin fad'uwar ba sai an fada ba glass d'in ya fashe, cikin rawar murya ta fara fad'in "D...don girman Allah, don son ka da Manzo SAW kayi hak'uri, wllh bada sani na na buge ka ba har wayan ta fad'i kaji na rantse..." abun ka da fara fuskarta har tayi jajur tunda take a rayuwarta bata ta6a kasancewa da Namiji haka ba don kusancin yayi yawa, bin ta kawae yay da ido da suke a d'an lumshe wanda suna daga cikin abun da ke tafiya da mata a tattare da shi, komai nasu da Haisam iri d'aya sai kace suma yan biyun ne don shima ya iya lumshe ido, kaman daga sama taji yace,

"What is ur name" idanu waje cikin rawar murya tace "n..ni suna...na...Fauziyya" shiru yayi kafin ya k'ara cewa "What's your relationship with the bride?" har saida ta had'iyi abu kafin tace "Ni..Best Friend din ta ce tare muke karatu" da k'yar take bashi amsa don har lokacin a firgice take, tambayar ta ya k'ara yi a wani Makaranta suke karatu ta bashi amsa da School of nursing Katsina, "A nan kike?" da alamun rashin fahimta tace ina, kaman bazai bata amsa ba sai kuma taji ya furta sunan Katsina nan ta gane yana nufin a Katsina d'in take, ce mashi tayi ita yar Funtua ce, hannu ya kai ya shafi beard din shi bayan ya janye hannun yace mata ina ne Funtua, duk da halin da take ciki saida taji Maganar kaman ta rainin wayau don sai taga ya za'ai yace bai san garin ba, amsa ta bashi da babbar local Government d'in Katsina ce, dan ta6e baki yay ya juyar da Fuskar shi gefe,

maido fuskar yay ya kalleta yace "Kinsan abunda kika fasa man yana da kud'i sosae?" da sauri ta jinjina mashi kai alamar eh, yace "Ok ina son ki biya shi" yamutsa fuska ta fara yi zata cigaba da kuka yay mata wani kallo ba shiri ta saki fuskar tace "Wallahi, tallahi kaji na rantse maka bazan iya biyan ka ba" still yay yana kallonta kaman bazai ce komai ba can yace "Ok sai ki sanar ma Dad d'in ki ya biya" girgiza kai ta hau yi "Wllh shima nasan bazai iya biyan ka ba....." Katseta yay ya d'age gira yace tasan kud'in shi ne, da sauri tace "a'a ban sani ba amman dai nasan zata yi kud'i sosae kuma mu wllh talakawa ne kawai dai muna da rufin asiri amman nasan baza'a iya biyan ka ba" tana rufe baki yace ai yasan basu rasa wani abu da za'a saida a biya shi, idanunta ne suka k'ara cikowa da k'walla suka zubo mata sharr ta kai hannu tana gogewa tace "saidae gidanmu kuma a ciki muke sai kuma gonar Baban mu ita kuma anan ake noma Abincin da muke ci wani kuma a saida ayi wasu hidindimun tunda baban namu ya aje aiki pension ake biyan shi kuma basu isa" shiru yay bayan ta gama kora mashi bayanin can yay sigh yace "Ok naji, but you must compensate me for the damage" yana rufe baki ta fashe mashi da kuka ya kai dogon yatsan shi jikin bakin shi yay mata alamar tay shiru, gunji ta koma yi tana yi tana kai hannu tana goge kwallan dake zubo mata ya kafeta da ido,

hak'uri taci gaba da bashi can yace "Ok I will do u one favor" da sauri ta jinjina mashi kai tun bata ji Alfarmar ba har ta d'an ji sassauci a zuciyarta, kafe shi tay da ido tana jiran jin Alfarmar slowly ya sauke idanun shi yana bin jikinta da kallo daga baya ya d'ago da su ya tsaida su cikin nata k'asa k'asa ya furta "You can pay me with your... Body" wani irin zaro ido Fauzy tay kirjinta yay wani irin mummunan Fad'uwa a razane ta hau girgiza mashi kai tama kasa cewa komai, slowly ya fara matsawa da fuskar shi yana niyyar had'e ta da tata aikuwa a gigice ta hau girgiza kanta sosae ta runtse idanunta cikin k'araji ta hau fad'in "Na rok'e ka don girman Allah kada ka cutar dani, nasan kafi k'arfinta don Allah don darajar iyayenka ka yafe man kada kai man komai wllh ni ba yar iska bace ban ta6a yin haka ba" ji tay yace kenan tana nufin shi d'an iska ne, tana jin hucin Maganar tashi akan fuskar ta Saboda kad'an ya rage ya had'e ta da tata, da k'yar ta bud'e idonta cikin muryar kuka tace "a.. a'a wllh ni ba haka nike nufi ba kawae dae ina son fad'i maka ne ni ban ta6a aikata hakan ba don Allah kar kayi man komae" bin juna sukai da ido tana ta kikkifta nata dake jik'e da k'walla, shigar da lip d'inshi na k'asa yay cikin baki ya dan tsotse shi kafin ya fiddo dashi gently yace mata ai yanzu ba wanda zai sani kuma in tana tsoro ne zai mata yadda bazata ji komai ba sai dae tay enjoying, shiru tay tana ta kallon shi ganin haka yasa shi d'age mata gira yace "agreed?" motsa baki ta fara ta rasa mi zata ce mashi wata zuciyar ta shiga raya mata ta yadda kawai in dai sau d'aya ne, cikin rawar murya ta tambaye shi daga wannan Shikenan, kawae sai gani tay yay wani kalan murmushi mai wuyar fassaruwa ya jinjina mata kai, shiru tay gabanta na cigaba da bugawa da k'arfi, ganin yana matso da fuskar tashi yasa tay saurin runtse ido tana numfashi da k'arfi har yana jin hucin shi akan fuskar shi idanunta sai motsawa suke duk da suna a rufe, had'e face d'in su yayi tana jin lips d'in shi ya had'e da nata kawai sai ta zame k'asa ta rufe fuskarta da hannuwan ta da suka sha k'unshi ta fashe da kuka tana girgiza mashi kai da d'an k'arfi take fad'in "ban iyawa wllh, Allah na ganin mu in muka aikata hakan zai kama mu ne kuma zan lalata rayuwata na rok'eka ka yafe man nasan kafi k'arfin ta don Allah ka k'yale ni" yana a yadda yake bai cire hannuwan nashi ba ya sunkuyar da kan shi yana kallon ta abun mamaki Fuskar shi na d'auke da d'an murmushi, cire hannuwan shi yay daga jikin k'opar ya tsaya yana kallonta kallabin ta har ya fad'i kuma har lokacin hannuwanta na rufe da fuskar, yadda tayin ne yasa shi yin murmushi don hakan saiya zame mashi wani bak'on abu har ya d'an bashi nishad'i ganin shi da Mata ke son ya ta6a su yau an samu wadda ta samu hakan amman tak'i yarda saidai dama akwae abunda yake k'ok'arin ganewa shiyasa yayi mata hakan, juyawa yayi ya nufi inda wayarta ke yashe ya duk'a ya d'aukko ta, bai yi mamakin ganin yadda glass d'inta yay kwatsa kwatsa ba, latsa power button yay haske ya kawo, screen d'in wayar lafiyar shi lau ya k'ura ma hoton ta dake kan screen d'in tana sanye da fararen Uniform ba Hijab haka kanta ma ba kallabi sai gashinta dake a fake kunnuwanta sanye da Stethoscope ta rik'e kan a hannunta tana dariya, sosae tayi kyau a hoton don ma glass d'in wayar ya faffashe, juyawa yay ya koma inda take duk'e har lokacin fuskarta a rufe take tana ta sheshsheka, rasa yadda zai yi mata magana yay don har yama manta yadda ta fad'i mashi sunan ta, wayar yasa ya d'an bubbuga kanta aikuwa da sauri ta d'ago idanunta sunyi jajur har sun d'an kumbura, mika mata wayar yay yace ta bud'e hannunta yana ta rawa ta amsa ta bud'e ta mik'a mashi ko damuwa da yadda taga glass d'in yayi bata yi ba, amsa yay ya juya cikin parlon ta bi bayan shi da kallo, inda ya taso ya koma ya zauna yana latsa wayar, bayan wani lokaci ya d'aga kai ya kallo inda take Saidae bai hango ta Saboda duk'ewar da tayi, maida idon shi yay akan Wayar can ya sake d'agowa a kausashe ya furta "Where are you?" Da sauri ta mik'e tsaye suka had'a ido, kasa jure ma kallon shi tayi sai d'an maida idon ta k'asa take, da hannu yayi mata nuni da kujera har ta nufo cikin parlon ta tuna da kanta ba kallabi ta juya ta d'aukko ta yafa, a bakin kujerun ta tsaya tana kallonshi da kai yay mata alamar ta zauna, a saman ta kusa da ita ta zauna gaba d'aya a d'arare take, aje wayarta yay saman table ya maida idon shi akan Tv, wani irin fitsari take ji saidae bata san ya zata yi ba gashi sosae ya matse ta don tun d'azu ta fara jin shi tsabar firgici, yamutsa fuska ta shiga yi ta kafe shi da ido tana cikin kallon nashi ya maido idon kan ta yay mata wani kallo mai kaman harara da sauri ta maida idon nata k'asa, jin fitsarin na niyyar zubo mata yasa ta mik'e da sauri har bata san lokacin data tunkare shi ba ya maido kallon shi kan ta, daga d'an nesa da shi ta tsaya fuska a yamutse tace mashi don Allah toilet take son shiga, shiru yay yana kallonta saida ya ga dama sannan ya furta mata bai sharing toilet, jiki a mace ta juya har ta fara tafiya sai kuma ta dakata ta juyo tace to don Allah y bud'e mata kopar ta fita ta ga in zata samu wani, ta6e baki yay ya d'age gira yace mata gidan su ne nan da sauri ta girgiza mashi kai jiki a sa6ule ta juya ya bita da kallo, in da ta taso ta koma ta zauna, kasa natsuwa tayi a wuri guda sai yan matse matsen jiki take ba K'aramin k'ok'ari take ba tana ruk'e fitsarin, tana haka taga ya mik'e da hannu yay mata alamar ta biyo shi aikuwa zumbur ta mik'e, Corridor d'in daya shiga d'azun ya shiga ta bi bayan shi, a bakin wata farar kopa ya dakata ya juyo suka had'a ido, ce mata yayi ta shiga ciki zata ga toilet ta d'aga mashi kai, har ta kai hannu ta tura kopar zata shiga kamar wadda ta tuna wani abu da sauri ta juyo yana tsaye bai motsa ba, yamutsa fuska tayi idanunta rau rau cikin karyayyar murya tace "t...to don Allah kada kayi man wani abu in na shiga" wani kallon rashin Arzik'i yay mata ya kalleta daga sama har k'asa kawai sai yay d'an tsoki ya juya ya nufi komawa cikin parlon, k'irjinta na bugu da k'arfi ta kai hannu ta tura kopar ta shiga, tsaye tayi bayan ta shiga tana bin d'akin da kallo sai kace ba wadda Fitsari ya matsa ba, d'akin ya matuk'ar Had'uwa shima komai na cikin shi fari da golden ne, katafaren gadon yasha farin bedsheet K'al da shi, ba wasu tarkacen kaya a cikin shi gado ne da table d'in shi sai side drawers da dressing mirror sai tafkekiyar glass wardrobe itama fara ce sai glass d'in gaban yana da d'an launin golden ana hangen kayan cike wasu a hanger wasu a linke, daga can gefe guda farin table ne d'auke da wasu littattafai harda Alqu'ani daga gefen su fitila ce irin ta karatu golden, wata k'opa data gani ta nufa bayan ta gama k'are ma d'akin kallo, tana tura ta taga toilet ne a d'arare tana yi tana waiwayen bayan ta hakanan dai tayi shahada ta shiga, shima dai Toilet d'in komae na cikin shi fari ne kuma ko ban fada ba an san shima ya had'u, bata dad'e ba ta fito da sauri ta nufi hanyar fita, yana zaune a inda yake d'azun ta shigo cikin parlon sumi sumi ta nufi inda ta tashi bai ko kalle ta ba idon shi akan Tv, bata dad'e sosae da dawowa ba tana ta yan kalle kalle wayar shi ta fara ringing, yana ji amman ko kallon ta bai yi ba Fauzy ta bi shi da ido a ranta tana raya yana ji waya na ringing yak'i d'auka, bayan kiran ya yanke ba'a dad'e ba wani ya sake shigowa shima saida ya kusa yankewa sannan ya mik'a hannu ya d'aukko wayar, bai yi picking ba ganin mai kiran nashi sai ma ya mayar da wayar ya aje, can bayan wani d'an lokaci ya mik'e ya nufi hanyar corridor Fauzy ta bishi da ido har ya shige, gyara zamanta tayi ta hau kujerar sosae tay jugum gaba d'aya ta rasa mike mata dad'i don bata san ko ya hak'ura ba gashi yazo ya jibgeta anan, saida ya d'auki kusan 30 minutes koma fi sannan ya fito da gani wanka yayi don ya canza kaya zuwa jeans da red t-shirt sai bazw uban k'amshi yake don yana fitowa ya kai hancin Fauzy, da sauri ta d'ago daga jingina da tayi da kujerar ta gyara zamanta, ciki ya wuce ya tsaya wurin table ya kai hannu ya dauko farar wallet d'in ya fiddo wasu abubuwa ya maida cikin wata dark blue kalar jeans d'in shi daya fito da ita, aje farar yay saman table d'in ya d'auki wayar shi daga haka ya juya ya nufi hanyar k'opar fita daga parlon, yana zuwa saitin Fauzy yace ta taso aikuwa da sauri ta mik'e, tana shirin bin bayan shi ya dakata ya juyo ta bi shi da ido, ce mata yay wata bar ma wayarta da sauri ta juya ta nufi wurin table da wayar ke a saman shi, har ta d'aukko ta juyo yana tsaye saida ta kusa zuwa wurin shi sannan ya juya yaci gaba da tafiyar, kamar yadda ya bud'e kopar ya shigo haka ya yi ta bud'e suka fita, da suka zo babbar k'opar shigowa gidan itama wani wuri ya ta6a ta bud'e bayan ya fita Fauzy ta bi bayan shi.

Bayan da Haisam ya kira Fauzy ta d'aga ta sanar mashi wayar na a hannunta, wayar Jidderh ya kira bayan tayi picking yace ta ba Fatuu tace mashi tana d'akin Mom bari ta kai mata yace kawae in taje ta fad'i mata su had'u a main parlor tace to, lokacin data je part d'in Mom Fatun na a zaune a parlor da wasu mutane suna kallo, wurinta ta nufa ta zauna da murmushi tace mata "Sannu Amaryar mu nasan dai yau kin sha gajiya" murmushi itama Fatun take mata ba tace komai ba, gaya mata sak'on Haisam tay ta mik'e tace tazo su je, d'an jimm tayi kafin tace mata to ai Mom tasa tazo part d'in kuma sai ta tafi Jidderh d'in tace Ok bari tama Mom d'in magana, bedroom ta nufa tana shiga ta ganta zaune a saman gado ita da yar uwar ta suna hira, gadon ta nufa ta zauna a bakin shi Hajiya Zainab dake kallon ta da murmushi tace mata ya gajiyar Walima tana murmushi tace mata ba gajiya, maida idonta tayi akan Mom ta sanar mata zancen kiran da Ya Haisam ke ma Fatuu da abunda tace, salati ta saka tace ai ita wllh tayi zaton ma ta tafi ne tun bayan da Sameer ya shigo zasu yi Magana da Mom d'in shi ta fita, saukkowa tay daga saman gadon suka nufi Parlor, inda Fatuu take suka nufa Mom d'in ta zauna ta kai hannu ta dafa Shoulder d'inta ta shiga bata hak'uri kan wai ta aje ta Fatun nata murmushi tace ba komai ai, kallon Jidderh dake tsaye tayi tace suje in ta ga Haisam d'in ta tabbatar an bata Abinci ta ci tace mata to, mik'ewa Fatuu tay har lokacin shaddar ce a jikinta tayi ma Mom data Mik'e saida safe suka tafi, lokacin da suka isa parlon Haisam d'in na tsaye yana latsa waya jikin shi sanye da jallabiya, a gaban shi ta tsaya ya d'ago suka sakar ma juna murmushi, calmly yace mata tasan zasu fita shine bata neme shi ba, d'an yamutsa fuska tayi tace yayi hak'uri tana part d'in Mom ne kuma wayarta na a hannun Fauzy shiyasa bata kira shi ba, fad'i mata yay Fauzy d'in bata gida ne tace Ok, ce mata yay zasu iya tafiya tay d'an jimm kafin tace bari ta canza riga yace Ok bari ya d'aukko Mota in ta gama ta same shi waje ta d'aga mashi kai, d'akin Jidderh ta nufa lokacin data shiga mutum biyu ta iske cikin yan uwan su zaune a saman gado suna latsa wayoyin su, d'agowa sukai suna gaishe da ita tana murmushi ta amsa masu, wurin trolley d'inta ta nufa ta bud'e ta shiga tunanin kayan da zata canza har wanka taso tayi amman bazai yiwuwa ba saidae ko in taje can inda zasu, k'arshe doguwar rigar material ta d'auka ta nufi toilet don ta sa, bayan ta fito ta d'auki kayan bacci ta tura a jaka ta linke rigar data cire ta saka ta a cikin trolley d'in, d'an babban gyale ta fiddo sannan ta rufe akwatin, bayan ta nad'a gyalen ta d'auki jakar hannun ta nufi hanyar fita, lokacin data fito daga cikin gidan har ya kawo Motar bakin Entry Hall tana zuwa ta zagaya ta bud'e gaba ta shige bayan ta rufe k'opar ya ja suka tafi.........

*ASM 082*

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

........Bayan su Fauzy sun fito daga cikin layin gidan titi ya hau sosae suka cigaba da tafiya, Sameer na cikin driving cikin ran shi yake tunanin abunda yakamata yayi, dama bai san ma mi zai mata ba da ya d'aukko ta tun farko, akwae inda yake son zuwa ana jiran shi tunanin in yace ya maida ita gida hakan zai 6ata mashi lokaci yasa shi yanke zuwa da ita in ya gama abunda zai je yi sai ya maida ta, tafiyar kusan minti 20 sukai suka iso wani babban wuri wanda rabin katangar shi fence ne ta yadda zaka iya hango ciki haka daga gaban katangar had'add'un Flowers ne a tsare sannan a jikin katangar akwae fitilu da suka haska ko ina, karya kan Motar yay ta kalli gate d'in wurin wanda shima na k'arafa ne irin na jikin katangar, saida ya jira wata Mota ta k'arasa shigewa gate d'in sannan shima ya shige, k'aton parking space d'in wurin ya nufa bai k'arasa wurin shi ba ya parker Motar daga gefe don kuwa parking space d'in dankam yake da motoci masu numfashi don kowacce ka gani ta had'u, sakin baki Fauzy tayi tana kallon wurin ta cikin glass d'in gaba dama tunda suka taho ba abunda take sai aikin kalle kalle, hannu ya kai gefe ya d'auki wayar shi da wallet hakan yasa ta maido idon ta kan shi, kallon ta yay suka had'a ido ta hasken da ya d'an haska cikin Motar fuskar shi ba d'igon annuri ya mik'a mata hannu yace ta bashi wayoyin hannunta, da sauri ta mik'a mashi saida ya kashe su gaba d'aya sannan ya bude glove box ya saka su, ba tare da ya kalleta ba ya juya ya bud'e Motar bayan ya fita ya maido k'opar ya rufe, zuru tay tana kallon shi dishi dishi ta glass d'in kopar daya fita har saida ta daina hango shi sakamakon wasu da suka zo wurin shi suka tafi bata san ina sukai ba ta dai daina ganin su, maida kanta tay jikin headrest tay shiru ta shiga tunanin k'ilan ana can anata nemanta tunda ba wanda yasan ta fito sai Ya Haisam kuma shi tasan ba lalle in zai fad'i ma Fatuu ba cewa bata gidan ba kaman yadda ta sanar mashi, shiru shiru har kusan bayan mintuna talatin bai dawo ba gaba d'aya Fauzy ta gama gajiya ga wata bak'ar yunwa da take ji sakamakon bata ci Abincin dare ba ga zafi ya ishe ta don ma ta bud'e glass d'in gefenta, gaba d'aya ta rasa mike mata dad'i sai yamutsa fuska take tana yan kalle kalle ta cikin Motar can ta kai hannuta a d'arare ta bud'e k'opar Motar, zuro kanta tayi tana k'are ma wurin kallo ba K'aramin had'uwa yay ba iya fitilun dake sakin haske a wurin abun kallo ne, kai idonta tay cikin wata had'add'iyar rumfa mai girma wadda mutane da d'an yawa ke acikinta, bazata iya gane Mutanen Musulmai bane ko Christians daga yanayin shigar su, wasu cikin su na tsaye suna buga snooker mata da maza yayin da wasu ke a zaune saman k'ayatattun kujeru zagaye da table suna kallon su yayin da saman table d'in ke d'auke da abubuwan ciye ciye dana sha wanda bazata iya gane ko su miye ba, daga gefen su kuma wasu ne ke yin ludu wasu kuma na yin wasan chess, ta d'an d'auki lokaci tana kallon su don yanayin wurin akwai d'aukar hankali can ta idasa fitowa daga cikin motar a tsorace gaba d'aya tayi kalar rashin gaskiya, jingina da kopar Motar tay ta na kallon cikin wurin Mutane sai kai da kawowa suke suma dai duk kalar irin shigar na cikin rumfar gare su wasu na fitowa daga cikin ginin wurin wasu kuma na shiga daga can gefen wurin wani irin k'aton swimming pool ne an k'awata shi mutane sai wanka suke mata da maza, daga inda take ta fara k'ok'arin ganin sunan wurin dake a sama yana ta sakin walwali saidae ta kasa gane mi aka rubuta dama bata gani ba da zasu shigo, gajiya tay da tsayuwar ta koma cikin Motar taja kopar ta rufe, shiru tay tana ta yamutse yamutsen fuska don Allah kad'ai yasan irin yunwar da take ji, wasa wasa ta shafe fin awa amman bai fito ba lokacin tuni ta fara yin k'walla abun har ya kai ta fashe da kuka a fili ta shiga fad'in "Wllh wannan mutumin mugu ne, in ya yafe man ba sai ya maida ni gida ba amman ya jibge ni a cikin Mota sai kace ba Mutum ba" haka tay ta sambatu. Sai wuraren k'arfe d'aya saura yan mintuna ya dawo, yana shiga cikin Motar idanun shi suka sauka akan Fauzy data langa6ar da kai, hannu ya kai ya kunna fitilar Motar haske ya gauraye cikin Motar ya bi ta da kallo, shi gaba d'aya ya manta ma da ya barta a Motar, da ganin fuskarta ta sha kuka da alama ma tana cikin yi baccin ya d'auketa don fuskarta duk jirwayen hawaye kallabinta data yafa ya zame, bayan wani lokaci ya fara k'ok'arin tada ita da fad'in "Hey...." Shiru bata ko yi motsi ba ya k'ara cewa hakan nan ma bata Motsa ba, hannu ya kai ya fara d'an bubbuga shoulder d'in ta lokacin ta fara motsi, a hankali ta fara bud'e idanuwanta tana yi tana k'ara rufe su cikin husky voice d'in shi ya furta "Wake up" aikuwa da sauri ta bud'e idanun gaba d'aya ai koda tay arba da Fuskar shi ba shiri ta shiga gyara zaman ta, bin juna sukai da kallo duk tayi wuri wuri da ita can k'walla suka zubo mata sharr da sauri ta juyar da fuskar ta daga barin kallon shi tana d'an yi sheshsheka a hankali,

"da wa ya buge ki?" taji ya furta, shiru bata bashi amsa ba bata kuma kalle shi ba, ya k'ara furta "am I not asking you?" Sai lokacin ta juyo ta girgiza mashi kai alamar ba kowa, d'age gira yay ya furta "shi wannan d'in na miye?" ta gane kuka yake nufi ta fara motsa baki ta kasa yin magana, ce mata yay kar ta k'ara sa shi ya maimaita mata magana ya k'ara tamke fuska da sauri cikin rawar murya tace mashi yunwa take ji, bin ta yay da wani kallo ganin haka yasa cikin yar in ina tace mashi bata ci Abincin dare ba, ta6e baki ya d'an yi ya janye idanunshi daga barin kallon ta ya koma kallon gaban shi, bin gefen fuskar shi mai d'auke da kwantaccen saje sumar tayi luff tayi da kallo, juyawa yay dama bai datse kopar ba ya fita tana ta kallon shi ya maido kopar ya rufe, maida kanta tayi jikin kujera tay shiru ba abunda take gani sai fuskar shi, bayan wasu yan mintuna taji za'a bud'e Motar da sauri ta kai idonta, shine ya bud'e ya shigo hannun shi ruk'e da abu, bayan ya zauna ya mik'a mata d'an babban cake ne nad'e a leda sai lemu irin na cikin kaman d'an cup da straw manne a jikinshi, a hankali tayi mashi godiya bai ko kalle ta ba ya maida kan shi jikin headrest, ruk'e su tay a hannu bata da niyyar fara sha sai yan kame kame take tana haka taji yace zasu kwana ana ne, abu ta had'iya kafin ta fara k'ok'arin ciro straw d'in jiki, bayan ta saka a cikin lemun ta bud'e cake d'in ta fara ci tana yi tana satar kallon shi, bayan ta d'an ci da yawa ta rage sauran duka a hankali ta juya ta kalle shi ya d'age kan shi idanun shi a rufe, bin fuskar shi tay da kallo Idan tace ga wani abu da bai yi ba a fuskar tashi to kuwa ta shirga babbar k'arya, tana cikin kallon nashi ba tare data ankara ba ya bud'e idanun ya kallo ta, in ina ta kama yi tace mashi ta gama ya kallo sauran data rage a hannunta ba tare da ya d'ago ba kawai sai gani tay ya maida idanun ya rufe, bayan d'an lokaci taji yace "Don't waste my time, else zan barki anan ne" ai tana jin Haka da sauri ta kai lemun baki taci gaba da sha, saida ta cinye komai sannan ta kalle shi tace ta gama shiru kaman bai jita ba ta k'ara d'an d'aga murya ta maimaita ta gama, slowly ya fara bud'e idon ya d'ago daga jikin kujerar ya fara k'ok'arin tashin Motar yana haka yace mata wannan d'in wani zata kai mawa ta d'an girgiza kai kafin tace bata san ina ake aje wa ba ya juyo yay mata wani kallo da sauri ta juya ta bud'e kopar ta wurga ledar da d'an cup d'in, rufe kopar yay daga haka ya fara yin reverse bayan ya fita daga wurin ya shiga juya kan Motar Fauzyn nata kallon wurin har lokacin da mutane kusan ma yafi cika yanzu.

Lokacin da suka iso gidan kusan k'arfe d'aya da rabi, a bakin Entry Hall ya parker Motar Fauzy ta bi shi da ido gudun kada tayi wani laifin, shiru kaman ba zai tanka ba can yace "Get out of my car" juyawa tay zata fita sai kuma ta dakata ta juya a d'arare tace mashi don Allah ya bata wayar kawar tata ta kai mata, sai da ya mula sannan ya kai hannu ya bud'e wurin da ya saka ba tare daya kalleta ba yace ta d'aukko, hannunta har d'an rawa yake ta kai shi ta d'aukko ta Fatun kawae a fusace yace waye ta bar ma d'ayar ta sake kai hannu ta d'aukko, d'an kallon shi tay tayi mashi godiya yay banza da ita jiki a sanyaye ta juya zata bud'e k'opar kaman daga sama taji yace ta sani dole zata biya shi damage d'in da tay ma wayar shi, juyowa tay fuska a yamutse tace "Don Allah kayi hakuri...Na fad'i maka wllh Allah ba zan iya biyan ka ba, d'age shoulder yay alamar bai dame shi ba kafin yace ta fita, bud'e k'opar tay bayan ta fita ta juyo idonta a kanshi ta kai hannu ta rufe mashi, nufar shiga cikin gidan tay tana yi tana waiwayen shi har saida ta kusa shigewa sannan taga ya ja Motar,

Lokacin da ta shiga main parlor d'in tsit kowa yayi bacci, kopar baya ta nufa tana waige waige tsoron ta kar wani ya ganta ta dawo a lokacin duk da bata san k'arfe nawa ba amman daga yanayin da ta ga garin ta fahimci dare yayi sosae, har ta fita baya ko motsin mutum bata ji ba ta nufi part d'in da suke, lokacin data shiga cikin parlon kwalam yake da sauri ta nufi d'akin su, sai da tay d'an jimm kafin ta sa hannu a hankali ta d'an tura kopar, d'an lek'awa tay ta hango kowa yayi bacci sannan ta k'arasa tura kopar ta shiga, cikin tafiya mai kaman sand'a don kar tayi sauti wani ya tashi ta nufi cikin d'akin, a bakin gado ta zauna tana kallon su Haulat dake ta shan bacci, maido idon ta tay tana kallon gabanta tayi shiru zuciyarta ta shiga tunano mata dukkan abun da ya faru tsakanin ta da Sameer, tunano lokacin da yake mata magana gab da ita ta shiga yi yadda hucin bakin shi mai had'e da k'amshi ya rink'a bugun fuskarta, kokonton kodai ba giya bace ya sha ta shiga yi wata zuciyar ta raya mata to ita tasan yadda giyar take ne ai k'ilan kala kala ce akwae mai kamshi, tunano lokacin da ya kawo fuskar shi ya had'e da tata tayi har bata san lokacin data rufe ido ba sai kuma ta bud'e da sauri kawae sai ta saki murmushi, wasi wasi ta shiga yi na inda ta amince mashin da gaske zai yi mata wani abu ko kuwa, wata zuciyar ta k'ara raya mata kawai dae k'ilan hakanan yay mata hakan amman ai bata kai yayi hakan da ita ba in ma yana yin, har saida ta d'an ta6e baki, tunanin ko mi yaje yi a wannan wurin ta shiga yi tana raya wurin kaman Club a yadda ta fahimta kuma dai tasan ana cewa ba abun arzik'i ake ba a can, a hankali a fili ta furta "ko ma ina ruwa na" ajiyar zuciya ta sauke ita kanta tasan ba K'aramin firgici ya sata ba, tunanin ko ya yafe mata ko kuwa da gasken yake sai ta biya shin kamar yadda ya fad'a mata yanzu da suka dawo ta shiga yi can ta ta6e baki a fili ta furta "ni dai ai na fad'a mashi gaskiya bansan taya zan biya shi ba kuma" shiru tay tana kallon wuri guda can tay murmushi tunowa da abubuwan daya kawo mata taci ta raya ashe yana da kirki, kunna wayoyin tayi gaba d'aya nan taga ashe a fly mode yasa wayarta ta raya k'ilan ma Aunty Mareeya ta sake kiran ta, ta d'an d'auki lokaci a zaunen can ta tuna da ko sallar isha bata yi ba ta mik'e ta nufi hanyar toilet bayan ta aje wayoyin, saida tayi wanka ta d'auro alwala ta fito d'aure da kallabin ta, wurin akwatin kayanta ta nufa, doguwar rigar bacci ta fiddo bayan ta saka ta d'aukko Hijab ta wuce inda abun salla yake ta d'aukko ta shimfid'a, bayan ta gama sallar tayi Addu'a anan ta kwanta ba tare data cire Hijab d'in ba, gaba d'aya bacci ya k'aurace ma idanunta tay shiru tana kallon wuri guda can ta rufe su nan take zuciyata ta shiga tunano mata sufar Sameer a haka har bacci ya kwashe ta.

Washe gari bayan sun tashi sallar Asuba kowa ya ganta sai ya tambayi ina taje ne jiya ba'a kwanta da ita ba cikin kama kai take basu amsa da sun fita ne bayan sun dawo kuma ta tsaya d'akin Jidderh fira, bayan ta gama sallar ta d'auki wayar Fatuu don ta kai mata, lokacin data je d'akin su Jidderh ma basu dad'e da gama sallar ba sun koma gado bayan sun gaisa ta tambaye ta Fatuu nan ta sanar mata ba a gidan ta kwana ba, bayan ta fito zata koma part d'in su a ranta ta shiga raya dama dalilin kiran da Ya Haisam ke ta mata kenan tay d'an murmushi, tana shiga cikin parlon suka had'e da Aunty Mareeya tana sanye da doguwar rigar bacci kanta sanye da hula har saida gaban ta ya fad'i, tana ganinta ta tsaya Fauzyn ta tunkareta tana k'ak'alallen murmushi, gaishe da ita tayi ta amsa tana mata wani kallo tace mata ina taje jiya, rasa amsar da zata bata tayi ta fara yan kame kame, tunanin ko tace mata tare suka fita da Zarah tay sai kuma ta tuna da har yanzu ita bata gidan k'ilan kuma Aunty Mareeyar tasan ba gidan zata kwana ba, hannu ta kai ta kama kunnanta tace "fad'i man ina kika je jiya har aka kwanta baki dawo ba, kuma na kira wayar ki baki d'aga ba k'arshe ma dana sake kira sai kika kashe" yamutsa fuska Fauzy tay alamar tana jin zafin kama kunnanta da tayi, hakanan taji bata son fad'i mata abunda ya faru don bata san ya zata d'auki zancen kai ta wani gida da Sameer yayi ba, k'ara murd'e kunnan tayi ta saki yar k'ara tace zata fad'i mata don Allah kar ta tsinka mata kunne, cikin yar in ina tace mata dama da wani abokin Ya Haisam ne suka fita, waro ido Aunty Mareeya tayi ta saki kunnan nata da alamun Mamaki tace "kuka fita ku ka je ina?" tana kikkafta ido tace gari suka fita ya zagaya da ita, hannu Aunty Mareeya ta hau tafawa da alamun d'an tashin hankali tace zaga gari shine har wurin sha biyu bata dawo ba don ma taji Zarah itama bata nan shiyasa hankalinta ya d'an kwanta tayi tunanin suna tare, abu Fauzy ta had'iya a ranta ta raya don ma bata san k'arfe nawa ta dawo ba, daga Maganar da Aunty Mareeya d'in tayi ta samu k'aryar da zata mata tace ai daga zaga garin wurin su Zarah d'in suka wuce, tambayar ta ina Zarah d'in taje tayi tace suna tare da Ya Haisam a wani gidan su, gaba d'aya tayi kalar rashin gaskiya don hakanan ta fad'i hakan bata san ina Fatun suka je ba, murmushi Aunty Mareeya tay tace "Uhm su Malam miskili kenan gaba d'aya yana neman takura ma Yarinyar Mutane" murmushi Fauzy tay cikin alamun kunya tace "to Aunty Mareeya ba duk ke ce ba" hannu ta kai zata kai mata bugu tana fad'in ita uban mi tayi Fauzy ta goce tana dariya, tambayar ta tay shi wanda suka fitan cewa yay yana son ta Fauzyn ta d'an girgiza kai tace a'a kawae dai sun fita ne, harara ta wurga mata tace ita kuma ga mara aji kawai sai ta bishi zararai zararai Fauzyn tay dariya,

"Amman gaskiya Fauziyya yakamata kiyi saurayi ko kema Kya zo kiyi aure don Allah Zarah bata burge ki ba" tana murmushi tace "ta burge ni sosae Aunty, kuma dama tun lokacin data tare naji nima ina son in yi auren to amman ni fa har yanzu banda saurayi...." A hasale Aunty Mareeya ta katse ta "ta gidan uban wa zaki saurayin bacin har yanzu kin kasa cire wanccan shashashan mayaudarin daga cikin Zuciyar ki" yanayin fuskar Fauzyn ne ya canza cikin karyayyar murya tace "Aunty dole fa Mujaheed ya tsaya man a rai ko ya ya ne, kar ki manta bansan soyayyar kowa ba sai tashi, tun bansan kai na ba nasan miye soyayya ya koya man son shi daga shi kuma ban k'ara son wani abu, tsawon lokaci muna tare" idanunta har sun ciko tab da k'walla, ta6e baki Aunty Mareeya tay tace "Shikenan kada Allah yasa ki cire shi daga ran naki kiyi ta zama kar ki yi aure har mahadi ya bayyana" tana gama Maganar ta juya zata tafi da sauri Fauzy ta k'ank'ameta ta baya ta saki kuka tana fad'in don Allah tayi hak'uri wllh a yanzu a shirye take da tayi Aure indai ta samu mai son ta tsakani da Allah kuma itama taji tana son shi, juyowa tay ta rungume ta ta kai hannu tana goge mata hawayen tana fad'in ya isa, bayan ta yi shiru tace "Yanzu shi wanda kuka fita d'in da gaske bai ce yana son ki ba?" Kai ta d'aga mata ta sake cewa "to in yace yana son ki zaki amince" shiru Fauzy tay a ranta ta shiga tunanin to waima ita waye zai ce yana son nata Sameer dai tasan ko fad'uwa zatai a gaban shi tana mashi magiyar ya so ta ba son ta zai ba balle har ayi Maganar aure shiyasa ma bata sa ma ranta wai taji ko tana son shi ba, ganin ta kafeta da ido yasa tayi d'an murmushi ta jinjina mata kai alamar eh, sakinta Aunty Mareeya tayi ta d'aga hannuwa ta fara fad'in,

"Ya Ubangiji ina rok'on ka da sunayen ka tsarkaka da suffofinka mad'aukaka, ga kanwata nan ka bata miji nagari wanda zai so ta Saboda kai, Ya Allah Idan wanda suka fita tare Alkhairi ne a tattare da ita kasa mashi son ta da k'aunar ta a zuciya ta yadda har Al'amarin zai kai su da Aure Alfarmar Annabin rahama SAW" a hankali Fauzy itama ta fad'i S.w.a ganin Aunty Mareeyar ta shafa itama ta shafa tana d'an murmushi ita tausayi ma Aunty Mareeyar ta bata wllh ganin ta shirga mata k'arya kuma ta yarda, a hankali tace mata ta gode da kaunarta da take tana dariya tace mata ai wannan dole ne ita dai fatanta ta cika masu burin su tace mata in sha Allah daga haka ta juya tana mata k'orafin Saboda ita bata koma bacci ba ta nufi hanyar Bedroom Fauzyn nata kallon ta har ta shige sannan ta sauke ajiyar zuciya ta juya.

Misalin k'arfe goma sha d'aya na safen Haisam da Fatuu zaune a saman Carpet cikin parlon gidan da suka je wanda d'aya ne daga cikin gidajen estate d'in Dad d'in shi su suke amfani da shi, gaba d'aya ta shige cikin jikin shi kamar wata yar mage breakfast suke yi wanda da kan shi ya had'a masu tana ta bacci saida ya gama ya tasheta jikinta sanye da rigar bacci kanta ba kallabi sai sumar ta dake a fake, bayan sun gama ta mik'e ta fara tattara kayan, d'aukar babban tray d'in tayi ta juya zata kai kitchen ya bi bayan ta da kallo Fuskar shi cike da annuri, shi kad'ai yasan yadda yake jin yarinyar a cikin ranshi kullum da kalar nishad'in da yake samu a wurin ta, dawowa tay idon shi akanta yana mata murmushi itama murmushin take sakar mashi, ware mata hannuwan shi yay ta tafi da sassarfa ta fad'a mashi ya maida hannuwan ya rungumeta sosae ta d'ago fuska tana kallon shi, kai fuskar shi yay ya had'e da tata yana d'an danna hancin ta da dogon hancin shi, dariya tay tace "kai Hubby in ka k'ara shigar man dashi fa dama kana ganin shi d'an bajajje" yar dariya yay ba tare da ya raba fuskar tasu ba yace mata shi haka ganin shi yake yafi na kowace mace a duniya kyau, d'an bud'a ido tay har zata fad'i wani abu sai kuma tay shiru, sun d'an d'auki lokaci a haka suna ta shan love sai zuba ma juna sweet nothings suke suna dariya, d'agota yay yace taje ta shirya su koma gida aikuwa ta tura mashi baki ya d'age gira ya tambayeta minene a shagwabe tace "ni dai Allah bazan koma ba, kawai yanzu kowa ya tashi ansan ba gidan na kwana ba sai a ganni tsugui tsugui na dawo hakan ma ai rashin kunya ne" gaba d'aya ya zuba ma bakinta ido har ta gama idanu a lumshe yace mata ai ba wani rashin kunya don tana tare da mijin ta kuma ai su ba yanzu ne sukai auren ba ko" shagwaba ta shiga yi mashi harda su mak'e kafad'a sai sakin k'ayataccen murmushi yake, tambayar ta yay yanzu ya take so ayi tace ita dae bazata koma ba sai dare yace ta manta yau akwai dinner ne tace to ai tasan bada wuri za'a tafi ba in akayi Magrib lokacin gari ya d'an yi duhu sai su koma, d'aga mata kai yayi alamar za'a yi hakan can kuma tace koma kawai ta shirya daga nan sai ya kira Aunty Laila yayi mata magana yace Ok.

Zuwa Azahar duk an san Fatuu bata gidan, sam Fanan bata wani ji hakan ya dame ta ba don itama shekanjiya da ta zo ba gidan ta kwana ba tana tare dashi a wani gidan nasu wanda tana tunanin can ya tafi da Fatuu. Ana gama sallar Magrib aka fara shirin dinner lokacin Aunty Laila ta d'auki kayan da Fatuu zata sa ta tafi can gidan da take a Motar ta, saida ta biya ta d'auki wadda zata mata Make up suka tafi tare, lokacin da suka je Fatun ita kad'ai ce a gidan Haisam ya fita tana sanye da doguwar rigar material d'in data sa jiya da zasu taho, ba tare da 6ata lokaci ba aka fara mata make up d'in don dama tayi wanka kafin su zo, a can gida ma tuni shirin yayi nisa su Jidderh da Fauzy da Mino harda Haulat Nameer ya d'auke su ya kai su wurin make up wanda daga can zasu wuce tsadaddiyar Event Center d'in da aka kama hall d'in da za'ayi dinner d'in, aikin Abinci da abubuwan sha wata k'awar Mom da Sana'ar tace aka ba kwangila,

Tubarakallah Ma sha Allah shine abunda na fad'a dana dawo kan Amarya Fatuu, doguwar rigar material light ash tasa rigar tabi shape d'inta daga wurin k'ugun an yi wata yar tattara ta net ta d'an rufe k'ugunta da rigar ta kama ya fito sosae, daga k'asan rigan ta baya ya ja k'asa, head dark blue mai shining aka nad'a mata tseps d'in sun hau sosae daga tsakiya an nad'e mata gashinta ya d'an fito, sark'a da yan kunnan Diamond d'inta aka saka mata harda zoben su da yan hannu guda biyu sai d'ayan hannun aka sa hadaddiyar agogo silver, wasu jigunannun takalma half cover masu igiya da clutch d'in su duka kalar head d'in ta saka sai d'aukar ido suke haka Material d'in kai kace adon stones d'in jikinshi da diamond akayi su don ba K'aramin had'uwa yayi ba yana daga cikin kayan da aka siyo a Dubai, Jama'a ku zo kuga Amarya Fatuu ita kanta tasan ba k'aramar had'uwa tayi ba har ta kasa rufe bakinta sai washe shi take nan aka shiga yi mata hotuna da Vedios, ana gamawa Laila ta d'aura su a status d'inta mutane suka fara gani harda yan can gida, Fanan ce ta gani ta nuna ma su Aunty Mareeya da tuni suma sun saka leshin su na anko wanda kalar head d'in da aka d'aura ma Fatuu ne duk da bai ciza kalar shi sosae ba kamar head d'in, nan fa aka hau yabo haka su Jidderh ma acan inda suke duk sun gani, bayan an gama da Fatuu aka fara yi ma Aunty laila bayan ta saka ankonta da ta taho dasu, wasu yan Arzik'in riga da skirt ne aka mata kalar na manyan yan matan Abuja, bayan an gama yi mata make up d'in aka nad'a mata kallabinta sosae ya tashi kamar head don anyi mashi starch. Misalin k'arfe tara saura aka fara d'aukar mutane ana kaiwa wurin event d'in, saida aka gama d'aukar kowa sannan Haisam yazo gidan da su Fatuu suke Abbas ne ya tuk'o Motar galleliyar ash, suna cikin parlor suka shigo Haisam d'in na sanye da babbar shadda gizner light ash dinkin yan ciki da babbar riga kanshi sanye da ash d'in hula haka agogon hannun shi da takalman shi half cover duk kalar shaddar ne sai uban k'amshi yake bazawa kai kace wanke shaddar akai da ruwan turare, Abbas ma na sanye da tsadadden plain yard kalar lace d'in su Laila anyi mashi d'inkin Senator style wadda gaba d'aya irin d'inkin da sukai kenan mazan, kai, abun dai ba'a magana wllh sha'anin manya na daban ne, hotuna aka shiga yi masu shida Fatuu daga baya suka yi da su lailar harda mai makeup da itama ta saka fitted gown ta ankon, bayan sun gama ya kama hannun Fatun su Laila suka take masu baya suka nufo waje, duk son Fatuu da takalma masu tsini wannan dakyar take yin tafiya dashi, a bayan Motar da suka zo da ita shi da Fatun suka shiga Abbas ya shiga kujerar driver Laila kuma da mai makeup suka hau Motar ta a tare suka tafi.

Bayan sun isa harabar wurin dankam take da motoci na Alfarma sosae Event Center d'in ya had'u, Laila ce ta fara fitowa taje Motar su ta sanar masu su jira kar su fito Abbas ya bud'e k'opar gaban ya fito, lokacin Motar Nameer ta danno kai cikin wurin, dakatawa Laila tayi suka k'araso bayan ya parker duk suka bud'e kopopin kusan a tare suka fito, kai Jama'a wannan gayu haka🤔 ai ni bamma gane su Fauzy da Mino ba gaba d'aya suma sun koma kalar yan Abujar, gaba d'aya anko ne a jikin su har Zainab ma na Fatuu ta saka amman saida aka sha mata su ba kamar wurin hips d'in, su duka riga da skirt ne banda Haulat ita doguwar riga ce kuma ita kad'ai ke da mayafi, Baby d'inta ma tayi mata gayu da yan kanti tana ruk'e a hannunta, Nameer ma ankon mazan ne a jikin shi yasa hula duk sumar shi ta fito ta baya da gefe abun saidai ace Ma sha Allah Angon Mino, wurin Aunty Laila d'in suka zo ta shiga yabon gayun su suna dariya haka ma Abbas yace ma Mino ai shi bai gane ta ba ma, ce masu tay su jirata anan ita da Abbas suka nufi cikin hall d'in, Motar saurayin Jidderh ce ta sake sako kai dama tare suke sun riga su isowa ne, bayan ya parker a tare suka fito ita straight gown ce aka mata shima saurayin nata Sadeeq ankon mazan ne a jikin shi suka zo wurin su Fauzy, kusan duk an hallara isowar Amarya da Ango kawae ake jira hall d'in yasha decorations, sosae ya had'u in nace in tsaya in bayyana tsaruwar wurin to kuwa dare yayi ba tare da na bayyana yadda Dinner d'in ta wakana ba, sosae kwalliyar hall d'in ta hau da dressing d'in mutanen wurin dama su suka za6i wanda za'ai masu, daga saman hall d'in nan aka aje leather chair mai kyau daga gabanta d'an table d'inta ne d'auke da abubuwan sha harda flower mai kyau, bayan wurin ya k'awatu sai sakin haske yake kala kala hatta saman hall d'in a lullube yake da irin decoration d'in da aka zagaye hall d'in, daga gaban hall anyi shimfid'u masu k'ayatarwa a gefen dama manyan speakers ne na masu DJ daga can bangaren hagu masu kid'an ganguna ne duk sun yi ready, daga su sai dogayen tebura suna kallon juna daga bayan su aka jera kujeru gaba d'aya an lullube su daga saman tables d'in an jera k'ayatattun flowers dake sakin walwali harda wasu sarkoki aka yi adon su abun dai sai wanda ya gani, a saman su k'awayen su Mom da Aunty ne da wasu Manyan mata yan uwansu,

daga su sai wasu had'add'un royal sofas da aka jera suma suna kallon gaban hall an jera k'ananun table d'in kujerun a gaban su a nan Hajiya Zainab take da yaran ta daga gefe kuma Mom ce da wasu matan manya harda matar Speaker house of rep da wasu matan ministoci, daga can d'ayan side d'in nan hamshaki Sameer yake a hakimce dasu Salim da Najeeb da wasu Abokan su yayan masu fad'a a ji duk ankon mazan ne a jikin su kuma gaba d'aya d'inki iri d'aya, sauran cikin hall d'in anyi seat arrangements na kujeru masu round an zagaye su da kujeru guda hud'u kowanne table an kuma nad'e su da covers kalar da suka hau da decoration d'in bangon hall d'in a kowanne table an d'aura flower mai kyau, iya dai hall d'in ka gani kasan ba k'ananun kud'i ya ci ba, bayan su Laila sun shigo wurin yan mata taje ta za6o wasu ta wuce wurin dasu Aunty Mareeya suke tace ma Fanan ta taso a shigo da ita tace to itama tana sanye da ankon anyi mata fitted gown wuyanta sanye da yar ziririyar sark'ar diamond da barima harda d'an hannu tayi kyau ba k'arya, Su Yadikko ma da gwaggo duk suna zaune sun sha anko Yaya ma na sanye da k'uri adakan leshin ta mai kaman bambalasta, Abbas ma wurin su Najeeb yaje ya sanar dasu su taso a shigo dasu Haisam, saida Laila ta je wurin masu Dj ta sanar dasu wak'ar da zasu saka sannan ta yi ma babban MC magana kan shigowar, bada jimawa ba MC ya sanar da shigowar su aka saki wakar Aure Martaba gaba d'aya hall d'in ya d'auka, su Haisam d'inne a tsakiya yana ruk'e da hannun Fatuu na dama Fanan na ruk'e da na hagu daga bayan su su Jidderh ne a 6angare d'aya sai su Abbas a d'ayan bangaren hamshak'i Sameer dai dama bai taso ba, suna shigowa ciki aka saki wata k'ara mai kaman jiniya, saida aka raka su saman kafin suka dawo cikin hall d'in, sakin dry ice smoke akai gaban hall d'in ya turnuk'e da hayak'i ya shiga fita yana bada k'ayataccen design kowa kaga fuskar shi d'auke take da murmushi, bayan duk an natsu Mc yay welcoming kowa da bayanin dalilin daya sa sukai gathering a wurin, agenda ta farko Abbas aka kira yazo yayi jawabin maraba, bayan ya fito cikin harshen turanci bayan yayi Addu'a yay ma kowa sannu da zuwa da dalilin taruwar su k'arshe yay ma ma'auratan fatan Alkhairi yayi godiya ga mahalarta taron musamman manyan iyayen su, bayan ya gama Mc ya fad'i next abunda za'ai wanda takaitaccen tarihin Ango za'a bada ya ambaci sunan Sameer matsayin wanda aka sa zai bada tarihin, yana a Hakimce akan kujera ya d'aura k'afa d'aya akan d'aya kai kace ba sunan shi aka kira ba duk wanda suka san shi idon su na akan shi sai da ya mula bayan Mc ya k'ara kiran sunan sannan ya d'an d'aga hannu yayi mashi alamar ya kawo mashi lasifikan, da yawa basu yi mamakin hakan da yayi ba ciki harda wanda suka ga lokacin da suka zo gidan su Haisam, bayan an Kawo mashi sai da ya d'an d'auki lokaci sannan ya d'an kai ta kusa da bakin shi cikin isa ya fara magana, tsit kake ji kowa shi yake saurare cike da gwanancewa da kwarewa yake bada tarihin da turanci kai kace ba bahaushe bane duk da dai za'a iya cewa ba cikakken bahaushen bane, zuru Fauzy tay tana kallon shi ta can gefen shi da suke zaune duk da gefen fuskar shi kawai take iya gani, sosae yasa jikin wasu tsuma yana gamawa ya janye lasifikan ya d'aurata saman table d'in gaban shi duk da Mc d'in ya taho ya amsa aka shiga tafawa, bayan Mc ya d'auka harda yi mashi godiya bai ko kalle shi ba nan fa wad'anda basu san shi ba suka fara tambayar waye shi, abu na gaba da Mc ya fad'i za'ayi shine bada takaitaccen tarihin Amarya wanda aka kira sunan Fauzy itace zata yi, mik'ewa Fauzy tay duk da ta shirya ma hakan sai da gabanta ya hau fad'uwa, gaban hall d'in ta nufa a d'arare duk kunya ta rufe ta Saboda rashin mayafi don bata saba ba ko Yaya ne in zata je abu irin haka tana saka gyale, wurin Mc d'in taje ya mik'a mata lasifikan bayan ta amsa tana juyowa ta sauke idanunta kan Sameer suka had'a ido wani irin bugu kirjin ta yayi da sauri ta maida idonta ya koma kallon k'asa, a nutse ta fara godiya da yabo ga Allah da neman tsira da aminci ga fiyayyen halitta kafin ta fara bada tarihin Fatuu, sosae tay k'ok'ari wurin yi da turanci ba wata gargada duk da fargabar da take ji, tana gamawa aka shiga tafa mata bayan ta bashi lasifikan ta nufo cikin hall d'in idanunta a k'asa Mc d'in na yaba mata, abu na gaba Amarya aka buk'aci ta bayyana irin farincikin da take ciki da kuma tarihin yadda suka fara soyayya da Angonta har suka yi aure, mik'ewa Fatuu tay gabanta nata d'an fad'uwa ta nufo saukkowa daga saman Mc d'in nata kod'a ta, mik'a mata lasifikan yay ta amsa ta juya ta kalli Mutane, ta saba yin magana a gaban mutane tun a Secondary School hakan yasa bata ji komai ba a nutse cikin sanyin murya ta fara magana, godiya tay ga Allah sannan tayi ga mahalarta taron, tiryan tiryan ta shiga bayyana tun farkon haduwarta da Haisam zuwa dawainiyar da yayi da ita a rayuwa da yadda Allah ya jarabe ta da son shi sakamakon kyautatawar da yake mata da kuma yadda ya zama mijin ta a lokacin da bata ta6a zata ba, gaba d'aya komai a tak'aice take fad'i, juyawa tay ta kalli Haisam ta fara yi mashi godiya akan sadaukarwar da yayi a gare ta wurin ganin ya maida ita mutum, sosae ta shiga yi mashi godiya tana nuna bata da abunda zata iya saka mashi saidai tayi mashi Alk'awarin zama mai biyayya da saka shi Farinciki, Haisam d'in sai kallon ta yake da d'an murmushi wani abun in ta fad'a sai ya lumshe mata ido, bayan ta gama nashi komawa tay kan Fanan farko yabonta ta fara yi tace tunda take a rayuwarta bata ta6a ganin mace irin ta ba, ta had'a komai na rayuwa amman hakan bai sa ta zama mai girman kai ba, ita a wurinta kirkinta har yayi yawa, tunda ta fara ganinta take k'aunarta har ta kai ta amince mata ta zauna da ita a matsayin kishiya ko kuma tace k'anwa Saboda farincikinta, nunawa tayi bata da kalmomin da zata iya yin amfani dasu wurin gode mata sai dai tayi mata Alk'awarin zama tamkar k'anwarta uwa d'aya uba d'aya da yardar Allah bazata zama matsala a gare ta ba saidae silar farincikin ta kuma tana son shaida masu ita da mijin su sune Mutanen da sukai mata kirkin da ba wanda ya ta6a mata irin shi a rayuwa duk da they're on a different level haka suka jata a jikinsu suka nuna mata duk d'aya suke, muryarta ce ta karye dama tuni k'walla sun fara zubo mata, Addu'oi ta shiga yi ma Fanan Mutanen cikin Hall d'in na amsa wa har ta kai kuka yaci k'arfinta kawai sai ta durk'ushe anan ana jiyo sautin kukan nata ta cikin loud speakers, Kusan a tare Fanan da Haisam suka mik'e suka nufota, Haisam ne ya riga saukkowa don da sauri ya nufo ta lokacin da Fanan ta k'araso ya d'ago ta tana zuwa kawae sai ta rungumeta ta saka kuka itama, baiwar Allah koda bata nuna kishi ba wai don bata jin shi bane ita kadae tasan battle d'in da take da zuciyarta kawai bata da mafita ne tasan hakan shi yafi mata Alkhairi,

Hannu Haisam ya bud'e ya rungume su aikuwa gaba d'aya aka hau tafi da sowa wasu suka fara yi masu Vedio daga inda suke, d'agowa yay ya kai hannu cikin aljihun shi ya fiddo farin hanky, d'ago da fuskar Fanan yay ya shiga share mata hawayen fuskarta itama tasa gefen gyalenta tana goge ma Fatuu, bayan sun gama goge gogen hawayen a tare suka kama hannun Fatuu ta yadda suka saka ta a tsakiya suka nufi komawa saman nan Mc ya shiga kwarzan ta su yana fad'in "What an emotional occurrence, What a beautiful Family...." Bayan sun koma saman a tare suka zaunar da ita ta sadda kanta k'asa tana ta sheshsheka, Mc ne ya sanar za'a jira Amarya tayi shiru sai aci gaba duk akai murmushi, after some few minutes yace ma Haisam saura shi suna so ya bayyana farincikin da yake ciki, tun kafin ya rufe baki ya girgiza mashi kai alamar bazai ce komai ba Mc hada kwa6e fuska ya juyo yace to anyi ma Ango laifi an sa Amaryar shi kuka don haka bazai yi magana ba aikuwa su Laila suka mik'e suna basu yarda ba yadda itama tayi shima sai ya yi nan fa wasu ma suka sa baki harda su Aunty abun sosae ya bada nishad'i, ganin an fi k'arfin shi yasa shi yi ma Mc d'in alamar ya kai mashi lasifikan, da sauri ya nufi saman ya mik'a mashi, yana amsa abunda yace shine yana matuk'ar son matanshi kuma zai yi matuk'ar kokarin ganin ya zama mai Adalci a gare su, yana fad'in hakan ya mik'a ma Mc mike d'in gaba d'aya aka hau tafi da sowa harda Sameer sarkin kamewa saida ya d'an yi guntun murmushi, mik'ewa Laila tayi ta nufi bayan hall d'in, cikin wani d'aki ta shiga inda ma'aikatan da zasu serving mutane Abinci suke gaba d'aya jikinsu sanye da farar t-shirt mai d'auke da tambarin wurin da suke aiki na k'awar Mom, umarnin fara kai Abinci ta basu dama abunda suke jira kenan ba 6ata lokaci suka fara zuzzubawa suna d'aurawa a saman manyan trays, a wuri na musamman aka zuba ma su Her Excellency da sauran manyan matan, ko ban fad'a ba ansan abinciccika ne na musamman nan suka shiga kai ma mutane duk abunda mutum yake so zai d'auka in ma fin plate d'aya ne mutum ke so na wani Abincin zai iya dauka, masu raba lemuna ma suka shiga kawo ma mutane shima ko nawa mutum ke so zai d'auka, samun wuri Mc yay yana fad'in bari yay refilling cikin shi ya k'ara samun karsashi duk aka sa dariya don cike da barkwanci yayi Maganar, a nutse kowa ke cin Abincin kuma ba wanda ya damu da yadda wani ke cin nashi har lokacin Fanan na saman tare suke cin Abincin harda ba Fatuu a baki tana murmushi ta bud'e mata bakin daga baya itama ta bata, Mc na gamawa ya mik'e yana fad'in to basu da lokacin 6atawa bari aci gaba da abunda ya tara su duk aka sa dariya ana fad'in sai da ya gama yasan basu da lokacin 6atawa, abu na gaba Ango da Amarya aka buk'aci su sauko su taka Haisam nuna wa yay bazai je ba Fanan ta nuna mashi kar yayi hakan baza'a ji dad'i ba, tare suka mik'e ya kama hannun Fatuu ita tayi gaba suka biyo bayanta, tana saukkowa ta koma cikin hall din Mc ya nuna masu inda zasu tsaya, suna zuwa wurin kawai aka fara sakin fireworks da dry ice smoke, Ya Allah har tsuma nike Saboda kayatuwar yadda ake sakin hayakin da kuma tartsatsin wutar kowa ka gani murmushi ne akan fuskar shi wasu kuma washe baki sukai, ita Fatuu ma d'an tsoron abun ne ya kamata yadda hayakin ya turnuk'e su da kuma yadda tartsatsin ke fita da k'arfi,

"Dama nasan da wuya H,Zee bai auri yarinyar can ba, tun da naga yak'i amince man in nemeta dama I ave suspected something ever since" Najeeb ne da yake zaune gefen Abbas yayi Maganar, yar dariya Abbas yayi yace mashi wllh ba wani abu a ranshi a lokacin daya wuce taimaka mata kawai Allah ne ya k'addaro zasu zama ma'aurata yace baya fad'i mashi yadda komai ya faru ba, hararar Abbas d'in yayi fuska d'aure yace "ai kaima ba sona kake da ita ba in ba haka ba why not ni ka kirani kai man Maganar Aurenta kaga in ban aureta ba" Sosae Abbas yake dariya bai dai ce komai ba acikin ran shi ya raya ai duk k'anwar ja ce, Salim dai d'an murmushi kawae yayi, kamata Haisam yay har hayakin ya washe, wak'ar Fall in love aka kunna masu yana rik'e da ita sai murmushi yake mata itama d'an murmushin take duk kunya ta lullube ta, a hankali yake d'an motsawa da ita har lokacin tartsatsin wutar na tashi a bangaren daman su da hagun su abun gwanin k'ayatarwa, masu hoto da Video nata yi harda wanda aka daukko, bayan d'an lokaci kafin wak'ar ta k'are Laila ta nufi wurin Dj ta fad'i mashi ya canza masu Wak'a tace yasa wak'ar breaker ta burina, a hankali taken wak'ar ya fara da kid'a mai sanyin dad'i kafin baitin wak'ar ya fara fita,

_Dubaaa kan ki ana kallonaa....babban buri na ki kasance dab dani, in zaakii k'irga masoya naki ki sanyo danii, dubaaa kan ki ana kallonaa majnunii ni kuma nace in dai kai na ki ne baan fad'i ba, sak'o ya bayyana ni tun daga zuciya, sannan k'aunar ki tana kaman zuciya......_

Kowa kaga ni fuskar shi d'auke da Murmushi wasu suna d'an juya kai suna bin wak'ar, lokacin da aka zo baitin da ake cewa _" kin rikirkita dukka tunani na, taimaka ki bani wurin kwana, son ki ya hana min bacci na, ina ganin ki har a mafarki na, son ki yanaiii min dad'i ban san mu rabu......"_ Laila da ke tsaye tana masu Vedio ta d'aga murya tace "Big Bro yi mata zaka rink'a yi fa" Murmushi kawae Haisam d'in yay Jidderh ma ta k'ara d'aga murya tana cewa ya saurara za'a k'ara maido mashi, baitin na k'arewa Laila tace ma Dj d'in ya maido baitin, yana maido shi duk aka maida hankali kan su Laila da Jidderh harda sauran k'annansu da wasu yan uwansu suka shiga fad'in yayi mata har saida suka ba Haisam d'in dariya Fatuu ma haka duk kunya ta rufe ta, lokacin da baitin ya kusa zuwa k'arewa kawai sai gani sukai ya bi harda nuna ta, wani irin ihu aka sa Fatuu ta 6oye fuskarta tana dariya, sosae abun yaba mutane nishad'i, Hajiya Zainab ce ta mik'e tana murmushi Momy ma ta mik'e suka nufi gaban Security detail d'inta na biye dasu hannunta ruk'e da jakar ta, wurin su suka je ta mik'a ma security d'in hannu ta bata jakarta, bandir d'in yan dubu dubu ta fiddo guda biyu haka Mom ma su ta fiddo daga cikin jakarta nan fa suka fara masu ruwan nera, ai kamar sun bud'e k'opa sauran manyan bak'in ma duk suka mik'e suka nufi gaban ai masu kid'an ganga na ganin haka ba 6ata lokaci suka hau bugun gangunan su suna wasa manyan matan nan fa Hall ya karad'e kid'a ko ta ina abun sai ya ba mutane ma dariya, Laila ce tayi ma Dj magana sannan ya kashe nashi, Laila ma lik'in ta fara masu Jidderh ma saurayinta ya fiddo bandir d'in d'ari biyar biyar ya bata taje haka su Nameer ma, daga wurin lik'in su Her Excellency da Mom dasu Aunty sauran manyan bak'in duk tafiya sukai, nan aka cigaba da rawa ana lik'i, wai ashe haka Laila da Jidderh suka iya rawa harda kama Haisam suna yin rawar, Yadikko ma saida taje ta amshi canjin yan d'ari biyu biyu tayi ma d'iyarta lik'i koda Fatuu ta ganta rungume ta tayi, gwaggo dai bata yi ba Saboda kunya tana zaune sai dariyar farin ciki take, Kawu Amadu da Tk da Nameer ma duk saida suka yi, Haulat ma saida taje tayi canjin yan d'ari biyu taje tayi haka Saude ma Hajiya dai dama bata zo ba, rud'ewa Fauzy tay tana son yin lik'in amman bata da ko sisi duka yan kud'inta dasu ta siya takalma da jaka da mayafi da zasu zo, tana ganin Aunty Mareeya ta nufo cikin hall d'in ta gama lik'in nata da sauri ta tare ta kaman zata yi kuka tace mata don Allah ta bata kud'i itama taje tayi, wani kallo ta mata tace wllh bata da kud'in da zata bata itama wanda tayi k'arfin hali ne kawai, komawa tayi ta zauna jiki a mace Zainab ce tace mata tana da yan kud'i suje suyi canjin ko d'ari biyu biyu ne, girgiza mata kai tayi tace taje tayi kawai, ba yadda bata yi ba amman tak'i k'arshe ta tashi ta tafi ita, takaici duk ya kama Fauzy abu goma da asirin, ga Vedio ta kasa yi Saboda wayarta data kwankwatse bata iya fiddo ta a wurin ga rashin kud'i, k'arshe kife kanta tayi saman table d'in jin tana niyyar yin kuka, bata dad'e da kife kan ba taji ana mata sallama, d'agowa tayi ta kalli mai sallamar wanda d'aya daga cikin ma'aikatan dake hidiman Abinci ne, gaida ita yay da d'an alamun mamaki ta amsa mashi kawai sai gani tay ya Mik'o mata kud'i bandir d'in yan dubu dubu guda biyu dubu d'ari biyu kenan, ce mata yay gashi aka ce ya kawo mata taje tayi lik'i, waro ido tay da alamun Al'ajabi ta tambayi waye yace a batan, nuna mata saitin da su Sameer suke yayi yay mata kwatance wanda ya badan don ya juya kan shi yana a Hakimce iya sumar shi kawae suke iya hangowa, jimm Fauzy tay saida ya k'ara ce mata gashi sannan a tsorace ta amsa ya juya ya tafi, bin kud'in tayi da kallo kafin ta kai duban ta kan su Aunty Mareeya dake ta hira basu ma lura da abunda ke faruwa ba, a hankali ta juya ta kai idanunta kan Sameer ta bishi da kallo ji take kamar ta je ta maida mashi saidae tsoro bazai barta ba, tana haka kwatsam ta ga ya juyo ya kalleta suka had'a ido, wani mugun kallo yay mata ya janye ido ya koma yadda yake, ba shiri ta mik'e hannun ta ruk'e da kud'in ta nufi gaban hall din a d'arare, koda tazo saitin su ta kai idon ta kanshi bai ko kalleta ba, tana zuwa ta shiga yin lik'in bayan bandir d'aya ya k'are ta bud'e d'ayan ta raba biyu ta mik'a ma Zainab data saki baki tana bin ta da kallon mamaki, cikin makad'an ne wani yazo ya tambayi sunan Fauzy ita bata san dalilin ba ashe wak'e ta zasu yi kaman daga sama taji ana angaida Hajiya Fauziyya mai ruwan naira har bata san lokacin da tasa dariya ba tana d'an kare fuska, kirarin da ake ma Fauziyyar ne ya jawo hankalin Aunty Mareeya ta Ankara da lik'in dubu dubun da Fauzyn ke yi,

wani jiri Fatuu taji yana niyyar kwasarta da sauri ta kai duka hannuwanta ta kama jikin Haisam, kallon ta yay ganin yadda take lumshe ido yasa shi tambayarta tana lafiya ta d'an yamutsa fuska ta kai hannu ta dafa gaban kanta a hankali tace mashi jiri take gani ba shiri ya kamata ya fara k'ok'arin barin wurin da ita wad'anda suka ankara suna tambayar lafiya yace masu eh, su Laila ne suka cigaba da yin rawar ya koma saman da ita, bayan ya zaunar da ita shima ya zauna cike da kulawa ya tambayi har yanzu tana ganin jirin, d'an murmushi tay ta girgiza mashi kai a hankali tace ya bari yace ta tabbata kodai su tafi gida still da murmushi tace mashi kada ya damu tasan tsayuwar da tayi ne yasa, Fauzy na son yin rawa amman ta kasa Saboda Sameer duk da bata san ko yana kallonta ba, bayan ta gama yin lik'in nufar komawa tay cikin hall d'in idon ta a k'asa, tana zuwa saitin Sameer ta saci kallon shi karaf suka had'a ido da sauri ta janye idon, tana zama a wurin zaman su Aunty Mareeya ta nufo ta da sauri har tana bugewa da kujera, zama tay a d'aya daga cikin kujerun ido a waje tace "Ke, ina kika samu kud'i haka da kikai lik'i har ana Wak'e ki?" murmushi tay tace mata Allah ne ya bata, wata uwar harara ta zabga mata tace zata gaya mata gidan uban wa ta same su ko kuwa, tana dariya tace mata wani ne ya bata, k'ara zabga mata harara tay tace wani wa, satar kallon Sameer tay sai sumar kan shi ta hango, maido idonta tay kan ta tace mata mutumin jiya ne ya bata, washe baki Aunty Mareeya tay a k'agare tace mata yana ina Fauzyn tay d'an jimm kafin tace mata ya fita bayan ya bata kud'in,

"Da alama dai Addu'a ta zata amsu, koma har yace yana son kin?" dariya Fauzy tay ta girgiza mata kai, tace ai duk aje a dawo in kaga kare na sunsunar takalmi to d'auka zai yi, tambayarta tayi har nawa ya bata tayi lik'in ta fad'i mata, zaro ido tay tace "ba dai duka kika lik'a ba??" Kai ta d'aga mata kafin tace duka, bud'e baki tay alamar Al'ajabi tace "amman dai ke anyi shashasha wllh taya zaki je ki lik'a duka wannan uban kud'in ba tare da kin rage ba, maimakon ma ki saka bandir d'aya a jaka ki lik'a d'aya" fuska d'aure ta k'arasa Maganar, ce mata tay ai lokacin yana kallon ta fa taya zata d'au wasu Aunty Mareeyar tace eh to gara da bata d'auka ba kada yay tunanin tana da son abun duniya gara abi komai a hankali ya shigo hannu ita dai Fauzy dariya kawai take.

Sai wuraren k'arfe sha biyu da wasu mintuna taron ya fara tashi, Kusan duk an tafi wasu daga cikin Abokan Haisam d'in ne suka rage su Abbas da Najeeb sai Na'eem Salim ya tafi haka Sameer ma tuni ya tafi, Aunty Laila bata tafi ba tana waje tana k'ok'arin ganin an maida kowa Nameer ma bai dad'e da tafiya dasu Fauzy ba, su Abbas suna tsaye a sama inda su Fatuu suka zauna Haisam ma na tsaye tare dasu suna magana, Laila ce ta lek'o cikin hall d'in ta sanar dasu kowa ya tafi fa Haisam ya d'aga mata kai, Abbas ne ya kalli Fatuu dake zaune yace "Mom Zarah an sha gajiya ko" d'an murmushi tay Najeeb ya kai idon shi kanta suka had'a ido shima d'an murmushin yayi mata, Kallonta Haisam yay yace ta tashi su tafi ta d'aga mashi kai, tana mik'ewa ta fara ganin jiri da sauri ta kai hannu ta dafe goshi bakin ta a d'an bud'e, wani irin duhu ta fara gani lokaci guda ta fara fita hayyacin ta, Abbas ne ya kai idon shi kanta yaga halin da take ciki da sauri ya furta "Mom Zarah lafiya??" gaba d'aya suka kai idon su kanta ko kafin suce mata wani abu gaba d'aya ta tafi zata fad'i cikin zafin nama Haisam ya tareta ta fad'a jikin shi, cikin tashin hankali ya shiga fad'in "Baby! Baby can you hear me? Mike faruwa?" tun tana lumshe ido tana bud'e su har ta k'arasa rufe su baki d'aya............

*ASM 083*

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

...........Cikin tashin hankali yake jijjigata yana kiran sunanta, Abbas ne ya d'aukko robar ruwa bayan ya bud'e ya mik'a ma Haisam ya tara mashi hannun shi ya zuba mashi, sau biyu ya shafa mata amman ba alamar zata farfad'o, Najeeb ne da shima fuskar shi ta nuna tashin hankali yace bai kamata su tsaya suna wasting time ba ai rushing d'in ta hospital, Na'eem ne yace akwae wani private hospital daya sani bada nisa sosae ba, yana rufe baki Abbas yace ma Haisam ya d'aukko ta ya nufi hanyar fita Hall d'in da sauri sauri gudu gudu, d'agota Haisam yay ya d'auketa suka nufi hanyar fita dasu Najeeb, suna fita Abbas ya iso da Mota bakin wurin Najeeb ya bud'e baya Haisam ya saka ta ciki shima ya fara k'ok'arin shiga lokacin Laila ta k'araso hankali a tashe ta shiga tambayar wai mi ya faru da ita don Abbas ya sanar mata game da fad'uwar da tayi da ya fito, Najeeb ne yace hakanan suka ga ta fad'i, Na'eem ne ya shiga driver seat Saboda shi yasan Asibitin Najeeb da Abbas suka nufi inda Motocin su suke Abbas ya shiga Motar Na'eem haka Laila ma da gaba d'aya ta gama rud'ewa, a saman cinyoyin shi ya d'aura kan ta ya shiga shafa face d'inta yana kiran sunanta duk hankalin shi ya tashi, tashin Motar Na'eem yay bayan ya juya ya tunkari gate d'in wurin da gudu Motocin su Najeeb suka rufa masu baya, suna a kan hanya Laila ta d'aukko wayarta ta shiga kiran Mom d'in su, bayan tayi picking tun kan tayi magana cikin Muryar rud'u tace mata gasu a hanyar Asibiti, tambayar ta tay mi zasu je yi Asibiti tace mata Bride d'in Big bro ce hakanan ta yanke jiki ta fad'i, daga muryar Mom d'in zaka fahimci ba k'aramar razana tayi ba lokacin da ta sake maimaita abunda Lailar tace mata, tambayar ta tayi to miya faru da ita ne Fuskar Laila a yamutse kaman zatai kuka tace "Wllh ba abunda ya same ta kawae ta mik'e za'a taho gida ne aka ga ta yanke jiki ta fad'i" tambayar ta tayi an yayyafa mata ruwa tace mata eh an shafa mata har sau biyu amman bata ko motsa ba, salati Mom ta rafka a kid'ime ta tambayi wane Hospital zasu tace mata itama bata sani ba Abokin big bro ne yake jagorantar su shine yasan Asibitin, tun kafin ta rufe baki Mom d'in ta katse Wayar, hannu ta kai ta dafe gaban kanta tana salati Hajiya Zainab dake zaune duk taji abunda suke Magana akai itama daga yanayin fuskarta akwae alamun tashin hankali, tambayarta tayi miya faru da matar Son d'in tayi mata bayanin da Laila tayi mata, jinjina kai tayi tace to Allah yasa lafiya ta yuwu stress ne ya mata yawa Mom dake kallon ta tace to Allah yasa,

kiran Senator tayi a waya saida ta kusa katsewa sannan yay picking, saida ta bashi hak'uri na tashin shi da tayi don tasan in ba bacci yake ba wayar bazata dad'e tana ringing ba batare da ya d'auka ba, ce mata yay ba komai Allah yasa dai lafiya cikin yar rawar murya ta sanar dashi abunda ke faruwa cikin daidaita natsuwa don kada ta tada mashi hankali, salati shima yayi ya tambayi asibitin da suka tafi ta fad'i mashi yadda Lailan tace yace Ok bari ya kira Son d'in, kiran Nameer Laila tayi a tunaninta ko basu kai gida ba don basu dad'e da rabuwa ba, ya tsayar da Motar kenan gaban Entry Hall kiran ya shigo, yana yin picking ta sanar dashi abunda ya faru cike da Al'ajabi ya maimata abunda tace su Fauzy dake niyyar fita daga cikin Motar cak suka tsaya suna sauraren shi, bayan ya gama wayar har suna had'a baki wurin tambayar shi abunda ke faruwa ya sanar masu, gaba d'ayan su razana sukai kar ma Mino taji gaba d'aya ta zaro ido kirjinta na mata wani irin bugu jin Adda Fatuu d'inta ta fad'i, Jidderh ce ta rok'e shi suje Hospital d'in yace Ok duk suka rufe kopopin Motar yaja suka tafi, tuni Mino ta fara kuka tana fad'in Allah yasa Adda Fatuu ba mutuwa tayi ba irin na mamanta, duk da su Fauzy na cikin tashin hankali haka suka shiga rarrashinta harda Nameer yace mata ta kwantar da hankalinta in sha Allah ba abunda zai sameta suyi mata Addu'a duk suka jinjina kai, nan fa Mino ta shiga yin Addu'oin a bayyane suna amsawa da Amin can ta kai hannu cikin jakarta ta fiddo wayarta ta shiga kiran gwaggo, lokacin da kiran ya shiga su gwaggon duk sunyi bacci, saida ya kusa katsewa ta farka lokacin data d'auki wayar kiran ya yanke, ganin mai kiran nata ta ambaci Mino to lafiya kira a wannan lokacin, tana niyyar kira saiga wani kiran ya shigo da sauri ta d'aga tun bata ji mi zata ce ba saida gabanta ya fad'i, cikin kuka ta sanar mata Gwaggon ta saka salati hakan ne ya tada Hajiya ta bud'e ido, bayan gwaggo ta gama wayar Hajiya dake kallonta ta hasken bedside lamps tace "Ya ya Mike faruwa ne miya samu Fateemar ne?" Cikin tashin hankali Gwaggo ta sanar mata ai ba shiri ta idasa tashi zaune, hannu ta kai ta d'aukko wayarta ta shiga kiran Haisam lokacin da kiran ya shigo mashi ya kife fuskar shi data Fatuu idanun shi a rufe sai Addu'oi yake mata, yana jin wayar na ringing amman a halin da yake ciki bai jin zai iya d'aukar waya, k'in d'aga wayar da yayi ya k'ara tada ma Hajiya da gwaggo dake kallon ta hankali, kiran layin Senator tayi tana fara yin ringing ya d'aga Hajiya tace mashi yaji abunda ke faruwa yace eh gashi nan ma zasu je Asibitin tace to bari su fito yace a'a ta yi baccinta in sha Allah ba abunda zai faru tace "taya wani bacci zai yuwu hankula duk sun tashi kaga uwar ta nan cikin tashin hankali gara dai muje da mu zauna zaman jiran tsammani" amsa mata yay da to,

Gaba d'aya Haisam ya rasa inda zai tsoma ran shi, fargaba ta cika shi zuciyar shi sai raya mashi abubuwa take, bawan Allah in ta raya mashi wani abun sai ya girgiza kai da sauri ya k'ara k'ank'ame Fatun, wani iri yake jin zuciyar shi gaba d'aya rayuwar shi da ita sai dawo mashi take ba abunda yake gani sai fuskar ta d'auke da Murmushinta mai burgewa, "ko dai dama Allah bai yi zaku rayu tare tsawon lokaci ba" zuciyar shi ce ke raya mashi hakan da sauri ya hau girgiza kai kawai sai jin kwalla yay suna zubo mashi bai ko yi yunkurin gogewa ba, gaba d'aya gani yake tafiyar tayi tsawo har saida yayi ma Na'eem magana yace sun kusa, bada jimawa ba suka k'araso Asibitin a Jere motocin nasu suka shigo cikin harabar, Laila ko inda aka tanada don parking motoci bata k'arasa ba ta parker Motar, da sauri ta bud'e k'opar ta fito lokacin cikin security guards d'in dake bakin gate da ya biyo bayan Motocinsu yace mata pls ta gyara fakin ba'a yi anan bata ko kalleshi ba ta furta mashi it's an emergency daga haka ta nufi cikin Asibitin ko rufe Motar ma bata yi ba, Na'eem na fakawa da sauri Haisam ya kai hannu ya bud'e kopar ya fara k'ok'arin fitowa da ita Na'eem ya zo wurin ya taimaka mashi su Najeeb ma da sauri suka k'araso, yana d'auke da ita suka nufi cikin Asibitin a bakin main entrance suka had'e da Laila ta taho da nurses sun turo gado, d'aurata akai nurses d'in suka turata ciki suma suka rufa masu baya, Amenity suka nufa da ita Lokacin Doctor da wata nurse taje tayi ma magana ya nufo su, yana zuwa wurin ya gaidasu su Abbas ne suka amsa mashi ya shiga tambayar su abunda ya faru da ita suna tafiya suke bashi amsa, bayan sun iso aka shiga da ita d'aki Dr yace su jira shi ya shige,

Shiru shiru tun bayan da likita ya shige bai fito ba sai nurses dake ta shige da fice cikin d'akin, can bayan kaman minti goma sai gashi ya fito nurse na biye dashi d'auke da sample na jini da gani na Fatun ne, tarar shi su Najeeb sukai suna tambayar ya ake ciki shi Haisam ido kawai ya bishi da shi don zuciyar shi tuni ta karye, ce masu yay in sha Allah she will be alright su d'an jira kad'an suna kan binciken dalilin sumar nata ne don da ran ta in sha Allah, har saida su Najeeb d'in sukai d'an murmushi tare da jinjina mashi kai ya wuce nurse d'in ta bi bayan shi, kallon Haisam daya jingina da bango Abbas yay fuskar shi tayi jajir haka idanun shi, dafa Shoulder d'in shi yay yace ya kwantar da hankalin shi in sha Allah ba wata babbar matsala bace da alama haka take suman ta don da ta yi miscarriage ma ai ta dad'e bata farfad'o ba duk da shi harda firgici yanzu kuma k'ilan gajiya ce tayi yawa,

Na'eem ne ya matso shima yace "ni ina ma tunanin k'ilan harda smoke d'in nan duk da ance baida illa amman kasan kowa da kalan yadda jikin shi ke karbar bak'on abu" jinjina kai sukai cike da gamsuwa ba laifi Haisam d'in ya d'an ji fargabar shi ta ragu, after some minutes Likitan ya dawo saida ya d'an d'aga masu hannu sannan ya tura k'opar d'akin ya shige, su Nameer ne suka k'araso bayan Laila ta yi masu kwatancen inda Asibitin yake, gaida su Abbas sukai Mino dai ta kasa cewa komai sai bin su da ido take Fuskar ta sharkaf da hawaye Abbas ne ya shiga kwantar mata da hankali tana jinjina mashi kai, bada jimawa ba Laila ta dawo wurin tare dasu Dad da Mom sai Hajiya da gwaggo, gaidasu su Najeeb suka shiga yi gwaggo dai kai kawai take d'agawa don hankalinta in yayi dubu to ya tashi gaba d'aya jinin ta akan akaifa yake, Dad ne ya tambayi ya ake ciki Abbas ya fad'i mashi bayanin da likitan yayi yace "Ok sai mu jira shi Allah yasa muji Alkhairi" duk suka amsa da Amin, kallon Haisam yay da tunda suka zo bai tanka ma su ba sai ido kawae yake bin su dashi, ganin yanayin fuskar shi yasa shi kai hannu ya dafa Shoulder d'in shi da d'an murmushi yace "Don't worry Son, she will be fine in sha Allah muyi mata Addu'a" jinjina mashi kai yay Dad d'in ya kai hannu ya fara k'ok'arin cire mashi babban rigar yana fad'in bari a cire yasha iska don duk yayi zufa duk da yanayin wurin ba zafi, bayan d'an lokaci da zuwan su Hajiya tace ko dai a yi ma likitan magana aji halin da ake ciki an bar mutane da zullumi Gwaggo tace mata in ba ya gama binciken ba ba abunda zai iya fad'i tunda bai samu sakamako ba Hajiyar ta d'aga kai, Senator ne ya nuna masu waiting seat yace ma su Hajiya su zauna, Mino ma da duk hankalinta a tashe yake yace mata ta zauna ta d'aga mashi kai, basu jima sosae da zuwa ba Doctor d'in ya fito da sauri su Mom suka mik'e haka Hajiya ma da gwaggo, yana ganin Dad ya d'an sunkuyar da kai ya gaishe dashi bayan ya amsa yace ashe patient d'in su ce yace eh matar d'an shi ce, jinjina kai Doctor yay ya d'an yi shiru with confusion on his face Hajiya tace "Dr kai muke saurare, mi binciken naku ya gano yayi silar fad'uwar ta" nannauyar ajiyar zuciya yay idon shi akanta yace "pls zan iya ganin wani daga cikin danginta?" kan kowa ne ya d'aure duk suka zuba mashi ido, Dad ne yay saurin cewa "da wani abu ne?" d'an girgiza kai yay yace "No, kada ku damu yalla6ai inaso zamu d'an yi wata magana ne da d'aya daga cikin danginta wanda suke da kusanci sosae" kwa6e fuska Hajiya tayi tace "to ai nan duk danginta ne tunda alak'ar Aure ta shiga tsakani ai duk an zama d'aya, in ma mafi kusancinta ne ai Mijinta ne gashi sai kuyi Maganar" ajiyar zuciya doctor ya k'ara yi ya kai hannu ya gyara zaman glass d'in shi gaba d'aya jikin kowa yayi sanyi don sun fahimci bai son fad'i masu halin da ake ciki, sosae Doctor ya shiga rud'ani kawai sai ya yanke ya sanar da Mijinta abunda suka gano k'ilan shi yana da masaniya kan ciwon nata, tambayar ina Mijinta yay aka nuna mashi Haisam yace "pls let me see you in my Office" mik'a ma Abbas rigar shi yay wani irin Fad'uwa gaban shi ke yi ya juyo yay ma Dr alamar suje da hannu,

"Shin wai Fateemar ko juna biyu ne da ita??" har likitan ya juya Hajiya ta furta hakan da sauri ya juyo ya kalleta, komawa yay wurinta a d'an fad'ace tace ya fad'i masu abunda ke faruwa duk miye na wani 6oye 6oye, d'an gyaran murya yay ya fara kora mata bayanin cewa abunda suka gano shine stress ne yay mata yawa ta yuwu tayi zurga zurga da yawa ta gaji sosae hakan yasa ta suma sai dai kuma abunda ya assasa suman nata shine sun gano tana d'auke da juna biyu na tsawon wata guda, ai tun kafin ya rufe baki suka hau washe baki su Jidderh da Mino harda sakin k'arar murna gwaggo ma bakinta a washe yake haka Mom dasu Abbas kowa ka gani sai washe bakin murna yake Senator ma fuskar shi d'auke da fara'a yanata fad'in Alhamdulillah nan aka kama anata fad'in Alhamdulillah, bawan Allah ango ai shi gaba d'aya ma ya kasa magana sai murmushi yake kawai sai gani akai ya duk'a yayi sujjadar godiya ga Allah duk aka kalle shi kowa fuskar shi da fara'a, bayan ya mik'e Senator ya dafa Shoulder d'inshi yace "Hankali sai ya kwanta ko Son" kawae sai Haisam d'in ya fad'a jikin shi Dad d'in yasa hannu ya rungume shi anata dariya shima Haisam d'in dariyar farinciki yake don kwata kwata ba abunda yake zato ba Kenan, sosae hakan da suke ya ba Dr mamaki har Fuskar shi ta kasa 6oyewa Dad ne da ya lura still Haisam na jikinshi yace ma likitan kada ya damu ba sabon Aure bane an kwana biyu da yi kawae yanzu ne ake shagalin bikin, wata ajiyar zuciyar samun relieve Dr d'in yayi don da he was completely confused ace ana cikin shagalin biki kuma ga Amarya da ciki hakan ba K'aramin Al'amari bane, shima sai ya shiga taya su murnar yanata murmushi,

D'ago Haisam Dad yay suka had'a ido ya d'an bud'a ido yace "Son da alama ma har kuka kayi ko, halan kana tsoron kada Amarya ta tafi ana tsaka da shan Amarci ne" Yar dariya Haisam d'in yay sauran ma duk aka sa dariya, hannu ya kai suka gaisa ya furta "Congratulations my man, soon you will become a Father" cikin cool voice d'in shi ya furta mashi "Thank you Dad" Laila ce itama ta matso tana washe baki ta taya shi murna yay mata side hug ya amsa Jidderh ma ta matso tana washe baki tace "Congrats bro" jinjina mata kai yayi haka ma su Fauzy duk suka matso suna taya shi murna Nameer ma wurin shi yazo yana murmushi ya rungume shi yana taya shi murna, Abbas na tsaye tare da su Najeeb suma duk farinciki ne akan fuskokin su don ba K'aramin tashi hankulan su sukai ba, Abbas na dariya idon shi akan Najeeb da yake yasan da zancen wanccan cikin ya furta mashi "gaskiya Mom Zarah Sharp shooter ce ta gaske kaga fa har ta maida wani" kafin Najeeb d'in yace wani abu kaman daga sama suka ji ance "Shi kuma abokin naku jarababbe ko" gaba d'aya waro ido sukai suka sauke su akan Hajiya data yi Maganar kuma ko kallon su bata yi ba gwaggo dake gefenta sadda kai tay cike da jin kunya, gumtse dariya su Abbas d'in sukai ba wanda yace wani abu, Hajiya ce tace ma likitan zasu iya shiga su ganta da sauri yay mata alama da hannu ya furta "Yes you can" nufar d'akin sukai gaba d'aya harda Mom da Dad da gwaggo dasu Fauzy, su Haisam d'in suka tsaya jiran su gama shiga Najeeb da Na'eem suka matso wurin shi suna taya shi murna, Abbas na zuwa ya kamo hannun shi guda yay mashi side hug yace "Mom Zarah ta biya mu bashi da wuri kuma da alama dai a G.r.a d'in aka sake samo mana" washe baki Haisam d'in yay wanda shi rabon da yayi irin dariyar ma ya manta, tabbas a yadda aka fad'i lokacin shi da alama a G.r.a d'in ta same shi nan ya gane k'ilan harda shi yasa ta jin jiri da suka sauka Abuja Allah yasa ma bata samu wata matsala ba, daga baya suka shiga cikin d'akin, duk a tsattsaye suka iske su an zagaye gadon da take kwance har lokacin head dinta na a saman kanta fuskar ta sanye da Oxygen mask haka hannunta guda na sanye da drip, Addu'oin Allah ya bata lafiya aka shiga yi daga baya Doctor yace masu akwae buk'atar a d'aura ta kan Bed rest don akwai chance na zata iya miscarrying cikin in ta cika zirga zirga dole ta samu hutu sosae har ya zauna duk aka jinjina kai, Dad ne yace yakamata su tafi don dare yayi sosae sai wasu su tsaya, Aunty Laila ce tace a barta Hajiya tace a'a shi Mijin nata ya tsaya gwaggo dake murmushi tace a'a abar shi yaje ya huta ai an sha hidima Abbas yace kada shima ya fad'i duk aka sa dariya, shi da za'a barshin ma daya fi son hakan don zai so ace yana a kusa da ita ta farka, sallama Dad yayi masu ya juya Mom ma haka Nameer yayi ma su Mino magana suma suka tafi Fauzy sai faman sakin murmushi take ji take inama tana nan Fatun zata farka, kallon gwaggo Hajiya tayi tace suje ko tana d'an murmushi tace ba komai Laila taje don itama tasha hidima da yawa ita ta zauna, murmushi Hajiya tayi tace kawai dai K'aunar ta motsa bata son barin autar tata, kunya ce ta kama gwaggo tay yar dariya Hajiya tace ma Laila d'in suje kawai, har zasu juya Hajiya ta dakata tana kallon gwaggo tace bari suje sai a kawo mata abun shimfid'a da na lullu6a an taho hankali ba kwance ba, da sauri tace a'a tunda ga Hijab d'inta kuma doguwa ce lafiya lau zata yi mata ba sai an kawo komai ba abari sai zuwa gobe tunda ma dare yayi sosae tace to Shikenan suka juya suka tafi,

Bayan fitowar su ganin Laila yasa Mom tambayar ya akai ta taho Hajiya ta fad'i masu yadda sukai da gwaggon Dad yace amman dai Laila din yakamata ta kwana Hajiyar tace mashi su je kawae ko gwaggon ta koma gidan ba bacci zata iya yi ba yar lelen ta na kwance a gadon Asibiti, yar dariya Dad yay yace ai ba ita kad'ai ce yau bazata iya yin baccin ba tana da d'an uwa yay Maganar idon shi akan Haisam duk akayi dariya, sallama su Najeeb da Na'eem sukai masu don wucewa zasu yi duk akayi masu godiya da Addu'ar Allah ya bar zumunci sukai ma Haisam Allah ya bata lafiya shima yayi masu godiya bayan sun shige Motocin su Senator yace ma Haisam suje shida Abbas su samo masu Abinci don tana iya tashi da yunwa yace Ok, a tare duk suka shiga cikin Motoci suka tafi.

Lokacin da suka isa gidan tuni wanda suke cikin gidan sunyi nisa a baccin su, a gaban Entry Hall duk suka parker Motocin aka firfito, bayan sun shiga main parlor anan sukai ma juna sai da Safe Senator ya nufi part d'in shi haka ma Mom da Hajiya da Laila, Fauzy tare da Mino suka nufi hanyar baya har sun d'an yi nisa Nameer dake tsaye yana jiran su Mom d'in shi su shige ya kira sunan ta, juyowa tay yayi mata alamar ta zo ta juyo ta nufo shi, daga gaban shi ta tsaya suka sakar ma juna murmushi yace "Hankali ya kwanta ko Adda d'inki bata mutu ba" dariya tayi tasa hannu ta rufe fuska kafin ta cire, wani irin kallon love yake mata sai murmushi take a hankali ya furta "in muka yi aure I don't want you to get pregnant da wuri sai mun gama shan love sosae tukun" da sauri ta kai hannu ta rufe fuskarta ta juyar da fuskar wata irin kunya ce ta kama ta, ce mata yay miye abun wani kunya tunda auren zasu yi kuma ma bai son a d'auki time don ya yanke zai sanar da Hajiya sai ayi magana da parents d'in ta kafin su tafi, jin haka yasa ta juyo a sanyaye ta kalle shi, ya lura da canjin fuskar tata hakan yasa yace koda wani abu ba sun gama magana ba kuma ta amince zata aure shi, da d'an yanayin damuwa tace mashi eh kawai tana tsoron kar a k'i amince mashi ya aure ta, wani kalar murmushi yay yace "to akan mi za'a k'i amince man tunda ni nace ina so kuma in hakane shima Big bro ai da an k'i amince mashi" shiru yay ya d'age gira ya sake cewa "We are meant for each other shiyasa muna had'uwa muka fad'a son Junan mu so Don't Worry babe you will soon be Mrs Nameer Ali Zakee" k'ayataccen murmushi Mino tayi tace "Promise me bazaka dawo ka canza ra'ayi ba" wani kalan lumshe mata ido yay ya furta "I promise u My yar fillo" dariya Mino tayi shima yar dariya yay yace mata yana bala'en son yaji tana magana shiru tay tana ta murmushi bashi kad'ai ba ko a school haka ake cewa ba kamar in tana yin karatu, d'an juyawa tay ta hango Fauzy tsaye tana jiranta tace mashi bari taje ana jiranta, lumshe ido yay yace Ok amman tayi mashi abunda zai ta tunawa yay bacci mai dad'i, had'e lips d'inta tay tana murmushi a hankali tace "like what" rolling eyes d'in shi yay k'asa k'asa yace "blow me a kiss" sai da ta waiga taga Fauzy bata kallon su sannan ta d'aga hannu ta hura mashi kiss d'in ya bud'e hannu kafin ya rungume su ya wani lumshe ido dariya Mino tay ta juya da gudu ta bar wurin ya bita da kallo yana dariya, yana d'aya daga abunda ke k'ara burge shi da ita ta cika kunya, daina gudun tay data kusa zuwa wurin Fauzy, bayan taje inda take tsaye hak'uri ta bata tace ta sa tana ta jira Fauzyn ta d'an yi murmushi idonta a kanta tace "tsuntsayen love na lura dai ba k'aramar soyayya kuke sha ba da zafi zafi" rufe fuska Mino tay tana dariya suka tafi, bayan sun fito bayan sun tunkari part d'in Fauzy na murmushi tace inama su Aunty Mareeya basu yi bacci ba su ji abun farinciki Mino tace wllh itama tayi farinciki Fauzy tace sai fatan Allah ya inganta ya raba su lafiya wayaga su Zarah an haihu tayi Maganar had'i da sa dariya Mino ma yar dariyar take Lokacin suka iso part d'in suka shige.

Bayan tafiyar su Hajiya wurin gadon da Fatuu take kwance gwaggo taje ta tsaya tana kallonta Fuskar ta d'auke da Murmushi, har bata san ina zata kai farinciki ba rayuwarta ta kasance fin yadda take mata mafarki, sai murmushi take tana haka fuskar Mahaifiyar Fatun ta rink'a dawo mata, girgiza kai ta shiga yi a ranta ta furta Allah kenan ya d'auke wata ya bata wata, a fili ta shiga yi ma mahaifiyar Fatuu Addu'a itama ta rok'a mata lafiya da kuma inganta abunda take d'auke da shi, juyawa tayi ta nufi kopar dake cikin d'akin wanda tasan toilet ne, Alwala ta dauro ta dawo cikin d'akin tunanin abunda zata shimfid'a tayi sallar tayi k'arshe ta yanke ta shimfid'a kallabinta kawai, bayan ta gama sallar Nafilar sosae tayi ma Fatuu Addu'a bayan ta shafa zama tayi taci gaba da tasbihi, tana haka aka k'wank'wasa kopar ta gyara zamanta tace a shigo, Abbas ne ya shigo da sallama hannuwan shi ruk'e da katan d'in ruwa da lemu bayan shi Haisam ne ruk'e da k'atuwar leda, sannu da zuwa gwaggo tayi masu suka amsa acan gaban gefen gadon suka aje kayan kafin suka juya suna gaishe da gwaggon da fara'a ta amsa tayi masu sannu, mik'ewa tayi ta d'auki kallabin tana ruk'e da shi ta nufi hanyar k'opa ta fita, tsaye sukai suna kallon fuskar Fatun gaba d'ayan su fuskokin su d'auke da Murmushi, wata irin sabuwar k'aunarta Haisam ke ji na ratsa zuciyar shi,

"Allah kenan gwanin hikima masanin sirrin 6oye, wato a duk lokacin da na kalli Mom Zarah sai na tuno farkon gani na da ita a kopar gidan Hajiya ranar an aiketa ta d'ebo ruwa" Abbas ne yay Maganar idon shi akan Fatuu, Murmushi ne akan fuskar Haisam don bai mance da ranar ba, Abbas yaci gaba "lokacin har ta tambaye ka bak'o kayi na bata amsa da ba bak'o bane d'an uwan ka ne nace mata Mom d'in mu d'aya aikuwa ta buga k'afa tace ita bata yarda ba yo ya zata ga wake da shinkafa kuma in ce gidan mu d'aya, duk na tuna Maganar nan sai nayi dariya, lokacin dana fad'i mata inada mata da yaro ne tayi man magana k'asa k'asa wai kai to ya kai bakai auren ba, ina niyyar bata amsa ka d'ago kayi mata magana gashi tana tsoron ka hakan yasa ta tafi, k'ilan dana fad'i mata da sa rana akan ka da bata kamu da son ka ba" murmushi Haisam kawai yake yana tuna komai a lokacin,

"Mom Zarah an yi kuruciya mai saka nishad'i ina rok'on Allah ya baku D'iya mai irin halinta sai kuyi ta tunawa da tata kuruciyar" yar dariya Haisam d'in yayi, Abbas ne yace mashi suje ko gwaggo ta komo ciki yace Ok ya sake cewa gashi ma ya gan tana salla asaman kallabi yakamata ace akwae prayer mat Haisam d'in yace zai zo da wuri sai ya taho dashi, matsawa yay wurin gadon ya sunkuya ya manna ma Fatuu kiss a saman goshinta Abbas nata sakin murmushi, gwaggo na zaune ta d'age kanta suka fito, sauke kan tayi ganin su yasa ta mik'e sukai mata saida safe ta koma ciki.

Misalin k'arfe biyu da yan mintuna Fatuu ta fara motsi, a hankali ta fara bud'e idanunta har ta ware su gaba d'aya, k'ura ma saman d'akin ido tay tana kikkafta idanu, hannu ta d'ago ta ta6a mask d'in hancin ta nan take ta gane inda take, cire mask d'in tayi ta juya kanta idanunta suka sauka akan gwaggo dake kishingid'e akan kujera idanunta a rufe, bin ta da kallo Fatuu tay fuskarta da d'an murmushi, motsi gwaggon ta fara yi dama tana cikin yin tasbih baccin ya kwashe ta, kokarin gyara kwanciya ta fara cikin disasshiyar murya Fatuu ta ambaci sunanta, bud'e ido gwaggon tayi suka had'a ido, da sauri ta tashi zaune kafin ta mik'e ta nufi gadon, zama tay bakin gadon suna kallon juna da murmushi tace mata ta tashi ta d'aga mata kai, sannu tayi mata nan ma kai ta d'aga mata suka d'an yi shiru,

"Gwaggo miya same ni ne har aka kawo ni Asibiti?" Fatuu ta fad'a tana ta kallonta, tana murmushi tace mata ta fad'i ne a wurin hidimar da akayi shine aka kawo ta, shiru Fatuu tay lokacin komai ya shiga dawo mata na lokacin data fad'i,
"To mi akace yake damuna?" ta sake tambaya gwaggo dake ta murmushi tay d'an shiru idonta akanta can tace mata gajiya ce tayi mata yawa anata zirga zirgar hidima, shiru Fatun tay bata kawo komai a ranta ba don tasan hakan na faruwa, mik'ewa gwaggon tayi tace bari ta fad'i ma nurse ta tashi koda abunda za'a mata ta d'aga mata kai, bayan fitar gwaggo maida idonta tay tana Kallon sama ta shiga tunano komai daya faru a wurin dinner, tuno da lokacin da Haisam ya bi Wak'a yayi mata tay nan take ta fad'ad'a murmushi sosae taji dad'in hakan da yayi mata don ya nuna zai iya yin komai don son da yake mata, gwaggo ce ta dawo tare da nurse suka nufo gadon, sannu nurse d'in tayi mata tana murmushi Fatun ta d'aga mata kai, tambayar ta tayi ba abunda ke mata ciwo nan ma ta d'aga mata kai alamar eh, cire mata oxygen mask d'in tayi da drip d'in da aka saka mata bayan ta gama yi mata abunda zata yi mata ta k'ara mata sannu sannan ta tafi, bayan fitar ta Fatun ta fara k'ok'arin tashi zaune cike da kulawa gwaggo ke mata sannu, zuru k'afafunta tay gwaggo ta tambayi ina zata tace fitsari take ji ta mik'e ta taimaka mata, nad'e mata rigar tayi ta baya kafin ta kamata Fatun na murmushi tace mata zata iya, cewa tay bari dai ta taimaka mata, a bakin toilet d'in ta saketa ta bud'e mata kopar Fatun ta shiga gwaggo na fad'in tabi a hankali don Allah ta d'aga mata kai kafin ta maido kopar ta rufe, cikin d'akin gwaggo ta koma ta gyara mata gadon bayan ta gama ta nufi inda kayan da su Haisam suka kawo suke ta bud'e ledar, fiddo robobin take aways d'in da ke ciki tayi, bayan Fatuu ta fito tace mata tazo to ta ci Abinci ta d'aga mata kai don kuwa yunwa take ji, a saman kujera ta zauna gwaggo ta bud'e robobi biyu fried rice ce da naman kaza sai guda biyu kuma na sakwara ne gwanin sha'awa a ido da gani ta daku sosae, da murmushi ta tambayi to mi zata fara da shi ta nuna mata sakwara gwaggon tace dama tayi tunanin ita zata ce Fatun tay murmushi, bayan ta fara cin Abincin gwaggo ta mik'e tana fad'in bari a cire wannan d'aurin ko ta sha iska, bayan ta cire head d'in gado ta nufa ta d'aukko net d'in data yafa tazo ta d'aura mata akan Fatun nata murmushin jin dad'in yadda gwaggon ke ta bata kulawa, bayan ta zauna a gefen ta Fatun ta kalleta tace itama taci Abincin mana tace mata taci dai, tura baki Fatun tayi a shagwabe tace "Don Allah ki ci, in baki ci ba zan aje nima in daina ci" dariya gwaggo tay ta d'an girgiza kai tace mata wai sai yaushe ne zata girma ta daina shagwaba tafa girma yanzu, tana murmushi tace mata ba rana kuwa, gwaggo da har lokacin dariya take tace lallai kam za'a rinka abun kunya in ta haihu uwa na shagwa6a d'a na shagwa6a Fatuu dake dariya tace kyau kenan ai, daga baya gwaggon ta fara ci, sosae Fatuu taci Abincin don saida ta cinye sakwarar tass gwaggo tace ta k'ara ta d'ayar robar dama Saboda ita yasa bata ta6a ba ita ta d'auki shinkafa tana ci, ce mata tay bari taci shinkafar itama, sai gashi itama ta cinyeta ganin gwaggo na kallonta tana murmushi yasa tace "Gwaggo ko dai hada ciwon cin Abinci nike yi" yar dariya tay tace waya sani, mik'a mata robar sakwara d'in tay tace ta k'ara da sauri ta girgiza mata kai tace cikinta fashewa zai yi in ta k'ara, leda mai kyallin data gani a ciki ta fiddo ta fara warwarewa tana fad'in bari taga minene a ciki, bayan ta bud'e tsire ta gani yasha kayan had'i su tumatir da koran tattasai da albasa tun kafin ta fara ci ta hau had'iye miyau kallon gwaggo tayi tace wai ta ci tana dariya tace to dama ai don aci aka kawo ko, sosae yayi mata dad'i tace ma gwaggo su ci tace taci ta rage mata in ma duka zata cinye ta cinye da sauri tace a'a zata rage mata, sai ga wadda tace cikinta zai fashe sai faman cin tsire take tana zuba har da tambayar yadda aka kawo ta Asibiti gwaggon ta shiga bata labari don dad'i take ji ganin ta haka saidai bata fad'i mata ainihin abunda ya ja komai ba, tambayar gwaggon tay ina wayar ta tace mata ta barota gida bata ji dad'in hakan ba don tana son jin muryar mijin ta.

Bayan su Haisam sun koma, wanka ya fara yi ya zura jallabiya Abbas ma ya shiga wankan, sallar Nafila yay ya kara godiya ga Allah da ni'imomin da yay mashi yayi ma Fatuu Addu'ar samun ingantacciyar lafiya harda Fanan ma yayi ma Addu'ar Allah ya k'ara bata lafiya, sosae yayi Addu'oi lokacin daya gama tuni Abbas ya kwanta Sameer yau ba anan zai kwana ba dama shi Abbas ranar da suka zo ne kawai ya kwana a wurin Salim yake kwana, bayan ya gama zaune yay yana ta tunanin ko zuwa yanzu Fatuu ta farka, sosae yake jin kewarta yana son jin muryar ta amman yasan ba waya a hannun ta daga baya ya mik'e yaje ya kwanta fuskar shi cike da annuri, ya d'auki lokaci idanun shi lumshe yana tunanin baby d'in shi a haka bacci yay awon gaba da shi..........

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM 084*

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

............Washe gari bayan Haisam ya dawo daga sallar Asuba a main parlor ya tsaya ya kira Jidderh a waya, lokacin tana akan abun salla kiran ya shigo, mik'ewa tay ta nufi bakin gado ta zauna sannan ta d'aukko wayar, picking tay tun kafin tace wani abu taji yace ta same shi a parlor ta furta Ok, mik'ewa tay dama jikinta tana sanye da hijab ta nufi hanyar fita, yana zauna akan kujera one seater hannun shi ruk'e da waya ta iso wurin a kujerar kusa dashi ta zauna ya d'ago ya kalleta da fara'a ta gaishe da shi bayan ya amsa ta sake cewa "ya kwanan farin ciki" murmushi yayi ya amsa da Alhamdulillah, Addu'ar Allah ya bata lpy tayi bayan ya amsa yace mata so yake ta shiga Kitchen ta had'a mashi breakfast ba mai taking time sosae ba, tambayar shi tayi Asibitin zai kai ya d'aga mata kai, cike da zumud'i ta mik'e tana fad'in to yanzun nan zata had'a. Fauzy na gama sallar Asuba ta nufi d'akin su Aunty Mareeya lokacin data shiga a zaune kan abun salla ta iske ta da Saude Feenah na kwance kan gado don bata salla Abdul kuma dama tunda suka zo yana wurin su twins, da fara'a ta k'arasa cikin d'akin ta zauna daga gaban Aunty Mareeya, gaishe da Saude tay ta amsa tana murmushi ta maida idonta kan Aunty Mareeya dake bin ta da kallo, ganin tana ta faman zabga murmushi yasa tace ya zata zo tunda safe ta tasa su a gaba tana faman yi masu murmushi kamar wata zautatta, yar dariya Fauzy tay kafin tace Albishirinta da sauri tace goro harda su gyara zama shiru Fauzy tay Aunty Mareeyar duk ta k'agara ta ji miye har sai da ta kai hannu ta bugi shoulder d'inta tace dalla miye wai, fad'i masu abunda ya faru jiya ta shiga yi tana rufe baki Aunty Mareeya ta buga wata uwar shewa ta furta "Da kyau yar gidana Zarah, kwalliya ta biya kudin sabulu wllh wannan iya biyan bashi haka, kai Alhamdulillah Wllh naji dad'i nayi farincikin jin Maganar nan" Saude ma Alhamdulillah ta shiga fad'i, shewar da Aunty Mareeya tayi ce ta tashi Feenah ta bud'e ido, jin abubuwan da take fad'i yasa ta d'ago kai tana tambayar abunda ke faruwa cike da Farinciki Aunty Mareeya ta hau bata labari, jinjina kai Feenah ta hau yi fuskarta da faffad'an murmushi tace kai ma sha Allah abu yayi dad'i Allah ya bata lafiya ya inganta, amsawa sukai da Amin Aunty Mareeya tace ana ta shan Dinner d'in biki ashe Amarya da juna biyun ta mak'ale,
labarin yadda likita ya kasa fad'a Fauzy ta shiga basu sukai ta dariya suna fad'in ai dole ya kasa fad'a don wannan ba K'aramin Al'amari bane.

Bayan su Laila sun gama salla take ma Fanan Albishir don jiya ta riga tahowa kuma lokacin data dawo tayi bacci, waro ido Fanan tay ta kai hannu ta rufe bakinta alamar mamaki Laila nata Murmushi, cire hannun tayi cike da farinciki tace kenan duk abubuwan nan da ake Zarah is pregnant Laila tace wllh ai Allah ma ya taimaka da ba abunda ya same shi, mik'ewa Fanan tay da sauri ta nufi bakin gado ta kai hannu kan bedside ta d'auki wayarta, Haisam ta kira lokacin ya koma part d'in shi don ya shirya, yana tsaye a gaban dressing mirror kiran ya shigo ya juya ya kallo wayar dake saman bedside kafin ya nufeta, yana ganin mai kiran yay murmushi ya kai hannu yay picking, daga muryarta zaka fahimci tana cikin farinciki tace mashi ashe jiya abunda ya faru kenan bayan ta baro wurin yana ta murmushi yace mata eh, ce mashi tay shine ko ya kirata ya sanar da ita abun farincikin daya same su tama yi fushi dashi, yanayin yadda tay Maganar har saida yayi yar dariya, hak'uri ya bata yace tayi bacci ne yana son ta huta sosae tace to miyasa yanzu da aka tashi bai sanar mata ba ai kamata yay ace shine mutum na farko daya fara sanar mata, hak'uri ya k'ara bata yace mata yana niyyar yazo ne da kan shi sai yay mata Albishir yanzu haka yana gaban mirror yana mata Kwalliyar da zai zo yi mata Albishir d'in, yana jiyo sautin dariyar ta dama ya fad'i ne don ya faranta mata, ce mata yay gashi nan zuwa yi mata Albishir d'in a d'okan ce tace she's waiting for him,

Bayan Jidderh ta gama komai ta had'a mashi a cikin basket part d'in taje ta sanar mashi ta gama yay mata godiya yace ta aje mashi a dining area tace to, har zata juya ya tsaidata, ce mata yay ta d'aukko ma Fatuu kayan da zata canza ta sa towel da brush d'inta sai ta aje mashi a wurin basket d'in tace to kafin ta tafi, bada jimawa ba ya fito yana sanye da k'ananun kaya bak'in jeans da dark blue t-shirt sumar nan ta sha gyara sai baza k'amshi yake, part d'in Laila ya wuce lokacin daya shiga ba kowa cikin parlon hakan yasa ya wuce Bedroom, knocking k'opar yay aka bashi izinin shigowa ya tura ya shiga da yar sallama, Duk suna kwance akan gado Laila tuni ta koma bacci sai Fanan ce idonta biyu ta kasa komawa baccin sai tunane tunane take, sosae taji farincikin samun cikin da Fatuu tay saidai ta wani bangaren zuciyarta ce ta k'ara sarewa ta shiga tunanin anya kuwa tana da rabon haihuwa a duniya ganin tana ta shan Magani kuma ana samun cigaba amman har yanzu ko 6ari bata yi ba tasan ma ko zata iya conceiving, a hankali take kai hannu tana share kwallan dake gangaro mata tana haka taji anyi knocking saida ta goge Fuskarta tass sannan ta bada izinin a shigo, tana ganin shi da sauri ta saukko daga gadon tana sanye da rigar bacci iya gwuiwa kanta ta saka hula gashin ta ya zubo ta gefe da gefe, nufo shi tay da sauri tun kafin ta k'araso ya bud'e mata hannuwan shi tana zuwa ta fad'a jikin shi ya maida hannuwan ya rungumeta sosae ta shiga fad'in she's happy for them bada jimawa ba zasu zama iyaye, murmushin jin dad'i ya shiga saki ya d'aura ha6ar shi a saman kanta tare da lumshe ido, daga lokacin data amince mashi ya cigaba da zama da Zarah ya gane irin son da yake mata, a yadda yake ji he can't live without her, jin tana k'ok'arin d'ago da fuskar ta yasa shi janye ha6ar tashi, d'agowa tay ta kalle shi suka shiga sakar ma juna k'ayataccen murmushi daka kalli fuskokin su zaka fahimci suna cikin farin ciki don cike suke da annuri, suna haka calmly taji ya furta mata "Thank you Sweetheart" d'an bud'a mashi ido tay tace akan me ya lumshe ido yace "For Everything" fad'awa tay jikin shi ta kwantar da kanta a chest d'in shi, yaci gaba da fad'in "har bansan ta yadda zan rink'a gode maki ba, nagode maki da kasance man mafi jin dad'in duniyar nan" wurin kunnanta ya kai bakin shi ya rad'a mata "al'mar'atussaliha" yana jin yadda ta k'ara shige mashi yana ta murmushi,

d'ago kai tay ta kalle shi tace "komai daga wurin ka na koya babe, sadaukarwa halin ka ne, baka da buri sai na kaga kasa mutum farinciki hakan ne yasa kai ma kake kasancewa acikin farinciki koda yaushe, Babe duk yadda na kasance maka kai kaja hakan you're a selfless and just person, da maza zasu yi koyi da halin ka da sun zauna lafiya da matan su koda sunfi d'aya don hakan zai rink'a rage masu radadin kishi, amman da yawa su suke jefa matan su a mawuyacin hali k'arshe suzo suna kauce hanya wanda hakan bashi ne way out ba sai ma mutum ya halaka, Idan ba kayi cuta ba bazaka ga cuta ba all one needs to do shine hak'uri tunda Allah da kan shi yace yana tare da mai shi in mutum yayi sai yaci riba,ina rok'on Allah yasa in ci ribar hak'uri though nama fara cin ribar ga baby nan zamu samu" ta k'arasa tana murmushi, still yay yana kallonta wani irin tausayin ta ne ke ratsa shi, maida kanta yayi jikin shi yace in sha Allah zata samu lafiya itama ta Haifa mashi yara masu irin halinta, tana murmushi tace Allah ya amince amman in ya kaddaro mata bazata haihun ba ba komai tasan daga cikin hikimar sa ne ya kawo Zarah ta Haifa masu, murmushi kawai yake wani lokacin sai yay ta ganin kaman ba ita ba don da kuruciyarta bata da hak'uri ga kukan banza, sigh yay ya d'agota yace bari yaje, tambayar shi tay inda zashi ya fad'i mata da sauri tace to bari ta shirya sai su tafi tare, ba tare da ya sake ta ba gently yace mata yana son yaje da wuri ne Saboda grandma d'inta ta dawo gida jiya ta kwana ba shiri ko blanket babu yasan bata yi bacci cikin dad'i ba ta bari ta shirya a nutse sai suzo da Laila in ma ita bazata zo ba in ta shirya tay mashi magana zaisa a kawo mata makullin Mota sai ya bata address na Hospital d'in, kai ta jinjina mashi ya d'an sunkuyo yay pecking goshinta had'i da furta "I love u" farfar tay da ido ta furta mashi tana son shi da kowane bugu na zuciyar ta, yar dariya yay ya saketa tace in yaje yay kissing baby d'in su dariya Maganar ta bashi yace mata har ya zama baby kenan tace eh ai zai zama ne in sha Allah, bayan ya fito dining area ya nufa ya d'auki basket d'in da yar jakar kayan sannan ya tafi.

Bakin gado ta koma cike da zumud'i ta d'auki wayarta ta fara k'ok'arin kiran Mom d'inta, saida kiran ya kusa katsewa sannan tayi picking, gaishe da ita Fanan tayi muryarta ciki ciki ta amsa, cike da Farinciki tace mata dama ta kira tayi mata Albishir Hajiya Maryam d'in tace mata miya faru ne, cikin washe baki ta hau bata labarin cikin da Zarah ta samu tana jiyo sautin d'an tsoki data buga kafin a hasale tace to shine zata tashe ta a bacci kaman dole kuma tasan a lokacin bacci take, hak'uri ta bata tace farinciki ne yayi mata yawa shiyasa ta kira don ta taya su murna, bata ce mata komai ba tay shiru can ta tambayi ina Noor ta bata amsa da tana a wurin su twins ta furta Ok, jin zata katse kiran yasa da sauri tace bata taya ta murna ba a dak'ile tace Allah yasa Alkhairi daga haka ta katse kiran sam Fanan bata ji komai ba, kiran Farha ta shiga yi bayan tayi ringing tay picking, gaishe da Fanan d'in tayi ta amsa ta tambayi ko bacci take ta bata amsa da No tana yin Assignment ne, ce mata tay ta tayata murna bride d'in su is pregnant Farhar tay d'an jimm sai kuma tace ta taya ta murna Fanan d'in tay mata godiya, tambayar ta tay yaushe zata dawo tace msta cikin week d'in da za'a shiga tay mata sai ta dawo daga haka sukai sallama.

Gwaggo na zaune akan kujera tun bayan data gama salla ta koma saman ta tana tasbih jin k'asan sanyi yayi yawa Saboda Ac dake ta aiki tiles d'in duk ya d'auka, Fatuu na kwance saman gado ta koma bacci bayan tayi salla da hijab d'in gwaggo, bata dad'e zaunen ba akai knocking k'opar ta tashi zaune sosae tace a shigo, turo kopar akai Haisam ya shigo da sallama Nameer na biye da shi, da fara'a ta amsa sallamar suka shigo ciki, daga gefen gadon Nameer ya aje basket d'in da jakar kayan ya koma wurin gwaggo da ke cikin gaisawa da Haisam, da murmushi ya gaishe da ita ta amsa mashi tay mashi ya gajiyan hidima yace tabi jiki ai, shiru ta d'an biyo baya kafin cikin girmamawa Haisam yace mata ga Nameer nan zasu tafi tare, tana murmushi tace ai da basu wahalar da kansu sun fito da sassafen nan ba yace mata ba wani abu, k'ok'arin mik'ewa ta fara yi tana fad'i mashi game da farkawar Fatuu jiya da daddare yanata d'an murmushi, sallama suka yi Nameer ya juya ta bi bayan shi suka tafi, wurin gadon ya nufa ya tsaya yana kallon Fatuu dake ta bacci rabin jikinta lullube da farin bargo wani irin Fresh yaga tayi mashi, ya d'an d'auki lokaci a haka yanata kallonta da murmushi akan fuskar ta shi, matsawa yay ya zauna a bakin gadon ya kai hannu ya d'an janye bargon, hannunta guda ya kama yana ta kallonta can ya kai d'ayan hannun ya d'aura a saman cikinta wani irin farinciki yake ji, k'amshin turaren shi ne ya kai mata cikin baccin a hankali ta fara motsi da sauri ya janye hannun shi dake akan cikinta gudun kada ya tasheta kawai sai gani yay ta fara bud'e idanunta, tana gama bud'e su suka sauka cikin nashi yanata sakar mata k'ayataccen murmushi, k'ura mashi ido tay tamkar bata gane shi ba calmly ya furta ta tashi maimakon ta bashi amsa sai tace "Hubby kai ne?" yanayin yadda sautin Maganar ya fita muryar tata ta d'an dishe, lumshe mata ido yay nan take ta tabbatar da shi d'in ne da sauri ta juyar da kanta ta hango babu gwaggo cikin d'akin, maido kan tayi taci gaba da kallon shi a sanyaye ta gaishe shi, bai amsa ba sai ya matsa gaba ya sunkuyar da kanshi ya had'e fuskokin su, slowly ya furta "ni yakamata in gaida ki Baby, a huge thank you to u for the amazing gift" lumshe ido tay ba tare data ce komai ba, d'ago fuskar yay yana kallon ta a hankali ta bud'e idanun nata ta bi shi da kallon rashin fahimta, ganin irin kallon da yake mata ne yasa k'asa k'asa tace mashi wace kyautar ban mamaki ce ta bashi jin haka da yanayinta yasa ya fahimci grandma d'in ta bata sanar mata ba, maida Fuskar shi yay gefen tata ya rad'a mata "mun k'ara samun abunda muka rasa ne" waro ido Fatuu tay with mouth agape ya d'ago yana kallon ta da murmushi ya d'age mata gira aikuwa da sauri tasa duka hannuwanta ta rufe fuskar ta yay yar dariya, hannu ya kai ya janye hannuwan nata suka had'a ido ganin tana k'ok'arin juyar da fuskar yasa shi k'ara had'e fuskokin nasu taji yace "I don't even know how to thank you enough Baby" murmushin dad'i kawai take saki, d'agowa yay ganin tak'i sakin baki tay mashi magana sosae yace ko bata farinciki ne, da sauri ta girgiza mashi kai da hannu tay mashi nuni da bakinta nan take ya gane tana nufin bata wanke bakin ba kawai sai gani tay ya kai fuskar tashi ya had'e mouth d'in nasu wato tama gane bai k'yamar bakin nata, ya d'an d'auki lokaci kissing her deeply kafin ya d'ago da sauri ta juyar da fuskar ta tana dariya, hannu ya kai yana k'ok'arin d'aga ta zaune yace ta tashi taci Abinci, bayan sun Mik'e tace mashi zata je toilet yace Ok bari ya taimaka mata tana ta murmushi tace mashi zata iya nan ya sanar mata tana akan bed rest ne sai an bi a hankali ta jinjina mashi kai, zaunar da ita yay bakin gadon yace yana zuwa, jakar kayanta ya bud'e ya ciro towel da brush da toothpaste sannan ya dawo bayan ya mik'ar da ita yay mata d'aukar jarirai ya nufi hanyar toilet d'in suna ta sakar ma juna murmushi,

bayan sun je toilet d'in taimaka mata yayi tay wanka har brush shi yayi mata tana ta dariya don abu ne wanda da wayon ta ba'a ta6a mata ba, kaman yadda ya d'auketa ya kai ta ciki haka yay mata ya fito da ita a gefen gado ya zaunar da ita, saida yaje ya kullo kopar d'akin ya dawo, shirya ta ya shiga yi harda mai cikin kayan ya shafa mata sannan ya fiddo kayan bayan ta saka undies, doguwar riga ce tasa da hula bayan sun gama ya kama hannunta suka nufi inda doguwar Leather sofa take ya zaunar da ita, d'aukko basket d'in yayi ya dawo wurin daga gefen ta ya zauna, warmer d'in ciki ya bud'e chips ne a ciki, d'aukar plate d'in cikin basket d'in yayi ya mik'e, wurin gado ya nufa ya d'auki bottle water ya nufi window don ya d'auraye shi Fatuu nata kallon shi, idon shi a cikin nata ya dawo suna ma juna murmushi, zuba mata Chips d'in yayi mai yawa ya bud'e ledar slice bread ya deb'o, d'aura plate d'in yay a saman kujerar ya shiga had'a mata tea mai k'auri, d'agowa yay tana ta kallon shi ya kai cup d'in bakinta ta fara sha, ganin yana ta bata yasa tace shi fa yace mata yayi safiya sosae ba yanzu zai ci ba ita dai da baby d'in su suci su k'oshi, mak'e mashi kafad'a tay ta tura baki tak'i amsar wanda yake bata a shagwabe tace in dai bai ci ba to itama ta k'oshi, d'an bud'a ido yay yana murmushi, hannu ta kai ta d'auki fork d'in itama ta d'ebo ta kai bakin shi dole ya bud'e ta ba shi, haka suka cigaba da ci a tare cikin salon kauna da k'yar ta yarda in aka bata sau ukku sai ta bashi da cewa tay bata yarda ba ayi sau d'add'aya dai yace mata to ai ita ba ita kadae bace akwae baby tana dariya tace ai bai fara cin Abinci ba ko, nuna mata yay ai sai tana cin Abincin zai girma ko tace to ita a bata sau biyu shi sau d'ayan yace ai yayi kad'an, da k'yar dai ta yarda da ukkun sai kace wata yar yarinya haka yake ta bi da ita, sosae taci ta k'oshi don saida ta cinye duka duk da dashi aka ci amman ba wani sosae ya ci ba, bayan sun gama ya kamata suka nufi toilet aka wanko baki da hannu duk da ba da hannun ma aka ci ba, akan kujera suka zauna suna kallon Tv ta kwantar da kanta a shoulder d'in shi, shima dai kallon ana yi ana shan love ake yin shi daga baya ta fara gyangyad'i har baccin ya d'auketa sosae, d'aukar ta yay ya kaita gado bayan ya kwantar da ita ta d'an bud'e idanunta ta kalle shi suka sakar ma juna murmushi, lullube mata rabin jikinta yayi ya sunkuyar da kan shi yay pecking goshinta ta furta mashi thanks, zama yay a bakin gadon yana ruk'e da hannunta guda yana d'an matsa mata shi tana ta murmushi a haka har ta koma baccin, mik'ewa yay ya koma kan Kujerar yaci gaba da yin kallon, ya d'auki lokaci a haka Yana yi yana kallo Fatuu dake ta shan bacci, wuraren k'arfe goma da wasu mintuna akai knocking d'akin sai lokacin ma ya tuna da kopar a rufe take ya mik'e don yaje ya bud'e lokacin Fatun ta bud'e idanunta sakamakon buga kopar da akai, Fanan ce ta shigo tana sanye da jallabiya coffee brown tay rolling veil d'in Laila na biye da ita itama tana sanye da jallabiya Navy blue ta d'aura gyalen saman kai, matsa masu yay suka shigo duk suna murmushi, Fatuu na ganin su ta fara k'ok'arin tashi zaune Fanan ta nufo ta da sauri, zama tay a bakin gadon tana washe baki ta kamo hannunta guda, gaidata Fatun tayi bayan ta amsa tace "we're really happy about this pregnancy Zarah" murmushi kawai Fatun ke yi mata ita kam sai washe baki take, Laila ce ta k'araso bakin gadon tana kallon Fatun da murmushi, gaishe da ita Fatuu tay ta amsa tay mata ya jiki tace taji sauki, Fanan ce ta tambayeta taci Abinci ta d'aga mata kai, kallo Haisam daya koma kan kujera tay tace mashi ya dai tabbatar taci ta k'oshi ko yana murmushi ya lumshe mata ido tace Yauwa to don kar abar masu baby da yunwa gaba d'aya Laila da Fatuu sukai dariya, komawa wurin Haisam Laila tay ita kuma Fanan ta shiga yi ma Fatuu tambayoyi da suka shafi cikin daga baya kuma ta koma yin hirar Babyn da za'a Haifa masu duk su Haisam na jinta sai dariya take ba su har Laila na cewa da alama tafi kowa murna da cikin tace mata abunda take ta fatan su samu kenan. A nan Haisam ya barsu Ya dawo gida,

Wurin k'arfe sha biyu su Hajiya Zainab sun gama shirin tafiya, zasu biya Asibiti su gaishe da Fatuu daga can zasu wuce, bayan ta fito tare da Mom da su Aunty da wasu mutane Security detail d'inta na biye da ita, Jidderh na a part d'in da su Fauzy suke suna zaune a parlor harda su Aunty Mareeya suna firar Dinner d'in jiya da kuma tashin hankalin da suka shiga lokacin da suka ji Fatuu ta fad'i, Yasmeen ce ta shigo da gudu ta nufe su tana d'an haki idon ta akan Jidderh tace mata ga Momy d'in Nasarawa can zasu tafi, zumbur Jidderh ta Mik'e ta ce ma su Fauzy suzo suje duk suka mik'e harda su Aunty Mareeya tana fad'in bari suma suyi mata bankwana don mace ce mai mutunci wllh, suna akan hanyar zuwa Aunty Mareeya ke ce ma Feenah in ka ga Sameer sai kace ba itace ta haife shi ba ta 6angaren hali Feenah na murmushi tace shima k'ilan in aka zauna dashi aga Mutuncin shi Aunty Mareeya tace amman dai da gani ba sai an fad'a ba yana da girman kai ba kamar Mahaifiyar tashi ba, gaba d'aya an fito waje bakin Entry Hall inda Motocin su suke a fake, tun bayan da Fauzy ta fito take ta wurga ido wai ko zata ga Sameer amman bata gan shi ba sai dai K'annan shi, tunanin ko yana a cikin Mota tay tabi Motocin da kallo saidai bazata iya ganewa ko yana ciki ba, Sallama Her Excellency tay da kowa ta nufi Mota da sauri aka bud'e mata bayan duk sun shishshiga ta d'aga ma mutane hannu kafin aka rufe kopar, a jere Motocin suka tashi ana ta d'aga masu hannu suka tafi jiniya na tashi, juyawa sukai suka koma cikin gidan, hakanan Fauzy take jin ta wani iri sai ganin fuskar Sameer take, a ranta ta raya k'ilan Shikenan bazata k'ara ganin shi ba har saida taji jikinta yayi sanyi yin tunanin, can kuma wata zuciyar ta raya mata k'ilan kuma sai ko bikin Mino da Nameer in Allah ya k'addara zasu auri juna, sukuku da ita ta koma part d'in su, koda ta shiga d'akin su ta nufa ba kowa a ciki ta nufi gado ta kwanta ta shiga tunano abubuwan da suka faru a tsakanin su wani lokacin tay murmushi wani lokacin kuma ta yamutsa fuska can zuciyarta ta raya mata wai ko dai son shi take shiyasa take ta tunanin shi haka da sauri ta hau girgiza kai saima ta yunkura ta mik'e ta nufi Parlor.

Wuraren sallar Azahar aka fara zaryar zuwa Asibiti ganin Fatuu, Yadikko tsabar farin ciki kamar ta zuba ruwa a k'asa ta sha, har su Baffan Fatun da Ard'o sai da suka zo gaba d'aya Asibitin saida aka shaida an kwantar da dangin masu Mota don Motoci ne iri iri ke ta sintiri cikin Asibitin, da la'asar Mom da Hajiya da Aunty da gwaggo suka zo, bayan sun shiga d'akin sun duba Fatun Hajiya tace ma Aunty ta duba ta in dai ba wata matsala gwara a sallameta su koma gida don anata faman zaryar zuwa in suka koma sai taci gaba da yin bed rest d'in a gida tace to, tambayoyi tayi ma Fatun daga baya ta fita ta nufi Office d'in Doctor, bayan sun gaisa tay mashi bayanin suna so ai discharging Fatuu tunda ba wata matsala a tattare da ita, bai da yadda zai yi dole yayi masu yadda suke so don ya gane Auntyn likita ce. Bayan sallar Magrib aka sallame ta suka dawo gida, d'akin Mom aka kaita nan fa akai ta zuwa gaishe ta ita dai sai faman murmushi take bayan an tsagaita da shigowa Mom ta tambayeta abunda take son ci tana murmushi tace mata komai aka bata zata ci itama da murmushi akan fuskar ta tace in akwae wani abu da take jin tana so ta fad'i tace mata ba komae, mik'ewa tay ta fita bada jimawa ba sai gata ta dawo ruk'e da plate mai d'an girma Fruit ne aka yayyanko wanda suke da amfani ga mai ciki ta kai mata tace ta fara shan su tay mata godiya, ganin tana k'ok'arin saukkowa daga saman gadon yasa ta tambayi zatai wani abu ne tace eh hannu zata wanko cike da kulawa tace Ok amman tabi a hankali tace to, tsaye tay har saida ta shiga ta wanko hannun ta fito bayan ta koma ta zauna sannan ta tafi, bada jimawa sosae ba sai gata ta k'ara dawowa hannunta ruk'e da babban tray, a saman Carpet ta aje tace ma Fatun ta zo ta zauna nan yadda zata ji dad'i sai ta ci tace to, bayan ta zauna da kanta ta bud'e mata plates d'in da aka rufo da wasu, d'aya tuwon semovita ne mulmule ukku sai miyar Alaiyahu data ji yan ciki a cikin bowl sai d'ayan plate d'in mai d'an zurfi farfesun kaza ne sai zabga uban k'amshi yake a ido kawai sai ya burge mutum daga gefe lemu da ruwa ne harda cup, tana murmushi tace mata ta ci ta k'oshi ta d'aga mata kai ta juya ta nufi hanyar fita daga d'akin,

tun bata saki jiki ba har dai ta saki ta shiga kwasar Abincin wasa wasa sai gashi ta cinye mulmule biyu sannan ta koma kan farfesun, Ita kanta har mamakin kanta take yanzu lokacin da ba'a san da cikin ba kwata kwata bata cin Abinci sosae yadda ta saba take ci amman yanzu sosae cin Abincin ya k'aru, shima farfesun sosae ta ci shi don ba K'aramin dad'i yayi mata ba amman ta rage, bayan ta gama ta rufe komai ta d'auki tray d'in don ta fitar, a daidai bakin k'opa suka had'e da Haisam da dawowar shi kenan daga Masallaci, hannu ya kai ya amshi tray d'in yace mata wa yasa ta d'aukko ta langa6ar mashi da kai, ruk'e tray d'in yayi da hannu guda yasa d'ayan ya bubbud'e ganin bata cinye ba yasa shi kallon ta tana ganin haka ta tura mashi baki a shagwabe tace wllh ta k'oshi sosae ta ci, d'an d'aure fuska yay yace su koma ta ida cinyewa ta yamutsa fuska kamar zatai kuka tana fad'in Allah cikinta fashewa zai yi, suna Haka Mom ta sawo kai cikin d'akin har saida Fatuu ta ji kunya da sauri ta juyar da kai, tsayawa tay gefe da murmushi ta tambayi ya akai yace mata bata cinye ba, kallon Fatuu tay tace "Daughter ya akai baki cinye ba?" Juyowa tay a kunyace tace mata Allah ta k'oshi taci sosae, hannu Mom ta mik'a ta amshi tray d'in ta duba, jinjina kai tay tace ba laifi ta ci sosae ta juya ta fita da shi, had'a ido sukai tayi mashi wani kallo ya kai hannu ya jawo ta jikinshi ta saka dariya, ganin abun na neman yin yawa ta fara k'ok'arin k'wacewa tana fad'in kada Mom ta shigo don Allah, kawai sai gani tay ya d'auketa gaba d'aya ya nufi gado da ita gaban ta sai fad'uwa yake, a saman gadon ya d'aurata shi kuma ya zauna a baki yana murmushi yace hira yazo taya ta.

Bayan Nameer ya shigo gidan daga Masallaci direct d'akin Hajiya ya wuce lokacin daya shiga parlon su gwaggo na zaune bata dad'e da gama yin salla ba suka zauna suna kallo ita da wasu yan uwan su da suke a part d'in Hajiyar, tsayawa yayi suka gaisa kafin ya wuce Bedroom, da sallama ya shiga ya hangota zaune akan prayer mat ta jingina da gado, wurinta ya nufa yana zuwa shima ya zauna a k'asa kan Carpet kusa da ita tana ta kallon shi fuskar ta a sake, ganin yayi shiru yasa ta ce mashi ya akai, gaishe da ita yay ta amsa, jimm yay sai d'an murmushi yake yama rasa ta ina zai fara, sake tambayar shi tay wai lafiya yazo ya tasata a gaba sai wani murmushi yake kaman wani zautacce, ce mata yay dama zuwa gaishe da ita yay ta d'an harare shi ya d'age gira yace ko bata so, d'an ta6e baki tay tace to ta gode sai kuma mi, saida ya d'an sosa k'eyar shi sannan ya fara Magana da yar in ina yace mata dama ya samu wacce yake so ne a wurin bikin nan kuma har sun daidaita ma to shine yake son don Allah tay ma Dad magana sai ayi magana da parents d'in ta, zuru tay tana kallon shi har ya gama tay d'an murmushi tace wacece ya ke son, fad'i mata yay k'anwar bride d'in Ya Haisam da d'an alamun mamaki tace wacce k'anwar tata yace mata Mino, d'an wara ido tay tace "Kai yaushe har kasan Ameenatun da zaka ce kana son ta kuma kun daidaita?" Fad'i mata yay anan bayan sun zo, shiru tay ta d'an jinjina kai idonta akan carpet shi kuma yanata kallonta yana jiran ya ji mi zata ce, maido idon tay kan shi tace Yanzu in aka yi magana da iyayen nata aurenta zai yi da sauri ya d'aga mata kai, d'an shiru ta k'ara yi sai kuma tace "ni da nayi tunanin kai ma yar gida za'a yi kai da yar'uwar matar yayan taka Farha" wata yar zabura yay ya bita da wani kallo na baka tsammaci jin abu ba, tana murmushi tace mashi eh ba sai a k'ara yin yar gida ba a k'ara dankon zumunci, da sauri ya girgiza mata kai yace "ni gaskiya bazan iya auren ta ba yarinyar da bata girmama mutane ko gaishe ni fa bata iya yi in ma na samu tayi man kallon arziki, d'auka na take wani tsaranta taya zamu yi aure haka, kuma ma dai ai saida soyayya ake aure ko to ni gaskiya ban mata irin wannan son" ya k'arasa Maganar ya d'an 6ata fuska, kallo kawai Hajiya ta bi shi dashi sai k'ara 6ata rai yake, jimm tay can ta tambaye shi ita Minon ya tabbatar suna son juna ba sai anyi magana ba kuma azo kuma daga baya wani cikin su ya canza ra'ayi da sauri yace mata wllh duk suna son juna sosae sun ma yima juna alk'awarin kan haka, harara Hajiya ta wurga mashi ya sunnar da kai yana dariya, ajiyar zuciya ta sauke tace Shikenan zata yi ma Baban nashi magana tana rufe baki ya matsa ya rungumeta yana fad'in shiyasa yake son ta, ture shi ta fara yi tana fad'in ba wani dad'in bakin da zai yi mata ina wani so yake yana k'ok'arin yi mata kishiya, sakin ta yay yana dariya har zai mik'e sai kuma ya dakata yace mata don Allah koda Dad zai k'i tay convincing nashi wllh yarinyar bata da matsala in ya aureta ya dace mata, hannu tasa ta ruk'e ha6a alamar mamaki ya mik'e yana dariya ya nufi k'opa yana fad'in Allah yasa yaji Alkhairi, bayan ya fita Hajiya ta d'an girgiza kai.

Wuraren k'arfe goma da yan mintuna Senator ya dawo gidan yana sanye da babbar riga da yan ciki na brown shadda kan shi sanye da hula mahad'in kayan haka agogon shi da takalman shi da alama Haisam gadon yin to match yay, ta main parlor ya shigo bai bi ta k'opar da ke kai shi part d'in shi ba kamar yadda yake yi in ya dawo da daddare, hannuwan shi ruk'e da fararen ledoji nasu d'auke da tambari a jiki ya nufi part d'in Mom, Fatuu zaune a saman gado har tayi wanka ta saka doguwar rigar bacci kanta sanye da hula su twins da Abdul da Noor zagaye da ita gaba d'aya idanun su na akan tv d'in cikin d'akin suna kallon cartoon da akai ma Fatuu dole take kallo, da Sallama ya shigo duk suka kai idanun su kan shi aikuwa da sauri su twins suka sauka daga kan gadon suka nufe shi da gudu suna fad'in "Oyoyo Daddy" bud'a masu hannuwa yay suna zuwa a tare suka fad'a ya rungume su yana dariya, d'ago kai yay ya kalli su Abdul da suma suka saukko daga kan gadon daga d'an gaban su suka tsaya suna kallon su da murmushi, ce masu yay su bazasu yi welcoming d'in shi ba Noor ta ruga itama ya rungume ta ganin haka yasa Abdul ma yaje shima aka had'a dashi aka rungume, sakin su yay yana fad'in to su shiga ciki Mubeen da Mubeena suka kai hannu suna fad'in ya kawo su ruk'e ya sakar masu leda guda d'aya yace to su je su kai ma Yayar su ta saman gado, da gudu suka juya suna zuwa suka mik'a mata ta amsa tana murmushi, nufo ciki yay ya tsaya daga gaban gadon Fatuu ta gaishe da shi Fuska a sake ya amsa yay mata ya karfin jikin tace Alhamdulillah, tambayar ta yay taci Abinci ta ce mashi eh yace sosae tana murmushi ta k'ara cewa eh,

"To ga Fura nan sai ki k'ara" kai ta jinjina a hankali tace ta gode, su twins ne suka dawo gaban shi Mubeena ta kai hannu tana k'ok'arin amsar leda guda tana fad'in suma a basu fura d'in, janye ledojin yay ya 6oye su a bayan shi yana fad'in babu na su, wani kallo Mubeen yay mashi ya turo baki yace to wannan duk na waye yace mashi d'aya na Hajiyar shi ne d'aya kuma shi zai sha, a shagwabe Mubeena tace to ya basu nashi furan, wani kallo yay masu mai kaman harara yace to shifa, har suna had'a baki wurin fad'in sai yayi hak'uri, girgiza kai yay ya d'an tura baki irin yadda suke yace "ni bazan hak'uri ba gaskiya ai don in sha na siyo ko, wai yama akai baku yi bacci ba?" dariya yadda yayi ya basu Mubeena tace rabon zasu sha furan ne yasa basu yi bacci ba yace to kuwa bazasu sha ta ba,

k'ok'arin kamo ledar suka fara yi ta bayan shi yana kaucewa can ya d'age su sama yace in suka kama to zai basu, tsalle suka fara yi harda Noor da Abdul Fatuu sai dariya take sosae abunda suke ya saka ta nishad'i, ganin sun kasa kamowa don Dad d'in nasu ba gajere bane tur6une fuska su twins sukai suka hau yi mashi magiyar ya basu, suna haka Mom ta fito daga toilet tana sanye da bathrobe kanta ta nad'o towel, nufo su tay fuskarta da murmushi ta tsaya gefe, sannu da zuwa tay mashi ya amsa ta kalli su twins ta tambayi ya akai, kafin su bashi amsa Dad d'in yace fashi suke son yi mashi na furar shi kuma bada su ya siyo ba, yar dariya tayi tace a taimaka a basu tun da sun gani suka had'a baki suna rok'on shi ya basu, kwa6e fuska yay alamar zai yi kuka yana fad'in bazasu tausaya mashi ba su bar mashi furar shi, Noor da Abdul ne suka ce sun bar mashi ya sha su twins kuwa girgiza kai sukai suna bubbuga k'afa, mik'a masu leda guda yay suka saki k'arar murna Mom tace to suje Parlor su sha suka nufi hanyar fita daga d'akin suna fad'in "Thank you Daddy, We love you" yana dariya yace tunda sun raba shi da abun shi ba, wucewa Mom tay wurin mirror tana yar dariya ya kalli Fatuu ganin ta aje ledar yace ta sha yanzu Saboda ta bi jikinta cikin girmamawa tace to ta kai hannu ta fiddo robar furar ta fara bud'ewa, tambayar ta yay ko a kawo mata cup da sauri tace a'a zata sha a robar, jinjina kai yay sai kuma yace ta saki jiki duk abunda take so tayi magana sannan kada ta cika yin zirga zirga zuwa ta samu lpy sosae a hankali tace to, kai idon shi yay kan Mom dake yin shafa ta cire towel d'in kanta tana taje sumarta Tubarkallah gashin har k'ugunta gashi bak'i wuluk, maido idon shi yay kan Fatuu yayi mata sai da Safe ta amsa ya juya ya nufi hanyar fita idon ta akan shi tana murmushi.

Bayan ya fito part d'in Hajiya ya nufa don kai mata Furar ta, dama in dai tana Abuja duk dare sai ya siyo mata in yana nan in kuma bai garin sai ya sa a siyo mata, a parlor ya isketa ya gaisa da Mutanen ciki kafin suka gaisa da Hajiyar ya bata ledar, mik'ewa tay tace mashi tana son magana da shi suka nufi Bedroom, bayan sun shiga a bakin gado ta zauna shi kuma ya zauna akan carpet tana ya zauna a bakin gadon shima mana yace lafiya lou nan ma, zancen da Nameer yazo mata da shi tay mashi, farko d'an jimm yay kafin ya kalleta yace to ya take gani tunda tasan yarinyar, ce mashi tay gaskiya ita a saninta bata da wata matsala ya sake cewa to tana ganin lafiya lau a barshi ya auretan tana murmushi tace tunda yace yana so kawai ai mashi fatan Alkhairi, jinjina kai yay yace to Allah ya tabbatar da Alkhairi ta amsa da Amin, shiru suka d'an yi kafin tace mashi Kakar ita Fateema d'in ta fad'i mata gobe zasu tafi don haka sai ayi masu magana da wuri yace in sha Allah, yar hira suka d'an ta6a daga baya ya mik'e sukai sallama ya tafi. Bayan ya koma part d'in shi toilet ya nufa don yayi wanka, after some minutes ya fito jikin shi sanye da bathrobe ya hau shiryawa cikin kayan bacci riga da wando, bayan ya gama parlon shi ya fito ya zauna ya kai hannu kan table d'in dake a gefen kujerar ya d'aukko jarida ya fara dubawa, bai dad'e da zama ba Mom ta shigo itama ta shirya cikin kayan bacci masu santsi bak'ak'e da layi layin ratsin fari kanta ta yafo d'an k'aramin farin gyale sosae tay kyau farinta ya fito, nufo cikin parlon tay hannuwanta ruk'e da d'an babban tray d'auke da kayan abinci, matsar da c-table tay gaban shi sannan ta d'aura tray din, kallon shi tay suka sakar ma juna murmushi, serving nashi Abincin wanda irin tuwon data kai ma Fatuu ne ta shiga yi, bayan ta gama a kujerar gefen shi ta zauna suna d'an ta6a hira tana kallo, bayan ya gama ta d'auke kayan ta fitar da su,

Dawowa tay d'auke da had'addan flask milk anyi mashi adon golden kai kace da gold akai adon harda cups d'in shi tray d'in ma duk mahad'in shi ne a saman c-table ta d'aura, bud'e Flask d'in tayi ta tsiyaya mashi ruwan shayin da ya sha kayan k'amshi da Zuma dama duk dare wadda take da kwana sai ta had'o mashi shi yau ita ke da kwana don bak'in shi wasu sun tafi d'azun da rana Saboda gobe Monday akwae aiki wasu kuma ba anan zasu kwana ba Mutum biyu yan Daura da Suka rage suna a part d'in da aka sauke su Ard'o, fuskar ta da murmushi ta mik'a mashi dama tunda ta shigo idon shi na akanta, k'ayataccen murmushi ya sakar mata ya furta "Shukran laki Ya Uwargida sarautar mata" dariya tay ta koma kujerar dake gefen shin ta zauna ta kai idon ta kan Tv shi kuma yana ci gaba da kurbar shayin nashi, jefi jefi suke yin magana a haka har ya shanye ta tambayi a k'ara mashi ya d'an d'aga mata hannu "tukunna bari inason zamu yi magana ne" kai ta jinjina ta maido hankalin ta gaba d'aya kan shi, d'an gyaran murya yay a nutse ya fara mata Maganar da sukai da Hajiya ta Nameer, shiru tay tana saurarar shi har ya gama a hankali ta maida idonta ta koma kallon Carpet d'in k'asa yanayin fuskar ta ya d'an canza, idon Senator na kanta ganin yadda tay yasa shi tambayar ko da matsala, maido kallonta tay kan shi ta fara magana "Nameer d'iyar Yaya Othman na Qatar nike son ya Aura Jahad, har nayi mashi Maganar kwanaki kuma ya nuna ma ya amince yanzu kuma ya zai zo da wannan Maganar?" sigh Senator yay ya jinjina kai kafin a nutse ya shiga kwatanta mata k'ilan dama kawai don kar yayi jayayya da ita ne yasa ya nuna mata ya amince ko kuma da gaske ya amincen yanzu kuma ya ga wannan yaji ita yake so, to shi abunda yake gani zai fi kyau ai mashi yadda yake so tunda can ba'a riga an tsaida magana ba, nuna mata yay yaran zamani yanzu ba'a cewa za'ai masu dole a 6angaren aure sun auri wadda suke so ma wasu ya aka kare bare kuma wadda basa so, shiru kawai tay still da yanayin canzawar fuskar ta,

"Ina son ki kwantar da hankalin ki nasan a koda yaushe kina masu Addu'ar mafi Alkhairi a rayuwar su don haka ki d'auka wannan d'in itace tafi Alkhairin a gare shi tunda Addu'ar mu karbabba ce a gare su, abunda ake mawa dama shine a samu asali mai kyau da kuma kyan hali Hajiya duk ta tabbatar man da wannan game da ita yarinyar hakan ne ma yasa ai tun farko ta goya ma shi Babban yayan nasu baya, kuma kinga yanzu in akace a hana shi zai ga anyi mashi ba daidai ba tunda shi yayan nashi an amince mashi, ba abunda zamu yi ma Allah sai godiya akan komai na rayuwar mu, Allah ya Albarkace mu da yara shiryayyu duk da yadda zamani ya canza ya cika da ababen rud'u amman hakan bai sa sun kauce hanya ba sam ni'imar da Allah yay masu bata sasu shagala ba a koda yaushe k'ok'arin su suyi abunda zai k'ara mana mutunci da k'ima suke suna mana biyayya bakin gwargwado ni ina ganin duk da mu muka haife su muna da cikakken iko dasu yakamata mu rink'a nuna godiyar mu a gare su ta hanyar faranta masu kamar yadda suke faranta mana sa6anin iyaye da dama ya'yan su sune silar bakin cikin su, wasu suna fama da cututtuka duk silar yaran su kullum Addu'ar su Allah ya shirya masu zuriar su don jarabawar yara babban jarabawa ce Saboda duk yadda hannun ka zai ru6e baka yanke shi ka yadda koda kuwa ka yanken to kuwa ba hutawa kai ba, don haka ni ina ganin mu k'ara gode ma Allah da ni'imar da yayi mana sannan duk abunda ya kawo mana matuk'ar abun nan baida illa to mu kar6e shi hannu biyu muyi mashi godiya don shi yasan sirrin dake tattare da komai sau da yawa abunda muke k'i sai kiga Alkhairi ne a gare mu" yar ajiyar zuciya ta sauke yanayin fuskar ta ya canza dama ita bawai Minon ce bata mata ba kawai tana son k'ara had'a dankon zumunci ne amman koda Nameer d'in ya nuna bai so bazata matsa mashi ba don ita mace ce mai matuk'ar son iyalinta bata da burin daya wuce ta faranta ma ya'yan nata da mijinta, d'an murmushi tay idonta akan shi tace Shikenan Allah ya tabbatar da Alkhairi, faffad'an murmushi Senator yay ya furta "Ameen My Queen" wani kallon love ta sakar mashi ya wani lumshe ido ta saki dariya, shima dariyar yay can yace "ai tunda ma yaran ba k'arewa sukai ba in sha Allah za'a had'a Auren zumuncin, yanzu kinga ga Affan nan ya tasa nan da yan shekaru zaki ga shima ya isa Aure ga Mubeen nan shima, ko bama mazan ba ai kinga ga mata nan Yasmeen da Mubeena tunda shima Yaya Othman d'in yana da Maza sai kiga an had'a, koma ba'ai dasu ba akwae wad'anda za'a k'ara haifa ai" ya k'arasa Maganar yana sakin murmushi idon shi a kanta, wani kallo tay mashi tace waye zai k'ara haifo yara ya d'age gira yace ita mana tunda tasan Aunty ba haihuwa take ba,

"ni kam dai na gama, yara takwas fa ai nayi k'ok'ari kai ma ai nasan wasa kake" Mom da ta d'an ta6e baki tace, tsuke fuska yay ya k'ank'ance ido yace wai taga wasa a idon shi har saida tay yar dariya, ce mata yay yara takwas sun mashi kad'an in son samu ne ishirin yake so to amman tunda ita kad'ai ce zai hak'ura da guda 12 yanzu sauran ta hud'u in kuma Allah yasa an k'ara samun twins Shikenan zai iya hak'ura da goma, da yanayin mamaki tace "pls are you serious?" Kai ya jinjina mata yana mata wani kallo yace yana son yaga yara yan dugui dugui a gidan, yamutsa fuska tay tace in dai wannan ne ai ga Daughter nan zata Haifa in Nameer ma yayi auren shima zasu Haifa, wani kallo yay mata mai kaman harara yace to wannan nasu ne kuma a gidan zasu cigaba da zauna ne abunda kowa kama gaban shi zai yi shi nasu yake so wanda koda yaushe zai rink'a ganin su, sosae ta kwa6e fuska tace hakan bazai yuwu ba taya yara na haihuwa itama zata wani haihu katseta yay yace ai yanzu hakan fashion ne shi ake yayi kana haihuwa yayan ka nayi ai duk Aure gare su ko, yamutsa fuska ta shiga yi a shagwabe take fad'in ita gaskiya wannan abun kunya ne wllh sai dariya yake mata can ya d'aga mata hannu yace Ok Shikenan tunda bata so ai duk ba abun daga hankali bane zai samo wata yar chick ya auro sai tazo taci gaba da haihuwar ita ta huta kawai, ai tun kafin ya rufe baki ta d'auki pillow d'in kujera ta jefa mashi ya ca6e shi yana dariya ita kuwa sai k'una k'uni take tana Allah ya gama k'aro wata a cikin gidan ta dai yi hak'uri ya auro Aunty to Shikenan an gama, d'age mata gira yay yace "to zaki k'ara haihuwa ko kuwa in nemo....." Kafin ya k'arasa ta taso da sauri ta zauna saman jikin shi ta toshe mashi baki sai 6a66aka dariya yake ni kam dai na yak'e baki abun ya ban nishad'i ashe ashe dai ko an manyanta ana buga love, ni wllh ma Senator kazo ina da k'anne don Allah ka za6i d'aya in ma basu yi maka ba akwai yar bahillot itama a kasuwa take abun ai duk namu ne🤓

cire hannun tayi har lokacin sai yamutsa fuska take shi kuma sai dariya yake, ce mashi tay don Allah yaran su sun isa haka tun kan ta rufe baki ya hau girgiza mata kai yana mata wani kallo yace "indai irin yaran da kike Haifa man ne basu ishe ni ba ina buk'atar K'ari" Murmushin jin dad'i tay ba tace komai ba ya d'age gira yace za'a k'ara Haifa mashi ko, d'an rolling eyes d'in ta tay tace Shikenan amman saidai tun daga rainon cikin har zuwa haife shi ba'a K'asar nan zata yi ba da sauri yace in hakan yayi mata ai ba matsala bane duk inda take so sai akaita kuma zai bi ta, dariya tay ta girgiza kai, tambayar shi tay ta k'ara mashi shayin ya d'aga mata kai, tashi tay daga saman jikin shi ta k'ara mashi, bayan ya shanye ta k'ara tambayar a k'ara yace a'a ya isa, mik'ewa tay zata dauke flask din yana kallon ta yace ta bari sai da Safe mana ta fitar da shi, mik'ewa tay tana d'auke da tray d'in tace mashi tana son taje ta tambayi Daughter ko akwae abunda take so kafin tay bacci ya jinjina kai ta juya, bin ta yay da kallo tana tunkarar hanyar fitan a kullum gani yake ta na k'ara mashi yarinta a maimakon manyanta, in yace ga wani nakasu nata daya sa shi k'ara Aure to yayi k'arya kawai dai yasan duk abunda Allah ya k'addaro ma bawan shi to tabbas sai ya faru da shi amman yana matuk'ar k'aunar matar shi a yanzu kam sam baida ma ra'ayin k'ara aure, su yar Munah da bahillot sai a fidda rai🤧

Misalin k'arfe goma sha d'aya da wasu mintuna su Fauzy na zaune a parlor suna kallo ita da Mino da Zainab Haulat dai tunda ta tafi kwantar da babynta bata dawo ba da alama tayi bacci, harda su Aunty Mareeya da su Yadikko ake ta kallon Film d'in, Fauzy na zaune jikinta sanye da doguwar rigar atamfa ta soke d'aurin kallabi ta yadda gashinta ya fito ta k'asa, wayarta ce dake a gefenta ta fara ringing ta kai idon ta, d'aukko wayarta tay ta zuba ma kwankwatsattsen glass d'in ido tana kallon bak'uwar lambar da ake kiran nata da ita, kaman bazata d'aga ba sai kuma tay picking, karata tay a kunne ba tare data ce komai ba tana jiran taji mi za'a je, jin shirun yayi yawa yasa tay sallama,

"Meet me in the parking lot" shine taji an fad'a da yar kakkausar murya daga haka kuma akai cutting kiran, cire wayar tay daga kunnanta ta bita da ido, tunanin waye wannan da yace ta iske shi a wurin ajiye motoci ta shiga yi, tunanin muryar waye ta fara yi can zuciyarta ta raya mata ta Sameer ce har saida gabanta yay wani bugu, kokonto ta shiga na anya kuwa shida sun tafi kuma in ma shine ta ina ya samu lambarta, zuciyar ta ce ta raya mata taje ba sai ta ga koma waye ba, mik'ewa tay ba wanda hankalin shi ya kawo kanta duk idanunsu na akan Tv, d'aki ta nufa ta d'aukko gyale ta yafa sannan ta fito tana ruk'e da wayar, tana a kan hanyar zuwa aka k'ara kira da lambar, tana d'agawa taji ance "Don't waste my time!" tana jin hakan ta tabbatar da Sameer, sauri ta shiga yi gabanta na d'an fad'uwa sai fargabar dalilin kiran nata take, lokacin data k'araso tsaye tay tana kallon cikin parking space d'in wanda yake dankam da motoci rasa a ina yake tay sai faman waige waige take, horn d'in da taji anyi ne yaja hankalinta da sauri ta kai idon kan Motar da taga ta saki danja wadda ke a d'an gabanta daga wajen parking space d'in, nufar Motar tayi a d'arare ta zagaya d'ayan 6angaren, tsaye tay a bakin kopar ta sake ji anyi horn hakan yasa ta kai hannu har rawa yake ta bud'e k'opar, wani irin k'amshi ne ya bugi hancinta ta d'an lek'a kanta yana zaune a driver seat jikinshi sanye da k'ananun kaya, murya na rawa ta gaishe dashi yay shiru tamkar bai ji ta ba kuma bai kalle ta ba, saida ya mula sannan taji yace ta shigo, a tsorace ta shiga ta zauna a kujerar gaban ba tare data rufe kopar ba hannun ta guda na ruk'e da ita, juyowa yay ya kalli kopar kafin ya kalleta ya d'aure fuska tamau nan take ta gane mi hakan ke nufi ta rufo k'opar, k'ara gaida shi tay yay d'an Jim sai kuma taga ya jinjina mata kai, shiru sukai sai Ac dake ta aiki tana bugun fuskarta, a k'alla sun d'auki wasu mintuna a haka ba tare da yace mata komai ba sai latsa waya yake tana ta d'an satar kallon shi saidai sam bata ji ta gaji da zaman ba, tana satar kallon nashi ta lura da wayar hannun shi kamar ba wadda ta fashe ba don wannan ta hango glass d'in ta lafiya lau, sai can sannan yay mata nuni da wani abu dake a gefen shi da Hannun shi taji yace ta d'auka cikin d'aurewar kai ta kai hannu ta d'aukko abun wadda yar jakar kwali ce k'arama tana da yan igiyoyin kamawa daga jikinta akwae hoto saidai bata duba ba balle ta gane ko ta miye, rik'e jakar tay a jikinta ta maida idon ta akan shi lokacin taji yace gashi nan ya biya ta damage d'in da yay ma wayarta saura ita, yamutsa fuska ta fara yi a marairaice ta fara bashi hak'uri tana fad'in Allah tasan bazata iya biyan shi ba, banza yay mata kuma har lokacin bai kalleta ba can tace mashi to ga wannan d'in ya bar shi ba sai ya biya ta ba Shikenan, kawai sai gani tay yay wani guntun murmushi wanda yafi kama da a kira shi na mamaki, sai lokacin ya juyo suka had'a ido gabanta yay wani irin bugu ganin yadda ya d'aure fuskar, "kina da waya ne?" Ya tambaya had'i da d'age mata gira wani miyau ta had'iya don ta fahimci tambayar yana nufin wayarta waya ce, a hankali ta girgiza mashi kai alamar a'a cigaba da kallon ta yay da yake wurin fayau yake da hasken fitilu kuma glass d'in Motar baida duhu sosae hasken ya d'an haska cikin Motar ba kamar da yake a inda suke akwae fitilar data haska saitin Motar, sai yan kame kame take ganin yadda ya kafeta da ido, janye idon yay taji yace ta tafi godiya tay mashi har ta juya zata bud'e Motar kamar daga sama taji yace "zaki aure yaushe?" Da sauri ta juyo ta kalle shi, sai ka rantse ba shi yay Maganar ba idon shi na akan Wayar shi, kokonto ta shiga yi na kodai kunnuwan ta ne suka ji mata ba daidai ba nan take ta gasgata hakan tana niyyar juyawa taji yace ba tambayar ta yay ba, maida idonta tay kan shi da tsananin mamaki take kallon shi har saida ta had'iyi abu kafin tace mashi ita ko rana ba'a saka mata ba ai,
"Why?" taji ya fad'a ba tare daya kalleta ba, ce mashi tay bata da wanda ta tsaida zata aura, shiru ya d'anyi kafin taji yace ko dai bata da masu sonta ne, har saida tay d'an murmushi tare da girgiza mashi kai tace mashi ana cewa ana sonta sosae itace dai bata bada dama Why, ya k'ara ce mata tay d'an jimm kafin tace akwae wanda ta tsaida zata aura amman sai ya guje ta ita kuma sai bata k'ara jin tana son wani ba, dakatawa yay da latsa wayar ya juyo ya kalleta suka had'a ido har lokacin Fuskar shi kaman a d'aure take har ta fara tunanin kodai haka yanayin fuskar tashi take, tambayar ta yay mi tay mashi ya gujeta idon shi a cikin nata, kikkafta idanu ta shiga yi ta fara bashi labarin tun farkon had'uwar ta da Mujaheed har zuwa lokacin da ta samu labarin auren shi sai dai a tak'aice take gaya mashi, lokacin data gama idanunta ne suka ciko da k'walla da sauri ta sunkuyar da kanta tasa gefen gyalenta tana goge kwallan, tana haka taji yace ai wannan ba wani abu bane he found someone da yake tunanin is better than her so he left her, da sauri ta d'ago ta kalle shi cikin muryar kuka tace "amman fa tsawon lokaci muna tare da shi in yasan bazai aure ni ba miyasa tun farko zai sa ni in yarda da shi har yayi man Alk'awarin Aure, Saboda shi bana saurarar kowa kuma yasan hakan amman ya yaudare ni, dama ashe yasan ba aure na zaiyi ba wai haka yace ma abokin shi daya fad'a man zancen yayi aure wai burge shi nike shiyasa yake tare da ni" har ta gama Maganar idon shi na akan ta, janye idon yay yana wani d'an murmushin bata san miye duniya ba shiyasa ta d'auki hakan wani babban abu, tanata goge k'walla ya juyo suka had'a ido cikin Maganar shi mai cike da isa yace mata in a relationship she shouldn't trust completely don abunda yafi hakan ma za'a iya mata koma miya faru da ita shi a wurin shi itace tay kuskure amman yasan hada don bata da wayau ne tana rayuwa a k'auye, shiru tay tana sauraran shi saidai sam bata ji komai ba a Maganganun da yayi don ita bata ma yi zaton zai iya yin magana da ita ba haka,

"You should forget about him and move on, in kin zauna a haka ke da shi waya ci gaba, I guess shine tunda yayi auren shi yana can yana enjoying life en shi, in kina ganin ya cuceki Allah yana nan ai, so you should focus on your self and your own happiness, ki ba masu cewa suna son ki chance you will definitely find the right person" jinjina mashi kai tay bayan yayi shiru, sosae taji ta samu k'warin gwuiwa ta wani bangaren kuma mamakin shi take yadda har ya yi Magana da ita haka, maida idon shi yay kan waya taji yace mata taje, godiya tay mashi ya jinjina mata kai ta juya ta bud'e kopar, bayan ta fita ta maido kopar ta rufe, nufar hanyar komawa baya tay sai murmushi take hakanan take jin wani irin nishad'i, jin k'arar rufe kopar Mota yasa ta juya baya shine taga ya fito daga cikin Motar ya nufo hanyar da take bi kawai sai ta tsaya tana kallon yadda yake tafiya irin ta kakkarfan namiji, tana tsayen har yazo saitin ta kaman bazai tsaya ba har ya d'an gota ta sai kuma taga ya tsaya taji yace mi taje jira, d'an murmushi tay tace taga ya taho hanyar ne shiyasa ta tsaya ya wuce, juyawa yay yaci gaba da tafiya, bai fi taku d'aya zuwa biyu yayi ba taga yayi mata alamun ta taho da hannun shi, a tare suke tafiyar tana daga d'an bayan shi, suna cikin tafiyar taji yace "When are you leaving?" amsa ta bashi da gobe bai ce komai ba yaci gaba da tafiyar shi can taga ya mik'o mata hannu cikin rashin fahimta ta kalle shi sai kawai ta mik'a mashi jakar hannun ta, girgiza hannun yay ya furta "Your phone" da sauri ta mik'a mashi wayar tata har zai bata ta cire password sai yaga a bud'e take don tunda ta fashe ta cire Saboda wuya take sha wurin bud'ewa, yana ta latsa wayar batare data san mi yake ba har suka iso baya, a daidai k'opar da zai bi ya tsaya ya mik'a mata wayar, amsa tay ya juya zai shige yaji tace "Kai yaushe zaka tafi?" Ita kanta sai dae jin Maganar tay ta fito, a wani slow ya juyo har saida gabanta ya fad'i ganin kallon da yay mata, motsa baki ta shiga yi ta waro ido duk ta sha jinin jikinta,
"Na zo don ke ne?" taji ya tambaya da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a, d'age gira yay yace to miyasa zatai mashi tambayar, cikin yar in ina tace "d...da..dama d'azunne naga yan gidan ku sun tafi,t.. to nayi tunanin ma harda kai aka tafi" da k'yar ta k'arasa Maganar, d'an k'ank'ance ido yay yace sa mashi ido take kenan a dabarbarce tace a'a wllh kawai don taga tare suka zo ne, yadda tay Maganar ne a tsorace yasa shi yin d'an guntun murmushi gefen kumatun shi ya d'an lotsa Fauzy ta bi shi da ido don ba K'aramin kyau murmushin ya k'ara mashi ba, juyawa yay ya nufi hanyar har zai shige ta ji da turanci yace gobe da sassafe zai tafi, da d'an d'aga murya tace "Allah ya kiyaye hanya" kaman bazai amsa ba sai kuma taji ya furta "Ameen" daga haka ya shige, washe baki Fauzy tay gaba d'aya yau abubuwan nashi burgeta suke, wucewa tay ta nufi part d'in da suke har ta kusa kaiwa taja ta tsaya, d'ago jakar kwalin tay sama tana duba hoton jiki wanda na inda ake saida wayoyi ne da kuma hotunan wayoyi kala kala da accessories nata, sauke jakar tay ta kai hannu ciki tana k'ok'arin fiddo abunda ke ciki, kwalin waya ne ta fiddo lokacin da idanun ta suka sauka akan rubutun jiki Kusan sik'ewa ta nemi yi ganin hoto da kuma sunan wayar wadda iPhone 15 ce irin ta Fatuu, wani irin bugu k'irjinta ya hau yi idanu waje baki bud'e take kallon kwalin, juyawa tay a razane ta kallo hanyar daya bi Al'ajabi ne ya kamata a ranta ta shiga raya don ya fasa mata waya shine zai bata wannan tsadaddar wayar, gaba d'aya tsoro ne ya kamata maimakon farinciki ta shiga tunanin yadda zatai da wayar, yankewa tay kawai taje ta nuna ma Aunty Mareeya ta kuma fad'i mata gaskiyar abunda ya faru tsakanin su, da sauri ta maida ta cikin kwalin kafin sauri sauri gudu gudu ta nufi part d'in nasu.................

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

85
Lokacin da ta shiga parlon Aunty Mareeyar ta tashi ita da Feenah, har zata bita d'akin sai kuma ta fasa ta juya, bakin kopar shigowa ta komo ta tsaya ta fara k'ok'arin kiran ta,saida ta kusa tsinkewa sannan ta d'auka cikin murya ta wanda ya fara bacci tace mata ya akai ne har ta fara bacci ta tasheta, hak'uri ta bata daga haka tay shiru saida Aunty Mareeyar tace miye to ta kirata sannan murya na rawa tace don Allah tazo taga wani abu, tambayar ta tayi wani abu da alamun mamaki, rasa abunda zata ce mata tay kawai sai tace dama akan wannan ne data fad'i mata abokin mijin Zarah ai tana jin Haka da sauri ta mik'e ta zuro k'afafunta k'asa, hanyar fita daga d'akin ta nufa tana ce mata gata nan zuwa, bayan ta fito cikin parlon ganin bata ciki yasa ta nufi d'akin su, nan ma bata ganta ba sai su Haulat da Mino dake bacci Zainab dai tana a parlon suna son k'arasa kallon Film d'in, a bakin kopar d'akin ta tsaya ta fara kiran ta, bayan ta d'aga a d'an hasale tace wai tana ina tasa ta fito kuma ita bata ganta ba tace mata tana a bakin kopar shigowa, jin haka har saida gaban Aunty Mareeyar ya d'an fad'i da yar fargaba ta nufi hanyar fita, tana tsaye a gefen kopar ta fito suka had'a ido, bin juna sukai da kallo ganin yadda Fauzyn tay zuru zuru yasa ta bita da kallo tun daga sama har k'asa, tsaida idon ta tay kan yar jakar hannunta sai kuma ta maido idonta cikin nata tun kafin tace mata wani abu Fauzyn ta Mik'o mata jakar, hannu ta kai ta amsa ta bi jikinta da kallo kafin ta kalli Fauzy da alamun rashin fahimta ta tambayeta miye tace ta duba abun ciki, hannu ta kai ta fiddo kwalin wayar koda tay arba da sunan wayar da sauri ta kalli Fauzy tace "Wannan fa, ta waye?" Sai faman zare ido take tace mata wai cousin brother d'in Ya Haisam ne ya siya mata, cikin d'aurewar kai ta tambayi waye cousin brother d'in nashi muryarta na d'an rawa tace mata Sameer, waro ido Aunty Mareeya tayi cike da Al'ajabi ta maimaita sunan Sameer d'in Fauzy ta d'aga mata kai, gaba d'aya kanta ya gama daurewa tama kasa magana baki a d'an bud'e take kallonta can tace "to ke taya akai kuka san juna, mike tsakanin ku da har zai baki wannan tsadaddar wayar?"

abu Fauzy ta had'iya kafin tace "d..dama shine wanda nace maki rannan ya d'auke ni mun fita tare kuma shine ya aiko man da kud'i in yi lik'i a wurin dinner" k'arasa bud'e baki Aunty Mareeya tay tsabar Al'ajabi, a rud'e tace mata amman taya wai ya santa da har hakan ta faru tsakanin su shi da ko kallon mutane bai yi balle ya tanka masu Saboda izzar bala'e, labarin yadda komai ya faru tsakanin su Fauzy ta shiga bata, lokacin data gama gaba d'aya Aunty Mareeya ta zaro idon ta sai kuma ta washe baki tana dariya cike da Farinciki tace "Allah buwayi gagara misali, wani hanin ga Allah baiwa ne, inyee yar gidan Hajiya, wannan dank'areren kamu haka, ashe ashe dai babban rabo ne ke bibiyar ki" dariya Maganar tata taba Fauzy tana yi tace mata itafa ba soyayya suke da shi ba bata fad'i mata yadda komai ya faru ba, baki a washe tace mata ai da hakan wani lokacin dama ake farawa,
still dariya Fauzy ke yi tace "Wannan ne zai so ni kema dai Aunty Mareeya, mutumin da farko kafewa ma yayi akan sai na biya shi ko yanzu fa da zai bani wannan wayar sai da yayi man maganar saura ni in biya shi nayi ta mashi magiya, amman ina ganin yanzu dai ya hak'ura tunda yace in taho" karaf Aunty Mareeya tace "in ma bai hak'uran ba sai mu biya shi ai, don nasan tunda ya kafe bayan kin nuna mashi baku da halin biyan to na gane biyan da yake nufi da soyayyar ki zaki biya shi baki ga har gwada ki yay ba, ai yasha kurumin shi in dai wannan ne za'a biya shi fin yadda yake zato, ana son shi wllh" dariya sosae Fauzy ke yi jin wani hak'ilo na Aunty Mareeya gaba d'aya ta hak'ik'ance kan wai son ta yake bacin ita dai tasan ko abu d'aya mai kama da nuna so bai yi mata ba in ba tamke mata fuska ba wanda tasan hakan bai cikin alamun so gashi k'arshe ma ai cewa yay taba masu sonta dama zata samu mutumin daya dace, Aunty Mareeya sai faman farinciki take bakinta yak'i rufuwa sai juya wayar take tana jinjina kai,

"Yanzu yaushe yace zai zo Katsina?" ta tambayeta taci serious Fauzy kau mi zatai in ba dariya ba, harara ta wurga mata tace ba tambayarta tay ba, cikin dariya tace "to ni Aunty Mareeya bansan mi zan ce maki ba sai kace baki fahimci bayanin dana yi maki ba, ni fa bai ce yana sona ba bai kuma nuna ko alamar hakan ba kece kike ganin haka, ba har na fad'i maki shawarar da ya bani dana bashi labarin abunda Mujaheed yay man ba" d'an jimm tay tana nazarin Maganar can ta sauke ajiyar zuciya tace "na fahimci komai, amman kinsan mi, ina tunanin yana son ki ba tare daya sani ba don mutum irin wannan hakanan bai iya sake maki haka gaskiya, in ma ace yana da kirki zai iya biyan ki wayar taki gaskiya bana tunanin da irin wannan tsadaddiyar duk gadai wayoyi iri iri nan cike da gari sai kawai ya siyo maki wannan don ya fasa maki glass d'in waya, ai kawae yar gidan Hajiya komar ki ta kamo mana gingimemen kifi wllh, Allah Ubangiji ka tabbatar mana da abun nan wllh har bansan irin farincikin da zan yi ba" ta k'arasa tana ta washe baki ita dai Fauzy murmushi kawai take can tace "to Aunty koda ace sona d'in yake ni ba sai in yayi man ba...." Tunkan ta gama Maganar ta kai hannu zata buge ta tana fad'in "Wllh yayi maki mak'aryaciya kawai, wannan d'in zaki ce wani bai maki ba, ke ko bai maki ba indai ya nuna yana son ki Allah kema sai kin so shi tunda ni yayi man, yanzu irin wannan yaushe ma ake jira sai sunce suna so ai da mutum ya samu dama yake cusa kan shi in da rabo sai kiga an dace haka kema ya kamata ki yi" tura baki tay tace Allah ita bazata wani cusa kanta a wurin shi ba hakanan ya wulakanta ta,

"Ai dama ba ina nufin kice kina son shi ba, tunda kinga kin samu dama ke zaki rink'a yin abubuwan da zaki jawo hankalin shi gare ki har ya furta yana son ki" shiru Fauzy tay tana jinjina zancen wai Sameer ya bud'e baki ya ce yana son ta tirkashi, tambayarta tay ai tana da lambar shi ko tace mata eh d'azun daya kirata, tace Yauwa to yanzu ta kira shi tay mashi godiya, d'an waro ido Fauzy tay tace amman fa dare yayi sosae ta bari sai gobe mana, harararta tay tace da zafi zafi ake bugun k'arfe ai sai yaga ma bata yaba ba tunda yasan dole a daren zata bud'e ta gani su fa ta irin haka ake janyo hankalin su, ba yadda Fauzy ta iya haka ta fara k'ok'arin kiran nashi Aunty Mareeyar sai kwatanta mata yadda zatai mashi godiyar take ita kuwa gabanta sai d'an fad'uwa yake, kiran ya shiga yana ta ringing amman bai d'aga ba har ya yanke, cire wayar tay tace mata ta sake kira k'ilan bai kusa da wayar yanzu kuma tunda yaji ringing d'inta zai taho don ya d'auka, yamutsa fuska Fauzy tay tace ita gaskiya bazata sake kira ba hakanan ta ja ma kanta wulakanci sufa irin su ba'a zak'e masu don ba'a cika yi masu gwaninta ba, jinjina kai Aunty tay alamar yarda da Maganarta tace Shikenan suje, Fauzyn ta tambaye ta yanzu ya zatai da wayar ita bata son a gani gaskiya tace mata to ta 6oye ta in suka koma gida sai taci gaba da amfani da abunta ta d'aga mata kai, suna niyyar juyawa su shiga wayar Fauzy ta fara ringing da sauri gaba d'ayan su suka kai idanun su kan screen d'in, ganin lamba yasa Aunty Mareeya ce mata waye idon Fauzy a d'an ware tace mata shine,

"Yauwa to, ki d'auka sai kice dama kinga wayar ne shine kika kira ki yi mashi godiya, kar kiyi mashi magana kaman wata sakarai kiyi exactly yadda na kwatanta maki d'azun" Aunty Mareeya da tay k'asa k'asa da murya ta fad'a har saida tasata dariya, picking kiran tay ta kai wayar kunne sai had'iyar miyau take Aunty na mata nuni da ta natsu da hannu, shiru yay bayan ta d'auka cikin kwantar da murya tay sallama nan ma shiru bai amsa ba, d'ago ido tay ta kallo Aunty da ta gwale ido tana kallon ta, alamun miye tay mata da hannu Fauzyn ta girgiza mata kai tay mata alamar bai yi magana ba, yi mata alamar taci gaba da magana kawai tay ta d'aga mata kai, a nutse tace mashi dama ta ga wayar ne shine ta kira tayi mashi godiya, tana rufe baki taji yace "You ave done that already" abu ta had'iya cikin yar in ina tace "eh, dama naga wayar babba ce shiyasa nace bari in k'ara yin godiyar, Allah ya saka da Alkhairi ya k'ara bud'i na Alkhairi" d'an shiru yay daga baya ya furta "Ameen" shiru sukai Fauzy sai kikkafta idanu take Aunty Mareeya tay mata k'uri sai tsuma take, can bayan wani lokaci taji ya furta "Gud nyt" da sauri tace mashi haka itama, tana ciro wayar Aunty Mareeya ta kai hannu kan kafad'unta ta jawota jikinta cikin washe baki tace haka yakamata tace "Gud nyt Masoyi na" yadda ta mak'e muryar ne yasa Fauzy kyalkyacewa da dariya itama dariyar farinciki take suka nufi ciki, lokacin da suka shiga cikin parlon ba kowa duk sun tashi an kashe kayan kallon, sakin kafad'ar Fauzyn tay cikin washe baki tace "ranki ya dad'e kije ki kwanta" dariya Fauzy ta saki tana fad'in kai Aunty Mareeya, sai da Safe tay mata tana washe baki tace "to your excellency Allah ya tashe mu lafiya" sosae Fauzy ke dariya ta juya ta tafi itama Aunty Mareeyar dariyar take ta nufi d'akin su, bayan Fauzy ta shiga bakin gado ta nufa ta zauna ta kai hannu cikin jakar ta fiddo kwalin wayar, bin shi tat da kallo can ta d'aura a saman cinyoyinta ta bud'e, bin wayar tay da kallo cikin ranta tana k'ara yin mamakin ta, Maganganun Aunty Mareeya ta shiga tunanowa na Sameer son ta yake, acikin ranta ta shiga mamakin taya hakan zata kasance wanda tasan tabbas dole yana da yan mata kuma bama k'ananu ba kamar ta, sannan y'ay'an Mayan masu kud'i da Mulki, zuciyarta ce ta tambaye ta yanzu in da gaske son nata yake zata so shi? jimm tay ta kasa amsa ma kanta don gaba d'aya ita gani take ba abu bane mai yuwuwa ma hakan yasa ta kauda ma tunanin gaba d'aya, d'aukar wayar tay ta fara jujjuya ta tana k'are mata kallo da d'an murmushi akan fuskar ta, aje wayar tay ta kai hannu ta tallabo ha6arta ta shiga tunano duk maganganun da sukai dashi a Mota, sosae tay mamakin yadda ya sake mata har sukai magana haka sai faman sakin murmushi take can ta maida wayar acikin kwalin ta saka cikin jakar ta mik'e, wurin kayanta ta nufa bayan ta bud'e akwatinta ta saka, ko tunanin ta saka kayan bacci bata yi ba ta wuce gado ta haye, rufe ido tay nan take zuciyarta ta shiga dawo mata da suffar Sameer.

Washe gari da wuri akai gama Breakfast saboda masu tafiya kuma ranar aiki ce, Senator na cikin yin Breakfast jikin shi sanye da jallabiya yan'uwanshi da suka rage maza suka zo part d'in shi don su gaisa su kuma yi sallama wanda ya'yan yan'uwan mahaifinsu ne suma duk dattawa ne, bayan sun gaisa ya tambayi sunyi breakfast d'in suka ce eh yanzun nan suka gama, zancen wadda Nameer yake so yay masu yace bari ya gama sai suje suyi ma iyayen nata magana cikin nuna farinciki suka ce mashi to, bayan ya gama a tare suka mik'e har zasu tafi Senator ya dakata yace masu yana d'an zuwa duk suka tsaya suka ce to, hanyar Bedroom d'in shi ya nufa ya shige, bada jimawa ba ya fito ruk'e da babbar leda mai rubutu a jiki, d'aya cikin yan uwan nashi Alhaji Musa ne ya nufe shi da sauri wanda matsayin K'ani yake a wurin shi ya kai hannu ya amshi ledar suka nufi part d'in da su Ard'o suke, lokacin da suka shiga parlon ba kowa basu dad'e da gama yin Karin kumallo ba suna ciki suna shirin Tafiya, Alhaji Musa d'in ne yaje bakin k'opar tasu ya kwankwasa tare da yin sallama, Baban Altine ne yazo ya bud'e yana ganin shi ya k'arasa fitowa cikin washe baki ya gaishe dashi tare da d'an sunkuyawa bayan ya amsa ya sanar dashi tare suke da mai gidan suna son yin magana dasu ne yayi ma su magana, da sauri idanu a d'an waje ya tambayi lafiya dai ko yana murmushi yace mashi lafiya lou sai ma Alkhairi da sauri ya jinjina kai ya juya d'akin, ba'a d'au lokaci ba sai gasu sun fito su duka duk sun saka kaya da zasu tafi dasu Ardo yasha babbar riga da hula ha6ar kada, cikin parlon suka nufo su Senator na zaune suka nufe su da sauri, hannu suka basu suka shiga gaisawa don Senator ya hana su duk'awa k'asan da suke in zasu gaisa amman duk da haka in zasu gaisan dasu sai sun d'an sunkuya, bayan sun gama gaisawar yay masu nuni da su zauna duk suka nufi kujeru suka natsu, a nutse Alhaji Ibrahim ya fara magana yace dama abun Alheri ne suke tafe dashi duk suka jinjina kai, bayani yay masu d'an shi k'anin wanda ya auri yar wajen su ne shima ya ga yar'uwarta yana so to shine suka zo sake rok'on iri in ba'a yi mata miji ba, tun kafin ya rufe baki baban Altine ya hau girgiza kai bayan yayi shiru da sauri yace mashi ba'a yi mata miji ba wllh kuma koda an yi ma za'a warware a ba d'an wajen nasu ko don Mutuncin su a gare su, shi Baffan Fatun ma ya kasa magana tsananin mamaki had'i da farinciki ne suka lullube shi don kuwa yasan wadda ake Magana koma wacece d'iyar shi ce tunda da iya yaran shi su Aysha aka zo, shi Ard'o sam bai fahimci inda aka dosa ba tunda dama ba wani fahimtar hausar yake sosae ba cikin harshen fulatanci yake tambayar Baffan Altine abunda aka ce cike da farinciki ya hau sanar dashi, ai tun kafin ma ya k'arasa da sauri Ard'on har yana yin kaman zai fad'o daga kan kujera tsabar saurin yayi Magana Baffan Altine ya tare shi, cewa yay an ba yaron duka don haka yanzu ma sai a d'aura aure kawai, gaba d'aya murmushi su kai Senator yace masu yaron yana karatu ne yanzu kuma ba'a K'asar nan ba amman nan da shekara guda zai gama zuwa lokacin sai ayi masu Auren dama akwae Yayar shi da za'a ma Aure a lokacin sai a had'a su yanzu sun yi magana ne don asan da Maganar, Baban Altine ne ya k'ara yi ma Ardon bayani yadda zai fahimta sosae sai faman d'aga kai yake, Senator ne ya sake cewa yakamata a kira yaran aji ta bakin su don a tabbatar kafin a tsaida magana duk suka ce hakan yayi, kiran Nameer yayi a wayar shi bayan ya d'auka saida ya amsa gaisuwar da yay mashi sannan ya bashi umarnin ya iske shi a part d'in sannan ya kira itama yarinyar da yayi ma Hajiya Magana akan ta, bayan ya cire wayar ne daga kunnan shi ya kai hannu kan k'atuwar ledar da suka zo da ita ya d'an tura saitin su yace gashinan suyi amfani da su, Baban Altine ne ya taso ya d'auka har da duk'awa yana godiya haka Baffan Fatuu ma sai da ya d'an zamo daga kan kujera yay godiya Ard'o ma sosae ya hau yin godiya, after some minutes Nameer ya shigo jikin shi sanye da k'ananun kaya, amsa mashi sallamar da yayi sukai ya k'araso ciki kan shi a k'asa, daga gefen su Dad d'in shi ya zauna a k'asa duk idon su na akan shi, d'an d'ago da kai yay ya gaishe dasu Dad bayan sun amsa ya juya kan su Ard'o ya gaishe dasu cikin washe baki babban Altine ya amsa shi kuma Baffan su Fatun murmushi yake ya amsa, bai dad'e da shigowa ba Mino ta shigo da yar sallama jikinta sanye da Hijab duk suka kai idon su kan ta suna amsawa, kan ta a k'asa ta k'araso cikin parlon, a d'ayan bangaren ta zauna ya zamana suna facing juna da Nameer, gaishe dasu tay ba tare da ta d'ago kanta ba duk suka amsa, shiru suka d'an yi kafin Dad yay d'an gyaran murya idon shi akan Nameer yace mashi Hajiya ta fad'i mashi sak'on shi shine suke son ji daga gare shi da gaske yana son ta, shiru Nameer yay kan shi a k'asa gaba d'aya idanun su na akan shi, ganin yak'i magana yasa cikin d'an d'aga murya Dad yace,
"C'mon Ka bud'e baki kai mana magana my friend! baka ji nauyin wadda ka ba sak'on ba sai mu" duk murmushi akai k'asa k'asa Nameer yace Eh,

"Eh what?" da k'yar ya furta eh yana sonta ba tare da ya d'ago ba, "kuma zaka Aure ta?" kai ya d'aga kafin yace eh,

"Ka sani in muka riga muka gama magana ba zancen ka dawo ka ce ka canza ra'ayi" da sauri ya jinjina mashi kai, maida idon shi yay kan Mino itama ya tambayeta tay shiru bata ce komai ba, k'ara tambayar ta yay nan ma tak'i tace komai baffan Altine ne cikin d'aga murya da fulatanci yace mata bata ji ana magana bane still bata ce komai ba idon Baffan ta na a k'asa, Ardo ne yay yar tsawa Dad yace su rabu da ita hakan data yi ta nuna masu ita cikakkiyar bafullatana ce, Albarka ya saka masu duk aka amsa da Amin yace su tashi su je,

A tare suka mik'e dukkan su kan su na k'asa suka nufi hanyar fita daga part d'in su Dad suka cigaba da tattaunawa, suna fitowa bakin k'opar part d'in Nameer ya kai hannu ya kamo hannunta ta waro ido ya jata tana ta waige waigen kada wani ya gan su, bayan part d'in ya nufa da ita sannan ya sake ta suka bi juna da kallo fuskokin su d'auke da murmushi,

"Yanzu hankalin ki sai ya kwanta sosae kin zama tawa na zama naki" Nameer ya fad'a yana dariyar farinciki, itama dariyar take sosae take ganin abun kamar a mafarki daga fara soyayyar su har an yi Maganar aure ta wani bangaren dad'i ne cike da ranta,
"Yanzu ya za'ai Maganar karatun ki don ni gaskiya dana gama nan da one year in sha Allah za'a d'aura mana Aure tare da Yaya Laila" cikin tabbatar mata da hakan yay Maganar, shiru ta d'an yi sai kuma tace mashi to yayi duk yadda yake so, yana murmushi ya d'age mata gira "kenan k'in amince muyi aure ko baki gama Secondary d'in ba?" Kai ta jinjina mashi tace in dae zai barta taci gaba,

"in kuma ban son kici gaba da karatun fa?" Still da murmushi akan fuskarta ta d'an yarfa hannu tace mashi Shikenan zata hak'uri, wani k'ayataccen murmushi ya saki yace ashe haka take son shi ita dai murmushi kawae take,

"Ki sha kurumin ki zaki karatu har sai kin ce ya ishe ki, saidae gaskiya bana son a rink'a kalle man ke ya za'ai kenan?" Yar dariya tayi tace sai ta rink'a rufe Fuskar ta to, lumshe mata ido yay ya furta "that's what makes me love u more babe, duk abunda nike so kina so in sha Allahu zan yi bakin kokarina wurin saka ki farinciki bazaki ta6a yin dana sanin amince mani ba" jinjina mashi kai tay tana ta murmushi,
"Kema zaki man haka?" Da sauri ta d'aga mashi kai kafin ta furta "in sha Allah" yace Allah ubangiji ya basu iko ta amsa da Amin,

"Gaba d'aya ji nike inama ba sai nan da one year zamu zama ma'aurata ba don gaba d'aya kin mamaye heart ena" yar dariya tay sai kuma tace "ni kai ne heart d'in nawa" tana furta hakan tasa tafukan hannuwanta ta rufe fuska, sosae yaji dad'in Maganar sai zabga uban murmushin jin dad'i yake, hannu ya kai ya cire hannuwan nata suka zuba ma juna ido wani sabon son junan su ke ratsa zuciyoyin su, kasa jurewa Mino tay ta sadda idanun ta k'asa,
"I'm going to miss you" d'ago ido tay a hankali tace itama haka, yar Ajiyar zuciya yayi yace yaso ya canza mata waya amman bai samu yin hakan ba, tambayar ta yay tana da bank account ta girgiza mashi kai alamar a'a, d'an jimm yay kafin yace Shikenan zai tura ma Uncle d'inta sai ya canza mata wayar don su rink'a yin Vedio call lafiya lou suna rage kewar juna, ce mata yay itama yakamata ace tana da account d'in zai sa a bud'e mata don ya rink'a tura mata kud'in da zata rink'a yin hidindimun ta, tana ta kallon shi har ya gama sannan tace mashi ya bar shi ba sai ya rink'a tura mata ba tunda ana mata komai, tun kafin ta rufe baki ya d'an yi mata hararar love yace tun yanzu ta sani hakkin ta ya hau kan shi tana dariya tace ai ba'a d'aura auren ba shima dariyar yake yace eh ai an bashi ita ko.

Bayan su Nameer sun tafi Senator yay ma Alhaji Ibrahim Maganar bada kud'in neman Aure, daga cikin Aljihun jallabiyar shi ya ciro kud'in bandir d'in yan dubu guda biyu wato 200k ya ba Alhaji Ibrahim d'in, mik'ewa yay ya nufi su Ard'o da sauri Baban Altine ya mik'e shima ya tare shi ya bashi kud'in, bayan duk sun koma sun zauna aka yi Addu'oi aka shafa. Bayan tafiyar su Senator Baffan Altine ya bud'e ledar daya basu nan suka ga shaddoji ne guda shidda wato kowa kala biyu, sam bakunan su sun kasa rufuwa tsabar farinciki sai yabon kirkin su Senator suke, mik'ewa sukai don suje su k'arasa shiryawa kowanne su bakin shi a washe, tsayawa Baffan Fatuu yay bayan sun tafi ya fara k'ok'arin kiran Yadikko, lokacin da kiran ya shiga tana cikin d'aki suna shiryawa Kusan ma sun gama kimtsawa, bayan ta d'auka cikin ladabi ta gaishe dashi ya amsa, tambayarta yay sun gama shiryawa tace mashi eh, d'an shiru yay kafin kuma yace Albishirinta tana Jin hakan da sauri ta bashi amsa da goro fari Kal, yadda tay Maganar har saida ta d'an bashi dariya yace mata wani abun Alkhairin ne ya same su yanzun nan, cike da k'aguwa ta tambayi miye, fad'i mata zancen neman Auren Mino dasu Senator suka zo yanzu yay harda shaddoji daya basu da kuma kud'in neman Auren, tun kafin ya gama fad'i mata ta mik'e tsaye don da a zaune take a bakin gado, gaba d'aya mamaki ne ya kamata ta kai hannu ta rufe baki shi kuma sai murmushi yake don ya fahimci taji Al'ajabin Maganar, muryarta na rawa tace "Yanzun Mino itama yaron gidan nan zata aura, to yaushe suka san juna haka mu bamu da Labari" fad'i mata yay a wurin bikin nan kuma an kira shi a gaban su ya tabbatar yana son ta zai aureta, wani irin farinciki ne ya lullube yadikko wanda tunda take bata ta6a jin irin shi ba a rayuwar ta gaba d'aya ta kasa rufe baki su Aysha da suka zuba mata ido ganin yadda take farinciki yasa suma suka shiga washe bakin haka innar su Altine ma dake zaune a cikin d'akin idon ta na akan ta, bayan sun gama wayar da sauri ta tambayeta ya akai taga tana ta farinciki ne nan take sanar mata, itama tsananin mamaki ne ya kamata ta waro ido can kuma sai ta mik'e zumbur ta nufa hanyar fita, d'akin su Yaya ta nufa duk sun shirya suma suna zaune a bakin gado suna had'a jakunkunan kayan su ta fad'o kamar an jefo ta duk suka d'ago kai suka kallo ta, Yaya ce ta d'an 6ata fuska tace lafiya zata fad'o masu haka ba sallama, hak'uri ta basu tay tsaye tanata zare ido ta ma rasa ta ina zata fara, ganin yanayin ta yasa Yaya tambayar ta lafiya, ai kaman tana jira ta hau fad'i masu zancen an nemi auran Mino itama zata auri yaron gidan nan, wani kallon mamaki gaba d'ayan su suka bita dashi Yaya ta maimaita Maganar cikin d'aurewar kai Babar su Altine tace wllh yanzun nan mahaifin su ya kira innar su yana fad'i mata, hannu Yaya ta kai ta ruk'e ha6a tana jinjina kai ita kuwa kishiyar tata murmushi ta shiga yi tana fad'in "kaga ikon Allah, ashe da rabon zamu k'ara zuwa gidan nan shan wani bikin, lallai iyalin Muhammadu masu jinin sa'a ne....." A dak'ile Yaya ta katseta da fad'in "Uhmm wai jinin sa'a, ai ni gaba d'aya sai yanzun ma na fahimci komai, wannan sa'ar ba ta Allah da Annabi bace, wato da suka ga ita ta farkon ta samu mai Arziki shine itama wannan sukai kulle kullen su suka tura ta binni, kai da ganin wannan kasan aikin asiri ne ace yana ganin ta ya fara sonta har an tsaida magana, ita kadae ce yarinya a wurin bikin ba ga yan mata nan yan binni ba, ke ita kanta babbar ma ni yanzu ban yadda hakanan mijin nata ya aure ta ba tun farko k'ulla soyayyar ta su akai shiyasa ta tashi hankalin ta da taji Ard'o ya bayar da ita, gaba d'aya sai yanzu na gano komai, ita ce ta kitsa ma Yarinyar ta gudu ta koma bayan tayi shiri sosae kan shi mai kud'in da shi Alhaji Lawan d'in shine ta zo har tayi nasarar sa shi janye Maganar aka kawo ta wanccan" Fuska a hautsine take Maganar cikin harshen fulatanci duk sun zuba mata ido, mik'ewa tay ta cize baki idon ta a kan su rai 6ace tace "gaba d'aya sai yanzu na gane komai daya faru mak'ark'ashiya akai, shima Ard'o harda shi aka ma Asiri shiyasa ya yarda aka fasa da wanccan ya kafe kan sai anyi da wanda ta Auran" jinjina kai innar su Altine ta hau yi fuskarta a yamutse gaba d'aya wata irin hassada ce ta mamaye mata zuciya, kai da kawowa Yaya ta shiga yi ta k'ank'ance idanunta ta shiga zurfin tunani,

"in dai ina raye to bazan bari Yaron ya auri Mino ba, tunda abun hakane nima zan yi abunda suka yin in sa a maida Auran kan d'aya daga cikin jikokina tunda ai ba fina iyawa su kai ba, ba abunda nike bari ya sha man kai, itama uwar Muhammadun da ta nemi zame man matsala ai ba k'aramar uk'ubata tasha ba kafin Allah ya d'auke abun sa, suma jikokin nata ban ta6a zaton haka abun zai kasance ba da tun wuri na d'auki mataki a kan su amman duk da haka lokaci ai bai k'ure man ba ko ya k'ure ba abunda zai gagara, har ita ta farkon sun ja bazan k'yaleta ba sai na raba Auran nata nasa ta dawo ruga anan zatai Aure......

86

...........bata samu k'arasa Maganar tata ba sakamakon buga katifa da d'ayar Matar Ardon mai suna Mero dake a zaune tayi fuska a matuk'ar d'aure ta fara magana "Sam bazan bari ki aikata hakan a gare su ba matuk'ar ina numfashi, duk abubuwan da kike yi mana k'yale ki kawae nike ba wai don ina tsoron ki bane, to yanzu an zo ga6ar da bazan zuba maki ido ba wllh sai in da k'arfi na ya k'are" gaba d'aya Al'ajabi ne ya kama su ganin yadda take maida mata martani ba tare da nuna shakkar ta ba kamar yadda suke yi tana juya su, hannu Yaya ta kai ta nuna kanta tace ita take gaya ma magana haka ta manta wacece ita,

"Ban manta ba, ke Mutum ce kamar ni saidai muna da bambanci sosae, ke mushirika ce wadda bata yarda da Allah ba ni kuma na Yarda da Allah ban yarda da shirka ba, don haka a wannan karon na d'aura d'amarar yin yak'i da shirka za kuma muga wanda zai yi nasara tsakanin k'arya da gaskiya, hakanan Saboda tsabar mugunta da rashin tsoron Mahallici mi Mutanen nan sukai maki da kika d'au karan tsana kika d'aura masu, in don mahaifiyar shi da take kishiyar ki ai ta bar maki duniyar ko, in kuma don kina ganin Ardo yafi ji dashi ne ai don yafi sauran yaran nashi gaskiya ne da ruk'on Amana, wato don kina aikata shirka shine kike ganin ita kowa ma ke yi, to tsaya kiji sirrin, matuk'ar mutum zai tawakalli ya dogara ga Allah ya mik'a mashi dukkan lamuransa to zai ta samun cigaba a rayuwar shi wannan dalilin ne yasa kika ga a komai Muhammadu da iyalan sa suke nasara koda kuwa kin aikata masu wani abu ina mai tabbatar maki bazaki yi nasara ba da iznin ubangiji, Idan kuwa ya baki sa'a don wani lokacin yana tara bawa ne kafin ya d'au mataki akan shi in har kika aikata wani abu da yay sanadiyyar fasa yin auren nan to sai na tona maki Asiri kowa yasan ke kika aikata masu wani abu kuma kinsan Mutanan binni bazasu ta6a kyale ki ba kotu za'a kai ki daga can sai gidan yari kuma na tabbatar d'aurin rai za'a maki don sai na fad'a cewa kina da sa hannu wurin mutuwar Innar Muhammadun k'ilan ma harda matar shi innar su inna wuro, a yanzu zan zuba maki ido ne amman zan sanar da Muhammadu da matarsa harda su yaran da Kakar su akan su dage da Addu'a dama dai kinsan ai su ba daga baya ba wurin ruk'o da Addini to har nima zan taya su zamu ga tsakanin mu da ke wanda zai yi nasara" rai a tsananin 6ace tana huci ta k'arasa Maganar dama can tara Yayar take, sototo sukai suna bin ta da ido,

mik'ewa tay tana d'an murmushi tace "ni zanje in taya murna don basu kad'ai abun Arzik'in ya shafa ba harda mu don haka ina mai baku shawara da ku kauda komai a ran ku kuyi farinciki hankali kwance ku dangwali Arziki, ke Yaya in kika kwantar da hankalin ki ma k'ilan Makka da kike ta mafarkin zuwa Masoyin ki Ardo da Ya'yan ki suka kasa kai ki duk da suna da halin hakan sai kiga ta sanadiyyar su kinje har ki k'ara ma sau ba adadi tunda kinfi kowa sanin halin iyalan Muhammadu basu da ruk'o in ba don haka ba da ko kallo a yanzu bazaki ishe su ba amman duk da tsangwama da tsanar da kike nuna masu hakan bai hana su jan ki a jiki ba wanda na tabbatar su wad'anda kike k'ok'arin ganin kin aikata shirka don ki jawo su a cikin Arzik'in ba lalle ko Habujar su bari ki rink'a zuwa wurin su ba balle har ta kai ga su biya maki Makka in ma ace burin naki ya cika kenan, in baki sani ba ki sani duk na kusa dake da kike ganin suna goya maki baya munafukan ki ne da sun samu dama zasu kaskantar da rayuwar ki kamar yadda kike masu" tana gama Maganar ta juya ta nufi k'opar fita, a razane Yaya ta bita da ido har ta fice haka Babar Altine ma, kallon juna sukai sun kasa cewa komai don abu ne da basu ta6a zato ba, sun d'an d'auki lokaci haka da k'yar innar Altine ta ja kafa ta matsa kusa da Yaya dake tsaye kamar an dasa ta, k'ok'arin k'arfafa mata gwuiwa ta shiga yi tana ce mata kada Maganganunta su dame ta ita tana tare da ita abunda za'ai kawae itama ai maganinta ta yadda bazata iya aikata abunda ta fad'an ba sai ayi yadda za'ai Auren ya koma kan d'aya daga cikin yaranta ita kuma ta mata alk'awarin duk abunda take so shi za'a rink'a yi in aka shigo cikin Arzik'in, bin ta da ido kawae Yayar tay daga yanayin fuskarta zaka fahimci ba k'aramar razana tay ba, ci gaba da k'arfafa mata gwuiwa tay can Yayar ta fara girgiza mata kai har saida gaban innar su Altinen ya fad'i,

matsawa Yaya tay ta zauna a bakin gado cikin mutuwar jiki tace mata akwae babbar matsala, dama bokan ta ya ta6a fad'a mata sai ta bi a hankali don a cikin gidan su akwae wadda zata kawo k'arshenta lokacin ta buk'aci sanin ko wacece yace bai samu gano kowacece ba amman tabbas sai tayi taka tsantsan don ba K'aramin tagayyara rayuwarta zata yi ba, a lokacin ta rok'e shi ya bata abunda zatai amfani dashi wurin yin maganin ta amman sai ya nuna bazai iya ba don a yadda ya gani ita bada asiri zata yak'e ta ba da ayar Allah ne, baki bud'e innar su Altine data durk'ushe a k'asa take sauraren ta, nannauyar ajiyar zuciya Yaya ta sauke ta hau jinjina kai tace "yanzu na gano k'arshe na da yace zata kawo wato shine in ta tona man Asiri aka kai ni gidan yari" sosae Yaya ta tsorata abun ka da mutumin kauye, nazarin Maganganun kishiyar tata ta shiga yi a cikin ranta tabbas tasan abunda ta fad'a kan iyalan Muhammadu gaskiya ne duk abubuwan da take masu basu nuna rashin d'a'a a gareta in akwae wadda zata ce tana mata rashin kunya to Fatuu ce ita kuma wannan ba ita kad'ai take mawa ba halinta ne haka kuma bayan ta girma yanzu duk ta bari, zuciyarta ce ta raya mata in tayi wasa to fa zata tashi a tutar babu ne, da sauri ta kalli innar su Altine tace mata su hak'ura kawai in ba haka ba zasu shiga matsala in dai suka aikata wani abu gara su goyi baya suma su ci Arzik'in ala bashshi in bikin yazo sai su tattaro sauran yaran da basu da Aure suzo dasu watak'il suma su dace, cike da amincewa innar su Altine ta jinjina mata kai don itama ta tsorata da Maganar da tace bokanta yayi don tasan muddin asirin Yaya ya tonu to itama kuwa bazata sha ba, da sauri Yaya ta yunk'ura ta mik'e tace mata ta taso suje su nuna suna farinciki kar ayi tunanin wani abu, da sauri ta mik'e buguzun buguzun suka nufi kopa,

Lokacin da Kishiyar Yaya ta shiga d'akin su Yadikkon bata isketa ba sai su Aysha kawai, da fara'a ta k'arasa wurin su ta tambaye su innar su suka ce mata ta fita taje ta dawo ta jinjina masu kai, a bakin gado ta zauna don ta jirata, bata jima sosae ba Yadikko ta dawo dama wurin gwaggo taje, a k'asa saman Carpet ta fara k'ok'arin zama ganin tana zaune a bakin gadon da sauri tace mata ya zata zauna a k'asa tazo ta zauna a bakin gadon mana Yadikkon na murmushi tace mata ai ba komai, gaisawa suka k'ara yi don sun gaisa da suka tashi, cikin nuna tsananin farinciki tace mata taji abun Alkhairin daya k'ara samun su a bakin innar su Altine taji dad'i sosae wllh, Addu'oi ta shiga yi Yadikkon sai murmushi take a cikin ran ta take amsawa Saboda nuna kunya ba kamar da Mino take y'a ta farko a wurinta, suna haka sai ga su Yaya sun turo k'opar kamar an jefo su gaba d'aya suka sauke idanun su cikin na kishiyar tata tana ganin su ta kauda fuskar ta, k'arasa shigowa ciki sukai ganin yadikkon zaune a k'asa yasa suma suka fara k'ok'arin zama a kan Carpet d'in, cikin girmamawa Yadikko tace masu don Allah su zauna a kan gado mana duk suka ce a'a bari dai suma su zauna a k'asan, gaisawa suka shiga yi sai faman washe baki suke kaman wad'anda akai ma Albishir da Aljanna su duk k'ok'arin da suke shine asan suna murna, bayan sun gama gaisawar ne suka shiga taya ta murna suna fad'in wllh sunyi farinciki jin abun Alkhairi da ya k'ara samun su, innar su Altine harda cewa ai ita d'azun tsabar farinciki ne ma yasa ta kasa cewa komai ta tashi da sauri ta nufi d'akin su don ta sanar ma dasu Yaya suma,

Yaya ma cikin washe baki take fad'in ita shiyasa bata ta6a k'alubalantar komawar su binni ba wllh Saboda tana ji a jikinta hakan zai zame masu Alkhairi ashe kuwa hakan ne aikuwa su Aysha ma sai a maida su can binnin suma kawai, jin hakan har saida kishiyar tata ta d'an yi guntun murmushi ta ta6e baki ita kanta Yaya da tayi maganar duk ta bi ta kama kanta har d'an d'aga kai tay ta kalli kishiyar tata ita dai Yadikko murmushi kawae take don gaba d'aya farinciki ya gama cikata, Mero ce ta fara tashi tana k'ara taya yadikko murna ta nufi k'opa ta bud'e ta fita, kallon juna Yaya da innar su Altine sukai duk sun yi kalar rashin gaskiya, mik'ewa Yaya tay tana washe baki tace ma Yadikko bari taje ta idasa kimtsa kaya jin haka yasa innar su Altine itama ta mik'e tace haka, bin su da ido yadikko tay har suka fita, lokacin da suka koma d'akin nasu Mero na zaune a bakin gado jakar kayanta a gabanta ko kallon su bata yi ba, wurin ta Yaya ta nufa ta tsaya daga gaban ta sai lokacin ta d'ago ta kalleta, cikin kwantar da murya Yaya tace "ina son ki sani Wallahi tallahi kwarankwasa gajimare ni bani na kashe Fatima Mahaifiyar Muhammadu ba, koda kika ji nace na muzguna mata har Allah ya amshi abun shi bawai nice na kasheta ba, nasan da zalunce ta tun bayan da Ard'o ya auro ta na fahimci ba K'aramin son ta yake ba na fara muzguna mata k'arshe na had'a mata da asirin daya sa Ard'on ya rink'a gudun ta duk aka tsaneta to bak'in cikin hakan ne ya haifar mata da ciwo har yay tsanani Saboda ba'a kulawa da ita k'arshe ta rasu, ita kuma Aisha Mahaifiyar inna wuro sau d'aya nayi yunkurin yi mata Asiri don in raba su Saboda tana yar binni tafi sauran matan Y'ayana komai amman sai boka yace man bazai iya ba Saboda tana da iskokai masu zafi bazasu bari Asiri yayi tasiri ba a kanta gara in rabu da ita don zasu iya maido shi kaina, to daga nan itama na rink'a nuna mata tsana har tazo ta kwanta ciwo akai tunanin na iskar ta ne ashe cuta ce a cikin cikinta amman ni wllh bani da sa hannu a cutar" idon Mero a kanta har ta gama sannan ta sauke ajiyar zuciya tace ai Mahaifiyar Muhammadu itace tay silar mutuwarta don haka alhakinta na akanta gashi ta rasu balle ta rok'e ta yafiyar abunda tayi mata, a k'arshe tace mata tana bata shawara ta tuba ta daina shirka don malamin su dake koya masu karatun Addini yace itace laifin da Allah bai yafewa in aka mutu ba'a tuba ba sannan kuma duk wanda ta zalinta tun wuri ta nemi yafiyar shi don Allah bai yafe hakkin wani a kan wani, cike da nadama Yaya tace to yanzu ya zatay da hakkin Fatima data mutu, shiru Mero tay can ta nisa tace to ita gaskiya bata sani ba amman zata tambayi malamin su kuma suma yakamata su rink'a zuwa karatun hakan zai sa su daina aikata wasu abubuwan, atare suka had'a baki wurin cewa to zasu rink'a zuwa da sun koma, a marairaice Yaya tace mata to don Allah zata rufa mata Asiri Meron tay d'an murmushi tace ai ita bata isa ta tona mata Asiri ba in Allah bai yarda ba in kuna yaso ko ba ta silar ta ba to sai asirin nata ya tonu, sosae jikin Yaya yay sanyi lakwas kamar an watsa ma kaza gishiri.

Bayan Fauzy ta gama shirin ta cikin bak'ar jallabiya tay rolling veil d'in ta, jakar wayarta ta d'aukko ba tare data bari kowa ya ankare ba don duk suna zaune a saman gado basu dad'e da gama yin murnar labarin da Mino ta shigo ta basu ba na neman auranta da akai, fitowa tay daga part d'in nasu ta nufi cikin gidan, part d'in Mom ta nufa lokacin data shiga a parlor ta isketa zaune itama jikinta sanye da jallabiya, tana murmushi ta kalli Fauzyn ta nufeta itama da murmushi akan fuskar ta, k'ok'arin zama take akan Carpet Mom ta nuna mata kujera tace ta zauna mana, bayan ta zauna gaishe da ita tay still da murmushi ta amsa mata, shiru suka d'an yi kafin tace mata ana ta shiri ko Fauzy ta d'aga mata kai a hankali tace eh tay Addu'ar Allah ya kai su lafiya ta amsa mata da Amin, shiru ta d'an yi kafin ta tambaye ta Zarah na nan tace mata eh ta shiga tana ciki, mik'ewa tay ta nufi hanyar Bedroom d'in, lokacin data shiga Fatuu na kishingid'e a gefen gado idon ta akan Tv tayi wanka tana sanye da doguwar rigar material mai red flowers ta yafa d'an jan gyale a kanta, jin sallama yasa ta kai idon ta kan kopar shigowa ganin Fauzy yasa ta washe baki tana gyara zaman ta, nufota tayi ta tsaya daga gabanta tana fad'in "mai ciki" dariya Fatun tay tayi mata alamar ta zauna da hannu, a gefenta ta zauna daga bakin gadon,

"Kina ta hutawa abun ki" Fauzy ta fad'a idon ta akan Fatun tana murmushi, itama murmushin take jin abunda tace sai kuma tace "wllh har na fara gajiya ma ni, daga ci sai kwanciya in nayi wani aiki to bai wuce zuwa toilet fa" yar dariya tay "tun yanzu, duka mi akai a bed rest d'in" d'an tura baki tay "wllh ji nike inama ku tafi da ni duk naji na damu da tafiyar da zaku yi" d'an shiru Fauzy tay tana murmushi sai kuma tace "ai ba yadda za'ai a tafi dake tunda ga halin da kike ciki, amman yanzu ni abunda ma yafi damuna shine ya za'ai da School kinsan ranar Wednesday d'in nan zamu koma tunda dama hutun 2 weeks ne" yanayin fuskar Fatun ne ya d'an canza tace "nima harda ita yasa na damu nike jin dama in bi ku, amman zan ma Hubby magana kan hakan tunda bai yuwuwa in zaune anan ana can ana karatu tunda ba wani ciwo nike ba ba sai na dad'e anan ba gaskiya" kai Fauzy ta jinjina,

shiru suka d'an yi sai kuma Fauzy tace "sai muka ji abun farinciki an nemi auren Mino wllh nayi matuk'ar murna baki ji ba" fad'ad'a murmushi Fatuu tay tace "wllh abun fa abun farinciki, ke ni farko ma da baffa ya kira ni ya sanar man tsabar mamaki kasa rufe baki nay jin abun kamar wasa duka yaushe suka had'u amman har an tsaida magana, sosae na taya Mino murna don Nameer sam bai da matsala wllh"
"Haka abun Allah yake matuk'ar ya k'addaro abu sai kiga ya faru aita mamaki" kai Fatuu ta d'aga,

"da rabon zamu k'ara zuwa shan wani shagalin don wllh bazan 6oye maki ba na nishad'antu da dukkan shagalin da akai kar ma dai dinner d'in nan duk aka zauna sai an tada zancen ta"

"Ai naga har wak'e ki akai Hajiya Fauziyya mai ruwan Naira, wai ni don Allah ina kika samu wad'annan kud'in da kika rink'a man wanka da su" Fatuu ta tambaya tana murmushi idon ta akan Fauzy, murmura mata ido tay tace itama samun su tay daga sama, kafin Fatun tace wani abu ta d'ago jakar da ta shigo da ita ta mik'a mata, amsa Fatuu tay ta bi jikinta da kallo kafin ta maido kallon kan Fauzy alamar rashin fahimta, ce mata tay ta duba abun ciki, hannu ta kai ta fiddo kwalin wayar saida tay d'an jimm tana kallo shi kafin ta fara k'ok'arin bud'e shi, bayan ta fiddo wayar bin ta tay da kallo tana d'an Jujjuya ta,
"Wannan irin wayata ce" kai Fauzy ta d'aga mata,
"ta waye?" Fatuu ta tambaya, shiru Fauzy tay tana d'an murmushi Fatun nata kallon ta alamar jiran Karin bayani,

"tawa ce wai, Cousin brother d'in Ya Haisam ya siya man" wani kallon rashin fahimta Fatuu ke bin ta da shi tace mata wane cousin brother d'in nashi, jimm Fauzy tay kafin ta bata amsa da "Sameer" a wani slow Fatuu ta fara bud'a idanunta tare da bakin ta duk a lokaci d'aya har saida taba Fauzy dariya,

"Sameer fa kika ce! Wai wane Sameer d'in kike nufi?" ce mata tay wanda dai ta sani,

"kina nufin wai Sameer Sameer d'an Governor???" Kai Fauzy ta jinjina mata, k'ara bud'e baki Fatuu tay idanu waje cike da tsantsar mamaki take kallon Fauzy tama kasa magana can ta sauke numfashi ta furta "this is unbelievable! Sameer ya siya maki wannan wayar! amman wai...taya akai kuka san juna ma tukun" Fauzy sai dariya take ganin yadda kan Fatun ya d'aure, labarin yadda akai suka san juna ta fara bata tiryan tiryan har da kud'in lik'in da ya bata zuwa jiya da ya bata wayar, lokacin data gama fad'i mata hannu Fatuu ta kai ta rufe bakinta tana dariya,

"Yau da alama so kuke ku kashe ni da mamaki, Mino da Nameer an tsaida Maganar Auren su yanzu kuma ga ke da Sameer, wayyo dad'i kashe ni" Fatuu tay Maganar tana yarfa hannu, Fauzy dake ta dariya tace mata ai ita fa ba wani abu ke a tsakanin su ba, katseta Fatuu tay tace "ke dalla ai daga haka ake farawa, ga misali nan tsakani na da hubby dana fasa mashi glass duk da ni daga haka zumunci ne ya k'ullu kema shine zai k'ullu amman na soyayya in sha Allah" ta k'arasa Maganar sai faman washe baki take itama Fauziyyar dariya take can Fatuu tace "Allah ubangiji ya tabbatar da abun nan kai, wllh sai nafi kowa farinciki, zan so in ga Fuskar mayaudarin nan Muntari yake kowa, wannan babban kamu haka ai nasan wllh sai ya girgiza in ma bai zauce ba, kinsan da yawan mutane basu son su rabu da kai suga kuma kazo kaci gaba" girgiza kai Fauzy tay tana ta dariya jin sunan da Fatun ta kira Mujaheed,

"Wai ku sai faman Maganar soyayya kuke haka ma Aunty Mareeya duk ta bi ta rud'e, nifa bai ce yana sona ba, mutumin da in banda harara da tamke fuska ba abunda yake man wannan ne son?"

"Ai kin san kowa da kalar nashi salon soyayyar ba kamar da shi ga yadda halin shi yake, amman mutum kamar Sameer da kwata kwata bai shiga harkar mutane yake maki haka kuma tun farko ga abunda ya had'a ku laifi kikai mashi amman shine harda baki kud'in lik'i da yi maki Maganar yaushe zaki aure uwa uba ya siya maki wannan tsadaddar wayar, haba Fauzy, kema dai kin so a ja Maganar ne kawae Allah, ai koda baki soyayya kefa ba yar primary ko Secondary bace ko Yaya ne zaki gane in mutum na son ki, ke dai Allah ya tabbatar mana yasa komai yazo cikin Sauk'i kamar nasu Nameer, aikuwa zanje in zuge Aunty Mareeya ta koya maki yadda zaki kama mana shi a hannu don na lura kina buk'atar lakca gaskiya duk Muntarin nan yasa kin rasa karsashi ta wannan fannin kuma irin su Sameer sai anasa karsashi a yin love da su" dariya sosae Fauzy ke yi tana fad'in Allah ya shirye ta, tambayar ta tayi har su Haulat sun shirya ne suma tace mata eh ba wanda bai shirya ba, sake tambayar ta tay taga Mom da zata shigo tace mata eh tana a parlor zaune, maida wayar Fatuu tay tana fad'in Allah yasa Alkhairi ya tabbatar masu da abunda suke fata, saukkowa daga gado Fatun tay tace mata suje tana son zuwa part d'in Hajiya ne, a tare suka fito har lokacin Mom na zaune a cikin parlon, kai idon ta tay kan su tana kallon su da d'an murmushi suka nufo ta, daga d'an can nesa da ita suka zauna Fatuu tay mata sannu ta amsa mata, shiru sukai tana son yin magana ta kasa Mom data fahimci hakan tana murmushi tace "ya akai Daughter ko akwae wani abu ne?" a sanyaye tace mata dama part d'in Hajiya take son zuwa zata bada sak'o, jinjina mata kai tay tace Ok taje amman ta kula tana murmushi ta d'aga mata kai, har zasu mik'e tace yama sunan Fauzy suka fad'i mata,ce mata tay ta tayata kulawa tana murmushi tace mata to, bayan sun fito daga part d'in Fauzy tace ma Fatuu wai wannan cikin nata in ta haihu shine jika na farko a gidan ko tace mata eh, Fauzyn tace haba shiyasa wannan gata haka wani abun ma sai an haiho babyn ita dai Fatuu murmushi kawae take, bayan sun iso part d'in Hajiyar a parlor suka tsaya suna gaisawa da Mutanen ciki duk akai ma Fatun ya jiki ta amsa, wucewa sukai bedroom da sallama Fatuu ta shiga Fauzy na biye da ita, Hajiya na zaune a bakin gado gwaggo kuma nata had'a kaya duk suka amsa masu sallamar tasu, ciki suka shigo fuskar Hajiya a sake take kallon su haka gwaggo ma data d'ago tana kallon su, daga gefen gadon suka tsaya suna gaishe dasu bayan duk sun amsa Hajiya ta nuna masu bakin gado tace su zauna mana sun toge anan, duk suka zauna,

"Hala an zo bankwana da Dije, ai da kin bari zata iske ki can sai kuyi bankwanan" Hajiya ce ta fad'a Fatun tay murmushi kawae haka Fauzy da gwaggon, tana son yi ma gwaggon Magana amman ta kasa sai bin ta da ido take, ganin yadda take ta kallon ta yasa tace mata ya akai, juya harshe tay ta fad'i mata abunda take son fad'i mata dama Haulat take son ba kyautar atampa a cikin kayanta, itama cikin harshen fulatancin tace mata itama tana son a bama su Yaya amman taga kayan duk manya ne kar ayi ba daidai ba,

"In sirri kuke son yi ai sai kuce in baku wuri ba ku canza harshe ba in d'auka gulmata kuke" Hajiya ta fad'a ta d'an kwa6e fuska duk sukai dariya, gwaggo ce tay mata bayanin cewa wai tana son ba k'awar ta atampa ne shine itama take ganin ya dace a ba su Yaya da yadikkonta amman bata san ko zasu iya hakan ba, hannu Hajiya ta kai ta ruk'e ha6a tace "Oni yasu, to Dije mi zai hana, ai kaya yanzu sun zama naku waya isa ya hana kuyi yadda kuke so da su in banda abun ki" gwaggo na murmushi tace dama wai taga kayan manya ne Hajiyar tace to ko manyan ne fa ai dai nata ne ko, kuma ai akwae atampopi suna nan da ba'a d'in ka ba tasan k'ilan bai wuce ma don hakan yasa ba'a d'inka su ba tunda yawancin kayan duk an d'inka, duk abunda zaku bada ku bada ba ruwan kowa da wannan" godiya gwaggo tayi mata tana yar dariya sai kawai ma Hajiyar ta mike ta nufi hanyar fita, Fauzy gwaggo tay ma magana ta mik'e taje suka sauke akwatunan, na kayan suka fiddo bayan an bud'e gwaggo tace ma Fatuu ta zo ta d'aukar ma Haulat d'in, wata atamfa mai golden tayi kyau sosae ta d'aukar mata, Su Yaya da Kishiyar ta da Yadikko suma duk atampopin aka d'aukar masu, ta Yadikko ma glitter ce mai kyau, wani lace tasa aka d'aukar ma k'annanta su Aysha sai k'awarta Zainab ma ta d'aukar mata wata sarka da yan kunne masu kyau dama ankon lace d'inta ta bar mata, su Aunty Mareeya ma da Feenah da Saude yan kunne fashion aka d'aukar masu kai da gani kasan zasu yi kud'i don ba k'ananu bane, akwatin cosmetics tasa Fauzy ta bud'e mata ta k'ara ma su Aysha da kayan shafa, gudun abun kar yay yawa yasa gwaggo da fullanci tace mata a bar su haka Fatun tace da su Baffan ta take son d'aukar ma shadda tace mata a'a an basu ta k'yale su in ma tana son basu ta bari a basu daga baya, Fatun tace to bari a basu ko turare ta d'aukar masu guda ukku daga haka gwaggo tace to a bashshi,

kallon Fauzy Fatuu tayi tace mata ta d'auki duk abunda take so da sauri ta girgiza mata kai tace wllh ba abunda zata d'auka duk uwar hidimar da akai dasu ga anko mai tsada har kala biyu gwaggo dai murmushi kawae take, madaidaicin akwati aka d'auko bayan an kwashe kayan cikin shi an maida cikin wani suka zuba kayan da suka d'aukar a cikin shi har Fauzy zata rufe Fatuu ta dakatar da ita, wani akwati ta nuna mata tace don Allah ta d'aukko mata, bayan ta jawo mata shi tasa ta bud'e, had'add'un dogayen riguna ne a ciki duk a Dubai aka siyo su Fatuu ta kai hannu ta ciro wata army green mai shegen kyau tasha adon stones, bayan ta saka cikin kayan tace ma Fauzy ta rufe, maida akwatunan sukai yadda suke da, tambayar gwaggo Fatuu tay jakarta da ta zuba kud'in da ta samu ranar Walima dama ita taba ajiya, bayan ta d'aukko mata ta bud'eta cikinta dankam take da kud'i, envelope d'in da Alhaji Lawal ya bata ta fiddo ta bud'e, kud'i ne a ciki bandir din yan dubu na dubu d'ari, maida su tay cikin envelope d'in ta d'auketa bayan ta rufe jakar ta mik'a ma gwaggo tace to ita da zasu tafi, ce mata tay ta tafin mata da ita kawae ba abunda zata yi da su don tana da kud'i sosae a account d'in ta.

A tare suka fito daga cikin d'akin Fauzy na janye da akwatin kayan, a parlor suka iske Hajiya zaune tace ma Fatuu ta k'yale su suje ita ta koma taje ta natsu wuri guda a marairaice tace mata tana son yin sallama dasu ne, lokacin da suka isa part d'in bayan gaba d'aya a parlor suka iske su don Abbas ya kira Feenah yace bada jimawa ba zasu tafi su zama cikin shiri, gaishe gaishe aka shiga yi ana k'ara yi ma Fatuu ya jiki bayan sun gama gwaggo tasa Fauzy ta bud'e akwatun, fiddo kayan su Yadikko tay harda turarurrukan su Ard'o ta nufi d'akin da suke don ta kai masu, suma na nan parlon Fauzy ta shiga fiddo na kowa tana bashi farko duk cewa sukai don Allah a bashshi banda duk uwar Hidimar da akai masu, saida gwaggo ta fito ta saka baki sannan suka amsa suna ta godiya da Addu'oi cike da Farinciki su Yadikko ma duk suka fito suna nuna masu nasu sai murna suke karma su Yaya da innar Altine su ji sam sun kasa rufe baki, fiddo kud'in da Fatuu tazo dasu tay ta shiga ba kowa dubu biyar biyar Haulat dae dubu talatin ta bata harda wanda zata yi kud'in Motar komawa Niger, nan fa parlor ya kacame anata farinciki Aunty Mareeya harda cewa in haka ake yin biki ai ba abunda zai hanata zuwa in dai ba ciwo ya kai ciwo ba duk aka sa dariya dama tun ran Asabar duk aka basu abubuwan da akayi na bikin, fakaitar idanun mutane Fatuu tay ta d'aukko trolley d'in Fauzy dake a cikin parlon, bud'e shi tay ta d'aukko jallabiyar da ta sako cikin kayan ta tura acikin akwatin kayan Fauzy data lura saboda a kusa da ita take tana niyyar yin Magana ta hau yi mata magiyar kar tace komai, wani kallo tay mata mai kamar harara Fatun ta saka dariya,

Gaba d'aya tare suka fito lokacin wuraren k'arfe goma yan Katsina da yan Adamawa harda wasu yan Daura, a gaban Entry Hall aka jere Motocin gaba d'aya duk an fito da yan tafiya da yan rakiya su Hajiya, Mom, Laila, Fanan, nan aka shiga yin bankwana Haisam da Abbas na daga can gefe sun jingina da Motar Abbas haka su Kawu Amadu da Tk da Kamalu ma duk suna gefe, Jidderh Saboda tafiyar tasu dama tak'i zuwa School Aunty dae ta tafi wurin aiki dama tayi sallama dasu kafin ta tafi Fatuu ji take kamar a tafi da ita, had'a ido sukai da Haisam ta yamutsa fuska ya saki murmushi don ya gane mi take nufi, Mino ma sai kallon love suke ita da Nameer suna sakar ma juna murmushi, Dad ne ya fito tare dasu Ard'o Fatuu ta nufe su ta gaishe su duk suka amsa Dad yay mata ya karfin jiki tace Alhamdulillah, kallon Baffan ta dake ta sakar mata murmushi tay itama murmushin take mashi sun kasa ce ma juna komai, kud'i Dad ya fiddo ya shiga raba ma duk masu tafiya aka hau godiya daga baya suka fara shiga cikin Motocin bayan an sassaka kayan su, d'aga ma juna hannu suka shiga yi kamar kar a rabu a Kusan tare duk suka tashi Motocin suna ta cigaba da d'aga ma juna hannu a haka suka tafi sai fatan Allah yasa a sauka lafiya, tsaye Fatuu tay idanun ta sun ciko da k'walla gaba d'aya har kewar su ta fara kamata, bayan barin Motocin aka tuk'o wadda Senator zai hau ta tsaya a gaban wurin dama a shirye yake, sallama yay da iyalin nashi duk sukai mashi sai ya dawo bayan an bud'e mashi k'opa ya shiga suka tafi, Haisam ne ya matso gaban Fatuu suka had'a ido a shagwabe ta tura mashi baki yay murmushi, Hajiya ce tace mata to suje ya kai hannu ya kamo hannunta duk kunya ta kamata suka nufi cikin gidan........

87

.......Alhamdulillah matafiya duk anyi waya da su sun isa lafiya gaba d'aya sai fatan Allah ya huta gajiya, bayan sallar isha Fatuu ta gama sallar tana zaune a saman gado jikinta sanye da voile material pink d'inkin riga da skirt tayi d'aurin kallabi mai kyau daga cikin kayan lefenta ne yayi mata kyau sosae, ruk'e take da wayarta tana bin chat d'in group d'in su na School da ake hirar komawa Makarantar bayan sun gama taya Fatuun murna data tura masu pics d'in bikin nata da akai,

Haisam ne ya shigo cikin d'akin jin sallama yasa ta d'aga ido ta kallo shi, k'arasowa yay ciki idon shi akanta suna ma juna murmushi, ta gefen inda take ya zagaya ya zauna a bakin gadon ta gaishe dashi ya jinjina mata kai, hannu ya kai ya shafi fuskar ta yace "Ya jikin ki?" tana murmushi tace mashi itafa lafiya lou take jin ta wllh, kai ya d'aga sai kuma yace to ya Baby d'in su tace yana nan lafiya bacci yake yanzu amman d'azun da suna fira yace ta gaishe mashi da Dad, dariya duk sukai yace Baby Boy ne kenan tace tana dai Fata amman duk wanda ta samu tana so ya jinjina mata kai, tambayar shi tay shi mi ya fi so ta haifa tun kan ta rufe baki ya girgiza mata kai yace kamar yadda ta fad'a duk abunda ta haifa zai yi farinciki yana fatan Allah ya k'ara mata lafiya da Babyn yasa ta haihu lafiya tana ta murmushi ta amsa da Amin, hannu ya kai ya jawota jikin shi da sauri ta shiga k'ok'arin kwacewa yay mata wani kallo, d'an yamutsa fuska tay tace mashi Mom take tsoron ta gan su haka, d'age mata gira yay yace in ta gan sun sunyi laifi ne a shagwa6e tace "to ai Hubby da kunya fa ka manta jinya nike" yadda tay Maganar ne yasa shi yin yar dariya har hak'oran shi suka bayyana, jawota yay sosae ya rungumeta a wurin kunnanta ya rad'a mata to Mom d'in bata nan sun fita da Aunty, shiru tay ta d'an ji hankalinta ya kwanta dama lokacin da ta gama sallar isha tana zaune kan prayer mat tana Addu'a taga shigowar ta bata jima ba kuma ta fita bayan ta yafa mayafi, tun bata saki jiki ba har dai ta saki ganin shi ba abunda ya dame shi, Maganar School tay mashi tace ran Wednesday suke komawa, jinjina mata kai yay yace ta bari zasu koma taci gaba da zuwa amman ba yanzu ba sai an d'an k'ara lokaci in ta kama sai ayi Magana can school d'in ta d'aga mashi kai, Wayar shi dake ruk'e a d'ayan hannun shi ya d'ago ya fara daddana ta idon ta akan Wayar, hotunan wasu Motoci ya fara nuna mata tana ta kallo har ya kai k'arshe guda Kusan Goma ne, maida idon shi kan Fatuu yay yace ta gan su ta d'ago ta kalle shi tace eh, tambayar ta yay wacce tayi mata da alamun rashin Fahimta tace bata gane abunda yake nufi ba, shiru ya d'an yi tana ta kallon shi kafin taji yace yana nufin tay choosing wadda take so a ciki, waro ido Fatuu tay da tsananin mamaki take kallon shi shima kallon nata yake da murmushi,

"Amman Saboda mi to zan za6a" ta tambaya da alamun mamaki yace mata Saboda za'a kawo mata ne, k'ara zaro ido tay ta furta "Motar!" Kai ya d'aga mata had'i da d'an lumshe ido a shagwabe tace "ni dai Hubby a'a ka barshi ba duk akwae Motoci ba har acan gidan Hajiya ma" kallon ta kawai yake sam bai yi mamakin jin hakan ba don yasan halin ta kan hakan bata son ya kashe kud'in shi yay mata abu in bai zama dole ba gashi kuma ita ba tambayar shi abu take ba, ganin kallon da yake mata yasa ta fara tura mashi baki ya kai hannu ya d'an matse bakin ta yi d'an sauti alamun taji zafi, sigh yay yace shima kyauta ce zai bata kan wadda ta bashi cike da shagwaba tace to ai ita ba ita ta bashi ba ko Allah ne ya bashi, yana murmushi yace yasan da wannan amman ai a jikinta yake ko, yamutsa fuska ta shiga yi yana murmushi yace mata wannan ce kyauta ta farko da ya fara bata a matsayin su na ma'aurata dole sai ta amsa tace ba ga uban lefen da yayi mata ba nan, ce mata yay Wannan ai ba gift bane tunda ya zama al'ada kuma bashi kadae yayi shi ba, sai shagwaba take mashi kanta na a kan shoulder en shi da alama ma ta manta da inda suke, bud'e mata Motocin yay yace in bata za6a ba bazai ji dad'i ba yayi zaton zatai murna ne ya bata gift in kuma wannan bai mata ba ta fad'i duk abunda take so, da sauri ta kai hannu ta tallabo gefen fuskar shi tace "a'a Hubby naji dad'i wllh kawae naga kaman wannan kyautar tayi girma ne kuma naga akwae Motocin" ce mata yay to su motocin dake akwae d'in nata ne ta girgiza mashi kai yace to yanzu ta za6a sai ya zama itama tana da nata ko, kai ta d'aga mashi tana murmushi har ta maida idanunta akan Motocin sai kuma ta d'ago da sauri tace "amman Aunty Fanan fa?" d'an murmushin gefe yay ya furta banda ita, waro ido tay sai kuma ta hau girgiza kai tace a'a don Allah bazata ji dad'i ba wllh itama gaskiya a bata yana murmushi ya furta Justice for Fanan da sauri ta d'aga kai tace eh, sosae yaji dad'in hakan data yi ta tabbatar mashi da Maganar da tayi mashi na zata taimaka mashi yayi masu Adalci, ce mata yay kada ta damu Fanan ma nada Mota a can Us ya siya mata ba'a dad'e ba,

"Da gaske?" ta d'age mashi gira shiru yay yana kallon ta, sake ce mashi tay da gaske yake ya siya mata yana murmushi yace "da k'arya" dariya ta saki don tasan wasa yake itama hakanan jan magana yasa ta tambayi da gasken tunda tasan bazai mata k'arya ba, maida idonta tay kan Screen d'in tace to bari ta za6a, gaba d'aya ta rud'e don kowacce ta had'u kama daga Camry, Hyundai, Corolla Mercedes da sauran su, wata Jeep ya bud'e har zai wuce da sauri tace mashi ya tsaya, k'ura ido tay tana kallon ta sosae ta burgeta don dama tana son Mota Jeep kuma tana son farar Mota to itama Jeep d'in fara ce, ganin tana ta kallon ta yasa shi ce mata tayi mata, jimm tay sai kuma ta d'aga ido ta kalle shi ya d'age mata gira alamar ta amsa mashi, kai ta d'aga ya furta Ok da d'an murmushi sai kuma da sauri Fatun tace "amman nawa take?" shiru kamar ba zai yi magana ba slowly yace tunda tayi mata Shikenan ai mi zatai da kud'in ta, a shagwabe tace ita dai ya fad'i mata gaskiya in mutum zai siya Mota ba sai an fad'i mashi kudin ba, dariya yay bai san ranar da zata daina wauta ba, ce mata yay to ita siya zata yi ne,

"eh ai tunda kai zaka siya man to kaman ni zan siya ko" ta k'are Maganar ta d'an tura mashi baki, d'an lumshe mata ido yay ba zato taga ya matso da face d'in shi yay pecking lips d'in nata ta d'an waro ido ya d'ago yana murmushi, rigimar sai ya fad'i mata kud'in Motar taci gaba da yi ya tambayi to mi zatai wai in taji kud'in tace hakanan take so taji, still murmushi yake wasu abubuwan ta kaman Hajiya, ya gane wai wayo take son yi mashi in taji tayi kud'i sosae tace bata son ta, girgiza mata kai yay yace an gama Magana ba sai taji ba shima ba siya yayi ba, k'una k'uni ta fara tana ita dae Allah bata yarda ba tunda shi yace ta za6a to ya fad'i mata kud'in, gaba d'aya yadda take mashi ta tafi da shi sai kallon ta yake dama d'an kwana biyun nan har ya fara jin kewar ta a tare da shi, ganin irin kallon da yake mata ne yasa ta dakata da abunda take suka zuba ma juna ido breathing d'in su na had'uwa, sun d'an d'auki lokaci a haka fuskar Fatuu da d'an murmushi kawai sai gani tay ya matso da fuskar shi ya had'e da tata, had'e lips d'in su yay farko fara k'ok'arin kwacewa tay amman yak'i bata dama daga baya kuma ta biye mashi don itama tayi kewar hakan,

"To, to da kyau, sannun ku da aiki" kaman daga sama suka ji an fad'i hakan gaba d'aya sai da suka d'an firgita da sauri Fatuu ta janye jikinta daga nashi a tare suka juya don ganin mai Maganar, Hajiya ce ta shigo tana dogara sandar ta jikinta sanye da kaftan ta atamfa tayi d'aurin kallabi irin nasu na manya idanunta sanye cikin glasses, wata irin kunya ce ta rufe Fatuu da sauri ta sunnar da kanta duk da bata san ko taga abunda suke ba don sun ba kopar shigowar baya to amman gaba d'aya tana a jikin shi ya tallabe ta a ranta ta raya da k'yar in bata ga abunda yake matan ba, idon Haisam a kanta har ta k'araso ciki ta tsaya daga gaban su ta d'aure Fuska, murmushi yay ya gaishe da ita ta wurga mashi harara tace "Yanzu miye wannan d'in, kasan halin da yarinyar nan take ciki amman shine bazaka iya hak'uri ka bari tabi dokar likita ba ta samu hutun da take buk'ata saboda tsabar jaraba, anya Haisam!" ta k'arasa Maganar ta d'an 6ata rai, still Murmushi yake ya d'an d'age mata gira yace "Yanzu nayi wani laifi ne" a fusace tace bata sani ba, yar dariya yay yace in dai hutu ne ai gashi tana hutawa ko, kwabe fuska tay ta jinjina kai tace eh tabbas ta gani hutawa take, maida idon ta tay kan Fatuu da tai tsumu tsumu kanta a k'asa ji take kaman ta nutse a wurin, ce mata tay ta tashi ta gama hutun anan don ba barin ta za'ai tayi yadda ya kamata ba, zuru da k'afafun ta tay still bata kalli Hajiyar ba ta mik'e, da sandarta tayi mata nuni da hanya tace su je, har zata tafi sai kuma ta dakata Hajiya ta tambayi ya akai k'asa k'asa tace zata d'auki kayanta ne, tambayar ta tay suna ina da k'yar ta d'an d'ago tay mata nuni da inda trolley d'in ta yake, nufar wurin tay tana dogara sandar, jawo shi ta shiga kokarin yi Haisam dake zaune yay yar dariya ya mik'e, wurin ta yaje yace ta kawo ya taimaka mata fuska a d'aure ta kalle shi tace bata so, hannu ya kai ya amshi akwatin ya fara ja Hajiyar ma ta fara tafiya da sauri Fatuu ta juya ta nufi k'opa sumi sumi,

Sun rigata zuwa bakin part d'in nata cikin d'an d'aga murya tace ma Haisam ya aje akwatin nan kar ya shigar mata d'aki ya kama gaban shi murmushi kawae yake ya shige dama ita Fatuu tuni ta shiga, tsaye tay a parlor yana shigowa suka had'a ido a tare suka saki yar dariya suna haka Hajiyar ta shigo da sauri Fatuu ta juyar da kanta, tambayar ta yay a ina za'a aje akwatin tace bata sani ba ya aje a duk inda ya ga dama tunda dai ya raina ta ai saida tace kar ya shigo amman ya shigo, shiru yay can kuma yace mata to tayi hak'uri don ya rage mata aiki ne kawai ba wani abu ba, kaman bazata tanka mashi ba sai kuma tace to ta gode yaje kar kuma ya sake ta k'ara ganin k'afafun shi a part d'in ta, yana dariya yace ai wannan dole ne ya zata d'aukko mashi mata tace kuma kar yazo ai dole yazo ko don ya duba tafiyarta ko, hararar shi tay tace ko don fitina dai, maida idonta tay kan Fatuu dake kallon gefe tace ta wuce ta shiga cikin daki ta nufi hanyar shiga d'akin ba tare data kalle su ba, hannu Haisam ya kai zai d'auki akwatin yana fad'in bari ya shigar mata da shi aikuwa ta d'aga sandarta zata kwad'a mashi da sauri ya kauce yana dariya yace "Sweetheart yau ni zaki buga" fuska a d'aure tace ai bai fi k'arfin shi ba in dai bai fita ya bata wuri ba Allah zata bubbuga nashi ita, cewa yay Allah ya bata hak'uri bari ya fita ai duk abu mai sauk'i ne, saida safe yay mata a dak'ile tace Allah ya tashe su lafiya ya juya ya tafi, d'an murmushi tay ta girgiza kai bayan ya fita ta kai hannu ta kama trolley d'in ta nufi Bedroom, lokacin data shiga Fatun na zaune a bakin gado suna had'a ido da sauri ta janye nata ta koma kallon k'asa, cikin d'akin ta nufo tazo bangaren da Fatun take zaune ta aje trolley d'in a wurin sauran akwatunan, juyowa tay ta kalleta ta tambayi taci Abinci a hankali tace mata eh bayan Magrib taci, "to yanzu kina jin yunwa" girgiza mata kai tay alamar a'a tace to ta kwanta, idasa hayewa gadon tay ta kwanta tay lamo duk tayi kalar rashin gaskiya, wucewa Hajiya tay ta nufi hanyar fita, jin fitar ta yasa Fatun d'ago kai ta kalli k'opar sai kuma ta saka dariya, wayarta ce ta fara ringing da sauri ta kai hannu ta d'agota taga Haisam ne ke kiran, picking tay tana kara wayar a kunne ta saka mashi dariya shima ita yake yi sai kuma a shagwabe tace mashi yaga abunda take ta gudu kenan yace kar ta damu ai ba wani abu bane kawae Hajiyar ce ta d'auke shi a wani abu, tambayar ta yay mi take yi tace mashi gata nan ansa ta kwanta yadda tay Maganar har saida ta bashi dariya itama ita take ta yi,

"Ina Hajiyan?" Ya tambaya, tace mashi ta fita k'ilan tana parlor ya furta Ok bari ya k'yaleta ta huta kar su k'ara wani laifin, har zai mata saida safe sai kuma ya tambayi akwae abunda take so tace mashi eh cike da kulawa yace Ok minene tace "Kai" maimaita abunda tace d'in ya yi tace "Eh Hubby, kai nike so" tana jin sautin murmushin shi yace mata ai shi ta riga ta same shi, cike da tsokana tace "to baby yace so yake ya kwana a part d'in Dad d'in shi sai kazo ka d'auke shi ko ka d'auke ta" yana dariya yace saidae yazo ya d'auki Maman Baby wanda daidai yake da tada yak'i tsakanin shi da Hajiya, labarin buga mashi sanda da tace zatai ya bata Fatun nata dariya, sai da Safe sukai ma juna cike nuna k'auna da kuma kewar juna,

Bayan su Mom sun dawo tana shiga Bedroom d'inta taga ba Fatuu bata kawo komai a ranta ba tay tunanin ko tana wurin Jidderh, bayan ta rage kayan jikinta a cikin Laundry room ta wuce toilet don yin wanka, tana cikin yin shafa Jidderh ta shigo zata fad'i mata abu nan ta tambayi Fatuu na d'akinta ne tace mata a'a ita rabon ta da ita tun kafin Magrib data shigo nan ta duba ta, bayan ta gama shiryawa cikin kayan bacci ganin har lokacin Fatun bata dawo ba yasa ta nufi k'opa, bayan ta fito daga part d'in nata part d'in Laila ta wuce tana shiga cikin parlon ta iske su zaune ita da Fanan duk suna sanye da k'ananun kaya suna kallo a Tv, maido kallon su sukai kanta jin sallamar ta suka amsa mata da murmushi, k'arasawa tay ciki ta zauna akan kujera Fanan ta gaishe da ita ta amsa Laila tace har sun dawo ta d'aga mata kai, tambayar ta tay Daughter na nan ne da alamun rashin fahimta ta tambayi wace daughter d'in tace mata Sis d'in Fanan d'an jimm tay don bata fahimci wadda take nufi ba, Fanan ce data gane tace mata Zarah take nufi, yar dariya tay tace ai cewa zatay matar big bro Mom d'in tayi d'an murmushi kawae, ce mata tay bata nan ai rabonta ma da nan part d'in tun kafin ayi D'inner, d'an jimm Mom tay duk idanunsu na akanta Laila ta tambayi Lafiya, fad'i mata tay tunda ta dawo bata iske ta a bedroom d'in ta ba kamar yarda ta barta tayi tunanin tana a wurin Jidderh kuma bata nan shine tazo nan, ce mata Laila tay to ba sai ta kirata taji ba Mom d'in tace ai bata da no d'in ta,

"To ko dai Big Bro ya fita da ita bari a kira shi a ji don nima banda no d'in nata amman zan amsa ko don irin haka" jinjina kai Mom tay tace bata tunanin Haisam zai yi haka tunda yasan halin da take ciki, Fanan ce tace bari ta kirata sai aji, bayan ta kira layin Fatun ya shiga ta d'auka tana fara'a suka gaisa tace mata tana ina ne nan ta sanar mata tana d'akin Hajiya tace Ok sukai sallama, fad'i ma Mom inda take tay tace to ta mik'e ta nufi hanyar fita Laila na zolayarta tana fad'in duk hankalinta ya tashi kar ace ta 6atar da Amarya tana murmushi ta fuce,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.