Trending Hausa Novels

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Asanadin_Makwabtaka_Part_3_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 4 of 4

part d'in Hajiya ta nufa tana shiga parlon ta isketa zaune tana kallo, ciki ta shiga ta zauna kujerar gefen ta tana murmushi ta gaishe da ita itama fuska a sake ta amsa mata, shiru ta d'an yi can tace dama ta dawo ne daga unguwa da suka je bata iske Daughter ba tun d'azu shiru ashe tana nan, d'an ta6e baki Hajiya tay tace "eh tana nan ni naje na taho da ita nan kuma bazata koma ba" da sauri Mom ta kalleta da alamun mamaki ta tambayi Lafiya ba dai wata matsala ta faru ba,

"Ba abunda ya faru saidai matsalar ake k'ok'arin janyo mata a an k'i barinta ta huta kamar yadda likita ya bada doka" fuska a kwa6e ta k'arasa Maganar, har saida gaban Mom ya d'an fad'i a ranta ta shiga tunanin to mi take ma Fatuu da zata ce haka ita a iya saninta tana hutawa yadda yakamata amman gashi tace wai an k'i barinta ta huta , tana cikin zancen zucin ta ji Hajiyar taci gaba da fad'in "in banda jarabar tsiya k'iri k'iri fa yasan halin da yarinyar nan take ciki amman yaje ya bi ya kaddadabe ta shiyasa na maido ta nan ai sai in ga ta yadda zai rink'a zuwa wurin nata balle har ya takura mata" har saida Mom ta d'an ji sanyi don ta fahimci wanda yay laifin, d'an murmushi tay ta bata hak'uri Hajiyar tace Uhm kawai, mik'ewa Mom tay tayi mata saida safe cikin sakin fuska Hajiyar ta amsa mata ta tafi,

Misalin k'arfe goma da yan mintuna Senator ya shigo part d'in har lokacin Hajiyar na zaune a parlor tana kallo, amsa mashi sallamar da yayi tay idon ta a kanshi ya k'araso cikin parlon, zama yayi akan kujera gefen tata cike da girmamawa ya d'an sunkuyar da kai ya gaishe da ita tana murmushi ta amsa tay mashi an dawo yace eh, Ledar hannun shi ya mik'a mata yace ga furar ta, amsa tayi tay mashi godiya da sa Albarka ya amsa har zai yi magana ta riga shi fad'in da yayi ta wahalar siyo mata Furar kullum mi zai hana ya rink'a siyo ta kwana biyu tunda ga fridge nan sai ta saka, yana yar dariya yace mata ai ba abun wahala bane yafi son tana shan fresh ba wadda ta kwana ba kuma ai ba shi yake siyowa ba kawai dai shi yana shigowa da ita ne, jinjina kai tay alamar gamsuwa sai kuma ya k'ara cewa shi d'in ma zai iya zuwa ya rink'a siyo mata ai tunda neman Albarka yake, dariyar jin dad'i tay tace mashi wannan kullum cikin samunta suke koda ba furar saidae kuma don samun lada tunda tana jin dad'inta yana murmushi ya jinjina mata kai, d'ayar ledar ya d'ago yace ga ta Daughter nan yaje part d'in Mom ya kai mata aka ce ta dawo nan Hajiyar ta ce eh neman hanata ake ta bi dokar likita shiyasa ta maido ta nan, jinjina kai yay yana murmushi don Mom ta fad'i mashi komai, mik'ewa yay yace bari ya d'aukko mata cup tasha ko ta bi jiki tace mashi to ai taga ma kamar bata lalata ciki, d'an fridge d'in cikin parlon ya nufa ya bud'e bayan ya d'aukko cup d'in ya dawo wurinta da kanshi ya ciro robar furar ya zuba mata, bayan ta fara sha ya d'auki d'ayar ledar yace bari ya kaima Daughter d'in Hajiyar tace Allah yasa ma bata yi bacci ba saida tace mata in zatai kallo ta fito tace a'a kwanciya zatai, Bedroom d'in ya nufa saida yay sallama sau biyu sannan k'asa k'asa ya jiyo Muryarta tana amsawa, shiga yay Fatuu data d'ago kai tana ganin shi da sauri ta tashi zaune dama a kishingid'e take suna chat da Haisam da kuma Fauzy, cikin d'akin ya shigo ya tsaya daga gaban gadon da fara'a take kallon shi ta gaishe da shi, amsa mata yay ya tambayi ya yanayin jikin nata tace mashi lafiya lou ya jinjina kai, matsawa yay ya mik'a mata ledar yace to ga furar ta sai ta sha da sauri ta kawo duka hannuwanta ta amsa tay mashi godiya, saida safe yay mata ya juya ya tafi.

Wuraren k'arfe sha d'aya da rabi Fanan ta gama shiryawa cikin had'add'iyar rigar bacci lokacin Laila tayi bacci, gaban dressing mirror ta nufa ta kwance gashinta ta fara gyara shi, bayan ta gama ta hau yan shafe shafe da feshe feshen turarurruka, press ta nufa bayan ta bud'e ta fiddo after dress cikin kayanta data jera, d'aura ta tay a saman rigar baccin tata da iyakar ta gwuiwa ta yafa veil d'in asaman kanta daga haka ta nufi hanyar k'opa, saida ta saka flat shoe dake a bakin k'opar sannan ta bud'e ta fuce, part d'in Haisam ta nufa bayan taje can ta cire rigar saman. Da Asuba bayan ya dawo daga Masallaci lokacin itama ta gama salla har ta koma ta kwanta, jikin shi sanye da farar jallabiya ya hau gadon idonta akan shi tana mashi murmushi ta gaishe da shi yay mata ta tashi lafiya ta amsa mashi, matsowa tay ta d'aura kan ta a saman chest din shi nan take mashi Maganar aikinta tace sunyi waya da Dad d'inta jiya yake tambayar yaushe zata koma don hutun data d'auka ya k'are har anyi mashi magana, shiru Haisam d'in yay kamar mai nazarin wani abu har saida ta d'aga kai ta kalle shi, ce mata yay nan da 2 weeks shima zai koma yana ganin in ba matsala ta bari sai su tafi tare tace Ok zata ma Dad d'in ta magana sai a k'ara mata hutun ya jinjina mata kai sai kuma ta k'ara mashi Maganar tafiyarta Lagos idon ta akan shi, d'age mata gira yay yace tana sauri ne tana murmushi tace a'a, ce mata yay ta bari ta k'ara ko 1 week tana murmushin jin dad'i tace to.

Sam Fatuu bata wani laulayin ciki ba kamar wanccan data samu ba wannan cikin bata wani ciwo kuma komai ci take gashi sosae cin Abincin ta ya k'aru, kawai wani lokacin in taji k'amshin da bai mata ba take jin zuciyar ta ta d'an tashi sai kuma in taci Abinci wani lokacin nan ma tana jin tashin zuciyar har ta d'an yi amai shima zata iya k'irga sau nawa tayi. Gaba d'aya Hajiya ta kasa ta tsare tun abun bai damun Fatuu har ta fara shiga damuwar hakan ba kamar data ga har lokacin Fanan na a gidan kuma dai tasan dole wani abu na shiga tsakanin ta da Haisam, Haisam d'in na yawan zuwa duba ta sai dae bata wani sakewa da shi koda yazo Hajiyar bata a cikin d'akin d'an bayan lokaci take shigowa tace yazo ya wuce ya bata wuri, kullum daga kwanciya sai kallo sai latsa waya ko main parlor bata cika zuwa ba Saboda a ranakun aiki yan gidan ma ba zama suka cika yi ba a parlon. Bayan sati d'aya ranar asabar Fanan ta tafi dama Hajiya Maryam nata k'orafin ta maido mata yarinya ta hanata zuwa School, bayan tafiyar Fanan su Laila da Nameer suma suka fara shirin tafiya, ranar laraba Laila ta tafi Malaysia Nameer kuma Haisam yace ya bari su tafi tare tunda a can yake karatun dama, gaba d'aya Fatuu ta k'ara shiga takura dama dasu Fanan d'in take yin hira wani lokacin ga damuwar tafiyar da Haisam zai yi ranar Sunday zaije Lagos daga can ran Monday zasu tafi, sosae Fatuu ta shiga damuwa don in tace bata buk'atar mijinta to tayi k'arya ba kamar in ta tuna zai tafi tare da Fanan sai zuciyarta tay ta raya mata zasu je can suyi ta shan soyayyar su,

Ranar Friday da yamma gaba d'aya Fatuu tunanin yadda zata je part d'in Haisam take tana haka dubara ta fad'o mata, tana sanye da riga da skirt na lace ta nufi cikin Bedroom lokacin Hajiya na zaune tun bayan data gama sallar la'asar take tasbih, daga gefenta d'an nesa da ita ta zauna akan carpet ta shiga yin wasa da yatsunta na k'afa, bata dad'e da zama ba taji Muryar Hajiyar tana tambayarta ya kai, shiru tay ta fara motsa baki da k'yar murya na d'an rawa tace mata dama tazo tambayar ta ne Ya Haisam ne yace taje ta had'a mashi kaya tay wuri wuri da ita ta k'arasa Maganar, bin ta da ido Hajiya tay ta shiga yan kame kame,

"Rabu dashi bazaki je ba, da da babu ke wake had'a mashi bashi ke had'a kayan shi ba, duk da abu ne mai kyau amman ai yasan halin da kike ciki ko" kallon ta Fatuu tay tana d'an kikkafta ido a hankali tace mata ai lafiyar ta lau bata jin komai, yar harararta Hajiyar tay "dama ai ba'a ce baki lafiya ba ko saidai gudun janyo ciwon ake" da sauri Fatun ta juyar da fuskar ta, d'an murmushi Hajiya tay tace mata taje taci gaba da kallonta bazata hau bene ba a halin da take ciki in dole sai ita yake so ta had'a mashi kayan tace ya kawo nan sai ta tayata su had'a mashi, jiki sukuku Fatuu ta mik'e ta nufi hanyar fita ta koma parlor, idanunta ne suka ciko da kwalla ta zauna tay shiru. Bayan sallar isha Haisam yazo dubata kaman ko yaushe lokacin tana a cikin Bedroom zaune a saman gado, ya lura da yanayin ta cike da kulawa ya tambayi mike damunta kawai sai ta saka mashi kuka tace ba shine zai tafi ba, rarrashinta ya shiga yi da k'yar ya samu tayi shiru daga baya ya tafi, bayan tafiyar shi cigaba da matse kwalla tay wani irin k'unci take ji acikin ranta, tunani ta shiga yi na ko in Hajiya tayi bacci ta tafi wurin shi don shi kan shi ta fahimci yana son hakan kawai ba yadda zai yi ne, to kuma in ta farka fa don tabbas Hajiyar na tashi da daddare wani lokacin toilet take zuwa kuma bata da nauyin bacci don sau da yawa in Fatun ta farka ko zata toilet data ji motsinta ita ke kunna lamp har ta tambaye ta lafiya, tasan muddin ta tafi da k'yar in bata farka ba taga bata a d'akin hakan kuma itama tasan zai ja masu matsala, sak'e sak'e ta ci gaba da yi bayan zuciyarta ta raya mata wanccan tunanin tana haka kawai sai wani abu yazo mata a rai lokaci guda ta hau jinjina kai alamar ta samu mafita, saida ta kai idonta kan k'opar shigowa tay d'an jimm kafin ta kai hannunta gefe da sauri ta d'auki wayarta ta shiga call log, layin Nameer ta shiga kira bugu biyu ya d'auka ya furta "Yayata ta kaina" bata ce komai ba kan hakan k'asa k'asa da murya tana yi tana kallon kopar ta tambayi yana ina, ce mata yay bai nan yana cikin gari ta tambayi yaushe zai dawo gida yace d'an anjima, jin tayi shiru yasa shi ce mata in da wani abu ta fad'i mashi ko tana son wani abu ne,

"Eh, don Allah akwae wani magani ne da nike son ka siyo man zan turo maka sunan shi saidae ni yanzu nike son shi gashi kuma kace sai d'an anjima zaka dawo" sai zare ido take tana kallon k'opa tay Maganar, da sauri yace mata ba matsala ai sai yazo ya kawo mata dama a kusa da inda yake akwae babban pharmacy, jin hakan har saida ta d'an yi murmushi tace to bari ta turo mashi, da sauri ta cire wayar daga kan kunnan ta hannunta har yar rawa yake ta fara k'ok'arin tura mashi sak'on sunan Maganin, bayan ta tura zuciyarta ta raya mata yanzu in ya kawo kuma Hajiya na zaune a parlor kuma ya bata fa gashi ansan ba kowanne magani take sha ba sannan tace mata na miye, wani irin bugu gabanta yay da sauri ta zuru da k'afafunta cikin sand'a ta nufi k'opar, a hankali ta d'an lek'a cikin parlon ta hango Hajiyar zaune da Aunty, wani irin waro ido Fatuu tay baki bud'e da sauri ta dawo cikin d'akin, can k'arshen gadon ta koma sosae hannuwanta ke rawa ta shiga sake kiran Nameer duk bugu d'aya tare yake da fad'uwar gabanta, har ta yanke bai d'auka ba a rud'e ta hau sake kiran nashi can k'asan mak'oshi take furta don Allah kayi picking Nameer, saida ta kusa yankewa sannan ya d'auka yace "Sorry Yayata ina cikin pharmacy d'in ne amman gashi nan na siyo yanzu zan kawo maki da sauri cikin rawar murya idanunta akan k'opa tsoronta kada Aunty d'in ta shigo dubata tace "N...namer..r ka gane, don Allah ban son asan da maganin kada ka bari kowa ya gani" d'an jimm yay sai kuma ya tambayeta amman to maganin miye, gabanta ne ya fad'i cikin yar in ina tace mashi maganin bacci ne saboda halin da take ciki bata samun isasshen bacci shine take so tasha ko tayi baccin amman in aka gani za'a iya hanata sha tunda ba kowanne magani take sha ba amman shi wannan baida wata illa zata iya sha, ce mata yay ta tabbatar dai bazai mata komai ba da sauri tace mashi eh wllh ai yasan dai bazata sha abun da zai mata illa ba yace Ok kada ta damu bazai bari kowa ya gani ba gashi nan zuwa, wani irin sanyi ta ji a ranta ta koma ta haye saman gadon, dama Aunty shigowa tay su gaisa da Hajiya bayan sun gama gaisawar ta tambayi ya mai bed rest Hajiya ta d'an ta6e baki tace tana cikin d'aki tana ta nukurci miji zai tafi, murmushi Aunty tay tayi mata sai da safe,

bayan kaman minti ashirin da tafiyar Aunty Nameer ya shigo cikin parlon Hajiya na a d'an kishingid'e da yake yaran gidan duk yini suke a School shiyasa basu cika zuwa mata hira ba Saboda gajiya kuma wani lokacin da daddare aikin Assignment suke da angama kuma aka ci Abinci da wuri suke kwanciya sai Weekend suke samun lokaci sosae har ayi abubuwan nishad'i, kujerar kusa da ita ya nufa ya zaune yana sakin faffad'an murmushi idon ta akan shi itama d'an murmushin take mashi, gaishe da ita yayi ta amsa tana gyara zamanta idonta a kan farar ledar hannun shi mai d'auke da tambari an rubuta Special soya, ce mashi tay mi ta samu ne ya d'an kalli ledar kafin ya kalleta ya girgiza ma ta kai yace ba nata bane Yayar shi ya kawo mawa taci ko Babyn su shima ya ci, ta6e baki tay tace ai kafin ai d'aran akai kwand'i dai masu Baby, yana dariya ya mik'e yace bari ya kai mata in ta ci sai ta yan mata, Fatuu na kwance tayi tsuru ta ji sallamar shi aikuwa da sauri ta d'ago suka had'a ido, cikin d'akin ya nufo ta yunk'ura ta tashi zaune, a bakin gadon ya zauna idon shi akanta yana murmushi ya gaishe da ita ta amsa itama da d'an murmushin, hannu ya kai cikin aljihun jeans d'in shi ya fiddo maganin dake cikin farar ledar magani a jiki anyi alamar guda d'aya za'a sha ya mik'a mata da sauri ta kawo hannu ta amsa tace mashi ta gode, mik'a mata ledar hannun shi yay yace gashi nan aba baby d'in su tay murmushi kawai ta amsa yay mata fatan Allah yasa tay baccin yau harda miyau tana dariya tace Amin, mik'ewa yay yayi mata saida safe ta amsa, yana fita da sauri ta kai maganin ta tura a cikin bra dinta sannan taji ta d'an samu natsuwa sai kuma ta shiga tunanin yadda zata ba Hajiya, tunanin ko taje ta d'aukko lemu a fridge ta saka mata sai ta bata tayi wata zuciyar ta raya mata ai ba lalle tasha lemu ba da daddaren nan, gaba d'aya ta rasa tunanin yadda ya kamata tayi duk fuskarta ta yamutse can furar da Dad ke kawo masu ta fad'o mata a rai tabbas a ciki yakamata ta saka mata to amman ta Yaya, zuciyarta ce ta bata ta koma parlon don yanzu Dad ya kusa zuwa in yazo sai tasan yadda zatai ta zuba mata, da sauri ta saukko daga gadon har zata tafi sai kuma tayi tunanin tayi dubarar tafiya da abunda Nameer ya kawo mata ta kai mata, d'aukar ledar tay ta nufi parlon gabanta nata fad'uwa, cikin parlon ta fito Hajiya ta d'aga ido ta kalleta ta nufe ta, daga gefenta ta zauna tana d'an murmushi ta gaishe da ita bayan ta amsa tace mata Allah yayi kenan ta fito, shiru tay bata ce komai ba sai kuma ta mik'e ta kai mata ledar tace gashi, d'an ta6e baki tay tace ta ci abunta tunda ita ya kawo mawa da yayi niyya ai da ya had'o da ita dama ba so yake taci ba don haka ta k'oshi, hak'uri Fatun ta bata tay d'an murmushi tace mata wasa take mata taci, juyowa tay taja table gaban Hajiyar bayan ta d'aura ledar ta fiddo nannadaddar foil paper d'in ciki, warwareta tayi wani uban k'amshi mai dad'i ya daki hancin su baki d'aya, wani had'addan gasashen nama ne a iya ido kawai sai ya burge mutum irin kalar suyar da aka mashi yasha su Albasa da koran tattasai harda soyayyan dankalin turawa naman dai yayi ba k'arya😋 bayan ta bud'e ta kalli Hajiya tace don Allah taci tay d'an murmushi tace ta ci ta k'oshi in ta rage sai taci, a marairaice Fatun tace a'a ita ta fara ci in ta rage sai taci, ganin in ba ci tay ba bazata k'yaleta baà kuma dai naman ya burgeta yasa tace ta zauna to sai su ci tare sosae Fatuu taji dad'in hakan ta zauna, a nutse suke ci sai faman dakon shigowar Dad take can wata zuciyar ta bata ta tambayi Hajiyar ko zata sha lemu sai taje ta d'aukko mata daga nan ta saka mata maganin, koda ta tambaye tan ce mata tay a'a bazata sha lemu ba ruwa kawai zata sha shima sai sun gama in kuma ma an kawo mata Furar ta Shikenan ita zata sha tana d'an murmushi tace to, sai Addu'ar Allah yasa akawo furar take a lokacin, cikin sa'a basu kaiga gamawa ba Dad d'in ya shigo lokacin Fatun kad'ai ke ci Hajiya ta daina ci, yana ganin su yay murmushi yana sanye da farar shadda babbar riga ya k'araso cikin parlon yana fad'in shagali suke haka Hajiya na yar dariya tace Nameer ne ya kawo ma d'an su abun dad'i ita kuma ta cinye mashi duk sukai dariya, zama yay ya gaishe da ita bayan ta amsa Fatuu ma ta gaishe da shi ya amsa cike da kulawa ya tambayi ya take badai wata matsala ko tace mashi eh yace haka ake so, yunk'urawa yay ya mik'e ya nufi kan c-table ya d'aura ledojin yace to shima ga nashi a had'a aci gaba da party duk sukai dariya Hajiya tay mashi godiya da sa Albarka Fatuu ma tayi mashi godiya yay masu saida safe, wani irin bugu k'irjin Fatuu ke yi ga k'oshi ga kwanan yunwa, ga dama ta samu amman bata san taya zata zuba ba, can ta mik'e tana fad'in bari ta zubo mata a cikin cup Hajiyar ta d'aga mata kai, hannu ta kai za ta d'auki ledojin furar Hajiya tace mata ta bar su taje ta d'aukko cup d'in mana da sauri tace to, kaman ta saka ihu haka take ji ta nufi Fridge d'in, bayan ta d'aukko glass cups d'in ta dawo ta kai hannu ta fiddo robar furar tana cikin bud'ewa taji Hajiyar tace ta matsu bari ta je toilet ta dawo yadda zata sha a nutse har Fatuu bata san lokacin data washe baki ba tace to, d'aukar sandarta tay dake gefe ta nufi hanyar shiga d'akin ai tana shigewa jiki na rawa Fatuu ta kai hannu ta fiddo ledar maganin sai kerma hannun ta Keyi duk ta rud'e tana yi tana kallon kopar shigowa da kuma ta bedroom, fiddo guda d'aya tayi har zata saka zuciyarta ta raya mata ba lalle ya narke da sauri ba don furar kitif take kuma k'ilan ma guda d'aya bazai gaurayeta ba har yayi aiki, k'ara ciro d'aya tay da sauri ta maida ledar cikin bra d'in duk ta rud'e, kamo ha6ar kallabin ta tay ta saka magungunan ta rufe ta kai baki ta d'an tattauna sannan ta bud'e ta kai bakin robar furar ta zuba, sakin ha6ar tay da sauri ta rufe robar ta d'auka ta hau Jijjiga ta, maida ta tay ta aje a saman table d'in tana ta zare ido da sauri ta gyara kallabin ta sai faman zare ido take zuciyarta ta shiga raya mata ta daidaita natsuwar ta kar a gane ta, fiddo d'ayar robar furar tay ta bud'e har lokacin hannunta rawa yake ta zuba a d'ayan cup d'in bayan ta rufe robar ta d'auki cup d'in ta fara sha, gaba d'aya idanunta na akan kopar Bedroom har bata san tana kai cup d'in bakin hancinta ba sai taji take ankara, bayan wani lokaci Hajiya ta sako sandarta ganinta wani irin Fad'uwa gaban Fatuu ya hau yi, k'arasa fitowa tay ta shigo cikin parlon, bayan ta koma inda ta tashi ta zauna da sauri Fatuu ta aje cup d'in zata zuba mata tace ta barshi bari ta zuba, idanun Fatuu akan furar dake sauka cikin cup d'in tsoronta kar taga 6ar6ashin maganin, bayan ta gama zubawa ta d'auka ta kai baki duk da hakan hankalin Fatuu bai kwanta ba ta shiga tsoron kada kuma ta tauna maganin, har Hajiya ta shanye tata Fatun bata gama ba saida tayi mata magana kan tayi sauri ta gama ko taje ta watsa ruwa ta cire wannan d'amammun kayan ta kwanta tace to, bayan ta gama ta maida robobin cikin ledojin ta kwashe su ta nufi bakin k'opa inda dustbin yake ta saka, saida safe tay ma Hajiyar tace mata Allah ya tashe su lafiya, koda ta shiga toilet ba'a nutse tayi wankan ba, bata d'au lokaci ba ta gama bayan ta fito cikin sand'a taje ta lek'a cikin parlon ta hango Hajiyar zaune a inda ta barta idon ta akan Tv, jiki a mace Fatuu ta juyo ta dawo cikin d'akin ta nufi bakin gado ta zauna jikinta sanye da rigar wanka, tunanin kodai maganin bazai mata aiki ba ta shiga yi, ta dan d'auki lokaci a haka can ta mik'e sukuku da ita ta nufi wurin kayanta, doguwar rigar bacci ta fiddo bayan ta saka ta d'auki ta wankan ta nufi toilet, koda ta fito saida ta sake zuwa ta lek'a still Hajiyar na a yadda take, yanayin fuskar Fatun ne ya canza idanunta suka ciko da k'walla ta nufi gado, gajiya tay da zaman a hankali ta kwanta tay shiru k'walla suka fara gangaro mata, a hankali take kai hannu tana gogewa k'wallan, sosae ta damu da tafiyar da Haisam zai yi gashi bata san lokacin da zai dawo ba don da ta tambaye shi ce mata yake daya samu time zai zo ya ganta,

"Fateema da kika ji ni shiru ba sai ki lek'o ba kiji lafiya ban taso ba ina can bacci ya fara d'aukata akan kujera" Hajiya ce data shigo tay Maganar tana yi tana hamma, gwalo ido Fatuu tay tayi shiru da sauri ta runtse idonta tana jin Hajiyar na fad'in ko bacci take a haka, gadon ta nufa bangaren da take kwanciya ta hau ta kwanta sai zabga uwar hamma take, tana kwanciya taci gaba da baccin dama da k'yar ta kawo kanta d'akin yau dai ko zaman yin Addu'a bata yi ba, Fatuu na jin saukar numfashinta da k'arfi ta gane tayi bacci, tashi tay zaune idonta akan Hajiya sai kace ta dad'e a kwance a yadda take baccin, hannu ta kai ta d'aukko wayarta ta duba time har k'arfe sha d'aya tayi, tunanin ta k'ara bata time tayi tay zaune tana yi tana kallon ta gaba d'aya ma sai taga time d'in bai gudu, bayan kaman minti goma ta yanke ta tafi sai kuma tay tunanin ta gwada tashin Hajiyar ta gani ko baccin bai yi nauyi ba in ta tashi sai tace mata dama taga bata canza kaya bane, da wannan tunanin ta mik'e ta zagaya side d'in da take ta fara kiran sunanta shiru hannu ta kai ta d'an bubbuga hannunta tana cigaba da kiran nata nan ma shiru, d'agowa Fatuu tay tana murmushi ta nufi wurin kayanta ta curo Hijab, bayan ta saka ta nufi bakin gadon ta d'auki wayarta, saida ta je ta ja duvet ta rufe ma Hajiyar rabin jikinta ta kashe wutar d'akin sannan ta nufi hanyar fita, a parlon ma saida ta kashe kayan kallon da hasken cikin shi sannan ta nufi hanyar fita, saida ta tsaya ta lallek'a ta tabbatar ba kowa sannan ta fito sauri sauri gudu gudu ta nufi hanyar baya, tana tafiya zuciyarta na raya mata to yanzu in Hajiyar ta farka kuma fa, girgiza kai tay ta tabbatar ma kanta tunda maganin yayi aiki bazata farka ba tasan har ta koma don maganin nada k'arfi gashi biyu ta saka mata,

Lokacin data haye benen k'opar parlon nashi a rufe take, da sauri ta d'ago wayarta ta shiga k'ok'arin kiran shi, yana yin picking tun kafin yace wani abu tace mashi yazo ya bud'e mata k'opa saida yaji mamakin hakan ya tambayi wace k'opa tace mashi ta shigowa part d'in shi ta baya, yana bud'e kopar suka had'a ido ta sakar mashi murmushi yana sanye da rigar bacci kimono broad chest d'in shi a bud'e, d'an waro ido yay alamar mamaki da sauri ta fad'a mashi ya kai hannu ya rungume ta, komawa yay ciki da ita bayan ya tura k'opar ya d'ago ta har lokacin murmushi take, da alamun mamaki yace mata ya akai tazo nan yanzu, farko shiru tay ta shiga tunanin bazata ce mashi magani ta bata ba sai kawai tace mashi ba tun d'azun take fama da ita ta barta tazo ta had'a mashi kaya ba amman ta k'iya shine yanzu da taga tayi bacci ita kuma ta taho, d'age gira yay sai kuma yay faffad'an murmushi yace mata bata tsoron ta tashi taga bata nan ta d'an tura mashi baki bata ce mashi komai ba,

"Yanzu kayan kika zo had'a man kenan?" ta d'aga mashi kai wani kallo ya bita dashi ta tura mashi baki, d'an murmushi yay yace mata to ai shi ya riga ya had'a kayan nashi ya za'ai kenan da sauri ta fad'a jikinshi tana fad'in suje a wargaza su ta sake had'a mashi, sosae yake dariya sai mutsu mutsu take mashi da kanta a chest nan take ta fara turning nashi on, hannu ya kai ya murd'a key k'opar ta rufe ya kai hannu ya d'auketa ya nufi ciki da ita. Duk yadda Haisam yaso kar ya xamo uncontrollable kaman yadda yake duk ya kasance da ita abun ya ci tura ba kamar kuma daya kasance ga halin da take ciki gaba d'aya ta canza mashi, bayan ya samu natsuwa hak'uri ya shiga bata yana tambayar is she Ok, shiru bata amsa mashi ba ta duk'unk'une guri guda, Jijjiga ta ya shiga yi yana kiran sunanta amman shiru, da sauri ya sauka daga saman gadon ya je ya kunna Switch, har saida gaban shi ya fad'i ganin yadda tay ta runtse ido hannunta guda dafe da cikinta, wani irin bugu gaban shi yay a rud'e ya dawo ya hau gadon, d'ago ta yay ya fara tambayarta lafiya miya faru shiru bata ce komai ba sosae ya razana, maida ta yay ya kwantar ya fara k'ok'arin sauka yana fad'in bari ya kaita hospital, ji yay ta ruk'e mashi hannu da sauri ya kai idon shi kanta kawae sai gani yay ta kyalkyace da dariya, wani kallo yake bin ta da shi ya d'an yamutsa fuska ta d'age mashi gira kawai sai ya yarfa hannu yace "Zarah wannan wasa ne?" Yadda ya kwa6e fuska yasa ta k'ara kyalkyacewa da dariya, hannu ya kai ya dafe goshin shi ya maida idon shi k'asa, da sauri ta tashi zaune ta kai hannu tana k'ok'arin cire mashi hannun tana fad'in yayi hak'uri, k'in bata dama yay ta cire hannun a shagwabe tace in bai hak'uri ba Baby zai fito ya bashi hak'uri yanzun, juyowa yay yayi mata wani kallo idanunshi sun d'an yi ja, wara mashi ido tay tana murmushi ya d'an harareta, ta6e baki tay ta kai hannu ta kama kunnuwanta ta furta "i'm very sorry My Hubby bazan k'ara ba" yadda tayi ne ya bashi dariya yayi har fararen hak'oran shi suka bayyana ya kai hannu ya jawota ya rungume ta a wurin kunnanta ya rad'a mata so take tasa heart d'in shi tay bursting ne da sauri ta girgiza mashi kai yace to karta k'ara mashi irin wannan wasan da sauri ta d'aga kai, tambayar ta yay wai yaushe zata girma ne tana murmushi tace mashi ba rana, zamewa yay ya kwanta tare da ita ta yadda kanta na a saman chest d'in shi, shafa kanta ya shiga yi wani irin nishadi suke ji suna haka taji ya furta Allah yay mata Albarka tana murmushi idanunta a lumshe ta amsa tace shima Allah ya yi mashi Albarka ya amsa da Amin a haka bacci yay awon gaba da ita, jin saukar numfashin ta a hankali yasa shi kwantar da ita ya saukko ya nufi toilet,

Kiran sallar Farko ya farka kamar koda yaushe, tashi yay zaune ya kai hannu ya kunna lamp, juyowa yay ya sauke idon shi a kan Fatuu dake ta shan bacci, ji yay kamar ya k'yale ta amman bai son Hajiya ta tashi taga bata nan ya zama wani issue kuma duk da bai san ma ko ta tashi ba, tashin Fatun yay bayan ta bud'e ido yace ta tashi ya rakata kar Hajiya ta tashi tana jin hakan da sauri ta mik'e, tare suka fito ta baya, lokacin da suka shigo cikin main parlon a d'arare Fatuu take, tare suka shiga cikin parlon Hajiya ya tsaya anan yace ta duba taga ko ta tashi, gabanta na d'an Fad'uwa ta nufi Bedroom, cikin sand'a ta zagaya side d'in da take kwanciya saida ta d'an saurara sannan ta kai hannu ta kunna lamp d'in wurin,tsaye tay tana kallon Hajiya dake kwance kan gado tana ta bacci, d'an murmushi tay don ta fahimci bata tashi ba don data canza kaya zuwa na bacci Saboda bata kwanciya ba tare data saka kayan bacci ba, juyawa tay ta koma parlon ta fad'i mashi bacci take ya jinjina kai sai kuma yace mata to in ta tashi da daddare fa bata gan ta ba, d'an waro ido tay sai kuma tace ita dai in tayi mata magana kan hakan to zata ce shi yazo tana bacci ya d'auketa, yar dariya yay ya kai hannu ya kamo ta jikinshi yace sharri ko tanata dariya, saida yay pecking kumatunta sannan ya juya ya tafi ita kuma ta nufi Bedroom d'in, bayan ta shiga cikin sand'a ta nufi side d'in da take kwanciya ta cire Hijab d'in jikinta sannan ta hau gadon ta kwanta, tunawa tay da she needs to take bath a hankali ta tashi saida ta kallo Hajiya sannan ta mik'e ta nufi toilet, tana fitowa aka fara kiran salla na biyu nan take alarm d'in wayar Hajiya ya fara k'ara da sauri har tana yin tuntube da carpet taje ta haye gadon ta cure guri guda tana zare ido, har alarm d'in ya yanke ya sake fara wata k'arar shiru bata ji Hajiya ta tashi ba, a saninta tunkafin lokacin salla Hajiya ke tashi tayi raka'atanil fajr a wurin zata zauna har lokacin salla yayi, a ranta ta raya to miyasa yau bata tashi ba, bata kawo komai a ranta ba ta saukko ta nufi wurin kayanta, doguwar riga ta saka ta maida Hijab d'in data dawo da ita ta kabbara salla, har ta gama Hajiya bata ko motsa ba, tana zaune akan prayer mat ta kai idonta kan Hajiyar a cikin ranta ta fara raya to wai lafiya bata tashi ba, zuciyarta ce ta bata taje ta tashe ta, tun Fatuu na kiran sunanta har ta kai ta fara d'an bubbuga hannunta, tsoro ne ya kama Fatuu ganin yadda take ta tada Hajiyar amman ko motsi bata yi ba, tun tana bubbuga ta har takai ta fara jijjigata tana fad'in Hajiya ki tashi don Allah, gaba d'aya Fatuu ta kid'ime tuni ta fara kuka Fuskar ta share share da hawaye zuciyarta ta shiga raya mata kodai maganin nan data bata ya kashe ta, da sauri ta kai hannu ta ta6a saitin Zuciyar ta sam ta kasa gane komai, kai kunnanta tai saitin fuskar ta taji gaba d'aya bata numfashi, d'agowa tay a gigice ta d'aura hannuwa a saman kai tana fad'in ta bani ta lalace badai ta kashe Hajiya ba, Haisam ne ya fad'o mata a rai ta juya tana laluben wayarta don ta kira shi sai dai bata gan ta ba can ta tuna ta baro ta a part d'in shi, a sukwane ta sauka daga saman gadon ta nufi hanyar fita da gudu.............

88

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

..........A daidai bakin k'opa tana k'ok'arin fita cikin parlor sukai karo da Mutum, a razane ta kai idon ta fuskar shi nan take ta gane Haisam ne don gari ya fara wayewa, dawowar shi kenan daga Masallaci ya zo don yaji yadda suka k'are, ganinta a rud'e fuska sharkaf da hawaye yasa shi saurin kama ta yana tambayar lafiya da hannu ta rink'a nuna mashi saitin Hajiya tana fad'in tak'i tashi, kamata yay suka nufi ciki ta bangaren gefen Hajiyar ya zauna a bakin gadon ita kuma ta zagaya ta haye saman gadon idanu waje take kallon Hajiyar sai kuma ta kalli Haisam dake bubbuga Hajiyar yana kiranta, hankalin shi ne ya fara tashi har Fuskar shi ta bayyana ya kalli Fatuu ya ce mata miya faru da ita ne, wani Wahalallan miyau ta had'iya sai motsa baki take gaba d'aya ta zaro ido duk tayi kalar rashin gaskiya, k'ara tambayar ta yay yace ta fad'i mashi miya faru da ita ne cikin kuka murya na rawa tace "Don Allah Ya Haisam kayi hak'uri, wllh bada nufin haka nayi ba na rantse maka da Allah" mamaki ne ya bayyana akan fuskar shi jin abunda tace wanda yake nuni da wani abu tay ma Hajiyar, ce mata yay ta fad'i mashi abunda ya faru zai fahimceta da sauri ta fara fad'i mashi tiryan tiryan abunda tay mata na maganin baccin data bata guda biyu, d'an waro ido Haisam d'in yay cike da Al'ajabi yake kallon ta ganin yanayin shi yasa ta hau yin rantse rantse, gaba d'aya shima Haisam d'in ya rud'e ya rasa tunanin da zai yi ga Fatun ta gigice sosae wanda a halin da take ciki bai kamata ace ta tashi hankalin ta haka ba,

Hannuwanta ya kamo ya shiga rarrashinta yana fad'in ta kwantar da hankalin ta ya fahimce ta zata tashi in sha Allah, ganin ta d'an sassauto yasa shi tambayarta shi maganin data batan ta tabbatar baida illa, da sauri tace wllh baida illa na bacci ne ko su suna sha in sukai karatu sosae suka kasa bacci, jinjina mata kai yay ya maida idon shi akan hajiya, k'ok'arin tada ta yaci gaba da yi Fatun na taya shi, ganin tak'i tashi yasa shi kallon Fatun yace bai kamata suna 6ata lokaci ba bari yaje ya d'aukko Mota sai ya kaita Asibiti aikuwa a rud'e ta kamo hannun shi da duka hannuwanta tana girgiza mashi kai tace "Don Allah Yaya Haisam kada aje Asibitin wllh in aka je za'a gane an bata wani abu ne gashi Nameer ne ya siyo man kuma ba lalle a fahimce ni ba" shiru yay ya rasa miye abun yi don gaskiya ta fad'a saidae kuma yasan kaita Asibitin shi ya kamata, tambayarta yay an rage sauran Furan ne da sauri ta girgiza kai "a'a, duka muka shanye robobin na a cikin dust bin a parlor",

"Ok, ki kwantar da hankalin ki Hospital d'in yakamata akai ta zan san yadda za'ai baza'a gane kin bata wani abu ba muyi Addu'a Allah yasa komai yazo da Sauk'i" da sauri tace Amin, har zai sauka daga saman gadon sai kuma ya maido idon shi kanta yace ta sa mata ruwa ne da sauri ta girgiza mashi kai tace a'a ko taje ta kawo, da hannu yay mata alamar ta tsaya shi ya mik'e ya nufi hanyar parlor, bada jimawa ba ya dawo hannun shi ruk'e da bottle water daya d'aukko daga cikin Fridge ruwan mai d'an madaidaicin sanyi ne, bayan ya koma ya zauna bud'e murfin robar yay ya tarba hannun shi ya cika shi da ruwan, sai da yay bismilla sannan ya watsa mata shi a fuska nan take tay wata ajiyar zuciya, k'ara zaro ido Fatuu tay suka kalli juna da shi atare suka shiga kiran sunanta saidae bata k'ara yin wani abu ba daga haka, da sauri Fatuu tace mashi ya k'ara watsa mata ruwan, yana k'ara zuba mata ta k'ara yin ajiyar zuciya suka cigaba da kiran sunanta, Motsi ta fara yi Fatuu ta fara d'an murmushi, Haisam ne ya rankwafa yasa hannu yana d'an bubbuga gefen fuskar ta yana fad'in "Sweetheart open your Eyes" a hankali ta fara bud'e idanun tana yi tana rufe su yana cigaba da ce mata ta bud'e idanunta, lokacin data bud'e su gaba d'aya sun yi ja sosae tabi Haisam da kallo tamkar mai son gane wanene shi kuma ya d'an rankwafa da kan shi sai murmushi yake mata,

"Kai, wane gardi ne wannan a kai na, lafiyaaa???" da wani irin sauti tay Maganar nan take Fatuu ta bud'a baki Haisam ya d'aga ido ya kalleta gaba d'ayan su sun fahimci maganin bugar da ita yay da alama yayi mata k'arfi ne sosae, k'ara ce mashi tay waye shi ya d'age mata gira yace mata masoyinta ne ta wani k'ank'ance mashi ido fuska a tsuke, kallon Fatuu tay ta k'ura mata ido duk Fatun tasha jinin jikinta sai motsa baki take, hannu Haisam ya kai ya tada ita zaune ta jingina da kan gado yace mata ta kalle shi sosae ta kuwa zuba mashi ido, bayan wani lokaci yace mata to ta gane shi kawae sai ji yay tayi d'an guntun tsoki tace to shi d'in ne bata sani ba, murmushi yay tace wai mi ya faru ne shi kuma miya kawo shi nan, yana murmushi yace "da yake kin samu kan ki ko",

kai idon ta kan Fatuu dake ta zare ido tayi tace ita kuma wannan mi akai mata tayi kuka Haisam d'in na k'ok'arin bud'e baki yay magana a rud'e Fatuu ta hau girgiza mashi kai alamar kada ya fad'i mata, yar dariya yay yace ma Hajiyar hankalinta ne ya tashi tana ta tada ita gari ya waye amman tak'i tashi, hannu ta kai ta dafe goshinta Haisam d'in yace mata lafiya tace ciwo yake mata, sannu yayi mata yace ta tashi tayi salla sai tasha magani, tambayar shi tay anyi salla ne yace eh tun d'azun, da alamun mamaki tace to wai miya faru da ita ne haka ya d'an ta6e mata baki, tunani ta shiga yi can tace mashi tana zargin furar data sha jiya ce ta sata Nauyin bacci haka don tun a parlor jiya ta fara yin bacci da k'yar ta dawo d'aki kuma daga nan bata k'ara sanin inda kanta yake ba gashi yanzu suma sun ce suna ta tada ita bata tashi ba tabbas Furar nan ce, gaba d'aya Fatuu ta rud'e sai zare ido take Haisam ya kalleta suka had'a ido yanayin fuskar shi kamar zai yi dariya, ganin tana ta Maganar furar yasa shi ce mata dama ya ta6a sata haka ne tace a'a yace to ba shi bane, da sauri tace ai dama fura na bugarwa wani lokacin fa yace to tunda tasan hakan ba Shikenan ba miye na dogon magana ta tashi taje tayi salla kawai Allah ya kyauta gaba,

ganin tana ta k'ok'arin saukkowa yasa shi mik'ewa ya taimaka mata ta tashi tsaye tay mashi alamar ya bata sanda sai faman hamma take, ce mata yayi ko baccin bai ishe ta bane a k'ara nemo wani Furan ya saci kallon Fatuu suka had'a ido ta tura mashi baki yay yar dariya, duk da sandar saida ya kaita har bakin toilet don sai fad'i take jikinta ba kwari yace mata sai ta fara yin wanka taji k'arfi ta d'aga mashi kai, tura kopar toilet d'in tay yana ta fad'in tabi a hankali, saida yaga ta shige sannan ya juyo ya dawo wurin gadon ta side d'in da Fatun take idonta akan shi, zama yay a bakin gadon ya mik'a mata hannu ta matso, jawota yay jikinshi kawai sai ta fashe da kuka ya shiga rarrashinta yana fad'in ba Shikenan ba tunda ta farka, bayan tayi shiru ya tambayi ba abunda ke mata ciwo ta d'aga mashi kai alamar eh, shiru suka d'an yi kafin can k'asa k'asa da murya ya rad'a mata ta rage sauran maganin anjima da daddare a k'ara bata suje part d'in shi a zabure ta d'ago ta kalleshi kawai sai gani tay ya saka dariya aikuwa ta kai hannu ta bugi chest d'in shi ta fara k'ok'arin raba jikinsu ya matseta yana cigaba da yin dariyar yace shima ai wasa ne yayi mata ko irin wanda tay mashi tay d'an murmushi tare da lumshe ido ta maida kanta saman chest d'in nashi sosae yanzu hankalin ta ya kwanta amman ba k'aramar razana tayi ba, kai bakin shi yay saitin kunnanta cikin rad'a yace mata kar ta k'ara irin wannan kuskuren da sauri ta d'aga mashi kai kafin a hankali tace bazata k'ara ba ya jinjina mata kai.

Da yake Weekend ne ana abubuwan nishad'i a gidan tuni Fatuu ta washe saidae taci alwashin ita da ta k'ara ba wani maganin bacci har a bada in dai ba patient ba a Asibiti shi ma sai in likita ne yace a bashi duk da tasan laifinta ne ita ta cika ma Hajiyar abun kuma ya had'u da shekaru, da daddare atare gaba d'aya wad'anda ke a gidan suka ci Abinci kamar dai da safe da kuma da rana, bayan sun gama cin Abincin daren sun koma part d'in su taje tayi wanka, bayan ta gama shiryawa da kayan bacci riga da wando tasa hula ta nufi Parlor wurin Hajiya da tuni ta wartsake tana zaune idanunta sanye da glass tana kallo, sannu tayi mata Hajiyar ta d'aga mata kai ta zauna itama, bata dad'e da zama ba Nameer ya shigo hannun shi ruk'e da ledojin Fura bayan sun gaisa ya d'aura akan c-table yace gashi nan Dad yace ya kawo daga haka yay masu saida safe, Fatuu ce tace mata ta d'aukko cup ta zuba mata Hajiyar ta d'an yamutsa fuska tace anya yau zata sha furar nan don gaskiya jiya itace ta bugar da ita wllh, duk sai Fatun bata ji dad'i ba ganin zata haramta mata abunda take so, wani tunani tay da sauri tace ma Hajiyar ita tana ganin ba daga furar bane k'ilan daga naman da suka ci ne ya had'u da furar shine suka bata reaction, Hajiyar tace anya sai kace dai kifi Fatun tace ai shima Naman yana iya sawa an koya masu a Makaranta Hajiyar tay mata wani kallo mai kaman harara tace to kuma shine ta bari suka ci, a dabarbarce tace ai bai cika sa wani abu ba kamar kifin ita tama dai fi tunanin k'ilan naman da aka sarrafa d'in ne keda matsala, ta6e baki Hajiya tay tace koma dai minene mai faruwa ai ta faru, da yake ranta na son furar tace mata ta zuba mata yar kad'an tasha in bata ji komai ba sai ta k'ara cike da jin dad'i Fatun tace to ta mik'e, bayan ta zuba mata ta bata itama ta zuba ta fara sha, suna cikin sha taji Hajiyar tace wai Haisam d'in ya had'a kayan tafiyar ko kuwa, d'an murmushi Fatuu tay ta sadda kai tace mata bata sani ba amman tasan k'ilan ya had'a zuwa yanzu tunda gobe zai tafi, d'an ta6e baki Hajiyar tayi sai kuma tace mata ta tashi taje ta gani in bai had'a ba ta had'a mashi in kuma ya had'a mata aiki ya tafi ya barta da wahala ita ta sani, kunya ce ta kama Fatun ta sadda kanta k'asa tana haka taji tace ta tashi taje, mik'ewa tay zata tafi Hajiyar tace to wa ta bar ma sauran furar ta d'auka taje da ita tana had'a kayan tana sha, d'auka tay sumi sumi ta wuce, a yadda take ta nufi hanyar fita daga parlon ta fuce, ta baya ta fita tana tafiya a ranta take raya gajen hak'uri gashi nan da kanta tace taje, wata zuciyar ta raya mata rabon kowa zai jigata ne tay yar dariya.

Washe gari tunda Fatuu ta tashi cikin damuwa take, a part d'in Haisam tay wanka don nan ta kwana bayan ta koma part d'in Hajiya ta canza kaya, bayan sun gama yin Breakfast part d'in Haisam d'in ta koma, gaba d'aya yini yay aikin rarrashinta don sai kuka take mashi, lokacin daya dawo sallar la'asar tana zaune a bakin gadon shi itama bata dad'e da gama yin sallar ba, zama yay a bakin gadon suna kallon juna slowly ya furta mata zasu wuce don 4:30 jirginsu zai tashi zuwa Lagos yanzu yakamata su tafi don hud'u ta kusa, kai kawae ta d'aga mashi yace bazata raka shi Airport ba, a marairaice tace mashi bata son taje tay ta kuka tunda yak'i daina zuwa, kai ya d'aga mata ya kai hannu ya rungumo ta ya furta zai yi missing d'in ta sosae cikin muryar kuka tace itama, d'ago da ita yay suna kallon juna yay mata d'an murmushi ya kai bakin shi yay pecking duka kumatunta ya furta "I love you My Baby" itama tace mashi haka ce mata yay ta tashi suje ya rakata cikin gida tace mashi a'a zata zauna anan sai anjima zata koma, shiru ya d'an yi kafin yace tay mashi alkawarin ta daina kukan cikin karyayyar murya tace ai shi yake zuwa amman zata bari ya d'aga mata kai, mik'ewa yay ya nufi inda trolley d'in shi yake ajiye dama saida ya gama shiryawa sannan ya tafi Masallaci, juyowa yay ya kalleta ya furta ta kula da kanta sosae ta d'aga mashi kai tana kikkafta ido, har ya kai k'opa yaji ta kira sunan shi ya dakata ya juyo, mik'ewa tay ta nufo shi a gaban shi ta tsaya idanun ta cike da k'walla tace bari ta raka shi, murmushi yay yace indai bata so ta barshi tace a'a zata je, dama ranar k'ananun kaya ce hakan yasa ta d'aura after dress da zata zo wurin shi gyalen rigar na saman kanta, ce mashi tay ya kawo akwatin ta ruk'e ya girgiza mata kai ya kawo d'ayan hannun shi ya kama nata suka tafi,

Gaba d'aya yan gidan sun fito bakin Entry Hall don yi masu rakiya lokacin da suka k'araso, harda Dad da Hajiya dasu Jidderh da Aunty ba wanda aka bari, a Jeep din da za'a d'auki Dad Aunty da Mom suka shiga sai Nameer ya shiga gaba, sai wata Jeep din Haisam ya shiga gaba Hajiya da Fatuu da Jidderh suka shiga baya sai k'aramar Mota Yasmeen da Affan dasu twins suka shiga a k'arshe kuma Hilux d'in escort ce a jere Motocin suka tafi. Bayan anje Airport d'in duk yadda Fatuu taso kar tayi kuka da zasu rabu abun yaci tura saida tayi akaita rarrashinta harda Dad a cikin masu rarrashin nata shi kan shi Haisam d'in wani iri yake jin shi, tana ji tana gani Hubby d'inta ya tafi.

Bayan sun baro Airport d'in ba gida suka koma ba bazama sukai Outing, sosae suka zaga gari harda wani babban park suka je sukai ta hawa liluna iri iri ita dai Fatuu an hana ta hawa sai aikin kallo take tana nishad'i don harda Dad dasu Mom aka hau wasu lilon Hajiya dae itama aikin kallon tayi daga baya kuma suka yi hotuna, bayan sun baro park d'in wani babban shopping mall suka je nan aka ce kowa ya za6i abunda yake so, Su Mom duk kayan shafa da turarurruka suka d'auka haka Jidderh ma da Yasmeen suma cosmetics d'in suka d'auka suka had'a da Undies, Su Twins da Fatuu wurin kayan zak'i suka nufa saida suka cika basket dinsu da su Sweets, biscuits, chocolate da sauran su Fatuu sai ce masu take su barshi haka amman suka k'i wai ai harda Baby d'in su shima za'a d'aukar mawa Fatuu sai dariya take, Hajiya ita k'in d'aukar komai tay tace bata buk'atar komai Senator ne ya za6ar mata turarurruka Mom kuma ta d'aukar mata dogayen riguna da tasan tana sa irinsu harda Fatuu ta za6ar ma wasu dogayen riguna tace zata ji dad'in su nan gaba, Affan ma underwear ya d'auka sai turare da kayan zak'i, kowa dai ya d'auki abunda yake so, suna cikin shopping d'in Haisam ya kira Fatuu ya sanar mata sun isa Lagos ta hau yi mashi shagwabar tana missing nashi, anan Mall d'in suka yi sallar Magrib bayan sun gama suka shiga Eatery d'in wurin, kowa abunda yake so shi aka kawo mashi ya ci, daga nan bayan sun gama gida suka koma lokacin da suka dawo an fara kiran sallar isha kowa ya nufi part d'in shi cike da annashuwa, basu zauna cin Abincin dare ba don duk a k'oshe suke saidai wad'anda suka fara jin yunwa ne suka d'an ci harda Fatuu acici ta k'ara.

Washe gari Monday da safe duk gidan ya rairaiye masu zuwa Makaranta sun tafi masu zuwa aiki ma sun tafi, Bayan Fatuu ta gama yin Breakfast na biyu don bayan da tayi sallar Asuba saida taci Abinci sannan ta koma bacci sai wuraren k'arfe goma saura ta tashi shine ta k'ara wani breakfast din, toilet ta wuce don tayi wanka, bayan ta fito ta shirya cikin k'ananun kaya skirt d'in jeans da t-shirt kanta ta saka hula sosae tayi kyau, zama tay bakin gado bayan ta gama tay shiru gaba d'aya ta k'agara su koma Katsina don tafiyar Haisam ta k'ara sawa taji duk zaman gidan ya gundureta, hannu ta kai ta d'auki wayarta dake a gefe ta fara lallatsawa can tay tunanin kiran Fauzy don tasan lokacin anyi break, tana fara ringing Fauzyn ta d'auka suka gaisa ta tambayi jikinta, Fatun da yanayin damuwa tace mata ita fa lafiyar ta lau wllh bata jin komai hakanan take ta zama gashi anata wuce ta a Makarantar don ma tana turo mata abubuwan da akai, tambayarta Fauzy tay an yi Maganar ranar da zasu dawo ne tace mata a'a ita ba wanda yay mata magana kan hakan da Ya Haisam kawae suka ta6a yin Maganar tun lokacin da suka tafi yace ta bari zasu dawo in aka d'an k'ara lokaci gashi yanzu har Sati biyu shiru ba'a ce zasu dawo ba, shawara Fauzyn ta bata tace ko tayi ma Hajiya Maganar taji tace mata to, yar hira suka k'ara yi kafin sukai sallama, aje wayar tay a saman gadon ta mik'e ta nufi Parlor, bayan ta fito cikin parlon ta shigo Hajiya na zaune tayi wanka tana sanye da d'aya daga cikin dogayen rigunan da aka siyo mata jiya, zama tay daga gefen ta idanun su a cikin na juna da d'an murmushi Fatuu tay mata sannu Hajiyar ta amsa tace harta shirya tace mata eh, jinjina kai tay ta maida idon ta akan Tv, shiru Fatuu tay tana tunanin ta yadda zatai mata Maganar, Hajiya na lura da yadda tay sukuku can ta tsaida idanunta a kanta tace mata ya akai ne, kallon ta tay ta fara d'an kikkafta idanu a hankali ta fara magana tace dama Maganar Makarantar ta ne wurin sati biyu kenan da komawa Fauzy ta fad'i mata anata masu karatu, d'an murmushi Hajiya tay tace "to Fateema ai lafiya tafi komai ko yanzu taya zaki wannan tafiya bacin likita ya sa dokar kar ki rink'a yin zirga zirga sosae, kiyi hakuri zaki koma ne ni kaina dole tasa nike zaune Saboda ke bawai don ina son zaman anan bane" kai Fatun ta d'aga ba tare data ce komai ba saidae yanayin Fuskar ta ya d'an canza, cigaba da kallo Hajiya tay ita kuma tay shiru ta kasa tsaida idon ta wuri guda can bayan d'an wani lokaci ta mik'e ta nufi hanyar Bedroom Hajiya ta maido idonta kan ta kafin ta maida su kan tv, tana shiga Bedroom d'in gado ta nufa tana zuwa ta fad'a kan shi nan da nan idanunta suka ciko da k'walla, kuka ta shiga yi k'asa k'asa ta rink'a kai hannu tana goge kwallan a haka bacci ya d'auketa.

Bayan komawar su Gwaggo su Kawu Amadu suka fara shiryen shiryen zana jarabawar su ta k'arshe shi kuma Tk ya fara shirin yin bautar k'asa, tun bayan da Fauzy ta dawo Katsina bata yi waya da Sameer ba tun tana saka ran zai kira har ta fidda ita kuma bata yi tunanin kiran shi ba don bata san mi zata ce mashi ba tunda shi bai kira ba gashi ta fahimci mutane irin shi ba'a cika yi masu gwaninta ba kuma basa son shishshigi, akai akai Aunty Mareeya ke kira bayan dawowar su ta tambaye ta ko ya kira, haka in taje weekend ma taita tambayar wai da gaske bai kira ba har ce mata ta ta6a yi ta kira shi ita Fauzyn tace gaskiya bazata kira ba to tace mashi mi Aunty Mareeyar tace ta gaishe dashi, ce mata tay a'a gaskiya wannan ai zak'ewa ne, daga baya ita ma Aunty Mareeyar ta rage yawan tambayar ta game dashi, saidai sosae Fauzy ke tunanin shi duk ta zauna tay shiru sai tay ta tuno fuskar shi wani lokacin tay murmushi wani lokacin ta girgiza kai ko ta bud'o hoton shi na wurin Dinner tai ta kallo.

A ranar Monday d'in bayan an tashi su Fauzy ta koma Hostel salla ta fara yi bayan ta gama ta nemi Abincin da zata ci tana gamawa ta nufi toilet tayo wanka, shiryawa tay cikin jan short skirt da bak'ar shirt mai gajeran hannu gashinta a fake, gado ta haye nan da nan bacci ya d'auketa, sai da akai sallar la'asar sannan ta tashi, bayan tayi salla jakarta ta d'aukko ta haye saman gado don tayi Assignment, bata d'auki lokaci ba ta gama ta d'aukko wani littafin ta fara yin karatu can ta aje ta kai hannu ta d'auko wayarta dake ajiye gefe, bud'eta tay ta kunna Data ta shiga WhatsApp, chat ta shiga yi da mutane daban daban harda Fatuu tana fad'i mata yadda sukai da Hajiya ta shiga kwantar mata da hankali tana nuna tasan in sha Allah bazata samu wata matsala ba a Makarantar k'ilan ma Ya Haisam d'in yayi Magana, bayan ta fita daga chat d'in Fatuu tana niyyar bud'e wani sak'o da wata k'awarta ta Funtua ta turo mata kawae taga sak'o ya shigo mata da wata bak'uwar lamba, bud'e sak'on tayi taga an rubuta,

-"How are you doing?"_

iya abunda aka rubuta kenan, maimaita karanta sak'on tayi da alamun mamaki a cikin ranta ta raya to waye wannan, har zata tambaya waye sai kuma ta lura da a Dp d'in akwae hoto, hannu ta kai ta ta6a profile d'in ya bud'e ta ta6a kan hoton, har saida gabanta ya d'an fad'i ganin Mutanen dake a Dp d'in wanda mutum ukku ne kuma duk turawa ne suna tsaye a gaban wani k'aton jirgi gaba d'ayan su k'ananun kaya ne a jikinsu kansu sanye da irin hular kwanon da injiniyoyi ke sawa duk sun yi murmushi sosae hoton yayi kyau, kan Fauzy ne ya d'aure ta shiga tunanin to su waye wad'annan ita miye had'in ta da turawa kuma, zooming hoton tay yadda zata k'ara ganin fuskokin su da kyau lokacin data sauke idonta akan na tsakiyar wanda duk yafi su tsawo sannan bai kai sauran haske ba waro ido tay a fili ta furta "Sameer!" k'ura mashi ido tay ta tabbatar ma kanta da shi d'in ne kuwa, tunani ta shiga yi inane nan da sukai hoton kamar dae ba'a Nigeria bane tana haka taga kiran video ya shigo mata da lambar, d'an jimm tay ta d'age ido kafin ta daidaita natsuwar ta gabanta na d'an fad'uwa ta latsa d'auka video call d'in ya bud'e, lokacin da idanunta suka sauka akan shi wani irin bugu gabanta yay, babbar waya ta had'u da gingimemiyar waya hakan yasa tarr take ganin shi sai kace a fili, yana kishingid'e saman wani abu data kasa gane gado ne ko kujera jikin shi sanye da vest fara K'al data bayyana surar k'arfin shi don ta kama shi zanen jikin shi ya fito rad'am kai da gani kasan yana bodybuilding ga cikin shi a d'ame yake tamkar bai cin Abinci, murd'add'un damtsen hannuwan shi dake a bud'e sun bayyanar da chocolate fatar shi da take a mulke har wani sheki take alamar hutu ya zauna yadda ya kamata, wani abun mamaki kamar yadda ake gane iyayen su da Haisam ta bambancin ido to suma launin k'wayar idon su ta bambanta tsakanin shi da Haisam sai ka natsu zaka fahimta shi Sameer d'in kwayar idon shi brown ce sa6anin Haisam da take bak'a sosae saidai gaba d'aya idanun nasu farare ne tass haka ta bangaren lips d'in su na Haisam sun yi kaman peach ne shi kuma Sameer pinkish lips gare shi, kasa magana Fauzy tay sai faman motsa baki take da d'an murmushi shi kuma ya kafeta da ido hannun shi d'aya na aje gefe d'ayan kuma sai lokacin ta lura da akan pillow ne ya d'aura shi yadda yay zaman ya d'an zame da kuma yanayin yadda hannuwan shi suke zaka gane ta laptop ne yake Vedio call d'in, baida niyyar yin Magana da k'yar Fauzy ta bud'e baki tace mashi ina wuni, shiru yay mata bai amsa ba still kallon ta yake hakan yasa ta shiga yan kame kame sai lokacin ta ankare da a yadda take ko kallabi babu a kanta gashi rigar jikinta ta kama jikin ta don roba ce boobs d'inta sunyi fam gashi ko bra bata saka ba dama kuma tana dasu Tubarkallah ta wannan bangaren har tafi Fatuu don ita kuma su ta gada a wurin Mahaifiyar su da take barumaya harda ma Hasken Fauzyn duk da shima Mahaifin su barumayen ne kuma ba bak'i bane sai dai Mahaifiyar tasu tafi haske sosae don fara ce tass gasu duk ba gajeru bane hakan yasa Fauzy ke da tsawo har Aunty Mareeya ma irin giant d'in matan nan ne tana da tsawo da jiki ita ma kuma akwae k'irji Tubarkallah,

"Can't you call people and greet them?" Sai da ya mula sannan ya furta mata hakan tare da d'an d'age mata gira, murmushin yak'e ta shiga yi cikin kama kai tace a'a tana ta son ta kira shi, shiru yay sai kuma taji yace miyasa bata kira ba ta shiga kikkafta idanuwa ta rasa mi zata ce, ganin ya kafeta da ido yasa tace mashi bata san ko bai son hakan bane, bai ce mata komai ba saima ya maida idon gefen da gani wani abu yake yi don hannun shi dake a kan gadon yana d'an motsawa, bin shi da ido tay tana ta k'are Mashi kallo ita sai ma yanzu take k'ara ganin kyaun shi sosae, tana cikin kallon nashi ya juyo suka had'a ido da sauri ta sunnar da kanta k'asa tana haka taji ya tambayi tana ina ne,

"Ina a School" ta bashi amsa a hankali bayan ta d'ago sun sake had'a ido nashi idanun a d'an lumshe kamar dai yadda Haisam ke yi, ce mata yay yanzu nan a Class take da sauri ta girgiza mashi kai "a'a ina a Hostel ne an tashi daga Class" shiru ya d'an yi kafin ya tambayi mi take a Hostel ta bashi amsa da ai ita boarder ce, maida idon shi yay gefe yaci gaba da yin abunda yake yi wanda bata san ko minene ba, bayan d'an wani lokaci ba tare daya juyo ba yace mata ba ayin Day ne School en nasu,

"A'a ana yi, ai ko matar Ya Haisam Day take ni kuma Saboda ba garin nike ba yasa nike yin boarding" sai lokacin ya juyo suka had'a ido yace mata amman ba tace tana a wurin Elder sister en ta bane, shiru tay tana kallon shi sam tama manta da tace mashi haka don lokacin da sukai Maganar a rud'e take, tana kikkafta idanu tace mashi eh haka ne amman da Weekend ne take zuwa wurin ta, shiru ya d'an yi sai kuma yace to miyasa bazata zauna a wurin ta ba,

"Ai a boarding d'in an fi yin Karatu ne shiyasa" tana rufe baki taga yayi mata wani kallo mai kaman harara kawai sai ji tay yace sai dae dama in ita bata da k'ok'ari ne, waro ido tay ya d'age mata gira ya furta "Yeah" d'an murmushi tay tare da yamutsa fuska tace mashi wllh ita tana da k'ok'ari kuma sosae, tunda suka fara Maganar sai lokacin yanayin fuskar shi ya canza yay kaman zai murmushi tare da d'an ta6e bakin shi ganin haka yasa ta k'ara cewa "ai nan School d'in ma wllh mara k'ok'ari ma bai iya yin ta, da banda k'ok'ari ai da tuni ma sun kora ni tun kafin in fara karatun" yamutsa fuska yayi tare da d'an murmushi itama murmushin take tana kallon shi suna haka ya d'ago hannun shi ya d'an shafi beard d'in shi can ya furta dama ya ganta online ne shine yayi mata magana just to check on her, bata ji abunda yace ba sosae hakan yasa tace mashi bata ji mi yace ba dama tunda suka fara Vedio call d'in k'asa k'asa take jin voice d'in shi, shiru yay baida alamar zai k'ara fad'in abunda yace d'in, rantsuwa tay mashi tace bata ji ba yace mata Shikenan, marairaice mashi tay tana yamutsa fuska ta furta "Don Allah kayi hakuri wllh kaji na rantse banji mi kace ba" yanayin sautin Maganar tata da yar shagwaba tayi ta wanda ita bata san tayi hakan ba kawai sai gani tay yay d'an murmushi har gefen kumatun shi ya d'an lotsa, lumshe idon shi yay tare da yin yar hamma ya kai hannun shi ya rufe bakin bayan ya gama ya bud'e idon suka shiga cikin nata tay mashi zuru sai lokacin ya maimaita mata abunda yace d'in tay murmushi kafin tace ta gode, shiru bai ce komai ba sai ma d'age kai da yayi idanun shi a lumshe, bin shi da ido Fauzy tay sun d'an d'auki lokaci a haka can ya d'ago slowly ya fara bud'e idanun nashi suka shiga cikin nata, d'age mata gira yay ya furta "any problem?" da sauri ta girgiza mashi kai tace mashi sai anjima ya jinjina mata kai a hankali ya furta "Take care" kai ta d'aga mashi tana murmushi kafin ta kai hannu tay disconnecting kiran, bayan ta kashe kiran Murmushi ta shiga saki ba abunda take gani sai fuskar Sameer hakanan take jin komai nashi na burge ta bata ta6a zaton haka daga gare shi ba a yadda farko take mashi kallon mai girman kai, maida bayanta tay jikin bango ta d'age kai tana cigaba da sakin murmushi tana haka taji wayarta tayi k'ara alamar shigowar sak'o, sauke kanta tayi ta fara k'ok'arin duba sak'on, lokacin data ga sak'on wanda credit alert ne na kud'i dubu d'ari biyar aka turo mata gaba d'aya zaro idanu waje tay ta kai d'ayan hannunta ta dafe k'irji baki bud'e take kallon screen d'in wayar, mamaki ne ya cikata don ta gane Sameer ne ya turo su, "to ya akai ya san account number d'in ta??" Itace tambayar da ta shiga jefa ma kanta, zuciyar ta ce ta fara raya mata k'ilan lokacin da ya d'auki wayar a gidan daya kaita wanda dama a lokacin take tunanin ya d'auki number d'in wayarta can kuma ta k'ara yin tunanin ko kuma ranar da ya bata waya da suka taho a hanya ya amshi wayar tabbas a d'aya daga cikin hakan ne ya d'auka, tama rasa murna zatai ko mi don sosae mamaki ya kamata na yadda ya turo mata wannan iyayen kud'in, ta d'an d'auki lokaci tana ta mamakin kafin tay tunanin kiran shi don tay mashi godiya, sau biyu ta kira bai d'aga ba kiran na biyun ma kafin ya katse taji yayi rejecting, Aunty Mareeya ce ta fad'o mata a rai da sauri hannunta har yana rawa ta shiga kiran ta, tana yin ringing biyu ta d'auka, gaisawa sukai tay mata ya School da yake yau Fauzyn ta dawo daga Weekend,

"Aunty Albishirin ki!" tana rufe baki da sauri tace "Goro d'an Governor ya kira ne? don Allah Fauziyya kice man shi ne ya kira" dariya Fauzy ta kyalkyace da ita Aunty ta buga wani tsoki a k'agare ta furta "dalla ni ki fad'i man in shine d'in ya kira" tsagaitawa da yin Dariyar tay tace mata eh ya kira, wata uwar hamdala ta saki ta fara fad'in Alhamdulillah Allah ya amsa Addu'ar da take tayi,

"Ya kukai da shi da ya kira?" Cikin washe baki Aunty ta tambaya,

"Kawai fa na hau online sai gani nayi an yi man magana da bak'uwar lamba na shiga cikin chat naga an tambayi ya nike to dana ga bansan ko waye ba sai na duba hoton dp naga shine ina cikin dubawar ma sai ga Vedio call ya shigo..
......." Nan ta kwashe komai ta fad'i mata, a d'okance Aunty tace "Kai Ma sha Allah abu yayi dad'i wllh, ai kece da shegiyar kafiya wllh ba yadda banyi dake ba akan ki kira ki gaida shi amman kika k'i da yanzu an wuce wurin k'ilan anata Maganar saka rana ma, su mutane irin wannan ai ba'a masu sanya tunda dai an samu dama irin haka ma mantawa suke da mutum wllh shima nasan Allah ne ya amsa Addu'a ta ya karkato hankalin shi gare ki, to yanzu Shikenan iya gaisuwar kukai ko da wani abu?" Fauzy dake ta yar dariya tace "a'a....." bata k'arasa ba Aunty ta katseta "yace zai zo kenan?" Dariya Fauzy ta k'ara sakawa tace "ni fa Aunty bamu yi hakan da shi ba, kud'i ne ya turo man yanzu bayan mun gama wayar 500k bamma san ya akai ya samu account number dina ba amman nafi tunanin k'ilan dai d'auka yay a wayata" jin har ta gama Maganar Auntyn bata ce komai ba yasa ta kira Sunanta tace mata tana jin ta, wata uwar ajiyar zuciya Aunty Mareeya ta sauke a razane ta furta "Yar gidan Hajiya dubu d'ari biyar fa kika ce, rabin miliyan fa kenan!"cike da tabbatarwa Fauzy tace mata eh wllh gama alert d'in nan, shewa Aunty Mareeya ta saka tana fad'in "Wayyo Allah dad'i kashe ni ni Mariyatu, Yar gidan Hajiya na fad'i maki komar ki ta kamo mana gingimemen kifi wllh Manya masu babbar kyauta, wannan irin kyauta haka farko Wayar fin miliyan yanzu kuma kud'i rabin miliyan a hakan ma wai ba soyayya ake ba to inaga in an fara Soyewa kina sakar mashi kalamai ai sai baki ATM kawai wllh" dariya sosae Fauzy ke yi itama Aunty dariyar take ta farinciki,

"Ina ganin yakamata a kira su Hajiya a sanar masu game da shi" da sauri Fauzy tace "a'a Aunty ni ina ganin bai kamata a sanar dasu ba...." Katseta tay cikin d'aga murya tace to Saboda me, Fauzyn tace "Saboda ban son suma su saka rai kamar yadda kika saka tunda kinga ba wani abu ke tsakanin mu dashi ba kece kawai kike ganin sona yake"

ajiyar zuciya Aunty ta sauke "hakane, amman yanzu dole wani abun ya shiga tsakanin ku na fahimci in aka daka ta tashi ba ranar da zai fito ya bayyanar da abunda ke ran shi don haka ki zo gida inada Meeting da ke" Fauzy dake dariya tace duka ba yau ta dawo Makarantar ba tace eh tazo dai tana son ganinta,

"amman yanzu fa yamma tayi Aunty ko a bari sai gobe in an tashi Class direct sai in taho nan"

"Ok hakan yayi, yauwa in kika fito ki tsaya wurin mai gashin kazar nan na wurin Asibiti ki siyo mana dankwala dankwala guda ko ukku koma biyar sannan nasan baki rasa sanin inda ake saida su shawarma ki tsaya ki siyo mana har da pizza dasu ice cream ba sai kin siyo lemu ba tunda akwae anan ni kuma nan zan yi had'addan Abinci don wannan abun farincikin dole muyi Walima" dariya sosae Fauzy ke yi tace to sai ta turo kud'in da zata siyo abubuwan data lissafan aikuwa a hasale tace su kud'in da aka turo matan don ta kalle su ne ya turo mata, cike da ankararwa Fauzyn tace "amma Aunty an ta6a mashi kud'i kuwa....",

Katseta tay "ajiya ya baki su ne, ko rok'on shi kikai, koma rok'on shi kikai sun halatta a ci su tunda ya baki" Fauzy tace "a'a Aunty kar fa a tada lissafi daga baya" tsoki ta buga tace "aita tadawar da yake ance maki shi K'aramin mutum ne, su irin su da sun ba mutum abu suke mantawa, ke in ma yace a biya shin ai muna da hali sai mu saida gonar gado" ta k'arasa tana kyalkyatar dariya itama Fauzyn dariyar take don ta gane dalilin da yasa ta sako zancen gona Saboda labarin data bata ne na Maganar gonar data yi mashi, cikin dariya Fauzy tace "Aunty ta ina ta zama gonar gado ga mai ita a raye, tace "ai shima gada yayi a wurin kakan mu ko kinga ai ta gadon ce kenan" dariya suka saka gaba d'aya daga baya sukai sallama kafin ta kashe ta tambayi to tayi mashi godiya ma kuwa ta sanar da ita yak'i ya d'auka tace ta kyale shi to sai wani lokacin in sun k'ara yin magana sai tayi mashi.

A ranar da daddare misalin k'arfe goma da wasu mintuna Senator yazo kawo ma Hajiya da Fatuu Fura kamar ko yaushe, tana zaune a parlor ya shigo bayan ya zauna sun gaisa da fara'a ya tambayi yau ina yar taya ta hirar ya ganta ita kad'ai ko har tayi bacci, d'an ta6e baki Hajiya tay tace tana d'aki yau fushi take shiyasa ta k'unk'ume a cikin d'aki, cike da kulawa ya tambayi abunda yasa take fushin Hajiyar ta fad'i mashi zancen karatun ta ne so take su koma taci gaba da zuwa shine tace mata ba yanzu ba tunda ba yadda za'ai tayi tafiya mai tsawo a yanzu, d'an murmushi yay yace "ina ruwan Daughter lafiya ai tana gaba da komai, na fahimce ta tana da babbar hujja inaga abunda za'ai za'a tuntu6i Makarantar tasu in za'a iya yi man Alfarma sai taci gaba da yin karatun ta online zuwa a k'ara d'an lokaci ta k'ara samun lafiyar da zata iya yin tafiya ba tare da tunanin wata matsala ba" kai Hajiya ta jinjina mashi tace in zai yuwu to ayi hakan don ba K'aramin son karatun take ba in ba cigaba taga tayi ba ta dingi damuwa kenan kuma hakan ma na iya haddasa mata wata matsalar don ba'a son mai ciki da damuwa, kai ya jinjina mata tare da mik'ewa yace bari ya gan ta ya k'ara kwantar mata da hankali, a bakin Bedroom d'in ya tsaya yayi sallama, sau biyu yayi shiru ba'a amsa ba hakan yasa shi shiga, hango ta yay kwance ta lullube rabin jikinta da duvet nan ya gane tayi bacci, juyowa yay ya dawo cikin parlon bayan ya zauna ya sanar ma Hajiyar bacci take yace in ta tashi sai a k'ara kwantar mata da hankali in sha Allah yadda yace d'in yana tunanin zai yuwu tace to, yar hira suka ta6a kafin yay mata saida safe ya tafi.

*Bayan Wata Biyu*

A kwana a tashi ba wuya a wurin ubangiji gashi cikin Fatuu har yayi wata ukku lokacin watan Haisam d'aya da rabi da tafiya, Sosae take samun kulawa a wurin dukkan Mutanen gidan ko tari tayi sai an tambaye ta lafiya, haka ta bangaren Abinci kullum ne da safe zuwa dare sai an tambayi abunda take so ta ci wani lokacin ta fad'i wani lokacin kuma tace zata ci abunda aka yi, sosae take hutawa don ko tsinke wannan bata kaudawa hakan yasa ta kara yin k'iba kumatunta sun k'aru ga wani irin fari data k'ara kamar Madara dama ita ba ja bace fara ce ta yi wani fayau ga fatarta tayi wani irin lukui lukui, ta bangaren jikinta ma hips d'inta sun k'ara saidai boobs d'inta sunfi k'aruwa sunyi fam dasu ga cikin nata har ya fito ana ganin shi ba kamar in tasa kaya da suka kamata sosae ake ganin shi, suna yin waya da Vedio call da Haisam akai akai don kullum ne sai sun yi wani lokacin wuni suke suna wayar in suna Vedio call har cikin take bud'e mashi ya gani haka Fanan ma sosae tayi murna ganin cikin ya fara fitowa tai ta kafa mata sharudd'a kan cikin ita kuma taita dariya, bangaren su gwaggo ma kullum sai tayi waya ko Vedio call da su gaba d'aya Mino ta k'osa ta dawo kullum sukai waya sai ta tambayi yaushe zata dawo, haka bangaren karatunta kamar yadda Senator yace ta Online d'in yanzu take yi har su Assignment da test duk ana mata hakan yasa ta kwantar da hankalinta, bangaren Fauzy itama tana kiran Sameer ta gaishe da shi saidai ba akai akai ba gudun kar ta zaqe saidai suna yawan yin magana ta chat wani lokacin shike fara mata magana ya tambayi yadda take da karatunta wani lokacin kuma ita ke mashi magana ta gaishe da shi sai dae tun Vedio call d'in da sukai rannan basu k'ara yi ba, Aunty Mareeya duk sukai waya ko ta koma weekend sai ta tambayi ko yace yana son ta tace mata a'a ita basu wannan Maganar da shi ba sai tay dariya tace ai sannu bata hana zuwa.

Ranar lahadi lokacin cikin Fatuu ya k'ara sati guda suna zaune da daddare a parlor suna shan furar su da Dad yasa aka kawo masu don shi yayi tafiya tare da Mr. President basu K'asar dama shi na hannun daman shi ne ana hasashen ma shi ne d'an takarar shi da zai tsaida a Za6e mai zuwa, suna cikin shan furar Hajiya tace "Fateema ina ga fa barin ki zan yi anan don hankali na yayi gida na gaji da zaman Abujar nan dama Saboda ke ne in ba don haka ba ni ina zan zauna haka" idanu waje Fatuu data dakata da shan furar take kallonta har ta gama, a marairaice ta fara rok'onta kan to su tafi tare mana Hajiyar tace mata a'a tunda dai tana karatun ta lafiya lou ta zauna ta k'ara lokaci, kwa6e fuska tay nan da nan idanun ta sukai rau rau sun ciko da k'walla, tsam ta mik'e ta matsa gaban Hajiyar ta duk'a a gabanta ta fara mata magiyar su tafi tare don Allah wllh ita lafiya lau take jin ta ba abunda ke damunta in sha Allah lafiya lau zasu je, Hajiya dake kallonta tace ta tashi bata ga halin da take ciki bane zata duk'a haka, k'wallan ne suka fara zubo mata tace to don Allah zasu tafi taren, ce mata tay ta tashi ta zauna ta yunk'ura ta mik'e, bayan ta zauna cigaba da yin k'wallan tayi, ajiyar zuciya Hajiya tayi tace ita ba k'in tafiya da ita take ba kawai matsala take gudu da sauri Fatun tace "in sha Allahu Hajiya ba abunda zai faru tunda ban jin wani ciwo kuma zaki iya sawa ma Aunty ta duba ni" shiru tay tana kallonta ta cikin glasses d'inta fuskarta da d'an murmushi, tasan in ta tafi ta barta bazata kwantar da hankalin ta ba zatai ta damuwa ne dama hada k'arin hakan yasa ta zauna, ajiyar zuciya ta sauke tace Shikenan zata yi ma Dad magana kan hakan in ya amince cikin satin da za'a shiga sai su tafi dama shima jibi zai dawo, rok'onta ta shiga yi kan ai ita zata sa shi ya amincen don Allah Hajiyar nata dariya tana fad'in wai ba nan da Katsinar duk d'aya bane Fatun tace mata eh amman tayi missing d'in su gwaggo ne.

Ranar talata da daddare Senator ya dawo sai washe gari da safe wurin k'arfe tara ya samu shigowa gaisawa da Hajiya ya shirya cikin galleliyar shadda light blue babbar riga da yan ciki sai hula da Agogo da takalma mahad'in kayan sai baza uban k'amshi yake, lokacin tana cikin Bedroom ya shigo bayan yayi sallama an bashi izinin shigowa, tana zaune a bakin gado jikinta sanye da cotton d'in doguwar rigar bacci Fatuu kuma na kwance itama jikinta sanye da kayan bacci riga da wando sai hula bata dad'e da gama yin Breakfast ba ta dawo ta kwanta, yana niyyar zama a kan Carpet Hajiya tace ya zauna a bakin gadon mana, tun bayan da ya shigo Fatuu ta tashi zaune idonta a kanshi tana d'an murmushi bayan ya zauna ta gaishe dashi ya amsa mata da fara'a tay mashi an dawo lpy ya amsa shima ya tambayi jikinta tace mashi Alhamdulillah, k'ok'arin sauka ta fara yi daga gadon yace mata tayi kwanciyarta ba dad'ewa zai yi ba, duk da haka saida ta sauka ta koma kan Carpet ta zauna, gaisawa sukai da Hajiya tayi mashi an dawo lafiya, bayan sun gama gaisawar ne ya fara yi mata maganar tafiyarta da suka fara ta waya tun yana can, tambayarta yay game da Fatuu yace in tana ganin ba matsala sai su tafi taren cike da zolaya tace "ai ina ganin ta zauna kawai in ta samu kaman wata biyar sai ta koma" ta k'arasa Maganar had'i da satar kallon Fatuu, tana jin haka ta yamutsa fuska idanunta sukai rau rau, ganin Hajiya na kallon Fatun tana yar dariya yasa Dad d'in shima kai idon shi kanta kawai sai ganin k'walla sukai sun zubo mata sharr da sauri ta sunkuyar da kanta k'asa, d'an murmushi Dad yay calmly yace "Daughter ko baki jin dad'in zama da mu ne" da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a ba tare data d'ago ba,

"To kukan na miye?" Ya tambaya da fara'a, shiru tay bata ce komai ba ya sake cewa "Ko kina kewar yan uwanki ne?" Da sauri ta jinjina mashi kai,

"Ok, ki daina kuka kin ji za'a duba in dai hakan bazai ja wata matsala ba sai ku tafi tare" kai ta d'aga mashi yace to ta d'ago yaga in ta daina yin kukan, saida ta goggoge fuskar da hannu sannan ta d'ago yana murmushi yace to yaga itama tayi ta d'an yi murmushin Hajiya dake kallonta ma ta yi murmushi, daga baya yayi sallama da Hajiyar tayi mashi Allah ya huta gajiya.

Bayan fitowar shi part d'in Aunty ya nufa lokacin tana cikin d'aki ta koma ta kwanta da yake saida rana zata aiki, tana kishingid'e jikinta sanye da jallabiya kanta a bud'e yasha k'ananun kitso hannunta ruk'e da waya tana amsa kiran da shi ya tashe ta daga bacci ya shigo cikin d'akin da sallama, saida ta cire wayar sannan ta amsa mashi, nufar gadon yay ya zauna ta tashi da sauri tace ma wadda suke wayar tana zuwa, kallon shi tay da murmushi tay mashi barka da shigowa da yake a part d'in shi ta kwana sun gaisa, bayan ya amsa mata ne yay mata Maganar Fatuu yace yana son ta dubata taga in ba wata matsala zasu koma tare da Hajiya, a nutse ta fara mashi bayanin cewa a yanzu dai gaskiya lafiyar Fatun lau don tana duba ta akai akai ba wata matsala a tattare da ita sannan shi miscarriage yana iya faruwa unexpectedly koda ana kiyayewa wani lokacin hakanan ma sai ayi ita abunda take gani a barta ta bita sai a bita da Addu'a kawai tunda barin nata k'arshe zai jefa ta a damuwa ne kuma hakan ma had'ari ne a gareta, sosae tayi mashi bayani tare da nuna mashi duk abunda Allah ya k'addaro sai ya faru duk da kiyayewar nada kyau har ta bashi misali da zuwan su akwae cikin jikinta kuma k'arami ma sosae haka suka hawo jirgi kuma lafiya lou, sosae ya fahimta daga baya ya tafi.

A ranar da daddare lokacin da ya kawo masu Fura Hajiya na zaune tare da Fatuu a parlor tana zaune akan kujera 3 seater ta haye saman ta gaba d'aya ta mik'ar da k'afafu gefenta bowl d'in Fruit ne tana ta sha dama bata dad'e da gama cin Abincin dare na biyu ba, da sallama ya shigo da sauri Fatun ta fara k'ok'arin gyara zama ya d'aga mata hannu yace tayi zaman ta, a kujerar kusa da Hajiya ya zauna bayan ya d'aura ledojin furan kan c-table, gaisawa sukai da Hajiyar Fatuu ma ta gaishe da shi ya amsa yana mata murmushi, juyawa yay kan Hajiya yace mata in Allah ya kaimu ranar Friday zasu tafi ta d'aga mashi kai tace Allah ya kaimu, maido idon shi yay kan Fatuu dake kallon su yace "Daughter sai a shirya in Allah ya kaimu ranar Friday zaku tafi" ba shiri ta washe baki duk dimples d'inta suka lotsa dama ga kumatun sunyi Tubarkallah da sauri takai duka tafukan hannuwanta ta rufe fuska alamar taji kunya duk sukai dariya, Maganar akwatunan ta Hajiya tay ma Senator yace ba matsala zuwa kafin su tafi za'a yi gaba da su. Tun daren Fatuu ta fara had'a kaya a ranar kwanan farinciki tayi.

FRIDAY

Akace komai aka sa ma rana zai zo har ma ya wuce, cike da Nishad'i Fatuu ta tashi har Fuskarta ta kasa 6oye farincikin da take ciki na tafiyar su yau ba kamar da Haisam ya sanar mata da sun koma zai zo, gaba d'aya ta gama shiryawa lokacin tafiya kawai take jira dama tun jiya Alhamis aka tafin mata da dukkan kayanta iya yar jakar kayan da zata yi amfani dasu ce zata d'auka haka Hajiya ma an tafin mata da akwatin ta iya yar jaka ce ta rage mata, da yake Friday ne da wuri yaran gidan suka dawo daga Makaranta bayan an saukko daga Masallaci a tare gaba d'aya suka ci Abincin rana a dining table kowa yaci gayun Juma'a, bayan sun gama cikin parlor suka koma harda Dad aka hau yin hirar bakwana dasu Hajiya har Jidderh na cewa ba don Makaranta ba wllh da bin su zatai taje tayi rainon Baby duk akayi dariya Mom tace da yake yazo duniya ko, Aunty ma cewa tay tana ganin Idan cikin ya kai wata takwas kamata yay ta dawo nan Abuja ta Haihu duk kowa yace haka yakamata ita dae Fatuu murmushi kawai take a k'agare take da su tafi har gani take Lokacin ma bai gudu, sai da akai La'asar sannan duk suka tashi don yin salla daga an gama kuma za'a tafi rakasu Airport..............

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

89

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

.........Wuraren k'arfe biyar da rabi jirgin su Fatuu ya sauka a Airport d'in Katsina, Kawu Amadu da Tk da Mino ne suka zo tarbar su, Mino na sanye da riga da skirt na atampa ta yafa gyale a saman kanta sumarta a fake daga bayan kan yayi tudu sosae, gaba d'aya a k'agare take da taga Adda Fatuu din ta, lokacin da suka k'araso cikin Arrivals d'in Fatuu na sanye da Dubai Abaya fara Sol tasha adon stones tayi rolling veil d'in ta hannuwan ta sanye da yan hannunta na diamond da zobe sai k'afafun ta na sanye da takalma brown da suka hau da kalar aikin gaban rigar masu d'an tudu ne don Hajiya ta hanata saka masu tsini, in ka kalleta sai ka rantse bata san hanyar ruga ba balle har ayi zancen acan aka haifeta don gaba d'aya in ka ganta sai kace ba yar Nigeria ba ce ko kuma ace ruwa biyu, Hajiya ma na sanye da doguwar riga mai had'e da mayafi idanunta sanye cikin glasses, akan idon Mino suka shigo aikuwa da sauri ta mik'e ta nufe su da gudu Fatuu na hango su ta fara sakin murmushi, tana zuwa gaba d'aya ta tafi zata fad'a ma Fatun Hajiya tace "a hankali dai Ameenatu" hakan yasa ta dakata a gaban Fatun tana ta washe baki, hannu Fatuu ta kawo ta d'an rungumo ta bayan ta d'ago da ita tay mata sannu da zuwa tana ta murmushi ta amsa mata ta juya kan Hajiya ta gaishe da ita itama da murmushi akan Fuskarta ta amsa mata, lokacin su Kawu Amadu da Tk suka k'araso duk suna sanye da k'ananun kaya, gaishe da Hajiya sukai bayan ta amsa sukai mata an dawo lafiya kafin suka maida idanun su akan Fatuu, Tk na k'ok'arin gaishe da ita da riga shi gaishe dasu duk suka amsa sukai mata an dawo lafiya, bayan sun gama yan gaishe gaishen Tk ya amshi jakar Hajiya ita kuma Mino ta amshi ta Fatuu a tare suka nufi barin wurin sam Mino ta kasa rufe bakinta sai faman juyawa take tana kallon Fatuu da gaba d'aya ta canza mata, inda sukai parking Mota suka nufa daidai lokacin Fauzy ta k'araso cikin Keke Napep, fitowa tay tana sanye da doguwar rigar material tayi rolling bak'in veil a kanta bayan ta biya mai Napep d'in tana juyowa ta hango su Fatun cikin d'an d'aga murya ta k'wala mata kira hakan yasa Fatuu dakatawa ta juyo, nufar su tay gaba d'aya sun dakata suna jiran ta k'araso, tana zuwa ta d'an rungumo Fatuu tace "Welcome back Bestie nah" Fatun tayi mata godiya tana ta murmushi, bayan ta d'ago ta juya ta gaishe da Hajiya tare da yi mata sannu da zuwa, kallon su Kawu Amadu dake d'an murmushi tay suma tay masu sannu da zuwa Mino ma ta gaishe da ita ta amsa da fara'a, maida idon ta tay kan Fatuu da still Murmushi ne akan fuskarta ta kai hannu ta d'an ja kumatunta ta furta "Wannan kumatu haka da kika aje Tubarkallah ko dai ke kike cinye Abincin gidan ne" tana rufe baki Hajiya ta bata amsa da "kamar kin sani" duk sukai dariya, ce masu Hajiya tayi su je a k'arasa gaisawa a gida duk suka juya, ganin Motar kamar bazata ishe su ba yasa Fauzy cewa bari ta samu Napep sai ta bi bayan su Kawu Amadu yace lafiya lou zata isa bari su zauna a gaba shi da Mino, bayan duk sun shiga cikin Motar Hajiya da Fatuu da Fauzy ne a baya suka tafi.

Lokacin da suka iso Unguwar su suna zuwa gab da gida Mino ta kira Gwaggo a waya ta sanar mata gasu sun dawo don da harda ita za'aje tarbar su to sai taga Motar bazata isa ba in aka d'aukko su hakan yasa ta fasa zuwa tace masu in sun dawo sai su sanar mata, A daidai bakin gate Motar ta tsaya su Officer suka taso da sauri suka zo bakin Motar aka zuge glass d'in cikin washe baki suka hau yi masu sannu da zuwa duk suka amsa, bayan an zuge gate d'in suka kutsa cikin gidan, part d'in Hajiya ya tunkara tace mashi ya kaisu cikin parking space kawai yadda ba sai yasha wahalar maido Motar ba tama mik'ar da k'afafunta, lokacin daya parker Motar Officer Jamil mijin Saude ya k'araso da sauri ya bud'e k'opar side d'in da Hajiya take Fauzy ta bud'e ta d'ayan side d'in haka su Kawo Amadu ma duk suka firfito, k'ara gaishe da Hajiya Officer yay cikin washe baki tayi mashi ya aiki ya amsa da Alhamdulillah kafin yace sun yi kewarta sosae cikin Fara'a tace "to ai gani na dawo kewa ta k'are ko" yana yar dariya yace hakane, kallon Fatuu yay ya yi mata ya jiki tace Alhamdulillah, tambayar akwai kaya yayi Hajiya tace mashi ba wasu kaya duk anyo gaba dasu ya je kawai yace to tare da yi masu Allah ya huta gajiya ya nufi komawa gate,

har zasu fita daga cikin wurin Hajiya ta kai idonta kan wata Mota dake a lullu6e da tamfal, dakatawa tay ta nuna Motar da sandar ta tace ma Tk wannan fa yace mata Tahir ne ya kawo ta kusan fin wata kenan yace Ya Haisam ne yace ya kawo, jinjina kai tay tace ko Mota ya canza ne Tk d'in yace bai sani ba, kallon Fatuu tay tace "Mijin ki ya fad'a maki yayi sabuwar Mota ne" shiru ta d'an yi kafin tace a'a bata san ko tashi bace amman dai ya nuna mata hoton motoci yace ta za6a tun ranar da su gwaggo suka dawo Hajiyar tace to k'ilan tata d'in ce, da sauri Tk yace bari ya bud'e taga in itace yace ma Amadu ya kama mashi, lokacin da suka bud'e Motar har saida gaban Fatuu ya fad'i ganin jigunannar Motar matsayin tata don ta shaida wadda ta za6a d'in ce, gaba d'aya maido idanun su sukai kan Fatuu suna son jin tata d'in ce saida Tk yace mata itace sannan ta d'aga mashi kai alamar eh jiki a mace, da tsananin mamaki duk suka shiga bin Motar da kallo don ta had'u dai ba k'arya,

"Yanzu kina nufin wannan jibgegiyar Motar taki ce?" Amadu ne ya tambayi Fatun da mamaki, murmushi kawai take ta kasa magana don itama sosae taji Al'ajabin ganin Motar a matsayin tata, Hajiya ce tay d'an murmushi tace "tunda ta fad'a tata d'in ce, ai ba abun mamaki bane Ahmad, ko kamanta Mijinta sune Mota" Murmushi yay tare da jinjina kai Hajiya tayi mata Allah ya sanya Alkhairi suma suka shiga yi mata Mino sai washe baki take tana ta6a jikin Motar haka Fauzy ma taji ma Fatun farinciki sosae, Saude ce ta k'araso wurin don bata san sun iso ba tana d'akinta acan baya saida Officer ya kirata yay mata Albishir d'in dawowar Hajiyar, cikin washe baki ta gaishe da ita tare da an dawo lafiya Hajiya na murmushi ta amsa tay mata ya gida Sauden tace "gidan duk ba dad'i wllh da baku nan" yar dariya Hajiya tay tace to ai gata ta dawo sai su dasa daga inda suka tsaya Saude ta fad'ad'a dariyarta, kallon Fatuu dake kallonta tana mata murmushi tay suka gaisa itama tay mata an dawo lafiya da ya k'arfin jiki, maida idonta tay kan Motar da taga ana kallo Hajiya tace mata wai Motar Fateema ce suka tsaya kallo Sauden tace "Ma sha Allah, ashe ta Fateema ce amma dai Motar tayi kyau wllh" kallon Fatuu tay tayi mata Allah ya sanya Alkhairi ta amsa tana murmushi, nufar barin wurin Hajiya tay tana fad'in ita dai ta wuce in sun gama ganin Motar sun shigo Saude ta bi bayanta,

tana barin wurin Mino ta had'e hannuwanta ta hau yin d'an tsallen Murna tana fad'in yanzu wannan Motar ta Adda Fatuu ce, dafa Shoulder d'inta Fauzy tay suka kalli juna tace mata ta taya ta murna wllh Allah ya sanya Alkhairi ya tsare ta amsa da Amin tare da Fad'in " kema Allah ya maida ke a damshi na" Fauzy tace "Wai.....to Amin dai" duk sukai yar dariya,

"Ikon Allah, Yanzu wannan bugaggar Motar ta wannan yarinyar ce da aka raina tare da ni" Kawu Amadu ne ya fad'a yana ta tatta6a Motar don ba K'aramin tafiya tay da shi ba duk sukai dariya Tk yace "baka ji ance dare d'aya Allah kan yi Bature ba" da sauri Amadu ya jinjina kai "tabbas na shaida hakan akan yar fillo" duk suka kwashe da dariya, cikin washe baki Mino tace yakamata a d'ana su, Tk yace yanzu tunda yamma tayi kuma ga su Fatuu basu dad'e da dawowa ba a bari sai gobe tunda Weekend ne sai su zagaya gari cike da murna tace to, fitowa sukai daga cikin parking space d'in suka nufi part d'in Hajiya sai santin Motar suke ba ma kamar Amadu har Tk na fad'in ya lura dae Motar tayi mashi yace wllh ai ta had'u ba k'arya,
"kuma kasan Motar can fa zata iya yin miliyan Ashirin wllh" Tk ne ya fad'a duk suka waro ido bama kamar Fatuu sai yanzu ta gane dalilin da yasa Haisam yak'i fad'i mata kud'inta, sosae suka jinjina kud'in Motar har Amadu na rok'on Fatuu akan wai tace a canzo mata guda biyu daidai kud'in wannan sai ta bashi d'aya harda cewa shi ko ma ba mai kud'i ba tata tafi tsada don Allah duk sukai dariya lokacin suka k'araso bakin entrance suka shige, lokacin da suka shiga Hajiya na zaune akan 2 seater gabanta Sofa table ne Saude ta kawo mata bottle water da cup har ta sha Saude na zaune kan one seater daga can gefe suna hira, ciki suka k'araso kowa ya samu wuri ya zauna aka cigaba da yin hirar, bada Jimawa ba gwaggo ta shigo da sallama tana sanye da dogon hijab Navy blue da ta fito da hasken ta sosae, da murmushi ta k'araso ciki duk idanunsu na akanta Fatuu na ganinta ta mik'e da sauri ta nufeta tana ga gwaggonta, tana isa gwaggon ta tareta ta hanyar ruk'e ta tana mata murmushi, a shagwabe tace "Don Allah gwaggota ki bari in rungume ki wllh nayi missing d'in ki sosae" yar dariya gwaggo tay Fatun ta k'arasa fad'awa jikinta, d'agota tay suka nufo ciki gwaggo na yar dariya Hajiya tace "ai ni dai bansan ranar da Fateema zata girma ba wllh, ga dai girman ya kamata amman tak'i ta gane" duk akai dariya, zama gwaggo tay ta shiga gaishe da Hajiya tare da yi mata an dawo lafiya bayan sun gama gaisawa Saude da Fauzy duk suka gaishe da ita da fara'a ta amsa masu, juyowa tay ta kalli Fatuu data sak'alo hannunta ta rungumo kafad'ar gwaggo suka bi juna da murmushi,

"Gwaggo kinga Kumatun Adda Fatuu kamar an tura biredi ko" Mino ce tayi Maganar duk suka kwashe da dariya, Saude tace ma Hajiya table a shirye yake ko ta kawo Abincin nan ta d'an girgiza mata kai "ni kam dai a k'oshe nike saida muka ci muka k'oshi muka taho kuma a jirgi ma mun ci Snacks sai dai ko su Ameenatu in zasu ci k'ilan kuma uwar biyu taci don ba mamaki ta fara jin yunwa yanzu" a d'okance Mino tace "Adda Fatuu yan biyu zata Haifa" d'an yarfa hannu Hajiya tay tace "wama ya sani, in don ta Abincin da take ci ne in akace yan hud'u ma zata Haifa ai ba'a gardama ba" duk akai dariya,

"Ga shi kun zo tarbar baki mu kuma ko tsaraba ba mu yi ba" duk suka ce a'a ba komai Hajiyar ta sake cewa "ai ko ba don ku ba ma dole in nemo tsaraba kafin yaran unguwa su fara shigowa" Saude tace aikuwa kullum ne akai akai ake shigowa tambayar Hajiya ta dawo,

"Ai na sani, bari kiga asan na dawo yanzu a cika parlon anzo yi ma Hajiyar sanata sannu da zuwa" in ji Hajiya, Fatuu ce tace tana da su biscuits da chocolates a cikin kayanta da akayo gaba dasu sai a basu, tana rufe baki Hajiya tace "a'a ruk'e abun ki ban shirya ma rikicin mai juna biyu ba, yanzu in amsar maki abu kizo ki burkice man ke sai irin su kike so ni ina zan nemo maki su tunda ga Ahmad nan yaje shago ya kawo man hankalina a kwance" gaba d'aya aka sa dariya harda Fatun, mik'ewa gwaggo tay zata tafi tay ma Hajiya Allah ya huta gajiya zumbur Mino ta mik'e tana fad'in suje taga hadaddar Motar da aka Siya ma Adda Fatuu, da alamun mamaki tace Mota tayi kenan Amadu yace "Mota kam mai sunan Mota wllh" murmushin farinciki gwaggo tay kafin tayi Allah ya sanya Alkhairi ta juya kan Hajiya ta hau yin godiya Hajiyar tace "to miye na yin godiya kuma Dije don miji ya siya ma Matar shi abu, nima bansan da ita ba sai yanzu da na gani, kinsan ya samu sabbin jini ya watsar da ni" duk akai dariya Gwaggo tace aikuwa dole zai dawo mata don da tsohuwar Zuma ake Magana Hajiya ta ta6e baki tace bata so ta yafe masu shi, k'ok'arin mik'ewa tay itama tana fad'in bari ta shiga ciki Magrib ma ta kawo jiki, a tare da gwaggo duk suka fito suka nufi parking space,

Tk da Amadu ne suka bud'e mata Motar ta gani ta hau yin faffad'an murmushi Mino tace "gwaggo ya kikab ga Motar?" jinjina kai tay tace "Ma sha Allah, tayi kyau sosae wllh, Allah ubangiji yasa Alkhairi ya kuma tsare" duk suka amsa da Amin harda Fatun, Amadu ne yace ta matso ta ta6a tasa Albarka Mino harda fad'i mata kud'in da Tk yace Motar take sosae gwaggo ta jinjina kud'in, bayan ta gama gani an maida an rufe suka fito daga cikin parking space d'in Tk yay masu sallama ya nufi baya inda d'akin shi yake, Fatuu tace ma gwaggon tazo suje part d'in ta tana murmushi tace tayi mata mi tace su k'ara gaisawa sai tayi salla a can, girgiza mata kai tay tace ta dawo wani lokacin a shagwabe tace ita da ba wani zuwa take ba, magiya ta fara yi mata gwaggon tace bafa zata je ba tunda dai sun gaisa, sallama sukai da ita ta tafi tare da Amadu su kuma suka nufi part d'in su Fatuu,

A bud'e kopar parlon take, lokacin da suka shiga wani irin k'amshi mai dad'i had'e da sanyin Ac ne suka tarbe su, parlon tsab da shi yasha gyara a wurin Saude, saman L-shape suka zauna wani irin farinciki Fatuu ke ji ganin ta a parlonta sosae tay missing part d'in nata, cire veil d'inta tay ta aje gefe Fauzy ta kalli kanta tace ba dai ta son kitso Fatun ta d'an yatsina baki tace wllh kitso takura mata yake, Fauzy tace harda don yana da yawa ne gashin ga kuma tsawo, hannu takai ta dafa Shoulder d'in Mino tace "Amaryar Nameer Ali Zakee ya Angon naki halan ana ta shan love?" dariya Mino tay sai kuma ta mik'a mata wayar hannunta wadda Samsung ce, bayan ta amsa Jujjuya ta tay tana k'are mata kallo kafin tace "Amman dai tayi kyau wllh, itace Wayar da aka Siya maki d'in" tay Maganar idonta akan Mino,

d'aga mata kai tay "eh, 300k ya turo sai Kawu Amadu ya siyo man, rannan ma ya k'ara turo man 200k" d'an waro ido Fatuu tay tace "Lalle Nameer ba K'aramin ji yake da ke ba, shi da yake d'alibi yake turo maki kud'i haka, koda yake yi mashi komai ake gara shima ya fara hidiman iyalin shi" duk sukai dariya,

"K'awata ke kuma ya ake ciki tsakanin ki da Sameer ince ko an samu cigaba kun fara shan love ku ma?" Yar dariya Fauzy tay kawai ba tare data ce komai ba, hannu Fatuu ta kai ta d'an bugi shoulder d'inta tace don Allah ta fad'i mata ya ake ciki,

"To ni mi zance maki ai duk abunda ake ciki kin sani, har yanzu yadda kika sani muke muna dai gaisawa yaji ya nake shikenan" d'an jinjina kai Fatuu tay "ba komai ai anyi mai wuyar tunda kunsan juna duk ya gama nuk'u nuk'un shi zai fito ya bayyana abunda ke ran shi ne ai sannu bata hana zuwa zamu yi ta zuba mashi ido har muga gudun ruwan shi" Fauzy na dariya tace haka Aunty Mareeya ke cewa,

"Allah sarki Aunty Mareeyata itama nayi missing d'inta Sosae wllh" Fatuu ta fad'a tana murmushi, Fauzy tace "kinsan kuwa da tare da ita zamu zo Airport don har ta shirya kawai sai tayi bak'uwa amma tace in maki sannu da zuwa sai tazo har gida" Fatun tace zama ta kirata kuma zata je har gidan ba sai ta zo ba. Sai da aka kira sallar Magrib sannan suka tashi suka nufin Bedroom, Fatuu ce ta fara yo Alwala sannan Fauzy ma ta shiga, ganin har zasu kabbara Mino na zaune yasa Fatuu dakatawa tace mata ita bazata tashi tayi sallar bane tay mata murmushi kawai, tambayarta tay bata yi ne ta d'aga mata kai Fatun ta d'an ta6e baki ta kabbara, suna gama sallar Saude ta zo ta sanar dasu ga Abinci can ta kawo kan table da sauri Fatuu ta mik'e daga kan prayer mat tana fad'in "Allah yay maki Albarka Aunty Saude kamar kinsan yunwa nike ji wllh" duk sukai dariya, bayan sun cire hijabs da sukai sallar gaba d'aya suka nufi parlon. Bayan sun yi sallar isha Fauzy ta mik'e tana fad'in bari ta tafi dare yayi Fatuu tace ta tsaya ta kwana mana,

"Kwana kuma?" Fauzyn ta fad'a tana yar dariya, Fatun tace eh,
"a'a gida zan tafi abu dai ana gari d'aya miye na in kwana kuma"

Fatuu tace to ai wanda take mawa dai baya nan kuma Mino ma anan zata kwana, shiru Fauzyn tay Fatuu ta k'ara cewa "Ke Allah ma sai kin kwana, dama bakuyi man kwanan Amarya ba to shi zaki biya ni" gaba d'aya suka sa dariya,

"To ai dama yanzu Kusan so ake a kashe kwanan gidan Amarya in an kaita wasu garuruwan ma dama ba'a yi don haka ba sai na biya ba" kafewa Fatuu tay kan ta kwana tace to ai bata tambayi Aunty Mareeya ba, hannu Fatuu ta kai ta d'aukko wayarta tana fad'in abu mai sauk'i in don wannan ne bari ta tambaya ma da kanta, tana fara ringing Aunty ta d'auka,

"Yar gidana ta kaina an dawo lafiya" tana murmushi ta amsa mata da lafiya lau,

"To ya jiki jikin?" Amsa mata tayi da Alhamdulillah, tace "anata laulayi kenan halan ma har ya fito?" k'asa k'asa ta bata amsa da eh,

"ma sha Allah, Allah ya inganta mana, ai naso in zo tarbar ki wllh sai nayi bak'uwa" tace haka Fauzy ta fad'i mata ai ba komai, tambayarta tay ya mijinta yana can K'asar turawa ko tace mata eh tace to Allah ya maido shi lafiya, bayan ta amsa tace mata dama so take ta roketa don Allah Fauzy zata kwana anan, da sauri Aunty tace "kai haba ba komai Zarah ta kwana, nan gaba ma kad'an ai sai kin fini iko da ita in ta zama Matar d'an uwan mijin ki d'an Governor don ma d'an bantan uban izza ta hana ya fito ya bayyana da yanzu k'ilan Maganar aure ake tunda da gani son ta yake wllh ba don haka ba yaushe zata samu ma ya rink'a kula ta" dariya Fatuu tay tace haka Fauzy ta fad'a mata har yanzu yak'i bayyanawa, a k'ufule Aunty tace "k'yale shi yayi ya gama ai ina nan ina jiran shi ya shigo hannu sai ya rabu da wannan cutar miskilancin don shi sai yama fi mijin ki magantuwa" dariya sosae Fatuu ke yi bayan ta tsagaita tace to shima na Mino a had'a da shi da sauri tace "ahhh anya Zarah, shi ai kinga baida irin cutar su ta miskilanci bawan Allah bakin shi a sake yake adai kamanta don in akai mashi irin nasu ba wuya zai zare" wata uwar dariya Fatuu ta kyalkyace da ita har Fauzy na fad'in ta dai bi a hankali kar tasa Babyn su ya fito, bayan sun gama wayar tay mata godiya suna yin sallama da sauri Fauzy tace bari tayi mata magana, bayan ta bata wayar a d'okance tay ma Aunty Mareeyar Albishir d'in Motar da aka Siya ma Fatuu, wata uwar gud'a ta rangad'a tace taba Fatuu wayar,

"Da kyau yar gidana, Wllh na taya ki murna Allah yasa Alkhairi ya tsare ya kuma raba lafiya, Wannan in dai za'a rink'a bamu kyautar Mota haka ai duk shekara sai mun haifa masa Baby" dariya kawai Fatuu ke yi tace mata sai tazo d'ani Fatun tace ai suna nan zuwa gobe da Motar a nuna mata tace to Allah ya kaimu tana jiran su, bayan sun gama wayar Mino ta kira Yadikko ta sanar mata zancen Motar sosae tay farinciki tasa aka ba Fatuu wayar ta taya ta murna da Addu'oi daga jin muryarta ba K'aramin farinciki take ba, tambayarta Fatun tay baffan su tace bai kaiga dawowa ba amman da ya shigo zata sana'ar mashi suka cigaba da yin wayar ta tambayi ya suka dawo da lafiyar Fatun duk ta amsa mata daga baya sukai sallama tana ta masu Addu'oi, bayan ta aje wayar mik'ewa tay har lokacin rigar da ta dawo da ita ce tace ma su Fauzy bari ta shiga tay wanka suka ce to kowannan su na latsa wayar shi, daga baya Mino ma ta mik'e tace bari taje gida ta canzo kaya Fauzy tace to bari ta rakata suka tafi tare,

After some minutes ta fito d'aure da towel a k'irjinta ganin ba su Fauzy a cikin d'akin yasata yin tunanin ko sun tafi parlor suyi kallo, shiryawa ta shiga yi cikin silky kayan bacci riga da wando blue bayan ta gama saka kayan ta feshe jikinta da turare, tana cikin gyara gashinta wayarta dake a saman side drawer ta fara ringing ta juya ta nufeta, saida ta zauna a bakin gado sannan ta kai hannu ta d'auko, ganin mai kiran nata yasa ta saki k'ayataccen murmushi dama da suna Airport a Abuja sun yi waya da shi, idasa hayewa tay saman gadon sannan tayi picking, tana d'auka taji yace suyi Vedio call tace to, yana zaune a cikin Office d'in shi jikinshi sanye da blue suit shirt d'in ciki fara ce sai bak'in bow tie sosae kayan sukai fitting d'in shi sumar shi a gyare luff, murmushi suka shiga sakar ma juna kafin ta gaishe da shi ya amsa yay mata sun dawo lafiya tace lafiya lou, tambayar ta Hajiya yay tace tana part d'inta su sun dawo nasu part d'in da Fauzy da kuma Mino ya jinjina mata kai still da murmushi a fuskokin su,

"What are u doing?" Ya tambaya idanunshi a d'an lumshe ta bashi amsa da wanka tayi yanzu ta gama shiryawa ya kira, shiru yay yana ta kallonta can ta tura mashi baki ya d'age gira "What?" A shagwabe tace "shine don kasan Mota d'in nan tana da kud'i sosae kak'i fad'a man ko" shiru yay yanata murmushi tace yayi Magana mana, tambayarta yay waya fad'i mata mai kud'i ce tace ita ta gane data ganta,

"nayi laifi kenan?" ya k'ara d'age gira, a shagwabe tace "a'a, kawai dai naga akwai wasu hidindimun bai kamata ka siyan man mai tsada ba sosae" yana murmushi yace "anything for you Baby ko banda halin abu indae kina so zan yi bakin k'ok'arina ki mallake shi wannan kuma ina da halin shi ne in ma fin shi kike so zan siya maki" wani kalan murmushin dad'i tayi ta lumshe ido irin yadda yake yi bayan ta bud'e a tare suka sa dariya,

"Where is our Baby, ya fara kicking?" waro ido tay ta d'an bud'e baki sai kuma ta saki dariya tace ai bai isa wannan ba ko abunda ko antenatal bata fara zuwa ba, tambayar ta yay sai yaushe zata fara zuwa tace kaman in yayi 4 Month amman ko yanzu tunda ta ya wuce 3 months zata iya fara zuwa ya jinjina mata kai, shiru suka d'an yi sai kuma tace bari babyn yaga Daddy d'inshi ta kai hannu ta d'aga rigarta farar fatar cikin da ya turo ta bayyana ta kai wayar saitin cikin, Kusan kullum ne in sukai waya sai yaga cikin wani lokacin shi ke cewa ta nuna mashi wani lokacin kuma ita ke nuna mashi kamar yanzu, maido wayar tay saitin fuskarta tana dariya shima ita yake yi yace mata yaga ya k'ara girma tace eh ai bata dad'e da gama cin Abinci ba taci ta k'oshi stiil yar dariya yake yace ai an fad'i mashi Abinci take ci sosae, jin haka yasa ta fara bashi labarin yadda a kai ta mamaki wai tayi uban kumatu harda Maganar da Hajiya tayi d'azun tace Saboda cin Abincin da take ko yan hud'u akace zata Haifa ba za'ai gardama ba dariya yay itama ita take yi, bin juna da kallo su kai mai cike da tsantsar k'auna bayan sun lafa da dariyar sun koma yin murmushi,

"Yar fillo zata Haifa yaron Ya Handsome" suna cikin kallon junan taji ya furta hakan, dariya ta k'ara sakawa ta kai hannu ta rufe idanunta alamar kunya can ta cire idanunshi akanta yana murmushi tace mashi mamaki yake a hankali ya girgiza mata kai alamar a'a, tambayar shi tay yaushe zai zo d'in yay d'an jimm kafin yace mata yay postponing lokacin sai nan da 3 weeks, k'amewa tay tana mashi wani kallo ta tsuke fuska yay d'an murmushi, yamutsa fuska ta shiga yi kaman zatai kuka tace ita dae bata yarda ba kenan ma bai yi missing d'inta ba an kusa fa wata biyu da tafiyar shi kuma shine yanzu zai ce ya d'aga lokacin da zai dawo, sigh yay yace itama tasan ko bai fad'i mata ba yana missing nata in every second yana jin kewarta a tare da shi,

"To miyasa ka d'aga dawowar" ta tambaya a shagwabe, hannu ya kai ya shafi gaban kanshi calmly yace mata an kusa bikin Saleem ne shine ya bari sai lokacin yazo so that he can stay a bit long, k'una k'unin shagwa6a ta shiga yi tana jujjuya kai ya hau bata hak'uri yana d'an murmushi, ganin tak'i barin abunda take yi yasa shi ce mata "Ok, in kina so in zo this coming week zan zo but bazan dad'e ba zan dawo tunda ina son zuwa bikin Saleem d'in amman hakan zai sa a ga na fara wasa da aiki tunda ban dad'e dana dawo ba kuma kinga na d'au lokaci anan" dakata tay da abunda take yi na shagwabar tace "Shikenan to na yarda ka bari sai lokacin ka zo amman fa sai ka maimaita man lokacin da kayi anan in kazo wata biyu da rabi zakai sannan ka koma" ta k'arasa ta d'an kumburo baki, yar dariya yay yace tayi mashi hak'uri kar tasa a kore shi a wurin aiki, kafin ta bashi amsa taji an turo k'opar bedroom d'in ta d'aga ido, Fauzy ce ta lek'o suka had'a ido tay mata murmushi, juyawa tay ta koma dama sun dawo ne shine ta lek'o taga mi Fatun ke yi,

"To ba Shikenan ba in sun kore kan sai ka baro masu K'asar su ka dawo nan kawai" ta bashi amsa,
d'age gira yay "to in na dawo ya zamu rink'a samun kud'i?" da sauri tace "to mi zamuyi da kud'in tunda muna da komai" yana yar dariya yace ta ta6a ganin rayuwa ta yuwu ba kud'i dole ai su buk'aci abubuwa kaman Abinci, kaya, da kuma kud'in yin wasu hidindimun gashi ma zata haihu dole su buk'aci kud'i,

nok'e kai tay tace "to ba sai Hajiya dasu Daddy ba su rink'a mana wannan" fad'ad'a dariyar shi yay itama dariyar take yace mata ta dai bari gara su nemi nasu yadda bazasu takura ma kowa ba har a gaji da su,

"to ai zaka iya samun wani aikin ma anan ko da baka fara ba kafin ka tafi" d'an rolling eyes d'in shi yay yace mata ai anfi samun kud'in sosae anan, tambayarshi tay wai dama Saleem bai yi aure ba yace eh an dai dad'e da akai engaging nasu to wadda zai auran tana karatu a London da za'ai auren sai tayi completing karatun a gidan shi daga baya kuma sai aka bari ta gama don shima Saleem d'in yaje ya k'aro karatu sai yanzu za'ai Auren, jinjina kai Fatun tay suka cigaba da hirar su ta k'auna, ganin ta fara hamma yace bari ya barta tayi bacci kar a takura ma Baby tay yar dariya, tambayarta yay ko akwae abunda take buk'ata da sauri ta d'aga mashi kai alamar eh yace miye take so, ce mashi tay irin tuwan Madara da gullisuwa da Popcorn d'in da yake siyo mata take son ci yace Ok zai ma Nana magana sai a kawo mata tomorrow, jin sunan Nana yasata tambayar wai tana nan yace eh, ta tambayi har yanzu bata yi Aure ba yace eh amman anyi engagement,

"Allah sarki na taya ta murna wllh, kai dai ai ka k'i ta" ta fad'a tana murmushi, shiru ya d'an yi sai kuma yace ai lokaci bai k'ure ba in tana son ya auretan da yayi Magana yasan za'a fasa da wanda aka sa masu rana sai ayi dashi, wani kallo tay mashi a d'an k'ufule tace "to a'a wllh, ba kasan da wasa nike ba" yadda ta yi ne ya bashi dariya yace "tunda tana sona da ki bari in k'ara da ita kinga kema kin yi man Alfarma irin na Fanan" yana rufe baki da sauri ta hau yamutsa tana girgiza kai tare da yarfa hannu tana fad'in "Don Allah Hubby mu bar Maganar nan, tunda an sa mata rana ba Shikenan ba nima dama ai wasa nike ko" dariya kawai yake ganin yadda tay k'utun k'utun da rai sai kace ba ita ta ja Maganar ba, ganin irin kallon da yake mata yasa taci gaba da fad'in "Allah ka gama aure, ba wata da zaka k'ara aura mu biyu mun ishe ka" dariya ya k'ara yi har jerarrun hakoransa suka bayyana sosae ita kuma taci gaba da yamutsa fuska tana k'una k'unin Allah bazai k'ara aure ba,

"Ki kwantar da hankali, tunda na same ki Baby na gama aure am just teasing you" wani irin murmushin jin dad'in Maganar ta shiga saki harda d'age kai sama, sauke kan nata tay idanunta suka shiga cikin nashi a wani slow ta lumshe mashi ido ta furta "Ina son ka har abada abadan abada Hubby" shima lumshe mata idon yay cikin cool voice d'in shi ya furta "You are the best thing that has ever happened to me Baby, you made me feel complete" murmushi kawai take saki looking at him with much luv, sallama sukai yace ta kwanta shima sun samu break ne zai yi lunch tace to ai duk yama cinye lokacin suna hira yana murmushi yace ba wani abu ai ko bai ci komai ba ganinta da yayi ya k'osar dashi tana dariyar jin dad'i tace duk da haka dai yaje ya ci Abincin kuma Baby yace ya tabbatar yaci ya k'oshi, yace a fad'i ma Babyn Dad d'in shi zai bi umarni gaba d'aya sukai dariya daga haka suka gama Vedio call d'in, kwance tay saman gadon tana ta faman sakin murmushi wani irin nishadi na ratsata ita kanta tasan ba K'aramin so take ma Haisam ba a yadda take ji yanzu da suka zama d'aya she can't survive without him, a haka bacci yay awon gaba da ita, bada jimawa ba Fauzy ta shigo don tayi wanka ganin yadda Fatun tay bacci yasa ta yin d'an murmushi, saida ta tashe ta don ta gyara kwanciyar ta sannan ta nufi hanyar laundry, d'aure da towel a kirjinta ta fito ta nufi gaban mirror don ta shafa mai bayan ta gama ta nufi closet ta bud'e, wata doguwar rigar baccin Fatuu ta fiddo don ta saka, tana gama shiryawa Mino ta shigo ita dama tun a can gida da suka je ta shiryo cikin kayan bacci riga da wando, gado ta nufa tana fad'in wllh bacci take ji Fauzy data juya tana kallonta tace ta hak'ura da ganin k'arshen film d'in kenan tace eh ai taga basu da niyyar gamawa daga haka ta haye gadon ta ja duvet ta lullube, bakin gado Fauzy ta nufa ta zauna tay shiru, gaba d'aya ganin Fatuu da ciki ya k'ara mata jin son yin aure, dama dalilin auren Fatun taji ta fara sha'awar itama tayi, "gashi ba mijin..." wata zuciyar ta raya mata har saida tay yar dariya, ita gaba d'aya ma ta kasa gane ko tana son Sameer kawai dai tasan yana burgeta, wayarta dake ruk'e a hannunta ta bud'e ta fara latsa ta, gallery ta shiga ta bud'e inda hotunan bikin Fatuu suke ta bud'o wani hoton Sameer da aka yi mashi a wurin Dinner dama tana yawan kallon hoton, k'ura mashi ido tay yana a hakimce kan kujera fuskar nan ba annuri a cikin Zuciyarta ta shiga raya shin da gaske yana sonta, in hakane to miyasa yak'i bayyana mata, kai anya ma kuwa ita sam bata tunanin hakan gaskiya don tana ganin bata kai ya so ta ba,
"in yanzu yazo yace yana son ki zai aure ki zaki amince?" wata zuciyar ta jefo mata tambayar tay shiru kamar mai nazarin wani abu lokaci guda jikinta yay sanyi tunowa da wasu abubuwa, fita tayi daga wurin hoton a sanyaye ta mik'e ta nufi bedside table ta aje wayar har zata juyo ta dakata ta kai hannu ta kunna lamp sannan ta juyo, wurin Switch ta nufa ta kashe hasken d'akin kafin ta juyo ta dawo wurin gadon ta haye gefe ta yadda sun saka Fatuu a tsakiya, lamo tay tana ta zancen zuci ta d'auki lokaci a haka kafin daga baya bacci ya d'auketa.

Washe gari bayan sun yi sallar Asuba komawa Fauzy tay ta kwanta Fatuu kau Kitchen ta nufa don ta samu abunda zata ci ita kuma Mino dama bata tashi ba don ba sallar take ba, sauran Abincin da suka ci jiya data ga bai yi komai ba ta d'umama sai ta had'a da tea, anan cikin kitchen d'in ta zauna taci bayan ta gama ta koma d'akin itama ta koma ta kwanta, wuraren K'arfe takwas saura Mino ta farka lokacin su Fatuu nata shan bacci ta wuce toilet, bata dad'e ba ta fito tayo wanka ta maida kayan baccin jikinta gaban mirror ta nufa ta shafa mai bayan ta gama ta juya ta nufi k'opa, a parlor ta d'auki hijab d'inta data cire da daddare ta saka sannan ta nufi gida don tayi shirin islamiyya.

Wuraren k'arfe sha biyu na rana suka fara shirin tafiya zaga gari kamar yadda akai jiya, bayan duk sun yi wanka suka shiga duba kayan da Fauzy zata saka saidai duk kayan Fatun bazasu yi mata daidai ba Saboda yanayin jikin su ba d'aya ba, k'arshe wata jallabiya suka samu da tayi mata daidai sabuwa ce acikin kayan lefenta da gani ita Fatun in tasa zata d'an yi mata yawa dama ko wadda taba Fauziyyar a Abuja itama tayi mata yawa yawanci dama da ganin dogayen rigunan wasu zasu yi mata yawa amman in ta saka takalma masu tsini ko tudu zasu iya yi mata daidai, itama Fatun shiryawa tay da riga half gown da straight skirt na atampa Fauzy ce tayi mata d'aurin kallabi mai kyau bayan an gama ta fiddo takalma da jaka da suka hau da atampar takalman masu dan tsini ne har Fauzy saida tay mata magana kansu tana murmushi tace ai tsinin nada gwa6i, rolling veil d'in jallabiyar Fauzy tay Fatuu kuma ta d'aukko mayafi daya hau da kayan sosae tayi kyau Fauzy ma ta yaba tace bari tayi mata hoto, atare sukai wasu hotunan bayan sun gama suka tafi gidan gwaggo don suga in su Mino sun shirya dama bayan sun yi Breakfast da suka je gaishe da Hajiya Fatuu ta sanar mata zancen fitar tasu. A can gidan suka ci Abincin rana lokacin Mino ta yi wanka kaya kawai zata saka haka Kawu Amadu ma ya shirya yana d'akin shi gwaggo ma da ita za'aje farko da tace bazata je ba suka matsa mata dole ta shirya, bayan kowa ya gama shiryawa Fatuu ta kira Tk ta sanar dashi yace gashi nan zuwa, bada jimawa ba yazo ya kira Kawu Amadu ya sanar dashi su fito, a tare duk suka fito gwaggo ta kulle gidan tana sanye da riga da zani na atampa tasa Hijab data hau da kayan hannunta ruk'e da purse, kowa fuskar shi da murmushi suka nufo Motar da sai shek'in sabunta take, ganin in suka zauna baya zasu iya matsewa yasa Kawu Amadu yace ma Mino tazo su zauna a gaba sai su kuma su ukku suka shiga baya, zagaya gari suka shiga yi suna hira cikin nishad'i ga Ac na ratsa sassan jikin su sai faman santin Motar suke ita dai Fatuu murmushi kawai take saki don ganin abun take kamar wasa wai wannan Motar ta ce, sosae suka zaga gari saida aka fara kiran sallar la'asar suka wuce gidan Aunty Mareeya, suna zuwa bakin layin gidan Fauzy ta kirata tace tazo ta tarbe su, Fauzy ce ta nuna ma Tk gidan yana Parker Motar gaban gidan sai ga Aunty Mareeyar ta fito tana sanye da doguwar rigar material ta yafa gyale saman kanta da ya bayyanar da gaban kanta daya sha kitso da alama dai tana son dogayen riguna koda yake mutane irin ta dama ita tafi dacewa da su don tana amsar su sosae, cikin washe baki ta nufo Motar duk suka bud'e suka fito, gaisawa suka shiga yi tana yi masu sannu da zuwa Fauzy ta nuna mata Motar tace ga Motar Zarah ta waro ido tana fad'in Don Allah wai wannan bugaggar Motar mai numfashi ce aka siya ma Zarah duk akai dariya, matsawa tay ta fara bin Motar tana dubawa sai faman fad'in ma sha Allah take tana zuba santi, bayan ta gama gani ta juyo tana fad'in wllh ta taya Zarah murna Allah yasa Alkhairi ya tsare gwaggo ta amsa tace masu suyi hak'uri tabar su a tsaye don Allah su shiga, a parlor duk suka zazzauna aka shiga k'ara gaisawa kafin ta mik'e tace ma Fauzy tazo suka nufi Kitchen, dawowa Fauzyn tay tana ruk'e da babban tray da aka jero kayan abinci Aunty Mareeyar ma ta biyo bayanta ruk'e da Warmers masu kyau babba da kuma madaidaiciya, tambayarta Fauzy tay ta kai dining table ne tace mata a'a akai cikin parlon yadda zasu fi jin dad'in bajewa su ci duk akai murmushi, farko cewa sukai duk basu jin yunwa don saida suka ci Abinci sannan suka fito Aunty tace ai tasan sun ci Abinci amman dole itama a ci nata ba kamar su Amadu da Tk da basu ta6a zuwa ba ta kalli Fatuu tace Maman biyu kedai ai nasan zaki ci ko ta d'aga mata kai tana dariya, Aunty tace "haba ai ina ganin wannan kumatukan da kika aje Tubarkallah nasan bakya wasa da Abinci" duk akai yar dariya ta sake cewa "ai angode ma Allah ma gara laulayin cin Abincin da ai ta amaye amaye" gwaggo tace aikuwa hakan yafi, saida kowa yaci Abincin bayan sun gama Amadu da Tk suka tafi Masallaci yin sallar la'asar da aka kira su gwaggo ma suka mik'e Aunty ta kai ta d'akin ta ita kuma Fatuu ta nufi d'akin Fauzy, bayan duk sun yi sallar har su Amadu ma sun dawo a parlon suka zauna aka shiga hira Aunty Mareeya na ta sasu dariya, sai wuraren k'arfe biyar suka fito Aunty tace ma Fauzy ita ta dawo gida ko da sauri Fatuu tace a'a sai gobe zata dawo Aunty tace "an gama ranki ya dad'e uwar biyu farincikin ki shi muke buk'ata yanzu" duk akai dariya tace gaskiya itama ya kamata ta d'ana Motar Tk yace to ta shiga sai ya zagayo da ita tace Yauwa to, seat d'in baya ta shiga ta wani hakimce har saida ta basu dariya, tsayawa sukai yaje ya zagayo da ita bayan sun dawo ta fito tana k'ara yabawa da Addu'oi, sallama sukai da mata tayi masu godiya tana fad'in taji dad'i sosae wllh Allah ya bar zumunci duk suka amsa tace ma gwaggo sai tazo yi mata yini tana murmushi tace to tana jiran ta daga haka duk suka shiga cikin Motar suna d'aga ma juna hannu suka tafi, k'ara zagaya gari sukai sai gab da Magrib suka koma gida harda tsaraba suka yo, gwaggo da Amadu aka fara ajewa tay ma Tk godiya da Allah ya huta gajiya suka wuce, har bakin part d'in Hajiya ya kai su bayan sun fito suka shiga ciki don kai mata tsaraba. A part d'in sukai sallar Magrib da isha suka ci Abincin dare bayan sun d'an yi mata hira sannan suka komo part d'in su Fatuu. Washe gari Lahadi bayan sun ci Abincin rana sun shirya suka tafi gidan gwaggo har saida tay ma Fatuu Maganar zuwan tace ba jiya ta zo ba tace ai jiya ba nan suka zo ba don zasu fita ne yau ne zuwan nata Fauzy nata masu dariya, bayan sallar La'asar lokacin Mino ta tafi Makaranta Fatuu tace ma Fauzy suje su gaida innar su Haulat suka tafi, lokacin da suka isa gidan sosae tay murnar ganin su tace ma Fatuu maimakon ta bari ita tazo ta dubata ai bata san ta dawo bane da tazo tana murmushi tace mata ba komai, sai gab da Magrib suka baro gidan suka koma gidan gwaggo, ana gama sallar Magrib tace ma Fatuu ta koma gida suka tafi tare da Fauzy da Mino, bayan sun yi sallar isha Fauzy ta fara yin shirin tafiya gida don gobe Monday, rigar material d'inta ta maida Fatuu na fad'in ta bar ta jikinta amman ta k'iya, duk da haka saida ta bata kyautar kayan shafa da turare guda biyu harda panties da vest mai had'e da wando sai sark'a da yan kunne masu kyau, farko k'in amsa Fauzyn tay tace ai abun yayi yawa ina laifin duk abubuwan Alkhairin da aka yi masu acan Abujar, magiya Fatun ta hau yi mata kan ta amsa tana fadin ai don tana da su ne ta bata ko k'arshe saida ta nuna mata 6acin rai sannan ta amsa tayi mata godiya da Addu'ar Allah ya sauketa lafiya, Tk ta kira ta tambayi yana gida yace eh yanzu dai yake niyyar fita ta rok'e shi kan ya aje Fauzy gida yace Ok ta fito, tare suka fito harda Mino suka nufi part d'in Hajiya don tayi mata sallama, tana zaune a parlor suka shigo bayan duk sun zauna suka gaishe da ita ta amsa Fatuu tace mata dama Fauzy ce zata tafi shine tazo yi mata sallama Hajiyar ta tambayi taci Abinci ne Fauzyn tace eh sun ci a gidan gwaggo, ce mata Hajiyar tayi bari a kawo mata ta k'ara sai ta tafi tana murmushi tace ta k'oshi ai basu dad'e da suka ci ba, Tk ne ya kira Fatuu yace gashi yazo parking space bai ganta ba ko bata fito bane tace mashi gasu nan zuwa, kallon Fauzy tay tace suje ga Tk d'in can yazo duk suka mik'e Hajiya tace ta bari a bata kud'in Napep Fatuu tace ai Tk ne zai kaita gashi can ma ya fito tace to hakan yayi tay ma Fauzy godiya da Addu'ar Allah ya bar zumunci ta amsa tana murmushi suka tafi, lokacin da suka fito har Tk ya fiddo Motar Fatun cikin harabar, bayan sun k'arasa a gefen Motar suka tsaya suna k'ara yin sallama Fatuu tace mata sai sun had'u gobe a School Fauzy tace "ai nayi zaton zaki k'ara hutawa tunda ana maki komai online" ce mata tay a'a zata cigaba da zuwa tunda ta dawo dama ba wani jin dad'in karatun take ta online ba tunda ba haka ta saba ba kawai don ya zama dole ne tace Shikenan to sai sun had'u goben tay ma Mino sallama ta shiga gaban Motar dama Tk na driver seat yaja suka tafi su kuma suka koma part d'in Hajiya.....

90

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

..........Washe gari Fatuu na gama sallar Asuba ta tashi Mino suka fara shirin tafiya Makaranta, Mino ce ta shiga Kitchen don ta had'a masu breakfast ita kuma Fatuu ta shiga wanka, bayan ta fito ta fara shiryawa itama Mino ta shiga tayo wankan, anan ta shirya dama tun jiya da daddare taje gida ta d'aukko Uniform d'inta, saida suka gama shiryawa sannan suka yi Breakfast suna gamawa Fatuu ta kira Tk ta sanar dashi sun shirya yace to su fito, a cikin Motar ta suka tafi saida aka fara ajiye Mino kaman ko yaushe sannan aka wuce da Fatun, lokacin data je sosae yan class d'in su suka nuna murnar ganinta aka shiga zuwa yi mata sannu da dawowa da tambayar jikinta, bata dad'e da zuwa ba Fauzy ma ta zo. Bayan an tashi Tk yazo ya d'auketa suka biya suka d'auki Mino, a gida Mino tace a ajiye ta sukai sallama da Fatuu tace sai ta dawo islamiyya zata zo suka wuce, part d'in Hajiya ta nufa bayan sun isa gidan don wata irin yunwa take ji a haka ma wai taci Abinci sosae da break sannan gab da za'a tashi ma saida tasha youghort da cake da ta aje Saboda in taji yunwa, saida ta cika cikinta sannan ta koma part d'in su tana zuwa ko Uniform bata cire ba ta haye gado ta hau yin bacci, saida akai sallar la'asar sannan ta farka ta nufi toilet, wanka tayo ta dauro Alwala ta fara shiryawa cikin doguwar rigar Atamfa ta kabbara salla, bayan ta gama gaban mirror taje ta shafa yar powder da lip glow tana yi tana murmushi itama tana ganin canzawar da tayi sosae, gyale ta d'aukko ta yafa ta d'aukko jakar Makarantarta ta nufi part d'in Hajiya, lokacin data isa Hajiyar na zaune a parlon ta nufo ciki da sallama ta juyo tana amsa mata, kujera ta nufa ta zauna idon Hajiya a kanta ta gaishe da ita ta amsa kafin tace "an dawo" kai Fatuu ta d'aga "Eh tun d'azu nan ma na fara zuwa lokacin kina bacci naci Abinci sannan na tafi" kai ta jinjina mata, tana k'ok'arin fiddo littafi taji tace "Yanzun wannan rigar da kika saka baki ji kin takura ba, illar matsattsun kayan kenan dole wani lokacin kana ji kana gani baka iya saka su yanzun d'an nan gaba kad'an ya za'ai ki saka wannan rigar ai bata sanyuwa a wurin ki kinga da wadatattu ne ko yaushe zaki saka abun ki amman irin wad'annan kayan ko bayan kin haihu da k'yar in zasu yi maki don wani lokacin k'ibar ciki bin mutum take" shiru Fatuu tay idon ta akan littafin data fito tana d'an murmushi,

"Sauran kayan da ba'a d'inka ba ki bada ayo maki wadatattun dinkuna da ko cikin naki ya tsufa zaki iya sakawa" d'agowa tay ta kalleta ta d'aga mata kai, karatu ta fara yi ita kuma Hajiyar na kallo can tace mata ko akawo mata fruit zata shi ta d'aga mata kai, Saude ta fara k'wala ma kira jin shiru bata amsa ba tace k'ilan tana baya jin haka yasa Fatun mik'ewa tace bari taje ta d'aukko har zata fita daga wurin kujerun ta dakata ta tambayi Hajiyar itama ta kawo mata tace eh, a cikin bowls ta yayyanko ta dawo saida ta fara aje ma Hajiya nata akan c-table sannan ta koma ta zauna, kallon Fruit d'in Hajiya tay ganin harda abarba ta d'ago ta kalli Fatun tace badai itama harda abarbar ta yanko ba tace mata a'a ai tun Abuja bata shan ta ta jinjina kai, cigaba da karatun tayi ta haye saman kujerar gaba d'aya tana yi tana shan fruit d'in, suna haka suka ji an yi sallama alamar wani ya shigo, a Kusan tare suka kai idanun su saitin k'opar suna kallon wanda yay sallamar, nufo ciki yay saida ya matso sannan Fatuu ta gane ko waye har saida gabanta ya d'an fad'i ganin shi, Gaye ne yana sanye da riga da wando na yadi kan shi ba hula harda agogo sanye a hannun shi yana ruk'e da leda gari yayi zafi, da murmushi ya k'araso inda suke ganin yana k'ok'arin duk'awa k'asa yasa Hajiya nuna mashi kujera tace ya zauna mana, bayan ya zauna ya gaishe da ita fuskarta a sake ta amsa ya juya suka had'a ido da Fatuu still da murmushi a fuskar shi itama ya gaishe da ita ta amsa a hankali tana d'an murmushi, hakanan taji wani iri ganin shi a parlon duk da suna had'uwa a hanya a haka ma don bata san da Hajiya tasan abunda ya ta6a faruwa tsakanin su ba,

"kwana biyu Malam Ashiru ka daina lek'owa mu gaisa Allah yasa lafiya" Hajiya ta fad'a idon ta a kanshi yanata murmushi yace mata lafiya lou tace ma sha Allah, Fatuu dai sai kallon shi take abubuwa na dawo mata, mik'ewa yay ya matsa gaban Hajiya ya aje ledar daya shigo da ita ya koma ya zauna, kallon leda d'in tay ta ce "To, mi na samu haka" ta d'ago ta kalle shi yana murmushi yace mata yaje Jos ne kafin ya tafi ma yazo bata nan, jinjina kai tay tace sun je Abuja ne yace eh haka aka fad'a mashi,

"kace tsaraba ce aka kawo man kenan" yace eh, godiya tay mashi ta tambayi ya ya baro Mutan Jos d'in yace duk suna lafiya, shiru suka d'an yi can ta tambayi ya aiki da yake ta sa an samu mashi aiki yana teaching a primary, amsa mata yay da Alhamdulillah

"Yanzu sai aure ko tunda kana sana'a ga kuma aiki ai lafiya lou zaka iya rik'e iyali" yana murmushi cikin girmamawa yace mata sai nan gaba dai,

"To Saboda mi, ai aure shine cika kamalar mutum ko baka son yin Auren ne?" da sauri ya girgiza mata kai yana yar dariya yace ba wadda yake tare da ita ne yan mata basu son malamin Makaranta, har saida Fatuu tay yar dariya Hajiya tace "to don me, aikuwa inda wanda yakamata aso to bayan malami ne tunda ai shine tushen kowane aiki ko, kawai dai ba'a basu k'arfin da Yakamata bane wannan kuma saidai aita Addu'a Allah ya kawo Shuwagabannin da zasu duba masu, in dai mutum zai rik'e ka ya tsare maka hakkokin ka ai kuwa ba abun gudu bane kwanciyar hankali shi ne abun buk'ata a gidan aure kuma ba Arzik'i ne ke samar da wannan ba, gaba d'aya Arzik'in ma ai na Allah ne in akai hak'uri sai akai matakin da ba'a ma ta6a zato ba ga misalai nan akan masu Arzik'in, da yawa in kaji ta yadda suka faru sai ka jijjina kai don mamaki rabon mutum ai baya ta6a wuce shi" gaba d'aya sun yi shiru suna saurarenta har ta gama duk suka jinjina kai, jin ta gama Magana yasa shi kallon Fatuu yana murmushi yay mata Allah yasa Alkhairin Auren ta tana murmushi tay mashi godiya,

"In kana son yin Auren akwae yarinyar da zan had'a ka da ita bata da matsala akwai kyaun hali sai kaje in Allah yasa kun daidaita to sai muyi Addu'ar Allah yasa ayi damu" jinjina kai yay ta kai hannu gefenta ta d'aukko wayarta ta fara latsawa, alamun ya taso tayi mashi ya matsa daga gefen ta, mik'a mashi wayarta tayi tace ga Lambar yarinyar nan ya d'auka ranar da ya shirya zuwa su gana ya fara kiranta ya sanar mata yace to, bayan ya d'auka ya bata wayar cikin girmamawa yay mata sallama tace ya gaida Maman shi Allah yasa kuma su ji Alkhairi a kunyance ya amsa ya juya kan Fatuu dake cigaba da shan fruit idon ta akan shi itama yay mata sallama ya tafi ta bishi da ido gaba d'aya mamakin shi take sai ka rantse da Allah ba Gaye bane don sosae ya canza yay fresh hatta Maganar shi ma ta canza a nutse yake yin ta gashi kuma sam ba mummuna bane kuma yana da haske ashe dama can harda shaye shaye suka k'ara mashi bak'i. Bayan sallar Magrib Mino tazo har lokacin Fatuu na a part d'in Hajiya a d'akin Saude ta isketa lokacin bata dad'e da gama yin salla ba, suna anan d'akin aka yi sallar isha bayan Fatuu ta gama tace mata suje Parlor yunwa take ji, saida taje Kitchen ta zubo Abincin harda Mino sannan suka nufi cikin parlor don yanzu bata jin dad'in cin Abinci akan dining table, akan carpet suka zauna basu dad'e da fara ci ba Hajiya ta fito, bayan ta zauna Fatuu tace mata ta zubo mata Abincin ne tace a'a taci gaba da cin Abincinta in Saude ta zo ta zubo mata, bada jimawa ba Sauden ta shigo part d'in ta baya ta nufo cikin parlon, daga gefen Hajiya ta duk'a suka gaisa harda Mino kafin ta tambayi Hajiya a shirya table tace mata a'a waye mai ci a table d'in itama ta kawo mata nan tace to, bayan sun gama Mino ce ta kwashe kayan da sukai amfani dashi ta kai Kitchen ita kuma Hajiya tana cikin cin nata, suna Zaune suna yin kallo Tk ya shigo ta baya zai d'auki Abincin shi hango su da yay a zaune yasa shi nufo cikin parlon, daga bakin kujerun ya tsaya ya d'an rankwafa yana gaishe da Hajiya data juya tana kallon shi ta amsa Mino ma ta gaishe da shi,

"Tk yaushe zaka fara koya man Motan?" har zai juya Maganar Fatuu ta dakatar da shi kafin ya bata amsa Hajiya ta tambayi waye za'a koya ma Mota ne Fatuu tace mata ita, wani kallo ta bita dashi kafin tace "kaman dole, kina a cikin wannan halin za'a koya maki wata Mota, in kinyi hakuri Allah ya sauke ki lafiya ba sai a koya maki ba" yamutsa fuska Fatuu ta fara yi tace in aka koya mata yanzu lokacin tasan ta k'ware,

"kaji fitina don Allah, to bada ni za'ai wannan aikin rashin hankalin ba gaskiya ba wata Mota da za'a koya maki sai Allah ya sauke ki lafiya" ta k'arasa Maganar ta d'aure fuska, magiya Fatun ta fara yi mata Hajiya ta ruk'e ha6a tana fad'in wato ciki yasa ta koyi kafiya ko to ta ga ta inda za'a koya mata wata Mota, tana rufe baki kawae sai ji tay Fatun ta saka Kuka, waro ido Hajiya tay ta kai hannu ta rufe baki,

"Ku ji jan sharri don Allah, daga nace kiyi hak'uri in kika haihu a koya maki shine zaki k'ware baki ki saka man kuka" cikin kukan tace to ai in ta Haihu Ya Haisam yace Us zasu tafi Shikenan kuma bazata yi amfani da Motar ba,

"To a can Us d'in ba'a saida Motoci ne?" tace to Shikenan ita wannan d'in hakannan aka siya baza tayi amfani da ita ba,

"Dole sai in ke kika tuk'a zai zama anyi amfanin da ita, baga Tukur nan sai yaci gaba da yi maki amfani da ita ba kuma in ita kike so sai akai maki ita US d'in bayan kin haihun" wani kallo take bin Hajiyar da shi fuska a yamutsa bayan ta gama Maganar ta shiga yi mata magiyar ta bari a koya mata Allah ba abunda zai faru in sha Allah,

"Uhmm Fateema da alama wasa kika d'auki koyon Mota to iya fargaba ma ai tana iya haddasa maki matsala ni kaina har na manta yaushe rabon da in tuk'a Mota tun ma ban tsufa ba haka na hak'ura Saboda fargaba duk da na iya, sai ke kina d'auke da yaron ciki zaki ce wani a koya maki Mota" Kukan taci gaba da yi idonta akan Hajiyar itama kallonta take ta kwa6e fuska yadda sukai har saida yaba Mino da Tk dariya, ganin tana son a koya matan yasa Tk ce ma Hajiyar ko ya fara koya mata anan cikin gidan tunda akwae space lafiya lou tun kafin ta bashi amsa Fatuu tace "Eh don Allah Hajiya ki bari ya koya man d'in anan cikin gidan kinsan bai tuk'in ganganci zai koya man lafiya lou" fuska a kwa6e take kallonta Fatun ta shiga motsa baki, k'arshe dai dole hajiya ta amince da hakan ganin yadda Fatun ta k'wallafa rai kuma tasan duk aikin cikin jikinta ne amman tace ba ruwanta.

Washe gari da safe lokacin su Fatuu sun tafi Makaranta Haisam ya kira Hajiya bayan sun gaisa ta tambayi yadda suke da aikin shi yace mata dama Maganar fara zuwan Fatuu awo zai mata sun yi magana da ita tace lafiya lou yanzu ma zata iya fara zuwa, ruk'e ha6a Hajiyar tay jin Maganar da yay mata tace wato shi ga mai d'a ita bata san abunda ya dace ba kenan yay yar dariya yace No ba haka bane, ce mashi tay to tana sane bari tay ya cike wata hud'u sannan ta fara zuwa tunda dai lafiyar ta lou duk abunda ya dace ana mata yace Ok, yar hira sukai ta tambayi lokacin da zai zo ya fad'i mata tay fatan Allah ya kaimu ya kawo shi lafiya daga baya sukai sallama.

Kamar yadda sukai anan cikin gidan aka fara koya ma Fatun Motar da yake tana so sosae take ganewa, lokacin da cikin ya kai wata hud'u daidai ranar Laraba da yamma suka shirya zuwa yin booking d'in awon da yake a private hospital d'in da suke zuwa ne zata rink'a zuwa awon, tare da Hajiya suka tafi a Motar Fatun Tk yaja su, bayan sun isa Asibitin suna shiga Opd suka had'u da Nurse bilki tana ganin Fatuu ta ganeta ta nufo su, Fatuu na ganinta itama ta gane ta suka gaisa ta tambayi wani ne ba lafiya Hajiya tay mata bayanin abunda suka zo yi da sauri tace to suzo suje 6angaren Mama ne, a bakin d'akin da ake awon suka tsaya ta shiga ciki bada jimawa ba ta fito tace su shigo, lokacin da suka shiga Mama na zaune kan kujera idanunta sanye da glass ganin Hajiya yasa ta mik'ewa tana masu sannu da zuwa ta nuna mata kujerar data tashi tace ta zauna Hajiyar tace Fatuu ta fita buk'ata ita ta zauna, jin haka yasa tace ma nurse bilki taje ta kawo wasu kujerun tace to ta juya ta fita, gaisawa sukai a mutunce kai kace dama sun san juna Fatuu ma ta gaishe da ita ta maido idonta akanta bayan ta amsa tace ashe har an maida rabo abu har yama fara girma ita dai murmushi kawai tayi Hajiya ce ta bata amsa, nan mama ta hau fad'i mata ai kwanaki data yi 6ari taje ta dubata a Amenity Hajiya tace Allah sarki gashi ai har an samu wani Mama tace ai wuyar abun ace dama ba auren, bayan nurse bilki ta kawo kujerun duk suka zazzauna nan Hajiya tay mata bayanin abunda suka zo yi tace Ok, katin awo aka yankar ma Fatun daga baya Mama d'in tace ai bari ma a fara mata tun yanzu Hajiya tace aikuwa sun gode, Bp d'inta aka fara dubawa ya nuna normal sai aka auna tsawonta da kuma nauyin ta, bayan duk an gama Mama ta had'a ta da nurse bilki tace suje lab ta tura awon fitsari da na jini da za'a mata suka tafi nan fa suka hau yin hira da Hajiya, ba'a d'au wani dogon lokaci ba duk akayi mata awon har an turo result mama ta duba tace Alhamdulillah komai lafiya lou, gado tasa Fatun ta hau ta fara mata scanning gaba d'aya idanunsu ita da Hajiya da nurse bilki na akan computer d'in dake gwado cikin Fatun, tana cikin yin Scanning d'in tace "ni wannan cikin ma yadda nike gani kamar ba d'a d'aya bane" tai Maganar tana d'age idanunta dake a cikin glass Hajiya tace "ko?" mama ta amsa da "eh Allah, amman dai sai d'an nan gaba za'a tabbatar haka dai nike gani" jinjina kai Hajiya tay "ba mamaki ba d'ayan bane tunda shi Mijin nata suna da gadon abun Mahaifiyarshi yan biyu ne kuma cikin K'annan shi ma akwae yan biyu ni dama tunda naga yadda take d'irkar Abinci na yanke hukuncin da k'yar in ba yan biyun bane" dariya duk sukai Mama tace ai ko cikin d'ayan ma akwae mai saka cin Abincin Hajiya na dariya tace dama itama ta dai yanke hukuncin ne kawai tasan haka, bayan an gama komai aka rubuta mata date da zata dawo, a tare harda Mama suka fito tayo masu rakiya Fatuu dai ta kasa gane farinciki take ko fargaba jin zancen ana tunanin ba yaro d'aya bane a cikin nata, har harabar asibitin inda suka parker Motar su Mama ta raka su Hajiya nata mata godiya saida taga tafiyar su sannan ta nufi komawa cikin Asibitin.

A kwana a tashi ba wuya har sati ukkun da Haisam yace zai dawo sun yi, tun ana gobe zai dawo Fatuu ke ta farinciki har Fuskarta ta kasa boyewa ranar ta kasance Juma'a Tk na d'aukko ta daga makaranta ita da Mino suka wuce kasuwa siyayyar kayan da zata mashi Abinci, Washe gari da wuri ta tashi ta hau shirin tarbar mai gida, anan part d'inta ta fad'i ma Hajiya za'ai abinci gaba d'aya hakan yasa Saude zuwa nan suka shiga Kitchen tare Mino kuma ta hau gyaran part d'in Tk kuma aka sa ya gyara harabar part d'in, zuwa sallar Azahar sun gama komai sai uban k'amshin girkin da sukai kala ukku ke tashi drinks ma kala ukku sukai harda lafiyayyen kunun Aya sannan sunyi had'addan tsiren hanta da grilled lamp daya gasu ya sha vegetables nad'e a cikin foil paper, bayan sun gama komai aka zuba na su Hajiya Saude ta tafi dashi Mino ma ta zuba mata wanda zata kai ma gwaggo tace ta shiryo daga nan zasu je d'aukko shi Airport a d'okance tace to ta tafi, tana shiga Bedroom ta fad'a toilet bata d'au lokaci ba ta fito don tafi son jirginsu yay landing suna a Airport d'in, shiryawa ta shiga yi tayi make up wadda rabon data yi irinta ta manta saidai ko wadda akayi mata da bikin ta, tana cikin yin shafar Haisam d'in ya kirata ya sanar mata gasu zasu taso daga Kano cike da zumud'i tace to tay mashi fatan isowa lafiya, shaf shaf ta k'arasa don tasan bada jimawa ba zasu iso, wata rantsattsar marron d'in shadda sabuwa dal a cikin kayan lefenta take tasha ubansun aiki ta fiddo, ba 6ata lokaci ta saka ta tayi d'aurin kallabi mai kyau ta fiddo jewellery da suka hau da kayan ta saka harda hannunta tasa Agogo da zobuna ita kanta taga kyaun da tayi data kalli Madubin, jaka da takalma da gyale ta fiddo wanda suka hau da aikin shaddar ta saka sosae tay kyau ga cikinta ya fito, tana gamawa ta kira Tk tace mashi sun kusa k'arasowa yace Ok su a had'u a parking space, lokacin data fito har ya fiddo Motar cikin harabar yana hangota ya tunkarota da Motar bayan ya tsaya ta bud'e baya ta shiga yaja suka tafi, a kan hanya suka had'u da Mino itama tayi wanka tayi kwalliya tana sanye da riga da skirt na blue lace ta yafa blue d'in gyale bakinta yasha jan jambaki sosae itama tayi kyau, gaban Motar ta bud'e ta shiga suka tafi. Basu fi minti biyu ba da zuwa jirgin su Haisam d'in ya sauka gaba d'aya Fatuu a k'agare take data gan shi don ba K'aramin missing d'in shi tay ba, gaba d'aya sun baza ido suna kallon masu shigowa can sai gashi ya shigo yana janye da trolley d'ayan hannun shi ruk'e da jakar laptop jikin shi sanye da bak'ak'en riga da wando ya d'aura jar coat, Fatuu na hango shi ta tafi da gudu har saida tasa hankalin shi ya d'an tashi ganin yadda ta nufo shi gashi takalman k'afarta half cover ne masu d'an tsini, da sauri ya saki akwatin itama jakar laptop d'in ya ajeta k'asa ya nufota da sauri yana fad'in ta tsaya tare da yi mata nuni da hannu amman ina ai saida ta k'araso tana niyyar fad'a mashi ya ruk'eta yana murmushi ita kuma ta washe baki gaba d'aya k'amshin jikin shi ya karad'e wurin, ce mata yay miyasa tasan halin da take ciki zatai gudu haka bata ce mashi komai ba sai faman dariyar farinciki take duk hankalin mutane ya dawo kan su, k'arasowa wurin su Mino da Tk sukai suna murmushi sukai mashi sannu da zuwa fuskar shi a sake ya amsa masu, kama trolley d'in Tk yay Mino kuma ta d'auki jakar laptop d'in ya tallabo kafad'ar Fatun gwanin sha'awa suka nufi barin wurin idonta akan shi sai faffad'an murmushi take shima haka, sosae yaga ta canza mashi kan yadda yake ganinta a Vedio call, inda Motar su take suka nufa ita dashi suka shiga baya Mino ta zauna a gaba suka tafi, kwantar da kanta tayi a saman shoulder d'in shi tana ta bashi labarai harda koya mata Motar da ake yana ta jinjina kai fuskar shi d'auke da Murmushi a haka har suka k'araso Unguwar su, a gida Mino tasa aka ajeta tayi ma Haisam Allah ya huta gajiya sukai sallama da Fatuu sannan suka wuce.

Kwana ukku da dawowar shi ya tafi Abuja hidimar bikin Saleem Fatuu ji tay kamar ta bishi saidai Saboda makaranta ta hak'ura Saboda yanzu karatun suke da zafi zafi Saboda shekarar k'arshe ce. Ranar Friday aka d'aura ma Saleem aure da amaryar shi Saleema wadda d'iyar Minister of Health ce sai fatan Allah ya sanya Alkhairi ya bada zaman lafiya da zuria dayyiba, Ranar Sunday Haisam ya dawo Katsina.

Bayan sati biyu.......

Ranar Friday Fauzy ta dawo Weekend gidan Aunty Mareeya kamar yadda ta saba, da yamma tana kwance akan gadonta cikin d'akinta tana lallatsa wayar ta, jin an turo k'opa yasa ta juyo taga Aunty Mareeya ce ta shigo tana sanye da riga da skirt na jan lace kanta ta d'aura kallabi daga baya ta lankwasa igiyoyin kitson ta Sosae kayan suka amshi jikinta sun bayyanar da k'irarta ta dirarrar giant d'in mace, gadon ta nufo hannunta ruk'e da wayarta ta zauna a baki idon ta akan Fauzy, ganin irin kallon da take mata ga yanayin fuskarta kamar da alamun tashin hankali ko kuma ace Al'ajabi yasa Fauzy tashi zaune itama riga da skirt d'in atamfa ne a jikinta kanta ba kallabi anyi mata kitso shuku jelar ta sauka k'asa,
"Aunty lafiya?" Fauzy ta tambaya ta d'an waro ido da alamun fargaba akan fuskar ta, ajiyar zuciya Aunty ta sauke ta d'an motsa baki tama rasa ta ina zata fara, hakan da tayi yasa hankalin Fauzy tashi tace "Aunty don Allah minene, ki fad'i man kin ji" wata ajiyar zuciyar ta sake saukewa ta yarfa hannu tace "to ai Fauziyya nama rasa ta ina ne zan fara tsabar mamaki wllh" da sauri tace mata mi akai,

"Dama kun fara soyayya ke da Sameer ne baki fad'i man ba?" da mamaki Fauzy ta furta
"Soyayya!" Kai Aunty Mareeya ta d'aga mata, girgiza kai ta hau yi "a'a wllh, ni ba wata soyayya da muke yi duk yadda muke da shi ai kin sani ko daga haka ba wani abu" shiru Aunty tay duk tayi zuru zuru,

"Amman Aunty miyasa kika ce haka?" Hannu ta kai ta ruk'e ha6a tace "Wai kinsan yanzu Baba ya kira ni da alamun tashin hankali yake tambayata wai wane yaro ne kike tare dashi basu sani ba kuma Sameer ne yake magana akai"

zaro ido Fauzy tay ba shiri ta gyara zama Aunty taci gaba "Wai kiran shi akai daga gidan gwamnatin Nasarawa kan ya bada rana za'a zo neman Auren ki kuma harda rana za'a saka" tun kafin ta k'arasa Fauzy ta k'ara zaro ido ta bud'e baki Aunty tace "Wllh, ke duk yadda nike fatan hakan baki ji yadda hankali na ya tashi ba don ban tsammaci abun haka ba" gaba d'aya bakin Fauzy ya mutu sai ido kawai sosae taji Al'ajabin Maganar don ita an fi sati ma ko ta WhatsApp basu yi magana da Sameer d'in ba, da k'yar ta iya cewa "Yanzu shi baban miya ce masu??" Aunty tace "wai ce masu yay don Allah su bashi lokaci zai kira su ya sanar masu don farko ma gardama masu yay kan bake bace saida aka tabbatar mashi ta hanyar yi mashi bayanin ki ya gasgata tabbas ke d'in shi shine ya kira ni yaji yadda abun yake baki ji yadda hankalin shi ya tashi ba bayan nayi mashi bayanin tsakanin ki da shi sosae yay mamaki" Fauzy ba baki sai ido kawai wani irin bugu k'irjinta yake mata sosae Al'amarin ya d'aure mata kai,

"Yanzu shi Baba so yake wai aji ta bakin ki don yama rasa yadda zai tafi da Al'amarin" shiru Fauzy tay idonta acikin na Aunty can ta fara girgiza mata kai "Aunty kice mashi kada ya amince su zo ban son Auren shi" waro ido Aunty tay "amman Saboda me Fauziyya, ba abunda dama muke fata ba kenan??" Idanun Fauzy ne suka ciko da k'walla cikin karyayyar murya tace "Haba Aunty ina ake haka fisabilillahi, ko don mu talakawa ne shine zai nuna mana iko haka, bafa soyayya muke dashi ba hasalima bai ta6a nuna man wani alamu na yana so na ba kawai kuma sai ace wai zai aure ni to wane irin aure ne haka zamu yi dashi don Allah?" Shiru Aunty tay tana kallonta k'wallan suka fara zubo mata, ajiyar zuciya Aunty tay tace "amman Fauziyya ba kina son shi ba?" Da sauri tace "ko ina son shi Aunty ni bazan yarda ya nuna man iko haka ba, don ina talaka ai nima inada daraja ba yadda za'ai yayi man wannan ikon, a tunanin shi komai ne ake iya nuna iko, to bazan Aure shi ba gaskiya" ta k'arasa tana girgiza kai harda d'an huci ta kumbura baki, hannu Aunty ta kai ta kama hannunta cikin kwantar da murya ta fara magana "ni ina ganin tunda kinsan halin shi Fauziyya bai kamata ki tada hankalin ki haka ba, k'ilan shi ba da niyyar nuna iko yayi hakan ba...." Katseta tay "iko ne mana Aunty tunda ai yasan ba Soyayya muke da shi ba" d'an cize le6enta na k'asa Aunty tayi kafin tace "watak'il fa shi a wurin shi a hakan soyayya yake dake kinsan Mutane irin shi suna da wuyar fahimta wllh, kiyi tunani tun farko da kuka san juna laifi fa kikai mashi amman kuma ya cigaba da kula ki yana maki abubuwan Alheri kinga ta yuwu kamar yadda nace a wurin shi soyayya yake dake, kuma tabbas yana son ki shiyasa har yasa a zo nema mashi auren ki, tunda kinsan halin shi Fauziyya hakan bai kamata ya dame ki ba har ki fatali da wannan babbar damar da kika samu wadda ko a film da wuya kiga wata ta samu irin damar ace dai d'an Governor zai auri d'iyar talaka " shiru Fauzy tay har lokacin da k'walla a cikin idanunta, still hannun Aunty na a ruk'e da nata,

"Tunda kina son shi ki amince kawai mu taru muyi fatan Allah yasa hakan Alkhairi ne kuma watak'il sakayyar abunda Mujaheed yay maki ne Allah yayi maki dama in dai aka cuci mutum yayi hak'uri ya bar ma Allah tabbas sai ya saka mashi" shiru tay tana ta bin ta da ido Auntyn tace mata tayi magana mana, motsa baki ta fara tana yamutsa fuska tace "to ni Aunty mi kike so in ce, wai ina aka ta6a Aure haka don Allah mutumin nan fa ko halin shi bamu sani ba shin yana da kyakkyawan hali ko mummuna ba wanda ya sani sannan kuma ni wllh ina zargin shi ma, akan ido na fa yasha giya kuma yaje Club taya mutum mai kyaun hali zai aikata hakan, ni dai gaskiya Aunty ina ganin gara mu hak'ura da shi kawai kar azo ayi abunda za'a dawo ana dana sani kema kinsan irin yaran masu kud'i da Mulkin nan sai a Hankali wllh" ta k'arasa tana girgiza kai,

"Amman mijin Zarah haka yake? Kuma ai baki da tabbas din giya d'in ce kika ga yasha ko tunda ai ke ba saninta kikai ba, kuma da ya sha kinga ya bugu ne tunda ai kun d'an jima tare sannan yayi maki wani abu na kaucewar hankali? In da ya bugu kema kinsan yadda kuka kasance ku biyu kawai wllh sai dai Allah ya k'wace ki kuma ko da bai bugu ba inda d'an iska ne na tabbatar da sai ya nuna maki halin shi a wurin, sannan Maganar zuwa Club tare kuka shiga ne? Ina ce a cikin Mota ya bar ki kinga kenan baki da ikon zargin shi tunda ai baki san miya shiga yayi ba duk da ansan ba wurin Arziki bane amma ba kyau ki munana mashi zato" kallonta kawai Fauzy take fuska a kwabe,

"Yanzu in don sanin halin shi ne ai Mijin Zarah na nan ko zan kirata in sa ta tambayar mana shi komai da muke son sani na tabbatar bazai 6oye mana komai ba, ni kuma na maki Alkawarin indai aka tabbatar yana da wani mugun hali da ya kamata a guje ma auran shi to zan goya maki bayan hakan" ganin bata ce komai ba yasa tace mata hakan yayi mata, d'an yamutsa fuska tay a raunane tace "to amman Aunty yanzu misali ace baida wata illa haka zan aure shi ko fa sona bai ta6a cewa yana yi ba, ni nafi tunanin ma Saboda labarin dana bashi na Mujaheed ne yasa ya yanke aure na matsayin ya taimaka man" d'an murmushi Aunty tay tace "in ma don hakan ne ai ba laifi bane sau nawa dama ake aure ba soyayya duk yawancin iyayenmu ba haka sukai auren ba kuma suka zauna lafiya, yanzu aure nawa ne akai a turbar soyayyar yazo ya lalace mudai fatan mu ai ya ruk'e mana ke da kyau ne kiji dad'in Auren, wani Maganar soyayya in kunyi auren kun yi in ma bai iya ba sai ki koya mashi abun ai duk mai sauki ne balle ma wllh irin wad'annan mutanen sun mugun iya love ki bari ayi Auren zaki ban labari dama yanzu ai bazai sake maki ba tunda yana ji da shegiyar izzar tsiya, ke ni ki bari indai damuwar ki ya furta yana son ki ne nayi maki Alkawarin sai furta wannan Kalmar ya zame mashi tamkar cin Abincin shi, yadda zai ci Abinci safe da rana da dare to ina mai tabbatar maki haka zai rink'a fad'in I love you Fauziyya",

duk da yanayin da take ciki saida ta d'an yi dariya Aunty ta k'ara cewa "Allah kuwa, ke baki ga yadda mijin Zarah ba ya shigo hannu sai faman rawar k'afa yake akanta ko ba'a fad'a ba daka gani kasan ta kama shi gamm to shima hakan zamu kama shi wuyarta dai ayi Auren hakan ba wani abun wahala bane wllh" d'an ta6e baki Fauzy tay tana d'an murmushi,

"Yanzu ya kika ce Your Excellency, a kira Zarah d'in ko mu fad'i mata abubuwan da muke so mu sani game dashi d'in?" wani kallo Fauzy tay mata tana yar dariya kafin a hankali ta d'aga mata kai alamar eh, da sauri Aunty ta kai hannu ta 6akar mata shoulder tace "su Excellency ana so ana kaiwa market" dariya Fauzy ta saka tana fad'in Allah ita ba wani son shi da take.

Fatuu zaune a parlor tana kallo tana sanye da doguwar riga Boubou ta lace cikin kayan data ba Kb ya d'inka mata daga baya akai mata d'inkunan da Hajiya tace , bata dad'e da fitowa daga Kitchen ba tayi ma Haisam Abinci da yake tunda yazo ita ke mashi Abinci har ce mata yay ta bari a rink'a yi acan part d'in Hajiya ita ta huta amman tak'i, wayarta dake a gefenta ce ta fara ringing ta kai hannu ta d'aukko, ganin mai kiran nata yasa tay d'an murmushi ta kai hannu tay picking,

"Aunty Mareeya ina wuni, barka da juma'a" ta fad'a bayan data yi sallama, amsa mata tayi ta tambayi ya suke harda unborn tana yar dariya tace mata duk lafiya lou suke ga unborn d'in ma yaji suna waya yace/tace a gaishe ta, dariya Maganar ta bata tace to tana amsawa ai in Allah ya yarda biyun ne duka ita dai Fatuu murmushi kawai tayi,

"Yauwa Zarah nace don Allah ko mijin ki na nan?" Fatun tace "a'a Aunty yau da safe ya tafi Kano yin wani aiki amman dai a yau zai dawo yace man in sha Allahu da Magrib jirgin su zai sauka" jinjina kai tay tace to Allah ya dawo dashi lafiya bayan ta amsa tace "Amman Aunty lafiya dai ko?"

"lafiya lou yar gidana sai ma Alkhairi in sha Allahu...." nan ta kwashe komai game da zuwa neman Auren Fauzy da za'ai da kuma yadda sukai da Fauzyn, tsananin mamaki ne ya bayyana akan fuskar Fatun gaba d'aya ta washe baki tana dariyar farinciki tace "Amman Aunty wllh naji dad'in wannan labarin wayyo Allah na, muna ta jiran ya furta yana son ta ko sun fara soyayya suyi aure ashe mai gaba d'aya zai yi.." Aunty ta amshe "Wllh haihuwa da hanji ba" dariya Fatuu tasaka nan ta fad'i mata abubuwan da take so ta tambayar mata Haisam a d'okance tace to in sha Allahu yana dawowa zasu yi Maganar Allah dai yasa suji Alkhairi Aunty tace "Amin ya Rabbi yar gidana shine abun da zamu yi fata kam" bayan sun gama wayar ta tambayi ina amarya Fauzy,
yar dariya Aunty tay tace "ga abu nan tayi wuri wuri Sameer yayi mata bazata" Fatun nata dariya tace a bata, bayan ta amshi wayar tsokanarta Fatuu ta shiga yi ita dai sai uhhm take daga baya ta hau yin Addu'ar Allah ya tabbatar masu da Alkhairi.

Bayan Magrib Haisam ya dawo bai dad'e da shigowa ba aka fara kiran sallar isha ya tafi Masallaci, bayan ya dawo toilet ya nufa yayo wanka ya zura jallabiya sannan ya fito don yaci Abinci da tuni Fatuu ta jera mashi akan c-table don in shi kad'ai zai ci yafi son a d'aura mashi anan, Serving nashi ta shiga yi saida ta tabbatar yaci ya k'oshi, tana k'ok'arin kwashe kayan Abincin ta kai Kitchen ya mik'e yace ta bari ya kai tace mashi tana son had'o masu Fruit salad ne, kallonta yay yana d'an murmushi yace zai had'o masu ta zauna huta, hura mashi kiss tay ta kashe mashi ido yay yar dariya, nufar Kitchen yay bayan ya d'auki tray d'in kayan ta d'an d'aga murya tana fad'in "Hubbyna I love you" kai ya jinjina mata ta k'ara fad'in "bazan iya rayuwa babu kai ba" tana fad'in hakan taji yace shima haka sosae yadda yay Maganar ya bata dariya, yana gab da shigewa cikin Kitchen d'in ta k'ara d'aga murya tace yabi a hankali kar ya yanke hannu Baby zai yi kuka in ya yanke, jinjina kai yay saida ya d'an juyo suka had'a ido ya sakar mata k'ayataccen murmushi tare da d'an girgiza kai ganin abunda take mashi da baki ya juya ya shige, after some minutes sai gashi ya dawo hannun shi ruk'e da acrylic bowl ana hangen fruit d'in, dayan hannun shi ruk'e da bottle water ya nufo ta suna ta sakar ma juna murmushi, a gefen ta ya zauna ya mik'a mata tasa hannu biyu ta amsa ta furta "thank you so much Daddyn Baby" hannu ta kai ta d'auki spoon d'in ciki ta fara sha tana yi tana bashi shima a baki can taga ya kawo hannu ya d'ago da k'afafunta ya d'auro su kan cinyoyin shi ya shiga matsa mata su sai murmushi take tana cigaba da sha shima tana bashi, yana ta matsa mata k'afafun idanun shi akan Tv yana kuma amsar fruit d'in in ta kawo can ya juyo yace mata tasha kada ya shanye ma Baby abu tay dariya, bayan ta shanye akan c-table ta d'aura bowl d'in ta d'aukko bottle water d'in, bayan tasha ta rufe ta maida kan c-table d'in,

"Hubby" yaji ta kira shi ya d'aga gira kafin ya juya ya kalleta, ce mashi tay dama so take ta tambaye shi yasan da zancen zuwa nema ma Sameer Auren k'awarta Fauzy, yanayin fuskar shi ne ya canza da alamun rashin fahimta ya tambayi wane Sameer tace mashi cousin brother d'in shi, shiru ya d'an yi idon shi a kanta yace bai fahimce ta ba, bayanin Maganar zuwa nema mashi auren Fauzy ta yi, sosae mamaki ya bayyana akan fuskar tashi yace mata shi bai san da Maganar ba ai tace mashi aikuwa d'azun Aunty Mareeya ta kirata take mata Maganar, jinjina kai yay yama kasa cewa komai sosae kan shi ya d'aure don abu ne da bai zaton ji ba,

"Ka yi mamaki ko?" Fatuu ta tambaya a hankali ya jinjina mata kai, tambayarta yay yadda akai suka san juna nan ta kwashe komai ta fad'a mashi harda wayar da ya siya ma Fauzyn tace ita ta mantane shiyasa bata fad'i mashi ba wllh, d'an tsoki yay ya furta "Sameer...." Shiru yayi Fuskar shi da d'an murmushi, sosae yaji mamakin yana son Auren Fauzy duk da yasan hakan ba wani abu bane in Allah ya k'addaro itace matar shi saidai shi yasan waye Sameer fiye da kowa bai ta6a tunanin zai iya Auren yarinya kamar Fauzyn ba sanin irin matan da yake tarayya da su,

"Wai suna son sanin game da shi ne don ita ko cewa yana sonta bai ta6a yi ba fa kawai dai suna d'an gaisawa yana yi mata Alkhairi kuma sai kwatsam suka ji zancen neman auren ta",
Yana murmushi yace "Yana sonta ne shiyasa yake mata hakan kawai bazai fito bane ya fad'i mata" gyad'a kai Fatun tay idon shi akanta yace mi suke son sani a tare da shi ne, ce mashi tayi kamar ya halin shi yake,

"Ok, what I know is that baya da wani hali mara kyau da za'a k'i auren shi Saboda shi" ya k'arasa yana d'an girgiza kai,

"amman ita wai tana zargin wasu abubuwa a tare da shi" tambayarta yay kamar mi take zargin, shiru Fatuu tay hakanan sai taji nauyin fad'in Maganar ya fahimci hakan ya d'age mata gira yace ta fad'i mashi duk abunda ya sani bazai 6oye masu ba,

"D....dama wai cewa tayi taga ya sha giya" da k'yar ta k'arasa ganin yadda ya kafeta da ido, yana jin abunda ta fad'a ya d'an waro ido mamaki ya bayyana akan fuskar shi ganin haka yasa ta zaro ido,

"A yaushe ne taga Sameer yasha wannan d'in?" da mamaki ya tambaya, wani abu Fatuu ta had'iya tana faman kikkafta ido tace "ai ba wai ta tabbatar bane fa, dama da ya je da ita gidan da na fad'i maka lokacin da sukai karon nan wayar shi ta fashe...to a nan ne taga wai ya bud'e Fridge ya fiddo kwalba irin ta giyar kuma bayan ya zuba a cup ma taga kalar kamar ita" ta k'arasa tana d'age baki, maida bayan shi yay ya jingina da kujerar fuskar shi a d'an kwa6e ita kuwa sai faman zare ido take can ya k'ank'ance ido yace "Kin koya mata taga mutane na shan lemu tace giya ko" hannu ta kai da sauri ta rufe baki ta hau girgiza kai yace mata eh mana, cire hannun tayi cikin yar rawar murya tace wllh ita fa ba ruwanta itace ta fad'i mata haka kuma ita ai bata ma ga abun ba ko, d'an ta6e baki yay yana murmushi can yay sigh yace "to bai shan giya inada tabbas akan hakan don shi yama tsane ta abunda taga yasha favourite drink d'in shi ne" da sauri ta jinjina kai yay mata wani kallo mai kaman harara tasa dariya, ce mata yay sai mi suke son sani,

"To zan fad'i maka amman fa kar kace ni nace abunda aka fad'i ana son sani ne" murmushi yay ya d'aga mata kai, "tace wai taga yaje wani wuri da suka baro gidan kuma wurin wai kaman Club ne" d'an lumshe ido yay ya d'aga mata kai "Yeah, yana zuwa Club" shiru tayi tana kallonshi don ba iya abunda suke son su ji ba kenan,

"da wani abu ne game da hakan" ya tambaya had'i da d'age mata gira, in ina ta fara "w..wai ita a tunanin ai ba abun Arziki ake yi a can ba, t..to shine wai...take ganin kaman yana...." dakatawa tay gaba d'aya ta waro ido yana dai ta kallonta taji yace uhum alamar taci gaba, "to na dai fad'i maka ai abunda ake son sani ne ba ana nufin yana yi ba" yana murmushi yace ai ta fad'i wannan ko yana jin ta, ce mashi tay wai ko yana neman Mata ne, ganin yayi shiru yasa tace mashi ya gane abunda take nufi har saida Maganar ta d'an bashi dariya,

"baya wannan, I'm absolutely sure about that, saidai he's touching women" waro ido Fatuu tay ya d'an jinjina mata kai yaci gaba "iya ta6a mata yake am very sure akan hakan don tun muna School abroad ina mashi fad'a akan hakan yace man ya bari amman kuma daga baya sai ya cigaba, kinsan hakan yanzu wasu basu d'auke shi komai ba suna d'auka wayewa ne duk da wanda yake Muslim yasan hakan is forbidden kuma babban laifi ne kamar dai yadda akwae abubuwa da yawa da ba kyau kuma ake yi" ajiyar zuciya Fatuu ta sauke da yanayin damuwa tace "to amman kasani ko yanzu ba iya hakan yake ba yana....." Shiru tayi ta kasa idasa Maganar, da murmushi akan Fuskar shi yace mata yana da tabbacin bai yin sex don yana da ilimin Addini sosae da bazai bari yayi hakan ba shima ta6a matan da yake kawai biye ma zuciya ne kuma harda Matan da ke yawan bibiyar shi sun k'ara taimakawa wurin sashi hakan, jinjina kai Fatuu tay ya kai hannu ya shafo gaban kan shi, yar ajiyar zuciya Fatuu ta sauke,

"Yanzu kana ganin hakan ba matsala bane?" Shiru ya d'an yi idon shi akan Tv kafin ya juyo kanta "a wurina hakan bazai zama problem da zai sa ak'i auren shi ba, Sameer mutumin kirki ne sai kayi mu'amala shi zakai understanding hakan duk da nasan yana da wuyar a saba da shi amman yana da Quality da mace za tayi Alfaharin samun shi as a husband" wani k'ayataccen murmushi Fatuu ta saki tare da kashe mashi ido d'aya ta furta "Kamar kai kenan" shiru yay yana kallonta da murmushi, "ina Alfaharin samun ka matsayin mijina Hubby" ta furta idanunta a d'an lumshe calmly ya furta shima hakan duk suna murmushi har lokacin kuma k'afafunta na akan jikinshi yana mammatsa mata,

"in dai tana son shi ina bata shawarar tay accepting na shi, shi matsalan dana fad'a tare dashi zata iya hana shi tunda yana sonta ba kamar kuma in sun zama d'aya" d'aga gira tay tace yana tunanin hakan is possible,

"yeah, ga misali nan akan mu" wani kallo tay mashi da rashin fahimta tace amman shi ai tasan bai abunda Sameer d'in yake ko, shiru yay yana mata wani kallo mai wuyar fassaruwa yanayin fuskar shi kamar zai murmushi itama murmushin take taji ya furta "ina nufin kaman yadda zaki iya hana ni abu koda ni ina so in baki so zan bari" wani kalan murmushin dad'i tayi had'i da lumshe ido tace "ai ba abunda zai maka wanda ni bazai mun ba, duk abunda kake so nima ina son shi Ya Handsome dina" yar dariya yay ya furta mata ya gode,

"Amman wai shi Sameer aikin mi yake?" gyara zama ya d'an yi kafin ya fara magana "yana da aiki mai kyau, shi Aerospace engineer ne" d'an yamutsa fuska tay ta maimaita sunan aikin nashi da ta maimaita tace "mi kenan?" Ce mata yay daga sunan tay guessing tayi shiru tare da d'an k'ank'ance idanunta tana son ta canka,

"Aerospace...Kaman ana nufin aeroplane ko?" ta tambaya tare da d'age baki, still da murmushi akan Fuskar shi yace "Yeah Kusan haka, shi engineer ne yana aiki da wani company a K'asar U.k, suna k'era jirgin sama ne bama shi kad'ai ba da wasu abu da suka danganci sama kaman satellites and rocket" zaro ido Fatuu tay a d'an rud'e ta furta "rocket kuma! ba itace mai kaman katuwar bindiga ba da in aka harba bullet d'inta ke fita kaman bomb ya tafi shuuuu yaje ya tarwatsa wuri??" dariya ta bashi yadda ta zaro idon yace mata eh shi wannan missile kenan shima rocket d'in ne, "Yanzu su ke had'a su?" Kai ya jinjina mata alamar eh kafin yace amman shi Sameer yafi experience sosae ta bangaren had'a jirgi don ya k'ware a kan haka shiyasa har wasu companies suna gayyatar shi aiki kaman a France da Germany, har nan US akwai wani Company da yake zuwa aiki a Washington, a nan Nigeria ma yana aiki da Ministry of aviation shiyasa akwai lokacin da yake d'an zama a Nigeria amman yafi zama a UK" jinjina kai ta shiga yi jin irin aikin da Sameer d'in yake can ta furta amman dai tasan yana samun kudi Haisam d'in yay yar dariya yace mata sosae,

"To amman kai ma kana samun kud'i kaman shi" wani kallo yay mata ta waro ido da sauri tace itafa hakanan ta tambaya tunda taga shima a K'asar wajen yake aiki, kawai sai gani tay yay d'an murmushi yace "tunda ina aiki ai dole in samu kud'i ko kawai kice kina son ki ji ni da shi waya fi samun kudi right?" Ya d'age mata gira ta d'an tura baki had'i da girgiza kai, sigh yay yace "kowa da kalar aikin shi so dole salary ya bambanta amman ta wani bangaren Kusan duk damar mu d'aya ne da shi kuma aikin namu suna da alak'a tunda duk sun danganci technology ne don akwae abubuwan da company d'in mu ke yi wanda suke amfanin da shi and nima kuma ina zuwa wasu Wuraren aiki saidai shi ya riga ni fara aiki abroad Saboda ni farko dana gama first degree na anan nayi aiki shi kuma tun daga School Company d'in suka zo suka d'auke shi nima tun lokacin an so a d'auke ni amman Dad ya hana don yana jin haushin yadda duk suke d'auke Mutanen mu masu hazaka a cewar shi hakan ne ya hana tamu K'asar cigaba kuma hakan ne, bayan naje yin Master's degree d'ina nan suka matsa na fara yi masu aiki amman dana gama sai Dad yace in dawo gida nan zan yi aiki lokacin sai na nuna masa interest dina kan yin aiki da su Saboda ina son bud'e Company shine ya amince amman sai na fara aikin anan, a lokacin nayi missing Hajiya sosae don tunda na tafi Karatu na bar wurinta haka dana dawo na fara aiki a Abuja sai dai in kawo mata ziyara har na sake komawa degree na biyu a lokacin tana kewa na sosae duk da bata fad'a man amman na sani duk na kawo mata ziyara in zan tafi sai naga idanunta sun canza ga kuma rashin mijinta da a lokacin yana damunta sosae wannan dalilin ne yasa na buk'aci canza wurin aiki nazo in zauna tare da ita......." dakatawa yay yana numfashi a hankali idon shi akan Fatuu da itama nata idanun na acikin nashi,

"........ashe zaman nawa wani babban Alkhairi ne zai same ni na had'uwa dake Baby, tunda kika shigo rayuwata farinciki na ya k'aru and I couldn't remember in akwae wani rana da nayi bakin ciki Saboda ke in ma akwae shi kenan, ban ta6a shiga damuwa ba sosae kaman ranar da zamu rabu zan yi aure, tun lokacin dana fahimci kin canja man na fara shiga damuwa har zuwa ranar, sosae kikai breaking heart d'ina har yanzu ina ganin image d'in wannan moment na ga Zarah a duk'e tana kuka sosae Saboda Ya Handsome d'inta gashi ni kuma ba abunda zan iya yi mata kan hakan, idanuwa na sun cika da tears a lokacin wanda bazan tuna when last naji hakan ba, koda muka shiga jirgi saidai kawae na d'age kai na na runtse ido ba komai nike ba sai tunanin halin dana baro ki a haka har muka isa Abuja...." Murmushi kawai Fatuu ke yi yayin da zuciyarta ta shiga tariyo hoton rabuwar tasu a airport, a lokacin wani irin soyuwa zuciyarta ke yi gaba daya ji tay kaman rayuwarta tazo k'arshe she felt empty, rayuwa kenan yanzu gashi komai ya zamo tarihi a gare ta duk sanadiyyar hak'uri da tawakalli,

"Ranar da kika sanar man zaki abortion naji tashin hankali amman bai kai na ranar da kika fad'i ba a wurin Dinner party, that was the second day dana shiga tsananin tashin hankali a rayuwa ta, daga ranar dana rasa grandpa dina mijin Hajiya lokacin ina a Secondary school sai kuma wannan ranar ganin Zarah kwance a jikina bata numfashi , zuciyata tayi ta sak'a man abubuwa....." Labarin irin halin daya shiga lokacin da zasu kaita Asibiti harda kukan daya yi ya shiga bata yana ta murmushi har ya gama ta hau girgiza kai har saida taji idanunta sun ciko da k'walla wata irin k'aunar shi take ji na ratsa mata jinin jikinta, Sigh yay ya kalleta da murmushi yace daga bayanin aikin shi da yayi mata ta fahimci abunda take son sani na wanda yafi samun kud'i tsakanin shi da Sameer, yamutsa fuska ta shiga yi a shagwabe tace itafa wllh hakanan ta tambaya ba don wani abu ba kawae subul da baka ne,

"ai dama kin cancanci kisan komai game da aikin mijin ki ko" ya fad'a yana murmushi, d'age mashi gira tay tace "to in haka ne ka fad'i man nawa ne salary en ka" tana rufe baki yay mata wani kallo mai kaman harara ta saka dariya tace to ba shi yace ta cancanci tasan komai ba,

"Wannan sirri ne banda shi" ya fad'a yana yar dariya itama har lokacin Dariyar take tace mashi ita bata yarda ba sai ya fad'i mata ai shi yace, ce mata yay to zai fad'i mata amman a kunne zai rad'a mata don kar aji, har saida ta d'an Jujjuya kafin ta tsaida idonta akan shi tace to ba su kad'ai bane, hannu ya mik'a ya nuna mata cikinta yace Baby yake nufi kada ya fad'a mata ya ji wata rana in ya buk'aci ya siyo mashi/mata abu yace baida kud'i ace mashi yana dasu tunda an ji salary d'in shi daya fad'i ma Mom, dariya sosae Fatuu ke 6a66akawa tace to ita bai gudun tayi mashi hakan sai Baby yace ai ita ya gane tausayinshi take ji bata son yana kashe kud'i amman yasan k'ilan in ya fad'i mata ta daina jin tausayin nashi da sauri ta d'aga hannu tace to Allah bata son jin salary d'in tay Maganar tana dariya tare da girgiza kai shima still dariyar yake, bayan sun tsagaita gaba d'aya jingina sukai da jikin kujerar suna kallon juna kowannansu wani irin nishadi yake ji duk ya kasance da d'an uwan shi,

"Na dawo daga tafiya kin hana ni in huta da tambayoyin ki" ya fad'a bayan yayi yar hamma, jin haka yasa ta sauke k'afafunta daga saman jikinshi da sauri ta fara k'ok'arin mik'ewa tana fad'in yayi hak'uri to ya tashi suje su kwanta, nuna mata bowl data sha fruit salad yay yace ta kai Kitchen bari ya kashe kayan kallon tace to, lokacin data dawo cikin parlon har ya kashe kayan kallon yana ganinta ya mik'e tsaye ta nufo shi tana murmushi, tana zuwa gaban shi kawae sai ta juya mashi bayan ta d'an rankwafa tace wai ya hau ta goya shi tunda shi bai iya goya ta Saboda ciki, dariya sosae ta bashi aikuwa tana a yadda take taji ya sunkuce ta gaba d'aya ta saka dariya, nufar hanyar Bedroom yay yana d'auke da ita ta sak'alo hannuwanta a wuyan shi tace wai bai jin nauyinta Slowly ya furta ai dama gaba d'ayan su nauyin su na a kan shi don haka bai jin shi, suna zuwa bakin kopar d'akin yasa k'afa ya tura ya shige da ita.........

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

91

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

............Washe gari Asabar Misalin k'arfe sha d'aya na safe Mom na kwance ta koma bacci bayan sun yi Breakfast, tana cikin baccin ta jiyo ringing d'in wayarta kamar bazata tashi ba da k'yar dai ta bud'e idanun ta ta kai hannu gabanta ta d'aukko wayar, duba screen d'in tay taga wanda ya kira har saida tay d'an yi murmushi ganin yar uwarta ce wato Hajiya Zainab, picking tay ta kara wayar a kunne, gaisawa sukai da juna jin yanayin muryar Mom d'in yasa tace yar gayu bacci ma take ko ta tasheta, Mom na murmushi tace gayu ai sai ita kawai ta koma bacci ne Hajiya Zainab na murmushi tace to ai saida hutu ake iya komawa baccin,

"Hhhh in wannan hutun ne ai kowa ma nada shi kema nasan baki so kwanciyar bane",

"Uhmm wani lokacin kam ai ko kaso ba dama ka koma Saboda schedules" Mom na murmushi tace ya za'ai sai Addu'a Allah ya k'ara d'aukaka ya kuma taimaka tace Amin,

"Sai kika ji Saraki ya samu Mata" shiru Mom tayi tana maimaita sunan Saraki da ta fad'a, da alamun rashin fahimta tace "mi kike son fad'i man, ba dai his Excellency ne zai aure ba?" Dariya Hajiya Zainab ta saki tace "inaaa, ai Excellency ya gama yin aure a gidan duniyar nan ya auru yadda ya kamata, Saraki wanda yay gadon Sarautar Grandpa nike nufi" shiru tay tana nazarin Maganar da tayi can tace "wai Son kike nufi?"

"Eh mana, wai kina nufin baki sani ba duk da anan gidan ya samu Matar" kan Mom ne ya d'aure ba shiri ta yunk'ura ta tashi zaune jikinta sanye da kayan bacci, ce mata tayi ita bata san da wannan Maganar ba gaskiya amman wacece wadda zai auran, fad'i mata game da Fauzy ta shiga yi, sosae Mom taji mamakin Maganar har tama kasa magana saida ta nisa sannan tace,

"Amman dai abun da mamaki wllh ace Saleem da kanshi yace yana son Auren yarinyar" daga d'aya bangaren Hajiya zainab tace "Wllh, it was a real surprise, kinsan farko Dad d'in shi ya tunkara da Maganar wai ya samu wadda zai aura ya tambaye shi a ina nan yake ce mashi yar Funtua ce tana karatu a Katsina koda Dad d'in nashi ya tambaye shi d'iyar waye sai cewa yay shima bai san shi ba kawai dae yasan Dad d'inta is a retired man yanzu Farmer ne, sosae shi kan shi Dad d'in nashi yay mamakin jin yarinyar da yake so ya Auran daga baya ya tuntu6e ni da Maganar ya tambayi wai ko nasan ta nace bazan iya tuna ta ba koda na ganta da bikin, amman I never thought Sameer would fall in love with such a local girl wllh, nayi mamaki ba kad'an ba duba da irin matan da ake mashi tayin auren su, kinsan ko bayan bikin Son saida muka shirya mashi had'uwa da yarinyar sarkin zazzau wadda Mom d'in ta Friend d'ina ce baki gan yarinyar ba very beautiful girl wllh gashi Kusan complexion d'inta iri d'aya da Sameer d'in don Mom d'inta balarabiyar Sudan ce bata dad'e da dawowa daga Saudiyya karatu ba shine Mom d'in nata tayi man Maganar mu gwada had'a su don tana son Sameer sosae, wllh Sis in gaya maki nasa yarinyar tazo nan ta kwana biyu wai don in yi kokarin had'a su, ranar dana kira shi don su gaisa a parlor ko kallon direction d'in da take bai yi ba saida nayi introducing nata sannan ya d'an kalleta daga baya nace bari in basu wuri su san juna sosae, na d'an jima sannan na koma parlon kawai sai na ganta zaune ita d'aya da mamaki na tambayi ina yake tace man ai ina tashi shima ya bar wurin baki ji yadda naji ba kunyar yarinyar ya kamani....."

Murmushi Mom tayi ta d'an girgiza kai,

"........Lokacin na iske shi a d'aki nace mashi miyasa zai baro falo bayan na tashi da bud'ar bakin shi sai cewa yay dama ba gaisawa ne zasu ba kuma sun yi hakan, sototo nayi ina kallon shi don na tabbatar ya san mi hakan dana yi ke nufi don ba yau ne na farko ai da aka had'a shi su gaisa da mace ba an yi hakan sau da dama kama daga yaran k'awayena dana Abokan Dad d'inshi har fa akwae d'iyar shugaban wurin aikin shi baturiya da shima shugaban nasu yaso had'a su amman yak'i har nan Nigeria ta ta6a biyo shi itama kyakkyawa duk da ba musulma bace, koda na nuna mashi ina son ya auri ita Raudha d'in data zo sai ce man yay bata yi mashi ba yarinyar da ko kallon Arziki bai mata ba taya zai san tayi mashi, lokacin na nuna mashi 6acin rai na kan to har sai yaushe ne zai samu wadda zata mashi yay aure kawai sai ya yi man wannan shu'umin murmushin nashi yace wai in kwantar da hankali na ya samu Mata soon zai yi aure, wllh ni duk na d'auka ya fad'a ne kawai Saboda in bar zancen Rauda ashe da gaske ne yarinyar nan yake nufi",

nannauyar ajiyar zuciya Mom ta sauke ta furta "ina ruwan Son amman dai wllh it was a real surprise to hear that Sameer has chosen that girl to be his wife, duk da dai gaskiya yarinyar ba mummuna bace tana da kyaunta daidai gwargwado amman dai dole ai mamakin jin ita ya fitar a matsayin mata kinga kaman shi Habiby ba za'ai mamaki ba sosae da yarinyar da ya aura tunda ba itace ta farko ba",

"Uhmm, ni kinga ma na kasa gane yarinyar yace man wai best friend d'in ita matar Son ce"

"Eh hakane, amman zaki iya tuna wata yarinya da aka kira ta bada biography na ita Amaryar a wurin dinner? Kaman itace mace ta farko data yi magana a wurin" shiru Hajiya Zainab tayi da alama tana k'ok'arin tunanowa ne can tay d'an tsoki tace bata jin zata tunata Mom tace bari ta duba cikin pictures d'in bikin tasan akwae hotunan ta sai ta turo mata ta gani tace Ok,

"To yanzu ya za'ai kenan? zaku amince mashi ya aure ta ne ko kuwa a'a" yar ajiyar zuciya Hajiya Zainab tayi tace "to, tunda yaji ya gani ita yake so ai Shikenan tunda bamu zamu zauna mashi da ita ba abu har ma an kira Mahaifin yarinyar kan Maganar, saidai bazan 6oye maki ba sam hakan bai kwanta man ba ba kuma don wani abu ba wai game da yarinyar kawai dai akwae wad'anda naso ya aura sosae kinga har Daughter Jahad nayi k'ok'arin had'a su saidai ban matsa mashi ba daya nuna bai so Saboda dama nayi tunanin ba lalle tayi mashi ba zai iya ganin tayi mashi k'arama to k'arshe gashi nan k'aramar ya samo zai aura" wata ajiyar zuciyar Mom ta k'ara yi cikin kwantar da murya tace "in dama Allah ya k'addaro ita ce matar tashi no matter what sai ya auretan don haka muyi mashi fatan Alkhairi kawai don kinsan in namiji na son Mace idon shi makancewa yake yanzu ga dai Son nan na fahimci ba K'aramin son Amaryar nan tashi yake ba" murmushi Hajiya Zainab tayi ta tambayi ya jikinta Mom d'in tace lafiya lou take ko laulayi bata yi tun kafin ma ta bar Abuja cikin har ya fito Hajiya Zainab d'in tace Allah sarki tayi fatan Allah ya sauketa lafiya Mom ta amsa da Amin,

"Jiya mun yi waya da Ummi da Abie" Hajiya Zainab ta fad'a Mom tace "eh haka suka ce man da na kira su da daddare, wai don Allah bazaki mana k'ok'ari ba su dawo nan kusa damu kamar yadda mukai magana kwanaki" dariya Hajiya Zainab tayi tace "ai tunda nayi ma Ya Othman magana kan hakan yace muma fidda rai bazasu ta6a dawowa Nigeria ba na hakura, kuma suma basu so" Mom na dariya tace "ban ga laifin su ba wa zai so ya baro k'asa irin Qatar ya dawo Nigeria dama dai a Ethiopia suke ne"

"Wllh, ai Al'amarin K'asar nan sai Addu'a kawae amman tak'i cigaba har yanzu baya muke sosae a abubuwan cigaba da dama" Mom tace "uhmm ai kune zaku taimaka mana ku farfad'o mana da ita" tana jiyo sautin dariyarta tace su a suwa suda suke k'ananu Mom tace to Allah ya dubesu ya kawo masu Shuwagabannin da zasu kawo cigaba ta amsa da Amin daga baya suka cigaba da Magana dangane da neman Auren Sameer,

Misalin k'arfe ukku Fatuu ta fito daga wanka tana zaune a gaban mirror tana shiryawa yayin da Haisam ke kwance a gado yana baccin rana, shirin zuwa gidan su Fauzy take kamar yadda ta yanke zuwa yau tayi masu bayanin da Haisam yayi mata game da Sameer, bayan ta gama yin shafa ta mik'e ta nufi Wardrobe, doguwar bak'ar riga roba ta fiddo ta saka rigar d'an guntun hannu gareta ta bi jikinta cikinta ya fito sosae bayan ta gama sakata ta kai hannu ta fiddo wani lifaya lace bak'i mai adon fulawowi ja da silver, musamman dama taje Hajiya ta koya mata nad'a lifaya kwanaki Saboda tana dasu a kayanta, gaba d'aya sark'a da yan kunne silver ta saka masu kyau sai Agogo shima silver, gaban mirror ta dawo tayi d'aurin kallabi Zarah buhari da wani bakin kallabi, sosae shigar tayi mata kyau sai faman sakin murmushi take, takalma Flat ta d'aukko silver sai yar purse, gado ta nufa bayan ta gama ta zauna ta bangaren da Haisam yake tana kallon yadda yake baccin hankalin shi kwance, murmushi ta shiga saki ta matsa saitin fuskar shi ta rankwafa tay pecking kumatun shi, tana d'agowa ya bud'e idanun shi slowly suka shiga cikin nata, bin ta da kallo yay kafin a hankali taji ya furta "kin yi kyau sosae" murmura mashi ido tay tace ta gode,

"Na gama shiryawa zan tafi" kai ya jinjina yace Ok bari ya kaita, da sauri tasa duka hannuwan ta akan shi alamar kada ya tashi tace ita zata je da kan ta, d'an waro ido yay cikin murya ta wanda ya tashi daga bacci yace "hannun ki fa bai fad'a sosae ba...." Da sauri ta katse shi "Wllh kau lafiya lou yanzu na iya driving d'in sosae rannan ma ba ni na kai mu School ni da Mino ba, wani kallo yay mata "amman ai ina Motan ko" tura mashi baki tay ta fara shagwa6a tana fad'in Allah lafiya lou zata je ai tana fita ita kad'ai taje gidan gwaggo ko, shiru yay kawai yana kallonta tace to bari taje sai yazo ya dawo da ita, kaman bazai ce komai ba sai kuma taga ya lumshe mata ido ta washe baki ya furta "You should be very careful pls" da sauri ta jinjina mashi kai, saida ta k'ara pecking lips d'inshi sannan ta mik'e yace bari yazo yaga fitar ta tace a'a don Allah yayi baccin shi, girgiza mata kai yay ya yunk'ura ya tashi zaune, yana ruk'e da hannunta suka fito daga cikin d'akin tace bari ta d'aukko abu a kitchen, bada Jimawa ba ta fito ruk'e da madaidaicin basket mai kyau acikin shi luxury Warmers ne guda biyu Abincin rana da tayi ne dama ta zuba zata kai ma su Fauzy,

Bayan sun iso parking space d'in shi ya shiga ya fiddo mata da Motar cikin harabar, bud'e kopar driver seat d'in yay ba tare daya fito ba yace mata ta bari suje kawai ta nok'e mashi kai tana d'an yamutsa fuska tace to in ba'a bari tana fita ita kad'ai ya za'ai ta saba, shiru ya d'anyi yana kallon ta har lokacin idanun shi a d'an lumshe suke, ba yadda ya iya tunda ta nuna tana so ya fito ita kuma ta shiga ta zauna sai faman sakin murmushi take bayan ta daidaita natsuwar ta ya rufe mata kopar, sauke glass tayi ta kashe mashi ido tare da furta kada ya damu ai yasan matar shi nada saurin gane abu yay murmushi kawai tace ya shigo ta aje shi a bakin gate sai ya koma ya girgiza kai yace zai koma, yana tsaye taja Motar ta tunkari gate Officer ya taso ya zuge mata shi da zata fita ya d'aga mata hannu tare da Fad'in Allah ya tsare ta sakar mashi horn, Jama'a kuzo kuga Fatuu yar fillo na tuk'a Jeep abun na Allah ne, bata yi tunanin tsayawa ba a gidan su shagon Kawu Amadu ma a rufe yake tasan bai wuce yana ciki yana bacci ta wuce.

Alhamdulillah, lafiya lou ta k'araso kopar gidan su Fauzyn, bayan ta parker ta fito kopar baya ta bud'e ta d'aukko basket d'in Abincin bayan ta rufe Motar tana niyyar nufar cikin gidan wayarta ta fara ringing tun bata ga mai kiran ba ta gane Haisam ne, d'auka tayi tana yar dariya tace ya kwantar da hankalin shi gata ta iso lafiya a hankali ya furta Alhamdulillah, tambayar shi tayi halan ma bai koma baccin ba yace mata ya kasa Saboda tunanin ta tane dariya tace to ai yanzu sai ya koma kafin ai la'asar ya furta Ok, tambayar ta yay yaushe zai zo ya dawo da ita tay d'an Jim kafin tace to asaman mi zai zo ko ya bari ta dawo da sauri yace a'a indai zata kai dare to bazata yi driving ba, k'arshe Tk tace to ya turo sai ya dawo da ita yace Ok, ba kowa a cikin parlon lokacin da ta shiga yaran Aunty Mareeya na tahfiz, sallama ta tsaya tana yi a cikin parlon jin shiru yasa tayi tunanin k'ilan bacci suke ta nufi d'akin Fauzy, tura kopar tayi ta shiga da sallama tana shiga ta hango Fauzy kwance a saman gado tana facing ceiling ta d'age k'afafun ta, saida ta isa bakin gadon sannan ta ankare da ita da sauri ta kai hannu ta cire earpiece d'in dake a kunnanta ta tashi zaune jikinta sanye da jeans da shirt, waro ido tay alamar mamaki Fatun ta zauna a bakin gadon bayan ta aje basket din,

"Yaushe kika zo har ban ji shigowar ki ba?" Fauzy ta tambaya da alamun Mamaki, yar harararta Fatuu tay tace "Yaushe dama zaki ji na zo kin dad'e kunnuwa" dariya tay tayi mata sannu da zuwa Fatun ta amsa,
"Ya yi kyau Amaryar Ya Haisam Mom twins in sha Allah, wannan wanka haka kinga yadda kika had'u sai kikai kaman wata shuwa Arab wllh" yar dariya Fatuun tayi "godiya nike Amaryar Sameer in sha Allah" yanayin fuskar Fauzy ne ya canza tana d'an murmushi had'i da d'an ta6e baki Fatun tace ita da zata ce Allah ya yarda tay murmushi kawai,

"ina Ya Haisam d'in shi ya kawo ki?" Girgiza mata kai tay tace ita kad'ai tazo tace Napep ta hawo kenan, k'ara girgiza kai tay tace a Motar ta, da alamun mamaki Fauzy tace "inyee, kice hannun ki ya fad'a sosae" kai ta d'aga mata tana murmushi, shiru suka d'an yi duk suna d'an murmushi Fauzy na son tambayar ta yadda sukai da Haisam ta kasa can dai tay k'arfin halin ce mata ta tambayi Ya Haisam d'in tace mata eh,

"to ya kukai da shi ne?" Wani kallo mai kamar harara tayi mata tace "ba ke zan fad'i mawa ba wadda ta bani sak'on zan fad'i ma yadda mukai dashi" gyad'a kai tayi tace Allah ya bata hak'uri Fatun ta saki dariya, tambayar ta tayi Aunty Mareeya tace mata tana d'aki ita da mijinta k'ilan ko bacci suke tun bayan dai da suka ci Abinci kowa ya shige d'aki itama tayi baccin ta farka ne,

"ko in kira maki ita a waya ne?" Da sauri Fatuu tace a'a tunda ba yanzu zata tafi ba ta k'yale ta in ta fito sunyi Maganar tace to, kallon basket d'in data shigo dashi tay tace "k'awata mi muka samu haka?" tana murmushi tace mata alkubus d'in fulawa ne tayi, matsowa bakin gadon tayi ta kai hannu ta d'aukko basket d'in, a saman gadon ta d'aura shi kafin ta kai hannu ta bud'e babbar Warmer d'in, sosae Alkubus d'in yayi kyau ya bada shape d'in robobin da tayi amfani dasu wurin yi, bud'e d'ayar warmer d'in tay nan miya ce da ta ji had'i tayi kitif tasha ganda mai had'e da tsoka sai uban k'amshi ke tashi, jinjina kai Fauzy tayi tana murmushi tace "Abinci mai sunan Abinci dai na a Warmers d'in yan gayu" yar dariya Fatuu tay tace "su ku kenan",
Fauzy tace ina ai su ba yan gayu bane, rufe Warmers d'in tay ta maido basket d'in k'asa bayan ta aje ta d'ago Fatuu tace bazata ci ba tace zata ci bari cikinta ya d'an k'ara fad'awa yadda zata yi mashi cin mutunci ta d'aga mata kai, hira suka shiga yi farko kan Sameer ne Fauzy na bayyana mata abunda take tunani game da ba sonta yake ba kawai hakanan zai aure ta in ma an amince mashi kenan ita kuma Fatun tana nuna mata bata tunanin hakan daga baya suka dawo hirar karatun su, suna haka aka fara kiran sallar la'asar bayan d'an wani lokaci Fatuu ta mik'e don tayi salla, cire nad'in lifaya d'in tayi ya rage doguwar rigar ce a jikinta Fauzy dake kallon ta tace "Ma sha Allah abu dai sai k'ara girma yake, kinsan har na k'osa inga Babyn ku don nasan dole zai yi ko zata yi ruwan kyau wllh" dariya kawai Fatuu tayi Fauzyn ta k'ara cewa Allah dai ya raba lafiya tace Amin ya Rabbi, toilet ta nufa idon Fauzy a kanta tana magana kan yadda hips d'in ta suma suka k'ara bud'ewa, bayan tayo Alwalar ta fito ganin Fauzyn bata da niyyar tashi yasa tace mata ita bazata yi sallar bane ta d'aga mata tace "tawa ta kai tuni" yar dariya Fatuu dake tsaye tayi tace yaushe rabonta da tace bata salla tun bayan da ta samu ciki Fauzy tace dama ita da period yanzu ai sai bayan ta haihu in kuma tana daga cikin Matan da basu yi ne in suna shayarwa to har sai ta yaye bayan na haihuwa ya d'auke ta d'aga mata kai, Hijab tasa Fauzyn ta bata bayan ta shimfid'a mata abun salla ta kabbara, nufar k'opa Fauzy tayi ta fita bada jimawa ba sai gata ta dawo ruk'e da plate ta duk'a a gaban basket d'in ta fara zuba alkubus d'in, komawa tay saman gado ta fara ci,

"Wllh k'awata ba zancen santi ba kin bala'en iya girki, yanzu dai ji yadda wannan alkubus d'in yayi dad'i sai kace na alkama ne wllh, wai don Allah ya akai kika iya sarrafa Abinci ne Allah sau da yawa ina mamakin hakan acikin rai na" ta k'arasa tare da tura tsokar nama idonta akan Fatuu data sallame salla tana kallonta da murmushi,

"wurin gwaggo da Aunty Saude na koya na kuma k'ara da tawa fasahar, in kina so ki zo in koya maki ki rink'a yi ma Angon ki Sameer yadda zaki kama mana shi da kyau" tana dariya tace wannan wane irin Abinci ne bai ci ai tasan dole yana cin masu dad'i Fatuu tace to ai itama Hubby d'inta na cin masu dad'in amman a haka yake santin nata duk in tayi hakan ai ba hujja bace da zata ce bazata k'ara koyan yadda zata rink'a yin Abinci mai dad'i ba, sosae Maganar taba Fauzy dariya tace sai kace ta ga anyi auren nasu Fatun tace ai in sha Allahu ma za'a yi Sameer bai da wata mata sai ita da yardar Allah, shiru tay don bata san mi zata ce mata ba gashi tak'i ta fad'i mata yadda sukai da Haisam,

"Wai Fauziyya ko Zarah ta zo....." Kaman daga sama suka ji muryar Aunty Mareeya tana fad'in hakan, had'a idon da sukai da Fatuu data juyo tana kallon ta yasa bata k'arasa Maganar ba ta d'an waro ido alamar mamaki, k'arasa shigowa tay ta nufi bakin gado ta zauna idon ta akan Fatuu dake ta mata murmushi tace "yar gidana yaushe kika zo ban sani ba sai yanzu da Abban su Hanif ya dawo daga Masallaci yake man Maganar Motar da aka parker a waje saitin gidan nan naje na lek'o ta ina gani nace wannan ai Motar Zarah ce?" Gaishe da ita ta fara yi kafin tace mata tun d'azu tazo Fauzy tace mata tana bacci, kallon Fauzy dake ta cin Alkubus tay ta d'an harareta "maimakon kije ki fad'i man tazo" yar dariya tay tace to tana tare da mijinta ya zata je mata d'aki, "to uban me ake a d'akin da bazaki je ba ko yau kika fara zuwa" dariya suka saki harda Fatuu Fauzyn tace "uhmm nidai ai ban ce wani abu ba ko nayi tunanin ko kuna bacci ne kuma da har zan kira ki ita tace tunda ba tafiya zata yi ba in k'yale ki gata nan ki tambaye ta" tsoki ta buga still dariya Fauzy ke yi tace mata ga Alkubus nan Zarah ta kawo masu ta jinjina kai, maido idon ta kan Fatuu tay tayi mata godiya ta tambayi mijin nata ya dawo lafiya dasu Hajiya da gwaggo duk ta amsa mata, mik'ewa tayi ta cire hijab d'in tana cikin ninketa Aunty dake kallonta tace "yar gidana abun Alheri dai sai k'ara girma yake ma sha Allah, amman ya fara motsi kuwa?" tana dariya tace mata a'a ai ba fa wani girma can yayi ba ta fad'i mata watannin shi Aunty tace to amman dai gaskiya in haka ne zata yi girman ciki yadda cikin farko bai cika wani girma ba k'ilan dai da gaske yan biyun ne, ita dai murmushi kawae take yi, bayan ta aje Hijab d'in ta nufi gadon ta haye idon ta akan Aunty Mareeya tace "kiyi hak'uri jiya kinata jira na naga dare yayi shine na yanke bari sai yau in zo in fad'i maki komai baki da baki" da sauri tace ai ba komai dama itama bata san ran a jiya zata kira ta fad'i mata yadda sukai ba ba kamar data ce bai gari,

"Na tambaye shi duk abunda kika ce harma da wanda baki ce ba wato aikin shi" a k'agauce Aunty tace aikuwa fa ba'a san aikin shi bama wllh to yanzu ya sukai da shi, tiryan tiryan ta shiga yi mata bayanin duk yadda sukai da Haisam gaba d'aya sun maida hankalin su akanta harda Fauzyn tayi cak tana kallon bakin Fatun, tun kafin ta rufe baki Aunty ta shiga washe baki ta fara fad'in "Alhamdulillah, Alhamdulillah dama ni wllh ban ji ina zargin shi da komai ba kawai a rai na ina jin sakayya ce ubangiji zai mata da shi" Murmushi Fauzy kawai ke saki bata ce komai ba Aunty ta kalle ta tace "to kin ji dai ai yanzu sai ki kwantar da hankalin ki tunda ga bayani nan daga bakin mai dil gashi nan kuma da kan shi yace abun kiyi Alfahari ne ma ita matsalar tashi da aka ce kada ki d'auketa a babbar matsala ke zaki zage damtse ki hana shi hakan sannan ki kore mayun kudajen matan da ke bibiyar shi wannan duk mai yuwuwa ne ba kamar in kika shige daga ciki in sha Allah za muyi k'ok'ari ya dawo bai sha'awar ta6a kowacce mace in ba ke ba" murmushi kawai Fauzy ke saki haka ma Aunty Mareeyar sai faman washe baki take gaba d'aya dad'i ya cikata farinciki ne bayyane akan fuskar ta can tace ma Fatuu to miye aikin shi data tambaya bata fad'i masu ba,
bayanin aikin nashi ta shiga yi tun kafin ta gama yanayin fuskar Aunty ya fara sauyawa lokacin data gama fad'i masu gaba d'ayan su zaro ido sukai da alamun razana Aunty tace wai bata gane su ke yin rocket ba wai wadda ta sani ko kuwa, Fatuu na dariya tace mata eh, aikuwa gaba d'aya ta k'arasa zaro idanun ta kai duka hannuwanta ta dafe k'irji tace "na shiga ukku ni Mariyatu, Zarah wannan abun fa ba shine ake ce ma makamin k'are dangi ba yanzu ace su suke yin shi" sosae ta rud'e don yanayin fuskar ta ya bayyana still dariya Fatuu ke yi tace mata itama wllh farko saida hankalinta ya tashi amman ai yace shi yafi k'arfi ta bangaren had'a jirgi kuma ba kowanne rocket ne missile ba, yarfa hannu Aunty tay ta d'an cize baki tace "ki gane Zarah irin abun nan ko wanda yasan inda ake saida su dole kaji tsoron shi balle kuma wanda ya san inda ake k'era su yake kuma aiki a wurin, haba, haba kice dole ma Sameer yak'i dariya suda ke k'era wannan mugun abun tashin hankalin ta ya zai rink'a ma sakin fuska, ai wllh Fauziyya ko baki son shi yanzu yazama dole ma ne ki amince mashi in dai ba so kike ya k'arar da kaf dangin mu ba koma ya tashi garin Funtua gaba d'aya",

Fatuu mi zatayi in ba dariya ba harda dafe ciki da 6ungulawa saman gadon don gaba d'aya Aunty fa ta rud'e, ita kanta Fauzy duk da ta d'an razana amman sosae Aunty ta bata dariya, bayan Fatuu ta tsagaita da yin dariyar ta taso zaune nan ta shiga kwantar ma Aunty da hankali tana nuna mata shifa ba'a ce dashi ake k'era wannan ba kuma koda dashi d'in shidai ai sana'a ce yake kuma misali don suna k'erawa hakan ba yana nufin sun iya amfani da shi ba tunda hakan ma wani ilimin ne, fuska a kwa6e Aunty ke kallonta hakan ya k'ara ba Fatuu dariya, da k'yar dai aka samu Aunty ta d'an kwantar da hankalinta Fauzy ta zuba mata alkubus ta fara ci duk in Fatuu ta kalleta sai ta saki dariya ita kuma saidai ta d'an girgiza kai ta tura Alkubus a baki, itama ta yaba alkubus d'in tana cikin ci tace ma Fauzy sai ta tsaya ta koya Abinci sosae in ba haka ba taje ta kwa6a mashi ya tarwatsa ta da rocket ita ta sani gaba d'aya suka kwashe da dariya Fauzy na fad'in ai fa sun bani da zancen rocket, bayan ta gama ci Fauzy tace yanzu sai ta kira Baban ta sanar mashi ko tana harararta tace ta sanar mashi da uban mi da ba tace bata son shi ba, Fauzy na murmushi tace to yanzu tana son shi Saboda kar a tashi Funtua suka saka dariya harda ita Auntyn,

Kiran Mahaifin nasu ta shiga yi tana fara ringing ya d'aga cikin girmamawa ta gaishe dashi tare da tambayar yadda suke duk ya amsa mata, a nutse ta shiga yi mashi bayanin sun yi magana da Fauziyya kuma ta nuna tana son shi har ma sun yi bincike akan shi, nan ta kwashe komai ta sanar mashi amman banda zancen ta6a mata da aka ce yana yi, nannauyar ajiyar zuciya mahaifin nasu ya saki yay d'an jimm har saida Aunty ta tambayi Lafiya da yanayin damuwa a muryar shi yace to ai abun ne ba K'aramin Al'amari bane d'an Governor fa, Aunty tace "Don Allah kar ka wani tashi hankalin ka Baba ai Allah baya daurawa bawa abunda bazai iya ba, kuma ai shi yaron yasan ita wacece tunda ta sanar dashi har ma aiki daka ajiye da noma da kake yi yanzu duk ta sanar mashi tunda yaji ya gani to kaga ai ba abun damuwa bane kuma dama ai ance wani hanin ga Allah baiwa ne k'ilan sakayyar abunda Mujaheed yayi mata ne" jinjina kai yay ya furta hakane kafin yace yanzu ita ya take ganin za'ayi don shi wllh gaba d'aya kan shi ya d'aure ganin abun yake ma kamar wani al'mara, dariya tayi tace ba al'mara bane da gaske ne ta kuma cewa "abunda nike gani Baba shine ka kira su kamar yadda kace masu sai kace cikin weekend mai zuwa in yayi masu sai su zo" shiru yay kafin yace mata hakan bai yi kusa ba kuwa tace a'a ai tunda neman Aure ne za'a zo ba wai bikin ba gara kawai a basu dama yanzu zata yi ma Yaya Mubarak magana duk abunda ya dace za'a yi in sha Allahu itama in dai zasu zo lokacin tana tunanin zata zo, a sanyaye yace Shikenan zai kira su d'in duk kuma yadda sukai zai kira ya sanar mata tace to, fatan Alkhairi yayi ya saka masu Albarka daga haka sukai sallama, suna gamawa ta k'ara ma wayar kud'i ta bank ta kira Mahaifiyar su, kamar yadda sukai da Baban nasu haka itama tayi mata bayani, sosae itama jikinta yay sanyi daga yanayin muryarta tace mata yanzu ita tana ganin hakan mai yuwuwa ne Aunty tace in sha Allahu su yi Addu'a kawai tace Shikenan zasu yi, bayan sun gama wayar kallon Fauzy tay da tay zuru ita kanta na Baban nasu ganin abun take kamar al'mara d'in tana murmushi tace mata to ta kira Baban nasu Fauzyn ta d'an ta6e baki tace umm Fatuu ta kai hannu ta dafata da murmushi tace wannan ba abun damuwa bane abun farinciki ne k'awata tay yar dariya,

"Yanzu ni abunda nike gani in sun amince zasu zo Weekend d'in kar a wani ce za'a takura kai tunda nasan maza ne masu zuwa kuma ko gidan namu suka gani zasu fahimci irin k'arfin mu, yanzu bari in je d'aki in natsu sai in kira Yaya Mubarak d'in tunda shine mai kud'in gidan yana aiki kuma dama ko ba yanzu ba kullum cikin yin hidima yake sai mu tsara abunda ya kamata duk dai a taru a had'a k'arfi da karfe, ina ganin har fenti yakamata ayi ma gidan sannan tunda a parlon Baba za'a tarbe su sai a gyara shi sosae a canza kujerun ciki da duk abunda yakamata, gaskiya dole ma in je" ta k'arasa Maganar tana jinjina kai, a sanyaye Fauzy tace to banda gadon Baban za'a canza Aunty tace tana tunanin ba sai an canza dashi ba tunda a parlor ai za'a zauna,

"Amman in suka ce zasu kwana fa?" Fauzy ta fad'a fuska a d'an yamutse, shiru Aunty tayi alamar nazari can tace gaskiya bata tunanin hakan su fa manyan mutane basu kwana wuri irin haka in ma ta kama masu a Hotel suke sauka amman ko don k'ilan su buk'aci shiga yin alwala ko wani abu akwae buk'atar a canza d'in hatta toilet d'in ma a gyara shi abunda ke buk'atar canzawa a canza, kai Fauzy ta jinjina sai kuma tace ma Aunty Mareeyar akwae kud'i a account d'in ta sai a had'a dasu da sauri tace Yauwa to aikuwa zasu taimaka sosae tunda suna da d'an yawa tana rufe baki Fatuu tace itama bari ta tura mata gudunmawarta duk sai a had'a,

"A'a Zarah don Allah ba sai kinyi wata dawainiya ba tunda kema ai baki rasa uzurorin kud'i ko" d'an murmushi tayi tace "ai Aunty Mareeya shine yanzu uzurin ya taso ko, ko bamu zama yan'uwa bane?" da sauri ta girgiza kai "tabbas mun zama Zarah, tun tuni ma" yar dariyar jin dad'i Fauzy tayi, nan take ta turo ma Fauzy 300k lokacin data duba alert d'in gaba d'aya ta zaro ido baki bud'e ta d'ago ta kalli Fatun sai kuma ta juya ta kalli Aunty dake niyyar tambayarta minene ta rigata ta hanyar d'aga mata wayar tana nuna mata credit alert d'in, waro ido itama tayi ta hau girgiza kai "gaskiya Zarah kud'in nan sun yi yawa a rage don Allah hidindimun rayuwar nan da yawa daga wannan fa sai wannan" girgiza kai Fatuu tay tace Allah ko an maido mata itama sai ta sake turowa, ba yarda Aunty bata yi da ita ba amman tace Allah baza'a rage ba ai don tana da su ne ta bada kuma in tasan zata k'waru ai bazata bada har haka ba inda ma tana dasu sosae fin haka zata bada to don ta tura ma Baffan ta wasu ya k'ara jari sannan kuma an siya mata shanaye, gaba d'aya fuskokin su sun nuna damuwa tana dariya tace don Allah wai ba an zama d'aya bane kuma itama ai ba wahala tayi ta same su ba nan ta shiga fadi masu da bikinta ta samu kud'i sosae don ko Mahaifiyar Sameer d'in 500k ta tura mata banda wanda k'awayen Mom suka babbata mai dubu hamsin mai dubu d'ari, daga baya godiya suka shiga yi mata Fauzy ta rungumeta ta saka kuka tana fad'in bata san da wane baki zata mata godiya ba tabbas dama tunda ta fara ganinta a school taji tana kaunarta ashe ita d'in Alkhairi ce a gareta, murmushi kawai Fatun ke yi tana ce mata haba ba komai fa,

"In rungume ku to nima in yi kukan" Aunty ta fad'a ta kai hannu ta rungumo su gaba d'aya Fatuu ta saki dariya, bayan ta sake su sosae tayi ma Fatuu godiya da Addu'oi daga baya ta mik'e tace bari taje suyi magana da Yaya Mubarak d'in, har ta juya Fatuu ta kirata ta juyo fuskarta da murmushi ta tambayeta ya akai ta d'an yamutsa fuska tace Abincin data dafa take son ci, hannu Aunty ta kai ta ruk'e ha6a tace "wani aikin sharri sai ciki, yanzu ki kawo mana wannan had'addan Abincin amman namu tagajan tagajan kike son ci" gaba d'aya sukai dariya Fauzy tace wllh ta manta ne bata zubo mata ba tunda tazo ko ruwa ma bata kawo mata ba Aunty tace gaskiya bata kyauta ba wato ta dafi abincinta mai dad'i kuma ita ko ruwa bata kawo mata ba hakan ai ba Adalci bane, da sauri Fauzy ta saukko tana fad'in ayi hak'uri tasan tayi ba daidai ba bari ta kawo mata suka nufi k'opa tare da Aunty,

bayan taje Bedroom d'inta nan ta hau fad'i ma mijinta Abban su Hanif yadda sukai da Fatuu game da bayanin da Haisam yayi kan Sameer da yadda sukai da Mahaifinta harda kud'in da Fatun ta bada, sosae yaji dad'in dukkan bayanan dama jiya da daddare Aunty ke fad'i mashi yadda sukai da Baban su, godiyar kud'in da Fatuu ta bada yay da Addu'ar fatan Alkhairi, kiran yayan nasu ta shiga yi bayan ya d'aga sun gaisa yace mata ai gashi ma a gida yanzu Baban su ke fad'i mashi yadda sukai yanzu ma suna niyyar kiran su Mutanen da suka kira din ne tace to duk yadda sukai dasu sai ya sanar mata, har zata mashi sallama yace mata ta dai tabbatar da duk bayanan da aka bada kan shi gaskiya ne ko don kada aga yana da nasaba ayi abunda za'a zo ayi dana sani daga baya ba fata ake ba, halin Haisam ta shiga fad'i mashi harda yadda ya auri Fatuu shima duk da ba ajin auran shi bace ta kuma tabbatar mashi da yadda yake ruk'e da ita yanzu daga baya ma sai ta mik'a ma mijin nata wayar don ya k'ara mashi bayani yana d'an murmushi ya amsa, bayan sun gaisa a nutse ya shiga yi mashi bayanin gaskiya Haisam mutumin kirki ne tun daga kan mahaifin shi da dangin shi yace yana da yak'inin bazai fad'i abun da ba haka bane akan d'an uwan nashi, hamdala Yaya Mubarak yay yace dama haka suke son ji tunda bai kamata ba ace ba ai wani bincike ba akan shi saboda aure ba abun wasa bane bayan sun k'ara tattaunawa daga baya sukai sallama ya mik'a ma Aunty wayar, cigaba da tattaunawa kan abunda yakamata ayi sukai daga baya sukai sallama.

Bayan sallar Magrib Aunty ta shigo d'akin Fauzy lokacin Fatuu na zaune akan abun salla cikin washe baki ta sanar masu yanzu Yaya Mubarak ya kirata yana sanar da ita an kira wurin su Sameer din yadda aka fad'a yayi masu sun ce ranar Asabar zasu je Funtua har saida gaban Fauzy yay wani irin bugu jin abun dai da gaske ne gashi ko waya da Sameer d'in ma basu yi ba, sosae Fatuu tayi murnar jin hakan sai faman washe baki take haka Aunty Mareeya ma da alama ta manta da zancen rocket, kiran Mahaifiyar su tayi tace mata ga Zarah d'in dama suna gaisawa da ita ta wayar Fauzy, cikin girmamawa kaman ko yaushe Fatuu ta gaishe ta bayan ta amsa ta tambayi su gwaggo da mai gidan nata duk tace mata lafiyar lau nan ta hau yi mata godiya da Addu'oi Fatun na murmushi tace mata ai ba komai duk an zama d'aya tace hakane kam. Bayan sallar isha Tk ya kirata yace gashi nan kopar gida ya zo tace to dama a shirye take don sunyi waya da Haisam yace mata ga Tk d'in nan zuwa, hijab Fauzy ta saka suka fito a tare, a cikin parlon suka iske Aunty Mareeya tana serving mijinta Abinci da Hanif shida k'annan shi guda biyu sultan da iman, tana ganin su tace badai tafiya ba Fauzy tace eh ga Tk nan yazo shi zai maida ta, mik'ewa tay tana fad'in maimakon to ya shigo, gaisawa sukai da mijin Aunty d'in yana d'an murmushi ya amsa tare da yi mata godiyar abun Alkhairi daya ji itama murmushin take tace mashi ba komai, Bedroom Aunty ta nufa bada Jimawa ba ta fito ta yafo gyale Fatuu tay ma mijin nata sallama yace ta gaishe da maigidan ta, harda su Hanif suka mik'e don yi mata rakiya, har zasu fita daga parlon Aunty tace ma Fauzy to ina basket d'in Abincin da sauri tace au ta manta wllh ta koma don ta d'aukko su kuma suka fita.

Bayan Fauzy ta gama komai ta kwanta ta fad'a duniyar tunanin Sameer, a yanzu ta gane tana son shi don da kafin suji bayani game dashi fargabar kada ace yana da wani mummuna hali ce ta kamata amman yanzu tunda taji bayanin da Haisam d'in yay take jin wani irin farinciki a cikin ranta sai faman yawo Sameer d'in yake mata a rai tun ma Fatuu na nan, hannu ta kai gefen filon data d'aura kanta ta d'aukko wayarta, bayan ta bud'e gallery ta shiga ta bud'o hoton shi ta k'ura ido tana kallo, zuciyar ta ce ta shiga raya mata in dai ta aure shi tabbas ba K'aramin dace da sa'a tayi ba wllh don ta ko ina Sameer yafi k'arfinta nesa ba kusa ba, shiru tayi tana cigaba da kallon hoton fuskar ta da d'an murmushi a zuciyarta ta shiga fad'in "da gaske kana sona ko kuwa matsayin taimakona zaka Aure ni" shiru tay don bata da amsar da zata ba kanta, tana ta faman zooming hoton tana k'are mashi kallo ji take kaman ta kira shi don sai taji tana son jin muryar shi, a ranta ta raya to in ma ta kira shi d'in tace mashi mi wata zuciyar tace ta gaishe dashi kamar yadda take yi, kokonton kiran nashi ta shiga yi k'arshe ta yanke bazata kira shi ba gaskiya kada yay tunanin ko don Saboda Maganar neman auren nata ne yasa ta kira, "to kuma in ba ki kiran nashi taya zai sake maki har ku saba tunda dai shi ga irin halin shi, kamata yay ki fara k'ok'arin jawo shi a jiki yadda zai sake maki har kiyi abunda Ya Haisam yace na raba shi da matan dake bibiyar shi" zuciyar tace ta raya mata hakan tay shiru tana ta d'an cizon k'umbar babban yatsanta gani take kaman hakan ba abu bane mai sauk'i can dai ta fita daga cikin gallery d'in ta koma phone bayan ta nemo number d'in shi saida tay d'an jimm kafin tay dialing nan take ta shiga, duk bugu d'aya tare yake da fad'uwar gabanta sosae fargabar kiran shi ta kamata yau ba kamar sauran lokuttan da ta kikkira shi ba a baya, har ta yanke bai d'aga ba sam bata ji komai ba don dama duk in ta kira bai d'auka sai daga baya ya biyo kiran, tun tana saka ran zai kira har ta fara fiddawa ta shiga sak'a ko bai son yin magana da ita ne ko kuma k'ilan wani uzurin yake k'arshe kuma ta yanke k'ilan ma yayi bacci ne, rufe idanunta tayi da niyyar yin bacci bayan ta gama Addu'a bata dad'e da rufe idanun ba wayarta ta fara ringing har saida gaban ta ya fad'i da sauri ta bud'e idanun, k'ura ma screen d'in ido tay bayan ta d'aukko wayar tana kallon sunan Sameer daya bayyana kaman bazata d'auka ba can dai a d'arare tay picking ta kai wayar kunnanta, shiru tayi shima kuma bai tanka ba can murya k'asa k'asa tace mashi ina wuni taji ya amsa da "lafiya" d'an murmushi ta saki jin voice d'in shi, tambayarta yay mi take bata yi bacci ba cikin daidaita natsuwa ta bashi amsa da ai ta kwanta baccin ne dai bai zo ba, bai ce komai ba suka d'an yi shiru can ya sake tambayar tana ina ne ta bashi amsa da tana gidan Sister d'inta tazo weekend k'asa k'asa taji ya furta Ok,

"Kai ma kayi baccin ne?" da k'yar ta tambaya harda d'an cize baki, amsa ya bata da eh acikin baccin ne suke magana nan take ta gane Magana ya gaya mata ta saki yar dariya da har saida yaji sautin ta tace "ai ina nufin ko kayi bacci ne na tashe ka,

"No, ina wurin Dad ena" d'an waro ido tay bata ce komai ba suka k'ara yin shiru, "akwae wani abu?" bayan d'an wani lokaci taji ya tambaya da sauri tace "a'a, dama na kira in gaida ka ne",

"Sai kin ga dama kike wannan kenan" ba zato taji yace haka ta d'an waro ido a ranta tace kaji shi ma ba sai ya ga dama yake kirana ba a fili kuma sai tace "a'a, ba haka bane, ina son in rink'a kiran to kuma ban san ko kana cikin aiki ba kada in takura maka,

"You can call whenever you want, in ina free zamu yi magana" bayan ya d'an yi shiru taji ya fad'i hakan wani irin dad'i taji tana murmushi tace mashi to,

"Yaushe zaki gama School?" d'an jimm tay alamar tunani kafin tace "nan da Kusan 7 Months masu zuwa" shiru ya d'an yi sai kuma taji yace Kusan ko kuma ya kai da sauri tace eh zasu yi good 7 Months kafin su gama ya furta Ok, shiru suka k'ara yi Fauzy sai faman sakin k'ayataccen murmushi take don wani irin dad'i take ji da suna wayar duk da ba wata Magana suke ba, bayan wani lokaci taji yace mata ta kwanta yadda zata tashi da wuri tace ai gobe ba School ya furta Ok ya manta,

"Yaushe zaka koma UK wurin aikin ka?" kawai sai ji tayi ta furta hakan da bud'ar bakin shi sai ce mata yay ya akai tasan a can yake aiki, waro ido tay ta bud'e baki don sai lokacin ta ankare da tayi 6aram6arama da ta fad'i hakan yanzu ya zata ce mashi yadda akai ta sanin tunda bai yuwuwa tace a wurin Haisam, tana haka taji yace yana jiran ta bashi amsa ta shiga yan kame kame can zuciyarta ta tuna mata da hoton shi data gani a Dp tare da turawa kuma akwae rubutu a k'asan dp d'in duk da bazata iya tuna mi aka rubuta ba, cikin yar rawar murya tace "d..dama a profile d'in ka ne naga hakan" tana yin Maganar gabanta ya hau fad'uwa gudun kada ace ba hakan a profile d'in, cikin ikon Allah kuwa a business profile d'in shi akwae bayani akan Company d'in nasu hakan yasa ya furta "Ok" wani sanyi taji a ranta ta d'an yi farfar da idanu alamar ta sha, ce mata yay zai koma soon,
"Allah ya kaimu ya kai ka lafiya" slowly ya furta "Ameen", shiru suka d'an k'ara yi taji yace yana son yin bacci ya gaji ya za'ai da sauri tace "to, gud night" shima hakan ya furta mata ta ciro wayar ta kashe kiran, mirginawa tay ta koma kallon sama tana ta murmushi sosae abun ke bata mamaki wai ace wannan mutumin data gani a d'akin Ya Haisam taita kallon shi har ya Harare ta ne wannan kuma ma wai aure zasu yi, jinjina kai ta hau yi still da murmushi akan fuskar ta a fili ta furta "ikon Allah kenan!" komawa tay tunanin to wai bai iya soyayya bane ko mi ace wai a haka soyayya suke tayi ma tunanin zai mata Maganar neman Auren nata amman bai ce komai game da hakan ba, wata zuciyar ce ta raya mata k'ilan kuma izzar ce ta sa haka kaman yadda Aunty tace ko kuma bai sake mata ne suyi soyayyar don kada ta raina shi, yar dariya tay ta raya in hakane kuma zai aureta, tunanin to su matan da akace yana ta6awa ba soyayya suke ba can kuma ta raya koda yake ai ance yawanci sune ke lik'e mashi, yin wannan tunanin yasa taji ranta ya 6aci ta d'aure fuska a fili ta furta "zanyi iya bakin kokarina inga na hanaka aikata hakan in sha Allahu" ta kai Maganar tana d'an jinjina kai, wayarta ce tay k'ara ta juya ta kai hannu ta daukko, sak'o ne aka turo mata bayan ta bud'e bin alert d'in tay da kallo na 200k daga Sameer, d'an murmushi tayi ta fita daga wurin tasan ko ta kira ba d'auka zai yi ba hakan yasa ta shiga WhatsApp ta tura mashi sak'on godiya, tunanin ko Aunty Mareeya tayi bacci ta shiga yi sai kuma ta raya bari ta jaraba kiran ta, wayar na fara ringing ta d'auka tare da tambayar Fauzyn miye tace "ashe baki yi bacci ba, dama zan sanar maki ne yanzu muka yi waya da Sameer" tana rufe baki tace "da gaske...,ya kira kenan?" Shiru Fauzy ta d'an yi kafin tace mata a'a itace ta kira ta gaishe shi,

"Ya yi kyau hakan kin kyauta dama bai kamata ki biye ma halin shi ba ta hakane zaki rink'a jawo shi jiki har ya sake maki kuma ki cire duk wani tunanin wai ko zai aure ki ne don ya taimaka maki da sauran su in bai son ki ba yadda za'ai ya aure ki tunda aure fa ba abun wasa bane da zai tsallake tarin yan mata ya za6e ki don taimako ba gama misali nan akan Zarah ba haka mukai ta nuna mata mijin nata na son ta shiyasa ya amince ya aure ta kuma sai gashi hakan ne" jinjina kai Fauzy tay tace to,

"ya yi maki Maganar zuwa neman Auren naki ne" da sauri tace "a'a wllh bai ce man komai ba game da hakan kawai waya mukai nace na kira in gaishe shi ne shine har yace wai sai naga dama nike hakan nace ai don kada in rink'a takura mashi ne shine yace zan iya kiran shi duk in ina so in dai yana free zamu yi magana",

Aunty ta furta da kyau ko wannan ma ai alama ce ta yana son ta, cigaba Fauzy tay tace mata ya tambayi lokacin da zata gama Makaranta ma, a d'okance Aunty tace "ina jin Saboda ranar da za'a saka maku ne ya tambayi wannan to",

da sauri Fauzy tace mata eh itama tayi tunanin hakan don dama data kira bai d'auka ba sai daga baya shine yace mata yana wurin Dad d'in shi ne, "Ma sha Allah abu dai nata tabbata" Aunty ta fad'a tana washe baki, fad'i mata zancen kud'in daya turo yanzu tayi Auntyn tace "wato shi soyayyar bada kud'i ya iya bata kalamai ba kenan, hakan yayi kyau yayi ta turo su muna mashi godiya don yanzu ba zamu rink'a mamaki ba tunda mun fahimci kud'in ne har sun mashi yawa" Fauzy na dariya ta furta "kai Aunty...",

"Allah kuwa Fauziyya a yadda aka fad'i aikin da yake na tabbatar ba k'ananun kud'i yake samu ba ga kuma Baban shi Governor kacokam, da ya turo maki kawai kiyi mashi godiya tunda k'arshe ma shi za'ai ma amfani dasu" murmushi kawai Fauzy tayi kafin tace mata yanzu ta turo mata su gaba d'aya ne tace a'a ta bari sai gobe zasu zauna su tsara abubuwan da za'a yi dasu don har sun gama Magana da baban su Hanif ranar Alhamis zata tafi sai ta bar su sultan d'in a gidan Maman taufiq ranar Friday in ta dawo daga School sai su dawo wurinta Fauzyn tace to,

"Oh ikon Allah ikon gaske, abu dai kinga kamar wasa kuma tabbata zai yi in sha Allah, gaskiya had'uwar ki da Zarah babban Alkhairi ne yo ke wannan ai ko karatun naki ma ba lalle ki amfana da shi ba kamar yadda kika amfana da sanin Zarah kawai dai shi ya zama sila ne",

"Wllh Aunty baki ji yadda nike jin ta ba a raina tamkar yar uwata uwa d'aya uba d'aya, ji yadda ta d'auki uban kud'i ta bada d'azun dama kuma tana man hidima sosae wannan ai ko wani dan'uwan naka mai hali wllh ba lalle yayi maka hakan ba,

"Ai tsakanin mu da ita sai dai Addu'a kawai wllh itace zamu iya saka mata da ita amman duk da hakan ina fatan ace munyi mata wani abu da zata ji dad'i sosae a ranta......" Da sauri Fauzy ta katseta da fad'in "Yauwa Aunty nima wllh ina tunanin haka, amman tunda ga bikin Mino za'ayi mi zai hana muyi kokari muyi masu wani abu da zasu ji dad'i sosae" kai Aunty ta jinjina "tabbas kuwa kin kawo shawara duk da bansan a cikin ku bikin wa za'a fara yi ba amman koma dai nawa aka fara ba abunda zai gagara kinga in ma naki aka fara komai zai zo mana da Sauk'i don lokacin nasan Atm Card d'in Sameer ya riga ya dawo hannun ki" Dariya sosae Fauzy ta saka tana fad'in kai aunty kin jiki da wata magana, bayan sun gama tattaunawa sukai ma juna sai da safe, a ranar kowa kwanan farinciki yay tsakanin Aunty da Fauzy da kuma Fatuu.

A kwana a tashi ba wuya a wurin Allah, ranar Alhamis tunda safe Aunty ta tafi Funtua, zuwa karfe sha d'aya ta isa gida lokacin data je har anyi ma gidan Fenti mai kyau kamar yadda sukai da Yaya Mubarak d'in su gaba d'aya gidan ya haske layin nasu dama kuma yana d'aya daga cikin gidaje masu d'an kyau a layin nasu, bayan sallar Azahar suka tafi inda za'a siyo furniture da ita da Kishiyar Maman su wadda itama suka d'auketa tamkar uwa a gare su don sam basu taso suka ga suna kishi ba da Mahaifiyarsu in ma suna yi to ba irin na tada fitina ko munafunci ba, wasu daga cikin K'annansu ma sai da suka girma ne suke gane wacece maman su, da yake Funtua akwae wuraren saida had'addun furniture da dama basu wani sha wahalar za6ar inda zasu ba don sun san inda zasu samu irin wanda suke so, bayan sun je wurin wanda katafaren bene ne sama da kasa duk kayan katakon ne iri daban daban, Manager d'in wurin suka buk'aci gani bayan anyi masu jagora wurin shi suka gaisa sannan Ya Mubarak yayi mashi bayanin dama kakara suke son suyi akwae kaya da zasu siya su kuma zasu za6i wasu sai suyi ciko cikin faran faran yace wannan ba matsala bane tunda suna yin hakan ya buk'aci ganin kayan suka sanar dashi suna gida amman akwai hoton su a waya, nuna mashi Vedio d'in kayan mahaifin nasu sukai ya gani kafin yace akwae buk'atar ya tura aje a gansu sai ayi masu kud'i sannan ayi cininkin, Yaya Mubarak ne yace to ba matsala a had'a shi da wanda zasu je d'in sai suje su dawo, ba 6ata lokaci aka had'a shi da Mutum biyu da zasu tafi Aunty Mareeya tace don Allah su kamanta ayi siyan mutunci Manager da suka fito tare da shi cikin show room d'in yana dariya yace karta damu su suna kamantawa sosae, a nan Aunty da Kishiyar Maman tasu da suke kira da gwaggo suka zauna akan kujeru don su jira su. Basu dad'e can sosae ba suka dawo ba laifi kam sun sayi kayan da mutunci don d'aki barin katako ne ba don dole tasa ba daba yadda za'ai Baban nasu ya yarda su siyar mashi da kaya Saboda yana son su ba tun yanzu bama sun so canza mashi kujerun yak'i yarda, za6ar wanda suke so suka shiga yi nan fa suka shiga ruwan idon wanda ya kamata, Manager d'in wurin ne ya basu shawarar d'aukar wasu lumbutsa lumbutsan leather chair yace tunda yaji suna d'akin mahaifin su zasu saka tunda shi Namiji ba'a san shi da k'yale k'yale ba, sosae kujerun sukai masu kyau saidai Aunty Mareeya tace ita abunda ke had'a ta dasu 6an6ara suke Manager yace ba dai irin wannan ba ai ko ita ta kalli leather d'in zata shaida ingancin ta yana mai tabbatar mata da ba abunda suke yi don ko shi irin su ne a parlon shi Aunty na dariya tace kodai abun su na yan kasuwa zai masu yace in yayi haka kuma ai kan shi ya kashe ma kasuwa ko, k'arshe dai su suka za6a harda dining table d'in su mai kujeru shidda, bayan sun gama da nan sama suka hau inda gadaje suke basu wani yi ruwan ido anan ba don sun san wanda ya dace su d'aukar mashi, bayan duk sun gama za6a Manager yace masu harda d'inkakkun labulaye suna dasu da agogunan bango in suna so Aunty tace yauwa bari su duba ya jagorance su nan ma suka za6a, bayan duk sun za6i abubuwan da suke so aka buga lissafi suka yi ciko wanda ya lillinka kud'in da aka Siya kayan nasu sosae, dama shima Ya Mubarak d'in ya bada tashi gudunmawar haka Baban su ma da yake ba K'aramin samu yake da Noma ba Saboda tsohon ma'aikacin Ktarda ne kuma ya kai babban matsayi kafin ya aje aikin banda babbar gonar da yake da ita anan garin yana da wasu k'ananu zasu kai ukku a wasu kauyuka dake kewaye da garin da alama dai Fauzy harda rud'ewa tasa tace ma Sameer mahaifin nasu bai iya biyan shi wayar data fasa mashi, a babbar Motar kamfanin aka zuba kayan su Aunty na gaba a Motar Yaya Mubarak suka tafi, bayan sun isa gidan tuni k'annansu har sun fito dana mahaifin nasu ta kopar shiga sitting room d'in shi ta waje, nan fa aka shiga sauke sabbin kayan yan unguwa suka shiga baza ido suna kallo, bayan angama aka d'aura nashi yan kamfanin suka tafi. Aiki ga mai k'are ka, aifa Aunty Mareeya bata ga ta zama ba dama ita ba mai son jiki bace bare abu kuma irin wannan nan fa suka zage ita da k'annanta maza da mata harda masu Aure guda biyu da suka zo aka shiga shirya parlon dama kuma tiles ne a k'asan kuma sam bai ji jiki ba Saboda ba yawan zirga zirga ake part d'in ba, zuwa bayan sallar La'asar sun gama komai gaba d'aya sashen ya koma kamar na Amarya sosae yay kyau yan gidan sai faman washe baki suke ba kamar yara sai tsallen murna suke, Vedio Aunty tayi ta tura ma Fauzy daga baya ta kirata ta sanar mata ta hau online ta gani, lokacin data yi arba da vedion bud'e baki tay ta waro ido nan ta shiga washe baki tana yarfa hannu sai faman fad'in Wayyo Allah take, da yamma mai gyaran Ac yazo don tuni ta lalace bata yi haka mai gyaran toilet ma, yan unguwa fa kan su ya kulle wasu da basu iya hak'uri sai tambayar ko biki ake gidan saidai ace masu a'a don Mahaifin nasu ya gargad'esu kan su ja baki suyi shiru sai komai ya tabbata. Sai da daddare Mahaifin su ya dawo gidan nan gaba d'aya aka taru a sashen nashi sai farinciki ake shima dai fuskar shi ta kasa daina murmushi Yay Addu'ar Allah ya tabbatar da Alkhairi duk suka amsa daga baya aka watse. Washe gari Friday shirye shiryen Abincin tarbar bak'i aka shiga yi da wuri su Aunty suka shiga kasuwa, a gidan Yaya Mubarak aka shirya za'a yi komai harda Warmers d'in da za'ayi amfani dasu plate duk anan za'a k'aro don Aunty Mareeya ta taho da wasu jigunannun Warmers d'inta dasu plates da sauran su.

Alhamdulillah Allah yayi dare gari ya waye an shigo Asabar lafiya, tun da sassafe yan gidan suka tashi aka hau gyaran gida masu aikin Abinci duk acan gidan Yaya Mubarak d'in suka kwana, Misalin k'arfe sha biyu na rana bak'in suka iso garin, kiran Mahaifin su Fauzy sukai suka sanar dashi game da isowar tasu don aje ayo masu jagora, dama Yaya Mubarak na gidan isowar su kawai ake jira shi ya tafi don ya taho da su, bada jimawa ba suka iso layin gidan Motoci guda biyu ne d'aya jibgegiyar bakar Jeep ce wadda anan bakin suke sai k'arama wadda itama bak'a ce sai faman salk'i motocin suke anan kuma security ne cikinta gaba da baya don a cikin bak'in harda Commissioner wanda d'an uwa ne kuma abokin mahaifin Sameer d'in ne sai sauran mutum biyun d'aya k'anin Governor d'in ne uwa d'aya uba d'aya sai d'ayan cousin brother d'in Governor d'in ne matsayin Yayan shi yake, Mahaifin su Fauzy ne tare da yanuwan shi guda biyu sai Yaya Mubarak da wasu daga cikin manyan Yayan shi maza guda ukku suka tarbe su cikin girmamawa kowanne cikin bak'in na sanye da babbar riga ta alfarma mutum biyu farar shadda ce sai d'aya ash, security d'in wanda jami'an yan sanda ne guda biyu sai guda biyu na civil defence ne su basu shiga ba suna a cikin Motar amman sun bud'e kopopin sai lokacin Jama'a suka samu abun baza ido da kyau yara da Almajirai ba sosae ba duk sun tsaya cirko cirko suna kallon Motocin haka Mutanen dake wucewa kowa idon shi na akan Motocin da kuma wad'anda ke zaune a bakin shaguna sai faman tambayar juna abunda ke faruwa a gidan suke wanda kuma ba mai amsa. A mutunce aka shiga gaggaisawa parlon sai zabga uban k'amshi yake daga baya aka fara gabatar da kai, su Aunty Mareeya ne suka fara shigowa da kayan abinci suna jerawa a saman Dining duk sun yi wanka sun sa kaya masu kyau, bayan sun gama suka shigo parlon duk suka zauna a saman Carpet suna masu sannu da zuwa tare da gaishe su, haka akai ta shigowa gaishe dasu ana fita, k'anin Governor d'inne da fara'a ya tambayi harda Amaryar acikin wad'anda suka zo gaishe dasu Yaya Mubarak yace a'a ita tana Katsina acan take zaune a wurin Yayarta yayi masu kwatancen Aunty Mareeya suka ce sun gane yace to a wurinta take, bayan an gama yan gaishe gaishen Yaya Mubarak yayi masu Maganar Abinci suka ce da su fara abunda ya kawo su tukun don ba dad'ewa zasu yi ba, neman Auren Fauzy sukai aka basu sannan aka fara maganar saka rana, a yadda suka ce shi Angon so yake asa lokacin da zata gama karatu amman in hakan bai masu ba suna da damar saka duk lokacin da yayi masu, shawara suka shiga yi Yaya Mubarak ne yace yana ganin su shiga ciki sai a tattauna harda iyayen su mata duk suka amince da hakan, ce masu suka yi bari su basu wuri su ci Abinci bayan sun gama sai a k'arasa saka ranar bak'in suka ce to ba matsala duk suka mik'e suka nufi cikin gidan Yaya Mubarak ne ya tsaya don yayi serving nasu Abincin,

A can cikin gidan gaba d'aya sun taru a parlon Mahaifiyar Fauzy harda Aunty Mareeya anata shawarwarin kan lokacin da za'a saka, shi mahaifin Fauzy nuna masu yake gaskiya wata bakwae kamar yayi kusa don yanzu lokaci gudu yake kaman gobe ne za'a ga yayi azo kuma ba'a gama shiryawa ba,

"Ni a ganina Baba kawai a amince da lokacin da Sameer d'in ke so Maganar shiryawa kuma in sha Allahu ba abunda zai gagara watak'il ma fa suce basu son ayi mata kayan d'aki" Aunty ta fad'a,
Malam Sama'ila k'anin Baban nasu ne yace "nima abunda nike tunani kenan tunda dai ai sun fi k'arfin duk wani abu da za'a yi ma Yarinyar",

gwaggo ce tace "hakane, amman dai bai kamata a dogara da hakan ba in dai basu suka ce kar ayin ba yakamata ayi mata komai daidai bakin gwargwado" Baban su ne ya kalli Mahaifiyar tasu yace ita bata ce komai ba tay dan murmushi a sanyaye tace "to ita a ganinta kawai a bi yadda yaron ke so don ko ya aka sa dai lokacin zuwa zai yi kuma indai a cikin wata bakwae ba'ayi shirin daya kamata ba to ko an wuce hakan ba lalle ayi yadda ya kamatan ba" Aunty Mareeya da Baba Sama'ila ne suka ce wannan gaskiya ne, suna haka Yaya Mubarak ya shigo ya gama zuzzuba masu Abincin, bayan ya zauna ya tambayi a wace matsaya aka tsaya Aunty tayi mashi bayani, to shima dai bayan Mahaifiyar su ya bi yace abunda ta fad'a gaskiya ne kawai a amince da hakan ayi fatan Allah ya kaimu ya kuma rufa asiri ai duk ba sai an zurfafa ba tunda dai ansan wacece za'a aura duk aka ce gaskiya ne, dariya Baba Rabi'u wanda Yayan mahaifin nasu ne yayi yace Fauziyya ta giggi6o masu aiki har sai anyi meeting sannan za'a saka mata rana duk akayi dariya. Lokacin da suka koma parlon har sun gama cin Abincin sun dawo sun zauna bayan sun zauna cikin girmamawa su Baba Sama'ila suka tambayi sun dai ci sosae ko suda suka yanko hanya suna fara'a suka ce Alhamdulillah sun gode, cigaba da zancen saka ranar sukai suka ce lafiya lou a saka hakan, tambayar Date d'in da zasu gama Makarantar sukai duk basu sani ba Yaya Mubarak ne ya tashi don ya tambayo Aunty Mareeya, itama cewa tayi bata sani ba aka kirawo Fauzy a waya tace itama bata san date d'in ba kawai watan ta sani, bayan Yaya Mubarak ya koma ya sanar masu yadda sukai k'arshe aka sa bayan ta gama Makarantar da sati biyu kawai, nan kowa ya amince aka hau Addu'oi da fatan Alkhairi, kud'i suka bada miliyan d'aya na neman aure da kuma kayan saka rana don basu taho da komai ba, anan parlon suka yi jam'in sallar Azahar gaba d'aya harda security d'in bayan sun gama aka shiga yin sallama su Aunty Mareeya ma duk suka zo suka yi masu sallama da godiya da kuma Addu'oin Allah ya maida su lafiya suna fara'a suke amsawa suka ce sai Allah ya kaimu biki kuma, tare duk suka fita dasu iyayen Fauzyn maza aka shiga k'ara yin sallama daga baya suka tafi, Aunty na komawa cikin gidan ta kira Fauzy lokacin tana zaune a saman gadonta tayi zuru tun bayan da aka kirata aka tambayi date d'in da zasu gama Makaranta gaba d'aya taji jikinta yay wani irin sanyi, lokacin da kiran Auntyn ya shigo har saida gabanta ya fad'i, hannunta har d'an rawa yake ta d'aukko wayar, tana yin picking Aunty ta rangad'a wata uwar gud'a tana fad'in Allah ya yarda an saka ranarta da Sameer suna gama Makaranta da sati biyu, runtse ido Fauzy tayi ta d'an cize baki Aunty tace bazata yi magana ba ko bata farinciki kawai sai ji tayi ta fashe mata da kuka, shewa Aunty tayi tace "yi kuka Fauziyya kin cancanci ki yi kukan farinciki" fad'i mata kud'in da suka kawo tayi cikin Muryar kuka ta tambayi yaushe zata dawo tace gobe in Allah ya kaimu, sauran yan gidan ne suka shiga amsar wayar suna mata Allah yasa Alkhairi harda gwaggo da Mahaifiyar ta, bayan sun gama wayar falon Baban suka koma baki d'ayan su harda iyaye mata aka cigaba da farinciki su Aunty suka sassauko da kayan Abincin nan cikin parlon kan Carpet aka cigaba da shagali don ba laifi sunyi abubuwa da d'an yawa kuma duka kad'an bak'in nasu suka ci, To Alhamdulillah sai fatan Allah ya nuna mana Auren Fauziyya da Sameer.......

92

_ASM BY ZAINAB BATURE_

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

.......A jiya Friday Haisam ya tafi Abuja daga can zai koma Us, lokacin da Fauzy ta kira Fatuu ta sanar mata da zancen saka ranarta tana a zaune parlon Hajiya, wata uwar k'arar murna ta saka ta hau yarfa hannu tana fad'in "Wayyo dad'i k'awata na taya ki murna wllh Allah ya sa Alkhairi ya kaimu lokacin da rai da lafiya" sai faman murna take ta kasa rufe baki, bayan ta gama wayar Hajiya ta tambayi abunda ya faru Fatun ta fad'i mata itama sosae tayi mamakin jin zancen Sameer zai auri Fauzy daga baya ta tayata murna tayi fatan Alkhairi, kiran gwaggo Fatuu tayi cike da Farinciki ta sanar mata dama tasan da Maganar itama murna ta tayata tayi fatan Alkhairi da Addu'oi,

Washe gari lahadi da yamma Aunty Mareeya ta dawo gaba d'aya bakinta bai rufuwa harda kudin da zasu siya kayan da zasu raba ma mutane aka bata, a ranar da daddare Mijin Aunty ya fita dasu suka je wani shopping mall dake kusa dasu suka siyo haddadun manyan biscuits dasu sweet kala kala da chocolate dama ta taho da goro da aka Siya acan Funtua, Washe gari bayan sunje Makaranta Fauzy taba Fatuu kayan ta raba ma mutane amman tace kada ta fad'i wanda zata aura haka Aunty Mareeya tace, sai bayan da aka yi masu break sannan ta rarraba ma yan ajin tana fad'i masu kayan sa rana d'in Fauziyya Ahmad ne akai ta mata Allah yasa Alkhairi harda yan ajin kusa dasu aka rarraba mawa, bayan an gama rabon ne Zainab tazo seat d'in su ta zauna a saman desk tace ma Fatuu amman da gani itama Fauzy dai mai kud'i ne zata aura ko, dariya Fatuu tayi tace miyasa tace haka tace ai ita tunda take bata ta6a ganin an raba irin wannan kayan a saka rana ba kana cin biscuit kunnan ka na motsi har saida ta ba Fauzy dariya, magiya ta hau yi ma Fatuu kan wai ta fad'i mata waye zata aura tana murmushi tace mata d'an uwan mijinta ne, zaro ido Zainab tayi tace bayan k'anwarta da zata auri k'anin shi itama Fauzy kuma d'an uwan shi zata aura tace mata eh cousin d'in shi ne, langa6ar da kai Zainab tayi ta marairaice fuska tace "Wayyo ni Zainabu baiwar Allah ni shine ban samu ko mai aikin gidan ba duk da ba son shi zan yi ba, Don Allah Fateema Ard'o nima ku samo man d'an uwan mijin naki" tana rufe baki Fauzy dake dariya tace mata basu son bak'ar mace sai fara Fatuu kau mi zatayi in ba dariya ba Zainab d'in tace abu mai sauk'i ai hakan ba abu ne mai wuya ba sai ta koma farar, Fauzy ta sake cewa to ai basu son farin bleaching, haka tay ta tsokanar Zainab d'in. Saida aka saka ranar da kwana ukku sannan suka yi waya da Sameer shima ita ta kira shi don ta gaishe shi kuma ko Maganar saka rana d'in bai mata ba har suka gama wayar a fili ta furta lalle akwai aiki a gabanta.

After a Month.......

lokacin cikin Fatuu ya shiga wata na shidda sai lokacin ta fara laulayi sosae, ba komai take ci ba yanzu ga amai da take yi duk da ba sosae take yin shi ba amman data ji k'amshi ko taci abunda bai mata ba sai tayi aman ga kuma kwadayin ciki tafi son abu mai tsami ko yaji a lokacin har an tabbatar da ba d'a d'aya bane a cikin nata sosae kuma ya k'ara girma.

Ranar Alhamis lokacin suna cikin Class wayar Fauzy ta fara vibration alamar ana kiranta, fiddo ta tayi daga cikin Aljihun rigarta lokacin data ga mai kiran nata d'an waro ido tayi gashi akwae malami ba damar ta d'auka, bayan kiran ya yanke sai ga wani ya sake shigowa hakan ya tabbatar mata da magana yake son su yi don in dai ya kirata sau d'aya bata kusa to bai sake kira har sai in ita ta gani ta kira sannan ya k'ara kira, d'agowa tay ta juya ta kalli Fatuu suka had'a ido ganin yanayin fuskar ta yasa k'asa k'asa tace mata ya akai ne sai da ta fakaici idon Malamin nasu sannan tace mata Sameer ne keta kira, d'an bud'a ido Fatuu tay sai kuma tace mata ta d'auki excuse sai taje suyi wayar ta d'aga mata kai, bayan ta maida wayar cikin aljihun ta mik'e ta nufi gaban ajin, tambayar malamin nasu tayi don Allah zata je ta yi fitsari da turanci ya d'aga mata kai ta juya da sauri ta fita, can k'arshen barandar ajin taje ta kai hannu ta fiddo wayar ta fara k'ok'arin kiran shi, har ta yanke bai d'aga ba tay tsaye tana jira ya sake kira aikuwa sai gashi bada dad'ewa ba ya sake kira, d'auka tayi a nutse tayi mashi sallama ya amsa tace ya kira tana cikin class ne kuma akwae malami yanzu ma excuse ta d'auka ta fito ya furta Ok, tambayar ta yayi k'arfe nawa suke tashi tace mashi k'arfe biyu saura kwata nan ma Ok ya furta daga haka taji yace ta koma Class, tsaye tayi turus a wurin a ranta ta shiga tunanin to miyasa ya tambaya, wata zuciyar ce ta raya k'ilan nufin shi ya sake kira can kuma wata zuciyar ta raya mata ko kuma zuwa zai yi, har saida gabanta yay wani dammm ta d'an zaro ido, kokonton anya zuwa zai yi ba tare daya sanar mata ko yazo garin ba ta shiga yi wani sashe na zuciyar tane ya shiga raya mata yana iya zuwan fa abunda tasan halin shi, tunanin kiran Aunty Mareeya tayi ta sanar mata,

"To iya haka yace maki?" Aunty ta tambaya bayan ta kirata tace mata eh, "humm, yanzu in zuwan yay ya zamuyi kenan, ace zuwa ba sanarwa in banda abun suriki na mak'erin rocket, shiru Fauzy tay tama rasa abun cewa, "kuma fa wllh da alama zuwan yayi tunda kince sau biyu yana kiran ki gashi kuma ya tambayi k'arfe nawa kuke tashi k'ilan zuwa zai yi Makarantar kuma dai in dai yazo wurin ki nasan ai da wuya bai zo nan ba" still shiru Fauzy tayi Aunty tace wai ta wani yi shiru bazata bada shawarar abun yi ba, d'an yamutsa fuska Fauzy tay ta yarfa hannu d'aya tace to ai ita tama rasa tunanin da zata yi ne, nannauyar ajiyar zuciya ta saki tace mata to ko ta kira shi ta tambayi zuwa zai yi shiru Fauzy ta d'an yi kafin ta d'an yi guntun tsoki tace gaskiya ba sai ta kira shi ba tunda da ya so ai da ya sanar mata ko kuma ma yana iya ganin kaman wani abu ne yasa aka tambaya, cewa Aunty tayi Shikenan bari tana ganin abunda za'ai kawai ayi shirin kota kwana yanzu dai lokaci ma ya k'ure in ace a shirya lafiyayyen Abinci in zuwan yayi tana ganin bari taje tayi ma maman taufiq magana akwae wata k'awarta chef ce

"In kuma ba zuwan yayi ba fa" Fauzy ta tambaya ta bata amsa da "ke zaki cinye shi kuwa" dariya Fauzy ta saka tace to ita miye laifinta tana yar dariya tace ita kuwa keda laifi tunda laifin shi nata ne don mi in baya ga yana 6aud'add'e zai zo bai sanar dasu ba, a kan hakan sukai sallama ta koma aji, sai bayan da malamin ya fita sannan suka yi magana da Fatuu itama dai zargin k'ilan zuwan zai yi tayi, gaba d'aya hankalin Fauzy ya kasu biyu tana tunanin ko zuwa Sameer zai yi tana kuma sauraren abunda ake masu a haka har aka tashi, tare suka fito da Fatuu ta rakata inda take Parking Motar ta kamar kullum, sallama suka yi tace mata k'ilan dai ba zuwan yayi ba tunda bai sake kira ba watak'il dama kiranta ne zai yi su yi magana Fauzy tace eh itama yanzu haka take tunani tayi mata Allah ya tsare sai sun had'u gobe,

Bayan tafiyar Fatuu juyowa tayi ta nufo hanyar hostel bata kaiga barin Class area d'in ba wayarta ta fara ringing, hannu ta kai cikin aljihun rigarta ta curota ganin shine yasa gabanta fad'uwa saida tayi d'an jimm kafin tay picking tana karata a kunne taji yace ta same shi a parking lot na Admin nasu, waro ido Fauzy tay baki bud'e ta curo wayar tana kallon screen d'in nan take gabanta ya hau fad'uwa tamkar ana mata luguden ta6are duk da tayi zargin k'ilan zuwan zai yi sosae taji Al'ajabin zuwan nashi don ko a chat bai sanar mata ba kuma ko jiya sun gaisa, har zata tafi sai kuma ta tuna da Aunty, Da sauri ta shiga kiranta tana d'agawa ta tambayi yaya ake ciki a d'an rud'e Fauzy tace wllh zuwa yayi gashi nan ya kirata wai yana a admin, jinjina kai tayi tare da murmushi mai sauti ta furta wani aikin sai surukin ta makerin rocket, ce ma Fauzy tay kada ta damu duk abunda ya kamata za'ai mashi tace mata to, cikin mutuwar jiki ta ci gaba da tafiya dama Admin d'in wurin hostel d'in su yake, tunda ta tunkaro wurin take ta faman wurga ido tana son gano wacece Motar shi a cikin jerin motocin Malaman su dake a wurin, tana gab da isa taga an bud'e wata galleliyar bak'ar Camry sai faman shek'i take kai da gani kasan sabuwa ce, wani d'an magidancin mutum ne ya fito daga driver seat d'in Motar jikinshi sanye da k'ananun kaya wando da riga mai ma6allai, suna had'a ido yay murmushi tare da yi mata alamar tazo da kai, a d'arare ta tunkare shi tana zuwa gaban shi ya d'an rankwafa ya gaishe da ita da murmushi akan Fuskar tashi, amsa mashi tay a hankali da hannu ya nuna mata back door d'in da take tsaye a gefenta yace mata bismilla yana ciki tare da kai hannu ya bud'e mata k'opar nan take wani irin fitinannan k'amshi ya huro wajen, d'an rankwafawa tay ta kallo cikin Motar idanunta suka sauka akan Sameer dake a hakimce a bayan idanun shi a lumshe, sanye yake da shadda wheat wadda Kusan ta saje da kalar fatar jikin shi kafafun shi na sanye da bugaggun takalma half cover coffee brown haka hannun shi ma agogon hannun shi fatar ta coffee brown ce, irin d'inkin da Haisam yafi so wato Senator style ne aka yi ma shaddar hannun yasa wasu had'add'un links masu d'an adon coffee brown daga tsakiya, sumar kanshi a kwance ta kawo har tsakiyar wuyan shi haka sajen shi ma a kwance yake luff, duk da shadda ce a jikinshi hakan bai 6oye komai ba na daga suffar shi kana ganin shi zaka gane k'arfafa ne na gaske, slowly ya fara bud'e idanun suka sauka a kanta ya bita da kallo still bai bud'e idon baki d'aya ba, d'an murmushi tayi mashi gabanta na bugawa a hankali tace mashi "ina wuni, an zo lafiya" shiru bai amsa mata ba sai kallon ta yake hakan yasa ta shiga yan kame kame tana cigaba da d'an murmushi, tana haka taji yace in bazata shigo ba ta rufe mashi k'opa yana fad'in haka ya janye idanun daga kanta ya maida su ya lumshe, d'agowa tayi ta d'an waiga bayanta sannan ta shiga cikin Motar ta d'an jawo kopar ba tare data rufeta baki d'aya ba, bin shi tay da kallo gaba d'aya yau tafi ganin kwarjinin shi fiye da sauran lokuttan da ta ganshi a baya,

"Ina wuni" ta sake gaishe da shi ya jinjina mata kai kawai ba tare daya kalleta ba, "an zo lafiya?" Shiru bai bata amsa ba atunaninta ko bai ji ba ne hakan yasa ta k'ara ce mashi hakan, jin shiru bai amsa ba yasa ta gane yana jinta ra'ayin amsawar ne bai da shi, tana cikin kallon shi ya juyo idanun shi suka shiga cikin nata ya shiga jefa mata wani mayen kallo nan take tasha jinin jikinta ta shiga yan kame kame tana d'an motsa baki kaman mai son fad'in abu ta kasa,

"Is that how you should welcome me?" cikin husky voice d'in shi ya furta hakan tare da d'age mata gira, wani k'afaffen miyau ta had'iya ta kasa bashi amsa sai faman zare ido take don ita a ganinta ai hakan da tayi ne daidai tunda shi kanshi ba sake mata yayi ba balle ta nuna tayi murnar ganin shi, tana haka taji yace ko bata yi farincikin ganin shi bane da sauri ta hau girgiza kai murya na d'an rawa ta furta "n...nayi sosae kawae dai naji mamaki ne tunda baka fad'i man zaka zo" d'an yamutsa baki yay ya d'age mata gira yace dole ne yayi hakan ta k'ara girgiza mashi kai tace a'a, kasa jure ma kallon shi tay ta maida idonta k'asa tana kallon yatsun hannunta ba zato sai gani tay ya kawo tattausan hannun shi mai d'an fad'i da kuma dogayen yatsu masu d'auke da dogayen gyararrun k'umbuna ya kamo hannunta bata gama Al'ajabin hakan ba sai ji tay ya jawota gaban shi ya had'e ta da jikinshi ya rungumeta ta gefe, wani irin shock Fauzy taji ya ratsa dukkan jikinta gabanta ya hau wani irin mugun bugu tsoro da Al'ajabi lokaci guda suka kamata jikinta ya fara d'an rawa, kai fuskar shi yay saitin kunnanta cikin wata irin magana mai kamar rad'a ya furta mata haka yakamata tayi welcoming nashi da sauri ta runtse idanunta jin yadda Maganar ta sauka a cikin kunnanta nan take wasu abubuwa suka fara mata yawo a jiki, sam ta kasa cewa komai wani iri take jinta don a rayuwarta in ba Mujaheed ba bata ta6a had'a jiki da wani Namiji ba haka ko yan uwanta saidai ko lokacin da bata mallaki hankalinta ba shima Mujaheed sai da k'yar ta fara yarda yake ta6a ta da yayi mata dad'in bakin Auren ta zai yi, suna haka taji ya tambayi karatunta da k'yar ta iya bud'e baki tace mashi Alhamdulillah, shiru sukai gaba d'aya k'amshin jikin shi ya cika mata hanci nan take wata kasala ta fara rufar mata jikinta taji ya fara yi mata wani iri aikuwa da sauri ta d'ago tana k'ok'arin raba jikinta da nashi taji ya saketa, bin juna sukai da kallo wani irin nauyi taji idanunta sun mata hakan yasa da sauri ta juyar da fuskarta daga barin kallon shi, jin yayi shiru yasa ta d'an juyo karaf suka had'a ido da shi yana kallonta da kaifafan idanun shi, tsarguwa tay da kallon da Yake mata cikin yar in ina tace mashi Makarantar tasu akwai tsauri ne in aka ganta haka zata samu matsala ne kuma nan wurin parking d'in motocin Malamai ne ana iya ganinta, har ta gama Maganar idon shi na akanta yanayin kallon da yake mata ne ya canza zuwa harara ya d'aure fuskar tashi da sauri ta janye idanunta daga kanshi ta koma kallon k'asa,

"Go and gather all your things!" Kaman daga sama taji ya fad'i haka, d'ago kai tayi da sauri ta kalle shi ya jinginar da kanshi jikin seat fuskar shi na kallon gaba ya d'an lumshe ido, da alamun rashin fahimta ta shiga bin shi da kallo ta kasa gane mi yake nufi da taje ta tattaro kayan ta, mi hakan ke nufi? shine abunda take juyawa a ranta ba dai fushi yayi da Maganar data fad'i mashi ba shiyasa yace haka, kenan ta daina karatun yake nufi ko mi, haka take ta sak'e sak'e a cikin ranta gashi yak'i ko kallonta balle ya bata amsa can da alamun rashin fahimta tace mashi bata gane abunda yake nufi ba da bud'ar bakin shi sai cewa yay bata understanding turanci ne tace a'a ta gane abunda yace amman in ta tattara kayan mi zatai da su, shiru kamar bazai bata amsa ba kafin taji yace ta daina boarding School a tak'aice yayi Maganar still idanun shi na a lumshe, kai ta jinjina kafin ta juya ta kai hannu ta bud'e kopar, Mutumin daya tuk'o shi na tsaye ya jingina da k'opar gaban suna had'a ido yay mata murmushi tare da Fad'in barka da fitowa a hankali tace Yauwa, daidai lokacin data fito akan idon su Zainab da Sa'adatu dake tahowa daga class zasu Hostel gaba d'aya idanun su na akanta har ta fito daga cikin parking space d'in ta nufi hanyar zuwa hostel aikuwa cikin d'aga murya Zainab ta k'wala mata kira, tsayawa tayi har suka k'araso ta d'an k'ak'alo murmushi tana yi masu, tambayarta Zainab d'in tayi bak'o tayi ne taga ta fito daga cikin wanccan galleliyar Motar kai ta d'aga mata alamar eh ta d'an waro ido tace "da sa ranar wani akan ki shine kuma kike saurarar wani ba kyau hakan wllh, kinga don Allah kawai ki had'a ni dashi tunda ke dai kin saida" yar dariya Fauzy tay Sa'adatu ta 6aka ma Zainab d'in bugu tana fad'in ita dai ta shiga ukku da son kudi wllh daga ganin Mota mai kyau shine zata ce a had'a su, a d'an harzuk'e tace a'a to wa zai k'i mai kud'i suma duk tasan inda mai Motar zai ce yana son su da gudu zasu yarda wllh, ganin suna 6ata mata lokaci yasa tace masu bari taje ana jiranta ne da sauri Zainab ta bita tana fad'in yanzu don Allah bak'in ciki zata mata ita tunda Allah ya bata mai kud'i ba sai ta taimake ta ba, tasan in ba fad'i mata wanene tayi ba bazata k'yaleta ba don ta cika nacin magana yasa tace mata ai wanda zata aura d'in ne yazo yanzu ma zuwa yay daukarta zata bar zama a hostel, gaba d'ayan su saida suka ji ba dad'i Zainab tace maimakon tace mashi ya barta taci gaba da zama tunda dai da sauran lokaci bikin nasu Fauzyn tace mata bai so, tare suka je d'akin nasu gaba d'aya don taya ta kwasar kayan, duk wani provisions dinta su ta raba mawa haka wasu daga cikin kayanta duk abunda wani yace mata yana so sai tace ya d'auka ba kamar Zainab duk tafi kwasar abubuwa har su bokitan ta da su robobi da plates duk su ta raba mawa iya trolley d'in kayanta sai wata yar babbar jaka ta saka sauran abubuwan da take so bata bayar ba, tare suka fito su hud'u Zainab tace to bazata yi ma mutane bankwana ba tace kawai sai gobe in Allah ya kaimu tazo har d'akin ma sai taje ta sanar ta saki, dama tunda Fatuu ta bar zama a hostel ita kad'ai take rayuwa a d'akin saidai masu zuwa taya ta zama ko kwana, a tare suka iso parking space d'in har lokacin mutumin ko ace driver d'in yana a tsaye yana ganin su da sauri ya bud'e kopar gaban ya rankwafa don ya bud'e boot d'in, bayan ya bud'e ya nufo wurin ya bud'e boot d'in suna kokarin saka kayan da sauri yace su barshi zai saka, kallon su Sa'adatu tay tana murmushi tace ta gode sai sun had'u in Allah ya kaimu suma godiyar suka yi mata har zata juya Zainab tace to 6oye masu mijin nata take da bazata had'asu su gaisa ba, d'an jimm Fauzy tay don bata san taya zata aikata hakan ba, ganin sunyi tsaye suna bin ta da ido alamar duk so suke su gaisa da shi d'in yasa tace bari tayi mashi magana, bud'e k'opar bayan tayi yana zaune a inda ta barshi yana latsa waya, rasa mi zata ce mashi tay tana a rankwafe ta bishi da ido, Slowly ya d'ago suka had'a ido tace mashi ga kayan nan ta d'aukko har an saka a boot ya d'aga mata kai kafin yace ta shigo, jimm tay tana d'an kikkafta ido ganin bata shigo ba yasa shi k'ara d'agowa tun kafin yace wani abu cikin yar in ina tace "d...dama wai k'awaye nane zasu gaida ka" shiru kaman bazai tanka mata ba sai kuma ya d'age gira yace mata yace yana son haka ne har saida ta had'iyi abu, d'an girgiza mashi kai tayi tace a'a dama sune suka taimaka mata ta tattaro kayan to sun tambayi miyasa zata bar hostel shine ta fad'a masu shine yazo daukarta, "ni wa?" taji ya jefo mata tambayar ta d'an waro ido don bata tsammaci jin tambayar ba da k'yar ta bashi amsa da wanda zata aura kawai sai gani tay ya d'an ta6e baki ya maida idon shi kan wayar dake hannun shi, tambayar shi tayi tace suzo su gaisan taga ya jinjina mata kai ba tare daya kalleta ba, d'agowa tay tace masu suzo su gaisa duk suka matso bakin Motar Fauzy taja gefe, a tare suka rankwafa suka ce mashi ina wuni a wani slow ya juyo gaba d'ayan su saida gaban su ya fad'i karma Zainab taji wani kallon k'urulla ta shiga bin shi dashi tana k'ok'arin tuna inda ta san shi, jinjina masu kai yayi kamar anyi mashi dole koda yake Kusan hakan ne yace masu ya School a tare suka had'a baki wurin amsa mashi da lafiya lou suka ce anzo lafiya anan dai kai suka samu ya jinjina masu daga haka suka ce sai anjima suka janye kan su, idanu a waje Zainab ke kallon Fauzy dake d'an murmushi tana son yi mata magana amman ba dama sai faman kallon ta take da alamun Al'ajabi, sallama ta k'ara yi masu ta shiga ciki har ta rufe k'opar sai kuma suka ga ta bude, kud'i ta mik'a ma Zainab rafar yan dubu dubu sabbi dal ta dubu d'ari tace gashi ance su raba saidai Sa'adatu ce ta amsa don gaba d'aya Zainab tayi Mutuwar tsaye, har Motar ta bar harabar Makarantar suna tsaye cirko cirko saida ta 6ace ma ganin su sannan suka juya kan Zainab nan fa suka shiga yaba irin kyaun shi har Sa'adatu na fad'in ko ina ta samo shi sai kuma tace ta tuna lokacin da aka raba kayan saka ranarta ance d'an uwan mijin Fateema Ard'o ne ba mamaki don an gan shi haka, Safiya ce tace amman dai da gani ya jik'u da Naira wllh ga mugun aji ji yadda yay masu magana ma, sai lokacin Zainab da still tsananin mamaki ke a kwance akan fuskar ta tace "to ku duk baku ma san wani abu ba, wllh wanccan mutumin da kuke ganin shi d'an Governor ne" zaro ido sukai tare da bud'e baki a tare suka furta "d'an Governor!!!" Kai ta d'aga masu cike da tabbaci tace masu da suka je bikin Fateema Ard'o Abuja a kan idonta suka zo shida Mahaifiyar shi da yan uwan shi a cikin jiniya d'an Governor d'in Nasarawa ne... Nan ta kwashe komai har yadda Sameer d'in ya fito daga cikin Mota ya shiga cikin gidan da dangantakar shi da Mijin Fatuu ta fad'i masu, nan fa duk suka shiga tsananin mamaki ba dai kamar Zainab da kanta ya gama daurewa ta yadda akai har suka san juna shida Fauzy har abun ya kai ga za'ai aure, a fili ta furta ashe shiyasa suna dawowa ta canza waya zuwa latest iPhone, gaba d'aya al'ajabi ma ya hana su yin murnar kud'in da aka basu da alama kuma gobe dole Fauzy tasha tambayoyi a wurin Zainab.

Suna fitowa daga cikin Makarantar cikin girmamawa driver d'in ya d'an juyo ba tare daya kalli Sameer d'in ba ya tambayi ina zasu, kallon Fauzy yayi da tayi zuru yace ta bashi address d'in gidan Sister d'in ta tace to, basu wani d'auki lokaci ba suka karaso Unguwar don kusa take da Makarantar tasu, kallon shi tay bayan sun tsaya ya d'an d'age kanshi jikin seat idanunshi a lumshe, ce mashi tay sun iso ya d'an d'aga mata kai ta k'ara cewa suje, shiru kaman bazai tanka ba can ya juyo suka had'a ido yace taje ta sanar ta d'aga mashi kai, lokacin data fito Driver d'in na tsaye yana ganinta cikin girmamawa ya tambayi kayan boot fito da su za'ai tace mashi eh, yana k'ok'arin d'aukar mata bayan ya fito dasu tace mashi ya bashshi zata d'auka yace to bari ya kai mata ko bakin gate tayi gaba yana biye da ita a baya, lokacin data shiga cikin parlon tsaye tay tana bin shi da kallo yasha uban gyara sai uban k'amshi ke tashi har labulaye an canza haka kujerun ma da gani har goge su akai don sunyi haske a ranta ta raya lalle Aunty tayi kokari, d'akin Aunty ta nufa lokacin data shiga a zaune ta isketa gaban mirror tana yin shafa, jin sallamar Fauzyn yasa ta juyo suka had'a ido, d'an waro ido tay tace to lafiya ta ganta da kaya nik'i nik'i tana murmushi tace sabon mai iko da ita ne yace ta dawo ta gama yin boarding, k'ara waro ido Aunty tay sai kuma tayi dariya, tambayar ina yake ta yi ta bata amsa da yana waje,

"Amman dai Fauziyya wani lokacin kaman d'an kai gare ki wllh ya zaki bar shi a waje maimakon ki shigo da shi" a d'an harzuk'e tayi maganar Fauzy ta bata amsa da ai shine yace ta shigo ta fad'i, da sauri Aunty ta mik'e tana fad'in don Allah taje ta shigo da shi ta nufi gaban wardrobe don ta saka kaya, a tare da shi suka shigo cikin parlon yana biye da ita, nuna mashi kujera tayi tana murmushi tace "have a sit" saida ya kalleta cikin ido sannan ya nufi kujera 2 seater ya zauna, tsaye tay ta had'e hannuwanta tana kallon shi da murmushi shi ma idon shi na kanta yana bin ta da wani kallo da sai kace yar harararta yake amman ta fahimci wani lokacin haka yake kallon shi, ganin tayi mashi kerere yasa ya furta mata bata iya neman wuri ta zauna, kujerar dake gefen tashi ta nufa ta zauna,

"Aunty tana zuwa yanzu" bayan d'an wani lokaci ta fad'a ya jinjina mata kai,

"Ka zo lafiya" ta tambaya still Murmushi take yay shiru sai kuma ya amsa mata da lafiya, janye idon shi yay daga kan ta ya jinginar da shi ajikin kujerar tare da lumshe ido, tana ta kallon shi can ta furta ya gaji ne yana a yadda yake ya d'an girgiza mata kai, juyar da kai tayi daga barin kallon shi a ranta tana raya magana dashi aiki ce babba, lokacin Aunty ta fito ta nufo cikin parlon tana sanye da doguwar rigar had'addan lace ta sa d'an kunnan zinari hannunta sanye da Agogo haka kanta tayi d'aurin kallabi mai kyau, tun kafin ta k'araso ta shiga washe baki idon ta akan Sameer da ya lumshe ido, saida tayi sallama sannan slowly ya bud'e idon nashi, a kujerar gefen wadda Fauzy take ta zauna tana faffad'an murmushi tace "Barka da zuwa, fatan an zo lafiya" amsa mata yay da lafiya lou ya janye idon shi daga kanta, k'ara tambayar ya ya baro Mutanen gida tayi ya amsa da lafiya ba tare daya k'ara kallon ta ba, shiru duk sukai tana murmushi idon ta akan shi can ta k'ara cewa "an gode da abubuwan Alkhairi Allah ubangiji ya k'ara girma da daukaka" slowly ya furta "Ameen" ta d'an kalli Fauzy dake d'an murmushi itama shine akan fuskar tata, shiru duk sukai parlon sai kace ba mutane Aunty Mareeya sai d'an kai idon ta take tana kallon shi acikin ranta ta shiga tuno da ranar data fara ganin shi da suka zo Abuja bata ta6a zaton akwai ranar da zasu zauna haka da shi bama balle ta kai ga zancen Auren k'anwarta, mik'ewa tay tayi ma Fauzy alamar ta biyo ta da hannu ta mik'e saida ta kalleshi tace mashi tana zuwa ya d'aga mata kai, wurin dining suka nufa Aunty ta nuna mata kayan abinci dake sama k'asa k'asa da murya tace "gashi nan sai ki mashi magana yazo ki serving nashi" kai Fauzy ta d'aga idon ta akan jigunannun Warmers d'in da aka jera a saman table d'in set biyu babba da k'arama set d'aya na Aunty ne ta san su d'ayan kuma sam bata san Aunty dasu ba a ranta ta raya k'ilan duk na chef d'inne amman sun had'u ba k'arya, bubbud'e mata su ta shiga yi babba d'aya farar shinkafa ce washarr washar gata zak'o zak'o sai k'aramar warmer d'inta tana bud'e ta wani irin kamshi mai dadi ne ya karad'e wurin vegetable soup ce gwanin kyau a ido ingredients d'inta an yanka su manya manya taji hanta, d'ayar babbar Warmer d'in kuma fried spaghetti ce tayi brown gwanin burgewa itama sai faman zuba k'amshin spices take gashi tasha vegetables su tsanwan tattasai Karas koran wake da dai sauran su gashi tasha nama ca6a ca6a, d'ayar warmer d'in ta k'arshe kuma pepper chicken ne ciki, bayan ta gama bubbud'a mata tace mata akwae coleslaw a cikin Fridge,

"Amman Aunty duka order d'in nasu kikai?" Fauzy ta tambaya k'asa k'asa,

"eh mana daga lokacin da kika fad'i man zai zo zuwa yanzu ina zan iya yin wani lafiyayyen Abinci har gara ma spaghetti za'a iya yi amman kuma ba komai nike da shi ba na kayan had'ata tayi kyau haka, kai Fauzy ta jinjina tace hakane, "amman ai sun yi haka ko?" da sauri Fauzy tace "ah sosae ma kin yi mana dubara naji dad'i wllh" yar dariya Aunty tay tace "jin dad'in ki your excellency shine nawa" hannu Fauzy ta kai ta gumtse dariya,

"Yanzu kije ki mashi magana yazo ya ci" kai Fauzy ta d'aga sai kuma tace "Allah ma yasa ba wahalar banza akai ba ta tanadar su don yana iya k'in ci wllh" da sauri Aunty Mareeya tace "in ya ki ci ai ke zaki sashi dole yaci ko, taya zai tako yazo kuma yace bazai ci komai ba ke kuma ki bishi da ido, anya Fauziyya, gaba d'aya wani lokacin sai ki kaman ba wayyaya ba wllh na lura kaman baki iya soyayya ba ko dai kin k'arar da ita a wurin shashasha d'in can, kije ki mashi magana in ya nuna bazai ci ba kice baki yarda ba sai ya ci a cikin sigar yar shagwaba shagwaba zaki mashi magana dole fa sai kin zage damtse wllh ke ce zaki koya mashi sakin jiki da mutane bama kamar ke in ba haka ba yana a haka d'in can wllh kece Masha wuya ki ga fa yadda magana ke mashi mugun wahala ga ba sakin fuska don ma dai d'aurewar na mashi kyau tunda kyakkyawan ne....kinga an bar shi shi kad'ai jeki ki mashi magana bari in d'aukko coleslaw d'in akwai ma lemuna a cikin Fridge d'in sai ki tambayi wanda yake so in kuma sai giyar da kika ce yana sha sai kije ki nemo mashi" gwalo ido Fauzy tay jin Maganar tata ta k'arshe Auntyn ta sa dariya ta juya tana fad'in taje, komawa tayi cikin parlon Sameer d'in nata latsa waya har zata zauna a inda ta tashi sai kuma ta tuna da hud'ubar Aunty a d'arare ta nufi inda yake a hankali ta zauna daga gefen shi, idonta akan shi tace "am sorry an bar ka kai kadai naje yin abu ne" kai ya jinjina mata ba tare daya kalleta ba,

"Muje ka ci Abinci" d'an jimm yay kafin ya juyo suka had'a ido tana mashi murmushi, kokarin mik'ewa ta fara taji yace mata ya k'oshi hakan yasa ta koma ta zauna,

"Amman ya zaka ce ka k'oshi bayan nan kazo dole ai kaji yunwa" d'an girgiza mata kai yay yace ba nan ya fara zuwa ba so ya ci Abinci a inda ya sauka, tambayar shi tay a ina ya sauka ya bata amsa da Government House, marairaice mashi fuska tay tace "to amman dai ai nan ma yakamata kaci Abinci tunda nasan Saboda n...." Kasa k'arasa Maganar tay idon shi a kanta slowly yace yana jin ta alamar taci gaba, kikkafta idanu ta shiga yi tana motsa baki ganin irin kallon da yake mata ne yasa da k'yar ta furta "Saboda ni ka zo" kawai sai gani tay yay d'an murmushin gefe wanda tunda yazo bai yi kamar shi ba don har gefen fuskar tashi ya d'an lotsa, d'age mata gira yay yace "Who told you dat?" shiru tay tana cigaba da kikkafta ido taji ya sake cewa ba tambayar ta yayi ba,

"Ba kowa, ni nayi tunanin hakan" shiru yay yana kallon ta cikin k'arfin hali ta furta "hakane?" wani kalan motsa baki yay tare da yi mata wani kallo yace in ta cancanci hakan to hakane, faffad'an murmushi tayi tace "eh nayi deserving hakan" d'an ta6e baki yay da alamun murmushi yace a matsayinta na wa ba tare da jin wani d'ar ba ta furta "Your wife to be in sha Allah" bin ta yay kawai da ido sai murmushi take tana niyyar k'ara yin magana Mijin Aunty Mareeya ya sawo kai cikin parlon da sallama su Hanif na biye da shi gaba d'aya suka kai idon su akan shi ganin shine yasa Fauzy saurin sauke kanta don sai taji kunyar zamanta a kujera d'aya da Sameer ta kamata, inda suke ya nufo yana zuwa gaban Sameer cikin sakin fuska ya bashi hannu suka gaisa yayi mashi an zo lafiya nan ma ya amsa mashi, d'an rankwafawa Hanif yayi yace mashi ina wuni ganin haka yasa su sultan ma suka yi duk ya amsa masu fuskar shi a d'an sake, juyawa Abban Hanif yay bayan sun gama gaisawar ya nufi hanyar Bedroom su Hanif na biye dashi gaba d'ayan su Uniform ne ajikinsu sun goya School bag da gani daga Makaranta ya d'aukko su ,

"Pls muje kaci Abincin" Fauzy ta fad'a da yar sigar shagwaba idon shi akanta yay shiru, mikewa tayi tana mashi wani kallo a kokarin ta na tayi abunda Aunty tace, shiru ya d'an yi kafin yace shi bai cin Abinci in ya riga ya koshi ya fad'a mata ya riga ya ci so ba sai yaci wannan ba, tsaye tayi tana kallon shi bayan ya gama yin Maganar shima kallon nata yake can ta nufi kujerar gefen shi ta zauna ta maida fuskarta tana kallon gefe,

"Are u angry?" tana haka taji ya jefo mata tambayar, juyowa tayi suka had'a ido tay shiru bata bashi amsa ba, "I'm asking you!" Ya sake fad'a, saida ta d'an had'iya miyau kafin a sanyaye tace "a'a kawai dai naji ba dad'i ne, saboda ni kazo kuma gashi kace bazaka ci Abinci bana at least ko d'an Yaya ne sai ka ci pls" d'an murmushi yay bai ce komai ba tana ta kallon shi can taji yace Ok zai ci sai taji dad'i, washe baki tay tana yar dariya sosae taji dad'in cewa da yayi zai ci don ko ba komai hakan ya nuna zata iya sashi abu, mik'ewa tayi tace suje ya taso shima ya mik'e, bayan sunje dining area d'in da kanta taja mashi kujera ya zauna, fara serving nashi tay ta zuba mashi farar shinkafar da veg soup d'in bata sa da yawa ba don tana son sauran ma yaci, a nutse ya fara ci tana zaune daga gefen shi can ya kalleta yace ita bazata ci ba tace sai ta gama Serving nashi, da kai yay mata alamar ta zauna ta ci murmushi tayi ta mik'e don ta zuba, yana kusa gama cinye shinkafar ya aje spoon d'in tana ganin haka tay saurin mikewa ta fara zuba mashi taliyar itama yar kad'an tasa ta janye plate d'in gaban shi ta tura mashi na taliyar ganin haka yasa shi d'agowa yana mata wani kallo cikin marairaicewa ta d'an langa6ar da kai tace "pls shima bai da yawa ai" cigaba da kallon ta yay yana d'an motsa baki kokarin mikewa ya fara yana fad'in bai san a ina take son ya zuba shi ba wannan ma ya gaya mata ai a k'oshe yake kawai sai ji yay ta kawo hannu ta ruk'e nashi alamar kar ya tashi ita kanta bata san ya akai ta aikata hakan ba, dakatawa yay ya kai idon shi akan farin hannunta dake a ruk'e da nashi kafin ya d'ago ya kalleta sai d'an zare ido take gabanta na faduwa, a hankali ta saki hannun nashi tare da sadda kanta k'asa bayan d'an lokaci jin shiru yasa ta d'an d'ago idanunta ta kalle shi karaf suka had'a ido yana ta kallon ta yan kame kame ta shiga yi ta kasa tsaida idon ta cikin nashi don idanun shi nada kaifi bazata juri irin kallon ba,

"Ka yi hak'uri, dama don Saboda kai ne akayi shiyasa" tana d'an kikkafta idanu ta fad'i hakan, bai ce komai ba sai gani tay ya kai hannu ya d'auki fork d'in ciki ya fara ci a nutse har bata san lokacin data saki murmushi ba ta koma ta zauna, kaman rabin wanda ta zuba mashi yaci tana ganin ya aje fork ta d'ago ya d'age mata gira yace Shikenan hakan yayi mata ya ci kai ta d'aga mashi still da d'an murmushi sai kuma tace amman da sauran wanda bai ci ba wani kallo mai kaman harara ya wurga mata tayi dariya tare da mik'ewa, pepper chicken d'in ta bud'e tasa mashi k'atuwar cinya hada tambayar shi ta k'ara yay mata shiru yana dai ta kallon ikon Allah don hakan bak'on abu ne a wurin shi yace bazai yi abu ba a matsa mashi zai iya cewa ba wanda ya ta6a mashi haka, turo plate d'in tayi gaban shi bayan ta janye na taliyar tace gashi itama ya ci don Allah ba yawa abu d'aya ne kawai, maida bayan shi yay jikin kujerar da yake zaune ba alamar zai ci sosae ta marairaice fuska tana mashi yar shagwabar ya ci daga shi shikenan, k'arshe dai saida tayi nasarar saka shi yaci cinyar rabi da kan shi ya tsiyaya ruwa a cup yasha kad'an yana k'ok'arin mik'ewa tace lemu fa ya d'an d'aga mata hannu, ganin ya tashi yasa itama ta rufe sauran abinciccikan ta biyo bayan shi, kujerar daya tashi ya koma ya zauna itama ta sake zama a gefen shi, bata dad'e da zama ba taji yace ita bata wanka ne har saida taji yar kunya tana d'an murmushi tace tana yin wanka sosae don kada ta barshi shi kad'ai ne yasa bata je ta yi ba, shiru ya d'an yi sai kuma taji yace taje tayi zasu je government House tare, har saida gaban Fauzy ya d'an fadi jin inda yace zasu je amman bata nuna komai ba tace mashi to,

"Amman lafiya lou a barka kai kad'ai ko in ma Auntynah magana?" ta fad'a bayan ta mik'e da bud'ar bakin shi sai cewa yay tayi mashi mi tace wai ko ta taya shi hira, d'an yamutsa fuska yay ya fara k'ok'arin mik'ewa bayan ya tashi tsaye yace zai jira ta a Mota amman kar tay keeping nashi bai hakurin haka ta d'aga mashi kai ya nufi hanyar fita daga parlon tabi bayan shi da ido har ya fuce, wani k'ayataccen murmushi ta saki tana jin son shi na ratsa mata zuciya tabbas tasan indai ta aure shi ba k'aramar mai sa'a bace ita, da sauri ta nufi hanyar Bedroom d'inta tana zuwa direct toilet ta nufa a can ta cire Uniform d'in jikinta, after some few minutes ta fito d'aure da towel a kirji ta nufi gaban dressing mirror, shaf shaf ta d'an yi yar light makeup bayan ta gama ta nufi wurin kayanta dake a cikin Wardrobe d'in bango, bata tsaya ruwan ido ba ta yanke ta saka jallabiyar da Fatuu ta bata dama sau d'aya ta ta6a saka ta da zasu je shopping dasu Hanif, bayan ta saka gaban mirror ta koma cikin sauri ta gyara fakin din gashinta sannan ta shiga nad'a gyalen rigar, sosae tayi mata kyau dama itama tasan tana mata kyaun shiyasa ta saka ta, takalma half cover da yar karamar side bag duk bak'ak'e ta saka saida ta gama shiryawa ta tuna bata fad'i ma Aunty zancen fitar ba, wayarta ta fiddo don ta kirata sanin Abban Hanif na nan, a cikin parlor suka had'e da ita bayan ta sanar mata ta waya tana ganinta ta hau yin murmushi tana fad'in kaga Matar d'an Governor, tambayar ta tayi amman dai yaci Abincin ko tace eh kowanne saida tasa ya ci duk da bada yawa ya ci ba Auntyn tace "yayi kyau hakan ma lafiya lou tunda dai ya ci kwalliya ta biya kudin sabulu, yanzu sai government House kenan your excellency?" Yar dariya Fauzy tay tace mata eh haka yace tace Ok sai sun dawo, saida ta rakota har bakin kopar parlon tana k'ara koya mata yadda zata rink'a mashi tace ta gaida mata da iyalan Governor, yana a d'an kishingid'e idanunshi a lumshe ta shigo cikin Motar bayan driver ya bud'e mata, slowly ya bud'e idon nashi ya sauke su akanta da murmushi tayi mashi sannu tace Allah yasa dai bata bar shi yana ta jira ba shiru kaman bazai tanka mata ba can ya d'an gyara zama yace kaman haka, saida driver d'in ya tambayi umarni kafin yaja Motar, suna cikin tafiyar idon Fauzy a gefe ba zato taji ya kawo hannu ya kamo nata hannun wani irin d'umi taji ya ratsa nata hannun taushin hannun shi kuwa ba sai an fad'a ba, kallon shi tay idanun shi na akanta da kai yay mata alama ta matso, shiru tay kaman bazata matsa ba sai kuma ta d'an matsa da kanshi ya k'ara matso da ita ya rungumeta ta gefe wani iri Fauzy ta ji don tasan hakan bai dace ba tunda ba d'aura masu aure akai ba bai kamata suna had'a jiki ba, shiru tay kanta na a saman kafad'ar shi haka hannunta guda daya fara ruk'owa har lokacin yana a ruk'e dashi tay lamo ta kasa yin wani yunk'uri na raba jikinta da nashi, bayan sun isa Government House d'in baza ido Fauzy tay tana k'are ma ko ina kallo ta yadda baza'a ga k'auyancin ta ba, lokacin data ganta gata ga first lady wadda k'awar Mom d'in Sameer ce mamaki da dad'i ne suka cikata don abu ne da bata taba zaton zai faru ba a rayuwar ta, cikin faram faram ta tarbeta bayan sun gama gaisawa fuska a sake ta d'an yi mata tambayoyi da suka shafeta Fauzyn na amsa mata Sameer na zaune akan d'aya daga cikin lafiyayyun kujerun da suke zaune daga baya ya mik'e ya nufi ciki Fauzyn na kallon shi har ya 6ace ma ganinta tayin Abinci First Lady tayi mata tace gashi can a table tana murmushi tace mata wllh a koshe take ta gyad'a kai, d'akin yaranta ta kai Fauzyn wai tafi sakewa yan mata biyu ne ta gani a d'akin d'aya zata yi sa'ar ta d'ayar kuma zata d'an girme ta, gaba d'ayan su daka kallesu zaka gane hutu ya zauna masu a jikinsu ga fatar su har wani shek'i take duk da ba farare bane can amman kuma baza'a kira su da bak'ak'e ba gaba d'aya k'ananun kaya ne a jikin su, sosae suka sake ma Fauzy babbar na d'an tambayar ta game da ita da yadda suka had'u da Sameer muryarta gwanin dad'i a gayance take magana, tun dai Fauzy bata saki jiki ba har ta saki suka shiga yin hira sosae anan ita babbar take ce mata gaskiya tayi dacen miji don Sameer k'arshe ne a komai amman ita bazata iya auren shi ba har saida Fauzy ta d'an ji mamaki ta kasa hak'uri ta tambayi dalili cikin yamutsa fuska Ammah tace mata ego d'in shi yayi mata yawa dole matar shi ba k'aramar dawainiya zatayi da shi ba ita kuma hakan ke bata iyawa, shiru Fauzy tayi tana d'an murmushi tasan ba k'arya tayi ba a ranta ta raya to dama Mulki ya had'u da Mulki taya d'aya zai dawainiya da d'aya.

Bayan gama sallar la'asar Sameer ya kirata yace ta same shi a parlor, tare da Ammah suka fito har yayi wanka ya canza kaya zuwa k'ananu sai baza k'amshi yake, Ammah na murmushi tace ma Sameer d'in "sannu bro" kai ya d'aga mata fuskar shi a d'an sake ta k'ara cewa ba dai tafiya zasu yi ba sai lokacin ya bud'a baki yace eh amman zata gaisa da Dad ne hakan yasa tace to suje ta raka su, parlon shi suka nufa lokacin da suka shiga yana zaune tare da First Lady da murmushi ya nuna ma Fauzy wuri yace "have a sit my Daughter" jikin Fauzy har wani tsuma yake yau itace gata ga Governor wanda saidai taga motocin su suna wucewa a hanya da jiniya sai kuma a Tv, cike da girmamawa ta gaishe da shi ya amsa ya tambayi tana lafiya da yan gidan su duk ta amsa mashi, shima dai yan tambayoyi yayi mata yadda bata 6oye ma su First Lady komai ba haka shima ta rink'a bashi amsa yana d'an jinjina kai daga baya ya saka mata Albarka da kuma fatan Allah ya nuna masu bikin, tare suka fito harda First Lady Sameer yace zai je ya dawo tace Ok su d'an jirata a parlon ta, kiran Ammah tayi tabi bayanta bada jimawa ba sosae ta dawo hannunta ruk'e da jakar kwali sai walwali take ta mik'a ma Fauzy tace gashi in ji Mom tana murmushi ta amsa tare da yin godiya sosae tace tayi mata godiya pls, har zasu tafi tace ta bata digit d'in ta zasu rink'a gaisawa Fauzyn tace to, bayan ta amsa sukai sallama ta juya ta nufi part d'in su, sosae Fauzy ta jinjina kirkin su sam basu da ji da kai har gara ma k'anwar tata itama ta fahimci bata da yawan magana ne ba wai ji da kai ba, Motar da suka zo ita suka hau saidai yanzu Sameer d'in ne zai tuk'a ta ba driver ba, bayan sun hau hanya ne taji yace tay leading nashi gidan Haisam tace to, ita ke nuna mashi hanya tana cikin haka ta tambayi bai ta6a zuwa bane farko shiru ya d'an yi idon shi akan hanya ta juya ta kalle shi suka had'a ido ta cikin mirror kafin ya kauda lokacin ya bata amsa da sau biyu ya ta6a zuwa Katsina Saboda baida business a cikinta d'an murmushi tay kawai sai kuma ta k'ara cewa amman ai ga grandmother d'in Ya Haisam a garin ya d'an d'age gira ba tare da ya kalleta ba ya bata amsa da ai shine dalilin da yasa yazo sau biyun ko. Lokacin da suka isa gidan Hajiya Fatuu na a part d'in sosae tayi farinciki ganin su tare ji take tamkar ta zuba ruwa a k'asa tasha ganin burin su dai ya tabbata, sosae Hajiya taji dad'in zuwan nashi bayan sun gaisa ta tambayi yan gidan su ya amsa mata daga baya tace wato da ya manta da ita tunda yaushe rabon da ya zo gidan tun suna karatun degree d'in su na farko da suka zo da Haisam sai yanzu dalilin zai mata kishiya ta samu ya sake ziyartar ta, murmushi yay jin abunda tace ba tare daya ce komai ba, koda tayi mashi Maganar Abinci cewa yayi ya k'oshi Hajiyar tace dama tunda Amarya ta cika shi da kayan dad'i ya zai iya cin Abincin tsohuwar mata duk suka d'an yi murmushi harda shi, kiran sallar Magrib da aka fara yasa shi mik'ewa don yaje Masallaci suma duk suka tashi don suje su yi, visitor room wanda yanzu ya koma kamar d'akin Fatun anan take komai taja Fauzy, bayan sun gama sallar cikin washe baki Fatuu ta shiga nuna ma Fauzy irin farincikin da ta ji nan ta shiga bata labarin yadda yasa ta kwaso kayanta daga hostel Fatun nata dariya tana fad'in yayi daidai, harda yadda suka samu Abincin da suka tarbe shi ta fad'i mata tace amman dai Aunty tayi dubara sosae daga baya Fauzy ta koma magana akan cikinta tana fad'in wllh tausayi take bata Fatun na yar dariya tace ai yana gab da zuwa kanta lokacin ita ta sauke sai itama ta rink'a tausaya mata ta d'an ta6e baki can kuma tace "waya ga su Fauzy da ciki alankoso kenan, ai na tabbatar sai kin fini juriya Zarah" Fatuu na dariya tace itama dole zata koyi juriyar in lokacin yayi, anan Mino ta iske Fauzy suka gaisa harda tambayar ta Angonta Nameer tana murmushi tace mata yana Makaranta, anan sukai sallar isha bayan Sameer ya dawo daga Masallaci ya kira Fauzy yace ko zai barta anan ne tace mashi a'a yace Ok ta fito yana parlor, tare suka fito su ukku Fatuu tace bari tay ma Hajiya Magana, bada jimawa ba suka shigo cikin parlon bayan sun zauna Hajiya tace wato dai tafiya zai yi bazai ci Abincin ta ba yana d'an murmushi yace wani lokacin zai ci ta gyad'a kai tace to Allah yasa tana da rabon ganin lokacin don bata sa ran nan kusa ba shi dai d'an murmushi kawai yake, su Fatuu ne suka yo mata rakiya suna zuwa bakin entrance tace mata ta koma ta girgiza mata kai tana murmushi tace suje ta raka ta ai duk cikin exercise ne, bayan sun fito cikin harabar Sameer na daga gaban su a nutse yake tafiya duk idanun su na akan shi k'asa da murya Fatuu tace wllh ganin Sameer yasa taji maraicin mijinta duk suka d'an yi dariya, bud'e Motar yayi ya shiga bayan ya k'arasa inda take suma suka karaso Fauzy tayi masu sallama tace ma Fatuu sai sun had'u School gobe, tana shiga cikin Motar ya bata rafar kud'i guda ukku yace ta ba Fatuu ta kai ma Hajiya ya k'ara bata wasu guda biyu yace ta ba Fatuu, fitowa tay har sun nufi komawa ciki ta tsaida su taje ta bata kudin, saida suka dawo tayi mashi godiya sannan suka tafi Fauzy ta shiga yaja suka tafi. Bayan sun baro gidan gari suka shiga yana driving da hannu d'aya yana latsa wayar shi da d'ayan hannun can taji ya furta Katsina K'aramin gari ne ba wurare masu kyau da mutum zai je yay having fun, ita dai shiru tayi mashi a ranta ta raya tunda dama ya saba zuwa had'add'un wurare harda su club ai dole ya fad'i haka, sai daga baya ta fahimci wayar da take latsawa yana searching wurare ne, bayan wani lokaci suka k'araso wani babban wuri kamar dai Eatery ne Kusan shine wurin cin Abinci daya fi kowanne girma da kawatuwa a garin Fauzy tasan wurin sai dae bata ta6a zuwa ba Saboda ba'a dad'e da bud'e shi ba yan Makarantar su dai na zuwa da samarin su, bayan ya parker jingina yay da kujerar ita dai Fauzy nata kallon wurin, bada jimawa ba wasu ma'aikatan wurin guda biyu suka fito hannuwan su ruk'e da ledoji suka nufo wurin parking d'in, horn Sameer d'in ya latsa hakan yasa suka nufo Motar tasu suka tsaya daga bakin kopar driver d'in slowly glass d'in ya d'an sauka ma'aikatan suka gaishe shi tare da yi mashi barka da zuwa yadda ya amsa ba lalle ma in sun ji ba yace masu su saka a seat d'in baya, bayan sun saka d'aya ya dawo gaban yace mashi ansa ya jinjina mashi kai har zai juya ya dakatar da shi, kud'i ya mik'a mashi masu yawa nan take ya hau washe baki yana godiya don ya gane kyauta ce yayi masu Saboda ya biya kud'in abubuwan da ya siya ta online d'ayan ma ya matso yayi godiyar, bayan barowar su wurin direct gida ya nufa da ita yace ta rink'a nuna mashi hanya da zata maida su tace to, a k'opar gidan ya parker bayan sun k'araso ta juya tana kallon shi, shiru sukai na d'an wani lokaci can taji yace mata gobe zai wuce in akwae wani abu ta fad'i mashi, shiru ta d'an yi kafin tace da wuri haka kaman bazai bata amsa ba yace to wani abu zai tsaya yi tay shiru kawai,

"You can go, zamu yi magana" ya fad'a tare da yi mata nuni da baya yace ta d'auki abubuwan da aka je, d'an jimm tay akwae Maganar da take son yi mashi amman tana jin shakkar yinta saidai tana ganin yakamata tayi mashi ita, kaman ya lura da tana son yin magana yace mata inda wani abu yana jin ta, saida ta tattaro karfin hali sannan murya na d'an rawa ta fara magana,

"D...dama akwae abunda nike son tambayar ka ne.....Ina so ka fahimce ni don Allah...." shiru tay tana jiran taji mi zai ce idonta akan shi taji yace yana sauraron ta, ci gaba tayi "dama akan aurena da zaka yi ne, nasan ba wani abu a tsakanin mu sai kawai naji Maganar aure kuma bacin bamu ta6a haka da kai ba...to shine nike son in tambaye ka miyasa zaka Aure ni tunda baka ta6a nuna kana...so na ba" da k'yar ta k'arasa Maganar da in ina tare da d'an nishi duk a lokaci guda, maida idon shi yay ya koma kallon gaban shi ta kafe shi da ido tana son gane yanayin fuskar shi da yake akwae haske sosae a layin ya d'an haska cikin Motar, sun d'an d'auki lokaci kafin taji ya furta "why did you ask me that?" Yay tambayar tare da Kallon ta, abu ta had'iya a Sanyaye tace "kawai hakanan ne inason in sani Saboda nayi mamakin hakan" tana rufe baki yace bata yarda dashi ba kenan da sauri tace "a'a wllh...kawai dai kai ne ka ta6a ce man kar in rink'a bada yarda gaba d'aya to shiyasa nike son in ji dalilin da yasa kake son aure na" kauda idon shi yay daga barin kallon ta sannan ya furta shima bai sani ba hakanan zai aure ta, tsit kake ji wani iri Fauzy take ji a cikin ranta hakan da ya fad'a, kallon ta yay daidai lokacin itama ta d'ago ido ta kalle shi calmly ya ce in tana ganin hakan bai mata ba lokaci bai k'ure ba za'a iya fasawa ai, tun kafin ya rufe baki k'irjinta ya hau bugun uku uku hannunta ya fara d'an rawa, kafeta yay da ido alamar amsarta yake jira ta fara motsa baki da k'yar cikin rashin dad'in rai ta furta "Shikenan, in hakan yayi maka nima yayi man" tana k'arasa Maganar da sauri ta sunkuyar da kanta jin k'walla sun fara tarun mata a cikin idanunta sam ba haka ta so taji daga gare shi ba a ranta ta raya Mujaheed yayi tarayya da ita don tana burgeshi shi k'ilan ma tasan koma burge shi d'in bata yi, kallon shi tay bayan tayi kokarin maida kwallar ta d'an k'ak'alo murmushi tace "Nagode Allah ya saka da Alkhairi Allah kuma ya maida ka lafiya" jinjina mata kai yayi tace mashi saida safe bin ta da ido kawai yay ya d'an yi jimm can ta juya ta kai hannu zata bud'e kopar..,

"I will marry u because....i love you Fauziyyah" kaman saukan aradu haka taji Maganar ta sauka akanta, da sauri ta juyo tana kallon shi idon shi na akanta amman sai ka rantse ba shi yay Maganar ba don Kalmar k'arshe daya furta kalma ce mai matuk'ar tsada a wurin shi in ba Mom d'in shi ba ba wadda ya ta6a fad'i ma hakan duk da uban matan dake rok'on shi kan ya furta masu hakan, d'an murmushi tay ta fara motsa baki cikin yar in ina tace "are you telling the truth?" wani irin lumshe ido yay duk da acikin duhu ne ta gani ta d'an hasken cikin Motar, dad'i ne ya kama Fauzy har bata san lokacin data ce mashi don Allah ba don taji dad'i ya fad'i hakan ba, d'an ta6e baki yay yace dama mutum na auren wanda baya so ne, murmushi kawai Fauzy ke saki tace mashi ta gode in sha Allahu zata zame mashi mata ta gari wadda zata bashi Farin ciki na har abada tana ganin d'an murmushin gefen da yayi, sai faman k'ayataccen murmushi take gaba d'aya dad'i ya cikata don abunda take fata ne ya kasance yana son ta, ce mata yayi taje sai sunyi magana tace to, har zata juya taji yace haka yakamata su rabu dakatawa tayi ta maido idonta kan shi ko da bai fito ya fad'i ba ta gane yadda yake nufin yakamata su yi bankwana, shiru tayi a cikin ranta tana raya gaskiya bai kamata tana biye mashi ba tunda hakan ba kyau kuma in dai tana son ta hana shi hakan dole ta fara ta kan su, cikin yar rawar murya tace "k...kayi hak'uri naga bamu kai ga yin aure bane ina tsoron mu samu zunubi....kuma hakan na iya shafar rayuwar Auren mu don naji anata wa'azi akan hakan" shiru yay still idanun shi na akan ta sai kame kame take can taji yace ta tafi wani iri taji sai taga kaman yayi fushi ne zata so ace tayi mashi abunda zai faranta mashi ba kamar da shima yanzu yay mata abunda ya saka ta farinciki amman tasan hakan shi yafi masu Alkhairi, a sanyaye ta furta mashi "Gud nyt" kai ya d'an jinjina mata kafin yace karta manta da abun baya daga yadda ya furta Maganar bazata iya gane yanayin da yake ciki ba. Lokacin data shiga cikin gidan a parlor ta iske Aunty Mareeya da su Hanif tana yi masu Assignment, da sallama ta shiga suka taso da gudu suna mata oyoyo, amsar ledojin suka yi ta dafa Shoulder d'in iman suka nufi cikin parlon idon Aunty a kan su tana ta washe baki, a kusa da ita ta zauna tace "yan tafiya an dawo?" Fauzyn ta d'aga mata kai,

"Amman wai tun da kuka fitan kuna government House d'in?" Kai ta d'an girgiza mata ta fad'i mata duk inda suka je, tambayar ina Sameer d'in tayi tace ya tafi kafin ta d'aga kai, hannu Aunty ta kai ta d'aukko jakar kwalin da ta ja hankalinta tace miye aciki Fauzy tace bata sani ba First Lady ce ta bata, bud'e ta Aunty tayi ta kai hannu ta fara fiddo abubuwan ciki, turare na guda ukku iya kwalin su abun kallo ne sai miski a yar babbar kwalba mai kyau tun ba'a fiddo turarurrukan daga cikin kwalin su ba har k'amshin su mai dad'i ya karad'e wurin, sosae Aunty ta yaba bayan ta maida su cikin jakar ta tambayi yadda suka kar6eta ta fad'i mata hakan ma taji dad'i sosae harda 6akar Fauzy a kafad'a tana fad'in ta dai zama dangin gwabnoni ita dai yar dariya tayi, tambayarta yadda Fatuu take ta k'ara yi tace halan tana nan tana ta ja tace mata eh, kallon ledojin tayi da yake akwae tambarin wurin da aka siyo kayan ciki tana dariya tace daga ziyarar chilling kenan suka wuce still Fauzy murmushi kawai tayi, fara janyo ledojin tayi su Hanif na Mik'o mata sauran ta shiga bubbud'a su, tarkacen su ice cream ne flavour daban daban dasu yoghurt sai su shawarma da pizza abubuwa dai kala kala kili guda tana cikin dubawa tace "ashe su suriki na ba iya kud'i aka iya badawa ba" tambayar Fauzy tayi cikin wurin suka shiga aka siyo tace a'a ta fad'i mata kawo masu akai tace ai dama ta d'an ji mamakin ace shiga sukai dashi aka siya, Hanif ne ya d'auki ice cream yace ma Aunty ya sha tace na Aunty Excellency ne ya tambayeta Fauzy ta d'an yamutsa fuska tace "kai Aunty don Allah" tana dariya tace tuba take, babbasu komai tayi kowa ya natsu suka fara ci itama ta d'auki shawarma tana ci, kallon Fauzy data jingina da kujera tayi shiru Aunty tayi tace "wai lafiya Fauziyya, na lura kamar akwai abunda ke damun ki tun bayan da kika shigo kin k'i sakin jiki sosae" d'an ta6e baki Fauzy tay ta furta "uhmm" dakatawa Aunty tayi da cin abun da take gaba d'aya ta maida hankalin ta kanta tace mata ya akai ne, ajiyar zuciya tayi ta fara motsa baki kafin ta shiga bata labarin yadda sukai da Sameer na tambayar da tayi mashi kan dalilin daya sa zai aure ta da amsar daya bata har zuwa yadda suka rabu,

"Ni Aunty ina ganin kaman yayi fushi" shiru Aunty ta d'an yi can tayi yar ajiyar zuciya ta dafa Shoulder d'inta tace "ba lalle ba, in dai da gaske yana da ilimin Addini to bazai ji komai ba tunda yasan gaskiya kika fad'i sai ma dai yaji dad'in hakan tunda ya gane wace kalar mata zai aura, kuma fa tana iya yuwuwa ma gwada ki yake kinsan Mutane in suna abunda suka san ba daidai ba to basu son su Auri mace mai hakan don haka karma ki wani damu wllh" kai kawai Fauzy ta jinjina amman ita tasan ba wani gwadata da yayi Saboda abubuwan da yayi mata, daga baya sakin jiki tayi suka cigaba da cin abubuwan anan Aunty ta ce yakamata ta sa yazo yayi breakfast gobe Fauzyn tace anya zai zo don yace gobe zai tafi amman dai zatayi mashi magana. Bayan ta koma d'aki a bakin gado ta zauna ta shiga tunanin ko ta kira shi saidai tana jin d'ar d'ar can dai tay k'arfin halin kiran nashi, har ta yanke bai d'auka ba ta ruk'e wayar tana dakon kiran shi kamar yadda suka saba bada jimawa ba kuwa sai gashi ya kira d'in har saida tayi murmushi taji d'an sanyi a ranta, bayan ya d'auka ya ya koma tayi mashi ya amsa mata daga haka suka yi shiru can taji yace da wani abu tace mashi eh dama Aunty d'in ta ce tace tayi mashi magana yazo da safe don Allah yayi breakfast, ce mata yay bazai samu zuwa ba don Flight d'in safe zai bi tace to tayi mashi saida safe itama yayi mata, bin wayar tayi da kallo tama rasa tunanin da zata yi jikinta ya d'an yi sanyi can dai ta mik'e don tayi shirin kwanciya...........

93

_ASM BY ZAINAB BATURE _

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

.......Washe gari bayan Fauzy taje School Zainab nata son yi mata magana sai dai bata samu damar hakan ba don tana zuwa malamin su ya shigo, saida akayi break sannan tazo seat d'in su da yake yanzu basu fita break Saboda nauyin da Fatuu tayi ita ke zuwa masu da Abinci to yau itama Fauzy tazo masu da shi, zama Zainab d'in tayi a saman desk suna cikin cin Abinci ta fara jero mata tambayoyin yadda akai suka san juna da Sameer shida ko kallon mutane ba yayi, sosae ta rink'a basu dariya yarda ta hak'ik'ance tana fad'in an cuceta, har aka dawo break bata k'yale su ba k'arshe tare dasu tayi break d'in, Fauzy nata so taba Fatuu turaren data kawo mata cikin wanda aka bata amman Saboda Zainab d'in ta k'i fiddo shi don tasan tabbas sai tace a bata shi kuma ita Fatun take son tayi amfani da shi, saida aka tashi sannan ta bata, tare Tk ya d'aukesu saida aka aje Fauzy gida har Fatuu ta shiga tayo fitsari sannan ta fito Fauzy ta rakota suka tafi. Bayan sallar Juma'a wuraren k'arfe ukku na rana Fauzy tayi wanka tayi kwalliyar Juma'a lokacin tuni sunyi waya da Sameer har ya koma, tana zaune a cikin d'akinta tana chat wayarta ta fara yin ringing, bin bak'uwar lambar da aka kira tayi da kallo kafin ta d'auka a nutse tayi sallama, bayan mai kiran ya amsa cikin girmamawa ya gaishe da ita da alamun mamaki akan fuskar ta ta amsa yace dama sak'o ne ya kawo mata yana waje, d'an jimm tay kafin ta amsa da to gata nan fitowa, bin wayar tay da kallo bayan ta cire a ranta ta shiga raya to waye wannan kuma wane sak'o ne ya kawo mata, mik'ewa tay saida ta d'aukko gyale ta d'aura akan gown d'in jikinta sannan ta tafi, lokacin data shigo cikin parlon ba kowa ta nufi hanyar fita, yana tsaye a gaban bak'ar Mota yana ganinta ya shiga washe baki kallo d'aya Fauzy tayi mashi ta gane shi, k'arasawa tayi fuskar ta adan sake suka k'ara gaisawa,

"Yauwa dama sako ne Yalla6ai ya bada akawo maki, Wannan Motar ce yace in kawo maki taki ce sannan ni zan rink'a kai ki Makaranta sannan yace in fara koya maki Motar in kika iya sai kici gaba da zuwa Makarantar" tunda ya fara Maganar tay sototo tana kallon shi har ya gama, ba don tasan yasanta ba da zata ce makuwa ce yayi an aike shi wurin wata duk da haka yanzu ma tunanin makuwar ce yayi tayi tana d'an murmushi tace mashi tana ganin yayi kuskure ba wurinta aka aiko shi ba,

"Hajiya ba kuskure nayi ba ko baki gane ni ba, ni ne wanda nazo jiya da Yalla6ai ba har na kai ku Government House ba, tabbas ke ce aka ce in kawo mawa don yau kafin ya wuce mukai Maganar" ido kawai Fauzy ta bishi da shi don kuwa bakinta ya mutu, mik'a mata makullin Motar yayi kaman bazata amsa ba jiki a mace ta mik'a hannu ta amsa,

"Yanzu yaushe za'a fara koya Motar ko zuwa gobe in yayi sai in zo tunda naga weekend ne kaman ba Makarantar" kikkafta idanu ta fara saida ta had'iyi abu kafin murya na d'an rawa tace "to...ai lambar da ka kira ni taka ce ko?" da sauri yace mata eh tace to zata yi mashi magana kan hakan yana murmushi yace to kafin ya tambayi yanzu za'a shigar da ita ciki ne ta girgiza mashi kai tace ya barta anan, sallama yayi mata ta d'aga mashi kai ya juya ya nufi hanyar barin layin da k'afa, bin bak'ar Camry d'in da akace tata ce da kallo tayi Zuciyar ta na d'an harbawa can ta maida idanunta akan makullin Motar shima ta kafe shi da ido, juyawa tayi jikinta kamar an zare mata laka ta nufi cikin gidan, tana shiga cikin parlon daidai Aunty Mareeya ta fito daga bedroom d'inta taci gayu da doguwar rigar shadda blue tasha aiki mai ratsin red takalman ta da jakar hannunta duk jajaye ne ta coge d'aurin kallabi sosae tayi kyau, tana ganin Fauzyn ta dakata tana jiranta ta k'araso, daga gefen Auntyn ta tsaya tana kallon ta,

"Ke kuma daga ina yaushe kika fita?" Shiru tayi tana kallon ta kawai ganin haka yasa Aunty cewa "lafiya naga kin tsura man ido?" Hannu ta d'ago ta mik'a mata makullin ta kawo hannu ta amsa, bin shi tayi da kallo ganin na Mota ne yasa ta d'ago tace mata makullin Motar miye, a sanyaye ta shiga fad'i mata abunda mai kawo Motar yace, waro ido Aunty tay nan take ta saki jakar hannunta ta furta "Makullin Motar ki ne!!" Kai ta d'aga mata tace wai haka yace dai, washe baki Aunty tay "haka d'in ma ne wllh, kai wannan dankareriyar kyauta haka tun baki shiga daga ciki ba!" Sosae ta shiga yin murna ganin yanayin Fauzyn ta kai hannu ta dafa Shoulder d'inta "wai ya na ganki haka duk kin yi sanyi keda zaki murna abun farinciki ya same ki haka" d'an ta6e baki tay da alamun damuwa tace "Amman Aunty indai tawa d'in ce to ni ya zanyi da ita, Mota fa!" Wani kallo tay mata "kaji ki da wata Magana, bangane ya zaki da ita ba, ba an fad'i maki abunda zaki da itan ba"

"Amman Aunty taya za'a ce kamar ni inada Mota" harara ta balla mata tace "Wllh matsalata dake wani lokacin k'auyanci komai sai kin nuna ke yar k'auye ce duk da kin shigo birni koda yake inda kika fiton ma ai ba k'auye bane kece dai haka, in banda abu irin ki mace nawa ce yanzu wadda bata kai ki ba take hawa Mota yanzu baga Zarah ba" still da alamun damuwa tace Amman ita ai matar aure ce ko, wannan karon k'ular da Aunty tayi a fusace tace "ai da yake ance mace in bata da aure bazata tuk'a Mota ba, dalla kin ma fara bani haushi in baki so ni sai ki bar man ina so, wllh ba za'a maida Motar nan ba in ma haka kike niyyar cewa, a baki abu don ki rink'a zuwa Makaranta ki tsaya kina wani fad'in k'auli da ba'adi ke da ba'a maki gwaninta" yar ajiyar zuciya tayi a sanyaye tace mata to tayi hak'uri cikin washe baki tace yauwa to ko itafa ai kawai ta kira tayi mashi godiya ita an ma yi a daidai wllh dama tana jin haushin hawa Napep, dariya Fauzy tay ita sai lokacin ma ta tuna da Aunty Mareeyar ta iya Mota, iyayensu ta kira gaba d'aya harda Yaya Mubarak d'in su ta sanar masu zancen zuwan Sameer d'in da kuma Motar da ya bata gaba d'aya sun jinjina abun sosae kafin suka sanya Alkhairi mahaifin nasu yace mata don Allah ta k'ara kulawa da ita sosae tunda yanzu a wurinta zata zauna tace in sha Allahu kar ya damu har Fauzyn ta ba duk suka yi mata Allah sa Alkhairi da Allah ya tsare itama Baban nasu saida yay mata yar nasiha kan ta k'ara kula da kanta ta guji duk wani abu data san zai ja mata dasu gaba d'aya matsala tace mashi insha Allahu zata k'ara kulawa sosae, bayan sun gama wayar Fatuu ta shiga kira lokacin Aunty ta tafi ta gano Motar, lokacin data sanar mata game da Motar wata uwar k'arar murna Fatuu ta saka cike da tsananin farinciki ta hau yi ma Fauzyn Allah sa Alkhairi cike da murna tace ikon Allah Yanzu ita tana da mota ita ma haka Fauzy tace wllh, daga baya sukai sallama tace sai tazo ganin Motar, bayan ta gama wayar hanyar wajen ta nufa a cikin harabar gidan sukai kacibus da Aunty Mareeya ta dawo sai washe baki take kamar wadda aka ma Albishir da Aljanna, tsayawa sukai cike da Farinciki ta furta "Fauziyya wannan Mota haka! da gani zata yi kud'i wllh don babba ce kuma sabuwa" dariya kawai Fauzy ke yi da sauri tace mata taje ta shirya suje yinin bikin tare a Motar Fauzy tace to ba matsala in sun hau tayi mata wani kallo tace to miye abun matsala abu tata, kai Fauzy ta d'aga tace bari taje to ta shiryo Aunty Mareeyar ma ta bi bayanta tana fad'in ai itama kaman sai ta sake shiga gaskiya sosae taba Fauzy dariya, gaba d'aya lace suka saka na Aunty bak'i ne da adon flowers pink ta saka takalma da jaka da gyale duk pink sosae tayi kyau ita kuma Fauzy nata Orange ne da torch d'in bak'i tasa takalma da jaka da mayafi bak'ak'e Wow abun sai dai ace Ma sha Allah don sosae sukai kyau,

tunda suka hau hanya suke ta faman sakin murmushin farinciki gaba d'aya sun kasa rufe baki Aunty sai faman santin Motar take, suna akan hanyar ta tuna da bata fad'i ma mijinta zancen Motar ba tasa Fauzy ta fiddo mata wayarta ta kira mata shi, bayan ta sanar mashi shima sosae ya nuna ya taya Fauzy murna Aunty tace ai saima yaga Motar, tambayar shi su Hanif tayi yace daga Masallaci sun wuce gidan Hajiyar shi tace to agaishe mata da mutan gidan, daga wurin yinin bikin da yamma fitowa sukai suka d'an zaga gari daga can suka wuce gidan Hajiya don suje su nuna ma Fatuu Motar.

A kwana a tashi cikin Fatuu har ya shiga wata na bakwai a lokacin tuni dama Hajiya ta hanata driving ganin yadda cikin yay girma ita kanta dama tuntuni ta fara jin rashin dad'in tuk'in, Sosae take samun kulawa don komi take so sai an mata haka ko wash tace sai Hajiya ta tambayi yaya in dai tana kusa da ita don yanzu tafi zama a part d'in, data dawo daga Makaranta nan take zuwa taci Abinci wani lokacin ma har wanka a visitor room take yi don akwai wasu daga cikin kayanta yawanci sai dare take komawa part d'inta tare da Mino, bangaren Haisam akai akai yake kiranta suna kuma yin chat sosae haka yan Abuja ma yanzu kullum sai Mom d'in Haisam d'in ta kirata ta tambayi yadda take haka Senator ma yana yawan kiranta su Jidderh wannan ba'a magana don sosae take kiranta tana tambayar Babies d'in su, bangaren gwaggo ma sosae take kulawa da autar tata kullum sai ta aiko mata da abun ci ba kamar wanda zai k'ara mata lafiya da yawan jini kamar ganyayyaki kullum sai tayi mata kwad'o mai dad'i.

Ranar Monday da yamma Fatuu na zaune a part d'in Hajiya tana yin Assignment hannunta ruk'e da agwaluma tana sha sai faman tsuke baki take tana d'an runtse ido Hajiya na dariya tace to kamar dole ta hak'ura mana tana yar dariya tace wllh wannan ta cika tsami ne Hajiyar tace to ba ga wasu nan a plate ba ta duba mara tsami sosae sai tasha tace to, d'agowa tayi da niyyar ta canza watan suka ji anyi sallama a tare suka kai idanun su kan k'opa Hajiya na amsawa, lokacin da wadda ta shigo ta k'araso ciki Fatuu na ganinta ta fara murmushi ganin k'anwar haulat tace "Mami ce" kai ta d'aga mata Fatuu ta nuna mata wuri tace ta zauna, gaishe da Hajiya tayi ta amsa ta juyo kan Fatuu itama ta gaishe da ita, amsa mata tayi idon ta akan fuskar ta don ta fahimci kaman kuka tayi idanunta sunyi ja sun d'an kumbura ma, a sanyaye tace "Mami lafiya dai ko?" tana yi mata tambayar ta fashe da kuka hakan ya rud'a Fatuu ta d'ago sosae tana tambayar ta abunda ya faru ido a waje, cikin kuka Mamin tace mata dama cewa akai tazo ta fad'i mata mijin Aunty Haulat yayi had'ari jiya an kai shi Asibiti yau Allah yayi mashi rasuwa, gaba d'aya Fatuu ta zaro ido waje tare da kai hannu ta dafe k'irjinta a razane ta furta mijin Haulat ya rasu! Mami dake ta kuka tace eh, kai Hajiya ta shiga girgizawa sosae ta girgiza da jin Maganar don Haulat ma yar gidanta ce, Kuka sosae Fatuu ta saka tana zabga salati tana fad'in Wayyo Allah Haulat, rarrashinta Hajiya ta shiga yi tana fad'in ta kwantar da hankalinta ko don halin da take ciki amman ina ta kasa daina kukan hakan yasa itama Mami d'in cigaba da rusa kukan, Saude ce ta fito daga cikin kitchen jin hayaniyar kukan su, cikin Falon ta nufo ganin su Fatun nata kuka yasa a rud'e ta hau tambayar lafiya Hajiya ce ta fad'i mata abunda ya faru itama ta girgiza sosae ta shiga yin salati, had'uwa sukai suna lallashin su har Fatun ta d'an yi shiru Mami ma ta daina tana ta goge Fuskar ta da gefen Hijab dibta, waya Fatuu ta d'aukko dake ajiye a gefenta ta shiga kiran gwaggo bayan ta d'auka ko sallama bata yi mata ba cikin kuka tace taji abunda ya faru gwaggon tace mata eh yanzu Mamin ta baro nan sai hak'uri lokacin shi ne yayi, cigaba da kukan tay gwaggo ta shiga rarrashinta tana nuna mata halin da take ciki Fatun sai faman fad'in to ta daina take, bayan sun gama waya da gwaggo Haulat ta shiga kira tana cigaba da yin kuka kad'an kad'an saidai wayar tak'i shiga dama haka take wuyar samunta a waya shiyasa sun fi yin Vedio call gashi yanzu tasan ko ta hau WhatsApp ma ba ganinta zata yi ba, aje wayar tayi ta yunk'ura ta mik'e da k'yar fuskarta jage jage da k'walla tace ma Mami bari tazo su je Hajiya ta tambayi ina tace mata gidan su Haulat d'in zata tayi ma innar su gaisuwa Hajiya tace mata ta bari ayi Magrib tunda ta kawo jiki sai suje gaba d'aya tace to, komawa tay ta zauna Mami ta mik'e tace masu ta tafi Hajiya tayi mata gaisuwa tace ta yi ma innar su kafin su zo Saude ma tayi mata gaisuwar ta tafi, mik'ewa Fatuu ta k'ara yi gaba d'aya duk ta rud'e Hajiya ta k'ara tambayar ya akai cikin muryar kuka tace mata fitsari take ji tace taje tayi ta shiga k'ara bata hak'uri tana fad'in ta kwantar da hankalinta kai kawai take d'aga mata Saude tace suje ta rakata d'akin Hajiya tace yauwa, saida ta rakata har cikin d'akin sannan ta fito ta koma Kitchen jikinta gaba d'aya yayi sanyi tausayin Haulat yakamata, bayan Fatuu ta fito daga toilet bakin gado ta nufa ta zauna ta kai hannu ta d'auki wayarta da taba Saude ta aje mata bayan sun shigo, Haisam ta shiga kira bayan ya d'aga ta gaishe dashi yana jin muryar ta ya gane ba daidai take ba ko amsa gaisuwar tata baiyi ba ya shiga tambayar ta lafiya Mike damunta, cikin kuka ta sanar mashi shima yaji abun sosae yayi mashi Addu'a kafin ya shiga rarrashinta yana kwantar mata da hankali shima sai faman ce mashi to take saida ya tabbatar ta kwantar da hankalin nata kafin sukai sallama, sai bayan da akai isha sannan suka fito don su tafi gaba d'ayan su sun sa dogayen hijabai harda Saude, Tk ne zai kai su a Motar Fatuu har Hajiya na fad'in ba don dare yayi ba ai da a k'asa suka lalla6a ko Fateema tayi exercise Saude tace to suje a k'asan tunda akwai wuta Hajiyar tace tunda dai ya fiddo Motar suje kawai ko don dare, a k'opar gidan su Fatuu Hajiya tasa ya tsaya tace ma Saude taje ta tambayi Dije in bata je ba ta fito su tafi tace to lokacin shagon Kawu Amadu a rufe yake da alama tunda ya tafi salla ya kulle shi, bada jimawa ba suka fito tare da gwaggon dama Saude gaba ta shiga, baya gwaggo ta shiga inda su Hajiya suke ta gaishe da ita ta amsa tayi mata jaje da gaisuwa, kallon Fatuu tay tace har yanzu kukan take ta girgiza mata kai kafin cikin disasshiyar murya ta gaishe da ita bayan ta amsa ta shiga kara bata hak'uri, lokacin da suka je gidan akwae mutane da suka zo gaisuwa innar ta tarbe su bayan duk sun zazzauna aka shiga gaisawa da yin gaisuwa, koda Fatuu tazo yi mata gaisuwar sai kawai ta fashe da kuka nan fa innar su Haulat d'in itama ta shiga matsar k'walla haka K'annan Haulat d'in suma duk suka dasa dama kuma auren Haulat d'in na zumunci ne duk dangi ne, mutane ne suka shiga basu hak'uri suna fad'in lokacin shi ne yayi yanzu Addu'a yafi buk'ata, daga baya sai ga Kawu Amadu tare da Tk sun shigo suma sukai masu gaisuwar, suna a gidan Baban su Haulat ya dawo daga Masallaci innar tasu ta fita tayo mashi magana ya shigo daga bakin k'opar ya duk'a nan aka shiga yi mashi gaisuwar yanata amsawa tare da yin godiya. Tun bayan da suka dawo Fatuu ke ta trying kiran Haulat ba ta shiga sai bayan da suka dawo part d'in su ita da Mino lokacin sun kwanta cikin sa'a sai gashi kiran ya shiga tana d'auka Fatuu ta saka mata kuka tana fad'in ashe abunda ya faru kenan cikin disasshiyar murya ta wanda yasha kuka Haulat d'in tace mata wllh, jajanta mata ta shiga yi tare da yi mata gaisuwa ganin yadda take ta Kuka yasa Haulat d'in ta shiga rarrashinta tana fad'in don Allah ta bari bata ga halin da take ciki ba Fatun tace wllh tausayin su take ji ba kamar Umma Salma duka yarinyar ko shekara bata yi ba Haulat d'in tace mata eh amman ta kusa saura wata d'aya, jajanta mata taci gaba da yi tana Addu'oi daga baya taba Mino itama tayi mata gaisuwa. Gwaggo da Kawu Amadu ne suka shirya tafiya gaisuwa Nijar Fatuu taso ace da ita za'a saidai itama tasan bazata iya yin wannan tafiyar ba a halin da take ciki, kwana biyu da yin rasuwar suka tafi suna can akai sadakar ukku kwanan su biyu suka juyo.

Bayan cikin Fatuu ya fita daga wata na bakwae ya shiga na takwas da sati d'aya Mom d'in su Haisam tazo tafiya da ita, kwananta biyu suka shirya tafiya bayan Fatuu tayi sallama da kowa Mino harda yar kwallar ta anata yi mata addu'o'in Allah ya sauketa lafiya lokacin da aka raka su Airport, Kusan gaba d'aya aka rakasu harda Hajiya dasu gwaggo Kawu Amadu da Saude da Mino su Aunty Mareeya da Fauzy kowa dai ita dai Fatuu sai d'an murmushi take zuciyarta nata saka mata abubuwa,

Alhamdulillah sun sauka garin Abuja lafiya har anje an d'aukko su sai faman murnar zuwan Fatun ake karma dai Jidderh dasu twins su ji, dole Jidderh ta matsa ta sauka a d'akin ta itama Fatun hakan yayi mata dad'i, washe gari Aunty ta tafi da ita Asibitin su aka yi mata awo don samun record d'in ta. Bayan dawowar ta Abuja Kusan doubling kulawar da take samu a Katsina akai mata, sosae ake ta haba haba da ita koda yaushe cikin tambayar abunda take so ake haka safe da dare cikin zuwa dubata ake duk wanda zai fita sai yazo ya dubata harda Dad da safe kafin ya fita sai yazo ya dubata haka in ya dawo ma da daddare sauran yaran gidan ma da safe kafin su tafi school duk sai sun zo sun dubata haka da sun dawo nan suke fara sauka bayan sun dubata sannan suje suyi wanka in aka shirya ma nan za'a dawo wurinta aci Abinci kullum Jidderh cikin fad'an an 6ata mata d'aki take gashi bata isa ta hana yaran gidan zuwa d'akin ba don ta kora su Mom da kanta ta maido su tace bata isa ta hana wani zuwa ba tunda ta rik'e Fatuu in kuma tana son a daina zuwan to saidai ta bari Fatuu ta bar d'akin ta kafe tace ba inda zata anan zata zauna har ta haihu tana fatan ma Allah ya kawo haihuwar da Sauk'i suna bacci kawai suga ta haihu har saida ta ba Mom da Aunty dariya suka ce to Allah ya sa ta haihu hakan dama Aunty tana d'akin Mom ta zo maido su Yasmeen da twins da aka kora daga d'akin, duk dare su Jidderh da Yasmeen dasu twins ke rakata strolling su zagaye gidan in ta gaji ta d'an rankwafa sai suma suyi hakan kaman sun yi sahun salla in ta mik'e sai su mik'e sosae suke bata nishad'i cike da shiririta ake yin tafiyar har a zagayo, haka in tana kwance ko zaune kan gado sai su zagaye ta suna mata hira ana mata tausa in wannan suka yi suka gaji sai su ba wannan, wani lokacin in tana kwance maida cikin nata suke kaman Tv suna kallon yadda yake motsi suyi ta faman kyalkyatar dariya suna fad'in wrestling ake tsakanin Hassan da hossein ko kuma Hassana da hosaina, gaba d'aya d'akin Jidderh ya koma dining area tun tana fad'a har ma ta gaji ta daina. Satin Fatuu biyu a Abujar lokacin cikin na gab da shiga wata tara Haisam yazo, lokacin da yay arba da Fatuu wani irin tausayin ta ne ya kama shi ganin yadda Baby d'in shi ta koma, bata yi wani muni ba saidai komai nata ya k'ara girma ga cikin ma Tubarkallah yayi girma sosae, a ranar ya maidata part d'in shi aikuwa washe gari Mom ta iske shi tace ba yadda za'ai ta zauna nan gaskiya shi bai ga halin da take ciki bane ya zata rink'a hawa bene, shima saida yay wannan tunanin don a jiyan yaga da k'yar ta hau saida ma ya taimaka mata gashi shi kuma gaskiya a wurin shi yake son ta zauna, k'arshe yanke dawowa k'asa yay daga k'asan part d'in Dad dama akwae wani ciki da parlon wanda wani lokacin Dad d'in ne ke amfani dashi ba kamar in yayi bak'i, a ranar aka sa masu aiki suka gyara part d'in fes suka tare, kulawa ta musamman Haisam ke bata tun bayan da ya dawo gashi kwata kwata bai nuna mata yana son wani abu ya shiga tsakanin su sosae yake d'aga mata k'afa to dama itama bata jin abun a kanta hakan ne ma yasa tun tana gidan Hajiya daya nuna zai zo sai tace yay zaman shi kada aga yana wasa da aiki hakan yasa ya d'auki lokaci bai zo ba, duk da haka sosae yake mata abunda yasan zata ji dad'i, a kwana a tashi har cikin Fatun ya shiga wata na tara, tun ranar da ya shiga aka fara saka ran haihuwar ta dama tuni Iya ta fara bata su maganin zak'i da sauran su haka akwae wanda gwaggo ta had'a mata ta taho dasu, shiru shiru ba haihuwa kaman tasan jiranta ake ko ciwon kai Fatun bata yi a haka har Edd d'inta ya wuce hakan ya fara tada masu hankali Aunty ta shiga nuna masu hakan ba matsala bane ai dama 2 weeks before ne ko after a d'an k'ara jira a gani in ya wuce haka kawai ayi mata Cs, itama Fatun da yake tasan hakan ba matsala bane bata wani damu ba, bayan sati guda da wucewar Edd d'in ta ranar ta kama lahadi ne gaba d'aya bata wuni a part d'in nasu ba sai dare ta dawo, Haisam ne ya taimaka mata kaman ko yaushe tashiga wanka bayan sun fito yana k'ok'arin taimaka mata ta shirya tace ya bari ta shirya yaje shima yay wankan, saida ya tambayi ta tabbatar zata iya lafiya lou tana murmushi tace mashi eh, bin shi da ido tay lokacin daya nufi toilet d'in wani irin tausayi yake bata tasan ba don bai buk'atar ta ba yake k'yale ta kawai Saboda tausayinta da yake ne, hakanan taji yau tana son wani abu ya shiga tsakanin su, lokacin daya fito har ta kwanta tana kallon shi da murmushi yake shiryawa shima yana yi yana kallon ta, bayan ya gama komai yay switching wutar dakin off ya nufi gadon, saida ya kunna lamp guda d'aya sannan ya hau gadon, zama yay daga gefen k'afafunta ya fara matsa mata su dama kullum haka yake mata har tayi bacci, yana cikin yi mata tausar yaga ta fara mashi wani salo lokacin daya fahimci mi hakan ke nufi ce mata yay ba komai kada ta damu amman ta nuna mashi lafiya lou ba komai, to daman dai a buk'ace yake da ita hakan yasa ya bata goyon baya, sosae suka faranta ran junansu duk da Fatuu tana yin wani abun ne kawai don ta faranta mashi shi kuma cike da taka tsantsan yake bi da ita, bayan tayi bacci ya tashi ya nufi toilet lokacin daya dawo shiryawa yay cikin jallabiya ya kabbara sallar Nafila don rok'on Allah ya Sauketa lafiya dama Kusan duk dare yana hakan, raka'a biyu yayi bayan ya gama Addu'oi ya koma gadon, rungumota yay ta baya dama a haka suke kwanciya ya lullube su...........

Around 2:00am

Wani irin fitsari ne ya tashi Fatuu dama ta saba tashi fitsari cikin dare sosae, zame jikinta tayi daga nashi ta lalla6a ta saukko kafin ta nufi hanyar toilet d'in da sauri don tana saukkowa taji kaman zai zubo mata, lokacin data duk'a don yin fitsarin wani kalan discharge da bata saba gani ba taga ya zubo mata amman sanin dama tana fitar da shi yasa bata maida kai ba, bayan ta gama fitsarin tayi tsarki ta fito, komawa tayi gado ta kwanta bata fi yan mintuna ba taji cikinta yay wani irin juyawa har saida ta cize baki, wani fitsarin taji ya kamata sosae da sauri ta saukko ta nufi toilet, koda ta duk'a don tayi d'an kad'an ya zubo tare da wani irin ciwo har saida tay d'an sautin rad'ad'i, da k'yar ta yunk'ura ta fito daga cikin toilet d'in ta koma gado, gaba d'aya kwanciyar ta gagareta don ciwon k'aruwa yake mata, wasa wasa tun tana a saman gado har ta kai ta saukko ta duk'e k'asa, duk abunan bata yi tunanin tada Haisam ba don gani take kaman ciwon zai lafa, tun tana juye juye har ta kai ta fara d'an yar fa hannu tana fad'in wash, ganin abun bana k'arewa bane don sai ma cigaba da yake yasa ta gane nak'uda ce take yi a wahalce ta fara kiran sunan Haisam tun dai bata d'aga murya har takai ta d'aga tana ta kiran sunan shi tana ya taimaka mata, ganin yak'i tashi yasa ta fara bubbuga katifa can acikin baccin ya jita a hankali ya fara bud'e idanun shi, daidai ya bud'e ta k'ara kiran sunan nashi tana ya taimaka mata, wata kalar wuntsilowa yay ya sauko da sauri ya zagayo inda take a durk'ushe shima ya duk'a ya shiga tambayar mike damunta hannuwan shi rarruke da ita, cikin ciwo tace mashi tana ganin kaman nakuda ce take a rud'e ya furta Ok bari ya fad'i ma Aunty, mik'ewa yay da sauri ya nufi k'opa har ya bud'e komi ya fad'o mashi a rai sai kuma ya kulle ya dawo cikin d'akin ya nufi wurin side drawer, wayar shi ya d'aukko ya dawo saitin Fatun ya fara k'ok'arin kiran ta, lokacin da wayar ta shiga duk bugu d'aya tare yake da fad'uwar gaban shi, sai faman sintiri yake a wurin saida wayar ta kusa yankewa sannan Aunty ta d'auka cikin muryar bacci ta ambaci sunan shi tare da tambayar lafiya a d'an rud'e yace mata Baby ce ke nak'uda da sauri tace to gata nan zuwa harda ce mata don Allah tayi sauri tana cikin ciwo sosae ta furta Ok gata nan, duk'awa yay ya tallabo Fatun fuskar shi har ta fara hautsinewa cike da tausayi yake ce mata sannu, after few minutes aka turo kopar Aunty ce ta shigo tana sanye da doguwar rigar bacci yana ganin ta ya mik'e yana nuna mata Fatun ta nufo su, a gabanta ta tsaya ta duk'a tana dubata tare da yi mata sannu, d'agowa tay tace ma Haisam nakuda ce da sauri yace to yanzu ya za'ai tace tana zuwa ya taimaka su d'aurata saman gado yace to, bayan sun d'aurata d'aukar abunda ta aje a bakin gado tayi wanda disposal gloves ce ta bud'e yar jakar ta ciro su ta fara k'ok'arin sama hannuwanta, bayan ta gama ta fara duba Fatun dama itama rigar bacci ce iya gwuiwa a jikinta, Haisam na tsaye yana ta kallon abunda take mata fuskar shi a a d'an yamutse sosae yake jin tausayin Fatun, bayan ta gama ta d'ago tana cire safunan tace mashi haihuwa ce amman da d'an saura, sake tambayar ta ya za'ai yayi tace tana ganin abunda yakamata shine su tafi Asibiti yaje ya d'aukko Mota bari ta shirya yace to ya nufi bedside don ya d'aukko makullai, har zai fita Aunty ta tsaida shi ta hanyar tambayar inda kayan haihuwa suke ya dawo ya bud'e mata wardrobe d'in bangon dake cikin d'akin inda kayan suke shirgi guda don ba abunda babu da ya danganci jariri dama tun kafin Mom taje ta taho da ita tuni an gama siyan komai na haihuwar da yawa ma daga Dubai aka siyo su Haisam ma ya taho da wasu trolley guda wanda shida Fanan suka je suka siyo su had'add'un kayan jarirai ne na gaske unisex wato wanda zasu yi ma mace da namiji komai guda biyu aka siya akwae saura ma da Fanan zata taho da su , bayan ya nuna mata ya juya da sauri ya tafi ita kuma ta fara fiddo abubuwan da za'a buk'ata anan kafin ta bud'e wurin kayan Fatuu nan ma ta d'auki abunda zata d'auka, a wata jaka ta zuba komai lokacin ya dawo yace mata ga Motar nan ya kawo bakin Entry tace to, gadon ta nufa yabi bayanta ta kai hannu ta taimaka ma Fatun ta mik'e kallon Haisam tay tace ya d'aukko mata hijab ko gyale da sauri ya furta Ok tare da juyawa, bayan ya kawo Hijab d'in ta zura mata kafin ta nuna mashi jakar kayan data za6a tace ya d'aukko tana rurruke da Fatun suka nufi hanyar fita yana biye da su, sai cije cijen baki Fatuu ke da nishi Aunty nata mata sannu haka ma Haisam, bayan sun shigo cikin parlon ta tuna da itama tana buk'atar mayafi tace ma Haisam ya aje jakar ya kamata suje Mota bari ta d'aukko mayafi, bata jima ba ta fito ta d'auro after dress a saman kayan baccin jikinta bata yi tunanin fad'i ma Mom ba don tasan ba lalle in tana a d'akinta ba, saida ta d'auki jakar sannan ta nufi k'opa lokacin data fita har ya saka Fatuu a bayan Motar shima yana zaune a wurin yana ta faman yi mata sannu, fitowa yayi ya koma gaba Aunty ta shiga baya ta kwantar da Fatun a jikinta yaja Motar da gudu suka nufi hanyar Gate,

Basu dad'e sosae ba Saboda gudun da yake shararawa suka iso Asibitin wanda babban private hospital ne kuma sananne, bayan sun shiga yana niyyar nufar parking space Aunty tace suje bakin entrance ya furta Ok ya nufi can, bayan ya parker a bakin kopar shiga cikin Aunty tace tana zuwa ta fito da sauri ta nufi shiga cikin Asibitin shi kuma ya fito ya koma bayan ya rungumo Fatuu a jikinshi yana cigaba da yi mata sannu kai kawai take d'aga mashi, bada dad'ewa ba Aunty ta fito Nurses guda biyu musulma da Christian na biye da ita sun turo Wheel chair Haisam na ganin su ya fito yana k'ok'arin fito da Fatun, bayan an d'aurata suka turata Aunty da Haisam suka rufa masu baya, Labour room suka nufa dama Aunty ta fad'a masu Vip zasu kaita suka nufi can da ita, gaba d'aya harda Haisam suka shiga cikin d'akin aka kwantar da Fatun saman gado bayan Aunty ta cire nata Hijab d'inta itama ta cire after dress dinta, daga gefen kanta Haisam ya zauna ya kama hannunta guda yana cigaba da yi mata sannu Fuskar shi a hautsine, ciwon kaman yasan an zo Asibiti nan ya shiga k'aruwa amman yana yi yana lafa mata in ya lafan har d'an gyangyad'i take, gaba daya Aunty da Nurses d'in biyu na a kanta suma suna ta yi mata sannu sai faman d'aga kai take tana yarfa hannu, in ciwon ya taso sosae hankalin Haisam ke tashi har sai ya lafa sannan hankalin shi ke d'an kwanciya, a haka saida aka shafe Kusan awa bata Haihun ba Haisam sai tambayar Aunty yake ya tak'i haihuwan tace mashi lokacin bai yi bane, sai bayan kamar awa d'aya da rabi sannan ciwon ya taso gaba d'aya daka kalli Fatuu kasan tana cikin Azabar ciwo don a lokacin ko anyi mata sannu bata iya amsawa gaba d'aya ta rurruke Haisam sai murkususu take tana kukan da ba hawaye cikin fitar hayyaci take fad'in "Ya Haisam bazan iya ba....kilan ma Mutuwa zan yi" sosae wannan Maganar tata ta k'ara rud'a shi tsantsar tashin hankali ne bayyane akan fuskar shi tayi wani irin ja fuskar yana ta ce ma Fadin "Pls Baby stop saying that....im here for you ba abunda zai faru in sha Allah zaki haihu lafiya" ganin abun yayi yawa a wurin shi yasa shi mik'ewa tsaye daga bakin gadon still yana ruk'e da hannunta guda, kallon Aunty dake tsaye a gefenta tana k'arfafa mata gwuiwa yayi yace "Aunty this is too much gaskiya, pls kiyi wani abu tana shan wahala da yawa" fuska a yamutse yayi Maganar, idon Aunty na akan Fatun tana mata kallon tausayi tace "bai yi yawa ba Son haka ake yi dama kuma duk abunda yakamata ayi mata an yi so sai mu jira Allah ya sauketa lafiya" wani kalan waro ido yay yace yanzu duk wannan Azabar ciwon da take sha ne da Sauk'i, kai Aunty ta jinjina mashi tace wasu suna spending whole day haka wasu ma 2 days ita kuwa bai fi awa d'aya da rabi da suka zo ba kuma in sha Allahu tana gab da haihuwan, girgiza kai yay idon shi akan Fatuu dake cigaba da murkususun azaba yace gaskiya to in haka ne ayi mata Cs kawai taya Mutum zai jure wannan wahalar, d'an guntun murmushi Aunty tay tare da d'an girgiza kai ta fahimci a wurin shi gani yake hakan sauki ne duk da tabbas in anyi nasarar yin shi lafiya lou yafi sauk'in, kara maimaita mata Maganar ayi mata Cs yayi ta kalle shi cike da jan hankali ta furta "ba sai an mata shi ba zata iya haihuwa da kanta, pls Son You should encourage her instead, wannan Maganganun da kake kana sata tana sarewa and kana anan ne don ka k'arfafa mata gwuiwa so is better if you do dat" d'an yamutsa baki yay jiki a mace yaja k'afa ya koma bakin gadon Aunty tace yayi mata Addu'a ya d'aga mata kai gaba daya rud'ewa tasa ya manta da yayi hakan, lokacin Aunty ta buk'aci amfani da wayarta ta tuna ta baro ta a gida tambayar Haisam tayi wayar shi ya girgiza mata kai alamar bai tare da ita,

"Nurse Haleema pls where is your phone?" Aunty ta tambayi d'aya daga cikin nurse d'in cikin girmamawa tace mata tana a station tasa caji tace mata in ba damuwa ta d'an aro mata da sauri tace to, har ta nufi kopar fita Aunty ta dakatar da ita ta tambayi akwae karatun Qur'ani a ciki da sauri tace eh sosae tace to ta kawo mata, bada jimawa ba ta dawo lokacin Haisam nata yi ma Fatun Addu'o'i ya rurruk'e ta, bayan ta kawo wayar Aunty tasa ta kunna karatu tace to, a saman drawer din gadon Fatun aka d'aura wayar karatun ya fara tashi daga Fatiha bayan ta k'are ya shiga baqara Aunty ta tambayi Fatun ta iya surar da ake yi tun kafin ta bada amsa Haisam yace mata eh ta jinjina kai,matsowa tayi ta kai hannu ta dafa goshin Fatun tace mata ta daure su rink'a bi tare ta jinjina mata kai tana ta nishin ciwo idanunta sunyi ja luhu luhu kanta a bud'e manyan kitson da Iya tayi mata guda goma sun bayyana, sosae tayi k'arfin halin bin karatun tana yi tana tsayawa sai kuma taci gaba Aunty ma na bi haka Nurse Haleema, zuciyar Haisam ce ta raya mashi ya tashi yayi sallar Nafila tunda lokacin kar6ar Addu'a ne, yin tunanin yasa shi mik'ewa da sauri Fatuu na ganin tafiya zai yi ta k'ank'ame hannun shi ya juyo ya kalleta cikin muryar wanda ke cikin rad'ad'in ciwo ta fara fad'in "Don Allah Ya Haisam kada ka tafi ka barni....ka tsaya in ma Mutuwa zan yi in mutu a gaban ka don Allah" sosae Maganar tata ta k'aryar mashi da zuciya amman sai yay k'arfin halin komawa ya zauna yasa hannun shi guda yana shafa kanta ta sigar lallashi yace ta daina fad'in hakan ta kwantar da hankalinta in sha Allahu ba abunda zai same ta zata haihu lafiya yanzu so yake yaje yayi salla sai yayi mata Addu'a sosae he's sure in sha Allah Allah zai amsa, shiru tay tana cigaba da nishi yace bari yace ta daure taci gaba da bin karatun ta d'aga mashi kai, mik'ewa yay slowly ya zame hannun shi daga cikin nata ya juya zai tafi Aunty tace mashi yaje Office d'inta sai yayi sallar acan ya d'aga mata kai, har ya kai k'opa idanun Fatuu na akan shi yana kama handle zai bud'e ya dakata ya juyo ya kalleta idanun su suka shiga cikin na juna gaba d'aya abu iri d'aya zuciyoyin su ke ayyana masu, tunda Fatuu ta fara ciwon bata yi k'walla ba sai yanzu suka zubo mata sharr ta fara yamutsa fuska tana kuka still kallonta Haisam ke yi shima kawai sai jin k'walla yay sun zobo mashi a tashi Fuskar da sauri ya juya ya bud'e kopar ya fice,

Bayan yaje Office d'in Aunty da yake babbar likita ce a Asibitin toilet ya wuce yayo Alwala, lokacin daya fito a saman kujera yaga prayer mat ya d'aukko ya shimfid'a kafin da k'yar ya samu ya daidaita natsuwar shi ya kabbara sallar, raka'a biyu ya fara yi bayan ya gama ya d'aga hannu yana ma Fatuu Addu'a k'walla na zubo mashi, k'ara tashi yay ya k'ara yin wasu raka'a biyu nan ma yayi mata Addu'a sosae a cikin sujjada bayan ya sallame zaune yayi zugudum yana tunanin ko a wane hali take ciki yanzu gaba d'aya ba cikakkar natsuwa a tare dashi don koda yana sallar halin da ya baro ta kawai yake gani a haka dai yake yi, ji yayi yana son ya koma d'akin don yaga halin da take ciki har ya mik'e wata zuciyar ta bashi ya k'ara yin raka'a biyu Shikenan sai ya koma gaba d'aya, bayan ya kai ta farko ya mik'e yana ta biyu lokacin Nurse Chioma ta fad'o cikin d'akin duk da ba saitin kofa yake kallon ba ya fahimci nurse ce ta shigo don ta gefen idonshi ya hango fararen kayanta, wani irin bugu gaban shi ya shiga yi ba kamar da yake da sauri ta shigo cikin d'akin tsoro da kuma fargabar shigowar tata ne suka cika mashi zuciya har baisan ko yana karatun sallar ma daidai ba a haka dai yaci gaba da yin sallar bai yi tunanin ya yanke ta ba, lokacin daya sallame a tsorace ya juyo ya kalleta kawai sai gani yay ta washe baki ta furta "Sir, Your Wife has deliver....." ai tun kafin ta rufe baki da sauri ya mik'e ya nufo hanyar k'opar saida ta tuna mashi da takalman shi sannan ya juyo ya dawo inda suke maimakon ya saka a k'afafun nashi kawai sai ya kwashe su a hannu ya juyo a haka ya fito daga Office d'in Nurse Chioma na biye dashi saida ta k'ara yi mashi magana tace da ya saka takalman don nan Asibiti ne akwai had'ari tafiya ba takalma sannan ya zubo su k'asa ya saka tare da furta mata thanks kafin yaci gaba da tafiya da saurin da shi bai san ma in ya ta6a yin irin shi ba a rayuwar shi, yana bud'e kopar ya shiga sai kuma yaja ya tsaya turus ido a ware yake kallon Fatuu dake faman jujjuya kai tana nishi da k'arfi tare da cize baki maida idon shi akan Aunty dake a gaban k'afafun Fatuu an lullube tun daga kan cikinta zuwa saman k'afafunta dake a d'age da blue d'in yadi, jiki a sake ya k'arasa gaban gadon cikin d'aurewar kai yace ma Aunty aka ce kuma ta haihu, d'an girgiza kai Aunty tayi tare da d'an murmushi don ta fahimci a rud'e yake kan matar tashi shiyasa har bai ji kukan jaririn daya karad'e cikin d'akin ba, da hannu tay mashi nuni da saitin da Nurse Haleema take tana goge jaririn dake ta faman tsanyara kuka sai lokacin ya dawo cikin hayyacin shi ya tuna da yan biyu ne aka ce a cikin nata, tambayar Aunty yay bata haiho d'ayan bane ba tare data kalle shi ba ta d'aga mashi kai tace gashi nan yana hanya tace yaje wurinta da sauri ya nufi wurin kan Fatun ya zauna tana ta kallon shi tana cigaba da nishi idon ta na d'an lumshewa ya kai hannu ya fara shafa kanta dayan kuma ya kamo hannunta guda yana "Sorry Baby kin kusa haihuwan d'ayan ki daina jin ciwon" kai ta jinjina mashi, bai dad'e da zama ba ta k'ara sautin nishin da take da sauri Aunty ta fara fad'in tay pushing sosae saidai da ta fara yunkurin sai kuma ta bari, hannu Aunty ta d'aga ma Haisam tace ya sata taci gaba da pushing ga Babyn nan nason fitowa aikuwa da sauri ya shiga ce mata "Push Baby..." da tayi sai ta bari tana ta jujjuya kai fuskar shi a yamutse yake ce mata don Allah ta daure tayi Ko babyn ya fito ta huta, a wahalce ta shiga fad'in "Ya Haisam k'arfi na ya k'are wllh....bazan iya ba" da k'yar take Maganar muryarta ta shak'e gaba d'aya ya k'ara rud'ewa ya juyo ya kalli Aunty ya fad'i mata abunda tace Auntyn tace mashi dole sai tayi hakan zata samu ta fito da shi don komawa yake, hannu Haisam ya kai ya ruk'e gaba d'aya shoulder d'in Fatuu yana k'ok'arin daidaita natsuwar shi cikin d'an kwantar da murya yace "listen Baby, I know you're strong so you can do it, nasan ke ba raguwa bace, pls ki daure ki pushing sosae" kai ta d'aga mashi tana nishi ta baki lokacin Aunty ta k'ara cewa tayi Haisam d'in ya hau jinjina mata kai still yana ruk'e da kafadun nata da k'arfi ya furta "push Baby...." ta daddage da iya karfinta na k'arshe tayi wani uban nishi kanta ya d'ago sama can kuma sai ta koma ta fad'a kan gadon yaraf idanunta suka shiga lumshewa a wahalce take fad'in ta gaji bazata iya ba ita dai, juyawa Haisam yay a hautsine yace "Aunty she's completely exhaust........" Bai k'arasa ba sakamakon jaririn da Aunty ta d'ago sama wani irin fari fat dashi jikinshi sam ba wata kazanta sosae Subul dashi gashi k'aton gaske, janye jaririn tay suka had'a ido da Haisam ta d'an tabe mashi baki tare da d'age gira ido waje yake kallon ta da babyn, nurse Chioma ta kira ta mik'a mata shi ta nufi inda d'ayan yake tana washe baki tare da Fad'in "What an Identical twins!" ta k'arasa inda nurse Haleema take nan suka shiga santin jarirai, ganin Aunty na niyyar maida idonta kasan Fatun yasa da sauri Haisam yace mata amman dai su kenan ko d'an girgiza kai tayi da d'an murmushi tace mashi da sauran wasu biyun ya gane wasa take hakan yasa shi yin shiru ya maida idon shi kan Fatuu da idanun ta ke a lumshe ya kai hannu ya rungumota jikinshi ta gefen shi yana mata sannu tare da fadin Shikenan ta haihu zata huta ta d'aga mashi kai, bin ta da ido yay wani irin mugun tausayinta ne ke ratsa mashi zuciya bama ita kad'ai ba gaba d'aya halittar mace tausayin su ya kama shi don yanzu yasan ainihin micece haihuwa, a hankali ya juya ya kallo inda jaririn suke cikin warming bed ana masu weighting and apgar test Aunty ce ke yi Nurse Haleema na rubuta sakamakon da take fad'i mata a jikin wani d'an white board dake a jikin bango, bayan an gama yi ma na farko komai Aunty ta kawo shi ta kwantar dashi rub da ciki a saman k'irjin Fatuu ta kalli Haisam da yayi zuru tana murmushi tace "Wato hankalin ka gaba d'aya yana akan Baby shi yasa ko tambayar abunda muka samu baka yi ba" murmushi yay cikin cool voice d'in shi ya tambayeta ta d'an harare shi tace bazata fad'a ba ya duba da kanshi, saida zata bar wurin sannan tace mashi duka Baby boys ne ya d'aga kai, gaba d'aya suka zuba ma jaririn da ta aje ido Fatuu ta bud'e idanunta sosae tana kallon jaririn da d'an murmushi wata irin k'aunar shi taji tana ratsa mata zuciya a hankali ta d'ago hannu guda ta d'aura a jikin shi ta rungume shi, zuba ma jaririn ido Haisam yay mamaki ne fal a cikin ranshi ta yadda Babyn shi ta haifo yaro haka ya shiga raya dole ta wahala ace daga jikinta ya fito kuma ta d'an wannan opening d'in ya k'ara raya iya wannan kawai ya isa mutum ya jinjina girman Ubangiji, kai jaririn ya fara d'agowa da alama yana jin k'arfi ne don tubarkallah K'ato ne, kallon Haisam yake yana yi yana rufe idon yana d'an lila kan shi Fatuu dake ta kallon shi tana sakin murmushin farinciki ta d'aga ido ta kalli Haisam cikin disasshiyar murya ta furta "He's looking at his Dad" Murmushi shima Haisam d'in yayi tace ya d'auke shi yay d'an shiru gani yake kaman in ya d'auke shi a haka ba kaya zai iya ji mashi ciwo a hankali yace ta bari a saka mashi kaya ta jinjina kai tana dai ta murmushi ita kanta tsantsar mamaki take a cikin ranta na wai wannan d'anta ne ita ta haife shi kuma tare da Haisam, k'ara kallon Haisam tayi tace "Allah ya amsa Addu'a ta kaga Babyn sak kai ne" kai ya d'aga mata don shima yaga Kamannin shi sosae yaron ya d'aukko, Nurse Chioma ce tazo zata d'aukki Babyn don a saka mashi kaya da murmushi ta kalle su ta taya su murna Haisam ne yayi mata godiya ita kuma Fatuu ta jinjina mata kai gaba d'ayan su da murmushi akan fuskokin su tana tafiya Aunty tazo da d'ayan jaririn shima ta d'aura shi a saman k'irjin Fatun tana fad'in gashi nan shima yaji dumin Mom Fatuu ta d'an fad'ad'a murmushin ta a hankali ta kai hannu ta d'ago da fuskar shi da alamun mamaki take kallon shi sai kuma ta d'aga kai ta kalli Haisam da shima fuskar jaririn yake kallo har Aunty zata wuce yace mata wannan ba shine aka d'auka ba yanzu ta d'an girgiza mashi kai tana yar dariya tace d'ayan ne identical twins ne suma sunyi k'ok'arin samun abunda za'a rink'a bambanta su sun kasa Haisam ya d'aga kai ta tafi, shima wanda aka kawon bin shi sukai da kallo suna ta murmushi gaba dayansu wani irin dad'i ne ke ratsa zukatan su ganin jariran, bada jimawa ba aka kawo Hassan d'in an shirya shi cikin set d'in fararen kayan sanyi masu kyaun gaske, Haisam aka mik'a ma shi saida ya gyara zama sannan ya amshe shi aka d'auki d'ayan shima don a shirya shi, shima kayan sanyin aka saka mashi amman nashi light blue ne anyi hakane don a iya bambanta su Aunty ce ta kawo shi tana ta murmushi tace ma Fatuu gashi itama ta d'aukka a hankali tace to ta fara k'ok'arin tashi Haisam yasa hannu guda ya taimaka mata ta zauna ta jingina da kan gadon dake a jikin bango har lokacin kuma rabin jikinta na lullube da blue yadin da aka rufa mata, sai faman washe baki suke gaba d'ayan su suna kallon yaran tsabar farinciki ma sun kasa magana sai dariya kawai suke yaran na d'an bud'e ido a hankali can na hannun Haisam ya fara kai hannu baki yana d'an tsotsa kallon Fatuu yay yace wannan k'ilan yunwa yake ji wane madara ake basu yaje ya samo bata san lokacin da tasa dariya mai d'an sauti ba tace su ai yanzu breast milk ake basu sai bayan wani lokaci ake fara basu Madara ya d'an jinjina kai a hankali yace yasan shi ake basu kawai yayi tunanin akwae wani Madara da za'a iya basu kafin ta warware sosae ta fara feeding nasu ta d'an girgiza mashi kai, dawowa wurin su Aunty tayi itama ta zauna bakin gadon daga wurin kan Fatuu ta d'ayan bangaren kallon Haisam tayi tana murmushi tace mashi yayi masu huduba ne sai lokacin ma shi ya tuna da hakan yace Ok bari yayi ta tambayi to wane suna za'a saka masu yay d'an jimm sai kuma ya juya ya kalli Fatuu da itama kallon nashi take tana son ta ji sunan da zai saka masu ganin haka yasa Aunty cewa bari ta basu wuri sai suji dad'in za6ar masu sunayen bayan ta mik'e tsaye tace ma Haisam sai yayi sauri don lokacin salla ya kusa yace to, dama tun lokacin da Fatun ta haifo na biyun akai kiran sallar farko,

"Wane suna kike so a sa masu?' calmly ya tambayeta tana murmushi tace mashi ai shine Baba ko shi yakamata ya zabar masu ya d'an girgiza kai yace ita tafi cancanta ta za6a masu sunan da take so tay d'an jimm kafin tace to shi ya zaba ma d'aya itama haka jin yayi shiru ta kai idanunta da suka shishshige ta kalle shi ta furta "hakan yayi maka?" lumshe mata ido yay tace to wane suna zai za6ar mashi yay d'an shiru kafin yace sunan Dad d'in shi ta jinjina kai tace yayi, tambayar ta yay ita wane suna ta za6ar ma shi tana ta murmushi tace sunan Kakan su Mijin Hajiya yanayin kallon da yake mata ne ya sauya da d'an alamun mamaki yace ita bata so asa mashi sunan Dad d'inta ne tace "ina so, amman dai nafi son asa wanda nace Saboda Hajiya nasan zata ji dad'i sosae" shiru yay yanata kallon ta can taji yace hakan bazai zama son kai ba kuwa har saida tayi yar dariya tace to miye abun son kai ai duk d'aya ne ko kuma sunan Baffan nata ko in ta k'ara haihuwar ba sai asa ba, da mamaki ya furta "zaki k'ara kenan?" shiru tay ta kasa bashi amsa a ranta tana tuna wuyar da tasha wadda yanzu har ta zama labari don bata wani jin ciwo a jikinta saidai rashin k'arfi tana jin ta wani irin fayau daba cikin, ce mashi tayi ai dole ta k'ara tunda yanzu ta fara, "amman dai wahalan yayi yawa gaskiya I think ba sai kin k'ara ba"

"Baka son Ya'ya ne?" Amsa ya bata da yana so amman tunda abun akwae wuya sai a hak'ura kawai tana yar dariya tace to ai duk haka ake haihuwan a haka ma ita nata da Sauk'i ya d'an ta6e baki yace haka wai Aunty tace, ce mashi tay yayi masu hudubar ya ce to bayan ya gama ya d'ago tace ko na hannun shi asaka mashi sunan Grandpa din tunda shine babba sai wannan asaka mashi sunan Dad ya d'aga mata kai slowly ya furta hakan yayi, mik'a mata Adam d'in yayi ya d'aukko na jikinta wato Aliyu shima ya fara yi mashi yana gamawa Aunty tazo ta tambayi an saka masu sunan yace mata eh ta tambayi wanda aka saka ya fad'i mata, jinjina kai tayi tace "Ma sha Allah, Allah ubangiji ya raya mana su ya Albarkaci rayuwarsu" Haisam ne ya amsa ita kuma Fatun a cikin rai ta amsa Auntyn ta k'ara cewa "Yakamata a kira gida a sanar masu nasan yanzu tunda Asuba tayi zasu gane bamu nan gashi duk mun taho ba wayoyi" Haisam ne yace mata bari in yayi salla sai yaje gidan ya fad'i tace to, bayan tafiyar Haisam su Nurse Haleema wurin gadon suka zo suka tsatsaya sai faman santin yaran suke gaba d'aya suma sai faman washe baki suke Nurse Chioma tace ita tunda ake haihuwar Twins a Asibitin ba'a ta6a haihuwan wanda suka matuk'ar bata sha'awa ba kaman wannan wllh ji take kaman a bata su kyauta Aunty dake dariya tace ai ga Mom d'in su nan ta tambayeta ta bata da sauri Chiomar tace ita tama fara bayan agabanta akai nak'udar su, Nurse Haleema ma Addu'ar Allah ya bata irin su tayi da sauri Chioma tace aikuwa ba bak'ar fata ba wllh bazata haife su ba ita bak'a bak'a mai d'an hanci Mijinta bak'i hancin shi mai d'an fad'i taya zasu Haifa irin su gaba d'aya aka saka dariya Haleemar ta kai hannu ta 6aketa a shoulder, mik'ewa Aunty tayi tace masu su kai babies d'in d'ayan gadon bari ta taimaka ma Mom dinsu ta tsaftace jikinta duk suka ce to, bayan ta taimaka ma Fatuu ta mik'e rigar jikinta duk ta 6aci da yake mai haske ce Aunty na ruk'e da ita suka nufi toilet wani iri take jin tafiyar ta don ma Allah ya taimake ta ko K'ari ba'a mata ba don Aunty harda Olive oil tayi mata amfani wurin fitowar na farkon.

Fitowa Dad yay don tafiya Masallaci saida yaje ya taso su Affan da Mubeen kamar ko yaushe suka tafi, lokacin da suka je parking space yayi tunanin ganin Haisam acan amman sai bai gan shi ba hakan yasa shi cewa su d'an jira shi, bayan d'an wani lokaci yayi tunanin kiran shi saidai har wayar ta yanke bai d'aga ba hakan yasa shi k'ara yin tunanin ko ya riga ya tafi duk da yasan ko yaushe a tare suke tafiya, koda suka je Masallacin basu gan shi a can ba har aka gama sallar suka juyo Dad nata d'an tunanin to ko lafiya Haisam d'in bai je salla ba, lokacin daya shiga Bedroom d'in shi Mom na zaune akan prayer mat bata dad'e data gama sallar ba tana tasbih, zama yay daga gefenta a bakin gado ta juyo ta kalle shi da d'an murmushi ta gaishe shi ya amsa, ganin yayi shiru yana kallon k'asa kaman mai tunanin wani abu yasa ta tambayi Lafiya ya d'ago yace mata Son ne bai je Salla ba kuma yanata kiran layin shi yana shiga bai d'auka ba tace to ko ya makara ne shine yayi sallar a gida, girgiza mata kai yay yace ai tun da zasu je ya kira shi bai d'aga ba sai yayi tunanin ko ya tafi ne to acan ma basu iske shi ba har aka gama sallar kum bai zo ba yanzu bayan sun dawo saida ya k'ara kiran shi tana ta ringing still bai picking ba,

"To ko lafiya?" Mom ta fad'a bayan ta d'an yi shiru, ce mata yay shima abunda yake ta tunani kenan, mik'ewa Mom tayi tace bari ta kira Daughter aji da sauri Dad yace yauwa, wurin side drawer ta zauna bayan ta d'auki wayarta ta fara kiran Fatuu, to itama dai har ta yanke ba'a d'aga ba da alamun mamaki ta kalli Dad yace itama bata d'auka ba ta jinjina mashi kai, sake kira tay nan ma dai shiru nan take dad ya hau girgiza kai yana fad'in anya kuwa lafiya Mom da har gabanta ya d'an fara fad'uwa ta mik'e tana fad'in bari taje part d'in nasu shima ya mik'e suka fito tare, a bakin part d'in ya tsaya ita ta shiga ba kowa a parlon ta nufi Bedroom a bakin kopar ta tsaya takai hannu ta fara knocking shiru ba'ai magana ba gashi ta lura da kopar ba'a datse take ba, d'an jimm tay zuciyarta ta fara raya mata abubuwa can dai cike da fargaba ta tura k'opar ta shiga harda yar sallama, tsaye tayi daga bakin kopar tana kallon d'akin da yake wayam ba kowa gashi tsab yake ba wani abu na alamun tashin hankali, tunanin to ina suke ta shiga yi zuciyar ta ta raya mata ta duba toilet ta raya to mi zasu zauna yi a toilet tsawon lokaci duk da haka ta nufi toilet d'in shima knocking tayi shiru ta tura kopar nan ma dai wayam ne, dawowa tayi cikin d'akin har zata nufi kopar fita idanunta suka sauka akan packet d'in gloves dake a yadde saman floor da sauri ta nufi wurin, d'aukko shi tay taga a bude yake ta lek'a tana kallon safunan dake ciki nan take ta shiga tunanin to ko Daughter nakuda ta fara ne sai lokacin ta lura da wayoyinsu d'aya na akan gadon gefen filon d'aya kuma na akan side drawer, da sauri ta fito tana ruk'e da ledar safar, Dad na ganinta ya tambayi ya akai ta nuna mashi tace tana tunanin nakuda ce ta kama Daughter d'in cikin dare k'ilan ko asibiti suka tafi da mamaki Dad yace "Asibiti kuma ba tare da sun fad'a ma kowa ba?" shiru Mom tay yanayin fuskar ta da d'an alamun damuwa can tace to ko da Aunty suka tafi da sauri Dad yace bari ya kirata su ji, to itama dai d'in Wayar har ta yanke ya k'ara kira duk ba'a d'aga ba lokacin gaba d'aya Hankulan su sun tashi da sauri Mom tace bari ta dubo ta a dakinta, lokacin data je d'akin nan ma wayam ne sai wayarta dake a gefen pillow, fitowa Mom tayi ta nufi d'akin Jidderh lokacin bata dad'e da komawa ta kwanta ba bayan tayi sallar Asuba, tura kopar tayi ta shiga ta nufi gadon Jidderh tana kiran sunanta jin kiran Mom d'in yasa ta bud'e fuskarta ta juyo tana kallon ta, tambayar ta tayi tasan ina su Daughter suke ai tana jin haka da sauri ta yunk'ura ta tashi zaune da tsananin mamaki tace "Mom basu nan ne?" Kai ta d'aga mata ta shiga fad'i mata an tashi duk ba'a gan su ba harda Aunty kuma duk wayoyin su na a gida a d'an firgice ta kai hannu ta dafe kirjinta da hannu guda baki bud'e take kallon Mom d'in da itama take ta kallonta can ta juya zata fita aikuwa da sauri ta saukko ta bi bayanta, tsaye sukai cirko cirko bayan ta sanar ma Dad d'in Auntyn ma bata nan da tashin hankali yace to in ma Asibitin suka tafi anya kuwa lafiya zasu yi irin wannan tafiyar Mom tace ita ma abunda ya tada mata hankali kenan jin haka yasa Jidderh ta fara yarfa hannu kaman zatayi kuka tace " Dad bai kamata muna wasting time ba don Allah mu bisu nasan bai wuce Asibitin su Aunty suka tafi tunda da gani suna tare" da sauri ya furta Ok dama jikinshi jallabiya ce Mom kuma akwai Hijab data yi salla Jidderh kuma kayan bacci ne riga da wando sai hula ko tunanin ta koma ta d'aukko mayafi bata yi ba suka nufi hanyar fita dama akwae makullin Motar da su Dad suka je Masallaci a aljihun shi, suna niyyar fita Haisam ya sako kai cikin parlon gaba d'ayan su kaman an latsa masu pause duk suka tsaya cak suna kallon shi atare kuma duk gaban su ya hau fad'uwa, kallon su ya shiga yi da d'an murmushi Mom ce ta fara magana tace "Habiby ina kuka je ne, ina Daughter take?" Kafin ya bata amsa Jidderh tace "Big bro ina sister Fatuu tana lafiya don Allah?" itama tana rufe baki Dad yace "Son, ya zaku fita baku sanar ma da kowa ba kuma duk kun bar phones d'in ku anan miya faru ne ina Daughter?" Yar dariya yayi jin yadda suka jera mashi tambayoyi, fad'i masu yay sunje hospital ne da sauri Mom tace nakuda Daughter d'in ta fara ne yace eh,
"To kuma sai ku kama ku tafi ba tare da kun sanar da mutane ba?" Dad ne ya fad'a ya d'an d'aure fuska Haisam d'in yace mashi lokacin sunga duk suna bacci ne shiyasa yana rufe baki Dad ya dalla mashi wata uwar harara da sauri Haisam d'in ya matsa wurin shi yana zuwa ya rungumo shi jikin shi yana sakin k'ayataccen murmushi yace "We're very sorry mun yi laifi amman yanzu time en farinciki ne, guess what?" da sauri Dad d'in ya girgiza mashi kai yadda suka yi sai kace wasu abokai,
"Kayi abokai..."tun kafin ya rufe baki Dad ya d'ago shi da sauri kafin yace wani abu Mom ta riga shi fad'in "ta haihu ne??" Kai ya d'aga masu kafin yace eh an samu baby boys yay maganar yana dariya gaba d'aya suka shiga washe baki Jidderh ta saki k'arar farinciki tare da daka tsalle Su Dad suka shiga fad'in Alhamdulillah, Mom ce tace su tafi ta nufi k'opa da sauri gaba d'aya bakinta yak'i rufuwa, juyawa Jidderh tayi da gudu ta nufi d'akin su Yasmeen da Affan ta fad'i masu nan fa suka shiga murna tare duk suka fito lokacin Haisam ya tuna da wayar shi yace bari ya d'aukko, Dad ne yaje ya d'aukko Jeep Mom da Jidderh suka shiga su kuma su Yasmeen da twins suka shiga ta Haisam a tare motocin suka fara tafiya bayan sun sha round suka nufi gate,

Bayan Aunty ta taimaka mata ta gyara jikinta sun fito ta d'aukko mata doguwar rigar da ta sako mata cikin kayan ta saka ta d'aura gyalenta, Aunty da kanta ta shirya mata pad a jikin pant d'in da zata saka ta bata ta sa kafin ta bata turare ta fesa bayan ta gama kimtsawa ta haye saman gadon da aka canza mata acan wani bangaren d'akin, juyawa tayi tana kallon babies d'in dake kwance a gefe da murmushi Aunty ma zama tay daga bakin gadon tana kallon su bada jimawa ba Nurse Haleema ta shigo ruk'e da d'an babban tray an d'auro kayan tea da bread a leda da yake a Vip d'in har Abinci ake badawa ta d'aura akan drawer tace ma Aunty gashi nan dama ita tasata taje ta amso bayan ta ajen ta juya ta fita, Aunty ce ta had'a mata kakkauran tea ta bata ta fara sha sosae taji dad'in tea d'in biredin ne take ci kad'an tana cikin sha Aunty tace bari ta amso mata magunguna da in ta gama zata sha tace to, bayan fitar ta juyawa tay tana kallon yaran nata tana sakin k'ayataccen murmushi gaba d'aya har yanzu ganin abun take kamar wasa wai ita ta haife su ita kanta sosae take ganin kyaun yaran sai kace larabawa duk da dai akwai jinin larabawan a jikin su, lips d'in su sak kalar na Haisam wato peach saidai nasu yafi cizawa gashin girar su ma a tsare yake kwance lub gashi bak'i ne sosae komai dai nasu mai ban sha'awa ne, bada jimawa ba Aunty ta dawo lokacin ta gama shan tea din ta bata magungunan tana cikin sha Hassan d'in ya farka yana motsi can ya kai hannun shi dake cikin mitten ya fara tsotsa Aunty dake kallon shi tace "da alama dai grandpa acici ne, tun ana goge shi ya fara mamulan hannu" Fatuu dake yar dariya tace d'azun ma da ta d'aura mata shi saida ya tsotsi hannun har ta fad'i mata abunda Haisam yace na siyo mashi Madara tana dariya tace ina ruwan sabon Baba, ce ma Fatun tay ta fiddo breast d'in aga in milk d'in ya zo tace to, bayan ta fiddo tasata ta matsa ba ruwan sai yellow d'in farko tace ta bashi ya sha ruwan zai zo, koya mata yadda ake ruk'on babyn in za'ai feeding ta shiga yi Fatun nata murmushi yayin da take jin wani iri daya kama sosae yake sha Aunty na mashi tsiya tana fad'in duk da suruki ne ta wani bangaren, suna haka aka tura kopar a tare suka kai idanun su wajen Jidderh ce ta fad'o cikin d'akin da sauri su twins na biye da ita suna ganin su Fatun suka nufo su da d'an gudu gudu daga baya Mom ta shigo Dad da Haisam na biye da ita duk suka nufo gadon, tsaye duk sukai a gaban gadon da sauri Fatuu ta maida breast d'in nata ganin su Dad tuni Jidderh ta d'aukko Hussein su Yasmeen da twins duk suka mik'a ma Fatuu hannu suna yar rige rigen wanda zai amshe shi sai dariya ake ganin d'aya yak'i hak'ura a ba d'aya yasa Aunty saka baki tace su bi a hankali kowa zai d'auka, gaishe da Dad Fatuu tayi yana ta faffad'an murmushi ya amsa tare da Fad'in "Sannu, sannu da kokari Daughter" kai ta jinjina mashi tana ta murmushi Mom ma tayi mata sannu da tambayar jikinta tace lafiya lou, had'a ido sukai da Haisam suka shiga yi ma juna murmushi Mom data k'agara ta d'auki jaririn ta mik'a ma Jidderh hannu tana fad'in tunda ta gani ta kawo,
"Ma sha Allah lakuwwata illa billah, Yanzu Daughter da kanki kikai wannan aiki?" Mom ta tambaya idanunta akan Fatuu tay murmushi kawai Aunty tace "ai gaskiya tayi kokari wllh" jinjina kai Mom tayi ta furta sosae kafin tace amman saida aka k'arata wannan ko Aunty tace a'a har saida fuskarta ta nuna mamaki ta shiga k'ara yi ma Fatuu sannu fuskarta d'auke da murmushin farinciki haka Dad ma sannun yake ta ma Fatuu, gaba d'aya kowa tsantsar farinciki ne akan fuskokin su kai kace ba'a ta6a yi masu haihuwa ba duk da dai an d'auki lokaci ba'ayi ba gashi wad'annan ne jikokin Farko, sai faman k'arba k'arba ake tsakanin yaran Jidderh ma sai sannu take ma Fatun, Dad ne ya tambayi an saka masu suna Aunty tace eh ta fad'i mashi har saida ya d'an waro ido alamar mamaki,

"Wannan dad'in bai mana yawa ba kuwa?" Dad ya fad'a idon shi akan Haisam dake murmushi ya k'ara fad'in "Son banda son kai fa halan kai ne ka zabi sunan gaba d'aya?" Kai ya d'an girgiza calmly yace shi ne ya za6i nashi ita kuma ta za6i na grandpa, kallon Fatuu Dad yay tana murmushi ya furta "Daughter in akai haka bamu so kan mu da yawa ba kuwa karfa ayi kura da shan bugu gardi da k'wace jaka" gaba d'aya aka saka dariya a hankali tace a'a ai duk d'aya ne duk suka jinjina kai Dad harda yin godiya ya tambayi waye abokin nashi waye kuma Baban nashi duk aka nuna mashi Aunty tace sun kasa gane yadda zasu bambance su shiyasa suka bambanta masu kaya dama fin set biyu ta d'aukko wai ko zata haifi fin biyun duk akai dariya, jin haka yasa Momy ta fara k'ok'arin duba su taga ko zata samu abunda za'a rink'a Gane su, tunawa tayi da yadda ake gane ta ita da Mom d'in Sameer hakan yasa ta k'ura ma na hannun Dad wanda ta bashi wato Aliyu ido tana kallon idon shi dake a bud'e dama tunda Jidderh ta sunkuce shi yana bacci ya farka sosae ta k'ura ma idon nashi ido harda d'an bud'awa taga k'wayar bata ciza ba sosae ta d'an yi brown, juyawa tay kan d'ayan dake a hannun Affan shima ta shiga dubawa sai gashi tashi bak'a ce wuluk tana ganin haka ta d'ago tana dariya ta fad'i masu suma ga yadda za'a rink'a bambanta su duk saida suka ji mamaki ganin abu yazo d'aya suka shiga fad'in ikon Allah, Addu'oi Dad duk yayi masu bayan ya gama ya tambayi an fad'i ma su Hajiya Aunty tace a'a Saboda ba waya yace Ok bari ya sanar mata, Lokacin da kiran ya shiga bata dad'e da tashi daga kan abun salla ba ta koma ta kwanta bayan ta d'auka cikin girmamawa ya gaida ta tare da tambayar yadda take tace mashi Alhamdulillah kafin ta ce kiran sassafe mai tattare da abu biyu Alkhairi ko akasin haka tana fatan Alkhairin ne yasa aka kirata Dad dake dariyar Maganar tata yace eh Alkhairi ne dama zai sanar mata ne tayi Ya'ya yan samari amman d'aya a ciki kuma miji ne Daughter tayi mata tana jin haka ta fahimci zancen, cikin washe baki ta hau fad'in ma sha Allah Fateema Allah yayi an sauka kenan, tambayar lokacin da akai haihuwar tayi ya fad'i mata yace gasu ma a Asibitin ko sallamarta ba'a kai ga yi ba ta kara tambayar to ya jikinta nan ma yace lafiya lou take bari ya bata ya mik'a ma Fatun cikin murmushi ta gaishe da Hajiya tace "Fateema yau ai ni ya kamata in yi gaisuwa nida aka Haifa ma sabon miji, to barka, barkanmu da Arzik'i Fateema, sannu da k'ok'ari Allah ya k'ara maki lafiya ya raya mana ya kuma Albarkaci rayuwarsu" kaman bazata amsa ba sai kuma can k'asan mak'oshi ta amsa Kafin ta tambayi yaushe zata taho tace ai don yau ta riga tayi da ta taho amman gobe in sha Allahu tana nan tafe ai bata zauna ba wannan abun Arzik'in ya samu, bayan sun gama wayar tana niyyar mik'a ma Dad Jidderh tayi karaf ta amsa ko gaida Hajiyar bata yi ba ta hau zuzuta mata kyaun jariran da kuma girman su Hajiyar nata fad'in Ma sha Allah Tubarkallah kafin a k'agare tace mata tayo mata Vedion su yanzun nan ta gani da sauri tace to, bayan Hajiya ta gama wayar Gwaggo ta shiga kira lokacin itama bata dad'e da komawa ta kwanta ba wayar ta fara ringing koda ta d'aukko ganin mai kiran saida gabanta ya d'an fad'i, d'auka tayi da sallama Hajiya ta amsa tun kafin gwaggon ta k'ara cewa wani abu tace "to barkan mu da Arzuki Fateema dai Allah yayi ta sauka lafiya an samu yan samari" ba shiri gwaggo ta tashi zaune cikin washe baki take ta fad'in Alhamdulillah daga baya tayi Addu'ar Allah ya raya ya Albarkace su Hajiya ta amsa tace ai ita gobe in Allah ya kaimu ma zata tafi don harda maigida a ciki ta fad'i mata sunayen su Gwaggo tace ah lallai yakamata ta tafi da wuri ta tarbi sabon maigida tayi Maganar tana dariya, suna gama wayar ta fito ta nufi d'akin Mino har ta koma bacci tsabar farinciki ta tasheta ta fad'i mata zo kaga murna don wani kalan wuntsilowa tayi daga kan gado ta duk'a k'asa tayi sujjadar godiya ga Allah don kullum damuwarta itace yadda Adda Fatuu zata haihu, da gudu ta fito ta nufi d'akin Kawu Amadu shima har ya koma bacci ta fad'a d'akin tana faman kwad'a mashi kira aikuwa a fusace ya farka don tunda ta fara kiran nashi yana ji yayi shiru sai daga baya ya farka har zai rufeta da fad'a dama suna yawan haka duk aka aikota ta tashe shi ko kuma wata buk'ata tata kamar in tana son yayi mata Assignment, da sauri ta tari hanzarin shi cikin tsananin murna ta fad'i mashi Adda Fatuu ta haihu yan biyu duk maza nan take ya waro ido sai kuma ya washe baki, Bayan Hajiya ta kira gwaggo Hajiya Maryam ta shiga kira bayan ta d'aga ta gaishe da ita ta amsa kafin tace to tayi Ya'ya harda sabon maigida a ciki da rashin fahimta ta tambayi wani ya'ya ta fad'i mata itama ta nuna farincikinta ta yi Allah ya raya masu, lokacin da Haisam ya kira Fanan ya sanar mata Kusan suk'ewa tayi don dad'i tace miyasa da ana labour d'in bai kirata ba sunyi tare yace mata ya rud'e ne, sawa tayi ya maida kiran Vedio call lokacin da taga yaran sai kawai ta fashe da kukan dadi baiwar Allah bata da burin daya wuce ta haifi yaro mai kama da Haisam ashe ba itace mai rabon hakan ba ta raya a ranta saidai sosae take farinciki don tana da yak'inin yaran zasu zama tamkar nata, gaba d'aya saida su Dad sukai mata barka ta cikin wayar tana ta washe baki take amsawa, kan kace mi duk an kira yan'uwa da Abokan Arzik'i an sanar dasu game da haihuwar anata ba Fatuu suna mata barka a haka ma don Wayarta bata a hannun ta, lokacin da gwaggo ta kira Aunty Mareeya ta sanar mata Fauzy na cikin yin shirin Makaranta Aunty tazo d'akin nata cikin tsananin farinciki ta sanar mata har saida ta daka wani uban tsallan murna tana ta faman fad'in Wayyo Allah da Alhamdulillah, kiran layin Fatun suka shiga yi ba'a d'aga ba Aunty tace k'ilan bata tare da wayar ne gaba d'aya Fauzy a k'agare take da suyi magana Haisam ya fad'o mata a rai gashi kuma bata da lambar wayarta shi tunowa tayi da tana da Lambar Jidderh to itama data kira ba'a d'aga ba don ta bar wayarta a gida,, zuciyar ta ce ta bata ta kira Sameer sai ta tambaye shi lambar Haisam d'in, bayan ta kira saida ta yanke sannan ya kirata, gaida shi tayi kafin tace mashi don Allah lambar Haisam take so farko shiru ya d'an yi sai kuma taji ya tambayi mi zatai da shi a tunanin ta yasan da haihuwar tace mashi tanata kiran layin matar shi ne tayi mata barka to bai shiga shine take son ta kira shi sai ya bata, tambayarta yayi barkan mi zata ma wife en nashi nan ta gane bai san da haihuwar ba ta fad'i mashi yace bai sani ba Allah ya raya, karanto mata lambar yay tayi mashi godiya suna gama wayar ya kira Haisam d'in bayan ya d'aga sun gaisa Sameer d'in yace mashi tunda shi bai so yasan sun yi babies yaji wani wuri Haisam d'in na dariya ya bashi hak'uri yace baya tare da wayarshi ne bai dad'e da ya d'aukko ta daga gida ba ya tambayi ina yaje ya sanar mashi suna hospital ne yace Ok, tambayar lafiyar yaran da Mom d'in su yay Haisam d'in yace mashi duk suna cikin k'oshin lafiya bari ya maida Vedio call ya ga babies d'in nan ma Ok yace, bayan ya maida kiran Vedio nuna mashi yaran ya shiga yi Sameer na kallon shi yanayin fuskar shi da d'an murmushi daga baya yaba Fatuu suka gaisa yay mata barka, bayan Haisam ya amsa Sameer d'in na wani murmushin gefen baki yace Babies d'in sun bayyana he's very active shiyasa sukai Kamannin shi Haisam d'in yay murmushi kawai don su Mom na wurin gudun kada ya k'ara fad'in wata Maganar yasa shi saurin ce mashi ga su Mom yayi masu barka, suna gama yin wayar da Sameer kiran Fauzy na shigowa Haisam ne ya d'auka bayan sun gaisa tayi mashi barka sannan ta fad'i mashi ko wacece ya mik'a ma Fatuu, cikin tsananin farinciki suka yi mata barka harda Aunty suma harda Vedio call suka ga yaran lokacin da Fauzy ta gansu murna kamar kamar me, haka dai akaita yin waya dasu ta wayar Haisam d'in har su gwaggo suma ta nan suka kira, bayan kiraye kirayen wayar sun lafa Dad yace ma su Yasmeen su tashi ya tafi dasu suyi shirin School tun kafin ya rufe baki Mubeen da Mubeena suka tur6une fuska cikin shagwaba suka hau rok'on a k'yale su yau ba sai sunje ba suna Welcoming Babies d'in su Mom tace to ba Babies na nan ba ko sun dawo zasu gansu, da k'yar suka tashi zasu bi shi Jidderh ma ta mik'e zata bi su don akwae abunda take son yi a gidan kafin a sallamo Fatuu, bayan tafiyar su Mom tace bari ta kira Iya a d'aura ruwa Aunty tace a'a tana ganin ba sai anyi wannan ba don bp d'in Fatun ya d'an hau so bata buk'atar ruwan zafi sosae yanzu lafiya lou in sun koma zata iya amfani da na heater zuwa bp d'in ya daidai ta duk da haka ba ruwa masu zafi zata rink'a amfani dasu ba Mom tace Ok kafin cike da kulawa ta kalli Fatuu tace maijego mi take son a dafa mata ne Fatun tayi murmushi kawai gaba d'aya idanunsu na akanta harda Haisam wani irin son ta ne ke mashi yawa a jini jiki, Aunty ce tace a yanzu dai ai tasan zata fi buk'atar farfesu tace ma Fatun hakane ko Daughter ta d'aga mata kai still da murmushi a fuskar tata, masu aikin girkin gidan Mom ta kira ta basu umarnin kalolin farfesun da zasu yi..........

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

94

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

...........Wuraren k'arfe sha d'aya na safe aka sallami Fatuu saida Haisam yay ma su Nurse Haleema kyautar kowa dubu hamsin, a bayan Mota ta zauna ita da Aunty sai Mom ta zauna a gaba tana ruk'e da Adam Aunty kuma tana ruk'e da Aliyu, lokacin da suka iso gidan a bakin Entry Hall ya parker Motar duk suka bubbud'a kopopin suka fito, suna fitowa Iya ta fito daga cikin gidan ta nufo su cikin washe baki tana masu sannu da zuwa ta nufi Fatuu ta rungume ta tana fad'in "Barkan mu, Barkan mu yar gidan Iya, barka da Arzik'i" dariya Fatuu ke yi ta d'agota tana k'ara mata sannu da tambayar jikinta tace mata Alhamdulillah, juyawa tay kan Haisam daya zagayo hannun shi ruk'e da Jaka tayi mashi barka shima fuskar shi a sake ya amsa ta juya kan su Mom suma tana masu barkan duk suka amsa ta amshi jaririn hannun Aunty duk suka nufi shiga cikin gidan lokacin Dad ya fito cikin Fara'a yake masu sannu da zuwa shima ya amshi jaririn hannun Mom suka wuce, parlon tsaf dashi yasha gyara sai k'amshi ke tashi suka nufi part d'in su Fatuu, suna shiga cikin parlon Jidderh ta tarbesu cikin washe baki ta rungumo Fatuu tana k'ara mata sannu itama murmushi take mata, bayan sun shiga cikin parlon shima dai yasha gyara hatta labulaye an canza sai k'amshi yake tashi, ganin zasu zauna a cikin parlon yasa da sauri Jidderh tace ba anan zasu zauna ba pls su shiga ciki Mom ta tambayi Saboda mi tace Saboda Sis Fatuu ta kwanta ta huta suma babies d'in ta gyara masu gadon su a kwantar dasu suji d'umi duk sukai murmushi suka nufi cikin harda Dad da Haisam ta matsa mawa saida suka shiga, a tare duk sukai tsaye cakk bayan sun shiga suna k'are ma d'akin kallo daya canza suffa yasha decorations daya danganci jarirai irin su Baby photo frames da wall decals an mammanna su a wurare daban daban masu k'ayatarwa wasu hotunan bishiyu ne wasu flowers suna ta sakin k'yalli harda masu yin haske kala daban daban hatta gadon d'akin ma yasha gyara an shimfida sabon bedsheet milk a saman shi an watsa jajayen Flowers suma labulayen d'akin an canza su, daga jikin bangon da kan gadon yake wani Wall decal ne mai kaman d'an allo anyi mashi shape mai kyau jikin shi na d'auke da rubutu kamar haka _"Welcome to the world, little ones. May your life be filled with love, laughter and light. We love you"_ gaba d'aya yanayin d'akin yayi kaman nursery sai dai komai ya tsaru ba'a cika ba, gaban su Jidderh tazo tana murmushi tace ya suka ga decorations d'in gaba d'ayansu suka hau yabawa fuskokin su d'auke da faffad'an murmushi kowa ya hau yaba mata ana fad'in tayi k'ok'ari Dad yace Saboda wannan abun da tayi ko gaba da Dubai take son zuwa K'arin Karatu zai kai ta, jin haka da sauri ta nufo shi tay mashi side hug Saboda jaririn da yake ruk'e da shi tace "That's why I'm always proud of you lovely Dad, You're a Father like no other" fad'ad'a murmushin shi yay yayi pecking saman kanta tare da Fad'in shima yana Alfahari da ita a koda yaushe, sakin shi tay ta koma kan Haisam tana fad'in big brother ya kaga decorations d'in shima yaba mata yay ya jawota yay hugging nata, Aunty ce ta tambayi zasu iya zama a kan gadon ko su kwashe flowers d'in duk akai dariya Jidderh tace a'a a haka zasu hau su zauna Mom tace ma Fatuu ta hau suma duk suka zauna a baki, Addu'a Dad ya k'ara yi masu yayi ma Fatuu sannu Fuskar shi cike da annuri ya mik'a ma Mom shi kafin ya tafi Haisam kuma ya nufi kan bedside ya zauna, Iya dake ta faman washe baki ta mik'a ma Aunty na hannunta tana fad'in bari taje ta kwaso ruwan wanka dama tunda su Jidderh suka dawo taji an haihun ta d'aura tuni ma ya tafasa Aunty ta kar6i babyn tana fad'in anya wankan nan bata buk'atar ruwa masu zafi sosae Iya tace to lafiya lou sai a bari su sha iska sosae tunda akwae magunguna da zasu k'ara mata lafiya da ruwan nono a ciki yakamata tayi wankan dasu Auntyn tace mata to ta juya da sauri ta nufi hanyar fita, gaba d'aya Mom da Aunty da Jidderh idanun su na akan Babies suna ta kallon su suna sakin murmushin dadi yayin da Haisam da Fatuu keta kallon juna suna murmushi can Mom ta d'ago ta kalle shi tace "New Dad ya gajiyan labour" murmushi kawai yayi Aunty da itama ta d'ago tana murmushin tace "aikuwa kam ansha labour harda su Kuka" waro ido Mom tayi "kice labour d'in koke koke akai kenan",

yar dariya Aunty tay "eh to ba sosae ba ya d'an yi hawayen tsoron kada ya rasa Babyn shi" dariya Mom ta saka haka Auntyn da Jidderh ma Haisam d'in ma ya d'an fad'ad'a murmushin shi Fatuu kuwa da sauri ta sunnar da kanta tana murmushin jin kunya, kallonta Mom tayi tana fad'in ai gaskiya tayi kokari sosae wllh angode ma Allah daya sauketa lafiya ba wata matsala gaba d'aya suka jinjina kai Mom d'in ta tambayeta bata jin wani ciwo sai lokacin ta d'ago da murmushi akan Fuskar ta tace mata eh kawai jikinne take jin shi wani iri tace mata ai wannan dama dole ne tunda yara fa har biyu suka fita daga jikin nata a hankali zata ji ta koma normal ta d'aga mata kai, masu aikin Abincin gidanne mutum biyu suka shigo kowanne na sanye da apron bayan sun gaishe da su suka yi masu barka Aunty ta nuna masu bakin gado tace su zauna, bayan sun zauna aka basu jariran nan fa suka shiga yabawa fuskar kowannen su d'auke da Murmushi, tambayar su Mom tayi sun gama aikin data sasu a tare suka amsa da eh tace Ok in sun koma sai su kawo shi nan cikin girmamawa suka amsa mata da to, Iya ce ta fara shigowa da ruwan wankan ta wuce toilet, bayan ta gama ta tambayi Mom ta fara yi ma jariran ne tace a'a bari ita tayi masu ta kawo mata ruwan tace to, bayan ta kawo tace ma Aunty ga ruwan Fatuu can ta kai toilet tace to suje sai ta taimaka mata tayi wankan ta amsa da to, tambayar dami za'ai wankan tayi Aunty tace mata towel Jidderh ta mik'e da sauri tana fad'in bari ta d'aukko mata Mom ma tace ta had'o da kayan wankan babies d'in, kallon Fatuu Iya tayi tace to suje ayi wankan tace to ta fara k'ok'arin saukkowa daga saman gadon lokacin Jidderh ta kawo towel d'in k'arami da babba Iya ta amsa suka wuce toilet. Gaba d'aya idanun su harda Haisam na akan Babyn da Mom ta fara yi ma wanka sai tsanyara kuka yake Aunty na fad'in "haba grandpa yada kukan wanka kai fa babba ne" gaba d'aya suna ta dariya kawai sai ji sukai Fatuu ta saki k'ara itama daga cikin toilet d'in da sauri suka kai idanunsu kan kopar toilet d'in dake a rufe cikin d'an d'aga murya Aunty ta k'wala ma Iya kira daga ciki ta amsa tace mata Lafiya, bud'e kopar tayi ta lek'o tana yar dariya Aunty tace badai cika mata ruwan zafin akai ba ko Iya tace "Wllh Aunty basu da wani zafi daidai daidai ne tunda kince kar a cika" kai ta jinjina mata tace Ok hakan yayi kafin ta k'ara cewa asata ta zauna ruwan sosae tace to ta koma ciki, Mom dake yar dariya tace sai a k'yale grandpa yay kukan shi tunda ga maman shi can itama tana yi duk sukai dariya, mik'ewa Haisam yayi yana murmushi yace bari yaje Aunty dake kallon shi tace shima tunda Angon jegon ne ya tsaya yay wankan, yar dariya yay har hak'oran shi suka bayyana Mom tace "gaskiya kam haka yakamata tunda ya taya nak'uda wankan ma sai ayi tayi" still dariyar yake bai dai ce komai ba yay masu sallama ya tafi, bayan angama ma Fatuu tana d'aure da Towel ta fito ta yafo gyalen rigar ta a kai duk su Aunty suka kalleta suna mata sannu tana d'an murmushi ta amsa ta nufi gadon ta zauna Jidderh ta mik'e don ta d'aukko mata kayan shafa, bayan Mom ta gama yima jariran wanka Iya ta fidda ruwan ta dawo da garwashin gashin cibiya Aunty tace ai tayi zaton za'a basu magani ne kawai Iya tace gashin yafi, bayan Fatuu ta gama shafa mai tasa Jidderh ta d'aukko mata kayan da zata saka sabuwar doguwar rigar lace ce Jidderh tace bari tayi mata makeup tunda ita amaryar jego ce duk aka yi murmushi, yar light makeup tayi mata ta d'aura mata kallabi sai gata ta fito a Amaryar jego sosae tayi kyau tana ta sakin kamshi su Mom ma duk suka yaba kwalliyar lokacin Iya ta gama gashin Aunty ta fara shirya jariran, Mom da kanta ta zuba ma Fatuu Farfesun da aka kawo Kusan kala hud'u akwae na yan ciki dana kaza sai na kifi da kuma na nama mai had'e da ganda gaba d'aya sunyi gwanin kyau a ido sai sakin kamshi suke a ido kawai kasan zasu yi dad'i, kowanne saida ta zuba mata taci ta k'oshi suma suka ci har Haisam ma aka zuba mawa Jidderh ta kai mashi, bayan sallar Azahar aka fara zuwa barka haka ta waya ma anata kiran Fatun ana mata barka har su gwaggo ma sun k'ara yin waya harda Vedio call suka ga yaran kowa sai farinciki yake.

Da daddare bayan sallar isha gaba d'aya yan gidan harda Dad nan part d'in su Fatun suka zo lokacin tuni sunyi wanka tun da yamma Fatuu na sanye da doguwar rigar Atamfa haka yaran ma anshirya su cikin set na Overall ash sai hira ake kan su ana nishadi, anan falon nasu aka ci Abincin dare sai wuraren k'arfe goma sannan Mom tasa su Yasmeen suje su kwanta Saboda zuwa school da safe itama dasu Dad duk sukai ma su Fatuu saida safe ganin Jidderh bata tashi ba yasa Mom ce mata mi take jira ta tashi su tafe sai Allah ya kaimu kuma a dasa zaman jegon cikin yar shagwaba tace ita anan zata kwana, wani kallo Mom tayi mata tace to shi Habibyn ya kwana a ina da sauri tace ba ga part d'in shi can sama ba ita kuma sai ta kwana ta taya Fatuu raino Mom tace to bazata kwana ba in don raino ne shi ya tayata,

"wayyo Mom don Allah ki barni in kwana wllh banson in yi nisa da y'ay'ana, kuma ai da ana da cikin su nima ba a dakina take kwana ba to nima yanzu zan rama ma k'ura aniyarta ne" dariya Mom tayi tace wannan kuma ai ita tasa kanta ko, dole Mom tasata ta mik'e tace daga baya ta kwana amman yau ta k'yale su suyi rainon babies d'in su da kan su tana tura baki ta bita bayan sunyi masu saida safe, babba babba ne wato da alama Mom ta fahimci Haisam d'in na buk'atar ke6ewa da matar shi ko kuma tasan zai so hakan don tun bayan da aka sallamo ta d'akin bai kasance ba mutane ba, bayan fitar su Mom bin juna sukai da kallo suna murmushi ita dashi yana zaune akan side drawer jikin shi sanye da farin voile, mik'ewa yay ya nufi gadon ya zauna daga baki gefen Fatun still da murmushi akan fuskokin su cikin cool voice d'in shi ya furta "Mai jego" dariya Fatun tay kafin tace "Na'am Angon jego" shima dariyar yayi ya maida idanun shi kan jariran dake a nad'e suna bacci asaman gadon itama kai idonta tayi kan su suka cigaba da kallon su a tare kowa dad'i ya cika mashi ranshi can Haisam d'in yay sigh ya furta "I'm forever grateful ya Rabbi" yana rufe baki Fatuu ta furta "We're forever grateful our perfect Rabb" jinjina mata kai kafin ya k'arasa hayewa saman gadon ya kai hannu ya jawota jikinshi ya d'aura habarshi a saman kanta sukai shiru suna ta sakin k'ayataccen murmushi, a hankali taji ya tambayi ya jikinta ta bashi amsa da ba abunda ke mata ciwo ya d'aga kai, shiru sukai kowa yana jin sabon son dan'uwan shi na ratsa zuciyoyin su can ta d'aga kai ta kalle shi ta tambayi yaushe Aunty Fanan zata zo ya bata amsa da jibi ta jinjina kai, kasa janye idonta tayi suka zuba ma juna ido breathing dinsu na had'uwa, sun d'an d'auki lokaci a haka can ta hura mashi iska a ido ya d'an kikkafta idanun ta saki dariya shima yar dariyar yayi ya k'ara matseta a jikin shi tare da furta "I Love You Baby, I don't even know how to tell you how much I love you" d'aga ido tay ta kalle shi tare da kashe mashi ido d'aya cikin wani irin salo ta furta "I can't get enough of Your love Hubby" tana rufe baki kawai sai gani tay ya had'e lips d'in su, da alama dai Fatuu har ta manta da nakudar da tayi shiyasa ta biye mashi, sun d'an d'auki lokaci a haka kukan jaririn daya karad'e d'akin ne ya dawo dasu hayyacin su da sauri suka saki juna suna dariya Fatun nata fad'in yanzu fa bashi kad'ai keda lokacin ta ba ya k'ara fad'ad'a dariyar tashi, Adam ne ya farka yana kukan tare da kai hannu baki yana tsotsa alamar yunwa yake ji, daukko shi tay ta shiga kiciniyar feeding nashi ganin haka yasa Haisam cewa ko ya taimaka mata tace eh ya kai hannu ya ruk'e mata shi, nursing pillow dake a ajiye gefe da d'azun tayi amfani dashi ta d'auko har ta iya yadda Aunty ta nuna mata bayan ta daidaita shi ta fara feeding d'in nashi sosae ya kama yana sha Haisam yay k'uri yana kallon shi can ya kalli Fatuu da alamun mamaki yace k'arami dashi yana shan abu haka ta saka dariya ta shiga bashi labarin yadda tun a Asibiti ya fara sha da tsiyar da Aunty tayi mashi, yana cikin sha d'ayan ma ya farka yana kuka Haisam ya tambayeta shima ko yunwa yake ji tace k'ilan yace to yanzu ya za'ai ga wannan na sha yadda yay Maganar har saida ya bata dariya tace ya d'auke shi wannan ya gama yace Ok ya k'arasa hayewa gadon ya d'aukko shi, yana d'aukar shi yayi shiru ya shiga mamular hannu idanunshi ya bud'e su sosae yana kallon Fuskar Haisam da shima kallon shi yake yana mashi murmushi, saida Adam d'in ya gama suka yi musaya ta amshi Aliyun, ganin yadda shima yake sha sosae yasa Haisam d'in ce mata anya zata iya shayar dasu duka kuwa, tana dariya tace mi zai hana ba ita ta haife su ba yace to amman in suna sha haka ai zata rame sosae tace a'a indai tana ci tana k'oshi lafiya lou, shima saida ya k'oshi sannan ta cire shi bayan ta goge mashi bakin shi da d'an towel mai taushi ta fara kokarin canza masu diaper d'in jikinsu kamar yadda Aunty tace kar ta bari su kwana dasu, koda ta cire basuyi komai ba dama ruwan zamzam ake basu amman duk da haka saida ta canza komai da zata buk'ata na daga gefenta cikin dresser dinsu mai kyau, bayan duk ta canza masu ta feshe su da turaren su ta maida komai, ganin ta kwantar dasu a kan gadon yasa Haisam ce mata ba ga gadonsu nan ba tace tunda dare ne gara ta kwantar dasu nan koda zasu tashi da daddare yace Ok, gaba d'aya bin yaran sukai da kallo suna masu murmushi su kuma duk sun k'ura masu ido sai kace sun san su waye su abun gwanin sha'awa, sun d'an d'auki lokaci a haka kafin Haisam ya kalleta yace yasan bata rasa jin yunwa ko tace a'a bata jin wata yunwa ai taci Abinci sosae da daddaren nan kawai tea take so zata had'a tunda ga kayan nan yace Ok bari ya had'a mata ya tashi tana ta kallon shi da murmushi ta furta "You're the best husband ever" k'ayataccen murmushi ya saki tare da furta mata thanks, tea mai k'auri ya had'o mata da kanshi ya rink'a bata tana sha bayan ta gama shima ta matsa mashi saida ya had'a duk da yace mata a k'oshe yake, bayan sun gama ya tambayeta akwae abunda zai taimaka mata yana son yay wanka tace a'a yaje yayi kaya kawai zata canza, a tunaninta a nan zai wankan sai taga ya nufi k'opa yace mata bari yaje sama yayi sai ya dawo tace to, bayan fitar shi mik'ewa tayi har zata tafi ta tuna wani abu ta koma kan gadon, Addu'oi ta shiga yi masu tana tofa masu Adam har ya koma bacci sai Aliyu ne idon shi biyu tana murmushi tace mashi Mom zata je tayi shirin kwanciya ta dawo sai kace yana gane abunda ta fad'a yay mata k'uri da ido, wurin kayanta ta nufa ta fara cire kayan jikinta bayan ta gama ta d'aura towel saida ta dauki pad da pant da zata canza sannan ta nufi toilet bayan ta yafa gyale a saman kanta, bata jima sosae ba ta fito ta koma wurin kayanta, shiryawa tay cikin bakar nursing nightgown ta d'aura brown robe a sama ta saka hula akanta bayan ta gama shiryawa ta nufi gaban mirror kallon kanta ta shiga yi tana fesa turare a cikin ranta take raya wai yanzu nan ita mai jego ce tana ta murmushi har ta gama ta juya ta nufi gado shima d'ayan har ya koma baccin, hayewa tay taja duvet ta lullube su tare da kai hannu ta rungumosu su duka, bayan wasu mintuna sai gashi ya dawo shima yayi shirin kwanciya sai zuba k'amshi yake, saida ya rufe k'opar d'akin sannan ya nufi gadon ta d'ago tana kallon shi ya kunna lamp kafin ya nufi switch ya kashe hasken d'akin sannan ya nufi gadon, ta d'ayan bangaren ya hau ya fara yin Addu'a bayan ya gama ya d'an tufa bangaren su Fatun da jikinshi sannan ya kwanta yana facing Fatun ta d'an hasken da ke akwai ya hangota tana mashi murmushi shima ya fara yi mata daga baya bacci ya kwashe su.

Washe gari talata bayan la'asar Hajiya ta iso, Haisam ne yaje ya d'aukko ta a Airport, bayan sun iso gidan gaba d'aya duk suna a part d'in mai jego Hajiya ta nufi can shi kuma Haisam ya nufi part d'inta don ya kai mata kayanta, suna zaune a falo harda mai jego har sunyi wankan yamma tana sanye da half gown ta sabuwar atamfa golden tayi yar kwalliyarta ta fito fess haka yaran ma duk anyi masu wanka an saka masu kaya iri daya light blue abun saidai ace Masha Allah d'aya na hannun k'awar Mom da tazo barka d'ayan kuma na a hannun d'iyarta wadda k'awar Jidderh ce dama tun d'azun aketa zuwa barka harda Abokan Dad ba'a ma dad'e da maido yaran ba daga part d'in Dad d'in harda kyautar kud'i aka yi masu, Hajiya na yin sallama gaba d'aya su twins dasu Yasmeen suka nufota da gudu suna fad'in "Oyoyo Granny" duk suka k'ank'ame ta Jidderh ma ta taso ta nufota tana mata Oyoyo, Hajiyar na dariya tace ma su Twins sai sun karyata tun bata ga sabon angon nata ba salon yace bai sonta duk suka d'ago suna dariya tace su shiga ciki, mik'ewa Mom da Aunty sukai suna mata sannu da zuwa tana amsawa ta nufi kujera ta zauna su twins d'in ma duk suka zauna a kusa da ita sun shishshige mata, zama su Aunty sukai suka shiga gaishe da ita tare da yi mata an zo lafiya K'awar Aunty ma ta gaishe da ita tare da yi mata anzo lafiya haka d'iyarta ma, Mom ce ta amso Babyn hannun Friend d'in tata ta kawo ma Hajiya Jidderh kuma ta amso na hannun d'iyar matar k'awarta ta zo gefen Hajiya dashi tana nuna mata, bin su da kallo Hajiya tay fuskarta d'auke da fara'a ta shiga fad'in Ma sha Allah, mik'ewa K'awar Mom tayi tay masu sallama tare da yi ma Hajiya barka suka tafi Mom ta rakasu, juyawa Hajiya tayi ta kalli Fatuu dake d'an murmushi tace "Sannu da kokari Fateema, sannu kin dai yi aiki ba kad'an ba wllh yara haka Tubarkallah, to Allah ubangiji ya raya mana ya Albarkaci rayuwar su kema ya k'ara maki lafiyar shayarwa" gaba d'aya harda su twins suka had'a baki wurin amsawa da Amin,

"To ni bansan wanene sabon Angon ba bansan waye kuma d'an ba a cikin su a bambance man" Hajiya ta fad'a da fara'a, gaba d'aya su Jidderh suka zuba masu ido suna kokarin bambanta mata saidai duk sun kasa Saboda duk bacci jariran ke yi balle su bambance su ta ido sai faman canki canka suke abun ma sai ya zama abun nishad'i Aunty nata dariya don ita tasan kowanne Saboda tare da Mom suka kaisu wurin Dad haka lokacin da za'a maido su ita Dad ya kira taje ta amso su tare da Yasmeen lokacin Jidderh bata a d'akin tun lokacin ta ruk'e Adam aka ba k'awar Mom sai d'iyarta aka bata Aliyun, ita kanta Yasmeen da suka amso su tare duk ta rud'e ta kasa bambanta su, Hajiya sai faman dariya take tana fad'in lalle ashe aiki ne tantance su, Haisam ne ya shigo Hajiya ta d'aga kai ta kalle shi tace "to kai Baban su sai kazo ka bambanta man su tunda duk sun kasa" murmushi yay kawai ya nemi kujera ya zauna tace ya zai zauna ko shima bazai iya banbance su bane ya d'aga mata kai alamar eh kafin cikin cool voice d'in shi yace duk suna bacci dama ta ido ake gane su, jinjina kai Hajiya tayi tace shima kenan sai ta idon zai iya gane su ya d'aga mata kai,

Aunty dake ta dariya tace to a tambayi Mom d'in su k'ilan ita ta gane su duk aka maida kallon kan Fatuu dake murmushi Hajiya tace tazo ta bambance mata su, mik'ewa tay ta matsa kusa dasu ta d'an sunkuya tana kallonsu, ta d'an d'auki lokaci kafin ta d'aga yatsa ta nuna na hannun Hajiya tace shine Hajiyar ta tambayi shine wa tana yar dariya tace Angonta,

"To wa zai tabbatar mana in daidai ta canka" Hajiya ta tambaya tana dariya Aunty tace daidai ta canka shine Hassan d'in don ta ruk'e tunda suka kaisu wurin Dad, da sauri Jidderh tace "Sis Fatuu ya akai kike gane su don Allah?" gaba d'aya akai dariya Hajiya tace tunda koda yaushe tana tare dasu tana k'are masu kallo dama zata iya samun abunda zata rink'a banbance su, duk su Yasmeen suka hau rok'on ta nuna masu yadda suma zasu rink'a gane su, nuna masu girar Adam d'in tayi tace tanan ta gane shi don zanen tashi ya d'an fi lankwasawa kad'an aikuwa duk suka maida idanun nasu kan su harda Hajiya Aunty ma ta taso daga kujerar ta tazo don ta gani sai gashi sun ga hakanne amman sai mutum ya natsu sosae zai gane, Mom ce ta dawo d'akin tana d'auke da madaidaicin tray an d'auro ruwa da lemu da glass cup Dad na biye da ita, ganin suna ta dariya yasa ta tambayi ya akai Aunty ta bata labari Dad yay dariya yace shima in dai ba idon su biyu ba bazai gane ba, zama yay kan kujera ya d'an sunkuyar da kai ya gaishe da Hajiya tare da yi mata anzo lafiya bayan ta amsa yace bai gidanne sun fita tare da bak'i tace ba komai sai kuma tayi mashi barka, saman c-table Mom ta d'aura tray din tace ma Hajiya a kawo Abinci anan ne tace mata a'a bata jin yunwa yanzu, hira suka shiga yi cike da nishad'i ana haka jariran suka farka daga bacci nan suka k'ara tantance su ta idon su, sai da akayi sallar Magrib sannan duk suka tashi don zuwa yin salla.

Washe gari wuraren k'arfe sha biyu na rana Fanan ta iso tare da Nameer suma Haisam ne yaje ya d'aukko su daga Airport tana sanye cikin brown coat dress tasa yar bak'ar himar sosae tayi kyau Nameer ma na sanye da k'ananun kaya jeans da t-shirt, gaba d'aya Fanan a k'agare take da taga jariran da suna hanyar zuwa gidan sai faman zumud'i take tana ma Haisam tambayoyi game dasu Nameer nata mata dariya, lokacin da suka isa ma'aikatan gidanne suka zo suka d'auki kayan su tare da yi masu sannu da zuwa suka nufi ciki, ba kowa parlon Fanan ta tambayi Haisam inda Fatun take ya nuna mata ta nufi part d'in da sauri shi kuma Haisam da Nameer suka tsaya don ganin an shiga da kayan nasu, lokacin da ta shiga parlon ba kowa hakan yasa ta nufi Bedroom d'in, Mom da Aunty sai Hajiya ne a ciki yaran gidan duk suna Makaranta Fatuu na a zaune tsakiyar gado tana sanye da doguwar rigar shadda tayi daurin kallabi mai kyau haka yaran ma suna sanye da fararen kaya suna bacci daga gefenta, da Sallama ta shiga duk suka kai idanun su kanta ta shiga ganin itace yasa gaba d'aya suka shiga yin murmushi harda Fatuu ta nufi gadon da sauri ta zauna a baki idonta akan yaran ta shiga sakin faffad'an Murmushin dad'i harda d'an yarfa hannu, saida ta gama kallon su sannan ta juyo tana gaishe dasu Mom Hajiya tace wato saboda zumud'in ganin yaranta sai yanzu zatai lokacin su tana yar dariya tace a'a, anzo lafiya suka yi mata ta amsa kafin duk suka yi mata barka tana ta washe baki idonta akan yaran take amsawa Fatuu ma ta gaishe da ita ta kalleta bayan ta amsa tace "Sannu sis, sannu da k'ok'ari don Allah. Look at them, very cute wllh" dariya kawai Fatun ke yi haka su Mom don gaba d'aya ta rud'e da ganin yaran, su Haisam ne suka shigo Nameer ya nufi gefen Hajiya ya zauna tare da gaishe da ita ta dafa Shoulder d'inshi tana mashi an zo lafiya bayan ya amsa ya gaishe dasu Mom suma duk suka yi mashi anzo lafiya, Hajiya ce tace mashi shi bai ga yaran nashi ba ya juya yana kallon su fuskar shi d'auke da Murmushi yace "Ma sha Allah, Allah ya raya mana su" gaba d'aya aka amsa da Amin, ganin yadda Fanan ta tsura masu ido yasa Hajiya tace to ta d'auke su mana da sauri tace "No, suna hutawa a k'yale su suyi baccin su in sun tashi na d'auke su suga Mom d'in su" Hajiyar tace to mai y'ay'a duk akai dariya, shiru Fatuu tay kamar mai tunanin wani abu idonta akan Fanan dake ta kallon yaran tana murmushi can ta kai hannu ta d'aukko Aliyu wato Hussein dake a kusa da ita hakan yasa Fanan kallonta kawai sai gani tay ta Mik'o mata shi tana d'an murmushi, kallon rashin fahimta ta bita da shi haka ma su Hajiya duk idanun su na akan su,

"Aunty Fanan gashi, na baki shi ",
da k'yar ta furta Maganar, d'an yamutsa fuska Fanan tay cikin d'aurewar kai tace "I..I don't understand you Sis Zarah", saida Fatuu ta had'iyi abu kafin tace "dama na fad'i ma Ya Haisam cewa in na haihu zan baki Babyn koda kuwa d'aya ne sai gashi Allah yasa na haifi biyu shine na baki d'in, Aunty Fanan wllh na baki shi har abada ga su Hajiya nan inason su zama shaida shiyasa nayi hakan a gaban su" da k'yar ta k'arasa Maganar Saboda karyewar da muryarta tayi, hannu Fanan ta kai da sauri ta rufe bakinta alamar Al'ajabin Maganar don abu ne da bata tsammaci ji ba, bin juna sukai da kallo ita da Fatun lokaci guda idanun Fanan suka ciko da k'walla cikin rawar murya ta furta "Yanzu Sis Zarah kina nufin duk wahalar da kika sha ta rainon cikin shi da kuma haifuwar shi kin bani shi ya zama nawa har abada?" Kai Fatuu ta jinjina mata itama idanunta sun ciko da k'walla kawai sai ji sukai Fanan d'in ta fashe da kuka itama Fatun k'wallan ne suka fara zubo mata gaba d'aya sun karya ma kowa zuciya can Fanan ta kai hannu ta karbe shi ta bishi da kallo tana murmushi,

"Ban ta6a tunanin wani zai man irin wannan kirkin ba a rayuwata har na rasa mi zan ce ma" cikin muryar kuka tayi Maganar tana kallon su Hajiya dake mata d'an murmushi, maida idonta tayi kan Fatuu bayan ta goge k'wallan tace "All i can say to you is thank you. Thank you so much for your generosity Zarah. You have shown me a kindness that I will never forget. Never" ta k'arasa tana jujjuya kai alamar tabbatar mata da abunda ta fad'a, jinjina kai Fatuu tay tana goge kwallanta gaba d'aya sauran Mutanen cikin dakin sunyi shiru suna bin su da kallo, mik'a mata Babyn tayi bayan Fatun ta amsa tana murmushi tace "Ba sai kin bani shi ba Zarah, We're one Family so duk abunda d'aya ya mallaka tamkar na kowa ne, I'm I right?" Da sauri Fatuu ta jinjina mata kai alamar eh Fanan d'in taci gaba "Gud, ko baki bani shi ba gaba d'ayan su yarana ne kuma in sha Allah zamu raine su mu basu tarbiya mai kyau tare" atare gaba d'aya aka had'a baki wurin furta "Allahu ya sha" Fanan tay d'an murmushi tace Ameen, Hajiya ce ta d'an yi gyaran murya duk suka maida idonsu kanta a nutse ta fara magana tace wannan abun daya faru babu wanda ya kai ta jin dad'i wllh, Fateema itama tayi abunda da k'yar a samu wadda zata iya yin hakan ga abokiyar zamanta kamar yadda itama Fanan d'in tayi gaba d'aya suka jinjina kai, kallon Haisam tayi tace "ina son ka sani duk Wannan sadaukarwar da suke Saboda son da suke maka ne hakan yasa duk suka fifita farincikin ka fiye da nasu don haka ina k'ara jan hankalin ka da ka k'ara jajircewa wurin ganin ka ruk'e su da amana ka kyautata masu, kaima ka fifita farincikin su fiye da naka don kuwa ba K'aramin dace kai ba wllh ka k'ara gode ma Allah, samun mata irin wannan a zamanin nan da muke ciki ba zan ce babu irin su ba amman ina mai tabbatar maka da samun su da wahala don koda mata suna son miji zaka ga basu damu da Farincikin shi ba Saboda haukan kishi kullum cikin tada mashi hankali suke a haka kuma wai don ana son shi ne, ina rok'on Allah daya k'ara had'a kan ku ya Albarkaci rayuwar ku gaba d'aya ya k'ara shirya mana ku ya kuma k'ara rufa mana asiri fiddunya Wal akhira yasa mu gama da duniya lafiya" a tare gaba d'aya suka amsa da Amin fuskokin su d'auke da Murmushi ta juya kan su Fatuu ta k'ara masu Nasiha kan su k'ara had'a kan su ta nuna masu hakan da suka za6ar ma kan su shi yafi masu Alkhairi don ko ba komai zasu kasance a cikin farinciki suma su cigaba da kyautata ma mijin su hakan shine kishin daya dace, sosae tayi masu Nasiha mai tsuma jiki duk fuskokin su d'auke da d'an murmushi suke jinjina mata kai, bayan ta gama dasu ta juyo kan Nameer dake manne da ita ta kai hannu cikin sumar shi tace "na dawo kan ka mage sarkin son jiki ko kuma in ce mazuru...." Gaba d'aya aka saka dariya, taci gaba "Allah kaima ya nuna mana bikin ka lafiya kaida yar fillon taka duk da dai ina jin ki shi" tay Maganar tare da d'an kwa6e fuska duk ta basu dariya, hira suka cigaba da yi gwanin sha'awa saida aka yi sallar Azahar duk suka tashi Fanan anan tayi sallar tun tana cikin yi yaran suka tashi suna kuka tana sallamewa ta taso ta nufo gadon tana tambayar mike damun su suke kuka Fatuu dake murmushi tace mata k'ilan yunwa suke ji tace to tay feeding nasu ta daina bari suna yin kuka pls yadda tayi Maganar har saida ta ba Fatuu dariya, ita ta taimaka mata ta fara shayar dasu saida duk suka k'oshi sannan Fanan ta d'auke su gaba d'aya tana masu wasa tana fad'in ga Mom d'in su tazo duk sukai mata k'uri da ido sai kace sun san mi take cewa sai faman saka Fatuu dariya take.

Bayan Fanan ta koma d'akin Laila dama anan take sauka in tazo gidan ta shiga kiran Mom d'inta wato Hajiya Maryam, bayan tayi picking suka gaisa tayi mata anzo lafiya Fanan d'in ta amsa mata tace ai tayi zaton zata tsaya Lagos ko duk murnar sunyi Y'ay'an ce tasa bata biya ba Fanan na dariya tace mata Kusan hakane ta k'agara da ta gansu gashi tare da Nameer suke tace to, "Mom you know What?" Fanan ta fad'a Mom d'in tace mata a'a mi akai, labarin abunda ya faru tsakaninta da Fatuu ta shiga bata yadda ta d'auki d'aya daga cikin yaran ta bata kyauta, d'an ta6e baki Hajiya Maryam d'in tayi tace mata in duk cikin salon neman wurin zama ne fa da sauri Fanan tace mata Wallahi har cikin zuciyarta ta bata don a gaban kowa akayi tace kuma su zama shaida, "to ce mata akai ke bazaki haihun bane?" Kai Fanan ta girgiza fuska a d'an yamutse tace "No Mom, kawai ta bani ne saboda k'aunata da take kuma taga ita ta riga haihuwan dama na fad'a maki wllh tana zaune dani da zuciya d'aya Mom, sam bata d'auke ni a matsayin kishiya ba" still bakin Hajiya Maryam d'in na a d'an ta6e tace mata to yanzu ita ta amshi yaron kenan tace mata a'a nan ta fad'i mata yadda sukai ta k'ara da cewa "nasan ko ban amsa ba bazata ta6a man iyaka da yaran ba so nima zasu zama kamar nawa ne kinga ko ban haihu ba na samu wanda zasu kira ni da Momy, don Allah Mom ki manta komai ki so Zarah sannan ki mana fatan Alkhairi" yar dariya tayi tace ita dama ai bata ce ta tsaneta ba tana masu fatan Alkhairi Allah ya k'ara had'a kawunan su itama kuma tana mata Addu'ar Allah yabata haihuwan, cike da jin dad'i cikin washe baki Fanan d'in ta amsa da Amin tare da Fad'in shiyasa take k'aunar ta Saboda she's a Mom like no other tana jiyo dariyar Hajiya Maryam d'in, tambayar yaushe zata zo taga Babies tayi tace mata tunda ita tana nan ba sai tazo ba, a shagwabe murya kamar zata yi kuka tace"Haba Mom, yanzu fa kika nuna man komai ya wuce kuma ai ni zuwana daban naki ma daban, don Allah ki zo, haka fa da biki kika k'i zuwa pls kizo hakan zai sa aga kin manta komai kuma ma yaran nan fa grandchildren d'in ki ne" tana dariya tace mata "to sarkin tsara zance wasa nike maki zan zo in sha Allah amman gaskiya sai Ranar suna don akwae kaya na da zasu iso ranar Asabar dole zan tsaya in ga isowar su" cike da Farinciki Fanan d'in tace to ba komai ai tunda zata zo d'in Allah ya kaimu Ranar lahadin harda tambayarta a cikin kayan da tayi Order d'in akwae na jarirai tace mata eh Fanan din tace to ta za6o ma Babies d'in su Unique ones masu yawa Hajiya Maryam d'in ta amsa da tunda ita ta bata kudin da ta siyo ko Fanan ta saka dariya, hira suka cigaba da yi Fanan bata tambayi Dad d'inta ba don tasan ta baro shi a America, kafin suyi sallama ta tambaye ta Farha tace mata tana d'akin ta k'ilan ko bacci take. Bayan sun gama wayar Farha ta shiga kira lokacin da tayi picking tana jin muryarta ta gane bacci take ta bata hakurin tashin ta da tayi tace mata ba komai, tambayar ta tayi tazo ne tace mata eh gata a Abuja nan ta shiga bata labarin irin kyawun Babies d'in da aka Haifa masu fuskar Farhar da d'an murmushi take sauraronta bayan ta gama tace Allah ya raya, tambayarta tayi zata biyo Mom tazo suna ko tace mata No, cikin sigar rarrashi tace mata don Allah ta manta komai ta d'auki Zarah matsayin yar'uwarta itama don tana da kirki sosae kuma tana k'aunarta, nan ta shiga bata labarin yadda ta bata kyautar Babyn da ta haifa tace in ba don tana kaunarta ba taya zata mata haka, daga k'arshe dai saida tayi nasarar shawo kan Farhar tace mata zata biyo Mom d'in nasu zo kaga murna a wurin Fanan.

Ranar Friday da rana Laila ta iso itama ta nuna farinciki sosae ganin yaran nan suka shiga shirye shiryen yin gagarumin suna, a ranar da daddare bayan sallar isha Haisam na zaune a parlon shi na saman bene yana operating laptop d'in shi jikinshi sanye da ash d'in jallabiya wayar shi tay k'ara alamar shigowar sak'o, hannu ya kai gefen shi ya d'aukko wayar ya shiga dubawa, bin sakon yayi da kallo bayan ya bud'e wanda credit alert ne na kud'i Naira miliyan d'aya da rabi daga Sameer, sam bai yi mamakin ganin kud'in ba duk da bai san na minene ba amman ba yau ya fara turo mashi kud'i ba don koda bikin shi da Fanan miliyan biyu ya bashi, fita yay daga cikin sak'on ya fara kokarin kiran Sameer d'in, saida ta kusa yankewa sannan ya d'aga suka gaisa Haisam d'in yace mashi suyi Vedio call ya furta mashi Ok, bayan ya maida kiran na gani Sameer d'in na zaune akan doguwar kujera a gidan shi dake a England wanda Company d'in su suka bashi, suma dare ne can har yayi shirin bacci yana sanye da robe da ta bayyanar da k'irjin shi wanda shima ke d'auke da kwantacciyar suma kamar dai yadda na Haisam yake, k'ara gaisawa sukai Haisam yay mashi ya aiki ya amsa da Alhamdulillah,

"Ya akai bakai bacci ba kai da kake gauro" Haisam ya fad'a yana murmushi Sameer d'in yay d'an guntun murmushin da iyakar shi lips d'in shi slowly yace mashi yana shan coffee ne Haisam d'in ya jinjina mashi kai suka d'an yi shiru kafin Sameer d'in ya tambayi ya Babies d'in su ya bashi amsa da suna lafiya, ce mashi yay yaga sak'on kud'i yanzu shiru Sameer din ya d'an yi kaman bazai ce mashi komai ba can yace mashi ya d'auki 1 million yaba wife en shi 500k yaran shi kuma a fad'i masu zai musu zuwa na musamman, murmushi Haisam yay yayi mashi godiya kafin ya tambayi bazai zo suna ba yace mashi yaso hakan amman aiki yayi mashi yawa amman yana nan zuwa bada dad'ewa ba Haisam yace Ok Allah ya taimaka ya amsa mashi da Amin, tambayar shi yay ina Amarya ya d'an ta6e baki ya bashi amsa da yanzu suka gama magana Haisam na murmushi yace abun nata matsowa Allah ya nuna masu can kasan mak'oshi Sameer ya amsa da Ameen suka dan k'ara yin shiru,

"Ina son zaka taimaka man da abu" Sameer ya fad'a Haisam ya jinjina kai tare da dan gyara zaman shi ya tambayi miye yace mashi dama yana son zai siya ma su bride d'in tashi gida ne, kai Haisam ya d'aga kafin ya tambayi to wane taimako yake son yayi mashi yace bai san taya zai yi hakan ba tunda shi ba sanin garin su yayi ba kuma bai san kowa ba so yana son ya bashi shawarar yadda za'ai Haisam yace ya yi Maganar da Fauzy ne ya girgiza mashi kai alamar a'a kafin yace yafi tunanin yin Maganar da wani babba ba ita ba, shiru Haisam yay alamar tunani can yace mashi ya bari zasu yi Maganar da Wife d'in shi sai ta kira Yayarta tayi mata Maganar Sameer d'in yace Ok zai jira shi ya fad'i mata in tayi ma Yayar tata Maganar tace mata su duba gidan da suke so mai kyau in za'a samu Haisam yace Ok, hira suka d'an k'ara yi yawanci duk akan bikin Sameer d'in ne daga baya sukayi sallama, suna gama yin wayar ya kira Fatuu lokacin suna zaune a Bedroom d'inta da su Aunty Laila anata shirya yadda za'ai suna, bayan tayi picking tambayar ta yay tana tare da mutane ne tace mashi eh yace Ok bari zai tura mata sak'o ta WhatsApp tace to, lokacin da ta karanta sak'on daya turo matan d'an waro ido tay alamar mamaki sai kuma ta hau yin d'an murmushi, sai wuraren k'arfe goma da rabi sannan duka aka watse daga hirar da ake a d'akin Jidderh ma da anan take kwana tace ma Fatun bari taje ta dawo, suna tafiya cike da zumud'i ta shiga kiran Aunty Mareeya, saida ta kusa yankewa sannan ta d'auka bayan sun gaisa ta tambayi twins Fatun tace mata k'ilan ma har tayi bacci ta tada ita ko tace mata a'a bata kusa da wayar ne, tambayarta ina Fauzy tay tace mata tana d'akin ta bata san ko tayi bacci ba ta tambayi ita zata ba wayar ne da sauri Fatun tace a'a dama sak'o ne aka bata da alamun d'an mamaki tace mata to waye ya bada sakon tace mata Sameer har saida Aunty ta maimaita sunan Sameer d'in kafin ta tambayi sak'on miye ya bada, bayanin da yayi Fatun tayi mata bayan ta gama da tsananin mamaki Aunty Mareeya ta maimaita abunda ta fad'a tace mata eh haka yace,

"Kinga Zarah wllh nama rasa mi zance maki tsabar Al'ajabi, yanzu duk uban hidiman da yake ma Fauziyya kuma harda wannan gingimemiyar dawainiyar Gida fa!" Dariya Fatuu tay jin yadda tayi Maganar tace " Wllh Aunty, yana da halin ne kuma k'ilan yana son canza gidanne Saboda bikin tunda kinga ba k'aramar hidima za'ai ba manyan mutane zasu zo" Aunty tace "hakane kam, dama muma munata shirin yin gyaran gidan don har an gama Magana ma da masu gyaran za'ai gyara sosae Saboda hakan yanzu kuma kinga ga Maganar da yayi ni bamma san to mi zan ce ba, amman abunda za'ai Zarah zan kira babban yayanmu sai muyi magana kan hakan tunda ma gobe zamu taho nan in muka zo komi mukai dashi zan fad'i maki sai ki fad'i ma Mijin naki" amsa mata da to Fatun tay tace Allah ya kawo su lafiya duk ta k'agara ta gan su wllh Auntyn na dariya tace suma bata ga yadda suka k'agara da su ganta ba amman sun fi k'agara da suka ga twins d'in su Fatun nata dariya Aunty Mareeyar ta k'ara cewa "ni kinsan abunda ma yafi damuna Zarah?" Kai Fatuu ta girgiza kafin tace mata a'a,

"Wllh abunda nike gudu kada sai mun zo munyi kayan d'aki suce basu so tunda kinsan Manyan nan yadda suke" kai Fatuu ta jinjina tace hakane kuma fa, Aunty tace wllh abunda take ta tunani kenan, shiru Fatun ta d'anyi kafin can tace mata to ko tayi ma Ya Haisam magana kan hakan da sauri Aunty tace "kice mashi mi Zarah! A'a kada kiyi mashi magana kan hakan kada kuma aga kamar so muke ace kada ayin, za'a yi mata komai iya karfin mu dama mun yanke za'a siya mata kayan ne kawai Babanmu ya yanke zai siyar da gonakin shi guda biyu sai a had'a da sauran kud'in da aka tanada in sha Allahu za'ai komai yadda yakamata" Fatuu tace Allah ya bada iko ta amsa da Amin,

"Ni kinsan ma abunda nafi so wllh shine in da zai yuwu da yaje Funtua sun gaisa dasu don duk fa ba wanda ya san shi in ba a hoto da aka nuna masu shi ba to kuma hakan nasan da kamar wuya tunda yanzu ma bai K'asar tun kafin ya tafi nayi ma Fauziyya Maganar kan tasa shi yazo sai ce man tayi wai ita gaskiya bata iyawa ni in yi mashi, to wai kar aga kai talaka ka zaqe yasa ban yin ba kuma ma dai nima nasan halin surukin nawa baud'add'e ne" Dariya Fatuu tasa Auntyn tace Allah kuwa yanzu dai ai sai kawai da biki sun gan shi, hira suka d'an k'ara yi kafin sukai sallama ta kira Haisam d'in tayi mashi bayanin abunda Aunty tace yace Ok Allah ya kaimu goben ya kawo su lafiya, cikin yar shagwaba ta tambayi yana ina yana murmushi yace mata gashi a part d'in shi tace mi yake ya bata amsa da yana wani aiki ne tay shiru yayin da zuciyarta ta shiga raya mata kilan ma a part d'in shi Fanan ke kwana jin tayi shiru yasa shi tambayar ta koda wani abu ne da sauri tace mashi a'a tayi mashi saida safe yana murmushi ya amsa har zata kashe taji yace tana tare da mutane ne a hankali tace mashi a'a ita kad'ai ce Jidderh taje ta dawo yace Ok bari yazo suyi bankwana da Babies tay d'an murmushi tace to, aje wayar tayi ta juya tana kallon yaran dake kwance saman gadon suna bacci sam basu da rigima da sun yi kuka yawanci yunwa suke ji, bada jimawa ba sai gashi ya shigo cikin d'akin da sallama ta d'aga kai ta kalle shi ya sakar mata murmushi itama haka, cikin d'akin ya nufo ya tsaya d'an nesa da ita yace bazatai welcoming nashi ba tunda shi bak'o ne yanzu, yar dariya tayi ta mik'e ta nufe shi tana zuwa gabanshi ta fad'a jikin shi ya rungumeta suna ta sakin murmushi ga k'amshin jikinsu ya cika ma kowa hanci, d'agowa tay tace mashi ya zauna atare suka zauna idon shi akan yaran ya tambayi ya suke itama kallon su take tace mashi lafiya lou, juyowa tay suka had'a ido ta d'an langa6ar da kai cikin lumshe ido Slowly ya furta mata "I'm missing you" dan buda ido tayi still da murmushi akan Fuskar ta k'asa k'asa tace "ba gani a kusa da kai ba" d'age gira yay yace ba shi ba itama ta d'age mashi tace wanne, wani irin kashe mata ido yay ta saki dariya shima yar dariyar yay ya jawota jikin shi, kai hannu tayi
tana shafa beard cikin salo tace "na gode ma Allah dayasa na haihu lafiya naci gaba da yin rayuwa da kai" lumshe mata ido yay a hankali yace shima haka tana niyyar k'ara yin magana suka ji an shigo a tare suka kai idon su kan kopar Jidderh ce tayi shirin bacci tana ganin su ta dan waro ido tana murmushi kunya ce ta kama Fatuu ta fara k'ok'arin raba jikinta da nashi saidai yak'i bata dama ganin haka yasa Jidderh cewa ta bashi 10 minutes zata je ta dawo harda jaddada mashi da hannu duk sukai yar dariya, bayan ta fita Fatuu ta maida idonta kan shi tace tana son yi mashi wata Magana ya d'aga kai kafin yace yana ji,

"Dama so nike in ce kaman yakamata Ya Sameer yaje Funtua su gaisa da iyayen Fauzy Saboda ba wanda yasan shi fa" shiru yay idon shi akanta can yace mata sun yi magana kan hakan ne da sauri tace a'a kawai itace tayi tunanin hakan, Wani kallo yay mata yace "Kai yar fillona yaushe kika iya yin wannan tunanin" dariya ta saka tace mashi tunda tay hankali ya d'age gira yace to shi miyasa bata ta6a ce mashi yakamata yaje garin su ba da sauri tace "to ai kai kaga Baffana ya sanka tun ma kafin muyi aure kuma gwaggota ma ta san ka amman shi fa ba wanda ya san shi gashi yanzu bai fi saura wata ukku ba bikin" shiru yay da alama nazarin Maganar yake can yay sigh yace mata yanzu dai bai K'asar amman yace zai zo bada dad'ewa ba in yazo zai ga abun da za'ai ta d'aga kai sai kuma tace "amman in kaga fa kaman da takura ko kawai ka bar Maganar in yaje bikin sun ganshi, kai ya girgiza mata yace ai yakamatan yaje saidai yazo,

"To ni yaushe zaka je garin mu?" yana murmushi yace biyanta zai yi kenan tace eh, yace Ok zasu je sai Babies sun k'ara girma harda tambayarta hakan yayi mata tace mashi eh, dawowar Jidderh tasa yayi mata sallama ya tafi. Washe gari Misalin k'arfe ukku na rana su Gwaggo suka iso yanzu ma kamar da biki Mota biyu suka yo da Tk da Saude da Aunty Mareeya, Feenah, Kawu Amadu, Abbas, Fauzy, Mino harda Nana wannan karon ba'a zo da Zainab ba, zo kaga murna wurin Fatuu suma sai murnar ganinta suke ba kamar da suka ga yaran Mino har ta kasa rufe bakinta don dad'i gwaggo ma sai faman murmushi take haka su Aunty Mareeya da Feenah Abdul ma sam ya kasa matsawa daga kusa da yaran sai d'auka d'auka ake d'akin ya cika anata farinciki, harda uban yajin jego gwaggo ta kawo, a Ranar bayan la'asar yan Adamawa suka iso su Yadikko da Kamalu Yaya sai wata k'anwar Baban su Fatuu da d'ayar Matar Ardo wadda ba'a zo da ita biki ba wannan karon ba'a zo da innar su Altine ba duk da taso tazo kamar kamar me amman ba'a zo da itan ba don gwaggo ta fad'i ma Baffan su Fatuu kada azo da yawa tunda ba'a dad'e da aka zo biki ba, wannan karon ma harda shanu suka kawo saidai ba daga Baffan Fatuu ba daga mai girma Ard'o ya ba yan tatta6a kunnan shi saida kowa yayi mamakin yadda suka ciri tuta har ya d'au shanu sukutum ya basu don abu ne da bai ta6a yi ma wani a yaran dangin su ba, basu dad'e da zuwa ba gab da Magrib wasu yan'uwan su Haisam yan d'aura suma suka iso nan fa gida ya dauki haramar suna, wannan karon ma a part d'in baya duk aka sauke su amman su Mino da Fauzy duk a part d'in Fatuu suka ce zasu kwana, Kusan raba dare sukai suna hira gwanin nishad'i. Washe gari Lahadi suna tun bayan da akai sallar Asuba ba'a koma ba aka fara hidiman suna wannan karon ma masu aikin Abinci aka d'aukko tunda safe aka fara yanka raguna harda shanun da Ard'o ya aiko aka yanka aka kuma k'ara da kaji nan fa aka shiga soyen hanji, Misalin k'arfe goma na safe lokacin Fatuu tayi wanka tayi shigar suna ta farko da babbar atamfa da akai mata half gown da straight skirt wuyanta da hannunta tasha gold Aunty Laila tayi mata makeup da daurin kallabi mai kyau sosae tayi kyau abun sai wanda gani, lokacin yan uwansu Mom daga Ethiopia suka iso Haisam da Nameer ne da Jidderh suka je d'aukko su, mutum biyar ne suka zo da Kakarsu sai k'annen Mom guda biyu sai kuma cousin dinta da kuma d'iyar yayan su wato Jahad da Mom taso Nameer ya aura, musamman Saboda sunan Kakarsu ta baro Qatar tazo Ethiopia shine suka taho, sosae akai farinciki da zuwansu su Aunty Mareeya sai yaba kyaun k'annen su Mom suke gaba dayansu suna yanayi da Haisam haka Jahad d'in ma kyakkyawace saidai bata da tsawo sosae kuma ba ramamma bace don zata fi Mino jiki amman Mino zata fita tsawo dukda da gani ta girmi Minon ma, nan fa hidiman suna ta kankama, zuwa sallar Azahar har an gama Abincin suna Kusan kala takwas anan gidan akai wasu wasu kuma k'awar Mom aka ba kwangilar yi haka Drink ma kala hud'u akai banda uban lemuna jibgi guda sai abunda mutum ke so zai ci ya kuma sha nama kuwa gashi nan cikin abinciccikan baje baje, ana yin salla Mai jego ta canza shiga zuwa rantsattsan leshi d'an dubu d'aruruwa anyi mata riga da skirt da suka hau jikinta sosae lokacin su Mom gaba dayansu su kuma ankon tsadaddiyar atamfa sukai ita da Aunty da Laila gaba d'aya dai yan gidan kaya iri d'aya suka saka harda Hajiya da Fanan haka Dad ma dasu Haisam suma ankon shadda sukai da sauran yara mazan gidan, kowa dai yaci gayun suna Gwaggo tasha leshi haka Mino ma lace tasa Fauzy kuma fitted gown d'in atamfa ta saka iri d'aya sukai da Aunty Mareeya, kai kowa dai yasha gayu don in natsaya bayyana kayan da kowa ya saka zamu 6ata lokaci, bayan an gama cin gayun an ci Abinci photographer da aka d'aukko ya shiga aikin d'aukar hutuna, ana cikin yin hotunan jiniya ta karad'e cikin gidan su Jidderh suka nufi kopar fita daga cikin parlon gidan da gudu suna fad'in ga Momyn Nasarawa nan ta iso jin hakan har saida gaban Fauzy yay wani irin bugu Aunty Mareeya ta kalleta tana yar dariya Fauzyn ta waro mata ido, matsawa Aunty tay wurinta tace mata tazo suje su tarbo surukarta da sauri ta girgiza mata kai Aunty ta juya tana fad'in ita bari taje, hakanan Fauzy taji gabanta na wani irin fad'uwa da sauri ta juya ta nufi baya inda suka sauka, cikin Fara'a her Excellency ke amsa barka da zuwan da ake mata tasha adon dangwatsetsen leshi da gold haka yaranta ma duk sunyi shigar alfarma Aunty Mareeya na kallon fuskar Ashraf dake a d'aure a ranta ta raya wannan da gani irin Sameer ne, bayan an gama yi mata barka da zuwa aka d'unguma ciki, suna shiga cikin parlon Aunty Mareeya ta wurga ido tana kokarin hango Fauzy saidai bata ganta ba, saida suka rakata har d'akin Mom sannan suka fito tana ta godiya, part d'in su Fatuu ta nufa don ta duba Fauzyn amman bata a ciki hakan yasa ta fito ta nufi baya, d'akin da suka sauka ta nufa tana tura kopar ta hangota zaune a bakin gado tayi zuru, k'arasa shigowa Aunty Mareeya tayi ta nufeta tana fad'in "lafiya kika zo kika k'umshe anan" d'an ta6e baki Fauzyn tayi ba tare da tace komai ba, a gefenta Aunty ta zauna ta dafa Shoulder d'inta tace mata wai lafiya, a sanyaye tace mata hakanan take jin ta wani iri zuwan Mom d'in su Sameer din gani take kaman bata yi na'am da ita ba Aunty tace "to in bata yi na'am dake ba kuma ta amince mashi ya aure ki, kar ki wani damu ni ina ganin ba wani abu don da alamun bata da wata matsala" da yanayin damuwa Fauzy tace "amman Aunty tunda aka saka Ranar mu fa bamu ta6a ko magana ta waya da ita ba yanzu har wata hud'u shiyasa dama can nike tunanin kaman bata son Auren namu kawai dai k'ilan don ya nuna yana so ta amince" d'an jimm Aunty tay don tasan da zancen basu ta6a magana da ita ba ita da kanta tana tambayar ta game da hakan, yar ajiyar zuciya ta sauke "kada ki damu Fauziyya in sha Allahu ba haka bane k'ilan dai abubuwa ne sukai mata yawa shiyasa bata nemi kuyi wayar ba kinsan Manyan Mutane yadda suke uzururruka yawa suke masu balle ita kuma da take First Lady, yanzu ki tashi muje sai kiyi mata sannu da zuwa" waro ido Fauzy tayi tace taje kuma ta d'aga mata kai tace haka yakamata, sakata tayi ta canza kaya zuwa lace mai kyau riga da skirt Aunty harda yi mata yar kwalliya ta kuma yi mata d'aurin kallabi mai kyau ta feshe ta da turare, komai dai Aunty tayi mata sai gata ta fito tayi kyau sosae dama kanta a kwance yake ta faka gashinta ya fito ta k'asan d'aurin da aka yi mata bayan ta gama shirya ta tasata ta d'aukko gyale mahad'in kayan da takalma masu d'an tsini suma sun hau da kayan ta kama mata hannu suka fito, sosae gaban Fauzy keta bugawa wata irin fargaba ce ta cikata har suka iso bakin part d'in Mom nan taja ta toge Aunty tace suje mana ba gata ba tare da ita, parlon Mom d'in cike yake da Mutane yan suna suka nufi hanyar Bedroom da anan Hajiya Zainab d'in take lokacin da suka shiga cikin d'akin nan ma dai cike yake da mutane k'awayen su Mom wasu a saman gado wasu asaman doguwar kujerar dake cikin d'akin wasu kuma zaune suke a saman Carpet sun jingina da tuma tuman tuntun d'in dake ajiye saman lallausan carpet d'in, Jidderh na zaune gefen Her Excellency tana zuba mata shagwaba da yake yar gidanta ce haka ma K'annansu da suka zo daga Ethiopia suma duk suna zagaye da ita a saman gadon su Aunty Mareeya na shigowa akan idon Jidderh cikin d'aga murya tace "Ga Bride d'in Ya Sameer nan" gaba d'aya yan d'akin suka maido idonsu kan su Fauzy yadda taji tamkar ta nutse a wurin ta kasa cigaba da tafiyar tay tsaye cak a wurin idonta a k'asa jikinta har d'an rawa yake, Jidderh ce ta taso da sauri ta nufo su tana zuwa ta kamo hannun Fauzyn ta jata ciki, kusa da Hajiya Zainab ta kai ta tace "Momy ga Daughter in-law d'in ki" Fuskarta da d'an murmushi ta kalli Fauzy data sunkuyar da kai cikin muryar ta mai dad'i ta furta "She's My Daughter not inlaw" jin haka yasa Aunty Mareeya dake a tsaye gefen Fauzyn sakin murmushin dadi ita kanta Fauzyn ta d'an ji wani sanyi a ranta da k'yar ta d'ago suka had'a ido cikin d'an rawar murya ta gaishe da ita tare da yi mata an zo lafiya tana ta murmushi ta amsa mata kafin tace ma Jidderh ta bata wuri ta zauna tace to tare da mik'ewa ta kalli Fauzyn tay mata nuni da hannu tace ta zauna, d'an can gefe da ita ta zauna har lokacin idonta na a k'asa taji tace mata ya School sai lokacin ta d'ago ta k'ara kallonta da d'an murmushi tace mata Alhamdulillah ta jinjina mata kai, kallon Aunty dake tsaye Hajiya Zainab d'in tayi tace mata ko itace Sister d'inta da take wurinta da sauri Aunty tace mata eh tana murmushi ta jinjina mata kai, Kallon k'annansu yan Ethiopia tayi da yaren su tace masu ga Wadda Sameer zai Aura su gaisa duk suka d'an d'aga ma Fauzyn hannu suka ce sunyi farincikin ganinta da turanci itama tace masu haka tay masu godiya, kallon Amal k'anwar Sameer tayi tace mata ita baza su gaisa ba tayi d'an murmushi tace ma Fauzyn ina wuni itama tana murmushin ta amsa mata daga haka suka yi shiru can kuma Her Excellency ta kalli Aunty tace mata ta zauna mana tayi tsaye ko ba wuri Aunty ta fara k'ok'arin zama akan Carpet Hajiya Zainab d'in tace ya zata zauna a k'asa ta kalli Amal tace ta bata wuri da sauri Aunty tace a'a don Allah ta k'yaleta ai ba k'asa bane tunda carpet ne tayi Maganar tare da zaunawa, ko ba komai sosae taji dad'in yadda ta mutunta su a cikin ranta, Mom ce ta shigo ta nufo gaban Hajiya Zainab tana murmushi ta kalli Fauzy tace mata suna gaisawa da Daughter ne ta d'aga mata kai sai kuma tace ita wadda Nameer zai aura bata zo bane da sauri Jidderh tace tazo bari ta kirawota ta mik'e ta nufi hanyar fita, gaba d'aya Fauzy ta takura da kallon da ake bin ta dashi ba kamar Yar'uwar su Sameer wato Jahad wani irin kallon k'urulla take bin ta dashi da alama tana tantance waya fi kyau tsakanin su don tana son Sameer sosae, ba'a dad'e ba sai gasu sun dawo tare gaba d'aya Minon rud'ewa tayi bayan sun shigo ganin yadda aka bita da kallo a harhard'e ta rink'a tafiya, gaban su Mom ta kaita sam ta kasa d'agowa ta kalli kowa kanta a k'asa ta gaishe da su, Hajiya Zainab na murmushi jin yanayin voice d'inta data gaishe su tace "to Daughter yar fillo in baki d'ago ba taya zamu san juna" duk akai murmushi da k'yar Minon ta d'ago suka had'a ido da ita a d'an dabarbarce ta k'ara gaishe da ita ta amsa, kallon yan Ethiopia ta k'ara yi tace masu ga Wadda Nameer zai aura kuma duk suka d'aga mata hannu tare da ce mata itama sunyi farincikin ganinta ta amsa masu Hajiya Zainab ta kalli Mom tace mata sunyi kama sosae da matar Son Mom d'in tace mata eh daka kalle su zaka gane yan'uwa ne, bayan sun gama gaisawar Mom tace masu su zo su gaisa da mutane gaba d'aya ji sukai kamar su nutse ba yadda zasu yi Fauzy ta mik'e suka bita ta shiga cikin d'akin dasu tana nuna ma mutane su, to duk dai yabon su suke suna fad'in suna da kyau wasu su ce gasu yara dasu, bayan sun gama gaggaisawar tace masu suje su gaisa da Ummin su wato Kakar Haisam sukai hanyar fita, mik'ewa Aunty tayi tay ma Hajiya Zainab sallama har zata juya ta tafi ta dakatar da ita tace mata anjima da daddare in an gama taro tana son zasu yi magana in ba damuwa da sauri Aunty tace to Allah ya kaimu ta k'ara yi mata sallama sannan ta tafi.

Taro ya kankama Mutane sai zuwa suke suna kuma kawo abun arziki, tun Fatuu na gane yawan kayan da ake kawo mata har ta kai bata ganewa, wasu kayan daga part d'in Mom ake aikowa dasu wasu daga wurin Aunty wasu daga wurin Hajiya har daga wurin Laila wanda k'awayenta suka kawo, wasu ma yan'uwan wanda Laila zata aura sun zo suma sun kawo abun Arzik'in haka ta 6angaren Jidderh ma wasu k'awayenta da suka zo sun kawo kaya harda surukarta Maman wanda zata aura wato Matar Minister tare da k'anwar shi da kuma Yayar shi sun zo suma duk sun kawo kayan suna, haka wasu daga cikin Matan Abokan Haisam ma duk sun zo harda Saleema matar Saleem itama ya kawota da yake dama a Abujar suke zaune Sa'adiya ma k'anwar Khalid tazo tare da Mahaifiyarsu wato Hajiya Rabi'atu sosae Fatuu tayi farincikin ganinta harda sak'o khalid ya bada a kawo mata, abun Arziki dai ta ko ina Aunty Laila da Fanan suna ta kai da kawon ganin an tarbi kowa yadda yakamata sai sannu ake masu. Ana yin sallar la'asar duk suka canza shiga Fatuu ta saka shadda da tasha ubansun aiki su Mom dasu Laila gaba d'aya yan gidan suka saka lace su Fauzy ma duk suka canza shiga nan aka shiga sake yin hotuna yanzu harda su Hajiya Zainab akai, Haisam na fitowa daga Masallaci shi dasu Abbas Fanan ta kira shi ta sanar dashi Mom d'inta sun iso suna Airport yace Ok bari suje su d'aukko su, Mota biyu suka tafi da ita shida Abbas da kuma Saleem, lokacin da suka iso gidan gaba d'ayan su sunyi shiga ta Alfarma abun gwanin sha'awa ita da Farha duk tsadaddun lace ne a jikin su kowannen su na sanye da zinari sai sauran yaran ma duk suna sanye da tsadaddun kaya Fanan na ganinsu ta nufo su da gudu cike da Farinciki ta tarbe su haka ma su Mom duk sun nuna farinciki da zuwan su, tunda suka shigo falon Mino da Fauzy suka bi Farha da kallo haka ma Fatuu komai ya shiga dawo mata daya faru tsakaninsu, amsar kayan su Fanan da Laila sukai suka nufi part d'in Hajiya dasu Aunty Mareeya da bata santa ba ta tambayi Feenah wacece ta sanar mata da d'iyar Hajiya ce Mom d'in Fanan tace Ok suje su gaisa da ita, duk an gaggaisa da ita an mata sannu da zuwa harda Gwaggo ma taje ta gaidata tayi mata sannu da zuwa fuska a sake ta amsa harda yi mata barka, wurin Fatuu gwaggo tazo tace mata taje tayi mata sannu da zuwa a sanyaye tace to ta nufe su tunda ta taho Suke kallon juna ita da Farha har ta tsaya a gaban su cike da fargaba ta gaishe da Hajiya Maryam d'in itama ta sakar mata fuska ta amsa tare da yi mata barka, kallon Farha tayi da d'an murmushi tace mata sannu da zuwa ga mamakinta sai gani tayi ta maido mata da murmushin itama ta amsa mata tare da yi mata barka hakan ba K'aramin dad'i yayi ma Fatuun ba dama ita a rayuwarta bata son taga wani ya ruk'e ta yana fushi da ita, lokacin Fanan suka dawo ganinsu tare da Fatun ba karamin dad'i taji ba nan tace suzo ayi masu hotuna kafin su shiga ciki, sai gashi harda Farha anyi masu, ana gama sallar La'asar Aunty Laila ta kunna Sound system d'in cikin parlon ta k'ure volume kai kace Dj ne aka kira nan fa suka shiga tik'ar rawa harda Fanan dasu Jidderh da alama dai Aunty Laila yar casu ce don sosae ta zage tana rawa su Fauzy dai suna a cikin yan kallo Aunty Mareeya da Feenah dai sun shiga, suna cikin rawar yan uwansu yan Ethiopia suka ba Laila wak'ar yaren su ta kunna masu nan fa aka basu fili kallo ya dawo kansu dama shigar su ta al'ada suka yi gashin su ya bud'e Laila da Jidderh ma da yake sun iya rawar da suke suma sukai joining nasu abun dai sai wanda ya gani gwanin k'ayatarwa cikin yan kallo harda Mom da Hajiya Zainab yadda suke ji an tada masu tsumi kamar su shiga saidai ba dama su Laila nata ce masu wai su zo ayi dasu sai dariya suke.

Alhamdulillah taro ya tashi lafiya an ci an sha anyi nishad'i ba kad'an ba an kuma raba souvenirs abubuwa iri daban daban masu d'auke da sunan jarirai amman ba hoto don Hajiya ta hana Saboda gudun bakin mutane dama shima Haisam bai so, abun dai sai san barka da fatan Allah ya raya Adam da Aliyu. Gaba d'aya Fatuu ta gaji likis haka jariran ma a daddafe tayi wanka bayan Magrib suma aka yi masu tana gama shiryawa tayi shirin kwanciya su Aunty Laila ma abun ba'a magana gaba d'aya sun gaji amman duk da haka suka shiga shirya kayan sunan da aka samu wanda suka zube a k'asa gefen gado kili guda kai kace Fatun k'aton shago zata bud'e don kaya ne aka tara ba yan kad'an ba kama daga manyan atamfofi laces materials kayan jarirai abun ba'a magana don ko Hajiya Maryam trolley guda ta kawo na kayan jarirai tsadaddun gaske da kuma manyan atamfofi guda biyu na Fatuu haka su Hajiya Zainab ma ta kawo had'add'un kaya na jarirai dana Fatun mutane da dama dai duk sun kakkawo kaya sosae harda su Baby gift set suma an tara su da yawa wasu had'addun baskets ne an nad'e su da yan flowers irin dai yadda ake ma kyauta, k'arshe dai wasu saidai nan aka barsu da safe an kimtsa su.

Bayan sallar isha Aunty Mareeya na gama salla jikinta sanye da Hijab ta nufi part d'in Mom don amsa neman da Her Excellency ke mata, lokacin da ta shiga cikin Bedroom d'in da sallama ba kowa a ciki sai su biyu duk suna zaune a saman gado jikinsu sanye da dogayen riguna kowannen su ba kallabi a kan shi suna ruk'e da glass cups mai d'auke da ruwan lemu mai sanyi da gani hira suke suna sha, da murmushi gaba d'ayan su akan fuskokin su suka amsa mata Sallamarta ta nufi gadon, daga gaban gadon ta tsaya tana kallon su don kuwa sun rud'a ta bazata iya gane wacece Her Excellency d'in ba a ciki, Mom ce tace mata sannu da zuwa ta amsa ba tare data gane wacece ba tana d'an murmushi tace masu dama tazo wurin Her Excellency ne daga yanayin yadda tayi Maganar suka fahimci bata gane su ba Hajiya Zainab d'in ce tace mata "Ok, ki ganta" jin haka yasa Aunty tayi tunanin Mom ce tayi Maganar don haka sai ta juya kan Mom da tayi tunanin itace Hajiya Zainab tace "ranki ya dad'e gani na dawo kamar yadda kika ce" kasa daurewa Mom tayi ta saki dariya haka Hajiya Zainab d'in ma yar dariyar tayi ganin haka yasa Aunty Mareeya d'an waro ido tana masu kallon rashin fahimta Mom ta nuna mata Her Excellency tace mata gata nan itace tayi mata Magana, d'an bud'a baki Aunty tay sai kuma ta saki dariya don ta gane wasa da hankalinta tayi, saukkowa daga saman gadon Hajiya Zainab tayi still tana yar dariya hannunta ruk'e da cup d'in lemun tayi ma Aunty Mareeya alamar su je da hannu ta nufi doguwar kujerar cikin d'akin tana bata hakurin abunda tayi mata tace it's just for fun Auntyn ma dariya take tace ai ba komai, zama tayi kan kujerar ganin tayi tsaye tace mata ga wuri nan ta zauna, daga d'an can gefenta Aunty ta zauna ta kai cup d'in hannunta baki tay sipping lemun Aunty nata kallonta a cikin ranta tana raya sai kace ba ita ta haifi Sameer ba don sam jikinta bai nuna hakan ba, d'aura cup d'in tayi saman d'an table dake a gefen kujerar kafin ta juyo suka had'a ido da Aunty a nutse cikin girma ta fara magana "amm, dama ba wani abu bane inason muyi magana ne akan shiryen shiryen biki nasan kun fara ko?" Da sauri Aunty tace mata eh tuni anata yi, jinjina kai tayi taci gaba "Yayi kyau, game da kaya da za'ayi nike son sanar dake ba'a buk'atar komai don shi wanda zata auran ba zaune yake anan ba koda yaushe, zai tafi da ita can ne kuma yana da gida da komai haka anan ma so ko anyi su ba wani amfani da zasu yi don haka sai a barshi ba sai anyi komai ba wani abu na al'ada da komai dai duk a barshi ayi Addu'ar Allah ya tabbatar da Alkhairi" wani irin dad'i ne ya cika Aunty sai dai bata nuna ba sosae kawae dai faffad'an murmushi tayi tace "Ma sha Allah, Mun gode, mun gode kwarae your Excellency Allah ubangiji ya saka da Alkhairi ya k'ara girma da daukaka, hak'ik'a wannan ya tabbatar da ku d'in masu tausayin talakawa ne kuma duk d'aya kuka d'auke mu da ku, irin ku K'asar mu ke buk'ata ina Addu'ar Allah ubangiji yayi maku President ko mun amfana" wata irin dariya Hajiya Zainab tayi ta amsa da "Ameen ya Rabbi, in Alkhairi ne amman yanzu su Sis ne akan layi sai mu taya su da Addu'a" kai Aunty ta jinjina "Allah ya tabbatar da Alkhairi, ai your Excellency duk d'aya kuke wllh in Allah ya baku K'asar nan tamu nasan zamu more don irin ku take buk'ata bama kamar mu talakawa tabbas zamu ji dad'i, in Allah ya basu suna gamawa sai kuma ku dasa Allah ya amince" fad'ad'a dariyar ta Hajiya Zainab tayi tace mata hakan kuwa bazai zama son kai ba Aunty na dariya tace a'a wllh ai dama Ana cewa da yuyuyu gwamma d'aya kwakkwara jinjina kai Hajiya Zainab tayi tace Allah dai ya tabbatar da Alkhairi ya za6a mana Shuwagabanni nagari Aunty ta amsa da Amin, hannu ta kai ta d'aukko lemunta ta kur6a bayan ta cire Cup d'in cikin girmamawa Aunty Mareeya tace mata ko zata iya kiran Mahaifiyarsu su gaisa ta jinjina mata kai tace eh lafiya lou ai tuni ma yakamata ace sunyi hakan to ita abubuwane ke mata yawa don ko ita Daughter Fauziyya basu ta6a Magana ba sai yau, kiran Maman tasu ta shiga yi bayan ta d'auka suka gaisa ta tambayi ya Abuja da masu jego tace mata duk suna lafiya nan ta sanar mata dama zasu gaisa da Her Excellency ne, cikin alamun rashin fahimta Maman tasu ta tambayi wacece nan ta sanar mata Mahaifiyar wanda Fauziyya zata aura ai tana jin hakan ta yunk'ura dama a kwance take ta tashi zaune ta shiga daidaita zamanta Aunty Mareeya ta k'ara cewa in sun gaisa sai tayi mata godiya don tace ba sai anyi ma Fauziyya komai ba na kayan d'aki, jin hakan yasa Maman tasu kai hannu ta rufe baki alamar Al'ajabi, bayan ta ba Hajiya Zainab wayar cike da girmamawa Maman tasu ta shiga gaishe da ita duk da kuwa ta girmeta nesa ba kusa ba itama Hajiya Zainab a mutunce take gaisawa da ita, sosae Maman tasu tayi mata godiya da kuma Addu'oi fuskarta da murmushi take amsawa, bayan sun gama wayar ne tace ma Aunty Mareeya Shikenan zata iya tafiya in kuma da wani abu sai tayi magana tace mata ba komai wllh ta k'ara mata godiya har zata tashi sai kuma ta dakata cikin yar ina ina tace don Allah in ba damuwa ko zata bata lambar ta don a rink'a gaisawa tace sure bari ta bata ta amshi wayar tata ta rubuta mata daga haka sukai sallama, wurin gadon Aunty ta nufa don tayi ma Mom sallama, da murmushi Mom tace mata har an gama tattaunawar Aunty tace mata eh sai kuma tace "Don Allah Mom a k'ara taya mu godiya wurin Her Excellency tace ba sai anyi ma Fauziyya komai ba naji dad'i wllh Allah ya k'ara maku girma da d'aukaka" tana murmushi ta amsa da Amin tace mata ai ba wani abu bane duk an zama d'aya tayi Addu'ar Allah ya bar zumunci Aunty ta amsa da Amin kafin tayi mata sallama ta tafi.

Tana fitowa baya ta tsaya ta shiga kiran Fauziyya, bayan ta d'aga tambayar ta tayi tana ina tace tana a inda suka sauka har ta kwanta ma tace to ta fito waje ta sameta tace to, bada jimawa ba Fauziyyar ta fito tana sanye da kayan bacci riga da wando sai hula a saman kanta, nufo Aunty tayi gabanta har d'an fad'uwa yake don tasan da Maganar cewa Hajiya Zainab na son ganin Auntyn tasan kuma bai wuce game da hakan yasa Auntyn kiranta, tana k'arasawa gabanta kawai sai gani tayi ta rungumota cike da Farinciki take fad'in "Fauziyya ki taya mu murna ance ba sai anyi maki komai ba wllh iya ke suke buk'ata, da sauri Fauzy ta d'ago daga jikinta ta waro ido da tsananin mamaki ta maimaita abunda Auntyn ta fad'a cikin washe baki tace mata Wallahi kuwa yanzun nan ta dawo daga wurin Hajiya Zainab din, nan ta shiga fad'i mata yadda suka tattauna harda gaisawar da sukai da Maman su ta shiga yabonta tana fad'in tana da kirki sosae tayi dacen suruka, shiru Fauzy tay ba baki sai murmushi kawai da take gaba d'aya ganin abubuwan take tamkar a mafarki,

"Ya naga kin yi shiru ne, ko baki farinciki bane yanzu fa Shikenan Baba ba sai ya sayar da gonakin shi ba hakan kuwa ai abun murna ne" yar dariya Fauzy tay a sanyaye tace "a'a Aunty naji dad'i sosae wllh, kawai abubuwan ne keta ban mamaki wllh duka yaushe akai Maganar gida yanzu kuma ga wannan",

"Ai kinsan haka abun Allah yake lokaci guda yake juya al'amurra, baki ji ana cewa dare d'aya Allah kan yi Bature ba to misalin hakan ne, ai tsakanin mu da Ubangiji wllh sai godiya Yar gidan Hajiya kin tako mana arzuki Allah yasa a wurin bikin wata ma cikin kannanmu ta samo mana wani irin Sameer d'in koma k'anin shi" dariya sosae Fauzy ta saka tana fad'in kai Aunty,

"Allah kuwa ai abun fata ne ke baki ji ana cewa da arzuki a garin wasu ba gara a naku a nakun ma a cikin gidan ku duk da bansan ma ko yana da K'ani babba ba k'ilan kuma wannan da na gani lokacin da suka zo shine ke bi mashi shima dai ai lafiya lou don ya isa Aure naga kamar Nameer yake, amman wannan ma anya zai iya Auren talaka shima naga alamun kamar Sameer d'in yake, koda yake shima Sameer d'in ba gashi ya fad'a komar yar manomi ba" Dariya kawai Fauzy ke yi Aunty ta shiga yin godiya ga Allah tana fad'in wllh har ta rasa ina zata sa kanta don farinciki Allah dai ya nuna masu bikin da rai da lafiya dole taci uwar sabada har ta hango shigar da zatayi, dariya kawai Fauzy ke yi suka nufi komawa part d'in da suka sauka, bayan Fauzy ta koma d'aki zama tayi a bakin gado tayi shiru ba komai take tunani ba face Sameer don a yanzu sosae take jin son shi duk in bata ji Muryar shi ba ko sukai Vedio call bata jin dad'i duk da har yanzu d'in ba wata soyayya suke ba amman ba laifi sun fi yin magana yanzu, ji tayi bazata iya kwanciya batare da taji muryar shi ba ta d'ago wayarta ta shiga kiran shi bayan ta yanke ta zauna tana dakon ya biyo kiran......

95

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

.............Bada jimawa ba sai gashi ya kira, bayan tayi picking a hankali ta gaishe shi da tambayar shi ya aiki, har saida ta d'an lumshe ido Jin muryar shi da ya amsa, shiru tayi tama rasa mi zata ce mashi tana hakan taji yace ya Abuja tana d'an murmushi tace lafiya lou yau anyi suna sai kuma tace mashi har ma sun gaisa da Mom d'in shi taji ya furta Ok, shiru sukai can ya k'ara cewa koda wani abu ne ta d'an tura baki shi haka yake duk ta kira shi tana jin shauk'i sai ya wani kama tambayar ta koda wani abu, Ji tayi ya k'ara cewa inda wani abu ta fad'a mashi ta d'an kara tura baki sai kuma a hankali tace "No, babu komai dama kawai na kira ne in ji mur....." Kasa k'arasawa tayi ta d'an waro ido don bata ta6a ce mashi hakan ba,

"ina jin ki" taji ya fad'i hakan, abu ta had'iya kamar ta canza abunda ta fad'an wata zuciyar ta shiga k'arfafa mata gwuiwa ta fad'i mashi hakan, "Dama naji ina son jin voice en ka ne" wani kalan murmushin gefe yay taji yace mi voice en nashi gare shi, d'an Farfar tayi da ido da k'yar ta furta mashi "Yana da dad'in sauraro ne" shiru taji yayi har saida gabanta ya d'an fadi don tasan shi wani lokacin ba'a cika yi mashi gwaninta ba, tambayar ta yay tana ina ne ta bashi amsa da tana a d'akin da suka sauka ya k'ara tambayar ita da waye tace su biyu ne kuma d'ayar bata kaiga shigowa ba taji ya furta Ok suyi Vedio call tace to, lokacin daya maida kiran na gani yana kwance a saman gado yau ma robe ce a jikinshi chest d'in shi a bud'e ya tashi zaune tare da jingina da headboard, bin juna sukai da kallo Fauzy nata mashi d'an murmushi shima yanayin fuskar shi kaman zai murmushin, ganin yanayin idanun shi a lumshe kaman mai jin bacci yasa tace "ko bacci kake ne?" saida ya k'ara lumshe su sannan ya d'an girgiza mata kai,

"Naga kaman har ka kwanta" ta k'ara fad'a idanunta cikin nashi yay d'an shiru can ya bata amsa da ya gaji ne yayi tafiya bai dad'e daya dawo ba ta jinjina mashi kai kafin tace "to bari in bar ka ka huta" wani kallo yay mata ya d'an shigar da lip d'in shi na k'asa kafin taji yace har ta gama sauraron muryan nashi ne, yar dariya tayi ta girgiza mashi kai alamar a'a sai kuma tace "to ai kai baka magana sosae" d'an yamutsa baki yay yace mata bai iya bane ta gyad'a kai ta k'ara cewa "in kana so sai in koya maka" murmushin gefen baki yay tare da girgiza kai yace yafi jin dad'in hakan tunda hakan ya sa6a nan ma kai ta gyad'a mashi suka k'ara yin shiru suna kallon juna,

"A gida kake ne ko hotel?" shiru kaman bazai bata amsa ba taji yace da wani abu ne ta tambaya da sauri ta girgiza mashi kai "hakanan kawai na tambaya" ta bashi amsa, ce mata yay yana a gidan shi ne ta gyad'a kai sai kuma ta k'ara cewa "kuma kai kad'ai kake zaune?",

"Zan zauna da wa?" Ya fad'a, tana murmushi tace "a'a dama ina nufin kai kad'ai ne ba wani wanda ke taya ka zama?" shirun dai yay yana bin ta da ido sai can yace mata yakamata ya samu abokin zama ne tace "kawai naga in kai kad'ai ne kaman kad'aici zai dame ka shiyasa nayi tunanin ko akwai wani da kuke zaune tare" lumshe ido yay tare da d'an girgiza mata kai alamar a'a sai kuma taji yace "akwai wata da zata zo" har saida gaban Fauzy ya fad'i da alamun rashin fahimta tace mashi wata zata zo nan ta zauna ya d'aga mata kai alamar eh, wani irin abu taji ya tokare mata k'irji a zuciyarta ta shiga raya kenan mata suke zuwa suna kwana tare dashi kuma a haka ace bai neman su cab, wani bangaren na zuciyar ta ya raya mata kika san wacece ko yar uwar shi ce, kasa daurewa tayi yana ta kallon ta yanayin fuskarta ya d'an canza tace mashi ita wadda zata zo d'in yar uwar shi ce kawai sai gani tayi ya girgiza mata kai alamar a'a yace kawai zata zo su zauna tare ne ya rage loneliness, abu Fauzy ta had'iya yanayin fuskar ta ya k'ara sauyawa ta koma kallon gefe tana d'an kikkafta idanu, "Any problem?" taji ya fad'i hakan ta juyo suka had'a ido wani irin abu mai zafi take ji a ranta ta bishi da kallo yanayin fuskar ta kaman zata saka kuka, d'age mata gira yay ya k'ara tambayar da matsala ne a sanyaye ta d'aga mashi kai yace miye matsalan to, ce mashi tay kawai taga ya zai kawo wata su zauna bayan ba muharramarshi bace ai yasan hakan ba kyau ko, yanayin yadda tay Maganar da yar shagwaba, d'an murmushi taga yayi yace mata ai kawai zata taya shi zama ne ba wani abu ba, yamutsa fuska Fauzy tay yadda take ji kaman ta saki kuka don tasan ko ba wani abun dole k'ilan bai rasa ta6a wadda zai kawo d'in tunda ance yana yin hakan ita yanzu ma ta fara zargin anya bai wuce hakan, ji tayi idanun ta sun ciko da k'walla kawai sai ta sadda kanta k'asa ta daina barin kallonshi shi kuma yanata kallon ta bayan d'an wani lokaci taji ya kira sunan ta shiru ta d'an yi bata amsa ba, a duniya tana jin ba wanda ya iya kiran sunanta kaman yadda yake yi don sosae yake fitar da ko wane harafi,

"ba ki ji na kira ki ba?" Jin ya fad'i hakan yasa ta d'ago ta kalle shi idanunta sun d'an tara k'walla a hakan ma tayi kokarin maida wasu, "baki so tazo ne?" yana mata wani kallo ya tambayi hakan da sauri ta d'aga mashi kai,
"Why?"
"To ai ba kyau fa hakan kuma nasan ka sani taya wata zata zo ta taya ka zama ina laifin ko abokin ka" cikin yar karyayyar murya ta mai son yin kuka tayi Maganar, shiru yay idonshi cikin nata tana ta yan d'aure dauren fuska can taga yay wani d'an murmushi tare da ta6e baki ganin haka yasa ta maida idonta k'asa kawai sai ji tayi k'walla sun zubo mata sharr kiran sunanta ya k'ara yi ta d'ago saida yay mamakin ganin kwallan duk da bai nuna ba, ce mata yay don wata zata zo ta taya shi zama shine yasa take kuka shiru tay bata ce komai ba tana ta yan kyafcen kyafcen idanu,

"In kuma wadda zata zo d'in Wife ena ce shima hakan ba kyau ne?" kaman daga sama taji ya fad'i hakan da sauri ta tsaida idanunta kan shi ya d'age mata gira alamar ta bashi amsa, shiru tayi tana juya abunda ya fad'a a cikin ranta tunanin to wacece Matar tashi ta shiga yi can zuciyarta ta raya mata ita yake nufi ko, sai lokacin ta gane kan Maganar tun daga farko tayi zuru zuru tana kallon shi yana d'an shigar da lip d'inshi na k'asa kafin ya saki yace bata bashi amsa ba, cikin jin yar kunya tace to ai bai fad'i mata hakan yake nufi bane ita tayi tunanin wata ce kawai da ba komai tsakanin su zai kawo, d'an ta6e baki yay kafin yace yar k'arama da ita tasan kishi, Maganar dariya ta bata tasa hannunta daya sha k'unshi ta d'an rufe fuskarta kafin ta cire a d'an shagwabe tace "nifa ba yarinya bace tunda na wuce 20yrs kuma baka ga ba Secondary nike ba, kuma ai ko K'aramin yaro yana kishin abunda yake so" ita kanta ji tayi kawai ta fad'i hakan, hannu ya kai ya d'an shafi beard d'in shi murmushi ya bayyana akan fuskar shi yace mata ashe tana son shi ta d'aga mashi kai yace amman ai bata ta6a fad'i mashi ba tace to ai bata san ko bai son ta fad'i mashi hakan ba yay shiru kawai yana kallonta, tattaro k'warin gwuiwa tayi idonta a cikin nashi ta furta "I love you with all my Heart" gani tayi ya d'an fad'ad'a murmushin da yake tare da d'an ta6e baki yanayin yadda yayin sai taga kaman abunda tace bata yi mashi gwaninta ba, abunda bata sani ba shine sosae yaji dad'in Maganar duk da ba bak'uwa bace a wurin shi kullum mata cikin fad'i mashi Kalmar suke don ko yau an fad'i mashi amman tata sai yaji tayi mashi dad'i shi kanshi yana mamakin kanshi sosae yadda akai Ya fad'a son ta don sosae yake jinta a ran shi (abun daga Allah ne), furta mata Thanks yayi ta d'an yi murmushi sai kuma tace to shi bai ce mata ba still da d'an murmushi a fuskar shi yace ai yayi wannan tun da yazo garin su ta d'an tura mashi baki tace wannan ai dalili ne yasa ya fad'i mata kuma yanzu bata san ya take a wurin shi ba, shiru yay kawai yana kallonta don Maganar tata ta bayyana yarintarta a wurin shi don in bai sonta Maganar auren su zata d'ore ne, d'an yamutsa mashi fuska tayi tace ita bazai fad'i mata ba d'in,

"Not now" shine abunda taji ya fad'a ta gyad'a kai, cigaba da kallon juna sukai tana ta mashi murmushi shima fuskar shi a d'an sake can ya kai hannu ya shafi forehead d'in shi bayan ya ciro hannun ya d'an yi yar hamma, tambayar ta yay har yanzu jin muryar nashi bai isheta bane yana son yayi bacci yadda yay Maganar har saida ya bata dariya cikin wasa tace "ai bata isa na in ina jinta ban k'i ma mu kwana ba inata jinta" d'an wara ido yay ya tambayi is she serious ta d'aga mashi kai kafin tace ko ba zai iya kwana yana hira da ita ba , shiru ya d'an yi yana kallonta kafin yace to mi zai sa su kwana suna magana ai sai Maganan ma ta k'are tana yar dariya tace ba gashi yanzu ma sun d'auki lokaci suna hira ba kuma maganan bata k'are ba ai haka hiran love yake in ana yi ba'a gajiya, wani kalan kallo Yay mata yace waye ke yin love d'in ta nuna shi sannan ta nuna kanta wani irin kallo yay mata ya furta dama ashe bata ji ko tana dariya tace a'a ita tana ji ai ba k'arya tayi ba love d'in suke taga ya d'an girgiza kai slowly yace shi bai yin love da yarinya jin Haka yasa ta tura mashi baki kaman zatayi kuka tace Don Allah ita ya daina ce mata yarinya kawai sai gani tay ya saki yar dariya har dimple d'in shi ya d'an lotsa dama ya fahimci bata son ya kira ta da yarinya, bin shi tayi da kallo ko k'yaftawa bata yi can ta furta mashi dariya yana k'ara mashi kyau sosae kawai sai gani tayi ya d'aure fuskar yace ta fara raina shi ko ganin yadda yayi Maganar ne yasa da sauri ta girgiza mashi kai tace "taya zan raina ka bacin kai mutum ne mai girma da daraja a wurina wanda yay man alfarmar da ban ta6a zaton zan samu irinta ba a rayuwata, kullum ina son in gode maka amman na rasa taya zan hakan don Kalmar Thank you isn't enough, but I promise you I will be a devoted wife to you, I will make sure I give you all the happiness a wife can give to her husband in sha Allah, ina baka hak'uri in Maganar dana yi ka d'auka raini ce ba haka bane wllh kawai ina jin dad'in in ka sake man muna magana tunda ba cika yi kake ba" yadda ta k'arasa Maganar kamar zata saki kuka, murmushi taga yayi tare da lumshe mata ido a hankali ya furta mata thanks tare da Fad'in yana mata wasa ne kawai, sosae taji dad'i tana ta murmushi tace to yayi mata fatan Allah ya bata ikon yi mashi abunda tace ya d'aga kai kafin yace hakan itama tace mashi thanks, sigh yay ya furta "My devoted wife pls allow me to sleep na gaji sosae" Dariya Fauzy ta saka jin abunda yace shima yar dariyar yayi tace mashi to ya kwanta saida safe Allah ya tsare mata shi harda cewa yayi mafarkinta ya d'aga mata kai ta d'an d'aga hannu tana mashi bye bye daga haka yay disconnect, bayan sun gama wayar d'age kanshi yay a jikin kan gado yana d'an murmushi wani irin nishad'i yake ji tunda yake hira irin haka da mata bai ta6a jin dad'in wata ba kamar wannan lokaci guda yaji ya k'osa su zama ma'aurata don ta kasance a kusa da shi, itama bayan sun gama fad'awa tay saman gado tana murmushin jin dad'i wani kalan nishad'i na ratsa dukkan jikinta don tunda take dashi basu ta6a yin hira ba haka, lumshe ido tay suffar shi na dawo mata nan ta fara imagination d'in sun zama ma'aurata can ta bud'e idanun da sauri tana yar dariya a fili ta shiga yin godiya ga Allah da wannan babbar ni'imar da yayi mata don ko a iya haka sanin Sameer d'in da tayi tasan ni'ima ce, tana ta tunane tunanen shi a haka bacci ya kwashe ta.

Washe gari Misalin k'arfe goma saura masu tafiya nata shiri, bayan Aunty Mareeya ta gama shiryawa ta nufi part d'in su Fatuu, lokacin data je har sunyi wankan safe ta koma ta kwanta saidai ba bacci take ba hira suke da Mino sai Aysha kanwarsu, da sallama ta shigo cikin Bedroom d'in Fatuu na ganinta ta yunk'ura ta tashi zaune tana fad'in sunanta ita kuma tana amsawa tana karasowa wurin gadon, a baki ta zauna Fuskar kowannen su da Murmushi su Mino suka gaishe da ita ta amsa tare da Fad'in har an shirya tace mata eh, gaishe da ita Fatuu tayi ta maido idonta kanta ta amsa tace har anyi wankan safe tace mata eh, kallon su Twins tayi dake cikin gadon su tace suma sun sha wanka suna ta bacci Fatuu tace eh sun sha wankan Kakar su Yadikko Aunty tace ah lalle dole suyi bacci ashe mata ce ta sulle su duk akai yar dariya, tunani Fatuu tay k'ilan ko Maganar da sukai ne tazo fad'i mata tunda dama tace sai tazo Abuja hakan yasa ta kalli Mino da fulatanci tace su d'an basu wuri tace to ta kamo hannun Aysha suka nufi hanyar fita, bayan fitar su ne Aunty Mareeya tace "Yauwa dama kamar kinsan magana nike son muyi duk da dai ma ba wata ta sirri bane ai kan Maganar da muka yi ta gidane, na kira Yayan mu yaje ya samu Baban mu sun tattauna, abunda ke faruwa Zarah gaskiya samun irin gidan da shi Sameer d'in zai so zai yi wuya a garin namu yawancin manyan gidaje duk masu su ne a ciki saidai za'a iya samun sabo wanda ba'a kammala ba sai a ida ginawa to amman irin wannan gaskiya sai a wajen gari haka, to yanzu dai shawarar da aka yanke itace wai ko kawai ayi renovating namu gidan tunda ba laifi d'an babba ne kuma gaskiya ginin shi mai kyau ne don da asali ginin k'asa ne irin na da d'in nan to a hankali lokacin Babanmu na aiki ya fara maida shi na bulon siminti zuwa lokacin daya aje aiki aka gama maida shi gaba d'aya na siminti kinga sai kawai a gyara a yi mashi dai irin adon zamani, kai Fatuu ta jinjina bayan ta gama tace "kuma hakan yayi Aunty Mareeya tunda kun saba da Unguwar gaskiya bazaku ji dad'in barinta ba kuma sai ma a maida shi na bene kawai" d'an zaro ido Aunty tay "na bene kuma Zarah, a'a ba sai anyi wannan uwar dawainiyar ba kar ma aga mun zaqe ki dai fad'a ma mijin naki yadda nace kar ai zancen benen nan" ta k'arasa tana yar dariya Fatun ma ita take yi tace ai da ta bari an fad'i hakan tunda dai yana da halin Aunty Mareeyar ta ce "ke dai kada ayi Maganar benen nan tawajena kinga sun duba mana sosae ban ma fad'i maki ba jiya fa Her Excellency tayi magana dani tace ba sai anyi ma Fauziyya komai ba na aure iya ita suke buk'ata" waro ido tay tace don Allah Aunty tace mata Allah kuwa, sosae Fatuu taji dad'i ta shiga washe baki tana fad'in kamar irin yadda akai mata itama ba'ayi mata komai ba Aunty tace ai yawanci Kusan duk kaddarar su daya da Fauziyya shiyasa Allah ya had'a su Fatuu tace hakane tay fatan Allah ya nuna masu bikin Aunty tace "Amin ya Rabbi, ai wllh a k'agare nike da inga anyi bikin nan ai dole ma ne muci uwar sabada bayan mun yi godiya ga ubangiji" dariya sosae Fatuu ke yi, bayan ta tsagaita tace "wai Aunty ina wannan mayaudarin daya yaudari Fauzy ya kuwa san da Maganar zata yi aure?"

"Oho, wama yasan duniyar da yake nasan gaskiya bai san da Maganar ba don kinsan fa Babanmu ya hana a bud'e Maganar yace a bari sai komai ya tabbata amman yanzu nasan da an fara aikin gidan zaki ga abun ya bayyana" jinjina kai Fatuu tay tace zata so taga fuskar shi ranar daya ji Maganar Aunty tay dariya tace shegen k'ilan har ciwon zuciya sai ya kama shi,

"Yauwa ina son dama in yi maki magana kan gyaran jiki kinsan fa jinin haihuwa na lalata duk wani shiri na jiki don haka dole sai kin k'ara yin sabon gyara" da sauri Fatuu tace eh dama tana son yi mata magana akan hakan, tambayar ta Aunty tay ai har yanzu jinin na zuwa ko tace mata eh ta sake tambayar ta yaushe zasu dawo Katsina ne tunda gama jarabawar su ta k'arshe ta taho tace sunyi magana da Ya Haisam kan hakan bada jimawa ba zata dawo Aunty tace "to abunda za'ai yanzu da mun koma zan tanadar maki masu kyau dama akwai wanda nasa za'a kawo ma Fauziyya daga Nijar don har yanzu ban fara bata komai ba Saboda kinsan in akwae k'ananun shekaru to ba buk'atar asha abubuwa sosae k'arshe yazo ya damu mutum shiyasa na bari sai gab da bikin amman dai ina bata nama mai romo sosae haka su fruit da fresh milk sosae nike sata tana ci Mino ma yakamata ace zuwa yanzu ana bata su sosae duk da dai bansan ko ana hakan ba amman dai zan ma gwaggo magana zuwa lokacin da za'a fara basu magungunan, shiri na musamman za'a yi masu in sha Allah",

Fatuu na dariya tace "shiyasa nike son ki Auntyn mu" itama dariyar take tace "ai bani da burin daya wuce inga kun kama mazajen ku gam gam wllh kuma ta wannan hanyar ne kawai in kuma aka had'a da biyayya ai magana ta k'are" kai Fatuu ta d'aga ta k'ara cewa "in dai kinga alamun ba nan kusa zaku koma ba to ki man magana sai in aiko maki dasu nan kema kuma sai ki dage da cin abubuwan dana lissafa kinga ma har twins d'in mu sun amfana suma tunda naga kaman kina da kyaun ruwan nono don cikin sati d'aya kinga Tubarkallah sun k'ara girma wllh" amsa mata tayi da to suka d'an k'ara yin hira kafin Aunty ta mik'e tace yadda sukai da Haisam sai ta sanar mata tace to in sha Allah yanzu bada dad'ewa bama zata yi mashi Maganar. Misalin k'arfe goma da rabi duk masu tafiya suka firfito lokacin tuni su Hajiya Zainab sun tafi harda Mahaifiyar su da yan'uwanta yan Ethiopia suka tafi can Nasarawa haka su Hajiya Maryam ma Farha harda musayar lambar waya ita da Fatuu don Hajiya saida ta k'ara masu fad'a da Nasiha kan rashin shirin da suke ta nuna masu duka duniyar nawa take, dama su Yadikko driver da ya kawo su ne zai mayar dasu shi dai Kamalu Katsina zai wuce dama da shirin hakan ya taho don sun gama magana da Kawu Amadu zai koma can shima yaci gaba da karatu Saboda yanata zama ba karatun tun bayan daya gama Secondary, yan d'aura ne suka fara tafiya gaba d'aya su Mom aka fito yi ma su gwaggo rakiya driver su Yadikko nan cikin harabar gidan ya shigo Haisam yaje bayan sun gaisa ya tambayi yadda aka yi dashi zai kawo su ya kuma maida su cikin washe baki driver d'in yace ai shi Abokin Mahaifin ita mai jego d'in ne to yadda sukai ya zuba mashi mai ne zai kawo su ya koma dasu sannan sai ya Sallame shi Haisam d'in ya tambaye shi nawa ne kud'in sallamar yanata washe baki yace mashi ai ko nawa ne aka bashi lafiya lou tunda dai duk abu na gida ne, kud'i masu yawa ya bashi yana ta godiya da sa Albarka sai daga baya ma ya gane shine Mijin inna wuron suma su Yadikkon saida ya basu kud'i wai susha ruwa a hanya su Yaya ana ta washe baki ana godiya, su Gwaggo ma saida ya basu kud'in dama da zasu zo saida ya tura ma Abbas da Tk kud'in mai, Gwaggo da Aunty Mareeya suna ta ya barshi don Allah shida yay hidima yana murmushi yace masu ba wani abu, Nameer na lik'e da Mino sai shagwaba yake mata wai dama ace Shikenan tazo bazata koma ba tana ta murmushi ita kanta ji take kamar kar su rabu ba kamar yanzu da taga ya wani k'ara yin Fresh, sallama suka shiga yi ma juna su Mom da Hajiya nata masu godiya da Addu'ar Allah ya bar zumunci duk suka shishshige cikin Mota Abbas ne ya d'an d'aga murya yace ma Mino in sun gama shan soyayyar ta taho su tafi in kuma su barta anan to su Mom duk sukai dariya Hajiya tace ai in sun bartan daidai kenan kawai sai a d'aura aure ya wuce da ita ba shikenan ba ita kuwa Mino kunya ce ta kamata, daga baya dai duk suka shishshiga ana ta d'aga ma juna hannu a tare Motocin suka tafi sai fatan Allah ya kai su lafiya sai kuma an sake had'uwa bikin su Mino da Aunty Laila.

Misalin k'arfe biyun rana lokacin Aunty ta dawo daga aiki don bata nan yan tafiya suka tafi bayan ta kimtsa ta nufi part d'in su Fatuu don duk su Aunty Laila na can harda Fanan anan ma suka ci abincin rana gaba dayansu don yaran gidan k'in zuwa School sukai wai gajiyar suna bata sake su ba, tana shiga duk suka yi mata Welcome kowa yana murmushi haka itama shi take masu ta nufi kujera tana ruk'e da wasu Manyan fararen ledoji masu d'auke da tambari ta zauna Jidderh ce ta tambayeta ta zubo mata Abinci tace eh ba da yawa ba ta d'an ci wani a wurin aiki tace to ta fita, bayan ta gama cin Abincin an saka su Yasmeen sun gyara d'akin Aunty ta d'ago jakar ta mik'a ma Fatuu tace gashi nan tayi amfani dasu ta d'ago d'ayar itama m'ika ma Fanan tace d'ayar Momyn twins itama gashi a tare duk suka bud'e, wasu had'addun laces ne kowa guda d'aya sai kuma manyan atamfofi na Fatuu guda biyu ita kuma Fanan guda d'aya, nan fa aka shiga yi ma Aunty godiya sosae Fanan taji dad'in hakan da tayi mata itama tayi mata godiya ta mik'e da sauri tana ruk'e da jaririn ta nufi hanyar fita tana fad'in bari ta je ta gwado ma Hajiya anata mata dariya don kowa ya fahimci taji dad'in kyautar, bata dad'e sosae ba ta dawo tana ruk'e da ledar cikin washe baki tace Hajiya tace ayi mata godiya sai ta shigo zata k'ara mata Aunty dake dariya tace sai kace wani abu Fanan d'in tace aikuwa wani abu ne don babbar kyauta ce nan suka cigaba da yin fira har aka yi La'asar, bayan sallar ne Fatuu tace ma Aunty Laila don Allah ta tayata su duba kayan da aka samu tace to nan aka shiga fiddo kayayyakin kili guda harda Fanan aka shiga bubbud'awa ana shirya su, Kusan raba kayan Fatuu tay wanda nata ne taba Fanan wai ta bata aikuwa tace wllh bazata amsa ba sai kace ita tayi mata nak'udar, K'arshe da k'yar ta amshi wata doguwar riga cikin wanda kakar su Haisam ta kawo mata daga Qatar tare da kayan jarirai had'add'un gaske duk da haka saida Fatuu ta k'ara mata da wata babbar atamfa ta rok'e ta kan ta amsa sannan ta amsa tayi mata godiya sosae, wasu masu yawa ta k'ara warewa tace ma Aunty Laila gashi ta kai ma Mom suyi amfani da su itama harda rok'onta Laila d'in ta d'an waro ido tace don me zata basu kaya haka ta marairaice mata, yar dariya tayi ta gyad'a kai tace tunda sak'o ne ta bata bari ta kai ma Mom d'in amman ashawarce ma da ta bar kayanta Fatuun ta girgiza mata kai tace Don Allah ta saka Mom d'in ta amsa, Bayan sun gama shirya kayan ta d'aukko jakar da kud'i suke suma ta fara kokarin fiddo su Laila dake kallonta tace mi kuma za'ai dasu tace mata wai su k'irga wani kallo tay mata tace har tama saka zata harareta tana matsayin Yayarta to shima k'irga kud'in aiki ne da bazata k'irga abunta ba, dole Laila tayi mata ta maida kud'in data fiddo bayan sun gama komai ta d'auki wanda ta basu ta tafi.

Bayan Sallar la'asar Fatuu na cikin yin chat saman gado Fanan ma na daga gefenta ta tasa su twins gaba saiga Mom ta shigo Laila na biye da ita d'auke da kayan da ta kai mata tana yar dariya, a saman gado Mom ta sakata ta d'aura kayan kafin ta zauna a sanyaye Fatuu ta gaishe da ita ta masa kafin tace ga kayanta nan ta maido mata a ina ake haka kawai ta kwashi uban kaya ta basu sai kace su aka ba, marairaicewa Fatuu tay ta shiga yi mata Magiya Mom d'in tace bafa za'a amsa ba gara ma kar ta wahalar da kanta, suna haka Aunty ta shigo ganin drama d'in da suke yasa ta zauna tana dariya Mom na cema Fatuu ko tayi Kuka ba za'a amshi kayan ba, tambayar abunda ke faruwa Aunty tayi Mom ta fad'i mata tare da nuna mata kayan ta kalli Fatun tace "to daughter taya za'ai hakan ai kayan ki ne ko kiyi amfani da abun ki" murya kamar zata yi kuka tace to ai kayan da yawa ya zatayi da su Mom ce tace ba tana da yan'uwa ba sai ta babbasu suma suci albarkacin twins suyi masu Addu'a,

"Amman Mom kuma ai yan'uwan nawa ne ko",

tana yin Maganar k'walla suka zubo mata Mom ta d'an bud'e ido tace miye abun kuka anan, Aunty ce tace yanzu dai tunda hakane Shikenan a d'an d'auka suma suci albarkacin twins d'in tunda haka take so, ba wasu kaya masu yawa ba suka d'auka duk da haka Fatun taji dad'i hannu ta kai ta d'aukko jakar da kud'i suke Laila na ganin haka tace "Mom see, wai kud'in ma sai an gani" wani kallo mai kaman harara Mom d'in tayi mata Fatun ta marairaice fuska tana niyyar yin Magana Mom tace "Daughter yaushe muka fara wasa irin wannan ne?" abu Fatuu ta had'iya ta d'an girgiza mata kai kamar zatayi kuka ta bata hak'uri tace dama tana son nuna masu ne Mom d'in tace mata ba buk'ata komai ta gani nata ne tayi duk abunda take so da su ta d'aga mata kai, abunda Mom ta ruk'o a hannunta ta mik'a ma Fatun tace to itama ga nata tunda ta kar6i nata Fatuu tabi yan kunnan zinari da take Mik'o mata da kallo Mom tace mata ta amsa mana ta mik'a hannu ta amsa gudun kada ta k'ara cewa ta raina ta, kallon Fanan tayi itama ta mik'a mata zoben zinarin tace itama ga nata ta waro ido tare da d'an bud'e baki cike da mamaki tace itama harda ita ta d'aga mata kai kawai sai ta matso ta rungume Mom d'in tana mata godiya su Aunty ma da Fatuu sukai mata godiya, bayan Fanan ta saketa ta saukko daga saman gadon ta nufi hanyar fita tace shima bari ta nuno ma Hajiya.

A Ranar da daddare duk suna a part d'in Fatun harda Hajiya da Haisam da Nameer gaba d'aya yan gidan anata hira ana cin naman suna ana korawa da lemu Aunty na ta cema su Jidderh wllh su bi a hankali ganin yadda suke ta d'irka kamar sun samu Abinci wai naman dad'i yafi wanda aka saba soya masu Hajiya tace ai haka naman suna yake, suna anan Dad ya dawo shima ya nufo nan part d'in su twins suka mik'e da gudu suna mashi oyoyo ya ruk'e su ganin bakin su jage jage da mai yace miye suke ci haka a tare suka ce naman suna ne ya d'an waro ido yace shine ko a tuna dashi suka ce ai akwai da yawa sosae ya d'aga kai suka nufo ciki, sannu da zuwa aka shiga yi mashi yana amsawa bayan ya zauna ya gaishe da Hajiya tayi mashi an dawo lafiya ya amsa Jidderh tace a zubo mashi naman shima yace anya dare ne fa suma suci a hankali in mutum yaci ya kwanta yana iya samun matsala Aunty Laila dake taunar naman tace ai zasu sha flagyl kafin su kwanta duk aka saka dariya, shima d'an kad'an yasa aka bashi ya fara ci abun gwanin sha'awa k'arshe dai saida Aunty tasa aka d'auke naman daga falon, Bayan Dad ya gama ne aka bashi tissue ya goge hannun shi ya kai hannu cikin aljihun rigar yar cikin shi dama saida yaje part d'in shi ya cire babbar rigar sannan ya nufo nan, wasu takardu ya fiddo guda biyu ya mik'a ma Mom yace taba Daughter gashi nan takardun gidaje ne guda biyu a cikin na Estate d'in shi yaba Abokanshi su daga yanzu kud'in hayar su nasu ne a bud'a masu Account a rink'a saka masu, wata irin shewar farinciki su Aunty Laila da Jidderh sukai su Mom da Aunty ma sai dariyar farinciki suke suna yi ma Dad d'in godiya da Allah ya kara girma da Arzuki, bayan an mik'a ma Fatuu takardun a sanyaye tayi mashi godiya da Addu'ar Allah ya k'ara girma da daukaka yanata amsawa, Hajiya ce tace wato salon sabon Angonta yaga bata yi farinciki da shi ba shiyasa zai masu wannan babbar kyauta haka to itama baza'a barta a baya ba ta basu d'aya daga cikin filayenta na Katsina wannan karon ihun murna Aunty Laila ta saka tana fad'in kaga yara masu k'ashin arzuki daga zuwan su duniya har sun zama masu arzuki,

"Wai to sai ba yaran kyauta kuke ita Mom d'in tasu fa?" Jidderh ce ta fad'a tana tura baki idonta akan Dad d'in su yana yar dariya yace yana sane da ita in sha Allah ita da yar'uwarta zasu je Hajjin bana amman tunda da sauran lokaci zasu fara zuwa Umra gaba d'aya gidan zo kaga farinciki su twins harda rawa suna fad'in dama an dad'e ba'a je dasu ba, Mom ce tace Shikenan ma in suka je sai a biya Qatar a gaido Abie Dad yace ba matsala ya kalli Fatuu yafe ta fad'i daga nan in akwai wata k'asa da take son zuwa Albarkacin su twins sai a wuce tayi shiru tana ta murmushi tama rasa mi zata ce don gaba d'aya bakin ta ya mutu su Aunty Laila na ta fad'i don Allah, Haisam ne yace sun kusa fara Final Exams d'in su ne bai fi nan da 2 Months ba Dad na jin hakan yace to a tsaya daga Qatar d'in, kallon Hajiya Jidderh tayi tace to itama bata ba Aunty Fanan da Fatuu kyautar ba ta d'an kwa6e fuska tace dole sai ta basu suma Aunty Laila tace eh gaskiya tace to ta basu kowa kaza da zakara suyi kiwo gaba d'aya aka saka dariya Fanan tace ta gode zata tafi US dasu tayi kiwon acan Aunty Laila tace gaskiya kyautar tayi kad'an Hajiya ta d'an harareta tace to ina laifi tasan Arzikin da zasu iya janyo masu Jidderh tace duk da haka dai gaskiya sunyi kad'an,

"To tunda had'in kai za'a nuna man Shikenan na basu kowa tunkiya da rago daga haka bazan k'ara ba" dariya aka fashe da ita Dad yace ai wannan ma ta basu mai yawa don tushen garke ne gaba d'aya sukai godiya,

"to wai shi Angon jegon fa banga an bashi komai ba" Aunty ta fad'a Dad na dariya yace "k'yale wannan mai kud'i ne shi" tace duk da haka dai shima a bashi gaskiya Arzik'in su twins Dad d'in ya kalle shi yace yana son wani abu ne a hankali ya girgiza kai yana murmushi yace a'a an gode da wanda aka bada Allah ya k'ara lafiya da Arziki suka amsa da Amin, Dad ya kalli Aunty yace to taji dai bai son komai tana yar dariya tace to ai ba haka yakamata a yi mashi ba shima sai a bashi kawai ba ai mashi tayin rowa ba duk akayi dariya Hajiya tace to ai shima ba za'a je dashi Umra d'in ba Aunty Laila tace wannan to na Dad ne saura ita ta bashi kyautar tace Shikenan shi ta bashi kaza da zakaran da suka guda duk aka kwashe da dariya harda Haisam d'in abun gwanin nishad'i haka suka cigaba da yin firar su lokacin Dad ya tambayi Hajiya nan da 2 weeks lafiya lou za'a iya yin tafiya da yaran Saboda suje su dawo Daughter ta koma School tace mashi eh yace to sai su shirya duk aka k'ara yi mashi godiya.

Bayan sati guda da yin suna yan Ethiopia suka koma lokacin saura sati d'aya su Fatuu su tafi Umra, sosae take samun kulawa gaba d'aya ita da yaran sunyi 6ul6ul dasu gwanin sha'awa, ana saura kwana ukku su tafi Hajiya tace mata in akwae kayan da za'a tafin mata dasu Katsina ta bada tunda da sun dawo zasu wuce can tace to. Lokacin da suka je Umra Fatuu harda kukanta na farinciki ganin gata ga ka'aba, sosae tayi Addu'oi daga cikin wanda tafi yi ma Addu'a akwae Mahaifiyarta da Mahaifinta sai mijinta da gwaggo, Hajiyar Sanata da kuma iyalin Sanata d'in sai sauran yan'uwanta da Abokan Arzuki harda Haulat bata manta da ita ba tayi mata Addu'ar Allah ya bata miji wanda zai kula da rayuwar ta da yarinyar ta, Satin su guda suka wuce Qatar sosae aka karramasu ba kamar Fatuu da su twins sai faman nan nan ake dasu gidan Yaya Othman d'in da suka sauka shi kan shi abun kallo ne don duniya ce mai zaman kanta ko ina walwali ke tashi kai kace da zallar gold aka yi gidan Fatuu ta girgiza da ganin gidan don bata ta6a zaton a rayuwarta zata ganta a cikin gida ba irin wannan, sun zaga garin sun sha hotuna sosae garin da suka je ya had'u Over don shine babban birnin su wato Doha, Birni ne na zamani kuma na duniya mai kyawun sararin samaniya, akwae gidajen tarihi da abubuwan jan hankali na al'adu kuma babbar cibiya ce ta kasuwanci da yawon bude ido na duniya, nan ma sati guda sukai suka juyo Abuja Haisam da Fanan kuma suka wuce US, kwanan su biyu da dawowa suka dawo Katsina, Ranar da suka dawo da daddare Fatuu ta nufi gidan su Haulat tare da Mino ta goya mata yaro guda don tana nan ta dawo anan take takaba don tun bayan rasuwar mijin nata bata jin dad'i hakan yasa aka dawo da ita nan yanzu ma har ta kusa gama takabar, lokacin da suka ga juna ita da Fatuu kuka sukai ta yi innar su na basu hakuri tana ruk'e da yaran tayi ma Fatuu barka tace taso tazo Abuja suna to Saboda yanayin da haulat take ciki yasa bata zo ba Fatun tace mata ba komai itama tana ruk'e da d'iyar Haulat, sosae tausayin Haulat ya kamata ganin yadda ta rame tana kwalla ta shiga rarrashinta kan ta rage damuwa tayi hak'uri tay d'an murmushi tace wllh ta bari ta rungumi kaddararta kawai abun ne wani lokacin in ya taso mata sai taji damuwa, k'arfafa mata gwuiwa ta shiga yi tace in sha Allahu zata samu miji wanda zai kula da ita ya ruk'e Umma Salma tamkar d'iyar shi a sanyaye Haulat d'in tace Allah yasa amman ita yanzu ma gaba d'aya auren ya fitar mata a rai Fatuu tace ta daina cewa hakan don zai zama tamkar bata yarda da kaddarar ta ba ta mik'a komai ga Allah in sha Allahu zai ji6anci lamuranta tace Allah yasa, anan ta kira Haisam ta bashi Haulat d'in ya k'ara mata gaisuwa, sosae Haulat ta yaba da su twins haka ma innar su sai faman fad'in Tubarkallah take daga baya sukai masu sallama suka tafi, Bayan komawar su gida Fatuu ta kira Aunty Mareeya ta sanar mata jini ya d'auke mata tun kafin su tafi Umra Saboda tafiyar yasa bata sanar mata ba amman ta fara amfani da wasu magungunan da Yadikko ta kawo mata tace to zata ba Fauzy sak'o ta kawo mata, washe garin da suka dawo ne Hajiya tayi ma Saude Magana akan ko za'a samo ma Fateema mai raino da zata rink'a taimaka mata Saboda zuwa Makaranta tace to za'a samu zata yi magana can gidan su, a Ranar da yamma Fatuu ta had'a uban kaya su atamfofi da lace harda dogayen riguna wasu daga cikin nata da tasan zasu yi ma Haulat da kayan shafa harda naman suna da kuma kud'i dubu hamsin taba Mino tace ta kai mata tace mata ta fara amfani dasu, lokacin da takai kayan Haulat kuka ta saka a haka cikin kukan ta kira Fatun a waya tace ya zatai mata wannan uwar dawainiyar tace mata ba komai tana dasu ne ita dai fatanta ta kwantar da hankalinta ta daina damuwa tace in sha Allahu ta daina, har gida washe gari innar su tazo tayi mata godiya harda rigunan jarirai ta kawo ma su twins taje tayi ma Hajiya barka anan take ce ma innar tasu ashe Haulat d'in gida ta dawo ta fad'i mata bata jin dad'i ne gashi ta saka damuwa a rai cike da tausayawa Hajiya tace ai dole ne don rashin miji ba K'aramin rashi bane tace ayi mata gaisuwa sai tazo innar tayi mata godiya kafin ta tafi.

Kamar yadda Hajiya tace taje tayi ma Haulat d'in gaisuwa tare da Saude suka je bayan sun dawo ne tayi masu Aiken kayan abinci masu yawa, sosae Fatuu keta gyara kanta bayan Aunty ta aiko mata da magungunan Saude kuma ta samo mata mai tayata rainon su twins tare suke zuwa Makaranta da ita, sosae take missing d'in Haisam sai bayan wata d'aya da dawowar su sannan yazo suka shiga shan sabon Amarci lokacin ne yayi ma Sameer magana kan zuwa Funtua gaishe da iyayen Fauzy da yake yana a K'asar, ya amince zai je harda cewa jirgi zasu hau ko Haisam na dariya yace mashi ai ba Airport acan dole a Mota zasu anan suka tsaida Ranar da zasu Haisam ya fad'i ma Fatuu ita kuma ta kira Aunty Mareeya ta sanar mata aikuwa sosae taji dad'i tace dole zata je don a tarbesu yadda yakamata. Ana saura kwana biyu suje Haisam ya tafi Abuja don daga can zasu wuce Aunty kuma washe gari ta tafi Funtua, Ranar da zasu zo ta kama Asabar da wuri suka taho Mota biyu sukai d'aya wadda suke ciki driver na jan su sai kuma d'ayar ta security, gaba d'ayan su farar shadda ce a jikin su anyi masu kalar d'inkin da suka fi so sai baza k'amshi suke k'afafuwan su na sanye da dakakkun takalma haka agogunan hannunsu ba sai na fad'i masu tsada bane yau dai kawunan su sun samu Arzik'in huluna amman shi Sameer bai saka ba tana dai ajiye k'ilan sai sun isa zai saka, duk tafiyar ta fara gundurar Sameer don har Fuskar shi ta nuna tun yana yin shiru har takai ya fara tambayar driver ko sun kusa isa sai yace mashi da saura, Haisam daya lura ran shi ya fara 6aci yana murmushi yace mashi gara ya saba kafin Ranar d'aurin aure ai tun kafin ya rufe baki ya fara girgiza mashi kai yace bazai k'ara wannan tafiyar ba Haisam da still Murmushi yake yace to ya za'ai Ranar d'aurin auren fuska a tamke yace oho shidai bazai zo a Mota ba, lokacin da suka iso garin gaba d'aya ran Sameer ya gama 6aci Haisam ya fara bashi hak'uri yana nuna mashi ai sun iso ya yamutsa fuska yace to mi akai tunda zasu koma, Yaya Mubarak ya kira ya sanar da shi gasu sun shigo gari yace Ok yana fara mashi bayanin inda zasu nufo su had'e ya mik'a ma driver wayar yaci gaba da mashi bayani, sai faman bin garin Sameer yake da kallo haka Haisam ba laifi Sameer yaga ba k'auye bane kamar yadda ya zata, lokacin da suka had'e da Yaya Mubarak yana ganin Motocin ya gane sune yay ma driver d'in alamun ya tsaya, nufar Motocin yay da sauri aka sauke mashi glass cikin girmamawa ya gaishe dasu tare da yi masu sannu da zuwa Haisam ne ke amsawa shi kuwa Sameer tunda ya d'aga mashi kai sau d'aya bai k'ara ba balle ya tanka, bayan sun gama gaisawar yace ma driver d'in ya biyo shi a baya ya koma Motar shi suka tafi, lokacin da suka k'arasa anata aikin gyaran gidan don Kusan ma an kusa gamawa don an d'aura bene komai dai ya kusa kammaluwa, a falon Baban su aka sauke su wanda tuni an canza mashi fasali don shi yace ko angama ginin bazai hau sama ba dama kuma da k'asan aka fara gyaran, sosae aka nuna farincikin zuwan nasu duk samarin gidan da yan'uwan mahaifin nasu harda shi mahaifin nasu sun zo sun gaisa dasu sai basu girma ake ba laifi Sameer d'in ya d'an saki fuska amman kowa daya gan su yake gane shine wanda Fauziyya zata aura don sun san labarin shi, Aunty Mareeya na a falon tana gabatar masu dasu da kuma dangantakar su haka suma su Haisam d'in tana gabatar masu da dangin nasu nan aka shiga yi masu godiya yawanci dai Haisam ne ke magana, koda Aunty tayi masu Maganar Abinci cewa sukai a k'oshe suke sai da ta matsa masu sannan suka d'an ci wanda ta kawo masu kan c-table dama tasan ana iya yin hakan shiyasa basu wani yi Abinci masu yawa ba, bayan sun gama zama tayi tana k'ara yi masu sannu da zuwa da godiya ta lura da yanayin Sameer duk da tasan halin shi tana murmushi tace "K'ani na ansha gajiyar Mota ko" kallon Sameer d'in Haisam yayi yana murmushi shima ya d'an yi kad'an ba tare daya ce komai ba, basu yi awa da zuwa ba suka ce zasu tafi lokacin iyayensu sun dawo cikin parlon aka ce basu bari su k'ara hutawa Haisam yace Saboda hanya kada yamma tayi masu, godiya Haisam ya shiga yi masu na auren da aka basu sai lokacin Sameer ya bud'e baki yay godiyar shima duk suka ce ba komai ai sune da Godiya anata faman dawainiya dasu, a tare gaba d'aya aka fito yi masu rakiya harda Aunty da k'annansu mata harda masu aure da suka zo su Fareeda Mahaifiyarsu ce kawai bata fito ba amman har gwaggo ma ta fito rako su, har zasu shiga Mota Sameer ya dakata ya kira Yaya Mubarak da sauri ya nufo shi, magana yayi mashi saidai ni kaina banji mi yace mashi ba kawai dai sunga Yaya Mubarak d'in nata d'aga kai daga baya ya juya ya shige security ya rufe mashi k'opar anata d'aga masu hannu suka tafi, bayan tafiyar su cikin parlon suka koma gaba daya aka dasa hirar su Haisam d'in sai faman yaba kyaun su ake ana fad'in Fauziyya tayi dace ta ko ina Mijinta yayi k'anin mahaifin su ne yace saidai yaga kaman magana na mashi wahala ga Fauziyya da surutu ya kenan zasu yi zaman auren duk akayi dariya Aunty Mareeya tace haka yake amman in yaso yana d'an yi, Yaya Mubarak ne yayi masu bayanin kiran shi da yayi yace Maganar aikin da ake ne ya tambaye shi ko da matsala sannan ya tambaye shi anan akwae furniture masu kyau yace mashi eh to yanzu yace in aka k'arasa aikin aje a za6i wanda ake su da za'a saka a ko ina sai yayi mashi magana nan fa aka shiga fad'in Ma sha Allah wannan hidima haka abu yayi kyau saidai iyayen Fauzy sun ma kasa magana don Al'amarin ya girmi tunanin su, bayan su Aunty Mareeya da sauran yan gidan mata sun koma part d'in da aka ware masu suke zaune Saboda aikin da ake nan suka dasa hirar su Haisam kowa na fad'in wanda yafi mata wasu suce Haisam yafi burge su wasu suce dukkan su sun yi don suna kama ai sosae,

"Ni wllh wannan farin yafi burge ni da yanzu zai ce yana sona da gudu zan yarda ni koma matsayin mai aikin shi ce in dai zai aure ni" wata k'anwar su ce Nusaiba tayi Maganar dama ga yanayin Maganar ta kamar ta sakarkaru aikuwa gaba d'aya aka saka dariya Aunty Mareeya tafi kowa 6a66aka dariyar ta kai hannu ta bugi shoulder d'in ta tana fad'in "Su an Nusi Nusi anga fari rainon Madara da carpet an rud'e ko, wato in zai aure ki to kima fidda rai don wanccan da kike gani ya auru zuciyar shi a gark'ame take da k'aton kwad'o da Zarah ta rufeta da shi kima fidda rai don ba samu zaki ba" tura mata baki Nusaibar tayi tace kaji Aunty Mareeya da mugun fata tasan abun Allah itama yace yana sonta kamar yadda ya faru da Yaya Fauziyya, Mahaifiyar su da tunda suke abun su bata saka masu baki ba sai murmushi kawai tace "aikuwa Nusaiba koda ace hakan ta faru bazaki aure shi ba, baki ji ana fad'in ana barin halak ko don kunya ba kar ki manta matar shi fa itace silar duk wannan Alkhairan dake samun mu" Gwaggo tace gaskiya kam, tura baki Nusaibar tayi ta juyar da kai sai kace Haisam d'in yace yana son ta yadda tayin ne duk ya k'ara basu dariya,

"Ni gaskiya na Fauziyya yafi burge ni yanayin kalar fatar shi ina son Namiji haka kawai dai na lura kamar miskili ne na bugawa a Jarida" Fareeda ce tayi Maganar Aunty Mareeya tace bari mijinta ya jita tana dariya tace yo yaji mana daga ta yabi mijin k'anwarta, Ummi ce tace ita gaskiya Haisam yafi tafiya da ita don shima da gani miskili ne ga shi yafi na Fauziyya sakin fuska, ganin abun na niyyar zama gardama yasa gwaggo tace bari ta bambanta masu shi na Fauziyya gaskiya kamar yana da izza ne shine kawai Aunty ta d'aga hannu tace yauwa gwaggo kin gane, lokacin da gwaggo ke magana Yaya Mubarak ya shigo jin abunda take cewa ya sashi yin dariya yana k'ok'arin zama yace ai shi ne zai basu labarin irin izzar Sameer tunda dashi suke Maganar aikin da ake yace "wllh ba K'aramin gasa ni yake ba yasa inta faman jiran ya bani amsa sai ya mula yasha iska sannan shiyasa har nafi son muyi chat duk da shima d'in wani lokacin zai duba amman fa ba lalle in samu amsa a lokacin ba haka dai nike ta bin shi sai kace ba Yayan matar da zai aura ba kuma ko a shekaru da gani na girme mashi sosae" gaba d'aya akai dariya Abubakar Yayan Fauziyya amman Kusan tsaran juna ne da ita yace tabb lalle aiki ya samu Fauziyya kafin ya bata amsa sai ta bushe, Gwaggo dake dariya tace ai bata anan tunda yana sonta ita zai iya sakar mata baki, haka dai sukai ta hira kan su Haisam d'in daga baya Yaya Mubarak yay masu sallama zai tafi su Aunty sukai mashi godiya, lokacin da mahaifin su Fauzy ya rako yan'uwan shi zasu tafi suka tsaya suna yin bankwana yana k'ara masu godiya wani makwabcin shi ya fito daga cikin gida ganin shi yasa shi nufo shi har zai juya ya koma ciki ya dakatar dashi ta hanyar kiran sunan shi "Barka Alhaji Rufa'i" dakatawa yay ya juyo ganin shi yasa shi yin murmushi yace "barka dai Alhaji Salisu" hannu ya bashi suka gaisa cikin yar in ina yaci gaba "dama Alhaji Rufa'i ina son tambayar ka ne amman ina gudun kaga kaman na saka maka ido shiyasa nayi shiru to yau dai naga ya dace in maka magana a matsayin mu na makwabta, yan kwanakin baya zuwa yanzu abubuwa na ta faruwa a gidan ka da suke ta jan hankalin mu muna ta ganin anayin bak'i wanda da gani manyan mutane ne tunda harda jami'an tsaro suke zuwa don ko na d'azun da suka zo suma naga haka ga kuma aiki da ya taso gadan gadan cikin d'an kankanin lokaci har an kusa kammalawa to gaskiya hakan yaja Hankulan mu sosae don bazan 6oye maka ba anata magana kan hakan shine na yanke in tambaya ko wani abun Alkhairin ne ya same ka bamu sani ba tunda ba alamun wani abun tashin hankali, amman dai kayi hakuri in nayi maka katsalandan don Allah" fad'ad'a murmushin shi Baban su Fauzy yayi yace mashi ko d'aya wllh dama yana niyyar ya sanar dasu to da rabon shi zai riga shi yin magana, nan ya fad'i mashi abunda ke faruwa tsabar mamaki bakin Alhaji Salisu kasa rufuwa yay yace yanzu Fauziyya dai yar wurin shi daya sani ce zata auri d'an gwamna yace mashi eh, "Yanzu Alhaji Rufa'i ana tare irin wannan abun Alkhairin ya same ka amman ace har tsawon wannan lokacin bamu sani ba, haba Alhaji ko dai baka d'auke mu yadda muka d'auke ka ba ko kuma munyi maka wani abun daya sa haka ne" ya fad'a cikin d'an kwantar da murya Baban su Fauzy nata Murmushi yace mashi ko d'aya kawai dai bai bari abun ya bayyana bane sai ya tabbata tukun tunda yasan sha'anin aure yadda yake, da sauri Alhaji Salisun yace kuma hakane hakan da yayi daidai ne saboda yan tsirku da mahassada to shidai wllh tllh ya taya shi murna sosae Allah ya tabbatar da Alkhairi ya nuna masu, Baban su Fauzy yace Amin shi bama don haka yasa ya 6oye ba kawai dai yafi son abun sai ya tabbata ne. Suna yin sallama Alhaji salisun ya nufi komawa cikin gidan shi wanda da fita ya fito zaiyi, tsaye matan shi sukai fuskar su d'auke da Al'ajabi da yana fad'a masu zancen haka ma yaran shi da suka ji zancen sai faman maimaita Fauziyya zata auri d'an gwamna suke, d'ayar matar shi ce ta buga hannu tace haba biri yayi kama da mutum ashe shiyasa abubuwa keta faruwa suke ganin dankara dankaran Motoci na zuwa gidan, d'ayar matar da bakinta ya gama mutuwa da tsananin mamaki ta tambayi maigidan nasu wai ya akai Fauziyyar ta had'u da yaron gwamna har yace yana sonta ya watsa hannu yace Allah nasani amman shima dai yaji mamakin abun ba kad'an ba, juyawa tayi zata nufi d'akinta tana fad'in bari taje gidan ya dakatar da ita yace ta bari ba yanzu ba don duk yan gidan na nan, d'aya daga cikin yaran shi ne yace ashe shiyasa d'azun yaga had'add'un motoci sun zo harda jami'ai mahaifin nasu yace eh wai shine yazo, kan kace mi matar shi daya hana zuwa har ta fita ta fara fad'a ma sauran makwabta kowa tsananin mamakin jin hakan ya yi. Bayan Yaya Mubarak ya fito saida ya biya wurin mahaifin su don yayi mashi sallama anan yasa shi ya zauna yace yana son zasu yi magana, bayan ya zauna ne a nutse ya fara mashi magana kan abunda suka tattauna da Sameer na furniture yace shi yana ganin da ya bar wad'annan tunda akwae kud'i a hannun su sai suyi kawai hidiman ta isa haka iya wannan ginin da ake masu ba K'aramin kud'i ake kashewa ba, nisawa Yaya Mubarak yayi shima a nutse yace to amman yana iya ganin ya nuna zai yi abu an hana shi don haka shi yana ganin ayi yadda yace d'in sai a fad'i mashi kud'i ba masu yawa ba in ya bada sai a had'a a zuba sababbin furniture d'in in ma ta kama sai a had'a da na gidan a sayar Alhajin nasu yar dariya yayi yace ko dai tsoron mijin Fauziyyar yake don yaga ba alamun wasa a tattare dashi shima dariyar yayi yace a'a kawai dai abunda ya sani su mutane irin su basu son a dakatar dasu kan abunda sukai niyya, mahaifin nasu ya jinjina kai yace Shikenan ayi yadda yace amman baza'a saida wasu kaya ba da niyyar a had'a in Sameer d'in ya turo shi ai mashi magana ya bada wasu sai a hada su kuma tsofaffin kayan sai a samu wasu a basu suma su dangwali arzuki ya k'are Maganar da murmushi shima Yaya Mubarak d'in murmushin yake yace to shikenan, addu'ar Allah ya k'ara mashi lafiya yayi ya amsa kafin yace mashi Shikenan zai iya tafiya sukai sallama, zuwa daren Ranar ai duk yan unguwa sun ji zancen auren Fauzyn anata mamaki wasu dai har sun zo jin kwakwaf da sunan fatan Alkhairi, Washe gari Aunty Mareeya zata baro funtuwar ta dawo Katsina.

Alhamdulillah su Haisam sun koma Abuja lafiya kwanan Haisam d'aya ya dawo Katsina, bayan dawowar shine shima yaje yayi ma Haulat gaisuwa tare da Fatuu anan ya tambayi Fatuu ta amsar mashi account no d'in Haulat bayan ya fito tace to, saida suka koma gida sannan ya tura mata kud'in dubu d'ari biyar nan ma dai Haulat kuka ta saka da taga sak'on innarsu tace rayuwa kenan Allah yana had'a ka da mutum baka san moriyar da zai maka ba ta shiga tuna ma Haulat lokacin da aka kawo Fatuu da yadda in ta k'ule ta take zuwa tace ma innar tasu ita dai ta gaji da abunda take mata tace mata tayi hak'uri, tana kallon Haulat da murmushi tace mata yau ga ranar hak'urin da tayi da ita nan Haulat d'in na d'an murmushi tana d'aga mata kai a cikin ranta tana ta tuna rayuwar ta da Fatuu ta baya. Daga baya har da kaya masu yawa Fatuu ta siya ma d'iyar Haulat kullum ne sai sunyi waya wani lokacin kuma taje Haulat har Magana tayi mata kan zaryar da take tace mata in bata yi mata ba wa zata mawa,

Watan Haisam guda anan sannan ya tafi lokacin Haulat har ta gama takaba su twins kuma watan su ukku amman in ka gansu sai kace sun yi wata biyar yaran Tubarkallah dasu sunyi girma duk inda aka gansu sai an tanka hakan yasa kullum Fatuu cikin yi masu Addu'oi take kamar yadda Hajiya da gwaggo ke yawan fad'i mata ta dage da yi masu Addu'a Saboda bakin mutane gwaggo har ruwan Addu'a da akayi da zam zam ta amso mata tana shafa masu, don ma yaran k'yuyar tsiya garesu iya wanda suke gani koda yaushe suke yarda dasu daga basu ba basu yadda da kowa Fauzy ma dakyar take samu suna yarda ta d'auke su.
Satin Haisam guda da tafiya suka fara yin School Final sosae suka dage don daga ita sai council Shikenan, suna cikin yin jarabawar ne Hajiya Zainab ta kira Aunty Mareeya a karo na farko don tun bayan da sukai exchanging number saidai ta gaishe da ita ta chat wani lokacin sai sak'on ma ya dad'e sannan take reply ta nuna mata uzuri yayi mata yawa ne, bayan sun gaisa ne tace mata dama suna son measurements na Fauzy sannan suna neman wata alfarma game da lefen Fauzyn tunda abu bana kusa bane akwae tafiya in akace a kawo kuma sannan in aka d'aura auren sai an kwaso an maido zai zama aiki don haka abunda suke tunanin ayi shine za'a kawo wanda zata yi amfani dasu in aka kaita sai su iske sauran, da sauri Aunty tace ai ba komai duk yadda sukai yayi wllh ta hau yin godiya da Addu'oi Hajiya Zainab d'in na amsawa daga baya sukai sallama, suna gama wayar ta kira can gidan su ta sanar masu Mamar su tace ita wllh hakan yayi mata dad'i ma Allah ya saka masu dai da Alkhairi,

Cikin sa'a suka gama sai kuma ta k'arshen wato council, bayan sati guda suka fara yin ta duka kwana ukku sukai suka gama, a ranar gaba d'ayansu cikin tsananin farinciki suke sun sha ankon atamfofi sun d'aura jacket mai d'auke da sunayen su a baya ta Fatuu an rubuta RN Zarah ta Fauzy kuma RN Fauzy abun gwanin k'ayatarwa nan suka shiga d'aukar hotuna mutane sai so suke suyi hoto da su twins amman sun k'i yarda, Zainab Muhammadu ce tace wllh basu isa ba ayi bikin uwar su tare da ita gari ya gari har Abuja taje amman Suk'i yarda da ita, dole da tsiya ta d'auke su suna ta kuka suna ta6e baki irin dai yadda Fatuu ke yi da k'uruciyarta in zata yi kuka suma haka suke yi don lokacin da Haisam yazo har Magana yayi akan hakan yace ita suka biyo in zasu yi kuka yadda take.

Alhamdulillah shine abunda su Fatuu keta fad'a da suka kammala karatun nasu lafiya, tare da Fauzy suka dawo gida saida suka fara tsayawa a gidan gwaggo akai ta taya su murna da Addu'ar samun sakamako mai kyau daga baya suka koma gida nan ma su Hajiya da Saude kowa dai ya taya su murna Haisam ma tun bayan da suka fito daga jarabawar ya kirata ya taya ta murna da fatan sakamako mai kyau haka ma Sameer shima ya kira Fauzy ya taya ta murna.

Kwana ukku da gama jarabawar su Sameer yazo Katsina Ranar ya kama Alhamis dama ya sanar ma Fauzyn zai zo ya tafi da ita Abuja can za'ai masu pre wedding pics, da yamma jirgin su ya tashi zuwa Abuja, duk da hawanta ne na farko ba laifi ta dake saidai itama taji juwa kamar yadda Fatuu tayi, gabda kiran Magrib suka sauka Aunty Laila ce taje d'aukko su don itama ta gama karatunta ta dawo dama komawar da tayi Final Exams zasu yi, gidansu suka wuce su Mom suka tarbeta hannu bibbiyu sosae Jidderh ta nuna farinciki da zuwanta shi dama Sameer ya wuce part d'in Haisam, d'akinta Aunty Laila ta wuce da ita tana zuwa salla ta fara yi bayan ta gama anan ta kawo mata Abinci da abun sha cikin fara'a tace mata ta taso taci d'an anjima zasu fita ne tace to, ba laifi ta saki jiki taci Abincin Jidderh na gefenta tana mata hira, ana gama sallar isha suka fito zasu tafi harda Jidderh tana jaye da wani madaidaicin trolley bayan sunyi sallama dasu Mom suka fito, a parking space suka had'e da Sameer yayi wanka ya canza kaya suka hau wata dankareriyar Jeep Sameer d'in ne ya shiga driver seat Fauzy na niyyar shiga baya Aunty Laila tace ta hau gaba su kuma suka shiga bayan yaja suka tafi. Wani sananne kuma tsadadden wurin hoto suka je wurin mai girman gaske ne gashi ya matuk'ar Had'uwa don iya ginin wurin abun kallo ne fitilu masu k'ayatarwa ne ta ko ina kai kace da rana ne, akwai manyan Studios d'in d'aukar hoto sai kuma na kwalliya haka akwae restaurant a wurin sannan akwai had'addan parlon hutawa ko jira, suna zuwa ba 6ata lokaci don ansan da zuwan su sunyi booking aka fara yi ma Fauzy Makeup abunka da kwararru ba'a d'au lokaci ba aka gama sosae Fauzy tayi kyau abun ba'a magana harda gashinta aka gyara, shima Sameer d'in saida aka gyara mashi fuska ya k'ara fitowa sosae, bayan sun gama ne suka nufi wurin canza kaya aka bud'e trolley d'in da suka zo da su wanda gaba d'aya sababbin kaya ne aciki wanda aka d'inka ma Fauzy tsadaddu kuma had'add'un gaske kala daban daban, hotuna daban daban aka shiga yi masu saida sukai kala goma kuma kowanne da kaya kala daban kama daga atamfa, lace, shadda, material, Abaya, English wears harda wanda aka yi masu da kayan aikin Sameer d'in irin kayan da injiniyoyi suke sakawa itama Fauzyn ta saka na mata ta saka irin hular da suke sakawa daga baya wurin wuyanta gashinta ya fito sosae tayi kyau kai kace ba bahaushiya ba, bayan sun gama ne aka yi masu wasu tare da su Aunty Laila. Aunty Mareeya bata yi niyyar fad'i ma iyayensu game da tafiyar Fauzyn Abuja tare dashi ba don tasan baban su bazai so hakan ba dole ya kalubalanci hakan saidai kuma tasan in aka yi hotunan dole suyi trending a social media kuma tabbas sai yan gidansu sun gani k'arshe Baban nasu zai iya gani shima, tunanin mafita ta shiga yi k'arshe ta yanke zata ce mashi kawai Katsina yazo akai masu. Washe gari ya sako Fauzyn jirgi ta dawo, a ranar da daddare saiga hotunan ya turo mata lokacin da ta gansu har saida tayi d'an ihun farinciki don sosae suka d'akku sunyi kyau har sun gaji gashi sun saka sutturu masu tsada haka d'inkunan da akai ma Fauzyn sun hau da jikinta sosae abundai saidai ace ma sha Allah, lokacin da Aunty ta gansu kasa rufe baki tayi tana ta faman yabawa tana fad'in Fauzyn kamar ba ita ba ta wanku iya wankuwa, kan kace mi hotunan har sun baza social media a daren Fatuu ma tun kafin Fauzy ta tura mata sai gashi ta kirata tana fad'in yayi kyau matar injiniya wannan zafafan hotuna haka, tambayar ta tayi a ina ta gansu tace gasu nan Aunty Laila ta d'aura a status harda su Jidderh har su Mom ma duk sun d'aura, sosae Fauzy tay mamakin yadda ake ta kiranta ana yaba hotunan tare da fatan Alkhairi abun har ta kasa rufe bakinta ma, gaba d'aya yan'matan Sameer sai yanzu suka san da zai yi aure ganin hotunan sosae mutane da dama sukai mamakin wadda zai aura sakamakon Comments d'in da aketa yi ana fad'in yar talakawa ce a Funtua local Government d'in Katsina take, haka aketa faman yin Comments mafi yawanci yabo ne ake tayi ana jinjina yadda d'an Governor ya auri d'iyar talakawa wasu na fad'in da ana yin haka a K'asar nan da an rage talauci sosae, wad'anda suka san Sameer d'in nata jinjina Al'amarin suna basu ta6a tunanin zai auri yarinya k'arama kuma yar talakawa ba, haka dai aketa maganganu gaba d'aya hotunansu sai trending suke ko ina ka shiga Maganar ake, ta 6angaren Sameer d'in yan matan shi sai kiran shi suke suna fad'in ya zai masu haka tare da jaddada mashi irin son da suke mashi wanda ya sani amman zai auri k'aramar yarinya kuma yar talakawa, to gaba d'aya dai amsa d'aya yake basu itace ita Allah ya k'addara mashi zata zama Matar shi kuma yana sonta, abokanan shi ma suna ta kira suna mashi Allah ya sanya Alkhairi.

MUJAHEED

Zaune yake a cikin parlon part d'in shi dake a cikin gidan su, dama gidan nasu Family House ne gaba d'aya shi da matar shi Rukky iyayen su anan suke dama Cousin ne shi da ita, gaba d'aya ya canza kamar ba Mujaheed d'an gayu ba yanzu sam ba wannan gayun don tun bayan daya yi aure kwanciyar hankali tayi mashi k'aranci, tashin farko matsalar daya fara fuskanta da Rukky itace bai sameta a budurwa ba bayan da suka yi auren haka dai aka yi Amarcin aka gama ba tare daya nuna mata komai ba don ita a zaton ta bai gane ba Saboda gyaran da ta sha, matsala ta biyu daya k'ara fuskanta itace k'azama ce sam bata san ta gyara muhallin da suke ciki ba ta dai iya tayi wanka tayi kwalliya amman kullum gida kaca kaca gashi sam bata iya wani girki ba, matsala ta ukku daya fuskanta a tare da ita itace sam bata bashi lokaci yadda yakamata Saboda aikin Asibiti da take dama da suka yi karatu a Malaysia ita medicine ta karanta shi kuma Business admin, a daddafe auren su yayi shekara guda don matsalolin daya ke fuskanta a tattare da ita sunyi yawa gashi har lokacin ko 6atan wata bata ta6a yi ba, Babbar Matsalar daya fuskanta a tare da ita wadda ta kusa zauta shi itace kamata da yayi red-handed tana aikata lesbian a cikin gidan shi, a lokacin yayi kuka kamar kamar me ita kanta hankalinta ya tashi sosae ta dingi bashi hak'uri tana ta tuba bazata k'ara ba amman ina dama ya gaji da auren ta hakan yasa ya tunkari iyayen su ya zayyana masu irin matsalolin da yake fuskanta a tare da ita k'arshe har lesbian daya kamata tana yi bai 6oye masu ba, suma hankalin su ya mugun tashi bama kamar Mahaifiyar shi anan tace ma Daddyn shi gaskiya a raba su amman ga mamakin su sai cewa yayi baza ayi hakan ba tunda dai abun duk na gida ne in abun ya bud'u to suma zai shafe su k'imar gidan ce zata ta6u a bari su kirata sai suyi mata fad'a insha Allahu zata bari, wani k'ululun bakin ciki ne ya tokare Mujaheed yana kuka ya shiga rok'on mahaifin nashi kan shidai a raba su kawai ya shiga girgiza mashi kai yana fad'in baza'ayi haka ba ai ba had'a su akai ba su suka fara son juna har sukai aure don haka kawai yayi hak'uri ayi mata fad'an, a lokacin Mujaheed ji yayi kamar ya mutu, bayan an kirawo ta sosae mahaifin nasu yayi mata fad'a ya nuna ta bashi mamaki yana ganinta mai hankali mai ilimi wanda a addinance da kuma a aikinta na likitanci duk tasan illolin hakan taya zata 6ata wayonta haka, sosae take kuka tana fad'in ayi hak'uri sharrin shaid'an ne amman ta bari in sha Allah zata gyara duk wasu matsalolinta da Mujaheed ya fad'a, sam Mahaifiyar shi bata so hakan ba amman ba yadda zata yi tunda Mahaifin nasu ya kafe, a haka suka ci gaba da rayuwa ba laifi a lokacin ta d'an gyara saidai sam shi hakan bai burge shi ba don ta riga ta fitar mashi a rai gaba d'aya sai lokacin ne ya gane dalilin da yasa ya sameta a ba budurwa ba ya shiga tunanin Allah kad'ai yasan tsawon lokacin da ta d'auka tana aikata hakan ashe shiyasa sam bata damu da ta bashi hakkin shi ba saboda tana bin mata yan'uwanta, yasan Rukkyn ta waye sosae amman bai ta6a tunanin zata aikata haka ba, a lokacin ne son Fauzy ya taso shi a gaba kullum cikin aikin tunanin ta yake haka cikin baccin shi yayi ta mafarkin ta saidai shi kan shi yasan samunta a lokacin abu ne mai matuk'ar wahalar gaske don yasan mahaifinta ba laifi yana da zafi hakan yasa bai ma yi tunanin zuwa gidan su ba, da yaga abun yayi mashi yawa ne ya yanke ya fara tuntu6arta in ta saurare shi sai yayi duk yadda zai yi yaga ya shawo kanta watak'il a bashi ita, Da wani yammaci ne ya shirya cikin Motar shi ya nufi gidan su Fauzy lokacin daya je a d'an nesa da gidan ya parker yana ta kallon kopar gidan yana dakon fitowar wani saida aka d'auki lokaci sannan yaga wani k'aninta da suke ce ma Abba ya dawo daga islamiyya a saman Keke yana ginin shi ya fito da sauri ya fara kiran sunan shi hakan yasa Abban tsayawa ya juyo Mujaheed d'in ya nufe shi ai koda yay arba da fuskar shi kawai sai gani yay ya tamke mashi fuska hakan yasa Mujaheed shan jinin jikin shi amman duk da hakan ya dake yana d'an murmushi yayi mashi sallama tare da ce mashi an dawo daga islamiyya ne kaman bazai amsa ba can dai cikin d'aure fuska yace mashi eh, jinjina mashi kai yayi yace yayi kyau Allah ya bada sa'a anan Abban bai amsa mashi ba sai ma ce mashi yay zai shiga gida da sauri Mujaheed ya dakatar da shi cikin yar in ina yace "a...m Fauziyya na nan?" Wani kallo mai kamar harara yayi mashi kafin yace bata nan, tambayar shi yay tana ina cikin kumbura baki yace "Oho ban sani ba nima" yana fad'in hakan ya ja keken shi ya shige, tsaye Mujaheed Yay sototo hakan da yayi mashi ba K'aramin k'aryar mashi da zuciya yay ba don bai zata yaron zai mashi hakan ba Saboda lokacin da yana tare da Fauzy suna shiri sosae da yaron don mutumina ma Mujaheed d'in ke ce mashi, da k'yar yaja k'afafun shi ya koma cikin Mota a ranshi ya shiga tunanin yaro ma yayi mashi hakan to ina ga Mahaifin kuma Fauzyn, jiki a mace ya ja Mota ya fara kokarin barin layin, yana driving yana tuna rayuwar shi da Fauzy a ranshi yana raya yasan da ita ya aura da ba K'aramin more mata zai yi ba don yarinyar na bala'en son shi kuma duk yadda yake so haka zai tafiyar da ita, haka ya dingi tuna abubuwa har ta kai yana kai ma steering Motar d'an bugu alamun takaici, tunanin yadda zai ga Fauzy ya shiga yi don tun kafin ya taho saida yayi trying layinta bai shiga, yana haka abokin shi Usman ya fad'o mashi a rai yay tunanin watak'il shi zai san inda take da sauri ya d'auki wayar shi ya kira shi bayan ya d'aga sun gaisa ne ya tambayi yana ina yace mashi gashi nan gidan shi yana shirin zuwa Masallaci yace Ok bari yazo, a tare suka tafi Masallacin bayan an gama sallar suka dawo ganin ya tsaya a bakin Motar shi Usman d'in yace mashi su shiga mana ya girgiza mashi kai, shiru yay yana kallon Mujaheed d'in don duk matsalolin da yake ciki ya sani,

"Kayi hakuri ka daina saka damuwa haka sosae a ranka Mujaheed kada ka ja ma kan ka wata matsalar kuma, ka dage da Addu'a Allah kad'ai ne zai maka maganin matsalar da kake ciki" shiru yay kafin ya jinjina mashi kai tare da kai hannu ya shafi gaban kan shi can yace "Usman bazaka gane ba amman ina cikin matsala wllh" ya k'arasa tare da cize lip d'in shi na k'asa,

"na sani abokina ai rashin dacen mata babbar matsala ce baka ji wak'ar nan da ake ta mace ta gari ba wllh duk abunda aka fad'a a cikinta hakanne da kaga mutum ba natsuwa duk ya firgice to da ka bincika zaka samu bai yi dacen mata bane, yanzu dai look at you kaman ba Mujaheed d'in dana sani ba duk ka fara fita hayyacin ka ko rannan saida nayi maka magana kan ka rage wannan k'asumbar taka wanda a da yaushe ma har wani zai maka magana kan haka" d'an murmushin takaici Mujaheed d'in yayi ba tare daya ce mashi komai ba, shiru suka d'an yi can Mujaheed d'in yace mashi don Allah suna magana da Fauzy har saida Usman ya d'an waro ido jin sunan wadda ya ambata tare da maimaita sunan Fauzy Mujaheed ya jinjina mashi kai, tambayar shi Usman d'in yayi mi zai da lambar tata yace mashi hakanan yana son suyi magana da ita ne zai bata hak'uri don yana tunanin duk abun nan dake faruwa dashi harda hakkinta, d'an murmushi Usaman yayi yasan ba iya dalilin daya sa yake son lambar ta ba kenan, k'ara tambayar shi Mujaheed yay in yana da lambar ta pls ya bashi Usman d'in yace gaskiya baida ita yana tunanin ta canza layi ne don ada suna gaisawa amman yanzu sun dad'e ma basu yi magana ba, tambayar shi yayi to yana ganinta cikin gari haka yace mashi a'a ai bata cika zama a nan ba yanzu Saboda ta koma Katsina wurin Yayarta acan take karatu, shiru Mujaheed yay yasan Yayar tata wato Aunty Mareeya amman bai san a ina take ba a Katsina, daga baya dai sukai sallama ya tafi Usman nata d'an girgiza kai ba yadda bai nuna mashi ba kar ya bar Fauzy don in yayi mata hakan bai kyauta ba amman ya k'i ji k'arshe ma abun ya zamar masu kamar fad'a gashi nan yanzu tun ba'a d'auki lokaci ba sosae ya fara nadama mara amfani. Tun daga wannan lokacin son Fauzy ke ta d'awainiya dashi gashi yayi duk yadda zai yi don ya had'u da ita ko kuma ya samu lambarta abun yaci tura, Wata rana ne kwatsam ya ganta a bakin titi duk yadda yaso ta tsaya ta saurare shi ta k'iya hakan yasa Ranar ya bi bayanta gida da daddare aikuwa yana zuwa suka had'e da Mahaifinta ya same shi yay mashi tatas yace Idan ya k'ara ganin shi a k'opar gidan shi to hukuma ce zata raba su nan Mujaheed d'in yayi ta bashi hak'uri yana fad'in yasan yayi kuskure bai kyauta ba amman don girman Allah ya bashi dama a yanzu zai gyara kuskuren shi ne, a lokacin wani murmushin yaro yaro ne mahaifin nasu yay kafin ya d'aga yatsa sama yace mashi "Na rantse da Allah daya hallicce ne ko bayan ba raina bazaka auri Fauziyya ba, yarinyar da kaso kashe man ita kawai don Allah yasa da sauran numfashinta a gaba shine yanzu don baka da kunya ka iya tako k'afafun ka kazo man gida, to bari kaji, ka bar kopar gidan nan tunda arzuki in ba haka ba....ka jira in shiga in fito zaka ga abun da zan sa ayi maka" cike da 6acin rai ya k'arasa maganar tare da juyawa ya shige cikin gidan, jiki a sa6ule Mujaheed ya juya ya nufi Motarshi yana k'walla ya bud'e ya tafi, duk wannan abun Fauzy bata san da an yi ba, tun daga ranar Mujaheed ya hak'ura da neman Fauzy amman fa kullum son ta da nadamar abunda yayi mata k'aruwa yake a cikin ran shi, (Allah ka kiyashe mu aikin dana sani mara amfani Amin).

Yana zaunen idon shi akan Tv wayar shi dake a gefen shi ta shiga yin ruri, kai idon shi yay kanta yaga Usman ne mai kiran nashi ya kai hannu ya d'aukko ta tare da yin picking, bayan sun gaisa ne yace mashi yaga hotunan dake ta trending a social media Mujaheed d'in yace mashi a'a tun d'azun rabon shi da online Usman yace mashi Ok ya hau Facebook yanzu tambayar shi yay lafiya yace ya dai hau zai gani yace Ok, bayan ya katse Wayar kunna Data d'in shi yayi a ranshi yana ta raya to miye zai gani, yana hawa hotunan su Fauzy ya ci karo dasu farko bai ganeta ba koda ya karanta rubutun dake sama wanda aka sa d'an Governor d'in Nasarawa Sameer Bello Abdullahi zai yi Wuff da yar talakawa daga jahar Katsina a garin Funtua mai suna Fauziyya Ahmad Rufa'i, shiga yay cikin uban comments d'in mutane ya fara bi yana karantawa duk da hakan bai gane ita bace yana cikin karantawar Usman ya sake kiran shi bayan ya d'aga yace mashi yaga wadda zata auri d'an Governor d'in yace mashi eh ya gani ance yar nan Funtua ce wannan maganar yasa Usman ya gane bai ganeta ba yace "wai baka gane Amaryar bane?" Amsa ya bashi da eh da alamun mamaki Usman yace "lallai Mujaheed baka a cikin hayyacin ka wllh, yanzu Fauziyya d'in ce baka gane ba?" jin sunan Fauziyya yasa shi maimaita sunan sai lokacin hankalin shi ya koma kan sunan Amaryar da ya gani an rubuta nan take ya gane Fauzy ce, wani irin bugu gaban shi yayi da sauri ya mik'e tsaye.........

96

_ASM BY ZAINAB BATURE_

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

............Da tsananin Al'ajabi Mujaheed yace "U.....sman wai kana nufin Fauziyyata ce wannan Amaryar?" Amsa ya bashi da eh mana bai duba hoton bane sosae, kan Mujaheed ne ya d'aure fuska a hautsine ya shiga fad'in amman taya hakan zata faru taya za'a ce zata auri d'an Governor, Usman na murmushi yace abun Allah ai ba abun mamaki bane don wannan kad'an daga cikin ikon sane,

"ka gane Usman abunda nike nufi irin wannan Mutanen had'uwa da su ba abu ne mai sauk'i ba balle kuma har ta kaiga ace zasu yi aure kuma nasan labarin mahaifin yaron ba K'aramin mai kud'i bane yana daga cikin Governors masu kud'in gaske fa taya za'a ce hakan zai faru kodai ba ita bace suna ne yazo d'aya!" hankali tashe yake Maganar,

"Wannan duk ba wani abu bane Mujaheed da Allah ya so Shikenan zaka ga ya kasance cikin sauki tunda gaba d'ayan mu duk bayin sane shi yake iko da mu" yarfa hannu Mujaheed yay kaman zai saka kuka yace amman wai taya suka had'u ma, Usman yay yar dariya yace "ta yadda Allah ya had'a ku haka shima ya had'a su, ance ta dalilin karatun da take a Katsina suka had'u ni kaina nayi mamaki sosae lokacin da naga hotunan don ina gani na gane itace amman don in tabbatar sai na kira wani abokina d'an layin su shine ya tabbatar man yace suma duk basu san da abun ba kawai dai suna ganin ana yin manyan bak'i a gidan sannan kuma yanzu haka ma an canza ma gidan nasu suffa ya zama had'addan ginin benen gaske gaba d'aya dai komai cikin k'ank'anin lokaci ya faru har ma hoton gidan nasu ya turo man bari ka gan shi" yana fad'in hakan ya katse kiran don ya tura mashi hoton, komawa Mujaheed d'in yay cikin Facebook ya shiga sake kallon hotunan gaban shi na mashi wani irin bugu, sai yanzu ya tabbatar da ita d'in ce yana haka Usman ya turo mashi hoton gidan su Fauzy, Safa da Marwa ya shiga yi wayar shi ruk'e a hannunshi da k'yar yake fitar da numfashin shi da yaji yana neman k'wace mashi k'arshe ma sai yay wurgi da wayar tashi ya durk'ushe k'asa saman gwiwowin shi wasu irin k'walla masu zafi suka shiga zubo mashi..........

Washe gari Friday ya kama saura sati biyu cuf d'aurin auren Fauzy da Sameer, a ranar ne aka tura wasu daga cikin akwatunan lefen Fauzy set biyu guda goma cuf wai nan kayan da zata ci biki ne sauran sai an kaita kamar dai yadda Hajiya Zainab ta fad'a ma Aunty Mareeya harda invitation cards masu kyaun gaske aka had'o, akwatuna ne ubansu su kan su abun kallo ne kai da gani ba sai an fad'a maka ba kasan zasu yi kud'i saima da aka bud'e kayan ciki Naira ta sha kashin gaske don kaya ne na gani na fad'a kuma duk a d'inke suke a ciki harda wanda Fauzy ta saka suka yi hotuna, kowa ya gani cikin yan uwansu cewa yake yo iya wannan ma ai lefe ne na gaske, lokacin da aka tura ma su Aunty Mareeya kayan zo kaga murna ita kanta fad'i take yanzun duk wannan uban kayan har sai an k'ara wasu, itama Fauzy har ta kasa rufe bakinta don farinciki koda ta tura ma Fatuu ita kanta ta yaba sosae anan take tambayarta sai yaushe zata tafi Funtua d'in ne tace mata sai zuwa jibi Lahadi akwae shirye shiryen da Aunty take son k'arasawa, itama Fauzy ta tambayi Fatun sai yaushe zata je can tace mata sai satin bikin ana saura kwana biyu aikuwa Fauzy tace ita dai bata yarda ba gaskiya inama laifin ana saura sati d'aya ta taho, dariya Fatuu ta saka tace wannan sai kace ita ce dai Amaryar inama laifin ana saura kwana biyun Fauzy ta kafe kan ita dai yayi kad'an Fatun tace mata gaskiya daga haka bazata k'ara ba don Lokacin Hubby dinta ya dawo taya zata taho ta barshi, dariya Fauzy ta saka tace ai sai ta fito tayi mata bayani ba taita yan kame kame ba duk suka yi Dariya. Ranar Lahadi tunda safe su Aunty suka d'auki hanyar Funtua a cikin Motar Fauzy driver d'in da ya koya mata Motar ne zai kai su. Alhamdulillah sun isa lafiya anata murnar ganin su ba kamar Fauzy Amarya sai faman nan nan da ita ake, sosae sukai mamakin yadda aka canza ma gidansu fasali duk da sun gani a waya amman yanzu da suka ganshi a zahiri sai suka fi ganin kyaun shi ya zama gidan yan gayu sosae wanda kaf layin su da duk ma rukunin su ba gida tamkar shi kai a yanzu ma yana d'aya daga cikin jerin gidaje masu kyau in za'a lissafa a garin, shirye shiryen hidima sun kan kama sosae bayan zuwan nasu duk da ba wani abu da Fauzyn zata yi anan Funtua Sameer har magana yayi mata kan ko zasu yi wani event tace mashi a'a abar wanda su zasu yi kawai wato Dinner bayan an kaita sai kuma Walima wadda za'a yi matsayin bud'ar kai. Ranar Laraba Haisam ya iso yana dawowa washe gari suka tafi Abuja da Fatuu harda Hajiya acan ma dai duk shirye shiryen bikin aketa yi, Ana saura kwana biyu bikin ya kama ranar laraba kamar yadda Fatuu tace Haisam yasa driver ya tafi da ita harda Jidderh, Bayan sun isa Fauzy tayi murna da ganin su sosae haka Aunty Mareeya da sauran yan gidan sai faman nan nan ake da su anata nuna Fatuu ana cewa itace k'awar Fauzy wadda zata auri d'an uwan mijinta nan fa akai ta yi ma Fatuu godiya hatta Mahaifinsu da kanshi yazo inda suke yay masu sannu da zuwa shima saida yayi mata godiya da Addu'ar Allah ya bar zumunci haka yayye da k'annen Fauzy duk saida suka zo suka gaishe da ita hadda Yaya Mubarak ma fuska a sake Fatuu ke amsa masu ana ta son a d'auki twins amman sun ki yarda sai faman fad'in Tubarkallah ake dama lokacin sun k'ara girma sosae, Yaya Fareeda harda cewa Allah yasa Fauzy itama ta haifi irin su anata dariya aka amsa da Amin. Hidima ta kan kama tun a ranar Jami'an tsaro keta faman sunturi a cikin garin ana ankarar da mutane hatta gidan su Fauzy an zuba security, Washe gari Alhamis su gwaggo suka iso tare da Kawu Amadu da Mino harda Haulat da Saude bayan zuwan su kuma su Zainab Muhammadu da wasu daga cikin k'awayen su ma suka zo haka makwabtan Aunty Mareeya ma su Maman taufiq suma sunzo gida dai ya cika sai zuwa ake.

FRIDAY....

Alhamdulillah Allah ya kawo mu ranar d'aurin aure, a ranar tunda farar safiya jiniya ta fara tashi ta ko ina wurin k'arfe sha d'aya na safe Abbas ya iso tare da Feenah, tuni Amarya Fauzy tasha had'addan k'unshi an kuma gyara mata kai haka jikinta ma yasha gyara don tun a Katsina ake ta mata gyaran jiki skin d'inta tayi wani irin sumul sai shek'i take, zuwa k'arfe sha biyu da rabi na rana garin Funtua ya cika makil da jama'a ba abunda kake ji sai jiniya ga kuma jibga jibgan motoci masu numfashi dake ta kai kawo a saman tituna da tuni an rufe su an hana mutanen garin bin su saidai suyi zagaye, kamar yadda Ango Sameer yaci alwashin bazai k'ara zuwa a Mota ba hakan ce ta faru don kuwa a helicopter suka zo harda Haisam bama su kad'ai ba wasu daga cikin manyan mutane ma a helicopter d'in suka zo daga filin da suka sauka ne Motoci na Alfarma suka daukko su, Jama'a kuzo kuga ango Sameer yasha kyau har ya gaji yana sanye da rantsattsiyar shadda light ash d'inkin yar ciki da babbar riga ba K'aramin kyau ya k'ara ba a cikin kayan ko don bai saba sakawa ba ne, su Haisam angwaye suma babbar rigar shadda duk suka saka gaba d'ayansu Abokan ango iri daya sukai suma tasu ash ce amman tafi ta Angon cizawa ba K'aramin tsaruwa sukai ba dama duk gasu yan Madara harda Abokan shi turawa da suka zo suma duk shigar suka yi abun dai sai wanda ya gani, shima Mahaifin Sameer d'in His Excellency da muk'arraban shi duk sun iso gaba d'aya jiniya ta karad'e ko ina a lokacin harabar Masallacin Juma'an da za'a d'aura auren ta cika makil da Jama'a kama daga manyan yan siyasa masu Mulki da masu Sarauta, manyan yan kasuwa da sanannun masu kudi, Manyan Mutane wanda sune Nigeria aka had'a a wurin wasu sun zo da kan su wasu sun turo wakilci taro dai yay taro malam Yan Jarida ko ta ina suna d'aukar rahoto nima dai ina daga cikin su inata rubuto maku rahoton cike da taka tsantsan gudun kada in sha na jaki a wurin jami'ai dake ta kai kawo a wurin don na lura a fusace suke duk suna ruk'e da manyan makamai gaba d'aya sun yi shirin ko ta kwana. Daga cikin wad'anda suka zo bikon Amarya harda su Mom da Aunty Laila Aunty Mareeya ta shiga gabatar dasu wurin yan uwansu tana ce masu yadda suka ga Mom haka Mahaifiyar Angon take don yan biyu ne, sosae Mom ta sakar masu fuska anata faman kawo mata gaisuwa tare da yi mata godiya da murmushi take fad'in ba komai duk an zama daya. Ana gama sallar Juma'a dubban mutane suka shaida d'aurin auren Sameer da Fauzy wanda Aminin Governor wato Senator Ali Adamu Zakee ne ya kar6a mashi akan sadaki Naira dubu d'ari biyar kamar yadda iyayen Fauzy suka buk'ata Jama'a sai fatan Alkhairi suke ma Governor mahaifin Sameer da Mahaifin Fauzy da kuma shi kanshi Angon da ba laifi ya saki fuska yana d'an murmushi haka Haisam ma sai murmushi yake shima ana mashi Allah ya sanya Alkhairi, ana gama d'aurin auren aka nufi inda aka tanada don yin reception wasu dai da yawa tafiya sukai, manyan motoci ne masu d'auke da Abinci iri iri aka bud'e a bakin Masallacin nan aka shiga rabama mutane a nutse don da mutum yay wasa yaji saukar dorina a gadon bayan shi, har gidan su Fauzyn ma Motar Abinci taje an sauke masu abun dai sai godiyar Allah, cikin wanda suka halarci sallar Juma'a aka kuma d'aura aure dasu bayan an tantance su Saboda tsaro harda Mujaheed da tun bayan daya san da Maganar auren baida cikakkar lafiya, daga nesa ya tsaya shida Usman suna hango Sameer lokacin da ake d'aura auren bayan an gama Usman yace mashi su tafi fuska kamar zai yi kuka yace mashi don Allah ya za'ai ya ga Fauziyya, waro ido Usman yay ya maimaita abunda yace Mujaheed din yace eh yana son ganinta kafin ta bar garin, ce mashi Usman yay gaskiya ganinta a yanzu abu ne mai wahala gara kawai su tafi amman ya kafe kan ya taimaka mashi yana son ya ganta ido da ido ko ya nemi yafiyar ta watak'il ya samu sauk'in abunda yake ji, nuna mashi yay Fauzy bata da matsala yasan tuni ma ta yafe mashi don haka ya hak'ura da ganinta karma suje suja ma kan su matsala, kafewa Mujaheed yay harda k'wallar shi ba yadda Usman ya iya gashi ya bashi tausayi sosae hakan yasa yace mashi suje gidan nasu amman shi yasan ganin Fauziyya a yanzu ba abu bane mai sauk'i suka nufi Motar Mujaheed bayan sun shiga yaja suka nufi gidan su Fauzy.

Ana gama d'aura Aure ba 6ata lokaci aka shiga shirin tafiya da Amarya don tafiyar Mota za'ai zuwa Abuja anan za'ai Dinner in an je daga baya sai a wuce da ita Nasarawa amman an sanar ma Aunty Mareeya cewa ba mutane da yawa za'a dasu Nasarawa ba iya mutum goma suke buk'ata zuwa dai Abuja wannan ko mutum nawa suka bada lafiya lou, tun bayan da su Mujaheed suka iso kopar gidan wuri suka samu daga can gefe don kopar gidan dank'am yake da mutane ga marok'a dake ta aikin kirari da masu kad'e kad'e, rasa ta yadda zasu ga Fauzyn sukai Usman yace mashi dama saida ya fad'i mashi bafa zai iya samun ganinta ba gara su tafi daga baya shi zai mashi k'ok'arin samun lambarta sai ya kirata ya rok'eta yafiyar, Shiru Mujaheed yayi shi kad'ai yasan abunda yake ji a cikin ranshi ga tsananin mamaki da yake ganin wai duk wannan taron Fauzy akai ma shi a ranshi ya shiga raya Allah kenan sosae nadama ke dawainiya dashi. Dank'ara Dank'aran Motoci ne suka shararo cikin layin zasu kai goma sai kuma motocin Security dake a gaba da baya tare da ta yan jarida abun burgewa gaba d'aya motocin bak'ak'e ne sai k'yalli suke, cirko cirko mutane sukai suna kallon yadda ake shirya motocin, bayan an gama ne aka sanar cikin gidan cewa a fito da Amarya, rantsattsan leshi Fauzy ta saka wuyanta da hannunta na sanye da gold an d'aura mata alkyabba sai walwali take, su Aunty Mareeya iyayen hidima itama kaya ta canza daga ankon atamfar da suka yi zuwa had'add'an kuma tsadaddan lace da aka mata half gown ta coge d'aurin kallabi ya kalli gabas maso kudu harda uban glass ta k'wama, haka sauran yan gidan su ma duk sun canza shiga zuwa lace su Fatuu ma duk lace d'in ne a jikin su, ba tare da 6ata lokaci ba yan kai Amaryar suka fara fita, Akan idon Mujaheed Aunty Mareeya ta fito da ita ta rungumo kafad'arta yana ganinta ya zabura zai nufeta aikuwa da sauri Usman ya maido shi yana ce mashi bai ga Jami'ai bane a wurin, wata jibgegiyar bak'ar Jeep dake ta salk'i aka bud'e ma Aunty anan za'a saka amaryar ta kalli Fatuu dake biye da ita tace mata itama ta shigo ta zagaya ta d'aya 6angaren aka bud'e mata ta shiga itama Fauzyn aka shigar da ita tana ta yar sheshsheka da tun bayan da akayi mata fad'a take kukan, Bayan Aunty ta saka Fauzyn fitowa tayi ta rufe k'opar ta shiga nuna wanda za'ai tafiyar dasu ana bud'e masu motocin suna shiga, su gwaggo dai Motar Abbas suka shiga ita da Feenah da Saude sai Kawu Amadu Haulat kuma da Mino Mota d'aya suka shiga da Jidderh haka su Zainab k'awayen Fauzy suma Mota guda akai masu su Mom dai dama da Jeep d'insu suka zo ita suka shiga su Twins d'in Fatuu na hannunta ita da Aunty laila, saida Aunty Mareeya ta tabbatar da an shigar da kowa Mota cikin masu tafiya sannan ta dawo tasu ta bud'e ta shige ba wanda ya shiga gaban tasu don bayan driver da zai ja Motar akwae Security zaune a seat d'in gefe, wai akace ga k'oshi ga kwanan yunwa tun bayan da aka shigar da Fauzy Mota Mujaheed keta kallon Motar gaba d'aya takaici ya cika shi ji yake tamkar ya fasa ihu, da shi a haukanshi da Usman bai hana shi ba zuwa zai yi wurinta yanzu kuwa saidai sukai tsaye suka bi sahun yan kallo, sai bayan da Aunty ta koma cikin Motar ne ta natsu tana k'are mata kallo tana yi tana jinjina kai a ranta tana raya ta dai had'u ba k'arya kuma da gani sabuwa ce don seats d'in harda ledar sabuntar su ga kujerun lumtsuma lumtsuma gwanin taushi a gaban seat d'in da suke akwae screen manne da kowacce kujera da mutum zai iya yin kallo ko yayi game har internet ma zaka iya shiga ko kai connecting Bluetooth da wayar ka da dai sauran su, tsakanin su da Mutanen dake zaune a gaba akwae d'an labule na leather kalar seat d'in Motar hakan yasa basu ganin su sannan gaba d'aya glass d'in Motar tinted ne ta yadda ba'a iya hango wanda ke ciki sai dai kai kaga na waje, sosae Motar dai ta jugunu sanyin Ac nata ratsa sassan jikin su, Bayan kowa ya shiga Umarnin tafiya ake jira daga wurin Jami'an dake clearing Main titi da zasu hau su tafi, hannu Aunty Mareeya ta d'aura jikin Fauzy tace "Amarsu har yanzu kukan ake" shiru Fauzyn bata ce komai ba kuma bata d'ago ba daga sadda kan da tayi hular Alkyabbarta ta rufe mata fuska Fatuu dake latsa wayarta ta d'ago ta d'aura idonta akanta tana d'an murmushi can ta kira Sunanta k'asa k'asa ta amsa tace mata tayi hak'uri ta daina kuka don Allah,

"Uhm kukan gulma ne ba wani abu ba, nan data shige daga ciki sai munci sa'a zata tuna damu" yar dariya Fatuu tay Aunty Mareeyar tace Allah kuwa Zarah, hannu Fatuu takai ta janye hular Alkyabbar ta d'an d'ago da Fuskar Fauzyn suka had'a ido idanunta sunyi jajur ta kai hannu tana goge mata k'wallan tana fad'in ya isa hakanan kada tayi ciwon kai tana Amarya Aunty tace ta fad'i mata dai, saida tasata ta daina yin Kuka ta d'ago Fuskarta sosae, a hankali ta fara bin Mutanen dake tsaye cirko cirko suna kallon Motocin nasu da kallo, tana haka idanunta suka sauka akan Mujaheed daya tsura ma saitin inda suke ido, har zata janye idanun nata sai kuma ta tsaya kamar an dakatar da ita ta k'ura mashi ido farko bata gane shi ba kawai dai sai take jin kamar tasan mutumin dake a tsaye saida ta d'an d'auki lokaci tana kallon shi ne ta fara ganin kamar shi, a ranta ta raya anya kuwa shine taya zai zo nan k'arshe ta yanke bashi bane k'ilan dai mai kama dashi ne tana janye idanunta ta d'aura su akan Usman dake gefen shi, tana ganin shi ta ganeshi a ranta ta raya Usman tana fad'in hakan da sauri ta maido idonta kan Mujaheed lokaci guda ta shaida shine da tsananin mamaki ta furta "M...UJAHEED!" har Kusan rigen kallonta su Aunty sukai da sauri tace "ina Mujaheed d'in" hannu Fauzy ta d'aga tana nuna saitinshi ta cikin glass gaba d'ayansu harda Fatuu suka zuba mashi ido shima kuma har lokacin saitin su yake kallo saidai baisan suma kallon nashi suke ba,

"To uban me ya kawo shi nan kuma, koda yake nama ji dad'i daya zo ya gane ma idon shi komai" Aunty ta fad'a ta d'aure fuska tare da yamutsa baki can kuma sai cewa tayi bari ma a bud'e glass d'in don ya shaida da kyau itace Amaryar, duk yadda taso ta sauke glass d'in ta kasa har ta kai tace ma Fatuu wai ta bud'e tunda dai ita tafi ta sanin takan kayan masu arzuki Maganar har saida taba Fatuu yar dariya itama ta fara k'ok'arin sauke glass d'in amman ta kasa can Aunty tace bari ta tambaya tunda ai dai sun san Amaryar yar talakawa ce bazai zama sun yi k'auyanci ba, dariya Fatuu tasaka Aunty Mareeyar ta kai hannu ta d'an janye labulan dake tsakanin su da Driver ta d'an lek'a a Kusan tare su duka na gaban suka juyo suka kalleta yadda ta sak'a kan kamar mage, da d'an murmushi tace masu sannun su suka amsa kafin tace don Allah glass d'in baya za'a sauke masu su dai sun duba basu ga inda ake saukewa ba, suma murmushin ne akan fuskar su Security d'in dake gefen driver duk da shima driver d'in kamar security d'in ne daga yanayin shigar shi yace mata kodai basu iya bud'e glass d'in bane, da sauri tace "a'a wllh Yallabai mun iya indai yadda ake sauke glass d'in kowacce Mota ne tunda dai muma muna da yan motocin nan, kuma koda ma ace ni ban iya bane ai d'ayar da muke tare ita dole ace ta iya tunda matar Cousin d'in Angon ce d'an Senator Ali Zakee nasan baku rasa sanin shi" kai ya jinjina mata tace to har itama tayi tayi ta kasa sauke shi balle ace sun yi k'auyanci, yanayin yadda take Maganar ne ya basu dariya don sun fahimci yar barkwanci ce, driver d'inne yace mata basu yi k'auyanci ba ta nan gaba ake sauke glass d'in da sauri tace Yauwa koda taji to a sauke masu don Allah Security d'in yay mata alamun ta koma ciki ta janye kan nata ya sak'o nashi inda suke ya mik'a yatsa yana nuna mata wani wuri a jikin k'opar Motar da ita kanta abun kallo ce yace mata in tana son yin magana da su nan zata latsa sai kawai ta fad'i abunda take son ayi ba sai ta lek'a ba ta jinjina mashi kai kafin tace kenan kamar yanzu da take son a sauke glass tana latsa wurin sai tace ayi haka yace mata Yess zata ga glass d'in ya sauka ta washe baki tana fad'in Allahu Akbar shima yar dariyar yay sai kuma ya nuna mata screen yace ga system nan in suna so sai suyi kallo ya shiga nuna mata yadda zata kunna yace akwae Movies a ciki saidai ba masu yawa bane amman in tana so zata iya connecting da wayarta sai ta kalli duk abunda take so har internet zata iya hawa tayi chat d'inta anan yana bayanin yana nuna mata yadda zata yi k'arshe kuma ya nuna mata game yace ga kuma game nan in tana son yi tayi mashi wani kallo tace sai kace dai wata k'aramar yarinya yay yar dariya, duk abun nan idon Fauzy na akan Mujaheed Fatuu dai kallon abunda ake nuna ma Aunty take tana yar dariya, bayan ya gama nuna mata ya maida kan shi kawai sai jin Maganar shi sukai ta karad'e bayan ta cikin wata yar speaker yana tambayar glass d'in wane side za'a bud'e masu ta bashi amsa da na hagu tana rufe baki glass d'in ya fara sauka, bin Mujaheed da kallo Fauzy tay gabanta ya hau d'an fad'uwa ganin yadda yay wani iri kamar ba shi ba Aunty kuwa yamutsa mashi fuska ta shiga yi tana hararar shi Fatuu ma bin shi tayi da kallo a ranta ta d'an ji mamakin ganin shi haka don ba haka Fauzy ta bayyana mata shi ba tace mata d'an gayu ne yanzu kuwa duk gashi ya cika mashi fuska gashi ya zumbula wata jallabiya sai kace liman, ganin irin Kallon da Fauzyn ke mashi ne ya bashi k'warin gwuiwa ya tunkaro Motar da sauri, saida ya kusa isowa kawai Aunty ta danna wurin da aka nuna mata da sauri tace a rufe glass d'in sai gashi ya fara rufewa slowly, burki Mujaheed yaci ya zuba ma Fauzy ido yayin da glass d'in ke rufewa, kallon Aunty Fatuu tayi da sauri tace "Aunty wannan ne Mujaheed d'in?" Fuska a Yamutse ta kwa6e baki ta bata amsa da eh shine banzan ko uban me ma yazo yi nan sai kuma tace koda yake gara da yazo ya gane ma idanun shi, yanayin fuskar Fauzy kaman zata yi kuka dama kuma shi ta gama yi ta kalli Aunty tace "Aunty da baki mashi haka ba zai zama kaman kin wulak'anta shi...." Tun kafin ta rufe baki ta katseta a fusace "au wai ke nan baki ji dad'in abunda nayi ba kike nufi komai, naji dad'i in har hakan da nayi mashi zai zama wulak'anci a gare shi da akwae wulak'ancin ma da yafi wannan to shi zan mashi, ke har kin manta da irin wulakancin da yayi maki zaki wani ce an mashi wulakanci",

11abu Fauzy ta had'iya k'walla suka zubo mata cikin karyayyar murya tace "abun da yay man d'in k'aruwa nayi ko raguwa Aunty, ni wllh na yafe mashi komai yayi man tun ma ba yanzu ba" ta6e baki Aunty tayi bata ce komai ba Fauzyn ta juya tana k'ara kallon shi yana a tsaya inda ya ja ya tsaya yana kallon Motar ya marairaice Fuska tare da had'e hannuwan shi ya d'an d'aga su sama alamar rok'o, kallon Aunty Fauzy tay tace "Aunty don Allah kisa a bud'e da alama akwae abunda yake so ya fad'a man ki bari muji miye don Allah baki ga yadda ya koma ba duk yayi wani iri kamar ba shi ba" wani uban tsoki taja rai 6ace tace "Wllh baza'a bud'e ba har yana da wani abun fad'i maki, to yace maki uban me kuma Maganar canzawa ya dad'e bai lalace ba wllh ko a kwalar vest d'ita, yanzu haka hakkin ki ne ke bibiyar shi tun ba'aje ko ina ba don haka ba abunda zance in ma hakan ne sai Allah ya k'ara in ma da k'ari ya k'ara mashi, Sakaran banza sakaran wofi" tana rufe baki Fauzy ta fashe da kuka, waro ida Aunty tay da tsananin mamaki tace "ke, mi nike gani haka, wai wanccan d'in kike ma kuka Saboda Maganganun da nayi to mi kike nufi da hakan??" Girgiza kai Fauzy tayi cikin kuka tace ita wllh ba abunda take nufi kawai dai ya bata tausayi ne don da gani yana cikin matsala mutumin da yake d'an gayu d'an Kwalisa a gan shi haka" ta6e baki Aunty tay tace ita dai ta sani, magiya Fauzy ta k'ara mata kan tasa a bud'e aikuwa a fusace Aunty tace "Wallahi tallahi baza'a bud'e ba, in kuma kikai wasa yanzun nan zan buk'aci a kirawo man Mijin naki ince ke kike son ganin shi da gaggawa yana zuwa in fad'i mashi abunda ke faruwa, kindai sani ai basai na fad'i maki ba tsaff zai kakkarya shi sai muga ta tsiyar tausayi, in ba ma yana mahaukaci ba shine zai wani jawo k'afafu kamar shebur wai zai yi magana dake wato shi ga mara ta ido ko duk abunda yay maki shine har zai wani nemi yin magana dake to kuwa yanzun nan zan sa a koya mashi kunyar da bai da ita" ta k'arasa tare da yin k'wafa, wani irin kuka mai sauti Fauzy ta saka dama k'iris take jira acikin ranta ta shiga tunano tun daga farkon had'uwarta da Mujaheed d'in yadda ya rink'a mata d'awainiya da tana Makaranta, sam lokacin ba ta tuno da sharrin shi ba sai Alkhairan shi, suna haka suka ji Muryar Security d'in ta cikin speaker d'in bayan yana tambayar lafiya wake kuka ne haka mike faruwa, zaro ido Aunty Mareeya tayi da sauri ta kai hannu ta jawo Fauzy jikinta tana k'ok'arin rufe mata baki tana fad'in ta bani kuji zata ja mata sharri taja a d'aureta, duk da yanayin da Fatuu take ciki na karyewar zuciya saida tayi yar dariya, k'ara tambayar su lafiya akai koda matsala ne da sauri Aunty ta latsa wurin Maganar ta bashi amsa da a'a ba komai amaryar ce ke kukan rabuwa da gida, wannan karon sosae ta ba Fatuu dariya, rarrashin Fauzy ta shiga yi tana fad'in Shikenan tayi hak'uri itafa duk Maganganun data yi 6acin rai ne yasa tayi su kuma bata ga amfanin tayi magana da shi ba tunda ita yanzu Matar aure ce ta rabu dashi kawai, cikin muryar kuka tace ba cewa tayi zata saka a kirawo mata Sameer ba ya kakkarya shi da sauri Aunty tace wllh duk cika baki ne ita tama fara kiran shi ta fad'i mashi haka yazo duk ya tarwatsa taron da rocket, dariya Kawai Fatuu ke yi a ranta ta raya yau Aunty ta tuno da rocket, suna haka aka ba motocin izinin tafiya a Kusan tare duk suka tashi jin haka yasa Fauzy d'agowa da sauri tana kallon Mujaheed d'in Motocin suka fara tafiya a jere gaba Motar Security ce haka k'arshe ma sannan a tsakiya ma abun dai gwanin burgewa nima dai ina a cikin ta yan jarida, tun bayan da Motocin suka fara tafiya Mujaheed yaji tamkar da jinin jikin shi suke tafiya a Hankali ya fara ganin jiri ya kai hannu ya dafe goshin shi ganin haka yasa Usman nufo shi da sauri ai ko kafin ya k'araso Mujaheed d'in ya tafi gaba d'aya zai kife cikin zafin nama ya tare shi duk wannan abun akan idon Fauzy dake ta kallon su ta glass da yake Motocin a slow suke tafiya, tana ganin haka ta juyo cikin kuka take ce ma Aunty ga Mujaheed d'in can ya fad'i kawai sai ta jawota jikin ta tana fad'in zai tashi ne in kuma ya wuce daga haka Allah ya jik'an shi.

Tafiya ce ake me cike da kwanciyar hankali daga baya Fauzyn ta sake bayan Fatuu ta rarrasheta Aunty ta kunna masu kallo suna ta yi abun su, lokacin da suka zo Zaria ne Aunty tace ita dai wllh k'ishi take ji yakamata ace ko wace Mota an aje lemuna da ruwa Fatuu tace ko ta tambaye su k'ilan ba'a rasawa tace to, latsa wurin tayi tace pls suna buk'atar ruwa kawai sai ji tayi an bata amsa da ta duba akwae a cikin Fridge, zaro ido Aunty tay ta d'an kakkali cikin Motar ita dai bata ga wani Fridge ba, tambayar su tayi anan bayan fridge d'in yake yace mata eh mana,

"to gaskiya saidai kuyi hak'uri kun d'aukko yar k'auye nidai wllh ban ganshi ba" ta fad'a tana k'ara kallon wurin, suna jiyo d'an sautin dariyar shi kafin yace Ok bari a bud'e masu daga can yana rufe baki kawai sai gani sukai daga d'an kasan dukkan seats d'in gaban ya bud'e har saida Aunty ta d'an firgita hakan saida yaba Fauzy dariya, d'an karamin fridge ne a jikin dukkan seats d'in kowanne akwae lemuna da ruwa harda snacks a ciki, tambayar Aunty akai yanzu ta gani ko tana dariya tace masu eh sai sunyi hak'uri abun ne ya had'u da yar k'auye suna jiyo dariyar shi, gaba d'ayan su lemu da snack suka d'auka suna sha harda Fauzy Aunty nata washe baki tana fad'in ikon Allah ashe da rabon zata shiga Mota fridge da aketa fad'i, suna cikin ci ne tace to wai yanzu kuma in suka zo suna buk'atar toilet fa tunda sun ci abu, kafin wani ya bata amsa ta sake cewa koda yake k'ilan ma ai baza'a rasa toilet d'in ba acikin Motar, dariya taba Fatuu tace "kai Aunty Mareeya sai kace dai wani jirgi" da sauri tace "ai wannan kaman jirgin ce mai tafiya kan titi kiga fa yadda take da abubuwa kar ki mamakin toilet d'in ma akwai nan da mun tambaya kina iya ganin sun ce akwae" Fatuu dai dariya kawai take cikin disasshiyar murya Fauzy tace don Allah sudai kada ta wani tambayi ko akwai toilet tayi mata wani kallo tace "to your Excellency kada inta bada ku ko " tura mata baki Fauzy tayi ba tare data ce komai ba ta kai hannu ta dafa Shoulder d'inta tace "sai faman wani sha man k'amshi kike ko duk don Mujaheed ne?" Kai ta d'an girgiza mata kawai ba tare data ce komai ba, sai dai tun bayan da suka taho ya tsaya mata a rai sai tunanin halin da yake ciki take da kuma abun da ke damunshi ya hautsine haka.

Alhamdulillah sun iso Kaduna Lafiya, government House d'in nan aka nufa dasu dama an shirya nan za'a tsaya a huta kafin a wuce, bayan sun huta an ci Abinci masu salla sun yi suka d'aura tafiyar. Sai bayan sallar Magrib suka iso garin Abuja, tun a gate d'in gidan da aka nufa dasu suka fara shan kallo Fauzy na ganin cikin gidan ta glass ta gane gidan da Sameer ya ta6a kawo ta ne, gaba d'aya Motocin saida aka shiga dasu cikin gidan, bayan duk an parker aka fara fitowa nan fa kowa ya shiga ba idon shi hakkin shi banda wanda suka san gidan da kuma wanda gidan ba abun kallo bane a wurin su, kowa dai cikin yan kawo Amaryar bai hana idon shi hakkin shi ba ta hanyar bin ko ina na gidan da kallo tare da jinjina ma had'uwar shi a cikin zuciya, Aunty na ruk'e da Fauzy suka nufi hanyar shiga cikin gidan kamar yadda aka basu izini suna cikin tafiyar ne k'asa k'asa da murya Aunty tace ma Fauzy nan ne gidan da Sameer ya ta6a kawo ta ko ta d'aga mata kai tace dama tana gani tayi tunanin hakan don taga yayi kaman yadda ta fasalta mata, saida suka zo bakin entrance d'in gidanne PA din Hajiya Zainab wadda da ita akaje bikon Amarya ta d'an dafa kai tace an samu matsala an manta ba'a bada card d'in da za'a bud'e gidan ba Mom ta tambayi to yanzu ya za'ai da sauri tace bari ta kira Her Excellency d'in, su dai su Aunty jugum sukai kowa na Al'ajabin jin sai da kati za'a bud'e kopar, bayan ta kirata itama nuna rashin jin dad'i tayi tace ta manta ta bada card d'in ne amman bari ta bud'e masu daga nan PA d'in tace Ok, hak'uri taba mutane na an barsu a tsaye bayan sun gama wayar tace gashi nan za'a bud'e, ba'a d'au wani lokaci ba suka ji kopar tayi wani d'an sauti PA din tace yauwa gashi nan an bud'e, ba sai na fad'i mamakin yan kawo Amarya ba, ana bud'ewa aka bada izinin a shiga PA d'in na gaba suka fara shigowa cikin passageway d'in, ita kopar falon dake anan k'asa lafiya lou ta bud'e masu ita kafin a shigar da Fauzy saida ta saci kallon hanyar benen da suka hau da Sameer, Jama'a kuzo kuyi kallon parlor mai sunan falo Aljannar duniya kenan, ashe dai yan kawo Amarya basu ga komai ba sai yanzu, wato wani irin tsararre kuma had'addan Falo ne daya jik'u da tsadaddun kayan alatu masu girgiza mutum, iya luntsuma luntsuman Sofas d'in dake cikin shi abun kallo ne ga wani musulmin Carpet dake malale a cikin shi wanda ya hau da kayan cikin Parlon, a tak'aice dai Idan nace zan tsaya bayyana had'uwar parlon to kuwa saidai in hak'ura da zuwa wurin dinner wadda za'a je da daddaren nan ni kuma gaskiya ina son ba idanuna hakkin su don haka na bar ma kowa ya fassalta had'uwar parlon a cikin zuciyar shi saidai nasan duk hasashen mutum ba lalle ya hasasho ainihin yadda yake ba tunda ba zuwa kai ba, gaba d'aya yan kai Amarya sakin baki sukai suna k'are ma falon kallo wasu na jinjina kai yayin da wasu suka kasa rufe baku nan su, ba anan aka sauke su na wani corridor aka nufa dasu sai gasu sun k'ara shigowa wani parlon, duk da bai kai had'uwar na farkon ba amman dai shima ba k'arya ya jiguna komai na cikin shi navy blue da milk ne sosae shima ya tsaru, anan aka sauke su duk suka zazzauna su Mom suka hau yi masu sannu da zuwa cikin washe baki suke amsawa, nuna masu d'akunan da zasu yi amfani dasu aka yi suna ta godiya duk suka tashi don suyi salla, bayan sun gama ne aka kawo masu lafiyayyen Abinci da lemuna aka sanar dasu in sun gama za'a tafi dinner suyi shiri lokacin Mom ta shigo tayi masu sallama tace zasu je suyi shirin dinner aka shiga k'ara yi mata godiya tanata fara'a take amsawa Fatuu ma sallama tayi masu Saboda kayan da zata saka suna can gidan tace ma Fauzy sai sun had'u wurin dinner d'in, bayan sun huta ne PA tazo da wadda zata yi ma Fauzy kwalliya harda kayan da zata saka ba 6ata lokaci aka fara. K'arfe goma saura aka zo d'aukar su ba'a bar kowa ba Amarya Fauzy ta sha kyau ba k'arya wani rantsattsan material ne golden brown aka yi mata fitted gown data hau jikinta sosae, lokacin da suka isa wurin dinner d'in shima dai ya had'u over da gani Naira ta sha kuka wurin tsara Hall d'in, tunda aka fara hidiman bikin Fauzy bata ga Sameer ba sai yanzu a wurin dinner d'in shima dai ya had'u sosae yana sanye da bugaggun Suit da suka hau da shigar Fauzyn, zuwa k'arfe goma da rabi kowa ya hallara har da uwar ango wato Hajiya Zainab tazo wurin, manyan mutane aka had'a a wurin hakan yasa ko ina ka juya jami'an tsaro ne mata da maza sosae aka zo kasantuwar wannan ce hidimar su ta farko, ba'a yi tak'amaimai anko guda ba gaba d'aya kowa da kalar wanda sukai saidae gaba d'aya lace ne aka saka kamar yan gidan su Haisam kalar lace din su d'aya haka ta bangaren su Sameer suma kalar nasu daban har kakar su ta zo da sauran dangin su yan Ethiopia haka yan Qatar ma sun zo, su Aunty Mareeya da sauran yan gidansu suma lace d'in su daban haka dai duk akayi ankon wasu kuma lace d'in su ne suka saka daban kamar su gwaggo da Aunty Feenah da Haulat dasu Zainab kowa lace d'in shi ya saka amman ita Mino irin nasu Fatuu ta saka ita ta d'inka mata Nameer dai bai samu zuwa ba don yana gab da fara yin Final Exams d'in shi, sosae kowa yayi kyau angwaye ma su Haisam duk wankan Suit sukai, ba 6ata lokaci aka shiga aiwatar da activities d'in dinner d'in abun gwanin k'ayatarwa. Gab da za'a tashi ne aka rarraba wata k'atuwar jaka mai d'auke da hoton Fauzy da Sameer cikinta uban souvenirs ne iri iri Aunty Mareeya aka ba na dangin su ta rarraba masu sauran da suka rage ta yanke aika ma Mamar su, Sai wurin k'arfe d'aya saura aka tashi abun sai godiyar Allah don an ci an sha an nishadantu yadda yakamata dinner ce da zata tsaya ma mutane a rai Aunty Mareeya dai taci uwar sabada kamar yadda ta ci alwashi kowa ka gani san barka yake dangin su Fauzy sai k'ara tayata murnar samun Sameer a matsayin miji suke ana ta fad'in ta dace ba kamar k'awayenta kowa jinjina irin rabon da take da shi suke, daga baya aka kwashe kowa aka maida su gida su Hajiya Zainab wani gidan nasu daban suka sauka wanda aka sauke su Fauzy kuma aka bar masu sai masu kula dasu.

Washegari bayan sun yi lafiyayyen breakfast wurin k'arfe tara na safe aka sanar wanda za'a maida Funtua su shirya, misalin k'arfe sha d'aya na safe masu tafiyar sun gama shiryawa ciki harda su gwaggo dasu Zainab k'awayen Fauzy iya wad'anda zasu je Nasarawa mutum goma ne aka ware daga dangin Fauzyn harda Aunty Mareeya itace cikon ta goman ko k'annen su maza da mata da suka zo duk komawa za'ai dasu Fatuu dai tana cikin ayarin iyalan Senator dole taje Nasarawa, bayan anyi sallama dasu suka tafi su kuma su Aunty Mareeya suka hau shirin tafiya nasarawa, sai bayan da akayi sallar Azahar sannan aka kwashe su Amarya Fauzy ansha kwalliya tana sanye da babbar atamfa an mata half gown tasa tsadaddun takalma da jaka da kuma gyale da suka hau da kayan nata, su Aunty ma duk sun sha gayu haka ta bangaren Fatuu ma kowa dai yayi kyau. Da yake ba wani nisa ke da akwae ba tsakanin Abuja da Nasarawa basu fi awa d'aya da rabi ba suka isa garin Lafia aka nufi Government House dasu, Alhamdulillah sun isa gidan gwamnati lafiya an yi masu kyakkyawar tarba don anan suka iske su Her Excellency sun riga su isowa, komai dai na gidan mai burgewa ne a part guda aka sauke su yana da babban parlor sai kuma bedroom da zasu kai ukku ko ina an k'awata shi da lafiyayyun furniture, d'aki guda Aunty Mareeya da Fatuu da Amarya Fauzy sai Fareeda suka sauka Aunty sai washe baki take tana fad'in Allah mai iko ko yanzu ta kafa tarihi taje gidajen gwamnati har biyu na Kaduna sai kuma nan Fatuu dai sai dariya take, da yake sai da suka ci suka k'oshi a Abuja kafin su taho d'an abun sha da taunawa aka fara tarbarsu dasu daga baya duk suka kwanta suna huta gajiya, sai bayan da suka yi sallar Magrib ne aka kawo masu lafiyayyun Abinci masu saka kunnuwa su motsa harda farfesun nama da lafiyayyun gasassun kaji da abubuwan sha kai kace wata Walima zasu yi, Aunty Mareeya ce ta zuzzuba ma sauran Mutanen da suka zo tare wanda su gwaggo ne kishiyar Maman su sai Yayye da kuma k'annen mamansu da Baban su sai babbar k'awar maman tasu, bayan ta gama da kowa suma ta zuba masu duk suka zauna anan falo suna ci, suna cikin ci Hajiya Zainab tazo k'ara yi masu sannu da zuwa tana ta fara'a haka suma ta tambaye su ba wata matsala duk suka ce a'a babu komai Alhamdulillah suna godiya Allah ya k'ara d'aukaka ta amsa kafin ta kalli Fauzy data sunkuyar da kai tana murmushi tace " Daughter an sha gajiya ko?" d'an d'agowa Fauzy tayi tana murmushi ta gaishe da ita ta amsa daga baya ta tafi bayan tace ma Aunty Mareeya inda wani abu they should feel free ta kirata tayi magana, bayan tafiyarta ne suka hau yabon ta harda su Mom yadda basu d'auki duniya da zafi ba. Misalin k'arfe goma duk sunyi shirin kwanciya harma sun kwanta saidae basu yi bacci ba suna ta hira har Aunty Mareeya na tambayar Fatuu su twins tace taga tun d'azu basu wurinta tace eh suna a wurin su Aunty Laila, Aunty Mareeyar tace ba ruwan su dai basu da rigima tace mata eh gaskiya in dai suna wurin su basu wata rigima saidai ko in suna jin yunwa kuma da an basu Abinci Shikenan har kwana ma suna yi a wurin su, kallon Fauzy dake kwance jikinta sanye da kayan bacci riga da wando tayi shiru Aunty Mareeya tayi tace "Amarya ya da yin shiru ko kinata tunanin Angon naki ne" d'an murmushi tayi bata ce komai ba Fatuu ta kalleta tana murmushi Yaya Fareeda dai har tayi bacci, Aunty bata dad'e da yin Maganar ba wayar Fauzy ta fara ringing ta kai hannu ta d'aukko ta, bin screen d'in tayi da kallo ganin mai kiran Aunty Mareeya ta tambayi waye ko angon ne a hankali ta d'aga mata kai alamar eh tace to ta d'auka mana ko sai ta yanke, picking tayi ta kara a kunne a sanyaye tayi mashi sallama tana jiyo Muryar shi k'asa k'asa ya amsa suka d'an yi shiru kafin yace mata ya gajiya tayi d'an murmushi tace babu gasu nan suna hutawa yace Ok sai kuma taji yace yana son ganinta gashi nan ya turo za'ai guiding nata inda yake, shiru tayi ta kasa ce mashi komai saida yace bata ji bane sannan ta d'an had'iyi abu tace to daga haka ya katse Wayar, ganin yadda tayi tsuru bayan ta gama wayar yasa Aunty Mareeya tambayar ta ya akai ne ta d'an yi shiru tana kikkafta idanu kafin ta fad'i mata wai cewa yayi yana son ganinta zai bata sak'o, jinjina kai Aunty tayi tana murmushi tace to kuma shine tayi kwance ta tashi taje mana ta tambayi tasan inda yake ne Fauzyn na k'ok'arin tashi ta d'an girgiza mata kai alamar a'a kafin tace yace za'a zo a rakata inda yake ta d'aga mata kai still murmushi take yi haka ma Fatuu, wurin kayanta ta nufa don gaba d'aya akwatunan da aka kai mata sun taho dasu tana niyyar bude wani akwati Aunty tace mi zata dauka tace mata Hijab, ce mata tayi ta manta ba Hijabai a cikin kayan ne tace Oh ta manta wllh ta d'ago duk ta wani sha jinin jikinta, kallon Aunty Mareeya tayi tace don Allah ta ara mata Hijab d'in ta da taga tayi salla d'azun tana murmushi tace to in ta bata kuma da Asuba tana son yin salla fa ta yafa gyale mana da sauri Fauzyn tace ai zuwa zata yi ta dawo yanzu kawai abu zai fad'i mata Aunty tace Uhmm ta nuna mata jakar kayanta tace ta duba tana ciki, bayan ta d'aukko ta saka ta koma bakin gado ta zauna tana jiran mai zuwa ya tafi da ita Aunty tace mata to bazata shafa ko d'an turare ba ta tura mata baki kaman zata yi kuka tace itafa ta fad'i mata sak'o kawai zai bata Aunty tace eh duk da hakan ai yakamata a matsayin ta na Amarya aji tana zuba uban k'amshi tunda shima ta tabbatar sai taji yana sakin kamshi sosae a matsayin shi na ango, jimm tayi tana masu wani kallo ganin su duka suna mata murmushi ta yamutsa fuska tace wai miye suke ta mata murmushi da sauri Aunty tace to kuka take son taga sun yi kawai suna murmushin jin dad'i ne ganin Allah ya nufa ta zama matar aure gashi har mijin nata na kiranta, shiru tayi bata ce komai ba Aunty ta k'ara ce mata ta d'an shafa turaren tace ai ta fesa lokacin da ta saka kayan baccin duk da haka ta matsa mata kan ta k'ara fesawa, tana cikin fesawar suka ji an yi sallama a bakin kopar shigowa d'akin jin muryar mace ce yasa Aunty ta bada izinin a shigo, wata mata ce ta shigo da gani yare ce tana sanye da short skirt baki sai farar riga kanta ba kallabi sai hular gashi daga yanayin shigar ta zaka fahimci kamar uniform ne, wurin gadon ta nufo ta tsaya daga gaban shi tana murmushi ta gaishe dasu Aunty Mareeya da turanci duk suka amsa mata cikin girmamawa tace dama itace aka turo zata tafi da bride Aunty tace to ta nuna mata Fauzy tace mata gata nan, a sanyaye ta nufo matar tana zuwa gabanta ta d'an rankwafa ta gaishe da Fauzyn bayan ta amsa mata ta tambayi zasu iya tafiya ta d'aga mata kai Matar ta shige gaba Fauzy tabi bayan ta tana fara tafiya Aunty tace mata Allah ya basu Alkhairi ta juyo ta tura mata baki duk suka sa Dariya, yar tafiya sukai ta wata hanya suka iso wani Corridor Matar ta dakata ta juyo tana murmushi ta nuna ma Fauzy wata dakakkar k'opa dake kallon su tace mata nan ne part d'in shi ta shiga yana nan ciki ta d'aga mata kai Matar ta juya ta tafi, gabanta na d'an fad'uwa ta tura kopar bayan ta bud'e a d'arare sai kace mara gaskiya ta shiga, tsaye tayi daga bakin kopar tana k'are ma wurin kallo wanda madaidaicin Parlor ne mara hayaniya komai na cikin shi Fari ne da ratsin golden tsit kake ji sai Ac dake ta aiki gaba d'aya ta sanyaya cikinshi ga wani k'amshi mai dad'i dake had'e da sanyin, a ranta ta shiga raya to ko yana ina ganin parlon k'walam ba kowa, tana haka wayarta ta fara ringing har saida ta d'an tsorata da sauri ta d'agota ta kalli screen d'in, shine yake kiranta ta kai hannu tay picking tana karata a kunne kafin tace wani abu taji yace tsayuwar mi take har saida mamaki ya d'an kamata don ta fahimci yana ganinta cikin yar rawar murya tace ai bata gan shi ba, ce mata yay akwae k'opa by her left ta bud'e ta shigo ta amsa mashi da to, tana tunkarar kopar gabanta na faduwa bayan ta isa gabanta d'an jimm tay kamar bazata tura ba sai kuma ta tuna da yana kallonta hakan yasa ta tura bayan ta bud'e ta shiga, Ya Subhanallahi shine abunda na furta lokacin da nayi arba da Bedroom din, shima baida wata hayaniya amman fa ya tsaru kuma shima komai na cikin shi fari ne da golden da alama dai yana son irin had'in kalolin don ko a part d'in shi na gidan daya kaita can ma kayan haka kalar su take duk da ba design d'in su daya ba saidai na ko ina sun had'u, nan gadon round bed ne yana da table a gaban shi sai kuma nightstands da akai masu shape wanda ya hau da gadon daga can gefen gadon babbar press c ta glass ana hangen kayan dake ciki sai opposite da ita nan wani elegant dressing mirror ne suma labulayen cikin d'akin sun tsaru suna da kyau da kuma k'auri, a d'an gaban gadon golden brown d'in carpet ne an mashi ratsin fari kai da gani ba sai an fad'a ba dole zai yi laushi don wani irin gashi gashi ne dashi, daga d'an can gaban inda furniture d'in suke reading nook ne wato wurin karatu akwae yar madaidaiciyar kanta wadda itama fara ce tana d'auke da littattafai daga gabanta farin Table ne d'auke da fitilar karatu da kuma wani d'an babban jirgi kamar na wasa, gefe opposite da kantar farar leather chair ce luntsumemiya mai mazaunin mutum biyu daga gabanta kuma Ottoman ne kalar kujerar. Sauke idonta tayi akan Sameer dake kwance saman gadon yana facing sama yayin da k'afafun shi dake a bayyane suke zube k'asa suna sanye cikin flip flops jikinshi yana sanye da jar robe da gani yayi shirin kwanciya ne, fargaba ce ta kama Fauzy ba kamar data ganshi haka don ita bata yi zaton a bedroom zata same shi ba, ganin bai d'ago ba kuma tasan yasan da ta shigo yasa tayi k'arfin halin shiga ciki tana tafiya kamar wadda k'wai ya fashe mawa a ciki, daga gaban shi ta tsaya d'an nesa dashi tana kallon shi gabanta na cigaba da d'an fad'uwa, ganin bai da niyyar tashi yasa a hankali tace mashi gata yay shiru kaman bai jita ba tanata kallon fuskar shi ya lumshe ido, sai da ya d'an d'auki lokaci sannan slowly ya fara bud'e idon tana ganin haka da sauri ta maida nata idanun k'asa, bayan ya bud'e su ya yunk'ura ya tashi zaune jin motsin tashin nashi yasa ta d'an saci kallon shi karaf suka had'a ido ta shiga yan kame kame da k'yar ta k'ak'alo Kalmar ina wuni tace mashi, bai amsa ba yana dai ta kallonta da idanun shi da suke adan lumshe kaman mai jin bacci ko kuma wanda ya farka baccin bai ishe shi ba, da hannu yay mata nuni da dab da shi yace mata ta zauna, saida ta had'iyi abu sannan ta matsa don ta zauna amman ba inda ya nuna mata ba sai da ta d'an matsa sannan ta zauna, kasa kallon shi tay ta zuba ma carpet ido sosae yanzu gabanta ke fad'uwa duk da ba wannan bane karo na farko da suka samu kusanci haka tunda da akai masu hotuna ma kusancin yafi wannan sai dai a yanzu harda yanayin shigar shi ta k'ara mata fargaba don gaba d'aya chest d'in shi a bud'e yake kwantacciyar sumar da take gani wani lokacin in suna yin Vedio call da daddare yau gata tana gani a zahiri, shiru kake ji kai kace ba mutane a cikin d'akin yana ta kallonta saidai ita batasan halin da yake ciki ba amman tayi tunanin kallon nata yake, suna haka taji ya kira Sunanta da wata irin murya gabanta yay wani irin bugu da k'yar ta amsa taji ya k'ara cewa bata son kallonshi ne da turanci da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a, gaba d'aya tsoron shi ne ya fara kamata ba kamar yanayin data ji yana mata magana, shiru bai k'ara cewa komai ba can kwatsam sai ji tayi ya kawo hannu ya jawota gabanshi ta yadda jikinsu ya had'u dana juna aikuwa nan take jikin ta ya fara rawa, k'ok'arin cire mata hijab d'in jikinta ya shiga yi aikuwa ta k'ank'ameta tak'i bashi dama hakan yasa shi dakatawa yana kallonta jikinta ya shiga yin 6ari sosae da k'yar ta d'aga idanunta da suka fito waje ta kalleshi taga ya d'aure fuskar tashi har saida ta had'iyi miyau Kutt da sauri ta janye idanunta daga barin kallon shi tana haka taji yaci gaba da kokarin cire Hijab d'in da sauri ta k'ara kankameta tana numfashi da d'an karfi, dakatawa ya k'ara yi cikin yar kakkausar murya yace mata miye hakan da take yi shiru bata ce komai ba ya k'ara ce mata ko yanzu ma ba kyau ne ya ta6a ta nan take ta gane Magana ya gaya mata don ta ta6a ce mashi haka lokacin daya fara zuwa wurinta a Katsina, kasa ce mashi komai tayi sosae tsoron shi ya shigeta idanunta sukai rau rau kamar zata saka kuka a lokacin ya k'ara kawo hannu zai cire Hijab din yanzu bata hana shi ba saidai yana cireta ta k'ank'ame jikinta tun ma kafin yayi mata wani abu ta fara yin k'walla cikin rawar murya ta fara ce mashi don Allah yayi hak'uri yay shiru yana bin ta da ido sai faman kerma take, d'age mata gira yay yace dame zai yi hak'urin da sauri tace kada yay mata komai don Allah, bai ce mata komai ba still bin ta yay da ido can yay yar ajiyar zuciya yace mata ta tashi taje shiru tayi don ta fahimci kaman da fushi yay Maganar amman Saboda halin tsoron shi da take yasa da sauri ta kai hannu ta d'auki hijab d'in ta maida kafin ta mik'e har zata tafi taji muryar shi yace "Su malaman da kika ce kinji suna preaching kan taba mace da ba muharrama ba baki ji suna yi akan mace data k'aurace ma mijinta ba?" dammm gabanta ya fad'i kaman an latsa mata remote ta tsaya cak zuciyarta ta hau harbawa don kuwa tun ma kafin ta mallaki hankalinta ta san kan abun a islamiyya tana jin malaman su suna fad'in duk macen data k'aurace ma mijinta Allah yana fushi da ita kuma zata kwana mala'iku suna tsine mata da ace zata mutu a wannan daren to kuwa ba makawa yar wuta ce, tuna hakan yasa da sauri ta juyo ta kalleshi idanun shi na akanta yana mata wani kallo mai tattare da 6acin rai, motsa baki ta shiga yi idanunta suka k'ara yin raurau suka cika da k'walla abu biyu suka tarun mata a cikin zuciya na farko fargabar abunda Sameer d'in zai mata sai kuma tsoron hukuncin ta in ta k'i amince mashi, jiki a mace ta koma ta zauna cikin rawar murya tace "D..don Allah kayi hakuri, d..dama ba wani abu yasa ba kawai naga kaman ba'a gama bikin bane tunda ko su Auntyna basu tafi ba yanzu ma muna cikin yin hira ka aika a taho da ni ina tsoron kada su gane wani abu in suka ga ban koma ba tunda ce masu nayi sak'o zaka bani" banza yay mata sai ma ya juyar da fuskar shi don abunda tay mashi sosae ya 6ata mashi rai ita kad'ai ce mace ta farko da take mashi abubuwa irin haka tun farko kawai don yana sonta ne yasa yake bi da ita yadda take so ta hana ya rink'a ta6ata duk da yasan hakan da tayi daidai ne amman bai yi tunanin a yanzu da aure ya shiga tsakanin su ba zata k'ara hana shi ya ta6a ta, mata da dama sun sha bashi damar ya aikata alfasha dasu wasu har rok'on shi suke amman bai ta6a kusantar wata ba koda yake ta6a mata bai ta6a aikata hakan da sunan ya biya ma kan shi buk'ata ba kawai don abun ya zame mashi jiki ne amman shi ba don yaji dad'i yake hakan ba, harda wannan dalilin yasa abunda tayi mashi ya 6ata mashi rai ganin yana da right da zai yi abunda yake so da ita amman ta hana kuma shi bai ma da niyyar aikata mata abunda ya fahimci tayi tunanin shi zai aikata mata, k'walla ne suka shiga zubo mata tana cigaba da bashi hak'uri amman yak'i ya kalleta don bai ma san mi zai ce mata ba a yadda ran shi ya 6aci yasan yana iya 6ata mata nata ran shiyasa yay banza da ita, can ba tare daya kalleta ba taji yace Shikenan taje da sauri ta girgiza mashi kai don sai taga kaman bai huce ba hakan da ya ce mata, zuciyarta ce ta raya mata tunda don ta k'i bashi damar ya ta6a ta ne yasashi yin fushin ita ta gwada yi mashi hakan k'ilan ya huce cike da k'arfin hali ta k'ara matsawa kusa dashi hannunta na rawa ta kai shi wurin nashi ta kamo hannun shi guda sai gashi a Hankali ya juyo ya kalli hannun nata dake ruk'e da nashi, ganin bai ce komai ba bai kuma janye hannun nashi ba yasa ta k'ara kai d'ayan hannunta ta kama d'ayan tana yin hakan ya d'ago ido ya kalleta cikin marairaicewa tace "Pls kayi hak'uri kada kayi fushi dani mala'iku zasu kwana suna tsine man" shiru yay yana dai ta kallonta har lokacin Fuskar shi a d'an d'aure take duk da Kusan shi koda yaushe haka fuskar tashi take amman dai yanzu tasan d'aurewar harda ta Fushi, ganin yak'i cewa komai yasa ta d'an matsa hannuwan nashi ta k'ara furta pls, jimm ya d'an yi kafin yay sigh ya furta mata is Okey duk da halin fargaba da take ciki saida ta d'an yi d'an guntun murmushi a hankali ta furta mashi ta gode ya d'an ta6e baki ganin haka yasa a d'an shagwabe tace ba yayi hak'urin ba ya d'an d'aga mata kai tace to ya saki fuskar pls kawai sai gani tayi ya d'an harareta tay d'an murmushi tare da maida idonta k'asa tana haka taji ya kawo hannu ya rungumota jikin shi duk da fargabar da take ciki saida ta d'an ji sanyi a ranta, runtse ido tay tayi lamo tana shak'ar daddad'an k'amshin da jikinshi ke saki gabanta na cigaba da fad'uwa bayan d'an lokaci taji ya kawo bakin shi saitin kunnanta cikin magana mai kaman rad'a yace mi yasa daga yin auren su ta za6i ta fara 6ata mashi rai bacin ita da kanta take cewa zata bashi happiness ko ta daina son shi ne, da sauri ta girgiza mashi kai ta d'ago tana kallon shi fuska a d'an yamutse kamar zata saka kuka tace " ba haka bane wllh kawai dai Saboda dalilin dana fad'i maka ne amman kayi hak'uri pls" yadda take Maganar da dumin numfashinta dake sauka akan face d'inshi suka k'ara turning nashi on ya tsura mata ido, a hankali tace mashi ai dai yayi hak'urin ko ya lumshe mata ido tare da kai hannu ya maidota jikinshi yay hugging nata tightly sai kace zai maida ta cikin jikinshi ita dai tay shiru tana cigaba da shak'ar daddad'an k'amshinshi, hannu ya kai ya cire Hijab d'in ya ajeta a gefe kafin ya d'aura ha6arshi a saman sumar ta yana shak'ar k'amshin da take, sun d'an d'auki lokaci a haka kafin ya kai hannun shi d'aya ya fara caressing bayanta lovingly nan take gaban Fauzy yaci gaba da bugu da k'arfi amman bata yi wani yunkuri da zai sa yaga kaman zata hana shi ba ko kuma bata so, d'ago face d'in ta yay idanun su suka shiga cikin na juna ya shiga jefa mata wani irin kallo mai tada tsigar jiki ji tay bazata iya jurewa ba tana k'ok'arin janye fuskar taji ya kawo duka hannuwan shi ya tallabo fuskar aikuwa da sauri ta runtse idanunta yanayin numfashinta na fita da d'an sauri, wani irin bugu k'irjinta yay jin ya had'e face d'in su suka shiga inhaling each others breathe, sun d'an d'auki lokaci a haka jikinta nata d'an kerma ba zato kawai taji ya had'e lips d'in su and he started kissing her deeply, a wannan lokaci gigicewa tayi jikinta ya hau yin kerma sosae bayan wani d'an lokaci gaba d'aya jikinta ya saki don da wani irin salo mai rikitarwa yake mata ganin abun take kamar a mafarki yake Faruwa da ita, kwantar da ita yay saman gadon daga baya ya shiga yi mata light love affair sosae take savoring ji take tamkar zata suke sai faman sakin yar ajiyar zuciya take, bayan wani lokaci ganin he's trying to make her go nicked yasa ta fara k'ok'arin hanashi hakan ta hanyar k'ank'ame jikinta cikin wata irin murya ya furta mata "Again...." Da k'yar ta iya tattaro kalaman bakinta ta furta mashi akwae haske ba tare daya ce komai ba ya mirgina can gaban gadon, wata yar sark'a ce kawai yaja hasken ya d'auke sai kuma ya kunna standing lamb guda d'aya ta d'an haska d'akin, salon abunda yake mata ne ya canza zuwa foreplay masu zautarwa, kasa hana shi aiwatar da abunda yake son yi tayi lokacin da aka kai wannan gabar gaba d'aya Fauzy loosing mind dinta tayi she was gasping heavily for breath suna haka taji ya kai bakin shi saitin kunnanta voice d'in shi da gaba d'aya ta gama canzawa ya furta mata why is she not romantic at all, shiru tay don bazata iya ce mashi komai ba da k'yar ma ta iya fahimtar abunda yace mata, k'ara ce mata yay she should do the same to him, da k'yar ta d'an fara maida mashi martanin tun bata saki jiki ba har dai ta saki ganin yadda yake nuna mata aikuwa hakan ya taimaka wurin sashi fara rasa control k'arshe abun fin k'arfinta yay gaba d'aya ta sakar mashi idanunta a runtse gam sai k'walla ke gangaro mata, jin abun ya d'au wata hanya ta daban yasata dawowa cikin hayyacin ta aikuwa a firgice ta fara k'ok'arin k'wace jikinta sai dai ina bata samu wata damar yin hakan ba, a gigice ta hau girgiza mashi kai ta fara mashi magiya tana fad'in don Allah yayi hak'uri banda wannan ba yanzu ba, ganin baida niyyar k'yaleta ne yasata fashewa da matsanancin kuka tana yin iyakar bakin kokarinta na ta k'wace kanta aikuwa ya nuna mata k'arfi ta yadda ko kwakkwaran motsi bata iya yi a lokacin gaba d'aya tayi giving up muryarta har ta disashe Saboda magiyar da take mashi,wani irin dogon numfashi taja kamar mai neman sukewa sai kuma ta k'wala wani irin ihu......

97

_ASM BY ZAINAB BATURE_

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

..........Kwance yake daga gefe yana breathing rapidly idanun shi a rufe shi kad'ai yasan yanayin da yake jinshi jikinshi har d'an rawa yake, da k'yar ya iya bud'e idanunshi da suka sauya kala ya juyar da fuskar shi ta kalli saitin Fauzy dake can gefe ta k'ank'ame jikinta sai rizgar kuka take kai da ka gani kasan tana a cikin mawuyacin hali, kiranta yay shiru bata amsa ba yay tunanin ko bata ji shi bane don muryar tashi ba sosae ta fita ba, da k'yar yaja jiki ya matsa wurin ta ya k'ara kiran sunanta nan ma shirun tayi mashi har lokacin kuma kukan take ba k'akk'autawa, hannu ya kai ya jawota jikinshi tana son ta k'wace sai dai bata iyawa don gaba d'aya jikinta yay mata wani irin nauyi ji take kamar an d'add'aureta ga wani rad'ad'in Azaba dake ratsa ko ina na jikinta k'afafunta sai faman kerma suke sosae, "Na yanka ki ne kike kuka haka?" Ya jefa mata tambayar yana nishi saidai sam bata ma sai mi yace ba kukanta take kawai, jin abun yayi yawa yasa shi janyeta daga jikin shi da k'yar ya tattaro karfi ya tashi da gwuiwowin shi ya matsa zuwa gaban gadon ya kai hannu ya ja sark'ar, lokacin da haske ya gauraye d'akin ya juyo Kusan Mutuwar tsaye yay lokaci guda gabanshi yay wani irin bugu ganin abunda ke a saman farin bedsheet d'in, aranshi ya raya ina aka samu abun da sauri ya maida idonshi kan Fauzy da duk da halin da take ciki lokacin da haske ya gauraye d'akin cike da k'arfin hali ta jawo wani abu da bata san ko minene ba ta rufa ma jikinta, komawa yay wurinta ya sa hannu ya d'agota a rud'e ya shiga tambayar ta minene, mi take ji ko yaja mata matsala ne, duk tambayoyin da yake mata bata tanka mashi ba sai kukan take cigaba da yi, gaba d'aya ya rasa ya zai yi gashi tak'i bud'e baki tayi magana balle yasan yadda take ji dama ace jirgi ce ita to da tuni yasan in ma matsala ce, sosae hankalin shi ya tashi har Fuskar shi ta nuna sai faman kallon gadon yake yana kuma kallonta, d'ago Fuskarta yayi ya tallabe ta da dukkan hannunshi cikin murya mai nuni da tsantsar tashin hankali ya shiga fad'in "Pls Wife talk to me, miye ne, akwae matsala ne, What are you feeling...? Pls tell me?" Sai faman jero mata tambayoyi yake amman bata da niyyar bashi amsar ko da d'aya ce ta runtse idanunta gam sai kuka take shar6a, jujjuya kai yay shi bai ta6a fuskantar abunda ya tada mashi hankali ba irin wannan ya rasa mike faruwa da ita da take ta faman yin kuka haka, had'e fuskar su yayi cike da damuwa yace mata don Allah tayi mashi magana yana cikin tashin hankali miya faru, da k'yar ta bud'e baki a wahalce tace mashi zafi take ji sosae duka jikinta ciwo yake k'ilan ma Mutuwa zata yi da sauri ya d'ago fuskar shi yana girgiza mata kai yace she should stop saying that pls ba abunda zai same ta zai yi mata yadda zata daina jin zafin shiru bata ce komai ba, tunanin abunda yakamata yayi ya shiga yi can wata zuciyar ta raya mashi ko yay googling k'ilan ya samu mafita sai kuma ya sake raya to mi zai fad'a shine problem d'in tunda ba sanin tak'amaimai ko miye matsalar yay ba, yanata tunanin Mafita can ya sake raya ko ya kira Mom d'in shi ya fad'i mata, karo na farko daya ji nauyin ya sanar da ita abu can Haisam ya fad'o mashi a rai, da sauri ya kwantar da ita ya jawo robe d'in shi ya maida saida yaja mata duvet sannan ya sauka daga saman gadon ya nufi wurin nightstand d'in da anan wayar shi take ajiye ya d'auka, k'ok'arin kiran Haisam ya shiga yi cikin sa'a ta fara yin ringing yana jin haka ya nufi cikin d'akin wurin inda ake karatu yayi hakan ne don in Haisam d'in ya d'auka yana iya jiyo kukanta, har ta yanke ba'a d'aga ba sai lokacin ya ga time Kusan k'arfe d'aya da rabi na dare a ranshi ya yanke yasan ko ya sake kira bama lalle Haisam d'in ya d'aga ba duk da haka ya shiga k'ok'arin sake kiran shi, har zai latsa kiran sai ga kiran Haisam d'in ya shigo dama lokacin daya kira shi yana cikin bacci yana farkawa kiran na katsewa lokacin da Haisam d'in ya ga shine mai kiran saida yay mamaki a ranshi ya ayyana ko lafiya, da sauri Sameer yay picking gaisawa sukai ya bashi hak'uri kan tashinshi da yayi yace mashi ba komai, shiru yay yama rasa ta ina zai fara Haisam na jin hakan yasan da wani abu dama tun daga kan yanayin muryarshi ya fahimci hakan, tambayar shi yay lafiya Sameer d'in yace mashi akwae wani matsala ne yana son ya taimaka mashi da sauri yace mashi Ok miya faru, bayanin halin da Fauzy ke ciki yayi mashi Haisam ya d'an yi salati kafin ya tambayi yanzu tana ina yace mashi gata can tana ta kuka da gani she's in severe pain, ajiyar zuciya Haisam ya sauke wani irin tausayin Fauzy ne ya kama shi don ya tuno da yadda hakan ta faru tsakanin shi da Fatuu gashi yasan halin Sameer sosae yasan k'ilan harda k'arfi ya nuna mata, tambayar shi Haisam yay ba akwae clinic anan ba da sauri yace mashi eh akwae yace to ya duba in akwae likita sai a dubata haka yakamata, d'an jimm Sameer d'in yay kafin yace mashi yanzu sai namiji ya dubata, d'an murmushi Haisam yayi kafin yace mashi a'a ba dole sai shi ba ya bincika in za'a samu mace sai ta dubata in kuma babu koda nurse ce sai ta dubata in taga abun babba ne a shawarce kawai ko namijin aka samu ya dubata ko kuma ya fita da ita waje ya kaita Asibiti amman a yanzu dai gaskiya tana buk'atar likita ya dubata don zai iya yuwuwa ko ta samu wound ne, kai ya jinjina mashi yayi mashi godiya Haisam d'in yay fatan Allah yasa ba babbar matsala bace a hankali yace Amin sukai sallama yace zai kira yaji halin da ake ciki, Bayan sun gama landline ya nufa da sauri idon shi akan Fauzy da ba laifi ta d'an rage sautin kukan, bayan ya kira tambaya yay ko akwae likita mace on call cikin sa'a aka ce akwae ya buk'aci a turo mashi ita, bayan ya gama wayar dawowa yayi gadon ya fara k'ok'arin maida ma Fauzy kayanta bayan ya gama bedsheet d'in ma ya yaye shi a ranshi ya shiga tunanin yadda zai yi dashi can ya juya ya nufi hanyar toilet yaje ya saka shi cikin washing machine, dawowa yayi ya zauna a bakin gadon idon shi akanta, hannu ya kai yana shafa gefen fuskar ta ya shiga jera mata sannu yace tayi hak'uri yanzu za'a zo a dubata zata daina jin zafin shiru bata tanka ba sai faman sheshsheka take, bada jimawa sosae ba akai knocking k'opar cikin d'an d'aga murya ya bada izinin a shigo, matashiyar likita ce tana sanye da lab coat kanta ta sanya farar himar idanuwanta na sanye cikin glasses yayin da hannunta ke ruk'e da d'an plastic first aid kit, da sallama ta shigo ya d'aga ido ya kalleta hakan yasa ta nufo shi, daga gefe ta tsaya fuskar ta a sake ta gaishe dashi ya amsa tace gata an buk'aci ganinta ya d'aga mata kai tare da nuna mata Fauzy a hankali yace ita zata duba ta furta Ok, aje kit d'in tayi ta kai idonta kan Fauzy data duk'unk'une tace mata sannu ko, shiru bata amsa ba hakan yasa ta rankwafa ta d'aura hannunta a jikinta ta k'ara ce mata sannu sai lokacin ta d'aga mata kai, tambayar ta tayi Mike damunta tayi shiru ta k'ara cewa ta daure ta fad'i mata hakan zai sa tasan wane treatment zata bata, da k'yar ta bud'e idanunta da sukai mata wani irin nauyi har sun d'an kumbura sunyi jajur haka lips d'inta ma sunyi ja ta shiga motsa baki amman ta rasa mi zata ce mata, tana niyyar sake tambayar ta Sameer dake kallon su ya bata amsa da she had her first night and she said she was feeling much pain, kai ta jinjina dama ta zargi hakan tunda tasan da yayi auren kawai don ta cika ka'idar aiki yasa ta tambaya, bud'e d'an akwatin tayi ta fiddo gloves bayan ta gama sakawa ta kalli Sameer tace mashi zata duba ta ya kauda kan shi tare da ce mata she should go ahead ta d'an yi murmushi tare da d'an ta6e baki ta maida idon ta kan Fauzy, saida taji tsananin tausayin Fauzy ya kamata a ranta ta yanke da gani ba tantama k'arfi ya gwada mata, sosae ta dubata tana yi tana yi mata sannu tare da d'an girgiza kai kuma har lokacin Sameer d'in na nan zaune ya had'e hannuwan shi ya d'aura Ha6arshi yana kallon gaban shi, d'agowa likitar tayi fuska a yamutse ta d'an saci kallon Sameer a ranta ta ayyana merciless, ganin bata buk'atar stitches tace mashi suna buk'atar ruwan zafi da d'an gishiri yace Ok akwai a cikin toilet gishirin kuma yace yana zuwa ya mik'e ya nufi hanyar fita, bayan fitar shi ne ta d'an zauna daga bakin gadon ta kai hannu ta d'ago da ita har lokacin sheshsheka take ta shiga rarrashinta, bada jimawa ba sai gashi ya dawo ruk'e da yar jakar gishiri ya kawo mata bayan ta amsa ta taimaka ma Fauzyn ta mik'e saidai tana yin yunk'urin tafiya ta saki yar k'ara da sauri ta fara k'ok'arin komawa ta zauna likitar tana ce mata sannu bata iya tafiyar ne tana nishi ta d'aga mata kai, Sameer ne yace bari ya kai mata ita yay mata d'aukar jarirai suka nufi toilet d'in, yana d'auke da Fauzyn har ta gama had'a ruwan ta kalleshi tace zai iya sauketa, ganin yayi masu tsaye bayan ya ajeta yasa tace Shikenan he can go kaman bazai tafi ba sai kuma ya juya ya tafin, yana komawa cikin d'akin Haisam ya kira a ranshi sosae yaji dad'in yadda ya nuna damuwa don ya gane bai koma bacci ba, bayan yayi picking tambayar shi halin da ake ciki yay ya sanar mashi da an samu Doctor din gata can tana treating nata Haisam ya furta Alhamdulillah in sha Allah zata samu sauk'i kada ya damu shima sun samu Kusan irin problem d'in da second wife en shi Sameer ya furta Ok, cike da tsokana yace mashi amman wai shi ya akai ya bari har hakan ta faru ma yana wani irin murmushi yace shi da yake da aure ma ya bari hakan ya faru balle shi da wannan ne first time en shi, yar dariya Haisam yay yace kawai dai ya fad'i mashi he lost control ya d'age gira yana murmushin gefe yace he never thought haka abun yake, dariya mai sauti Haisam yay kafin yace ai da ya tsaya yana ta cutar kanshi Sameer d'in ya furta wllh sukai dariya, kafin suyi sallama yace mashi pls ya lalla6ata sosae ya furta Ok, duk yadda likitar taso Fauzy ta zauna ruwan abun yaci tura sai faman koke koke take tana fad'in zafi bazata iya ba sai fama take da ita, jin kukanta yayi yawa ya sashi dawowa cikin toilet d'in ya tambayi ya akai likitar tayi mashi bayanin tak'i ta zauna ruwan ne yadda yakamata da bud'ar bakin shi sai cewa yay to dole sai ta zauna ne, ba don shine yayi Maganar ba daya samu amsa daidai dashi dama ya bata haushi yadda taga yayi ma Yarinyar, amsa ta bashi da eh Saboda ta samu rauni ne dole sai tana zama ruwan ne zata warke ya jinjina kai alamar gamsuwa kafin ya maida idon shi kan Fauzy da ta d'an d'osana ta zauna a bakin bathtub tana ta jan majina tare da yar sheshsheka, tambayar likitan yay daga zaman ruwan zafin sai mi tace tana buk'atar taci Abinci sai tasha pain relievers, tambayarta yay tazo da magungunan tace eh akwai wasu da zata bata yace Ok taje kawai ta aje mashi su nan zai sakata a ruwan tace Ok amman yanzu wannan tasan yasha iska akwae buk'atar a canza wani yace Ok ta canza, har ta juya ya tambayi tsawon lokacin da zata yi a ruwan ta fad'i mashi kafin tace ya bita a hankali yadda ruwan zai shigeta yadda ake so yace Ok, da biyu ta fad'i hakan don a tunaninta yana iya cewa ya gwada mata k'arfi, bayan fitar likitan rarrashin Fauzy ya shiga yi cikin kwantar da murya kai kace bai iya hakan ba, kuka taci gaba da yi tana cewa ita dai bazata iya shiga ba zafi yake k'ara mata, shiru yayi ya rasa yadda zai yi mata idon shi akanta sai faman juye juyen ciwo take, k'arshe dai dole saidai k'arfin ya gwada mata ya d'auketa cak tana ta kuka kamar za'a ma k'aramar yarinya wanka, daga baya da ruwan ya shigeta sosae ta d'an d'auki lokaci a ciki sai gashi ta fara jin dad'in shi ta saki jiki, bayan ta d'auki lokacin da aka fad'i mashi ya canza ruwan ya shiga yi mata wanka bata yi yunk'urin hana shi ba don tasan ba lalle ya k'yaleta ba gashi dama gaba d'aya ba k'arfi a jikinta saidai kawai ta runtse idanunta, bayan ya gama yi mata yace mata tayi na tsarki yana tsaye tayi ta gama ya d'aukko babban towel ya rufa mata ya sake d'aukko wani short ya lulluba mata a kai ya kara d'aukkota suka fito cikin d'akin, a saman gado ya d'aurata ya mik'e ya nufi wurin dressing mirror, mai da yake amfani dashi ya d'aukko yazo ya shafa mata yana ta kallonta har lokacin idanunta a rufe suke, bayan ya maida mai d'in wurin press d'in shi ya nufa ya bud'e yay d'an jimm yana tunanin kayan da zai d'aukko mata tasa kafin zuwa da safe, wasu riga da wando masu taushi ya d'aukko mata duk da yasan zasu yi mata yawa sosae amman zata fi jin dad'in su, shi ya saka mata kayan ganin kanta ya tsane yasa bai yi tunanin a busar dashi ba, ana gama saka kayan ta kwanta duk wannan abun bata bari ta had'a ido dashi ba, ganin yadda ta takure ya ja mata Duvet tare da mik'ewa ya nufi hanyar fita daga cikin d'akin, lamo Fauzy tay duk ta damu tunaninta yanzu taya zata je wurin su Aunty Mareeya a haka ta fara yin gyangyad'i, ya d'an d'auki lokaci sannan ya dawo yana d'auke da wani madaidaicin tray ya aje a saman table, cup d'in tea ne mai k'auri sai bread da wainar kwai Kitchen yaje yasa aka had'o mashi, wurinta ya nufa har tayi bacci kana ganin yanayin da take yin shi zaka gane shi is not alright, bai sha wahalar tashinta ba don baccin ba wani mai nauyi bane, farko nunawa tayi ta k'oshi kaman zata yi kuka da yayi mata Maganar Abincin saida ya rarrasheta sannan da kanshi ya fara bata, ba laifi ta d'an ci da yawa don wani irin fayau cikin ta yay mata, bayan ta nuna ta k'oshi tana niyyar kwanciya da sauri yace ta bari tasha magani sai ta kwanta, a saman nightstand ya d'aukko su guda biyu ne kowanne an rubuta yadda za'a sha ya 6allo mata da sauran tea din data rage ya bata tasha bayan ta gama fuska a yamutse tace ruwa zata sha da sauri ya furta Ok ya nufi hanyar fita, a hankali ta juya tana kallon bayan shi ganin shi take kamar bashi ba, a parlor ya d'aukko bottle water tare da glass cup ya kawo mata bayan ya bud'e ya zuba mata ya kai bakinta zai bata ta d'aga hannu ta amsa fuskarta na kallon gefe, kaman rabi tasha ta mik'a mashi ya amsa suma ya aje su saman table, zaune tayi bata kwanta ba yay tsaye yana kallonta ya lura da kaman fushi take dashi don tak'i ta ko kalle shi, cike da k'arfin hali ta fara kokarin mikewa yana ganin haka ya tambayeta mi take so ne tace mashi d'akin da suke zata koma da sauri ya matsa ya kamata yana fad'in taya zata koma a wannan halin ta kwanta anan ai lafiya lou zuwa da safe in ta k'ara samun sauk'i sai ta koma, shiru tay dama dai kawai ta fad'a ne amman itama ba son komawa take a wannan halin ba kuma tunda su Aunty suka ga ta dad'e tasan tuni ma sun zargi wani abu, janyewa tayi daga kamatan da yayi ta kwanta yaja mata duvet, d'auke tray d'in yay ya nufi hanyar fita, a parlor ya zauna ya idasa cinye sauran data rage don shima yunwa yake ji bayan ya gama anan ya bar kayan ya dawo cikin bedroom d'in, toilet ya wuce bayan wasu mintuna ya fito k'ugunshi d'aure da towel ya nufi press d'in shi, shima riga da wandon ya d'aukko ya fara sakawa yana yi yana kallon Fauzy bayan ya gama kimtsawa ya nufi gadon saida ya kashe wutar d'akin sannan ya daidaita kwanciyar shi, hannu ya kai zai rungumota jikinshi kawai sai ji yayi ta k'i bari yayi hakan nan ya gane idonta biyu ko kuma baccin bai d'auketa ba sosae, matsawa yay ya had'e jikinsu tana ta son k'wacewa ya kai bakin shi saitin kunnanta cikin magana mai kamar rad'a ya fara magana, "I'm very sorry Wife, I know I hurt you kiyi hak'uri pls bansan ya akai komai ya faru haka ba I don't know what came over me" sheshshekarta da yaji k'asa k'asa yasa shi gane kuka take, k'ok'arin juyo ta ya shiga yi ta dawo suna facing juna da yake a d'an kwai haske ya kai hannu yana goge mata k'wallan yana k'ara bata hak'uri yana bai san ya akai hakan ta faru ba, cikin Muryar kuka tace amman ba saida taita rok'on shi ba kan yayi hak'uri ya k'yaleta ba amman ya k'iya, a rud'e yace mata ya rasa control ne he didn't know that's how it was gaba d'aya tun farko ma baida niyyar wannan, shiru tayi bata ce komai ba ya shiga shafa gefen fuskarta yana fad'in Pls she should forgive her husband yasan yayi mata ba daidai ba, aka ce tsakanin mata da miji sai Allah ce mashi tayi shikenan tayi hak'urin, rungumeta yay sosae yana murmushi yayi mata godiya tare da Fad'in he knows he is blessed daya sameta matsayin mata shiru ta d'an yi sai kuma k'asa k'asa ta furta itama haka ya k'ara k'ank'ameta cike da jin dad'i yace "I Love You so much Babes" yay Maganar tare da pecking kumatunta, rufe ido tayi a ranta ta raya wato dama daya ta6a ce mata ba yanzu zai fad'i mata hakan ba yana nufin sai wannan lokacin kenan, shiru sukai wani irin nishad'i suke ji ba ma dai kamar Sameer ji yake yau is the happiest day of his life, jin saukar numfashinta a nutse yasa shi gane tayi bacci ya gyara masu kwanciya bada jimawa ba shima baccin ya d'auke shi.

Kiran sallar Asubar farko alarm ya tashe shi, duk da bai jin k'warin jikinshi amman Saboda ya saba yin raka'atanil fajr yasa ya daure ya tashi bayan ya janye Fauzy a hankali, toilet ya nufa yayo Alwala bayan ya fito ya nufi press ya canza kaya zuwa jallabiya kafin ya nufo inda zai yi sallar, bayan ya gama zaune yay yana tasbih yana yi yana kai idon shi kan Fauzy dake ta bacci cikin Duvet fuskar shi a sake kaman zai yi murmushi, yana a wurin har lokacin sallar Asuba yayi ya tashi ya kabbara don ji yay bazai iya zuwa Masallaci ba, bayan ya gama yayi Addu'oi kafin ya mik'e ya nufi gadon, bayan ya haye yana k'ok'arin janyota jikinshi ta fara motsi a hankali ta fara bud'e idanuwan ta, tana bud'e su suka shiga cikin nashi ba laifi sun d'an k'ara washewa amman duk da haka yanayin su basu dawo daidai ba sunyi kalar na mara lafiya, bin shi da kallo tayi yay mata murmushi yace ta tashi ta d'an d'aga mashi kai, tambayarta yay ya take ji yanzu da k'yar ta bud'e baki ta bashi amsa da da sauki ya kai hannu yana shafa mata kai yace zata koma normal in sha Allah ta d'aga mashi kai, shiru suka d'an yi can yace mata ko tana jin yunwa ya samo mata abunda zata ci ta d'an girgiza mashi kai alamar a'a sai kuma ta tambaye shi gari ya waye ne yace mata eh anyi sallar Asuba ita ya gama yanzu, tana jin haka ta fara k'ok'arin tashi zaune ganin haka ya kai hannu ya taimaka mata, bayan ta zauna ya tambayi salla zata yi ta d'an yi shiru sai kuma tace mashi so take ta koma d'akin da suke in taje tayi sallar a can, ce mata yay miyasa ta damu da ta koma ne nan ba d'akin mijinta bane kuma ai ba komai don ta zo don anan ma zata zauna kafin su tafi UK, yamutsa fuska tayi kaman zatai kuka tace tafi son ta koma can in suka tafi sai ta dawo nan d'in yace Ok ta fara yin sallar, shi ya taimaka mata ta mik'e da k'yar ta fara taka k'afafun tana yin tafiya a hankali yana mata sannu k'arshe ma ganin yanayin tafiyar tata sai kawai ya d'auketa ya nufi toilet da ita, bayan anyo Alwalar Hijab d'in da tazo da ita ta saka kafin ta kabbara sallar, bayan ta gama ne ya nuna mata ya za'ai ta koma can a wannan halin ko tafiya bata iya yi sosae tace mashi gara dai ta tafi in ta zauna anan kowa zai san abunda ya faru gashi ba gama hidiman bikin akai ba ko yau ma za'a yi Walima, shi kan shi bai son abun ya bud'u hakan yasa yace suje ya rakata, farko kama mata hannu yay tana tafiya a hankali ganin bata sauri yasa shi d'aukarta tana ta fad'in don Allah ya ajeta kar a gansu yace mata ba wanda zai gansu tunda Asuba ne baza'a fito yanzu ba, suna zuwa bakin kopar Falon su tace ya ajeta shi da wai har cikin Falon zai shiga da ita ta kafe sai da ya sauketa, saida ta kalle shi sannan ta juya yay tsaye yana kallon ta har ta shige, tsaye tayi a bakin k'opar shiga Bedroom d'in da suke tana zullumin shiga can wata zuciyar ta raya mata to da tayi tsaye nan in kuma wani ya fito daga wani d'akin ya ganta fa, yin wannan tunanin yasa ta kai hannu a d'arare ta tura kopar a hankali, tana sa kai cikin d'akin suka had'a ido da Fatuu dake zaune akan abun salla bata dad'e da gamawa ba, har saida gaban Fauzy ya fad'i da suka had'a ido cikin kama kai da sauri ta janye idonta ta nufi ciki, cike da k'arfin hali take tafiya a k'ok'arinta na kada a gane saidai duk yadda taso tayi tafiyar sosae abun yaci tura dole a hankali take taka k'afafun, a bakin gado ta zauna tak'i yarda ta k'ara kallon Fatuu bayan d'an wani lokaci Fatuu ta taso ta nufo gadon itama ta zauna a gefenta tana kallonta da murmushi tace mata ta dawo, kai ta d'aga mata ba tare da tace komai ba sukai shiru can Fatuu ta dafa Shoulder d'inta tace mata ya akai ne wai sai lokacin ta d'an kalleta tana k'ok'arin k'ak'alo murmushi tace mata ba komai, Aunty Mareeya ce ta fito daga cikin toilet tana yarfe ruwa ganinta saida gaban Fauzy ya fad'i sosae tayi saurin janye idonta, nufo cikin d'akin tayi tana fad'in "Zarah kin gama sallar ki ara man Hijab d'in ita waccan mai amso sak'on ta tafin man da Hijab saida dama nace...." bata k'arasa ba sakamakon ganin Fauzy da tayi a gefen Fatuu, da sauri ta nufo inda suke ta tsaya daga gaban su tana fad'in ashe ta dawo Fatuu ta d'aga mata kai, tana kallonta tace "ke malama mai amso sak'o sai muji ki shiru kika sa munata zaman jira ko kayan dad'i ne ya siyo maki ki kawo mu tattamna muma" shiru bata ce mata komai ba bata kuma kalleta ba ganin haka yasa ta kirata "Fauziyya" shiru bata amsa ba, kallon Fatuu tay tace mata ya akai ne ta d'an rausayar da kai tace bata sani ba, tambayarta Fatun tayi yaushe ta dawo tace mata bada dad'ewa ba bayan ta gama salla itama tayi mata magana ta ganta haka, jinjina kai Aunty tay ta juya kan Fauzy ta kai hannu ta d'ago Fuskarta da d'an murmushi tace "Yar gidan Hajiya ya akai ne ko mun fara yar kunya ne" tana rufe baki Fauzyn ta fashe mata da kuka tare da kifa fuskarta a jikinta, d'an gwalo ido Aunty tay sai kuma ta fad'ad'a murmushinta ta kai hannu tana d'an bubbuga bayanta tana fad'in ya isa to miye abun kuka, jin yadda take ta kukan ne yasa ta d'ago fuskarta tana share mata hawayen tana fad'in ya isa Shikenan haka girma yake zuwa ma mutum, kukanta ne ya tashi Yaya Fareeda dake bacci da yake bata salla, tambayar Aunty tayi lafiya take kuka tana faffad'an murmushi tace mata ba komai Yaya Fareedar bata kawo komai a ranta ba don jiya tayi bacci aka tafi da Fauzyn, zama Aunty tay kusa da ita daga d'ayan 6angaren a hankali tace mata akwae abunda ke mata ciwo ne ta d'aga mata kai ta tambayi mike mata ciwon cikin muryar kuka tace duka jikinta, d'an jimm tayi tana ta kallonta can tace badai ta samu matsala ba ko tace mata likita tazo ta dubata tace wai ta rink'a zama a ruwan zafi sai magunguna da ta bata, a hankali suke Maganar amman duk su Fatuu na ji, jawota Aunty tay jikinta tana bata hak'uri tace zata daina jin ciwon bada dad'ewa ba sai faman murmushi take, tambayarta tayi yanzu ta zauna ruwan zafinne ta girgiza mata kai alamar a'a tace Ok bari tayi salla sai ta taimaka mata ta d'aga mata kai, mik'ewa tay tace ma Fatuu ta bata Hijab d'in jikinta bayan ta amsa da sauri ta nufi wurin yin sallar, bayan tafiyarta cigaba da yin sheshsheka Fauzy tay wani irin tausayinta ne ya kama Fatuu ta d'agata tana bata hak'uri tare da yi mata sannu haka ma Yaya Fareeda kai kawai take d'aga masu, bada jimawa ba Aunty ta gama sallar ta nufo su tana cire Hijab ta mik'a ma Fatuu kafin ta kalli Fauzy tace suje Toilet din, mik'ar da ita tayi har zasu tafi ta dakata tare da kai hannu tana fad'in a cire Hijab d'in ko, tana cirewa tabi kayan jikin Fauzyn da kallo kafin ta saki yar dariya tare da Fad'in "Sunan wani k'anin tsohon mu Baba Salmanu, wannan kayan fa?" tana rufe baki su Yaya Fareeda suka kwashe da dariya da sauri Fauzy ta fad'a jikinta tare da sakin wani sabon Kukan, rarrashinta ta shiga yi tana fad'in tayi hak'uri shegen bakinta ne da bai gani yayi shiru taga bada su ta tafi bane shiyasa ta tanka, da k'yar ta samu tayi shiru tayi ma su Fatuu alamar su daina yin dariyar kowa ya gumtse ta kamata har zasu tafi tace ma Fareeda ta bud'e akwatin Fauzy ta d'aukko mata towel ta kawo mata sannan suka nufi hanyar toilet tana tafiya a hankali Aunty Mareeyar tana ta mata sannu harda cewa ko ta goyata da sauri ta girgiza mata kai alamar a'a, Bayan sun je toilet d'in a cikin bathtub ta tara ruwan zafin bayan ta toshe tasa Fauzy ta cire dogon wandon baccin da yake rigar ta rufeta sosae ta kawo mata har wurin gwuiwa, itama saida ta tittirje mata wurin zauna ruwan ganin yadda take yi ne yasa Aunty ce mata wai ta tabbatar bata samu matsala ba cikin nishi tace mata eh likitar ta dubata amman tace ta samu rauni, yamutsa fuska Aunty ta shiga yi tana d'an Jujjuya kai alamar tausayi kafin tace "shi kuma surukina ya da gaggawa haka, duk da dai abun farinciki ne amman banji dad'i ba d'an jakar uba ya wahalar man dake" tana rufe baki cikin yamutsa baki Fauzy tace "Aunty ki daina zagin shi shima yace bada son ranshi hakan ya faru ba" gwalo ido Aunty tay da alamun Al'ajabi tace "iyyeee, ah lallai miji dad'i, to tuba nike your Excellency ayi hak'uri su6utar baki ce" tayi Maganar tare da d'an harararta Fauzyn ta d'an tura baki tana kikkafta idanu kaman zatai kuka, sosae ta sakata ta zauna ruwan daga baya ta baro mata toilet d'in tace tayi wanka, after some minutes ta fito d'aure da towel d'in da Aunty ta kai mata su kuma kayan baccin Sameer d'in ta ninkosu lokacin Fatuu bata a d'akin taje tay feeding su twins da yake wurin su Mom suka kwana sai Yaya Fareeda itama har ta koma bacci, taimaka mata Aunty ta shiga yi ta shirya cikin doguwar jallabiya ta d'aura kallabin Aunty tace mata tasan bata rasa jin yunwa ko ta d'aga mata kai alamar eh, shiru tayi tana d'an tunani kafin tace ina wayarta ta kira shi tace tana jin yunwa, sai lokacin ta tuna da ita taje part d'in nashi hakan na nufin ta manto ta can ta fad'i mata, ce mata tayi to ta d'an kwanta aga zuwa d'an anjima k'ilan a kawo masu breakfast da wuri ta d'aga mata kai ta fara k'ok'arin hawa gado ta kwanta Auntyn na k'ara yi mata sannu sosae take jin tausayinta don tasan dole ma taji jiki, bayan ta kwanta itama Aunty Mareeyar kwanciya tayi basu dad'e ba da kwanciyar akai sallama bakin k'opa Aunty ta d'ago kai tana bada izinin a shigo, wata yar dattijuwar mata ce ta shigo tana ruke da wani had'addan basket sai k'yalli yake jikinta sanye da apron Aunty na ganinta ta mik'e zaune, nufo ta tayi da murmushi ta gaishe da ita ta amsa mata itama tana murmushin tace dama Yalla6ai Sameer ne yace ta kawo ma Amarya Aunty tace to ta tashi tsaye ta kar6a, kafin matar ta tafi ta nuna mata magunguna dake ciki basket d'in tace hada su aka ce ta kawo ta sake cewa sai kuma wannan ta Mik'o mata wayar Fauzyn, amsa tayi tay mata godiya Matar ta tambayi da wani abu Aunty tace mata a'a ta k'ara mata godiya ta juya ta tafi, nufar side drawer tayi ta d'aura kwandon kafin ta shiga bud'e had'add'un Warmers d'in dake ciki, d'aya farfesun kaza ne yaji kayan k'amshi gwanin kyau a ido, bayan ta rufe ta bud'e d'ayar soyayyen dankalin turawa ne da dafaffun k'wai sai kuma Flask wanda da gani set ne da Warmers d'in nan tea ne da yaji kayan k'amshi daga gefe akwae plates da cup sai cokulla sai Madara da milo da kwalin sugar, Murmushi Aunty ta shiga yi a fili ta furta "Su surukina kenan tunda fa an cuci yar mutane dole aita nan nan da ita" a ranta kuwa dad'i ne ya kamata don da alama komai ya kasance yadda take so, tashin Fauzy ta shiga yi bayan ta bud'e ido tace mata ta tashi ga Abinci nan Angonta ya aiko mata ta kamata ta tashi zaune, Fauzy taji dad'in Abincin dama a lokacin ta fara jin yunwar sosae, ba laifi ta ci sosae ba kamar kazar Aunty tasata tasha romon sosae, ganin tana ta ci yasa ta kalleta cikin d'an disashewar murya tace mata itama ta ci mana Aunty Mareeya tayi d'an murmushi tace ita dai ta ci ta k'oshi tukun don ta fita buk'ata, tana cikin ci sai ga kiran Sameer ya shigo Aunty ta d'auki wayar ganin shine tay d'an murmushi, picking tayi ta kara ma Fauzy a kunne shiru tay ta dakata da cin Abincin taji ya kirata da Babes d'an kallon Aunty tay data ruk'e mata wayar kafin can k'asan mak'oshi ta amsa, tambayar ta yay jikin a hankali tace mashi da Sauk'i yace ya manta bai sata ta zauna ruwan ba ta bashi amsa da tayi anan yace Ok sai kuma ya tambayi taci Abincin da aka kawo tace eh gashi nan tana ci yace Ok bari ya barta taci amman pls taci sosae sai tasha magani ta amsa da to ya katse kiran, bayan ta k'oshi ta bata magungunan tasha kafin ta koma ta kwanta sannan Aunty Mareeya itama ta zuba tana cikin ci Yaya Fareeda ta farka wai k'amshin abincin ne ya kai mata cikin bacci tama yi zaton Mafarki take Aunty tay dariya tace ango ne ya aiko ma amaryar shi shine take cin saura itama ta wanko baki tazo taci tace to. Wuraren k'arfe tara da rabi aka kawo masu breakfast lokacin Fauzy nata shan bacci tun bayan data ci Abinci, sanin ba yunwa take ji ba yasa Aunty bata tashe ta ba su Gwaggo nata tambayarta aka ce masu bacci take, bayan sun gama zama sukai anan falo suna kallo kafin zuwa k'arfe sha biyu suka fara shirin Walima don ana gama sallar Azahar za'ayi Saboda masu tafiya don gobe Monday, sosae Fauzy tasha bacci don saida Aunty ta tasheta Saboda shirin Walima kaman zata yi kuka tace ita dama an k'yaleta tayi kwanciyarta a d'aki Aunty tace ai tasan hakan bazai yuwuwa ba ta dai daure da anyi angama ai shikenan. Zuwa bayan Azahar kowa ya shirya Amarya Fauzy ansha rantsattsiyar shadda da ta sha ubansun aiki wuyanta da hannunta duk diamond ne, ba tare da 6ata lokaci ba aka shiga gudanar da Walimar data samu halartar manyan mata k'awayen su Her Excellency kowacce ka gani hamshakiyar kanta ce tsadaddun sutturu kawai kake gani kowa tayi shiga mai sunan shiga ansha gwalalai abundai sai wanda ya gani suma su Aunty ba laifi sun yi shiga mai kyau daidai k'arfin su, sai la'asar aka gama an ci an sha an kuma ba Fauzy kyaututtuka, ana gama Walimar su Mom sukai shirin tafiya harda yan Ethiopia zasu tafi can Abuja tare suma su Gwaggo suka ce tunda dai an gama mi suke jira akace Aunty tayi ma Her Excellency magana, koda tayi mata cewa tayi a'a yamma tayi su bari sai gobe da safe za'a maida su, sosae Fauzy taji dad'i da har ta shiga damuwa da suka ce zasu tafi, Fatuu ma da zata bi su Mom Aunty Mareeya ta rok'eta ta tsaya sai in zasu tafi koda ta kira Haisam ta sanar mashi cewa yay ba komai Allah ya kaimu, bayan gama Walimar ne aka kawo masu sauran akwatunan lefen Fauzy set biyu suma guda goma an narka uban kaya su Aunty suna ta jinjina yawan akwatunan har guda ashirin, bayan sun natsu ne Fauzy tace ma Aunty ta d'aukar masu kaya cikin lefen tunda dama wanda aka fara kaiwa ba'a d'auki komai ba don kayan duk a d'inke suke Fatuu ma tace mata ta d'auki abunda take so tace mata a'a ta bar shi aikuwa Fauzy tace in dai bata d'auka ba to tasan zaman da zata yi da ita wato ita ta amshi nata sai itace zata k'i amsar nata Fatuu na dariya tace to ai abun ba gasa bane ko kuma ita duka yaushe akai sunan su twins ta samu kaya sosae, duk da haka matsa mata Fauzy tayi sai ta d'auka k'arshe dai sai Aunty Mareeya ce ta d'aukar mata wasu abubuwan. Da daddare bayan sun yi shirin kwanciya Aunty tace ma Fauzy ta tafi wurin mijinta ta kwa6e fuska tace bazata je ba su Fatuu nata dariya ganin abun ya zamar masu drama Yaya Fareeda k'asa ta kwanta kan Carpet ganin gadon bazai ishe su ba don ga su twins. Washe gari bayan sunyi breakfast suka hau shirin tafiya gaba d'aya Fauzy duk tayi sukuku da ita, Misalin k'arfe sha d'aya na safe duk suka fito don tafiya Fauzy nata k'walla suna ta bata hak'uri Hajiya Zainab data rako su tana murmushi tace ma Fauzy nan ma ai gida ne ko, sha tara ta Arziki akai masu harda kud'i aka babbasu ganin da gaske tafiya zasu yi yasa Fauzy yin kuka sosae har ta karya ma Aunty Mareeya zuciya itama saida tayi k'wallan, aure kenan mai raba Y'a da uwa mai kuma raba dan'uwa da dan'uwa dole Aunty Mareeya taji kewar Fauzy don sun saba sosae, tana ji tana gani suka tafi suka barta sai fatan Allah ya kiyaye hanya ya kai su lafiya. Bayan tafiyar su Aunty part d'in Hajiya Zainab aka tafi da Fauzy anan Sameer ya sameta tana zaune a parlor ita kad'ai tana kallo saidai hankalin ta ba'a kan tv d'in yake ba damuwar tafiyar su Aunty ce a ranta yaran gidan duk sun tafi Makaranta da Amal ta zauna suna d'an yin hira jefi jefi don basu saba ba daga baya ta tashi don itama shirin barin K'asar take ta koma Makaranta dama bikin ne yasa ta zo, yana sanye cikin sabuwar farar shadda sai baza k'amshi yake ya zauna a kujerar gefenta, a sanyaye ta gaishe shi ya amsa yanata kallonta ganin yanayinta yasa a hankali ya tambayi ko har yanzu jikin nata su tafi hospital ta d'an girgiza mashi kai yace to ya ya ganta haka kaman abu na damunta tace mashi ba komai, shiru yay yana mata wani kallon ta kauda idonta can ya mik'e tare da kama hannunta yace suje, marairaice mashi tayi tace Momy ce ta taho da ita nan ya za'ai su tafi yace to sai ta zauna ita kadai tace ai tasan zata dawo sai kuma ta sameta bata nan, ce mata yay zai kirata ya sanar mata shi ya tafi da ita tana niyyar k'ara magana ya d'an d'aure fuska yace bai son gardama dole tayi shiru yana ruk'e da ita suka nufi barin falon, bayan sun fito ne ganin bata iya tafiyar sosae yasa hannu ya d'auketa gabanta sai fad'uwa yake kar wani ya gansu ahaka cikin sa'a har suka isa part d'in nashi basu had'u da kowa ba, bayan sunje a bakin gado ya d'aurata shima ya zauna ya kai hannu ya kamo nata yace ta fad'i mashi Mike damunta in ba ciwon bane, k'walla ne suka ciko mata cikin karyayyar murya tace mashi ba wani abu bane kawai ta damu da tafiyar da su Auntyn ta sukai ne tana yin Maganar k'wallan suka zubo mata sharr, jawota yay jikinshi ya sa hannu yana shafa bayanta alamar rarrashi can ya kai bakin shi saitin kunnanta yace mata ba gashi tare da ita ba miyasa zata damu, lamo tayi tana ta shak'ar daddad'an k'amshin shi mai narkar da zuciya, sun d'an d'auki lokaci a haka kafin ya d'ago fuskar ta suka had'a ido nata sun d'an lumshe, tambayar ta yay jikin yana sauk'i ta d'aga mashi kai ya k'ara tambayarta ta zauna ruwan zafin yanzu tace mashi eh lokacin da tayi wanka da safe yace Ok bari a bari zuwa anjima sai ta k'ara a hankali tace to, bin juna sukai da kallo yanayin fuskar shi da d'an murmushi haka itama sun d'an d'auki lokaci haka jin bata iya jurewa yasa ta fad'a jikin shi tana d'an murmushi, kai bakin shi yay saitin kunnanta ya rad'a mata wata magana sai gashi ta d'ago da sauri tana kallon shi idanunta a d'an waje ya d'age mata gira, yamutsa fuska tayi idanunta sukai raurau alamar zata saka kuka kawai sai gani tay yay yar dariya har fararen hak'oran shi sun bayyana, maidota yay jikinshi ya rad'a mata he won't do it again until she've healed, murmushi ta shiga yi idanunta a rufe tana jin wani irin son shi na ratsa zuciyar ta.

Ana gama bikin Fauzy aka tsaida lokacin da za'a yi nasu Nameer da Aunty Laila nan da wata ukku lokacin sun gama duk wani abu daya danganci karatun su, Fatuu bata koma Katsina ba dama hada karatu ke zaunar da ita can yanzu kuma ta gama k'arshe ma Haisam yanke tafiya da ita Us yay ta shiga yin shiri, ta bangaren Amarya Fauzy ma itama barin K'asar zasu yi bayan bikin da sati d'aya don har anyi mata passport, ana saura kwana biyu su tafi ranar laraba suka zo Abuja zo kaga murna wurin Fatuu su Mom ma sun yi farinciki da zuwansu suka tarbi Fauzy hannu bibbiyu, bayan sun ke6e da Fatuu a part d'in su ne ta shiga yaba canzawar da tayi cikin d'an lokaci har tana fad'in lalle Sameer ya iya tarairaiya Fauzy dai sai dariya take itama tace ma Fatun ai itace za'a ce ta canza don gaba d'aya yanzu ta koma kalar hajiyoyi haka dai sukai ta hirar nishad'i tsakanin su, anan suka wuni sai k'arfe biyar na yamma suka tafi Fauzy harda ce ma Fatuu in taje Us d'in zata sa Sameer ya kawota wurinta. Ranar Friday Jirginsu ya tashi zuwa England sai fatan a sauka lafiya. Washe gari Asabar Haisam da Fatuu suka tafi Katsina don yin sallama dasu Gwaggo ta kuma d'aukko kayan da take son tafiya dasu, har gidan Aunty Mareeya taje dama tasa tayi mata tanadin kayan gyara ta amso suka yi bankwana haka gidansu Haulat ma taje sunyi bankwana harda abun Arzik'in da ta saba tayi mata, washe gari Lahadi wuraren Azahar suka komo Abuja ta ci gaba da yin shiri don gobe in Allah ya kaimu suma jirginsu zai tashi zuwa Us, da yamma bayan anyi La'asar suka tafi inda za'a mata k'unshi da gyaran kai, Washe gari da Safe sukai bankwana wad'anda ke a gidan sukai masu rakiya zuwa Airport Jidderh kaman zata yi kuka wai zata yi missing yaranta Abie da Grandpa kaman yadda suke ce masu Mom na dariya tace koda su basu tafi ba ai itama tafiyar zata yi Dubai ta barsu ko tunda a cikin satin zata tafi itama. Tuni jirginsu Fatuu ya d'aga sai Fatan a sauka lafiya Fanan na can tana shirya masu kyakkyawar tarba sai faman farinciki take yaranta su Twins zasu zo gareta.

Satin su Fauzy d'aya da zuwa lokacin tuni ta warke suna ta shan Amarci na gaske har yanzu ko ruwa bata ta6a dafawa ba bayan sunyi aure don anan d'in ma akwai mai aiki namiji da dama shi yake ma Sameer d'in Abinci da gyaran gida, koda tayi mashi magana kan ya sallame shi ta rink'a yi sai cewa yayi ba buk'atar sai tayi Abinci a marairaice ta nuna mashi ita dai tana son ta rink'a mashi girkin sai yace to ba yanzu ba, saidai ta ci ta sha ta ji da Sameer d'in, Washe gari ya kama Asabar ta kira Aunty lokacin bayan Azahar ne Sameer ya fita, Aunty na kwance tana bacci kiran ya shigo, saida ta kusa katsewa sannan ta farka ta duba tana ganin Fauzy ce ta saki murmushi tare da yin picking, bayan sun gaisa ta tambayi yadda suke ta bata amsa daga haka tay shiru, Aunty ta fahimci kaman akwae abunda take son fadi hakan yasa ta ce mata ya akai ne, ai kamar tana jira cikin murya kamar zata yi kuka tace "gaskiya Aunty wllh akwae Matsala" jin haka yasa Aunty Mareeya yunk'urin tashi zaune tana fad'in "Matsala kuma!, Allah ya rabamu da ita" bayan ta zauna sosae da alamun d'an tashin hankali tace mata wace matsala ce,

Shiru tay kaman bazata yi magana ba saida Aunty ta k'ara tambayarta tace bazata fad'i mata ba ko so take hankalinta ya tashi ne sannan tace "Aunty kwanaki ba cewa kikai in dai matsalata yace yana sona ba ke zaki sa shi ya rink'a fad'i man hakan kaman cin Abincin shi safe da rana da dare ba" da sauri Aunty tace "eh hakane, bai fad'i maki hakanne?" Da sauri tace "a'a yana yi amman fa....Ke ba wai kina nufin zai rink'a ce man hakan ba?" ta canza Maganar zuwa tambaya Auntyn tace mata eh mana haka take nufi,

"To nidai wllh ba ta yadda kika ce ba yake fad'i man Allah" da alamun rashin fahimta Aunty tace to taya yake fad'i mata, shiru tayi kaman bazata yi magana ba Aunty tace tana jinta taya yake fad'i mata, yar in ina ta shiga yi "n..ni Aunty bansan ya zance maki ba amman gaskiya abun yayi yawa wllh" yadda tayi Maganar kamar zata saka kuka lokaci guda Aunty ta gane mi take nufi ta shiga yin dariya jin haka yasa Fauzy ce mata yanzu dariya zata yi mata don Allah, tana yin dariyar tace mata "to Yar gidan Hajiya kece da wani abun dariya wllh, dama kawai sai ya zaune yay ta faman ce maki I love you Fauziyya kamar wani zautacce, yadda yake maki dama ta hakan nake nufi kuma wllh naji dad'i sosae k'ok'arina bai tashi a banza ba kenan kema farinciki ya kamata kiyi ba k'orafi ba" tura baki tayi tana yamutsa fuska tace to ai gaskiya abun yayi yawa bata iyawa, ta6e baki Aunty tay tana faffad'an murmushi tace "ba wani yawa, kowacce mace da kika gani da kalar mijinta haka kowa take hak'uri, bai kamata ace tun yanzu kin fara k'orafi ba yayi wuri da yawa yar gidan Aunty, kiyi hakuri a hankali zaki saba kada ki sare ko ki nuna gazawa ta wannan hanyar ake kama miji a hannu ni wllh baki ji dad'in da naji ba don hakan ya tabbatar da kwalliya ta biya kudin sabulu, ina son in ja hankalin ki dole sai kin jajirce in ba haka ba to kuwa zaki ja ma kan ki matsala ne tun ba'a je ko ina ba don yadda yanzu yasan takan abun to kuwa in baki wasa ba zai iya zarta halin shi da aka fad'i don haka kiyi hak'uri kada ki bari ki zama raguwa kawai ki dage da gyara kan ki kinji yar gidan Aunty Mareeya" kai Fauzyn ta d'aga kafin tace to don ta tsorata da Maganar Aunty da tace zai iya zarta ta6a matan da aka ce yana yi wanda shi kanshi k'ok'ari take ta saka shi ya daina kwata kwata duk da bata san ko har yanzu yana hakan ba, cigaba da kwatanta mata Aunty tay tana fad'in wannan dama ce a gareta da zata maido gaba d'aya hankalinshi a kanta Fauzyn nata fad'in to, bayan ta gama ne tace mata dama tana ta son tayi mata magana game da Motarta da suka dawo da ita nan tana ganin da aita ajiyeta mi zai hana a kai mata ita can Nasarawa in suka zo sai taci gaba da yin amfani da abunta Fauzyn tace to zata yi mashi magana kan hakan daga baya sukai sallama Aunty nata yar dariya. Sai bayan da akayi la'asar ya dawo gidan lokacin har tayi wanka ta canza kaya zuwa skinny jeans da yar top kanta tayi parking gashinta ba kallabi da yake da kanshi ya nuna mata irin kayan da yafi so tana sakawa kenan shiyasa ko da yaushe cikin k'ananun kaya take ko fita zasu yi da yake yana yawan fita da ita zaga gari a haka suke fita saidai in kaman zasu fita daga Mota ne ko siyan wani abu sai ta d'aura After dress, tana zaune a parlon su mai kyau mara hayaniya mai d'auke da lafiyayyun kujeru leathers ya shigo hannunshi ruk'e da wata yar jaka yana sanye da k'ananun kaya shima, juyawa tay ta kalle shi yana cire takalma a bakin kopa a wurin da aka tanada don yin hakan in mutum ya cire wanda ya shigo dasu sai ya saka wasu kaman slippers su kuma na shigowa cikin parlon ne, mik'ewa tay tana murmushi ta nufo shi tana zuwa daf da shi ya d'an wara mata hannuwa ta fad'a jikinshi ya rungumeta gaba dayansu sai sakin kamshi suke, d'ago kai tayi tace mashi welcome back ya d'aga mata kai fuskar shi da d'an murmushi yay sunkuyo yay pecking goshinta, nufo cikin parlon suka yi yana tallafe da ita suka nufi kujera 2 seater ya zauna tare da ita, k'ok'arin raba jikinsu ta shiga yi tana fad'in bari ta kawo mashi ruwa yak'i sakinta tare da girgiza mata kai alamar ba zai sha ba tana mashi wani kallo tace to bari ta kawo mashi lemu sai lokacin ya bud'e baki yace mata ta barshi bai jin k'ishi ya mik'a mata jakar hannun shi ta amsa tare da bud'ewa, tsadaddun kayan zak'i ne a ciki su biscuits, chocolate, Sweet da dai sauran su a ido kawai mutum ya gansu sai ya had'iyi miyau tun ma kafin yaci, d'agowa tay tana murmushi ta furta mashi "Thank you Honey, I really appreciate" wani kalar kallo yay mata tayi yar dariya don tasan dalilin kallon yace ba haka zata rink'a mashi godiya ba ita kuma kunya take ji, da k'yar ta kai bakinta tay pecking gefen fuskar shi ta d'ago tana murmushi shima shi yake yi, shiru ta d'an yi tana kallon shi slowly yace mata da wani abu ne ta d'aga mashi kai, Maganar Mota da Aunty tayi mata tay mashi, farko shiru ya d'an yi kafin ya tambayi Motar na gidansu ne tace mashi eh, ce mata yay ita Aunty d'in nata bata amfani da ita ne tace mashi eh tunda ai ba tata bace, hannu ya kai ya d'an shafi beard d'in shi tare da shigar da lip d'in shi na k'asa bayan ya sake shi yace mata ta kirata tace mata ta d'auka in tana so, waro ido tay tace yana nufin ta zama tata yace eh ita in suka koma Nigeria d'in zai siya mata wadda zata rink'a amfani da ita a can, wani irin farinciki ne ya lullubeta har fuskarta ta bayyana bata san lokacin da ta kai hannu ta tallabo fuskar shi ba tana washe baki ta furta "Thank you Honey, Allah ya kara Arzuki mai Amfani, I love you more than words can say" tana gama fad'in hakan ta kai bakinta saitin nashi ta manna mashi kiss tana d'agowa suka had'a ido kawai sai ta fad'a jikinshi tana dariya, shima yar dariyar yay don yanzu bai ma sanin yana yin ta, sosae yaji dad'in hakan da tayi mashi don bata cika yi mashi ba Saboda kunya saidai shi yayi mata da wuya ta fara mashi abu irin hakan, abunda bai sani ba shine tsoron ta tak'alo ma kanta take don yawanci daga hakan zancen yake sauyawa, kiran sunanta yay ta amsa ba tare data d'ago ba yace ta d'ago ta kalleshi, d'agowar tay tana murmushi ya bita da wani kallo can sai ji tayi ya mik'e da ita anan aka bar jakar tsarabar.

Bayan sallar isha ta kira Aunty Mareeya lokacin data sanar mata zancen an bata Motar salati ta saka tace "Fauzy badai nuna mashi kikai a bani ba?" Da sauri tace mata a'a wllh ta kwashe yadda sukai ta fad'i mata, wata shewar farinciki Aunty tay tace "Sai surukina mak'erin rocket wato da alama ya fahimci ba K'aramin k'ok'ari nayi mashi ba wurin gyare ki wannan ina jin tukuici ne aka bani" dariya Fauzy tayi, godiya ta shiga yi cike da Farinciki ta tambayi yana nan tace mata a'a yaje salla amman tasan bada dad'ewa ba zai dawo tace Shikenan in ya dawo zata kira tayi godiya amman kafin nan don Allah ta fara yi mashi godiyar yadda ya kamata Fauzy na murmushi cike da Kunya tace ai tayi wannan, yar shewa Aunty tayi tace yauwa ko ita fa haka yakamata itama ta kasance da zafinta ita dai Fauzyn murmushi kawae tayi, suna cikin yin wayar ya shigo Fauzy ta nufe shi tana zuwa gabanshi ya kai hannu ya rungumota jikinshi tace mata gashi ya dawo kafin ta kanga mashi wayar a kunne k'asa da murya tace Auntynta ce, sosae Aunty tayi mashi godiya ya nuna mata ba komai. Satin su Fauzy biyu anan suka tafi Honeymoon wasu kasashen, daga cikin k'asashen da zasu je akwae, France, Germany, italy sai US kaman yadda Fauzy ta bukaci su kai ma su Fatuu ziyara sai Saudia da zasu je suyi umra daganan zasu dawo England. Bayan zuwan su Haisam Us yaso su d'an zaga wasu k'asashen tare da Fatuu suma matsayin Honeymoon da basu je ba to saidai Saboda aikin shi don yan tsakankanin nan yaje Nigeria sosae hakan yasa ya yanke bari sai bayan bikin su Nameer sai ya d'auki hutu suje duk da haka ya zagaya da ita wurare sosae a nan inda yake wato California daga baya kuma suka je wasu states na K'asar cikin wanda suka je akwai, Texas, New York, Florida, Washington sai Massachusetts.

98

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

............Wata d'aya da rabi da zuwan Fatuu Us wata ranar Lahadi ta tashi da wani irin ciwon kai har da yar juwa take ji ranar dama Haisam a d'akinta yake su twins kuma na wurin Fanan dama haka suke yi in yana d'akin Fanan to a d'akin Fatuu zasu kwana haka in yana d'akin Fatuu to a wurin Fanan zasu kwana duk da suna da Nursery wato d'akin su wanda aka k'awata shi da abubuwan da suka danganci yara amman basu kwana a ciki, ganin yanayinta yasa yace mata su tafi Hospital amman sai tace mashi tana ganin basai sun je ba tunda ciwon ba wani tsanani yayi ba dama kuma lafiya lou ta kwanta tana ganin in tasha magani zata warke k'ilan harda gajiyar zirga zirgar da suka yi ne ya nuna gamsuwa da Maganar ta, ganin basu kaiga yin Breakfast ba yasa ta bari in taci Abinci sai tasha maganin dama suna dasu a first aid kit d'in su, Saboda yanayin da take ciki yasa bata samu zuwa Kitchen ba don had'a breakfast tare da mai aikin su wadda take baturiya, dama mafi yawancin lokutta tare suke aikin Fanan ma wani lokacin takan shiga saidai ba kowane lokaci ba Saboda aiki da take zuwa, a daddafe tayi wanka ta shirya cikin k'ananun kaya riga da skirt bayan an gama shirya masu table aka sanar dasu, gaba ɗayansu kowa yayi wanka suna sanye da k'ananun kaya lokacin da suka zauna zaman yin Breakfast d'in har su twins ma an masu gayu in ka gansu a lokacin sai kayi tunanin sunyi shekara ɗaya Koma sun fi don gaba d'aya sun yi wani irin girma sunyi 6ul6ul dasu ga bak'ar sumar su a nad'e gwanin burgewa haka idanuwansu farare tass dasu lips ɗinsu ma sun k'ara cizawa ta bangaren fata kuwa tamkar ka ta6a jini ya zubo har wani sheƙi take don mayukan fata masu tsadar gaske ake masu amfani dasu haka na gashin kan su ma, Bayan sun gaisa da juna Fanan ta kalli Little Grandpa dake hannunta da turanci tace mashi "Say Hello to Mom" kallon Fatuu yay ganin tana mashi murmushi yasa shima yay mata Fanan ta k'ara ce mashi yace mata hello ya d'aga hannu cikin Maganar shi da bata fita yace mata hello d'in itama Fatun ta d'ago mashi, kallon Abie dake hannun Haisam tayi tace mashi shima yace mata Hello ɗin yay shiru yanata kallonta ta sake maimaita mashi still baida niyyar cewa hakan yasa Fanan tace da alama shi kalar Dad d'in shi ne don tana lura bai cika yin magana ba kamar grandpa duk sukai murmushi ƙarshe saidai Haisam ya kamo hannun shi ya d'aga ma Fatun itama ta d'ago mashi sai lokacin Abie ɗin yay kaman zai yi murmushi, bayan sunyi bismilla a nutse suka fara cin Abincin baka jin komai sai k'arar cokulla Haisam na ci yana ba Abie haka Fanan ma tana ba grandpa sosae yaran suke ci, tun bayan da Fatuu ta fara ci taji kaman zuciyar ta na tashi haka dai ta daure tana cigaba, basu dad'e sosae da fara ci ba da sauri ta aje fork d'in hannunta ta dafe k'irji jin kaman amai na taho mata, Fanan ce ta fara lura ta kalleta tana tambayar ta lafiya hakan yasa Haisam kallonta shima yana niyyar yin Magana suka ga ta tashi da sauri ta nufi hanyar corridor da zai kai ta inda Bedrooms d'in su suke saidai ko kafin ta shiga corridor d'in Aman ya zubo nan ta duk'a ta shiga kwarara shi, har Kusan rigen mik'ewa ake tsakanin su suna rungume dasu twins suka nufeta, sannu gaba d'aya suka shiga yi mata Fanan ta dafata grandpa na ganin halin da Fatuu take ciki ya fashe da kuka ganin yana kuka yasa Abie shima ya saka kukan, kallon Haisam Fanan tayi da alamun damuwa akan fuskarta ta tambaye shi dama bata lafiya ne ya fad'i mata yadda sukai da ita da safen nan sam bata kawo komai a ranta ba tace mashi gaskiya yakamata su tafi Hospital a duba ta sosae da sauri yace Ok don shima halin da take cikin ya d'aga mashi hankali, saida ta gama sannan Fanan ta taimaka mata ta mik'e ta nufi hanyar Bedroom da ita don ta shirya su tafi Asibiti Haisam yabi bayan su yana ruk'e da su twins da ya rarrashesu sun daina yin kukan, ba tare da 6ata lokaci ba suka fito don tafiya Fanan tayi ma mai aikin su magana kan tazo ta gyara wurin aman kafin suka tafi, Haisam ne ke driving Fanan na front seat gefen shi tana ruƙe da su twins ita kuma Fatun an bar mata baya ita kad'ai ta zame jikinta ta kwantar da kanta, akai akai suke juyowa suna mata sannu da d'an murmushi take amsa masu tace ai taji ta samu sauk'i ma da tayi aman can tace ma Fanan ta kawo yaro d'aya ta rik'e mata harda tambayarta zata iya tace mata eh ta mik'a mata Abie, Asibitin da Fanan ke aiki suka nufa bayan sun isa ya parker Motar a inda aka tanada duk suka fito, basu wani tsaya Jira ba wurin ganin likita tunda dama nan ne asibitin da suke zuwa duk da Fatun wannan ne zuwanta na farko bayan tazo ƙasar, bayan Fanan tasa anyi mata duk wani abu da ake yi kafin ganin likita aka tura sunanta, tare gaba d'aya suka shiga wurin likitan wanda Bature ne yana ganin Fanan ya washe mata baki yana mata Welcome itama murmushi ta yi mashi ta amsa mashi ya maido idonshi kan Haisam suka gaisa haka Fatuu ma, mik'a ma Fanan hannu yay alamar ta bashi Adam dake hannunta ta mik'a mashi sai gashi bai mashi ƙyuya ba ya yarda dashi, nuna ma Haisam leather sofa dake gefe Yay alamar ya zauna itama Fatuu ya nuna mata ta gaban table d'in shi Fanan ma ta zauna akan wadda take facing ta Fatuu, Fanan ce tayi mashi bayanin abunda ke damun Fatun tace tana ganin ya kamata ai mata aune aune shiyasa suka zo ya furta Ok, maida kallon shi yay kan Fatuu yace mata sannu ta amsa kafin ya shiga yi mata tambayoyi, cikin tambayoyin ne ya tambayeta yaushe rabonta da period tace mashi bayan data haihu ya dawo tayi sau d'aya daga nan bai sake dawowa ba, tambayarta watannin su twins yay ta bashi amsa da shidda da rabi, bayan ya gama yi mata tambayoyin ne yace ma Fanan ya tura tests da za'a mata ta amsa da Ok tare da mik'ewa ta kai hannu ta kamo Fatuu tace suje, kallon Haisam tay tace mashi bari suje su dawo ya d'aga mata kai, ganin zasu fita yasa Adam dake kan cinyar Doctor fashewa da kuka yana Mik'o masu hannu, dakatawa sukai Fanan ta nuna mashi saitin Haisam tana fad'in "Look at Dad he's here" juyawa yay ya kalli saitin Haisam da take nuna mashi yana ta6e baki kamar zai cigaba da yin Kukan, juyawa sukai suka tafi bayan sunje lab ɗin ba 6ata lokaci aka d'ibi jinin Fatuu don yin gwaje gwajen, bayan an d'iba dawowa sukai Office ɗin likitan Fanan tace ma Fatuu ta zauna kan kujerar da Haisam yake ita kuma ta koma kan ta gaban table d'in Doctor suka shiga tattaunawa irin tasu ta likitoci, ba'a d'auki lokaci mai tsawo ba aka turo results d'in Doctor ya sanar dasu gashi an turo duk suka maida idanun su kanshi, duk awon da aka mata ya nuna lafiya lou sai guda d'aya na ciki da yake nuna akwai na tsawon sati shidda wato wata d'aya da rabi kenan tunda tazo K'asar ta same shi, tsananin mamaki ne ya bayyana akan fuskokin su ba kamar Fatuu don ita a tunaninta tunda bata period bazata samu ciki ba, da mamaki Fanan tace ma Doctor ɗin is he sure about what he said cike da tabbaci yace mata haka result d'in ya gwada tare da juyo mata da computer d'in don ta gani, bayan ta tabbatar da sakamakon d'agowa tay ta kalli Fatuu da tayi zuru tana kallon su kafin ta maida idonta kan Haisam da shima mamaki ya bayyana kan fuskar shi tace mashi yaji wai Zarah is pregnant ya jinjina mata kai, Doctor d'inne yace masu ana yin hakan su kwantar da hankalin su Haisam yay sigh kafin yace ma Doctor ɗin gaskiya yayi wuri da yawa ace tana da ciki at least jikinta na buk'atar Hutu sosae tunda bata dad'e da haihuwa ba gashi kuma twins, jinjina kai Doctor din yay yace hakane yanzu ya za'ayi shiru Haisam ya d'an yi yana kallon Floor da alama yana nazarin wani abu ne can ya d'ago ya kalli Doctor ɗin yace ya yake gani in a fitar dashi, nuna mashi yay akwae risk sosae fitar da ciki amman kaman nata da yake k'arami sosae ba'a ciki samun matsala ba Magani kawai za'a bata in akai sa'a zai fita ba tare da wata matsala ba in sun amince, jinjina kai Haisam yay kafin yace a bata maganin a tare Fatuu da Fanan suka kalle shi da sauri kowa da yanayin mamakin jin Maganar, da alamun damuwa Fatuu tace "A...amma Hubby kai da kan ka zaka ce a zubar da shi bacin kasan ba kyau hakan laifi ne" shiru Fanan tayi yanayin fuskarta ya sauya kaman zatai kuka a yadda take ji inama ace cikin a jikinta yake don sai taji bata son a zubar dashi ji take kamar ta rok'e su kada a zubar dashi amman tana gudun aga ta zaƙe, shima Haisam da alamun damuwa ya shiga kwatanta mata duka yaushe ta haihu gashi tasha wuya dole jikinta na buk'atar Hutu kafin ace ta sake wahalar wani cikin ga wahalar rainon su twins suma tunda ba yaye su tayi ba, haka ya dingi kwatanta mata matsalolin yace tunda k'arami ne kuma zata iya cutuwa haka su twins ma ba laifi bane in an cire, shiru tay tana d'an tunani ita kanta bata ji tana son cikin ba amman kuma sai taji bata goyon bayan a zubar dashi, gaba ɗaya idanunsu na akan Fatuu da tayi shiru ta kasa cewa komai ganin haka yasa Doctor ce masu ko suje gida suyi shawara in still suna son a fitar dashi ko Dr Fanan zata iya d'aura su kan hakan, yana yin Maganar da sauri Fanan ta kalle shi zuciyarta ta shiga harbawa don bata jin da hannunta zata taimaka ayi abortion ga wata ma balle kuma wannan, Haisam ne yace ma Doctor ɗin a bata maganin kawai ya furta Ok yana k'ok'arin tashi a ruɗe Fatuu ta kalli Haisam tare da girgiza mashi kai tace "a'a Hubby a barshi kawai kar a cire ana iya zuwa kuma a samu matsala tunda Allah ya bamu kawai mu barshi muyi fatan ya zama Alkhairi kada mu cire kuma muzo daga baya muna so Allah yak'i bamu wasu ma da yawa suna nema basu samu ba" yanayin yadda ta k'are Maganar kamar zata yi kuka, shiru Haisam d'in yay idon shi akanta wani irin tausayinta yake ji na ratsa shi dama dalilin tausayin nata yasa yace a cire ba wai don bai son cikin ba, Maganar k'arshe da Fatuu tay ita ta ƙara karya ma Fanan zuciya har bata san idanunta sun ciko da kwalla ba saidai ji tayi sun zubo da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa, duk yadda taso kar tayi kuka abun yaci tura, jin sheshshekarta a hankali yasa su kallonta da sauri ganin yanayinta yasa Fatuu kiran sunanta ta amsa cikin Muryar kuka ba tare da ta d'ago ba aikuwa zumbur ta mik'e ta nufeta, a gabanta ta tsaya tasa hannu tana k'ok'arin d'ago da fuskar ta, bin fuskar Fanan da tayi sharkaf da hawaye tay da d'an rud'ewa ta hau tambayar "Aunty Fanan what happened? Miya sa kike kuka don Allah?" Girgiza mata kai tayi kafin cikin kuka tace mata ba komai, shiru Fatuu tay tana yamutsa fuska itama kamar zata yi kuka ta shiga tunanin miya sa Fanan d'in kuka lokaci guda zuciyarta ta tariyo mata da Maganar da tayi, waro ido Fatuu tay tare da ɗan buɗa baki da sauri ta shiga faɗin "Aunty Fanan wllh ba dake nike ba da nayi Maganar kawai na bashi misali ne ban san abun zai ta6a maki zuciya ba don Allah kiyi haƙuri" idanunta har sun ciko da ƙwalla, girgiza mata kai tayi tace "No Zarah, baki man laifi ba ai abunda kika faɗa gaskiya ne kuma ni ai nasan ba dani kike ba Saboda ni inada yara ko?" Da sauri Fatuu ta jinjina mata kai tare da kai hannu ta fara goge mata ƙwallan Fanan ɗin na ɗan murmushi, bayan ta gama goge mata hawayen ta tambayeta itama bata son a fitar da cikin ko farko shiru Fanan ɗin tayi kafin ta ɗan jinjina mata kai alamar eh, juyawa tayi ta kalli Haisam cikin harshen turanci tace mashi Auny Fanan ma bata so don haka koda ita bata son cikin to zata haƙura ta haife shi, murmushi yay tare da ɗan lumshe ido haka ma likitan don yanzu ya fahimci komai da bai gane abunda ke faruwa ba saboda da Hausa suke Maganar sai jefi jefi suke saka turanci, kama hannunta Fanan tay ta d'an girgiza mata kai tace duk da bata ta6a haihuwa ba tasan tun daga rainon ciki akwae wahala in dai itama taji tana son a cire d'in kada Saboda ita ta canza ra'ayi Fatun tace a'a da gaske bata son a cire har cikin ranta ta amince a bar mata suyi mata Addu'a Allah yasa kada ta sha wahala kuma ta haife shi lafiya Fanan na murmushi tace in sha Allah daga yanzu ta fara mata Addu'a kan hakan har zuwa ta haihu ta kalli Haisam dake kallon su fuskarshi a sake tace daga yanzu su fara mata Addu'a ya jinjina kai, tattaunawa Fanan ta shiga yi da Doctor kan maganin daya kamata a bata wanda zai sa ta daina amai ta rinka cin Abinci haka su twins ma suma za'a basu wanda zai k'ara inganta lafiyar su Haisam ya tambayi yanzu zata iya cigaba da breastfeeding nasu doctor din yace k'warae ba wani abu taci gaba da basu koda har zuwa ta haihu ne kuma a rinƙa basu maganin da zai basu yay mashi godiya.

Bayan sun baro Asibitin tun akan hanya Fanan ta shiga kiran yan Nigeria su Hajiya da Mom ta sanar masu harda Gwaggo ma kowa yay mamakin jin samun cikin daga baya duk sukai Addu'oin Allah ya inganta ya raba lafiya. Sosae Fanan ke kulawa da Fatuu bayan da suka san da cikin haka su twins ma in dae tana gida bata je aiki ba ita ke duk wata ɗawainiya dasu dama tana kulawa dasu sosae yanzu sai ta k'ara don komai ita ke masu kama daga yin wanka shirya su basu Abinci yi masu wasa da sauransu haka Haisam ma in yana a gidan tare dashi ake masu komai koda Fatuu tayi yunƙurin yi masu wani abu sai suce ta bashshi ta huta duk da jikin nata da Sauk'i sosae iyakar ta shayar dasu sai kuma in suna zaune tare dasu ta d'auke su har tayi masu wasa, k'arshe ma Haisam cewa yay yakamata a samo masu nanny Saboda in basu nan ba sai ta rink'a wahalar kulawa dasu ba amma sai ta nuna mashi ba sai an samo ba tunda ba wani ciwo take ba zata iya wannan amman ya nuna ta bari dai a samo ganin hakan yake so yasa ta amince amman tace to ya bari tunda sun kusa tafiya biki in suka dawo sai a samu ya amince da hakan.

A kwana a tashi ba wuya a wurin Ubangiji, bikin su Nameer nata matsowa har ya rage saura sati ukku lokacin watan Fatuu biyu da sati guda a Us, a yadda sukai da Haisam in ya rage saura Sati biyu zata tafi shi kuma sai ana saura sati d'aya zasu taho shi da Fanan, gudunmawar miliyan biyu ya bata yace in basu isa ba tayi mashi magana cike da nuna farinciki ta nuna mashi sun isa har ma sun yi yawa, a yadda sukai da gwaggo bayan ta kirata kan Maganar kayan ɗaki ce mata tayi tana ganin kawai za'a siya mata ne ready made har ma tayi ma Aunty Mareeya magana kan hakan tace in an tashi siya akwae inda zata kai su suna da kaya masu kyau wanda za'a siya ma Minon, Fatuu taji dad'in jin hakan gaba d'aya gudunmawar da Haisam ya bata ta tura ma gwaggo tace saura tata in tazo Gwaggon tace wannan uban kuɗi haka da ɗanta ya bada anya basu yi yawa ba Fatuu na yar dariya tace mata a haka ma cewa yay in basu isa ba tayi magana ya ƙara da sauri gwaggo tace don Allah kada ta ƙara tambayar shi ko Naira wannan ai Kusan ma shi zai mata kayan ɗakin, tambayarta Fatuu tayi kamar ya za'a mata kayan gwaggo tace wai da ita a tunaninta ayi mata saitin gado da kujeru masu kyau wanda da an gani ansan masu kud'i ne tunda Baffan su ma sunyi Magana kan kayan ɗakin ta nuna mashi ya turo kuɗi kawai a siya sai duk a haɗa a siya mata, cewa Fatuu tay gaskiya kamata yay ayi mata komai set biyu kujerun da gadon don tasan gidan da za'a kaita babba ne alabashshi ko sai a siya set ɗaya masu kuɗi sosae sai ɗayan koda wanda basu kai su kuɗi ba Gwaggon tace to hakan ma bari in aka harhaɗa kuɗin sai aga kaman ya za'a siya mata don itama tana son a yi mata kaya sosae tunda ita ba'a yi mata komai ba Fatun tace komai kenan sai tazo sai suje a siya in sha Allah ba abunda zai gagara bane, itama Gwaggon tace in sha Allah nan take faɗi mata Hajiya tayi mata magana kan inda za'a ɗaura aure sun roƙi alfarmar in ba takura a ɗaura a nan Katsina sai a haɗa da na Laila a ɗaura gaba ɗaya anan sai a tura Mota can Adamawa ta ɗaukko masu zuwa ɗaurin auren nan don in akace ayi acan sannan ayi na Laila a Abuja za'a takura mutane don zirga zirgar zata yi yawa to ta kira Baffansu kan hakan shima yayi magana da yan'uwanshi duk sun amince da hakan shi Arɗo ma ance ba lalle yazo ba don bai jin daɗi Fatuu ta tambayi abunda ke damun shi tace mata kawai harda tsufa wai jikin nashi ne bai jin daɗin shi, fatan Allah ya bashi lafiya Fatuu tayi kafin suyi sallama Gwaggo ta tambayi ina Y'ay'anta Fatun tace gasu can wurin Aunty Fanan wai tafiya take koya masu, yar dariya gwaggo tayi tace da wuri haka Fatun tace eh wai daga taga sun fara tsayuwa shine ta fara koya masu Gwaggo na dariya tace ina ruwan ɗiyarta tana dai kula da yaran sosae Fatun tace sosae don yanzu har aiki take tafiya dasu ta bada su wurin raino a can har makaranta aka so saka su amman ta hana wai ai a wurin rainon ana koya masu abunda ake koyawa a Makarantar, da alamun mamaki gwaggo tace "wace irin Makaranta kuma yaran da basu wuce wata bakwae ba" yar dariya Fatuu tayi tace mata su nan haka suke yi kamar wurin raino ne to sai a rinƙa nuna masu abubuwa don su taso sun sani gwaggon tace ta gane aikuwa bari itama tazo ta koma Makaranta ko ta ƙara sanin abubuwa kada suzo su ƙureta harda ma turanci zata koyo, Fatuu nata Dariya itama gwaggon Dariyar take daga baya ta tambayeta ya jikin nata ta bata amsa da Alhamdulillah tace badai ta laulayi sosae ko Fatun tace mata eh ai maganin da take sha kullum yana hana ta yin amai ko tashin zuciya lafiya lau take cin Abinci saidai wani lokacin tana jin kasala taita kwanciya sai kuma ciwon kai da take yi wani lokacin shima, Addu'ar Allah ya inganta ya sauketa lafiya gwaggon tayi Fatuu na murmushi tace "Amin ya rabbi, Allah ya amsa gwaggota mahaifiyata, ina tsananin son ki da dukkan zuciyata" wani irin murmushin daɗi gwaggo tayi itama tace "nima ina ƙaunar ki autata Fateema, ina roƙon Allah ya ƙara ma rayuwar ki albarka data zuriyar ki ya jiƙan Mahaifiyar ki" wani irin lumshe ido Fatuu tayi nan da nan idanunta suka ciko da kwalla don a lokacin nan koda yaushe Mahaifiyarta na a ranta sosae take jin maraicinta tana jin inama ace tana raye rayuwarta tayi albarka haka, jin tayi shiru yasa gwaggo kiran sunanta ta amsa a hankali tana jin yanayin muryar tata ta gane kuka take, itama zuciyarta karyewa tayi abubuwa suka fara mata yawo a rai tay ƙarfin halin ce ma Fatuu ta daina Kuka tayi mata Addu'a in sha Allahu ta dace a sanyaye ta amsa da Allah yasa, kafin suyi sallama gwaggon tace in kusa Fanan take ta bata su gaisa tace to, bayan ta kai ma ta a Nursery ta sanar mata ga gwaggo zasu gaisa cike da nuna jin daɗi ta amsa cikin washe baki suka gaisa gwaggo tace ai an faɗi mata tana nan tana ta aikin koya tafiya Fanan d'in tay dariya tace eh so take su iya kafin su zo biki yadda in suka zo zasu je ko ina da ƙafafun su gwaggon tace lallai kam akwae aiki yanzu nan da sati guda kenan take son su iya tafiyar tana ta dariya tace eh itama gwaggon dariyar take tace to Allah ya taimaka ya bada sa'a ta amsa da Amin kafin suyi sallama harda kara ma Adam wayar wai yace mata Hello sai gashi yace ɗin cike da jin daɗi gwaggon ta shiga yi mashi magana da hausa tana tambayar yadda suke shida ɗan'uwan shi yay zuru yana zaro ido Fanan da Fatuu sai yar dariya suke ganin yadda yay ganin sunata dariya yasa shima yin dariyar gefen kumatun shi duk suka lotsa Madarar kyau abun sai dai ace tubarkalla, amsar wayar Fanan tay gwaggo tace ko basu yi masu magana da Hausa ne tace a'a suna yi masu Momynsu ma harda Fulatanci tana masu magana haka Dad d'in su ma yana masu larabci zasu taso suna jin yare hudu Gwaggo tace Masha Allah Allah yay masu albarka da sauri ta amsa da Amin da zasu yi sallama Fanan ɗin harda cewa "We love you so much granny" gwaggo na murmushi da hausa tace "nima ina son ku Y'ayana, Allah ya ƙara ma rayuwar ku albarka ya ƙara haɗa kan ku ya kauda idon maƙiya da mahassada ya kare ku daga dukkan sharri" cike da jin daɗi Fanan ta amsa harda lumshe ido daga baya ta ba Fatuu wayar don suyi sallama.

Shirye shiryen biki nata kankama a dukkan 6angarorin angwaye da amaren, Bayan sati guda Fatuu ta taho da wata babbar Mata da zata zo Kano harda iyalinta Haisam ya haɗasu don su taimaka mata da su twins dama damuwar shi kenan yadda zata yi dasu shiyasa ma bata wani kwaso kaya ba iya ɗan babban trolley ne da yar jaka sauran sai zasu zo su taho mata dasu, bayan sun iso Kano Matar tace mata in ba jirgin da zai je Katsina yanzu sai su tafi gidanta kafin lokacin tafiyar yayi Fatuu na murmushi tace mata ai da Haisam ya siya mata ticket online akwae wanda zai tashi bada daɗewa ba yaran Matar suka shiga faɗin wayyo ba haka suka so ba sun so su bisu gidansu don basu gaji da ganin su twins ba ita dai Fatuu murmushi kawai take, itama Matar da wani matashin mutum da zai tafi Katsina ta haɗa su don ya taimaka mata shima a first class zai zauna inda Fatun zata zauna, lokacin Haisam ya kira don yaji in sun sauka Fatuu taba Matar waya sukai magana sosae yayi mata godiya tana ta fara'a irin tasu ta manyan Hajiyoyi tace ai ba komai duk yima kaine tana fatan wata rana in yazo ƙasar zai kawo mata su yace in sha Allah daga baya ta sanar dashi itama ta damƙa su a hannun wani da zasu zauna tare don ta bincika bata samu mace da zata zauna anan ba yace to ba komai ya ƙara mata Godiya kafin sukai sallama, Wuraren karfe sha biyu na rana suka sauka Katsina, cike da Farinciki su Gwaggo da kawu Amadu da Amarya Mino sai Tk daya kai su suka tarbe ta basu zo da Kamalu ba shi Kawu Amadu ya baro ma shago, kowa yay mamakin ganin yadda Fatuu ta canza har sun kasa rufe bakunansu gaba ɗaya hutu ya zauna mata sosae tayi 6ul6ul da ita ga skin ɗinta ta ƙara mulkewa ta ƙara haske in tayi dariya abun gwanin burgewa ga cikinta har ya ɗan fito, su Twins kam abun ba'a magana su wannan tun a jirgi aketa santin su, sai so suke su ɗauke su amman sun ƙi yarda dama Adam ne me ɗan yarda a ɗauke shi shima sai yaga Fatun na a kusa, da ƙyar ya yarda Mino ta ɗauke shi daga wurin mutumin da ya ruƙe shi a jirgi sai faman ta6e baki yake zai yi kuka Fatuu ta shiga rarrashinshi da turanci tana ce mashi itama Minon Mom ɗin shi ce, shi dai Abie na liƙe da ita da alama ma tsoronsu yake don har fuskar shi ta nuna ya waro ido tubarkalla sai bin su da kallo yake, Sosae su gwaggo sukai ma mutumin godiya yana murmushi ya nuna masu ba komai kafin sukai sallama ya tafi, bayan sun fito wurin da aka parker Motar su ukku suka shiga baya kawu Amadu ne yanzu zai tuƙa Motar don ya iya bayan tafiyar Fatuun Tk ya koya mashi da Motar tata tare da amincewarta, yana fara driving Fatuu ta shiga yaba mashi ganin har ya iya Tk dake gefen shi yace ai yanzu ba inda bai zuwa da mota, bayan sun bar Airport ɗin suna ta hira Fatuu ke tambayar Hajiya Tk na murmushi yace tana nan lafiya tana can tana jiran isowar su, lokacin da suka iso ƙopar gidansu tsayawa Fatuu tasa akai don ta gaisa da Yayanta Kamalu yana ganinta ya hau washe baki yace bari ya rufe shago yazo su ƙarasa gidan tare, a gaban Motar Tk ya matsa mashi suka tafi suna isa gate su officer suka taso suna masu sannu da zuwa daga baya aka buɗe masu gate suka shige, a gaban entrance ya parker Motar duk suka firfito lokacin Saude ta fito cikin washe baki ta nufo Fatuu itama tana ganinta ta fara mata murmushi tana zuwa ta ɗan rungumota tana mata sannu da zuwa aikuwa Abie na ganin haka ya fashe da kuka da sauri Aunty Saude ta saketa tana faɗin ashe ba'a ta6ata ta shiga ba shi haƙuri tana faɗin ai ta saketa to yay shiru ai kamar ma tana ƙara tunzura shi sai kukan yake ƙara yi ganin haka yasa Sauden cewa to ko dai tsoron baƙaƙen Mutane yake Gwaggo tace taga alama don tun ɗazu duk ya bi ya ƙanƙame Uwar tashi, ganin Abie ɗin na kuka yasa Adam shima fashewa da kukan dama ƙiris yake jira Mino ta matso dashi wurin Fatun don ta rarrashe shi, Hajiya ce ta fito tana dogara sandarta ta alfarma idanunta sanye cikin glasses ta nufo su tana faɗin ita dai tayi gajen haƙuri ta fito, ganin su twins na kuka yasa ta tambayi mi ya faru duk suke kuka Saude ta faɗi mata ta jinjina kai tana dariya tace aikuwa aiki ya same su in dai tsoron baƙaƙen mutane suke tunda ƙasar su suka zo duk akai dariya, gaishe da ita Fatuu tay ta amsa tana ta fara'a tay mata sannu da zuwa kafin tace to a shigo ciki a zauna yadda za'a gaisa sosae suka ce so ta kalli su twins da suka bita da ido tace masu barkansu da zuwa ƙasar baƙaƙen fata, tambayar ina mai gidan nata yake tay Fatuu ta nuna mata shi a hannun Mino tace wato ita kenan don tana fara ya yarda da ita duk sukai dariya, cikin gidan duk suka nufa a parlor aka zazzauna ana ƙara gaisawa da ƙara yi masu sannu da zuwa Hajiya ta tambayi Fatuu jikinta tana ta murmushi tace Alhamdulillah tay fatan Allah ƙara ingantawa ya sauketa lafiya ta amsa tare da su Saude, sake tambayar ya ta baro su Haisam Hajiyar tay tace lafiya lou duk suna gaishe su suna nan zuwa, Saude nata kallon Fatuu don komai tayi burgeta take can ta kasa haƙuri tace mata har ta canza sosae Hajiya tace ai dole yanayin ƙasa ba ɗaya ba, Maganar Abinci Hajiya tayi ma Fatuu tace gashi can an shirya akan table in kuma a kawo nan to tace eh a kawo nan cikin parlor Saude ta amsa da to ta miƙe, sallama gwaggo tayi masu Hajiya tace ta tsaya sai sun ci Abinci sannan, lafiyayyun Abinci da abun sha aka jere akan carpet duk Saude tay serving nasu abun yay kamar yar Walima har gwaggo na faɗin to kada kuma su cinye ma baƙi abinci Hajiya tace ai dama harda yan tarbar baƙin aka yi, a nutse suka fara cin abincin harda Hajiya a kan c-table aka ɗaura mata bayan ta fara ci tace ma Mino ta kawo mata Adam, kuka ya saka bayan ta kawo mata shi yana miƙa hannu alamar Mino ta ɗauke shi Hajiya ta shiga rarrashin shi tana faɗin "Haba mai gida yada tsoron Mata inata farincikin tarbarka sai kuma kaƙi yarda dani" su Gwaggo nata murmushi Hajiya ta kalli Fatuu tace "to wai ma yana fahimtata ko sai anyi turanci" amsa ta bata da eh suna gane hausa amma sun fi fahimta in akayi turanci, komawa Hajiya tayi tana rarrashin shi da turanci har ya fara yin shiru manyan idanun shi a kanta yana ta6e baki ita kuma tana ta faɗin yayi shiru shagwa6a66an maigida, lokacin da suka gama cin Abincin an kira Azahar Kawu Amadu da Tk suka tafi Masallaci gwaggo ma tayi ma Hajiya sallama su Fatuu da Mino suma suka fito don tafiya part ɗin su wanda tuni Saude ta gyara mata shi, bayan sallar la'asar lokacin Fatuu tayi wanka ta canza kaya haka su twins ma an yi masu wanka an canza masu kaya iri ɗaya suka tafi gidan Gwaggo, a can gidan ma anyi masu abincin tarbar su Fatuu tace sai anjima sai suci tunda yanzu basu jin yunwa suka shiga tattaunawa game da shirye shiryen bikin Minon nan Gwaggo ke sanar mata Abbas ya bata gudunmawar dubu ɗari biyu Fatuu taji daɗi tay godiya da Allah ya saka da Alkhairi, anan Haulat tazo ta iske Fatuu tsaf tsaf da ita tana sanye cikin doguwar rigar material mai kyau tayi rolling veil in ka ganta baka ta6a cewa ta ta6a aure tana ruƙe da hannun ɗiyarta lokacin data zo itama tsaf da ita an sa mata kaya masu kyau haka kanta ba laifi tana da gashi ma sha Allah, gaba ɗaya sunyi farincikin ganin juna Fatuu tace ai da tana niyyar zuwa gidansu bayan Magrib shiyasa bata kirata ba ta tambayi ya akai tasan ta dawo tace mata kawu Amadu ne ya kirata ya sanar mata, nan suka shiga yin hira itama saida ta tanka kan yadda Fatun ta canza tana dariya tace ai itama ta canza taji daɗin ganinta haka don da alama ta kwantar da hankalinta Haulat ɗin tace mata eh, duk yadda Haulat taso ta ɗauki su twins sun ƙi yarda kuma sun ƙi bari Fatuu itama ta ɗauki ɗiyar Haulat ɗin da tayi yunƙurin ɗaukarta sai su fashe da kuka abun ma sai ya zama abun dariya, tana nan har aka yi sallar Magrib bayan an gama ta tafi.

Washegari bayan sun gama yin breakfast ita da Mino ta shirya suka tafi gidan gwaggo don anjima zasu tafi siyayyar kayan ɗakin Mino kamar yadda suka tsara jiya da gwaggon da har tace ta bari sai gobe lokacin ta ƙara huta gajiya Fatun tace a'a gara su tafi ayi komai a gama don bikin nata matsowa, bayan sallar azahar Aunty mareeya ta iso dama ita suke jira ruƙe da babban kwali Kawu Amadu da Kamalu sun kamo mata suka shigo, a falo suka zauna aka shiga gaisawa ta ƙara yi ma Fatuu sannu da zuwa dama jiya tayi mata a waya, sai gashi ita lafiya lou su twins sun yarda da ita ta ɗauke su harda Abie su gwaggo sukai ta mamaki Aunty Mareeyar na dariya tace ai ita dama da wuya yara suyi mata ƙyuya Mino tace kuma dama itama fara ce ƙilan shiyasa suka yarda da ita da mamaki Aunty mareeya ta waro ido tace tsoron baƙaƙe suke ne aka ce mata eh aikuwa ta ƙyalƙyace da dariya tace bata ga laifin su ba wake son baƙi duk akai dariya, bayan an gama gaishe gaishen Gwaggo tasa Mino ta zubo mata abinci da sauri ta dakatar da ita tace wllh a ƙoshe take don daga kan abinci ta taso Fatuu tace to ai dai ko lemu tasha tace to a bata, bayan ta gama sha ne ta buɗe jakar ta ta fiddo kuɗi bandir biyar, miƙewa tay ta matsa daga gefen gwaggo ta aje bayan ta dawo ta zauna tace gashi nan gudunmawarta ce ita da Fauzy ga kuma wasu kayan Kitchen nan a haɗa ayi mata amfani dasu, gaba ɗayan su waro ido sukai suna kallonta da tsananin mamaki gwaggo ta kama baki kafin tace "Ƴata wannan gudunmawa haka ai tayi yawa gaskiya" tana dariya tace a'a ba wani yawan da tayi in so samu ne ma ai tafi haka tunda duk hidimarsu ce, Fatuu na niyyar yin magana Aunty Mareeyar ta dakatar da ita harda zare mata ido duk ta basu dariya, godiya sosae Gwaggo ta shiga yi mata tana addu'ar Allah ya bar zumunci haka Fatuu ma, tambayar yanayin yadda za'a siya kayan ɗakin Aunty Mareeya tayi Fatuu ta faɗi mata kowanne set biyu tace hakan yayi amman fa za'a sha kuɗi gaskiya don kaya yanzu sai Addu'a ko dai a siya set ɗin kujeru ɗaya masu kyau sai ayi gado biyu gwaggo tace ita da cewa tayi ma a yi kowanne seti ɗaya Auntyn tace a'a ayi dai gadon biyu sai kujeru ɗaya sai sauran kayan Kitchen da electronics suma nan ba ƙaramin kuɗi za'a kashe ba ga kuma labulaye, tambayar Fatuu tayi tasan yanayin gidan da za'a kaita ne don asan yawan labulayen da za'a siya tace a'a gaskiya Aunty tace yakamata kuma a sani ko akwae wanda zata iya tambaya, shiru ta ɗan yi kafin tace gashi Jidderh bata nan itace zata iya tambaya lafiya lau Aunty Mareeya tace ko ta kira Laila sai ta nuna mata labulaye ne ake son yi ai ba wani abu bane tace to, bayan ta kira Laila ɗin sun gaisa tayi ma Fatun an zo lafiya ta amsa itama tayi mata ya shirye shiryen hidima Laila tace Alhamdulillah Fatuu tay fatan Allah ya nuna masu ta amsa da Amin, tambayarta tay kamar yadda Aunty Mareeya tace Laila ta bata amsa da gidan bene ne ta fasalta mata yadda tsarin gidan yake Fatuu tayi mata godiya har zasu yi sallama Laila ta dakatar da ita tace amman fa saman benen Nameer yasa mashi kaya kar suce zasu yi kaya harda nan kuma duka gidan ma an sa labulayen ƙasa da sama sai dai kawai in zasu ƙara mata ne Fatun na murmushin jin daɗi tace to tare da yin godiya, bayan sun gama yin wayar tayi ma su Gwaggo bayani gaba ɗaya suka washe bakin farinciki Aunty Mareeya tace yauwa sunga kujeru set ɗayan sun isa tace a bata takarda da biro suyi list ɗin abubuwan da za'a siyo yadda da sun je ba tare da 6ata lokaci ba su fara yin siyayyar Fatuu ta ƙwala ma Mino kira tace ta taho da paper da biro, tare suka shiga faɗin abubuwan da za'a siya tana rubutawa, bayan ta gama suka miƙe don tafiya dama Motar Fatuu na a ƙofar gida, su ukku suka fito Aunty Mareeya na ruƙe da Adam Fatuu kuma Abie aka bar Mino a gidan, bayan sun fito ne cike da farinciki gwaggo ta sanar ma Kawu Amadu gudunmawar su Aunty Mareeya shima sosae yaji daɗi yana ta faffaɗan murmushi ya shiga yi mata godiya tana faɗin haba ba komai ai an zama ɗaya. Lokacin da suka isa wurin siyayyar babban bene ne hawa ukku gaba ɗaya manyan show rooms ne a ciki shaƙe da ƙawatattun furniture da rantsattsun kayan adon gida na gani na faɗa, cikin haba haba mai wurin wadda babbar Hajiya ce da yaranta suka tarbe su tana ta washe masu baki harda yunƙurin ɗaukar su twins suka ƙi yarda, bayan sun gama gaisawa suka yi mata bayanin kaya suke so tace gasu nan sun zo gidan kaya masu kyau da Quality ta shiga nuna masu suna jinjina kai da yabawa don ba ƙarya akwae kaya a wurin Aunty Mareeya tace ai tasan suna da kaya masu kyau shiyasa tayo masu jagora Hajiyar ta shiga yi mata godiya, ba 6ata lokaci suka shiga za6a ba tare da wani yin ruwan ido ba don kowane kaya haɗaɗaɗun kan su ne, kamar yadda suka tsara gado biyu suka za6a sai set ɗin kujeru da labulaye harda Carpet da wasu kayan ƙawata falo da ɗaki harda kitchen da kuma wasu kayan Kitchen amman banda electronics don Fatuu tace su bari suje EE inda Haisam ke zuwa gym su siya acan don suna da sauƙin kaya, kaya masu sunan kaya suka zazza6a saidai an kashe kuɗi ba kaɗan ba, bayan sun gama siyayyar suka ce ma matar ba yanzu zasu tafi dasu ba in ba matsala a cikin satin nan da za'a shiga za'a zo a ɗauka da sauri tace lafiya lou ba damuwa da ta basu receipts shikenan za'a ware masu kayan yanzu, bayan sun biya ta basu shaidar siyayyar harda ba Aunty Mareeya tukuici tana dariyar jin daɗi tayi mata godiya itama tayi masu godiyar harda cewa tana fatan suma zasu kawo mata customers suka ce in sha Allah tunda ta duba masu, bayan sun bar nan wurin siyan electronics suka wuce nan ma suka siya kayan kallo da fridge, Electric cooker harda injin wanki da sauran su, saida suka siya komai da suke buƙata sai abunda ya rage wanda sai sunje kasuwa zasu siya harda kayan gara dana abincin da za'a ci da biki, a gida suka sauke Aunty Mareeya suna ta mata godiya tana faɗin haba ba komai ta tambayi lokacin da zasu je Kasuwar Gwaggo tace ita ta fidda lokacin da take da halin zuwa, a daren ranar bayan isha Kawu Amadu ya shigo bayan ya dawo daga Masallaci nan suka shiga tattaunawa kan gyaran da za'a ma gidan Fatuu tace da da hali ma da sababbin furniture aka saka gwaggo tace a'a a gyara su kawai hidiman da yawa don ma an samu gudunmawa sosae an gode ma Allah suma kuma sunyi ƙokari ita da Kawu Amadu haka suma iyayen su Baffa da Yadikko tace ba ƙaramin ƙokari sukai ba sun bada kuɗi da yawa, suna murmushi itama gwaggon suka yaba mata tayi murmushi tare da fatan Allah ya nuna masu bikin lafiya duk suka amsa.

Washe gari da safe gwaggo taje wurin Hajiya tayi mata magana game da ɗaukar kayan ɗaki tace to zata kira can Abuja tayi masu magana harda cewa tana fatan badai su takura kan su ba wurin yin kayan gwaggo na murmushi tace eh. A cikin satin suka je Kasuwa ƙarasa yin siyayyar harda wasu zinarai Fatuu ta tafi dasu tasa Aunty Mareeya ta rakata inda ake saida su ciki harda wanda aka siya mata da kuɗin da Haisam ya ta6a bata da zai yi aure lokacin da kuma zasu yi aure gwaggo ta canzo mata shi da kuɗin daya bata sai gashi sosae yayi daraja harda yan'kunnan da wata ƙawar Mom ta bata da bikin su suma ta saida gaba ɗaya kuɗin taba Gwaggo tace a haɗa ayi gara dasu tace mata don me zata saida abunta duk kuɗin data bada basu isa ba tana murmushi tace to ai ƙarin zasu yi amfani kuma dama amfanin ajiye abun kuɗin kenan Aunty Mareeya na murmushi tace naka sai naka duk suka yi murmushi gwaggo tace hakane Aunty mareeyar ta ƙara faɗin "Allah ka bar mu da yan'uwanmu ka ƙara mana ƙaunar juna da abunda zamu taimaki juna" duk suka amsa da Amin. A kwana a tashi abu nata matsowa ranar Alhamis da daddare Hajiya ta kira Fatuu ta sanar mata gobe Juma'a za'a ɗauki kayan Mino sannan jibi su Aunty zasu kawo lefenta gwaggo tace to Allah ya kaimu, washe garin wurin ƙarfe sha ɗaya na safe Motar ɗaukar kayan ta iso gwaggo ta kira Aunty Mareeya tace to su haɗu can wurin da za'a ɗauki kayan, a Motar Fatuu suka tafi harda Kawu Amadu da Tk Motar kayan tabi bayan su, bayan sun je ba 6ata lokaci aka fara fiddo kayan ana shiryawa a cikin Motar wanda zasu iya fashewa aka ware su bada su za'a tafi ba aka kai ƙaton kwalin su Motar Fatuu, bayan sun gama da nan wurin ɗaukar electronics aka wuce suma aka ɗaukko su gaba ɗaya Motar ta ɗauke kayan da yake babbace sosae, Aunty mareeya ce ta tambayi gwaggo baza'a bi su ba Saboda shirya kayan in anje tace ita sam bata ma yi tunanin hakan ba, kiran Hajiya gwaggon tayi bayan ta ɗaga sun gaisa ta sanar mata an gama shirya kayan za'a sa wani ya bisu ne saboda shirya kayan Hajiyar ta bata amsa da ba dole bane masu kai kayan na gida ne in sunje zasu shigar dasu ciki shiryawar kuma ko in an kai amaryar sai ayi wannan tace to tare da yi mata godiya, daga nan su Kawu Amadu Keke Napep suka hau suka koma gida su kuma suka wuce kasuwa don yin siyayyar kayan abincin da za'a tarbi su Aunty masu kawo lefe daga can wurin Chef Ƙawar su Aunty mareeya za'a kai su ita zata yi abincin.

Washe gari Asabar anata shirye shiryen tarbar lefe, sai bayan Azahar suka iso da yake tafiyar Mota ce, a gidan Hajiya suka fara sauka su biyu suka zo Aunty da babbar Ƙawar Mom sai wata yar'uwar Senator da ta zo daga Daura ta jira su anan gidan Hajiya, saida suka huta bayan la'asar suka fito don zuwa kai lefen harda Hajiya dama ba'a fiddo akwatunan daga cikin Jeep ɗin da suka zo da ita ba, Mota biyu suka yi su Aunty driver daya kawo su ya jasu sai su Hajiya Tk ya jasu suka nufi gidan, gidan har anyi sabon fenti yay kyau lokacin da suka isa su Aunty mareeya da Feenah da inna zaliha sai ƙawar gwaggo da innar su Haulat ne suka tarbe su, falo aka nufa dasu bayan anzazzauna cikin sakin fuska aka gaggaisa dasu tare da yi masu an zo lafiya, su Tk da Kawu Amadu ne suka fara shigowa da akwatunan har suka gama set ukku ne masu guda biyar gaba ɗaya akwatunan guda goma sha biyar ne kowane set da kalar su sun haɗu sosae, Aunty mareeya ce da Feenah suka shiga duɗewa ba abunda kake ji daga bakunan mutanen wurin sai Ma sha Allah Gwaggo sai sakin murmushin farinciki take haka ma Fatuu don an zuba kaya ba ƙarya itama an ɗinka mata wasu da yawa ga uban ƙananun kaya da gani Nameer ɗin na son su haka su Aunty Mareeya suka faɗa, kaya dai sai son barka itama harda zinarai da sarƙar diamond mai kyaun gaske, sai faman yabawa ake Hajiya ta kalli Tk da Kawu Amadu dake tsaye suma suna kallo tace "ku baku da ma niyyar yin auren balle akai naku lefen" dariya sukai Tk yana ɗan sosa ƙeya yace "ai ni harda ma lefen ke ƙara man tsoron auren wllh, A.A ne ya yakamata yay niyya ya fiddo mata kwanan nan don nasan lefe ba matsala bace a wurin shi don ya daɗe yana tara kuɗin shago" duk akai yar dariya shima Amadun faffaɗan murmushi yay yace ai ba ƙananun kuɗi ke haɗa lefe ba balle kuma irin wannan shi in son samu ne ma a yafe mashi lefen yay Maganar idon shi akan Haulat, a hankali ta juyo zata saci kallon shi karaf suka haɗa ido da sauri ta janye ta koma kallon kayan Aunty Mareeya tace aikuwa ko ance an yafe dole sai ya fiddo tarin shagon da yake yi yayi shi don bazai ɗauki tsawon lokaci yana amshe ma yan unguwa kuɗi ba sannan yaƙi yin lefen yana dariya yace ai gini zai yi da wanda ya tara tace ya kawo Matar nan cikin gidan tunda ga ɗaki nan za'a bari in Mino ta tafi Auntynsu Haisam na dariya tace dole dai sai yayi lefen kenan itama Aunty Mareeyar dariyar take yi tace eh, bayan an gama ganin kayan aka yi addu'o'i kafin aka fara shigo masu da Abubuwan da aka shirya masu na ci farko cewa sukai a ƙoshe suke sun ci abinci a gidan Hajiya Gwaggo ta marairaice tana roƙon su ci Aunty mareeya ma tace yakamata na nan ma su ci tunda don su aka yi, ƙarshe dai yanke bin su akai dashi Mota tunda sun ƙi su ci aka ce in sunje gidan Hajiya sai su ci, anata masu godiya Gwaggo ta tambayi amman dai ba yau zasu koma ba ko taga yamma tayi Aunty tace eh sai gobe da safe in Allah ya kaimu, da daddare Nameer ya kira Mino aka shiga yin hira irinta masoya masu muradin juna anan tayi mashi godiyar lefe yace miye abun godiya don yayi abunda yake hakkin shi ne tana murmushi tace duk da haka dai yana murmushi yace mata in akwae abunda take so wanda babu a ciki karta ji komai tayi mashi magana zai siya ya aje mata da sauri tace babu komai yayi, tambayar ta yay taga english wears dake ciki tace mashi eh yace to su yake son ta rinƙa sakawa shiyasa ma ya siyo su daga US da ɗan alamun kunya tace to, daga yadda ta bashi amsa ya gane taji kunya yace mata yana bata shawara duk ta bar wannan kunyar a gida kafin tazo in ba haka ba shi zai cire mata ita har saida ta ɗan runtse ido kafin tace to, kafin suyi sallama ya tambayi ba wani event da zasu yi ne anan tace eh tunda za'a yi Dinner da Walima anan yace amman yakamata tayi ko don Friends ɗinta tace to bari zata yi ma Adda Fatuu magana kan hakan yace Ok in sun fidda abunda zasu yi sai ta faɗi mashi tace to, bayan sun gama wayar ta iske Fatuu a ɗakin gwaggo suna tattaunawa ganin hakan yasa ta juyo da niyyar ta fito Fatun ta kirata ta komo ciki, bayan ta zauna Fatun na murmushi tace "Amaryar mu ya akai ne" Gwaggo ma kallonta take tana murmushi, faɗi mata yadda sukai da Nameer tayi ta ɗan yi shiru kafin tace to ko tayi ko Friend's Eve ne tunda tana da yan ƙawaye anan kuma tunda ba kusa za'a kaita ba ba zuwa zasuyi ba balle ayi Dinner ɗin dasu Minon tace to bari sai ta faɗa mashi zata yi shi gwaggo tace amman kada ta bari ya turo mata kuɗi masu yawa don hidimar da yawa Fatuu tace eh ko a part ɗinta ma sai suyi abun su ba sai ance a kama wuri ba Mino tace to,

"Su Mino Amaryar Nameer, na lura dai ba ƙaramin ji dake angon nan yake ba sai faman nan nan da ke yake" Fatuu ta faɗa tana dariya Minon ta rufe fuska da sauri gwaggo dake dariya itama tace to ba dole yaji da ita ba,
"Wllh gwaggo baki ji daɗin da nike ji ba da zata aureshi don shima Nameer ba daga baya ba na tabbatar zai kula da ita sosae" kai gwaggo ta jinjina kafin tace ai abun farincikine irin mazajen da suka samu tayi Addu'ar Allah ƙara masu fahimtar juna ya zaunar dasu lafiya yasa mutu ka raba Fatuu ce ta amsa da Amin,

"Yanzu ke ya za'ai da karatun ki gashi ko Ssce ba kiyi ba" Fatuu ta tambaya idonta akan Mino, shiru ta ɗan yi tana murmushi kafin tace Nameer ɗin yace zata yi jarabawar bayan an yi, tambayarta Fatuu tayi bayan an yi mi tayi shiru tana bin ta da ido ta ƙara ce mata bayan an yi wai me zata yi jarabawar, shiru tayi tana kikkafta idanu gwaggo dai murmushi kawai take don ta fahimci mi Fatun ke so ta faɗa, ganin ta kafe sai ta faɗi mata bayan an yi mi zata yi jarabawar yasa ta tura baki tana yamutsa baki tace "Wayyo Adda Fatuu ba kin gane ba" girgiza mata kai tayi alamar bata gane ba tay shiru can ta saci kallon gwaggo ganin haka yasa Gwaggon ta juyar da fuskarta, juyawa tay ta kalli Fatuu data kafeta da ido ƙasa ƙasa da murya ta furta "Auren" tana faɗin haka ta tashi da gudu ta bar ɗakin duk suka saka dariya gwaggo tace ina ruwan Mino sarkin kunya.

Washe gari da safe su Aunty suka tafi a ranar da daddare Haisam da Fanan suka iso, Washe gari Litinin Jidderh ta iso daga Dubai a ranar da yamma Haisam ya taho Katsina don gaba ɗaya a ƙagare yake da ganin Baby Fatuu ɗin sa, ko gaya mata zai zo bai yi ba saidai ta gan shi yazo sosae taji daɗi amman duk da haka saida tayi mashi shagwabar miyasa bai faɗi mata zai zo nan ba yace yana son yi mata surprise ne su twins ma sun yi murnar ganin Daddyn su, a daren ranar sun nuna yadda sukai kewar juna sosae, Washe gari aka fara program na Laila a Abuja don su zasu yi abubuwa bayan Dinner da walima da za'ayi in aka kawo Mino su zasu yi Ethiopian Night da Arabian, a ranar yan Adamawa suka iso babbar mota guda nan fa gidan gwaggo ya cika kamar yadda Yaya sukai da innar su Altine duk sun kwaso yan matan gidan a nufin su na suma su samu mazaje a dangin su Haisam, zuwa dare gidan har ya fara fita hayyacinshi don ma Yadikko na ɗan tsawatar ma yaran, har bayan isha Fatuu na gidan anata hira su twins tun bayan da aka cika gidan suka fara koke koke sun ƙi yarda a ɗauke su hakan yasa ta kai su wurin Hajiya don yanzu suna yarda da ita kuma Haisam na nan, suna hirar ne ake tambayar Fatuu inda gidan su yake ta faɗi masu ba nisa da an fita ne nan wasu suka ce wai zasu bita suga gidan sai su kwana kan ta basu amsa Gwaggo tace ai Mijinta na nan hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba don ƙarshe tasan mi zai biyo baya in suka bitan, sai wurin ƙarfe goma saura ta baro gidan ta dawo gidan su lokacin data je part ɗin Hajiya ba kowa a cikin parlon hakan yasa ta wuce Bedroom ɗinta, da sallama ta shiga Hajiyar har ta kwanta amman bata yi bacci ba jin sallamarta yasa ta ɗago Fatun ta shiga, nuna mata bakin gado tayi alamar ta zauna, bayan ta zauna ta gaidata ta amsa kafin tace ai tayi tunanin ta dawo tuni gajiya tasa bata shigo ba Fatun tace a'a yan Adamawa suka zo ta tsaya yin hira dasu ne, tambayar yaushe suka iso tayi ta bata amsa da tun ɗazun zuwan nasu ne ma yasa ta aiko dasu twins don suna ta kuka sunga mutane tace "Allah sarki, sun zo lafiya ko?" amsa mata tayi da eh lafiya lou tace to Ma sha Allah, shiru suka ɗan yi kafin Hajiyar tace mata su twins ɗin na wurin babansu ya tafi dasu can part ɗin nasu ta amsa da to, miƙewa tay tayi mata sallama har zata juya Hajiya ta dakatar da ita da faɗin to maimakon ta taho da wasu nan su kwana tunda ga ɗakuna nan ko wanda suka zo ɗin basu da yawa ne ta bata amsa da suna da yawa tace to ai data rago wasu don su samu walwala gidan, shiru tayi bata ce komai ba a ranta tace ita yaushe zata rakito su suzo suyi ba daidai ba kawai sai gani tayi Hajiyar ta kai hannu gefen pillow ta ɗaukko wayarta, kiran layin gwaggo tayi bayan ta ɗaga ta amsa gaisuwar da take mata kafin tace hidima ta fara kankama Gwaggon na murmushi tace eh wllh Hajiyar tayi fatan Allah yasa taron ya tashi lafiya da sauri gwaggo ta amsa da Amin, ce mata tayi Fateema tace waɗanda suka zo da ɗan yawa to ta turo wasu sai su kwana anan ta amsa mata da to don ba damar ta musa mata, bayan sun gama wayar tace ma Fatuu da tayi tsaye sototo shikenan taje ta ƙara yi mata sallama ta juya ta tafi, sam Gwaggo bata so hakan ba duk da za'a samu sauƙin cukowar da aka yi amman tana fargabar tura wasu su kwana can, ƙarshe Yadikko ta kira gefe ta sanar mata ta bada shawarar a tura su Yaya da Mero sai innar su Altine sai kuma in za'a ƙara wasu amman su tana ganin lafiya lou bazasu yi ba daidai ba tunda sunje Abuja sun san wasu abubuwan na yan gayu gwaggo ta ɗauki sha'awararta, bayan anyi masu magana gwaggo taja Mero gefe don tana da natsuwa ta roƙe ta kan kada ta bari ayi ma Hajiyar ba daidai ba tace to suka tafi tare da Gwaggon ta raka su. Ranar Alhamis Mino tayi Friend's Eve anan part ɗin su Fatuu akayi decoration mai kyau a cikin harabar part d'in harda kujeru, cikin kuɗin da Nameer ya turo mata ta ba Aunty mareeya aka yo abubuwan ci da sha harda wanda zata raba, ba laifi kuma ƙawayenta yan makarantar bokon su da islamiyya da na nan cikin unguwa duk sun zo an ci an sha anyi rawa anyi nishaɗi sosae, a ranar bayan Magrib iyayen su maza harda Baffan su suka iso a gidan Hajiya ɗakin Tk aka sauke su shi kuma ya koma ɗakin Kawu Amadu, yan'uwan su Hajiya mata na nan Katsina da Daura duk sun wuce Abuja mazan kuma sun tsaya ɗaurin aure yan Daura ma sai gobe da safe zasu taho nan Katsina har angwayen da dangin su duk sai gobe in Allah ya kaimu zasu taho, da daddare Hajiya ta kira gwaggo take sanar da ita game da ɗaukar Amarya ance mutum biyar ake so su bada don a jirgi za'a tafi da ita tunda tafiyar bata kusa bace sosae hakan yayi ma gwaggo daɗi Hajiya tace da fatan ba'ai masu ba daidai ba da sauri gwaggo tace a'a wllh hakan yayi ai hidiman da yawa hakan ma ba ƙaramin ƙokari akai ba, Maganar sauran kayan ɗakin Minon da akwatunan lefenta gwaggo tayi ma Hajiyar,

"Wane kayan ɗaki kuma suka rage banda uwayen kayan da kuka takura kai kuka yi mata, ai dana san haka zaku yi mata kaya da bazan bari ba to bansan irin kayan da akai mata ba sai da akai kai su ake man magana abu duk ba an zama ɗaya ba sai a kama a matsa ma kai haka" da faɗa faɗa take Maganar Gwaggo na ɗan murmushi ta bata haƙuri tace ba takura ma kai akai ba an samu gudunmawa ne sosae Hajiyar tace "haka dai kika ce tunda ba sanin yadda akai akayi mata kayan nayi ba, yanzu su kayan da suka ragen su minene?" da sauri Gwaggon tace "dama kayan adon ɗaki ne da zasu iya fashewa sai akwatunan sai kuma kayan gara",

fuska a tur6une Hajiyar tace "dawa yace ayi mata wata gara?" shiru gwaggon tayi Hajiyar tace to ba wata garar da za'a ɗauka zata yi Magana yanzu da Senator kan sauran kayan amman kada a sake a kai wasu kayan abinci da sunan gara in kuma ba'a ji Maganarta ba to rai kuwa zai 6aci, Gwaggo na murmushi tace in sha Allahu baza'a kai ba ta bata haƙuri Hajiyar tace ta saurareta yanzu zata yi Magana game da kayan zata kirata cike da girmamawa tace to, bada jimawa ba sai gashi ta sake kiranta ta sanar mata goben in Allah ya kaimu kafin a ɗaura auren za'a turo Mota da zata kwashe sauran kayan in ma akwae wanda zasu bi Motar lafiya lau su wanda zasu tafi ta jirgin sai su fidda su zuwa da safe zata ƙara kira su yi magana, Sosae Gwaggo tayi mata godiya da Addu'oi kafin suyi sallama saida ta jaddada mata kan kada a sake a saka kayan garar nan suyi amfani da abun su Gwaggo na murmushi tace in sha Allah baza'a saka dasu ba suka yi sallama, bayan sun gama wayar dama Gwaggon ware kanta tayi da suna wayar ta shiga tunanin to suwa za'a bada su tafi ta jirgin bata son wani yaga an yi mashi ba daidai ba, tunanin kiran Fatuu suyi shawara tayi dama tana gidan, bayan tazo ne tayi mata bayanin da Hajiya tay game da ɗaukar Minon Fatun tace "ni hakan ma wllh yayi man daɗi dama ji yadda suka kwaso uban mutane kuma nan nufin su duk gaba ɗaya za'a dasu kai Amaryar, kawai mutum biyar ɗin asa Aunty mareeya, Aunty Feenah sai ke sai kuma babbar ƙawar Mino sai cikon ta biyar ɗin asa...." shiru tay tana tunanin wadda za'a sa ta tambayi Gwaggo ko hada Yadikko za'a tace mata a'a ita da take Uwar Amarya tace to wa take ganin za'a sa na biyar ɗin gwaggon tace "sai ke ko, ai baki sa kan ki ba" Fatun tace shikenan hakan yayi da yanayin yar damuwa Gwaggo tace amman hakan baza'ai ma abun wata fahimta ba ace ba dangin Baffan su da kuma Mahaifiyarta Fatuu tace to su kawai sai a saka su a Motar da aka ce suyi gaba Gwaggon tayi ɗan shiru kafin tace ita bata son abunda zai ja rashin fahimta aga tayi ba daidai ba bari dai a kira Yadikko a faɗi mata aji mi zata ce, bayan an kira ta faɗi mata hannu ta kai ta rufe baki kafin ta cire tace mi zai ja a ɗaura yan Adamawa a jirgi ai abun kallo da magana zasu ja gara ayi yadda Fatuu tace ala bashshi su Yaya da Mero da innarta wato Kakar Mino sai Yayarta hansai su sai a ɗaura su a Motar Gwaggo tace tana ganin hakan lafiya lou tace eh in ma wani yayi tsegumi kan hakan sai ace basu da abubuwan da ake buƙata na yin tafiyar dasu a jirgi, hakan da tace yayi ma Gwaggo akan wannan matsayar suka tsaya, sai wurin ƙarfe sha ɗaya da rabi Fatuu ta koma gida direct part ɗinta ta wuce ba kowa a parlon ta wuce Bedroom, lokacin data tura ƙopar ta shiga a saman gado ta hango haisam yayi shigar bacci haka su twins ma ya saka masu kayan baccinsu da alama ma har wanka yayi masu Abie na a saman ƙirjin shi yana bacci Grandpa kuma na a ta gefen shi ya rungumo shi jikinshi da hannun shi guda gaba ɗayan su bacci suke yadda sukai kwanciyar abun gwanin burgewa, ta ɗan ɗauki lokaci tana ta kallonsu tana sakin murmushi kafin ta nufi hanyar laudary, after some minutes ta fito ɗaure da towel da ƙaramin towel tana goge jikinta kanta yasha kitso da Mero tayi mata ɗazun, press ta nufa ta fiddo kayan baccin da zata saka Nursing pajamas, bayan ta gama sawa gaban mirror ta nufa tana kallon kitson da aka mata yar yar sosae taga yayi mata kyau ko don bata saba yi bane, mai da take shafawa da daddare ta shafa harda na tafin hannu da yatsu sannan ta goga roll-on bayan ta gama ta feffeshe jikinta da turarurruka masu sanyin ƙamshi, wurin gadon ta nufa saida ta gyara ma twins nasu gadon kafin ta kai hannu a hankali don kada ta tada Haisam ta ɗauko Abie ta kai shi saman gadon shi, tana ƙoƙarin daukar Grandpa Haisam ɗin ya buɗe ido slowly suka sauka kanta ta sakar mashi murmushi tare da kashe mashi ido shima yay mata murmushin, shima Adam gadon shi ta kai shi ta juyo tana ce ma Haisam sun ci Abinci ne taga har ta kwantar dasu ba wanda ya farka ya lumshe mata ido kafin a hankali yace ya basu kafin suyi bacci yana gama Maganar ta faɗa jikin shi tana faɗin thank you Daddy wai a madadin su twins ɗin ya ƙara faɗaɗa murmushin shi, bin juna sukai da kallo kowa fuskarshi da annuri can yace yadda ta kwantan baza tayi hurting kan ta ba tace ai bata danne cikin sosae ba ya lumshe ido, tambayarta yay ya hidima tace anata yi gaba ɗaya a gajiye take don ma Gwaggo na hanata aiki sosae ya jinjina kai kafin ya kai hannu ya fara shafa kitsonta ya furta yayi kyau ta furta thanks tare da lumshe mashi ido irin yadda yake, yana ɗaya daga cikin abunda take so tattare dashi kenan duk in kayi abunda ke buƙatar yabawa sai ya ya6a sa6anin da yawan wasu mazajen basu iya yaba ma matan su in suka yi kwalliya ko wani ado wasu har sai matan sun tanka sun ce wai baka ga nayi abu kaza ba sannan in an ci sa'a yace yayi kyau wani kuwa saidai yace shi bai ma lura ba irin hakan kaman cin fuska ne ace kana tare da mace a wuri guda amman tayi abu kace wai baka lura ba shiyasa da yawan matan basu yin adon akai akai tunda wanda suke yi domin su basu yabawa sai waɗanda ya zamar ma jiki ne sun saba suke cigaba da yi koda mazan basu yabawa, Maza yakamata su gyara yaba kwalliyar mace nasa taji daɗi ta ƙara ƙaimi wurin yi akai akai sannan yana ƙara soyayya don ita mace abu kaɗan kesa a siye zuciyarta, sauketa yay daga jikin shi yace mata yana zuwa ta ɗaga mashi kai, toilet ya nufa yana shiga wayar Fatuu ta fara ringing har saida gabanta ya ɗan faɗi ta raya wake kiranta a wannan lokacin sha biyu har ta wuce, saukkowa tayi ta nufi gaban dressing mirror inda wayar take har lokacin ringing take ta kai hannu ta ɗaukko tana duba mai kiran ta saki murmushi ganin Fauziyya ce,

"Ƙawata Amarya ko kun iso ne?" ta fada bayan ta ɗaga daga can ɗayan bangaren Fauzy ta bata amsa da eh yanzun nan suka sauka Abuja, cikin nuna farinciki Fatuu tayi mata anzo lafiya ta amsa ta sake tambayar Nasarawa zasu wuce tace mata a'a gidan su na Abuja zasu tsaya don gobe yana son zuwa ɗaurin aure dasu Daddyn Haisam Fatun tace suma goben zasu haɗu kenan in suka kawo amarya harda cewa ta ƙagara taga yadda ta koma Yaya Sameer ya iya kiwo Fauzyn tay yar dariya mai sauti daga baya sukai sallama, aje wayar tayi ta juya zata koma gado lokacin Haisam ya buɗe ƙopar laundry ya fito ta juya ta nufe shi suna haɗuwa ya rungumeta tana kallon fuskar shi da murmushi ta faɗi mashi Fauzy ce ta kirata ta sanar mata sun sauka Abuja yanzu ya jinjina kai kafin yace sun yi waya da Sameer kafin su taho, ɗaukarta yay ya nufi gado da ita tana ta dariya tana faɗin wai sai yaushe zai fara jin nauyin ta yay murmushi kawai, bayan ya kwantar da ita mikewa yay ya kunna lamp ta side ɗin da yake kafin ya nufi wurin Switch ya kashe hasken ɗakin ya dawo gadon ya fara mata tausa cikin salon ƙauna tana ta lumshe ido tare da yaba abunda yake matan sun ɗan ɗauki lokaci yana mata massage ɗin kafin ya fara canza salo tana ganin haka itama ta fara bashi nata salon daga haka suka lula wata duniya da ma'aurata ke zuwa.

FRIDAY

Alhamdulillah Allah ya kawo mu ranar ɗaurin aure, ana tashi aka shiga yin hidima ba kama hannun yaro, tunda safe jirgin yan ɗaurin aure ya sauka daga nan gidan su na G.R.A suka wuce kafin lokacin ɗaura auren yayi, suna isa gidan ango Nameer ya kira amaryar tashi ya sanar mata gasu sun iso yana son yaga fuskar kyakkyawar amaryarshi ta sanar mashi tana gidan Hajiya part ɗin su Adda Fatuu yace Ok gashi nan zuwa, yan Abuja basu daɗe da zuwa ba suma 6angaren angon Laila convoy ɗin su ya iso daga Kano, jerin danƙara danƙaran motoci ne masu numfarfashi tare da na security a gaba da baya da yake wanda zata auran wato bashir ɗan sanannan mai kuɗi ne a Nigeria, a Vip na haɗadɗan hotel Hillside Royal Suites suka sauka kafin lokacin ɗaura auren yayi, tunda wuri Aunty Mareeya ta taho gidan bikin saida ta biya ta ɗaukko Feenah kamar yadda sukai da ita, bayan isowarsu aka shiga yin aiki ba kama hannun yaro don ma Abincin wasu ba anan za'ai ba abunda za'ai a nan gidan kaɗan ne, ganin yadda Fatuu ke ta kujiba kujiba yasa aka fara mata magana kan ta rinƙa hutawa saboda halin da take ciki sai lokacin wasu da yawa suka san da ciki gareta har Haulat da Feenah basu gane ciki gareta ba duk an zata ƙibar da ta ƙara ne yasa ta ɗan yi tumbi, wuraren ƙarfe sha ɗaya Hajiya ta kira Gwaggo tace a fiddo da sauran kayan Minon ga wanda zai ɗauka nan yazo Gwaggo tace to ta sanar da ita akwae wanda zasu bisun sannan akwatunan na nan part ɗin su Fatuu aka maido su bari tayi mata magana sai tazo a fiddo su Hajiyar tace to ayi ma mutanen magana su fito kar a 6ata lokaci don tafiyar bata kusa bace, suna gama wayar tayi ma su Yaya da sauran wanda Yadikko tace aje dasu magana dama tun jiya ta sanar masu zasu tafi da safe, zo kaga rawar jiki wurin Yaya anji zanjen tafiya Abuja ita kuwa innarsu Altine kamar zata saka kuka tsabar takaici ita bama don yaran yan matan da suka kwaso da baza'a tafi dasu ba ita kanta da bazata ba yasa ta shiga matsananciyar damuwa sai faman roƙon a tafi da ita take Gwaggo tace ta bari aga Motar inda wuri sai ta bi su, cikin sa'a sai gashi Motar yar babba ce mai seat ukku a boot da bayan Motar aka saka akwatunan da kwalayen sauran kayan ba'asa kayan gara ko ɗaya ba tunda Hajiya ta hana, a layin tsakiya Mutum huɗu suka zauna harda innar su Altine data kasa rufe baki don murnar za'a da ita a gaba Mero ta zauna wasu harda cewa ai za'a iya ƙara mutum guda a gaban Driver ɗin yace a'a zai takura a bar mutum ɗaya yayi, Altine na tsaye bakin ƙopar Motar harda ƙwallarta tana roƙon aje da ita don Allah kofa da bikin Fatuu ba'a je dasu ba, daga cikin Motar innarsu ta wurgo mata harara tace ina za'a je da ita ra6e ra6e da Y'ay'a ko an gaya mata Abujar ruga ce Gwaggo ce ta rarrasheta tace tayi haƙuri watarana zasu je ko in Minon ta haihu fuska a yamutse tace ai ana iya ƙin zuwa da ita Gwaggon tace in sha Allahu in Allah ya kaisu lokacin ita zata sa aje da ita sannan ta ɗan kwantar da hankalinta, har Driver zai tada Motar Fatuu ta nufo Motar da yar sassarfa tana ruƙe da hannun ƙanwar su Aysha ganin tana ɗaga hannu yasa aka yi mashi magana ya dakata, bayan ta ƙaraso roƙon shi tay kan a bari ta zauna a gaban jikin inna mero da yake yasan wacece Fatun cikin kwantar da murya yace abunda yake gani Abuja ba kusa bace da za'a ce ta zauna a jikinta har suje dole su duka su gaji da alamun damuwa Fatun tace mashi to ya za'a yi don Allah ƙanwar amaryar ce gashi ta ƙwallafa rai sai Kuka take jin baza'a da ita ba, fitowa yay daga cikin motar yace bari yaga in zai iya samar mata wuri, kayan cikin boot ɗin ya gyaggyra haka akwatunan dake seat ɗin baya suma ya gyara tsarinsu ya rago guda biyu ya maido boot sai gashi an ɗan samu wuri a bayan yace ma innar su Altine tunda ita bata da jiki ta dawo nan baya sai ita yarinyar ta zauna a wurinta mutanen seat ɗin ma sun fi sakewa da sauri tace to ai ita ko a cikin boot ne indai za'a je da ita to zata shiga har saida ta ɗan ba Drivern dariya, bayan ta koma Aysha ta zauna a wurin ya rufe masu kopar kafin ya koma driver seat ya zauna saida yay Addua sannan ya tashi Motar aka shiga ɗaga masu hannu ana masu Addu'oin Allah ya tsare daga haka suka tafi.

Ƙarfe sha biyu na yi sun gama ayyukan da suke su Aunty mareeya da Feenah suka tafi don su shiryo zuwa kai amarya Fatuu ma ta wuce gida don ta shirya zuwa lokacin tuni gidan ya cika da mutane ƙawayen gwaggo da yan'uwanta harda iyalin Kawu shibaɗo da shi kan shi yazo daurin auren, Jirage kawai keta kai da komowa yan ɗaurin aure sai zuwa suke zuwa lokacin Mutane sosae sun taru a gidan su Haisam na G.r.a yan uwa da abokan arzuƙi da abokan siyasa na Senator duk sun hallara har Sameer ma ya iso haka ma 6angaren Angon Laila duk sun dawo nan gidan don a tafi tare , lokacin sallar Juma'a na masallacin da za'a ɗaura auren wato Masallacin Banu Commassie na gabatowa aka shirya convoy na Motoci masu sunan Motoci aka tafi Magana ake ta harkar masu arzuƙi daya amsa sunan Arzuƙi abun sai wanda ya gani don alƙalami bazai iya zayyana ainihin ƙayatuwar ba, suma can 6angaren iyayen Mino Maza Tk da Kawu Amadu ne suka ɗaukko su a Motoci, Massallaci fa ya cika dankam da mutane ga tsaro ta ko ina don ma yana da girma da ba lalle ya isa ba, ana gama salla ɗaurin Auren su aka fara yi bayan waliyyai na kowanne 6angare sun hallara aka fara ɗaura na Dr Bashir da Dr Laila bayan an gama aka ɗaura na Engr Nameer da Ameenatu kowanne akan sadaki Naira 500 dubban mutane suka shaida, bayan angama kowa fuskar shi ɗauke take da farinciki aka shiga gaishe gaishe da fatan alkhairi ga ma'auratan yan jarida muna ta aikin ɗaukar rahoto, bayan an gama mutanen 6angaren Angon Laila Hotel ɗin da suka sauka can suka koma don yin reception bangaren su Senator kuwa G.r.a suka koma acan zasu yi nasu a Masallacin ma an raba ma mutane uban Abinci da lemuna sai Addu'oi ake ma ma'auratan da kuma Senator Ali Zakee ana faɗin Allah yayi mashi President sai murmushi yake yana gaisawa da mutane har saida jami'ai suka dakatar dasu, acan 6angaren gidan su amarya duk sun sha ankon atampa mai kyau da suka yi kowa ka gani yayi kyau cikin atampar har Hajiya da Saude duk suma ita suka saka anata hotuna da wayoyi, yan G.r.a na gama yin reception ɗin gidan Hajiya suka nufo harda Senator nan fa unguwa ta cika ango Nameer yasha babbar rigar bugaggar shadda light blue haka hular shi da agogon shi zuwa takalmanshi duk sun hau da kalar shigar da yayi sam ya kasa rufe baki hakanan ma yayi murmushi balle yanzu da dalili Allah ya mallaka mashi Babynshi yar fillo, su Kawu Amadu abokan ango duk sun sha shaddoji kowa dai yayi kyau Hajiya na ganin Nameer ta rungume shi tana faɗin duk da tana kishi tana farinciki kuma da Allah ya nuna mata wannan rana su Senator dasu Kawu Mani yan Daura nata dariya, bangaren amarya Mino kuwa tana a part ɗin Fatuu ƙwararriyar mai makeup dake a Katsina wato Munah Beauty tana tsantsara mata kwalliya, fitted gown din rantsattsan lace Navy blue da ratsin light da kuma fari mai kaman silver tasa sai net light blue an ci bakin shi da bakin lace ɗin jikinta aka yafa mata sai head ɗinta shima light blue ne clutch da takalmanta kuma silver sai sarƙarta da yan kunnanta na Diamond, Wow Ma sha Allah shine abunda aketa faɗi, bayan Munah Glam ta gama tsantsara mata kwalliya ta naɗa mata head su Aunty Mareeya suka shiga tambayar ina aka samo mai makeup ɗin nan Fatuu ta bata amsa da Babbar ƙawar Mino wato Safnah ta kawo masu ita tace da Sunan Yayarta ita tayi masu Makeup harda ma ƙunshi na zane dana salataf duk tana yi Feenah tace kenan har ƙunshin ita tayi masu Safnah dake zaune gefen Mino itama tana jira ayi mata make up ɗin ta bata amsa da eh har itama nata duk ita tayi masu, sosae suka yaba da ƙunshin shima Aunty Mareeya tace ansha da ita da ta sani itama tare dasu akai mata ya zanu raɗam haka ta ɗan harari Fatuu tace duk laifinta ne da bata sanar masu ƙwararrar mai ƙunshi zata masu ba suma ayi masu Fatuu na dariya ta bata haƙuri tace itama bata santa ba saida Safna ta kawo ta, dafa shoulder ɗin mai makeup da ƙunshin Aunty Mareeya tayi ta tambayeta irin abubuwan da take yi ta fara lissafo mata bangaren kwalliya tace suna yin ta Amare da masu Jego ko ta Birthday ko simple da za'a ma mutum don zuwa biki ko suna sannan tana koya ma mutum in yana so a bangaren ƙunshi kuma tana yin baƙi na zane da kuma ja na zane dana salataf irin wanda ke yin maroon ko kuma baƙi sannan suna yin kitso iri iri sai wanda mutum keso sannan kuma suna yin Home service wato in mutum naso a iske shi a gida ayi mashi kowanne cikin abubuwan data lissafa, tambayarta Feenah tay ya yanayin price ɗin aikin nata yake ta shiga faɗi mata ai tun kafin ta ƙarasa Aunty Mareeya ta miƙa mata waya da sauri tana faɗin yar albarka saka man lambar wayarki aikuwa su Fatuu da Aunty Feenah suka kwashe da dariya Feenah na faɗin su Maman Hanif an ji sauƙi tana dariya tace to yanzu a rayuwar nan ai sauƙin ake nema harda tsawwalawar da wasu masu makeup ɗin ke yi yasa da yawa wasu suke haƙura da yin gayun duk da suna so amman ba hali Feenah tace gaskiya kam wasu kuma sai hidima ta kama sannan suyi duk da mace da gayu aka santa amman in dai mutum zai samu Munah Glam saidai in shi ke bai son gyara kanshi, Aunty Mareeya tace ta bari kawai ai ita yanzu kakarta ta yanke saƙa gayu sai in ba'a yi yanzu ta ƙara samun tarkon da zata ƙara damƙe zuciyar Abban su hanif dama shi ɗan son gayu ne shiyasa bata wasa yanzu kuma zata ƙara ƙaimi da Munah Glam, bayan ta saka mata lambar ta miƙa mata tana cikin yin saving Feenah tace itama ta karanto mata tace to ta fara karanto mata lambar kamar haka 08169856268, Bayan an gama shirya amarya Mino Fatuu akai mawa da yake wadda za'a mata ba irin ta Mino bace hakan yasa ba'a ɗauki lokaci sosae ba aka gama aka ɗaura mata kallabi abun sai wanda ya gani Babyn Haisam itama ta fito kamar Amarya, Safnah aka shiga yi mawa bayan Fatuu ana gama mata Aunty mareeya tace itama duk da tayo kwalliyar daga gida a gyara mata ita ana cikin yi mata Haisam ya kira Fatuu yace mata ta kawo Mino part ɗin Hajiya yanzu tace to, ita da Safnah suka tafi kai Minon, lokacin da suka shiga parlon Hajiya gaba ɗaya idanu suka dawo kan su da sauri Mino ta sadda kanta ƙasa a haka suka nufi cikin parlon ango Nameer sai sakin ƙayataccen murmushi yake yaga yar fillon shi ta zama tamkar tauraruwa gashi yanayin shigarsu ta haɗu don head ɗin da aka ɗaura mata da mayafinta da kuma fulawoyin lace ɗinta sun yi kala ɗaya da shaddar shi da gani dai tsara hakan sukai, idon Haisam na akan Babyn shi Fatuu da yaga ta ƙara mashi kyau sosai wurin Hajiya suka nufa da ita tana ta murmushi ta miƙo hannu ta kamo na Mino ta zaunar da ita a gefenta tana yaba kwalliyarta harda cewa wato shine aka ƙi kawo mai yin kwalliyar tayi mata don ansan in aka yi mata sai tafi Amaryar kyau duk akai dariya su Fatuu da suka zuƙunna akan Carpet suka shiga gaishe da mutanen ciki suna ta amsawa harda Senator sukai mata ya hidima, Mino sarkin kunya gaba ɗaya ta kasa ɗagowa balle ta gaisa da mutane hakan yasa Hajiya tace ma Fatuu ta kamata ta kai ta wurin su Senator, a gaban shi suka tsugunna da ƙyar Mino ta ɗago ta gaishe shi yana ruƙe da Adam ya kai ɗayan hannun shi ya dafa shoulder ɗinta yana murmushi ya tayata murna tare dasa ma Auren nasu Albarka yace yana farinciki da shigowarta Family ɗin tare da yin Addu'o'i ya juya kan Fatuu yace ita Daughter yanzu ta zama yar gida sai dai ta tarbi wasu Fatun tay yar dariya ta ɗaga mashi kai tare da faɗin hakane saida tayi magana sannan Adam ya gane itace ya fara miƙo mata hannu yana faɗin Momy duk akai dariya don sun fahimci bai ganeta ba farko saboda Makeup da aka mata, Hotuna aka shiga yi anan cikin parlon Hajiyar lokacin da Mino ta jera da Nameer za'a yi masu har saida na furta Ma sha Allah wato kyau ya haɗu da kyau sai ya bada Madarar kyau.......

99

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

.......Har gwaggo Hajiya ta kira a waya tace tazo ayi masu hotuna ba 6ata lokaci ta zo gidan tana sanye da Atamfar anko yau dai su Gwaggo gyale aka yafa sai gashi ta fito ɗas da ita baka ta6a cewa Fatuu jikar tace tafi kama da ace ɗiyarta ce, ana gama yin hotunan Hajiya ta sanar ma Gwaggo suje su shirya ana gama sallar La'asar zasu tafi tace to, tare da Mino da Fatuu suka fito saida suka fara zuwa baya inda iyayensu Maza suke don ayi ma Mino faɗa suka kuma yi sallama dasu, to nidai bansan mi suka ce mata ba don gaba ɗaya da Fulatanci sukai mata magana naga dai tana ta ɗaga kai tana kai hannu tana goge ƙwalla, bayan sun gama da nan gidan Gwaggo suka wuce anata yabon gayunta aka kaita wurin mahaifiyarta Yadikko don tayi mata faɗa amman ta kasa ce mata komai gaba ɗayansu sun sadda kai ƙasa da alama ma Yadikkon kuka take, koda aka ƙara mata magana kan ta daure tayi mata nasiha da ƙyar murya na rawa tace ai tasan Gwaggo zata yi mata kuma acan in an kai ta iyayenta mata da suka yi gaba zasu yi mata duk akace mata duk da haka a matsayinta na Mahaifiyarta ya kamata tace mata wani abu, hannu ta kai saman kan Minon tace "Ubangiji Allah yayi maki Albarka ya Albarkaci aurenki yasa gidan zaman ki ne na har abada, ayi biyayya kuma aita haƙuri" da kyar ta kai ƙarshen Maganar a wawware saboda Kuka, ana ƙokarin miƙar da Minon da sauri ta faɗa jikin Yadikko ta saka wani irin kuka mai ta6a zuciya, da ƙyar aka raba su Aunty Mareeya ta tafi da ita don ta shiryata, bayan duk anyi salla Motoci guda biyu Jeep da ƙarama suka zo ɗaukar su tasu Hajiya da wasu yan uwansu Hajiyoyi guda biyu na biye da ita sune sukai bikon amarya aka fito da ita tana sanye da Alkyabba sai faman rizgar kuka take sai kace ba gidan masoyinta Nameer za'a kai ta ba, yan tafiya duk sun shiga Mota anata ɗaga masu hannu Fatuu taso aje da Haulat amman bai yuwuwa su Kawu Amadu suda ke abokan ango har sun wuce Airport sai fatan Allah ya kaisu lafiya.

Alhamdulillah yan kawo Amarya sun isa Abuja lafiya har sun iso gidan sun samu kyakkyawar tarba daga dangin angon, biki na Abuja don gidan shaƙe yake da Mutane yan uwansu yan Ethiopia da Qatar duk sunzo haka Hajiya Maryam da iyalinta har Hajiya Zainab ma da nata iyalin harda surukarta Fauzy tuni sun hallara suma duk sun sha ankon haɗaddar atampa kowa yayi kyau, Fauzy da Fatuu suna ganin juna suka rungume juna cike da farinciki haka Jidderh ma sosae ta nuna farincikin ganin Fatuu sai kace sun shekara basu haɗu ba, Aunty Mareeya baki yaƙi rufuwa anga yar gaban goshi Fauzy, bayan an gama tarbar Amarya da gaishe gaishe part ɗin baya suka nufa dama su Yaya na can, lafiyayyun Abinci da abubuwan sha aka tarbe su dashi duk da bama wata yunwa suke ji ba, ana gama sallar Magrib aka fara shirin tafiya Dinner, ɗakin Laila aka kai Mino acan za'a shirya su tuni har an fara tsantsara ma Laila Makeup tasha ubansun ƙunshi haka jikinta sai sheƙi fatar ta ke yi kai da gani kasan ba ƙaramin gyara tasha ba haka sumar kan ta ma, bayan sallar isha duk an shirya gaba ɗaya ankon lace akai saidai na iyaye daban ne haka ƙawayen Laila ma kalar nasu daban su Fatuu dasu Jidderh nasu kala ɗaya ne duk sun sha ɗinkuna styles iri iri, tuni aka fara kwasar mutane zuwa wurin da za'ayi saida aka gama kai kowa sannan aka zo ɗaukar Amare lokacin da nayi tozali dasu har saida alƙalamina ya kusa faɗuwa to Laila ma ta tsara wani a bikin shi balle kuma nata ai sai abunda ya ture ma buzu naɗi, rantsattsan Material ne kala ɗaya suka saka ita da Mino, Material ɗin baƙi ne yana da adon golden brown sosae yay wani baza baza sai walainiya yake gaba daya fitted gown akai masu kowa daidai jikin shi sai aka ɗaura masu golden brown head wuyansu da hannuwansu sun sha gold haka takalmansu da clutch ɗin su duk golden brown Mino sai tayi kamar yar ƙanwarta saboda ba jiki don ma tana da tsawo, Uhmm wurin Dinner din abun ba'a magana don ya tsaru iya tsaruwa Naira tasha kashi, Ma sha Allah shima mijin Laila kyakkyawa dashi gashi da gani ba yaro bane don zai yi tsaran Haisam koma ya girme shi shima ba fari bane amman kuma baza'a ce mashi baƙi ba kamar dai yadda Laila ɗin take shima yana da haske gashi da ganin shi hutu ya zauna mashi sosae, shima shida Nameer kaya iri ɗaya suka saka plain yard baƙi kai da gani tsadadde ne anyi masu babbar riga aikinta kuma brown haka agogunan su ma brown ne gaba ɗaya suna sanye da dakakkun takalma baƙaƙen cover, suma dangin Mijin Laila kalar lace ɗin su daban sun sha ɗinkuna gasu duk wayayyu ne baka jin komai sai turanci gashi ba Maganar saka gyale yawanci masu ɗan gyalen duk iyaye ne haka kowane wuya da hannu ka kalla gwalagwalai ne kawae kake gani, ba 6ata lokaci aka shiga gudanar da activities ɗin dinar kowa kaga fuskar shi ɗauke take da annuri, lokacin da aka fiddo ƙawar Mino Safnah ta bada tarihinta sosae ta burge mutane gata ƙarama amman turanci a bakinta kamar zubar ruwa sosae Fatuu taji daɗin yadda tayi dama Mino ta faɗi mata tana da ƙokari gashi dama makarantar su babbar private ce da turanci ake magana shiyasa ba laifi itama Minon tana ganewa, lokacin da aka fiddo amaren da angwayen don su taka rawa kasa yin rawar Mino tayi dama gaba ɗaya a kunyace take da shigar jikinta saida Nameer ya kama mata hannuwa nan fa aka shiga zuwa yi masu liƙi ganin ana cunkushewa yasa Mc raba su yace su Nameer su koma in aka gama ma su Laila sai suma su fito sai gashi an koma yin liƙin a tsare, Su Kawu Amadu na zaune a inda aka tanadar ma abokan ango shida Kamalu da Tk gaba ɗaya ankon maza ne a jikinsu plain yard brown ɗinkin Senator style harda yar falmaran a sama sosae sukai kyau cikin kayan sumarsu duk tasha gyara in ka gansu baka cewa suma ba Ya'yan masu kuɗi bane karma Kamalu yaji don yafi kawu Amadu fari ga sumar shi a kanannaɗe take bangaren kyawun fuska kau ba'a magana dama shi Mamarsu ya biyo wato Aysha ita kuma babansu ita da kawu Amadu shi ta biyo hakan yasa Kamalun ya ɗaukko dogon hancinta ga ƙaramin baki dama ba kalar shape ɗin bakinsu ɗaya da Fatuu ba ga girarshi ta zanu raɗam ɗauke da baƙin gashi mai santsi, ganin anata zuwa ana yin liƙi yasa shi ce ma Kawu Amadu ya bashi kuɗi suma suje suyi Amadun yay yar dariya yace shi ina yaga kuɗin da zasu je suyi liƙi yana ganin uban kuɗin da ake ta liƙawa yan kuɗin da ke a jikin shi yan kaɗan ne, Tk na dariya yace ai masu yin canjin kuɗin ana masu transfer sai suba mutum Cash Kawu Amadun yace "kai rabu dasu ba wani liƙin da zanyi nima kuɗin aure nike tarawa",

"Kaman gaske, kai da har yanzu baka da niyya" Tk ya faÉ—a yana dariya,

"Serious kwanannan zan baka mamaki don mai gaba É—aya zanyi saidai kaji Maganar aure kawai da an bani dama" Kawu Amadun ya faÉ—a,

"to Allah yasa, in ba haka ba sai dai kaga na shige na barka don bazan biye maka ba in ƙi more rayuwata gashi har mun yi 30yrs",
Amadun yace mashi yasha kurumin shi sai ma ya riga shi yi in sha Allah, hango Fatuu Tk yayi ta dawo daga wurin yin liƙi yace ma Kamalu yaje ga Hajiya Fatuu can ya amso kuɗin liƙin, kai idon shi yay kan Fatun kafin ya miƙe da sauri zai je wurinta Amadu na faɗin shima ya amso dashi ya ɗaga mashi kai, da sauri ya tunkareta don bai son ta koma wurin zaman su saboda akwae mutane, cikin rashin lura yaji ya kai ma mutum karo har abu ya faɗi ƙasa da sauri ya maido idon shi kan wadda sukai karon ta kai hannu ta dafe goshi tana sanye da irin lace ɗin su Fatuu anyi mata wasu irin style na riga da skirt kai kace a jikinta aka ɗinkasu don sun kamata sosae sun fito da suffarta wadda da gani ba ramamma bace kuma tana da shape gaba ɗaya wuyanta da kafaɗunta a bayyane suke farar fatar ta fat ta bayyana, tun daga kunnanta wuyanta zuwa hannunta data dafe goshinta gold ne, sosae hankalin Kamalu ya tashi ya wara ido yana kallonta duk da bai ga fuskarta ba ya shiga motsa baki ya rasa taya zai bata haƙuri da ƙyar yay ƙarfin halin ce mata don Allah tayi hakuri bai kula bane shiru bata ce mashi komai ba bata kuma ɗago face ɗinta ba, saida ya ƙara bata haƙurin sannan ta janye hannun idanunta suka shiga cikin nashi ta shiga kallon shi fuska a tamke, lokacin da Kamalu ya haɗa ido da ita saida gaban shi yay mugun faɗuwa tsoro ya kama shi ganin kalar ƙwayar idonta, kasa jure ma kallonta yayi ya sauke idon shi ƙasa gaban shi na ɗan faɗuwa ganin yadda ta ɗaure fuska gashi bai san wacece ita ba,

"Are you blind?" kaman daga sama yaji zazzaƙar muryarta ta faɗa har saida ya haɗiyi abu kafin ya ɗago ya kalleta tunanin bata jin hausa yay da yake yayi Secondary kuma yanzu da yake shirin cigaba da karatu Kawu Amadu na koya mashi wasu abubuwan harda turanci dama kuma yana ja don duk yan ɗakin su Fatuu ba laifi kan su na rabawa,

"I'm sorry please i bump into you, it was an accident my attention was elsewhere" ya faɗa da yar rawar murya sautin turancin gwanin daɗi abunka da Bafullatanin Asali, bin shi tay da ido kawai tana ƙare mashi kallo ba tare da tace komai ba shikam da ƙyar yake jure ma kallon gray eyeballs ɗinta ganin bata ce komai ba yasa shi ƙara ce mata please he's sorry sai lokacin ta motsa baki a hankali ta furta "is okey" ganin tana ƙokarin duƙawa ta ɗaukko haɗaɗdar purse ɗinta yasa shi rigata duƙawa ya ɗaukko mata ya miƙa mata still kallon shi take tayi, tana amsa sai ji yay ta furta "Nagode" daga haka ta wuce ta nufi gaban hall ɗin dama itama liƙin zata yi, saida Kamalu yay mamakin godiyar da tayi mashi gashi yay tunanin bata jin hausa ne, juyawa yay ya nufi komawa wurin zaman shi don Fatun tuni ta zauna kuma sai yaji ma yin liƙin ya fitar mashi a rai, yana komawa su Kawu Amadu suka tambayeshi miya haɗa shi da wadda suka hango su tsaye ya faɗi masu ya bugeta ne bai gani ba har jakar hannunta ta faɗi Tk yace bata yi mashi masifa ba yace a'a kawai tace mashi shi makaho ne da turanci sai ya bata hakuri ya nuna mata hankalinshi na wani wuri tace shikenan Tk ɗin yace yayi sa'a don masifaffa ce, tambayar shi yay ya santa ne yace mashi eh itama jikar Hajiyar Senator ce sunanta Farha ƙanwar kishiyar Yayar shi Fatuu Kamalun ya jinjina kai Amadu yace ya bai amso kuɗin liƙin ba ya bashi amsa da ta riga ta zauna cikin mutane a bashshi kawai, Tk na dariya yace yanzu sai ace bazasuyi ma Mino liƙi ba gaskiya da basu kyauta ba, ƙarshe dai sai tansfer ɗin Amadu yay aka basu Cash suka haɗa dana Tk sukai liƙin,

Alhamdulillah an gama Dinner lafiya anci an sha an nishanÉ—u an zubar da galan galan na farinciki an cashe iya cashewa an raba souvenirs iri iri wasu cikin nasu Laila harda hotunansu nasu Mino dai sunan su ne kawai wasu kuma tare aka sa sunan nasu baki É—aya dasu Laila, bayan sun koma gida kowa a gajiye yake Fatuu taso tayi fira da Fauzy amman ta gaji sosae hakan yasa tayi wanka su twins ma tayi masu suka kwanta.

Washe gari ana tashi aka fara shirye shiryen Walima don da wuri za'ayi saboda ƙarfe ukku na rana za'a tafi da Laila Kano can za'a kaita itama tafiyar Jirgi za'ayi Mino kuma sai bayan Magrib za'a kaita gidanta, bayan sun gama yin Breakfast Gwaggo ta iske Hajiya bayan sun gaisa tace mata dama zata tambaya ne ko za'aje a shirya ma Mino ɗaki tunda da aka kawo kayan ba'a biyo an shirya ba Hajiyar tace ai tana tunanin kamar ma an shirya mata amma bari ta tambaya, Mom ta kira a waya bayan sun gaisa tayi mata Maganar shirya gidan Minon tace ai ansa an shirya kayan tun bayan da aka kawo su tace to, bayan sun gama wayar ta faɗi ma Gwaggo tace saidai ko in suna son zuwa ganin gidan da sauri Gwaggo tace a'a tunda za'a je kaita sun gani, ana yin salar Azahar aka fara yin Walimar Amare sun sha shaddoji da akayi ma tsantsararren ɗinki kowa kalar tata daban Walimar ma harda ankon Material voile aka yi kowa yayi kyau mutane nata zuwa itama Mino harda kyaututtuka aka rinƙa bata, Walima ta ƙayatu anci ansha anata fatan alkhairi ga ma'auratan, Misalin karfe ukku da yan mintuna duk aka fito harabar gidan rakiyar Laila da aka zo tafiya da ita, cikin wanda zasu tafi kaita harda Hajiya Maryam da Aunty da Jidderh da wasu yan uwan su yan Ethiopia sai wasu ƙawayenta da kuma wasu yan uwansu na Katsina da Daura harda Fanan Fatuu dai banda ita, anata bankwana da ita ta canza shiga zuwa jigunan lace duk yadda ta daure saida ta matse ƙwalla lokacin da Mom ɗin su ta rungumeta haka Hajiya ma, su Kawu Amadu na daga can gefe suna kallon yadda aketa bankwanan, bayan masu tafiyar sun shiga motoci anata ɗaga masu hannuwa suka tafi sai fatan Allah ya kiyaye, Fatuu na tare da Fauzy har sun juya zasu koma ciki Fatuu taji an kirata hakan yasa ta dakata ta juya don taga waye ya kirata, Kamalu ne ya nufota yana sanye da farar shadda bayan ya ƙaraso inda suke da murmushi ya gaishe da Fauzy itama tana murmushi ta amsa tay mashi ya hidima, don ta basu wuri yasa tace ma Fatuu ta isketa ciki tace to, tana murmushi tace ma Kamalun da wani abu ne yace eh wllh kuɗi yake son ta bashi zasu shiga gari ne shi kuma baida ko sisi ko jiya ma har zai zo ta bashi na yin liƙi sai Kawu Amadu ya bashi, wani kallo tayi mashi tace "Duk yadda kai kalar Ya'yan masu kuɗin nan amman kake tambayar kuɗi"

dariya yay yace "to ai kinsan komai dai ba É—an masu kuÉ—in bane É—an masu shanu ne" yadda yay Maganar ne ya bata dariya tace to ai suma masu shanun suna da kudi yace uhm ayi shiru dai amman ga inda masu kuÉ—i suke nan, tambayar shi tay ya akai baida kuÉ—i yace to ai anyi hidima ya kuma yi É—inkuna tace hakane gashi nan ai yanata saka kaya sai kace shima É—an Senator É—in ne ya saka dariya, ce mashi tay yaje zata tura mashi yace tunda dai ga wayar nan a hannunta ta tura mashi yanzu zasu fita bazasu ma koma cikin gidan ba,

"Kodai kun yi yan mata ne zakuje siya masu ice cream" tay Maganar tare da yi mashi wani kallon tuhuma yana dariya yace waye zai so su haka basu da ko sisi tana ƙoƙarin tura mashi tace ai ba'a ganewa, duk wannan abun idon Farha na akan su tun lokacin da Kamalun ya taho wurinta, dubu asharin ta tura mashi tace gashi nan suyi maneji don a Abuja ba wani abun kirki zata siya masu ba bata da kuɗi sosae yana murmushin jin daɗi yace a hakan ma ya gode sosae Allah ya barta da Baffan su twins tana dariya tace Amin tay mashi sai sun dawo, tana niyyar juyawa ta tafi Farha ta ƙaraso wurin itama ankon Material ɗin da kayi ne a jikinta suma riga da skirt ne aka mata tayi ɗaurin kallabi Zarah Buhari dark ash ɗin sumarta ta zuba a gadon bayanta, Kamalu na ganinta gaban shi ya faɗi don ya ganeta ya bita da kallo, murmushi Fatuu tayi mata tace mata sannu itama ɗan murmushin ta mayar mata ta gaishe da ita bayan ta amsa ta maida idonta kan Kamalu suka haɗa ido a hankali yace mata sannu ta ɗaga mashi kai kafin ta maido idonta kan Fatuu tace mata brother ɗinta ne taga kaman sun yi kama tace mata eh Yayanta ne shi take bi mawa ta jinjina kai sai kuma ta ƙara cewa the same parents suke dashi kenan Fatun tace eh su biyu ne Mom ɗin su ta haifa kafin ta rasu a hankali tace Allah ya jiƙanta Fatuu ta amsa da Amin daga haka Farhar bata ƙara cewa komai ba ganin haka yasa Fatuu ce mata bari ta shiga ciki tace Ok, tana juyawa Kamalu ma ya juya zai tafi da sauri Farhar tace "Hey..." dakatawa yay ya kalleta ta bishi da ido kaman bazata tanka ba bata san daurewa kawai yake yana kallon idonta ba, sai bayan ɗan lokaci tace mashi ya bugeta jiya amman bazai iya tambayar ya take ba, sai da ya haɗiyi abu sannan cikin kama kai yace tayi haƙuri yaga wurin kaman lafiya lou, ɗan yamutsa baki tay tace dole sai wuri ya fashe ne ko yayi alama zai yi ciwo girgiza mata kai yay yace "to kiyi haƙuri fatan wurin bai yi maki zafi" ɗan murmushi tay ta ɗaga mashi kai, shiru suka ɗan yi can tace mashi a Yola suke ko yace mata eh,

"kai ya baka zo Katsina ba?",

ya bata amsa da ai yanzu a Katsinar yake zaune, kai ta ɗaga sai kuma tace "can i know your name?" amsa ya bata da sunan shi Kamalu ta ɗan yamutsa fuska tace suna ne haka yana murmushi ya bata amsa da eh, gyaɗa kai tayi tace bata ta6a jin sunan ba ko nasu ne na fulani yar dariya yay har haƙoranshi suka bayyana gefen kumatun shi duk ya lotsa kamar yadda na Fatuu ke yi, tambayarta yay to tasan suna Kamal ta jinjina kai alamar ta sani yace to sunan shi kenan tace amman miyasa aka maida nashi haka ya bata amsa da haka ya taso ana ce mashi shiyasa tace ya hana ana ce mashi hakan Kamal yafi, ce mata yay ai an riga an saba yanzu zai wuya a bari tace Ok, wayar shi ce ta fara yin ringing ya ɗagota yana kallon mai kiran ganin Kawu Amadu ne yasa bai ɗaga ba ya kalleta yace bari yaje ana jiran shi ta furta Ok, har zai juya tace ya bata lambar shi idan wurin da ya buge mata na mata ciwo zata kira shi yazo ya kai ta Hospital daga yadda tay Maganar ya gane wasa take yana murmushi yace to, bayan ya bata tace zata kira yanzu sai yay saving yace Ok daga haka yay mata sai anjima ya juya ta bishi da kallo hakanan bata san miyasa ba komai nashi burgeta yake, yana zuwa wurinsu Amadu yace wai mi ya tsaya yi wurin wanccan Kamalun yace mashi ba komai tazo wurin Fatuu ne to shine tayi mata bayanin shi Yayanta ne Amadun yace to kuma shine sukayi tsaye bayan Fatun ta tafi, ce mashi yay ta tambayi sunan shi ne, kafin Amadu ya sake cewa wani abu Tk na yar dariya yace to Kodai ta ƙyasa da ɗan fillo ne Amadu ya ɗan ta6e baki yace da dai wata ba waccan ba har abada bai tunanin zata yi soyayya da talaka,

Tk yace "ka san abun Allah, ai dama irin su ta haka Allah ke kama su, da kuma abun ya bada kala É—an fillo da baturiya"

dariya Kamalu yay ya tambayi baturiya ce Tk yace Babanta ne bature yace ashe shiyasa yaga idanunta wani iri daga haka suka tafi, Bayan Fatuu ta koma ciki part ɗin data zauna lokacin data haifi twins ta nufa dama acan ta sauka Mino ma da Aysha da Safnah duk suna tare, a parlor ta iske Fauzy zaune dasu Safnah harda Mino ta miƙa mata hannu tace ta taso su shiga ciki, bayan sun shiga cikin Bedroom ɗin a saman gado suka zauna Fatuu na murmushi tace "Amaryar Ya Sameer bamu samu mun zauna ba inata son in tambaye ki ya amarci" ɗan ta6e baki tay tana murmushi tace ai yanzu amarci ya wuce Fatun tace duka wata ukkunne zata ce amarci ya wuce tace Uhmm kawai, hira suka cigaba da yi harda ta makaranta suna cikin yi Fauzy ta kai hannu ta ɗaukko jakarta dake a saman bedside data aje tun ɗazu ta buɗe, wata yar farar roba mai kyau ta fiddo tare da farin hanky ta maida jakar bayan ta daidaita zamanta ta latsa saman robar ya buɗe Fatuu nata kallonta a zaton ta wani abun ci zata fiddo kawai sai gani tay ta kai bakinta saitin inda ya buɗe ta zubda miyau kafin ta saki marfin ya rufe tasa hanky ɗin tana goge gefen bakinta, sakin baki Fatuu tay tana kallonta da alamun mamaki, kallonta Fauzy tay suna haɗa ido tayi murmushi tace mata ya akai ne, hannu Fatuu ta kai ta kama ha6a tace "Ke wai tsaya mi hakan da kikai ke nufi, ni nayi zaton ko Sweet ce zaki fiddo sai inga kin zubda miyau!" Dariya Fauzy tayi tace tun ɗazun yake damunta tana ta daurewa ta haɗiye saboda mutane, waro ido Fatuu tay ta buɗe baki da tsananin mamaki tace "Wai kaddai ciki gare ki Fauzy?" tana murmushi ta ɗaga mata kai alamar eh, hannu Fatuu tasa ta rufe baki sai kuma ta cire cikin washe baki tace "Ashe shiyasa naga kin ƙara haske sosae saidai kuma baki yi ƙiba ba sai ma ɗan ramewa da kikai ni na ɗauka duk amarcin ne yasa haka wllh" girgiza mata kai tay tace wahala ce don laulayi take sosae tayi mamakin ma yadda da tazo bikin ya rage sosae har abinci take ci acan ai ko abincin bata iya ci ga yawan amai har magani aka bata wanda zai sa ta daina aman in tana sha kullum to in ta sha sai ya rinƙa damunta in bata yi aman ba sai kawai wani lokacin ta ƙi sha, tambayarta Fatuu tayi watan cikin tace mata ɗaya da rabi,

"Kenan ma kice da kuka je Honeymoon kika same shi" kai ta É—aga mata tace saida yay sati ukku sannan suka san dashi ko Aunty Mareeya bata sani ba sai yanzu tana ganinta ta gane Fatun tace "Ni kinga wllh ban gane ba saboda banyi tunanin Ya Sameer É—in zai bari ki samu ciki da wuri ba daga yanayin shi",

"Aikuwa yay farinciki dana samu ni kaina saida nayi mamaki don ko Maganar haihuwa bai yi man nayi zaton bazai so cikin ba sai gashi baki ga yadda yake nan nan da ni ba, dafa wai ma bazai zo bikin nan dani ba Aikuwa nayi ta mashi kuka yace shi tsoron shi kada wani abu ya samu cikin nace mashi ai kema da cikin kika taho bikin ko shine yace to zai taho dani da yake kuma gaskiya bai son yaga damuwata yanzu kinga ya rude",

yar shewar dariya Fatuu tay tace "kice dai kin damƙe ya Sameer a hannu aikin Aunty Mareeya yayi kyau",

tana yar dariya tace "Aikin Aunty Mareeya ko aikin jawo ma mutum wahala ke wllh saida ta kai ina tsoron shi dana ji sallamarshi sai gabana ya faɗi har Aunty Mareeya na ta6a kira nayi mata complain taita ƙarfafa man gwuiwa daga baya dole na saba tunda naga yana son hakan sosae" Fatuu na dariya tace "kice dai Ya Sameer ya Magantu yadda Aunty Mareeya ke so" Dariya Fauzy ta saka tace wllh ita farko ma yay ta bata mamaki sai kace ba shi ba Fatuu dake ta dariya tace haka suke fa miskilan nan dama Aunty Mareeya ta faɗa ta haka ake jin bakin su,

"Amman dai ba wata matsala da kike fuskanta a wurinshi ko" Fatuu ta tambaya bayan sun gama yin dariyar, girgiza mata kai Fauzy tay tace "Wllh baida wata matsala gaba ɗaya yadda nayi tunanin shi ba haka ba, sosae yake sake man yana bani kulawa dana nuna inason abu sai yayi man in kuma na nuna banso shikenan, kamar farko kinga mata na kiranshi har ya amsa wayar a gabana tunda na nuna 6acin raina shikenan ya daina lokacin harda bani haƙuri don fushi nayi dashi duk ya ruɗe tun daga lokacin bai hana ni ɗaukar wayar shi da kaina nabi na goge duk lambar wata mace da saƙonni kuma bai ce man komai ba, ko tari nayi sai ya tambaye ni lafiya haka in ina wani abun yana taya ni duk da ba wani aiki ma nike ba da nace ya sallami mai mashi girki in rinƙa yi to yanzu saboda cikin nan ma yace ba za'a sallame shi ba harda mace ma ya ƙaro man da take man aikin gida",

tunda ta fara magana Fatuu keta faman sakin murmushin farinciki har ta gama tace amman taji daɗin labarin nan sosae wllh wani hanin ga Allah baiwa ne da bawa yayi haƙuri sai yaga ya kai matakin da bai ta6a zato ba,

"Bari Zarah, kullum cikin gode ma Ubangiji nike wllh don yayi man ni'imar da zatona bai ta6a zata man ba, wani lokacin cikin raina sai in ta raya yanzu da nayi rashin haƙuri lokacin da aka yaudare ni na illata kai na koma na halaka kai na da shikenan nayi asara biyu gata rasa wannan babbar ni'imar ga kuma rasa ta ubangiji" girgiza kai Fatuu tay tace idan mutum yay nazari sau da yawa abubuwa masu daɗi suna samuwa ne daga marasa daɗi ita kanta ji yadda al'amarinta da Ya Haisam ya kasance data yi haƙuri gashi tanata cin ribar hakan tuni ma ta manta da irin raɗaɗin data ji a wanccan lokacin, Fauzy tace hakane haƙuri kaɗan ke haifar da jin daɗi na har abada sannan rashin haƙuri kaɗan na haifar da dana sani na har abada, nima dai mai rubutun nace wannan haka yake Allah ya ƙara mana haƙuri Amin, Hira suka cigaba da yi cike da nishaɗi har Fatuu na mata Addu'ar Allah yasa ta haifi yan biyu tana dariya tace haka ma Aunty Mareeya tace amman ita tafi son ɗayan ma. Ana gama sallar Magrib aka fara shirin kai Mino Fatuu tasa ta canza kaya bayan tayi wanka zuwa lace baiwar Allah duk tayi zuru zuru Gwaggo tazo ta tafi da ita baya wurin danginsu don ayi mata Nasiha,, bayan an kawo motoci bakin entry hall aka sanar a fito Fatuu ce ta kamo ta suka nufo cikin babban parlon gidan lokacin su gwaggo ma duk sun fito suna biye dasu, bayan sun shigo Gwaggo ta kama Minon suka nufi part ɗin Mom harda su Yaya, a falonta duk suka zazzauna bayan an gaggaisa Gwaggo tace sun kawo amarya ne suyi sallama sannan su damƙa amanarta duk da sun san ko basu bada ba za'a ruƙe masu amanarta kamar yadda aka ruƙe ta yar uwarta sannan sai anyi haƙuri don zata iya yin wani abu ba daidai ba saboda ƙarancin shekarunta in tayi kuskure a nuna mata duk da akwae yar'uwarta saidai itama ba wata babba bace kuma ba lalle su kasance tare ba gaba ɗayansu dai duk sukai ba daidai ba a kwatanta masu don su gyara Mom na murmushi tace insha Allahu kada suji komai za'a ruƙe amana yadda yakamata sannan yadda suke nuna ma yaransu in sun yi ba daidai ba suma hakan za'a yi masu tunda suma tamkar Ya'yansu ne, sosae suka ji daɗin Maganarta sukai ta godiya tare da yi masu Addu'o'i daga baya suka fito don tafiya Mom ɗin tayo masu rakiya, cikin masu zuwa harda Hajiya Zainab da Hajiya dasu Aunty Mareeya da Feenah kusan duk mutanen da suka rage zasu je Motocin da aka kawo sun kai goma, bayan duk an shishshiga harda akwatunan kayan da Minon tayi amfani dasu waɗanda su Yaya suka taho dasu kuma da sauran kayan an kai su can gidanta, a tare Motocin suka fara tafiya suka tunkari gate, ba wata tafiya mai nisa sukai ba suka iso gidan dake a Asokoro dama gidan Senator ɗin a Maitama yake basu da nisa sosae, tun a bakin gate zaka fara shaida haɗuwar shi bayan mai gadi ya buɗe masu motocin suka kutsa kai ciki, wuri daban daban akai parking don asamu duk Motocin su shiga wasu a cikin parking space ɗin gidan mai ɗaukar motoci huɗu aka shigar dasu wasu daga can gefe gefe Motar da Minon take ciki har cikin entry hall aka shigar da ita, bayan an samu duk Motocin sun shigo aka bubbuɗe kofofin motocin aka fara fitowa nan fa aka shiga bin gidan da kallo waɗanda basu san shi ba, ba laifi gidan yana da girma tunda har harabar shi ta ɗauke duka motocin hasken Fitilu ko ta ina ga shukokin fulawoyi wurare daban daban a tsare sun sha gyara, daga bakin gate akwae ɗakin mai gadi sai ɗayan bangaren nan parking space din yake sannan gaba ɗaya harabar gidan malale take da interlock daga tsakankanin su anyi adon ratsin grass carpet, bangaren ginin gidan kuwa tun daga cikin entry hall aka malala tiles ga wata babbar fitilar sama mai matukar kyau a saman daga nan zaka shiga cikin gidan ta dakakkar ƙopar da ke a wurin, kana shiga ɗan passageway ne wurin shima akwae fitila a sama da kuma flower vases sun saka ƙopar shiga falon tsakiya ana buɗeta za'a shiga cikin parlon wanda babba ne yasha manyan labulai maroon da akai ma wani irin design mai ɗaukar hankali, gaba ɗaya parlon tiles ne ruwan madara kalar fentin falon daga tsakiya aka saka kujerun Mino wanda haɗaɗɗun royal ne brown da ɗan ratsin maroon an jere throw pillows, daga tsakiyarsu lallausan carpet ne brown tsakiyarsu an aje Ottomon kalar yadin kujerun daga angles ɗin parlon an aje flower vases da suka hau da kayan ciki sai bangaren wurin kayan kallo an manna babbar plasma ɗin da aka siya mata a jikin babban Tv stand mai drawers ta kwance da kuma ta tsaye shima cikin saitin kayan yake daga baki bakin shi anyi mashi irin design na adon da aka ma kujerun daga gefe da gefen Tv stand ɗin sound systems ne, iya wurin kayan kallon abun kallo ne, daga can bayan kujerun matattakalar hawa bene take anyi mata wani irin design ta lanƙwaya ƙarafan jiki silver ne sai ɗaukar ido suke itama matattakalar anyi mata fenti ruwan madara kalar na cikin parlon sannan an shimfiɗa carpet brown yabi jikin stairs ɗin har sama, daga gefen hagun benen Dining Area ce an aje dining table da kujerun shi guda haɗu suma mahaɗin kujerun parlon ne, daga can gefen shi nan aka aje standing freezer daga gaban shi anan ƙopar shiga Kitchen take daga jikin ɗayan bangon wurin wani haɗaɗɗan console ne golden manne daga gefe da gefen shi an aje flower vases sosae wurin yay kyau daga ƙasan Dining table ɗin nan ma lallausan carpet ne maroon da ratsin brown, daga tsakiyar parlon bayan kujerun corridor ne inda bedrooms suke guda biyu suna kallon juna da toilet a tsakiya ba laifi Bedrooms ɗin suna da girma a ɗaya Royal Bed ne Milk da wardrobe ɗin shi mai guda shidda a jikinta anyi adon madubi kana ganin kanka haka a jikin bedside din ma gaba ɗaya set ɗin kayan sun haɗu ba ƙarya wani irin design akai masu mai jan hankali a ƙasa an sa carpet milk, a ɗayan ɗakin kuma Simple Modern Bed ne Coffee brown da wardrobe ɗin shi mai gida hudu sai nightstands da dressing mirror daga gaban gadon an sa carpet coffee labulayan ɗakin ma coffee ne, kowanne ɗaki akwae toilet irin na zamani irin wanda ya amsa sunan toilet ɗin masu kuɗi komai na cikin shi fari da silver ne, a 6angaren Kitchen kuwa drawers ɗin ciki L-shape ne dark ash haka cupboards ɗin sama suma L-shape ne an tsara Kitchen ɗin shima yayi kyau sosai, Bayan yan kawo Amaryar sun shigo ciki nan fa aka hau jinjina haɗuwar gidan Gwaggo sai murmushin daɗi take haka Fatuu ma su Yaya da Kakar su Minon mamaki ne shimfiɗe akan fuskokinsu ganin wai wannan Aljanar duniyar Mino zata zauna gaba ɗaya sun kasa rufe bakunansu, yadda aka shirya komai yayi ma su Gwaggo kyau sai yabawa suke, a ɗaya daga cikin ɗakunan aka kai Mino inda keda Royal Bed su Aunty Mareeya suka fito suna ƙara dudduba gidan danginsu Nameer suma suna ta yabawa suna faɗin gaskiya anyi ƙoƙari da yake sunji Hajiya na magana kan kayan da akayin tana faɗin sun kashe kuɗi sosae hakan yasa suka gane danginta sukai mata kayan ɗakin hatta Hajiya Zainab saida tace gaskiya anyi ƙoƙari, har saman bene suka hau wanda nan part ɗin Nameer ne babban falo ne an zuba luntsuma luntsuman baƙaƙen leather chairs da ƙaton carpet baƙi da ratsin ruwan toka mai duhu da kuma mai haske sai labulaye suma baƙaƙe ne da ratsin ash akwae kuma kayan kallo harda freezer falon baida hayaniya amman yayi kyau sosae, Bedroom guda ɗaya ne mai ɗauke da set ɗin gado ɗan Dubai sai toilet ko ina dai yayi kyau sai yabawa ake, har bayan gidan suka je akwae wurin yin basket ball da kuma ɗan madaidaicin Swimming pool daga gefenshi kuma akwai rumfa ta shaƙatawa mai ɗauke da tebur da folding chairs irin wanda ake linkewa, bayan sun gama zazzagaya gidan Aunty Mareeya da Fatuu suka ɗaukko kwalin kayan adon da aka kawo suka fara jera su a jikin gidajen Tv stand wasu kwalaben turaren wuta ne an masu ado wasu kuma kayan ƙawata wuri ne kowanne aka sashi a inda ya dace sosae falon ya ƙara ƙawatuwa suka jona wata jigunannar burner aka saka turaren wuta nan da nan ƙamshi mai daɗi ya fara karaɗe parlon ya haɗe da sanyin A.c, su Amadu ne suka shigo da katan katan na lemuna da abubuwan ci suka aje a saman carpet Aunty Mareeya tace sannunsu abokan ango sukai murmushi kafin suka shiga bin falon da kallo suna murmushin daɗi don ya burge su Hajiya ce tace masu to su zagaya mana su gani da kyau suka ce to, zama sukai kan kujeru suka fara cin abubuwan da aka kawo ana ɗan yin hira Hajiya tasa Fatuu ta ɗiba ta kaima Mino da ƙawarta dake a cikin Bedroom, suna cikin ci Hajiya ta kalli Gwaggo tace wato Dije kwance kwance ashe kuɗi ne daku ko shiyasa kuka zuba ma Ameenatu kaya haka duk aka yi dariya Hajiya Zainab dake cikin cin Shawarma tana murmushinta na manya tace ba Fulani bane su Hajiya tace sune na asali ma tace ai dama kuɗi garesu da an saida shanaye sai kaga uban kuɗi duk akai dariya Gwaggo dai murmushi kawai take don an kashe bakin, bayan wani lokaci suka miƙe don tafiya wasu suka fita wasu kuma suka je yin sallama da Mino harda Gwaggo da Hajiya dasu Aunty Mareeya, ai tana jin zasu tafi ta ruɗe ta saka kuka duk tabi ta ƙanƙame Gwaggo aka hau bata haƙuri Hajiya tace Ameenatu sai kace an kawo ki gidan yari, sam taƙi jin rarrashi sai fullanci take tana ce ma Gwaggo don Allah kada a barta ita kaɗai su tafi da ita Fuskarta duk tayi jage jage da hawaye har saida tasa idanun Gwaggon suka ciko da ƙwalla ita Fatuu ma har sun fara zubowa Hajiya ta tambayi Gwaggo mi Minon ke cewa ne ta faɗi mata wai su tafi da ita tay ɗan murmushi tace ina su ina tafiya da ita ai nan gidantane tazo kenan tayi haƙuri zata saba, ganin taƙi jin rarrashi yasa Hajiya ta kira Nameer a waya bayan ya ɗaga ta tambayi yana ina yace gasu nan a harabar gidan tace to ya shigo ya samesu a Bedroom yace to, bada jimawa ba sai gashi ya shigo cikin ɗakin da sallama yana sanye da riga da wando na Farar shadda fuskar nan sai annuri take ga uban ƙamshi dake tashi daga jikinshi, gaishe dasu yay bayan sun amsa mashi Hajiya ta nuna mashi Mino tace gata nan yazo ya rarrashi matar shi ta hana su tafiya wai bin su zatai, kai idon shi yay kan Minon da tabi ta ƙanƙame Gwaggo ta kifa Fuskarta a jikinta, tsaye yay kawai yana kallon su Hajiya tace yaje ya kamata ko sun tafi in kuma so yake su kwana to still bai matsa ba don kunyar yaje ya kamata yake sai ɗan murmushi yake ganin haka yasa Fatuu ta kai hannu ta ɗago da ita suka haɗa ido tace mata ya isa ta daina kukan ita zata zauna tare da ita jin hakan yasa ta faɗa jikin Fatun Hajiya tace masu su tafi, bayan duk sun fita ya rage saura Fatuu da Safnah sai Nameer da hannu Fatuu tay mashi alamar yazo ya rarrasheta, Moving yay zuwa inda suke ya tsaya a gabansu cikin kwantar da murya ya kira sunanta shiru bata amsa ba bata kuma ɗago daga jikin Fatun ba, hannu ya kai ya fara ƙoƙarin ɗago da ita ta turje su Fatuu nata bata haƙuri ganin taƙi rabuwa da jikin Fatuu yasa shi nuna mata ƙarfi ya ɗagota da ƙarfi tana barin jikin Fatun da sauri ta kamo hannun Safnah suka nufi hanyar fita daga ɗakin Minon nata rizgar kuka tana ƙoƙarin kwacewa ta bisu hakan yasa shi haɗeta da jikin shi ya rungumeta tightly ya kai bakin shi saitin kunnanta a hankali ya shiga rarrashinta yana faɗin ba gashi tare da ita ba, sukuku Fatuu ta dawo duk tausayin Mino ya kamata daga baya ta sake suka shiga yin hira da Fauzy kowa na tuna lokacin da aka kai shi ɗakin miji Safnah dai har ta kwanta don itama jikinta yayi sanyi saboda yanayin da suka baro Aminiyarta, suna cikin yin hirar Sameer ya kira Fauzy ta ɗaga kiran, tambayarta yay tana ina tace gata nan sun dawo gidansu Ya Haisam yace Ok gashi nan zuwa zai dauketa tace to, bayan sun gama wayar Fatuu na murmushi cike da tsokana tace su Fauzy ana waya da miji an wani kwantar da murya dariya tayi tace ai saida hakan, faɗi mata tay zai zo ya ɗauketa ne Fatun tace maimakon tace mashi zata kwana anan su kwana tare Fauzyn ta ɗan buɗa ido tare da jinjina kai tace ai tasan ko tace haka ba lalle ya bari ba Fatuu tace bai iya kwana ba tare da ita ba kenan,

"Kusan hakan, kinsan fa koda muna London bayan mun dawo daga Honeymoon in zaije wani wuri indai kwana zai yi dani yake tafiya, ai Honey ba sauƙi sai da na samu cikin nan ne ganin ina wahala ake ɗan raga man" Fatuu na dariya tace ai hakan ake so a damu da kai sai ta dage taita gyara kanta don ma halin da take ciki ba komai zata iya sha ba Fauzyn tace eh tama daina shan wani magani Aunty ma tace a halin da take ciki ba sai tasha komai ba, bada jimawa ba Sameer ɗin ya kirata ya sanar mata gashi a gaban entry hall, tare da Fatuu suka fito tayo mata rakiya suna ƙarasowa gaban Motar ya buɗe Motar tun kafin ya idasa fitowa ƙamshin turarenshi ya karaɗe wurin, sanye yake cikin ƙananan kaya Fuskarshi tayi wani irin Fresh har yar ƙiba ya ƙara da yake wurin fayau yake da haske, bayan ya fito gaisawa sukai da Fatuu fuskarshi a sake yay mata ya hidima ta amsa da Alhamdulillah yace Allah yasa alkhairi, bayan ta amsa ya ambayi ina yaranshi tace suna wurin Mom yace a gaishe mashi dasu, maida idon shi yay kan Fauzy data jingina da Motar ta langa6ar da kai slowly yace "hope u'r Ok?" lumshe mashi ido tay ta ɗan ɗaga mashi kai yace to suje tare da yi mata alama da kai, tare suka zagaya ɗayan bangaren ya kai hannu ya buɗe mata ƙopar saida ta juyo ta kalli Fatuu dake tsaye tana ta murmushi ta ɗan ɗaga mata hannu itama ta ɗago mata sannan ta shige ya maida ƙopar ya rufe bayan ya zagayo driver side yayi ma Fatuu sallama ya buɗe ya shige, saida yaja Motar sannan ta juyo komowa cikin gidan tanata murmushin daɗi ganin yadda Sameer yake kulawa da Fauzy harda su buɗe mata ƙopa abunda bata ta6a zaton zai yi ma mace ba, bayan sun hau titi sosae ya juya ya kalli Fauzy data kwantar da kanta jikin headrest ya kai hannun shi dake gefenta ya kamo nata daga yadda take ta juyo da kan ta kalle shi yace mata ko jikin ne ta girgiza mashi kai alamar a'a ya sake cewa ko tana jin yunwa ne nan ma ta girgiza mashi kai yaci gaba da driving da hannu ɗaya ɗayan kuma yana ruƙe da nata can bayan wani ɗan lokaci ya sake juyowa ya kalleta ya tambayi ko tana son wani abu ta ɗan yi shiru kafin tace tana son ice cream yay ɗan shiru tare da maida idon shi kan hanya taji yace tana shan abu mai sanyi sosae ba ba'a son suna sha ba, ɗan yamutsa fuska tayi ta sigar shagwa6a tace to ai cikin ne yake mata zafi sai tasha abu mai sanyi take jin sauƙi ya jinjina kai, a bakin wani babban cold store ya parker tare da buɗe Motar yace mata yana zuwa ta ɗaga mashi kai, nufar shiga wurin yay tanata kallon shi ta glass wata irin ƙaunar shi na ratsata, After few minutes ya fito ruƙe da leda mai tambarin wurin ya dawo wurin Motar, bayan ya shiga ya miƙa mata ta amsa tare da furta "thank you Honey" jinjina mata kai yay ya ja suka tafi, bude ledar tayi ta fiddo roba ɗaya bayan ta buɗeta fara sha, tana cikin sha ta ɗebo ta kai bakin shi idon shi akan hanya ya buɗe ta zuba mashi bayan ya shanye ya furta mata "Love you Babes" tana murmushi tace "love you too Honey.....the best Husband ever" ɗan juyowa yay yayi mata wani kallo tana murmushi ta kashe mashi ido yay faffaɗan murmushi tare da maida idon shi kan titi bayan ɗan lokaci suka iso gidan su inda ya ta6a kawota.

Bangaren Amarya Laila tuni suka isa Kano aka ɗaukko su daga Airpot a cikin jigunannun motoci masu numfashi, gidan su Angon aka nufa dasu dake a Nasarawa G.r.a, katafaren gida ne daya amsa sunan gidan masu kuɗi sosae gari guda zagaye shi a ƙafa ba ƙaramin aiki bane an narka uwar dukiya tun daga kan ginin, gidan yana da part part da yawa don matan Mahaifin Angon nata ukku surukar Laila ɗin ce ta farko hakan yasa gidan suna da ɗan yawa, a part ɗin Momyn Bashir ɗin wanda ƙarshe ne wurin haɗuwa aka saukesu sun samu kyakkyawar tarba daga danginsu, bayan sun huta aka kawo masu lafiyayyun abinci da abubuwan sha, misalin karfe biyar aka shiga shirin yin buɗar kai da za'ayi anan cikin harabar gidan har an yi haɗaɗɗan decoration gidan ya ƙara cika da Jama'a harda anko aka yi, bayan duk an shirya Amarya Laila ma ta canza shiga haka su Jidderh duk sun canza kaya ba 6ata lokaci aka shiga gabatar da buɗa kan, Sai bayan isha'i aka gama An ci an sha an yi hotuna da Vedios Sosae aka nishaɗantu, ana gama yin buɗar kan aka fara shirin kai Laila gidanta wanda shima ke anan cikin G.r.a ɗin dama duk mazan gidan masu aure anan unguwar gidajen su suke don Mahaifinsu nada gidaje a cikin unguwar sosae wasu hayar su ake, jerin motoci ne aka kawo don ɗaukar yan kai Amaryar bayan duk an shishshiga a tare motocin suka tafi, ba wata tafiya akai sosae ba aka iso gidan tun daga wajen gidan zaka shaida haɗuwarshi, gaba ɗaya motocin saida suka shige cikin harabar gidan don babbane sosae an ƙawata cikin harabar da shuke shuken fulawoyi masu kyau da tsari ga hasken fitulu sun haske ko ina, bayan duk an firfito Aunty na ruƙe da Lailar Hajiya Maryam na daga gefe suka nufi shiga cikin gidan wanda ginin bene ne, sosae su Hajiya Maryam suka yaba da tsarin gidan ita Aunty dama sun zo da aka kawo kayanta duk da basu ne suka shirya mata kayan ɗaki ba masu shirya gida aka ɗaukko suka yi aiki su kawai umarni suka rinƙa badawa, gidan Laila sai san barka an kashe naira ba ƙaɗan ba wurin yi mata kayan ɗaki sai yabawa ake, idan nace zan bayyana yadda tsarin gidan yake to kuwa ba ƙaramin lokaci zan ɗauka ba kawai dai abunda zance shine gidan Laila ƙarshe ne wurin haɗuwa Aljannar duniya ne an zuba mata kaya na gani na faɗa sai fatan Allah yasa gidan zamanta ne na har abada, tare dasu Aunty aka dawo gidansu Angon aka barota ita kaɗai anan zasu kwana gobe in Allah ya kai mu su juyo Abuja.

Washe gari da Asuba Fatuu ta tashi don tayi salla su Aysha da Safnah ma da suka kwana anan ta tashesu, bayan duk sun gama komawa sukai suka kwanta don kowa a gajiye yake gashi yau su Safnah zasu tafi dasu Gwaggo amman banda Fatuu don Haisam yace nan zata tsaya, Fatuu bata daɗe da komawa ba har ta fara yin gyangyaɗi wayarta ta fara ringing ta kai hannu gefen filo ta ɗaukkota, koda taga mai kiran nata da alamun mamaki ta maimaita sunan Nameer a hankali ta furta "to lafiya???" gabanta har ɗan faɗuwa yake tay picking tare da ƙoƙarin tashi zaune, sallama tayi jin shiru bai yi magana ba bayan ta ɗaga sannan ya amsa ya gaishe da ita muryar shi ƙasa ƙasa bata ji komai ba don ya saba gaishe da ita, bayan ta amsa shiru yay bai ƙara cewa komai ba itama shirun tay tana jin fargabar abunda yasashi kiranta a wannan lokacin, jin baida niyyar magana yasa tace "Nameer lafiya kuwa ka kira kuma naji kayi shiru" tana jin sautin yar ajiyar zuciyar da yayi a hankali yace mata dama Don Allah wani taimako yake son tayi mashi da sauri tace to wane taimako taji yace zai zo ya ɗauketa yanzu in ba damuwa zasu je gidan shi, bugun da gabanta ke yi ne ya ƙaru cike da fargaba har muryarta ta bayyana tace mashi to amman lafiya kuwa shiru ya ɗan yi kafin yace mata lafiya lou ba wani abu bane Minon ce har yanzu keta kuka shine yake son taje ta rarrasheta, shiru Fatun ta ɗan yi tana juya abunda yace a ranta lokaci guda kuma zuciyarta ta raya mata wani abu da sauri tace mashi to yazo ya ɗauketan yace Ok gashi nan ma ya taho don Allah ta fito bakin entry hall da yazo sai su tafi bai son wani ya ganshi tay ɗan murmushi tace to, bayan sun gama wayar Haisam ta kira tana fara yin ringing ya ɗauka saida ta gaidashi sannan ta faɗi mashi zancen zuwa ɗaukarta da Nameer zai yi ya tambayeta lafiya tace haka yace mata lafiya lou Minon ce keta Kuka dama jiyan da ƙyar suka rabu yace Ok kafin yace ina su Abie tace bari ta kawo su nan wurin shi kafin ta dawo, Abie ta fara ɗaukkowa ta nufi part ɗin shi tana zuwa bakin benen suka haɗe da Haisam ɗin ya amshe shi ta juyo don ta ɗaukko Adam, sauri sauri ta canza kaya zuwa jallabiya tay rolling veil ta ɗauki purse bayan ta saka wayarta ta nufi ƙopar fita, tana fitowa daidai Motar Nameer ɗin na ƙarasowa yana tsayawa ta nufi gaba ta buɗe bayan ta shiga yaja suka tafi, yana sanye da brown ɗin jallabiya mai gajeran hannu gaisawa suka ƙara yi ba tare da ya kalleta ba daga haka basu ƙara cewa komai ba har suka ƙaraso gidan bayan an buɗe masu gate ya shiga a gaban entry hall ya parker Motar kusan a tare suka fito ya zagayo inda take ya ɗan kalleta tare da ce mata suje suka jera, saida yasa makulli ya buɗe kopar sannan suka shiga parlon tsaf dashi sai sanyin Ac mai haɗe da ƙamshi ke tashi, hanyar Bedroom ɗin suka nufa suna zuwa bakin corridor ɗin ya tsaya ta kalle shi yace mata ta shiga tana nan ciki, tambayar shi tayi a wane ɗaki take yace wanda suka barta jiya ta ɗaga kai tare da juyawa ta shige cikin corridor ɗin, a hankali ta tura kopar gabanta na faɗuwa ta leƙa kai, acan saman gado ta hango Mino ta takure guri guda jikinta lullu6e da duvet, a hankali tayi sallama ta shiga shiru Minon bata motsa ba ta nufi gadon, zama tayi a baki idonta a kanta har lokacin gabanta faɗuwa yake, kiran sunan Minon tayi shiru bata amsa ba hakan yasa ta ƙara ɗaga murya ta kirata lokacin Minon ta yaye duvet ɗin da sauri, koda Fatuu tay arba da fuskarta wani irin bugu da ƙarfi gabanta yay ganin yadda fuskar tay jajir ga idanuwanta duk sun kumbura haka la66anta ma sun ɗan kumbura sunyi ja kamar jini ya kwanta, yaye duvet ɗin tayi da sauri ta nufo Fatuu tana zuwa ta faɗa jikinta ta fashe da matsanancin kuka har sai da Fatuu ta ɗan runtse ido jin yadda jikin Minon yay zafi sosai, cikin fullanci take mata Magiyar don Allah ta tafi da ita gida kada ta sake barinta anan mutuwa zatayi gaba ɗaya a gigice take hakan yasa Fatuu ruɗewa ta ɗagota Fuska a yamutse take ce mata mi ya faru ta faɗi mata cikin kuka take faɗin Ya Nameer ne bai sonta mugu ne shi ashe bata ga abunda yayi mata ba so yake ya kasheta, cikin sheshsheka take Maganar jikinta sai 6ari yake Fatuu tay shiru ta bita da ido sosae take jin mamakin Maganar Mino a cikin ranta ta shiga raya badai Mino bata san miye aure ba, maidata tayi jikinta ta shiga ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi tana faɗin tayi shiru to in dai tana son ta tafi da ita ɗin aikuwa sai gashi ta daina sai ajiyar zuciya da take saukewa a jere, ɗagota Fatuu tay tana ɗan murmushi ta shiga goge mata ƙwallan fuskarta bayan ta gama bin ta tayi da kallo ta rasa ta ina ma zata fara fahimtar da ita can tace mata a Makarantar su ba'ayi masu bayani kan Aure ba, cikin disashshiyar murya Mino ta tambayeta islamiyya ko boko Fatun tace mata duka tace a islamiyya ana yi masu wa'azi kan mata ta rinƙa yima mijinta ladabi da biyayya kuma ta rinƙa nuna mashi soyayya sannan in ta haihu taba yaran tarbiyya mai kyau sannan a Boko a islamic studies anyi masu bayanin minene aure da kuma yadda ake yin shi, kai Fatuu ta jinjina kafin tace to ba'a yi masu bayanin yadda ake haihuwa ba tace anyi masu a cikin Biology a Reproduction Fatun ta tambayeta ma'anar shi ta faɗi mata harda ire iren shi, gyara zama Fatuu tayi don anzo inda take so cikin types ɗin ta tambayeta wanda ya shafi abunda take son ta sani tace tayi mata bayanin shi ta shiga yi mata tiryan tiryan, murmushi Fatuu tay tace to bata san haɗuwar da ake nufi in mace da namiji sun yi ba ake samun cikin da ta faɗa Minon tace mata ana nufin in akayi aure aka cigaba da soyayya, jinjina kai Fatuu ta shiga yi don ta fahimci da gaske Minon bata fahimci abunda ake nufi ba,

"Ba daga anyi aure ana soyayya ba ake samun ciki ba tunda in hakane ai kafin kuyi auren kuna soyayya miyasa baki samu ba, abunda ya faru tsakanin ki da Nameer shi ake nufi da in mace da namiji sun haÉ—u don haka ba laifi yayi ba, hakan kusan shine auren ma dole sai ana hakan zaki samu ciki kuma duk lokacin da hakan ya faru tsakanin ku lada zaku samu",
yamutsa Fuska Minon ta shiga yi idanunta cike da ƙwalla murya na rawa tace "amman Adda Fatuu da wuya fa sosae wllh har matuwa nayi na dawo" tana kai Maganar ta fashe da kuka kasa daurewa Fatuu tay saida tayi yar dariya tace ta suma dai ana mutuwa a dawo ne, Kuka sosae Minon keyi Fatuu ta zura mata ido bata ji mamaki sosae ba don tasan akwai ƙarancin wayewa a tattare da Mino gashi ita ba mai shiga mutane bace sosae kuma bata da shige ma ƙawaye wani lokacin kamar miskila haka take, ajiyar zuciya Fatuu ta sauke ta dafata tana faɗin to miye abun kuka ai ba ta dingi jin zafin ba kenan daga yanzu bazata ƙara ji ba, duk da haka taƙi daina yin kukan sai faɗin Allah bazata iya ba da wuya take,

"Aikuwa indai kika ce bazaki bashi hakkin shi ba sallamar ki zai yi ya auro wata" Fatuu ta faɗa ta ɗan ɗaure fuska hakan yasa Minon ta ɗan tsagaita kukan Fatun ta ɗage mata gira tace hakan take so ko ya saketa da sauri ta girgiza mata kai alamar a'a tace aikuwa indai tace gudunshi tace zata rinƙa yi abunda zai faru kenan tunda hakan shine auren don haka indai tana son cigaba da zama dashi dole ta daure a hankali zata saba, tana matsar ƙwalla take faɗin Allah kuwa azaba gareshi Fatun tace bata faɗi mata daga yanzu bazata ƙara jin zafin ba duk wadda take gani anyi ma aure dole hakan sai ta faru da ita taga suna baro gidajen auren nasu ne daga baya ake sabawa ko itama hakan ya faru da ita har Asibiti aka kaita da ɗinki ma za'a mata, waro idanunta da sukai luhu luhu tayi a razane tace ɗinki kuma Fatun tace eh wasu har aiki ake masu ai ɗinki in hakan ta faru dasu sai sunyi jinya kuma basu baro gidajen mazajen nasu saboda sun san dole sai hakan ta faru, wuri wuri tayi tana kifce kifcen ido ta daina yin kukan, tambayarta Fatuu tay ba'a kaita Asibiti ba da sauri ta ɗaga mata kai tace sai dae ko in da ta sume murmushi Fatuu tay tana kallon ta da sauri Minon ta sunkuyar da kanta can ta miƙe tare da kamo hannunta tace suje toilet, kokarin miƙewa ta fara Fatuu ta taimaka mata ai tana fara taka ƙafafun ta saki ƙara ta ƙanƙame Fatun ta fashe da kuka tana faɗin ƙafafuwanta sun karye Allah bazata iya tafiya ba Fatun tay yar dariya ta girgiza kai abu yazo ga su alanƙoso, duk da halin da Fatun ke ciki haka ta duƙa tace ta hau bayanta bayan ta haye ta miƙe da ita suka nufi toilet, basu daɗe da shiga ba Fatuu ta fito ta nufi wurin akwatunan Minon ta fiddo towel bata ɗaukar mata brush ba don ta ganshi a toilet ɗin, bayan ta dubata ta shiga taimaka mata sun ɗauki lokaci a cikin toilet ɗin kafin suka fito Mino na ɗaure da towel a ƙirji ta yafo short a kai ta dafo kafaɗar Fatun yanzu lafiya lou ta tako kafafun duk da a hankali take yin tafiyar, a bakin gado ta zaunar da ita ta nufi wurin kayanta tana faɗin yakamata a jera kayan nata, mai ta ɗauko da turarurruka da undies sai ta ɗauko mata doguwar riga mai kyau da gyalenta, da kanta ta shafa mata mai sannan ta bata undies ta saka bayan ta gama ta bata rigar itama tasa ta fesheta da turare harda roll on ta bata ta shafa, bayan ta gama shiryawa ta miƙe tace mata tana zuwa ta nufi ƙopar fita, parlor ta fito Nameer na zaune kan kujera duk lokacin nan yana ganin Fatuu ta fito ya miƙe da sauri ta nufo shi tana ɗan murmushi, a gaban shi ta tsaya tace mashi tayi mata abunda ya dace duk da jikin nata yayi tsami yakamata tun da wuri ta zauna ruwan ɗumi da sauri yace saida ya kira wani abokin shi likita ya faɗi mashi abunda yakamata to taƙi yarda ne data ganshi sai tayita yin ihu kamar taga Dodo har magunguna daya turo mashi yaje ya siyo amman ya rasa taya zai bata ya ƙarasa yana ɗan murmushin kunya itama yar dariya tay tace ina ruwan mino ta tambaye shi ina magungunan ya zura hannunshi cikin aljihun jallabiyarshi ya fiddo mata su, amsa tayi har zata juya sai kuma ta dakata tace mashi yakamata ta fara cin abinci don tasan bata rasa jin yunwa yace mata akwae su shawarma da kaza a cikin Fridge tace a'a mai ɗumi yakamata taci ta tambayi akwae kayan tea yace eh akwae komai a cikin store bari yaje sai ya haɗa mata, yana niyyar juyawa tace a'a bari tayi shi yaje wurin Minon yay ɗan yi jimm kafin ya tambayi lafiya lou yaje har saida yaba Fatun dariya tace ko ya fara jin tsoronta ne yay yar dariya yace kusan hakan, bayan taje Kitchen deep freezer dake ciki wadda Nameer ɗin ne ya siyeta don ba ita suka siya ma Minon ba anan dai suka ganta jiya ta buɗe, shaƙe take da vegetables da ɗanyan nama harda kaji jiya a rufe take shiyasa basu ga kayan ba, store ɗin ta nufa shima yau a buɗe yake sa6anin jiya da yake a rufe koda ta buɗe shi shima dankam yake da kayan Abinci ba abunda babu har saida Fatun ta jinjina kai tana murmushi ba 6ata lokaci ta ɗaukko abunda take buƙata ta fara yin aikin, ɗakin ya nufa gaban shi har ɗan faɗuwa yake don ba ƙaramin tada mashi hankali tayi ba, saida yay jimm a bakin ƙopar kafin ya kai hannu ya tura yasa kai tana jin an turo ƙopar ta ɗago kai ta kalli ƙopar suka haɗa ido, da yar sallama ya ƙarasa shigowa ya nufo gadon tana ganin shi ta yunƙura ta tashi zaune ta ɗan kalleshi kafin ta sadda kanta ƙasa yana ganin haka ya zauna bakin gadon idonshi a kanta ya furta "My Baby..." shiru bata amsa ba bata kuma ɗago ba saida ya ƙara kiran nata sannan ciki ciki ta amsa ya kai hannu ya kamo nata slowly yace fushi take dashi har yanzu a hankali ta ɗan girgiza mashi kai alamar a'a, ƙarasa hayewa yay saman gadon ya jawota jikinshi ya rungumeta yashiga bata haƙuri yana faɗin bai so yasa ta wahala ba amman ba yadda zai yi dole tay passing through hakan amman daga yanzu bazata ƙara shan wahala ba ta jinjina mashi kai, wani irin daɗi ne ya ratsa shi ganin ta saukko ya kwantar da kanshi saman nata tare da furta mata yana sonta sosae a hankali tace itama haka ya lumshe ido, bayan wani lokaci Fatuu ta gama haɗa masu Breakfast chips tayi masu da farfesun kaza sai ta haɗa tea, a saman babban tray ta jera komai ta ɗaukka don ta kai masu, a bakin kopar ta tsaya tayi sallama shiru ba'a amsa ba ta ƙara yi nan ma shiru hakan yasa ta aje tray ɗin tasa hannu tay knocking sai lokacin Nameer dake rugume da Mino bacci ya kwashesu yaji ya ɗago tare da cewa Yes hakan yasa ta shigo ta nufo gadon har lokacin Mino na a jikin shi tana bacci, a saman table ɗin gadon ta ɗaura ta kalleshi tana murmushi tace Ango gashi nan ta gama yace Ok bari ya tasheta sai ta bata tace shi bai iya batan yace yana son taci sosae ne in ita ta bata sai tafi ci tace to bari taje ta ɗaukko plate ta zuba mashi da tare ta zubo masu yace ba saura a Kitchen ne tace akwae yace ta bari zai je ya zuba ita sai suci tare tana dariya tace ango da zuba Abinci, shima dariyar yake yace da yaci sa'a ma daba shi ya dafa ba, bayan ya tashi Minon shi ya ɗauko table ɗin ya maido saitin da Minon take Fatuu ta zauna shi kuma ya tafi, a nutse ta shiga bata a baki tana ci can Minon tace itama ta ci tana murmushi tace zata ci ta fara ƙoshi tukun, ba laifi taci sosae itama Fatun taci bayan ta gama ta bata magunguna, cigaba da kwatanta mata rayuwar aure Fatun tay "daga yanzu kada ki ƙara gudun mijin ki kinji yar ƙanwata hakan ba kyau indai ya nemi hakkin shi kika hana Allah zai yi fushi dake mala'iku kuma su kwana suna tsine maki saidai idan baki lafiya sai ki faɗi mashi, ta hakane zaki kama zuciyar shi ya zama kullum kece a ranshi saboda hakane ma kafin auren kika ga ana baki wasu abubuwa kina sha don ki ƙara daraja a wurin shi ne ki kuma haɗa da biyayya ai Gwaggo duk ta maki bayani kan hakan, sannan ki dage da yin ado da kuma kwalliya nasan baki da matsala da wannan dama kin iya shafa jambaki da hoda to yanzun ne zasu yi maki amfani kinga dai mijinki tubarkallah ta ko ina yayi irinsu yan mata rububin su suke don haka sai kin dage ki rinƙa yi mashi abunda yake so sannan kisan irin kalar shigar da yafi so kina yi mashi...." da sauri tace mata ƙananan kaya yake so ya faɗi mata Fatun tace to ta rinƙa yawan saka su in yana gida ko kuma in tasan zai dawo amman kamar in tana sanye dasu tayi baƙi maza sai ta ɗaura after dress amman suma sauran kayan nata kada tace zata jubge su ta rinƙa sakawa akai akai tana cin gayu ba kamar ranar Juma'a Minon nata ɗaga mata kai bayan ta gama yin Maganar a hankali tace to ko ta canza kayan jikinta yanzu tasa wanda yake so ɗin fatuu tay murmushi tace a'a ta bar rigar tunda bata jin daɗi zata fi sakewa tace to, bayan sun gama yin Maganar tace mata ta kwanta ita kuma ta ɗauki tray ɗin kayan ta nufi ƙopa, lokacin data fita ba kowa a parlon ta wuce kitchen, wanke kayan da akai amfani dasu tayi tay tunanin tayi masu girki kafin ta tafi, tana cikin aikin girkin Nameer ya shigo tun yana sawo kai ƙamshin turarenshi ya karaɗe kitchen ɗin, da alama wanka yayi yana sanye da ƙananun kaya wanda da gani sababbi ne sumar shi tasha gyara sai salƙi take haka sajen shi, daga gefen ta ya tsaya ya aje tray ɗin kayan Breakfast ɗin yana murmushi yace "sannu da aiki Yayata ta kaina" wani kallo tay mashi tana murmushi tace na daɗin baki ko,

"Amman kinsan ai tun da kika zama Yayata nike girmama ki ko" ɗan ta6e baki tay yana dariya yace yanzu ma zai ƙara girmamata tunda ta mashi aiki tay dariya kafin tace ai biya zai yi da sauri yace ta faɗi ko nawa ne zai bata in ma baida su zai samo tace bada kuɗi zai biya ba alƙawari zai yi na bazai ma Mino kishiya ba yana murmushi yace in don wannan ne dama baida wannan ra'ayin itace kaɗai matar shi har ya mutu ta ɗan harare shi tace ita zai ma daɗin baki,

"Ba daɗin baki bane am serious mizai sa in ƙara Aure inada Ameenatu, tamkar rainonta zanyi fa lokacin da zan manyanta lokacin zata ƙara cika mace to mi zai burge ni a wurin wata" murmushi Fatuu tay tace wasa ma take mashi ita ai tana da kishiyar ko yace to shi da gaske yake daga Babynshi ya gama tace Allah ya barsu tare ya basu zaman lafiya da zuriya ɗayyiba ya amsa da Amin kafin ya tambayi mi zai tayata da shi tace ba komai duk ta cimma aikin ma sauran ƙarashe yace Ok tare da yi mata godiya ya juya ya fita, farar shinkafa da miya tayi sai coleslaw tayi farfesun yan ciki saida ta wanke komai data 6ata ta zuba abincin a cikin warmers masu kyau ta kai kan Dinning table, bedroom ɗin Minon ta nufa bata yi tunanin Nameer na ciki ba saida ta shiga ta ganshi rungume da Minon suna bacci tay murmushi ta wuce inda ta aje purse ɗinta ta ɗauka kafin ta fito, parlor ta dawo ta fiddo wayarta nan taga missed call ɗin Gwaggo har biyu, sake kiranta tayi bayan ta ɗaga sun gaisa tace ta kira bata kusa ne Gwaggon tace eh tayi tunanin hakan dama zasu tafi ne taga bata ganta ba suyi sallama saida suka fito ɗanta Haisam ke faɗi mata tana gidan Mino tace eh tare da tambayar yanzu sun tafi kenan tace mata eh gasu a Mota, fatan Allah ya tsare tay tace sai tazo, kafin suyi sallama ta tambayi ya Minon tana yar dariya tace lafiya lou dama taƙi kwantar da hankalinta ne tana ta koke koke amman yanzu ta kwantar da hankalin Gwaggo na murmushi tace ina ruwan Mino a hankali zata saba sukai sallama tace tayi ma su Yaya da Safnah Allah ya tsare tace to, bayan sun gama wayar tunanin zaman mi zata zauna yi tay hakan yasa ta shiga kiran Haisam bayan ya ɗaga tace in bai komai yazo ya ɗauketa pls yace Ok, after some minutes ya kira yace mata yana a harabar gidan ta miƙe ta nufi hanyar fita, saida ta buɗe kopar gaban Motar taga ashe harda su twins yazo da yake Motar tinted ce gaba ɗaya an yi masu wanka suna sanye da kaya iri ɗaya suna ganinta Adam ya washe mata baki Abie kuma yay mata ɗan murmushi duk suka miko mata hannu suna son ta ɗaukesu suna faɗin Momy, saida ta zauna sannan ta ruƙe su gaba ɗaya ya tashi Motar suka tafi, bayan sun hau hanya take ce mashi ashe su Gwaggo sun tafi ya ɗaga mata kai tace ta kirata har sau biyu bata kusa da wayar, shiru suka ɗanyi can ya tambayeta lafiya gidan Nameer ɗin tay faffaɗan murmushi idonta akan shi tace mashi laifi yayi ne shine aka kaita rarrashi Haisam ɗin ya ɗan buɗa ido tare da ɗage gira sai kuma yay murmushi ba tare da yace komai ba, suna cikin tafiyar take tambayar shi yaushe zata je Katsina ya bata amsa da Us zasu tafi tace bazata je sallama ba yace in tana so sai taje amman yana son zasu je Adamawa su duba jikin arɗo yaji su Dad ɗinta suna faɗi ma Dad ɗinshi bai lafiya, sosae taji daɗi jin zasu je tace mashi eh bai jin daɗi yace Ok cikin next week sai suje.

Bayan sallar Azahar su Aunty yan Kano suka dawo an cika su da abubuwan arzuƙi Jidderh harda kukan baro Aunty Laila duk tayi sukuku koda ana Maganar Lailar bayan sun dawo sai ta sake saka wani sabon kukan Hajiya na faɗin itama ba Auren zata yi ta tafi ba, Bayan sallar La'asar su Hajiya Maryam suka wuce lagos su Hajiya Zainab ma lokacin suka tafi harda Fauzy.

Alhamdulillah Yan Katsina sun isa lafiya sai fatan Allah ya huta gajiya, a ranar bayan sallar isha duk suna zaune a cikin parlon Gwaggo suna yin hirar bikin baka jin komai sai fullanci dake tashi su innarsu Altine sai zuzuta gidan Mino suke suna faɗin ai Aljannar duniya aka kaita, suna cikin yin firar Amadu da Kamalu suka shigo jin firar da suke ne yasashi kunna Vedio ɗin gidan Minon da yayi lokacin da suke zagayawa ya miƙa ma Yadikko ta fara gani, sakin baki tay da tsananin mamaki take kallon Vedio ɗin tana faɗin yanzu anan Minon take aka bata amsa da eh su Altine da basu je ba duk sun zagayeta sun saki baki galala suma suna kallo, ƙarshe dai kukan farinciki Yadikko ta saka ta hau gode ma Allah da kuma Gwaggo tana faɗin koda tayi aikatau a Abuja bata ta6a tunanin wani nata zai zauna a can ba balle kuma ƴarta, inna Mero matar arɗo ce tace hada halin kirkinta yaja mata yadda ta ruƙe ƴaƴan kishiyarta da Amana bata zalunce su ba ta ɗaukesu tamkar nata gashi nan hakan yayi mata rana tunda data zalunce su ba yadda za'ai Gwaggo ta ruƙa mata ɗiya har itama tayi aure gidan daula su Kakar Minon suka shiga faɗin hakane wllh Yaya kuwa duk tabi tasha jinin jikinta sai murmushin yaƙe take, suna haka wayar Kamalu ta fara ringing ya kai idon shi kan screen ɗin yaga baƙuwar lamba saida ya fito waje saboda hayaniya sannan ya ɗaga tare da yin sallama daga ɗayan bangaren zazzaƙar muryar mace ta amsa mashi tare da tambayar ya yake ya bata amsa da lafiya lou kafin ya tambayi wacece, farko shiru tayi kamar bazata tanka ba saida ya ƙara tambaya sannan tace kenan data amshi number ɗin shi tace zata kira yay saving bai yi ba kenan, jin haka yasa ya ganeta da sauri yace tayi haƙuri ya manta ne da yake lokacin jiran shi ake tace Ok kafin ta tambayi ya suka koma yace Alhamdulillah itama ya tambayeta sun koma ne ko suna Abuja tace mashi No sun koma, ɗakinsu ya nufa suka cigaba da yin wayar saidai itace ke fara yin magana sannan yayi harda tambayarshi game da karatunshi ya bata amsa da bayan ya gama Secondary acan garin su bai cigaba ba dalilin da yasa yanzu ya dawo nan kenan don ya cigaba har ma ya siya Jamb zai yi tace Ok tare da yi mashi fatan Akhairi yayi mata godiya daga baya tace mashi tana son zasu zama Friends in ba damuwa har saida ya jinjina Maganar a ran shi don baiyi zaton jin hakan daga wurinta ba jin yayi shiru tace ko bazai yi abota da ita ba, da sauri yace a'a zasu yi suka cigaba da yin wayar kafin daga baya sukai sallama ya tashi ya koma shago.

Ranar Juma'a lokacin sati guda da bikinsu Nameer Jirginsu Fatuu ya tashi zuwa Yola, a yadda Haisam ya shirya masu zasu sauka a gidan wani abokin Dad ɗin shi wanda shima Senator ne mai suna Buba daga nan sai suje garin su Fatun, bayan sun sauka wurin ƙarfe goma na safe Driver ne tare da ɗan mutumin mai suna Amir wanda zai yi shekara ashirin da biyar suka je ɗaukko su, kyakkyawar tarba suka samu daga iyalan mutumin harda shi aka saukesu a part guda cikin ƙaton kuma haɗaɗɗan gidan nashi anata so a ɗauki su twins sunƙi yarda, lafiyayyun abinci da abubuwan sha aka kawo masu bayan sun ci suka huta har lokacin sallar Juma'a yayi Haisam suka tafi Masallaci tare da Senator Buba da yaran shi maza, bayan sun dawo ne ya sanar mashi zasu tafi can garin su Fatuu yace ai yayi zaton zasu kwana su ƙara hutawa ya tambayi zasu kwana acan ne Haisam ɗin yace mashi ita zai baro ta can ta kwana biyu shi zai dawo nan yace tunda hakane yana ganin kaman yanzu lokaci ya ƙure kar suyi dare ya bari gobe tunda safe sai Driver ya kaisu yadda shima zasu gaisa sosae Haisam ɗin ya amince da hakan. Washegarin wuraren ƙarfe tara da yan mintuna sukai sallama da mutanen gidan suka tafi, tafiyar Awa guda sukai suka iso tun shigowarsu bakin garin Fatuu ta fara murmushin farinciki sosae tayi kewar garin don kusan fin shekara ukku rabonta dashi da yake yanayin damuna ya fara don wasu wuraren sun fara samun ruwa ciki harda nan garin hakan yasa ganyayyaki da tsirrai sun yi kore shar shar gwanin sha'awa ga makiyaya nata koro garken shanaye da tumakai za'a tafi kiwo, Haisam dake zaune seat ɗin gaba nata kallon garin bayan sun shigo Fatuu ce ke nuna ma Driver hanya yana bi har suka ƙaraso kopar gidan tace mashi nan ne, wasu dattawan mutane da a ƙalla zasu kai biyar na zaune a ƙarƙashin ƙatuwar bishiyar dake a ƙopar gidan wasu daga cikin su yan gidan ne ciki harda Mahaifin Fatuu daya zauna yana dakon zuwan su da yake da zasu baro Yola ta kirashi ta sanar mashi sai mutum biyu a cikin su duk yayyen shi ne sauran biyun kuma abokai ne, daga can gefen su yara ne ba masu yawa ba suna ta wasa, bayan ya parker suka buɗe ƙofofin Motar suna fitowa Mutanen dake zaune suka miƙe a kusan tare suka nufo su, cikin washe baki suka shiga yi masu sannu da zuwa Baffan su Fatuu dai murmushi yake idon Fatun na akan shi itama tana murmushin farincikin ganin shi, bayan sun gama gaisawa da Haisam itama ta gaishe su suna ta fara'a suka amsa mata duk wanda yay yunƙurin ɗaukar su twins sai su ƙanƙame jikin iyayen nasu da yake kowa na ɗauke da guda ɗaya, bayan an gama yi masu sannu da zuwa Baffan tare da yayun nashi sukai ma Haisam jagora zuwa ciki, suna shiga cikin soro su Aysha suka shigo da gudu suka nufi Fatuu suka ƙanƙameta cike da farinciki suke mata sannu da zuwa da fullanci Adam dake hannunta ya fara ta6e baki zai yi kuka don sun rungumeta Aysha ta ɗago tana miƙa mashi hannu ya ƙiya sai kallonta yake kaman mai son tuna ta don da bakin su Mino ya yarda da ita Fatuu ta rinƙa faɗi mashi kowacece da fulatanci sai gashi ya tuno ta ya miƙa mata hannu cikin washe bakin jin daɗi ta ɗauke shi, ganin an amshi Adam yasa tace ma Haisam yabata Abie kafin suka idasa shiga cikin gidan mutane duk an leƙo ana masu sannu da zuwa Fatuu ke amsawa shi kuma Haisam kai yake ta jinjina masu fuskarshi a sake.......

100

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

.........Bangaren da Arɗo yake aka kaisu can gefe da inda nasu Yaya yake an kewaye wurin da yar gajeruwar kanta daga cikin wurin harda siminti a ƙasa, shiga sukai cikin ɗakin wanda yana da ɗan matsakaicin girma akwae madaidaicin gado na katako yana da wardrobe mai gida biyu samantaa an ɗaura wasu tsofaffin akwatuna na fata dana ƙarfe akwae yan durowoyi na gadon sai wata yar kanta da aka ɗaura al'quranai da wasu littafan addini daga jikin bango kuma wanda ke shafe da siminti an rataye abubuwan fulani harda takubba a cikin gidajen su daga saman ɗakin anyi ceiling irin na da da ake yi da itatuwa ƙasan ɗakin kuma gaba ɗaya a rufe yake da ledar tsakar ɗaki harda ɗan madaidaicin carpet daga tsakiya wannan duk aikin Baffan su Fatuu ne don kullum cikin yi ma mahaifin nasu hidima yake dama kuma yafi duk yan uwan shi wayewa, lokacin da suka shiga Arɗon na kwance a saman gadon jikin shi sanye da riga da wando na yadi mara nauyi sai hula ha6ar kada a saman kan shi suna shiga ya fara ƙoƙarin tashi zaune bayan Baffan su Fatuu ya sanar mashi ga su Inna wuro da maigidan nata sun iso da yake yasan da Maganar zuwan nasu duba jikin shi, saida aka taimaka mashi sannan ya zauna Haisam na niyyar zama a saman carpet da sauri cikin muryarshi data disashe yace kar ya zauna nan Haisam ɗin bai ma ji abunda yace ba ya dai gane ta hanyar hannu daya ɗaga mashi hakan yasa ya dakata Arɗon ya kalli Baffan su Fatuu da fullanci yace ya ɗaukko masu darɗuman makkan shi a cikin kayan shi, Makkan da ya shekara kusan fin talatin da zuwa wasu Ƴaƴan shi ma basu san da yaje ba balle kuma su Fatuu jikoki, bayan ya ɗaukko dardumar wadda ba laifi bata ji jiki ba saboda ji yake da ita don ta shiga cikin tarihin zuwa makkan shi tana da girma, shimfiɗa masu yay a saman carpet suka ce ma Haisam ya zauna Fatuu ma ta zauna daga gefe suma Yayun Baffan dashi duk suka zauna daga gefe nan aka shiga ƙara gaisawa ya juya suka gaisa da Arɗo tare da yi mashi ya jiki a hankali yake amsawa Fatuu ma ta gaishe shi da fullanci tayi mashi ya jiki ya amsa yayi mata sunzo lafiya da tambayar ya suka baro sauran mutane duk ta amsa masu ya kalli su twins yace wannan sune Ƴaƴan nashi da bai sani ba tana murmushi tace eh ya miƙo hannu alamar a bashi su Babban ɗanshi wanda yana cikin wanda suka shigo shima ya manyanta sosae yana murmushi yace ai basu yarda da mutane duk da haka Fatuu ta miƙe da Abie tayi ma Aysha dake daga can bakin ƙopa alamar ta kawo Adam suka kai mashi su, kamar ma tsoron Arɗon suke duk sun waro fararen idanunsu tubarkallah suna bin shi da wani irin kallo daya miƙo masu hannu sai su ƙanƙame su Fatun ƙarshe saidai a hannun nasu ya gansu ya saka masu albarka harda tofin Addu'a yayi masu yace ma Fatuu kafin su koma zai bada magungunan kariya a rinƙa basu tace to, a nutse Haisam cikin cool voice ɗin shi ya tambayi an kai shi Asibiti ne don asan abunda ke damunshi Modibbo ya bashi amsa da sun kai shi Babbar Asibiti ta Jumeta anyi mashi gwaje gwaje an tabbatar ba abunda ke damunshi kawai shekarune to sun bada wasu magunguna sannan sun ce ya rinƙa samun hutu sosae to ya gama shan magungunan kuma yana samun isashshen hutun don ko zama a fadar shi ma bai yi yanzu shiyasa ma jikin nashi da sauƙi sosae, kai Haisam ya jinjina kafin yace yana ganin yakamata a kai shi Asibitin ƙwararru dake a Yola a ƙara mashi bincike sosae suka ce to shidai Baffan su Fatuu shiru yay saidai a ranshi yaji daɗin hakan da Haisam yace don ba yarda baiyi ba a kaishi can amman yayun nashi suka ce kawai 6arnar kuɗi ne tunda an tabbatar da lafiyar shi lau, nuna ma Fatuu wata yar ƙwarya dake a rufe da faifai Arɗo yay yace mata ga fura nan taba Haisam da sauri Baffanta yace mashi ya barta tashi ce yasha suma ga ta can an haɗa masu yanzu zasu je sai su sha ya ɗaga kai Modibbo yace yakamata suje an barsu ko ruwa ba'a basu ba Baffan yace to tare da miƙewa suka ce ma Haisam suje suci Abinci duk suka miƙe harda Fatuu,

Bayan sun fito bangaren su Fatuu suka nufa lokacin da suka isa Fatuu taji daɗin ganin yadda aka ƙara gyara wurin kai kace ba'a cikin gidan bane sai ma da suka shiga cikin parlor shima an ƙara gyarashi akan lokacin da tazo da za'a yi mata aure da Khalid, an sake mashi fenti na zamani haka kujerun ciki ma ba wanda ta sani bane an canza wasu manya abunda yafi burgeta shine yadda ƙasan falon aka sanya tiles daga tsakiya kuma an sa carpet haka jikin ƙopopi ma labulaye masu kyau ne harda abun maƙalesu a jikin bango ga kayan kallo harda freezer yanzu duk babu kwalliyar ƙorai da aka yi an kunna Generator fanka nata yi parlon tsaf yayi irin na yan birni, cike da farinciki Yadikko datai shiga mai kyau tana sanye da riga da zane na lace ta tarbe su tana masu maraba Fatuu ta nufeta ta ɗan rungumeta tana dariyar farincikin ganinta ta miƙo ma Abie hannu zata daukeshi yaƙi yarda Aysha ta miƙa mata Adam tana faɗin ga mai yardar nan sai gashi itama ya yarda ta ɗauke shi, bayan duk an zauna aka shiga gaisawa tare da yi masu an zo lafiya fuskar Haisam a sake yake amsawa yayi mata ya mai jiki bayan ta amsa ta tambayi mutanen gidansu duk yace mata Alhamdulillah suna gaishe su, basu daɗe da zama ba aka fara zuwa gaishe da Haisam tare da yi masu sannu da zuwa tun yana amsawa har ya koma yana ɗaga kai don sai zuwa suke Manya da yara ba alamar zasu ƙare saida Baffa yayi magana kan a bari su ci Abinci sai a zo a gaisa sosae sannan aka tsagaita da zuwa, kwanonin Abinci da ƙurai aka shiga kawo ma baƙi duk aka jere su anan tsakiyar Parlon Yadikko ta kawo masu ruwa da lemu masu sanyi da kofunan glass duk ta zuzzuba masu ta basu ta juya ta nufi cikin ƙuryar ɗaki bada jimawa ba ta dawo ruƙe da babban tray mai ɗauke da plates da cokulla da serving spoon sai Warmers guda biyu Aysha ma na biye da ita da wasu kulolin abincin Masu kyau babba da ƙarama suka aje a saman carpet bayan Yadikko ta miƙe tay ma Fatuu alamar tazo ta nufi ƙurya Fatun tabi bayanta, bayan sun shiga tace mata yanzu ya za'ai Haisam ya saba cin abinci a saman table gashi babu wai ko a ɗauki drawer ɗin gado sai a ɗaura mashi sama Maganar dariya taba Fatuu tace mata ai lafiya lou yana ci a ƙasa Yadikkon ma dariyar take tace yauwa to shikenan,

"Baki tambayi Mino ba" Fatuu ta faɗa tana murmushi, ɗan yarfa hannu Yadikko tayi tace tana son ta tambaya wai kada aga tayi rashin kunya ta tambayi tana lafiya ita da mijin nata Fatuu tace eh sunyi waya ta gaya mata zasu zo harda cewa wai don Allah a taho da ita tace waye zai yi wannan haukan duka sati guda da yin aure ta marairaice mata kaman zata yi kuka tace ai ko kukan jini zata yi bazasu zo da ita ba, Yadikko dake dariya tace ai lalle kam kafin da sauri tace taje ta zuba ma Haisam Abincin tace to ta juya ta fita, miƙewa Baffansu yay yace ma Aysha taje tace ma Yadikko ta zubo ma wanda ya kawo su abinci sai ta kawo mashi waje tace to yace ma Haisam bari ya barsu suci Abinci Fatuu ta kalleshi tana mashi murmushi shima shine akan fuskarshi ya juya ya fita, a saman carpet suka zauna Fatuu tay serving nasu abincin wanda shinkafa da miya ne sai kuma burabusko sai gasassun zabbi cikin miyar abincin an cacca6a nama sai uban ƙamshi ke tashi, ba laifi Haisam yaci abincin sosae ba kamar burabuskon yayi mashi daɗi harda ce ma Fatuu bata ta6a yi masu irin shi ba tay yar dariya tace tunda yayi santi daga yanzu zata rinƙa yi yay murmushi ba tare daya ce komai ba su twins ma da alama yayi masu daɗi sai cin shi suke Aysha na daga gefe tana ba Adam ita kuma Fatuu tana ba Abie, bayan sun gama Aysha da Fatuu suka kwashe kayan suka kai Kitchen bayan sun dawo cikin parlon Yadikko ta fito masu da Fura a cikin jug dama ita take haɗawa a cikin ɗaki da kanta ta zuba ma Haisam yana ɗan murmushi yace mata ya ƙoshi yaci abinci sosae tace ya zai zo ruga bai sha fura ba yace to a bari kafin ya tafi zai sha jin haka yasa da sauri tace wai badai yau zasu koma ba cikin cool voice ɗin shi yace a'a shine zai koma Yola ita tana nan sai gobe zai dawo su tafi tace yauwa to Aysha ma ta washe bakin murna, miƙa ma Fatuu furar data zuba tayi tace ita to tasha ta amsa Aysha tace a zubo wata taba Adam, sosae Furar tayi daɗi don harda zuma aka sa ga dawon sabo ne haka nonon ma Fresh ne Fatuu nasha tana ba Abie duk ya 6ata saman bakin shi da ita harda su tanɗe baki yana yin ɗan sauti sai dariya yake basu cike da tsokana Yadikko ta kai hannu tace a bata furarta tunda bai yarda da mutane amman ya iya shanye masu abu yana ganin Fatuu ta miƙa mata cup ɗin ya fara ta6e baki zai saka kuka da sauri Yadikko ta maido mata tana dariya tace sak irin yadda take kuka da ƙuruciyarta haka suma suke yi Fatun tay murmushi ta ɗan saci kallon Haisam suka haɗa ido ya ɗan yi murmushin gefe tare da juyar da idon shi, Fatuu ce ta tambayi Yadikko ba'a samun wuta ne taga sai generator aka kunna tace wutar lantarkin ce ke yawan samun matsala daga can titi da aka jawo ta in ta lalace sai su daɗe babu ance wai ko zata daidaita sai ansa transformer anyi babban aiki ta jinjina mata kai, Baffan su Fatuu ne ya dawo yace ma Haisam ya fito yayi alwala lokacin salla ya ƙarato yace to tare da miƙewa ya kaishi ɗakin shi da shima yake tsab ga toilet a ciki ya nuna mashi yace akwae ruwa aciki zai jirashi a ƙopar ɗaki, a ƙopar gidan inda aka saba yin salla sukayi bayan angama akai ta gaisawa da Haisam ana ma mutane bayanin ko wanene daga baya suka dawo cikin gidan tare da Baffa lokacin Yaya da Mero da sauran manyan mata iyaye suka shigo gaisawa dashi Yaya nata washe baki tace ai sun bari su huta ne su twins dai sai dae a kalle su, wuraren ƙarfe ukku Haisam yace ma Fatuu yana son suje gidan Alhaji Lawal su gaisa dashi sai a maidota shi kuma ya wuce tace to, shiryawa tayi ta canza kaya su twins ma ta canza masu sannan suka tafi harda Aysha ta riƙe Adam. Lokacin da suka je Alhaji lawal ɗin na nan da yake Weekend ne sosae suka nuna farincikin ganinsu a falon Alhaji lawal aka saukesu Hajiya Rabi'atu na murmushi tace wannan zuwan bazata haka ba'a sani ba balle a shirya tarbarsu sosae suna murmushi suka ce mata ai ba komai, ruwa da lemu da Abinci aka kawo masu duk suka ce a ƙoshe suke Alhaji Lawal yace bai yarda ba ya za'ai suzo gidan shi suƙi cin abinci ƙarshe saida suka ci kaɗan, koda Alhaji Lawal yaji zancen tafiyar Haisam Yola sai yace ya bari mana su kwana gaba ɗaya anan gidan sai shi driver daya kawo su ya koma tunda nan akwae driver koda zasu buƙaci fita, da yake Haisam ɗin bai cika son kwana ba tare da Babynshi ba sai dole gashi kuma sun nuna suna son ya kwana bazai iya gardama masu ba sai ya amince da hakan, bayan anyi sallar La'asar Alhaji lawal yace ko zasu zagaya suga gari driver ya kai su Haisam ɗin yace ba sai Driver ya kaisu ba bari yay driving ɗin da kan shi, cike da zolaya Alhajin yace kada fa ya 6ace a garinsu Senator ya turo masu bataliyar sojoji Haisam ɗin yay dariya yace bazai bace ba tunda yana tare da yar gari, tare da Fatuu da Aysha suka fito Haisam ne ke tuƙa Motar suka shiga cikin garin Jumeta, bayan sun zagaya garin can da Yamma suka nufi ruga, lokacin da suka shiga garin makiyaya mata da maza cikin shiga ta fulani nata dawowa daga kiwo suna sanye da kayan fulani dabbobi ko ta ina suna ta 6ullowa, juyawa Haisam yay ya kalli Fatuu da turanci ya tambayeta itama tayi irin haka tay dariya tace ita fa yar lelen Baffanta ce duk irin wannan abun bai bari tana yi ko tallar Nono da yan matan gidansu ke yi lokacin ita bata taba yi ba, murmushi yay idon shi akan hanya yace ai ko don kada ta jawo mashi rigima ya hana tayi Fatun ta kyalkyace da dariya, ta bayan gidan su tasa su bi tace zata nuna mashi ƙoramar dake wurin, bayan sun je wurin parker Motar yay duk suka fito suka shiga zagaya wurin ruwa nata gudana ga wani irin ni'imtaccen sanyi ga bishiyun kayan itatuwa da sukai ma wurin ƙawanya duk sun nuna gasu ƙasa ƙasa Fatuu tace bari ta tsinko masu Haisam ɗin ya hana tasa Aysha ta tsinko masu itama yace ta bari kada wani abu ya cije ta tana dariya tace mashi ai suna zuwa ba abunda ke samun su sannan ya bari, basu daɗe a wurin ba harda hotuna yay masu suka tafi saboda yamma tayi sosae, wata hanya Fatuu ta nuna mashi tace su bi nan zasu 6ullo ta ɗayan gefen gidan, suna zuwa wani wuri jikin gidan nasu da sauri ta ɗaga hannu tana nuna mashi wurin tace ya ganshi ya ɗaga mata kai tace to a daidai nan ne ta ta6a yin shuka har ta jefe ma Jibo Akuya har baisan lokacin da yay dariya ba har haƙoranshi suka bayyana don ta tuna mashi ranar data bashi labarin Akuyar itama dariyar take Aysha dai bata san akan mi suke magana ba, lokacin da suka iso gidan ƙopar gidan cike yake da mutane wurin sai kace yar yara, bayan ya parker Motar suka fito cikin mutanen da ke zaune a ƙopar gidan harda Baffa da yau yaƙi zuwa ko ina saboda zuwan su suka taso suka tarbesu Fatuu da Aysha suka wuce ciki shi kuma a nan ya nuna zai tsaya shima aka bashi wurin zama bayan sun shiga ne Fatuu ke faɗi ma Yadikko zancen kwanan da zasu yi a gidan Alhaji Lawal, anan sukai isha suka ci Abinci harda wata sabuwar Fura aka dama masu mai sanyi sai gashi duk sun fi shan furar ma akan Abincin shima Haisam sosai tayi mashi daɗi su twins kau ba'a Magana hannu bibbiyu suka ruƙe cup suna sha duk sun ƙara yi ma bakin su dama dama sai tanɗan baki suke ana dariya sai gashi suma an sasu yin dariyar Yadikko har tana ce ma Fatuu kodai bata basu Fura ne tace mata eh gaskiya don lokacin da suka fara cin abinci basu ƙasar sai da suka zo bikin nan kuma lokacin da aka sha Furar a gidan Gwaggo basu gidan Yaddikon tace to gaskiya a rinƙa basu tunda dai sun gani da idon su suna so, kallon Haisam Fatuu tay ta tambaye shi a US ana samun Furar kuwa ya bata amsa da baza'a rasa ba tunda ana samun abubuwan mu na nan sosae saboda akwae mutanen mu acan shima Furar ba'a rasa masu yin shi suna saidawa in suka koma zai bincika Yadikko tace yauwa gaskiya asamo ma angwayenta Fura harda cewa don ma nesa bata maganin kusa ai da ta rinƙa yin Furar tana aika masu can don tasan koda an samu sai tata tafi daɗi duk sukai yar dariya, wurin ƙarfe takwas da rabi suka fito zasu tafi gidan Alhaji Lawal Fatuu ta ɗaukko jakar kayanta sukai sallama dasu kan sai gobe, har bakin Mota Baffan su Fatuu ya rako su har yana ce ma Haisam zai gane hanya cikin daren nan ko ya rakasu sai ya dawo yana murmushi yace mashi lafiya lou zai gane yayi mashi godiya sukai sallama, suna kan hanya ne Fatuu ke tambayar shi yanzu ya za'ai baida kayan baccin da zai saka tunda kayan shi na Yola yana murmushi yace mata sai ta bashi cikin nata yasa ta kyalkkyace da dariya tana faɗin in yana so sai ta bashi in dai zasu shigeshi, tun akan hanya su twins sukai bacci Fatuu na dariya tace Fura tayi aiki yay murmushi, bayan sun iso a harabar gidan suka iske Alhaji Lawal ɗin zaune kan kujera hannun shi ruƙe da Jarida yana ganin su ya taso ya nufo Motar bayan duk sun fito yana murmushi yay masu sannunsu da dawowa yace ai zaman dakon jiransu yake don da basu dawo ba yanzu bin sahun su zai duk sukai dariya tare da gaishe shi, tare suka shiga cikin gidan Hajiya Rabi'atu ta tarbesu, a part ɗin baƙi aka saukesu yana da parlor da kuma Bedroom an gyara masu shi tsaf sai ƙamshi da sanyin Ac ke tashi Hajiya Rabi'atu ta nuna masu kayan abinci da aka jere kan dining table tace gashi nan sai suci in sun huta harda tambayar ko a turo wadda zatai Serving nasu Fatuu tace a'a lafiya lou zatayi, duk da ba wata yunwa suke ji ba saida suka ci lafiyayyun abincin da aka yi masu saboda ɗazun da suka zo basu wani ci sosae ba, suna cikin cin Abincin Alhaji Lawal ya shigo cikin parlon hannunshi ruƙe da wata babbar farar jakar siyayya ya nufi kan kujera ya aje daga nan inda yake yace ma Haisam gashi nan yayi amfani dasu yace to tare da yi mashi godiya, bayan sun gama cin Abincin ya duba kayan ciki wanda kayan bacci ne kala biyu na maza sai kuma ɗinkakkun shaddoji suma kala biyu farare da brown kamar Alhajin yasan irin dinkin da yake so don gaba ɗaya kayan irin ɗinkin ne sai wasu yan ƙananun kwalaye guda biyu nan kuma agoguna da links ne a ciki harda biro akwae kuma kwalayen turarurruka guda biyu gaba ɗaya kayan sunyi kyau da ganin ba ƙananun kaya bane, bayan sun gama duba kayan ya kalli Fatuu cikin cool voice ɗinshi yace ba rabon yasa kayan baccinta kenan ta faɗa jikinshi tana dariya ya haɗa da ita da ledar ya sunkuceta suka nufi Bedroom.

Washe gari misalin ƙarfe goma saura gaba ɗayan su sunyi wanka suna parlon Alhaji Lawal suna yin Breakfast tare Fatun na ruƙe da Abie Hajiya kuma na ruƙe da Adam ta samu yanzu ya yarda da ita dama shi in dai zaku wuni tare to zai fara yarda da kai, baka jin komai sai ƙarar cokulla sunyi nisa a cikin cin Abincin suka ji anyi sallama cikin parlon a kusan tare duk suka kalli entrance, wani irin bugu gaban Fatuu yay da tayi arba da wanda ya shigo ba kowa bane face Khalid yana sanye da ƙananun kaya idanunshi na sanye cikin farin glass irin nasu na likitoci har yanzu dai yana nan yadda yake bai yi ƙiba ba, da sauri ta kauda idonta daga barin kallonshi ya nufo dining area ɗin yana ta sakin ƙamshi, bayan ya ƙaraso a gefe ya tsaya kusa da Dad ɗinshi ya gaishe da shi ya amsa tare da ce mashi yazo lafiya da tambayar iyali duk ya amsa mashi kafin ya kai idon shi kan Hajiya yana ɗan murmushi ya furta "Mom, Good Morning" itama murmushin take ta amsa mashi tare da tambayar Matar shi da kuma ɗiyar shi Zarah ya amsa mata da suna lafiya suna gaishe ta, tace maimakon ya taho masu da Zarah still murmushi yake yace lokacin da zai taho bata tashi ba ta jinjina kai, a cikin ran Fatuu ta shiga maimaita sunan ɗiyar shi da aka faɗa tana kokonton dalilin saka sunan, Alhaji ne ya nuna mashi Haisam da idon shi na kan Abincin gabanshi kamar bai ma ji shigowar Khalid ɗin ba yace mashi "ga baƙon mu mijin ɗiyata Fateema" kai ya jinjina Alhaji ya kalli Haisam yace mashi ga babban ɗan shi Khalid su gaisa sai lokacin ya ɗago fuskar shi a sake kafin yace wani abu Khalid ya miƙa mashi hannu ya aje cokalin hannunshi shima ya bashi nashi suka gaisa yayi mashi anzo lafiya Haisam ya amsa mashi da lafiya lou, bayan sun gama gaisawar maida idon shi yay kan Fatuu da taki ɗago kai ta kalle shi ya furta "Fateema an zo lafiya" damm gabanta ya faɗi ta haɗiyi abu saida tay ƙoƙarin daidaita natsuwarta sannan ta ɗago tana yin ɗan ƙaƙalallen murmushi ta gaishe dashi da ƙyar ya amsa don saida gabanshi ya faɗi ganin yadda ta koma saidai bai bari an fahimci wani abu ba, tana gaishe dashi da sauri ta janye idonta daga kanshi, kallon Abie dake hannunta yay yace "Wannan yaran mu ne?" kafin ta bashi amsa Mom ɗin shi ta riga ce mashi eh twins ne ta nuna mashi Adam dake hannunta ya jinjina kai tare da kai hannu zai amshi Adam da yake Mom ɗin na kusa dashi Adam ɗin ya ƙanƙameta alamar bazai je ba Mom tace mashi suna yin ƙyuya ne sai sun saba da mutum suke yarda ya ɗaukeshi yana murmushi ya furta Ok, Dad ɗinshi ne ya nuna mashi seat da ba kowa yace yay joining nasu yasan ƙilan bai yi Breakfast ba tunda da wuri ya taho, gaba ɗaya Fatuu ta takura zaman Khalid a wurin da ƙyar take cin Abincin can ta saci kallon Haisam taga idon shi na kan Abincin gabanshi tana son ta gane yanayin fuskar shi amman ta kasa, Khalid bai daɗe da zama ba Haisam ya miƙe duk suka kalle shi Alhaji yace badai har ya ƙoshi ba yana murmushi yace mashi eh yace to amman ai kamar bai ci sosae ba still da yanayin murmushi ya bashi amsa da yaci da yawa Alhajin yace shikenan ya manta ma Yan gayu basu cin Abinci sosae Haisam ɗin yay yar dariya haka ma Hajiya Rabi'atu Khalid kuma murmushi yayi Fatuu kam bata ma ɗago ba balle aga yanayin fuskar ta, bayan tashin Haisam wurin duk sai taji ta ƙara takura sau biyu tana satar kallon Khalid taga ita yake kallo abunda bata sani ba dana sani kawai yake acikin ranshi don ganinta ya fama mashi babban tabon sonta dake cikin zuciyarshi sai kallon su twins yake yana raya ƙilan da yanzu su yaranshi ne, gaba ɗaya Abincin ya fice ma Fatuu arai haka shima Khalid ɗin ba don yana jin daɗin shi ba yake ci, Haisam bai daɗe ba da tashi itama ta miƙe Dad yace wato Romeo ya ƙoshi shine itama Juliet zata tashi Fatun tay yar dariya kafin tace ta ƙoshi ne, cikin parlon ta nufa inda Haisam ke zaune yana latsa waya, Bayan sun gama cin Abincin gaba ɗaya a falon aka zauna ana hira jefi jefi Haisam ke saka baki anan ma Fatuu ta lura da yadda Khalid ke fakaitar idanun mutane yana kallonta cikin sa'a bayan ɗan wani lokaci Abie yay bacci ta miƙe tace zata je ta kwantar dashi, bata daɗe da tafiya ba shima Adam yayi baccin Hajiya ta bita dashi ya rage saura Alhaji da Khalid sai Haisam suka cigaba da yin hira wadda yawanci akan aikin su ne suna cikin haka Haisam ya roƙi Khalid kan yana son ya shige ma su Baffan Fatuu gaba zasu kai Arɗo Asibitin da yake aiki a duba shi sosae yace mashi ba matsala, suna zaunen har lokacin sallar Azahar yayi Dad yace suje suyi kafin su tafi Haisam ya kira Fatuu a waya yace ta shirya da sun dawo daga salla zasu je can ruga suyi bankwana dasu sai su koma Yola ƙarfe biyar jirginsu zai tashi zuwa Abuja tace to, suna dawowa sallar ya sanar ma Dad zancen zuwa rugar yace Ok amman zasu dawo ta nan ko sai Driver ya kai su Yola ɗin Khalid na jin haka yace bari suje rugar tare sai ya duba jikin arɗon in sun dawo sai su wuce Yolar tunda shima komawa zaiyi Alhaji yace yauwa to hakan yayi, Part ɗin da aka sauke su Haisam ya wuce don ya shirya lokacin daya je Fatuu har ta gama shiryawa cikin doguwar rigar shadda ta saka sarƙa da yankunnan Diamond su twins ma ta saka masu ƙananun kaya iri ɗaya, yana shigowa ta nufeshi tana murmushi ya buɗe mata hannu yay hugging nata can ƙasan maƙoshi ya furta mata "I luv you with every single beat of My Heart Baby" lumshe ido tayi jin yadda hucin Maganar ya bugi kunnanta, shiru yay yana breathing a hankali can ta ɗago da fuskarta ta kalle shi sai taga kaman wani yanayi da bata sani ba akan fuskar shi, tambayar shi tayi ko da wani abu a hankali ya lumshe ido tare da ɗan girgiza mata kai daga haka yay pecking goshinta ya saketa yace bari yay wanka, juyawa yay ya nufi hanyar toilet tabi bayan shi da kallo can ta ɗan ɗaga murya tace "....Know dat am breathing because of you Hubby" dakatawa yay ya juyo yay mata murmushi itama shi tayi mashi kafin ya juya, zama tayi a bakin gado tay shiru kamar mai nazarin wani abu, bai daɗe ba ya fito sanin tafiya zasu yi ita ta taimaka mashi ya shirya yasa brown shaddar cikin wanda Alhaji ya kawo mashi sosae ta hau jikinshi ita ta ɗaura mashi agogo ta saka mashi links ta feshe shi da turare yanata mata murmushi, bayan sun gama shiryawa sun tattara komai suka fito kowa na ɗauke da yaro guda abun gwanin sha'awa, koda su Alhaji da Hajiya suka gansu saida suka yi santin kyaun da sukai Khalid dai murmushin karfin hali kawai yake shi kaɗai yasan mike faruwa a cikin zuciyarshi, har bakin Mota su Alhaji suka rako su sukai masu sai sun dawo, tunda suka hawo hanya Fatuu bata bari ta kalli saitin Khalid ba shi ke driving ɗin Haisam na a kujerar gefe ita kuma tana baya saitin kujerar Haisam, bai wuce sau ɗaya zuwa biyu ba sukai magana shida Haisam har suka iso, a tare gaba ɗaya suka je ɗakin Arɗon bayan sun gaishe shi Khalid ɗin ya shiga dadduba shi tare da yi mashi tambayoyi da fulatanci yana bashi amsa bayan ya gama ya faɗi ma su Baffan su Fatuu ranar da zasu kai shi asibitin suka ce to nan Haisam yayi mashi sallama da fatan Allah ya bashi lafiya ya amsa yana ta mashi godiya da saka mashi Albarka, wani ƙumshin leda yasa Baffa ya ɗaukko mashi yaba Fatuu yace ga magungunan nan ya faɗi mata yadda zata masu da yadda zata rinƙa ba su twins har itama yace tasha da Haisam sukai mashi godiya, bayan sun fito ƙopar gida Khalid ya koma su kuma suka nufi bangaren su Yadikko sai faman leƙowa ake ana kallon su, a parlor aka zazzauna suka shiga gaisawa bayan ɗan lokaci Haisam yayi ma Yadikko sallama tanata mashi godiya da saka albarka ya kai hannu aljihun rigarshi ya fiddo kuɗi masu yawa ya miƙa ma Baffa yace gashi a raba ma mutanen gidan sannan ya tambayi Account ɗin shi yace zai tura kuɗin da za'ai ma Arɗo amfani a Asibitin Baffan nata roƙonshi kan ya barshi za'a kai shi yana murmushi yace ba wani abu yayi niyya ne, kuɗi masu yawan gaske ya tura har saida Baffa ya jinjina kuɗin yace hidiman tayi yawa shidai ba komai kawae yake cewa, Godiya sosae sukai mashi ya miƙe yace ma Fatuu in ta gama yana waje Baffan ma ya miƙe suka fita tare, bayan fitar shi ne Yadikko ke mata tsegumin Khalid don taji dashi suka zo Fatuu ta faɗi mata yadda akai suka taho tare tace kuma Haisam bai nuna komai ba tace mata a'a, itama Fatun saida taba Yadikko kuɗi harda Baffanta ta bada ta bashi dasu Aysha sukaita Godiya ta ɗaukko mata wasu magunguna da zasu inganta lafiyar ta data cikin jikinta da kuma wanda zata samu sauƙin haihuwa ta faɗi mata yadda zatayi amfani dasu, tare da Yadikko suka zazzagaya yi ma sauran mutane sallama nan fa aka shiga ba su twins kyautar abubuwa su kaji, zabbi harda akuyoyi cikin wanda suka basu akoyoyi harda Yaya, duk Yadikko ta amsa tace zata kiwata masu kafin daga baya a aika masu tunda ba'a Mota zasu koma ba, bangaren su Yadikkon ƙwai masu yawa suka basu da uban dawon fura da Nono harda zuma mai yawa da man shanu duk akai masu dubara yadda ƙwan bazasu fashe ba haka Nonon ma harda ƙanƙara aka saka mashi yadda zai tsaya da sanyin shi gaba ɗaya cikin wata jaka aka saka su a haka ma kayan sunyi ma Yadikko kaɗan tace inda da Mota suka zo sai an cika boot ɗinta da fura da Nono saboda su twins Fatuu nata dariya tace a haka ma ai da yawa, kusan gaba ɗaya gidan aka fito rakiyar su waje anata masu Allah ya tsare hanya, bayan sun baro rugar gidan su Khalid suka koma anan suka ci abincin rana kafin sukai masu sallama Hajiya Rabi'atu taba Fatuu kyautar atampopi masu kyau guda biyu da lace harda humra masu ƙamshi da turarurrukan wuta su twins ma ta basu kaya sosae tayi mata godiya harda Haisam, har bakin Mota suka rako su lokacin da suka baro gidan ƙarfe ukku na rana zuwa karfe huɗu da wasu mintuna suka iso Yola, har gidan Senator Buba Khalid ya kai su da har yace bari ya jira su sai ya kai su Airport Haisam yace mashi ya bashshi kawai kar su 6ata mashi lokaci akwae Driver da zai kai su yayi mashi godiya kafin ya amshi lambar shi yace zai kira yaji yadda ake ciki dangane da jikin Arɗo Khalid ɗin yace Ok, harda kuɗi yaba su twins Fatuu tace ya barshi yana murmushi yace ai ba ita yaba ba yaranshi yaba ta amsa tayi mashi godiya tare da cewa ya gaishe da iyali yace zasu ji daga haka ya tafi, da suka shiga cikin gidan basu daɗe ba salla kawai sukai koda aka basu abinci cewa sukai a ƙoshe suke sukai masu sallama nan ma saida aka ba Fatuu da twins kaya Senator Buba ma ya basu kyautar kuɗi masu yawa zumunci mai daɗi, a wata jibgegiyar Jeep aka tafi kai su Airport harda Senator Buba yay masu rakiya, suna akan hanyar ne Fatuu taji ƙarar shigowar saƙo a wayarta, lokacin data duba saƙon har saida gabanta yay bugu da ƙarfi don ta gane Khalid ne ya turo duk da bata da lambarshi amman daga yanayin saƙon ta gane nashi ne, da turanci ya rubuto mata yana mai bata haƙuri da kuma neman yafiyarta akan abunda ya faru a tsakaninsu a baya yayi nadama da kuma danasanin da yasan har ya mutu bazai daina yi ba sai dai ta wani bangaren yayi farincikin shigowarta rayuwarshi don ta dalilinta Allah yasa ya daina duk wani abu mara kyau a ƙarshe yana son ta sani ta zamo wani bangare na rayuwarshi wanda hakan ne ma yasa shi saka ma ɗiyarshi sunanta, tana gama karantawa ta ɗan saci kallon Haisam dake gefenta taga idon shi na a gaba suna yar hira da Senator Buba dake a seat ɗin gaba, kamar ta share Khalid ɗin ba sai ta mayar mashi da amsa ba sai kuma wata zuciyar ta raya mata yana iya cewa zai ƙara turo mata wani saƙon saboda rashin jin amsarta hakan yasa ta maida mashi da amsa, itama da turanci tace komai ya rigada ya wuce don har tama manta kuma tun bayan da aka fasa aurensu ta yafe mashi don haka tana fatan shima ya manta sannan ta gode da karar da yayi mata ya gaida mata da Zarah da Mamanta, tana tura saƙon ta goge duka nashi daya turo mata da nata data tura mashi sannan tayi blocking ɗin lambar tashi yadda bazai iya sake turo mata saƙo ba ko ya kirata tay shiru zuciyarta ta shiga tariyo mata da abubuwan da suka faru tsakaninsu yadda ya rinƙa yi mata a cikin Mota da gidan gonarsu da ya kaita, idanunta ne suka fara tara ƙwalla da sauri ta fara ƙoƙarin mayar dasu tare da kawar da tunanin daga ranta.

Bayan sun dawo Abuja Washe gari Fatuu taje gidan Mino kai mata tsaraba Haisam ne ya kawota su twins a gida ta barsu, taji daɗin ganin yadda Mino ta saki jiki suna ta shan amarci da Nameer ta sha kananun kaya riga da wando, bayan data je ne Nameer ɗin ya fita, sosae Mino taji daɗin tsarabar data kai mata tace itama bada daɗewa ba zata je Yola Fatuu ta ɗan harareta tace ba yanzu ba sai ta shekara Minon ta noƙe kai tace "kai Adda Fatuu shekara yayi yawa ni dai gaskiya nan bada daɗewa ba zanje nasan dana nuna ma My Love ina son zuwa zai bar ni ƙilan ma tare zamu je" ɗan buɗa ido Fatuu tay ta ruƙe haba ta maimaita My Love ɗin da ta faɗa Mino ta saka dariya tare da rufe fuska alamar kunya, hira suka cigaba da yi anan Fatuu ke mata zancen Karatunta tace kar ta bari soyayya tasa ta shashantar dashi koda SSCE ne tayi ta samu result ɗin gama Secondary Minon tace eh rannan sunyi magana yace zata zana jarabawar sannan in zai tafi yin Master's Degree ɗin shi US zasu tafi tare sai taci gaba da Karatu a can, sosae Fatuu taji dadin jin hakan anan take sanar mata zancen komawarsu Us Mino ta marairaice fuska kamar zatayi kuka tace yanzu shikenan tafiya zatayi ta zama bata da kowa a nan Fatun tace mata kada ta damu tasan bazata yi maraicin rashinta ba tunda ga yan gidan su Nameer nan tasan zasu zame mata tamkar yan'uwa, tare suka shiga Kitchen yin abinci suna cikin yin aikin ne Mino ke faɗi mata wai Nameer yace in tana so a samo mata mai aiki da sauri Fatuu tace to ya tace mashi Minon tace cewa tayi ba sai an samo ba tunda ba wani aiki sosae sai yace wai ko gyaran gida ne a rinƙa yi mata, girgiza kai Fatuu tay tace kada a samo mata wata mai aiki ai gyaran gidan ma zata iya tunda ba wani datti yake yi ba inda take amfani dashi kullum kamar Bedroom, toilet da Kitchen su ta rinƙa gyara su kullum shi kuma falon tunda yana da girma in kamar taga bai 6aci ba tana iya bari sai bayan kwana biyu ta rinƙa sharewa amman zata iya kullum tasa towel ta goge kayan kallo da kujeru sai ta rinƙa saka turaren wuta akai akai koda zata yi mai aiki a bari ba yanzu ba sai kamar in ta samu ciki tayi nauyi kuma mai aikin ma kada ta bari a samo mata yarinya ko budurwa in ba haka ba a kwace mata My Love tana gani, dariya Mino tayi tace ita so take ma Aysha ta dawo wurinta shikenan ma ba sai tayi wata mai aiki ba Fatun tayi ɗan jimm alamar nazari kafin tace mata hakan ma yayi amman ta bari ba yanzu zata ɗaukkota ba tace to, bayan sun gama girkin saida suka gyara ko ina sannan suka zauna suka ci tare, Sai bayan Magrib Haisam yazo ɗaukarta lokacin Nameer ya dawo ya shigo cikin parlon suka gaisa Mino ta kawo mashi abun ta6awa da lemu daga baya sukai sallama. A ranar da daddare Haisam ke faɗi mata nan da sati guda zasu tafi Us, ana saura kwana ukku su tafi taje Katsina yin bankwana, har gidan Aunty mareeya da Feenah taje sannan taje gidansu Aminiyarta Haulat harda abun arziƙin data saba tayi mata taba Kawu Amadu makullin Motarta tace yaci gaba da yin amfani da ita, kwananta biyu ta dawo Abuja Washe gari wurin ƙarfe sha ɗaya suka tafi harda Mino amarya akai masu rakiya Airport daga nan Lagos zasu je wurin Fanan sai da daddare zasu tashi zuwa Us.

Fauzy taso zuwa Funtua bayan zuwan su amman Sameer yace tayi haƙuri ba yanzu ba don tana iya samun matsala in tayi wannan tafiyar a mota dole ta haƙura anan Nasarawa suka tsaya don zasu ɗan kwana biyu kafin su koma London, Bayan bikin Mino da kamar wata ɗaya lokacin satin su Fatuu biyu da komawa da daddare bayan sallar isha Gwaggo na zaune kan abun salla tun bayan data gama sallar take zaune a wurin kamar mai tunanin wani abu can ta kai hannu ta ɗaukko wayarta dake ajiye gefen abun salla ta shiga kiran Amadu, bayan ya ɗaga ta tambayi sun dawo daga masallaci ne yace mata eh ta ƙara tambayar ina Kamalu yace gasu nan tare a shago tace to shi ya shigo tana son ganin shi yace to, bada daɗewa ba ya shigo ɗakin da sallama ta ɗaga kai ta kalleshi tana amsawa ya nufi kan kujera ya zauna, gaishe da ita yayi ta amsa yace gashi ta ɗaga kai, shiru ta ɗan yi yanata kallonta can tace "Dama so nike in tambayeka wai kai baka son yin Aure ne?" ɗan waro ido yay sai kuma yayi yar dariya yace yana so mana amman miyasa tace haka ta ɗan ta6e baki tace taga baida niyya ne gashi yanata girma yanzu har ya fita daga shekara talatin amman bata ta6a jin yayi zancen yana da budurwa ba, yana dariya yace kawai shi soyayyarce ya ɗauketa 6ata lokaci don da yawa sai yaga an daɗe ana soyayya amman sai kaga anzo ba'a yi aure ba shiyasa Amman daya samu wadda suka fahimci juna zai yi auren, kai Gwaggo ta jinjina ta ɗan yi shiru tana kallon ƙasa ya fahimci kamar akwae wani abu a ranta hakan yasa shi tambayarta koda wani abu ta ɗago tana murmushi tace "Dama wata shawara ce nike son baka nace mi zai hana ka auri Haulatu duk da ba budurwa bace amman bata da wani aibu ina son yarinyar don tanada halin kirki kuma abunda aka fi buƙata kenan a wurin macen aure na tabbatar duk wanda ya aureta sai yaji daɗin zama da ita saboda tana da haƙuri sosae, ka duba yadda aka kasa yin ƙawance da Fatuu saboda halinta lokacin kuruciyarta amman haka Haulat ta jure duk da halinta na cika mutum haka taita haƙuri sa ita sukayi ƙawance har suka zama tamkar yan'uwa",

Shiru Kawu Amadu yay idonshi a ƙasa ganin haka yasa Gwaggon tace ita shawara ce ta bashi ba dole take mashi ba in bata yi mashi ba shikenan tana mashi Addu'ar Allah ya bashi wadda zasu daidaita mai halin kirki, ɗagowa yay yana murmushi yace a'a bawai bata yi mashi bane kawai yana mamakin yadda tunaninsu yazo daya ne don tun bayan dawowarta yaji yana son aurenta saida ya bari ta gama takaba sannan kwanaki yaje mata da Maganar amman sai bata yi na'am ba tace wai tursasa mashi akai kan ya aureta kuma tasan bai wuce Fatuu ce tasa saboda tausayinta da take amman in akace ya aureta ai an ƙware shi tunda ita yanzu ba budurwa bace, lokacin ya nuna mata shi ba wanda yasa shi shiya kawo kanshi to sai tace wai ya bata lokaci zata yi shawara to har yanzu zaman jiran amsarta yake ko bayan bikin su Mino saida yayi mata maganar amman sai ta ƙara cewa ya dai ƙara mata lokaci, Murmushi Gwaggo tayi tace ina ruwan Haulatu, duba agogon wayarta tayi taga lokaci kafin ta fara ƙoƙarin miƙewa tana faɗin bari taje gidan su, miƙewa yay shima yace suje ya rakata, bayan sun fito Amadu ya kwala ma Kamalu kira ya leƙo yace mashi zasu je su dawo yace to ya gaishe da gwaggo ta amsa tana murmushi, suna tafe suna hira gwanin sha'awa har kama Gwaggon yake lokacin da suka iso gidan a waje ya tsaya ita ta shiga, lokacin da tayi sallama innarsu Haulatun na a tsakar gida ta tarbeta da fara'a tana mata sannu da zuwa suka nufi ɗaki, bakin gado ta nuna mata Gwaggon tace bari ta zauna a kan tabarma dake shimfiɗe innar tace ya zata zauna a ƙasa don Allah, Gwaggo tana murmushi tace to ai ita ba baƙuwa bace ko kuma ai ba'a ƙasa bane tunda kan tabarma ne, itama innar zama tayi gefen gwaggon suka shiga gaisawa ta tambayi wurin su Fatuu da Amarya Mino duk tace mata suna nan lafiya, bayan sun gama gaisawa Gwaggo tace mata ina Haulat ne ta bata amsa da tana ɗakin ta ko ta kirata Gwaggon tace a'a tukunna, tambayar innar tayi ko sunyi magana data danganci Amadu da itane da alamun rashin fahimta ta bata amsa da a'a gaskiya, Gwaggo na murmushi a nutse ta shiga yi ma innar bayanin abunda ke faruwa tsakaninsu da Amadu sosae tayi mamaki har fuskarta ta bayyana tana murmushi tace wllh sam bata san da Maganar ba,

"To ko dai tana da wanda take so ta aura ne?" Gwaggo ta tambaya innar ta ɗan yi jimm kafin tace gaskiya bata tunani don har yanzu bata ga ta tsaya ma da wani ba tun bayan data gama takaba amman dai bari a kirata sai aji, Haulat na kwance a saman gado tun bayan data gama yin salla ta kwanta don tasa ummasalma bacci, tuni ma yarinyar tayi baccin ita kuma ta faɗa duniyar tunani wanda a yanzu ya zamar mata jiki ciki harda na Kawu Amadu don idan tace bata son auren shi to tayi ƙarya saidai gani take shi ba don yana sonta bane zai aure ta, innarsu ce ta shigo da sallama ta ɗago kai ta kalleta tare da amsa mata, tambayarta tay ko har ta fara bacci ne tace mata a'a ta kwantar da salma ne tace mata to tazo ɗakinta yanzu da sauri ta tambayeta lafiya innar tay ɗan murmushi tace in tazo taga ko menene ta juya, innar na shiga ɗakin itama ta shigo tana sanye da doguwar rigar bacci ta yafo gyale a kanta, koda taga Gwaggo bata kawo komai ba a ranta ta ɗauka an kirata ne su gaisa ta duƙa a gabanta tana ɗan murmushi ta gaishe da ita itama fuska a sake ta amsa ta tambayi Salma tace mata tayi bacci, shiru ta ɗan biyo baya can Gwaggo ta sauke yar ajiyar zuciya ta kalleta tace mata dama taji abunda ke faruwa tsakaninta da Amadu sai dai yadda tayi tunani ba haka bane ba wanda ya saka shi ya nemeta tsakanin ita da Fatuu basu ma san da yayi mata Maganar ba in ba yanzu daya faɗi mata ba kuma ita a ganinta koda sashi akai ya nemi Aurenta ai don an yaba da kyawawan halayenta ne,

"Ko akwai wanda kike so ne?" innar su ta jefa mata tambaya ta girgiza mata kai ba tare data ɗago ba Gwaggo tace to in dai har taji tana son Amadun ta bashi dama tunda ba haramun bane wai don yana saurayi sau nawa akai ga misali nan ma akan Manzon Rahama, shiru suka ɗanyi kafin Gwaggo tace mata ta tashi taje ita dama tazo ne don ta Warware mata abunda take tunani in Allah yasa sun daidaita to suna Farinciki, miƙewa tay ƙasa ƙasa da murya tace ma Gwaggon saida safe ta amsa mata, bayan fitar Haulat yar hira sukai da innar tasu kafin Gwaggo tayi mata Sallama suka miƙe tare, har bakin zaure ta rakota tayi mata Godiya da Addu'ar Allah ya bar zumunci sukai ma juna saida safe, lokacin da ta fito Amadu na zaune bisa ɗan dandamalin gaban gidan dake kallon nasu Haulat yana latsa waya, yana ganinta ya miƙe ya nufo ta, a gabanta ya tsaya yace har ta fito tana murmushi tace eh suje ya ɗan sosa ƙeya yace to ya ake ciki tay mashi wani kallo mai kaman harara tace yadda ake waje yay yar dariya ta ƙara ce mashi suje in sunje gida yaji yadda akai, ɗan ƙara sosa ƙeya yay yace ko taje ya taho daga baya tayi murmushi tare da ɗan girgiza kai tace dama ba rakota yay ba kenan abun shi ya kawo shi, daga haka ta juya yana dariya yace mata a'a yanzu zai taho ƙilan ma ya sameta a hanya, bayan tafiyarta wayar shi ya ɗago ya shiga kiran Haulat bayan tayi ringing ta ɗaga tayi mashi sallama ya amsa ta gaishe dashi nan ma ya amsa daga haka tayi shiru yace mata in ba damuwa yana son ganinta a ƙopar gida tay ɗan jimm jin haka yasa yace mata in bazata samu fitowa ba ba damuwa bari ya tafi, a hankali tace mashi a'a gata nan zuwa, shiru tayi tana tunanin yadda zata fita hakanan sai taji wata irin kunyar shi ta kamata can dai ta miƙe ta nufi wurin kayanta ta curo doguwar Hijab ta daura saman rigar jikinta, tsaye tayi bakin kopar ɗakin tana jin nauyin zuwa ta tambayi innarsu can dai ta nufi ɗakin saida ta ƙara yin jimm kafin ta kai hannu ta ɗaga labulan ta shiga da yar Sallama, innar tasu har ta kwanta ta amsa mata tare da ɗago kanta tana kallonta Haulat ɗin ta sadda kanta ƙasa da ƙyar tace mata dama wai Kawu Amadu ne ke son ganinta a waje, murmushi innar tayi tace mata to taje, har ta juya taji ta kirata ta juyo ta kalleta,

"So nike in tambaye ki kina son Amadun ne ko kuwa?" maida idonta tayi ƙasa sannan ta ɗan jinjina mata kai alamar eh,

"To idan kinje yay maki Maganar Aure ki bashi dama a turo kawai" ɗagowa tay ta kalli innar cikin sanyin murya tace ita gani take kamar yayi wuri da yawa kada aita yin surutu, innar na murmushi tace to miye abun surutu abu kusan shekara da rasuwar Mijin nata wasu ma suna gama takaba da sun samu miji suke yin auren su tunda rashin yin auren ai ba abunda zai canza ko to duk miye na jinkiri tunda Allah ya kawo mai sonta kuma ma Mutum kamar Amadu ta amince mashi kawai ta amsa da to ta juya, yana tsaye gefen ƙopar gidan ta fito ta tsaya a jikin kopar ya juyo yana kallonta da murmushi da yake akwae haske itama ɗan murmushin take mashi ta gaishe shi ya amsa tare da tambayar ina ɗiyar shi tace mashi tayi bacci,

"Allah yasa dai kema ba baccin kike ba na tado ki" a hankali ta girgiza mashi kai alamar a'a suka ɗanyi shiru suna kallon juna can yace "na cika naci ko, kiyi haƙuri kinsan abunda rai ke so ba kamar kuma ga baƙon abun gaba ɗaya na kasa samun natsuwa da aka ƙi amince man" Murmushi tayi kawai bata ce komai ba ya sake cewa "Gwaggota tazo kun yi magana ne?" kai ta daga mashi alamar eh,

"To yanzu kin yarda ba tursasa man akai in aure ki ba ni ke son hakan?" kai ta ƙara ɗaga mashi,

"To yanzu an yanke shawara game da buƙatar tawa ko sai na ƙara jira?" shiru tayi tana ɗan yi murmushi kafin a hankali tace an yanke yace to yana saurarenta Allah yasa yaji Alkhairi ya tsareta da ido yana mata wani kallo gaba ɗaya duk sai taji nauyin shi take ji ganin abun take kamar a Mafarki wai ita da Kawu Amadu ne suke soyayya har ma da zancen aure abunda bata ta6a kawo wa a ranta ba, cikin kwantar da murya yace mata pls a tausaya mashi kada aja mashi aji, kallon shi tayi tana murmushi a hankali ta furta "an amince maka" ɗan buɗa ido yay yace "You Mean kin amince zaki aure ni?" kai ta ɗaga mashi ya wani lumshe ido tare da kai hannu ya dafe saitin zuciyarshi ya furta "Alhamdulillah, har bansan yadda zan bayyana daɗin dana ji ba yau dai ɗan Gwaggo zai yi bacci hada munshari da ana niyyar a zautar mata da yaro" Dariya Haulat tayi har haƙoranta suka bayyana tace "Kai Kawu Amadu" buɗe idon shi yay sosae yace "Allah kuwa kullum da tunanin amsar da zaki ban nike kwana kinsan ni ba sanin kan abun nayi ba gaba ɗaya na zurma har na fara tunanin ko ban shiga fagen Soyayyar ba a sa'a da naga kamar ba'a so na",

"Ai kai da wuya ace ba'a son ka kawai don baka cewa kana son ne" É—age gira yay yace Why ta faÉ—i Hakan,

"Saboda kana da duk wani abu da mace zata so a wurin Namiji" da ƙyar ta ƙarasa Maganar yana murmushi yace a hakan shi da baida kuɗi abunda yanzu kusan mata saboda su suke son Mutum,

"Ai Kawu Amadu banda kuɗi Kyau ma nasa a so mutum kuma kana dashi" ɗan juya ido yay yace mata kenan ita don kyau take son shi tana dariya tace "a'a, don ka cancanci in so ka Kawu Amadu saboda kana da halin kirki" wani kalan murmushin daɗi yay yace "To nagode Allah ya tabbatar mana da Alkhairi ya ƙara mana ƙaunar junanmu, amman pls ina neman wata alfarma wannan Kawu Amadun da ake ce man a aje shi a gefe a rinƙa kirana da sunan da zansan nima na fara soyayya da aketa man gori da surutu ashe ma ni tuni Allah ya za6a man mata lokaci ne kawae baiba yanzu gashi lokacin yayi ta bayyana" gaba ɗayansu kallon juna suke cikin ido suna sakar ma juna ƙayataccen murmushi cikin kwantar da murya ta furta "Ok My Dear an canza maka in ma wannan bai yi ba sai a canza wani" wani farfar yay da ido yace "yayi sosae Sweetie nah" da sauri ta kai duka hannuwanta ta rufe fuska alamar kunya Amadun ya sa dariya, suna haka Mahaifinta ya dawo yabi su da kallo Amadu ya sunkuyar da kai ya gaishe dashi bayan ya amsa yace "kamar Amadu ko" kai ya ɗaga mashi yace eh shine Mahaifin nata yay ɗan murmushi tare da furta Ma sha Allah, daga haka ya juya zai shiga da sauri Haulat taja gefe tana mashi sannu da zuwa ya amsa kafin ya shige, kallonta Amadu yay yace Allah yasa data koma gidan Baban yace mata ace ya turo tana murmushi tace da wuri haka yace eh mana mi zasu tsaya yi gara suyi auren alabashshi sunyi soyayyar a gidansu tayi dariya, Mahaifinta na shiga ɗakin innarsu ya wuce tana kwancen har ta fara yin bacci saidai bai yi nisa ba, yana yin sallama ta buɗe ido ganin shine ta fara ƙoƙarin tashi zaune tana mashi sannu da zuwa ya nufi wurin gadon yana amsa mata, a bakin gadon ya zauna ta fara ƙoƙarin saukkowa tana faɗin bari a kawo Abinci ya dakatar da ita ta hanyar faɗin tukunna ta koma ta zauna, tambayarta yay mike tsakanin Haulatu da Yaron can Amadu ne ya gansu tsaye a ƙopar gida, murmushi tayi nan ta kwashe komai game da zuwan gwaggo ta faɗa mashi tun kafin ta ida ya hau jinjina kai tare da yin murmushi bayan ta gama faɗi mashi yace amman dai yayi farincikin jin zancen wllh don Amadu ba dai hankali ba ga ƙoƙarin neman na kai itama tace sosae taji dadin al'amarin don tana son Amadu, Mahaifin nasu yay fatan Allah ya tabbatar masu da Alkhairi ta amsa da Amin, bayan shigar Mahaifin Haulat basu jima ba sosae suka yi sallama harda kuɗi ya bata yace da safe ta siya ma Salma abunda takeso tace mashi don Allah ya barsu yay mata wani kallo yace badai iko zata nuna mashi da ɗiyar tashi ba, da sauri ta bashi haƙuri tana murmushi shima shi yake yi ta amsa tare da yi mashi godiya sukai bankwana cike da nuna ƙauna, kamo hanyar gida yayi sai faman sakin murmushi yake sai kace zautacce yana isowa ciki ya shige ya nufi ɗakin Gwaggo lokacin har ta kwanta ya shiga da sallama ta ɗago tana amsa mashi tare da kunna wayarta haske ya kawo tace mashi ya kunna wutar ɗakin, bayan ya kunna kujera ya nufa ya zauna sai faman murmushi yake Gwaggo ta tashi zaune tana kallonshi tace mashi ya akai ya bata amsa da Haulat ɗin ta amince mashi yanzu sai kawai a saka rana, ɗan buɗa baki Gwaggo tayi ta kai hannu ta ruƙe ha6a tace ko kunyarta bai ji da sauri ya sunkuyar da kai yana yar dariya yace yaga kamar tana son yayi auren ne shiyasa ta ɗan ta6e baki tace shikenan Allah ya tabbatar masu da Alkhairi zata yi ma dangin Baban shi magana kan hakan ya ɗago yace to, har zai miƙe yaji tace to yana da kuɗin yin Auren ko ya kalleta tare da ɗan sosa kai yace bazasu gagara ba tayi yar dariya tace yaje Allah ya taimaka yayi mata saida safe ya juya tabi shi da kallo tana murmushin daɗi don yana ɗaya daga cikin burinta a yanzu taga auren autan nata, yana fitowa wayar shi ta fara yin ringing ya duba ganin Haulat ce yasa shi nufar ɗakin shi da sauri saida yaje bakin kopar shiga ya ɗaga tare da ƙarasa shigewa, ce mashi tay dama ta kira ne taji ya ya koma gida jama'a zo kuga washe bakin daɗi wurin Amadu yace haka ta damu dashi wannan in sukai aure yasan ba ƙaramar kulawa zata bashi ba tana murmushi tace mashi in sha Allah fatan itama zai kula da ita da sauri yace tamkar ƙwai in sha Allah duk sukai dariya, a saman ƙatuwar katifar shi daya canza tuni ya kwanta suka cigaba da shan soyayya, sun ɗan ɗauki lokaci kafin sukai bankwana, bayan ya gama kiran Kamalu yayi ta wayar yace mashi ya kullo shagon ya shigo shi gashi nan har ya kwanta, a ranar kwanan farinciki yan gidan su Amadu da Haulat sukai karma dai su Masoyan.

Washe gari wurin misalin ƙarfe goma na Safe Gwaggo ta kira Fatuu bayan tayi ringing Fatun ta yanke ita ta kira dama haka take duk suka kirata, gaisawa sukai ta tambayi jikinta dasu twins da Babansu da Fanan duk ta amsa mata da suna lafiya,

"Dama na kira in maki Albishir ne duk da bansan ko wani yayi maki ba" da sauri Fatun tace mata a'a basu yi waya da kowa ba a ƙagauce ta tambayeta wane Albishir ne nan Gwaggon ta faɗi mata game da Amadu da Haulat, wata uwar ƙarar farinciki Fatuu ta saka ta hau fadin Alhamdulillah ya Allah Gwaggo nata dariya, bayan ta tsagaita da yin murnar da alamun mamaki ta tambayi Gwaggon ita tasa shi ya nemi auren Haulat ɗin ne tace mata a'a ta faɗi mata yadda sukai dashi,

"Kai amma naji dadi wllh, kinsan Gwaggo tun kwanaki nike raya inama Kawu Amadu ya auri Haulat, sai dai gani nike kamar bazai amince ba tunda ba budurwa bace abun Allah ashe har ya furta mata kuma ni bata yi man maganar ba ma" daga jin yadda take Magana zaka fahimci ba ƙaramin farinciki take ciki ba, Maganar saka rana Fatun tayi mata gwaggon tace yau take niyyar kiran dangin babanshi ta faɗa masu sai suzo nema mashi auren daga nan a saka rana gaba ɗaya, da sauri Fatuu tace "Gwaggo don Allah a saka sai bayan na haihu Ya Haisam yace bazan ƙara zuwa ba har sai na haihu kuma yanzu saura wata biyar tunda yayi wata haɗu" a marairaice tayi Maganar Gwaggon na dariya tace ai itama bata son a saka da wurin don tana son ayi ma gidan gyara sosae don anan take son su zauna tare, cike da murna Fatun tace yauwa hakan yayi ta tambayi kamar wata nawa za'a saka Gwaggon tace ko shidda ko bakwai Fatun tace a bari bakwai ɗin lokacin har wanka ta gama tace hakane to sai a barshi bakwai ɗin daga baya sukai sallama, suna gama wayar parlor ta nufa da sauri don taje ta faɗi ma Haisam da yake Weekend ne yana gida, yana kishingiɗe kan doguwar kujera su twins na kwance a kan ƙafafun shi suna yin kallo ta nufo su cikin Washe baki Haisam ya juya yana kallon ta, ganin farinciki akan fuskarta yasashi yi mata murmushi a kan hannun kujerar da ya jingina ta zauna ta kai hannu cikin sumar shi ta fara ɗan sosai mashi, ɗago fuskarshi yay ya kalleta idanunshi a ɗan lumshe ya tambayi ya akai yaga tana farinciki ta kashe mashi ido tace tana Bedroom ta tuno da shine mijinta shine take farincikin, wani kalan murmushin gefen baki yay yace ai kullum tasan shine mijinta yasan bata mantawa da hakan tana murmushi tace hakane in ma ta manta to kuwa bata cikin hayyacinta, faɗi mashi tayi Gwaggo ce ta kirata ta sanar mata da Kawu Amadu zai auri ƙawarta Haulat" sosae shima ya nuna farincikin shi yace Amadun ya kyauta ya tambayi yaushe za'a sa rana ɗin ta faɗi mashi yadda sukai da Gwaggo na sai nan da wata bakwai saboda za'a gyara gidan tana son su zauna anan ya jinjina kai yace Allah ya kaimu ta amsa kafin ta maida idonta kan su twins daketa kallon su kamar suna fahimtar abunda ake a Tv da fulatanci tace basu ga Mom bane Adam ne ya kalleta yana mata dariya shi kuwa miskili Abie ko kallon nata bai yi ba, saukkowa Adam yay da yake sun fara iya tafiya ya nufota yana zuwa ta ɗaukeshi ya kai hannu yana ta6a ƙirjinta alamar yana son tayi feeding nashi saida ta gyara zama sannan ta fara bashi Abie na ganin haka shima ya saukko daga kan kujerar zai nufota ta ɗan harare shi yaja ya tsaya yana kallonta da idanunshi tubarkallah Haisam nata kallon su yana murmushi, ganin kallon da take mashi yasa ya fara ta6e baki zai yi kuka da turanci Fatun tace mashi tunda bai damu da ita ba itama bata ƙara bashi abunta kawai sai ya kife fuskarshi a jikin Haisam ya fashe da kuka, suna haka Fanan ta fito tana sanye da skinny jeans da yar top ta nufo su da sauri tana faɗin waya ta6a mata Little Abie yanzu suyi faɗa, daukar shi tayi tana tambayar waye ya saka shi kuka da hannu ya nuna mata Fatuu ta juya tana kallonta ta ɗan ɗaure fuska tace miyasa zata saka shi kuka kafin ta bata amsa Adam ya saki breast ɗin ta dago yana gwaranci shi ala dole magana yake duk ya basu dariya, tambayar Haisam tayi abunda ya haɗa su yana murmushi ya faɗi mata ta nufi gefen Fatuu tana faɗin ayi haƙuri dasu haka halin su yake ba shareta sukai ba ta zauna kusa da ita tace ma Abie din yace mata Sorry saida ta maimaita mashi kusan sau ukku sannan ya faɗi Sorry ɗin, bayan ta gama ba Adam ɗin ta amshe shi shima ta fara bashi anan take faɗi mata zancen auren Amadu da Haulat itama Fanan ɗin ta nuna farinciki sosae tayi fatan Alkhairi.

A ranar Gwaggo taje ta sanar ma Hajiya itama tayi farinciki sosae tace Amadu ya kyauta Saude ma ta nuna farinciki, Tk na jin zancen Auren Amadun yace aikuwa bazai riga shi yin aure ba shima zaisa aje a nema mashi aure, da yamma Amadu na shago Haisam ya kira shi a waya cikin girmamawa ya gaishe dashi bayan ya ɗaga Haisam ɗin yace mashi yaji abun farinciki Allah yasa Alkhairi Amadun na murmushi ya amsa tare da yi mashi godiya, tambayarshi Haisam ɗin yay akwae gida na kusa da gidan su yana son sanin wanda ke ciki haya suke ko kuwa nasu ne da alamun rashin fahimta Amadun ya tambayi wanne ciki yace duka na left da right ya bashi amsa da na bangaren dama gidan kansu ne sai na hagu wato gidan su Umar su haya suke Haisam ɗin yace mashi yasan mai gidan yace mashi eh wani Alhaji Isah ne shima anan unguwar yake daga can ƙasa yace mashi yana da lambarshi Amadun yace a'a gaskiya, tambayar shi yay zai iya samo mashi lambar tashi da sauri Amadun yace eh yace Ok ya samo mashi harda ta shi wanda yake hayar gidan Amadun yace ita yana da ita yace to ya fara turo mashi ita kafin ya samo mashi ta mai gidan yace to zai tura mashi yanzu sukai sallama. Da yamma bayan sallar la'asar sai ga Baban su Umar yazo shagon Amadu cikin fara'a suka gaisa kafin cike da farinciki yake sanar dashi ɗazun mijin yar'uwar shi ya kira shi yake ce mashi yana buƙatar siyan gidan da yake ciki ne shine yace zai siya mashi gida da zai zauna har ma yace mashi ya nemi gidan da yake so in ya samu sai yayi mashi magana, sam Amadu bai kawo komai a
ranshi ba ya nuna ya taya shi murna sosae, Bayan sallar isha Tk ya samu Hajiya a parlonta daga gefenta ya zauna ya gaishe da ita tana murmushi ta amsa, shiru yay ya maida kan shi ƙasa yana wasa da yatsun hannunshi Hajiya ta lura da Magana yake son yi tace "Ya akai ɗan gidan Hajiyar Sanata mi ake son faɗi man ne?" ɗagowa yay yana murmushi ya kasa mata magana tace mashi ko sun fara yar kunya ne still murmushin yake bai ce mata komai ba tace kar yaji komai ya fadi mata abunda yake son fadi mata da ƙyar yana yar in ina yace dama so yake a je a nemo mashi Aure, ɗan buɗa ido tay tana kallonshi tace "Wato ashe dama kana da wadda kake so shine tuntuni kaƙi yin niyya sai yanzu da kaji abokin ka zaiyi kana gudun yayi ya barka ko" yana ɗan sosa kai yace a'a yaga bai fara aiki ba shiyasa bai yi niyya ba tace to yanzu aikin ya fara ne yay shiru yana murmushi,

"Ai ganin baka da niyya yasa banyi Maganar a nema maka aikin ba tunda mi zakai da aiki ba iyali amman yanzu tunda kayi niyya zanyi magana sai a nema maka sai kayi Addu'a Allah yasa a dace, Maganar zuwa nema maka aure kuma zan yi ma mahaifinka magana amman tukunna sai ansan wacece kake so tunda ba'a kama nema maka aure ba tare da anyi bincike ba" dakatawa tayi kafin ta tambaye shi sunan yarinyar da kuma yar gidan waye ya faɗi mata sunanta Asma'u tare suka yi karatu har ya kwantanta mata ita yace sun ta6a zuwa ta gaishe da ita Hajiyar tace ta ganeta yanzu zata sa ai bincike sosae kafin tayi ma Mahaifin nashi magana sai a turo mutum ɗaya ko biyu itama zata kira Kawu Mani sai su haɗu suje, Godiya yayi mata tare da Addu'o'i tana murmushi tace Allah ya nuna mata bikin Tukur ɗan autanta yana murmushi ƙasa ƙasa yace Amin kafin yayi mata sallama ya tafi.

Washe gari bayan sallar La'asar sai ga Abbas yazo tare da wasu Mutane bayan sun gaisa da Amadu ya tambayeshi Gwaggo na nan ne yace mashi eh, juyawa yay wurin Motar mutanen da suka zo tare su biyu yace masu yana zuwa suka furta Ok ya juyo ya nufi gidan, a bakin ƙopar zauren ciki ya tsaya yana sallama Gwaggo ta leƙo daga cikin falo tana amsawa tana ganin shine ta washe baki tana faɗin "ɗana Abbas ashe kai ne ka shigo mana" yana murmushi ya nufo falon Gwaggon ta koma ciki, bayan ya shiga a kujera ya zauna suka gaisa ta tambayi su Abdul yace mata duk suna lafiya kafin yace mata yaji abun murna na auren Amadu Allah ya sanya alkhairi tana fara'a ta amsa da Amin, ce mata yay dama yazo tare da injiniyoyi zasu duba gidan da alamun rashin fahimta Gwaggon tace gida kuma ganin yadda tayi Maganar yasa yace mata basu yi Magana da Haisam bane akan aikin da za'ayi a gidan da sauri ta girgiza kai tace gaskiya basu yi Magana ba sai dai ko Amadu, yar dariya Abbas yayi yace ina ruwan H,Zakee nan ya shiga yi mata bayanin aiki za'a ma gidan don har ma anyi cinikin gidan dake makwabtaka dasu Haisam ɗin ya siya za'a haɗe da wannan ayi sabon gini, zaro ido Gwaggo tayi baki buɗe take kallon shi a ɗan ruɗe tace "anya dai ɗana Abbas haka maganar nan take" yana dariya yace mata tabbas haka take ƙilan da Amadu sukai maganar, cike da mamaki tace anya ai daya faɗi mata amman bari ta kira shi taji, wayarta ta ɗaukko ta shiga kiran nashi bayan ya ɗaga tace mashi ya shigo yanzun tana son ganinshi, bada daɗewa ba ya shigo da sallama ya nufi kujera ya zauna yace mata gashi, tambayar shi tayi ko sunyi maganar za'ayi aikin gidanan da ɗanta Haisam da alamun rashin fahimta ya girgiza mata kai alamar a'a kafin ya faɗi mata yadda sukai dashi game da gidansu Umar da lambobin daya tura mashi sai kuma zuwan da Babansu Umar yayi cike da farinciki ya bayyana mashi sunyi waya da shi yace yana buƙatar siyan gidan da yake ciki shi kuma zai siya mashi wani ya zauna, Abbas na murmushi yace to ai su ya siya ma gidan za'a haɗe da wannan a maida shi babban gini shi ya ɗaura ma kan aikin shine ma yazo da injiniyoyi don su fara duba gidajen, gaba ɗaya Gwaggo da Amadu idanunsu a waje suke kawu Amadu ya kai hannu ya rufe baki alamar Al'ajabi da alama mamaki ya kashe masu bakuna can da tsananin mamaki kawu Amadu yace "Wai Yaya Abbas yanzu kana nufin saboda mu ya siya gidan su Umar ɗin kuma har ya siya masu suma gida?" kai Abbas ya ɗaga mashi yace eh a yadda sukai za'a haɗe sai ai babban Flat a fidda ma Gwaggo part ɗinta sai shima Amadun a fidda mashi nashi da zai zauna da iyalinshi harda ma 6angaren baƙi, nannauyar ajiyar zuciya Gwaggo ta sauke ta shiga girgiza kai da alamun damuwa tace "Amman gaskiya ɗana Abbas wannan hidiman tayi yawa sosae ace ya siya masu gida sannan ya siya wanda suke ciki kuma a haɗe da wannan a fara sabon gini yadda gini kede cin kuɗi ai gaskiya abun yayi yawa nidai da za'a bi ta tawa don Allah ya barshi in ma dole so yake yayi to a gyara wannan namun kawai ni sai in koma can ɗayan ɗakin shi kuma Amadun sai su ɗauki dakina da nan falon za'a ma iya ƙara girman falon tunda ga ɗan sauran wuri nan daga gefe har banɗaki ma za'a iya yi masu a ƙuryar lafiya lau wannan ma zai ishe mu" fuskarta ɗauke da damuwa tayi maganar Abbas na dariya yace "to Gwaggon mu waya ƙi cigaba tunda shi yayi niyya yana da halin yi ne karki wani damu tunda daya san zai takura da bazai fara cewa zai yi ba, a yadda ma ya faɗi man dama yana ta son a canza ginin gidan to yadda yake son a maida gidan bazai isa ba kuma yasan kun riga kun saba da unguwar bazaku ji daɗi ba in ya yi maku ginin wani wuri Hajiya ma yasan bazata so ku rabu ba shine yanzu yay tunanin yin hakan harma anyi cinikin gidan ya biya shi kuma wanda aka siya ma gidan dama can yanada rabo a wurin shi ne, yanzu dai na bar mutane a waje zan iya masu magana su shigo?" duk tayi sukuku da ita ta ɗaga mashi kai alamar eh ya miƙe yana dariya yana faɗin karta wani damu abun farinciki ne don haka tayi farinciki kawai ta ɗan yi murmushi ya juya kan Amadu da yayi duruduru yace ya taso yaje gidan su Umar ɗin yaga in mai gidan na nan yace za'a shigo a duba yace to tare da miƙewa suka fita, Gwaggo dai tayi zuru tana ta jinjina abun a ranta tasan dole gidan su Umar ɗin yayi kuɗi don yafi nasu girma ga gida kuma da aka siyan masu sannan azo a dasa gini, Bayan duk sun gama dubawa Abbas yace ma Gwaggo za'a kawo hotunan gidaje sai su za6a tace to kawai sukai sallama, zaune sukai falon Gwaggo ta kasa yin magana sai Amadu dake ta faman jinjina abun yana faɗin to wai hakanan ya yanke yi masu ginin ko kuwa dai yaji batun gyaran gidan saboda aurenshi shine zai yi masu, wannan Maganar da yayi yasa Gwaggo ta ɗaukko wayarta ta shiga kiran Fatuu, bayan ta yanke Fatun ta kira suka gaisa nan take tambayar ta wai sunyi maganar gyaran gida da tace mata tana son ayi kafin bikin Amadu da Haisam ne tace mata a'a kawae dai ta sanar mashi zancen shine ya tambayi yaushe za'a saka rana ta fadi mashi yadda sukai da ita na ba yanzu ba sai an yi gyaran gidan Gwaggon ta sauke ajiyar zuciya, da sauri ta tambayeta miya faru ne nan ta kwashe komai ta faɗi mata ita kanta Fatun tayi mamaki sosae ido waje ta shiga jinjina Maganar aikin tace gaskiya hidiman tayi yawa sosae Gwaggon tace wllh itama duk ta damu Fatun tace bari tayi mashi magana gaskiya in ma aikin yake son yi masu to a gyara gidan nasu kawai Gwaggo tace itama abunda tace kenan to Abbas yace ai har ya riga ya siya gidan kuma shi Baban su Umar yanzu in aka hana yana iya ganin anyi mashi baƙin ciki, tana cikin yin Maganar Amadu ya miƙa hannu ta bashi wayar bayan sun gaisa da Fatun yace mata kawai a kyaleshi ai mashi godiya yanzu ko anyi mashi magana kan ya bari sun san dai ba fasawa zai yi ba, a sanyaye tace shikenan sukai sallama,

Bayan sun gama yin wayar Haisam ta shiga kira da yake su safiya ce yana wurin aiki, bayan yayi picking tace mashi tana son suyi vedio call ya furta Ok, yana zaune a Office ɗin shi jikinshi sanye da baƙaƙen suit fuskar shi sai annuri take, fuska a tur6une ta gaishe dashi yana ɗan murmushi ya amsa ya gane laifi yayi mata daga yanayin face ɗinta, daga gaisuwar tayi shiru tana ta tura baki, lumshe mata ido yay ya furta "ya akai ne My Baby?" wani kallo tayi mashi a marairaice tace taji abunda yayi amman gaskiya hidiman yayi yawa in aikin za'ayi to ayi iya gidansu basai ya kashe uban kuɗi ba haka, murmushi kawai yake ganin har yanzu halinta na rashin son ya kashe kuɗi sosae na nan, ganin bai ce komai ba ta tura baki tace bazai yi magana ba,

"Yanzu nayi laifi don zan ma Family ena abu?" ya tambaya tare da ɗage mata gira, kaman zatayi kuka tace "a'a ni bance kayi laifi ba Amman gaskiya kashe kuɗin zai yi yawa" sigh yay still murmushi yake yace "bazai yi yawa ba akwae kuɗin Baby so don't worry" yamutsa fuska tayi tace to in suka ƙare fa har saida yayi yar dariya ganin taƙi ta girma har yanzu tana behaving kamar da yarintarta duk da yasan yanzun ma ba wani girma tayi ba tunda yanzu take 20yrs, yana yar dariya yace mata bazasu ƙare ba saboda yana dasu da yawa akwae Dollars ya tara cike da tsokana yayi Maganar ta zaro ido ya ɗage mata gira,

murmushi tay tace "baka tsoron insa ai kidnapping ɗinka kana faɗi man ka tara Dollars" dariya yay har haƙoranshi suka bayyana yace ai tuntuni ta riga tayi kidnapping ɗin Heart ɗinshi yanzu ko duka kuɗin dake gareshi tace ya bata zai tattara ya bata, wani kallo tayi mashi tace is he serious ya jinjina mata kai yace amman zai fidda na aikin gidan da za'ai don kar aga yayi magana biyu sai kuma wanda zai ciyar dasu kafin ya sake tara wasu kada Allah ya kama shi ya barsu da yunwa, wani irin kallon ƙauna ta shiga bin shi da shi shima kallon nata yake idanu a ɗan lumshe cikin sanyin murya ta furta mashi "Thank you for loving me unconditionally Hubby. You have shown me what true love is, and I am forever grateful for that. I couldn't imagine my life without you" tana gama Maganar kwalla suka zubo mata sharrr, lumshe ido yay tare da ɗan murmushi yasa yatsa saman screen ɗin yana yin alamar goge mata ƙwallan hakan yasa ta yi yar dariya, Godiya ta shiga yi mashi sosae da Addu'o'i a hankali yake amsa mata daga baya sukai sallama cike da nuna ƙauna, a ranar haɗaɗɗun abinciccika suka haɗa mashi ita da mai aikin su da daddare kuwa duk da halin da take ciki saida ta tabbatar tayi mashi godiya ta hanyar gigitashi ta yadda har saida suka zubda hawaye su duka..........

101

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

.......Ranar Alhamis Hajiya ta kira kawu Mani na Daura ta tambaye shi gobe Juma'a zai shigo Katsina ne yace mata a'a amman in tanason ganin shi sai yazo tace mashi in bazata takura shi ba tana son ganin shi yace to ba damuwa zai shigo.

Washe gari kafin ayi salla ya iso Ya yi shigar manyan kaya ya fito a dattijo mai kamala anan gidan yayi sallar Juma'a suka ci Abinci tare da Hajiya a dining, bayan sun gama cin abincin ne suka dawo falo yana zaune a kujerar dake gefen ta Hajiya yace "Hajjaju gani na amsa kira Allah yasa na lafiya ne" tana murmushi ta bashi amsa da lafiya lou sai alkhairi ya furta Alhamdulillah shi suke fata a koda yaushe, Maganar zuwa neman auren Tk tayi mashi tace tana son ya shige gaba tasa anyi mata bincike akan gidansu yarinyar an tabbatar mata da basu da matsala shi mahaifin nata asali mutumin Gombe ne aikin custom ya kawo shi Katsina daga nan zaman ya É—ore don yanzu har ma yayi retired to tana son ya tuntube shi kan su bada lokacin da za'aje neman auren, jinjina kai yayi yace to ba matsala a yau ma kafin ya tafi sai ya tuntube shin a bashi Address ko kuma lambar wayar shi tace to dama ta amshi lambar a wurin tukur É—in, bashi lambar Baban Asma'un tayi yayi saving ya É—ago yana murmushi yace ashe sun kusa shan bikin É—an gidan Hajiya itama murmushin take tace aikuwa yay fatan Allah ya sanya alkhairi ya nuna masu,

bayan ta amsa da Amin tace "Kai ma in kana son ƙara Auren akwae mata a ƙasa zan baka" waro ido yay ya ɗan buɗa baki sai kuma yayi dariya yace yasan ai wasa take, ɗan ta6e baki tayi tace dama ana wasa da Maganar aure, yana dariya ya tambayeta wacece matar, tace "Kana so ne?"

"To Hajjaju taya zansan ko ina so ba tare dana ganta ba" yana ta dariya yay Maganar,

"To ai in kai baka santa ba ni na santa kuma na yaba da ita ne shiyasa nayi maka maganarta tuntuni ma nake kwaÉ—ayin wani cikin Family ya aureta saboda kyawun halinta Allah bai nufa nayi ma wani maganarta ba sai kai da nayi mawa yanzu",

"To ai Hajjaju kyau dai in ganta" still dariyar yake itama haka tace "ai ina ganin ma kasan wacece Kakar matan su Haisam da Nameer ce, ba wani tsufa tayi ba kawai don anyi mata auren wuri ne da yake asalin Fulanin daji ce in ba don haka ba bazata aje ma jikoki kamar su ba don ina ganin ka girmeta kaga kai baka dade daka samu Yan jikokin ba" shiru yay yana ƙoƙarin tuna ko yasanta can yace gaskiya ya kasa ganeta koda ya santa Hajiyar tace bari taga ai kaman akwai hotonta da akayi da bikin su Nameer anan falonta kuma shima ranar yana nan dashi akai hotunan, hoton gwaggo da tayi tare da Mino a ranar ta buɗo mashi ta miƙa mashi ya amsa ya bi hoton da kallo yana ɗan murmushi can ya ɗago ya tambayi Hajiyar bata da aure ne tace inda tana dashi zatayi mashi tayin auren nata ne ya sake tambayar abunda ya rabata da mijin nata ta faɗi mashi aurenta biyu na farko na dole ne akai mata da yake ta taso marainiya shine kawunta da ya riƙeta ya aura mata abokin shi to hardai zaman ya ƙare basu haihu ba bayan ta dawo wurin kawun nata Daura tana zuwa tallan nono a kasuwar mashi Allah ya haɗa ta da mijinta na biyu data aura shine suka haifi yara biyu kafin ya rasu sanadiyyar haɗarin mota tun daga nan kuma bata ƙara yin aure ba kusan shekara ashirin da biyar duk da tana da masu son auren nata itace bata so cikin dangin mijinta daya rasu wani ya samo mata aikin asibiti tana yi farko ma a gidan shi ta fara zama daga baya saboda rashin jituwar da suke samu da matarshi ta baro mashi gidan tazo ta gina wannan da take ciki a filin da suka gada, nan ta bashi labarin yadda mahaifiyar Fatuu tayi aure ta haifesu su biyu da yadda Gwaggon ta ɗaukko su ta riƙe ta kuma shiga nuna mashi kyawawan halayenta, ajiyar zuciya Kawu Mani ya sauke ya sake kallon hoton gwaggon kafin ya miƙa ma Hajiya wayar ta amsa tare da tambayar tayi mashi ko kuwa yana yar dariya yace tunda tayi mata tana son ya aureta in dai zata amince zai auretan,

"A'a ba wani tunda tayi man inason ka aureta salon kaja man matanka su ƙullace ni, kawai in kaji kana son ta zaka aureta to in kuma bata yi maka ba lafiya lau ka fito ka faɗi man ai ba wani abu bane dama don naga kana da ra'ayin mata fiye da ɗaya ne tunda yanzu haka biyu gareka shiyasa nayi maka Maganarta" sosae yake dariya jin abunda tace bayan ya tsagaita yace to yanzu koda tayi mashin in ita taƙi amincewa dashi fa tunda tace tana da masu son aurenta itace bata so Hajiyar tace ai sai suma su jaraba sa'ar su ƙilan Allah yasa ta amince dashi, gyaɗa kai yay yace to yanzu ya za'ai tasan dashi,

"Wannan mai sauƙi ne in ka shirya haɗuwa da ita kuyi magana sai in kirata in mata magana", yar ajiyar zuciya ya sauke yana murmushi yace abunda za'ai yanzu zai kira mahaifin ita wadda tukur ke so yayi mashi maganar haɗuwarsu in ya bashi dama da yayi sallar la'asar sai ya tafi yanzu abunda za'ai tayi ma ita Matar magana in ya fita sai ya fara tsayawa wurinta su gaisa kafin ya wuce, wani kallo Hajiya tayi mashi tace "Humm, su Mani anga farar fata har an zurma da anaso ai man bariki" Dariya ya 6a66ake da ita harda buga ƙafa yace "Sai Hajjaju mai dalilin aure, saboda dai kina so ne kawai"

"To tunda hakane a barshi kawai na janye....." da sauri ya katseta "a'a Hajjaju ba'a yi haka ba tunda dai kinyi niyyar haɗawa kada kima kan ki buƙulun lada ki kiratan kawai sai inje mu gwada sa'ar" wani kallo mai kaman harara tayi mashi ya saka dariya, ce mashi tay ya bari ayi sallar la'asar ɗin zata kirata Kawu Manin harda ce mata to ai kada ta fita unguwa Hajiyar na dariya tace ya dawo wani lokacin,

"gara dai ayi komai yau hajjaju kinsan ance da zafi zafi ake dukan ƙarfe" Dariya Hajiya tay tare da girgiza kai, bada daɗewa ba aka kira sallar la'asar ya miƙe don yaje masallaci itama Hajiya ta tashi tana ruƙe da sandarta ta nufi hanyar Bedroom don taje tayi sallar, bayan ta gama ne ta kira layin Gwaggo wayar na fara yin ringing ta ɗaga cikin girmamawa ta gaishe da ita tare da yi mata barka da juma'a bayan Hajiyar ta amsa ta tambayi tana gida tace mata eh bata daɗe data dawo bama daga wurin aiki, an dawo lafiya tayi mata Gwaggon ta amsa da lafiya lau Alhamdulillah,

"to ga baƙo nan na turo zai zo ku gaisa" ɗan jimm Gwaggo tay a ranta ta maimaita abunda Hajiyar tace kafin ta amsa mata da to sukai sallama, zugudum Gwaggo tay ruƙe da wayar tana ta nanata zancen zuwan baƙon don abun sai taji shi wani iri saboda basu ta6a haka da Hajiyar ba wai tace mata ga wani nan zai zo su gaisa, Bayan sun gama yin wayar fitowa Hajiya tayi cikin falon kusan a tare suka dawo da Kawu Manin, bayan sun zauna ya gaishe da ita tana murmushi ta amsa tace yayi na yara duk sukai salla sai sun gaishe da mutum shima murmushin Yay yace ai haka yakamata kafin yace mata yanzu bayan ya fito ya kira Mahaifin yarinyar har ya bashi Address zai je ya same shi daga can zai wuce Daura duk yadda sukai dashi zai sanar mata ta amsa da to tare da yi mashi Allah ya kiyaye hanya, shiru suka ɗan yi bai miƙe ba can yace mata bata kirata bane tay dariya tace ai ta zata ya manta yaje ta kirata a waya, tambayar inda gidan yake yayi ta kwatanta mashi da shagon Amadu tace in yaje yaronta ne mai shagon sai yasa shi yaje yayi mata magana ya amsa da to tare da miƙewa tana murmushi tace Allah yasa taji Alkhairi ya amsa da Amin ta ƙara cewa zata turo mashi kuɗi yanzu sai ya zuba mai yayi mata godiya itama tayi mashi da fatan Allah ya kiyaye hanya tace ya gaida iyali daga aka ya fito,

A daidai shagon Amadu ya parker Motar shi lokacin basu daɗe da dawowa daga Masallaci ba, fitowa yay bayan ya kulle ƙopar Motar ya tunkari shagon, a gaban shagon ya tsaya fuskarshi ɗauke da murmushi yayi masu Sallama tunda ya fito Amadun ke kallon shi yana ganin kaman ya sanshi saida ya ƙaraso gaban shagon ya gane shi shima Amadun murmushin ya mayar mashi bayan ya amsa sallamar cikin girmamawa ya gaishe dashi Kamalu ma dake zaune kan plastic chair yana latsa waya ya ɗago kai ya gaishe dashi shima da murmushi ya amsa mashi, tambayar waye Amadu a cikin su yayi Kawu Amadu yace shine ya nuna Kamalu yace to shi kuma wannan fa ya bashi amsa da ɗan Yayarshi ne,
"Kenan É—anka ne" Amadu na murmushi ya bashi amsa da eh,

"Ko shine Yayan Matar Haisam" da sauri Amadun yace mashi eh,

"Allah sarki, Allah yayi maku Albarka ya jiƙan Mahaifiyarsu da Mahaifin ka" a tare duk suka amsa mashi da Amin,

"Yauwa ka shiga ciki kace ga baƙon ya iso" ya faɗa still da murmushi akan fuskarshi, da alamun rashin Fahimta Amadun yace wa zai faɗi ma hakan Kawu Manin yace mashi ita mai gidan zaije yace ma ga baƙon da Hajiya tayi mata magana yazo da sauri ya amsa da to ya juyo ya buɗe shagon ya fito, lokacin daya shigo gidan Gwaggon na cikin ɗakinta tun bayan data yi waya da Hajiya dama tana kan abun salla ne bata tashi ba, da sallama ya shigo ta amsa tare da juyowa ta kalleshi ya sanar mata zancen zuwan baƙon tay ɗan jimm kafin a hankali tace mashi ya shigo dashi falo yace to ya juya, shiru tayi a ranta ta shiga tunanin to wane baƙo ne kuma wace irin gaisawa zasu yi kaman yadda Hajia tace, tana jin lokacin da suka shigo Kawu Manin yay sallama, bayan ya shigar dashi yazo ɗakin ya sanar mata gashi can a falo kai kawai ta ɗaga mashi ya juya ya tafi, miƙewa tayi duk tayi sukuku ganin Hijab ɗin jikinta lafiya lou dama gogagga ce ta ɗaukko tayi sallar da ita ta nufi ƙopar fita, lokacin data tunkari falon gabanta har ɗan faɗuwa yake, da sallama ta saka kai cikin falon ƙamshin turaren shi ya bugi hancinta yana zaune akan 2 seater ya ɗago yana kallonta da murmushi ya amsa mata sallamar suna haɗa ido ta gane shi ta nufi kujera mai mazaunin mutum ɗaya daga can gefen tashi ta zauna idon shi akanta yace mata "Barka da Fitowa", ɗan murmushi tayi ta amsa tare da gaishe dashi yana ta murmushi ya amsa, kanta ne ya ɗaure ganin shine don bata ta6a zaton shi zata gani ba matsayin baƙon don tunda tasan Hajiya tasan shi yana zuwa gidan matsayin ƙanin Hajiya tsawon lokacin kuma bai ta6a zuwa nan gidan ba sai yau, miƙewa tayi ta nufi Fridge ya bita da kallo bayan ta buɗe ta ɗaukko lemu da robar ruwa tare da glass cup bayan ta rufe tana juyowa suka haɗa ido ta maida nata ƙasa ta nufo inda ɗan table yake ta ɗaura sannan ta ɗaukeshi ta matsar dashi gabanshi, buɗe lemun tayi ta zuba a cikin cup ɗin ba tare data kalleshi ba tace gashi yasha yana murmushi ya furta "Shukran" ɗan murmushi tayi ta koma inda ta taso, ɗaukar cup ɗin yayi ya kai baki saida ya kur6a kamar sau uku sannan ya aje tare da furta Alhamdulillah ya ɗaura idon shi kan Gwaggo dake kallon Carpet yace "Fatan na same ki lafiya, ya gida ya yara ya aiki kuma" ɗago ido tayi ta kalleshi da ɗan murmushi ta amsa mashi da lafiya lau Alhamdulillah shima ta tambayi ya nashi iyalin da aiki yana sakin ƙayataccen murmushi ya amsa mata, shiru suka yi can ta miƙe tace bari a kawo mashi abinci da sauri ya dakatar da ita yace lemun ma ya isa a ƙoshe yake ta koma ta zauna,

"Yauwa, kamar yadda Hajjaju ta sanar maki ita ta turo ni don mu gaisa da juna kuma tunda mu ba yara bane nasan kin gane wace irin gaisawa ake nufi, ni dai na gan ki kuma kin mani don haka in an amince man Aure nike son muyi tunda duk naji duk wani abu dangane dake nima kuma in kina son sanin abunda ya dangance ni zaki iya yi ma ita Hajjaju magana da fatan za'a amince man" tunda ya fara Maganar ta sunkuyar da kanta har ya gama ta kasa ɗagowa balle tace mashi wani abu, ganin taƙi yin magana yasashi ce mata ita yake saurare ta taimaka ta bashi amsa, gaba ɗaya ya ɗaureta ta rasa amsar da zata bashi don sai taji bata iya ƙin amince ma buƙatar daya zo da ita kodan Hajiya gashi ita ta cire sake yin aure a ranta, a hankali ta ɗago suka haɗa ido tayi saurin kawar da nata kafin tace mashi tana buƙatar yin shawara ya ɗan bata lokaci, yana murmushi yace "Har sai anyi shawara kuma, to kodai ban samu kar6uwa bane?" kallon shi tayi da ɗan murmushi tace a'a kawai tana buƙatar yin shawara ne tunda tana da babban yaro, ɗan buɗa ido yay yace "dashi za'ai shawarar kenan karfa yasa aƙi amince man don kinsan wasu yaran sukan taya iyayensu maza kishi" yar dariya tayi kawai,

"Yanzu har tsawon wane lokaci zan jira Hajiya" yay Maganar yana mata wani kallo da gani shima za'a dashi ta bangaren soyayya, tana murmushi tace malama dai ya wani ɗage gira yace "Ni Hajiya na gani" shiru tay kawai tana murmushi ganin ya kafeta da ido tace mashi ko mi kenan zata sanar mashi ya furta Ok bari ya bata lambar shi amman don Allah kada a ɗauki lokaci asa ya kasa samun natsuwa tace uhmm kawai, wayarta ya tambaya yasa mata lambar tashi ta miƙe tace bari ta ɗaukko tana ɗaki, bada jimawa ba ta dawo ta miƙa mashi wayar ya amsa yana murmushi ya ɗan jujjuyata yace "amman Hajiya sai naga kamar kinfi ƙarfin wannan wayar" murmushi tayi tace tafi jin daɗin amfani da irinta ne yace to amman ga na zamani ai sai a haƙura da tsohon yayi gaskiya yakamata a canza ta tace mashi tuntuni yara keson canza mata ita ce bata so,

"To ai yanzu sai aba maigida dama ya canza" da sauri ta kalleshi ganin kallon da yake mata yasa ta kauda fuskarta yace "na cika azar6a6i ko tun ba'a sanar dani matsayi na ba har na yanke hukunci, ayi haƙuri abunda rai ke muradi ne" juyowa tay ta kalleshi tana ɗan murmushi, lambar tashi ya saka a tata ya kira kafin yayi mata saving tashi ya miƙa mata yace gashinan ya saka mata Alhaji Mani ya tambayi ita kuma Hajiya wa zai saka mata tace Dije ya ɗan yamutsa fuska yace "Wannan na zamanin da ne bari in saka na zamanin yanzu Khadija ko kuma Khadijatul Khubra" Gwaggo bata san lokacin da tayi yar dariya ba shima ita yake yi bayan ya gama saving ɗin ya ɗago ya kalleta yace "to Hajiya Khadija ni bari in zo in wuce inada wani uzuri da zan aiwatar kafin na hau hanya sai naji daga gareki ina fata kuma za'a duba man inji abunda nike fatan ji" murmushi kawai take, miƙewa yay ya zura hannu cikin yan cikin babbar rigar shi ya fiddo kuɗi masu ɗan yawa ya ɗaura akan table ɗin yace gashi nan a ba ɗan shi da jikanshi, da sauri ta kalleshi tace don Allah ya barshi yana mata wani kallo yace bata ji waɗanda yace taba bane dole tayi shiru, tafiya ya fara yi zai fita daga cikin falon ta ɗan juya tana kallonshi har ya kusa ƙopa ya tsaya ganin zai juyo yasa da sauri ta kauda idonta tana haka taji muryarshi yana faɗin bazata raka baƙon nata bane tay ɗan jimm kafin ta kalleshi suka haɗa ido yana mata murmushi, jiki a sanyaye ta miƙe ya furta yauwa ko ita fa ya juya tana biye dashi, saida suka kusa ƙopar fita ya juyo yace to ya gode ta koma kada ya wahalar da Hajiya ta ɗan yi murmushi tare da yi mashi Allah ya kiyaye hanya ya amsa, falo ta dawo ta zauna kan kujera tayi jugum ta rasa ma tunanin da zata yi ganin abun take kamar ba'a gaske ba duk da ba yau aka fara zuwa neman aurenta ba wannan sai taji yayi mata girma sosae ba kamar daya haɗa da Hajiya, tana haka Amadu ya shigo da sallama ta ɗaga ido ta kalleshi ta amsa a hankali, nufo inda take yayi ya zauna a kujerar dake gefen tata ya ɗan yi shiru yana kallonta kamar mai nazarin wani abu ita kuma ta kauda idonta daga barin kallonshi,

"Gwaggota lafiya kuwa?" taji muryarshi yana tambaya, kallonshi tayi da ɗan guntun murmushi tace mashi lafiya lou yace amman to ya ya ganta kamar wani abu na damunta ta ɗan yi shiru kafin tace mashi ba komai, shiru ya ɗanyi yanata kallonta can ya sake tambayarta to lafiya Kawu Mani yazo gidansu yaga bai ta6a zuwa ba tunda suke a gidan, shiru Gwaggo tayi tana tunanin mi zata ce mashi ya kawo shin tunda gashi yasan bai ta6a zuwa gidan ba can zuciyarta ta bata kawai ta faɗi mashi abunda ya kawo shi tunda dama ko ba yanzu ba dole zata faɗi mashi, ajiyar zuciya ta sauke tare da kallonshi kaman mai zullumin faɗi mashi shi kuma ya ƙura mata ido alamar ita yake jira tayi magana can dai tayi ƙarfin halin faɗi mashi Hajiya ce ta turo shi wai ya nemi aurenta, ɗan waro ido Amadun yay kafin da sauri yace "to kin amince mashi zaki aure shin???" a hankali ta girgiza kai kafin tace ce mashi tayi sai tayi shawara amman ita....kafin ta ƙarasa abunda take son faɗin kawai sai gani tayi ya kamo hannunta yace "Don Allah Gwaggota ki amince mashi kada ki ƙi kamar yadda kike yi a baya na roƙe ki, wllh ba wuce kiyi aure kikai ba tsofaffi tukuf ma zaki ga suna da aure tunda shi ibada ne, kinga in kika amince mashi muma a ƙalla zai zama muna da Baba a cikin gidan nan" shiru tayi tana kallon shi ta wani bangaren ta ɗan ji mamaki don bai ta6a nuna mata ya damu da tayi aure ba irin yanzu yawanci da anzo neman aurenta ta nuna bata so sai yace shikenan tunda haka take so, tana haka sai gani tayi ya saukko daga saman kujerar ya duƙa a saman guiwowinshi cikin marairaicewa yace "Don Allah Gwaggota ko don ni ki amince mashi nima dai ace inada wanda zan kira da sunan BABA ba tare dana haɗa da sunan shi ba, tun tasowa ta ba wanda nike kira da sunan Baba ba tare da nace Baba wane ba kamar Baba shehu, Baba musa da sauransu kinga yanzu in kika aure shi Baba zan rinƙa kiranshi ba yadda za'ai in haɗa da sunan shi nima a ƙalla in muna hira da wasu zance Babanmu ka za...." kasa ƙarasawa yay saboda ƙwallan da suka tarun mashi suna niyyar zubowa, wani irin tausayinshi ne Gwaggo taji ya kamata tun yana ɗan shekara shidda ya rasa mahaifinshi, girgiza hannunta yay ya furta "Don Allah Gwaggota..." ajiyar zuciya ta sauke tana ƙoƙarin ƙaƙalo murmushi tace "baka tunanin ba lalle ya zama kamar uba a garekan ba kamar yadda yake faruwa sau da yawa wasu ma sai kaga sun raba uwa da ɗanta..." da sauri ya tari hanzarinta,

"A'a Gwaggo ina da yaƙinin bazai yi hakan ba tunda kika ga Hajiya ta turo shi to tasan baida matsala ne, na tabbatar mutumin kirki ne ai ina ganin shi a gidan Hajiyar muna gaisawa, don Allah ki amince?" shiru tay tana kallon shi ƙwallan idon shi har sun zubo mashi can tace shikenan tunda haka yake so zata amince mashi, da sauri ya miƙe ya zauna gefenta tare da ƙanƙameta cikin tsananin farinciki ya shiga yi mata godiya harda su Kiss ya manna mata a gefen fuskarta ita dae sai dariya take zata iya cewa bata ta6a ganinshi cikin farinciki irin wannan ba in ma ta ta6a gani to ta manta, sakinta yay sai faman washe baki yake ya shiga laluban wayarshi yana faɗin bari ya sanar ma Fatuu wannan abun Farinciki, da sauri Gwaggo tace kada ya sanar mata yace a'a yakamata ta sani da zafi zafi, ƙoƙarin amshe wayar Gwaggon tayi ya miƙe yana dariya ya shiga yin safa da marwa a tsakar falon cikin harshen fullanci Gwaggon ke faɗin tana wasa dashi wai sai dariya yake itama yar dariyar take, tana fara yin ringing Fatun ta yanke sai gashi ta kira yana ɗauka ko gaisawa basu yi ba da sauri yace mata Albishirinta a ƙagauce ta amsa da goro fari ƙal yace banda shi ango sun ƙara samun Amarya a gidansu nan ya shiga faɗi mata zancen auren Gwaggo aikuwa wata uwar ƙarar murna ta saki tana faɗin Alhamdulillah abubuwan farinciki sai faruwa suke dasu Amadun yace Wllh kuwa da sauri tace mashi ina Gwaggon ya bata wayar bari ta maida Vedio call taga fuskar amarya yace to, duk Gwaggo na jin su da yake a speaker yasa kiran sai girgiza kai take tana ɗan murmushi, bayan an maida kiran na gani ya miƙa ma Gwaggon saida ta ɗan harareshi sannan ta amsa Fatuu na ganinta ta daddage ta rangaɗa guɗa duk da bama ta wani iya ba sosae Gwaggon tayi yar dariya, cikin washe baki ta gaishe da ita kafin ta shiga yi mata shaƙiyanci tana faɗin ashe dai da rabon za'a mata makeup na amare a ɗaura mata gwaggaro nan take Gwaggon ta tuna da lokacin da Fatun ta faɗi haka can shekarun baya kafin ta girma ta shiga yin dariya, da sauri Amadu ya fita ya kirawo Kamalu suka dawo falon nan suka haɗu suna ta mata iya shege har saida tace in suka isheta zata fasa Allah sannan suka shafa mata lafiya. Washe gari sai ga Kawu Mani ya kirawota wai ya kira yaji yadda suke nan take sanar mashi ta amince ma buƙatar shi, sosae ya nuna jin daɗin shi harda ce mata shi dama yasan zata amince don su jinin sa'a ne tayi murmushi kawai kafin tace mashi amman ko za'a ɗaura masu aure sai anyi na Amadu yace mata amman mi zai hana a riga yin nasu yadda zasu aurar dashi tare tace mashi ita dai tafi son a riga nashi kuma gidan nasu ma Haisam yasa za'a mashi gyara ne tunda anan zata zauna yace duk yadda take so haka za'ayi tunda anan take son zama lafiya lou ya rinƙa zuwa dama yana yawan zuwa katsinar ko can baya saida yayi tunanin yin mata anan yace alabashshi sai ya rinƙa biyanta kuɗin hayar zaman da take, da sauri tace mashi a'a ba sai yayi hakan ba yana murmushi yace to ai saboda ya fita hakkinsu tunda gidan gado ne tace mashi ai itama tana da kaso a ciki lafiya lou kawai dae fatan ta ya ruƙe su amana kada tayi dana sanin yin auren bayan tsawon lokaci, yar dariya mai sauti yayi yace "Kada ki damu Amaryata, Hajjaju tasan zan ruƙe amanarki shiyasa tayi man maganar ki ni kuma ina ganin ki mashin son ki ya soke man zuciya ba shiri na faɗa tarko" Yadda yayi Maganar har saida tayi dariya don ta fahimci ɗan barkwanci ne sai ga Gwaggo an saki jiki ana shan Love😍

Bayan wata guda aka fara aikin gidan nasu gadan gadan lokacin har Baban su Umar ya samu gida an siya mashi sun tashi Tk ma an saka ranar aurenshi daidai dana Amadu wato rana ɗaya za'a ɗaura masu aure, 6angare guda aka ware masu suke zaune kafin aikin yazo inda suke. Cikin sa'a Kamalu ya rubuta Jamb ya samu point da ake buƙata don yin karatu a Jami'ar daya cike wato Umaru Musa Yar'adua University Katsina (Umyuk), bayan sun yi post Utme cikin sa'a ya samu Admission don fara karatu inda zai yi Degree akan Computer Science, a lokacin sosae suke waya da Farha sun shaƙu da juna ta kai har kuɗi ta turo mashi don ya canza waya saboda in suna yin Vedio call wani lokacin wayar shi na basu matsala, lokacin daya yi ma kawu Amadu magana kan ya rakashi su sayi wayar jin itace ta turo mashi kuɗin saida ya tambayeshi mike tsakaninsu wai dama yana lura da yawan wayar da suke, Kamalun bai 6oye mashi yadda sukai da ita ba na cewa da tayi tana son su zamo abokai, sosae kawu Amadu yayi mamakin jin hakan, bayan an siyo wayar ne suka je nuna ma Gwaggo itama dai tayi mamakin jin Farha ce ta turo mashi kuɗi ya siya saida ta tambayi yadda akai suka san juna ya faɗi mata, sam Gwaggo bata kawo komai ba a ranta tayi tunanin jinin su ne ya haɗu tayi mashi Allah ya sanya Alkhairi, lokacin daya fara karatu ita kuma ta gama Degree ɗinta a Jami'ar Lagos ta nemi da a turo ta Katsina bautar ƙasa da yake suna da hanya sai gashi an turo ta Katsinar har saida Hajiya tayi mamaki lokacin da Hajiya Maryam ta sanar da ita zancen zuwan Farhar wurinta ta zauna don yin service kuma ita ta za6i hakan, lokacin da za ta zo harda uban sababbin kayan sawa da takalma da jakuna irin wanda samari ke amfani dasu a Makaranta ta kawo ma Kamalu, ranar data zo ta kama Friday da rana tunda Tk ya ɗaukkota daga Airport tasha gayun ƙananun kaya ta tambayeshi Kamal yace bai san ko yana nan ba amman bari in sunje bakin shagonsu sai su duba, lokacin da suka iso Kawu Amadu ne kawai a ciki Tk ya tambayeshi Kamalu yace bai nan yana School Farhar harda gaishe da kawu Amadun ba laifi ya ɗan saki fuska ya amsa mata tare da yi mata sannu da zuwa, bayan ta amsa ne ta tambayi kaman zuwa ƙarfe nawa zai dawo yace mata sai anyi La'asar daga haka suka wuce, suna zuwa parlon Hajiya lokacin tana zaune Farhar ta nufeta da gudu taje ta rungumeta Hajiya ta nuna farincikin zuwan ta sosae Tk ya tambayi ina zai kai kayanta Hajiya tace ya kai su Visitor room, bayan sun gama gaisawa Hajiya tayi mata Maganar abinci tace mata bata jin yunwa sai anjima tace to taje ta huta ko, koda taje ɗakin wanda tuni an gyara mata shi ta kwanta a gado kasa yin baccin tayi don ba wanda take son gani irin Kamal ƙarshe sai ta ɗauki wayarta ta shiga lallatsawa, tana haka akayi la'asar ta miƙe ta nufi toilet tayo wanka, shiryawa tayi da atampa mai kyau anyi mata straight gown ta kamata sosae tayi ɗaurin kallabin Zarah Buhari a wurin Fanan taga tana yawan yin shi kuma yana mata kyau shine itama take yi kuma yana mata kyau sosae harda yar kwalliya tayi duk da ita bata cika son yin kwalliya a fuskarta ba kamar Fanan, tana cikin shiryawa Hajiya ta shigo cikin ɗakin da sallama ta juyo tana kallonta da murmushi Hajiyar tace "au ni nayi zaton ma kina nan kinata bacci naga anyi La'asar gashi baki ci komai ba nace bari in zo in tashe ki ashe ke kina nan kina ta rangaɗa kwalliya", still murmushin take yi bata ce komai ba,

"To wannan kwalliyar ta mecece daga zuwa kodai angon nawa anan yake shine zai zo yin sannu da zuwa?" dariya Farhar tayi tace mata No kawai tayi ne kuma tana son ta fita jikinta ya ɗan saki Hajiyar tace to ita ina ta sani da zata je, ɗan jimm tay kafin tace ko gidan su Zarah sai ta gaishe da Granny ɗinta, sosae Hajiya taji daɗin jin hakan don ya tabbatar mata da Farhar ta canza da gaske tace mata to tazo ta fara cin abinci kafin ta tafi suka nufi ƙopar fita harda kama Hajiyar tace wai bari ta taimaka mata taga bata yin tafiyar sosae Hajiya na dariya tace da wannan sandar tata sai tayi tafiyar da ita bata iya yi, lokacin da suka fito daga cikin corridor Saude na niyyar shiga Kitchen ganin su yasa ta dakata tana murmushi tana niyyar gaishe da Farha sai ji tayi ta rigata gaishe da ita Sauden ta amsa tare da yi mata anzo lafiya da tambayar yan'uwanta da Momynsu duk tace mata suna lafiya Hajiya ta tambayi Farhar a dining zata ci abincin tace a'a a kawo mata a parlor yadda tana ci suna hira Saude ta juya da sauri tana faɗin to bari ta kawo mata can suma suka nufo cikin parlon, a saman c-table aka shirya mata kayan abincin bayan tayi serving nata tace mata aci lafiya Farhar na ɗan murmushi tayi mata godiya, lokacin da Saude ta nufi hanyar Kitchen sosae take mamakin canzawar Farhar a ranta, ba wani sosae taci ba tace ta ƙoshi Hajiya dake yin kallo ta kalleta tace dama wannan ɗamammiyar rigar ai bazata bari taci wani abinci sosae ba basu son suna ɗinka wadatattun kaya suyi ta faman takura kai, murmushi kawai Farhar tayi itama ta maida idonta kan Tv tana kallon abunda Hajiya ke kallo can bayan wani ɗan lokaci ta miƙe ta nufi hanyar bedroom, bada daɗewa ba ta fito tana ruƙe da ƙatuwar leda mai tambarin Shopping Mall ɗin Mamanta, cikin parlon ta dawo daga bakin kujeru ta tsaya tace ma Hajiya zata je ta dawo ta ɗaga mata kai har zata juya tace mata to ina mayafi kuma ta kalleta tana ɗan yamutsa fuska tace takura mata yake gashi sai yayi ta faɗuwa saboda bata saba sakawa ba Hajiya tace mata amman bai kyautu kuma ai ta fita haka ba tana yar musulma kuma ma ba kyau fita hakan ai ta sani tunda tana zuwa islamiyya su kan su waɗannan kayan bai kamata tana saka su ba ta fita indai ba lullu6e jikinta zatayi ba komi mutum zai yi ya rinƙa tuna lahirar shi, ɗan murmushi tayi tace Ok zata gyara ta aje ledar ta juya don ta ɗaukko mayafi Hajiya ta bita da kallo tana murmushi sosae take jin daɗin yadda ta canza don inda da ne tayi mata Maganar shigar da tayi yamutsa fuska zatayi kuma bazata canza ba, gyale ta yafo daya shiga da atamfar saman kafaɗa duk da baida wani girma yadda ta yafan ya rufe mata bayanta bayan ta ɗauki ledar tayi ma Hajiya sai ta dawo, ko a bakin gate saida su Officer sukai Maganar canzawarta bayan ta gaishe su ta wuce, tana zuwa saitin shagon kallo ɗaya tayi ma na ciki ta gane Kamalun ne duk da ya juya baya yana sanye da riga da wando na light blue shadda, tsayawa tayi tana murmushi cikin zazzaƙar muryata tace a bata Sweet yace wane iri saida ta wurga idonta saitin ledojin Sweet ɗin taga wani ansa mango da sauri tace mashi shi yace Ok guda nawa tana yar dariya tace pack guda, ɗaukko jakar Sweet ɗin yayi yana juyowa idanunshi suka shiga cikin nata har saida yay alamun tsorata Farhar ta saka dariya, da tsananin mamaki yace da gaske itace tana murmushi ta ɗaga mashi gira tare da furta yes,

"Amman yaushe kika zo?" still da mamaki ya tambaya tace mashi É—azun ai tazo nan ta tambaye shi Uncle nashi yace bai dawo ba bai faÉ—i mashi bane yace mata lokacin daya dawo daga School É—in shi kuma ya tafi kasuwa to basu haÉ—u ba shiyasa bai san data zo ba,

"Amman ko fa yau da safe munyi waya baki faɗi man yau zaki zo ba" ɗan farfar tayi da ido tace "i want to give you a surprise" yana murmushi yace aikuwa gashi ta bashi shi har tsoro ma yaji daya ganta tana yar dariya tace ai ta gani, shiru sukai ta shiga jefa mashi wani kallo shi kuma yana ɗan murmushi can tace "Ka ƙara kyau" yar dariya yay duk dimples ɗinshi suka lotsa yace "ina wani kyau kullum ina zaryar School rana yana buguna" tace duk da haka ita taga ya ƙara kyau kodai saboda ya fara zuwa University yana haɗuwa da yan'mata shiyasa yake gyara masu kanshi, tayi Maganar tana mashi wani kallo yay yar dariya yace shida bai daɗe da fara zuwa ba kuma shi karatunshi ya saka a gaba ba ruwan shi da wasu yan'mata ta ɗan yamutsa fuska tace Allah yasa gaskiya yake faɗa mata, rantse mata yay kan shi ba ruwan shi da wasu yan'mata ta ɗan yi murmushi ta furta Better gara ya maida hankali yayi karatu ya bar duk wani shiriritar yin yan'mata ya furta mata in sha Allah,

"Ka bar ni a tsaye haka ake welcoming baƙo" ta faɗa ta ɗan tura baki da sauri ya bata haƙuri yace ko zata shigo cikin shagon ga kujera ta girgiza mashi kai tace ciki zai shigar da ita zata gaisa da Grandma ɗin shi yace to, fitowa yay ya kulle ƙopar shago ta zagayo wurin shi yanata mata murmushi ganinta da kaya yace ta kawo ya ruƙe ta sakar mashi hannu guda suka kama tare suka nufi cikin gidan, faran faran Gwaggo ta tarbeta cikin sakin fuska a falo suka zauna ta gaishe da Gwaggon tana murmushi ta amsa mata tare da yi mata anzo lafiya da tambayar yan gidansu tace mata duk suna nan lafiya Kamalu yace ma Gwaggo tazo yin bautar ƙasa ne nan cikin fara'a tayi mata fatan alkhairi da fatan Allah ya bada sa'a yasa a gama lafiya ta amsa da Amin, miƙewa Gwaggo tayi ta fita daga cikin falon lokacin Farhar tace mashi kayan shi ne a cikin ledar akwae ma saura a gida bata iya ɗaukkowa sai dai in zata koma sai su je tare ya daukko, da mamaki ya buɗe ledar ya shiga duba kayan kafin da tsananin mamaki ya ɗago ya kalleta yace ya zata yi wannan hidiman haka sosae ta yamutsa mashi fuska tare da yi mashi wani kallo tace What are Friends for abunta nashi ne so bata son yana yi mata irin haka kawai inta bashi abu ya amsa shikenan, yana murmushi yace to tayi haƙuri yayi mata godiya tare da faɗin Allah shima ya bashi ikon kyautata mata haka tace bata buƙata iya haka da ya saki jiki da ita ya wadatar, ruƙe da tray mai ɗauke da kayan abinci Gwaggo ta dawo ta daura akan table ta matsar dashi gaban Farhar tana niyyar buɗe Warmer ɗin Farhar tace wllh ta ƙoshi yanzu taci abinci Gwaggon tace ai abun marmari ne taci ko ba yawa tunda ita baƙuwar su ce, Waina ce da miya taji alaiyahu da nama sai ƙamshi take Gwaggo ta kalleta tana murmushi tace ta dai iya cin waina ko tay yar dariya tace eh ana masu shi, bada yawa tasa ta zuba mata ba ta nufi Fridge ta ɗaukko mata ruwa da lemu ta kawo mata, bayan ta koma ta zauna Kamalu ya taso da kayan ya dawo wurin Gwaggo ya nuna mata yace ita ta kawo mashi tace ma akwae saura zasu je ya ɗaukko, duba kayan gwaggo ta shiga yi kafin ta ɗago da mamaki ta kalli Farha dake cin waina a nutse tace harda hidima haka banda wadda akai ai da ta bassu kada ɗawainiyar tayi yawa idonta a ƙasa tana ɗan murmushi tace mata a'a ba komai, godiya Gwaggon tayi mata da Addu'ar Allah ya saka da alkhairi, bayan ta gama ci harda ɗaukar tray ɗin zata fitar da sauri Kamalu ya miƙe ya kar6a yaje ya kai Kitchen bayan ya dawo tashi Gwaggo tayi ta fita, tambayoyi ta shiga yi mashi kan karatun shi yana bata amsa suna haka aka shigo siyan abu sai lokacin ya tuna da ya baro shago a buɗe yace mata zai koma shago zata zauna anan tace a'a bari su fita tare, bayan sun fito Kamalun yayi ma Gwaggo magana ta leƙo sukai sallama sannan suka fito shi ya shiga cikin shagon ita kuma ta tsaya daga gaba tana kallon yadda yake sallamar yaron da yazo siyayyar tana ta murmushi, bayan ya sallami yaron ya tafi tace mashi gaskiya irin wannan business ɗin bai dace dashi ba kamata yay ace a Haɗaɗɗan Office yake A.c na hura shi har saida yayi dariyar da haƙoran shi suka fito yace shi ina zai samu irin wannan aikin abunda ma duka yanzu ya fara karatun yace ai gara ma wannan sana'ar a cikin shago yake kuma akwae fanka a garinsu kafin yazo nan rake yake saidawa akan table wani lokacin cikin rana ma ta ɗan buɗa ido alamar mamaki, ganin tana ta tsayuwa yace mata ko zata shigo tace a'a bari ta wuce yaushe zai zo amsar sauran kayan yace ko in anyi Magrib daga masallaci sai ya shigo tace ok tare da ce mashi Bye, tana niyyar tafiya ya tsaidata ya miƙo mata ledar Sweet ɗin ta ɗan girgiza mashi kai alamar a'a ya ɗan mariraice mata fuska yace please wannan ce kyauta ta farko daya ta6a mata duk da ba wata mai yawa bace ta amsa zai ji daɗi in kuma bata son irin shi sai ya canza mata wani, murmushi tayi tace ba kowane Sweet take sha bane yace ok ta faɗi mashi wadda take sha sai ya kira Uncle ɗinshi tunda yana kasuwa ya taho mata da ita tace No ba sai yayi haka ba tunda wannan ya bata zata sha ta miƙa mashi hannu ya bata tayi mashi godiya kafin ta ɗaga farin hannunta fatt tana mashi bye bye shima yayi mata ta tafi ya leƙo kai yana kallonta itama tana yi tana waiwayen shi tana mashi murmushi har saida ta kusa gida sannan ya maida kan shi, sai gab da Magrib Amadu ya dawo lokacin daya ga kayan da Farha ta kawo ma Kamalun shima ya jinjina abun har yana faɗin Allah yasa dai kar yazama wata matsala Gwaggo tace Amin, bayan sun gama sallar Magrib Kamalu yace mashi zai je ya amso sauran kayan kamar yadda yace mata Amadun ya tafi shi kuma ya wuce part ɗin Hajiya, a parlor ya iske Farhar tana kallo da yake ba salla take yi ba Hajiya kuma na bedroom ɗinta, sosae ta nuna jin daɗin zuwan nashi ya zauna nan suka shiga yin hira, har aka kira sallar isha suna zaune tace mashi yaje yayi salla in ya dawo sai ta ɗaukko mashi yace to, koda aka gama yin sallar ya dawo hirar suka cigaba da yi har Hajiya ta fito ta iske su suka gaisa dashi cikin fara'a ta tambayi ya karatunshi yana dai maida hankali ko yace mata sosae, ita kanta Hajiya saida ta ɗan yi mamakin ganin yadda suka saba da juna ƙarshe saida Farhar ta matsa mashi suka ci abinci tare bayan sun gama yace mata zai tafi harda ce mashi ai gobe ba School ko yace ya baro Uncle ɗin shi yana jiranshi ne sannan taje ta ɗaukko mashi tace ma Hajiya zata rakashi ta dawo tace to, tare suka kama ledar kayan suna tafe suna hira har suka iso bakin shagon yayi mata godiya ta gaishe da Amadu ya amsa mata ya ɗan saki fuska kafin tayi ma Kamalun saida safe ta tafi yana shiga cikin shagon Amadu ya wurga mashi harara tun ma kafin yayi magana yana murmushi ya bashi haƙuri yace itace ta ruƙe shi da hira, a ɗan fusace Amadun yace shi kuma da yake tsoronta yake ji da bazai ce mata zai tafi ba Kamalun nata ɗan murmushi ya ƙara bashi haƙuri yace bazai sake ba, Bayan Farha ta koma saida Hajiya ta tambayeta yadda akai tasan Kamalu har suka saba haka tace mata a Abuja wurin bikin Yaya Nameer suka san juna itama Hajiyar bata kawo komai ba a ranta tayi tunanin jininsu ne ya haɗu don shima Kamal ɗin kamar Fatuu yake yana da farin jini dama kuma yawanci Mutum mai kyau haka yake da shiga rai, bayan sun tashi daga shagon sun shiga gidane Kamalu ya haɗa duka kayan yace ma Amadun ya ɗauki wanda yake so da sauri yace mashi a'a yayi amfani da kayanshi, marairaice mashi yayi yana mashi magiya da ƙyar ya ɗauki wasu jeans da t-shirt yace sun isa ya gode duk da haka saida ya ƙara mashi da agogo da takalma, Washe gari Gwaggo ta kira Fatuu anan take sanar mata game da abubuwan da Farha ta kawo ma Kamalu sosae tayi mamaki tace banda kuɗin da akace ta turo mashi ya canza waya Gwaggon tace mata wllh kuwa kaya sosae ta kawo mashi Fatun tace ita gaskiya abubuwan da take mashi basu kwanta mata a rai ba tunda ansan halinta duk da ta canza kada daga baya abu yazo ya zama wata matsala ko tace zata yi mashi gori, Gwaggo na murmushi tace to ai dai ba roƙonta akayi ba ita taji ta gani duk da dai tana kyautata mata zaton da zuciya ɗaya take mashi Fatun tace to Allah yasa amma dai duk da haka a daina amsar mata kaya zata kira Kamalun ma tayi mashi magana Gwaggon tace gashi can ɗaki bari ta bashi tace to, bayan sun gaisa ta tambayi ya karatu ya amsa mata tambayar shi tayi wai mike tsakaninshi da Farha ne yace mata shi wllh ba komai daga dai abotar data ce mashi tana son suyi shikenan Fatuu tace to ita bata son yana amsar mata abubuwa ko yace zai tambayeta wani abu don zai iya zama matsala duk abunda yake so ita ya kirata in sha Allahu indai baifi ƙarfinta ba zata mashi yace mata to tare da yi mata godiya daga baya sukai sallama.

Bayan su Farha sun shiga Camp sosae take kiran Kamalun a waya su kuma yi Vedio call a lokacin aikin da ake yazo kan inda suke zaune aka buƙaci sai sun tashi Gwaggo ta yanke kama masu hayar inda zasu zauna kafin a gama anan unguwar, a bakin Kawu Mani Hajiya taji zancen hayar da Gwaggo zata kama ta kirata tace ba sai ta kama wata haya ba tunda ga wurin zama a gidanta su dawo nan kawai zuwa a gama aikin, ba dama ta musa mata tayi godiya sosae, a ɗakin Tk Amadu da Kamalu suka koma sai ita kuma Gwaggo Hajiya ta bata ɗakin dake kusa da nata, tun gwaggo bata saki jiki ba har dai ta saki in dai tana gida tare suke aikin gidan da Saude har Hajiya saida tayi mata magana kan waya sakata ta rinƙa yin aiki tana dariya tace mata ta saba ne in bata yi ba jikinta bai mata daɗi Hajiyar tace to kar dai taja mata sharri tunda ita dae bata sakata ta rinƙa yin aiki ba Maganar har saida taba Gwaggon da Saude dariya, zaman su a gidan gwanin daɗi tare suke cin Abinci da Hajiyar wani lokacin harda su Amadu in suna gida, ana haka su Farha suka fito daga Camp lokacin data dawo ta iskesu a gidan sosae ta nuna jin daɗin hakan shaƙuwa sosae taci gaba da shiga tsakaninsu da Kamalu koda yaushe in tana gida zaka gansu tare in kuma suna shago ta bishi can har Assignment in an ba Kamalun take taya shi suyi harda lesson suke yi ta koya mashi turanci da yake tana yawan yi mashi magana da turanci ya ta6a ce mata shi ba sosae ya iya ba shine take koya mashi ita kuma sai tace ya koya mata fullanci yadda suke abun gwanin sha'awa in suna yi a gaban su Hajiya da Gwaggo suyi ta burge su shidai Kawu Amadu yanzu ya zura masu ido kawai har abinci wani lokacin tare suke ci su biyu.

A kwana a tashi cikin Fatuu nata ƙara girma yana gab da shiga wata tara, ta bangaren Arɗo kuwa tuni an kai shi Asibitin da taimakon Khalid anyi mashi duk abunda ya dace ba'a samu wata babbar lalura ba a tattare dashi ba kawai tsufa ne da gajiya sai yan ƙananun cututtuka an bashi magunguna da abubuwan da zai kiyaye ba laifi yanzu ya ƙara samun lafiya duk harkokin shi na mulki kuma Baffan su Fatuu ya ɗaura akai masu tsegumi nata yi. Lokacin da cikin Fatuu ya kai wata tara har an kammala aikin gidansu Gwaggo gida ya zama na yan gayu wanda yana ɗaya daga cikin gidaje masu kyaun gaske a unguwar abun sai wanda ya gani yanzu ta gate ake shiga gaba ɗaya harabar gidan interlock ne duk da bata da girma sosae don ginin ya cinye filin amman Mota biyu zata iya shiga daga jikin gidan gefen gate aka fitar ma da kawu Amadu babban shago wanda yana da ƙopa da zai rinƙa shiga gidan ta ciki, gidan part biyu ne na Gwaggo da kuma na Amadu sai akwai ɗaki da falo daban matsayin na baƙi, a kowane bangare na Gwaggo da Amadu akwae ɗan babban falo sai Bedroom guda biyu da toilet a tsakiyar su sai kuma Kitchen daya sha cabinet sai akwae toilet na waje cikin haraba, iya fentin gidan da yadda aka tsara ginin da ƙopopi zuwa winduna da fitilun da aka saka abun kallo ne kana ganin ginin zaka san ba ƙaramin kuɗi aka kashe ba su Gwaggo baki yaƙi rufuwa sai farinciki ake mutane yan'uwa da abokan arziƙi nata zuwa yin Allah ya sanya Alkhairi har Hajiya ma tazo taga gida itama ta yaba sosai ta kuma yi Addu'o'i, lokacin da Fatuu taga Vedion gidan zo kaga murna harda cewa ba don cikin jikinta yayi girma sosae ba da sai tayi tsallan murna Gwaggo nata dariya haka Mino ma data gani ita harda tsallan tayi tace bada daɗewa ba zata zo ta gani Gwaggo tace ta bari tunda ga bikin Amadu ya matso sai tazo tace ita dai tana son zuwa kusan wata biyar fa yanzu rabonta da Katsina in bikin yazo ta ƙara zuwa, Bayan gama ginin kuma sai ga kuɗi Haisam ya turo ma Kawu Amadu wai a siya furniture Gwaggo harda ƙwalla tayi ma Haisam da tasa aka kira mata shi Vedio call tace hidiman nan tayi yawa shima yaji da nashi hidindimun yace mata ba wani abu ai duk ɗaya ne, godiya sosae suka yi mashi harda Baffan su Fatuu ya yi mashi godiyar, Kawu mani ma yazo yaga gida ya yaba ya kuma yi Allah a sanya Alkhairi sannan shima ya bada gudunmawar shi ta siyan furniture har Baffan su Fatuu da Hajiya duk saida suka bada gudunmawar kuɗin siyan furniture daɗi har yayi ma Gwaggo yawa sai godiya take ga Allah, cikin sati guda aka zuba furniture ɗin gaba ɗaya Bedrooms ɗin part ɗin gwaggo an saka set na gadaje sai falon ma an saka kujeru masu kyau da carpet harda kayan kallo da labulaye komai dai na ƙawata wuri an saka kai kace part ɗin yarinyar mace ne, haka part ɗin Amadu a bedroom guda ɗaya an saka set ɗin gado sai falon an saka carpet da labulaye sai ɗayan ɗakin mai falo wanda yake matsayin na baƙi a bedroom ɗin irin ƙatuwar katifa da bata hawa gado aka saka da carpet da labulaye sai falon kujerun falon gwaggo na da aka gyara suka koma sababbi aka saka ko ina dai ya fito yayi kyau daidai daidai.

Cikin Fatuu har yayi wata tara da yan kwanaki lokacin su twins shekararsu guda da wata biyu har sun yaye kan su don da kansu suka daina shan Nono, Ranar wata laraba da safe gidan ba kowa sai ita kaɗai da mai aikin su Fanan da Haisam na wurin aiki haka su twins ma suna makaranta tana cikin baccin safen data koma wani irin ciwon mara ya tasheta, jin tana jin fitsari yasa ta lalla6a ta tafi toilet don tayi, tana duƙawa don yin fitsarin taga discharge irin wanda ta gani da haihuwar su twins tana gani ta gane haihuwa ce ba arziƙi ta fito daga cikin toilet ɗin ta nufi wayarta dake a gefen filo ta shiga kiran Fanan dama kullum sai tace mata data ɗan ji ciwo ko yaya ne in bata gida tayi sauri ta kira ta, tana fara yin ringing Fanan ɗin ta ɗaga kafin Fatun tace wani abu ta rigata tambayar haihuwan yazo ne cikin nishi tace mata eh gata nan mararta ta fara mata ciwo da sauri tace Ok gata nan zuwa ta katse kiran, tana katse kiran mai aikin su ta shiga kira wadda babbar mace ce baturiya bayan ta ɗaga ko amsa gaisuwar da take mata bata yi ba cikin sauri ta bata umarnin taje part ɗin Fatuu ta fara labour ta taimaka mata ta shirya gata nan zuwa da sauri mai aikin ta amsa mata tana katse kiran ta nufi part ɗin Fatuu, bayan wasu mintuna Fanan ɗin ta iso a Motar asibitinsu tare da wasu nurses guda biyu lokacin da suka shiga bedroom ɗin da Fatuu take ta shirya da taimakon mai aikin nasu ciwon kuma ya ɗan ƙara tsananta ba 6ata lokaci suka ɗaurata akan wheelchair da nurses ɗin suka shigo da ita Fanan kuma cikin sauri ta ɗauki abubuwan da za'a buƙata dama ashirye suke, saida suka hau hanya sannan ta kira Haisam ta sanar mashi nan take hankalinshi ya tashi jin Babyn shi na naƙuda don bai manta yadda aka sha wanccan gumurzon ba da sauri yace ma Fanan gashi nan zuwa asibitin don Allah kada ta bari ta wahala sosae tace mashi to suyi mata addu'a, suna isa asibitin aka nufi labour room da ita aka shiga yi mata duk abunda ya dace kan kace mi naƙudar ta ida kankama gaba ɗaya Fanan ta ruɗe sai faman yi mata sannu da Addu'o'i take kaman zata mata kuka, cikin ikon Allah basu fi minti talatin da zuwa ba ta haiho san6aleliyar jaririya dama tun wurin scanning an faɗi masu mace ce sai gashi hasashen su ya tabbata zo kaga murna a wurin Fanan sam ta kasa rufe baki sai faman faɗin Alhamdulillah take, koda Haisam ya iso ai saidai ya taras da Baby shima har fuskarshi ta kasa 6oye farincikin sosae yaji daɗin yadda bata sha wahala ba kamar tasu twins, lokacin da aka bashi Babyn zuba mata ido yay yana kallonta da murmushi sak fuskar Fatuu ta ɗaukko in akwae abunda za'a ce ta ɗaukko nashi to ƙilan saidai ko farinshi don jajir take da gani zata fi Fatuu fari amman komai na fuskarta na Fatuu ne Fanan ma saida tace Zarah ta biyo, tun a asibitin bayan yayi mata huɗuba ya raɗa mata suna AISHA wato sunan Mahaifiyar Fatun, yan Nigeria sai farincikin jin haihuwar ake kowa daya ga Babyn a Vedio sai ya faɗi kamanninta da Fatuu, Sosae itama Fatun tayi farinciki ganin Babyn data haifa koda Fanan ta faɗi mata sunan da aka saka mata saida tayi ƙwalla wata irin ƙaunar yarinyar ta mamaye mata zuciya. Bayan sati biyu da Haihuwar suka iso Nigeria nan aka Shiga shirin yin suna wanda na iya yan Family ɗin su ne, sati guda da dawowarsu akayi sunan duk yan'uwa sun zo su Gwaggo da Hajiya har Aunty Mareeya ma tazo Farha dai na Katsina bata biyo Hajiya ba, su Hajia Zainab ma sun zo Fauzy dai ba'a zo da ita ba a Nasarawa aka barta don tayi nauyi sosae haihuwa ko yau ko gobe gashi itama an tabbatar da yan biyu ne, Aunty Laila ma ciki ne da ita har ya fito sosae don zaiyi wata biyar, Mino na ganin cikin Lailan ta ƙara shiga damuwa dama tana ta zura ido taga ta samu ciki amman shiru har yanzu kusan wata bakwai da yin aure, bayan an gama yin shagalin sunan da daddare Mino ta samu Fatuu a Bedroom ɗinta cikin sa'a ita kaɗai ce sai Baby Esha kamar yadda aka yanke za'a ringa kiranta, a bakin gado ta zauna Fatuu na kallonta ta gane akwae abunda ke damunta cike da kulawa tace "Amaryarmu ya akai kamar akwai abunda ke damun ki ko?" kai Minon ta ɗaga mata Fatun ta tattara hankalinta gaba ɗaya a kanta tace ta faɗi mata miye kaman zata yi kuka tace dama ce mata zata yi ita taga har yanzu bata samu ciki ba kuma ga Aunty Laila nan da aka yi bikinsu tare har ta samu nata harma ya girma Fatun tay kasaƙe tana kallonta tama rasa mi zata ce mata can ta tambayeta tana period lafiya lou da sauri tace mata eh tana yi kamar yadda ta saba kuma shina abunda tace mata sai anayi ake samun cikin sosae suke yi, kunya ce ta kama Fatun ta juyar da kanta gefe a ranta ta raya bata san ranar da Mino zata rabu da wauta ba, juyowa tayi Minon ta ƙura mata ido a nutse tace mata ta kwantar da hankalinta tunda ba wata matsala zata samu dama ba daga anyi aure ake samu ba kowa da yadda yake har ta bata misali da Fanan tace mata bata ga har yanzu itama bata samu ba kuma ga Auntyn su Nameer ma itama har yanzu bata haihu ba....katseta Minon tayi idanunta sun cika da ƙwalla tace yanzu itama bazata haihun ba kenan da sauri Fatuu tace "ni bance bazaki haihu ba, kawai na baki misali ne don haka ki kwantar da hankalinki don shi in ka tada hankalinka to baka samu, sannan kada ki sake kiyi ma wani irin wannan Maganar da kikai man za'a ɗauke ki mara kunya ne in dae kina da wata matsala game da gidan auren ki ni zaki rinƙa sanar mawa kamar yadda kikai yanzu" da sauri ta ɗaga mata kai Fatuu tace ta saki ranta in sha Allahu kwanan nan zata samu Minon tayi ɗan murmushi kawai, miƙewa tay zata tafi Fatuu ta tambayeta anan zata kwana ne tace mata eh tace to ta kwanta anan mana tunda ita kaɗai zata kwana su twins ba anan zasu kwana ba Minon tay ɗan jim kafin da ƙyar tace mata Ya Nameer yace a part ɗinshi zasu kwana Fatun tay ɗan murmushi tare da ɗaga mata kai tace taje saida safe ta juya ta tafi Fatuu nata kallonta har ta fice ta ɗan girgiza kai a ranta ta raya ta zata haihuwar sauƙi ne da ita, dasu Gwaggo zasu tafi Fatuu ta bata akwatuna set guda data siyo ma Amadu acan na lefe tace mata da set biyu ma taso ta siyo to kayan zasu yi yawa ne Gwaggon tace ai dama sun siya set guda, da shi Amadun ma set biyu yaso a siya tace mashi tunda Fatun tace zata taho da wasu a barsu haka. Bayan sati biyu da yin sunan Fatuu Fauzy ta haiho twins duk mata saidai ita Cs aka mata, yaran saidai ace Tubarkallah masha Allah sak Sameer suka biyo gasu identical ne suma kamar na Fatuu amman su ta gashinsu ake banbanta su Hassanar nata baƙi ne wuluk hussainar kuma kalar na sameer ne baida baƙi sosae kowa yaga yaran sai ya yaba zo kaga murna wurin dangin Fauzy karma Aunty Mareeya taji sam bakinta ya kasa rufuwa sai kiranta ake itama ana mata barka, saboda aikin da aka mata akace baza'ai taron suna ba saidai duk akaje Nasarawa aka yi masu barka aka kuma yi ma maijego alheri sabon Baba Sameer sai nan nan yake da Babies ɗin da kuma mamansu ko kunyar mutane bai ji yaran sun ci sunan Mahaifiyar Sameer data Fauzy wato Zainab da Haleema. Sati guda da haihuwar Fauzy Fatuu ta tafi Katsina dama haihuwar ta tsaidata lokacin saura sati ukku bikin Amadu da Tk, saida taje ta ƙara jinjina yadda gidan nasu ya haɗu, tana zuwa Washe gari suka tafi kasuwa da gwaggon don ƙarasa siyayyar kayan lefen daga can wurin K.b tailor suka wuce dama Fatuu tasa Kawu Amadu ya kai mashi wasu kaya ya ɗinka lokacin da suka je har ya gama su suka bashi wasu cikin wanda suka siyo Fatuu tace don Allah nan da sati ɗaya suke son su kai lefen za'ai, yana dariya yace ai tasan bai mata wasa ko don kada ya 6ata ran Maigidanshi Haisam itama saida tayi dariya don ta fahimci da biyu yayi Maganar saboda tun farkon fara kawo mashi ɗinkinta da akai, bayan zuwan Fatun tayi ma Aunty Mareeya magana kan tana son magunguna masu kyau da Haulat zata yi amfani dasu ta can bangaren Haulat ɗin ma tana amfani da wasu da aka kawo mata daga Nijar, kwana biyu da zuwan Fatuu aka kai lefen Tk akwatuna set ukku masu guda huɗu guda sha biyu kenan kuma bako ƙwandalar Tk a ciki komai Hajiya tayi mashi sai su Senator da Hajiya Maryam da suka bada gudunmawa, a yadda Hajiya ta tsara a nan part ɗinta zai zauna Senator har Maganar siya mashi gida yayi amman tace a kusa da ita take son ya zauna, sam hakan baima Hajiya Maryam daɗi ba tace ma Hajiyar ba gwara ta bari a siya mashi gida ba yanzu nan part ɗinta a ina zai wani zauna Hajiyar tace lafiya lau tunda falonta yana da girma sosae zata sa a maida shi bangare biyu sai suyi amfani da ɗaya bedrooms kuma tunda guda huɗu ne biyu ita ke amfani dasu biyu kuma na baƙi sai su zauna a ɗaya in kuma biyu suke buƙata sai ta basu na baƙin sai ɗayan nata ya koma na baƙi Hajiya Maryam ɗin ta nuna yanzu kuma idan wata hidima ta kama ko suka zo taya bedroom ɗaya zai ishe su in ta basu biyu Hajiyar tace to ba ga Bedroom ɗinta ba sannan ga wangamemen gidan Yayanta can a G.r.a sai a tafi can, duk da haka ta nuna hakan bai mata ba ƙarshe Hajiya tace shikenan in taga da takura daga baya zata sa a ƙara wasu Bedrooms ɗin a can ɗayan bangaren falon wurin Dining Area tunda akwae fili sai a barsu matsayin na baƙi amman tare zata zauna da Tukur don matsayin ɗa yake a wurinta yaron da tun yana ɗan ƙarami aka bata shi miye don ta zauna tare da iyalinshi dole Hajiya Maryam ta haƙura, har kiran Tk Hajiya tayi ta faɗi mashi yadda ta yanke game da zaman su tare tace bata san ko hakan zai takura mashi ba amman in yafi son zama daban lafiya lou sai a siya mashi gidan bawan Allah harda kukan daɗin shi yace mata Wllh dama damuwarshi kenan yadda zai rabu da ita yana kuka yake mata godiya da Addu'o'i, har iyayenshi ya kira yana kuka ya faɗi masu irin gatan da Hajiya tayi mashi Mahaifinshi har saida yazo yayi mata godiya shima harda kukan nashi, to Kamar yadda Hajiyar tace haka akayi ma falon nata ba raba shi akai ba kawai anyi wani ɗan gini mai kamar ado ta yadda falon ya koma bangare biyu sai Kitchen ma da yake yana da faɗi da tsawo shima aka maida shi bangare biyu sannan gaba ɗaya gidan aka yi mashi Fenti mai kyau don ba wani gyara da yake buƙata komai lafiya lou don gini ne bana wasa ba. Ana saura sati biyu bikin aka kai lefen Haulat akwatuna takwas harda babbar ghana must go, ba laifi an zuba manyan kaya kai kace lefen budurwa ne budurwar ma wadda tayi sa'a sai faman yabo ake farinciki ya cika iyayenta ita kanta Haulat ɗin harda kukan daɗinta don ko a aurenta na farko bata samu kaya haka ba duk da shima dai anyi mata kayan ba laifi, bukukuwa nata matsowa ana ta shirye shirye bangaren Amadu ba wani shagali da za'ai don Haulat ta nuna bata so dama shima Amadun ba damunshi sukai ba kawai dai zata yi Wa'azi sai Walima bayan an kawota, bangaren Tk kuma shi za'ayi kamu ana gobe ɗaurin aure sai Walima bayan an kawo Amarya amman can bangaren Amaryar zata yi wasu abubuwan, ana saura sati guda Hajiya ta kira Gwaggo a waya tace mata mi zai hana ta bada dama a ɗaura auranta tare dana Amadun lokacin duk mutane sun haɗu don kowa ya shaida tana ganin hakan zai fi dole Gwaggon tace to duk da ita a yadda taso su Kawu Manin suje can wurin kawunta shibaɗo a ɗaura auren nasu acan Daura, ana saura kwana biyar bikin Amarya Mino ta iso Fatuu ce taje Airport ta ɗaukko ta, ana sauran kwana ukku su Yadikko suka iso shi Baffan su Fatuu sai daren ɗaurin aure zai zo, sosae sukai Al'ajabin ganin yadda aka maida gidan sunata yabawa, a ranar akayi ma Amaryar Tk jere Bedroom biyu wanda Saude ke amfani dashi da kuma na kusa dashi Hajiya ta basu don gado biyu aka mata sai haɗaɗɗun kujeru dasu kayan kallo haka Kitchen ma an zuba mata kaya sosae daga yanayin kayan zaka fahimci suna da hali, washe gari lokacin saura kwana biyu akayi ma Haulat itama jeren an mata tsadaddun saitin gado da kujeru harda kayan kallo amman su Amadu ne ya siya mata da freezer sai Kitchen ma anyi mata kaya ba laifi harda su cooker gas da sauran kayan amfani na zamani.

Alhamdulillah Ranar Asabar da Misalin ƙarfe sha biyu da rabi na rana Jama'a suka shaida ɗaurin auren Amadu da Haulat sai Khadija (Gwaggo) da Kawu Mani a masallacin gidan Hajiya su ango Kawu Amadu ansha babbar rigar farar shadda sai washe baki yake ganin abun yake kamar a mafarki, sosae mutane suka halarci ɗaurin auren har Nameer yazo da kuma Senator, misalin ƙarfe biyu bayan anyi sallar Azahar aka ɗaura auren Tukur da Asma'u wadda ake cema Husna a Masallacin G.r.a dake layout Senator ne ya kar6ar mashi auren sai fatan Allah yasa alkhairi yaba ma'auratan zaman Lafiya, Gidan Gwaggo ya cika da yan biki duk an sha anko baka jin bakin kowa sai Aunty Mareeya sai shegantaka suke ma Gwaggo har saida suka matsa mata ita da Fatuu sukai mata kwalliya sai ga amarya Gwaggo ta fito fess kai kace ba ita ba tasha leshi mai kyau gaba ɗaya duk sun cikata da kunya, bayan sallar La'asar jerin Motoci suka je daukko Amaryar Tk bayan an kawota aka ɗaukko Haulat abun sai san barka komai ya tafi daidai dangin Hajiya sun yi ma Tk kara tun daga kan yan Daura da yan nan Katsina duk sunzo har Hajiya Maryam ma tazo haka Fanan dasu Mom ɗin Haisam duk sun zo, ta bangaren Tk ɗinma danginshi duk sun zo, Washe gari da wuri akai Walima saboda masu tafiya su Hajiya Maryam da Mom har Nameer ranar zai koma Mino dai ta roƙi ya barta ta ƙara kwana biyu ya amince, a ranar da daddare angwaye suka shiga ɗakunan Amaren nasu sai fatan Allah yasa Albarka ya bada zuriya ɗayyiba.

Bayan sati guda da yin bikin su Fatuu suka koma lokacin Esha ta fara girma tubarkallah washe garin tafiyar su ranar Lahadi ango Kawu Mani yazo gidan harda akwatunan shi guda biyar na kaya da yayi ma Gwaggon da Kayan abinci sosae ta nuna jin daɗinta tayi mashi godiya, ta ɗauka zai tafi ne sai taga ba haka ba ashe zuwa yay shima wurin Amaryar tashi duk da ba haka taso ba taso ace sai bayan kaman wata guda da bikin su Amadu saidai ba yadda zatayi dole ta bashi haɗin kai suma suka shiga shan amarci sauƙin ta ma kowa da bangaren shi bawan Allah Kamalu an bar shi da tsaron shago sauƙin shi ma Farha na nan kuma yana zuwa Makaranta.

Bayan wata guda da bikin su Amadu aka É—aura auren Ashiru wato gaye da Amaryarshi Jamila mai awara dama itace Hajiya ta haÉ—asu yanzu ta zama babbar budurwa har ma ta gama karatunta a Health technology Haisam ne ya É—auki nauyin karatun da bikin ma shida Hajiya suka yi mata kayan É—aki shima gayen sun bashi gudunmawa sosae Fatuu ma ta aiko mashi da tata gudunmawar kuÉ—in ta wurin Gwaggo sai fatan Allah yasa Albarka a cikin auren Amin.......

102

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

.......Zaman su Hajiya da Husnah matar Tk gwanin daɗi, sosae take mata biyayya dama kuma Tk ya jaddada mata irin muhimmancinta a wajen shi, haka ma Saude suna shiri da ita kusan tare ma suke yin aiyukan gidan Abinci ma wasu lokuttan tare suke ci da Hajiyar har Farha ma ba laifi tana shiri da ita da yake Husnar wayayya ce gata fara tana da kyau ba laifi da yake fulanin Gombe ce, ba don Tk ya shigo birni ba da wannan ta wuce ajin auren shi, A bangaren Haulat ma wannan ko ban faɗa ba ansan zata yi ma Gwaggo biyayya tamkar uwa da ɗiya suke zamansu haka aiyukan gidan ma tare suke da yake tun kafin a ɗaura Auranta da Kawu Mani ya nuna bai son taci gaba da aikin da take yi to tun bayan ma da aka ɗaura auran bata je wurin aikin ba yanzu ma shirin ajewa take, Haulat har ce mata tayi ta bari ta rinƙa gyara mata part ɗinta tana yin Abinci Gwaggon tace to ita ta zauna tayi mi, Auransu na yin wata biyu upper ɗin aikinsu Tk da Amadu ta fito gaba ɗaya sun samu aiki a bangaren Lab na Teaching hospital kowa yayi farinciki har gida Gwaggo da Haulat suka je yi ma Hajiya Godiya don ita tasa aka samar masu aikin.

Za6e ya taho wanda kuma na canza shuwagabanni ne ma'ana waɗanda ke akan mulki tenure ɗin su ce ta ƙarshe, daga cikin masu sauka harda mahaifin su Sameer sannan cikin yan takarar neman shugabancin ƙasar nan da suka fito a ƙarƙashin Jam'iya mai mulki harda Mahaifinsu Haisam wato Senator Ali Adamu wanda mutane suka tursasa mashi dole ya fito don shi ba so yake ba ciki harda shugaban ƙasan da zai sauka shi ya fidda matsayin ɗan takararshi, Bayan ansha gwagwarmayar zaben fidda gwani na jam'iyar mai mulki cikin sa'a Senator Ali ne ya lashe saura Babban za6e nan da wata ukku, cikin lokacin aka shiga gudanar da Campaign saƙo da lunguna na ƙasar nan, A Katsina gidan Hajiya na cikin wuraren da ake raba kayan Campaign su Tk da Amadu na cikin masu gudanar da Campaign saƙo da lunguna tun ma kafin ayi za6en mutane keta hasashen Senator Ali ne zai lashe don sosae yay farinjini wurin al'umma a kudu da arewa ko ina ya samu kar6uwa dama shugaban da zai sauka ba musulmi bane kuma sai ya fiddo Senator Alin matsayin ɗan takarar shi, a Masallatai ma ana ta mashi Addu'o'i kan in Alkairi ne Allah ya bashi ko ina sai faɗin kyawawan halayenshi ake ana cewa ba don kuɗi yake takara ba don da nashi kuɗin ma aiki yake ma Al'umma yana taimakon su talakaw, ana gab da yin Babban za6e su Fatuu suka zo don yin za6en suma anan Abuja suka sauka. Alhamdulillah ranar za6e tazo cikin lumana aka fara gudanar da zaben an zuba matakan tsaro ko ta ina, bayan an kammala aka shiga zaman jiran sakamako wanda sai dare aka bayyana, Allah dai ya amince Senator Ali ne wanda ya lashe kujerar shugabancin ƙasa zo kaga murna wurin mutane gaba ɗaya Social Media ta ɗauka cikin gari aka fara celebrations wani abun sai ma a Katsina ban tunanin Mutane zasu yi bacci ranar saboda tsabar murna, Bayan an bayyana sakamakon Hajiya ta kira shi don ta taya shi murna da fatan Alkhairi yana ɗaukar wayar kawai sai ya saka mata kuka wanda har cikin ranta taji shi ita kanta tasan ba son mulkin yake ba, rarrashin shi ta shiga yi tace yayi haƙuri ya rungumi mulkin tunda Allah ya bashi cikin muryar kuka ya amsa mata tare da roƙonta kan a tayashi da Addu'a tana murmushi tace wannan koda yaushe cikin yi mashi take yanzun kuma zata ƙara zage damtse yayi mata godiya ta shiga yi mashi Addu'o'in Allah ya dafa mashi ya kare shi yanata amsawa da Amin daga baya sukai sallama, haka akaita kiraye kirayen wayoyi ana taya yan'uwa murna. Bayan wasu watanni aka gabatar da inauguration Ceremony a Eagle Square dake Abuja wuri ya cika maƙil da Jama'a an sha anko mai tambarin jam'iya da hoton President Ali da Vice ɗin shi wanda christian ne su Mom da Aunty an sha gwaggwaro suna gefen mai girma shugaban ƙasa harda Hajiya ma tana a wurin dasu Hajiya Maryam harda Hajiya Zainab da maigidanta dasu Sameer da iyalan sabon shugaban ƙasan su Haisam harda su Fatuu da Mino duk suna a wurin Laila ma tazo da Mijinta tare da kyakkyawar Babynta data haifa wadda taci sunan surukarta wato Safeeya suna ce mata Mimi, su Gwaggo dai suna a gida suna kallo a Tv, bayan Senator Ali yayi rantsuwar karbar office aka tabbatar dashi a matsayin cikakken shugaban ƙasa, daga nan rakiyar tsohon shugaban ƙasa aka tafi bakin city gate ana dawowa aka raka President Ali Adamu Aso rock presidential Villa abun na Allah ne sai ga su Fatuu da Mino yan fillo a Villa, daga cikin waɗanda suka lashe kujerun yan Majalissar tarayya harda Alhaji Lawal mahaifin Khalid, bayan sati ɗaya da komawar su Mom Villa su Haisam suka tafi wannan karon harda Nameer da Mino don zaici gaba da karatun shi itama Mino har ya samar mata makaranta zata yi Nursing a can,

Bayan tafiyarsu Fatuu da sati biyu matar Tk ta haiho san6aleliyar budurwa mai kama da mamanta Hajiya na jin Haihuwar ta dawo don tunda aka rantsar da shugaban ƙasa sun ƙi bari ta dawo, zo kaga murna a wurin Tk an zama baba tun a ranar ya raɗa mata sunan Hajiya wato Hauwa'u suka yanke zasu rinƙa kiranta da Jiddah Hajiya tace a rinƙa kiranta da sunanta kada a wani 6oye mata suna shikenan ita ta samu ƙawa kuma takwara, Haulat ma a lokacin ciki ne da ita wurin wata shidda da yake Husnar ta rigata samu, tunda Mino taji batun Haihuwar matar Tk gaba ɗaya ta ƙara shiga damuwa da rashin Haihuwarta har Asibiti Nameer ɗin yasa suka je ganin yadda ta damu aka tabbatar masu da lafiyar su lou nan ya shiga rarrashinta yana nuna mata lokacin haihuwar ne bai yi ba kuma shi koda bata haihu ba bazai damu ba zasu yi zaman su a haka ko kuma su amshi yaro a wurin Adda Fatunta tunda ita tana haihuwa akai akai yasan bazata hana su ba wannan Maganar tashi tasa ta ɗan kwantar da hankalinta ta maida hankali kan karatunta, ganin Mino na karatu yasa Fatuu tayi ma Haisam magana kan in zai yuwu itama tana son taci gaba da karatun Medicine yace mata shima yana son hakan saidai matsalan shekarun suna da yawa gashi kuma suna gab da komawa Nigeria amman in tana so ita sai ta zauna anan taci gaba da Karatun ko kuma ta bari in suka koma Nigeria sai tayi Karatun a India inda Fanan tayi shekarun karatun basu kai na nan America ba ta amince da hakan, tuni Farha ta gama bautar ƙasanta amman taƙi komawa gida tay zaune abunta gidan Hajiya kuma ba saboda kowa bane face Kamalu.

Bayan President Ali ya hau mulki da wasu watanni ya za6i Ministocin da zasu yi aiki tare ciki harda Hajiya Maryam ita ya za6a matsayin Minister of Industry, Trade and Investment wato Ministan Masana'antu, Kasuwanci da Zuba jari wanda babban muƙami ne acikin ministoci kuma ya bi cancanta ne shiyasa ya bata saboda kasuwanci ta karanta gata babbar yar kasuwa, Haisam ma yaso ya bashi Minister of Communication and Digital Economy lokacin daya tuntu6eshi kan yana son bashi muƙamin Haisam ɗin ya nuna mashi hakan zai iya zama wani abun magana ace yaba ɗan shi Minister Daddyn nashi yace shi ba ruwan shi tunda cancanta ya bi ba son rai ba amman Haisam ɗin ya bashi haƙuri yace yaba wani wanda ya cancanta saboda shi yafi son ya maida hankali akan Companyn shi da ake cikin ginawa anan Abuja, ƙarshe sai dai wani ɗin aka ba dama kujerar sonta ake, Mahaifin Sameer ma ya bashi Minister of Foreign affairs wato Ministan harkokin waje haka Kawunsu Mani mijin Gwaggo ya bashi P.A ɗin shi haka dai akaita rarraba muƙamai saidai duk cancanta ya bi bayan an tantance su a National Assembly suka shiga gudanar da aiyukansu su Hajiya Maryam an samu dalilin soke kallabi da hujja,

Bayan shigar su Hajiya Maryam Office tace ma Farha ta dawo Lagos don ta kula da ƙannanta saboda ita yanzu bata cika zama a Lagos ba, gaba ɗaya ita da Kamal sun shiga damuwar rabuwa da juna don sun shaƙu sosae haka dai suka rabun ta tafi Abuja don Hajiya Maryam ɗin na can Villa a apartment ɗin da Ministoci ke zama daga baya Farhar tare da Dad ɗin su da ƙannan nata suka koma Lagos saboda karatun su da kuma aikin Dad ɗin su, su Gwaggo Matar P.A Duniya sabuwa jin daɗi na musamman ake tuni har ta fara canzawa gashi wani ikon Allah sosae Kawu Mani ke ji da ita duk da tafi sauran matanshi manyan taka, cikin Haulat na cika wata tara ta haiho ƙaton saurayi mai kama da Kawu Amadu sak kowa yayi murna karma Fatuu taji Lokacin data ga Vedio ɗin jaririn ji tayi Kamar tayi tsuntsuwa ta taho yaron yaci sunan mahaifin Amadu wato Abdullahi,

Tun bayan da Farha ta koma gida ta rasa mike mata daɗi don gaba ɗaya kewar Kamal ta addabeta duk da suna yin waya sosae suna kuma yin Vedio call duk hakan bai mata ba so take kawai ta gan su a tare hakan yasa ta gane ta kamu da son shi ta shiga tunanin yadda zata sanar mashi, ana haka Cousin brother ɗinta wato ɗan Yayan Mahaifinta mai suna Emran shima Bature ne ɗan America da suke soyayya dashi duk iyayensu sun san da Maganar yayi mata Maganar aure tunda ta gama karatu, yana mata zancen aure taji gaba ɗaya ya fitar mata a rai bata son auren shi hakan yasa tace mashi ba yanzu zata yi aure ba don zata cigaba da Karatu ne ya nuna mata ai lafiya lou zasu iya yin auren sai taci gaba da karatun a America, ganin ya takura mata da Maganar ita kuma sai kauce kauce take mashi yaƙi ya k
Ƙyaleta ƙarshe ma sai cewa yayi zai ma Dad ɗin shi Maganar suyi Magana da Dad ɗinta sai kawai ta fito mashi a mutum tace mashi itafa ta daina son shi don haka bazata aure shi ba, sosae hankalinshi ya tashi da yake Vedio call suke ta faɗi mashi hakan harda ƙwallan shi yana faɗin ya zata yi mashi haka bayan suna son junansu duk an sani yanata zaman jiranta har ta gama karatu kuma sai yanzu tace bata son shi, magiya ya shiga yi mata kan in laifi yayi mata tayi haƙuri ta faɗi mashi zai gyara in kuma wani abu take so ko minene ko nawa yake ta faɗi mashi zai siya mata amman don Allah kar ta guje shi don itace rayuwar shi bazai iya rayuwa ba tare da ita ba, duk yadda yay da ita taƙi canza ra'ayi ƙarshe ma sai ta faɗi mashi ta samu wani ne shi take son ta aura aukuwa wannan Maganar ba ƙaramin dugunzuma ran shi tayi ba, bayan sun gama yin wayar zugudum tayi ta rasa mike mata daɗi don tabbas tasan Emran na masifar sonta sosae yake mata ɗawainiya kullum cikin turo mata kuɗi yake kuma itama tana son shi amman yanzu gaba ɗaya taji ya fitar mata a rai ba wanda ke mata yawo a cikin zuciya sai Kamal, sanin tabbas Emran ɗin zai faɗi ma iyayenta abunda ya faru kuma za'a iya kiranta a tambayeta waye wanda tace yanzu shi take so yasa ta yanke faɗi ma Kamal cewa tana son shi, Vedio call ta kira shi lokacin da yamma ne bai daɗe da dawowa daga Makaranta ba yayi wanka ya ɗan kwanta yana hutawa kafin a kira Magrib, yana murmushi suka gaisa daga haka tayi shiru tana ta kallonshi ya lura kaman tana cikin damuwa hakan yasa ya tambayeta wani abu na damunta ne ta ɗaga mashi kai alamar eh, jin haka yasa shi tashi zaune da sauri cikin nuna kulawa ya tambayi mike damunta ne, shiru ta ɗan yi kafin tace mashi in yaji damuwarta zai mata magani ne da sauri yace in yana da ikon yin hakan zai yi tace yayi alƙawari yace mata eh,

"Kamal ina son ka, kuma so nike muyi Aure ni da kai" Kamar saukar aradu haka yaji Maganar gaba ɗaya ya zaro idanun shi yana kallonta cikin rawar murya yace amma dai tana mashi wasa ne ko ta girgiza mashi kai kafin tace da gaske take bayan ta dawo ne ta gane ta kamu da son shi, gaban shi ne ya shiga faɗuwa don bai ta6a zaton zatayi mashi irin wannan Maganar ba koda suke shiri da juna, gaba ɗaya rasa amsar da zai bata yayi sai kallonta kawai yake itama haka can tace mashi yayi shiru bai ce komai ba gashi yayi mata alƙawarin maganin damuwarta da ƙyar ya buɗe baki yace mata shi ai baisan wannan ce damuwarta ba, da ɗan alamun tashin hankali tace kenan bai amince da soyayyarta ba,

"No Farha, kawai dai ina ganin Soyayya tsakaninmu bazata yuwu ba tunda kinga muna da bambanci sosae kuma kince so kike muyi aure ni kuma yanzu ba yadda za'ai in yi aure saboda ban daɗe da fara yin karatu ba kinga ba aiki nike ba da zan iya auren ki" da yanayin damuwa yayi Maganar itama fuskarta a yamutse tace mashi ba wani bambancin dake tsakanin su tunda ai duk ɗaya suke a wurin Allah kuma ai ba dole sai ana aiki za'ayi aure ba tunda yana yin business lafiya lou zasu iya yin aure sai a faɗaɗa business ɗin, ganin dai da gaske take yasa shi bata haƙuri yace gara su ci gaba da ƙawancensu su bar Maganar soyayya da aure don abu ne da shi yasan ba mai yuwuwa bane a tsakanin su ba lalle gaba ɗaya a amince masu ba ba kamar shi za'a ga yayi ƙarami da yin aure, idanunta ne suka ciko da ƙwalla cikin karyayyar murya tace yanzu duk da yana da ikon cire mata damuwa shine zai watsa mata ƙasa a ido tunda take dashi tana jin wannan ce buƙata ta farko data zo mashi da ita amman shine bazai taimaketa ba ya amince mata kuma da yake cewa baza'a amince masu ba sai dai in basu nuna suna son junansu ba sannan Maganar yayi ƙarami ai tasan shekarunshi yana da shekaru 26 ɗin ne zai ce bai isa aure ba wasu ma basu kai shekarun shi ba suke yin aure wani ma Matar ta girme shi suke yin auren balle su da ya girmeta, duk tabi ta ruɗa shi ganin yadda take magana tana yin ƙwalla sai bata haƙuri yake tace ita ba wannan take so ba kawae ya amince mata don in yaƙi za'a mata auren dole ne kuma ita shi take so in bai aureta ba to zata mutu kowa ya huta, zo kaga ido a wurin ɗan fillo yaji zancen za'a mutu saboda shi a razane ya shiga roƙonta kan ta daina cewa haka yanzu ta ɗan bashi lokaci zai yi shawara tunda yanzu tazo mashi da Maganar yana buƙatar yayi shawara idanunta sharkaf da ƙwalla tace har tsawon wane lokaci zai yi shawarar yace bada daɗewa ba zai kirata tace shikenan tana jiran shi, tana yanke kiran hannun shi har rawa yake wurin kiran Fatuu saida ta yanke sai gashi ta kira suka gaisa ta tambayi mutanen gidan da karatun shi ya amsa mata tana jin yanayin muryarshi ta tambayeshi ya akai ne da damuwa yace mata akwae matsala ne da sauri ta tambayi miya faru nan ya shiga faɗi mata yadda sukai da Farha ita kanta ta jinjina abun tace mashi to ita dae a shawarce ya rabu da ita don ta tabbatar ba abu bane mai yuwuwa ƙarshenta rayuka ne zasu 6aci ba kamar yanzu da Mamanta take babba a da ma ba son talaka suke ba balle yanzu ita kanta Farhar don ta nuna ta canza ne amman ba ƙaunar talaka take ba, nan ta kwashe komai daya ta6a shiga tsakanin su ta faɗi mashi tace koda ace auren ya yuwu a tsakaninsu to bata tunanin zata mutunta yan'uwansu don ance mai hali baya barin halin shi don haka ya bata haƙuri kawae kada wani tsara kalamenta su ruɗe shi gara taga bai mata daidai ba akan abunda zai je ya dawo ya amsa mata da to sukai sallama, zaune yay jugum bayan sun gama yin wayar gaba ɗaya ya rasa mike mashi daɗi Maganar Fatuu ta kashe mashi jiki sosae, suna gama yin wayar Gwaggo Fatuu ta kira bayan sun gaisa ta kwashe komai ta faɗi mata itama sosae ta jinjina abun ta kuma goyi bayan abunda Fatun tace mashi tace gara haka zama lafiya yafi zama ɗan sarki, Kamalu na zaunen har aka kira Magrib ya tashi don yaje masallaci jikinshi duk yayi sanyi lakwas, tun akan hanyarsu ta zuwa Kawu Amadu ya lura da kamar akwae abunda ke damunshi ya tambayeshi amman sai yace mashi ba komai ya gaji ne Amadun yace mashi halan kuma yayi baccin yamma ya bashi amsa da eh yace shi yasa, bayan an gama sallar sun dawo suna niyyar tsayawa shago Gwaggo ta kira Amadu ta tambayi sun dawo daga salla ne yace mata eh gasu nan sun tsaya shago tace to su shigo shida Kamalun tana son ganin su yace to, a falonta suka isketa zaune suma duk suka nemi wuri suka zauna cikin kwantar da murya ta fara magana idonta akan Kamalu tace taji yadda sukai da Farha a wurin Fatuu tana son ya sani ba wai ana ƙoƙarin hana shi yin soyayya da ita bane kawae ana gudun matsala ne don duk abunda Fatun ta faɗa mashi gaskiya ne ya faru don haka kamar yadda sukai da ita ya bata haƙuri shi ya fi don ko ya amince mata mawuyacin abu ne a barta ta aure shi, kai Kamalun ya jinjina a sanyaye yace to zai yi yadda suka ce da alamun rashin fahimta kawu Amadu ya tambayi mike faruwa ne tsakaninshi da Farhar Gwaggo ta kwashe komai ta faɗi mashi, shima jinjina abun yay yace ina ai ba abu bane mai yuwuwa ma shi dama tunda yaga take takenta yasan da wuya bata ce tana son shi ba to gara ya bata haƙuri kawae don ko kowa ya amince mamarta yasan bazata ta6a yarda wai ta aure shi ba an auri mijin ɗiyarta tayi ma mutane tijara ina ga kuma yanzu ace ɗiyar tata za'a aura ai sai yaƙi tsakaninsu balle yanzu da ta zama wata a ƙasa ita kanta Farhar ai ba kanwar lasa bace kawai dai don suna shiri ne yasa yake ganin kamar bata da matsala, ɗan murmushi Gwaggo tayi tace ƙilan da gaske ta canza tunda tun kafin tasan Kamalun ta canza sai ai mata kyakkyawan zato Amadun yace to ko dai ita lafiya lou wannan Maman tata ba lafiya lou ba, haka suka dingi tattaunawa daga baya suka fito suka koma shago, bayan sallar isha yana shago sai ga kiran Farha saida ya fito daga shagon ya nufi gate ɗin shiga gida sannan yay picking, bayan ya ɗauka tace yay keeping nata tana ta jira kuma yace bada daɗewa ba zai kirata, haƙuri ya bata yace dama yana niyyar kiran nata bai gidane amman gashi nan zai je ɗaki sai suyi magana tace Ok, bayan ya shiga cikin ɗakin da yake zaune ya nufi katifa ya zauna saida yay ƙoƙarin daidaita natsuwarshi sannan ya fara mata magana ya nuna mata yayi magana da yan'uwan shi kanta gaskiya duk sun nuna ba abu bane da zai yuwu don haka yana bata haƙuri ba wai don bai sonta ba sai don ba'a goyi baya ba,

"Nasan saboda abubuwan da suka ta6a faruwa tsakani na da Sister ɗinka ne yasa zasu ƙi goyon bayan ka aure ne amman ai i'm a changed person now, na canza tun ba yanzu ba kuma nayi dana sanin komai bazan sake ba, yanzu nasan da mai kuɗi da wanda baya dashi duk ɗaya ne at least they should give us chance zan tabbatar masu da na canza gaba ɗaya bazan basu matsala ba" cikin breaking voice take Maganar gaba ɗaya tausayinta ya kama shi don daga yadda take yin Maganar ya tabbatar da gaske tana son shi kuma yaji ya amince da cewa ta canza ɗin, jin yayi shiru tace mashi in shi bai son tane to zata haƙura amman ya sani tana ƙaunarshi kuma ta fara son shi ne tunda ta fara ganinshi wannan dalilin ne yasa suka shaƙu bata gane hakan bane sai yanzu da sauri yace mata a'a wllh shima yanzu yaji yana son ta to amman kowa gani yake hakan ba mai yuwuwa bane za'a iya samun matsala don ba lalle iyayenta su Amince ba, katse shi tayi tace ita buƙatarta itace shima ya sota ya kuma amince zai aureta Maganar iyayenta zata yi duk yadda zata yi in ma basu amince ba tasa su amince yace mata shikenan shima yana sonta kuma zai je yanzu suyi magana da gwaggon shi zai nuna mata ta canza yasan zata amince tunda tana da sauƙin kai tace Ok tare da yi mashi godiya yana murmushi yace to ta daina yin kuka bai jin daɗin hakan ace tana kuka saboda shi, a hankali tace ai ba kuka take ba yace shida ya santa sosae ai daya ji muryarta zai gane tace to ta bari sai kuma ta ƙara cewa ai duk laifin shi ne da son shi yay mata babban kamu yay yar dariya yace to ai shidai yasan abota suke bai san ya akai abun ya koma haka ba nan ta shiga bashi labarin bayan ta dawo gida gaba ɗaya ta shiga damuwar rashin shi a kusa da ita kullum cikin tunaninshi take nan ta gane son shi take yace to ai shima duk hakan ya faru dashi bayan tafiyarta ko abinci bai mashi daɗi duk sai ya rinƙa jin shi kamar mara lafiya har Uncle ɗin shi saida ya gane saboda tafiyarta ne ya shiga damuwa haka a School ma Friends ɗinshi suna ta tambayarshi mike damunshi koda ya faɗi masu saboda tafiyarta ne sai suka ce sonta yake shi kuma ya ƙaryata su yace kawai abota suke, tana murmushi tace duk sun faɗa son juna ba tare da sun sani ba yace hakane, daga haka suka shiga shan soyayya Farha ba wasa dama gata ruwa biyu ta wani bangaren a wurinta ba abun kunya bane don ta riga cewa tana son shi nan fa ta shiga yi mashi kalamai harda faɗi mashi irin soyayyar da zasu sha in suka zama married couple, shima Kamalun ba laifi ya shigo birni ya iya kalaman soyayya masu daɗi, sun ɗan ɗauki lokaci suna wayar kafin Farhar tace mashi ga Brother ɗinta yazo zata taimaka mashi yayi wani Assignment Kamalun yace Ok sukai sallama cike da nuna ƙaunar juna, bayan gama wayar zaune Kamal yay yanata sakin murmushi wani irin nashaɗi yake ji sai yanzu yake jin son Farhar sosae na shigarshi amman ada bai ta6a tunanin jin yana sonta ba don gani yake tafi ƙarfin shi ta ko ina, yana haka ya tuna da kalaman su Gwaggo zuciyar shi ta bashi yaje ya faɗi ma Gwaggon yadda sukai da ita da sauri ya miƙe ya nufi hanyar fita, bayan ya fito part ɗin Gwaggon ya nufa lokacin daya shiga a parlor ya isketa zaune tana kallo ruƙe da Abdallah yaron Amadu yana bacci, ciki ya shiga gabanshi na ɗan faɗuwa saboda fargabar kada ta ƙi amincewa da zancen Farhar, bayan ya zauna yay mata sannu da fulatanci idonta akan shi ta amsa mashi daga haka ya sunkuyar da kai ya rasa ta yadda zai sanar mata, tana ɗan murmushi da fullanci tace mashi ya akai ne ya ɗago cikin kama kai yace dama sunyi magana da Farhar ne Gwaggon tace to ya sukai da ita nan ya faɗi mata abunda tace na ta canza yanzu tasan mai kuɗi da talaka duk ɗaya ne bazata bada matsala ba in aka bata dama za'a tabbatar da haka, yar dariya Gwaggo tay tana kallon shi tace to ai su dama ba matsalarta suke hange ba ta iyayenta da za'a iya samu ba kamar Mahaifiyarta, da sauri ya tari numfashin Gwaggon yace suma tace ita tasan yadda zata sa su amince Gwaggon tay shiru kamar mai nazarin wani abu can ta tambayeshi yana Son Farhar ne da sauri ya sunkuyar da kai alamar kunya tace ita ya bata amsa ba wani sunkuyar da kai ba a yadda yake ya ɗaga mata kai alamar eh yana sonta tay ɗan jimm tanata kallon shi bayan ɗan wani lokaci tace ya tashi yaje zuwa da safe zata neme shi yace to tare da miƙewa yay mata saida safe ta amsa da Allah ya basu Alkhairi, bayan tafiyar shi tunani ta shiga yi a cikin ranta ita dai sam bata son Al'amarin ya haifar da fitina ƙarshe ta yanke zuwa ta sanar ma Hajiya kawai.

Washe gari ya kama Juma'a da safe wurin ƙarfe sha ɗaya da rabi Gwaggo ta nufi gidan Hajiya sai da ta tsaya a bakin gate suka gaisa da Securities wanda yanzu sun kai su Biyar don bayan Senator ya zama shugaban ƙasa an ƙaro wasu, bayan ta shiga a parlor bangaren Hajiyar ta isketa zaune tana ruƙe da ɗiyar Tk tana mata wasa da abubuwan wasa, da murmushi Gwaggo ta ƙarasa cikin parlon Hajiya ta ɗago tana mata maraba bayan ta zauna kan kujera suka gaisa,

"Ana wasa da ƙawa ne"

Gwaggo ta faɗa tana yar dariya Hajiyar tace wai ta hana uwar yin aiki ne shine ta riƙe mata ita take mata wayo duk su kai yar dariya, shiru Gwaggo tayi ta rasa ta ina zata fara yi mata Maganar data kawo ta don sai kuma taji tana jin nauyi,

"Ya akai Amaryar Mani kinyi shiru koda wani abune?" Hajiya ta faÉ—a idonta akan Gwaggon tana murmushi itama murmushin take mata tace eh,

"sai kuma ki kama kiyi shiru koda yake mufa yanzu surukai ne ko, to ina jin ki ya akai ne Allah yasa in ji Alkhairi" yar dariya Gwaggo tayi jin abunda Hajiyar tace na su surukai ne, a nutse ta fara faÉ—i mata tiryan tiryan yadda Kamal yay da Farha Hajiya ta É—an ta6e baki tana murmushi take sauraronta har ta gama,

"To Ke Dije Matar Mani ina ruwan ki da shiga harkar yara irin haka, ta bayyana mashi tana son shi in shima yana sonta sai kiyi masu fatan alkhairi ba shikenan ba" shiru Gwaggo ta É—anyi kafin tace "Dama ni kawai ina gudun abunda zaije ya dawo ne shiyasa",

"Mi zai je ya dawon?" ta tambaya ta kafeta da ido da ƙyar Gwaggon tace mata can bangaren iyayen Farhar kar azo hakan bai masu daɗi ba ƙarshe abun yazo ya haifar da bacin rai,

"Uhm, to ke kin isa ki hana faruwar wani abun ne, yaran yanzu ana hanasu abunda suke so ne, kina iya kiga ai kin hanashi yin tarayya da ita su zagaye can suna soyayyarsu ƙarshe kuma abunda kike gudun yazo ya faru don haka ki rabu dasu ayi masu fatan alkhairi ba abunda zai faru face abunda Ubangiji ya ƙaddaro zai faru", kai Gwaggo ta jinjina tace hakane Allah ya tabbatar da alkhairi Hajiyar ta amsa da Amin tace shikenan, Gwaggo har taji ta ɗan samu natsuwa bayan wani lokaci tayi mata sallama ta tafi. A ranar Minister Hajiya Maryam ta sauka Lagos dama duk Friday take dawowa sai ranar Lahadi da yamma ta koma a yadda suka tsara da maigidan nata wani lokacin shi zaije can Abujar tare da yara, sosae sukai murnar zuwan Momyn nasu tayi shiga ta alfarma ada ma tayi ado balle yanzu da suke da ƙasa, bayan an gama murnar zuwan nata Bedroom ɗin Daddyn su ta wuce dama shiya ɗaukkota daga Airport, da daddare tare suka ci abinci cikin nishaɗi bayan sun gama suka koma falo nan ta shiga tambayar yaran nata buƙatunsu kowa na faɗi da aka zo kan Farha yamutsa fuska tay tace ita bata da wata buƙata kawai so take su kasance tare koda yaushe don kula da yaran nan na bata wahala Hajiya Maryam ɗin na dariya tace to wace wahala take sha abunda akwae masu aiki ba girki take masu ba ba wanki da guga take masu ba haka ba shara take ba Farhar tace duk da haka basu barin kunnuwanta su huta Hajiya Maryam ɗin tace to ta ɗan ƙara haƙuri bada jimawa ba zasu koma Abuja baki ɗaya sai suci gaba da yin School acan nan kuma da Weekend ko lokacin hutu sai su rinƙa zuwa nan fa su Abraham suka shiga yin murna, sun ɗan dauki lokaci a falon kafin sukai ma juna saida safe kowa ya wuce part ɗin shi itama suka wuce tare da Dr Mohammad part ɗin shi suna saƙale da hannun juna, Washe gari Asabar tun da wuri aka kai yaran gidan islamiyya ya rage sai Farha don ita tunda tayi sauka ta daina zuwa, wuraren ƙarfe goma suka zauna yin breakfast duk sunyi wanka sai ƙamshi suke, Farha ce ta fara tashi daga kujerarta alamar ta ƙoshi Dad ɗinta yace ta jira shi a parlor zasu yi magana tace Ok, a tare suka gama da Hajiya Maryam ɗin suka nufi parlon duk suka zazzauna tun ma kafin Dad ɗin yayi magana ta yanke a ranta Maganar Emran zai mata, bayan sun zauna a nutse da turanci Dad ɗin nata ya fara mata magana yace mike faruwa ne tsakaninsu da Emran ya kirashi cikin tashin hankali yace tace bazata aure shi ba gaba ɗaya ya tada ma iyayen shi hankali suma sun kira shi kan Maganar, da alamun mamaki Hajiya Maryam ta maimaita bazata aure shi ba Dad ɗin yace haka Emran ɗin yace mashi tace, kallon Farha tayi tace miya faru tsakanin su ne da zata ce haka ta fara yamutsa fuska ta kasa yin magana Dad ɗinta yace kar taji komai ta faɗi masu in wani ƙwaƙƙwaran dalili ne zasu goya mata baya, muryarta kaman zata yi kuka tace ita ta daina son shi gaskiya ta samu wani wanda take so shi zata aura, a tare iyayen nata suka kalli juna alamar mamaki,

"Yaushe kika samu wanin da mu bamu sani ba?" Hajiya Maryam ta tambaya Farhar ta shiga motsa baki kafin tace sun ɗan daɗe tare sun fi shekara, tambayarta Dad ɗinsu yay waye shi kuma a ina yake saida cikinta ya ɗan kaɗa fargabar faɗin ko waye ta kamata ba kowa take tsoron yaji ko waye ba face Hajiya Maryam don inda Dad ɗinta ne kaɗai bazata ji komai ba zata faɗi mashi, Mom ɗin su ce ta ɗan ɗaga murya tace ita suke saurare suna da abun yi, da ƙyar ta tattaro ƙwarin gwuiwa idonta akan Dad ɗinsu tace a Katsina y
ake Yayan abokiyar zaman Sis Fanan ne, É—an waro ido Hajiya Maryam tay tace wace abokiyar zaman Fanan É—in badai wannan dangin shanun take nufi ba cikin tura baki Farhar tace ita, wata gigitacciyar tsawa data daka mata sai da suka tsorata su duka hada Dad É—in
a fusace tace "tsabar kin raina mu yasa kike dubar idanun mu kina faɗin Mutumin daji zaki kawo mana mu aura maki!!!!" idanun Farhar ne suka ciko da ƙwalla tana tura baki tace ai ba a daji yake ba ko yana nan gidan kakar shi a Katsina kuma yanzu haka yana cikin yin Degree ɗin shi a Umyuk,

"Over my dead body.....!!! Wllh bazaki auri wannan dangin ƙarnin ba, anya ma kuwa kina cikin hankali ki...Not at all, Farha dana sani bazata ta6a son wani ɗan wannan Family ɗin ba so kuma na aure there must to be something behind all this..." har huci take tana Maganar cikin kuka Farhar tace ita Wllh itace kuma shi take so ai talaka da mai kuɗi duk ɗaya ne a wurin Allah aikuwa tun kafin ta rufe baki Hajiya Maryam ɗin ta yunƙura tare da kai hannu zata maketa da sauri ta goce tare da miƙewa ta nufi Dad ɗinsu ta faɗa jikinshi tare da ƙanƙame shi tana kuka tana faɗin ita Allah she will not marry Emran don bata son shi Kamal take so shi zata aura, aikuwa Mom ɗin ta ƙara yin kukan kura zata kai mata bugu Dad ɗin ya tare ta yana girgiza mata kai yace abi komai a hankali kada ta ji mata ciwo a fusace tace ai gara ta lahanta ta tunda ta raina mutane bata da hankali har su zata zo ma da wannan Maganar to in ma bata cikin hankalinta ne gara tun wuri ta dawo cikin shi don matuƙar tana raye bazata ta6a auren shi ba har taya ma aure zai yuwu tsakaninsu ai kalar zaren ba kalar yadin bane, ɗago kan Farhar Dad ɗin su yay yana kallon fuskarta da tayi jage jage da hawaye ta sigar lallashi yace mata ba gara ta auri Emran ba shida ya gina rayuwar shi yana da komai wannan da take so tace yanzu yake cikin yin karatu yaushe ya gama har ya samu aiki tunda ba yadda za'ai suyi auri bai da hanyar samun kuɗi, cikin muryar kuka tace ai yana yin business Dad ɗin ya tambayi wani irin Business tace suna da provision store a jikin gidansu tun kafin ta rufe baki cike da takaici Hajiya maryam ta kai hannu ta ciro hular kanta ta jefa mata a fuska Farha ta fashe da kuka tare da miƙewa ta nufi hanyar Bedroom tana tafiya tana bubbuga ƙafa tana faɗin ita Wllh shi zata aura itama Sis Fanan ba wanda take so aka bata ba cikin zafin nama Hajiya Maryam ta yunkura zata bi bayanta da sauri Dr ya riƙo hannunta ta juyo ta kalleshi tana huci kamar zakanya ya girgiza mata kai tare da yi mata alamar ta zauna, bayan ta koma ta zauna cikin kwantar da murya ya fara lallashinta tare da nuna mata komai a hankali yakamata a bi shi yaro ɗan lallashi ne in ta kwantar da hankalinta cikin rarrashi da kalamai sai taga tayi nasara akanta, haka ya dingi kwatanta mata har ta ɗan saukko ta miƙe tace bari ta sameta shima ya miƙe suka nufi ɗakin Farhar, lokacin da suka shiga tana saman gado ta kife fuskarta sai rizgar kuka take kai kace an faɗi mata saƙon uwarta ta mutu ne, a bakin gado duk suka zauna cikin kwantar da murya Hajiya Maryam ɗin ta kira sunanta shiru bata amsa ba saida ta ƙara sannan cikin kuka ta amsa tace ta tashi zasu yi magana ta fara ƙoƙarin ɗagowa idanunta har sunyi ja, zama tayi tana cigaba da yin kukan Mom ɗin tasu ta kai hannu tana goge mata tana faɗin ya isa, bayan ta ɗan tsagaita ne ta tambayeta yadda akai suka haɗu da Kamal ɗin cikin disashshiyar murya tace mata a wurin bikin Ya Nameer ne ta taho zata je yin liƙi shine ya bugeta bai gani ba har purse ɗinta ta faɗi ya bata haƙuri ya ɗaukko mata to tun daga nan taji ya burgeta daga baya ne tasan shi Yayan Fatuu ne har suka yi exchanging phone number suka fara gaisawa daga haka suka shaƙu shine ma dalilin daya sa taje bautar ƙasa Katsina, wani murmushin takaici Mom ɗin tayi tace "i know, wannan ba yin kan ki bane asiri ne" wani kallo Farhar tayi mata Hajiya Maryam ɗin ta ɗaga mata gira cike da tabbatarwa tace yess asiri ne ke ɗawainiya da ita Farhar tace amman shi ai bai santa ba ko sai ranar suka fara haɗuwa taya zata ce asiri yay mata tana murmushi tace mata ai su dama mutanen daji irinsu da an haifi yaro ake tsafe jikinshi don ya kasance yadda ake so to su tana jin na asirin nasara akai masu wannan dalilin ne yasa har Ƙanwarshi tayi nasarar auran Haisam ba don ta kai matsayin ya aureta ba kuma ya kasa sakinta haka Nameer ma shima abun ya faɗa kanshi yana ganin ƙanwarsu yaji yana sonta to itama kusan hakan ne, shiru Farha tay da alamun maganar ta ɗan yi tasiri a zuciyarta ta shiga tunanin ko shiyasa lokacin daya bugeta ta kasa yi mashi faɗa sai ma ji tay ya burgeta ko asirin ne ya shigeta can kuma wani bangare na zuciyarta ya shiga raya mata amman da asirin ne miyasa tunda suka haɗun bata ji tana son shi ba sai daga baya kuma koda ta furta mashi tana son shi farko bai amince ba kuma yan gidan su ma basu amince ba, koda ta faɗi ma Hajiya Maryam cewa itace fa ta fara cewa tana son shi kuma yangidan su da suka ji basu amince ba cewa sukai su haƙura gudun matsala sai cewa tay ai duk dubara ce sun san cewa sun riga sun asirce ta dole bazata iya haƙura dashi ba, shiru Farha tayi tana nazarin maganar a cikin ranta wani bangare na zuciyarta ya ƙi gasgata zancen asirin wani bangare kuma na son gasgatawa, lokaci guda ta fara ganin fuskar Kamalu ɗauke da ƙayataccen murmushin shi da maganarshi mai daɗi wata zuciyar ta raya mata yanzu shikenan sai ta haƙura dashi ƙilan ma Mom ɗin nata duk daɗin baki ne tayi mata ba wani abu ba, kamo hannunta Hajiya Maryam tay tace kada ta bari asirinsu yay tasiri akanta tazo taƙi mai sonta da gaskiya wanda zai treating ɗinta kamar Queen wanda zai mata duk abunda take so wannan kuma ƙarshe zata yi dana sani ne don ba iya ruƙeta zai yi ba kawai zai yi auren jari ne da ita don haka ta cire shi a ranta, shiru Farhar tayi tana kallonta yayin da zuciyarta ke ƙara tabbatar mata da wayau ne Mom ɗin nasu ke mata in ta rabu da Kamal kanta tayi mawa dama danginshi ba so suke ba dama, wani irin son Kamal ɗin ne taji ya taso mata cikin yamutsa fuska tace ma Mom ɗin ita ta tabbatar ba Asiri bane Allah ne ya saka mata son shi ita dai shi take so Wllh yanzu bata jin son Emran, wata uwar harara Mom ɗin ta wurga mata tare da sakin hannunta a fusace tace to tunda ita keda kanta ai sai ta aureshi ta gani daga haka ta tashi fuuu ta nufi hanyar barin ɗakin Farhar ta fashe da sabon kuka tana buga katifa Dad ɗinta ya matsa tare da jawota jikinshi ya rungumeta yana faɗin shikenan tayi shiru kada taja ma kanta ciwo cikin kuka take faɗin "Dad i love him, help me marry him pls" shiru yay yana shafa bayanta shi in don tashi ne indai har yaron yana da hali mai kyau to zai amince ta aure shi don mutum ne mai tsananin son yaranshi dama kuma haka turawa suke da son yara gashi suna ba yaran su yanci sam bai son abunda zai tada masu hankali ko ya 6ata masu rai shiyasa duk abunda suke so to yana son shi, jin ta ɗan lafa da yin kuka yasashi ɗagota yace ta kwantar da hankalinta indai har yaron baida matsala to yana tare da ita zai yi bakin ƙoƙarinshi ya ga ya taimaka mata ta samu abunda take so da sauri tace mashi wllh baida matsala ya kira Hajiya ya tambayeta yana da ilimin addini kuma yana da ƙokari gashi yana da ƙoƙarin neman na kan shi sam baida kwaɗayi don ko abu tayi mashi da ƙyar yake amsa, murmushi Dad ɗin yayi yace yayi kyau ya tambayi tana da hoton shi ya gani da sauri tace eh ta juya tana laluban wayarta, bayan ta ɗaukko ta shiga gallery ta dawo jikin Dad ɗin ta shiga nuna mashi hotunan Kamal wasu tare sukai wasu kuma shi kaɗai yana murmushi yace yana da kyau ta ɗaga kai ya sake cewa amman kamar ta girmeshi a shekaru tace a'a ya ɗan girmeta yace Ok yana son ta kwantar da hankalinta duk abunda Allah ya ƙaddaro shine zai faru ta ɗaga mashi kai,

Hajiya Maryam na fita ɗakinta ta nufa a zuciye tana shiga ta nufi bakin gado ta zauna ta shiga cize baki abun ya matuƙar daure mata kai wai ace Farha data sani itace zata ce tana son yaron wannan dangin tabbas bata tunanin yin kanta ne, a fusace ta kai hannu ta rarumo wayarta ta shiga kiran Hajiya bayan tayi ringing Hajiyar ta ɗauka murya ciki ciki ta gaishe da ita ta amsa daga haka tayi shiru Hajiyar tace ya akai ne taji muryarta wani iri ai kaman tana jira ta miƙe tsaye yadda zata ji daɗin kora bayani ta shiga faɗin wai Farha ce tazo masu da wani banzan zance na bata son wanda ke sonta ɗan dangin shanun nan take so ashe ma dalilin zuwan ta wurinta kenan yin service duk saboda shi ne, Murmushi Hajiya tayi tace ai tasan da Maganar suna son junansu, da tsananin mamaki Hajiya Maryam ɗin tace amman shine kuma ta ƙyale su bata hana abun ba,

"To akan mi zan hana Maryam, yara suna son junansu",

"Saboda bai kai yayi soyayya da ita ba Hajjaju", yar dariya Hajiya tayi "saboda shi ba mutum bane ko mi?",

"Mutum ne amman wanda bai kai yayi soyayya da ita ba" ɗan ta6e baki Hajiya tayi tace "to ni a wurina ya akai shiyasa ban dakatar da abun ba" yarfa hannu Hajiya Maryam tayi muryarta har tana sarƙewa wurin faɗin "Wai Hajjaju miyasa a koda yaushe kike goyon bayan bare ne taya za'ace wai kamar Farha ta auri wannan dangin ƙarnin" faɗaɗa dariya Hajiya tayi tace "A'a Maryam banda sharri, anan ai ba bare na goyi baya ba tamun na goya ma baya tunda ita ta fara nuna tana son shi hasali ma su dangin yaron ba so suke ba don kakarshi har nan ta same ni tayi man magana kan hakan kinga da bare na goya ma baya to zan ƙi abun ne", cikin huci tace ai duk wannan munafurci ne don sun san sun asirce Farhar Hajiya ta shiga girgiza kai tace "anya Maryam, taya akai wai kike neman barin imanin ki yay rauni ne, komai kice anyi asiri",

Murya kamar zata yi kuka tace to in ba asirin ba taya Farha zata kamu da son wannan yaron Hajiyar tace ta in Allah ya ƙaddaro hakan don haka tana bata shawara tabi komai a hankali in har Allah ya ƙaddaro aure tsakanin su to dole zasu yi, ai kamar Hajiyar ta watsa mata garwashin wuta a cikin zuciya cike da cin alwashi tace Wllh bazata bari Farha ta auri wannan yaron ba Hajiya tace ai shikenan ɗiyarta ce tayi duk abunda take ganin yayi mata Hajiya Maryam ɗin tace zatayi kuma ta faɗi ma kakar yaron in ma wani abu sukai ma ɗiyarta suyi gaggawar warware shi in ba haka ba duk abunda ya faru dasu to su suka siya ma kansu Hajiya tace tsakaninsu ne tazo da kanta sai ta faɗi masu,

tana niyyar kashe wayar Hajiya tace "Maryam ina son ki sani yadda kike uwar zamani haka Farha take É—iyar zamani sannan yin jayyaya da ikon Allah tamkar É—aukar dutsen Dala ba gammo ne don haka ina mai baki shawara da ki bi komai a hankali sannan kibar ikon Allah yay aikin shi, ki gaida man da kowa" daga haka ta yanke wayar,

komawa Hajiya Maryam tay ta zauna da6as saman gado ta shiga juya Maganar Hajiya ta ƙarshe nan take ta yanke wani abu a ranta, gaba ɗaya yinin ranar a cikin ɗaki Farha ta wuni koda lokacin cin abinci yay aka aiko kiranta ƙin fita tayi ƙarshe saidai Dad ɗin su yazo ya fito da ita suna zuwa Dining ɗin Hajiya Maryam ta miƙe ta bar wurin hakan yasa Farhar fashewa da kuka Dad ɗinta ya shiga rarrashinta, ganin abunda ya faru yasa da daddare Dad ɗin bai matsa ma Farhar ta fito ba bayan sun gama cin abincin ya ɗauki nata ya kai mata ɗaki saida ya zauna taci sannan ya baro ɗakin, a daren ta kira Fanan tana kuka ta faɗi mata abunda ke faruwa itama rarrashinta ta shiga yi tace tunda Dad ya nuna zai taimaka mata ta kwantar da hankalinta tasan Momynsu nada zuciya dole bazata goyi bayan abun ba ta cikin sauƙi amman itama tana goyon bayan abunda take so don haka zata tayata da Addu'a itama ta dage da yi tace to tare da yi mata godiya, suna gama yin wayar Fanan ta kira Mom ɗin nasu ko daga yanayin muryarta ta fahimci tana cikin 6acin rai, bayan sun gaisa cikin kwantar da murya Fanan ɗin ta fara lallashinta tana nuna mata ba aibu bane don Farha ta auri Kamal tasan kawai don basu da arzuƙi ne matsalansu kuma shi na Allah ne a duk lokacin daya so sai ya azurta bawa haka mai kuɗin ma duk yawan kuɗinshi cikin few seconds sai ya maida mutum talaka don haka suyi fatan alkhairi a gare su kawai, har ta gama maganarta Mom ɗin bata katseta ba saida ta gama tace mata ta gama Fanan ɗin tace eh kawai sai ta kashe wayar tare da buga uban tsoki, gaba ɗaya Farha ta koma rayuwar ɗaki washe gari lahadi da yamma Hajiya Maryam ta shirya komawa Abuja taci gayu cikin jigunannan lace ta soke kallabi bayan ta fito ne ta nufi ɗakin Farha lokacin data shiga tana kwance kan gado kamar mara lafiya tana ganin Mom ɗin nasu ta shigo ta yunƙura ta tashi zaune tana kallonta can ta gaishe da ita a hankali Mom ɗin ta ta6e baki tace ta ruƙe gaisuwarta bata so ai yanzu bata da daraja a wurinta saboda dangin shanu shiyasa bata iya zuwa ta gaishe da ita, idanun Farhar ne suka ciko da ƙwalla tace mata tayi haƙuri Hajiya Maryam ɗin ta ƙara ta6e baki tace ita ai zata ba haƙuri don tazo ne ta sanar mata nan da sati biyu za'a ɗaura auranta da Emran don haka gara ta tsaida hankalinta wuri ɗaya tana gama faɗin hakan ta juya ta tafi Farhar tasa wani irin kuka tana faɗin Wllh bazata aure shi ba Kamal zata aura in ba haka ba mutuwa zatai, daidai Hajiya Maryam ta kai bakin ƙopa ta watsa mata hannu daga haka ta fuce. Gaba ɗaya hankalin Dr ya tashi ganin halin da Farhar take ciki kullum cikin kuka ta daina cin abinci sai ya rarrasheta dole hankalinshi ya kasu biyu wurin aiki da kuma gida a haka har sati ya ƙare Hajiya Maryam ɗin ta dawo ya sameta don suyi magana ya nuna mata gara a bar Farhar ta auri wanda take so don tana niyyar lahanta kanta Hajiya Maryam ɗin tace ya rabu da ita duk tana yi ne don a saduda a goyi bayanta da an ɗaura masu aure da Emran ya tafi da ita America zata koma daidai, bayan ta gama Weekend ta koma an shiga wani satin ganin yana niyyar rasa ɗiyarshi yasa ya kirawo Hajiya ya sanar mata halin da Farhar ke ciki da hukuncin da Hajiya Maryam ta yanke na ɗaura masu aure da Emran a satin Hajiya na jin haka ta saka salati tace Maryam badai taurin kai ba ai ita bata san da ta yanke wannan hukuncin ba tace ma Dr ɗin abunda za'ai yasa Farha ta rubuta takarda cewa tunda an hanata wanda take so to ta shiga duniya kuma kada a nemeta don baza'a sameta ba in ta rubuta sai ya turo mata ita amman kada ta hawo jirgin Katsina ta hawo na Kano in ta sauka sai ta hau Motar haya ta ƙaraso Katsina sannan kada ya bari kowa yasan da wannan plan ɗin daga shi sai Farhar kuma ya siya mata sabon layin waya sannan itama wayar ya siya mata ƙarama tata ta baro ta nan gida, bayan sun gama wayar tasa ya kai ma Farha wayarshi ta sanar da ita yadda sukai da Mahaifinta tace mata ta kwantar da hankalinta ta samu niƙab in ta isa kano ta saka shi a fuskarta har ta iso Katsina sannan kuma tayi dubara ta saka dogon Hijab a park ɗin data iso Katsina sai ta kirata ta sanar mata zata sa azo a ɗauketa da sauri tace to, kamar yadda suka tsara haka sukai ya sakata ta siya ticket ta online washe gari ya kama talata lokacin duk ƙannanta sun tafi School shima Dad ɗin ya fito daga gidan matsayin ya tafi aiki bayan wani lokaci ya kirata ta sabon layinta yace ta fito daga gidan koda wani zai tambayi ina zata tace zata je Abuja ne wurin Mom ɗinta, tana janye da madaidaicin trolley ta fito cikin sa'a har ta fito daga gidan ba wanda ya ganta sai Security dake gadin gate da suka gaisa suka tambayi unguwa zata je ne tace eh zata Abuja wurin Mom ɗinta har wani yace to ina driver ta fito ita kaɗai tace bai dawo daga kai su Noor School ba tana sauri zata hau taxi kawai sukai mata Allah ya kiyaye, bayan sun haɗu da Dad ɗin nata inda ya tsaya tace ya bari ta hau taxi tunda in ya kaita Airport za'a iya gane plan ne tunda akwae cctv yace ta bari in suka kusa isa sai ta hau taxi ɗin, tun a cikin Motar ta naɗa gyalenta tayi kamar niƙab a cikin Motar suka yi bankwana da Dad ɗin nata duk ya damu, bayan ta fito saida ta samu taxi ta hau sannan Dad ɗin nata ya tafi har suka isa Airport bata buɗe fuskarta ba sai bayan data shiga tana janye da trolley da zasu tafi sannan ta buɗe, bayan sun iso Kano fuskarta a rufe ta bar Airport ɗin ta hau keke napep don ya kaita tasha, wuraren azahar ta iso Katsina ta kira Hajiya ta sanar mata ta tambayi inda take bayan ta faɗi mata ta kira Tk ta sanar dashi ya ɗauki Mota tinted yaje ya taho da Farhar tace kada ya ɗaukkota a tashar in ya kusa isa ya kirata ta fito sai su haɗu kan hanya ya ɗaukkota, duk yadda Hajiya ta tsara haka akayi lokacin da suka iso gidan Hajiya na Bedroom bata daɗe da gama yin sallar Azahar ba Farhar ta shigo tana hangota ta nufota da sauri tana zuwa ta faɗa jikinta tana kuka Hajiyar na murmushi tace mata ya isa miye abun kuka, gaba ɗaya su Saude da Husnah harda Tk saida Hajiya taja kunnansu kan kar wanda ya sake ya bayyana Farhar na gidan koda za'a tambaye su nan gaba har su Gwaggo tace kar a bari su san da zuwanta gidan duk suka ce to, itama Farhar tace mata kada ta bari kowa yasan tana gidan har Kamalun tace to. Lokacin da Dr ya kira Hajiya Maryam da alamun tashin hankali ya sanar mata zancen barin Farha gida da takardar data bari harda wayarta zo kaga rawar jiki da tsananin tashin hankali ta shiga tambayar ina taje ya akai har ta bar gida ba wanda ya sani yace to shi dai ya tafi wurin aiki yara kuma an tafi kai su School koda ya dawo dubata kamar yadda yake yi sai dai takarda ya gani kuma ya tambayi security sun tabbatar mashi da fita tayi kuma cewa tayi wurinta zata zo Abuja, a fusace tace to ubanwa yace su bari ta fita Dr yace sunce ba'a basu umarnin su hana wani ya fita ba sai lokacin ta tuna da haka gaba ɗaya ta gama ruɗewa tace mashi a bibbincika inda ake tunanin zata iya zuwa pls yace mata bai tunanin zata tsaya kusa don da gani ta shirya ma abun bazata tsaya inda za'a ganota ba shi dama abunda yaketa kwatanta mata kenan tace yanzu ba lokacin wannan bane duk da haka adai bincika ko ina itama zata kira wasu wuraren taji ko taje can, abu kamar wasa har zuwa yamma ba'a ji taje wani wuri ba, lokacin da ta kira Hajiya ta tambayi ko Farha tazo da alamun mamaki ta tambayi ina Farhar taje farko shiru Hajiya Maryam ɗin tayi saida Hajiya ta ɗaga mata murya tace bazata faɗi mata ba sannan tace aje takarda tayi wai tunda baza'a bata wanda take so ba ta shiga duniya, wani salati da Hajiya ta saka baka ta6a cewa tasan inda Farhar take da alamun tashin hankali tace yanzu duk Maganar data yi mata shine bata ji ba saida tayi sanadin barin ta gida kamar Hajiya Maryam ɗin zatai kuka tace yanzu dai don Allah ta bar Maganar a taya su bincikawa inda ake tunanin zata iya zuwa, zuwa dare har zancen 6atan Farhar ya fara baza wurare har Mai girma shugaban ƙasa yaji sosae hankalinshi ya tashi ba kamar da yaji cewa takarda ta aje ta tafi shima da kan shi ya shiga kiran yan'uwa na jiki yana tambayar ko taje in aka ce bata je ba sai yace to a taya su bincikawa, lokacin da ya kira Hajiya nan ta warware mashi komai tace su kwantar da hankalinsu Farhar na wurinta amman kada a bari Hajiya Maryam ɗin taji in ba haka aka yi mata ba bazata saduda ta ƙyale yarinyar ba hakan kuma na iya haifar da abunda za'ayi dana sani tunda yaran zamani ba'a cewa za'a yi masu dole yace ya fahimta, Washe gari tunda safe Hajiya Maryam ta koma Lagos nan fa aka hau bincike wurare daban daban har gidajen radio da Tv aka kai cigiya ko wani ya ganta har binciken lambar wayarta akayi aka tabbatar wayar da tayi ta ƙarshe anan Lagos ne, kan kace mi zancen 6atan ya karaɗe social media ana ta faɗin ɗiyar ƙanwar shugaban ƙasa kuma Minister Maryam Adamu Zakee ta 6ace sai dai ba wanda yasan dalilin 6atan nata don ba'a bayyana ba da yawan mutane sun tafi akan ƙilan kidnapping ɗinta akai, har su Fanan sun samu labarin sosae hankalin Fanan ya tashi har ta fara shirin tahowa Nigeria Haisam ya kira Hajiya kan 6acewar Farha ɗin nan ta bayyana mashi komai tace su kwantar da hankalinsu amman kada wanda ya sanar ma Hajiya Maryam ɗin saida Fanan taji haka sannan hankalinta ya kwanta har waya sukai da Farhar amman ita Hajiya Maryam duk sai suka nuna mata hankulansu ya tashi, da yake abun na masu ƙasa ne an zurfafa bincike sai gashi zuwa yamma an tabbatar da ta siya ticket online kuma ta hau jirgin Kano a jiya nan da nan bincike ya koma Kano, bayan an tabbatar da taje kano Hajiya Maryam ta kira Hajiya ta sanar mata ta tambayi ko ta ƙaraso nan Katsina Hajiya tace a'a bata zo ba ai in nan zata zo mi zai sa ta hau jirgin Kano, cike da nuna Al'ajabi Hajiyar tace "to amman wai mi zaisa Farha taje kano, ko kinada mutanen da kike tunanin zata iya zuwa can wurinsu??" cike da damuwa Hajiya Maryam tace tana da abokan kasuwancinta acan saidai Farhar bata san su ba sai kuma abokanta da sukayi karatu tare suma ba kowanne Farha ta sani ba sai wata ƙawarta guda Hajiya Turai kuma ta kirata ta tambayi ko Farhar taje wurinta ta tabbatar mata da bata je ba,

"Oh ya Allah, shiyasa aka ce maganin kada ayi to kada a fara yanzu ina amfanin haka ace budurwa kamar Farha ta 6ace ai dole a shiga dumuwa da tashin hankalin halin da take ciki, yanzu da ta tafi Kano mi taje yi can in ma acan ɗin ta tsaya, to ko dai yin Film ta tafi ne don naji ance dama wasu yan wasan hausan sanadin auren dole suke tafiyar su su shiga, to in ma dai Film ɗin taje yi ai da sauƙi don tana farawa za'a ganta tsorona ace ba a Kanon ta tsaya ba ta haɗu da wata yar Kano to Jidda ta hure mata kunne kan ta gudo wurinta ta fitar da ita waje....." da sauri Hajiya Maryam ta katseta da faɗin "Don Allah Hajjaju ki daina yin wannan fatan",

"To Maryam na bari Hankalina ne ya tashi na rasa tunanin da zanyi kan inda ta dosa amman in sha Allahu tana a hannu nagari Allah zai tsareta" da sauri Hajiya Maryam ta amsa da Allah yasa kafin a zuciye tace "In dai ba'a ganta ba zuwa gobe ina nan zuwa Katsina zan sa a kama yaron nan da kaf danginshi a tuhume su na tabbatar basu rasa sanin inda take don haka sai sun nemo man yarinyata",

da sauri Hajiya tace "akan me, ke waya faÉ—i maki su suka É—auketa, yarinyar da daga gani ita ta shirya ma kanta hakan tunda har da takarda ta aje to ina ruwan yaro da dangin shi anan?" a fusace tace ai zai iya yuwuwa shiya tsara mata,

"Ba wani tsara matan da yayi yaron da tun farko ita ta bayyana mashi so nan fa Kakarshi tazo cikin damuwa kan bata son al'amarin gudun matsala sai kuma suja ma kan su matsalar, don haka ni ban amince kisa ayi masu wani abu ba don na tabbatar basu da sa hannu a 6atan ta in kuma kika ƙi jin maganata kika sa akai ma yaron mutane wani abun ita mai guduwar ta samu labari al'amarin ya ƙara kwa6ewa to ba ruwana kar ma kice zaki kirani dama yanzu ai harda ƙin jin maganata yasa hakan ta faru don haka na dai gaya maki ban amince kisa ayi masu wani abu ba muci gaba da Addu'ar bayyanarta da kasancewarta cikin ƙoshin lafiya" a sanyaye ta amsa mata da Amin kafin sukai sallama, bincike ya tsananta a Kano a gidajen radio da tv da social Media harda Airport anata cigiya harda hotunan Farhar da ranar data zo kano harda kayan jikinta, duk abun nan su Gwaggo basu sani ba kawai dai Kamalu nata kiran layinta bai shiga har ya fara shiga damuwa dama lokacin da tana gida cikin halin damuwa sunyi waya har yake mata magana kan jin muryarta ta canza tace mashi bata jin daɗi ne duk sai tunanin shi ya tafi akan ko ciwon ne yay tsanani yasa ba'a samunta a waya, sai ranar juma'a lokacin kwana ukku da 6acewarta Kamalu yaje School wani abokin shi da suke tare ya nuna mashi hoton Farhar a Facebook yace mashi wai wannan ba itace wannan ɗiyar Minister ɗin ba ƙawarshi da yake ganin hotunanta a wayarshi da sauri Kamalun yace mashi eh itace miya faru nan yake ce mashi wai nemanta ake ta 6ace ai da sauri ya warci wayar yana dubawa nan ya tabbatar da hakan yana bashi wayar ya miƙe sai gida, Lokacin daya dawo a falon Gwaggo ya isketa tare da Amadu da Haulat duk sunyi jugum tun bayan da Amadu ya shigo masu da labarin 6atan Farhar suke haka kowa ya kasa yin ƙwaƙƙwaran motsi, shima zama yay cikin tashin hankali yace masu ko sun samu labarin daya samu yanzu a School wai Farha ta 6ace duk suka ɗaga mashi kai ai shima sai ya nemi wuri ya zauna, bayan wani lokaci Gwaggo ta sauke nannauyar ajiyar zuciya cike da damuwa tace ita dai fatan ta Allah yasa ba dalilin abunda tazo dashi bane tunda dama tace ma Kamalu ita tasan yadda zata sa iyayenta su amince in ko har hakan ne to kuwa akwae babbar matsala, jin Maganar Gwaggo yasa cikin Kamalu juyawa Amadu yace mashi suna waya da ita ne nan ya faɗi masu rabon shi da ita a waya Haulat tace Allah yasa dai ba dalilin hakan yasa ta 6ace ba Allah kuma yasa a ganta duk suka amsa da Amin, Amadu ne yace bari ya kira Fatuu yasan ta bakinta zasu iya jin dalilin 6acewar tata, bayan ta kira sun gaisa yake mata zancen Farhar yace da gaske wai ta 6ace tace mashi eh ya tambayi tasan dalilin 6acewar tata nan ta faɗi mashi guduwa tayi don harda takarda ta aje Mom ɗin su taƙi yarda da Kamalu shine ta yanke yi mata auren dole da Cousin ɗinta da suke yin soyayya a satin data gudun, salati Gwaggo ta saka tare da rufe ido ta dafe goshi shi kuwa Kamalu zumbur ya miƙe yay hanyar ɗakin shi yana zuwa sai toilet, Fatun bata fito ta bayyana masu inda Farhar take ba duk da ta sani saboda Hajiya tace kar a faɗi ma kowa sai dai ta shiga kwantar masu da hankali tace in sha Allahu za'a ganta tunda har an gano ta hau jirgi taje kano Amadu yace to Allah yasa ta amsa tace ina Gwaggo yace gata nan tayi jugum duk tsoro ya kamata tace Kamalu fa yana yar dariya yace shi wannan yana tunanin yana toilet don yana jin bayanin data yi ya miƙe yay hanyar ɗaki Fatun tay yar dariya tace su kwantar da hankalinsu tasa aka ba Gwaggo suka gaisa nan ta shiga kwantar mata da hankali ita dae sai uhmm da to kawai take cewa, suna gama yin wayar Gwaggo ta miƙe tace bari taje tayi ma Hajiya jaje Haulat ma ta miƙe tace bari ta sako Hijab suje, lokacin da suka je Hajiyar na bedroom Farha kuma tana a ɗayan bedroom ɗin Husnah tanata shan bacci abunta dama nan Hajiya tasa ta zauna gudun kada Momynta tayi zuwan bazata, Saude ce ta kirawo masu Hajiyar bayan ta shigo cikin falon tana ɗan murmushi tayi masu sannu da zuwa tare da yi masu barka da Juma'a duk suka amsa suka gaisheta, Gwaggo ce ta fara mata jajen tace su wllh basu san abunda ke faruwa ba sai yau da su Amadu suka ga ana cigiyarta a waya Hajiya na ɗan murmushi tace tsakaninta ne da uwarta taƙi goyon bayan wanda take so ƙarshe ma sai ta yanke yi mata auren dole to dama yaran zamani ana masu dole ne shine ta kaɗa kai tayi gaba abunta, cike da damuwa Gwaggo tace wllh tun farko irin haka take ta gudu don tasan abu ne mai wuya iyayenta su amince Hajiya tace shi mahaifinta ma ya amince uwarce taƙi da yake taurin kai ne da ita sai kuma ta samu yarinya irinta sai suyi ta cakusawa, itama Haulat jajen tayi mata da Addu'ar Allah ya bayyanata ta amsa da Amin ganin yadda Gwaggo tayi gwalau duk ta shiga damuwa yasa Hajiyar yin yar dariya tace "Amaryar Mani ya ya, ko kina tsoron hukuncin da Minister zata yi maku na kun yi silar 6acewar ɗiyarta" ɗan motsa baki Gwaggon tayi kafin tace a'a kawai dai 6acewar mutum bata da daɗi ba'a san a wane hali take ciki ba, Hajiyar tace mata kar su damu za'a ganta ne suka ce Allah ya sa, bayan sun mata sallama sun fito ne Haulat tace ma Gwaggo ita sai taga kamar Hajiya tasan inda Farhar take don taga kamar bata damu ba Gwaggo tace itama ta lura ƙilan kuma kawai ƙarfin zuciya ne Haulat ɗin ta ƙara cewa ko kuma shiri ne akai don Hajiya Maryam ɗin ta saduda Gwaggo tayi shiru tana nazarin Maganar, har aka shiga Weekend shiru Farha bata bayyana ba Kamalu kuwa yana can yana zazza6in zullumi, ranar Lahadi Dr mijin Hajiya Maryam ya kira Hajiya anan yake sanar mata ba ƙaramin tashi hankalin Hajiya Maryam yayi ba ko isasshshen bacci bata yi taita kuka tana faɗin tayi sanadin 6acewar ɗiyarta waya sani ma ko ta mutu shi yanzu tausayi take bashi sosae gashi sai zuba kuɗi take ana cigiya a gidajen tv da radio yanzu har kuɗi tasa masu yawa na duk wanda ya kawo ta ko ya faɗi inda take zata bashi, murmushi Hajiya tayi tare da ɗan ta6e baki tace mashi ya ƙyaleta ta ɗan ƙara jin jiki tukun su kuma kuɗi da take 6atarwa na cigiya ai tana dasu ne don haka suma kafafen sadarwar ta fitar masu da zakka Dr ya ɗan yi shiru kafin yace shi abunda yake gudu kada wani ciwon kuma ya haye mata Hajiyar tay murmushi mai ɗan sauti jin yanzu kuma ta matar shi yake tace mashi kada ya damu ba ciwon da zai haye mata in ba hakan aka yi mata ba bazata daina taurin kai ba, bayan sun gama yin wayar shiru Hajiya tayi ta ɗan ta6e baki a ranta ta shiga raya in ba don ta kama ba ita kanta ai bazata so ta tada ma ɗiyarta hankali ba, damuwa tasa Hajiya Maryam ƙin komawa Abuja har wata rama tayi daka ganta kasan tana cikin damuwa bayan Hajiya ta warware ma President komai ya kira Hajiya Maryam ɗin sosae yayi mata faɗa yace al'amarin irin wannan ai a hankali ake bi da ta saurari Hajiya duk da hakan bata faru ba yakamata ta daina saurin fushi ta rinƙa bin komai a hankali tana ƙwalla tace mashi in sha Allahu zata rinƙa bin komai a hankali su Mom ma duk sun kirata sunyi mata jaje har suna cewa zasu zo Lagos ɗin suyi mata jaje tace ba sai sun zo ba kawai dai don Allah a tayasu bincikawa ba kamar wurin mutanensu dake Kano suka ce dama duk sunsa anata cigitawa in sha Allahu za'a ganta, Fanan ma ce mata tayi tana son tazo Nigeria ɗin amman ta ɗan ƙara saurarawa ne ko Farhar zata taho wurinta daga Kanon Hajiya Maryam ɗin tace hakan yayi kada ta taho, a ranar Monday da daddare Hajiya ta kira Hajiya Maryam tace mata gobe tazo tana son ganinta tana jin haka da sauri tace mata ko Farhar tazo wurinta ne tace mata a'a tana son yin magana da ita ne...........

103

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

........Washe gari da safe jirgin su ya sauka tare da security detail ɗinta aka ɗaukkosu zuwa gidan Hajiya motocin escort gaba da baya sai Jeep ɗin da take ciki a tsakiya, koda Hajiya ta ganta saida ta jinjina yadda ta rame, a bedroom ɗinta suka zauna tana kallonta tace ashe ta damu da Farha har haka amman shine taƙi goyon bayan abunda take so Hajiya Maryam ɗin ta ɗan yamutsa fuska kafin cikin karyayyar murya tace ai dole ta damu ace yarinyarka budurwa tabar gida ita damuwarta a wane hali take ciki ina taje, tana yin Maganar ƙwalla suka zubo mata sharr Hajiya tace "in sha Allahu tana cikin ƙoshin lafiya kuma a hannu nagari" a hankali ta amsa da Allah yasa,

"Yanzu in aka ganta zaki goyi bayan abunda take so ko?" Hajiya ta tambaya tana kallonta tay ɗan jimm kafin tace "Hajjaju ni a ganina ba kowanne abu yaro ke zuwa dashi a goya mashi baya ba, komai da nike yi saboda rayuwarta ta inganta ne taya za'a ce Farha ta auri yaro kamar wannan bacin ga wanda ya gina rayuwarshi wanda zai ruƙeta da kyau muna gani sai mu barta taje ta jefa rayuwarta a wahala"

ɗan murmushi Hajiya tayi tace "idan abunda yaron yazo dashi baida wani aibu lafiya lou sai a goya mashi baya mana, sannan Maganar gina rayuwa ai shima baki san abunda Allah zai yi ma tashi rayuwar ba tunda yanzu yake kan gina ta, sannan Maganar jefa rayuwa a wahala shi wanda kike hangen zai ruƙeta da kyau saboda kuɗi ke a tunaninki mai kuɗi ne ke ruƙe mata da kyau, Matan masu kuɗi nawa ne suke cikin damuwa a gidajen auransu har suna ganin dama talaka suka aura wanda zai basu farinciki, ko kuwa don ke kin dace sai kike ganin kowace mace ma hakan take a wurinta to kije ki bincika na tabbatar zaki samu mata da dama wanda kuɗaɗen mazajensu basu sa sun kasance a cikin farinciki ba face damuwa",

É—an yamutsa fuska tay da yanayin damuwa tace "Yanzu dai fatana Farhar ta bayyana shine kawai, gani kince kina son ganina",

Hajiya na É—an murmushi tace ta dameta ko shiyasa take son a canza Maganar, da sauri tace mata a'a kawai dai taga ba abunda yakamata su maida kai akai bane tunda wadda ake Maganar don ita ba'a san inda take ba Hajiyar tace hakane Allah ya bayyana masu ita ta amsa da Amin,

"Kinzo na tsare ki da surutu ban baki abinci ba kuma halan ko breakfast baki yi ba" Hajiya ta faɗa idonta a kanta, warware gyalen haɗaɗɗar doguwar rigar dake jikinta data laga tayi ta kwanta a saman gadon tana faɗin tasha ɗan tea Abincin ne kwata kwata bai mata daɗi gashi duk in tazo ci sai tayi ta tunanin ko Farha taci abinci, yadda ta ƙarasa Maganar kamar zata saka kuka Hajiya na murmushi tace in sha Allahu taci mai kyau ma,

"Yanzu tea ɗin za'a ƙara haɗo maki sai a haɗa da wainar ƙwai muna da farfesun kaza ma, in kuma duk baki son su sai ki faɗi abunda kike so a haɗa maki" shiru ta ɗan yi kamar bazata yi magana ba can ƙasa ƙasa tace rana tayi abar tea ɗin a kawo mata farfesun taga in zata iya sha Hajiya tace to ko a soya doya sai ta haɗa da sauri ta girgiza mata kai tace abu mai ruwa ruwa kawai take ɗan iya ci Hajiya tayi murmushi tace to bari tasa a kawo mata anan, wayarta ta ɗaukko ta shiga yin kira bayan an ɗaga umarnin kawo ma Hajiya Maryam farfesu ta bayar tare da lemu da ruwa daga haka ta kashe wayar idanunta akan Hajiya Maryam data rufe ido kamar mai yin bacci, ba'a jima ba aka turo ƙopar ɗakin Farha ta shigo tana sanye da ƙananun kaya kaman ko yaushe kanta ba kallabi sai dark ash ɗin sumarta dake a fake ta lanƙwasa ta, bata yi sallama ba Hajiya tay mata nuni da gaban gadon saitin inda Hajiya Maryam ke kwance tace taje ta aje anan kan carpet, har ta aje Hajiya Maryam bata buɗe ido ba Farhar ta ɗago tana kallonta wata irin kewar Mahaifiyar tata taji ita kanta taga canzawar da tayi bata ta6a tunanin za'a samu ranar da zasu samu sa6ani da Mom ɗin tata ba don sun shaƙu kamar abokai haka suke dalilin shaƙuwarsu ne ma yasa Farhar bata fita ƙasar waje yin karatu ba tayi a nan, da hannu Hajiya tayi mata alamun ta gaishe da ita cikin ɗan rawar murya tace mata ina kwana still bata buɗe idon ba da alama ma bata ji ba, saida Hajiya tace mata ana gaisheta sannan ta ɗan ɗaga hannu alamar ta amsa, tsaye Farhar tayi tana ta kallonta a hankali ƙamshin turarenta ya fara kurɗaɗawa cikin hancin Hajiya Maryam lokacin data shaƙe shi sosae da mamaki ta ayyana ƙamshin kamar na Farha, zuciyarta na raya mata hakan da sauri ta buɗe idanun nata suka shiga cikin na Farha dake tsaye ai a sukwane ta tashi zaune tana kallonta idanu waje, muryarta har tana sarƙewa wurin faɗin "Wannan kamar Farha a gabana Hajjaju kodai gizon data saba yi man ne dama sai inta ganinta koda yaushe" Hajiya na murmushi tace itama kamar ita take gani, maido idonta tayi kan Farha dake ta kallonta sai kuma ta maida kan Hajiya, murmushin da taga tana yi ne yasa ta gane Farhar ce aikuwa da sauri ta miƙe tsaye cikin rawar murya ta furta "F...Farha, it's You...???" shiru ta ɗan yi kafin a hankali ta furta "Yes, Mom" zaro ido Hajiya Maryam tayi gaba ɗaya ta juya kan Hajiya cike da al'ajabi tace "Amman Hajjaju ya akai kika samota ko nan tazo?" ɗan ta6e baki Hajiya tayi tare da ɗan girgiza kai tace dama tana nan, cikin ɗaurewar kai ta maimaita abunda Hajiya ta faɗa ta ɗaga mata kai alamar tabbatar wa,

"Yanzu Hajjaju kina nufin duk abun nan Farha na wurin ki?" Hajiya tace mata eh ita ta tsara mata komai tasa ta taho wurin ta, wani kalan yarfa hannu Hajiya Maryam tayi tare da yamutsa fuska ta koma gado ta zauna yaraf kamar zata yi kuka tace "But Why, Hajjaju, miyasa don Allah zaki tada mana hankali har haka kika sa anata cigiya mutane nata kashe kuÉ—i suna zuwa jaje amman ashe tana wurinki kuma kina sane da dole hakan zai tada mana hankali ba kaÉ—an ba" wani irin É—aure fuska Hajiya tayi da hannu tayi ma Farha alamar ta zauna a kan carpet, bayan ta zauna ta maida idonta kan Hajiya Maryam fuska a É—aure ta fara magana,

"Nasani hankalin wanda bai san da tana wurina ba zai tashi kamar ke sannan Maganar kashe kuɗi da zuwa jaje duk nasan za'ai hakan saidai ina son ki sani na za6i yin hakan ne don in baki misalin irin tashin hankalin da kike niyyar janyo mana kenan koma wanda yafi wannan, saboda taurin kan ki kina ƙoƙarin ki saka mu a damuwa da danasanin da har mu mutu bazamu daina ba to aka me zamu zura ido muna kallo ki jefa mu a hakan, kina sane da illolin da auren dole ke tattare dashi amman shine kika rufe ido saboda wani kurman ra'ayin ki zaki jefa rayuwar yarinya a halaka, baki tunanin zata iya kassara rayuwarta ba ko kuma ta ƙyaleki ki ɗaura mata auren shi mijin ta illata shi ba, in hakan ya faru wane irin tashin hankali kike tunanin hakan zai haifar mana, so kike mu zama abun misali a idon duniya ki jaza mana tambarin da bazai ta6a goguwa ba har ƙarshen rayuwar mu?"" a fusace take yin Maganar,

jin tayi shiru ne yasa Hajiya Maryam É—in cewa "amman Hajjaju wannan ai ba auren dole bane tunda akwae soyayya tsakaninsu ta tsawon lokaci kuma su duka suna son junansu kwatsam kuma sai ta dawo tace wai bata son shi....."

Katseta Hajiya tayi taci gaba "tace bata son shin ai ba laifi tayi ba dama yana faruwa yau kaji kana son mutum gobe ka dawo kaji baka son shi dama ana samun haka wanda aka ɗauki lokaci ana soyayya sai kiga bashi Allah ya ƙaddaro za'a aura ba sai daga baya mijin ya 6ullo ta inda ba'ai zato ba yasha faruwa koma yana kan faruwa ma shiyasa wasu suke gudun 6ata lokaci wurin yin soyayya suke bari sai sun shirya ma aure sannan su fara wasu kuma suna yin soyayya da shirin kota kwana, shiyasa ba'a so ana soyayya ai ta ma juna ƙaryayyaki da alƙawura tunda mutum bashi keda kan shi ba ta yuwu wanda kake hasashen aura bashi Allah ya ƙaddaro zai zama abokin rayuwarka ba shiyasa yana da kyau a gina soyayya kan wannan turbar kowa yasa hakan a zuciyarshi sai kiga koda rabuwar tazo baza'a ji ciwo sosai ba, don haka ki rabu da yarinya ta auri wanda take so wataƙil dama wannan shine wanda Allah ya ƙaddaro zai zama abokin rayuwarta" ba alamun wasa Hajiya ke yin Maganar,

"Naji Hajjaju, in bata son Emran ɗin shikenan amman nidai gaskiya ban goyon bayan ta auri yaron don haka ta nemi wani" fuska a yamutse tay maganar aikuwa a fusace Hajiya tace "bata neman wanin wanda take son shi zata aura matuƙar Allah ya ƙaddara hakan, ke waya hana ki auren wanda kike so, wato yanzu kin kawo ƙarfi ke ga uwa shine zaki nemi ɗaga ma mutane hankali ke wa yay maki haka, inace lokacin da kika haɗu da Mahaifinsu kina da samarin da kuke soyayya lokacin in ban mance ba yaron nan soja ɗan wurin abokin Mahaifinku gashi nan da suna.....Nasir yauwa ba wanda bai yi tunanin shi zaki aura ba daga haɗuwa da mahaifunsu duk kika ruɗe ke kinga mai jan kunne rana ɗaya kika zo mana da zancen ke shi zaki aura, a lokacin Allah ya jiƙan rai mahaifin ku shine ma yaso ya ƙi abun don shi mutum ne mai kishin ƙasar shi da al'ummarshi ni na rarrashe shi kan ya ƙyale ki har Allah yasa kukai aure, in ma kin manta ne to gashi nan na tuna maki don haka yadda ba wanda ya hana ki auren wanda kike so haka itama ba wanda zai hanata auren wanda take so" idanun Hajiya Maryam ne suka ciko da ƙwalla suka zubo mata sharr cikin 6acin rai ta shiga faɗin amman ita ko a lokacin data kawo mahaifin su ai ya gina rayuwar shi ko shikenan sai ace an taru anata auren dangin su kowa su Haisam da Nameer sun auresu ga Kakar tasu ma kan su za'a ƙare,

"Zancen gina rayuwa ko ɗazun nayi maki maganar saurin mi kike ki jira shima kiga baki san yadda Allah zai da tashi rayuwar ba sai kiga ya zamo abunda baki ta6a zato ba ai shi arzuƙi na Allah ne Maryam kema ai ba wayon ki ne ya baki ba ko, sannan Maganar anata auren su alamar suna da nagarta ne ai ko a kasuwa zaki ga ana rububin abu mai nagarta, wasu Familyn ma zaki ga basu auren bare sai yasu yasu ma don haka don anata auren su ai ba aibu bane" shiru Hajiya Maryam ɗin tayi tana goge ƙwalla,

"Ina son jan hankalin ki Maryam al'amari in dai akace na Allah ne ki daina kafiya irin haka, wannan abun daya faru yanzu tamkar ishara ne Allah ya nuna maki, nan yarinyar nan Fateema daga ta auri mijin É—iyar ki kika É—aga masu hankali kikai ta kumfar bakin ke É—iyarki bazata zauna da ita matsayin kishiya ba don bata kai matsayin tayi kishi da ita ba waye waye, to yanzu ga É—iyar ki nan ta cikin ki Allah ya É—aura mata son Yayanta so mai tsanani itama yar jakar ubar nan harda ita aka hana Fateema zaman lafiya amma kinga soyayya ta rufe mata ido ko kunya bata ji ba tazo tace tana son Yayanta..." ta juya tana kallon Farha tare da É—an harararta Farhar ta É—an tura baki a hankali tace "pls Hajiya let bygones be bygones, ba kinsa mun shirya tuntuni ba",

ta6e baki Hajiya tay tace "da yake fa abunsu kike so kyace haka, shiyasa ita fitina bata da daɗi sam, yanzu da baku shirya ba kina tunani shi wanda kike son zai saurareki ne alhali kina tsangwamar yar'uwar shi, to da ya zaki da son ko sai kije ki faɗa rijiya mai kwala6e?" yar dariya Farhar tay ta sunnar da kai, maida idonta tay kan Hajiya Maryam da 6acin rai ya bayyana akan fuskarta cikin kwantar da murya tace "Wato shi Ubangiji yana yin abubuwa cikin hikima, daya halicci bayinsa sai ya kasasu wasu yayi su masu wadata wasu masu rufin asiri wasu kuma wanda basu dashi gaba ɗaya hikimar yin hakan shine don kowa ya amfana da kowa don inda yaso zai ba kowa arzuƙi amman sai bai yi hakan ba, duk wanda kika ga Allah ya ba arzuki bai bashi don ya amfana shi kaɗai ba face don ya taimaki wanda bashi dashi wanda ta silar haka zaka samu ɗunbin lada har kasamu shiga aljanna haka wanda bashi dashi in yayi haƙuri da yadda Allah yayi shi ya rungumi ƙaddarar shi bai sa6i Allah ta dalilin hakan ba shima sai kiga ya cinye jarabawar shi ta hanyar hakan har ya shiga aljanna, wasu da yawa Allah na saka arzuƙin su a hannun wasu shine zaki ga ta silar taimakon da kayi ma wani in ma aiki ka sama mashi ko kuɗi ka bashi ko auren shi kai da sauransu sai kiga hakan yayi silar arzuƙin mutumin, to dana yi nazari sai na gano kusan hakan ce Allah ya ƙaddaro tsakaninmu dasu Dije shiyasa har ya haɗamu maƙwabtaka kuma in kikai la'akari da ai basu kaɗai bane makwabtana akwae wanda muke tare tun kan suzo zaki shaida hakan, Allah yasa rabon wadatuwar su a hannun mu don haka bamu da ikon hana hakan koda kuwa ace bamu so to wllh sai rabonsu dake tattare damu ya isa gare su, don haka inason ki kwantar da hankalinki ki ɗauka mu dasu yanzu mun zama Family duk abunda ya taso tsakanin mu dasu in dai mai kyau ne to mu rungume shi hannu bibbiyu muyi fatan alkairi" shiru Hajiya Maryam tayi ta maida idonta ƙasa,

"Yanzu kin amince mata kan abunda take son?" Hajiya ta tambaya idonta akanta, ba tare data É—ago ba tace "taje Allah ya taimaka",

"Ba haka yakamata kice ba Maryam fatan alkairi zaki yi mata matsayinki na mahaifiyarta sannan ki yaƙi zuciyar ki ta rinƙa kallon abun a alkhairin" shiru tayi duk idanunsu na akanta can ta ɗago ta kalli Hajiyar tace Allah ya tabbatar da alkhairi, murmushi Hajiya tayi ta amsa da Amin Farha ta shiga yin murmushin farinciki tana washe baki tace "Thank you so much Mom, I love u" wata uwar harara ta wurga mata Hajiya tay yar dariya tace "in kina harararta fa zata ƙara 6acewa" ɗan gutsirin murmushi Hajiya Maryam ɗin tayi bata ce komai ba da sauri Farhar ta miƙe ta nufi hanyar fita daga ɗakin,

tana fitowa ɗakin Husnah ta nufa tana niyyar shiga Husnar ta fito daga ɗayan bedroom ɗin nata cike da farinciki Farhar ta sanar mata Mom ɗinta ta amince ma soyayyarsu da Kamal ta ɗan buɗa ido kafin tana murmushi tace ta tayata murna Allah ya tabbatar da alkhairi ta amsa da Amin ta ƙarasa shigewa cikin ɗakin, gyale ta yafo saman kanta tana fitowa falo ta nufi hanyar fita, gidan Gwaggo ta nufa bayan ta fito koda tazo shagon Amadu a rufe yake ta shige gate, tana niyyar shiga entrance Amadu na sako kai dama wanka ya shigo yi yana ganinta yaja ya tsaya yana ƙare mata kallo ita kuma tana ɗan murmushi ta gaishe shi bai amsa ba da tsananin mamaki yace mata an ganta kenan tay yar dariya tace dama ba 6acewa tayi ba tana nan gidan Hajiya, da alamun rashin fahimta yace kuma shine aketa cigiyarta, nan ta kwashe komai ta faɗi mashi sosae ya jinjina abun yace lallai Hajiya ta iya shirya abu kamar Film, tare suka shiga ya nufi part ɗin Gwaggo da ita lokacin Haulat ma na can sun fara aikin abincin rana, a falo suka tsaya Amadun ya shiga ƙwala ma Gwaggo kira yana ta fito taga wani abu, tana fitowa tayi arba da Farha itama zaro ido tay cike da al'ajabi tace kamar Farha take gani Amadu na murmushi yace itace da sauri ta tambayi ina aka ganta nan Amadun ya faɗi mata ashe wai tana gidan Hajiya Gwaggon ta washe bakin farinciki tace dama sai da Haulat ta zargi hakan da suka je jaje nan ta shiga ƙwala ma Haulat kira, bayan ta fito daga cikin Kichen ɗin itama saida ta nuna mamakin ganin Farha cikin washe baki Gwaggo ta shiga faɗin zarginta ya tabbata ashe wai tana wurin Hajiya Haulat ɗin tace ita dama tunda suka je ta lura da sam Hajiyar bata cikin damuwar 6acewar tata, zama sukai kan kujeru Amadu yace ma Farhar yaga mamanta ma tazo ɗazun ta gano tana nan kenan tace mashi a'a sai bayan data zo, nan take faɗi masu ai yanzu ta amince da tarayyarsu da Kamal ɗin cike da tsokana Amadu yace ai da ta haƙura da Kamalun tabi abunda Mom ɗin nata ke so ta wani tura mashi baki tare da ɗaure fuska duk sukai dariya, tambayar shi tayi Kamal ɗin tace ko yana School yace mata ai rabon shi da School tunda yaji labarin ta gudu saboda shi yanzu haka yana ɗaki bai jin daɗi, ai tana jin haka zumbur ta miƙe ta nufi hanyar ɗakinshi tana faɗin bari taje ta faɗi mashi ba guduwa tayi ba duk suka bita da kallo, juyowa Amadu yay ya kalli Gwaggo dake murmushi yace Allah ya haɗata da suruka ƙwara ba kunya duk sukai dariya, lokacin data shiga cikin ɗakin yana kwance kan katifa idanunshi a rufe tay tsaye daga gaban ƙopa tana kallonshi da murmushi can ta kira sunan shi "Kamal" a hankali ya fara motsa idanun shi masu ɗauke da zarazaran gashin ido kafin ya buɗesu ya ƙura ma gabanshi ido duk ɗaukar shi muryarta ce ke mashi gizo, saida ta ƙara kiran nashi sannan da sauri ya ɗago kai ai koda yay arba da ita a firgice ya ƙarasa tashi zaune yana kallonta ita kuma sai murmushi take mashi ya murje idanun shi ya buɗe ganin still tana nan yasa shi nunata tare da kiran sunanta ta ɗage mashi gira tare da amsa mashi da Yes, zumbur yay ya miƙe tsaye da alamun al'ajabi yace don Allah da gaske itace yadda yay tambayar ne ya bata dariya don duk alamun tsoro ya bayyana a tattare da shi tace mashi itace mana amman tunda taga bai yi farincikin ganinta ba bari ta koma da sauri yace a'a ta tsaya pls ya nufeta, a ɗan gabanta ya tsaya har fuskar shi ta faɗa da tsananin mamaki yace mata yaushe aka ganta ne kuma miyasa zatai haka, saida ta matso gaban shi sannan tace mashi itafa ba 6acewa tayi ba dama duk shiri ne nan ta shiga faɗi mashi yadda akai, shima sosae yayi mamaki cike da farinciki ta kai duka hannuwanta ta kamo nashi tace "guess what?" da sauri ya girgiza mata kai ta sanar dashi yanzu babu wata matsala zasu yi soyayyarsu hankali kwance don Mom ɗinta ta amince masu ya ɗan buɗa ido yace don Allah da gaske tace eh mana yanzu haka Mom ɗin nasu na gidan Hajiya, ƙayataccen murmushin daɗi ya shiga saki tace yayi haƙuri ta saka shi ciwo in ba hakan akayi ba Mom ɗin nasu daba lalle ta amince masu ba, da sauri yace ba komai ai yanzu ma yaji ya warke shi dama abunda yafi damunshi shine a wane hali take ciki hakan har kuka yake saka shi, bin juna sukai da wani irin kallo mai nuni da tsantsar ƙaunar da suke ma juna can Farhar ta furta "I love so much Kamal, pls dont turn your back on me",

"I will never do that to you, My Love, i'm very grateful for accepting me for who i am, ban ta6a tunanin zaki so ni haka ba saboda tazarar dake tsakanin mu ajin ki ya wuce na ki soni shiyasa koda kika nemi da muyi ƙawance saida na jinjina abun sosae yanzu gashi kin za6i ma in zama abokin rayuwarki, i can't thank you enough, but, i give you all my heart in return" wani kalan murmushin daɗi tay ta faɗa jikinshi tare da lumshe ido yay shiru ƙirjin shi na bugawa don hakan abu ne da bai ta6a faruwa dashi ba ya haɗa jikin shi da mace koda kuwa yar'uwarshi tun bayan daya balaga duk da su a al'adarsu hakan ba wani abu bane amman su da yake suna da ilimin addini sun san hakan haramun ne shiyasa bai ta6a kowacce mace, hannu ya kai ya ɗagota suka haɗa ido tana ɗan murmushi ta furta yayi haƙuri taji daɗin Maganarshi ne, dama tun ba yanzu ba da suna ƙawance tana yawan ta6a shi tun yana sharewa ganin abun na yin yawa yace mata ta bar ta6a shi ba kyau kada su rinƙa samun zunubi, ce mashi tayi yazo suje ya gaida Mom ɗin ta ya ɗan waro ido tare da buɗa baki yace ba matsala kuwa tay yar dariya tace mashi he should be a man ba abund zai faru shima yay dariya yace to ko ta jirashi a falon Gwaggo ko Aunty Haulat ya shirya tace Ok ta juya tana faɗin yayi kyau sosae yace to, shiryawa yay cikin ƙananun kaya baƙin jeans da jar t-shirt anyi bakin rubutu a gabanta ƙafafunshi yasa baƙaƙen takalma sai agogo itama baƙa sumar nan tashi tubarkalla dama koda yaushe a kwance take ya ƙara gyarata sai salƙi take ya feshe jikinshi da turare ko maƙiyinshi sai dai don ƙiyayya yace bai yi kyau ba, lokacin da suka fito Amadu na shago yaje yace mashi zai je gaida surukarshi yay mashi Addu'a yay Maganar yana dariya shima Amadun dariyar yayi yace to Allah yasa a wanye lafiya in sun ji shiru kuma zasu zo beli Kamal ɗin yay dariya, tunda suka shigo harabar gidan gabanshi ke ɗan faɗuwa hakanan ya daure, lokacin da suka shigo cikin parlon ba kowa su Husnarh na Kitchen don rana tayi ta nufi bedroom ɗin Hajiya tare dashi, ita ta fara shiga shi kuma yay tsaye saida ta kalli cikin ɗakin taga yadda suke sannan ta juyo tace mashi ya shigo mana, ƙasa ƙasa da murya yace ta fara faɗi masu mana Hajiya dake kishingiɗe akan lallausan carpet ɗin gaban gado ta tada kai da tuntun ta ɗan ɗaga murya tace ita da waye anan ta maido kanta cikin ɗakin tana murmushi tace Kamal ne, tashi zaune sosae Hajiyar tayi tana faɗin to ya shigo mana shida ɗakin matarshi, tare suka shiga yay sallama ta amsa tana murmushi lokacin da idanunshi suka sauka akan Hajiya Maryam dake kwance saman gado ta rufe odo ƙananun kitson kanta sun bayyana sai da gabanshi ya buga sosae da sauri ya kauda idon, nuna mashi wuri Hajiya tay gefenta tace ya zauna Farha ma ta zauna cikin muryarshi mai daɗi ta bafullatanin daya ji hausa ya gaishe da Hajiya ta amsa tare da yi mashi ya jiki tace ai tukur ya faɗi mata yana can yana zazza6i Masoyiyarshi ta 6ace, da sauri ya sunnar da kan shi don wata irin kunya ce ta rufe shi data yi maganar Farha dake murmushi tace ko School baya zuwa,

"To ai yanzu sai kaci gaba da zuwa tunda gata ta bayyana" ta faɗa tana yar dariya shima murmushi yake bai ce komai ba, juyawa tay kan Hajiya Maryam tace tayi bacci ne ga ɗanta yazo su gaisa shiru bata motsa ba Hajiyar tace ƙilan tayi bacci dama bayan ta gama cin abinci tace bacci take ji, miƙewa Farha tay ta rankwafa saman gadon ta shiga ɗan bubbugata, buɗe ido tay da alamu baccin ne ya ɗauketa fuska a yamutse tace lafiya ta tashe ta nuna mata saitin Kamal tayi tace dama shine yazo gaidata ta wurga mata wani kallo mai kamar harara, har zata faɗi wata magana sai kuma tayi shiru ta maida idonta kan Kamal Farha tace mashi su gaisa ya ɗago ido ya kalli Hajiya Maryam ɗin cikin faɗuwar gaba yace mata ina wuni kamar bazata amsa ba sai kuma ta ɗaga mashi kai ya ƙara cewa an zo lafiya kamar wadda akai ma dole tace lafiya daga haka ta maida idanunta ta rufe, cigaba da jan shi da magana Hajiya tayi har tana tambayar yanayin karatunshi yana dai maida hankali ko yace mata eh, bayan wani ɗan lokaci yay mata sallama ya miƙe Farha ma ta miƙe Hajiya ta kalleta tana murmushi tace Juliet za'a raka Romeo tayi dariya, buɗe ido Hajiya Maryam tayi tabi Kamal ɗin da kallo har suka fita Hajiya data lura da tana kallon Kamal ɗin bayan fitar su tana murmushi tace to ya taga surukin nata tayi shiru bata ce komai ba,

"Inda zaki ɗauki shawarata kija yaron nan a jiki ki gina rayuwar shi sai yafi ma ruƙe maki ɗiyar taki da daraja" shiru Hajiya Maryam ɗin tay saida Hajiya tace bata jita bane sannan ta ɗan ta6e baki tace nawa akai ma haka amman suka butulce da sauri Hajiya tace sai dai dama can in butulun ne amman tana da yaƙinin zuri'ar Dije ba butulu bane Hajiya Maryam ɗin tay shiru bata ce komai ba can Hajiyar ta ƙara cewa "bari in maku da yaren daku yan siyasa kuka fi ganewa, yanzu aji kinja shi a jiki kin ginashi sannan kin ɗauki ɗiyarki kin bashi wane irin farin jini kike tunanin zaki a wurin mutane ta yadda koda nan gaba kin fito takara hakan zai iya saka mutane su za6e ki don ansan baki ƙyamar talaka kuma su naki ne, yanzu kamar yaron nan Sameer yadda ya auri ƙawar ita Fateema akai ta jinjina abun yanzu bashi ba ko mahaifinshi ya fito wata takara mutane da dama sai sun za6e shi dalilin haka, amman kawai misali ne na baki kan amfanin taimakon talaka a wurin ku yan siyasa nafi son komai zaki mashi kiyi mashi don Allah, ɗan jimm tayi kamar bazata tanka ba can ta tambayi Hajiyar mi yake karanta ta ɗan yi shiru alamar tunani kafin ta faɗi mata,

"Yanzu kenan ita Farhar zatayi ta zaman jiranshi har ya gama karatun?" ta tambaya idonta akan Hajiya tace mata to yanzu duka ba saura shekara ukku ba ganin lokacin ne mai wuya ai amman yadda yanzu shekara ta zama kamar wata ai kaman gobe ne zai gama in kuma zasu bashi yana karatun to sai a kawota nan Katsina shi yana karatunshi Hajiya Maryam É—in ta É—an ta6e baki bata ce komai ba, tambayarta Hajiya tayi yaushe zata koma tace tana tunanin ko zuwa anjima Hajiyar tace ta bari sai gobe mana tana kallonta tace to dama ba dalilin Farhar yasa ta kirata ba Hajiya tana murmushi tace "Eh, amman ban gaji da ganin yar autar tawa ba" ba shiri Hajia Maryam É—in tayi murmushi,

"Kina yarinya Haƙuri ne dake sosae ba wanda zai ce in kin girma zaki zama rigimamma" tana murmushin tace mata ita ai bata rigima sai akan abunda take ganin shine daidai Hajiya na dariya tace haka dai tace,

"Yanzu da Farhar zaki tafi ne?" Hajiya ta tambaya tace mata eh saboda su Abraham suna zaune gida su kaɗai Hajiya ta jinjina kai kafin tace yakamata ma su koma gabanta can Abujar tace eh tana shirin yin hakan sai kuma Hajiya ta sake cewa to shi Dr ɗin sai a barshi a Lagos shi kaɗai Hajiya Maryam tace to tunda can yake aiki dole can zai zauna sai su rinƙa zuwa mashi Weekend ko kuma shi yaje Abujar in anyi hutun School ma sai yaran suje mashi hutu,

"To ki bashshi kawai ya ƙara aure mana" wani kallo tay ma Hajiyar sai kuma tayi ɗan murmushi tace ashe bata sonta har haka Hajiyar tayi dariya tace miye abun rashin so daga ta bata shawara yadda zata yi ma Dr adalci tace ai bata mashi rashin adalci tana kamantawa kuma itama ai bata rayu da kishiya ba ko, Hajiyar tace ai ita shine ke tafiya can aikin sojan shi ya barta ba itace ke barin shi ba kamar ita, Hajiya Maryam ɗin tace ai koda take barin shi bai zarta ƙa'ida ba da har zai sashi ƙara wani aure, ruƙe ha6a Hajiya tayi tace oh kowa gudun kishiya ita ko da ba'a yi mata ba General ɗin ne bai ra'ayi ba wai ita ta hanashi ba, Hajiya Maryam dake ɗan murmushi tace ai ba abun daɗi bace ita ko sunanta ma bata son ana faɗa,

"anya Maryam, adai rage zafin kishi tunda ba'asan abunda Allah ya ƙaddaro ba" da sauri tace "in dai ta wannan bangaren ne ba abunda ya ƙaddaro in sha Allah auren zobe mukai da shi" dariya Hajiya tayi tace banda wanda aka ɗaura masu a Masallaci kenan wani suka ƙara ɗaurawa tsakaninsu Hajiya Maryam ɗin na murmushi tace mata eh, haka suka cigaba da yin hira sama sama har baccin ya sake ɗaukar Hajiya Maryam.

Washe gari da safe ta koma tare da Farhar, sosae Dr Mahaifin Farha yay farincikin amincewar da Hajiya Maryam ɗin tayi, bayan dawowarta ne Dr ɗin yasa suka zauna don yin shawara game da Kamal yadda zasu inganta rayuwar shi nan ya bada shawarar su fitar dashi ƙasar waje yayi karatu a can ita kuma Farha sai taci gaba da yin Master's degree ɗinta ta amince da hakan, Hajiya ta kira ta sanar da ita suna son fitar da Kamalun waje tace ta sanar da dangin shi, Gwaggo ta kira ta sanar mawa koda Amadu yaji zancen bai goyi baya ba haka da aka sanar ma Fatuu cewa tayi gaskiya kada a amince a ƙyale shi yaci gaba da karatun shi anan salon nan gaba ayi mashi gorin an ɗauki nauyin karatun shi Gwaggo tace to ai ba roƙonsu akai ba su suka yanke hakan Fatun tace ita dai gaskiya bata goyon bayan hakan tunda ai karatun nan ma lafiya lou zai yi ya kuma samu aiki mai kyau, Gwaggo tace itama in son samu ne tafi son a ƙyale shi tunda ma har ya fara yin nisa saidai kuma bata son Hajiya taga anyi masu ba daidai ba, Amadu yace ai Maganar bata Hajiya bace ita da saƙo aka bata yasan zata fahimce su in aka nuna mata tunda ya riga ya fara anan har ya shiga shekara ta biyu a barshi ya ƙarasa, Gwaggo da kanta taje wurin Hajiyar cikin fahimta tayi mata bayanin da Amadun yayi tace itama saida tayi tunanin hakan to amman tunda saƙo ne aka bata shiyasa ta isar, kamar yadda sukai da Gwaggon haka Hajiya ta sanar ma Hajiya Maryam hakan yasa ta fara tabbatar da su bama su Kwaɗayi bane sanin da wuya ai ma wani tayin karatu a ƙasar waje amman ya maida, Soyayya sosae su Farhar suke sha ita da Kamalu don sun samu yanci daga baya ta fara shirye shiryen fara cigaba da karatunta.

Bayan sabuwar Gwamnati ta fara ayyuka sosae Haisam ya tuntubi Alhaji lawal kan buƙatar ayi ma garin su Fatuu hanya a kuma gyara masu wutar lantarki kasantuwar shine ɗan majalissarsu na tarayya ya bashi tabbacin za'ayi masu, tuni aikin ginin Kamfanin Haisam wanda ƙwararran kuma sanannen Companyn gini anan Abujar keyi ya kankama, a yadda aka tsara zuwa nan da shekara guda za'a gama, tuni Al'umma sun fara sheda cewa sabuwar Gwamnati data hau ta aiki ce don kuwa anfara gudanar da ayyuka gadan gadan a faɗin ƙasa bayan hawan ta mulki ciki harda shirye shiryen da zasu tallafa ma talaka ya dogara da kan shi da yake ba laifi mai girma shugaban ƙasa ya samu abokan tafiya da shawara na ƙwarae masu tausayin talakawa, Kawu Mani har Abuja ya fara zuwa da Gwaggo acan ya samu inda ya kaita aka fara koya mata turanci don ta iya karatu, kan kace mi Gwaggo ta canza ta ƙara murmurewa duk alamun tsofanta daya bayyana yanzu babu sosae farinta ya ƙara fitowa tayi dumurmur abunta dama gata doguwar mace abun dai saidai ace tubarkallah, a bangaren First Lady kuwa wato Mahaifiyar su Haisam abun ba'a magana yanzu jin daɗi ya ninninku ta ƙara wani irin kyau Jama'a kowa yabon kyaunta da kuma kirkinta ake don mace ce mai sauƙin kai wadda kowa nata ne mutane har so suke a nunota tana jawabi don ta iya magana ba ƙaɗan ba, a yadda mutane keta faɗa ba'a ta6a First Lady kamarta ba wadda ta ko ina tayi, su Fatuu da Mino ana can America Mino ta maida hankali tanata karatu haka Nameer ma.

Lokacin da za'ayi bikin cikar President shekara ɗaya a kan kujerar mulki aka shirya buɗe Companyn Haisam, da lokacin Hajji yayi gaba ɗayansu suka je harda shi shugaban ƙasan da Hajiya dasu Mom suma su Fatuu da Mino da Fanan da Haisam da Nameer nan Nigeria suka zo suka tafi tare harda Aunty Laila da Mijinta harda Jidderh ma duk wanda suka isa aikin Hajji a Familyn shugaban ƙasan saida suka je haka bangaren Minister Hajiya Maryam taje ita da Mijinta da Farha, sosae sukai ma shugaban ƙasa Addu'oi kan Allah ya tallafa mashi ya taya shi sauke nauyin dake kan shi kamar yadda ya roƙesu kan suyi mashi Addu'oin, Haisam ma sunyi mashi Addu'oin Allah yasa ya buɗe Companyn shi a sa'a, bayan gama aikin Hajjin suka dawo gida Nigeria, abun na Allah ne su Fatuu an zama Hajiya harda haƙorin Makka tasa haka ma Mino kuma sosae yay masu kyau, bayan dawowar su sun ɗan zauna a Nigeria Haisam ya duba ginin nashi wanda tuni yayi nisa lokacin Fatuu da Mino suka tafi Katsina Hajiya dai President ya ruƙeta kan sai ta ƙara hutawa sosae ita Hajiya Maryam ma cewa tayi kada ta koma Katsina ta dawo nan da zama kawai shima President ɗin dasu Mom suka nuna goyon bayan hakan Hajiyar ta nuna tafi son zama a can don ta saba da mutane kuma bai kamata ace duk sun baro can ba tunda nan ne tushen su, bayan zuwan su Fatuu Katsina har gidan Aunty Mareeya da Feenah taje ta kai masu tsaraba harda Abdul ɗan gidanta shima yasha tsaraba haka Aminiyarta ma Haulat tayo mata tsaraba kullum tana a gidan Gwaggo anan ma take kwana tunda shi Haisam na Abuja, bayan sati biyu suka koma America, bayan komawarsu ne Haisam yaba Fatuu da Fanan damar za6a ma Companyn suna yace yana son duk sunayen su ya fito a ciki nan suka shiga haɗa sunaye ita Fatuu tace ko asa HAIFAN ita kuma Fanan tace HAIFAT zai fi, ƙarshe dai HAIFAT TechWorld aka yanke saka ma Companyn.

A kwana a tashi ba wuya har gashi shekara guda da hawan su President Ali Washegarin da akayi bikin murnar cika shekarar aka buɗe katafaren Companyn Haisam wato HAIFAT TechWorld, Kamfani ne da zai rinƙa ƙera kwanfutoci da saida bangarorinta da building softwares products da kuma Internet services daban daban da Online Services tare da kuma Consulting Services, sosae ginin kamfanin ya ƙeru yana da bangarori daban daban harda elevator ke akwae da zai kai mutum can sama abun sai dai ace Ma sha Allah, Mutane da dama ne suka halarci bikin buɗe shi ciki harda Mahaifin Haisam ɗin da manyan ƙososhin Gwamnati harda na wasu ƙasashen makwabta sannan ta bangaren danginsu kowa yazo har su Gwaggo harda Baffan Fatuu da Yadikko haka yan uwansu yan Ethiopia su Hajiya Zainab da Sameer harda Fauzy tare da twins ɗinsu da suka girma abun sai dai ace tubarkallah, abokan aikin Haisam ma turawa duk sun zo ciki harda waɗanda ya ɗauka zasu yi aiki tare gaba ɗaya duk wani masoyin Haisam da Abokan shi suna a wurin harda su Abbas da Najeeb da Saleem, ba ƙaramin mutane aka haɗa ba kowa yayi shiga ta alfarma kar ma su Mom suji su Fatuu ma ansha rantsattsan leshi iri ɗaya ita da Fanan wuya da hannu sun sha danƙararrun gold Haisam ma yasha bugaggun fararen suit sai necktie baƙi haka ƙafafunshi na sanye da dakakkun baƙaƙen cover suma abokan aikin nashi duk suit ne a jikinsu, yaran su gwanin burgewa duk sun girma su Twins yanzu shekararsu ukku da watanni amman sai kace sun fi hakan don suna da tsawo da kuma kauri suma suna sanye da suit na yara Esha kuma shekarunta biyu itama tana sanye da ƙananun kaya riga da wando an raba mata baƙar sumarta biyu ta saukko har ta wuce kafaɗarta kunnanta na sanye da barimar diamond da yan hannu ba ƙaramin kyau yaran sukai ba duk wanda ya kallesu sai ya ƙara yan jarida duk sun zagaye wurin suna ta aikin ɗaukar rahoto, bayan jin bayanai da suka danganci sabon kamfanin daga bakunan wasu masu ruwa da tsaki a kamfanin ciki harda Chief Executive Officer (CEO) wato Haisam da Mr President da wasu turawa a tare Haisam ɗin da Fatuu da Fanan suka yanka ribbon ɗin da aka zagaye ƙopar shiga cikin kamfanin mutane suka sa tafi ji kake "raf...raf...raf...) wasu suka shiga faɗin "Behind every Sucessiful Man there is woman or women" duk akasa dariya kafin akai bismillah suka sa kai, ginin bene ne hawa ukku akwae Ofisoshi daban daban da bangarorin gudanar da aikin kamfanin ko ina an zuba nagartattun furniture da suka dace da wurin wani abun ma sai Office ɗin Haisam wata daula ce guda akwae kuma ɗakin taro wanda aka sa haɗaɗɗan zunguren tebur aka kewaye shi da kujeru mahaɗin shi, haka akai ta zagayawa wurare ana ɗaukar hotuna da Vedios Mutane sai yabo da sa Albarka suke yan jarida nata yi ma mutanen tambayoyi ciki harda su Fatuu aka tambayesu irin farincikin da suke ciki, bayan an gama duba ko ina saida akayi addu'o'i sannan aka fita daga nan kuma Villa aka nufa don yin lunch event, komai dai ya ƙayatar an ci an sha anyi hani'an sai fatan Allah ubangiji yasa ma kamfanin albarka ake, a ranar kusan kowacce tashar Tv saida aka nuna bikin buɗewar haka Social media Maganar sabon kamfanin kawai ake da gidajen radio ana tallata irin ayyukan da kamfanin zai rinƙa yi har da tashoshin wasu ƙasashen an nuna dasu bbc, a ranar da daddare Khalid na zaune a falon gidanshi yana kallon bikin buɗewar a NTA, lokacin da aka nuno Fatuu na magana da turanci tana murmushi shima ɗan murmushin yayi saidai nashi yafi kama dana takaici don kuwa shi yasan yayi babban rashi kuma har abada bazata fita a ranshi ba, matarshi Hafsat ce ta dawo cikin falon daga kwantar da ɗiyarsu Zarah bayan ta zauna ya nuna mata Fatuu cikin Tv ɗin yace mata wannan itace Fateema, kallon Tv ɗin tayi kafin ta juyo ta kalleshi da alamun rashin fahimta tace mashi wace Fateema yay shiru kawai tana ta kallonshi can yace mata ta garinsu yana faɗin hakan ta gane don tasan labarin da ita zai aura aka fasa saidai bata san dalilin fasawar ba, maida idonta tayi kan Tv ɗin lokaci guda taji Fatun ta burgeta ta juya da ɗan murmushi tace mashi tana da kyau sosae yay ɗan guntun murmushi kawai bai ce komai ba can sai ya miƙe ma ya nufi hanyar Bedroom ta bishi da kallo.

Bayan buɗe kamfanin ranar Monday aka fara aiki a cikin shi, a yadda Haisam ya shirya zasu ɗan daɗe anan daga baya sai su koma America suyo parking ɗin dawowa Nigeria gaba ɗaya dama ya aje aikin kamfanin da yake acan saidai ba kwata kwata ya daina aiki dasu ba akwae wanda zai cigaba da yi masu sannan shima akwae aikin da daga can za'a rinƙa yi mashi a Companyn shi, bayan wata biyu akayi bikin Jidderh da Saurayinta Sadeeq ɗan Minister wanda bayan hawan Senator Ali kujerar shugabanci ya sake ba Mahaifin nashi muƙamin Minister, ba ƙaramin shagali aka sha ba auran ɗiyar shugaban ƙasa da kuma ɗan Minister wanda anan Abuja aka ɗaura ya kuma samu halarta manyan mutane daga ko ina ciki da wajen ƙasar nan sai fatan Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba. Tuni aiki ya kankama a kamfanin Haisam anata neman aiki bayan wata ukku da buɗeshi lokacin wata guda da yin bikin Jidderh suka koma America, sati biyu sukai suka dawo acan aka baro Nameer da Mino sai sun gama karatunsu nan da shekara ɗaya da wasu watanni suma zasu baro can, Bayan dawowarsu Haisam Nigeria a yadda ya tsara zasu zauna a gidanshi ne, dama duk mazan gidansu kowa yana da gida da Dad ɗinsu ya mallaka masu saboda ba zaune suke ba dundundun yasa basu zauna acan ba suke zama a gidansu in sunzo Abuja, shi Nameer wanda yake zaune inda aka kai Mino shine nashi shima Haisam nada nashi shima a Asokoro saidai bayan dawowar tasu Dad ɗinsu yace mashi su fara zama anan gidanshi inda suka baro suka koma Villa don kar a bar gidan hakanan in aka ƙara wasu shekaru sai su koma nasu, hakan aka yi anan gidan suka zauna duk da yayi masu girma sosae, bayan dawowar su bada daɗewa ba Fanan ta samu aiki a National Hospital Fatuu kuma Haisam yay mata magana kan tafiyarta ƙasar india yin karatun Medicine amman sai tace mashi tunda anayi anan kawai ya bari sai tayi nan ba sai ta tafi wata ƙasa ba, ta yanke hakan ne don bata son yin nisa dashi yace mata amman karatun nan zai iya mata wahala tace lafiya lou in dai za'a koya mata to zata iya ya amince da hakan dama shima kawai don ya cika mata burinta ne zai barta taje India amman ba don yana son yin nisa da ita ba, cikin sa'a ta rubuta Jamb kuma points ɗinta ya kai yadda ake so don karatun likitancin, ba tare da wata wahala ba ta samu Admission a ABU Zaria Haisam ya kama mata gida mai kyau a zariar harda Security aka aje mata sannan tasa Iya ta samo mata mai aiki yar'uwarsu wadda dattijuwa ce daga can Daura suka zauna tare, lokacin data fara karatun tayi ma Haisam magana kan yasa akawo mata motarta daga Katsina amman sai yace tunda Amadu ke amfani da ita ta bari za'a kawo mata wata daga Kaduna hakan kuwa akai,

Gidan Haisam ya zama biyu Abuja da Zaria, duk Weekend yake zuwa Zaria wani lokacin a mota ko kuma ya hau jirgi zuwa Kaduna daga nan ya wuto Zaria idan kuma bai samu zuwa da Weekend ba cikin ranakun aiki yake ware rana yazo ya kwana sai ya koma wani lokacin kuma Fatun ce ke zuwa can Abujar akwae driver musamman dake kai ta, su Twins da Esha dai duk suna a Villa wurin Mom sai Weekend Fanan ke ɗaukkosu nan wurinta, sosae Fatuu ke jinjina ƙokarin da Haisam ke yi na zaryar zuwa wurinta ta san duk don ƙaunarta da yake yi ne, duk in yazo haka zatai ta mashi godiya da Addu'o'i, bayan wasu watanni da fara karatun nata suka ji Yadikko ta haihu abun yazo masu a bazata don basu san da tana da ciki ba aikuwa sunyi murna karma Fatuu da Mino suji don ta daɗe bata haihu ba sun ma ɗauka ta gama ne duk da Yadikkon bata wani manyanta ba haka shima Baffan nasu ba wani manyanta yayi ba haihuwa ta biyar ce tayi gashi namiji ta haifa dama bata da ɗa namiji Fatuu taji daɗi data haihu cikin Weekend, da satin suna ya zagayo ranar Friday tana gama lectures ta wuce Abuja washe gari Asabar suna da safe suka bi jirgi zuwa Yola ita da Esha harda Fanan, daga gidan gwamnatin Yola aka tura Motar da zata ɗaukesu harda ta Security suka wuce garin nasu, lokacin da suka isa tayi mamakin ganin yadda aikin hanyar da ake masu yayi nisa harda rijiyoyin burtsatse aka yi masu Fanan sai yaba garin take tana faɗin ya burgeta, anan ta iske Gwaggo da Haulat su jiya suka zo sosae kowa ya nuna farincikin zuwan nasu sai nan nan ake dasu ba kamar Fanan, Yadikko ma sosae tayi murnar zuwansu nan Fatuu ta bata saƙon su Mom harda Aunty kayane masu kyau da tsada atamfofi da laces sai kayan baby wanda yaci sunan Arɗo wato Ibrahim, Fatuu sai santin Babyn take harda ce ma Yadikko ta bata shi tana dariya tace ta ɗauka Fanan da tunda suka zo tana ruƙe dashi tace a'a ita za'a ba sai dariya ake masu, lokacin da Fatuu ta kira Mino Vedio call harda ƙwalla tayi ganin an haɗu banda ita, washe gari da wuri suka fara shirin tafiya saboda bayan sun koma Abuja a ranar kuma Fatuu zata wuce Zaria, tunda Aysha taga suna shirin tafiya ta shiga roƙon Fatuu ta tafi da ita harda ƙwallanta Gwaggo tace da kuma tace ita zata bi Ayshar tace a'a yanzu Adda Fatuu take son bi, to itama Fatun taji tana son tafiya da ita dama Mino na niyyar ɗaukarta tace mata ta shirya kayanta su tafi, Yadikko najin hakan tace ya za'ai ta kama ta tafi da ita ba tare da izinin mijinta ba ai bai kamata kawai ace ta ɗauketa taje masu da ita ba Gwaggo tace hakane kamata yay ace sai ta ambayi izinin shi duk da tasan bazai ƙi ba amman dai yana da kyau ta tambaye shi izni tace to, lokacin data kira Haisam ta faɗi mashi tana son tahowa da Aysha don ta nuna tana son biyota Murmushi yay yace yanzu don zatayi hakan shine sai ta faɗi mashi kada ta manta shi da ita abu ɗaya ne duk abunda yayi mata to shima yayi mashi tana murmushin jin daɗi tayi mashi godiya, wurin ƙarfe sha ɗaya na safe aka zo ɗaukar su suka yi sallama da kowa sai Godiya da Addu'ar Allah ya bar zumunci ake ma Fanan, harda uban naman suna aka basu dana su Mom dama saboda su aka fara aikin naman tunda wuri, kamar kar a rabu haka aka rakosu tare da Aysha dake ta faman washe baki harda su Gwaggo da Haulat su sai gobe zasu tafi suma ta jirgi suka zo kuma tashi zasu koma. Tare da Aysha Fatuu ta koma Zaria Asabe mai aikin Fatun ke kula da ita in ta tafi Makaranta daga baya itama Ayshar Haisam ya sakata a wata private dake anan layout unguwar da suke aka sata aji ukku na Secondary.

Cikin ɗan lokaci HAIFAT TechWorld ya samu kar6uwa a faɗin ƙasar nan, bama nan kaɗai ba harda wasu ƙasashen don kamfani ne da babu kamar sa a yankin Africa ta bangaren technology dama kuma yanzu harkar fasaha ba ƙaramin ci take ba, akwae abubuwa da dama da kamfanin ke samarwa wanda ada sai an dangana da ƙasashen turai yanzu kam nesa tazo kusa a kowacce rana ba ƙaramar riba Kamfanin ke samu ba. A kwana a tashi ba wuya a wurin Ubangiji gashi har kamfanin yayi shekara ɗaya da buɗewa anyi Addu'o'i da bikin murnar cika shekarar inda aka bayyana irin nasarorin da companyn ya samu da kuma irin ayyukan cigaba da ya kawo ma ƙasar nan aka ƙara samun masu son saka hannun jari, an ci an sha an ba ma'aikatan kamfanin masu ƙwazo kyaututtuka shima Haisam ya samu lambobin yabo abun saidai ace Alhamdulillah, bayan cikar kamfanin shekara ɗaya da wasu watanni su Nameer suka dawo Nigeria gaba ɗaya don duk sun gama karatun su, bayan dawowar su Nameer ya fara aiki shima a kamfanin a matsayin Software engineer, ganin Fatuu na karatu a Zaria kuma tana zaune a can Nameer ya yanke nemawa Mino Admission don ta yi degree kan abunda ta karanta a America wato Nursing dama matsayin diploma ce tayi, ba tare da wata wahala ba aka samar mata itama ta fara karatu a can ta zauna a gidan Fatuu, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma Fatun ba dama gidan babban gida ne kowacce da part ɗinta in mazajen su suka zo amman in suka tafi gaba ɗaya harda Aysha a part ɗin Fatuu suke zama rayuwar karatun nasu gwanin daɗi sam basu da wata matsala.

A bangaren Kamalu har ya shiga shekara ta ukku itama Farha tana cikin yin Master's Degree ɗinta a jami'ir Lagos, a bangaren soyayyarsu suna cigaba da gudanar da ita sosae saidai matsalar da Kamalun ke fuskanta a wurinta shine ta cika kishin tsiya ba dama ta kirashi taji yana waya ko bai ɗauka ba sai ta fara zargin ko da wata yake waya ko kuma ya rage sonta haka dai yake ta haƙuri don yasan saboda son da take mashi ne yasa take mashi hakan kuma shima yana son ta sosae.

Kwance tashi har Kamalun ya gama karatun shi na Degree, cikin sa'a result ɗinshi yayi kyau sosae saura kuma yin Nysc, result ɗin nashi na fitowa Fatuu tayi ma Haisam magana kan in zai yuwu ya ɗauke shi aiki a company ɗinshi tunda abunda ya karanta ya danganci aikin kamfanin yace mata lafiya lou zasu ɗauke shi daya gama Service sosae taji daɗi dama ita abunda bata so shine ace Hajiya Maryam ce ta samar mashi aiki gudun wata rana a goranta mashi, Abuja Haisam yasa aka kawo shi yin bautar ƙasan a kamfanin shi ya zauna a gidan su kullum in Haisam ɗin zai tafi aiki tare suke tafiya hakan kuma ba ƙaramin daɗi yayi ma Fatuu ba, tun ma kafin Kamalun ya zama ma'aikacin kamfanin Haisam ya yaba da ƙwazon shi cikin ɗan lokaci Kamalun ya ƙara murmurewa ya zama kalar samarin Abuja, gab da Kamalu zai kammala bautar ƙasar aka fara shirye shiryen yin za6e yayin da waɗanda ke akan mulki duk suka bayyana muradinsu na yin tazarce ciki harda Dad ɗinsu Haisam wanda shi tun kafin ma ayi za6en mutane har sun za6e shi kawai don ya zama dole sai anyi zaben amman Al'umma basu ƙi kawai yaci gaba ba don a mulkinshi sun shar6i romon demokaraɗiyya ba kaɗan ba, a cikin shekaru huɗun da yayi abubuwa da dama sun inganta kama daga ilimi, lafiya, harkar tsaro, wutar lantarki, ruwan sha hanyoyi da dai sauransu gashi an tallafa ma talakawa ta yadda da yawa sun samu abun yi yanzu tun a makaranta ake koya ma yaro sana'a don ya tashi yana da sana'ar yi haka manoma ma harkar abinci ta inganta sosae ake amfani da abincin nan gida gashi da yawan mutanen mu masu ƙwazo dake aiki a ƙasashen waje yayi yadda yay suka dawo suna ma ƙasa aiki hakan ba ƙaramin inganta bangarorin da suke aiki yayi ba ciki harda Asibitoci yanzu saidai don ra'ayin mutum yaje asibitin ƙuɗi ko ya kai ƴaƴanshi makarantun kuɗi ba wai don rashin ingancin na gwamnati ba don komai ya gyaru haka tsofaffin masana'antu da suka daɗe da daina yin aiki duk an farfaɗo dasu abun dai sai son barka (Allah ka bamu shuwagabani irin haka Alfarmar Annabin rahama (S.A.W), Amin ya Hayyu ya ƙayyum).

Bayan gudanar da za6e tuni President Ali Adamu Zakee ya koma kan kujerar shi aka ci gaba daga inda aka tsaya, bayan yin za6en Kamfanin Haisam ya cika shekara ukku batun nasarorin da ya samu ko yake samu abun ba'a magana, a yadda suke yi duk ƙarshen shekara ake raba ribar da aka samu kuma duk in suka raba sai yaba Fatuu da Fanan wani kaso mai tsoka zuwa shekaru ukkun sai gashi Fatuu ta tara kuɗi masu ɗan yawa a yadda ta tsara in suka kai kuɗin zuwa Hajjin mutum biyu sai ta biya ma Baffanta da Gwaggo. Kamalu na gama bautar ƙasar shi aka fara shirye shiryen auren shi da Farha lokacin itama ta kammala karatunta, ba ƙaramin shagali aka sha ba bikin ɗiyar Minister ɗiyar shugaban ƙasa, gaba ɗaya hidimar bikin a Abuja aka yi ta gashi wata gwaninta da Hajiya Maryam tayi ta ban mamaki itace gaba ɗaya Amaryar da Angon ta haɗa tayi masu lefe dama tunda bikin ya taho ta sanar ma Hajiya a faɗi ma su Gwaggo kada ayi ma Farhar lefe lokacin har wasu sukai tunanin ko don tasan ba lalle Kamalun yayi lefen daya dace bane sai gashi ta bada mamaki ai kuwa gaba ɗaya ƙasa ta ɗaukka sai zancen ake na ta ba talaka ɗiyarta kuma tayi masu lefe gaba ɗaya, tun kafin bikin Haisam ya roƙi Dad dinshi kan yaba Kamalun gidan da zai zauna kafin ya mallaki nashi tunda zasu fara aiki tare, ɗaya daga cikin gidajen shi na Sabuwar Estate ɗin shi dake a Gwarinpa ya ba Kamalun, ganin babban gidane yasa Haisam ɗin yace mashi ya faɗi mashi yadda zai rinƙa biyan haya Dad ɗin nashi yace dama ɗa yana haya a gidan babanshi ne ai Kamalun kamar ɗan shi yake don haka bashi yay ya zauna kafin Allah yasa ya mallaki nashi, sosae Haisam yaji daɗin hakan yay mashi godiya da Addu'oi, lokacin har Hajiya Maryam tayi niyyar basu gidan da zasu zauna aikuwa hakan da Haisam yayi ba ƙaramin daɗi yayi ma Fatuu da Amadu ba dama sune masu gudun ayi ma Kamalun abun da za'a iya goranta mashi, ko ban faɗa ba kunsan ba ƙananun kayan ɗaki akai ma Farhar ba wanda in nace zan bayyana to ni kaina wasu abubuwan bansan ya zan faɗe su ba gida dai yayi kyau! yayi kyau!! abun saidai ace Ma sha Allah Kamalu anyi auren gata abun na Allah ne, ƙarshe dai Farha ta zama matar Kamalu ɗan fillo duk wanda yaga hotonunsu da sukai na pre wedding sai ya sake kallo wasu mutanen ma har ƙaryata cewa Kamalun ɗan talakawa ne suke domin ba kama ba alama, sai fatan Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba Amin, bayan bikin Hajiya Maryam ta basu kyautar motoci masu kyau Kamalun ya fara yin aiki a Kamfanin Haisam ita kuma Farhar Mom ɗinta ta samo mata aiki a Federal Inland Revenue.

A cikin shekarar lokacin da zuwa aikin Hajji yayi Kawu Mani ya biya ma Gwaggo bayan duk Matan shi ya biya masu sunje aikuwa sosae su Fatuu sukai Farinciki itama Gwaggon tayi farincikishi sai hamdala take, bayan gama murnar biya ma Gwaggon Haisam da Nameer sukai ma su wata irin bazata Haisam ya biya ma Baffansu shi kuma Nameer ya biya ma Yadikko wayyo daɗi! farincikin yayi yawa saida aka dangana da yan koke koke, bayan tafiyarsu ne ciwo ya tasar ma Arɗo sosae har saida su Fatuu da Haisam da Nameer suka je dubashi kafin su baro saida su Haisam ɗin suka kai shi Yola asibiti aka kwantar dashi ya miƙa kulawar shi a hannun Khalid, bayan kwana biyar aka sallame shi ba laifi ya ɗan samu sauƙi suka koma gida, gaba ɗaya hankalin Baffansu Fatuu a tashe yake da jin zancen ciwon sosae yake ma mahaifin nashi Addu'a acan Makka kan Allah ya bashi lafiya, Alhamdulillah Mahajjata sun dawo gida lafiya su Gwaggo an zama Hajiya ma sha Allah, kwana ukku da dawowar su Baffa Allah yay ma Arɗo cikawa, akace mahaifi mahaifi ne duk da dama arɗon ya tsufa sosae Baffansu Fatuu yaji mutuwar tashi harda kukan shi don yasan mahaifin nashi ba ƙaramin son shi yake ba ko kafin ya rasu saida ya bar wasiyyar cewa shi zai gaji mulkin shi na arɗo kuma ya roƙe shi kan ya haɗa kan iyalin kada ya bari a samu 6araka, lokacin da Fatuu taji labarin rasuwar sosae ta damu harda kukanta sa6anin lokacin da tana yarinya bata da burin daya wuce arɗon ya rasu duk da harda ƙuruciya, washe gari suka tafi gaisuwa suna can Mom da Aunty suka je dasu Fanan da Jidderh har Aunty Laila ma tazo Lokacin Fauzy basu ƙasar shiyasa bata zo ba amman Hajiya Zainab tazo, sosae suka yi ma su Fatun kara har mai girma shugaban ƙasa ya turo wakilci an zo anyi masu gaisuwa, duk a ranar dasu Mom suka zo suka koma amman su Fatuu sai da akayi sadakar uku washe gari suka dawo.

Ƙarshe dai kuɗin da Fatuu ke tarawa canza ra'ayi tayi tunda an kai Baffan nata makka ta yanke buɗe Foundation da zata fara tallafa ma talakawa a Katsina, koda Fanan taji niyyarta nan tace itama tana so su buɗe tare Haisam daya ji ya basu goyon baya harda gudunmawa, haka su Mom harda Hajiya Maryam da President duk suma sun basu gudunmawa, daga baya aka buɗe Foundation ɗin mai suna HAIFAT FOUNDATION, bayan buɗe shi a hannun Gwaggo suka damƙa kula da shi su kawu Amadu da Tk da matansu su Haulat da Husnah suka zama masu taimaka mata wurin gudanar da ayyukanshi harda Aunty Mareeya da Feenah duk sun shiga cikin masu gudanar da ayyukan shi sai fatan Allah ya sanya albarka,

Bayan komawar President Ali kan mulki da shekara ɗaya da wasu watanni ne Hajiya ta kwanta rashin lafiya, farko daga zazza6i ranar wata lahadi ta tashi da shi bayan tasha magani ta ji ta samu sauƙi, da daddare bayan ta kwanta ciwo ya dawo mata zuwa wayewar gari jikinta yayi zafi sosae lokacin da Tk ya dawo daga Masallaci ya je gaisheta kamar yadda yake yi kullum da ƙyar ta amsa mashi sallama, bayan ya shiga a kwance ya isketa saman carpet tana sanye da Hijab da ƙyar tayi ƙarfin hali tayi Salla, jin yadda ta amsa mashi gaisuwar tana nishi dama gashi ya ganta a kwance ƙasa yasa shi tambayarta kamar bata lafiya tace mashi tun jiya take jin zazza6i sama sama tasha magani to da daddare ya idasa rufeta yanzu ma da ƙyar tayi salla yana jin haka da alamun tashin hankali yace bari ya fiddo Mota su tafi asibiti, batare daya jira jin mi zata ce ba ya miƙe da sauri ya nufi ƙopar fita, bayan ya fito saida ya shiga yayi ma Husnah magana kan taje ta taimaka ma Hajiyar ta shirya sai su tafi asibitin tare, itama hankalinta ya ɗan tashi jin Hajiya ba lafiya don da wuya kaji ciwo ya kwantar da ita kaji dai tana cewa bata jin daɗi, bayan zuwan su Asibitin wanda suke zuwa ba 6ata lokaci aka dubata tare da yi mata aune aune bayan an turo result likita ya yi masu bayanin zazza6in malaria da typhoid ne ke damunta har saida Hajiya ta ɗan yi mamakin jin harda typhoid, da likitan yace ko a bata gado don a dubata sosae ta kuma huta tace a'a adai yi mata abunda ya dace yanzu ta koma gida sai taci gaban da shan magani, bayan anyi mata allura an bata maguguna suka tafi, sai bayan da suka dawo Saude tasan da rashin lafiyar nata nan fa suka shiga bata kulawa kowa ya damu Hajiya ba lafiya Tk yace ko ya kira Haisam ya sanar mashi Hajiyar tace a'a kada a tada masu hankali zata samu sauƙi in sha Allah, Amadu ne ya kira Tk kan ya fito su wuce wurin aiki yaga lokaci na niyyar ƙurewa ya sanar mashi da Hajiya ce ba lafiya, Gwaggo na jin Hajiya ba lafiya suka taho harda Haulat da Amadun, gaba ɗaya duk kowa ya shiga damuwa gashi bata cin abinci sai ɗan abu mai ruwa shima daga baya aman abunda tasha ta fara yi ganin haka yasa tk yace ko su koma asibitin tace mashi a'a dama haka zazza6i yake da naci ai zata samu sauki, wasa wasa saiga ciwo nata gaba maimakon a samu sauƙi cikin kwana biyu sai gashi ya kai komai sai su Saude sun yi mata lokacin da Gwaggo tazo taga halin da take ciki ta tambayi Tk yan Abuja sun san bata lafiyar cikin damuwa yace Hajiyar ta hana a sanar masu Gwaggon tace ai ba biye mata za'ai ba, nan take ta buga ma Haisam waya ta sanar dashi da alamun tashin hankali ya tambayi abunda ke damunta ganin ko jiya sunyi waya da ita amman bai gane bata lafiya ba tayi mashi bayani, ana gama sallar Magrib sai ga Haisam ɗin ya iso Tk ne yaje ya ɗaukko shi tun suna kan hanyar zuwa gidan Dad ɗin shi da Hajiya Maryam suka kira suna tambayar ya isa ya jikin Hajiyar yace masu yana hanyar zuwa gidan, lokacin da yaga yanayin jikin Hajiyar bayan ya iso hankalinshi ya ƙara tashi don duk ta faɗa da gani tana jin jiki Haisam ɗin yace ma Tk tun yashe ne bata lafiya cike da damuwa yace kwananta biyu nan ya sanar mashi yadda sukai da likita harda kwantar da itan da akace za'a yi taƙi, bayan Dad ɗinshi ya kirashi ya sanar mashi gaskiya tana ɗan jin jiki Hajiya Maryam harda Vedio call suka yi taga Hajiyar nan fa hankalinta ya ƙara tashi tace ma Haisam gobe da safe zata zo ta ɗauketa, a daren ranar mutanen da suka ji zancen ciwon duk da zullumi suka kwana, washe gari wurin ƙarfe bakwai Hajiya Maryam ta iso nan ta hau su Tk da faɗan ya tana rashin lafiya zasu ƙi kira su sanar tunda ta fara ciwon, bawan Allah harda yar ƙwallan shi yace mata Hajiyar ce ta hana don kada a tada masu hankali aikuwa ta ƙara balbale shi da faɗa harda cewa ko don ba Mahaifiyarshi bace, wannan kalma ta saka shi fashewa da kuka, cikin halin ciwo Hajiya tace mata don me zata faɗi mashi haka bata ji yace ita ta hana ba ko so take yay mata rashin biyayya yaƙi jin Maganarta ganin ran Hajiyar ya 6aci ga kuma halin da take ciki yasa ta ba Tk ɗin haƙuri kan Maganar da tayi, wuraren ƙarfe sha ɗaya suka tafi da Hajiyar Abuja aka bar su Tk da kewa da damuwa sai Addu'ar Allah ya tashi kafaɗun Hajiyar suke, su Gwaggo ma duk sun damu haka yan'unguwa da yawanci duk basu san da Hajiyar bata lafiya ba sai yau da aka tafi da ita duk an damu yara da manya anata mata Addu'o'i.

Bayan zuwa da Hajiya Abuja a babban private hospital ɗin likitansu na Germany wanda yana ɗaya daga cikin likitocin da Shugaban ƙasa ya maido nan wanda yana aiki a Asibitin Gwamnati sannan kuma ya buɗe private hospital ya zuba ƙwararrun ma'aikata wanda wasu abokan aikinshi ne a can, bayan anyi mata aune aune aka tabbatar da abunda akace yana damunta a Katsina suke damunta kuma ma da sauƙi sosae nan aka tabbatar da jikinta yana buƙatar hutu sosae wataƙil bata hutawa sosae ko tana yawan yin zurga zurga, ran Hajiya Maryam ne ya 6aci tace ita dama ba son zamanta take a Katsina ba kawai don ta nuna hakan take so tunda basu a kusa da ita dama ai abunda taga dama zatai tayi ba mai hanata ko aikin NGO da take da ƙyar aka samu ta daina, ita dai Hajiya jin abunda likitan yace kawai tayi don tasan ita ba wata zurga zurgar da take yi, a ɗaki na musamman aka kwantar da ita sosae ake bata kulawa hatta zuwa dubata an ware lokacin da za'a rinƙa zuwa don kada a dameta, bayan sati ɗaya sai gashi jikin nata ya fara yin kyau lokacin har massaging jikin ake mata ana kuma bata lafiyayyun abinci da zasu ƙara mata ƙarfi da kuzari, bayan tayi satin su Tk da Gwaggo suka zo dubata harda Amadu gaba ɗaya sunji daɗi ganin yadda ta fara samun sauƙi ba kamar Tk kullum da zullumin ciwon nata yake kwana duk ya damu kwanansu biyu suka koma, bayan sati biyu aka sallameta suka wuce Villa da ita, zo kaga murna Hajiya ta warke kowa sai farinciki yake duk sun haɗu harda su Fatuu, a can Katsina ma sai murnar jin Hajiya ta samu lafiya ake, anan Villa aka cigaba da kula da ita tana shan magunguna, bayan tayi sati biyu ya kama watan ta guda a Abuja lokacin ta warke sosae har ɗan ƙara jiki tayi da haske tace ma President tana son komawa Katsina nan fa ya shiga roƙonta kan ta haƙura da zaman Katsina taci gaba da zama nan amman ta nuna mashi ita tafi son zaman can, koda Hajiya Maryam taji itama zuwa tayi suka haɗu da President ɗin suna roƙonta kan ta zauna nan Hajiya Maryam harda yin ƙwalla tana faɗin su basu son su rasata ne yanzu da basu yi gaggawar ɗaukkota nan ba da Allah kaɗai yasan mi zai faru Hajiyar na murmushi tace abunda Allah ya ƙadarro shi zai faru da lokacinta yayi sai ta tafi kuma a tunaninta su suka sa ta warke ne, Hajiya Maryam ɗin tace eh duk da hakan dai gara ta zauna anan tafi samun kulawa, ƙarshe dai saida suka yi nasarar tursasa mata ta dawo nan amman tace masu dole zata koma tayo sallama da mutane Hajiya Maryam harda cewa in don wannan ne ai sai suje rana ɗaya tayo su dawo tace a'a tana buƙatar lokaci ba wai daga taje zata dawo ba don haka aƙalla zata yi wata guda Hajiya Maryam tasa rigimar gaskiya yayi yawa da ƙyar aka tsaya kan sati biyu shima saida Hajiyar ta kafe kafin ta amince, kafin su tafi ne tace tana son bar masu wasiyya ko ba yanzu ba in ajali ya risketa tana son kada su tada Tk daga gidanta koda zasu yi amfani da gidan to a ware mashi isasshshen wurin da zai zauna ta bashi halak malak sannan su Saude ma a barsu suci gaba da zama har sai in su suka buƙaci tashi ko kuma su in suna buƙatar su tashi to sai su siya ma Sauden gida, gaba ɗaya suka haɗa baki wurin cewa in sha Allahu zasu yi kamar yadda tace Hajiya Maryam tace amman ta daina faɗin wasiyyar nan tana tada masu hankali, Hajiyar tayi yar dariya tace to miye abun tashin hankali abunda ya zama dole da lokacinta yayi kuma su ai yan gata ne tunda sun rayu da ita tsawon lokaci wasu da yawa ma basu san Mahaifiyarsu ba, Hajiya Maryam ɗin tace duk da hakan dai suna roƙon Allah ya yasa su cigaba da rayuwa da ita tsawon lokaci tana murmushi ta amsa da Amin, bayan kwana biyu ta dawo Katsina harda First Lady da Aunty suka rakota, zo kaga murna Hajiyar Sanata ta dawo kar ma su Tk gaba ɗaya bakunansu sun ƙi rufuwa dama Tk kusan yafi kowa shiga damuwar ciwon nata zuciyarshi tay ta raya mashi kodai mutuwa Hajiyar zata yi shi bama damuwar shi makomarshi ba a'a yadda zai rayu babu ita shine yafi tada mashi hankali don ba ƙaramin shaƙuwa yayi da ita ba ko Mahaifiyar shi bai jinta a ranshi kamar yadda yake jin Hajiya, Mutane sai so suke su shigo gidan suga Hajiya amman ba dama don ƙopar gidan dankam take da Security wasu kuma sun zagaye gidan wanda babu wasa a tattare dasu gasu da manyan makamai, su Gwaggo dai sun shiga har sun gaisa da Mom da Aunty sun masu ya maijiki, haka manyan mutane mata da maza da yan siyasa sun zo duk an barsu sun shiga sun gaisa da su Mom tare da yi masu ya mai jiki har Governor da First Lady ɗin Katsina sun zo unguwa fa ta ɗinke ba abunda kake gani sai motoci masu numfashi da jiniya, Washe gari su Mom suka tafi bayan tafiyarsu ne Tk ya faɗi ma Hajiyar mutane yan unguwa nata son su shigo su gaishe ta an hana su, tana jin hakan ta bada iznin duk wanda yazo a barshi ya shigo nan fa yan unguwa sukai ta shigowa dubiya manya da yara da dattawa Hajiya tayi amfani da wannan damar duk wanda yazo gaidata sai tayi mashi bankwana ta nemi yafiya, gaba ɗaya gwuiwar mutane sai tayi sanyi kuma jin Hajiyar zata bar Katsina harda masu yin ƙwalla tun ma ranar tafiyar bata yi ba, kowa ya nuna rashin jin daɗin tafiyar da zata yi tana ta ce masu kada su damu ai ba shikenan an rabu ba indai da sauran rayuwa za'a cigaba da zumunci kuma ga Tukur nan zai cigaba da zama a gidan don haka ba abunda zai fasu tsakaninsu, tunda su Tk da Saude da Husnah suka ji zancen komawar Hajiyar Abuja gaba ɗaya suka shiga damuwa kowa jikin shi yay sanyi, bayan dawowarta da sati ɗaya ne ranar Friday da daddare ta kira Tukur da Saude a cikin Bedroom ɗinta, a kan carpet suka zauna ita kuma tana zaune a bakin gado idanunta sanye a cikin gilashi, sun ɗan ɗauki lokaci shiru tana ta kallonsu su kuma duk sun sunnar da kai yayin da ƙirjinsu ke bugawa tamkar ana masu luguden ta6are can Hajiyar ta nisa kafin a nutse ta fara magana,

"Na buƙaci ganin ku ne don yin maganar da nasan bazaku ta6a jin daɗin ta ba kamar yadda nima ba don daɗin yasa zanyi maku ita ba, da farko dai ina mai matuƙar godiya a gare ku godiya mara iyaka, gaba ɗayan mu bamu da wata dangantaka ta jini face ta kasancewar mu musulmai amman Allah ya haɗamu muka zauna tare tsawon lokaci har muka zama tamkar dangin juna, ina son ku sani, ku mutane ne masu matuƙar muhimmanci a gare ni wanda wasu ma da yawa da nike da alaƙa ta jini dasu basu da irin muhimmancin a wurina, Tukur, kai tamkar ɗan dana haifa kake a wurina duk da kafi kama da jikana amman kallon ɗana na jini nake maka, haka kema Saudatu ina matuƙar jin ki a rai na ba kuma don hidimar da kike man ba sai don ƙaunar ki a gare ni wadda nasan ita tasa kika zauna tsawon lokaci kina hidimta man ba tare da gajiyawa ba kuma daidai da rana ɗaya bazan iya cewa ga lokacin da kika sa6a man ta hanyar yi man rashin biyayya ko makamancin hakan......to, gaba ɗaya dai ba abunda zance sai dai ince maku Nagode, Nagode Allah ubangiji ya saka maku da mafificin Alkhairinsa ya ji6anci al'amuranku, ina kuma roƙon shi da yadda ya haɗa mu a gidan duniyar nan ya haɗa mu a gidan aljanna muci gaba da yin rayuwa tare, nasan bazaku rasa jin zancen komawata Abuja ba duk da bamuyi maganar da ku ba kafin yanzu, nasan dole kuji ba daɗi amman ina mai baku haƙuri dama haka rayuwa ta gada in har aka haɗu to tabbas wata rana sai an rabu koda kuwa ba mutuwa ba, don haka inason ku kwantar da hankalinku dan na tafi ba yana nufin an rabu ba kenan indai da rayuwa dole aci gaba da zumunci, kai Tukur zaka cigaba da zama a gidan nan koda kuwa bayan bani a duniya kana da kaso a cikin sa so nike Hajiyar Sanata taci gaba da wanzuwa ta dalilin ka, haka kema Saudatu zaku cigaba da zama keda mijinki har zuwa lokacin da kuke so ke bazance ki zauna dundundun ba saboda yanayin aikin mijinki a koda yaushe za'a iya canza mashi wuri dama ni na roƙa aka bar man shi tsawon lokaci muna tare ba'a ɗauke shi ba saboda ina jin daɗin zaman shi sai kuma yazo ya aure ki aka ƙara zama ɗaya...., akwae gida da nike son siya maki koda bani ba na faɗa za'a siya maki in kun buƙaci barin nan, A ƙarshe ina mai ƙara godiya a gareku sannan ina roƙon yafiyarku saboda ance zo mu zauna zo mu sa6a indai nayi maku ba daidai ba da sani na ko akasin hakan ina mai roƙon ku da ku yafe man ni dai na yafe ma kowa sannan ina mai roƙon ku da kuci gaba da kyautata ma abokan zaman ku",

Saida ta gama Magana ta fahimci gaba ɗaya kuka suke jin sheshshekarsu tay shiru tana kallon su dama itama ƙarfin hali kawai take, bayan wani lokaci tace "To duk kun tasani a gaba kunata kuka ko nima so kuke ɗan ƙarfin halin da nike in karaya in sa kukan ne?" a tare suka haɗa baki cikin muryar kuka suka ce "a'a......" tace to su daina suyi haƙuri don Allah tun farko tasan dama dole suji ba daɗi to amman sai ayi haƙuri wataƙil dama Allah ya ƙaddaro zamanta Abujan ne tunda tuntuni suke son ta koma taƙi hardai yanzu sukai galabar sata ta koma suyi haƙuri ai ba'a rabu ba kenan kamata yay ma su gode ma Allah daya sa ta miƙe, nasiha sosae tayi masu suna ta sharar ƙwalla daga ƙarshe tace suje, har zasu miƙe tace to su basu yafe matan ba wannan magana ba ƙaramin ta6a masu zuciya tayi ba duk suka ce mata su wllh ba abunda ta ta6a yi masu ba daidai ba tace duk da haka dai su yafe mata, a tare suka haɗa baki suka ce sun yafe mata tare da yi mata Addu'o'i, bin su tayi da ido lokacin da suka nufi ƙopa, bayan fitar su ta maido idonta tana kallon gabanta can ta sa hannu ta ɗaga gilashin idanunta ta goge ƙwallan da suka gangaro mata...........

104

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

.........Suna fitowa Tk ya wuce ɗakin su Saude kuma ta nufi baya inda ɗakinta yake, a bakin gado ya zauna yaci gaba da yin kukan mai cin rai yana haka Husnah ta shigo ciki ma gareta har ya girma, zama tayi a kusa dashi fuskarta ɗauke da damuwa ta shiga bashi haƙuri kai kawai yake ɗaga mata, da yake tasan wurin Hajiya suka je cike da damuwa ta tambayeshi tafiyar dai zata yi da gaske ya ɗaga mata kai alamar eh ta ɗan girgiza kai itama duk wani iri take ji can ta kai hannu ta fara goge mashi ƙwallan tana bashi haƙuri, Saude ma tana komawa ɗakinta ta faɗa gado ta saka kuka mai sauti gwanin ban tausayi, ta ɗan ɗauki lokaci kafin Officer ya shigo ya isketa a haka, da alamun tashin hankali ya nufi bakin gadon ya zauna ya kai hannu yana ta6ata tare da kiran sunanta yana tambayarta lafiya miya faru, cikin kuka tace mashi da gaske Hajiya tafiya zata yi, cikin sanyin jiki yace mata eh yasani nan da sati guda ya shiga bata haƙuri yana nuna mata ai ba an rabu ba kenan za'a cigaba da zumunci yanzu ma daga wurinta yake tace ma zasu iya cigaba da zama a gidan, haƙuri yaci gaba da bata can ta ɗago idanunta sunyi jajir ta saukko daga saman gadon a tunanin shi wani wuri zata ko toilet kawai sai gani yay ta duƙa a gabanshi cikin kuka a marairaice tace mashi don Allah tana neman alfarma a wurin shi tana rokon ya dubi girman Allah yayi mata, gaban shi ne ya fara faɗuwa yace mata in sha Allah in bata fi ƙarfin shi ba zai yi mata, a marairaice tace mashi tunda dama a nan gidan suka haɗu har sukai aure kuma Allah bai sa sun samu rabon haihuwa ba don Allah tana roƙon shi ya sawaƙe mata Allah ne shaidarta tana jin Hajiya har cikin ranta bata jin zata iya cigaba da zama a gidan nan ba tare da ita ba, shiru yay yana kallonta duk da yaji ba daɗi data yi Maganar amman ta bashi tausayi yace mata yanzu in ya sawaƙe matan garinsu zata koma kenan tace a'a zata roƙi Hajiyar ne ta tafi da ita, shiru yay yana kallonta ta langa6ar da kai tana mashi magiya can yay yar ajiyar zuciya yace mata shikenan ta bari sai da safe zasu yi Maganar tunda yanzu dare yayi ya kama hannunta ya miƙar da ita yace suje ta wanke fuskarta. A wannan daren baccin su gaba ɗaya harda Tk ragagge ne, Washe gari Officer na dawowa daga sallar Asuba part ɗin Hajiya ya wuce, bayan ya ƙwankwasa ƙopar daga ciki ya jiyo muryarta tana bashi izinin ya shigo, zaune take kan darduma hannunta ruƙe da cazbaha, da hannu tayi mashi alamar ya shigo ya nufi inda take ya duƙa a kan carpet, bayan ta shafa Addu'a ta kalleshi da ɗan murmushi da sauri ya gaishe da ita ta amsa tayi mashi ya suka tashi ya amsa da Alhamdulillah daga haka yay shiru idon shi akan carpet, daga yanayin shi ta fahimci da wani abu tana ɗan murmushi tace mashi tana fatan dai lafiya ko da wani abu, dagowa yay a nutse yace mata dama Saudatu ce jiya da daddare ta roƙeshi kan yay mata wata alfarma to yace ta bari sai zuwa da safe shine yaga ya dace ya fara tuntu6arta gudun yay mata ba daidai ba, kai Hajiya ta jinjina ta tambayi wace alfarma take son ya yi mata ne nan ya faɗi mata duk yadda sukai da Sauden,

"Humm, Saudatu Kenan, to yanzu kai ka amince zaka sawaƙe matan ne?" Hajiya ta faɗa tana ɗan murmushi idonta akan shi, ɗan shiru yay farko kafin yace tunda ta nuna hakan take so zai mata Hajiyar tace bai son auren ne ko kuwa, da sauri da alamun damuwa yace wllh yana son zamanshi da ita Allah ya sani kawai dai ya fahimci in bai yi mata yadda take so ba ba lalle zaman nasu yaci gaba da yin daɗi ba don ta nuna bazata iya cigaba da zama ba tare da ita ba, yar ajiyar zuciya Hajiya ta sauke ta juya ta kai hannu ta ɗaukko wayarta ta shiga kiran layin Saude bayan ta ɗaga tace mata tazo dakinta tana son ganinta, ba'a ɗau lokaci ba Sauden ta shigo cikin ɗakin da sallama tana sanye da doguwar Hijabi duk suka amsa mata ta nufo ciki, gefen Officer Hajiya ta nuna mata alamar ta zauna, bayan ta zauna ta gaishe da Hajiyar tare da yi mata an tashi lafiya da tambayar ƙarfin jikinta duk ta amsa mata daga haka Sauden ta sunkuyar da kanta idon Hajiya a kanta tana ɗan murmushi, a nutse cikin dattako ta fara magana tace taji yadda sukai da maigidanta saidai sam bata jin daɗin jin hakan ya fito daga bakinta ba a matsayinta na wadda take gani mai hankali taya zata tunkari mijinta da zancen ya saketa kenan ta za6i bauta a ƙarƙashin wani fiye da ubangijinta, da sauri ta girgiza mata kai alamar a'a,

"Aure shine mutuncin kowace mace Saudatu, nasan saboda kauna da sabo yasa kika za6i hakan saidai ni a wurina zaman ki a ɗakin mijinki shine abun alfaharina ba kamar in na tuna a gidana kuka haɗu har akai auren, kiyi haƙuri don na tafi ba yana nufin shikenan an rabu ba in sha Allahu za'a cigaba da yin zumunci in dai da rayuwar" ɗagowa Sauden tayi idanunta sharkaf da ƙwalla ta ɗaga mata kai kafin cikin disashshiyar murya tace mata to zata koma Daura,

"To auren fa Saudatu, taya zaki koma can bacin ga mijin ki anan?", shiru ta ɗan yi idonta a ƙasa kafin tace "Hajiya don Allah ki bari in koma Allah ne shaidata bazan iya cigaba da zama ba a gidan nan in baki nan" shiru Hajiya tayi tana ɗan murmushi idonta a kan ta, cikin sigar rarrashi tace mata ta dai yi haƙuri ta zauna saboda aurenta Sauden tayi shiru tana matsar kwalla can Officer yace in hakan take so lafiya lou shi ya amince ta koma Daura din Hajiya tace to ya za'ai hakan yace ba komai indai hankalinta zai fi kwanciya sai ya rinƙa zuwa, ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tace shikenan bari ta gani in zata iya neman alfarma sai a maida shi Daura da aiki dama tuntuni abunda yasa ya daɗe anan gidan ita ta roƙi alfarmar abar mata shi yanzu abunda za'ayi tunda dama zata siya ma Sauden gida in ta amince sai a siya mata acan Daurar sai su zauna a cikin shi, da sauri Sauden ta ɗaga kai alamar ta amince Hajiyar tayi murmushi tace to wurin ina take son a siya mata gidan tasa a bincika mata Sauden ta ɗago ta faɗi mata tace shikenan, kallon Officer tay tace ya jirata Maganar canjin wurin aiki ya yi kuma Addu'a Allah yasa a maida shi can yace Amin ta ƙara ce mashi zata turo mashi saƙon kuɗi sai ya juya ya haɗa da aikin nashi Allah ya ƙara rufa asiri ya amsa da Amin tare da yi mata godiya da addu'o'i ta amsa tare da cewa shikenan zasu iya tafiya.

Tun bayan da Hajiya tayi magana dasu Tk game da tafiyarta gaba ɗaya duk sun shiga damuwa gidan ya koma shiru sam basu da wata walwala a haka har ranar tafiyar tata tazo, ranar ta kama Juma'a da safe jirgin Hajiya Maryam ya iso tazo tafiya da ita, bayan zuwan nata nan da nan gidan Hajiyar ya cika da manyan mutane musamman yan siyasa sun zo yi ma Minister sannu da zuwa da kuma yin sallama da Hajiya, da lokacin sallar Juma'a yayi gaba ɗaya a Masallacin gidan duk sukai salla, misalin ƙarfe huɗu na yamma ana gama sallar La'asar aka firfito don raka Hajiya Airport tuni an fito da akwatunan kayanta an saka a Mota don iya su kawai zata tafi dasu ba'a dauki komai na gidan ba, a gaban entrance aka jere motocin lokacin da Hajiya ta fito sanye da rantsatstsiyar lifaya tana dogara sandarta ta alfarma Tk na daga can gefe a tsaye idanunshi sunyi ja don tun da safe yake matsar ƙwalla, har su Gwaggo sun zo suma zasuyi rakiya Amadu ne zai kai su a Motar Fatuu, bayan an fara shiga cikin motoci Amadu ya nufi wurin Tk ya dafa kafaɗarshi yana bashi haƙuri yace mashi yazo suje suyi mata rakiya idanunshi cike da ƙwalla ya girgiza mashi kai yace su je kawai, ganin yanayin shi yana cikin matsananciyar damuwa yasa Amadun ƙyale shi ya juya, a tare Convoy ɗin motocin suka tashi gaba da baya motocin security ne idanun Hajiya na akan Tk dake tsaye har suka isa gate suka ta ɗan girgiza kai tare da rufe idonta, lokacin da suka fito kopar gidan cike yake da mutane yan unguwa tun dazu suke son shiga yin bankwana da Hajiya amman Security sun hana, motocin na fitowa suka shiga daga masu hannu suna faɗin sunan Hajiyar Sanata ganin haka yasa Hajiya tasa a dakata, bayan Jeep ɗin da take ciki ta tsaya ta sauke glass aikuwa mutane na ganinta suka nufo ta da sauri nan fa aka shiga tutsetseniyar kama hannun nata ana kiran sunanta harda masu yin kuka daga baya ma sai ta buɗe Motar ta fito aikuwa matan unguwa da yara aka shiga rungumeta ana kuka cike da ƙarfin hali take basu haƙuri tana kwantar masu da hankali tace ai ba an rabu ba kenan in sha Allahu za'a cigaba da zumunci kuma duk abunda take yi baza'a bari ba tunda ga Tk nan, ganin suna 6ata lokaci yasa Hajiya Maryam tayi ma security magana suka sallami mutanen Hajiyar ta koma cikin Mota, duk yadda ta daure saida ta matse ƙwalla motocin suka tafi anata cigaba da ɗaga ma Hajiyar hannu, mutane rahama ko iya haka za'a iya cewa Hajiya ta dace. Hajiya ta tafi ta bar mutane da kewa ba kamar su Tk don tun bayan tafiyarta yake ta zazza6i bawan Allah don ma Allah yasa yana da mata tanata aikin rarrashin shi duk da itama sosae take kewar Hajiya don ba ƙaramin shaƙuwa sukai ba ita kanta ɗiyar su Hauwa'u duk ta damu ko yaushe cikin tambayar yaushe Hajiyarsu zata dawo take sai an kira mata ita ta waya sunyi magana ko Vedio call take kwantar da hankalinta, ta bangaren Saude ma taso tafiya Daura bayan tafiyar Hajiya Officer ya rarrasheta kan tayi haƙuri tunda Hajiya tace zata nema mashi transfer sai su koma can baki ɗaya da haka ya samu ta haƙura, su Gwaggo ma duk sun yi kewar Hajiyar duk da su bama gida daya suke da ita ba amman da sun zauna suna hira sai sun yi maganarta, sai bayan wani lokaci Tk ya warware amman ko yaushe cikin jin kewar Hajiyar shi yake.

Bayan komawar Hajiya Abuja da yan watanni Allah ya sauki Farha ta haiho san6aleliyar ɗiyarta mace kai kace ɗiyar aljanu ce don kyau gaba ɗaya mamanta da babanta ta biyo, a fuska da Kamalu take kama amman farinta na Farha ne sannan ƙwayar idonta ma ta Farha ce gashin kanta kuma baƙi ne wuluk kalar na babanta, cikin sa'a lokacin da akai haihuwar su Fatuu na hutu hakan ba ƙaramin daɗi yay masu ba, kowa ya ga Babyn sai ya furta ma sha Allah ana ta farinciki Hajiya Maryam ma lokacin data ga Babyn sam kasa rufe bakinta tay sai farin ciki take, bayan sun koma gida daga asibiti da daddare Lokacin da Kamal ya shiga wurin maijegon yana ruƙe da babyn yake sanar mata da sunan da yake son sakamata wato sunan Hajiya Maryam Farhar tace mashi ba gara yasa sunan late Mom ɗin shi ba yace mata tunda Fatuu tasa su bari in ta ƙara haihuwa sai su saka sunan Mom ɗin nashi, harda yar harararshi tayi tace ita wannan wahalar da tasha ta gama haihuwa yana murmushi tare da yi mata kallo mai cike da tsantsar ƙauna yace tayi haƙuri pls ta ƙara mashi yana son su haifi yara tare, itama murmushin tayi ta kai idonta kanshi tana mashi kallon love tace indai irin yaran nan zata rinƙa haifa tare dashi to zata ƙara wasu Amman sai ta huta sosae yay murmushin shi mai burgewa tare da jinjina mata kai alamar amincewa da zancenta tana murmushi ta kwantar da kanta a kan shoulder dinshi tana kallon Kyakkyawar Babyn su tana haka taji ya furta "Thank you my lovely wife for loving me for who i am" ɗago kai tayi ta kalle shi ta kashe mashi ido tare da furta "i will always love u Babe" yadda tayi maganar har sai da ɗumin bakin ta ya bugi fuskarshi saboda kusancin da fuskokin nasu suke dashi, shiru sukai suna kallon juna wani lokacin har mamaki Kamal yake a cikin ranshi irin yadda take nuna mashi ƙauna bata ƙi a ce koda yaushe suna manne da juna ba, a iya zaman da sukai matsayin ma'aurata ba ƙaramar zazzafar soyayya ta nuna mashi ba hakan yasa shima yake ƙokari wurin faranta mata a koda yaushe bai ta6a yin wani abu da zai nuna ta takura mashi ba zaman su suke lafiya sam baida matsala da ita kawai dai tana da zafin kishi wannan kuma tun kafin suyi auren ya sani shiyasa yake taka tsantsan da duk abunda yasan zai haifar masu da matsala, lokacin da Hajiya Maryam taji sunanta aka saka ma jaririyar murnarta ninkuwa tayi jin anyi mata takwara, bayan kwana biyar da yin haihuwar aka maida maijegon Villa don acan za'ayi suna, saida Hajiya Maryam tayi ma jaririyar saitin akwatuna ukku masu guda huɗu haɗaɗɗun gaske shaƙe da kayan jarirai na gani na faɗa da sauran kuma abubuwan da suka danganci jarirai ita kanta mai jegon ita tayi mata kayan da zata fita suna harda shi ma Baban jaririyar tayi mashi ɗinkuna na alfarma abun dai gwanin daɗi, ranar suna ta kama Juma'a suna na gani na faɗa akayi a Villa maijego ta samu iyayen kaya ita da Baby, mai girma shugaban ƙasa kyautar ƙaton fili yay ma jaririyar haka dai aka cika su da abubuwan arzuƙi kowa yayi bajinta su Gwaggo da Haulat harda Kawu Amadu da Tk da matarshi duk sun zo suna, zo kaga farincikin ganin juna wurin Hajiya da Tk harda rungume shi tayi, suna yayi suna abun sai son barka bayan gama sunan anan Villa apartment ɗin da Hajiya Maryam take Farha ta zauna sai ta gama wanka zata koma.

A kwana a tashi ba wuya a wurin ubangiji gashi President Ali har yayi shekara biyu da komawa kujerar mulki lokacin yaran Fatuu duk sun girma su Twins nada shekara takwas Esha kuma nada shekara bakwai, tun bayan da Esha ta fara girma gaba ɗaya halayenta sak na Fatuu da tana da ƙuruciya ne don sam bata jin magana ga masifa sannan tana da ƙarfi sosae don abu kaɗan sai ta kai bugu ko su twins bata ƙyalesu ba da ɗan abu ya haɗa su sai ta kama bugun su duk da suna maza bugunsu take har ta saka su kuka kuma duk sun fita tsawo amman tana da jiki bulbul take, kullum cikin rabata faɗa ake da yara a gida da kuma makaranta
gashi saboda ansan ko ita wacece yasa ba'a ta6a kai ƙorafin halinta ba ga iyayenta har sai watarana data fasa ma wata yar ajin su baki daga ta taka mata colour bata gani ba ta karye tana bata haƙuri amman duk da haka saida ta kai mata bugu saitin bakinta aikuwa bakin ya fashe yay ta jini lokacin Class Aunty ɗin su ta yanke yin magana da Dad ɗinta don ai mata faɗa ta rage faɗa da yara da yake suna da lambobin wayoyin iyayensu, bayan ta kira Haisam cike da girmamawa tayi mashi bayanin dalilin kiran nashi harda bashi haƙuri kan hakan da tayi tace taga abun yana yin yawa ne kada wata rana ta illata wani student sosae, Haisam ɗin yace mata ba wani abu ya gode da sanar mashi da tayi, a ranar da daddare bayan ya dawo daga sallar isha ya zauna a main parlor dama duk dare in ya dawo daga salla nan yake zama su Twins da Esha din su kawo mashi Assignment ɗin su ya taya su bayan sun gama sai ya rakasu ɗakunansu su kwanta, su Twins ɗakin su ɗaya sai ita kuma Esha a Bedroom ɗin Fanan take kwana, bai daɗe da zama ba sai gasu sun fito duk suna sanye da ƙananun kaya su Twins Jeans da t-shirt sai Esha tana sanye da blouse da ɗan gajeran skirt duka kalar pink gashinta na fake a tsakiya ya sauka har kusan tsakiyar bayanta dama kusan koda yaushe sai dai ka ganta da gyaran gashi don bata son kitso, kowannensu ya ɗaukko ƙatuwar jakar Makarantarshi, suna ƙarasowa inda Haisam yake zaune Esha ta saki jakarta ƙasa ta washe baki duk gefen kumatunta suka lotsa sosae ta nufi Haisam da yar sassarfa tana faɗin "My Daddy.." dama ita yar gidan Daddy ce sosae suke shiri kowa ma ya sani daddie's pet ma ake ce mata ko rashin ji take da ance in ya dawo sai an faɗi mashi take cewa ta bari kada a faɗi mashi don Allah, haka in ya dawo gidan in suna nan haka zata nufeshi da gudu tana mashi welcome ya ɗagata sama yana faɗin His little Angel tun bata girma ba yake mata haka har kuma yanzu data girman a haka suke tarbar juna, haka in yana zaune ma tana zuwa zata faɗa jikinshi tana mashi dariya shima yayi mata har gyaran gashi yake mata da wanka cikin Weekend da yake yana ƙoƙarin basu lokaci sosae a ƙarshen sati har fita yake dasu outing wani lokacin kuma anan cikin gidan zaije dasu Field suyi wasanni harda Fanan in Fatuu ma tazo Weekend da ita ake yi, Esha ɗin na zuwa zata faɗa jikin Daddy ɗin nata yay saurin dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu fuskarshi a ɗan ɗaure hakan yasa ta ja ta tsaya a gaban shi tana kallon shi da manyan idanunta masu ɗauke da zarazaran gashin ido, da alamun ɗan mamaki take kallonshi don ta gane ya ɗaure mata fuska su Twins ma tsaye sukai suna kallonshi can yace masu su zauna dukansu suka zauna akan carpet dama anan suke zama in za'ayi Assignment ɗin shima Haisam ɗin sai ya saukko ya zauna akan carpet ya fara nuna masu yadda zasuyi koda sun iya ƙa'ida sai tare da Haisam ɗin zasu yi don haka suka saba, yawanci ma duk Assignment ɗin da aka basu suna iya fiddawa dama gasu da ƙoƙarin tsiya sune gaba gaba a cikin ɗalibai masu ƙwazo a Makarantarsu, bayan duk sun zauna harda Esha ɗin zuru sukai suna kallonshi duk sun fahimci ya canza masu fuska, Adam ne cikin shan jinin jiki ya gaishe dashi da turanci Haisam din ya jinjina mashi kai ganin haka yasa Abie ma gaishe dashi ya amsa a hankali da sauri itama Esha tace "Good Evening My Daddy" wani kallo yay mata mai kaman harara ba tare daya amsa ba nan take ta gane da ita yake fushi ta shiga kikkafta idanu tana motsa baki, ba tare daya saukko daga saman kujerar ba still fuskar shi a ɗaure take ya fara magana cikin cool voice ɗinshi da har yanzu bata canza ba idon shi akan Esha yace dama duk faɗan da ake mata kan ta daina rashin ji bata ɗauka, da sauri tace mashi ta bari Allah,

"Kin bari shine kika fasa ma classmate ɗinki baki?" ya faɗa tare da ƙara ɗaure fuska ta ɗan waro ido jin abunda yace don tunda take rashin ji a School ba'a ta6a yi mata maganar ba a gida, cikin ɗan tura baki tare da yamutsa fuska tace ai itace ta karya mata colour ko, aikuwa a ɗan fusace Haisam yace miye colour da don ta karya zata kama bugunta har ta fasa mata baki kuma ai ba shine rashin ji na farko ba da take a School ɗin dama ance ta saba bugun students kan ƙaramin abu kuma wani lokacin ita take fara jan su sannan tana ma malamai rashin kunya, tana jin abunda yace ta fara ta6e baki tana ɗan nishi idanunta suka ciko da ƙwalla cikin muryar kuka ta fara faɗin Allah karya ake mata ita bata rashin ji kuma duk wanda ta buga shi ya fara jan ta kawai dai teachers ɗin nasu sun tsaneta shiyasa za'a yi mata sharri, shiru Haisam yayi yana kallonta kawai don komai take yi ƙuruciyar Fatuu take tuna mashi yasan gaba ɗaya halinta ne na yarinta ta gado shiyasa bai cika damuwa da rashin jin ta ba don yasan zata daina, sai faman rantse rantse take tana faɗin karya malaman ke mata Haisam ɗin dai bai ce mata komai ba idon shi na kanta, yadda take faɗin malaman su ƙarya suke mata sun tsaneta sai ta tuna mashi da can baya lokacin ƙuruciyar Fatuu ta ta6a faɗi mashi magana makamanciyar wannan, ba tare daya saki fuskar shi ba ya katseta ta hanyar faɗin Teachers ɗin nasu take ce ma suna ƙarya idanunta sharkaf da ƙwalla tace to ai ita bata rashin jin da aka faɗi mashi, juyawa yay ya kalli su Twins dake ta bin su da ido sai kace an aje photocopy ɗin Haisam don sak fuskar su irin tashi ce komai da komai, tambayar su yay abunda aka faɗa game da Esha ɗin gaskiya ne Abie yay shiru don shi magana wuya take mashi Adam ne yace eh gaskiya ne bata jin magana taita bugun Students kuma tana ma Teachers rashin kunya har suma da suke Yayyenta ta raina su tana masu rashin kunya kuma har bugunsu take aikuwa yana rufe baki tai kukan kura ta nufe shi, da sauri Adam ɗin yace ma Haisam ya gani ko gashi nan zata bugeshin aikuwa a fusace ya daka mata tsawa ta hanyar kiran sunanta yace in ta sake ta buge shi sai ya 6ata mata rai, wani irin kuka mai sautin gaske ta fashe dashi ta shiga faɗin ita kowa yayi hating nata shiyasa sai ai ta mata sharri, kukanta ne yasa Fanan fitowa tana sanye da wando skin tight da yar top kayan sun bi shape dinta kanta a buɗe brown sumarta ta saketa ta zubo gefe da gefen wuyanta, tana nan yadda take bata canza ba saidai hutu ya ƙara zauna ma jikinta ta ƙara wani irin fayau da ita sannan ta ɗan ƙara jiki kaɗan, da sauri ta nufo cikin parlon tana faɗin "What's Happening Sweetheart....." Esha na jin muryarta ta miƙe daga durƙuson data yi ta nufeta da gudu suna haɗuwa ta faɗa jikinta, ɗago kanta Fanan ɗin tayi ta sake tambayarta mike faruwa waya sakata kuka ne,

"Momy, they made Dad angry with me" Esha ɗin ta faɗa fuskarta jage jage da hawaye ita damuwarta fushin da Haisam yayi da ita, ɗan buɗa ido Fanan tayi tace mata su waye suka sa Dad ɗin yayi fushi da ita cikin kuka tace Teachers ɗin su kuma harda su Twins, kama hannunta tayi suka nufi inda su Haisam suke, a kusa da Haisam ɗin Fanan ta zauna da yake akan kujera mai mazaunin mutum biyu yake ta zaunar da Esha ɗin akan cinyoyinta sai kallon Haisam ɗin take tana sheshsheka shi kuma yaƙi kallon su, hannu Fanan ta kai ta kamo hannunshi tana murmushi ta furta "Babe, What happened?" shiru kaman bazai magana ba sai kuma ba tare daya kalleta ba ya shiga faɗi mata abunda aka kirashi daga School ɗin su aka fadi mashi, zaro ido Fana tayi tana kallon Esha dake yan kifce kifcen idanun rashin gaskiya,

"Sweetheart, Why? Miyasa zaki hakan duk nasihar da nike maki kan ki daina faɗa kina bugun mutane ki natsu ashe baki ji" Fanan ta faɗa da turanci ta ɗan daure fuska cikin kuka Esha tace "Momy ba itane ta karya man colour ba" Fanan ɗin tace mata amman ai tasan ba tana sani tayi mata hakan ba ko, da sauri Adam yace eh zata wuce ne ita kuma Esha tazo sakawa a cikin locker ɗin seat dinta shine color ɗin ya faɗo ƙasa ya gangara ita kuma tazo wucewa shine ta taka mata Esha ɗin ta juya ta wurga mashi harara tare da kumburo baki, nasiha Fanan ta shiga yi mata tana nuna mata ba komai ake fushi ba ta rinƙa haƙuri pls ta hakane zata zama Good Girl,

Cikin yamutsa fuska Esha ɗin tace "Momy, am i not a Good Girl?" da sauri Fanan ɗin ta kai hannu tana shafa kumatunta tace "Oh no, Sweetheart you are a Good Girl, kawai dai in kina haƙuri da abubuwa shine zaki ƙara zama yarinyan kirki ki rinƙa jan Friends ɗin ki a jiki da yan'uwanki kuyi wasa ba tare da kunyi faɗa ba amman yanzu kowa bai jin daɗin yin wasa dake saboda yawan faɗan ki, We are not happy yadda kowa ke maganan baki ji pls ki bari yadda za'a rinƙa cewa Esha Good Girl ce tana da haƙuri da kirki" kai Esha ɗin ta ɗaga mata tace to zata rinƙa yin haƙurin, Fanan ta tambayi ta yi promise ta bari da sauri ta ɗaga mata kai alamar eh tace yauwa haka take so amman in ta ƙara ji ta bugi wani har tayi mashi rauni itama zata 6ata da ita, da sauri Esha ɗin ta girgiza mata kai tace Allah bazata ƙara ba, kallon Haisam Fanan tayi da duk abun nan bai kallesu ba tayi ɗan murmushi kafin ta maido idonta kan Esha ta kai hannu ta matso da kanta ta raɗa mata ta sauka ta duƙa gabanshi ta bashi haƙuri da sauri ta ɗaga mata kai don sosae ta damu da fushin da yayi da ita, saukkowa tayi a ɗarare ta matsa saitin shi tayi kneel down cikin karyayyar murya ta furta "i'm Sorry Daddy, i won't do it again i promise you" shiru bai ce komai ba bai kuma kalleta ba har lokacin fuskar shi a ɗaure take, cikin mutuwar jiki Esha ɗin ta juya ta kalli Fanan tana ta6e baki da kai tayi mata alamun ta ƙara matsawa kusa dashi ta bashi haƙurin, sanin tunda suke dashi bai ta6a bugunsu ba yasa bata ji tsoron matsawa dab dashi ba ta ƙara maimaita haƙurin data bashi sai lokacin ya maido idanun shi kanta ganin haka yasa ta marairaice mashi fuska tana dan motsa baki, ganin baice komai ba yasa ta kalli Fanan ta ƙara yi mata alamun ta kama hannun shi ta bashi haƙurin, hannunta har ɗan rawa yake ta kai ta ɗan kama hannun Haisam guda ganin bai janye ba yasa ta kai ɗayan ta kama duka hannuwan shi tace "pls My Daddy, am Sorry..." tana faɗin haka su Twins suka haɗa baki suka ce please Dad Sorry, hannu Fanan ta kai ta dafa kafaɗarshi tace "Sorry Babe, please forgive her, tayi alƙawarin bazata ƙara ba" Sigh yay cikin muryarshi mai cike da natsuwa idanun shi akan Esha ɗin yace mata kada ta ƙara aikata abu irin haka in ba haka ba zai ɗauki mataki akan ta kuma ba ruwanshi da ita, da sauri ta jinjina mashi kai ya saki fuska tare da ɗago da ita aikuwa da sauri ta faɗa jikin shi tana murmushin farinciki haka su Twins ma murmushin suke harda yi masu gwalo Fanan ma dariyar take ta furta "Esha, Daddy's pet", harda Fanan aka zauna yin Assignment ɗin abun gwanin burgewa, Washe gari Haisam ɗinne ya kai su Makarantar yayi shigar zuwa aiki yana sanye cikin suit, har class ɗinsu yaje yasa aka kira mashi yarinyar data buga ya bata haƙuri itama Esha yasa ta bata haƙurin yace ma Esha daga yanzu su abokai ne su rinƙa yin wasa tare kada ya ƙara jin tayi faɗa da wani tace mashi to, harda kyautar kuɗi masu yawa yaba class Aunty ɗinsu kafin ya tafi, ba laifi a lokacin ta rage rashin jin saidai ance wai mai hali baya barin halin shi koda ya barin wani lokacin bata cikin sauƙi ba.

Cikin sa'a Mino ta kammala karatunta na nursing saida Fatuu taji ba daɗi zata koma Abuja ta barta sauƙinta ma Aysha na nan lokacin itama Aysha ajinta shidda suna gabda yin jarabawar gama Makaranta, bayan result ɗin Mino ya fito wanda yayi kyau sosae ta fara shirin fara yin bautar ƙasa, a wani Weekend da Haisam zaije Zaria ne ya tafi tare da abokinshi Na'eem yayi mashi rakiya daga nan shima zai gaido danginshi don ɗan Zaria ɗinne amman iyayenshi a Abuja suke zaune, bayan sallar Juma'a suka iso Zaria lokacin da suka isa gidan Fatuu bata dawo daga makaranta ba sai Aysha kawai da mai aikinsu, tana sanye cikin riga da skirt na atampa ta zama budurwa sak irin jikin Mino gareta itama doguwa ce kuma bata da jiki gashi tana da kyawun Fuska saidai bata kama dasu Fatuu sosae kamar yadda Mino ke kama da ita, ita ta tarbesu cikin fara'a tana masu sannu da zuwa gaba ɗayansu fuskokinsu a sake suna mata murmushi suka amsa mata, a parlor suka zauna ta kawo masu ruwa da lemu tace bari ta shirya masu table Haisam yace ta bari ba yanzu zasu ci abincin ba sun ci a Kaduna sai ko zuwa ɗan anjima tace to, har zata tafi taji ya tambayi ya karatunta ta tsaya tana murmushi ta amsa mashi da Alhamdulillah suna ta shirin yin jarabawa yay mata fatan sa'a haka ma Na'eem daketa kallonta yana murmushi shima yay mata fatan sa'a ta kalleshi tay mashi godiya kafin ta juya ta tafi, bayan tafiyarta ne Na'eem ya maida idonshi kan Haisam yace mashi amma daga ganin wannan sister ɗin Madam ce ko ya ɗaga mashi kai, tambayar shi yay zuwa tayi Haisam din ya bashi amsa da anan take wurinta tana tayata zama itama tana karatu, jinjina kai Na'eem ya ɗan yi yay shiru can kuma sai yace mashi zasu bashi ita don ya ganta kuma tayi mashi,

"Ita kuma wife en naka fa?" Haisam ya tambaya yana murmushi shima Na'eem din murmushin yake yace zai ƙara ne kamar yadda shima yake da biyu, murmushi kawai Haisam yay bai ce komai ba ganin haka yasa Na'eem yace shi yake saurare Haisam ya tambayi wai is he serious ya ɗaga mashi kai yace Allah tayi mashi da gaske yaji yana sonta da aure, murmushin gefe Haisam yay yace mashi ai ƙarama ce yanzu zata gama Secondary Na'eem din yace ai abun ba'a nan yake ba tunda dai ta balaga lafiya lou za'a iya yi mata aure tunda ta isa, shiru ya ɗan yi kafin ya gyaɗa kai yace in da gaske yake sai ya nemi soyayyar yarinyar Na'eem ɗin ya gyaɗa kai ya tambayi sunanta ya faɗi mashi, anan falo suka zauna suna kallo har akayi sallar La'asar suka tafi Masallaci, bayan dawowarsu Haisam yace suje ciki ya huta yace a'a yana son zai yi magana da Aysha Haisam yace Ok shi zai shiga ciki Na'eem ɗin yace Ok pls ya turo mashi ita, a saman doguwar kujera ya zauna bada daɗewa ba sai ga Ayshar ta fito ta nufo cikin falon, daga gabanshi ta tsaya tana murmushi shima shi yake mata tace gata Yaya Haisam yace yana kiranta yace mata eh tare da nuna mata gefen shi yace tazo ta zauna, saida tayi ɗan jim kafin ta nufi inda ya nuna matan ta zauna daga can ƙarshe ya gyara zaman shi ya dawo yana kallonta,

"Aysha ya School?" ya tambaya da muryarshi ta yan gayu, tanata murmushi tace mashi lafiya lou ya sake tambayar tana dai maida hankali ko tace mashi eh ya tambayi wane department take tace mashi Science,

"Ko kema kina son zama Doctor ne?" kai ta É—aga mashi alamar eh yace ashe da future Doctor yake zaune tayi yar dariya,

"To za'a rinƙa duba ni in an zama Doctor en?" kai ta ɗaga mashi kafin cikin yar muryarta tace in yana so yay yar dariya yace in mutum bashi da lafiya har sai yana so likita zai duba shi murmushi tayi bata ce komai ba, ta lura da irin kallon da yake mata hakan yasa ta fara yin wasa da yatsunta tana yi tana ɗan kallonshi tana murmushi,

"Yanzu in kiga gama karatun zaki aure ne sai kici gaba da karatun ko?" da sauri ta kalleshi tare da É—an waro ido tace "Aure kuma!" kai ya É—aga mata ta É—an girgiza mashi nata tace ba aure zata yi ba Karatun zata cigaba,

"Why bazaki aure ba, ai ana karatu koda aure ba kiga sister en ki ba itama tana da aure harda yara ma kuma tana karatunta",

"To ai ni ko Saurayi ban dashi" ta faÉ—a tana ta murmushi, wani kallo yayi mata yace wasa dai take mashi amman kamar ita ya za'ai tace bata da saurayi, da sauri tace "Allah da gaske nake maka ni ko ance ana sona ban yarda saboda Karatu nike son yi" yadda take mashi magana sosae yake burgeshi gashi daga yanayin Maganarta zaka gane yarintar ta,

"Yanzu ace ki samu wanda yake son ki kuma kema kina son shi bazaki yarda kuyi auren ba sai kici gaba da karatun?" da alamun rashin fahimta tace "wa?" yace mata misali ne ya bata tay É—an shiru alamar tunani yana ta kallonta can tana murmushi tace to in su Adda Fatuu sun amince sai tayi,

"Ai ba su zasu zauna maki ba ko Aysha, in kina so nasan bazasu hana kiyi auren ba" kai ta É—aga mashi alamar eh yace in ta samu wanda take son kenan zata yi auren ta sake É—aga mashi kai kafin ta sunnar da kanta alamar kunya,

"Ok, dama wani ne ya ganki kin yi mashi yaji yana son auren ki da Kin gama School, to har nayi ma Yayan ki Haisam Maganar yace ya nemi amincewar ki shiyasa nace to bari in maki magana" ba shiri ta É—ago tana kallon shi da alamun mamaki har ya gama ta waro idanunta tubarkalla tace mashi "ni kuma!" kai ya É—aga mata ta sake cewa "a ina ya sanni"? Yadda tayi ne ya sashi yin yar dariya kafin yace yaga hoton ta ne tay shiru tana kallon shi,

"Aysha baki ce komai ba game da wanda na faÉ—a maki yana son ki" dan yamutsa fuska tay ta É—an yarfa hannu alamar bata san mi zata ce ba, ganin ya kafeta da ido yasa tace to ai ita bata san shi ba,

"In kin ganshi yayi maki zaki amince?" shiru tayi tana ta kikkafta idanu, ɗage mata gira yay yace ita yake sauraro a sanyaye ta ɗaga mashi kai alamar eh, bin ta yay da wani irin kallo ta ƙara maida kanta tana wasa da yatsunta, tana haka taji muryarshi yace "Aysha ni ne na ganki naji ina son ki kuma auren ki nike son yi in kin gama School amman sai in nayi maki nima" da sauri ta ɗago ta kalleshi idanunta a ware fuskarta ta nuna tsananin mamakin Maganar shi yana murmushi ya ɗan lumshe mata ido, ƙirjinta ne ya fara bugu da sauri da sauri ta maida idonta ƙasa,

"Sunana Na'eem, ni abokin Yayinki Haisam ne, inada mata da yara biyu sannan ina aiki da Central Bank, ban san ko na ta6a ganinki ba kafin yanzu tunda muna yawan kasancewa da Haisam duk wata hidima data danganci Family ɗin su ina zuwa saidai a wurina yau na fara ganinki zuwan mu nan, kuma cikin ikon Allah ina ganinki naji na kamu da son ki abunda bature ke cewa, Love at first sight, nayi ma shi yayan naki magana kan haka shine yace to in nemi soyayyar ki idan Allah yasa kinga nayi maki to zan aure ki da kin gama School sannan zan barki kici gaba da Karatun ki in sha Allahu" shiru bata ce komai ba bata kuma ɗago ba abun ya ɗaure mata kai sosae don bata yi tunanin zai mata wannan Maganar ba, ganin taƙi tace komai yasa shi kiran sunanta ta amsa ba tare data ɗago ba yace tayi shiru bata ce komai ba still taƙi cewa komai ɗin,

"Ayshat" amsa mashi tayi ba tare data ɗago ba yace "Look at me" saida tay ɗan jimm kafin a hankali ta ɗago idanunta suka sauka akan kyakkyawar doguwar fuskarshi mai ɗauke da kwantaccen saje, yanayin fatarshi ba za'a ce mashi fari ba kuma ba baƙi bane yafi kama da a kira shi da wankan tarwaɗa, sosae yanayin hutu ya bayyana a jikin fatar ta shi yana da kyawun fuska wadda take a cike ɗauke da dogon hanci da kuma madaidaicin baki mai dauke da jerarrun fararen haƙora harda yar wushirya, a bangaren yanayin jiki sam ba gajere bane don da kaɗan Haisam ya ɗara shi tsawo sannan kuma ba siriri bane yana da cikar jiki, ganin tanata kallonshi yasa shi ce mata kada taji komai in taji bata son shi ta faɗi mashi bazai ji komai ba kuma ko Yayanta bazai faɗi ma yadda sukai da ita ba, motsa baki ta fara da ƙyar tace mashi shikenan idan Yaya Haisam ya amince to ta yarda, ɗan girgiza mata kai yayi yace mata aure ba abu bane da wani zai amince maka tunda bashine zai zauna maka ba sannan aure ana yin shi in ana son juna don haka ita zata amince mashi in taji tana son shi, shiru tayi tana yi tana maida idonta ƙasa ya ɗan ɗage mata gira yana murmushi, sai faman yan kame kame take don taji itama yayi mata don Na'eem ba irin mazan da suke furta ma mace so taƙi amincewa bane kawai dai abun ne taji yayi mata girma ba kamar da yake wannan ne karo na farko da tayi Magana irin haka da Namiji,

"Amman...ita Matarka to zata amince ka aure ni ne?" da ƙyar ta furta mashi hakan, gyara zama yay kafin yace "Ayshat ba kowace mace bace ke son a ƙara mata abokiyar zama ba saidai inada kyakkyawar fahimta da mata na nasan zata amince koda hakan bai mata dadi ba amman tasan inada ikon ƙara wata matar kuma dama ban ta6a mata alƙawarin zan kasance da ita kaɗai ba don haka nasan bazata bani matsala ba in kin amince zaki aure ni" kai ta ɗaga mashi kafin tace shikenan,

"Kin amince zaki aure ni kenan?" kai ta ƙara ɗaga mashi ya sake cewa "ina fata dai ba saboda wani dalili ko don ni abokin yayanki bane yasa kika amince man, nafi son ki amince man don kema kinji kina sona" kai ta jinjina mashi yana mata wani kallo yace "nayi maki kina so na?" kan dai ta sake ɗaga mashi,

"Ok in dai da gaske kike kema kamata yay ki faɗi man da bakinki kamar yadda na faɗa maki" ɗan murmushi ta shiga yi tana motsa baki ya ɗage mata gira alamar ta bashi amsa, da kyar ta furta "nima ina son...ka" tana yin Maganar da sauri tasa duka hannuwanta masu ɗauke da dogayen yatsu ta rufe fuskarta Na'eem ɗin ya shiga yin yar dariya, da yake wayayye ne sai gashi yasa ta saki dashi sun shiga yin firar soyayya, suna haka Hajiya Fatuu ta shigo cikin falon tana sanye da riga da skirt na lace da suka amshi jikinta tare da gyale mahadinsu, tana nan yadda take bata ƙara ƙiba ba saidai ta ƙara cikowa tay dumdum fatar nan tata har wani sheki take hutu ya zauna mata sosae, ƙafafunta na sanye da wasu takalma masu tsini mai ɗan gwa6i har yanzu halinta nason takalma masu tudu nan, ta bangaren hips dinta kuwa abun saidai ace tubarkalla don suna nan sai ma ƙara cika da sukai duk da gyalen jikinta babba ne amman kana kallonta zaka san tana dasu, hannunta na hagu na rataye da yar babbar jaka da take ɗauke da kayan karatunta sai kuma ɗayan hannunta na hagu ta ruƙo Lab coat dashi, tana ganin Na'eem ta fara yin murmushi hakan ya bayyanar sa fararen haƙoranta kamar auduga masu ɗauke da haƙorin makka daya ƙara ƙawata fuskar tata, cikin falon ta nufa sam bata yi mamakin ganin Na'eem ɗin ba don da sukayi waya da Haisam ya sanar mata tare suka zo, a saman kujera dake gefen wadda suke ta zauna Na'eem daya maido idonshi kanta yana murmushi shima yay mata sannu da dawowa ta amsa tare da gaishe dashi da yi mashi anzo lafiya, bayan ya amsa ya tambayi karatunta tace mashi Alhamdulillah itama ta tambayi matar shi Fadeela da yaransu duk yace mata lafiya lou suke, saida suka gama gaisawa sannan Aysha tayi mata sannu da zuwa ta maida idonta kanta tana murmushi ta amsa ta tambayi ya School tace mata lafiya lou, yar hira sukai da Na'eem kafin ta miƙe tace bari ta ɗan shiga ciki yace Ok. Sai bayan sallar Magrib sun dawo daga masallaci suka zauna cin abinci gaba ɗayan su Na'eem da Aysha sai satar kallon juna suke suna murmushi, bayan sun dawo daga sallar isha gaba daya a falo suka zauna suna kallo, wuraren ƙarfe tara Haisam ya miƙe yace ma Na'eem bacci yake ji ya taso suje ya kai shi ɗakin da zai kwanta yana murmushi yace shi da Aysha basu gama yin kallon ba yace Ok yazo suje ya nuna mashi in ya gama sai yaje ya kwanta ya miƙe, bayan tafiyar su ne Fatuu ma ta miƙe tayi ma Ayshar saida safe dama duk in Haisam yazo a ɗayan bedroom ɗin dake part ɗin Fatuu take kwana tare da mai aikin su Asabe, bada jimawa ba Na'eem ya dawo a saman kujera mai mazaunin mutum ukku ya zauna yace ma Aysha ta dawo nan, a can gefe kamar ɗazu ta zauna ya jingina kanshi da jikin kujerar ya shiga sakar mata kallon love da alama dai shima gwani ne ta bangaren soyayya, hirar soyayyarsu suka shiga yi ba laifi ta saki jiki sun ɗan ɗauki lokaci wurin ƙarfe goma saura yace bari ya barta taje tayi bacci kadda ya gajiyar da amaryarshi tayi dariya suka miƙe a tare.

Washe gari bayan Haisam ya dawo daga sallar Asuba itama Fatun tayi sun koma sun kwanta ta tada kanta a saman jikinshi yake mata zancen son auren Aysha da Na'eem keyi ya faɗi mata yace mashi ya nemi amincewarta to har sunyi magana kuma ta amince, sosae Fatuu ta jinjina abun don ita koda ta gansu tare bata kawo komai a ranta ba saboda tasan Ayshar nada saurin sakin jiki da mutane ba kamar Mino ba, da alamun damuwa tace mashi amman bai ganin hakan zai iya haifar da matsala tsakaninsu da matar shi taga anyi mata ba daidai ba tunda sun san juna suna gaisawa, yana ɗan murmushi yace itama ba sun san juna ba da Fanan kuma ta aureshi, juyawa tay tayi mashi wani kallo tare da ɗan tura mashi baki tace to ai ita bata san da Auren ba ko ya ɗage mata gira yace data sani bazata amince ba kenan tay shiru tana kallon shi yace ta bashi amsa, yamutsa fuska tay ta sigar shagwa6a tace to tunda dai an riga anyi ya wuce miye na maido maganar, yana murmushi yace Ok tunda itama ya aureta kuma sun san juna da Fanan itama Ayshar ba wani abu bane don ta auri Na'eem, shiru Fatuu ta ɗan yi kafin tace ya sani fa Aunty Fanan daban take a cikin mata don da wuya a samu wadda zata iya jarumtar da tayi, shiru yay yana sakin murmushi yayin da zuciyarshi ta shiga dawo mashi da fuskar Fanan. Wuraren ƙarfe goma na safe suka zauna yin breakfast, kowa cikinsu yayi wanka Haisam da Na'eem na sanye da ƙananun kaya wando da riga Fatuu kuma da Aysha suna sanye da dogayen riguna masu taushi suna da gajerun hannuwa kowa ya saka hula a kanshi daga bayan hular yay tudu sosae saboda gashin su, bayan sun zauna a kujerun dining ɗin suka shiga gaishe da juna kafin Fatuu ta shiga yin serving nasu, bayan ta gama a nutse suka fara ci baka jin komai sai ƙarar cokulla sai kuma Ac dake a wurin tana ta aiki, bayan sun gama gaba ɗaya a falo suka zazzauna suna yin hira wadda Haisam da Na'eem sai Fatuu ne ke yi ita dai Aysha tayi shiru tana saurararsu akai akai kuma suke haɗa ido da Na'eem su sakar ma juna murmushi, suna cikin yin firar Na'eem yace ma Fatuu "Madam ko in ce Yayata, ina fatan Yalla6ai ya isar maki da saƙona na naga ƙanwarmu tayi man ina neman iri pls, yace man in nemi amincewarta da yake mu indai ta wannan bangaren ne bamu failing tuni har an amince man ance ana sona" ya kai idon shi kan Aysha yace "Ayshanah hakane ko, kin amince zaki aure ni ai ko?" ai tana jin abunda ya faɗa tay zumbur ta miƙe da gudu ta nufi hanyar bedroom duk suka bita da ido suna yar dariya, bayan barinta wurin ne Fatuu tace mashi sunyi Maganar da Hubby taji daɗi saidai tana gudun hakan ya haifar da matsala tsakaninsu da Fadeela tana iya ganin an yi mata ba daidai ba, yana murmushi yace mata kar ta damu zai faɗi mata shi yaga Aysha yaji yana sonta kuma akai sa'a itama tana son shi ba wanda ya haɗa su in sha Allah ba wata matsala da zata faru tsakaninsu Fatun tace Allah yasa, tambayar ta yay lokacin da zata gama School Fatun ta faɗi mashi yace Ok nan da sati ɗaya in sha Allah zaije Yola ya gaida Parents ɗin su Haisam yay mashi wani kallo kafin slowly yace mashi saurin mi yake ne tunda ta amince mashi yabi komai a hankali da sauri Na'eem ɗin yace ai ba mata irinsu ake bi a hankali ba wurin neman aurensu nan tana gama Secondary zaiga masu son ta suna ta kunno kai ƙarshe asamu wani yayi mashi overtaking shiyasa yake son tana gama School ɗin yayi wuff da ita duk sukai yar dariya, hira suka cigaba da yi bayan wani lokaci Haisam ya tambaye shi yaushe zai je gaida relatives ɗin nashi Na'eem ɗin ya duba agogon hannunshi kafin ya bashi amsa da zuwa ƙarfe sha biyu zai tafi Haisam yace Ok in lokacin ya ƙarasa sai suje ya raka shi,

"No, kai zaman ka kaida kazo Weekend Madam na buƙatar ka a kusa da ita koda yaushe ka ƙyale ni in je ni kaɗai, ko kuma tunda nima ga Amaryata sai ta rakani kawai kaga ma sai inyi amfani da daman in fara introducing nata ga Family na" Na'eem ya faɗa yana murmushi suma duk murmushin sukai basu ce komai ba, ganin lokacin fitar nashi ya ƙarato yasashi ce ma Fatuu pls yana neman alfarmar fita da Aysha tana murmushi tace an mashi yay mata godiya kafin yace to ta taimaka tayi ma Amaryar tashi mai kunya magana ta shirya tace to tana dariya tare da miƙewa shima Na'eem ɗin ya miƙe yace ma Haisam bari ya shirya ya ɗaga mashi kai, a bedroom ta iske Aysha kwance saman gado ta nufeta tana faɗin kwanciya tayi kenan Ayshar ta ɗago tana kallonta, a bakin gadon ta zauna tana kallonta da murmushi tace mata Amaryar Na'eem Ayshar tayi murmushi kawai, shiru Fatun ta ɗan yi kafin tace mata ta tabbatar da yayi mata tana son shi don shi da gaske yake aurenta zaiyi tana gama School, shiru Ayshar tayi tana kifce kifcen idanu Fatuu tace mata ta buɗe baki tayi mata magana, a hankali tace mata eh in dai baida wata matsala Fatun tace gaskiya Na'eem bata tunanin yanada wata matsala a yadda ita ta sanshi mutumin kirki ne kuma tasan da yanada matsala ma tun Farko Haisam bazai bashi damar ya nemi soyayyarta ba kawai inda take tunanin matsala wurin matarshi ne duk da itama tana da kirki to amman wata baka gane rashin kirkinta sai za'a mata kishiya kawai dai suyi addu'a Allah yasa ta fahimta ta kuma kar6i abun kamar yadda Aunty Fanan tayi Ayshar ta amsa da Amin kafin tace "amman fa Adda Fatuu wllh Aunty Fanan ta daban ce" murmushi Fatun tay tace ta sani samun irinta cikin mata da wuya in ma akwae duk da tasan akwai mata da yawa wanda in mijinsu yaje masu da zancen ƙara aure duk da basu so amman suna karbar abun a matsayin ƙaddararsu tunda sun san Allah ne ya halarta masu yin jayayya da hakan kuma wahalar da kai ne ƙarshe mutum ya jefa kan shi a halaka, faɗi ma Ayshar tayi zasu fita da Na'eem ɗin yana son zuwa da ita wurin danginshi ya gabatar masu da ita, tana jin haka ta ɗan zaro ido kafin tace amman da wuri haka, miƙewa Fatuu tay tana yar dariya tace shifa da gaske yake yace ma nan da sati ɗaya zaije Yola gaishe dasu Baffa don haka ta fara shiri don ita amarya ce,

"Amman Adda Fatuu ban yi ƙarama ba da yin aure" Aysha ta faɗa da yar damuwa, Fatuu dake tsaye a gaban wardrobe ɗin bango tana ƙoƙarin za6o mata kaya ta bata amsa da "ba wata ƙarama da kikai Aysha, ke ai gara kema akan Mino, ita fa ko gama Secondary bata yi ba akayi mata aure gashi ko a jiki ma kin ɗan fita kauri lokacin" ta ƙarasa Maganar tana dawowa wurin gadon hannunta ruƙe da riga da skirt na lace kalar blue da ratsin golden brown, ita ta taimaka ma Ayshar ta shirya cikin kayan ta saka mata yan kunnan zinari da zobe sai kuma agogo golden mai kyau, yar light make up tayi mata ta ɗaura mata kallabi sai gashi ta fito tayi wani irin kyau, bayan an gama saka kayan ta yafa gyale mahadinsu haka jaka da takalmanta suma duk kalar kwalliyar lace ɗinne takalman masu dan tudu ne kadan don tana da tsawo don bata cika saka takalma masu tsini ba, lokacin da suka fito falon Na'eem din har ya gama shiryawa ya dawo suna zaune da Haisam, shima shadda ce ya saka brown wadda ta hau da kwalliyar lace ɗin jikin Ayshar sai baza ƙamshi yake, Na'eem na ganin shigarta yana murmushi yace ko daga yanayin shigar su hakan ya tabbatar da sun dace da juna duk akayi yar dariya Aysha ta sunnar da kai, har bakin galleliyar baƙar Motar Haisam da suka zo da ita suka rako su bayan sun shiga sukai masu sai sun dawo, yana driving suna hira irin ta masoya haka suka shiga zaga gidajen yan'uwan su Na'eem wanda duk mawadata ne, duk inda suka je sai ya gabatar da ita matsayin matar shi ta biyu da zai aura nan bada jimawa ba anata yabata tare da fatan alkhairi, lokacin da suka je gidan Kakarshi wadda ta haifi Mom ɗinshi shima haɗaɗɗan gidane mai girma don yana da parts da yan'uwan mahaifiyarshi maza ke zaune da matansu haka itama kakar 6angarenta daban an ƙawata shi ai kace ba sashen tsohuwa ba, lokacin daya gabatar mata da Aysha matsayin wadda zai ƙara mata cike da zolaya irinta Kaka ta yamutsa fuska tace in baya ga rigima irinta namiji mi zai ci da wannan yar ƙaramar bafullatanar bayan yana da mata ƙaƙƙarfa kamar ita, ita dai Aysha murmushi kawai take kanta a ƙasa haka shima Na'eem ɗin yar dariya yake yace ina wani ƙarfi a tare da ita, sosae ta sake ma Aysha tana ta mata tambayoyi game da ita tana bata amsa da yake tasan Haisam sosae ta yaba da al'amarin tayi Addu'ar Allah ya sanya alkhairi, duk sauran parts ɗin gidan saida ya kai ta ko ina an yi mata tarba mai kyau, daga baya bangaren Kakar suka koma sai bayan sallar La'asar ya dawo daga Masallaci yace mata zasu tafi tace ma Aysha tunda a garin take zaune ta rinƙa zuwa gaishe da ita tana kama ƙafa in tana son ta amince ta aurar mata miji in ba haka ba ita dashi saidai kallo, tana murmushi tace mata in sha Allahu zata riƙa zuwa sukai mata sallama cike da tsokana Na'eem yace tunda ita mai ƙarfi ce sai ta taso ta raka su bakin mota ko, wurga mashi harara tayi tace Allah ya kyauta tayi ma kishiyarta rakiya duk sukai dariya, bayan sun baro gidan Shopping ya wuce da ita, koda yace mata ta ɗauki duk abunda take so cikin marairaicewa tace mashi ai ita tana da komai yana mata wani kallo yace duk da haka ta ƙara so yake daga yau ta fara amfani da kayan mijinta, ba yadda ta iya haka ta fara ɗaukar yan abubuwa tana sakawa a cart da ya ɗaukko mata, ganin bata ɗaukar kayan sosae yasa shi fara za6ar mata da kanshi yana yi yana tambayar wanda take amfani dasu, bayan sun gama da wurin kayan shafa wurin dogayen riguna suka nufa tana ta roƙon ya barsu tana da su da yawa amman duk da haka saida ya daukar mata guda biyar da takalma guda ukku bayan sun gama da nan bangaren undies suka nufa duk yadda take jin kunya saida ya sakata ta ɗauka, abunda bata sani ba yana amfani da hakan ne wurin sanin size ɗinta saboda in zai yi mata lefe, saida ya cika Shopping cart ɗin taff da kaya sannan suka nufi wurin biya aka saka masu kayan a ledoji bayan an saka a Mota suka tafi.

Kamar yadda Na'eem yace wani ƙarshen satin na zagayowa suka shirya zuwa Yola da Haisam, ranar asabar da safe suka bi jirgi zuwa Yola bayan sun isa aka tura Mota ta ɗauke su zuwa garin su Fatuu, bayan sun isa sun samu kyakkyawar tarba daga mutan gidan aka sauke su a part ɗin su Yadikko nan aka shiga zuwa gaishe da su kan kace mi an jere masu kwanonin abinci iri iri koda Yadikko tayi masu Maganar cin abinci cewa sukai a ƙoshe suke Baffa dake zaune yana murmushi yace duk da haka yakamata su ci tunda tafiya suka yo, ba wani mai yawa suka ci ba saidai sun sha fura ba laifi, bayan sun gama ne Haisam ya gabatar masu da Na'eem matsayin shine mai son auren Aysha in ta gama School, dama an riga an sanar masu game da zuwansu, sosae suka nuna farinciki da Addu'ar Allah ya sanya alkhairi bayan sun amsa Haisam ya sake cewa yana son a faɗi mashi lokacin da zasu turo a saka rana Baffa na murmushi cikin Maganar shi mai tattare da natsuwa yace ai tunda ga shi Haisam ɗin shima matsayin Mahaifi yake wurin Aysha don haka a nemi aurenta a wurinshi duk yadda ya yanke yayi lafiya lou tunda ba abu bane na kusa kada aita wahalar yin zarya, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma Na'eem ba shima Haisam yaji daɗin yadda ya girmamashi yay mashi godiya da Addu'ar Allah ya ƙara girma da lafiya yana murmushi ya amsa shima yay mashi godiyar abubuwan alkhairi da ake ta masu da Addu'ar Allah ya ƙara girma da arzuki duk suka amsa da Amin, shiru falon ya ɗan yi kafin Baffan yace masu bari ya kai su bangaren shi sai su huta Haisam yace ai ba daɗewa zasu yi ba zasu koma Yola anjima zasu koma Abuja Baffan yace amman zasu kai azahar ko yana son bayan an gama sallar azahar lokacin duk yan uwanshi sun haɗu sai su gaisa dasu yace to, bangarenshi ya tafi dasu don su hutan kafin ayi sallar, bayan gama yin sallar azahar a ƙopar gida a fadar dake a cikin soro inda arɗo ke zama kafin ya rasu wadda yanzu Baffa ne ke zama don shine arɗon suka shiga harda sauran yan'uwan nashi, bayan sun gaggaisa Baffa ya gabatar masu da Na'eem, duk sun nuna farinciki kan al'amarin tare da Addu'ar Allah ya sanya alkhairi, da fulatanci Baffa yay masu bayanin lokacin da Aysha zata gama Makaranta yake son ayi auren ya kuma bada izinin a nemi auren a wurin shi mijin inna wuro kada zaryar tayi yawa, gaba ɗaya dai sun nuna hakan yayi Baban altine harda cewa ai Haisam ɗin yanzu shima na gida ne kuma ga abun alkhairi da yake ta kawo masu, bayan sun gama gaisuwar kuɗi masu yawa Na'eem ya aje masu yace suyi amfani nan fa suka shiga yin godiya Haisam ma ya ƙara aje masu wasu bandir bandir ɗin zo kaga godiya da addu'o'i, bayan sun fito bangaren su Baffa suka koma yasa Yadikko ta kaisu su gaisa dasu Yaya, cikin faram faram Yaya ta tarbesu akayi masu shimfiɗa suka zauna Yadikko taje tayo ma su Mairo Magana duk suka zo nan ɗakin aka shiga gaisawa dasu da tambayar Haisam yadda su Fatuu suke fuska a sake yake amsa masu daga baya ya gabatar masu da Na'eem, duk sun nuna farincikin su suma sunyi Addu'ar Allah ya sanya alkhairi ya kuma nuna masu, nan ma saida suka aje masu kuɗi masu yawa kafin su taso, basu daɗe ba bayan sun koma falon Yadikko sukai masu sallama suma saida suka aje masu kuɗi Baffa yace don Allah su bar shi kada hidiman tayi yawa wanda suka bada sun isa Yadikko tace mashi ko can wurin su Yaya ma saida suka bada masu yawa, duk yadda sukai dasu kan su barshi basu ɗauka ba dole sukai masu godiya, har bakin mota duk aka rakosu su suka yi bankwana dasu kafin suka tafi, a kan hanya ne Na'eem ke yabon Baffan su Fatuu yace ya burge shi wllh sosae kai kace ba mutumin ruga ba yana da natsuwa da wayewa in ba don haka ba bazai sake masu ba matsayin su na surukai Haisam yay murmushi yace haka yake ya fita daban a cikin su. Gab da sallar Magrib suka dawo Abuja sosae Na'eem yayi ma Haisam godiya da zasu rabu, saboda tafiyar da su Haisam ɗin sukai yasa wannan Weekend ɗin Fatuu ce tazo Abuja, da daddare bayan sun kwanta ne Haisam ke ce mata mi zai hana Baffansu ya baro ƙauye ya dawo ko Katsina tunda gasu Gwaggo sai ya siya mashi gida su zauna, itama Fatuu ta nuna tana son hakan tace zata tuntu6eshi kan hakan, Washe gari da safe ta kira Baffan bayan sun gaisa ne take mashi Maganar, farko shiru yayi kafin yace mata zai so hakan saidai barin ruga yanzu ba abu bane mai yuwuwa a wurinshi don arɗo ya bar mashi amanar gidan yace kada ya bari kan iyalin ya tarwatse yanzu in yace ya tafi yasan za'a iya samun 6araka kuma shi kan shi yafi sabawa da nan tunda anan ya taso yace taba Haisam haƙuri kuma tayi mashi godiya kan kudirin nashi tace to, koda ta sanar ma Haisam ɗin ya fahimci Baffan ya nuna mata bakomai, da yamma ta shirya komawa Zaria ta jirgi Esha ta saka rigimar sai ta bita Fanan ta shiga rarrashinta tace ta bari in akayi hutun School sai suje mata hutu kamar yadda suke yi sannan ta haƙura suka yi mata rakiya gaba ɗayansu harda Haisam Airport tabi charter flight zuwa Kaduna daga can driver zai wuce da ita Zaria.

Cikin sa'a Mino ta fara yin bautar ƙasarta a Asibiti, wata biyu da farawa kwatsam sai ga ciki ta samu, zo kuga farinciki a wurin Mino duk yadda take da kunya saida ta kasa 6oye murnarta haka kowa ma yayi farincikin samun cikin karma dai Fatuu sosae tayi murnar samun cikin na Mino, ta bangaren Nameer shima yayi farinciki don duk yadda yake nuna bai damu ba yana son yaga ɗanshi na cikin shi, bayan samun cikin sai kuma ta fara yin laulayi sosae ta yadda har saida ta daina zuwa Asibitin da take bautar ƙasan nata ƙarshe ma saida ta kai Nameer ya maidata wurin Mom ɗin su don bata iya cin komai duk abunda kuma ta samu ta ɗan ci sai ta amayar dashi tun lokacin ta gane ciki ba wasa bane, saida tayi wata biyu a Villa kafin ta dawo gidanta lokacin cikin ya kai wata ukku kuma ba laifi ta ɗan rage yawan laulayin amman bautar ƙasan da take yi saidai aka tsaida shi daga baya tayi, cikin na wata biyar akayi bikin Aysha da Na'eem anan Abuja, a gidansu Haisam akayi hidiman bikin don Haisam su Baffa suka amince mawa ya bada aurenta, yan Katsina da yan Adamawa duk nan suka zo ranar ɗaurin auren ya kama Juma'a kafin lokacin yin salla su Baffa suka iso, ana gama salla aka ɗaura masu auren akan sadaki naira dubu ɗari ukku sai fatan Allah ya sanya alkhairi ya basu zuri'a ɗayyiba, ana gama sallar Magrib jerin motoci suka zo ɗaukar yan kai Amarya zuwa gidanta dake a Garki, ba'a gida ɗaya zasu zauna da kishiyarta ba ita tana a gidajen manyan ma'aikatan bankin da yake aiki wato CBN, gidan da aka kai Ayshar babban Flat ne mai kyau, ba laifi anyi mata kaya daidai gwargwado wanda da yawa Haisam ne yayi mata su Fatuu ma da Kamalu dasu Gwaggo sun taka rawa wurin yin kayan ɗakin, shi kanshi angon Na'eem ya siya wasu abubuwan na gidan kafin a kawota kamar labulaye dasu carpets sannan part ɗin shi ya zuba komai, tun kafin ayi bikin Fatuu ta fahimtar da ita komai game da aure gudun kada a maimaita na Mino sai gashi a yadda ta fahimta Ayshar tasan miye auren wanda bata yi mamakin hakan ba don tafi Mino wayewar kai lokacin da aka yi mata aure, an kai amarya ɗakinta lafiya tana ta kuka aka barota sai fatan Allah ya basu lafiya.

Ana gama yin bikin Aysha su Haisam suka fara shirye shiryen komawa gidanshi na Asokoro, ƙara sawa a gyara gidan Haisam yayi duk da sabo ne ba'a ta6a shigar shi ba amman za'a ƙara ƙawata shi, Jidderh na jin zancen shirin komawar tasu ta roƙi Haisam kan ya bata kwangilar shirya gidan in an gama gyaran sai gashi ya bata aikuwa sosae taji daɗi dama yanzu ta ƙware ta fannin shirya wuri har ta buɗe Company Hajiya Maryam ma na taimaka mata wurin gudanar da kamfanin harda hannun jari ta zuba kuma da yake ita babbar yar kasuwa ce tana yo mata Order ɗin kaya daga wasu ƙasashen, kafin tayi Odar kayan gidan saida ta fara zuwa ta gano shi don bata ta6a zuwa ba ta dai san da Haisam nada gida, bayan ta gano gidan ta tuntu6i Fatuu da Fanan don taji irin kalar kayan ɗakin da suke so duk suka faɗi mata sannan ta fara ƙoƙarin yo Order ɗin kayan da taimakon Hajiya Maryam. Saida aka ɗauki wata ukku wurin ƙara gyara gidan da kuma shirya shi kafin aka gama, ranar da zasu koma ya kama Friday bayan an gama sallar Juma'a akai convoy harda President da Mom da sauran yan uwa da abokan arzuƙi aka raka su lokacin Fatuu na kan Hanyar dawowa daga Zaria, lokacin da suka iso tun daga bakin gate ɗin gidan abun kallo ya fara, dakakken electric gate ne wanda ake amfani da remote wurin buɗe shi idan kuma ba wuta akwai inda ake dannawa sannan a zuge shi saidai sai mutum ya iya sannan zai iya buɗewa haka saman katangar gidan da aka tsarata nan ma zagaye take da electric fence, daga bakin gate din akwae Security guda ukku ruƙe da bindigu, bayan an buɗe masu gate ɗin duk suka kutsa Motocin cikin harabar gidan wadda take mai girman gaske, to Salamu alaikum mun shigo daular su Fatuu, tsaye nan ina kallon ƙasan harabar gidan wadda na kasa gane glass ne a ƙasanta ko kuwa wani kalar tiles ne da ban sani ba don gaba ɗaya harabar wani irin salƙi take kai kace in Mota ta taka ƙasan zai fashe saidai abun mamaki ko gezo bata yi ba, bayan duk an parker motocin wasu a parking space ɗin gidan guda biyu dake a 6angaren hagu da dama da zasu ɗauki motoci shidda shidda wasu kuma a gaban danƙareren ginin gidan duk aka parker su, akwae shukokin fulawoyi masu ban sha'awa su kansu an tsara su ta yadda sun ƙara ƙawata farfajiyar gidan, bayan duk an firfito harabar aka fara tsayawa ana kallo kafin aka nufi shiga cikin ginin wanda yake ƙaton ginin bene ne, koda nayi arba da ƙopar shiga shiru nayi na shiga tunanin ta yadda za'a buɗeta ban gama tunanin ba naga Haisam ya nufi ƙopar a wani ɗan rami mai glass ya ɗaura saman babban yatsan shi sai gashi ta buɗe ashe ƙopar mai fingerprint sensor ce, ganin yadda ya buɗe yasa Hajiya dake bayan shi tace yanzu wannan in mutum na gaggawa sai ya tsaya yan ta6e ta6e kuma su yara in tsawon su bai kai ba taya zasu ta6a har ta buɗe duk akai murmushi Haisam ya bata amsa da ana cire fingerprint ɗin a buɗe lafiya lou ko kuma in cajin ƙopar ya ƙare Hajiyar ta jinjina kai, bayan ƙopar ta buɗe aka fara shiga ciki, wata yar hanya ce zaka fara shigowa tun anan zaka ji wani ni'imtaccen sanyi ya ratsa sassan jikin ka, saman wurin na ɗauke da wata irin babbar fitila mai sarƙoƙi da suka zubo ni dai har saida na ɗaura hannuwana a saman kai don sai naga kamar zata faɗo man, ta cikin wurin matattakalar bene take ta wani lanƙwaya daga bangon dake kallon mutum kuma nan ma wata dakakkar ƙopa ce ita Haisam ya buɗe aka bi bayan shi nima na saka kai, a wani irin haɗaɗɗan falo mai sunan falon masu arziki na tsinci kaina, gaba ɗaya na ruɗe na rasa ma ta ina zan fara, falon nada girma ba laifi gaba daya fentin cikinshi fari ne sai walwali yake haka ƙasan shi malale yake da tiles, akwae set na jajayen kujeru royal masu ratsin golden brown haka lallausan carpet ɗin dake tsakiyan kujerun shima kalar kujerun ne, komai na falon mai daukar hankali ne tun daga kan inda kayan kallo suke da sound systems haka Dining area ɗin dake a can gefe nan ma abun mutum ya tsaya kallo ne akwae dining table da kujeru suma royal kalar na falon da gani mahaɗinsu ne akwae glass door deep freezer wadda marfinta na gilas ne kana hango abubuwan dake a cikinta sannan akwae display Carbinet ta glass mai ɗauke da cups da dishes da wasu kayan ƙawa dake ta walainiya, sosae wurin ya ƙawatu harda flower vases masu ɗauke da fulawoyi masu ban sha'awa a jikin bangon wurin daga gefe ƙatuwar ƙopar shiga Kitchen take, babban Kitchen ne U-shape gaba ɗaya kayan cikinshi kalar ja da fari ne hatta cabinet ɗin sama da ƙasa katakon fentin ja da fari ne sosae Kitchen ɗin ya tsaru ya sha tsadaddun kayan amfani kama daga masu amfani da wuta zuwa wanda basu amfani da wuta a cikin shi ƙopar store take shima shaƙe yake da kayan abinci, a jikin bangon falon ba'a liƙa komai ba don irin tsarin bangon ba'a fasa shi sai daga wurin adon gidajen da aka saka kayan kallo ne aka aje manyan hotunan masu gidan dana sauran Family ɗinsu su Dad da Mom da Hajiya da dai sauran su, daga wurin bangaren cin abinci wato dining area akwae wata matattakalar benen da itama zata kai ka sama wato daga nan falon zaka iya bi ka hau sama ka sauka ta ɗayan matattakalar dake a waje ko kuma daga ta wajen ka hawo ka saukko ta cikin falon, daga bangaren dama na falon part ɗin Fanan yake sai na Fatuu na a bangaren hagu, a kowane part ɗin nasu akwae madaidaicin falo sai ɗakuna guda biyu, a falon Fanan komai na ciki blue ne kama daga lumbutsa lumbutsan kujerun ciki wadda suke na fata wato leather chairs zuwa carpet da labulaye duk suma kalar kujerun ne akwae kayan kallo da kuma kayan ƙawata falo harda wani haɗaɗdan console wato madubin falo mai hade da table ɗin shi anyi masu design masu ban sha'awa, sosae falon ya haɗu ba kamar da fentin cikinshi ya kasance fari sai ya ƙara mashi kyau sosae, a Bedroom ɗaya gadon ciki italian royal ne shima blue da Wardrobe ɗinshi bango guda sai side drawers da dressing mirror, a ɗayan bedroom ɗin shima gadon italian ne amman mara hayaniya katakon irin mai salƙi ne komai na cikin shi fari da ratsin baƙi ne, a cikin kowanne ɗaki akwae toilet kalar na zamani komai na cikinshi fari da silver ne, a cikin toilet ɗin da Royal bed yake har da laundary room wato wurin yin wanki mai ɗauke da injin wanki da kuma cabinet mai marfin glass anan tawul suke da rigunan wanka, in muka koma bangaren Hajiya Fatuu itama kamar yadda bangaren Fanan yake haka nata yake wato falo da kuma ɗakuna biyu, a falonta itama leather chairs ne maroon sai dai nata L-shape ne, tun daga kan Carpet da labulayen ɗakin suma duk marron ne akwae tabur ɗin tsakiyar falo wato center table na glass haka daga can ƙarshen kujerar akwae wani madaidaici an ɗaura ɗan madaidaicin abun saka fulawa shima kalar maroon cikinshi ɗauke da fulawoyi green da ja wanda ya ciza yay kamar maroon sai kuma farare, itama akwae kayan kallo kamar na falon Fanan, a Bedroom ɗin farko itama italian royal bed ne kalar maroon da sauran mahaɗinshi sai dayan ɗakin simple modern italian ne wato itama mara hayaniya kamar na Fanan amman nata kalar ruwan toka ne suma sai salƙi suke jikinsu nada sul6i, a kowane ɗaki akwae toilet itama komai na ciki fari ne da silver sosae aka kashe mashi kuɗi ba abunda babu na banɗakin masu kuɗi da suka amsa sunan masu kuɗi harda shower cubicle wato ke6antaccen wurin yin wanka na glass, bayan an gama da ƙasan benen sama aka hau saidai Hajiya bata hau ba tace suyo mata Vedio Haisam harda cewa bari ya ɗauketa ta watsa mashi harara, Mino ma an hanata hawa don cikinta ya tsufa ya shiga wata na takwas itama a falon ƙasa ta zauna tare da Hajiya, saman benen 6angaren Oga Haisam ne akwae ɗan babban falo mai ɗauke da kujeru leathers kalar ruwan madara suma L-shape ne haka carpet da labulayen duk ruwan madara ne akwae kayan kallo daga inda suke anyi adon gidaje an saka hotuna haka daga gefen kujerar an aje ɗan tebur na glass an ɗaura fitila mai kyau haka a tsakiya ma an aje wani tebur ɗin, akwae bedroom guda biyu a bangaren dama da hagu, a bangaren dama Bedroom ɗin Haisam yake yana ɗauke da saitin italian bed shima mara hayaniya ruwan madara a ciki akwae laundary room da kuma toilet, ɗayan ɗakin ake kusa dashi nan kuma ɗakin daya danganci aikin Haisam ne duk kayan aikin fasaha ne a ciki, daga ɗayan bangaren falon nan ma wasu ɗakunan ne ɗaya nasu Twins ne yana da ɗan girma an saka yan gadajen katako guda biyu iri ɗaya harda drawers ɗinsu sannan akwai wardrobe ɗin bango daga can gefe kuma wurin karatu ne aka ware masu akwae ɗan babban tebur da kujerunshi guda biyu sai kuma daga gefe yar kanta ce mai ɗauke da littattafai harda toilet ke akwae a cikin ɗakin, a ɗayan ɗakin kuma nan ma akwae gado kalar coffe brown da drawers ɗinshi da madubi sai wardrobe ɗin bango itama kalar coffe brown nan kuma matsayin ɗakin baƙin Haisam ne, abun saidai ace Masha Allah kawai komai yayi an narka dukiya ba kaɗan ba a wannan gida gashi akwae free internet access wato damar hawa yanar gizo da mutum ya buɗe wi-fi shikenan sai yay ta browsing da chat basai kana da Data ba, bayan an gama da ciki bayan gidan aka nufa wanda gaba ɗayan shi malale yake da grass carpet, akwae swimming pool wanda aka ƙawata tsarin shi gwanin burgewa ruwa har ta sama yake zubowa sannan ta ƙasa ma akwae wasu haɗaɗɗun kan famfuna dake zubo da wani ruwan, daga gaban shi wani wuri ne da aka zagaye da waya ciki kayan wasan yara ne kamar dai park, akwae wurin wasanni guda biyu na ƙwallon kwando wato basketball da kuma ƙwallon raga wato Volley ball sai wasu rumfuna biyu na shaƙatawa ne sai ɗayar wadda ta gini ce ita kuma anyi tane don yi ma yara lesson, daga jikin gidan ta baya akwae ƙopar fitowa sannan akwai wani ɗaki mai babbar ƙopa cikinshi ma yana da girma nan kuma Gym ne wato ɗakin motsa jiki mai ɗauke da kayan motsa jikin iri iri harda treadmill irin wanda Fatuu ta ta6a hawa ya wujijjigata har ta suma...

105

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

......... Alhamdulillah Allah yayi mun gama zagaya ko ina sai yaba gidan ake ana an dai kashe kuɗi, cike da tsokana Dad ɗin su Haisam wato Mr President yace mashi anya bazai sa EFCC su bincike shi ba don an kashe ma gidan kuɗi da yawa duk akai dariya Hajiya tace in an tashi bincikar tashi sai a haɗa dashi tunda ai shine ƙarfin nashi, Dad ɗin na yar dariya yace shi ai gida kawai yasan ya bashi amman ba hannunshi a wannan uban kayan daya zuba ma gidan Hajiyar tace aikuwa shike da hannu tunda ai shiya biya mashi yaje yayi karatun fasahar da yake samun kuɗi duk akayi dariya harda Security dake biye dasu, itama Mom yaba ma Jidderh tayi tace bata san kamfaninta sun ƙware haka ba sai yanzu gaba ɗayan kayan da aka zuba ma gidan sun hau kuma sunyi kyau nan fa duk aka shiga yaba mata tanata dariyar jin daɗi haka mijinta Sadeeq shima yaji daɗin yabon nata da ake Dad ɗin su har yana cewa zai bata kwangilar zuba ma gidan su kaya in ya sauka zasu koma, cike da jin daɗi tayi mashi godiya Aunty ma tace zata rinƙa samo mata kwangila kuwa tunda sun ƙware haka Hajiya Zainab ma itama tace zata rinƙa samo mata dama harda ita aka zo don yanzu sunfi zama a Abuja bayan an ba Dad ɗinsu Sameer Minister, Fauzy dai basu ƙasar kuma har yanzu bata sake haihuwa ba itama don Sameer yace sai ta huta sosae ba kamar daya ga Cs aka yi mata, ganin Dad ɗinsu na niyyar tafiya yasa Haisam ce mashi please ya bari suci abinci ya ɗan buɗa mashi ido kafin yace ai baya jin yunwa Jidderh dake murmushi tace ai na murnar sabon gida ne ya kamata yaci yana murmushi yace to tunda hakane a bashi ya tafi da abunshi duk akayi dariya dama ya iya barkwanci, Fanan ce ta nufi cikin gidan da sauri dama sunyi Order ɗin abinciccika saboda masu rako su sabon gidan, bada jimawa ba ta fito ruƙe da manyan ledoji guda biyu ta nufo shi dasu, har rige rigen amsa muƙarrabanshi daya zo dasu suke amman sai yace masu su bari shi zai ruƙe abunshi don kada wani ya cinye mashi aikuwa mi za'ai ba dariya ba kuma shi ɗin ya kar6i abun shi anata ya kawo don Allah a ruƙe ya ƙi badawa, Addu'o'i yayi masu na Allah ya sanya alkhairi yasa sun dawo a sa'a ya karesu daga dukkan sharri anata amsawa daga baya sukai sallama aka buɗe mashi mota duk sauran abokan tafiyar nashi suma suka shiga motocin saida aka ga tafiyar su sannan suka koma cikin gidan harda su Mom, a falo aka zazzauna zaman cin abincin abun gwanin sha'awa su Mom sai kace ba First lady ba sun saki jiki cikin yan uwa ana ta cin abinci ana hirar nishaɗi. Sai gab da Magrib Fatuu ta iso Haisam yaje ɗaukkota tasha gayun doguwar rigar shadda, tun a bakin gate ɗin gidan ta fara sakin baki don itama ba sanin gidan tayi ba ta dai san shi a hoto, lokacin su Mom duk sun tafi sai su Mino da Aysha da kuma Jidderh da suka tsaya su tarbeta, sosae aka nuna farincikin dawowarta bama kamar su twins, Esha tana ganinta ta ƙanƙameta tana mata welcome tare da nuna mata sabon gidan su, sam Fatuu ta kasa 6oye al'ajabinta da kuma farincikin gidan sai faman bin gidan take da kallo idanu waje tana kuma sakin murmushi duk a lokaci guda, zagayawa suka shiga yi da ita harda Fanan Haisam kuma ya tafi Masallaci, bayan sun gama ganin ko ina ciki suka dawo don yin salla, sosae Fatuu tayi godiya ga Allah da yadda yake ta mata ni'imomi da bata ta6a zaton samu ba a rayuwarta, harda kukan daɗinta sannan tayi ma Mijinta Addu'o'i sosae shima, bayan sallar isha aka zo ɗaukar su Mino anata mata Addu'ar Allah ya raba ta da cikinta lafiya haka Aysha amarya ma ba'a daɗe da ɗaukar Mino ba itama angonta Na'eem yazo ya ɗauketa, Jidderh ce ta ƙarshe da aka ɗauka duk saida mazajen nasu sukai ma Fatuu Allah ya sanya alkhairi kafin su tafi don ɗazun da suka zo bata nan, bayan Haisam ya dawo a tare gaba ɗaya suka zauna cin abinci a dining area fuskokin kowannensu cike take da annuri, bayan sun gama cin abincin ne Haisam yace suyi alwala suyi Nafila duk suka ce to harda yaran, anan babban falon sukayi sallar raka'a biyu ta godiya ga Allah bayan sun gama kowa yayi addu'a Esha tana yi tana dariya tana leƙen fuskokin su twins, a falo suka zauna nan Fatuu tayi ma Haisam ɗin godiya da Addu'oin Allah ya ƙara mashi lafiya da arzuƙi mai amfani harda su Fanan dasu Esha ake amsawa, kallo suka yi zuwa ƙarfe tara da rabi Haisam yace ma su twins suje ya rakasu su kwanta aikuwa Esha na jin haka ta fara tura baki tana ƙunƙunin ita ba'a yi mata ɗaki ba a saka mata ɗan gadonta itama duk sukai dariya Fatuu tace ita dake da ma ɗakuna har biyu ga ɗayan na part ɗinta ga kuma na Momynta sai inda take so zata kwana ta tura baki tace ai duk gadon sun mata ƙato ita kalar nasu twins take so, Haisam dake a tsaye yana murmushi yace mata tayi haƙuri in ta samu sister sai ayi masu ɗakinsu suma su biyu ta wani yarfa hannu tace to ba Aunty da Momyn suƙi su haihu ba tayi ƙanwa duk sukai dariya, jawota Fanan tayi jikinta tana bata haƙuri tace bada daɗewa ba zata yi ƙanwa da Aunty ta gama karatu,

"To Momy ke ki haihun man younger sister tunda ita sai ta gama karatun" ta faɗa a shagwa6e, murmushi Fanan ɗin ta shiga yi tana ɗan kikkifta ido ta kasa ce mata komai, hannu Fatuu ta kai ta dafa kafaɗar Esha ɗin tace "Momy zata haifar maki sister in sha Allahu, daga yanzu duk kikai salla pray for her, kuma su twins ku rinƙa yi ma Momynku Addu'ar Allah yasa ta haiho mana Baby mai kyau" ta ƙarasa tana murmushi duk suka ce to Haisam nata murmushi bai ce komai ba ya kama hannuwansu bayan sun yi masu saida safe suka tafi yadda ya ruƙe su abun gwanin sha'awa, bayan sun haye bene Fanan ta miƙe tana ruƙe da hannun Esha tace suje itama ta kwanta ta ɗaga hannu tana ce ma Fatuu "Good night, Aunty" itama hannun ta ɗaga mata tace "Goodnight, Esha Darling" ta saki dariyarta mai kyau suka tafi, bin su da ido Fatuu tay har suka shige ta ɗan girgiza kai wani irin tausayin Fanan take ji game da rashin haihuwarta don ta san dole tana tsananin son ta haihun, lokacin da su twins suka fara girma duk sun ɗauka Fanan ɗin ce ta haife su saboda yawan jan su a jiki da take, koda ta fahimci hakan don sun fi sakewa da ita da kanta ta sanar masu da cewa Fatuu ce ta haife su Adam har saida yaje ya tambayi Fatun wai da gaske ba Momy bace ta haife su ta tambayeshi waya faɗi mashi hakan yace ita, jin haka yasa taje tayi mata magana kan miyasa zata yi masu wannan Maganar tana murmushi tace yakamata su sani ne don uwa ba wasa bace in bata faɗi masu ba zasu iya ƙin bata muhimmancin daya kamata lokacin har saida su duka sukai ƙwalla, daga baya ne Fatun tace masu suci gaba da ɗaukar Fanan matsayin Momyn su ita kuma su rinƙa ce mata Aunty, miƙewa tayi ta nufi Bedroom ɗinta inda keda royal bed, bayan ta shiga shirin yin wanka tayi dama duk kayan sawarsu an riga an kawo su tun kafin su dawo har ta ware wasu masu yawa zata aika ma Gwaggo a bada su sadaka a Foundation ɗinsu wanda yanzu sosae ya cigaba ana tallafa ma marasa ƙarfi ba kamar yan gudun hijira da akwae su sosae a yankin Katsina, su twins ma da Esha duk an ware kayan su da yawa za'a bada Fanan ma haka, a cikin laundary ta cire kayan jikinta ta ɗaukko rigar wanka ta saka tana ta kallon kanta ta cikin ƙaton madubin wurin, gaba ɗaya ganin komai take kamar a mafarki gashi sai take ganin komai ya faru da wuri wato dai ashe cin ribar haƙuri haka yake da daɗi, lafiyayyan wanka tayi lokacin data fito sai faman sakin wani irin ƙamshi take, Bedroom ta shiga ta zauna akan kujerar gaban madubi tana kallon kanta tana goge lemar ruwan jikinta data kanta, tana haka Haisam ya shigo cikin ɗakin da sallama ta juya tana kallonshi suna haɗa ido ta fara sakar mashi ƙayataccen murmushi shima ya shiga maido mata, tun kafin ya ƙaraso gareta ƙamshin turarenshi ya rigashi isowa yana sanye da kayan bacci riga da wando farare masu taushi wanda da gani sababbi ne, wurinta ya nufo yana zuwa ya tsaya yana kallonta suna sakar ma juna murmushi can ya miƙa hannu ya amshi towel ɗin da take goge jikin ya cigaba da goge mata sai dai nashi da wani irin salo mai tsuma zuciya yake yi suna yi suna kallon juna ta cikin madubin suna cigaba da sakin ƙayataccen murmushi mai tattare da tsantsar ƙaunar juna, bayan ya gama goge mata da kanshi ya shafa mata man da yasan tana amfani dashi da daddare, gaba ɗaya shi yayi mata shafe shafe da goge gogen da take yi da daddare da yake gashinta bai jiƙe ba sosae iya baki baki ne hakan yasa bai busar mata dashi ba, bayan ya gama miƙewa tayi da niyyar taje ta saka kaya kawai sai ji tayi ya janyota ya haɗe jikinsu kafin ya haɗe fuskokinsu suka shiga shaƙar numfashi da ƙamshin juna, slowly ya kai lips ɗinshi ya haɗe da nata ya shiga bata deep and hot french kiss, tun ƙafafunta na ɗaukarta har suka kasa gaba ɗaya ta ƙanƙame shi, ya ɗan ɗauki lokaci kafin ya saketa ai da ƙyar take iya kallonshi hakan yasa shi yin ɗan murmushi mai sauti ya kai hannu ya ɗauketa gaba ɗaya, yana ɗauke da ita ya nufi switch ya kashe hasken ɗakin kafin ya nufi haɗaɗɗan royal bed ɗinta daya sha lafiyayyan zanin gadon da ko mutum bai yi niyyar bacci ba ya kwanta sai ya ɗauke shi, sosae Fatuu tayi ma Haisam godiya ta hanyar faranta mashi daren ranar ya shiga cikin tarihinta, Washe gari da safe ita da Fanan suka shiga Kitchen don yin Breakfast sai mai aikinsu ta wancen gidan da suka taho da ita ita kuma tana gyara gidan duk da bai wani 6aci ba, suna cikin aiki ne Fanan take ce ma Fatuu yakamata a ƙara masu aiki don yanzu aikin dole zai yi yawa ba kamar wanccan gidan ba tunda shi iya inda suke amfani ake gyarawa Fatun tace mata tana ganin a ƙara guda ɗaya tunda in ta gama karatunta zata dawo da Asabe mai aikinta ta can
Zaria nan,

"Allah sarki, har na tuna da Aunty Saude mace mai kirki gashi sam bata da son jiki, in mutum ya samu mai aiki kamarta ya more don tana da amana" Fatuu dake juya dankalin turawa cikin mai ta faÉ—a, Fanan na jin abunda tace itama tace gashi ta iya girki kamar me Fatuu tace wllh,

"To ko ayi mata magana in tana da wadda zata turo mana, dama ni ban cika son irin wanda agent ke turowa ba don baka san mutum ba wasu mutanen are evil" kai Fatuu ta jinjina tace to zata mata magana dama basu daÉ—e da sukai waya ba tayi mata barka don ta haihu, É—an buÉ—a ido Fanan tayi "Don Allah fa!" Fatuu tace mata wllh,

"Amman ban samu labari ba ai da nayi mata barka kuwa, ikon Allah, itama tunda tayi aure bata haihu ba sai yanzu duk da bansan ko tana Family planning bane tunda ance tana da wasu yara" Fatuu tace mata eh tana da yara da tsohon mijinta kafin ta ƙara cewa "kema in sha Allahu Aunty Fanan zaki haihu" tana murmushi tace to Amin in tana da rabo in kuma bata da rabo already Allah ya bata ta wata hanyar Fatuu tay murmushi,

"Amman fa in kin mata Maganar mai aiki kada a samo yarinya ko budurwa babba kamarta zaki ce" Fanan ta faɗa tana motsa farfesu, cikin rashin fahimta Fatuu tace to dama aikin gidan nan babbar zata fi, yar dariya Fanan tayi don ta fahimci bata gane dalilin da yasa ta faɗi haka ba tace mata ita saboda kada a ƙwace masu miji ta faɗi haka don tana jin labarun faruwar irin haka, dariya sosae Fatuu tay harda ɗage kai Fanan dake dariya itama tace Allah, bayan Fatuu ta tsagaita da yin dariyar tace ai Hubby bazai yi hakan ba,

"Uhmm, wani lokacin suna ba mutum mamaki fa ba kamar shi da ya cika tausayi hakan na iya saka shi ya auri mai aiki",

shiru Fatuu ta ɗan yi tana ɗan murmushi, jin tayi shiru yasa Fanan ɗin kallonta nan take ta fahimci yanayin fuskarta ya canza da sauri ta kai hannu ta dafata tace "Zarah bafa nayi Maganar saboda ke bane wllh, i just said it as an example, Babe wani irin mutum ne shi yana da kirki sosae, inda kirki yana yin yawa to zance kirkin shi har yayi yawa abunda baka tunanin zai iya yi sai kiga ya yi, kamar yadda ya aure ki da niyyar taimako nima haka ne, gara ke ma don na tabbatar yana son ki kawai bai sani bane, amman ni na tabbatar baya sona lokacin daya aure ni kawai yayi ne don ya faranta man ganin na shiga mawuyacin hali saboda shi, amman saboda kirkin shi tunda nike dashi bai ta6a wulaƙanta ni ba daidai da rana ɗaya gashi ko haihuwa bana yi, Babe na musamman ne" ta ƙarasa idonta a sama tana murmushi, itama Fatuu murmushin ta shiga yi tana tunano tun daga farkon haɗuwar su,

"Amman Aunty Fanan nace mi zai hana mu ɗan hada mashi surprised party matsayin godiya da wannan sabon gidan" Fatuu ta faɗa tana kallon ta, da sauri Fanan tace wannan shawara ce mai kyau ya take gani za'ai Fatun tace ayi mashi cake sai ai decorating falonta, Jidderh suka yanke zasu kira kan tazo ta shirya falon Fanan ɗin in zasu yi mashi partyn bazatar, waya Fatuu ta ɗauka bayan ta kira Jidderh ta ɗauka sun gaisa take faɗi mata abunda suke son yi, tambayar ta tayi yaushe suke son yin partyn Fatuu ta kalli Fanan ta tambayeta tay ɗan jimm alamar tunani kafin tace ko gobe ko Fatun tace to ai kuma ita gobe zata koma, ce ma Jidderh sukai in zai yuwuwa zuwa da yamma kamar wurin ƙarfe biyar tace Ok lafiya lau zata masu ƙoƙarin hakan,

Misalin ƙarfe huɗu Jidderh ta iso gidan a Motarta, saida ta fara kiran Fatuu ta tambayi in Haisam bai a babban falo tace mata eh yana Masallaci, tare da wata abokiyar aikinta yare suka zo, bayan sun fito daga cikin Motar suka fara kwasar kayan da suka zo suna shiga dasu, bayan sun kai wasu Fanan da Fatuu suka biyo su suma suka taya su ɗaukar wasu, ba 6ata lokaci Jidderh da abokiyar aikinta suka fara shirya falon, bayan sunyi nisa ne Fanan da Fatuu suka tafi su shirya,

wuraren ƙarfe biyar Fanan ta kira Haisam a waya ta tambayi yana ina ya bata amsa da yana a sama suna yin lesson dasu twins tace pls in ba damuwa ya zo part ɗinta tana son ganin shi ya furta Ok, ba'a ɗau lokaci ba ya turo ƙopar yana sanye da ƙananun kaya da suka amshi jikinshi, yana niyyar yin sallama ya dakata sakamakon wani ƙyalƙyali daya zubo mashi har saida ya ɗan runtse ido, bayan ya tsagaita da zubo mashi yasa hannu yana kakka6e wanda ya maƙale mashi a jiki da saman sumar shi, yana ɗagowa ya kalli gaban shi idanunshi suka sauka akan wata yar banner da aka yi rubutu mai walwali an rubuta _"Thank you for our new home, We really love you our Husband"_ ƙayataccen murmushi ya saki ganin rubutun kafin ya juya ya kalli cikin falon wanda aka ƙawata shi da baloons wato balo kala kala sannan an aje manyan hotunan bikinsu shida Fanan da kuma wanda akayi mashi da Fatuu a Dinner ɗin su da akai a Abuja sannan an aje wanda sukai su duka da yaran su harda babban cake mai hawa biyu anyi decoration da hotunan Haisam da zasu kai biyar sannan an yi rubutu in icing an rubuta "Home sweet home" sannan daga saman baki bakin cake ɗin anyi topping da fresh fruit da suka ƙara ƙawata shi, nufo shi Fatuu da Fanan sukayi sun sha gayun ƙananun kaya riga da wando da suka bayyanar da dirin su gashin kan su gaba ɗaya sun sake shi kai kace hausa bazata fito daga bakunansu ba, ko a iya matan da Allah ya ba Haisam za'a iya cewa ba ƙaramin dacewa yay ba don mata ne da suka amsa sunan mata uwa uba gasu da hali na gari, a gabanshi suka tsaya suna sakin murmushi tare da ƙara yi mashi godiyar yanata murmushi ya ware masu hannuwanshi a tare suka faɗa jikinshi suna ta yar dariya Jidderh da abokiyar aikinta ma dariyar suke ta shiga yi masu Vedio, bayan sun ɗago daga jikinshi kamo hannuwansu yayi suka nufo ciki, a saman doguwar kujera suka zauna dama a gabanta aka aje cake ɗin, bayan zaman su Jidderh tace yakamata a kira su twins suzo a yanka cake tare dasu Fanan ta miƙe ta nufi inda wayar landline take ta kira part ɗin Haisam, Esha ce ta ɗauka cikin zazzaƙar muryarta tace waye ne ke kiran Dad to bayanan da turanci tayi Maganar Fanan na murmushi tace to Momynsu ce, waro ido Eshar tayi sai kuma tayi dariya ta kira sunanta ta amsa tare da tambayarta ina su twins tace mata gasu nan tace to suzo part ɗinta yanzun nan akwae surprise da sauri Esha ta maimaita abunda tace tare da waro ido Fanan ɗin tace mata eh, kife kan telephone ɗin tayi cike da zumuɗi ta faɗi ma su twins abunda Momy tace ta nufi hanyar fita da gudu, Esha ce ta fara shigowa da gudu tana sanye da ɗan skirt na jeans da farar t-shart bayan ta shigo su twins suka biyo bayanta suma ƙananun kaya ne a jikinsu, koda Esha taga yadda akai ma Falon da tsananin mamaki taja ta tsaya a gabansu ido waje ta furta "Wow! what a surprised!!" hannu Fanan ta miƙo mata ta nufesu tana washe baki, a saman jikinta ta ɗaurata gaba ɗaya ta ruɗe sai faman tambayar su Dad ake ma Birthday take, saida Adam ya nuna mata rubutun jikin cake ɗin sannan ta fahimci mi ake, a tare gaba ɗaya suka kama ma Haisam ɗin hannu suka yanka cake Jidderh nata masu Video, bayan an yanka kowa ya ɗauka ya bashi a baki kafin shima ya basu har shafa mashi icing ɗin jiki sukai a fuska suna ta dariyar farinciki daga baya Fanan ta kama hannunshi da turanci tayi mashi kalami masu tsuma zuciya kan muhimmancin shi a wajenta da kuma yadda take son shi ƙarshe tayi mashi godiya da Addu'oi, bayan ta gama Fatuu ma tayi suma su Esha saida sukai mashi abun dai gwanin burgewa daga baya aka shiga yin hotuna, harda music Fanan ta kunna aikuwa Esha ba ƙaramin cashewa tayi ba sosae taba mutane dariya, sosae Haisam ya yaba da abunda sukai mashi shima saidai yay masu kalamai kan yadda suke a wurinshi saida aka kira sallar Magrib suka gama.

A cikin satin akaita zuwa ganin sabon gidan da yi masu Allah yasa Alkhairi har Laila ma tazo daga Kano ita da mijinta da yaranta biyu don ta ƙara haihuwa, ranar Friday su Gwaggo suka zo da Kawu Amadu da Tk da kuma matansu sai yaransu don dukkansu sun ƙara haihuwa ita matar Tk mace ta ƙara haihuwa itama Haulat mace ce mai sunan Gwaggo wato Khadija, zuwan nasu yasa Fatuu ta ƙara zuwa Abujar kowa saida ya jinjina haɗuwar gidan akai masu Allah yasa Alkhairi da Addu'oi, a yadda suka shirya zasu bi Gwaggo ne apartment ɗin da take zama in tazo amman Fatuu ta hana tace anan zasu kwana harda gwaggon tunda ai don su suka zo, ƙarshe dai anan suka kwana don Haisam da Fanan duk sun saka baki kan su kwana anan, Washe gari Asabar bayan sunyi lafiyayyan breakfast suka shirya fita harda su Fanan da Fatuu sukai Mota ukku data Fatuu dasu Gwaggo suka zo da ita sai kuma ta Fanan sai wadda Haisam zai hau, Villa suka fara zuwa duk an nuna farincikin zuwansu karma Hajiya sosae tayi murnar ganin su akai masu tarba mai kyau, daga Villa gidan Mino suka wuce zo kaga murna har tana ce ma Gwaggo amman dai bazata koma ba har ta haihu ko Gwaggon na dariya tace a'a abunda da saura amman zata kwana biyu in ta haihun ta dawo, da ƙyar ta barsu suka tafi harda roƙonsu kan su dawo su kwana anan suka ce to ƙilan su dawo, daga nan gidan Aysha aka wuce itama taji daɗin ganinsu har ta kasa rufe baki gashi tayi masu lafiyayyan abinci don tasan da zuwan nasu, bayan gidan Aysha gidan Kamalu aka nufa nan ma dai sun nuna farincikin zuwan nasu hannu bibbiyu Farha ta kar6e su Babynsu har ta girma tubarkallah, gaba ɗaya ko ina roƙonsu ake kan su kwana ƙarshe saidai rabawa sukai Haulat da Husnah suka koma gidan Mino Tk da Amadu kuma gidan Kamalu zasu kwana Gwaggo kuma gidan Aysha sai dare su Fatuu suka koma gida,

Washe gari gaba É—aya suka koma gidansu Fatuu a yadda suka shirya tare da ita zasu tafi Zaria su kwana washe gari Monday da safe sai su wuce Gwaggo dai anan zata tsaya sai ta kwana biyu,

Kwance tashi cikin Mino ya shiga wata na tara lokacin watan su Fatuu ɗaya da komawa sabon gida kuma Fatun na gida don sun samu hutu, tun ranar litinin ta fara yin naƙuda tsaitsaye zuwa washegari talata ciwo ya kankama amman koda aka kaita asibiti sai aka ce da saura su dawo gida taita yin exercise, kan kace mi duk ta fita hayyacinta dama abu ga sabon shiga tuni ido ya raina fata sai murƙususun azaba take har zuwa Fatuu tay ta dubata itama taga da saura ɗin haka tay ta ƙarfafa mata gwuiwa har tana ce mata kodai dama bata yin exercise da cikin ya tsufa cikin ciwo tace wllh tana yi, sai dare Fatuu ta koma gida Nameer ya dasa yin jinyar, wuraren ƙarfe sha biyu ba arziƙi ya kwasheta suka koma asibitin, wannan karon an kwantar da ita a vip wato ɗaki na musamman ita kaɗai ce aciki duk da haka an faɗi ma Nameer cewa da sauran lokaci, koda Fatuu ta kira taji ya jikinta Nameer ne ya sanar mata sun dawo asibiti an kwantar da ita amman ance still da saura tana jin haka tace gata nan zuwa, bayan zuwanta Asibitin Auntynsu Nameer ma tazo, shiru shiru ba haihuwa gashi ga dukkan alamu tana cikin azaba wasa wasa sai gashi har asuba bata haihu ba lokacin ta gama jigata ƙarfinta ya ƙare, gari na wayewa Aunty ta bada umarnin ayi mata Cs, sosae hankalin Nameer ya tashi jin zancen aikin amman ba yadda ya iya haka ya saka hannu, Wuraren ƙarfe tara na safe aka shiga da ita ɗakin tiyatar lokacin duk yan uwa sun zo harda Mom, Aysha ma tazo sai kuka take ana ce mata tayi mata Addu'a, ita kanta Fatuu hankalinta a tashe yake ƙarfin hali kawai take tana ta yi mata Addu'oi, bayan kamar minti ashirin da shiga da ita sai ga likitan ya fito yana ta murmushi ya sanar dasu tama haihu da kanta ba'a riga anyi aikin ba, zo kaga murna Aysha har da tsalle sai ga mai kuka ta koma yin dariya Fatuu da Nameer harda sujjadar godiya ga Allah sukai, lokacin da aka fito da Babyn wanda namiji ne baka jin komai daga bakunansu sai tubarkallah ma sha Allah Babyn kyakkyawan gaske gashi ƙato, daga baya itama Mino aka fito da ita saman gado baiwar Allah har an saka mata rigar aiki, bayan an canza mata ɗaki duk aka shiga ana mata ya jiki da barka, su Mino an ɗanɗana tun a asibitin ta rinƙa faɗin ta gama haihuwa aikuwa mi Fatuu zatayi in ba dariya ba tace wasa take ai yanzu ma ta fara sai gata harda kukanta sha6e sha6e tana ta rantsuwar ita Allah ta gama, da yamma aka sallameta ganin lafiyarta lau suka koma gidanta aka cigaba da zaman jego har ranar suna tazo yaro yaci sunan mahaifinsu Fatuu wato Muhammad aikuwa ba ƙaramin farinciki su Fatuu sukai ba, bayan suna da kwana ukku ta koma Yola acan zatayi wanka kamar yadda ta buƙata a wurin Nameer.

Bayan sati biyu da haihuwar Mino ranar Alhamis lokacin hutun su Fatuu na gab da ƙarewa tana kwance saman gado da safe wurin ƙarfe sha biyu na rana jikinta sanye da turkish dress riga da wando kalar Yellow gyalen kayan na daga can gefe hakan ya bayyanar da kanta da akai ma kitson sunan Mino sati ɗaya daya wuce, tana cikin yin baccin Esha ta shigo ɗakin da gudu koda ta hangota kwance sai ta nufi gadon, hayewa tay ta fara bubbuga jikin Fatuu tana faɗin "Aunty, wake up!, wake up pls!! ki tashi" yanayin yadda take Maganar kamar zata saka kuka, buɗe ido Fatun tayi ganin Esha ce ke tashinta yasa ta tamke fuska da alamun 6acin rai ta furta "Esha! Why do you always disturb my sleep for God's sake! Banda dama in kwanta sai kin tashe ni kuma bada wani dalili ba kawai baki so ki ganni a kwance!" yamutsa fuska Esha ɗin ta shiga yi idanunta suka ciko da ƙwalla, a fusace Fatun ta ƙara cewa "yanzu da kika zo kina buguna haka miye zan maki??" cikin karyayyar murya Esha ɗin tace "Ba Momy ne bata lafiya ba kuma tayi amai da kuka" waro ido Fatun tay ta maimaita "amai da kuka!" da sauri ta jinjina mata kai aikuwa ba shiri ta wuntsilo daga saman gadon ko ta kan gyalen kayan bata bi ba ta nufi hanyar ƙopa Esha data saukko itama tabi bayanta da sauri, lokacin data shiga Bedroom ɗin Fanan kwance ta sameta a saman gado rabin jikinta lullu6e da duvet sai nishi take su twins sun sakata tsakiya fuskokinsu duk ƙwalla, a ruɗe Fatuu ta nufi bakin gadon ta zauna tare da kai hannu ta ta6a fuskarta tana tambayarta mike damunta haka, cikin nishi tace mata tunda ta tashi bata jin daɗin jikinta haka ta rinƙa daurewa har sukai breakfast to bayan sun gama ta dawo ɗaki taji zuciyanta ta fara tashi daga baya kuma sai amai yazo mata bayan tayi ne zazza6i da ciwon kai suka rufeta tana haka su twins suka zo yanzu ma bata daɗe data ƙara yin aman ba gashi harda juwa take ji shiyasa tasa a kira mata ita ganin ciwon na gaba, cike da damuwa Fatuu tace ai da tun da taji bata lafiya tasa aka kirata, wayar Fanan ɗin ta ɗauka ta kira Haisam bayan ya ɗauka cikin tashin hankali ta sanar mashi da halin da Fanan take ciki Shima hankalinshi ya tashi ba kamar daya ga lafiya lou suka yi breakfast, ce mata yay ko ta kaita Asibitin Villa tunda yafi Kusa zai iskesu yayi wasu baƙi ne daga Lagos amman bada jimawa ba zai sallamesu yazo duk yadda ake ciki pls ta sanar mashi da sauri tace to, suna gama wayar Mom ɗin shi ya kira ya sanar mata tace bari ta kirasu, bayan ta kira wayar Fanan ɗin Fatuu ta ɗauka ta tambayi yanayin jikin Fanan ɗin da damuwa Fatun tace to gata nan da gani dai tana jin jiki tana tunanin fever ce ke damunta Mom ɗin tace Ok su taho nan sai a dubata, dama Fanan ɗin a shirye take don duk sunyi wankan safe gyale Fatuu ta ɗaukko mata itama ta ɗauki wani cikin nata ta yafa, a tare harda su twins suka kamo Fanan ɗin yaran duk sun shiga damuwa gwanin tausayi, a Motar Fanan suka tafi, bayan sun isa Mom ta tarbesu aka wuce da ita Asibitin, suna zuwa kwantar da ita akai a ɗaya daga cikin lafiyayyun dakunan da ake kwantar da marasa lafiya da suka danganci gidan gwamnatin tarayyar, tambayoyi likitan daya kar6eta ya shiga yi mata tana bashi amsa ciki harda rabonta da period ta bashi amsa da tayi last Month sai wannan watan ne bata kaiga yi ba amman dama wani lokacin tana fita daga wata sannan har tsallaken wata ma tana yi nan tayi mashi bayanin lalurar data yi a baya amman tace mashi ta samu sauƙi, lokacin da ake mata tambayoyin Mom ta kira Hajiya Maryam ta sanar mata ga Fanan an kawo ba lafiya nan take hankalinta ya tashi ta shiga tambayar abunda ya sameta Mom ɗin tace ba'asan taƙamaimai ba amman gashi nan likita na bincikawa tace to gata nan zuwa, jininta aka ɗiba aka tafi yi mata gwaje gwaje, ba'a jima ba Hajiya Maryam ta ƙaraso tana ganin yanayin jikin Fanan ɗin a ruɗe ta hau tambayarta abunda ke damunta Fatuu dake zaune a wurin kanta tayi mata bayanin yadda ciwon ya fara sam ba wanda ya kawo komai a ranshi Mom tace su jira likita yazo ya faɗi sakamakon gwaje gwajen, bayan wani ɗan lokaci Hajiya Maryam ɗin ta miƙe tace bari dai tabi bayan likitan don ta ƙagara taji mike damunta haka, tana niyyar fita likitan ya sako kai da sallama taja gefe, yana shigowa ta hau tambayar shi mike damunta ne fuskarshi ɗauke da murmushi yace ta kwantar da hankalinta abun farinciki ne, su Mom na jin haka duk suka miƙe suka nufo shi, tambayarshi Hajiya Maryam ta sake yi miye abun farincikin yace sakamakon gwajin ciki da akai mata ya bayyana tana ɗauke da ciki na tsawon sati ukku, yadda kasan wutar jikinsu ta ɗauke gaba ɗaya bin shi sukai da ido ba mai ko ƙwakkwaran motsi shi kuma likitan sai murmushi yake,

"Wait Dr, wai abunda kake son faɗi mana shine kana nufin ita Fanan ɗin ke ɗauke da ciki?" da tsananin mamaki Hajiya Maryam ta tambaya cikin girmamawa yace mata eh haka sakamakon ya nuna tana dashi na sati ukku yay maganar tare da miƙo mata wata farar takarda da aka naɗe, har saura kaɗan ta saki wayarta dake a hannunta wurin rawar hannun ta amsa, bayan ta buɗe Mom da Fatuu suma suka shiga dubawa nan idonsu ya tabbatar masu, da tsananin farinciki suka shiga washe baki Fatuu harda sa hannu guda ta rufe bakinta alamar mamaki, nan fa aka shiga yin murna su Esha harda tsalle suna faɗin Momy is pregnant zata haifa masu baby Allah ya amshi addu'ar su, nan fa aka fara kiraye kirayen waya ana ma yan'uwa albishir, ko ban faɗa ba ansan dole ai tsananin farincikin samun cikin, Mom ce ta kira Haisam lokacin ma yana kan hanyar zuwa tayi mashi albishir to shima dai ba ƙaramin mamaki da murna yay ba , kan kace mi ɗakin ya cika har Hajiya tazo da Farha anata farinciki, kyautar miliyan guda Hajiya Maryam tayi ma likitan daya faɗi masu zancen cikin Haisam ma ya ƙara mashi wata miliyan guda ɗin kakar likita ta yanke saƙa har ya rasa irin godiyar da zai yi, Mom na dariya tace to ai itama yakamata a bata kyautar tunda ita ta kirata ta sanar mata zancen ciwon duk akai dariya Hajiya Maryam ɗin tana dariya tace to ta bata kyautar Mota duk akai shewar murna, Mom nata dariya tace ita ta yafe Doughter yakamata a ba kyautar tunda ita ta kawota asibitin Hajiya Maryam ɗin tace to ta ba Fatun Motar, da sauri Fatuu tace a'a ta barta ai duk abun farincikin nasu ne Hajiya Maryam ɗin tace ta riga ta bata in bata so sai ta bayar, Esha na jin haka ta ruƙe ƙugu tace to ai suma tare dasu aka kawo Momyn a basu kyautar, hannu Hajiya maryam ta kai ta ɗan ja kumatunta tace ta faɗi abunda duk take so da sauri tace stroller take so da zata rinƙa tura baby aikuwa mi za'ai in ba dariya ba Hajiya Maryam ɗin tace an gama in ma guda goma take so zata siya mata ta juya kam Adam tace shi mi yake so yace kayan wasa da zai rinƙa yima Baby wasa harda Mota da zasu rinƙa shiga tare suna zagaye gida tace to shima za'a siya mashi, juyawa tay kan Abie da yayi shiru kai kace babu shi a wurin tana dariya tace "kai kuma miskilin mu mi kake so?" shiru yay yana bin ta da idanunshi da suke a ɗan lumshe duk da idanun nasu manya ne amman wani lokacin sai su lumshesu kamar dai yadda na Haisam ke yi, shiru yay bai tanka mata ba duk idanunsu na akan shi ana son aji mi zai ce don Magana mugun wuya take mashi wannan da alama ma sai yafi Haisam miskilanci dama ance wai kyawun magaji ya zarta, ganin baida niyyar magana yasa tace mashi in fa bai faɗi mi yake so ba to in aka haiho Babyn saidai ya rinƙa kallonshi do n baza'a bashi ba ya ɗauka balle har ya yi mashi wasa, ana jin abunda tace su Mom suka ce mashi ya faɗi mata ko so yake su Esha su rinƙa ɗaukar baby suna mashi wasa banda shi, a hankali ya fara motsa baki kafin da ƙyar cikin sanyayyar muryarshi ya furta Water Bottle yake so da zai rinƙa ba Babyn ruwa aikuwa mi za'ai in ba dariya ba har Haisam saida yayi dariyar Hajiya dake zaune tace ai shine Water Bottle ɗin aka ƙara yin dariyar, Fatuu dake zaune gefen Fanan ta lura da ita kamar bata farincikin samun cikin don ko uffan bata ce ba duk abun nan tana kwance sai ɗan murmushi da take in anyi abun dariya hakan yasa ta dafata tace "Aunty Fanan ya naga kamar baki farincikin samun cikin ko jikinne?" wannan Maganar da tayi ce ta maido hankulan yan ɗakin kan su Hajiya Maryam tace itama ta lura don ta ɗauka jin zancen cikin zai sa ma ta wartsake, ganin duk sun zuba mata ido yasa tayi ɗan faffaɗan murmushi tace tana farinciki mana saidai ita a wurinta already tana da yara so bata jin wannan kamar a cikinta na farko, gaba ɗaya Maganar tayi masu daɗi Hajiya dake murmushi tace gaskiya ne Maganarta, Auntyn su Haisam ce tace ya kamata a barta ta huta sun zo suna ta surutu a kanta Mom tace abun farinciki ne ya samu dole ayi murna, tambayar likita Aunty tay in ba wata matsala zasu tafi da ita ta huta sosae yace eh lafiya lou zai bata magunguna saboda zazza6i da ciwon kan sai kuma na amai da take, bayan sun koma cikin Villa a ɗaki daban ta kwanta aka kawo mata abinci da ƙyar ta ɗan ci bayan ta gama Fatuu ta bata magunguna tasha ta buƙaci yin wanka Fatuu ta taimaka mata, bayan tayi wanka kwanciya tayi nan da nan bacci ya ɗauketa, a ranar iyalan cikin farinciki suka kasance koda aka sanar da Laila itama tayi murna har tana cewa wannan dole tazo ta dubata, Fatuu nata so ta sanar ma Gwaggo saidai ta baro wayarta a gida, anan suka wuni sai bayan Magrib suka shirya komawa gida Hajiya Maryam tace ma Fanan ita mi zai hana ta tsaya ta ɗan kwana biyu tunda ba sanin irin yanayin tayi ba zata fi samun kulawa anan tana murmushi tace ai sister Fatuu ta sani zata kula da ita tunda tana cikin hutu dole tayi shiru amman ba don taso Fanan ɗin ta tafi ba a lokacin, bayan sunyi sallama da kowa Haisam ya ɗaukko su a jigunannar Jeep ɗin shi da bai daɗe da siyanta ba ita kuma Motar Fanan aka barta anan, saida Hajiya Maryam ta rakasu bayan sun isa gidan haka tay ta faman faɗi ma Fanan ɗin abubuwan da zata kiyaye gudun kada cikin ya samu matsala tace ma Haisam aiki ma ta daina zuwa ta ɗauki hutu har zuwa ta ƙara warwarewa yace Ok, ta ƙara cewa abinci ma asata ta rinƙa ci akai akai koda tana amayar dashi wani zai tsaya nan ma yace mata to kafin ya sake cewa likita ma yace maganin daya bata zai sa ta daina yin aman ta rinƙa cin abinci sosae in ma baiyi mata ba akwae wanda Zarah tayi amfani dashi a Us yana da kyau sosae sai yasa akawo mata cikin nuna jin daɗi tace to daga baya tayi masu sallama kamar kar ta baro Fanan ɗin don gani take kaman cikin zai iya samun matsala haka dai ta taho Fatuu da Haisam suka yo mata rakiya ta tafi, bayan sun koma ciki gaba ɗayansu a bedroom ɗin Fanan suka zauna tana kwance su Esha sun zagaye ta, hira suka shiga yi cike da farinciki daga baya Fatuu ta tambayi ko tana son wani abu ta haɗa mata da sauri ta girgiza mata kai tace ai bata daɗe data ci abinci ba a Villa Fatun tace to bari ta kawo mata fruit ba tare data jira cewarta ba ta saukko daga gadon ta nufi ƙopa, bayan fitarta bin juna sukai da kallo ita da Haisam suna sakar ma juna ƙayaaccen murmushi, saida Fanan ɗin tayi bacci sannan Fatuu ta koma ɗakinta lokacin ta kira Gwaggo ta sanar mata samun cikin ai tana ji ta shiga yin hamdala cikin tsananin farinciki ta tambayi ina Fanan ɗin ta tayata murna da sannu da jiki tace tayi bacci Gwaggon tace to in Allah ya kaimu zata kira, bayan ta gama wayar da Gwaggo Aunty Mareeya da Feenah ta kira suma ta sanar masu kowa yayi farincikin jin zancen samun cikin suna ta addu'oin Allah ya inganta, daren ranar gaba ɗaya Fatuu da Haisam saida suka yi nafila tsakar dare suka gode ma Allah tare da Addu'ar Allah ya inganta masu cikin ya sauketa lafiya. Kulawa sosae suke ba Fanan ɗin ba laifi kuma maganin da take amfani dashi yana mata aiki don tana cin abinci, bayan hutun Fatuu ya ƙare tace ma Haisam ko yayi ma Mom magana a turo Iya ta dawo nan gidan tunda ita dattijuwa ce zata taimaka ma Fanan ɗin sosae yace Ok, koda akai ma Mom magana cewa tayi lafiya lou sai ta dawo nan ɗin, ana washe gari Fatuu zata tafi Iya ɗin ta dawo nan gidan hakan ya ƙara kwantar ma da Fatuu hankali da tana ta zullumin tafiya ta barta duk da suna da masu aiki har biyu amman tafi son ace akwae wani babba na jiki a tare da ita hakanne ma yasa tayi tunanin a maido Iya ɗin nan.

Kwance tashi cikin Fanan ɗin har ya fito kuma bata wani laulayi sosae don har ta koma aiki, lokacin da cikin ya kai wata takwas ne aka tabbatar da in aka bari ta haihu da kanta zata iya samun matsala don haka aka yanke yi mata Cs in ya kai wata tara, Hajiya Maryam na jin haka tace zata fitar da ita waje kawai ta haihu a can amman Fanan ɗin taƙi amincewa tace ko taje can duk abu ɗaya ne don anyi mata bayanin matsalar da ake hasashe ta kuma gamsu da hakan don saida aka yi mata duk binciken daya dace kafin a tabbatar kuma likitan da yayi mata binciken ƙwararre ne kuma shima da a ƙasar wajen yake aiki wato likitansu mai aiki Germany dole Hajiya Maryam ta ƙyale ta, bayan cikin ya shiga wata na tara kafin zuwa ranar da za'ayi su Fatuu duk cikin zullumi suke duk da Fanan ɗin lafiyarta lou, ana gobe za'ayi aikin ranar ta kama lahadi amman Fatuu bata iya ta koma Zaria ba, gaba ɗaya duk sun shiga damuwa suna ta Addu'oi a ranar kusan raba dare Fatuu da Haisam sukai suna nafilfilin roƙon Allah yasa ayi aikin lafiya itama Fanan ɗin ta yi ma kanta Addu'oin, har su twins Fatuu ta tada sukai Nafila suma sukai mata Addu'a, Washe gari Monday su Esha ƙin zuwa Makaranta sukai saboda aikin da za'ayi ma Mommynsu, misalin ƙarfe goma na safe aka shiga da ita aikin Fatuu harda ƙwallarta haka su Esha sauran yan'uwa ma duk suna a asibitin anata fatan nasara, Hajiya Maryam dai har bata iya magana saboda fargaba sai Addu'o'i take a cikin ranta, bayan an shiga da ita a Office ɗin Doctor ɗin wanda yake mai girma ne akwae kuma kujeru suka zazzauna kowa yayi jigum, bayan kamar minti arba'in da biyar da shiga aikin Doctor Taj wanda shine likitansu na Germany kuma shine yayi aikin ya shigo cikin office ɗin ai suna ganinshi duk suka mimmiƙe kusan gaba ɗaya suka haɗa baki wurin tambayarshi yadda ake ciki yana murmushi yace anyi aikin cikin nasara an fiddo mata da Baby Boy, zo kaga murna Haisam da Fatuu da Hajiya Maryam a tare suka duƙa sukai sujjada su Esha na ganin sun yi suma duk suka yi haka ma Farha da Jidderh, tura baki Esha tayi bayan ta gama yin sujjadar tace miyasa Momy ta haiho Baby Boy ita Baby Girl take so ta samu ƙanwa duk akai dariya akace tayi haƙuri in zata ƙara haihuwa in sha Allah zata haiho mata Baby Girl ɗin, Aunty ce ta kawo masu Babyn wanda ina gani na furta Ma sha Allah saboda tsananin kyaun shi sak Haisam ya biyo hakan yasa yay kama da yan biyun Fatuu sosae, sam bakunansu sun kasa rufuwa sai faman kar6a kar6ar Babyn ake, a ɗaki na musamman dake Amenity aka kwantar da Fanan din duk yan uwa sun cika shi itama Fanan ɗin idonta biyu tana amsa ya jiki da barkar da ake mata fuskarta ɗauke da murmushi, zuwa yamma duk yan'uwan da abokan arzuƙi anata zuwa dubata sai yaba Babyn ake, wuraren ƙarfe biyar Dad ɗinsu Haisam yazo tare da muƙarrabanshi suka dubata tare da yi ma Baby addu'a, kwananta biyu a Asibitin kafin aka sallameta suka koma gida, a ranar da suka koma da daddare lokacin su Esha sunyi bacci Fatuu ma ta koma part ɗinta sai Fanan ɗin tare da Iya babyn kuma na kwance cikin net yana bacci Haisam ya shigo jikinshi sanye da jallabiya, bayan sun gaisa da Iya ta miƙe don ta basu wuri, murmushi suka shiga sakar ma juna ya tambayi ya jikinta tace da sauki sosae ya jinjina kai kafin yace Allah ya ƙara mata lafiya ta amsa da Amin tay mashi godiya, juyawa yay yana kallon babyn ta cikin net ganin haka tace ko ta fiddo mashi shi ya girgiza mata kai alamar a'a, kallonta yay ya tambayi wane suna take son a saka mashi ne tace ai tayi zaton ma ya riga ya saka mashi suna ya ɗan girgiza mata kai kafin yace ya bari a sallameta sai ta za6ar mashi sunan da take so, shiru ta ɗanyi tana murmushi can tace mashi sunanshi take son a saka mashi wato Haisam, ɗan buɗa ido yay yana murmushi yace yayi tunanin zata saka mashi sunan Dad ɗinta ne tay shiru kafin tace "nafi son a saka mashi sunan ka Babe" ɗage mata gira yay ya tambayi saboda mi,

"Saboda ni a wurina sunan yafi kowane suna muhimmaci kuma shine sunan da ya cancanta a saka mashi, kayi man abubuwan alkhairi da yawa Babe, ka aure ni don ka faranta man sannan ka zauna dani tsawon lokaci ba tare dana haihu ba kuma daidai da rana ɗaya baka ta6a nuna man damuwarka ba ko kayi man wulaƙanci kaine ma kake ƙarfafa man gwuiwa kan hakan, kuma nasan ba don Allah ya ƙaddaro aure tsakaninka da Zarah ba na tabbatar zaka iya rayuwa dani a haka ba tare da ka ƙara aure ba kawai don farinciki na, kai na daban ne Babe, I know I can never repay you for everything you have done for me, amman ina son ka sani Babe ina son ka da kowanne bugun zuciyana sannan ina mai godiya a gareka mara iyaka Allah ya bar mu tare har abada, ina roƙon Allah ubangiji ya ƙara inganta rayuwar ka Babe ya dawwamar da kai a cikin farinciki ya saka maka da gidan aljanna maɗaukakiya..." ƙwallan da suka tarun mata a idanu ne suka fara zubowa tasa hannu tana gogewa, matsawa yay gabanta da yake a kishingiɗe take saboda aikin da aka mata ya kai hannu yana goge mata ƙwallan cikin cool voice ɗinshi yace mata ya isa haka shima yana matuƙar alfahari da ita sannan yana farinciki da Allah ya bata lafiya har ta haihu yayi Addu'ar Allah ya raya masu shi da sauran yaransu ta amsa da Amin ya Rabbi.

Saboda aikin da aka mata yasa aka ɗaga yin taron suna sai bayan sati biyu ita Fanan ɗin ma cewa tayi a bar taron ba sai anyi ba amman kowa ya nuna yana so, gaba ɗaya satin Fatuu bata samu komawa Zaria ba tana gida sunata zaman jego sai ranar lahadi ta tafi, hidima ba yar kaɗan ba Hajiya Maryam tayi ma jaririn don shima saida tayi mashi dozin ɗin akwatunan kaya sannan tayi ma Fanan kayan fitar suna ciki harda wata danƙareriyar sarƙar zinari ta miliyoyin kuɗi hatta Haisam da Fatuu ma saida tayi masu kayan fitar suna haka su twins ma tayi masu kayan fitar sunan sannan kowannen su ta siya mashi abunda yace yana so a Asibiti hatta Abie ta siyo mashi robobin ba yaro ruwa masu tsananin kyau yan ƙasar waje da zasu kai goma sannan Fatuu ma tasa an kawo mata Motar data bata itama mai jegon ta canza mata tsadaddiyar Mota, kowa yaji daɗin abunda tayi duk da haka kuma Haisam ma saida yayi masu kayan fitar sunan shima, waɗannan kayan fitar sunan dai ban tunanin za'a iya saka su gaba ɗaya ranar sunan don sunyi masu yawa, Ranar Alhamis Fatuu ta dawo nan suka shiga hidiman sunan da za'a yi ran Asabar a maimakon ranar litinin saboda ranar ta kama ta aiki duk mutane suna zuwa wurin aiki, Washe gari Juma'a su Gwaggo suka iso da Haulat da Husnah harda Aunty Mareeya da Feenah sosae Fanan da Fatuu suka ji daɗin zuwan nasu, a daren ranar sunan aka kira Haisam a waya cewa saƙon shanu daga Yola ya iso wanda Baffan Fatuu ne ya aiko mashi dashi a yanka ma yaro, har Fatuu bata san da aiken ba saida Haisam ya kirata a waya ya sanar mata aiko taji daɗin hakan da yayi sosae, Alhamdulillah Allah ya kawo mu ranar suna hidima ta kankama ba kama hannun yaro, a ranar da safe sai ga su Yadikko da Yaya da Mairo sun iso harda dawon furarsu mai uban yawa da kuma Nono sai zuma da ƙwai masu yawan gaske, zo kaga murna wurin su Aysha da Mino anga Mahaifiya, bayan sallar azahar gida ya fara cika da yan suna mai jego da Fatuu da kuma yaransu suna ta cin uban gayu, zuwa sallar la'asar taro yayi taro malam hidima data amsa hidiman manyan masu kuɗi ake har bansan ma ta yadda zan bayyana yadda hidiman ke wakana ba don abun na neman fin ƙarfin al'ƙalamina kawai sai na koma yar kallo, ina cikin kallon manyan Hajiyoyin Abuja dake ta zuwa kwatsam sai ga Hajiya Kubra wato Momy ta iso a Motarta harda iyalanta suma sun zo suna, ina hangota cikin Washe baki na nufeta muka gaisa nace ashe zata zo sunan cikin fara'ar ta tace man ai ita tana yin Fanan sosae dama tana cikin wanda suka damu da halin rashin haihuwarta lokacin data ji labarin haihuwar sosae tayi farinciki ta kuma yi godiya ga Allah dama ance shi maharƙuci tabbas mawadaci ne nace wannan gaskiya ne Momy Allah ya ƙara mana haƙuri da kuma dangana ta amsa da Amin kafin suka shiga ciki ni kuma naci gaba da baza idanu ina ganin danƙara ɗanƙaran, jibga jibgan Motoci masu numfashi dake ta sawo kai cikin harabar yayin da wasu kuma ke tafiya, a taƙaice dai Abuja ce ta haɗu a gidan Haisam don First lady na nan da sauran matan muƙarraban shugaban ƙasa. Alhamdulillah taro ya tashi lafiya yaro yaci sunan Haisam suna ce mashi Junior, an ci an sha anyi wadaƙa da nishaɗi sannan an raba kayan suna masu ɗauke da sunan Baby kawai ba'a saka hoton shi ba, a bangaren maijego Fanan ta samu kayan suna kai kace zata buɗe ƙaton shago ne ita kanta saida tayi mamakin kayan da aka tara mata, a daren ranar su Fatuu da Farha harda Aunty Mareeya suka shirya kayan kafin su kwanta, Washe gari Lahadi yan Katsina da Yola suka koma duk an cikasu da abubuwan arzuƙi, haka sauran yan'uwan su Haisam yan Katsina da Daura da suka sauka a Villa duk suma sun tafi, Fatuu ma taso tafiya Zaria a ranar saidai da sauran abubuwan da zatayi a gidan dole ta bari sai gobe da sassafe sai ta koma, kusan raba kayan da Fanan ta samu nata tayi taba Fatuu duk yadda taso taƙi kar6a Fanan ɗin ta kafe, har rage kayan tayi ta maida mata wasu amman taƙi kar6a ƙarshe ma sai ta nuna mata 6acin ranta sosae hakan yasa dole ta amsa tayi mata godiya da kuma Addu'oi.

*BAYAN SHEKARU BIYAR*

Abubuwa da yawa sun faru a cikin waɗannan shekarun daga ciki abu na farko daya faru shine saukar President Ali Adamu daga kujerar mulki tuni kuma wata sabuwar gwamnatin ta hau, a lokacin daya sauka al'umma sunyi kukan rashin jajirtacce kuma nagartaccen shugaban ƙasa, bayan saukar shi Katsina suka koma da zama a gidansu dake G.r.a a lokacin tsohuwa mai ran ƙarfe wato Hajiyar sanata ta koma gidanta da zama saidai bana dundun dundun bane zo kaga murna a wurin yan unguwa karma Tk yaji, Saude da har zata dawo Hajiyar ta hana tace ai ba daɗewa zatayi ba tunda ga matar tukur nan lafiya lou tayi zamanta a ɗakin mijinta, shekara guda sukai a Katsina kafin suka koma Abuja.

Bayan saukar shi da shekara ɗaya Fatuu kuma ta gama karatunta cikin nasara har ta fara aiki bayan shekaru biyu da fara yin aikin nata ne ta ƙara haihuwar yan biyu duk mata an saka masu Khadija da kuma Fateema wato sunan Gwaggo da kuma Mom ɗin su Haisam, Esha tayi murna kamar kamar me da samun ƙanne mata, a lokacin wasu sun ƙara haihu wasu kuma nada ciki, a cikin wanda suka ƙara haihuwa harda Jidderh da kuma Fauzy ta ƙara haihuwar Namiji an saka mashi sunan mahaifin Sameer wato Bello, Aysha ma ƙanwar Mino a lokacin tayi haihuwarta ta farko ta haiho Baby girl an saka mata sunan Yadikko wato Jameela, Mino dai har lokacin bata ƙara haihuwa ba don tace ba yanzu ba bata manta kwakwar data ci ba ansamu dai ta amince zata ƙara yaronta yanzu shekararshi shidda, Farha ma ta ƙara haiho Namiji an saka mashi sunan Mahaifinsu wato Muhammad, Haulat ma ta ƙara haihuwar Namiji an saka mashi sunan mahaifinta wato ishaq, a bangaren Fanan kuwa ita bata ƙara samun cikin ba tun bayan Haisam Junior wanda yanzu shekararshi biyar da yan watanni, duk a cikin lokacin akai ma wasu aure ciki harda Yasmeen ƙanwarsu Haisam ta auri yaron Yayan Mahaifiyarta na Qatar mai suna Abdurrahman suna zaune a can ƙasar haka ƙanin Sameer wato Ashraf shi kuma ya auri Jahad itama ɗiyar yayansu ɗin na Qatar suna a Abuja zaune burin su Mom ya cika na son haɗa yaransu auren zumunci.

A bangaren Haisam kuwa tuni Kamfaninshi ya ƙara ha6aka sosae yanzu ana ƙera wasu abubuwan ba iya kwamfutoci ba yanzu harda su Tv da kuma wayoyi, a lokacin arzuƙin shi ya ƙaru sosae don har ya ƙara buɗe wasu rassa na Kamfaninshi a Lagos, PortHarcourt, Kano da kuma Sokoto yana da kuma burin ƙara buɗewa a wasu States ɗin in Allah ya yarda, a yanzu Haisam ya zama Billionaire wanda yana ɗaya daga cikin Manyan masu kuɗin ƙasa don har private jet ya mallaka wato jirgin kanshi wanda ake hidimar iyalinshi da kuma Kamfanoninshi, daga baya aka fara yin hayar jirgin ganin akwae riba yasa Haisam ɗin yayi ma Dad dinshi Magana kan su haɗa su sayi wani jirgin na haya ya amince da hakan koda Sameer yaji zancen siyan jirgin hayar shima sai ya nuna yana ra'ayin saka hannun jari haka Hajiya Maryam ma dama duk suna da hannayen jari a Kamfanin shi na Technology, daga baya suka buɗe kamfanin sufurin jirage mai suna HaiFat Air wanda a yanzu suke da jirage guda ukku biyu manya wanda har yan Hajji ake kaiwa dasu sai ɗaya ƙarami wato private jet suma jiragen suna niyyar ƙara wasu da yardar Allah, A cikin shekaru biyar ɗin nan a duk shekara Haisam sai ya kai wasu a cikin dangi Makka, a shekarar farko daya fara kai mutane makka ne yace ma Fatuu ta bada mutum biyu cikin danginta ta bada sunan Gwaggo da kuma Kawu Amadu su Gwaggo za'a sake sauke farali sosae tayi farinciki, Hajiya na jin zancen tafiyar Amadu Hajji itama ta biya ma Tukur wato Tk Har Haisam yace ta bari shekara mai zuwa zai biya mashi tace ai shida Amadu kamar yan biyu suke bai ga ko aure tare sukai ba ya bari ta biya mashi ai duk ɗaya ne, da wata shekara ta zagayo ya sake cewa ta bada mutum biyu sai ta bada Yaya da kuma kishiyarta Mairo sannan ita kuma da kuɗinta ta biya ma Aminiyarta Haulat, da rabon dai Fatuu ita zata kai Yaya Makka a lokacin ƙurucyarta ta ta6a ce ma Haisam in ta girma tayi kuɗi zata kai kowa Makka amman banda Yaya saboda ta tsaneta har yayi mata Nasiha kan muhimmancin yafiya, Sosae su Mero sukai farincikin biya masu Makka saidai ita Yaya akwae abunda ke damunta a cikin rai shine hakkin Mahaifiyar Baffan su Fatuu dake a kanta don tun Maganar da Mero ta ta6a yi mata a Abuja kan hakan bata manta ba, ƙarshe samun Mairo tayi ɗakinta cike da damuwa tace mata ita tana tsoron taje tayi aikin Hajjin Allah yaƙi kar6a saboda hakkin A'isha dake kanta, shawara Mairo ta bata kan taje ta samu Baffansu Fatuu ta roƙe shi yafiya ta roƙeta kan ta rakata, tare suka iske Mahaifinsu Fatuu a bangarenshi wanda yanzu ya koma babban falo da Bedroom da suka sha kayan alatu don Haisam ya bashi kuɗi masu yawa Fatuu ma ta ƙara mashi an gyara part ɗin nasu ya koma babban Flat saida aka ƙara faɗaɗa shi, sauran bangarorin ma anyi gyare gyare don yanzu gaba ɗayan tsakar gidan siminti ne ko ina sannan an zagaye gidan da katangar bulon siminti haka gaban gidan ma ya koma irin na yan birni harda gate, fadar da Baffa ke zama itama ta koma irin ta zamani, bayan sun zauna anyi gaishe gaishe shiru Yaya tayi ta rasa ta ina zata fara sai Mairo ce ta fara magana tace mashi dama Yaya ce tazo neman yafiya a wurinshi kan abubuwan da suka faru a baya ta juya kan Yaya tace tayi magana, cikin karyayyar murya ta shiga roƙonshi akan abubuwan data yi masu a baya ta bayyana mashi ta zalunci mahaifiyarshi don ita tayi mata asiri duk gidan aka tsaneta harda arɗo wannan ne yay silar ta kamu da ciwon zuciya har ta mutu haka shima tay ta zaluntar shi bayan rasuwarta ganin arɗo ya damu dashi shima tayi mashi asiri ya daina ji da shi sai bayan daya girma ne da yake shi mai yawan ibada ne sosae sai ya zama ko tayi asirin bai kamashi hakan yasa soyyyarshi ta dawo ma arɗo sai kuma ta rinƙa yi mashi makirci haka iyalinshi ma ta ɗauki karan tsana ta ɗaura masu, shiru Baffa yayi kan shi a ƙasa yayinda ƙwaƙwalwarshi ta shiga dawo mashi da lokacin don bazai ta6a mantawa da irin rayuwar ƙuncin da mahaifiyarshi tayi ba a gidan lokacin yanada ƙuruciya har zuwa mutuwarta lokacin haka ya rinƙa kuka yana roƙon shima Allah yasa ya mutu ya bita, kawai saboda yana da haƙuri sosae da kuma kawaici irin na fulani yasa bai nuna masu komai amman ba wai don ya manta ba, saukkowa Yaya tayi kan carpet ta duƙa cikin kuka ta shiga bashi haƙuri tana mashi magiyar ya yafe mata, Mairo ce da idanunta suka ciko da ƙwalla cikin kwantar da murya ta shiga roƙonshi ya yafe mata Don Allah duk irin abunda tayi mashi gashi nan bai hana rayuwarshi yin albarka ba ƙarshe ma gaba ɗayansu sun koma karkashin kulawarshi yayi koyi da mai sunan shi wato manzon Allah (S.A.W) wanda haƙuri da yafiya halin shi ne, ɗagowa yay idanunshi sun yi ja sun cika da ƙwalla cikin karyayyar murya yace shikenan ya yafe mata sai taita istigfari ta roƙi Allah ya yafe mata abunda tayi ma Mahaifiyar shi, godiya sosae ta shiga yi mashi fuska jage jage harda su majina ta shiga yi ma Mahaifiyar tashi Addu'o'i a hankali yake amsawa daga baya suka tafi, bayan tafiyarsu kuka sosae ya shiga yi yana tunawa da mahaifiyarshi tare da yi mata Addu'a, bayan Yaya ta koma ɗaki saida ta kira Fatuu a waya itama ta roƙeta yafiya kan abubuwan da tayi mata na tsanarta da tayi tana murmushi tace mata ba komai ai ya riga ya wuce ta yafe mata taita mata godiya da Addu'oi, sai lokacin Yaya taji hankalinta ya ɗan kwanta da tafiya Hajjin da zatayi tun daga ranar kullum da cazhaba zaka ganta tana ta istigfari.

Ta dalilin Fatuu yanzu yan ƙauyansu suna karatun boko sosae, a gidansu ma an daina yi ma mata auren wuri sai sunyi boko har Abuja yan'uwan nasu suke zuwa hutu wurinsu inda rabo ƙilan wasu su ƙara samun mazaje a can. A can Katsina yanzu Foundation ɗin su Fatuu ya ha6aka sosae anata taimakon mutane yanzu a unguwarsu Gwaggo ita ta koma matsayin Hajiyar Sanata sosae take taimakon Makwabtanta, rayuwa dai ta inganta ga dukkan bangarorin. Ta dalilin Addu'oin da wanda Haisam ke kaiwa Hajji ke mashi sosae hakan yake ƙara ha6aka arzukin shi wanda yanzu shi kanshi Haisam ɗin bai sai iya adadin dukiyarshi ba har gida ya gina ma Abbas ya kuma kaishi Makka harda Feenah sannan ya ɗauki nauyin karatun Abdul wanda yanzu ya girma, a bangaren Aunty Mareeya itama Sameer ya gina masu babban gida har sun koma kuma duk sunje Hajji suma. Bayan wani lokaci Haisam yasa aka fara gina ma su Fatuu Asibiti anan Abuja wato private Hospital ita da Fanan wanda aka yanke saka mashi HAIFAT SPECIALISTS HOSPITAL sai fatan Allah yasa a gama lafiya a kuma buɗeshi lafiya yasa kuma mutane su amfana, Amin.

Fatuu zaune a gaban madubi da daddare tana yin shafa bayan ta fito daga wanka yayin da Haisam ke zaune a saman gadonta ya ɗaura Laptop a saman table ɗin gaban gado yana daddanawa da alama wani aikin yake jikinshi sanye da robe haka idanunshi na sanye cikin glass ya ƙara manyanta saidai duk da haka ba sosae jikinshi ya nuna ba saboda har yanzu yana motsa jiki sosae, kamar an jefo Esha ta faɗo cikin ɗakin tana ƙwala ma Fatuu kira tana faɗin "Auntyyy!" itama yanzu ta ƙara girma don tana shekara ta sha huɗu duk da bata da tsawo sosae sak irin jikin Fatuu tana yarinya gareta,

"Esha! Wai sai yaushe zaki hankali ne, didn't i warn you to always say salaam before entering into a place???" a fusace Fatuu tay mata Maganar ta ɗaure fuska, tura baki Esha ɗin tayi tana ɗan murmushi tare da noƙe kai tace "to Sorry Aunty mantawa nike bari inje inyi salaam ɗin" tayi maganar tare da juyawa ta nufi kopa, bayan ta fita daddagewa tayi ta kwaɗa wata uwar sallama har saida Haisam ya ɗan yamutsa fuska Fatuu kuma ta girgiza kai kafin tace wani abu Esha ɗin ta ƙara kware baki ta rafko wato sallamar tare da faɗin "Aunty in shigo???" ba arzuƙi gudun ta sake yin wata da sauri Fatun tace mata ta shigo, shigowa tayi tana dariya Fatuu ta wurga mata harara, bayan tazo gabanta tace mata miya kawota ɗakinta yanzu cikin zazzaƙar muryarta tace "Momy ce tace ki bata charger ɗin phone en ki in baki using dashi mun shanye mata caji zata saka nata ya ƙiya kafin tomorrow Dad ya kawo mata wani" yadda kasan abun faɗa yadda tayi Maganar, maida kanta tayi kan madubi tana cigaba da shafar ta tace mata gata can jikin socket wurin bedside drawer taje ta ɗauka, maimakon taje ta ɗaukan sai ta tsaya tana kallon fuskar Fatun ta cikin madubi tana wani murmushi tace "Aunty Daddy kike ma makeup?" dakatawa Fatuu tay ta watsa mata harara, dariya Esha ɗin tayi tace "ai nasan Dad kike mawa don ke Babynshi ce....." tsawa Fatun ta daka mata "Esha! Will you go and take the charger ko zaki tsaya kina surutun banza ne!!" da sauri ta wuce tana dariya, tana zuwa saitin Haisam ta furta "My lovely Dad" dagowa yay ya kalleta yay mata murmushi tare da miƙa mata hannu suka kashe yace taje ta ɗauki charger din ana jiranta tace to, bayan ta ɗauko cazar ta nufi hanyar fita, har ta kusa fita ta tsaya da ƙarfi ta furta "Babyn Daddy kin yi kyau...." robar mai Fatuu ta wawuro Esha na ganin haka ta fice da gudu tana dariya, tsoki Fatuu tayi tare da girgiza kai idonta akan madubi ta furta "i think Aisha needs to see a psychiatrist gaskiya" murmushi Haisam yay ba tare daya kalleta ba can idonshi akan screen ɗin kwamfuta yace mata saboda mi, juyawa tay da sauri ta kalleshi tace "baka ga yadda take behaving abnormal bane, wataƙil in aka kaita aka binciki ƙwalwarta aga tana da problem",

"An yi maki hakan ne?" Haisam daya ɗago yana kallonta ya furta, da alamun rashin fahimta tace to ita akan mi za'a kaita wurin likitan kwakwalwa, yana murmushi yace saboda da tana kamarta itama tana buƙatar hakan amman ba'a kaita ba to don haka itama ba sai an kaita ba zata bari ne kuma in ma tana tunanin tana da matsalar kwakwalwa to ita tata matsalar da tana yarinya ta linka tata tunda ita Esha har yanzu bata fasa ma wani glass ɗin Mota ba, waro ido Fatuu tay jin abunda yace ta bishi da kallon mamaki bakinta a ɗan buɗe shi kuma sai murmushi yake, da alamun mamaki ta furta "kana son kace nayi hauka lokacin?" ɗan ƙanƙance ido yay cike da tsokana ya furta kusan hakane, ƙara zaro ido tay ya shiga yi mata faffaɗan murmushi can ta miƙe a fusace ta nufe shi, lokacin data tashi har saida alƙalamina ya kusa su6ucewa ganin irin haɗaɗɗar rigar baccin dake jikinta gaba ɗaya ta fito da dirinta na babbar mace yar 30s tana tafiya ko ina na jikinta na amsawa abun saidai ace tubarkalla, tana zuwa gaba ɗaya ta faɗa jikinshi har saida yay ɗan sautin zafi batai wata wata ba ta hau bugunshi saidai bugun yafi kama da a kirashi dana soyayya, haƙuri ya fara bata yanata dariya har haƙuranshi sun bayyana cike da shagwa6a data riga ta zame mata jiki ta shiga faɗin Allah bata yin haƙurin tunda ya kirata da mahaukaciya yana ta dariya yace shifa bai ce mata haka ba itace ta kira kanta da haka, cigaba da bugun nashi tayi tana faɗin ai haka yake nufi ko yace to tayi haƙuri taga ƙopa a buɗe take amman taƙi bari aikuwa ya nuna mata ƙarfi ya burkice da ita ta yadda ko ƙwaƙkwaran motsi bata iya yi, ɗaure mata fuska yay yace tunda abun yar haka ce ya bata haƙuri taƙi to shima ya warware yarjejeniyar dake tsakaninsu ta glass, tana ɗan nishin nauyi tayi murmushi tace ai yanzu ba wannan yarjejeniyar tunda tayi abunda yace a lokacin, fuskarshi a daure yace shi ba ruwan shi sai ta biya shi, ɗage mashi gira tayi tace in don dai miliyan goma yanzun nan zata biya shi ya ɗaga ta, girgiza mata kai yay yace ba kuɗi yake so ba ta kanne mashi ido tace to mi yake so, ce mata yay yara zata haifa mashi yawan hakan yanzu tayi biyar saura biyar kuma a lokaci ɗaya yake son ta haiho mashi yan biyar, bata san lokacin data ƙyalƙyace da dariya ba tace kawai yace mata ya gaji da ita so yake ta mutu in ba haka ba taya zata haifi yara har biyar, still fuskar shi a ɗaure take yace ai ana haihuwan har ma fin hakan tana dariya tace ta sani amman ita dai bata iyawa yayi haƙuri yace bazai yi ba sai ta ƙara mashi yara biyar lokaci guda, lumshe mashi ido tay tace yafi ƙarfin hakan a wurinta don haka indai ya bata yara biyar ɗin to zatayi ƙoƙari ta haifa mashi, jin abunda tace yasashi sakin murmushi itama shi take mashi ya mirgina gefenta suka shiga bin juna da wani irin azababben kallo mai cike da tsagwaron ƙauna can Fatun ta saki yar ajiyar zuciya ta fara magana,

"Thank you Hubby, Thank you for your support and guidance. You didn't just change my life, you became a part of it and loved me unconditionally. You have shown me what true is.Thank you for choosing me to be your life partner. You are truly my best friend and my soulmate, and I couldn't imagine my life without you. Thank you from the bottom of my heart for everything that you have done for me......"

( Nagode Hubby, Nagode da taimakon ka da jagorancinka a gare ni, ba wai kawai ka canza rayuwata ba, ka zama wani bangare a cikinta kuma ka so ni so mara iyaka, ka nuna man mene ne soyayya ta gaskiya. Na gode da za6ata a matsayin abokiyar rayuwarka. Haƙika kai ne babban abokina kuma abokin ruhina sannan bana iya tunanin rayuwa ba
tare da kai ba, Ina mai matuƙar godiya a gareka daga can ƙasan zuciyata akan duk abin da ka yi min....." muryarta ce ta karye hawaye suka shiga gangaro mata, matsar da fuskarshi yay saitin tata ya shiga kissing hawayen kafin can ƙasan maƙoshi yace shima yana godiya a gareta sosae data saka shi yake jin yafi kowane namiji sa'ar mata a duniya, haɗe fuskokinsu yay inhaling each others breathe, ganin yana ƙoƙarin hade lips ɗinsu da sauri ta ankarar dashi ƙopa a buɗe take hakan ya sashi dakatawa, saukkowa yay don yaje ya rufe a lokacin nima naga ya dace na bar masu cikin ɗakin.

*Alhamdulillah!* *Alhamdulillah!!* *Alhamdulillah!!!💃💃💃💃💃💃💃*

*A nan na kawo karshen littafin A Sanadin Makwabtaka wanda na ɗau lokaci ina rubutawa😍*

_Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah subhanahu wata'ala, the Most Compassionate, the Most Omnipotent and the Most Omniscient da ya bani ikon kammalawa cikin ƙoshin lpy kamar yadda na fara, to him be all the glory🙏, tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi muhammad(S.A.W) da Ahalinsa da Sahabbansa baki ɗaya😍, Darussan dake ciki Allah ubangiji yasa mu amfana dasu🙏 ya sadar da ladan gareni da mahaifana da zuri'ata, yan'uwana da malamai na, kura kuren ciki ina roƙon Allah ubangiji ya yafe man Alfamar Annabin rahama (S.A.W)🙏_

_Gaisuwar ban girma ga Mahaifiyata Hajiya Rabi'atu Yahaya, she is my first luv and my everything💘,Allah ya ja da rai ya ƙara maki lafiya my sweetheart😘, My beloved Siblings💞waɗanda littafin nan Sadaukarwa ne a garesu, Nafisat, Aisha, Khadija, Maimunatu, Hafsat, Abdul'azeez, Fatima, Maryam, Ameenatu, I luv you so so much, kune ni, in baku bani, I really appreaciate ur Encouragement💪,prayers and all-round support👍, Allah ya kara haɗa kawunanmu ya jiƙan Mahaifinmu, Ameen_

_Gratitude To my Sweetheart😍, who is ever glad at every inch of my progress, I really appreaciate ur Support, Encouragement and prayers, Allah ya bar mu tare ya ƙara daukaka, Amin_.

_Special thanks to My lovely Sis Hafsat Bature Writer Of Abban Sojoji and Kurkukun Ƙaddara na gode da ƙarfafa man Gwuiwa Allah ya baki ikon Kammala naki cikin ƙoshin Lafiya yasa ya amfani al'umma Amin, Abubakar Sadeeq AlQuramy, Uncle Isma'il ina matuƙar godiya a gareku da taimakon da kuka bani Allah ya ƙara taimakon ku a dukkan Al'amuran rayuwar ku🙏, My P.A Munah Bature sannu da ƙokari Allah ya ƙara ma rayuwar ki Albarka ya kawo miji nagari Amin, ina matuƙar godiya agareki😘_

*To My Novel's Fans*

*Ina matuƙar godiya a gareku musamman waɗanda suka saka kuɗin su suka sayi littafin nan ina roƙon Allah ya ƙara arzuƙi yasa ku amfana da littafin, Members Of Comment Section na gode da ƙaunarku da uzurinku a gareni kamar su, Asma'u sani, Asma'u Kebbi, Bajatu, Bahillot, Dr Hamida Gandi, Mrs Mu'utassim, Sofix, Minat Sgy, Shafa Adill, Zeefakhad Collecion, MaryamSalisu, Rababs222, Angel love, A'isha Abdurrahman, Fadeelamande, Queen, Shafar Dauran, Aunty wasee, Amina Sulaiman, Habibty, Aunty Hadiza, Aunty Sa'adatu, Salma Nijar, Fatima Fannami, Hauwaabubakar, First Lady, Maman Amir, Ummulkhairi Nijar, Satheyer, Maman Naeem, Deejarh da sauran waɗanda bansamu na lissafo sunayensu ba, ina sane daku, ina matuƙar godiya a gareku ur comment means a lot to me, bansan da wane kalmomi zanyi amfani wurin gode maku ba, sai dae ince Allah ya barmu tare don ku ɗin kun wuce fans kun zama yan'uwa agareni,*

*Ina Gwanar wata ga tawa💃😍 Jinjina a gareki Hajiya Kubrah (Momy) Mace mai irin halin Hajiyar Sanata, Allah ya ƙaro mana irin ku acikin al'umma, har bansan da wane irin kalmomi zanyi godiya a gareki ba sai dai kawai ince Allah ya ƙara girma da ɗaukaka ya raya maki zuriya ya ƙara danƙon kauna keda Oga yasa afi haka ya kuma sa a gama da Duniyar nan lafiya, ya bar mana zumunci daga nan har Aljanna, Amin ya Hayyu ya Ƙayyum🙏*

*Ban mance da irin gudunmawar da kika bani ba Miss Walida Ɗanwaire Fulanin Yola ina matuƙar Godiya a gareki Allah ya barki da Oga ya raya Baby Maryam, Maman Afra kema ban mance da irin taki gudunmawar ba ina miƙo godiya lodi lodi Allah ya raya zuri'a ya bar ƙauna keda Oga, ya jiƙan Habiba (Ummy), Amin ya Rabbi, haka ban mance da taki gudunmawar ba wato Nabila Yar Gata Fulanin Daura kema Allah ya bar ƙauna keda Oga ya baku zuriya ɗayyiba*

*Allah Ya bar mana zumunci daga nan har Gidan Aljanna, Allah Yabiya maku dukkan buƙatunku, Allah ya baku ikon Yin amfani da darussan dake acikin Labarin nan, Ina matuƙar godiya Da irin haƙurin da kuka yi da kuma uzirin da kukayi mun har Allah ya bani Ikon Kammala Littafin nan, Yanzu gashi komai Ya wuce no more kiran ayi man uzuri, lols😂*

*Littafin nan Ya ƙunshi darussa daban daban Na rayuwa,Ya ilmantar,Ya faɗakar,Ya kuma nishaɗantar, Manyan darussan cikin shi sune Muhimmacin Haƙuri da kuma Taimako wanda gaba ɗaya labarin ya ginu ne akan hakan💃💃💃*

  
*Taku Mai ƙaunarku da zuciya ɗaya, ZAINAB BATURE (Zee Laluh/Oum Imam).*

*Ga mai buƙatar wannan littafin Complete tun daga na ɗaya har zuwa na ukku sai ya tuntu6i ɗaya daga cikin waɗannan lambobin wayar, 09013804524 ko 08169856268.

 

 

  

  

 

  

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.