Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Cinikin_Rai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 12 of 29
Wani taro da aka yi na siyasa ta hadu da Mr Amjad, sakamakon sakata da wani dan majalisa yayi tayiwa wani mutum barazana, a inda ake taron. Haka yarinyar nan ta ratsa cikin mutane, ta riko wuyar dan siyasan.nan, ta ce zata kashe shi ta kuma jin ya soki lamirin wancan mutumin, wannan abin da tayi ya saka Amjad nimanta..ya kuma fara kashe mata kudi domin kudirin dake ransa.
Tare da bata shawaran tayi karatu domin zata ci gajiyar iliminta. Dakyar da sudin goshi ta gama, domin sai da Ammy da Inna suka yi tsaye akanta, shima ta gama da uban CO, a lokacin ita kanta tayi namijin kokari, take fada amma tabbas rayuwar da take bashi ne mafarkinta ba, mafarkinta yana can wani wurin.
*Present*
After 13 back.
"Dr Saddikah ba za a iya aikin ba ne yanzu? Yarinyar nan tana wahala, idan ta cigaba da zama haka zamu iya rasata!" Inji Ammyy.
"Ba aikin bane wahala, ana yin aikin ne a garin Michigan state, sune kawai suke da alhakin tab'a kanta, anan kuma ana yi a Menk Jordan World cares, shi daya ne s faɗin ƙasar nan, idan aka ce za ayi mata aikin ana bukatar miliyoyin kuɗi ne."
Shiru suka yi, abin da yazo ran Ammyn gidan da suke zaune, a sayar da shi kadai a mata jinya, ta kare gidan na tsawon shekaru da amana, sai ta tashi za aji ta bakinta.
----
Amjad.
Kiran wayar shi MD yayi ya ce mishi.
"Yallabai yarinyar nan tana samun takun saka da sabuwar yar sanda da aka kawo, me zamu iya mata?" Tsaki yayi ya ce.
"Kaji shaidaniyar yarinya ba, don Allah ka saka min idanu akanta, zata lalata min shirina ni da nake son a wanke min ita."
"An gama yallabai " ya kashe wayar, yana wurgi da ita, kafin ya mike yana me leka waje. Ko sati biyu bai yi da fara kwana a cikin gidanshi ba, tsabagen tsoron Malik Menk Jordan.
Sake labule yayi ya rufe yana ajiyar zuciya , kafin ya nufi uwar dakinshi.
***
Lalla Salmah.
Zaune suke suna cin abinci, kallon yarta tayi a nutse kafin ta ce mata.
"Princess, yau zan tafi ganawa da Malik Menk Jordan." Sake spoon din hannunta tai, tare da ware idanunta.
"Maama da gaske? Zan bi ki please"
Girgiza kai tayi, tana faÉ—in. "Zan so haka, amma haduwar mu ba zai min kyau ba, shi mutum ne da baya bukatar ba zata, yana bukatar a sanar mishi kome kafin ya iso gare shi."
Kwabe fuska tayi tana faÉ—in. "But me yasa?" "Ki shirya next week zaki tafi Demark wurin su Wahiba da Wahida, tare da Nadrah, ki kame kanki bana son zubda aji, ka da ki manta Nadrah Khamis Shatima har an saka ranar baikonsu da Malik yayi rejected É—inta, and Malik yana bukatar macen da zata kula da Wahiba da Wahida ne, so ki kula da su. Domin mu samu Malik duk abin da kika yi matukar me kyau ne, zasu gayawa Malik. Kada ki sake Nadrah Khamis Shatima ta rena ki, kin ji ai? Domin Elbashir ya gaya min saura three months su gama karatu, and na shirya miki wani course na musamman, idan kuka dawo zaku sauka a gidan Malik ne, kada ki manta Malik yana cikin jerin members na PEL, na Europe. Iya wannan kawai aka ce ya mutu ya bar miki me kike tunani? And ki san yadda zaki nemi digital dinsa. Da zafi zafi ake dukan karfe. Babban burina na auri Malik na mamaye shi, amma samunki ya rufe min mafarkina, idan kika shiga zan miki bayanin yadda zaki yi da kowa........
#MaidaLalla
#Nadrahshatima
#Zeenobiahadejia
#Malikmenkjordan
[8/28, 6:46 AM] Mmn Khaleel: CINIKIN RAI....8
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>
Don kar abin ya tsaya a ran yaran, ya mike tana karkad'e jikinshi ya ce musu.
“Babu abin da ya faru, kawai sun min haka ne don ban biya su kudinsu ne, amma nasan babu abin da zai kuma faruwa, In sha Allah." Ya fada yana kokarin goge bakinsa. Domin baya so su fahimci hakan a matsayin zalunci, baya kaunar zalinci kuma ba zai yarda na kusa da shi yayi ba. Da wannan suka tattara sauran yan kudadensu, suka koma gida.
-----
Malik.
Shigowa wasu kartin maza suka yi, suka tsaya tare da ƙamewa, "Mene ne labari?" "Mun share duk wani shaida da yan sanda zasu yi Investigation akai, babu wani alama domin mun rufe tarihinsu." Ajiye pen din yayi ya koma da baya, yana me jingina da kujeran da yake kai, yana wani irin murmushi tare da juyawa da kujeranshi.
"How dare zasu bude min wani kasuwanci? Bayan ina nan a raye? Duk wanda zai bude wani kasuwanci dole yazo ya lashe kafata. I'm the only king bana buƙatar gasa da takara. Duk wanda ya taba min dukiyata a aika min shi in da aba dawowa."
Murmushi bakidaya wannan shine Kasuwancinsu, a kashe ko a raya su suke da ra'ayi da yadda zasu yi, shi yasa daga su har Malik din dukiyarshi yake kara habbaka. Hahawan rashin mutuncin da yake wakana a tsakaninsu da kananun yan kasuwa, ya kara kuntatta mutane. Gashi wani abin takaici duk abin da yake faruwa gwamnati bata da ikon magana, tow ai mutanen da zasu yi magana sune a jikin Malik, akwai wanda ya isa yayi magana ne? Babu kuwa.
----
Washi gari.
Mutanen Wasim sun sake dawowa, kuma dama wannan shi ne, fatan Zeeno kenan kuma sun dawo din, saman kwanon rumfar shi ta hau idan ka yadda yarinyar nan take makale a jikin rumfar sai tsoro ya kama ka, amma kuma haka bai sakata jin ko dar ba, duwatsun da ta tara a cikin jakar fata, take cirowa a hankali taja dankon ta sake shi da ƙarfi. Sai dai mutum ya ji "Kul!" Tare da ihu me karfi suke sakawa, tsayawa tayi, ganin suna nimanta, sai bata kuma Harbin ba, incredible kawai sai da ta bari sun sake har suna yiwa mutumin farkon fada, kawai yarinyar nan tayi ta sake musu, babu kakkaunatawa. Baki daya ta hana su sakat. Sai da ta buwaye su ta zame musu alakakai kamar, daga sama suke jin al'amarin Harbin, babu shiri suka juya da gudu suka bar bakin ruwan, sai da suka tafi sannan ta sauko daga saman rumfar. "Abba basu kuma dawowa." Ta fada tana kallon, tana kallon shi, rike da dankon. Karba yayi ya boye. "Zeeno me yasa kika yi haka? Babu kyau kar ki kuma yin haka." Gyada kai tayi, ganin haka ya rufe shagon suka bar wurin. Ko da isa gida yana shiga suka rufe kofar. "Maman Abbas, kin ga yar nan da zuciya yau kore min mutanen Wasim tayi, yanzu ban san ya zan yi ba."
"Mun nime Allah ya kawo mana iyakarsu, sai Allah ya bamu ita don haka babu abin da zance sai Alhamdulillahi." Ta zaunar da Zeeno ta zuba mata abinci. Kadan taci ta tsame hannunta, tana faÉ—in. "Ina Abbas?" Kallon dakin tayi kafin ta ce mata. "Yana barci" gyada kai tayi. Ta mike ta kai sauran abincin dakin girki. Sannan ta wuce dakin Ammyn Abbas ta kwanta.
Washi gari da suka fito bakin ruwa, sun sami Wasim da mutanen shi. "Wani dan shegiyar ne ya jefi mutane na?" Maida Zeeno baya Alhaji Badaru yayi, zai tura ta gida. "Waye ya daki mutane na?" "Ni ce!" Ta fada da karamin murya. Bud'a mata hanyar aka yi, kanta a kasa, kafarta da babu takalmi tana wasa da ƙasa. "Ke!" Ko gizau bata yi ba, ta maida hannunta baya, tana rike da karfen rodin da ta dauka bayan Alhaji Badaru Daniyal ya maida ta baya, tana wasa da ƙafarta. "Kai dauko min wancan yar hanji!" A yadda ya ganta ya zata irin yaran nan ne masu shegen baki da tsoro, lokacin da ya iso sai da ya duka ya ce mata. "Yarinya wasa kike ko da gaske!" Kamar wacce wani abu ya shiga jikinta, ba tare da ta bude idanu ba, ta kaiwa fuskarshi wani mahaukacin duka da karfen sai da ya cilla can. Hannunta yana rike da rodin ta wani mika shi. Zaka rantse irin yaran cartoon din nan ne, na Avatar ko wonder woman, lokacin tana karama. Yadda tayi dukar hatta Wasim sai da ya sauko a samar motar shi, ya gwalalo idanu waje. "Kai ku min fata-fata da namar yar tsiyakin nan!" Murmushi tayi, tare da jan kasa baya ta ce. "Idan kuka tab'a ni, zan kyale ku salin alin ku yi fata-fata da ni, idan na kararaya kasussuwanku, babu wani shugaba sai Baba na!" Ta fada tana kallon s kou. Idan da wani zai iya bada shaida tow abun da zai fada shi ne tana cikin mutanen da ayi experiment dinta aka yi, nan kuwa babu abin da yake aiki akanta sai wannan harsashin da yake jikin ƙwaƙwalwarta kamarshi. Murmushi tayi ganinsu tika-tika kamar giwaye, hatta gudun da suke kasa tana amsawa kamar zata burma. Da'ira suka mata, yadda zaka fahimci Yarinyar nan hatsabibiya ce, domin wani irin dukar su take babu kakkautawa. Kamar mayunwaciyar xakaya haka take musu duka da karfe ga hannunta baya sab'a abin hari dake akwai karfe rodin sai da ta gama musu dukar kawo wuka, sannan ta tsaya cak, zubewa suka yi. Ta d'ago fuskarta da yayi kaca-kaca da jini da zufa. Ta nufi Wasim kafin yayi wani yunkurin guduwa ta jife shi da karfen sai da ya fadi a ƙasa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.