Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Cinikin_Rai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 4 of 29
“Eh haka nake son na gaya miki!” kallon hotel ɗin take, tana me gyada kai kafin ta ce. “Akwai Cctv a cikin hotel din nan, daga shigowa zuwa nan harabar guda shida ne, don haka a nad'e mun duk wani bayani da aka shigar na wata shida baya, har zuwa yau. Sannan a kai ni dakin da aka yi taron.” “Tow muje ma" haka ta shige har cikin hotel. Ganin yadda ma'aikatan hotel suke cikin damuwa. Murmusawa musu tayi tana faɗin. “kada ku damu, aikin mu zai yi shi ne bisa goyan bayanku. Sannan idan muka gama, zamu tafi." Inji dan sandan da yake bin bayan. Shiru tayi tana kallon fuskar mutanen wurin. Kafin ta ce musu. “A wani daki aka yi taron?”
Fitowa Manager din hotel din yayi, yana fadin. “Sunana Nuhu Kasim, ni ne manager na hotel din, muje na muku iso cikin dakin taron.” gyada kai tayi, suka shiga cikin hotel ɗin, sannan suka fara zaga cikin dakin taron. “lokacin da aka gama taron baki daya suka fito ko daya bayan daya suka fita?” girgiza kai yayi ya ce mata.
“Mr Elbashir Jamal Arab ta fara fita, tare da yan majalisunsa, sai Prime minister.” kallon shi tayi tana kallon agogon hannunta. “an samu minti nawa a tsakaninsu?” shiru yayi yana kallon sama kafin ya ce mata. “Za a kai minti Talatin zuwa arba'in!” gyada kai tayi tana cewa. “Ok ina son zan duba dakin da Cctv din ku yake.” “Ok Ma” da ya fada, tare da yiwa ɗan sanda da suke tare jagoranci har dakin. Ita kuma ta cigaba da zaga dakin taron tana kallon wurin.
Har yamma suna zaune a wurin, kafin karfe uku garin yayi tsit, a hotel ɗin tayi salla, sannan suka koma office dinsu. Anan ta ga an kama mutane dayawa, wasu yan jagaliya ne, kallonsu tana faɗin. “waɗanan sune aka kama ko?” “Yes ma!” wucewa Office dinta, ta nufa tana me zama a kujerenta. “Ma ya zamu yi da su?”
“A rufe su, kada a ba da belinsu, a tura su ga kotu.” shiru yayi kafin ya ce mata. “ Ma akwai mutanen Xno kuma ba a kama su da laifin tadda zaune tsaye ba, kawai dai sun fito ne zasu kai Yara asibiti aka kama su” “Umarni aka ba ni, idan shima Xno din ya taka doka a karya shi, don haka kayi yadda nace.” shiru yayi sannan ya ce mata. “Mace ba namijin ba ce.” d'ago gajiyayyun idanunta tayi tana faɗin. “ Mace ce kuma yar daba?” ta tambaye shi, gyada mata kai yayi. “Ku tattaro min files na masu laifi bakidaya, don haka babu zancen sake su.”
Shiru yayi yana kallonta, bata san inda take tura kanta ba ne hala. “Hala baki san wace ce ita ba? Gaskiya ba zan iya wannan aikin ba, kawai a sallame mutanen.” sake baki tayi tana kallon shi,.kafin ta ce mishi. “Nawa take biyanka?” murmushi yayi mata sannan ya ce mata. “Ai ko daya bata biyana amma kuma ina gaya miiki gaskiya ne domin su yan jagaliyar nan sun fi mu, yanci don haka ki kyale mata Mutanenta, domin kowani lokaci zata iya zuwa kuma zata dauke su.”
Murmushi tayi sannan ta ce mishi. “Ok ina jiran zuwanta. Ina jiran abin da zata yi.”
-------
Bubuga kofar dakinta ake, domin tun bayan da tayi sallah hafsy ta fita. Ƙwanciyarta tayi abin, bata san wainar da ake toyawa ba, abun da ya faru kuwa tighgas da ake wurgawa ne ya haifarwa Chu-chu numfashinta ya fara sarkewa wanda yasa dole Black da Dundurosu suka fita da ita zuwa asibiti basu gaya mata, bayan sun kai ta asibitin ne, shi ne Black ya ce bari ya zo ya sanar halin da ake ciki, ai kuwa yana barin asibitin yan sanda suka kama shi, duk yadda ya musu bayani amma fir suka ki yarda suka saka shi cikin yan kame. A gidan kuwa kiran Dundurosu suka yi ya gaya musu, ai ya turo Black an kwantar da Chu-chu. Ai ko ba gaya musu ba, an kama Black. Jin bugub ba na kare bane, yasa ta bude kofar “Zeeno an kama Black ” barcin da bai gama wartsakewa bane ya neme shi ta rasa. “Garin yaya?” nan suka gaya mata.......
#Mmmj
#Zeeno
#Beauty
#Beast
#RomanceS
#Tycoon
#WeatherMan
#Rumors
#Jelousy
#Cursed
#Mai_Dambu
*08130269641 for more info*
[8/28, 6:46 AM] Mmn Khaleel: *CINIKIN RAI......*
Beauty and the beast♡
Mai_Dambu
BOOK ONE
004
“Meeeee?” ta kuma tambayarsu a hargitsassen murya. Diriricewa suka yi bakiɗaya tai musu ba wani irin kwarjinin da suka kasa samun damar bata amsa. “Nace, garin ƙaƙa hakan ya faru?” sake shiga rudani suka yi, juyawa tayi cikin dakin ta tsaya cak, tama ruɗe baki ɗaya tana me kallonta a madubi. Juyawa tayi ta kalle su. “Kuna nufin an kama Black?" “Eh Zeenobia!” suka bata amsa. Doguwar rigar da tayi sallah la'asar da shi ta saka, sannan ta dauki key din motorcircly tare da hilmet, kallon shigar jikinta tayi sannan ta koma wurin kayanta ta sauya riga da wando sai top da ta saka. Sai wasu chain da tasaka a wuyarta.
Kana ganin shigarta kasan sai a hankali kawai, domin daga sama har kasa zaka gane abin ya motsa ne. “Zeeno ko zamu raka ki ne?” da ta watsa musu harara tilas suka janye kudirinsu nason lallai sai sun bita. “Paul fito min da bike dina.” jikinsa na rawa ya fitar, ya shiga karkad'e mata. Tana isa wurin ta saka key ta tashi machine din, wangale mata kofar gidan yayi. Ta cilla kan babban titi a guje. Ta ina zata fara ma? Ta ina zata shiga? Babban asibiti ta fara nufa, inda ta shiga bin lunguna da yake cikin garin. Har ta isa asibitin, shima da kyar aka bude mata kofar, tana shiga cikin asibitin ta wuce emergency room.
Mikewa Dundurosu yayi yana faɗin. “Xnoo!” takawa tayi har wurinsa ta kalli Chu-chu da take barci. “Ya jikinta?” numfashi ya sauke sannan ya ce mata. “Sunce zuwa dare zasu sallame ta, sai dai kuma ina ga an kama Black.” cizon leɓenta na kasa tayi sannan ta ce. “Ba gani ba ne, sun yi ram da shi ne, amma ai sun san mutane na, wani shafaffe da mai ne zai kama min iyalai na?” saka hannu tayi a cikin aljuhun wandonta, ta ciro katin banki ta mika mishi. “zan tafi ka tabbatar idan an sallame ku, ka isa lafiya ko kuma ku kwana a nan, bayan nan kada ka saka rayuwarka cikin kasada.” ta dunkule hannunta, shima ya dunkule na shi, suka dan naushi juna, alamar Goodluck.
Yadda ta fita bata tsaya ba, nufar shingen yan sanda tayi, tana zuwa kafe machine din tayi, ta nufe su. “Xnoo! Da fatan lafiya dai?” murmusa musu tayi sannan ta ce musu. “Ina dan gidana da kuka kama?” shiru suka yi, kafin suka yi kasa da murya. “Xno yana can babban office din mu, nasan Ammar yana can yana ƙoƙarin ganin an sake shi, ai ba zamu iya rike miki shi." Murmushi tayi sannan ta bar wurin. Kai tsaye babban office din yan sanda ta nufa, duk inda ta wuce babu wanda yayi yunkurin dakatar da ita, tana isa office din ta kafe machine din. Ta cire hilmet ɗinta nufi cikin office ɗin. Tana shiga ciki ta hadu da dan sanda da ya su a sake black. "Ranki shi dade, da Kanki?” “Eh ina mutumina?” shiru yayi sannan ya ce mata. “Kiyi hakuri amma.” gyara tsayuwarta tayi, sannan ta ce mishi. “baka ji me nace ba ne?”
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.