Complete Hausa Novels

Darasi Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Darasi Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 2 of 10

Daga cen b'an garen Falmata tace"oky ranki ya dad'e ina jiran zuwanki,yawwa ni kuwa kin Samu kinje Yola din kuwa wajen Maman Yallabai Ammar?".

"Banje ba kuma bazan je,don wallahi na rantse Miki da Allah abinda matarnan tayi min Nima saina Rama,don tana tutiya d'anta ne ni kuma ina tutiya da mijina ne".

"Hhh mutuniya ta Kenan shiyyasa na ke son ki,kiji dadinki matar Yallabai,Insha Allah sai kin haifi magajin Gidan Yallabai Ammar".

Wata dariya Sakinat tayi sannan ta ce"ai ni wando Ce dai dai nake da k'ugun kowa"itama dariya Falmata tayi sannan tace"to ina jiran zuwanki don akwai Wanda mukayi alkawarin fita dashi.

Suna Gama wayar ta shigo cikin sashenta Wanda fadin iya haduwarsa ma b'ata Baki ne,har zata Shiga dakinta sai kuma ta dawo sannan ta nufi wajen wani kyakkyawan hoton wani matashi Wanda ya saka kakinsa na soja,yayi bala'in kyau sai Ka kasa gane Balarabe ne ko kuwa wani half-caste ne,don yana da wani irin sirrin kyau na ban mamaki.

Shafa hoton Sakinat tayi sannan tace"ilove u mijina inason Ka da yawa".

Ganganci ne mace ta rabe Ka,na sani ko ban sani ba ciki kuwa harda wacce ta kawoka duniya,don ni kadai a kayi Ka General Ammar Muhammad Lamido ina matukar so da kaunarka,dafatan Ka wayi gari lfy tana fadin hakan tayiwa hoton kiss ta shige daki abinta,tana kulla Yadda za tayi don itama taga ta ajje kwanta a acikin wannan babbar gonar.

Ammar yana zaune cikin k'aya taccen office dinsa Wanda ya gaji da haduwa,kyakkyawan matashi ne wanda ya gaji da haduwa cikin kayansa na kaki,ya d'aga kansa yana wani tunani,Anya kuwa yana yiwa kansa da mahaifiyarsa adalci kuwa,rabonsa daya saka k'afafunsa a Yola yau shekara 5 Kenan fa,yaso ace kafin wannan tafiyar da ta kamasa zuwa kasar Tunesia yaso yaje,Amman ya dauki alkawari Insha Allah idan ya dawo zai je,ya share wata kwalla da ta cika mishi idonsa,yana cikin tunanin yaji k'arar wayarsa Wanda yasan ba kowa bane illa matarsa Sakinat don ita kadai ce ta ke da numbersa.

"Ranka ya dad'e dafatan kana lfy,Allah ya Kara maka lfy,Allah ya Kara mana dank'on soyayya Amin,shima amsawar yayi da Amin.

nan dai suka Bata lokaci suna soyewarsa da sahibarsa Sakinat.

*UMMU MAHER ce*
*DARASI!!*

Free page 2

Rabiatu Bashir
(ummu maher)miss green.

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajarsu ta online zasu biya 2k*
02

......yana Gama waya da Matarsa Sakinat ya d'aga wayarsa ya Kara a kunnensa cikin nutsuwa shiru sukayi gaba kidayansu sanin halin Ammar,Amir ya ce"Kai fa haka kake Ammar Amman sai Ka bugowa mutum waya Ka yi shiru"?.

Shirun Ammar ya k'ara yiwa Amininsa Amir Wanda yanzu ya ke a America da Matarsa da yayansa 4,Gajiya Amir yayi sannan ya ce"Ammar lafiya me ya faru?cikin damuwa Amir yake fadar hakan don yana matukar Jin tausayin abokinsa Ammar don ya hadu da shu'umar mata,baiyi tsammani ba yaji Ammar ya ce"so na ke Ka turomin da number Umma"!.

Mamaki da wasu hawaye ne suka Fara zubowa a fuskar Amir, bakinsa yana kakkarwa ya ce"yanzu Ammar number mahaifiyarka karasa acikin wayarka? abin ya daure min Kai".

"Don Allah Amir Ka tausayamin Ka turomin number Umma,na kasance cikin bakin ciki, kwakwalwata tana gab da tarwatsewa kunnuwa na suna yimin kuwwar muryar Umma na,ina San inji Muryar Umma na",sai wasu hawaye masu zafi suka zubo masa.

Kashe wayar Amir ya yi hawaye yana fitowa a idanuwansa ya saka handcachiep dinsa ya goge hawayen da ya zubo masa,ya Danna message ya Nemo number Umma yana kuka ya turawa Ammar number.

Tunda Amir ya kashe wayar Ammar ya tashi tsaye a office dinsa ya buga tebur idanuwansa sukayi jawur sosai kamar garwashi,allurar Soja ta tashi,gashin jikinsa ya Fara mimmik'ewa,ya Rasa abinda yasa duk wata mace in dai ba Sakinat ba,Baya taba ganinta da gashi ciki kuwa harda Mahaifiyarsa wato Umma,wacce take matukar sonshi da k'aunarsa itace ta dauki nauyin karatunsa tun kafin ya Zama wani Abu ta shige mishi a gaba ya zamo abinda ya Zama tun bayan rasuwar Mahaifinsa,yana cikin wannan tunanin Yaji k'arar shigowar sako,da sauri ya dauka yana sharce wata uwar zufar da ta zubo masa,hannunsa yana kakkarwa ya dauka ya duba number Umma ya kirawo Hannunsa sai k'erma ya ke.

Wayar tana hannun Khalisat wato kanwar Ammar,tana Assignment an Kira yafi sau 3 taki dagawa sai tsaki take tana cewa"gaskiya ko waye wannan ya iya nacin jaraba",ta Fadi hakan cikin yaran Fillo wato fulatanci,sai da wayar ta kusa tsinkewa sannan ta d'aga cikin dakusasshiyar murya tace"waye"?.

"Common ki kawai wa Umma stupid!".

Da sauri jikinta ya Fara kakkarwa don tabbas ta gane muryar yayanta,hawaye suka Fara zubo mata da sauri ta haye step,tana kwalawa Umma Kira wacce alokacin ta ke sallar duha,wato sallar walaha, Khalisat cikin kuka ta ce Umma ya Yaya Ammar a waya"!.

Lokaci daya Umma taji kanta ya Shiga sarawa sosai,zuciyarta taji tana bugawa ta saka hannunta ta danne saitin zuciyarta daya tsananta buga mata.

Khalisat tasan za'ayi haka Amman sai ta goge hawayenta ta ce"Umma ki daga wayar nan kiji me zaice Miki,ki ajje fushinki a gefe ki janyo danki a jikinki don Allah".

Hannun Umma yana k'erma ta saka hannunta ta amshi wayar,sai dai ta kasa saka wayar a kunnenta.

Yaron da ta keso ta ke k'aunarsa Amman yau an wayi gari ya wofantar da ita,ya guje ta tamkar wata mujiya,idan Bata manta ba yau tsahon shekara 5 rabon da ta saka Ammar a idaniyarta balle har ya bugo mata waya.

Duk abinda a keyi Ammar yana Ji,kuma yana jiyo kukan Amminsa,hankalinsa ya tashi jijiyoyin kansa suka tashi sosai ya dafe kansa yana kuka.

Da sauri Khalisat ta saka wayar a handsfree don Umma taji muryar d'anta sosai,ai kuwa tana saka muryar taji Ammar yana cewa.

"Ammina"!

Sai kuka yaci k'arfin Ammar wani amai ya taho masa,ya ajje wayar ya ringa kwarara amai kamar me yaron ciki,ta cen bangaren Umma tana Jin Ammar ya Fara amai,hankalinta ya tashi ta Fara Kiran sunansa tana cewa"Ammar don Allah Kada Ka saka kanka cikin wani Hali Nima Ka sakani,don Allah kayi magana inji Muryar Ka".

Itama anan kukan yaci k'arfinta ta yarda wayar tana matsanancin Kuka,Khalisat ma hawayen ta ke tana sharewa Umma hawayen sannan tana bubbuga bayan Umman kamar k'aramar yarinya.

Kiran wayar Ammar Khalisat ta ringa yi Amman Bai daga ba,k'arshe ma taji an kashe wayar,hankalinta ya tashi ta Rasa Yadda zatayi gashi,ga Umma ciwon zuciyarta ya tashi da k'er ta Samu ta balli maganinta ta Bata ta Samu bacci,gashi kuma Yaya Ammar shima yana cikin wani Hali.

Kifa kanta tayi tana kuka me tsuma zuciya,tana kuka tana cewa"Anty Sakinat Baki kyauta mana ba kin rabamu da sanyin idaniyarmu,kin raba D'a da uwa,kin raba soyayya me k'arfi,Why me yasa kika yi mana haka?Meye ribarki?".

Nan dai Khalisat ta ringa surutai marasa Kan gado,daga Baya ta tashi ta yi alwala ta Fara sallar Nafila tana kuka tana rokon Allah subhanahu wata'ala ya kawo musu sauki da haske cikin wannan lamarin.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.