Darasi Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Darasi Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 9 of 10
Tunani kawai ya ke yi a game da makomar aurensa shi da wannan mummunar yarinyar,sam ba irin kalar Sakinat ya ke buƙata a matsayin matar aurensa ba,gaba ki ɗaya ma dai ya tsani yarinyar sosai,har bai san adadin tsanar da ya yi mata ba.
Yana zaune kiran Amir ya shigo wayarsa ya ɗaga a hankali kamar ba soja mazan fama ba,nasiha mai ratsa jiki Amir ya dinga yi mai a game da auren da mahaifinsa ya yi masa,kada ya bijirewa mahaifansa ya yi abin da suke so wataran zai tsinci haƘurin a gaba.
Tnx kawai ya cewa Amir sannan ya kashe wayarsa saboda tsabar haushi,don shi haryanzu bai yarda zai tsinci wani alkhairi a gurin wannan fush girl É—innan ba.
Ammi ma ta rasa mai yasa tunda Mijin na ta ya yi mata albishir da ɗaura auren Sakinat da ɗanta ta tsinci kanta a mai mummunan faɗuwar gaba ta rasa me ya ke yi mata daɗi,ba wai auran ta tsana ba a ah kawai zuciyarta ce bata aminta dashi ba,musamman yadda taga Ammar gaba ki ɗaya ya canza alokaci ɗaya,ta tsani abinda zai ɓata ran Ammar tana yi masa wani irin mugun so da tausayinsa a matsayinta na mahaifiyarsa,Allah kaɗai yasan irin zaman da zasuyi shi da yarinyar,amman koma dai menene tana roƙon Allah ya kawo sauƙinsa cikin ruwan sanyi.
Sannan tana yi masa fatan samun zaman lfy . . ..
"Tunanin me ki ke yi Zulaihat"?.
da sauri Ammi ta cire tagumin da ta yi ta yiwa mijin na ta murmushi don kada ya fuskanci halin da ta ke ciki.
Murmushi ya yi sannan ya ce"Zulaiha na sanki tun kafin ki kai shekarun haka shekararki 14 aka auramin ke alokacin ni kuma ina da kusan talatin kuma ina matsayin soja a wannan lokacin,ki kayi haƙuri ki ka zauna dani a halin da na ke ciki na yaron soja don kowa yasan halin zuciyar soja awannan lokacin harma da yanzu,to me yasa ki ka kasa haƙuri akan wannan auren dana ɗaurawa ɗanki?aƙwai abubuwa da yawa dana duba kafin in haɗa wannan aure ba da ka na yi saba,wannan yarinyar ba tada gata sai Allah akan ɗanmu ta kamu da ciwon zuciya fa?idan ƴarki ce zaki so hakan ya faru da ita?to kinga ba zaki so ba."
Tun daga nan Ammi bata sake haÉ—e ranta ba kullum cikin yiwa É—anta nasiha ta ke,tare da addu'ah.
Tafiya ce ta kamasi zuwa bauchi garin aminin Alhaji Muhammad,da ammi za aje amman kuma sai ta ce ta fasa tana da buki,da Khalisat da Sakinat aka yi tafiyar sai Alhaji don shi uban gayyar Ammar yana Abuja.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.
Aranar bayan sun tafi kan hanya sukayi hatsari aka nufi dasu asibitin da ke kusa,shi dai Alhaji abin sai addu a,Sakinat da Khalisat kuwa É—an kukkurjewa ne kawai.
Aka kirawo su Ammi a waya cikin tashin hankali tazo,yadda taga mijinta abin sai addu'a,ta kirawo Ammar tana kuka ta ce yazo ta faÉ—a masa halin da suke ciki,kai tsaye daga Abuja ya taho hankalinsa a tashe.
Da ƙer Alhaji ya fara magana yana yiwa Ammar nasiha akan Sakinat,kuka kawai Ammar ya ke na ganin halin da mahaifinsa ya ke.
*Miss green ce*
*✨🌈DARASI!!!🌈✨*
(Topic)
*` _``a love&```_ destiny story*
By
Ummu Maher(Miss green)ðŸ€ðŸ’š
*Littafin na kuɗi ne ban yarda ki karanta mun baki biyani ba,Gamai buƙata n cigaban labarin zai biya ₦300 normal* group...Vip group
₦500... Special₦1k....zaku iya Turo da katin MTN ta wannan number 07068606171
ko kuma ku tura ta wannan account number 2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith Bank.
*Free page*
18/19
Maganar ƙarshe da mahaifin Ammar ya faɗa shine"Ammar kada ka wulaƙanta wannan yarinyar kada ka juya mata baya,don kaga bani da rai,kada ka taɓa rabuwa da ita ma'ana ka saketa matuƙar ka saketa to ka saka a ranka babu ni babu kai."
wannan maganar ita ce ta ƙarshe da ya faɗa ya fara wani irin tari mai sarƙe maƙoshi daga nan rai ya yi halinsa,babu irin kukan da Ammar bai yi ba na rashin mahaifinsa ga abu goma da ashirin wai kada ya yarda ya saki Sakinat,shi ya rasa me yasa ma ƙwata2 ko kallonta ba yasan ya yi,yadda kasan wata mujiya haka take a wajen Ammar amman ya zamar masa dole ya fara sakin jiki da ita ko don nasihar mahaifinsa.
Bayan wata biyu rannan Sakinat tana zaune suna hira da Ammi,aka yi sallama da gudu Sakinat ta rungume Falmata ƙawarta ta yarinya ta,sosai taji daɗin zuwan Falmata don tunda ta yi aure ko dangin mahaifiyarta basu zo ba,don basu san ma ta yi auren ba.
Kalle2 Falmata ta shiga yi sosai irin kallon tsaf É—innan,Ammi sai kallonta take tana mamakin hali irin na wannan baiwar Allah.
Sai da Sakinay ta ɗan dunguri Falmata sannan ta dawo cikin hayyacinta,tana harar bayan Sakinat don gani take Sakinat bata dace da wannan gidan ba ita ce ta dace dashi,don haka ko ta halin ƙaƙa sai ta zauna itama a wannan gidan kuma ta fitar da ƙawarta Sakinat.
Tunda Falmata tazo gidan babu abinda take sai zuga Sakinat akan cewa wai tsabar baya sonta har yanzu yaƙi ya kaita gidanta ya barta a gidan iyayensa,wani lokacin kuma ta ce kinga gidansu kamar aljannar duniya ko ina gwanin sha'awa,duk yadda akayi komai shi yake a gidan kuma yana jin maganar mahaifiyarsa.
Da ya ke Sakinat sokuwa ce sai maganganun Falmata suka fara tasiri aranta har ta fara ganin ayanzu za ta iya fito na fito da Ammi don tun ba yau ba tana ganin irin abubuwan da Ammar ya ke wa Ammi,yana matuƙar girmama maganarta don har yafi jin maganar mahaifiyarsa da ta mahaifinsa.
Acikin satin Ammi babu irin rashin kunyar da ba ta gani ba awajen Sakinat kuma ta lura Falmata ce ke ƙara zugata,don haka duk sai ta watsar da su ta cigaba da sabgoginta,don dama Khalisat tana boarding Ammar kuwa ya yi tafiya zuwa ƙasar England wani aiki.
Ƙwanan Falmata biyar ta haɗa kayanta don tafiya gida,ta tambayi Sakinat ina ne ɗakin Hajiya,babu musu Sakinat ta nuna mata ta ƙwanƙwasa alokacin Ammi tana azkhar.
Ammi ta buÉ—e mata ta shigo tana gaida Ammi,ta amsa tana mamakin ganinta bata gama mamakin ba ta jiyo Falmata tana ce wa.
"Da man gida zan tafi shine na ce bari inyi miki sallama sannan in faɗa miki wata magana don nasan baki sani ba,lulluɓin biri aka yi muku.
Da mamaki Ammi ta ke kallonta tana mamakin hali irin na Falmata na munafurci,wato don taga ƙawarta ba ta nan shikkenan sai kuma ta yi gulmarta.
"Hajiya Sakinat fa kafin ta auri É—anku sai da aka cire mata ciki har sau biyu,kuma wallahi har yanzu bata daina bin maza ba".
da sauri Ammi ta É—aga mata hannu sannan ta ce cikin tsawa"get out in my room".
da sauri Falmata ta fito har tana haÉ—a hanya tana da na sanin zuwa wajen Ammi don yadda kasan zaki haka ta juye mata.