Complete Hausa Novels

Deejamah Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Deejamah_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 7 of 19

Page:1️⃣1️⃣--1️⃣2️⃣🖊️

_________Tunda suka shigo cikin school din kallonsu ake daga student din har lecturer's din,bawai kwalliyar su kadai ke burge mutane ba,hadda salon tafiyar su day kyansu da iya magana ke burge mutane,uwa uba Kuma ga kwanya suna jinsu kamar gifted.

Shigar larabawa sukayi gaba daya,Wanda yasake haskasu.
Shiga hall sukayi domin gabatar da Exam nan sukayi suka gama batare da sun kula kowa ba.

Bayan sun fito suka wuce gida Cike da gajiya,da yake yau khadee ce da girki,cake kawai sukasha da lemu ta Shiga kitchen don dora girki.

Sai da aka yi sallar magrib sannan khadee ta sauke shinkafa da miyar souce Wanda yaji attarugu,basuci abincin ba sai da suka gabatar da Isha tukuna sannan sukaci abinci sunayi suna shewa da hira.
Sun kammala cin abinci ,Fauzi ta dubi Shakeerah tace"babee muna jinki.
Murmushi Shakeerah tayi tace"dama nasan kina Nan kina kwakwa da kokarin son Jin labari.
Dariya suka sa gabadaya,khadee tace wallahi nima haka shi naketa kwa-kwan son ji.

Shiru tayi ta dauki tsawon minti 3 zuwa can tafara magana kamar haka.
"Da fari dai ni Sunana Maryam Muhammad Adali, Ni haifaffiyar Zaria ce anan na girma anan nataso,gaskiya tun tasowar mu muka taso masu rufin asiri azahiri bamu dashi domin kuwa mu ba 'yayan masu kudi bane,ba musan wani Abu karatun boko ba sai dai na Allo wannan fa akwai shi Wanda mahaifin mu yatsaya Kai da fata yabamu nida Aunty ta.
Mu biyu ne Abba ya haifemu Dani da yayata mafi soyuwa a gareni ta nuna mun so fiye da komai,kun ganni hatta talla nayi tallan biredi saboda tsaban rashi,tun Ina karama ake daurawa Aunty Saudah tallah,macace mai hakuri tare da kawaici irin Ammi,kada kuyi tunanin Wai a son ran iyayen mu muke talla a'ah Babu CE takawo haka,tun farko Abba shagon Saida agoguna yake Rana Daya Bari suka tsiyatar dashi.

Aunty Saudah haka zata dauki tallah batare da ta karya ba,Kai hatta ni mutan gidan,da yawa idan takai ba siya ake ba sai dai a lallatsa a tafi a bar mata,wani ma a kwance aci,ace baza'a siya ba.

'Yan uwan baban mu suna da Hali dai dai gwar-gwado sai dai temako ne baza suyi ba.
Aunty Saudah kuwa duk abinda ke faruwa bashi yake hanata gobe fita da bread ba,ana cikin haka na girma Wanda na taso da shegen rashin ji da fitsari,ba anuna mun yatsa a maida lafiya ba'amun na kyale,tun Ina gida,dalilin haka yasa Ammi ba kasa fai take Bari na fita ba.

Koda nakai 9years tsiyata kuwa ta karu,domin kuwa rigima nasa akan abarni Nima nadinga fita talla kamar yanda Aunty Saudah ke fita,munada kyau daga mu har iyayen mu,Amma tsabar wahala tasa mun kode,kafafuwa na kuwa duk Sunyi faso tsabar gantali yamun yawa da yawo Babu takalmi.
Kullum nasihar Ammi da Abba shine mu natso,nikuwa Shiga takeyi tanan tafita ta can.

Tallah nafara bin Aunty Saudah ita a lokacin tana da 14years, Nikuma Ina Daukar pure water.
Wata rana muka dauki tallah da ita gashi garin da Rana sosai,wani gareji mukazo wucewa kunsan dai garejin masu gyaran motoci to nan.

Alamu sukayi mana da baki kamar fito, Aunty Saudah ce ta juyo da Sauri ta nufi wajen su,domin ita burin ta a kullum da tafito a siye tanajin nauyin komawa gida ba ayi ciniki ba.

Zugwi-zugwi nabi bayanta kamar tsohuwar munafuka,wasu maza ne suka kariso tare da Daukar bread din,Daya ya bude ya dauki na hamsin ya ciye tassss tare da Daukar pure water na yasha,gyatsa yayi irin na 'yan iskan Nan,shikuwa dayan da ya dauki bread din rabi yawafce sannan ya aje ragowan.

Daure face Wanda yacinye ledan bread Daya yayi,sannan ya dubi Aunty Saudah yace"wareee anan wajen,Cike da tsoro Aunty Saudah ta sungumi farantin bread dinta domin gudu.
Dubana yayi yace"kema dauki wannan ajawon ruwan naki ki wuce,yayi maganar Yana wurgi da bucket din ruwana.
Nan kuwa ruwa ya fadi wasu Kuma suka farfashe,cikin bacin Rai na dago na dubeshi sannan na dube bucket dina.
Daya a cikinsu yace"ba magana ake Miki ba don uwarkiiiiii?
Itakuwa Aunty Saudah fara jana tayi Cike da tsoro tana cewa"Shakeerah zo mune gida mu barsu da Allah .
Fusge hannuna nayi na nufi inda bucket Dina yake,da yake irin na karfen nan ne Mai murfi,dauka nayi ba nufo su,sukuma a lokacin sun juya sai dariya suke tikawa ba suyi aune ba sukaji saukar bucket akan daya a cikinsu,ihu yasaka,a firgice dayan shima yajuyo Aiko na sakin mai bucket din a gushi,duk cikansu ihu sukasa domin wajen ya fashe bucket din datsan su yayi.
Cikin Sauri ragowar mutanen dake garejin suka kariso ana tambayar meke faruwa?a ciki kuwa harda ogan wajen.
Cikin bacin rai nafara magana"Saboda zalunci irin naku da mugunta akan me zakuci bread kuce mutafi sannan kuyimun fatali da bucket din ruwa,oho dayake tasaba zuwa ita kadai dama kume masu Mata haka Koh?to idan ita ta dauka Ni bazan dauka ba eheeee,na karishe maganar Ina murguda baki.
Ogan su ya tambayi ba'asi Nan kuwa na zauna na zayyane komai harda karawa da gishiri,Cike da bacin rai yake dubansu yace"lallai abinda yarinyar nan tayi tamun dai-dai gaba kwasake......cikin Sauri nace"wallahi gobe ma kuka sake sai nayimuku mafiyin wannan,kudena ganina 'yar karama akan ahalina babu abinda bazanyi ba,kowa Cike da mamaki take dubana sukuwa samarin tsoro na ne yashigesu.
Tambaya na shugaban garejin yayi ruwan nawane?nace jakar leda uku CE.
Nan kuwa yaciro dari biyar ya bani,sannan yace bread na nawa sukaci?bashi amsa nayi da cewa da bread din hamsin da rabi sannan ai ba yau sukafara mata haka.
Karshe dai Sai da mukabar gareji da Naira dubu Daya da dari uku,sannan nace"Babu Wanda ya Isa yahanamu kawo talla garejin.
Daukar bucket Dina nayi muka tafi,a ranar dai nayi dambe Yafi a kirga,Kuma duk akan bread da ruwa,masu yima Aunty Saudah rainin wayo sai da na Rama Mata.

Abin mamaki mun siye bread din nan tass Babu ko lankare, murna sosai Aunty Saudah tayi.
Haka kuwa muka nufi hanyar gida muna Cike da farin ciki,a hanya muka hadu da wani wan baban mu akan mashin dinsa Sabo fil,harara yabimu dashi Yana cewa shegu 'yayan Allah shirya masu kama da almajirai,Baku da aiki sai gantalin talla.
Juyowa nayi nace"Kaine dai babban almajiri Mai yawon maula,Kuma ai da sauki mu gumummu muke ci,wasu kuwa gumin haramun suke ci.
Ashe ramawar Nan danayi ya Sosa masa rai Aiko Nan yafara tsiya,kome yafada na bashi martani a karshe dai tsaki naja mai tare da tofar da miyau muka wuce.
Ni ban Sani ba Ashe hakan ya bata masa Rai sosai.
Aunty Saudah kuwa tsiya tadinga mun a hanya akan nadena rashin kunya,dukar da kai nayi kamar gaske nace toh Aunty Saudah nadena.
Tayi farin ciki sosai da amsar da nabata,wato nadena.
Gida muka Shiga Cike da farin ciki na fada jikin Ammi da Abba nace"Ammi Abba yau munyi ciniki Sosai,domin gabadaya aka cinye,murna sukayi sosai kamar su goyamu,tuwon dawar da Ammi tayi da miyar kukan da ko isashshen magi baiji ba muka fara ci Cike dajin yunwa.
Ammi kuwa tasamu tayi tana kallon mu tana Murmushi Cike da kaunar mu a ranta,shikuwa Abba daki yashiga.
Langa-langar kofan mu aka bugo da karfi Wanda yasamu zabura gabadaya,baba Ayuba ne yashigo Yana masifa,ganina yasashi yowa inda nake direct.
Nikuwa ganin haka yasa na Miki nayi hanyar bayin mu,ai kuwa baba tsalha ya biyo baya na shima a gunen , da yake wajen da santsi sai na zille nayi gefe guda.
Yana kuwa karisowa wajen santsin jiake timmmm baba tsalha yafadi,Kara yasaka tare da fadin"wayyo Allah na kunguru na.
Nikuwa mezanyi Banda dariya,dariya nake sosai harda rike Cike,Cike da bacin Rai yadago Yana dubana.
Abba ne yakariso cikin Sauri Yana fadin "Subhanallah yaya Ayuba meyasa Meka?cikin Sauri Abba ya kamashi ya dagashi,Nuno ni da yatsa yayi yace"wancan tsinanniyar yarinyar taka Mai Kama da aljanu nan yashiga bawa Abba labarin komai.
Cike da bacin Rai Abba yadago Yana duba na yace"Mama haka kayi?
Girgiza Kai nayi cikin Sauri nace"A'ah Abba kawai don ya tsaneni ne shiyasa zaice haka,gaishe kawai nayi yahau zagina don yaga bankula shi ba shine yabiyo ta nan.

Gabadaya bude mouth baba Ayuba ya bude Yana kallo na,Yana mamakin wani irin hatsabibanci ne dani haka?
Shiru yayi batare da yayi magana ba ya fita daga gidan,karyayyen langa-langar mu yabuga yafita, Abba ne yadawo da dubanshi kaina yace"zonan mamana,tsakanin ki da Allah meyafaru?Jin ta tambayi tsakani na da Allah yasa nafadi gasky,Nan ko Abba ya Shiga yimun fada inda yake Shiga banan yake fita ba,Ammi ma haka Bayan sun gama suka dasa nasiha akan narage tsiwa da rashin kunya.
Amsa kawai na Basu da toh sannan na nemi yafiyarsu,Sam banson bacin ran iyayena a gefe guda kuwa ta shiga tanan ne tafita ta can tabi iskaaaaa.
Washe gari kuwa muka sake daukar tallan bread din duk idan muka fita sai mun siye tasss,dalilin haka kuwa Allah ya albarkaci Dan ribar dubu dayan da muke samu,ganin haka yasa Abba yasamu a islamiya,ajinmu Daya da Aunty Saudah tunda inada kokari sosai,kwana na biyu a islamiyar sunana ya zagaya makarantar,a dalilin na fasa ma wani yaro kai yakawomun wargi,kullum sai iyayen yara sunkawo karana wajen headmaster,ganin haka yasa headmaster ya sanar ma da Abba,wanna Karan fushi Abba ya dauka sosai a kaina domin har zaneni yayi yace Kuma zai cire ni a makarantar.
Hakuri Nashiga bashi,sannan nayi mai alkawarin bazan Kara ba,tsaki yaja yace"keda Kika Saba da dama tuban mazuru.
Ita dai Ammi ko me akayi sai dai Ido.

~After 3 month~

Mun cigaba da zuwa islamiya Alhamdulillah Allah nata rufa Mana asiri,sannan a gefe guda bamu dena zuwa tallah ba.
Ranar sati na shirya ni kadai na tafi islamiya da yake Aunty Saudah bataman tabi kanwar Ammi Agadez domin Ammi 'yar agadez ne can wani kauye,namanta sunan shi,ita Kuma tana aure a cikin garin nijar.
Latti nayi,da yake malam shafi'u azzalumi ne yasan bansan duka,Aiko nan yamun dukan tsiya,kuka nayi sosai tare da duban hannu na yanda ya fashe.Don haka na dauki alwashi da ramuwa da *daukan fansa* a dalilin dukan wallahi sai na Rama.
Washe gari kuwa Bayan antashi islamiya na dai-dai ci dai-dai lungun da malam shafi'u ke wucewa na zuzzuba kososhi tunda ga farkon lungun har tsakiya,sannan nasu wani waje na boye,hannu na da katon icce.
Aiko bayan antashi malam shafi'u ya shigo lungun,kunnensa sanye da earpeace bai ankare ba yaji mashin tafara selow slow slow alamun Babu iska,sauka yayi tare da Jan tsaki,Yana duban tayar mashin dinsa Bai ankare ba yaji saukan sanda a bayansa say kwala masa,wani irin ihu yasake tare da gantsarewa,cikin bacin Rai ya juyo Cike da mamaki da takai ci yake duba na,nikuwa hade rai nayi kamar wata babba ku Kuma wani sa'a na nace"ai dama ramuwar gayya tafi ta gayya zafi Ina magana Ina jujjuya sandar da take hannu na.
Cikin bacin rai yanufo inda nake,Aiko na hau tsalle tsalle kamar 'yar Cali-cali Allah kuwa yabani nasara nashige ta osin shi,abin fitsarin shi na Kama na murdeeee,duk da a lokacin bansan menene ita ba,kawai hannu na ne yakai kanta.
Kyalkyalewa da dariya su Fauzi sukayi,khadee tace"lallai Shakeerah kin bar history a unguwar ku.
Murmushi Shakeerah tayi tace"hmmmm ku dai Bari,in takaicemu ku tunda na Kama abin fitsarin shi na murde sai da yayi ihun wahala nasake shi,sannan na dauki icce na kwala ma goshin sa Aiko atake anan yafashe goshin yafara fitar da jini.
Nesa dashi nayi sannan na nuna masa hannuna da ya fasa da dorina nace"kaga wannan somun tabu ne,Ina Gama fadar haka na arta a 360 na bar wajen nayi gida.

Washegari na dauki tallar pure water da bread dina natafi wajen Sha daya na dawo Bayan nayi ciniki ansaye tasss.
Tunda nashigo gidan daga Ammi har Abba babu wanda ya kalleni daka gansuu kasan ransu a bace yake,Cike da farin ciki na nufi jikin Ammi na fada kamar yarda na Saba nace Ammi kin.........ko karisawa banyi ba naji saukar Mari,Wanda yasani gigicewa duk da bansan Wanda ya mareni tsakanin Ammi da Abba ba to nafi kyautata zaton Ammi saboda shi Abba mutum ne Mai sanyi kamar yanda Ammi take,babban cinsu Ammi na duka Abba Kuma ba yayi.
Ihu nake Ina fadin na Shiga uku,sanda Ammi ta dauko tace"au don ma bandake kiba shine kike kokarin tara mun jama'a?iccen miyar tsanya ta dauko zata zabga mun tana cewa"Bari inmiki Mai dalilin inyaso kyayi kukan da hujja.
Zumbur na mike nanufi Bayan Abba ina cewa"A'ah Ammi kuyahakuri wallahi bazan sake ba nayi alkawari.
A halin Ammi na kunya ko me muka Mata bata iya dukan mu a gaban Abba domin tana ganin kamar cin fuska ne.
Jawo ni Abba yayi gabansa ya dorani a Kan tabarman da yake ya dubi Ammi yace"kikawo Mata abbin Karin kumallo,da toh Ammi ta'amsa ma Abba,sannan tashiga dakin Wanda yake ciki dai-dai guda biyu,daya nata da Abba Daya Kuma nida Aunty Saudah,sai bayin mu da kitchen waje guda.

Dauko mun Karin kumallon tayi ta aje tare da dallamin harara.
Cike da yunwa najawo kofin Koko na da roban kosai na mike naje na wanke hannu nadawo,bismillah nayi na fara cin abinci.
Bayan na gama Abba yadubeni yace"mama na meya hadaki da malamin islamiyar ku har Kika masa rauni?shiru nayi kaman munafuka Ina tunanin wani karyan zan gindayo ma Abba......katse tunanin nawa nayi a dalilin Jin yace anjima zai daukeni muje har islamiyar,idan nice da lefi zaisa amun assembly a zaneni.

Kirji na ne yabuga na fara kokarin samo mafita.

Xahratty ce✍🏽
Lallai Alqalami 🖋️Yafi takobi 🗡️
💕💕
❤️
[7/18, 2:05 PM] Xahratty🥰😘: 💐✨ *DIAMOND LADIES* 💐✨
( Daukar Fansa )

Story& writing
By
PATEEMA ZAHRA LAWAL
______✍🏽______

*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*
🔱(( Home of Expert and talented writers,da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah))

*_T.W.A_*
_________________________
https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/
_________________________

Marubuciyar⬇️

_ _A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_

*DA*

_ _MIJIN ZAHRA_

*Littafin diamond ladies (Daukar Fansa) na kudi ne duk maiso ya turo katin Naira dari#100 katin waya ta wannan number 08060710719,sai nayi adding din mutum a group din.*

Bismillahir-rahmanir-raheem.

*Da sunan Allah Mai rahama Mai Jin Kai....*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.