Complete Hausa Novels

Fansar Fatalwa Book 1 Complete Hausa Novel

Reading file: FANSAR FATALWA.txt

Chapter 1 of 2

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_ 💀☠️).

_Tsarawa / Rubutawa_

© *SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S* *ASSOCIATION*

*SADAUKARWA* _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku Anty Hadiza D_ _Auta_Anty Binta Umar Abale, _sis Amira Adam_ _Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda kuke ina son ku fisabillillahi._

*NOTE*
Wannan labarin haƙƙin mallakata ne ban yadda a juyamun labari ta kowace fuska ba yin hakan babban kuskure ne.Sannan Labarinnan ƙirƙirarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wani ko wata ba kamanceceniyar labari akasine.

*Free book*

-------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*001*
_________________________

*ƘAWAYE* ! Hmmm idan naji wannan kalmar a kullum sai naji zuciyata kamar zata tarwatse saboda yadda na tsani jin an ambaci kalma mai kama da Ƙawance,tabbas Ƙawaye sun min babbar illa a rayuwata,tabbas Ƙawaye sun zama wani sashe daga cikin sashin tarwatsewar farin cikina,tabbas Ƙawaye sun illata rayuwa ta illa mafi muni. A wasu lokutan Ƙawaye su kan zama alkhairi ga rayuwarmu while a wasu lokutan kuma su kan zama babban sharrin da yake tarwatsa duk wani farin ciki na daga cikin rayuwar tamu kamar yadda ya faru a kaina. A zamanin baya Ƙawaye tabbas su kan zama alkhairi a rayuwar mu amma banda wannan zamanin da muke ciki in da kaso tamanin daga cikin kaso ɗari na Ƙawaye suke ba abun yadda ba,da yawa daga cikin ƙawaye suna zaune da juna ne ba da zuciya ɗaya ba sakamakon hassada da ta yiwa zukatan su katutu.Na tsani Ƙawance! na tsani duk wata kalma mai alaƙa da Ƙawance,na kasance mai wata iriyar zuciya wadda nake saurin yadda da mutane musamman Ƙawaye ina matuƙar basu muhimmanci kafin su min Illah,idan zan zauna da mutum to ina bashi duk wata yarda da ta dangance ni sannan akan Ƙawa na gwammaci a cimun mutunci akan a ciwa Ƙawata,duk bayanin da zan muku ba zaku taɓa gane irin yadda na yadda da Ƙawance ba,sai dai ashe bansan cewa hakan babban kuskure bane nake aikatawa Sai da suka mun Illa kafin na farga. Ƙawaye sun illata rayuwa ta illa mafi muni inda suka yi nasarar tarwatsa duk wani jin daɗi da farin cikin da na mallaka ba kuma komai ne ya janyo hakan ba sai tsantsar hassada da kuma son zuciya.

****
Gudu take tsalawa a kan titin wanda zamu iya ƙiran shi da gudun ceton rai duba da yadda take gudun ko kallon inda take jefa ƙafarta ba tayi, dare ne sosai ƙarfe biyu da rabi, bakajin motsin komai face kukan ƙwaruna da baza'a rasa ba,Tsananin duhun daren ya sanya ko tafin hannun ka baka iya gani,ga wata irin tsawa da ake yi mai firgitar wa wadda hakan yake nuni da cewar akwai hadiri sosai a garin wanda a kowane lokaci ruwa zai iya ɓarkewa. Juyawa tayi ta kalli bayanta don ganin shin ko ta tsaracewa abun da take gudu ɗin,sai dai kash! Da ta san abun da zata yi tozali da shi da bata juya ba domin kuwa tana juyawa tayi arba da abun da take gujewa ɗin daf da ita,wani irin ihu ta sake tana fatan ko Allah zai sa wani ya jita domin a kawo mata ɗauki duk kuwa da cewa ba lalle ko an jita ɗin a fito ba,sai dai abun da bata sani ba shine duk ihun da take ɗin babu mai jin ta. Bata ankara ba sai ji tayi taci karo da wani ƙaton dutse da yake gefen titin sai gata warwass a ƙasa take ta fara gangarawa zuwa gefen titin inda yake wani wawakeken rami ne a wajen,daf da ta kusa faɗawa cikin ramin taji an ruƙota buɗe idanunta ta fara yi a hankali tana jin zuciyarta tana mata wani irin bugu, Tarwal ta buɗe idon nata take tayi arba da abun da take gujewa ɗin wanda hakan ya sanya ta ɗaukewar jin ta da ganin ta sakamakon tsoratar da tayi ɗin. Zazzafan ruwan da taji ya sauƙa a jikin ta ne ya bata damar farfaɗo wa daga sumar da tayi ɗin,wani marayan kuka ta sake inda ta fara magana cikin wahaltacciyar murya.

"AMRAH dan Allah ki yi haƙuri ki taimake ni kar ki kasheni, wallahi nayi dana sanin duk abun da muka aikata miki dan Allah ki duba girman Allah ki yi haƙuri".

Wata dariya AMRAH ta sake wadda ni kaina sai da kunnuwana suka É—auke ji na wani lokaci,take kuma ta fashe da wani irin kuka mai ban tsoro a lokaci guda kukan suka shiga fitowa tare da dariya, haÉ—e fuska tayi kamar ba ita tayi dariyar ba sannan ta fara magana cikin muryar ta mai tsoratar wa.

"Ashe kinsan girman Allah!?, Afrah nace ashe kinsan Allah!?,Hmmm wai shin ko kin manta irin tozarta mun rayuwa da ku kayi?,shin kin manta jefamun rayuwa da ku ka yi a cikin tashin hankali da masifa?,ki sani idan maye yaci ya manta to uwar ɗa ba zata taɓa mantawa ba.Sannan ki sani wallahi nayi alƙawarin yadda kuka rabani da farin ciki a rayuwata to tabbas kuma sai kun ɗanɗani baƙin cikin dana ɗanɗana,ai matuƙar ban dawo ƊAUKAR FANSA ba to bazan taɓa yafewa kaina ba, domin kuwa rama cuta ga macuci ibada ne,dan haka ki shirya girbar abun da kika shuka".

AMRAH tana kaiwa nan a zancen ta ta saki wata mahaukaciyar dariya wadda ta sanya wa tsuntsaye saurin tashi daga kan bishiyoyin da su ke tsabar tsorata,ita kuwa Afrah take wannan dariyar ta sanya mata ɗaukewar jin ta da ganin ta na wani lokaci, AMRAH ce ta sanya dogon hannunta mai cike da dogayen farata ta cakawa Afrah a tsakiyar ƙwayar idonta,wani gigittaccen ihu Afrah ta sake sannan ta tafi luuuu zata faɗa cikin wannan ramin,harshenta AMRAH ta sanya wanda ya kusa kaiwa tsayin wani mutum ɗin sannan ta nannaɗe Afrah dashi ta jata ta nufi wani Daji da yake gefen titin da ita.

*****
Yau gidansu Afrah tun ƙarfe shida da suka farka basu koma ba sakamakon shirin auren Afrah ɗin da suke ta yi wanda za'a ɗaura nan da kwana uku in sh Allah shiri sosai akeyi a gidan kowa ka kalla fuskar shi cike take da farin ciki.

Wata farar mata ce doguwa ta fito daga cikin wani ɗaki ta sha ƙunshi na jan lalle abun ka da farar fata sai ya mata kyau sosai,kallo ɗaya zaka mata ka fahimci cewa mahaifiyar Afrah duba da yadda suke mugun kamanni, kallon ƴanmata da suke zaune a kan kujerar falon tayi suna shirya kaya a cikin wani akwati,wanda sun kai su goma sannan tace.

"Fadila wai nikam ina Afrah take ne har yanzu bata fito ba gashi har mai mata lalle ta ƙaraso?".Ta faɗa tana mai kai duban ta ga ɗaya daga cikin ƴanmatan.

"Hmmm Mom kinsan halin ƴar gidan naki bata son kwana a cikin mutane wallahi tana ɗakin baƙi jiya a can ta kwana ita ɗaya" ɗaya daga cikin ƴan matan ta faɗa tana mai cigaba da sanya kayan a cikin akwatin.

"Ke Husnah je ki taso ta dan Allah ta haƙura da wannan baccin asarar da take ɗin ita da bacci baya isar ta" cewar Mom ɗin tana juyawa dan komawa cikin ɗakinta.

Tashi Husnah tayi ta nufi hanyar ɗakin baƙin domin dubowa Afrah ɗin,turus! taja ta tsaya lokacin da ta shiga cikin ɗakin ganin ba kowa a cikin ɗakin,bakin toilet ta ƙarasa tana ƙiran sunan Afrah amma shiru ba alamar za'a amsa mata.

Da sauri ta kama handle ɗin jikin ƙofar toilet ɗin sannan ta tura ƙofar to her surprise sai gashi ƙofar ta buɗe shiga tayi cikin toilet ɗin inda ta fara ƙarewa kowace kusurwa da take cikin toilet ɗin kallo sai dai babu Afrah babu alamar ta, juyawa tayi ta fito daga cikin toilet ɗin cikin sauri ta nufi hanyar komawa cikin falon dan sanarwa da Mom abun da yake faruwa ɗin,tun daga bakin ƙofar ɗakin baƙin ta shiga ƙwalawa Mom ƙira cikin ruɗewa.

"Kai Husnah wai lafiyarki kuwa kike mun wannan ƙiran haka kamar zaki tashi sama,ina Afrah ɗin?" Mom ta faɗa wadda take fitowa daga cikin ɗakin nata.

"Mom ina kuwa lafiya Afrah fa bata cikin ɗakin baƙin".Husnah ta faɗa tana mayar da numfashi kamar wadda tayi gudu.

"Bangane ba wace irin magana kike haka wai Afrah bata ɗakinta?" Mom ta faɗa tana nufar hanyar ɗakin baƙin.

Juyawa itama Husnah tayi tabi bayan Mom ɗin inda suma su Farida suka miƙe gabaɗaya tare da rufawa Mom ɗin baya.

Duk wani bincike da su Mom zasu yi a cikin ɗakin sun yi shi amma babu Afrah babu alamarta,tun abun bai fara ɗaga musu hankali ba har takai sun fara tsorata da lamarin domin kuwa tun suna bincike iya cikin ɗakin har takai sun fito sauran sashin cikin gidan amma ko mai kama da Afrah basu gani ba,sosai hankalin su ya tashi inda suka koma cikin gidan Mom ta ɗauki wayarta ta ƙira Dad ɗin Afrah domin shaida mishi halin da ake ciki kasancewar tun da yayi sallar asubah bai shigo cikin gidan ba suna massallacin ƙofar gidan tare da mutane.

Yana ɗaga wayar Mom ta fashe da kuka tana sanar mishi ganin Afrah ɗin da ba'a yi ba,shima sosai hankalin shi ya tashi inda ya nufo gidan cikin sauri tare da yayun Afrah ɗin.A tsaye suka tarar da mutanen gidan cirko-cirko a harabar gidan tashin hankali ya bayyana ƙarara akan fuskokin su,da sauri mahaifin Afrah ya ƙarasa wajen su

"Hajiya mai ya ke faruwa ?" Cewar mahaifin Afrah hankalin sa a matuƙar tashe

" Alhaji ina kuwa lafiya mun nemi Afrah sama ko kasa a cikin gidan nan mun rasa" ta faÉ—a cikin fashewa da kuka.

"Innalillahi wa'innailaihi rajiun" mahaifin Afrah ya faÉ—a cikin tsananin tashin hankali sannan ya cigaba da magana

"A garin yaya hakan ta faru? Ya za'a yi a ce a cikin gidannan an nemi mutum an rasa gaskiya abun da mamaki!".

"To Alhaji ni ya za'a yi na sani, wallahi nima abun ya matuƙar bani mamaki kuma duk inda ya kamata mu duba mun duba a cikin gidannan amma bamu ga Afrah ba,wannan wace kalar masifa ce ace ana saura kwana uku biki an nemi amarya an rasa" Mom ta ƙarashe maganar cikin karyewar murya.

Shiru mahaifin Afrah yayi na wani lokaci kafin daga baya kuma yace.

"Shikennan yanzu bara naje wajen Æ´an sanda na sanar da su".

"Amma Alhaji ya kamata mu ƙira Anwar mu sanar da shi halin da ake ciki shima ya sani a matsayin shi na wanda zai auri Afrah ɗin".

Saurin dakatar da ita Mahaifin Afrah É—in yayi sannan yace

"A'a ba za'a yi haka ba, yanzu ki bari muje wajen ƴan sandan muji abun da zasu ce tukunna"ya faɗa yana juyawa tare da nufar wajen motar shi, da sauri wani yayan Afrah wanda ake ƙira da Aliyu ya bi bayan shi.

Gudun da Aliyu É—in yake a titin shi ya sanya basu wani É—auki tsawon lokaci ba suka isa police station É—in.

Kai tsaye office ɗin DPO suka nufa inda basu wani tsaya ɓata lokaci ba suka zayyane mishi abun da yake faruwa.

Shima DPO ɗin sosai ɓatan Afrah ɗin ya tsaya mishi a rai domin kuwa wannan abu da ɗaure kai yake,a hankali ya ɗago kan shi yana juya biron da yake hannun shi sannan ya kalli su Aliyu ɗin yace.

"Amma ranka ya daɗe wannan auren da zaku yiwa ƴarku da son ranta ne ko kuwa zaɓin kune?".

Wani murmushin takaici mahaifin Afrah É—in yayi sannan yace.

"DPO meyasa kamun wannan tambayar?"

"Ka fara bani amsar tambaya ta tukunna kafin ka jefa mun wata tambayar" Cewar DPO É—in yana kafe mahaifin su Afrah É—in da ido.

"Tabbas da son ranta za'a yi wannan auren asali ma zaɓin ta ne ba zaɓin wani ba".

Shiru DPO É—in ya sake yi kamar mai nazarin wani abu sannan ya dube su yace.

"Shikennan Alhaji za ku iya tafiya mu kuma inshAllah zamu yi duk mai yiwuwa dan ganin mun nemo inda Afrah take,ina buƙatar photon yarinyar taka idan kuna dashi ko a waya ne ku tura mun,sannan gidan ka ma ku kasance a cikin shiri domin kuwa a kowane lokaci binciken mu zai iya biyowa ta cikin gidan naku. Abu na ƙarshe shine ina son ka bani address da kuma wasu information akan wanda Afrah zata aura shima zamu yi bincike a kanshi domin kuwa a halin yanzu ko kuma baku fice daga cikin suspect ba".

Sosai mahaifin Afrah suka cika da mamakin maganar DPO ɗin har ya buɗi baki zai ce wani abu Aliyu ya dakatar dashi inda ya sanarwa da DPO ɗin duk abun da ya buƙata game da Anwar ɗin.

Ranar gidan su Afrah kwanan zaune suka yi domin kuwa waɗanda suka iya yin Bacci a cikin gidan ƴan ƙalilan ne,kowa ka gani hankalin shi tashe yake.

Washegari kuwa ƙarfe takwas dai-dai ƙiran wayar DPO ya shigo wayar mahaifin Afrah ɗin a lokacin gaba ɗaya ƴan gidan suna hallare a cikin falon gidan sun yi tsumu-tsumu kamar an jiƙa ɓera a buta.

Cikin sauri mahaifin Afrah É—in ya É—aga wayar gabanshi yana dukan uku -uku sannan yayi sallama.

"DPO ya ake ciki fatan dai akwai wani sabon labari?".

"Alhaji gamu a ƙofar gidan ka zamu iya shigowa".Fita Mahaifin Afrah ɗin yayi sannan ya musu iso tun da ya isa inda suke faɗuwar gaban shi ta tsanan ta sakamakon arba da wani abu da yayi an lulluɓe shi da wani farin yadi a ajiye a ƙasa.

"DPO ya ake ciki?" Mahaifin Afrah É—in ya jefawa DPO wannan tambayar cikin tsananin tashin hankali da rawar murya.

"Alhaji mu shiga ciki tukunna domin kuwa maganar ba zata yiwu a nan wajen ba"

Gaba mahaifin Afrah ɗin yayi inda DPO ya umarci wasu ƴan sanda guda uku da su ɗakko wannan abun da yake lulluɓe ɗin sannan suka bi bayan shi suka shiga cikin gidan,a falon gidan suka yada zango inda suka ajiye wannan abun da ba wanda ya san meye a ciki.

"Bisimillah DPO ga wajen zama" Mahaifin Afrah É—in ya faÉ—a yana nuna musu kujera.

"Alhaji ai zama bai kama mu ba tukunna, inspector jamil buÉ—e musu wannan gawar su gani ko an dace"

Daram gaban duk jama'ar cikin falon ya buga jin abun da DPO ɗin ya faɗa,ai basu ƙara tsinkewa da lamarin ba sai da suka yi arba da abun da yake cikin wannan zanin a lulluɓe,take wasu daga cikin mutanen falon suka dinga zubewa suna sumewa masu ƙarfin halin cikin sune kawai suka tsaya a ihu kawai.

*MANGA* ✍️
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_ 💀☠️)

_Tsarawa/Rubutawa_

© *SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S* *ASSOCIATION*

*SADAUKARWA* : _Wannan book É—in gaba_ _É—ayan shi Sadaukarwa_ _ne gareku Anty Hadiza D_ _Auta, Sis Adam Amira_ _Alkhairin Allah ya_ _kai muku a duk inda_ _ku ke ina son ku_ _fisabillillahi_ .

*Free book*

----------------------------------------
*Bissimillahir rahmani* *rahim*

*002*
__________________________

Ba komai mutanen suka yi arba da shi ba wanda ya firgita su face arba da suka yi da gawar Afrah wadda idanunta duka biyu suke a ƙwaƙule, idan ban da shi babu wani abu da zaka kalla a jikin ta kace gawa ce domin kuwa babu ta inda aka bar alama ko shedar irin kisan da aka mata ɗin.

Ihu ne ya cigaba da tashi a cikin falon nan da nan kafin kace mai masu raunin zuciyar cikin su har sun fara yanakar jiki suna zubewa a ƙasa suna sumewa, ciki kuwa har da mahaifiyar Afrah, masu dauriya da ƙarfin halin su ne waɗanda suka tsaya a kuka kawai, gaba ɗaya falon ya hautsine baka jin komai sai iface-ifacen mutane. Duk yadda wannan Dpo ɗin ya su ya sa mutanen falon su yi shiru abun ya gagara,da ƙyar dai wasu suka ɗan tsagaita inda Dpo ɗin ya dubi mahaifin Afrah mai suna Alhaji Shareef yace.

"Alhaji kuyi haƙuri da abun da ya faru ku ɗauki hakan a matsayin ƙaddarar ku,domin kuwa ita ƙaddara bama iya hanata aukuwa,duk yadda muka so mu kauce mata hakan ba zai taɓa yiwuwa ba,sai dai mu rungume ta hannu bibbiyu ko da kuwa bata zo mana da daɗi ba" Dpo ɗin ya ƙarashe maganar cikin son ya kwantarwa da mahaifin Afrah hankali duk da kuwa ya san abu ne da kamar wuya.

Ɗago kai mahaifin Afrah yayi wanda idon shi suka kaɗa suka yi jawur sannan cikin shesheƙar kuka ya fara magana.

"Yanzu Dpo da gaske ƴata ce Afrah a kwance a gabana?, innalillahi wa'innailaihi rajiun,wannan wace kalar BAƘAR ƘADDARA ce haka?, fisabillillahi mai Afrah ta aikata wanda ta cancanci wannan hukuncin?, Wallahi duk wanda ya aikata mana wannan mummunan aikin ba zamu taɓa yafe mishi ba". Ya ƙarashe maganar yana fashewa da kuka kamar wani ƙaramin yaro.

"Ahhh Alhaji Shareef abun da nake so da kai shine dan Allah kuyi haƙuri a halin yanzu Afrah addu'ar ku kawai tafi buƙata, shi kuma duk wanda yake da hannu a cikin wannan aika-aikar inshAllah zamu yi iya bakin ƙoƙarin dan ganin mun gano ko waye kuma mun bi mata haƙƙin ta".

"Wallahi duk wanda ya aikatawa ƴar uwar mu wannan aikin zaluncin ba zamu taɓa yafe masa ba, sannan ko waya sai mun yi Shari'a da shi matuƙar aka gano shi" Cewar Aliyu yayan Afrah.

A dai-dai wannan lokacin ne kuma Anwar saurayin Afrah da zata aura ya faɗo cikin falon kamar an jaho shi,kallo ɗaya zaka yiwa fuskar shi ka hango tsantsar tashin hankalin da yake kwance a kanta. Da gudu ya ƙarasa kan gawar Afrah ɗin da take shimfiɗe a tsakar falon inda ya zuba duka gwaiwowin shi a saitin ta,kamar wani zauttace haka ya fara magana.

"Afrah wana marar imani da tausayin ne ya aikata miki wannan ɗanyen aikin?, Afrah meyasa za'a raba mu?, Afrah meyasa zaki tafi ki barni?, Kai! Ƙarya ne Afrah ki tashi nasan kina jina kuma nasan baki mutu ba, Afrah dan Allah ki tashi ki gayamana wanda ya aikata miki wannan aika-aikar" Anwar ya ƙarashe maganar cikin sakin wani kuka mai ratsa zuciya ga fuskar shi duk ta ɓaci da hawaye da majina.

DPO ɗin ne ya ƙarasa inda Anwar yake tsugune sannan ya dube shi cikin tausayawa ya fara magana.

"Haba mana aboki na be a man mana,ya zaka zauna kana kuka kamar wata mace, common share hawayen ka dan Allah,ka sani kamar yadda na muku alƙawari inshAllah zamu yi iya bakin ƙoƙarin mu dan gano wanda yake da hannu a cikin wannan kisan". DPO ɗin ya ƙarashe maganar cikin ƙarfafa gwaiwa.

Hannu Anwar ya sanya ya share hawayen da suka ɓata mishi fuska sannan ya dubi DPO ɗin yace.

"DPO dole nayi kuka domin kuwa an cuce ni matuƙar cutarwa, DPO wannan wana irin zalunci ne ace sai ana saura kwana uku aure na a kashe mun mata,ai kuwa kaga kuka ya zama dole, Allah ya ji ƙanki Afrah, Allah ya tona asirin duk wanda ya miki wannan aika-aikar".

A dai-dai wannan lokacin ne kuma mahaifiyar Afrah ta farka daga suman da tayi ɗin,inda ta farka da wani razannannen ihu ta koma kamar wata taɓɓaɓiya ta dinga wani irin fisge-fisge tana wasu irin surutai marrassa kan gado.

"Ku ƙyale ni in je wajen ƴata wallahi ƙarya kuke mun ƴata bata mutu ba bacci take", Haka ta dinga faɗa inda daga baya sai ta koma daga ta yi kuka sai kuma tazo ta kwashe da wata irin dariya irin dai ta mahaukata sabon kamu,da ƙyar aka shiga riƙe ta tana fisgewa duk wanda yake cikin falon sai da ta bashi tausayi, da yawa sai suka daina kukan mutuwar Afrah suka koma kukan tausayawa mahaifiyar ta.

Waya DPO ya ɗaga inda ya ƙira ma'aikatan asibiti akan su zo su wuce da gawar Afrah mutuary har sai an kammalla bincike, lokacin da ma'aikatan lafiyar suka ƙaraso sai da likita ya ƙara duba Afrah inda ya ƙara tabbatar mu su da cewar Afrah fa ta riga mu gidan gaskiya. Ita kuwa mahaifiyar Afrah sai da aka mata allurar bacci wai dan ta yi bacci amma kamar wanda aka ƙara kunnata haka wannan allurar ta maidata.wani tashin hankali ma sai da aka zo fita da gawar Afrah a nan ne fa aka kafa sabuwar sumewa daga wajen ƙanne da yayun Afrah ɗin ita kuwa mahaifiyar ta daman tunin ta sume ya kai sau ba adadi.

Haka dai suna ji suna gani aka fice da gawar Afrah É—in aka kaita asibiti aka ajiye ta a mutuary har zuwa sanda Æ´an sanda zasu gama binciken su.

*****

Yau Sati guda Kennan da mutuwar Afrah amma gidan su afrah kamar yau aka yi mutuwar domin kuwa su kullum mutuwar sabuwa take zamowa a wajen su.

A ɓangaren Anwar ma kullum a gidan su Afrah yake yini har zuwa dare kafin daga bisani ya tafi gidan su. Yau ma kamar kullum ƙarfe goma ya tashi tafiya gida kamar yadda ya saba, lokacin da ya isa gidan bai tarar da ƴan gidan su a falo ba kowa ya shige ɗaki ya kwanta, shima ɗakin nashi ya nufa,inda ya tura ƙofar ɗakin ya shiga,kasancewar wutar ɗin ɗakin a kashe yake ya sanya ya nufi wajen makunnar wutar ya kunna, tabbas da Anwar ya san abun da zai yi tozali da shi idan ya kunna wutar da bai fara kunnawa ba, lokacin da haske ya gama gauraye illahirin ɗakin ne ya juya da niyyar nufar wajen gadon shi. Turus! Ya ja ya tsaya sakamakon arba da mace da yayi a zaune a tsakiyar gadon shi ta juya mishi baya kanta ba ɗankwale gaba ɗaya gashin ta ya barbazu a kan gadon, wani mugun tsoro ne ya mamaye zuciyar Anwar ɗin har sai da ya haɗiyi wani yawu ji kake Muƙuttt wucewar yawun zuwa maƙoshin shi, a hankali ya fara takawa ya nufi wajen gadon duk da irin bugun da zuciyar shi ta ke mishi hakan ba sai ya dakata da isa wajen gadon ba,hannu ya miƙa da niyyar juyo da fuskar ta ta sai dai tun kafin hannun nashi ya sauƙa a jikin ta ta juyo da kanta suka yi arba da juna fuskarta shaɓe-shaɓe da hawaye sai dai kuma a maimakon ya ga ruwan hawaye sai ya ga jini ne yake kwaranyowa daga cikin idanun nata, suman tsaye Anwar yayi cikin rawar murya ya fara nuna ta da hannun shi yana ƙoƙarin furta sunan ta Amr..... Amma ina! Tun kafin ya ƙarasa yaji kamar an saka igiya an ɗaure mishi wuya take ya yanki jiki ya faɗi a wajen.

Anwar bai tashi tsintar kan shi a ko ina ba sai a gadon asibiti ana mishi ƙarin ruwa, ƙoƙarin miƙewa zaune yake amma ya kasa a hankali ya fara ƙoƙarin tuno abun da ya faru dashi amma abun mamaki hakan ya gagara duk wani ƙoƙarin sa na ganin ya tuno abun da ya faru ɗin ya kasa inda take ya ji kan shi ya ɗauki wani matsanancin ciwo,dafe kan nashi yayi tare da runtse idanun shi, mahaifiyar shi ce ta fara mishi sannu.

"Sannu Anwar ka tashi ya jikin dai?". Ta jefa mishi wannan tambayar da sauri yayi saurin buɗe idanun shi da suke a runtse dan ganin wanda yake mishi sannun domin kuwa a maimakon ya ji muryar mahaifiyar shi sai ya ji wata murya daban wadda ko shekara ɗari yayi wannan muryar bazata taɓa zama sabuwa ko baƙuwa a gare shi ba,ga mamakin shi yana buɗe idon nashi sai yaga mahaifiyar tashi ce take mishi sannu, Innalillahi wa'innailaihi rajiun ya shiga maimaitawa a cikin ran shi tare da jefawa kan shi tambayar to mai hakan yake nufi?, Mai yasa muryar ta take mishi gizo?. A hankali ya fara jin alamar kuka a kusa dashi saurin juyawa yayi dan ganin waye aikuwa a take yayi arba da ita a zaune a kusa dashi fuskar ta sharkaf da hawaye, wani ras ya ji gaban shi ya faɗi,da sauri ya juya ya dubi inda mahaifiyar shi take zaune ko ita ma taga abun da ya gani ɗin,sai dai daga yanayin fuskarta ya fuskanci cewa bata ga abun da ya gani ɗin ba,sake juyawa yayi inda take zaune ɗin still tana zaune sai dai a wannan karon murmushi take mishi, addu'a ya fara yi duk addu'ar da tazo bakin shi, aikuwa ba'a ɗauki lokaci ba ya nemeta ya rasa, kallon mahaifiyar shi yayi sannan ya buɗi baki da niyyar sannar da ita abun da ya faru ɗin sai dai kamar mai cutar mantau haka yaji komai ya kuma shafewa a ƙwaƙwalwar shi.

*****

*AHMADU BELLO* *UNIVERSITY ZARIA*

Babbar jami'a ce da ta amsa sunan ta jami'a domin kuwa tana ɗaya daga cikin manyan jami'o'in da muke da su a Nigeria,ko ina ka waiga a cikin jami'ar ɗalibai ne ta ko ina kowa yana harkar gaban shi. Wata matashiyar budurwa na hango wadda a ƙalla bazata haura shekaru ashirin da biyu zuwa da uku haka,tafe take a cikin makarantar ta fito daga wajen Admin Block inda ta nufi hanyar hostel ɗin mata, fuskarta kaɗai zaka kalla ka fuskanci tsananin farin cikin da take ciki,wayar ta ce ta fara kuka alamar tana neman agaji,ɗaukan wayar tayi murmushi shimfiɗe a kan fuskar ta sannan ta kara wayar a kunne tare da furta.

"Dad barka da rana"

Daga ɗayan ɓangaren wani dattijon mutum ne zaune a wani ƙayattaccen falo wanda ya gaji da haɗuwa amsawa yayi tare da furta.

"Daughter ya result domin kuwa idan ban manta ba yau kika ce zasu manna muku?".

Murmushi tayi kafin daga bisani tace.

"Dad as usual Kai ma kasan ai bazan taɓa baka kunya ba,Dad result ɗina yafi na kowa kyau na kasance wadda tafi kowa highest mark a Depertment ɗin namu".

"Masha Allah Daughter congratulations Ubangiji ya cigaba da dafa miki,ya sanyawa karatun ki Albarka".

Da Ameen ta amsa sannan suka yi sallama ta kashe wayar, a dai-dai sannan kuma ta ƙaraso bakin ɗakin su,inda ta sanya mukuli ta buɗe ƙofar,Chaɓal taji ta jefa ƙafarta a cikin wani abu mai yauƙi, cikin sauri ta kai duban ta kan ƙafarta da take ƙoƙarin zarewa daga cikin abun, Daramm gaban ta ya faɗi sakamakon arba da jini da tayi male-male a tsakiyar ɗakin nasu kamar an yanka rago,jikin ta ne ya fara wani irin karkarwa take wata irin zuffa ta fara keto mata, ai bata gama shiga ruɗani ba taga wannan jinin ya fara dunƙulewa waje guda a hankali har ya gama curewa waje ɗaya sai gashi ya fara komawa siffar mutum, wata irin mummunar hallita ce ta bayyana a gabanta idon hallitar guda ɗaya ne kuma a tsakiyar ka,sai wasu ƙafo masu matuƙar tsini guda biyu da suke gefen idon, tsayin hallitar kuwa ba zai faɗu ba domin kuwa tsayin ta har ya tokare silik ɗin ɗakin, lokaci guda kuma fuskar wannan hallitar ta juye zuwa fuskar Amrah. Ido ta zaro waje take kuma ta buɗe baki da niyyar yin ihu sai dai kafin ta kai ga sakin ihun taji wata irin guguwa ta kwashe ta inda ta jita a sama tana gudu kamar wani jirgi,da ƙoƙarin da take na ganin ta buɗi baki tayi ihu ko zata samu mai kawo mata agaji hakan ya faskara inda aka shiga gwara mata kai a kowane kusurwa na cikin ɗakin,take aka haɗa mata jini da majina,sai da ta suma ta farfaɗo saboda azaba kafin daga bisani aka yi jifa da ita ta bugu da jikin ƙofar toilet ɗin ɗakin,sannan aka shiga ƙiran sunan ta da wasu irin muryoyi mabanbanta.

"Azraaaaaaàa!,Azraaaaaa!, Azraaaaaa! yau zaki girbi abun da kika shuka,yau zan ɗauki Fansar abun da kuka aikata mun, FANSA! FANSA!FANSA! Na dawo ɗauka". Ana kaiwa nan a maganar aka bushe da wata irin dariya mai haɗe da kuka wadda tayi sanadiyar Sumewar Azraa.

*MANGA*✍️
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_ ☠️💀).

_Tsarawa/Rubutawa_

© *SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION* .

*SADAUKARWA*: _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku Anty Hadiza D auta, Sis Amira Adam_ _Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda kuke_ _ina son ku fisabillillahi_ .

*Free book*

----------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*003*
__________________________

Sauƙar ruwan sanyin da taji a jikin ta ne ya sata farfaɗo wa daga sumar da tayi ɗin,a hankali ta shiga buɗe idanun ta wani irin haske ne mai ƙarfi da ta gani ya sanyata saurin mayar da idonta ta sake rufewa,ƙarar takun tafiya ta dinga ji wanda sautin tafiyar yake bayar da ƙarar tafiyar dawakai,ƙirjin ta ne ya shiga dakan lugude zuciyarta kamar zata fito saboda tsananin tsoro da firgicin da take ciki.

Da ƙyar Azra ta iya ƙarfin halin sake gwada buɗe idanun inda take ta tsinci kanta a wani wawaken fili a tsakiyar dokar daji ba gida gaba bare baya.

Ƙoƙarin miƙawa ta fara yi domin guduwa, Sai dai ta kasa sakamakon wata irin sarƙa (ankwa) da aka sanya aka ɗaure ta da ita,kiciniyar kunce kanta ta fara amma ina kamar ma wanda take ƙara ɗaure wannan sarƙar a jikin ta gashi har a wannan lokacin bata daina jin ƙarar sautin tafiyar dawakan ba.

Kamar wadda aka ce ɗaga kan ki sama aikuwa ta hango mace daga nesa cikin shigar baƙaƙen kaya ta nufo inda take, tun daga yanayin tafiyar matar ta gane wacece, numfashin ta ne taji yana barazanar ɗaukewa sakamako arba da fuskar wadda ko ta mutu ta dawo ba zata kasa gane ta ba, ƙoƙarin magana ta fara yi amma kamar wanda aka sanya abu aka shaƙe mata maƙoshi haka ta kasa furta ko da kalma ɗaya, wasu hawayen azaba ne da nadama suka shiga kwaranyowa ta kumatun ta.

Murmushi mai haÉ—e da kuka Amra ta fara sakarwa Azra har ta iso dai-dai wajen da Azra É—in take É—aure sannan ta sanya hannun ta É—ago fuskarta tare da fara magana.

"Azra har yanzu banga alamar tsoro ko danasani a tare da ke ba?, Azra nasan fuskata ba zata taɓa zama baƙuwa a wajen ki ba".

Sai a sannan Azra taji an sake mata maƙoshi inda ta fara magana cikin rawar murya.

"Amrah daman baki mutu ba? Amrah wallahi nayi nadama, Amra dan Allah kar ki kashe ni, Amrah wallahi ban shiryawa mutuwa a yanzu ba".

Wata irin dariya mai sauti Amra ta sake wadda har sanda gaba É—aya dajin ya amsa kafin kuma daga bisani ta haÉ—e fuska kamar ba ita tayi dariyar ba sannan take ta rikiÉ—e ta koma wata irin shirgegiyar hallita ba daÉ—in kallo, sannan ta fara magana cikin wata iriyar murya marar daÉ—in ji da sauraro.

"Azra tabbas zaki mutu kuma a yau ba sai gobe ba,tabbas zaki yi mutuwa marar daɗin kallo,tabbas zaki wulaƙantacciyar mutuwa, Azra mutuwar ki zata zama mutuwa mafi muni daga cikin mutuwar da Five Stars zasu yi, oh I mean Four star's domin kuwa ni bana cikin ku, na daɗe da cire ku a cikin abokanai na, Azara mutuwar ki sai ta hargitsa duk wani mutum da yake numfashi a doron ƙasa domin kuwa sai na yagalgala ki yadda ko gawar ki da ƙyar za'a iya ganewa,hatta ƴan jarida sai sun ji tsoro da shayin yaɗa gawar ki saboda tsananin munin da gawar ta ki zata yi, zaki yi mutuwar wulaƙanci fiye da wadda Afrah tayi domin kuwa tata mutuwar Nafila ce idan har aka ga taki,Hmmm Azra ai ko zan yafewa kowa ban da ke, Azra kin manta cewar kece ummul aba'isin duk wata cutarwa da aka mun, ki sani tun ina yarinya na yadda da wannan karin maganar ta hausawa wadda ake cewa Rama cuta ga macuci ibada ne".

Da sauri Azra ta É—ago ta kalli Amra sannan tace.

"Amrah wai kina nufin ke kika kashe Afrah?".

"Ƙwarai kuwa nice ko kina tantama ne".

Buɗe baki Azra tayi da niyyar yin magana sai dai wata shaƙa da azra ta mata ya sanya ta kasa furta komai,kamar yadda Amra ta cakawa Afrah farce a ido lokacin da zata kashe ta haka yanzu ma ta aikatawa Azra,wani mugun ihu Azra ta sake sannan daga haka bata ƙara sanin abun da ya faru da ita ba sakamakon ɗaukewar da numfashin ta yayi, Amrah hannu ta sanya ta tsaga wuyan Azra ɗin inda ta ciro maƙoshin ta, daga haka ta dinga bin duk wani sassan jiki na Azra wanda yake guda biyu ne ta dinga cire guda ɗaya sai da ta gama da wannan kafin kuma ta zo ta cire mata gaba ɗaya kayan jikin ta ta ɗauke ta a bayan ta suka ɓace daga cikin dajin a lokacin Azra ta daɗe da sheƙawa barzahu.

Kai tsaye Amrah tsakiyar cikin jami'ar Ahmadu Bello University ta wuce da gawar Azra ta yasar da ita a tsakiyar makarantar yadda kowane ɗalibi zai ganta gata tsirara haihuwar uwar ta, kasancewar lokacin ƙarfe biyu na dare filin makarantar tsit shiyasa ba wanda ya san abun da ya faru.

*****

A can Hostel ɗin su Azra kuwa ƙawayen ta Amira da Anisa ne suka shigo cikin ɗakin inda basu tarar da Azra ba, basu kawo komai a ran su ba suka ci gaba da harkokin gaban su, inda suka yi tunanin ko tana Library ne.

Amira ce ta juya ta dubi inda Anisa take kwance hannun ta riƙe da littafi sannan tace.

"Ke Ani nifa na fara tsorata da rashin dawowar Azra, ko ta faÉ—a miki inda zata je ne?".

Rufe littafin hannun ta Anisa tayi sannan ta dubi Amira tace.

"Wallahi nima kawai dai nayi shiru ne amma tun É—azu gaba na sai faÉ—uwa yake, amma bari mu ga zuwa anjima idan bata dawo ba sai muje mu duba ta ko a Library É—in ne".

"Ok to shikennan Allah dai ya sa lafiya ni kam".

Da Ameen Anisa ta amsa sannan ta koma ta kwanta.

Sai dai abu kamar wasa sai gashi har zuwa ƙarfe goma na dare ba Azra ba labarin ta,tun hankalin su baya tashi har ya kai sun fara shiga damuwa,inda suka fara tambayar ɗakunnan da suke kusa da nasu ko da wanda ya san inda Azra ɗin taje amma kowa sai yace bai ganta ba.

Library suka nufa suka duba amma nan ma bata nan, duk wani waje da suke tsammanin zasu ga Azra ɗin basu gan ta ba,gashi sun ƙira wayar ta sai ringing take ba'a ɗaga ba.

Abun da ya ƙara sanya hankalin su tashi shine duk inda Azra zata je bata wuce ƙarfe sha ɗaya na dara zata dawo, sai gashi yau har sha ɗaya da rabi babu ita ba alamar ta.

Haka suka kama hanya suka juya suka koma Hostel zuciyoyin su cike da zulumi, suna shiga É—akin Anisa ta fara cin karo da wayar Azra a yashe a gefe,sunkuyawa tayi ta É—auki wayar gaban ta yana cigaba da bugawa sannan ta juya ta kalli Amira tace.

"Tabbas ba lafiya ba, tabbas na yadda wani abu ya faru da Azra domin kuwa ni na tabbata Azra ba zata taɓa fita ta bar wayar ta ba, duba da yadda Azra take da waya ko toilet bata yadda ta shiga ba tare da ita ba".

"Innalillahi wa'innailaihi rajiun, to mai yake shirin faruwa haka?" Amira ta faÉ—a ita ma cikin tashin hankali.

"Nifa wallahi daman tun ranar da aka ce an kashe Afrah jikina ya fara yin sanyi, ya Ubangiji kasa ba wani abu bane ya faru da Azra". Cewar Amira É—in tana zama a bakin gado tare da dafe kan ta.

"Ameen ya Allah Amira yanzu mu bari zuwa safiya sai muje muyi repoting a School management domin a san matakin É—auka tun kafin wani abu ya faru, tun da kinga yanzu past twelve Kinga dare yayi ko".

Ita dai Amira bata iya cewa komai ba sai juyawa da tayi ta kwanta tana jin zuciyarta kamar zata fito saboda tsoro fa tashin hankali da kuma firgicin da take ciki É—in.

Haka dai su Anisa da Amira suka kwana cikin taraddaddi, ba wanda ya iya wani isasshen bacci a cikin su.

*****

Yau tun asubar fari jami'ar Ahmadu Bello É—in aka tashi da wani mummunan tashin hankali wanda ya gigita duk wani mazaunin cikin makarantar,domin kuwa wannan sabon abu ne a tarihin makarantar shine tsintar gawar Azraa da aka yi cikin mummunan yanayi.

Filin makarantar tunin ya fara cika da É—alibai inda duk wanda yayi arba da gawar Azra É—in sai ya zubar mata da hawaye, mata kuwa take wasu masu raunin zuciyar suka dinga zubewa a wajen domin kuwa kallo É—aya zaka yiwa gawar ta ta kaji a ranka baka sha'awar sake ganin ta.

Da gudu Anisa da Amira suka ƙaraso wajen waɗanda suka sami labari yanzu.

Kutsawa suka fara yi ta tsakanin mutanen inda take aka shiga basu hanya sanin irin ƙaƙarfar alaƙar da take tsakanin na su.

Amira ce ta fara tozali da gawar Azra ɗin cikin mummunan yanayi, tun daga kallon farko da ta yiwa gawar bata ƙara sanin inda kan ta yake ba.

Ita kuwa Anisa durƙushe wa tayi a wajen ta daskare inda ta zama kamar mutum-mutumi harbawar da numfashin ta yake ne kawai zai tabbatar maka da cewar tana da rai amma duk wani magudanar aiki na jikin ta take suka daina aiki.

Haka aka sure su ita da Amira aka yi asibiti da su.

A dai-dai wannan lokacin ne kuma hukumar makarantar suka ƙaraso wajen tare da ƴan sanda.

Darewa mutane suka fara yi inda aka bawa jami'an tsaron hanya suka shiga inda gawar Azra É—in take.

Saurin rintse idanuwan su suka yi sannan Inspector Rasheed (inspector ɗin da case ɗin Afrah yake hannun shi) yayi saurin cire rigar sanyin da take jikin shi kasancewar doguwa har gwaiwa ce inda yayi saurin lulluɓe jikin Azra da ita, sannan ya juya cikin ɓacin rai ya dubi dandazon maza da matan da suke wajen.

"Allah wadaran naka ya lalace, yanzu kaf cikin ku aka rasa wanda zai suturtawa wannan baiwar Allahn jikin ta, idan ƙanwar ku ce zaku bar ta haka ne?, Ku duba halin da wannan yarinyar take ciki tsirara haihuwar uwar ta amma ba wanda yayi tunanin rufe mata jiki, Allah ya kyauta".

Duk wajen shiru suka yi inda wasu suka fara ƙoƙarin Sunkuyar da kan su wai saboda kunya.

A dai-dai wannan lokacin ne kuma jami'an lafiya suma suka iso, inda wani likita daga cikin su ya fara ƙoƙarin gwada Azra ɗin duk da kuwa kallo ɗaya zaka mata ka fuskanci ta daɗe da zama gawa.

Sai da ya gama gwada ta sannan ya dubi inspector Rasheed yace.

"Inspector wannan yarinyar fa ta daÉ—e da zama gawa".

"Likita na riga da na sani dan haka ku É—auke ta ku wuce da ita zuwa Mutuary kafin zuwa mu kammalla investigation a kan ta".

Ƙarasowa wajen ma'aikatan asibitin suka yi inda suka fara ƙoƙarin ɗaukan ta, a lokacin kuwa tunin ƴan jarida sun cika wajen inda suka shiga nasu aikin kowa buƙatar shi shine ya ɗauki hoton gawar domin ya samu abun yaɗawa yau.

Har ma'aikatan asibitin sun fara ƙoƙarin ɗaga Azra kawai suka tsinkayi muryar Inspector Rasheed yana cewa cikin ƙaraji.

"Ku dakata!"

Ya faÉ—a yana kai duban shi zuwa dai-dai wuyan Azra É—in.

Saurin kallon shi mutanen wajen suka yi kowa buƙatar shi shine yaji dalilin da ya sanya Inspector Rasheed ɗin ya dakatar da ɗaukar gawar.

Wasu daga cikin mutanen wajen ne suka kai duban su saitin inda suka ga Inspector Rasheed É—in yana kallo domin su ma su bawa idon su abinci.

*MANGA*✍️
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_☠️💀 ).

_Tsarawa/Rubutawa_

© *SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku Anty Hadiza D auta, Sis Amira Adam_ _Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda kuke ina son ku fisabillillahi_ .

*Free book*

------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*004*
___________________________

Kallon wani jami'in ÆŠan sanda Inspector Rasheed É—in yayi sannan yace a bashi safan hannu (Hand gloves) sanyawa yayi a hannun shi sannan ya nufi kan gawar Azra É—in.

Durƙusawa yayi dai-dai saitin wuyan ta.

A hankali ya sanya hannu ya ɗan sake janye rigar da ta ɗan rufe mata wuya, wani ƙatoton zanen tambari ne mai alamar tauraro (Star) ya bayyana a wuyan Azra ɗin.

Kafe wajen Inspector Rasheed yayi da ido sannan sannan ya fara tunanin inda ya taɓa ganin wannan zanen.

"Afrah!" Ya faɗa da ɗan ƙarfe sannan ya miƙe tsaye ya juya ya dubi sauran jami'an tsaron yace su tafi asibitin da aka kai gawar Afrah yanzu.

Aikuwa gaba É—aya mota suka shiga tare da ma'aikatan lafiyan da kuma hukumomin makarantar wasu daga ciki inda suka nufi asibitin da aka je aka adana gawar Afrah É—in, tare da tafiya da gawar Azra domin zuwa a adana tata gawar ita ma.

Suna isa cikin asibitin kai tsaye É—akin da ake ajiye gawarwaki su Inspector Rasheed suka nufa.

Babban ɗaki ne mai girman gaske wanda tsayawa faɗin girman ɗakin ma ɓata lokaci ne.

Akwatuna ne a jere a cikin É—akin sun fi guda hamsin da alamu sune akwatunan da ake ajiye gawarwaki a cikin sa.

Wani akwati da yake can gefe aka wuce da gawar Azra aka sanya ta a ciki.

Wajen wani akwati Inspector Rasheed ya nufa sannan ya buƙaci ma'aikatan asibitin da su buɗe mishi akwatin.

Ana buÉ—ewa kuwa sai ga Afrah a kwance a ciki kamar kace mata tashi ta tashi.

Kallon ta ya fara yi tun daga sama har a ƙasa take idon shi ya sauƙa akan wannan ƙaton zanen na wuyan ta mai alamar tauraro irin wanda ya gani a wuyan Azra ya bayyana.

Ya É—auki tsawon lokaci yana nazarin wannan zanen kafin daga bisani ya sanya wayar shi yayi snapping wajen sannan ya juya suka fice a É—akin.

Suma ma'aikatan asibitin juyawa suka yi suka fita.

Ko gama rufe ƙofar ɗakin ba su yi ba Amrah ta dira a cikin ɗakin cikin mummunar suffa.

Lokacin da inspector Rasheed suka fita daga cikin É—akin da aka adana gawarwakin motar su suka nufa sannan suka tayar da motar suka nufi komawa police station É—in na su.

Sosai Inspector Rasheed ya shiga tunani da nazarin wannan zanen da ya gani a wuyan su, to mai hakan yake nufi?, Shin wannan zanen na meye ne?.

Jami'in ÆŠan sandan da yake gefen Inspector Rasheed ne ya juyo ya dube shi sannan ya lura da halin damuwar da shugaban nasu yake ciki.

"Yallaɓai akwai damuwa ne?". Ɗan sandan ya tambayi inspector Rasheed cikin girmamawa.

Sauƙe numfashi inspector Rasheed yayi kafin ya dube shi yace.

"Kofur Bala wallahi wani abu ne ya fara É—aure mun kai game da waÉ—annan gawarwaki biyun da aka tsinta".

Shiru ya É—an yi kafin daga bisani ya cigaba da magana

"Watau abun da yake É—aure mun kai wanda nasan ba lalle ku kun lura da shi ba shine, shin baku lura da cewar irin kisan da aka yiwa Afrah shi aka yiwa Azra ba?".

ÆŠan shiru Kofur Bala yayi kafin daga bisani yace.

"Tabbas Yallaɓai sai yanzu tunanina ya kai kan abun,to mai hakan yake nufi Kennan?".

"Tabbas na fara zargin wani abu domin kuwa duba da irin kisan da aka musu ya zama iri É—aya sannan ga wani alama da makashin na su ya bari wadda dole za'a zargi cewar mutum É—aya ne yake kisan".

Inspector Rasheed ya faÉ—a yana kai kallon shi zuwa kan titi.

"Kennan yallaɓai kana nufin kace mun makashin waɗannan ƴammatan mutum ɗaya ne?".

Cewar Kofur Bala É—in cike da mamaki.

"Ina tunanin hakan amma koma mainene bincike zai tabbatar da gaskiyar lamarin".

A dai-dai sannan ne kuma suka ƙaraso bakin ofishin na su.

Lokacin da suka isa ne ake sanar dashi cewar mahaifin Afrah sun zo neman shi amma sun ce zasu dawo.

Bai amsa ba sai wucewa cikin office ɗin shi yayi domin kuwa yana buƙatar kaɗaicewa shi ɗaya domin yin nazari game da kisan waɗannan ƴammatan.

*****

A cikin gidan su Azra kuwa mahaifin ta ne zaune akan dining table suna breakfast da shi da mahaifiyar Azra É—in cikin farin ciki da annashuwa.

Wayar shi ce da take gefe ta fara ruri alamar tana neman agaji.

Miƙa hannu yayi sannan ya ɗauki wayar inda ya ga baƙuwar number ce, tsaki ya ja sannan yayi rejecting call ɗin ya ajiye wayar a gefe.

Kallon shi mahaifiyar Azra tayi da mamaki sannan tace.

"Ranka ya daɗe lafiya kuwa?,tun da muka zauna a wajen nan naga ana ta ƙiran wayar ka a jere a jere a ƙalla an maka ƙira ya kusa goma amma kana rejecting, ka daure ka ɗaga kaji wataƙila ƙiran gaggawa ne ".

"Hmmm ba wani ƙiran gaggawa fa,ke kin fi kowa sanin policy na bana ɗaga ƙiran baƙuwar number dan haka ba wani ƙira da zan ɗaga, duk masu buƙatar magana dani su nemi ni da number ɗin da na san su".

Mahaifin Azra ɗin ya faɗa yana mai kurɓar ruwan tea ɗin da yake gaban shi.

"Amma Ranka y........

Saurin É—aga mata hannu mahaifin Azra É—in yayi sannan yace.

"Kinga dan Allah muci abinci,kinga har wajen ƙarfe tara ban tafi wajen aiki ba, ki share masu min ƙiran nan nasan ba zasu wuce irin ƴan neman taimakon nan ba".

Iyayen Azra irin waɗannan mutanennan ne waɗanda basu da abokin gaba kamar talaka,mahaifin Azra ya kasance mutum ne da babu wanda yake raɓar dukiyar shi face tillon ƴar shi Azra da kuma matar shi kasancewar iyayen shi sun rasu to sai ya zamana ko dangin shi basa cin kuɗin shi balle kuma wani bare. Duk da irin tarin dukiyar da Allah ya masa ɗin, mahaifin Azra ƙwararran lauya ne wanda ya san aikin sa inda a yanzu haka har ya kai matakin justice. A wani ɓangaren kuma ɗan kasuwa ne domin kuwa yana da manyan shaguna a kasuwannin Kano da kuma Kaduna da Zaria, sai dai ya ɗauki wata banzar aƙida ta ƙin talaka ya dasa a ƙashin ranshi sai kuma aka yi dace ya haɗu da mata mai irin halin shi,sunan shi Justice Kabir inda ita kuma mahaifiyar Azra sunan ta Hajiya Ikilima. Sai kuma gashi Allah ya basu yarinya wadda take bata da tarbiyya ko kaɗan ko dan daman ba'a koya mata ba.

*BACK TO THIS* 👇🏻

Murmushi mahaifiyar Azra É—in tayi

"Aikuwa dai kasan talakawan nan da shegen naci wallahi, basu ajiye maka ba amma sai shegen roƙo".

Dariya suka yi gaba É—aya
sannan suka cigaba da cin abincin har suka kammalla.

Miƙewa yayi yana shirin ɗaukan jakar office ɗin shi,a dai-dai sannan ne kuma mai gadin gidan ya shigo inda ya zube har ƙasa ya fara gaishe da su.

A yatsine mahaifin Azra É—in ya amsa sannan yace.

"Lafiya kuwa Iro?".

Duk da kasancewar mutumin tsoho wanda na tabbata zai iya haifar mahaifin Azra ɗin amma kuma hakan bai sanya ya bashi girma ba sai ya ƙira shi da sunan shi garangatsau.

"Ranka ya daÉ—e daman jami'an Æ´an sanda ne suka zo suna waje sun ce a musu magana da kai".

Kallon juna suka yi shida matar ta shi kafin kuma ya sake furta kalmar Æ´an sandan da mai gadin nashi ya faÉ—a.

"Ƴan sanda kuma?, Kuma suka ce maka wajena suka zo?".

"Eh Ranka ya daÉ—e".

Mai gadin ya ƙara bashi amsa yana ƙara risinawa.

Kallon mahaifiyar Azra yayi sannan yace.

"Ikilima bari naje na gani".

"A'a Yallaɓai ai tare zamu je ƙafata ƙafar ka,domin kuwa wallahi jikina ya bani ba lafiya ba, kar kaji yadda ƙafafuwa na suke rawa" mahaifiyar Azra ɗin ta faɗa fuskarta da alamun damuwa sannan suka juya suka nufi harabar gidan inda ƴan sandan suke.

Suna isa Mahaifin Azra ya fara bin su da kallo sannan ya ce.

"Lafiya kuwa na ganku a gidana da safiyar Allah nan?, Nasan dai idan wani case ne a office zaku same ni ba'a gida ba".

Ya faÉ—i maganar yana yatsina fuska.

Murmushi inspector Rasheed yayi sannan ya miƙa mishi hannu su gaisa.

"Yallaɓai duk wani ƙoƙari da zamu yi na muga mun samu wayar ka ba sai mun zo gidan ba abun ya gagara domin kuwa mun maka ƙira yafi sau a ƙirga baka ɗagawa".

"Tsarina ne bana ɗaga baƙuwar number".

Mahaifin Azra ya faɗa a taƙaice.

Murmushi Inspector Rasheed yayi domin kuwa ya daÉ—e da sanin halin Justice Kabir É—in dan haka wannan ba abun mamaki bane a wajen sa.

"Ok to shikennan Yallaɓai ,magana ce take tafe damu magana ce wadda take buƙatar nutsuwa, waɗannan mutanen da kake gani hukumomi ne da ga cibiyar karatu ta Ahmadu Bello dake nan garin na Zaria, mun zo ne idan ba damuwa muna so ka biyo mu da kai da matar ka zamu je asibiti da ku".

Wani lalattaccen kallo mahaifin Azra É—in ya bi Inspector Rasheed da shi kafin kuma yace.

"Kaga Inspector ka tafi direct to the point ka sanar dani mai yake tafe daku,domin gaskiya ni ba wani asibiti da zanje yanzu haka ma ga shi nayi lattin fita kotu".

Ya faÉ—a yana kai duban shi kan agogon hannun shi tare da sake tsaki.

Kallon juna mutanen wajen suka yi kowa a zuciyar shi yana Allah wadaran halin Justice Kabir domin kuwa alamu sun nuna bai san darajar É—an Adam ba.

"Ranka ya daÉ—e a haka zaka daure muje asibitin domin kuwa zuwan naka yana da muhimmanci".

ÆŠan shiru yayi kafin kuma daga bisani yace.

"Muje".

"Hajiya har da ke muke buƙatar zuwan ki"

Inspector Rasheed ya faɗa yana kai duban shi wajen Hajiya Ikilima da tayi tsumu-tsumu kamar an jiƙa ɓera a buta .

Haka suka juya gaba É—aya suka nufi asibitin da aka adana gawar Azra É—in shi dai mahaifin Azra ba wai dan ran shi ya so ba.

Suna isa asibitin suka nufi É—akin adana gawa (Mutuary) kai tsaye.

Turus Justice Kabir da Hajiya Ikilima suka ja suka tsaya suna duban Inspector Rasheed duba irin na mai zamu yi a nan É—in.

"Ranka ya daÉ—e ku shigo mana".

Ai da sauri Hajiya Ikilima tace

"Mu shiga ina?, ÆŠakin ajiye gawar!, Ai wallahi idan ka ganni a lahira to kai ni aka yi, Alhaji idan zaka shiga ka shiga amma ni kam ba inda zan shiga".

Juyowa Justice Kabir yayi ya watsa mata wani kallon da bata san sanda ta yi shiru ba, sannan ya juya ya dubi inda Inspector Rasheed yake tsaye tare da cewa.

"Wai Inspector mai hakan yake nufi kunce zamu zo asibiti kuma kun tashi kun wuco damu É—akin ajiyar gawa?".

"Kaga Ranka ya daɗe sai fa kun yi haƙuri domin kuwa dole ce ta sa hakan".

Izuwa yanzu tunin Justice Kabir da Hajiya Ikilima sun fara shan jinin jikin su domin kuwa take jikin su ya basu tabbas akwai wani mummunan al'amari da yake shirin faruwa.

Haka dai suka daure zukatan su inda suka bi bayan su Inspector Rasheed ɗin suka shiga cikin ɗakin ajiyar gawar domin kuwa sun saddaƙar komai ma ya faru.

Suna shiga cikin É—akin Inspector Rasheed ya dubi mai kula da É—akin sannan ya mishi alama da ya janyo akwatin gawar da Azara take ciki.

Kasancewar kowane akwati da sunan gawar da take ciki a manne a jiki ya sanya ana janyo wa akwatin gawar Azra ɗin idanun su Hajiya Ikilima ya sauƙa akan sunan da yake manne a jikin akwatin,sai dai basu kawo komai a ran su ba a tunanin su wata ce mai irin sunan ɗiyar ta su duk kuwa da cewar kowanne da sunan mahaifa a jiki.

In banda rawa babu abun da jikin Hajiya Ikilima yake tsananin tsoron da take ciki har ba zai misaltu ba.

Buɗe akwatin gawar aka fara inda idanun Justice Kabir da na Hajiya Ikilima suka sauƙa akan mutum kwance a miƙe a cikin akwatin sai dai har zuwa wannan lokacin basu fahimci wadda take kwancen ba.

"Alhaji sai haƙuri domin kuwa a rayuwa kun san duk wani mai rai mamaci ne kuma babu wanda ya isa ya tsallake wa mutuwa idan lokacin sa yayi,wannan da kuke gani gawar ƴar ku ce da aka tsinta yau da asuba a cikin jami'ar su wa.......

Ai tun kafin Inspector Rasheed ya kai ƙarshen maganar da yake ɗin Justice Kabir ya maƙure mishi wuya tare da fara magana cikin ƙaraji.

"Sai dai idan ubanka ne ya kashe mun ƴa ta, kaji ɗan bantan uba wanda baya neman gamawa da duniya lafiya". Da ƙyar sauran ƴan sandan suka sanya hannu suka ɓamɓare hannun Justice Kabir daga wuyan Inspector Rasheed ɗin.

Ita kuwa Hajiya Ikilima tun da taji maganar da Inspector Rasheed ɗin ya fara taji gaba ɗaya jikin ta ya ƙara tsanan ta rawar da yake ɗin.

A hankali ta shiga taka ƙafafuwan ta ta nufi wajen akwatin gawar take duk wani tsoron da take ji ya kau.

Aikuwa tana ƙarasawa wajen idanun ta suka sauƙa akan fuskar ƴar ta tillo guda da take da ita cikin mummunan yanayi.

Sulalewa ƙasa tayi ta zube a wajen take numfashin ta ya tsaya cak duk wata jijiya da take jikin ta take ta daina aiki.

Ƙarar faɗuwar Hajiya Ikilima ɗin ne ya dawo da su Justice Kabir daga hargagin da yake musu.

Warwas suka yi arba da ita a ƙasa ba alamar rai bare numfashi a tare da ita.

Tashin hankali Kennan wanda ba'a sa masa rana,kar fa ace Justice Kabir jana'izar gawa biyu zai yi rana?.

*MANGA*✍️
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_💀☠️).

_Tsarawa/Rubutawa_

© *SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda kuke ina_ _son ku fisabillillahi_.

*Free book*

-------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*005*
____________________________

Da gudu Justice Kabir ya nufi kan ta yana ƙiran sunan ta, amma ina! Hajiya Ikilima ko alamar motsi ba tayi balle ya sa ran zata amsa.

Ihu Justice Kabir ya shiga rusawa yana ƙiran ma'aikatan asibitin yana cewa

"Ku yiwa girman Allah ku zo ku taimaka ku ceci rayuwar matata, dan Allah ku taimaka ni, Ikilima dan Allah ki tashi nasan wasa kike, Ikilima wallahi ƙarya suke mana Azaran mu bata mutu ba tana da rai".

Ya ƙarashe maganar cikin hargowa kamar zai tashi asibitin gaba ɗaya.

Da ƙyar aka ƙira wasu Nurses suka zo suka ɗauki Hajiya Ikilima ɗin inda nan ma da ƙyar Justice Kabir ɗin ya bari aka ɗauke ta ɗin.

Shi kuwa Inspector Rasheed wani irin mugun haushin Justice Kabir É—in yake ji yana mishi kallon jahili kuma marar hankali.

Lokacin da aka zo za'a shiga da Hajiya Ikilima ɗakin taimakon gaggawa ma nan ma da ƙyar aka dakatar da Justice Kabir dan wallahi cewa yayi shikam sai ya bi su ciki,da ƙyar dai ma'aikatan suka hana shi, sannan ya haƙura, amma duk da haka zarya ya dinga yi a bakin ƙofar ɗakin yana jiran fitowar likita.

Gwajin farko da likita ya yiwa Hajiya Ikilima ya gano cewar rai yayi halin sa ta riga mu gidan gaskiya sai dai muce Allah ya ji ƙanta.

Fitowa likitan yayi daga É—akin sannan ya dubi Justice Kabir zai yi magana sai dai cikin sauri Justice Kabir É—in ya riga shi inda ya fara magana cikin tashin hankali.

"Likita ya ake ciki dan Allah kar sanar dani labari mai daÉ—i game da matata, likita dan Allah ka cemun matata ta farka".

Duk a lokaci guda Justice Kabir ya jefawa Likitan waÉ—annan tambayoyin.

Zare glass É—in shi likitan yayi sannan ya dubi Justice Kabir cikin tsananin tausayawa kafin yace.

"Justice Kabir sai dai haƙuri Allahn da ya baka ita ya karɓi abin shi".

Saurin riƙo hannun shi Justice Kabir ɗin yayi yana zaro ido waje kamar zasu faɗo ƙasa sannan yace.

"Likita bangane ba?, Mai kake shirin faÉ—a mun?".

"Justice Kabir Allah ya yiwa matar ka rasuwa kasan duk wani mai rai mamaci ne ba wanda ya zo duniya domin yayi gadin ta dan haka ay........".

Innalillahi wa'innailaihi rajiun shine abun da mutanen wajen suka fara faÉ—a cikin tsananin tausayin halin da Justice Kabir É—in zai shiga.

Sai a wannan lokacin inspector Rasheed ya É—an ji wani tausayin Justice Kabir É—in ya kama shi.

Tabbas tsayawa faɗin irin tashin hankalin da Justice Kabir ya shiga ɓata lokaci ne domin kuwa a take ya fara wasu irin surutai marrassa kan gado wasu ma saɓo kawai yake danƙarawa.

Mutanen wajen ne suka kama shi ganin abun nashi yana neman wuce gona da iri sannan aka nufi motar shi da shi, inda wasu kuma suka je suka É—akko gawar Hajiya Ikilima aka sanya ta a mota domin a je a mata sutura.

Tabbas duk wani mai zuciyar imani sai ya tausayawa halin da Justice Kabir ɗin ya shiga domin kuwa zan iya cewa shima mutuwar ne kawai bai yi ba. Mutane da yawa sun mishi uzuri domin kuwa mutuwar da aka mishi mutuwa ce dai sai mai ƙarfin imani ne zai iya tawakkali,ga ƴa ga mata duk a kwance ba rai.

Su kuwa wasu daga cikin talakawan da suka san halin shi musamman ma'aikatan da suke ƙarƙashin shi take su ka rinƙa Allah ya ƙara duba da yadda daman ba wani kyautata mu su yake ba. Shiyasa a rayuwa duk abun da zaka aikata ka zama ka aikata mai kyau ko dan gudun goben ka. Allah ka kar ka sanya mu daga cikin masu wulaƙanta na ƙasa damu Ameen.

An je an sallaci Hajiya Ikilima inda aka dangana ta da gidan ta na gaskiya.

Har aka je aka kai Hajiya Ikilima Justice Kabir bai bar surutai ba, domin kuwa wasu ma cewa suke ƙwaƙwalwar shi ta taɓu.

*****

A can asibitin da aka kai su Anisa da Amira kuwa sai da suka kwana suka yini ba tare da sun san duniyar da suke ba.

A hankali Anisa ta fara buÉ—e idanunta da suka mata nauyi tare da jin kan ta kamar zai rabe gida biyu saboda yadda yake mata ciwo.

Wata irin faÉ—uwa gaban ta yayi sakamakon jin abu kamar ruwa ya É—iso mata a fuska.

Hannu ta sanya ta gogo wajen da taji É—isar abun, innalillahi wa'innailaihi rajiun mai Anisa zata gani! Jini ta gani a hannun nata.

Saitin wajen da abun ya zubo mata tabi da kallo duk da irin matsanancin faÉ—uwar gaban da take ji.

Jini ta gani yana biyowa ta jikin silin É—in É—akin da suke kwance É—in.

Gaba ɗaya saitin wajen da take kwance ɗin jini ne yake ɓullowa har ya bada shape ɗin Star, kafin kuma ya fara ɗisowa ɗis ɗis ɗis akan fuskar ta.

Jikin Anisa idan ban da rawa ba abun da yake yi, wani gigitaccen ihu ta sake wanda ya sanya ma'aikatan asibitin saurin shigowa cikin É—akin da gudu hankali tashe.

Suna shigowa suka ganta kwance a gadon illahirin jikinta idan banda rawa ba abun da yake ga jini da suka gani a fuskar ta kamar an mata feshi.

Hannun ta ta ɗaga tana ƙoƙarin nuna musu sama sai kuma ta tafi luuuu ta sume.

*****

A ɓangaren Anwar kuwa tun da ya ji labarin mutuwar Azra hankalin shi ya ƙara tashi, take mutuwar Afrah da ta fara bin jikin shi ta sake dawo mishi sabuwa.

Gashi kullum sai Amrah ta zo mishi watarana a fili watarana a cikin bacci, sannan kullum cikin kuka taka zuwar mishi ya rasa dalilin hakan.

Duk ranar da tazo mishi a farke ba'a bacci ba to sai ya suma idan ya farfaÉ—o kuma to a take zai manta duk wani abu da ya faru É—in.

Idan kuwa a mafarki ta zo mishi to idan ya farka yana iya tunawa da mafarkin sai dai bai taɓa yunƙurin sanarwa wani ba, shidai kullum cikin addu'a yake.

Yau ma kamar kullum kwance yake akan gadon shi yana bacci lokacin ƙarfe ɗaya na dare ne.

Mafarki ya fara yi wai gashi a wani ƙatoton fili inda ba gida gaba bare baya.

Wata iska ce take kaɗawa ƙarar ta mai cike da abun tsoro, suuuuuiii ka ke jin ta tana wucewa.

A can nesa dashi ya hango ta zaune a ƙasa ta haɗa kan ta da gwaiwa.

Sannu bisa hankali ya fara tafiya har ya ƙarasa inda take ɗin.

Isar shi wajen yayi dai-dai da É—ago kan ta, tare da kafe shi da ido. Murmushi ta fara mishi kafin kuma daga bisani ta fashe da wani irin kuka mai sauti.

A maimakon ya ga hawaye yana fitowa a idanun ta sai ya ga jini hadda guda-guda suna fitowa daga cikin idanun nata.

"Amrah!".

Ya ƙira sunan ta cikin tsananin ruɗani.

"Anwar sun cuce ni!, Anwar sun kashe ni da rai na!, Anwar shin zaka ga laifi na dan na dawo É—aukar fansa".

Shikam tun da Amrah ta fara magana ya kasa fahimtar inda maganar tata ta dosa, buɗe baki yayi da niyyar tambayar ta su waye suka cuce ta ɗin sai dai kuma take ya fara ganin ƙasar wajen da Amrah ɗin take zaune ta fara zaizayewa, a hankali sai ga wani rami ya bayyana a wajen take kuma Amrah ta shige cikin ramin, shigewar ta keda wuya ƙasar wajen ta koma tare da haɗe kan ta.

A dai-dai wannan lokacin kuma Anwar ya farka daga wannan mafarkin da yake gaba ɗaya jikin shi ya jiƙe sharkkaf da gumi.

Miƙewa yayi zaune cike da ɗumbin mamakin wannan mafarkin da yayi ɗin.

Shin mai yake shirin faruwa ne dashi?, Shin mai yasa Amrah take yawan zuwar mishi a cikin bacci?, Shin su waye suka cuce ta haka har take iƙirarin ɗaukar fansa.

Ganin bashi da amsar tambayar tashi ko É—aya ne ya sanya ya tashi tsaye tare da shigewa toilet ya É—auro alawla sannan ya fito.

Sallah ya zo ya tayar kafin kuma daga bisani bayan ya idar ya É—aga hannun shi ya fara addu'a, sai da ya yiwa Afrah addu'a sosai kafin kuma daga bisani ya tashi ya koma ya kwanta zuciyar shi cike da zulumi.

*MANGA*
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_💀☠️)

_Tsarawa/Rubutawa_

© *SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda kuke ina son ku fisabillillahi_ .

*Free book*

-------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*006*
____________________________

Yau kwanan su Anisa da Amira uku a gadon asibiti kuma a yau ne likita ya sallame su suka koma Hostel.

Sai dai har zuwa yanzu mutuwar Azra tana nan a cikin zukatan su ta kasa goguwa duk da kuwa mutuwar daman ba wani lokaci ta É—auka ba.

A cikin kwana biyu ɗin da suka yi a asibiti babu wani abun tsoro da ya sake razana Anisa ɗin tun na ranar da taga wannan jinin, sai dai kuma kullum zuciyarta cike take da fargaba da tsoro. Gashi sai tayi niyyar sanarwar da Amira abun da ya faru ranar can ɗin sai taji bakin ta kamar an sanya zare an ƙulle shi.

Komawar su Hostel ɗin da kwana biyu aka kafe musu time table ɗin exam wanda hakan ya sanya Suka duƙufa wajen karatu ba kama hannun yaro.

Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya,kamar yadda aka kafewa su Anisa circular ɗin exam ɗin to yau ta kama ita ce ranar da zasu fara exam.

Babban abun da yafi ɗaurewa Anisa kai kuma ya tsorata ta,bai wuce karatu da idan sun yi tana shiga ɗakin jarrabawa zata ji ta nemi komai ta rasa kamar ma ba'a taɓa koya mata ba.

Wannan abun ba ƙaramin tsorata ta yake ba domin kuwa tun tana ganin abun kamar wasa har ta zo ta fara tsorata da lamarin.

Yau ma kamar kullum zaune suke ita da Amira suna karatu, É—ago kai Anisa tayi ta kalli Amira sannan tace.

"Amira nikam akwai wani abu da yake É—aure mun kai wanda na rasa yadda zan yi".

Ajiye littafin hannun ta Amira tayi sannan tace

"Anisa wannan wane abu ne haka?, kar ki manta lokacin da muke, wannan lokacin ba lokacin da zaki na sanya abu a ranki bane domin kuwa kin fi kowa sanin cewa daga wannan jarrabawar da muke rubutawa sai ta kammalla makarantar mu".

Ajiyar zuciya Anisa ta sauƙe sannan tace

"Hmmm Amira kennan!, wallahi a wannan halin da nake ciki jarrabawar ma ba lalle na ci ba, domin kuwa kullum da kike ganina ina karatu ne kawai amma da zarar na shiga ɗakin jarrabawa komai yake ƙwace mun na rasa mainene dalili".

Anisa ta ƙarashe maganar kamar zata yi kuka.

"Subhannallah Anisa mai nake jin kina faÉ—a haka!, dan Allah ki bar wannan maganar ma yanzu ba wasa ne ya kamace mu ba".

Amira ta faɗa tana kawar da kai gefe domin kuwa duk a tunanin ta Anisa kawai wasa take mata kasancewar ta san wacece Anisa a kaf cikin ƙawayen su tafi kowa nacin karatu, idan har za'a yi exam to ba wanda yake finta ci daga Azra sai ita sune ƙwarin mate ɗin nasu wanda kowa ya san ƙoƙarin na su duk da kuwa ita ma Amira ba baya ba wajen ƙoƙari.

"Amira kennan kina É—aukan wannan lamarin kamar wasa ko?,wallahi ba wasa nake miki ba amma koma mainene result zai nuna"

Ta faɗa tana mai miƙewa ta shige toilet ganin duk irin bayanin da zata mata ba yadda zata yi ba.

Yau ita ce ranar ƙarashe ta jarrabawar su zaune suke a exam hall ɗin hankalin kowa yana kan amsa tambayar da take rubuce a jikin question paper ɗin shi amma banda Anisa wadda take zaune in banda juya biro ba abun da take.

A hankali taji wata murya wadda har duniya ta naɗe ba zata taɓa mantawa da wannan muryar ba tana ƙiran sunan ta cikin murya mai firgitar wa.

"Anisaaaaaa! Anisaaaaaa! Anisaaaaaa!"

Da sauri ta ɗago kanta tare da bin wajen da take jin ana ƙiran sunan nata da kallo sai dai tana kai kallon ta wajen taga fitar ta waje.

Kamar wadda aka tsikara da allura haka taji gaba ɗaya zaman hall ɗin ya gagareta inda kuma ta wani ɓangaren taji ba abun da take so kamar ta fita tabi bayan ta.

Miƙewa tsaye tayi sannan ta fice daga cikin hall ɗin inda ba wanda ya lura da fitar ta ta.

Wata hanya daban taga Amrah ta bi inda hanyar jeji ne.

A hankali Anisa ta shiga bin ta domin kuwa da ta tsaya sai taji jikin ta kamar ana watsa mata ruwan zafi.

Haka ta dinga binta har suka ƙurewa ganin mutanen.

Anisa bata ankara ba sai ganin su tayi a wani ƙasungurmin daji mai cike da wasu irin bishiyoyi masu duhu da raishen su kamar zai taɓo sararin samaniya saboda tsawo.

Waige-waige Anisa ta fara domin kuwa shigowar su jejin keda wuya ta nemi Amra sama ko ƙasa ta rasa.

*****

A ɓangaren Inspector Rasheed kuwa sosai ya duƙufa wajen bincike domin gano makashin su Afra da Azra ɗin.

Sai dai har zuwa yanzu ba wata ƙwaƙwarar shaida da ya samu wadda zata taimaka mishi wajen gano wanda yake aikata kisan.

Zaune yake a cikin office É—in shi yana Æ´an rubuce-rubuce, haka kawai jefi-jefi sai ya saki tsaki sakamakon ji da yayi kwata-kwata baya son yin aikin yau É—in.

Tashi yayi daga kan kujerar sa sannan ya fita bakin kanta inda ya tarar da su kofur Bala a zaune.

Duban shi ya kai wajen Kofur Bala É—in sannan yace.

"Kofur Bala a fito da mota zamu je asibiti da gidan Justice Kabir da kuma gidan su marigayiya Afrah".

Sara mishi Kofur Bala yayi sannan yace.

"Ok Sir".

Motar aka fito mishi da ita inda suka shiga suka nufi asibitin da gawarwakin su Afrah suke.

Sai dai rashin sani yafi dare duhu domin kuwa inda Inspector Rasheed ya san irin aikin da zai ƙara rattaɓowa kan shi da bai je asibitin ba.

Lokacin da suka isa asibitin kai tsaye suka wuce É—akin adana gawarwakin.

Kasancewar ma'aikatan wajen sun san shi yasa basu hana shi shiga ba.

Suna shiga cikin ɗakin ya buƙaci da a janyo akwatin gawar da Afrah take ciki.

Abun mamaki da ɗaure kai ana janyo akwatin suka tarar da akwatin wayam kamar ba'a taɓa ajiyar gawa a ciki ba.

Innalillahi wa'innailaihi rajiun shine abun da Inspector Rasheed ya shiga maimaitawa duk kuwa da cewar bai tabbatar da hassasshen nashi ba.

Gaba É—aya suma mutanen da suke wajen take mamaki da ruÉ—ani ya ziyarci fuskokin su a lokaci guda.

Kofur Bala kuwa ji yayi kamar ace mishi ƙit ya fice a guje domin kuwa shi daman wallahi tun farko ba san wannan Case ɗin yake ba.

Saurin kallon ma'aikatan wajen Inspector Rasheed yayi hankalin shi a matuƙar tashe sannan yace.

"Mai nake kallo haka?, Ina gawar cikin akwatin nan take?".

Ya faÉ—a fuska ba annuri.

"Ranka ya daÉ—e ai wannan lamari sai dai mu tambayi juna domin kuwa wallahi ban san amsar da zan baka ba".

ÆŠaya daga cikin ma'aikatan Mutuary É—in ya faÉ—a.

"Wannan wane irin zancen banza ne kake son gayamun alhalin kune masu gadin É—akin, idan ban tambaye ku ba wa ku ke so na tambaya?"

Inspector Rasheed ya faÉ—a cikin tsawa.

Gaba ɗaya wajen shiru ya ɗauka,domin kuwa wannan baƙon al'amari ne kuma sabon abu a wajen mutanen asibitin baki ɗaya, duba da cewar wannan shine karo na farko tun daga lokacin da aka kafa asibitin da aka taɓa neman gawa aka rasa a cikin ɗakin.

"A fito da akwatin É—aya gawar".

Suka tsinkayi muryar Inspector Rasheed ya faÉ—a fuska ba fara'a.

Su kam ma'aikatan wajen duk jikin su yayi sanyi aka rasa wanda zai iya tunkarar akwatin da Azra É—in take ciki balle a buÉ—e shi.

Kallon su Inspector Rasheed yayi sannan yace.

"Wai ko baku ji abun da na faÉ—a bane?".

A hankali ɗaya daga cikin su ya nufi akwatin da aka sanya Azra ɗin a ciki ƙirjin shi sai bugawa yake, miƙa hannun shi da yake rawa yayi ya janyo akwatin sannan ya buɗe.

Buɗe akwatin da Azra ɗin take ciki keda wuya mutanen wajen suka shiga tashin hankali fiye da na farko sakamakon tozali da akwatin Azra ɗin da suka yi shima wayam sai wasu irin ƙananan tsutsotsi ne suke shawagi a ciki.

A wannan lokacin da zaka tsaga jikin rabin mutanen wajen to ba zaka tarar da jini ba Saboda yadda suka shiga matsanancin tsoro.

Nan fa aka shiga kallon-kallo a tsakanin mutanen wajen domin kuwa lamarin a yanzu ya daina basu mamaki sai tsananin tsoro.

Duk wanda ka kalla a wajen tsoro ne zaka gani ya bayyana ƙarara akan fuskokin su, idan ka ware Inspector Rasheed kaɗai wanda ya shiga bin akwatunan da kallo ɗaya bayan ɗaya kamar mai nazarin wani abu.

Umarni ya bayar da a buÉ—e wani akwatin gawar.

Da sauri ƴan wajen suka kalli juna cikin tsananin tashin hankali,kafin daga bisani wani daga cikin su yayi ƙarfin halin janyo wani akwati da yake kusa da akwatin Azra.

Sai dai a wannan karon akwatin da aka buɗe ɗin gawar tana nan lafiya a kwance a cikin akwatin ba alamar wani baƙon abu a tattare da ita.

Shiru wajen ya ɗauka baka jin motsin komai sai ƙarara sauƙar numfarfashin su wanda yake nuni da alamar ruɗani da tashin hankalin da suke ciki.

Can dai inspector Rasheed ya É—ago idon shi da suka yi jawur ya buÉ—i baki da niyyar yin magana sai kuma ya fasa ya fice domin kuwa a yadda yake jin zuciyarshi tana mishi idan yace zai yi magana za'a samu matsala.

Yana fita daga cikin É—akin adana gawar kai tsaye office É—in shugaban asibitin ya nufa domin kuwa wannan lamari ne da dole a san matakin É—auka tun da wuri.

*****

Haka Anisa ta shiga kai komo a cikin wannan daji mai cike da abun tsoro, ita kam a yanzu ta saddaƙar da cewar mutuwa zata yi wani irin matsanancin tsoro ne ya rufe ta sakamakon tozali da wata bishiya da tayi kaman tana mata dariya.

Bata gama shiga tashin hankali ba sai da ta tabbatar da cewa da gaske fa bishiyar dariya take mata.

Jikin ta ne ya shiga wata irin karkarwa kamar mazari take kuma ta fara jin sautin dariya ta ko ina a cikin dajin yana amsa kowa.

ÆŠaga idon da zata yi kawai tayi arba da gaba É—aya bishiyoyin cikin dajin suna mata dariya, daga baya kuma kawai taga sun fashe da kuka har da hawaye.

Ai Anisa na ganin haka bata san sanda ta durƙushe a wajen ba ta shiga rusa ihu tana neman agaji, sai dai ina babu mai jin ta balle a kawo mata taimako.

FaÉ—owar abu da taji a kusa da ita ne ya sanyata saurin É—ago kai tare da ja da baya.

Mai zata gani in ba gawar Anisa da Azra ba kwance a gefen ta wasu tsutsotsi suna biyowa ta tsakanin idanun su.

Wani gigitaccen ihu Anisa ta sake sannan ta zube a wajen sumammiya.

Tsananin zafin ranar da ake ne ya buge ta wanda yayi sanadiyar farfaÉ—owar ta.

Idanunta take ƙoƙarin buɗewa dan taga hasken duniya, sai dai mai duhu ta gani a maimakon taga haske.

Gaban ta ne ya faɗi inda cikin sauri ta sanya hannu ta shafo idanun nata sai dai wayam taji gurbin idon nata a shafe kamar ba'a taɓa hallitar ido a wajen ba.

BuÉ—e baki tayi da niyyar yin ihu amma kuma muryar tata ta katsea sakamakon dariyar da taji a gefen ta da kuma kuka a lokaci guda suna tashi.

"Dan Allah wacece ke?, Dan Allah mai ya sami idona?,Mai na miki kike son ganin bayana?".

Duk a lokaci guda Anisa ta jefamata waÉ—annan tambayoyin.

A maimakon taji an bata amsa sai taji an cigaba da ɓaɓɓaka dariyar da kuma kukan har dajin sai da ya ringa amsawa.

Ita kam Anisa zuwa wannan lokacin ta cire rai da sake rayuwa, take kuma duk wani tsoro ya gushe mata zuciyarta ta bushe cikin ƙaraji tace.

"Mai kuke jira da nine da ba zaku kashe ni ba?, Ku kashe ni nace tun da kun raba ni da abu mafi muhimmanci a rayuwata".

Anisa ta ƙarashe maganar cikin sakin kuka mai tsuma rai.

"Anisa mai kike ci na baka na zuba, ai ko baki nemi ki mutu ba to tabbas zaki mutu saboda daman mutuwa ita ta kama ce ki a wannan lokacin kamar yadda sauran ƴan uwan ki suka mutu, amma kafin nan sai kin ɗanɗani baƙin cikin da na ɗanɗana, sai kin fara girbar abun da kuka shuka, sai kin gane cewar cin amana ba abu ne mai kyau ba".

"A.....m......r.......a.....h.....ke.....ce..."

Anisa ta faÉ—a cikin rawar murya.

Wata mahaukaciyar dariya Amrah ta kwashe da ita sai da ta É—auki tsawon lokaci tana yin ta kafin tace.

"Kina mamaki ne wadda ku ka zalunta ku ka yi sanadiyar mutuwar ta ta dawo?, Tabbas nice na dawo ÆŠaukar Fansaaaaaaaaaa".

*MANGA* ✍️
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_💀☠️).

_Tsarawa/Rubutawa_

© *SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_.

*Free book*

--------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*008*
____________________________

Jin wannan mummunan labari da hukumar makarantar suka yi ba ƙaramin dugunzuma hankalin su ya yi ba inda ba tare da ɓata lokaci ba suka ɗunguma suka nufi bayan makarantar.

Innalillahi wa'innailaihi rajiun shine abun da bakunan mutane ya shiga furtawa a lokacin da suka isa wajen suka yi arba da gawar ƴanmata uku rigis kuma aminan junaa kwance cikin jini, sannan gaba ɗayan su ba mai arziƙin sutura a jikin ta.

Wannan abu ba ƙaramin tayar da hankalin mutane yayi ba.

Babban abun da ya ƙara tayarwa da hukumar makarantar hankali shine, su dai sun san cewar gawar Azra da ta Afrah tana can asibiti a adane a ɗakin adana gawa,to amma ya aka yi kuma yanzu suka tarar da gawarwakin a wajen?.

Tambayar da suka shiga yiwa kan su a cikin zukatan su Kennan amma kuma ba amsa.

Kan kace mai labarin tsintar gawarwakin da aka yi a bayan makarantar har ya karraɗe rabin makarantar inda tunin wasu daga cikin ɗaliban suka shiga haɗa kayaryakin su domin kuwa a take mutane da yawa suka ce sun haƙura da karatu a makarantar domin kuwa wannan abun abun tsoro ne,dan haka gwanda su tafi tun da an fara yin ɗauki ɗai-ɗai a ƴanmatan makarantar.

Allah sarki a ɓangaren Amira kuwa har zuwa yanzu bata da masaniya akan gawar Anisa ɗin da aka tsinta a bayan makarantar domin kuwa ita kam tana can bakin gate tana baza ido dan ganin ta wane ɓangare Anisa zata ɓullo.

Ana cikin wannan halin ne kuma Inspector Rasheed suka ƙaraso da shi da muƙarraban shi sakamakon ƙiran gaggawar da ya kuma samu daga hukumar makarantar.

Tun daga shigowar su cikin makarantar Inspector Rasheed ya fahimci ba lafiya ba duba da yadda ya ga É—alibai suna ta fita da jakanku nan su.

Iso aka mishi zuwa bayan makarantar inda gawarwakin su ke.

Zallan maza ne a wajen domin kuwa matan makarantar ba wadda ta iya tsayawa a wajen kasancewar raunin zuciya da mata su ke da ita.

Darewa mutane suka fara yi inda Inspector Rasheed ya shiga wajen har zuwa kan gawarwakin inda sai a sannan ya fuskanci dalilin ƙiran da aka mishi ɗin.

Zare glass É—in shi ya fara yi a hankali yana jin zuciyar shi kamar zata fito waje.

A wannan karon duk irin dauriyar da Inspector Rasheed ɗin yake da ita sai da ya ji zuciyar shi ta karye sakamakon tozali da gawar ƴanmata ukun an musu mummunan kisa na wulaƙanci.

Saurin mayar da hawayen da ya ji yana ƙoƙarin zubo mishi yayi gudun kar mutane su lura.

"Innalillahi wa'innailaihi rajiun, Na shiga uku na lalace,wannan wane azzalumi ne yake aikata ma rayuwar mu haka?, Shin mai muka aikata haka wanda ake kashe mu?, An kashe Afrah!, An kashe Azra! Yanzu ga gawar Anisa! Yanzu hakan yana nufin saura niiiiiiii........."

Kasa ƙarasa maganar tata tayi inda kawai sai ƙarar faɗuwar ta aka ji timmm a ƙasa.

Da sauri mutanen wajen suka juya inda suka nufi kan Amira É—in wadda isowar ta wajen kennan.

Shi kuwa Inspector Rasheed umarni ya bada na a rufe makarantar ba shiga ba fita a yau É—in gaba É—aya.

Haka aka É—auki Amira wadda bata san ina kan ta ya ke ba sannan aka wuce da ita clinic É—in da yake cikin makarantar.

Tunin labarin mutuwar Anisa É—in ya isarwa iyayen ta inda suka iso makarantar cikin matsanancin tashin hankali wanda ba zai faÉ—u ba.

Duk inda tashin hankali ya kai to iyayen Anisa sun shige shi, a nan ne kuma mahaifin ta ya buƙaci a bashi gawar ƴar shi zai wuce da ita gida su mata salla.

Sai dai kuma nan take Inspector Rasheed ya dube shi sannan yace

"Ah Ranka ya daÉ—e maganar gaskiya ba zamu iya bada gawar wannan yarinyar ba har sai mun gama bincike don gano wanda yake da hannu a cikin wannan kisan".

"Binciken banza binciken wofi wannan ai maganar banza ce, bayan har zuwa yanzu kun kasa É—aukar wani mataki game da lamarin, ai ba wani maganar bincike don na lura ba abun da zaku iya".

Mahaifin Anisa ya faɗa cikin tsananin ɓacin rai.

Cike da mamaki Inspector Rasheed ya shiga bin shi da kallo tun lokacin da ya fara maganar har zuwa lokacin da ya gama.

"Ranka ya daɗe wannan wane irin magana ka ke faɗa haka?, Kar ka manta komai bisa sannu ake binshi idan aka ce za'a yi gaggawa to out come ɗin ba zai taɓa yin kyau ba".

"Ni dai Wallahi na gama magana babu uban da ya isa yasa na bar gawar ƴata a hannun ku, alhalin ina da labarin gawar ma ba ƙyale ta aka yi ba".

Duk yadda Inspector Rasheed ya so ya tanƙwara mahaifin Anisa ya bar gawar abun ya gagara inda haka suka haƙura tun da ƴar shi suka bashi gawar ya tafi da kayar shi.

Sai a sannan Inspector Rasheed wani tunani ya zo mishi game da wannan zanen tauraron da yake gani a jikin gawarwakin ƴanmatan da kuma farar takardar da ɗazu ya tsinta Kennan hakan yana nufin Anisa ita ce ta uku, tabbas idan kuwa haka ne wannan makashin bai gama aikin shi ba to kar fa ɗayar ƙawar ta su ita ce ta huɗu?, tun da gashi gaba ɗayan su ƙawaye ne".

Aikuwa in dai haka ne to ya zama dole ya sanya ido sosai a kan ta domin a yanzu ita kaÉ—ai ce target É—in shi da zata iya É—aura shi akan hanyar gano makashin.

Yana kaiwa nan a zancen zucin da yake É—in ya juya da sauri ya bar wajen ya nufi clinic É—in da aka kai Amira.

*****

Yau kwana uku da mutuwar Anisa inda har an kai ta gidan ta na gaskiya.

A ɓangaren Amira ma yau kwanan ta uku a asibitin ba tare da ta san a wace duniyar take ba, numfashin da take ne kawai zai tabbatar ma da cewar tana raye.

Mahaifiyar ta har ta zo tana wajen ta inda jira kawai take ta farka ta ɗauke ta su koma gida, domin kuwa alƙawari ta yi cewar Amira tana farkawa zata wuce da ita gida ta gama karatun kennan haka kawai tana ji tana gani ba za'a kashe mata ƴa ba.

Da mugun ihu ta farka inda ta sanya hannu ta cisge ƙarin ruwan da ake mata sannan ta miƙe zata fita da gudu.

Da sauri mahaifiyar ta da take zaune akan sallaya ta riƙo ta tana cewa.

"Innalillahi wa'innailaihi rajiun Amira ina zaki je?".

"Umma ki bar ni dan Allah na fita, wajen Anisa zan je nasan wallahi bata mutu ba, Umma nasan cewar mafarki nake Umma dan Allah ki taimaka ki sake ni".

Amira ta faɗa tana fashewa da wani irin kuka mai taɓa zuciya.

"Subhannallah Amira ki tsaya dan Allah, jama'a ku kawo mun É—auki".

Mahaifiyar Amira ta ƙarashe maganar cikin kururuwar neman taimako.

Ma'aikatan wajen ne suka shigo da gudu inda da ƙyar aka kama Amira aka kwantar da ita saboda wani irin ihu da take, ga wasu irin surutai marrassa kan gado da take sai kace hauka sabon kamu.

Allurar bacci likitocin suka mata amma ina!, Kamar an ƙara mata haukar da take, inda da ƙyar wata Nurse ta shiga tofa mata addu'oi kafin daga bisani bacci yayi awun gaba da ita.

Zama a gefen ta mahaifiyar ta tayi tana sharar hawaye cikin tausayin Æ´ar ta ta.

A can makarantar su Anisa kuwa tunin gwamnati ta aiko da sanarwar a rufe makarantar na wasu lokuta kafin a ga abun da Allah zai yi.

Kafin sannan kuwa daman iyaye da yawa sun samu labarin abin da ya faru É—in inda suka shiga zuwa suna jidar Æ´aÆ´an su suna mai da su gida a cewar su ba za su bar Æ´aÆ´an su a mahallaka ba.

A ɓangaren Anwar yau ya shirya tsaɓ domin zuwa ya dubo Amira da take kwance a gadon asibiti.

Lokacin da ya isa asibitin Amira kwance take akan gado tana bacci sakamakon addu'ar da aka mata É—in.

Gaisawa suka yi da mahaifiyar ta inda ya fara magana

"Umma ya jikin Amira É—in dai?".

Bakin zanin ta ta sanya ta share hawayen da suka zubo mata kafin daga bisani tace

"Jiki Alhamdulillahi É—annan amma fa lamarin Amira É—in sai addu'a, domin kuwa kwana mu ke idon mu biyu ba bacci, yanzu haka wannan baccin da kaga tana yi da taimakon wata addu'a da aka tofa mata ne ta samu ta yi wannan baccin, amma kaga jiya yadda muka ga dare haka muka ga rana".

"Bakomai Umma ki cigaba da mata addu'a a matsayin ki na mahaifiyar ta in sh Allah zata samu lafiya, daman dole abun zai zo mata wani iri ganin yadda ta rasa aminan ta guda uku rigis a kusan lokaci guda, tun da kin ga an yi rasuwar Afrah ba'a fi sati ba aka zo aka yi na Azra, nan ma bai fi kwanaki ba aka yi na Anisa, ga mutuwar Amrah a baya wadda tsakanin ta da Afrah wasu watanni ne, to kin ga dole abun zai matuƙar ɗaga mata hankali".

Anwar ya faÉ—a cikin tsananin tausayawa halin da Amira É—in take ciki.

Sai da ya kwantarwa da mahaifiyar Amira hankali sosai kafin daga bisani ya mata sallama ya tafi.

*****

Ƙarfe Ɗaya na dare Amira ta farka inda ta waiga gefen ta taga mahaifiyar ta a zaune akan kujera tana bacci.

Da sauri ta miƙe sannan ta zari ɗan kwalin ta ta fice daga cikin ɗakin ƙafa ko takalmi babu.

Tun da ta fita daga cikin clinic ɗin ta shiga tsula gudu kamar mai shirin tashi sama, ƙafafuwan ta kamar za su taɓo ƙeyarta saboda ƙarfin gudun da take ɗin, a haka har ta isa bakin gate ɗin makarantar, jami'an tsaro ta hango tun daga nisa a tsaye cirko-cirko sun zagaye waje da cikin makarantar.

Ras gaban Amira ya faÉ—i inda ta shiga tunanin hanyar da zata bi domin ta samu ta fice daga cikin makarantar ba tare da sun gan ta ba.

Wata dabara ce ta faɗo mata, inda ta shiga bin jikin bango kamar wata ƙadangaruwa har ta isa bakin ƙofar ɗakin securities makarantar wanda yake can daga gefe kusa da gate ɗin.

A hankali ta leƙa cikin ɗakin inda ta tarar da su a kwance suna bacci kamar gawa.

SaÉ—af saÉ—af saÉ—af ta shiga takawa a hankali har ta isa bakin tagar É—akin wadda take ta waje.

Hannu ta sanya ta buɗe a hankali sannan ta fara ƙoƙarin haura window ɗin.

Wani security ne taga ya motsa sakamakon wayar shi da tayi ƙara ai take hanyar cikin ta ta kaɗa, bata tsaya wata-wata ba ta dirƙa windon ba tare da ta duba inda ta faɗa ɗin ba.

Dafe hannun ta tayi da taji ya zogi alamar ta kuje amma duk da haka bata dakata da abun da tayi niyya ba, haka ta miƙe tsaye ta runtuma a guje ba tare da ta san inda take jefa ƙafar ta ba.

Gudu ta shiga tsulawa akan titin wanda yake shiru ba alamar motsin wata hallita,ko tsoron daren bata ji ba burin ta kawai bai wuce ta samu ta isa inda take son isa É—in ba lafiya, sannan ba tare da kowa ya ganta ba.

Haka ta cigaba da gudu tana yi tana waiwaye ko wani yana biye da ita cikin ikon Allah kuwa ba wanda ya ganta ma bare ya biyo ta kasancewar dare ya tsala sosai.

Idan kaga gudun da Amira ɗin take zaka iya cewa ba da ƙafafu take gudun ba saboda yadda take gudun kamar zata tashi sama, tsabar gudun da take ɗin ko gaban ta bata kallo balle ta san inda take jefa ƙafar ta.

Ita dai burin ta da damuwar ta bai wuce ta gan ta a inda take da burin zuwa ba, domin kuwa ko damuwa da duhun daren bata yi ba kai kayi tunanin da rana ne tsaka take wannan gudun.

*Manage it pls yau bana jin daɗi sosai ban ma yi zaton zan muku typing* *ba wallahi* 🥺👏🏻.

*MANGA*✍️.
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_💀☠️ )

_Tsarawa/Rubutawa_

*© SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam, Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_ .

*Free book*

-------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*009*
____________________________

Duk irin gudun da Amira take bata ji ko alamar gajiya ba balle kuma ta ji a ran ta wai ko zata tsaya.

Tayi Gudu mai nisa kasancewar makarantar ta su a bayan gari take ya sanya bata samu damar ƙarasowa inda take so ɗin ba sai da ta ɗauki tsawon lokaci tana wannan gudun.

A dai-dai bakin wani gini naga taja tunga ta tsaya, a hankali kuma ta shiga mayar da numfashi kaÉ—an-kaÉ—an sannan naga ta É—aga kai ta dubi ginin inda ta kai duban ta kan rubutun saman ginin ashe ma police station ne.

Tafiya ta fara yi cikin sauri har ta ƙarasa bakin police station ɗin inda ta shiga bubbuga ƙofar police station ɗin da sauri da sauri kamar an aiko ta.

Jin irin bugun da ake yiwa wajen ne ya sanya ƴan sandan da suke aikin kwana a wajen saurin miƙewa tare da ciro bindigogin su sannan suka nufi bakin ƙofar wajen ɗaya daga cikin yana furta.

"Waye a nan wajen".

Ya faÉ—a yana saita bindigar a saitin inda Amira take tsaye.

"Dan Allah ku taimaka ku buɗe ƙofar na zo ne domin naga DPO".

Amira ta faÉ—a cikin rawar murya.

Jin muryar mace da ƴan sandan suka yi ya sanya su saurin nufar bakin ƙofar amma duk da haka ba su mayar da bindigogin na su ba.

Ƙarasawa bakin ƙofar su ka yi sannan suka buɗe ƙofar, ai suna buɗewa kamar abun da Amira take jira kennan ta fara ƙoƙarin ture su dan shiga cikin police station ɗin ko tsoron bindigar hannun su bata yi ba.

Cikin sauri suma ƴan sandan suka riƙe ta tare da hankaɗo ta waje har sai da ta faɗi ƙasa, cikin fushi ɗaya daga cikin ƴan sanda ya dube ta sama da ƙasa sannan yace.

"Ai ni sai yanzu na lura ashe da mahaukaciya mu ke magana ban san ni ba, Kofur Audu ka kalle ta fa ƙafa ko takalmi ba bu wai take iƙirarin ta zo ganin DPO, to ke an gayamiki cewar DPO ɗin mutumin banza ne da zaki ɗebo dattin ƙafafuwan ki da wannan tsakiyar daren wai kin zo ganin DPO, ko an gayamiki haka kawai ake zuwa kai tsaye a ce za'a ga DPO ɗin? ".

Ya faɗa yana nuna ƙafar Amira yadda ta yi bututu kamar an tono ta daga rami tare da fashewa da dariya.

Shima ɗayan ɗan sandan dariya ya fara sannan ya tako ya iso har inda Amira take yashe wadda tun da suka cillo ta waje bata miƙe ba.

"Ke mahaukaciya mai ya kawo ki nan wajen?".

Ya faÉ—a da alamar izgilanci domin kuwa su har ran su sun É—auka mahaukaciyar ce da gaske.

Wani abu ne ya taho ya tokare wutan Amira saboda takaici amma kuma ta sanyawa ran ta in sha Allah duk wani rashin mutunci da zasu mata zata jure shi har sai ta aiwatar da abun da ta ta yi niyya.

Miƙewa tsaye tayi tare da karkaɗe jikin ta sannan ta share hawayen takaicin da suka zubo mata tare da ƙara runtuma a guje ta hankaɗe su ta shige cikin police station ɗin tana cewa.

"Wallahi ni ba mahaukaciya ba ce, DPO dan Allah ka fito kana ina wallahi kai nake son gani".

Amira ta faɗa tana ƙarasa shigewa cikin police station ɗin tare da fara ƙolawa Dpo ƙira.

Wani É—an sanda ne ya fito daga cikin wani office sanye da Kayan Æ´an sanda sakamakon hayaniyar da ya ke ji É—in ya sa ya farka daga baccin da yake É—in.

A dai-dai wannan lokacin ne kuma waɗannan ƴan sanda guda biyun suka ƙaraso wajen kamar an jefo su inda suka fara ƙoƙarin kama Amira za su sake fitar da ita.

Ai Amira tana ganin haka ta nufi wannan ɗan sandan da yake tsaye tare da ruƙunƙume shi tana cewa.

"Yallaɓai wallahi ni ba mahaukaciya ba ce, wallahi DPO na zo gani dan Allah ka taimaka kar ka bar su su fita da ni, idan kuma kai ne DPO ɗin ka sanar dani na ganka".

Amira ta ƙarasa maganar tana ƙara ƙanƙame shi domin kuwa ji take kamar waɗannan ƴan sandan za su fitar da ita waje.

"Yallaɓai ka gani ko wallahi wannan yarinyar mahaukaciya ce dan bana tantama cewar ba daga dawanau ta tsinko ta gudo ba".

Cewar Kofur Audu ɗin yana ƙoƙarin ƙarasawa wajen Amira domin ya kamo ta ya fito da ita daga wajen.

Hannu wannan ɗan sandan ya sanya ya ɓamɓare Amira daga jikin shi wadda tun daga yanayin yadda ya ganta ya tabbatar da cewar ba a hayyacin ta take ba.

Ai Amira tana ganin ya ɓamɓare ta daga jikin shi ta fashe da wani irin kuka sannan ta fara magana.

"Dan Allah ka taimaka mun wallahi matuƙar ban ga DPO a yau ba,rayuwa ta tana cikin matsala, dan Allah kar ka karo ni na rantse maka da Allah ina da hankali, wallahi mai hankali ce ni, dan Allah ka haɗani da DPO".

Amira ta faɗa tana zubewa a wajen tare da ƙanƙame ƙafafuwan wannan ɗan sandan.

Da sauri ya É—ago ta sannan ya kamo hannun ta tare da kai ta kan wata kujera ya zaunar da ita sannan yace.

"Kin ga Æ´anmata ki nutsu, ki dawo hankalin ki sannan ki sanar da ni mai ke tafe da ke".

Shiru Amira ta yi tare da kafe gefe guda da ido sannan ta fara ƙoƙarin yin magana amma sai gani aka yi jikin ta ya shiga rawa,inda ta shiga nuna musu wani dungu a cikin police station ɗin tana zaro ido waje lokaci guda kuma ta sulale ƙasa ta sume a wajen.

Murmushi Amrah ta yi wadda take tsaye a dungun da Amira ɗin ta nuna cikin wata irin mummunar siffa, haƙoran ta zaƙo-zaƙo ga wani gashi da ya fito a duk wani sashi na jikin ta, hawaye take amma kuma hawayen jini kamar yadda ta saba kullum, cikin wata iriyar murya mai matuƙar tsoro tace.

"Kash!! Amira ban zo wannan wajen da niyyar cutar da ke ba, domin kuwa da kina daga cikin waÉ—anda zan É—auki Fansa a kan su da ba zan bar ki har ki kawo wannan lokacin ba, ai ke baki cutar da ni ba kawai laifin ki É—aya da ki ka kasa fitowa ki yiwa duniya bayani a lokacin da aka cutar da ni aka jefa rayuwa ta cikin tashin hankali wannan shine kawai laifin da ki ka mun, dan haka ni ba zan cutar da ke ba sai dai nasan dole daman idan kin yi arba da ni ki tsorata".

Amrah ta na kaiwa nan a zancen da take É—in wanda ita kaÉ—ai ta san mai take faÉ—a ta yi wata irin girgiza sannan ta bi ta jikin ginin police station É—in ta fice daga wajen.

Ganin wannan halin da Amira ɗin ta shiga ya sanya wannan ɗan sandan umurtar Kofur Audu da ya miƙo mishi ruwa da gaggawa.

Aikuwa ana kawo mishi ruwan ya É—eba a hannun shi tare da watsawa Amira a fuskarta.

A firgice Amira ta farka tana sakin wani irin gigitaccen ihu tare da miƙewa da gudu zata fice daga wajen tana cewa.

"Wallahi idan har ba ku yi gaggawar haÉ—a ni da DPO ba ku ka bari har ta yi nasarar hallaka ni kamar yadda ta hallaka Æ´an uwana to tabbas alhakin mutuwa ta ya rataya a kan ku".

Da sauri Æ´an sanda biyu nan suka kamo ta tare da zaunar da ita ganin da gaske fa ta fice a hayyacin ta.

A wannan lokacin duk wani mai rai da yake kusa da cikin police station ɗin sai da ya farka hatta waɗanda suke cikin cell a rufe sai da suka farka suka tashi suka zazzaua, sakamakon ihun da Amira ɗin take ba na wasa bane, inda wasu suka shiga leƙowa dan bawa idon su abinci gashi lokacin ƙarfe uku har ta yi.

Wayar shi wannan É—an sandan ya zaro sannan ya shiga contact É—in shi ya binciko wata number tare da yin dialing É—in ta.

*****

A can Clinic É—in makarantar su Amira kuwa bacci mahaifiyar ta take ba ta san abun da yake faruwa ba sakamakon yadda baccin na ta ya yi nisa duba da yadda kwanakin biyun nan bata samun rintsawa, yau É—in ne kawai ta samu ta rintsa da yawa har haka.

Can wajen ƙarfe uku kamar wanda aka zabure ta, ta farka firgigit sakamakon wani mummunan mafarki da ta yi, inda taga Amira ɗin a cikin wani mummunan yanayi.

Wannan mafarkin ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba inda ta farka cikin sauri tare da miƙewa zaune tana kai duban ta kan gadon da Amira ɗin take kwance.

Kasancewar wutar lantarkin É—akin a kunne take shi ya bata damar hango gadon da Amira É—in take kwance wanda yake wayam ba alamar mutum a kai.

Daram gaban ta ya bada wani irin sauti mai ƙara lokaci guda kuma ta dafe ƙirjin ta tare da miƙewa tsaye tana furta.

"Innalillahi wa'innailaihi rajiun mai nake gani haka!, Ina Amira ta shiga kuma?".

Ta faÉ—a tana nufar hanyar toilet dan dubawa duk kuwa da cewar bata ga alamun cewar akwai mutum a cikin toilet É—in ba.

Sai da ta fara ƙwanƙwasa ƙofar sannan ta fara ƙira sunan Amira ɗin.

"Amira kina jina kuwa".

Ta faɗa tana kasa kunne a jikin ƙofar ko zata ji alamar motsin mutum, sai dai shiru ba alamar da mutum a cikin toilet ɗin.

Tura ƙofar tayi inda ta shiga cikin toilet ɗin sai dai wayam ba alamar cewa ma wani ya shiga cikin toilet ɗin.

"Hasbunnallahu wa ni'imal wakil innalillahi wa'innailaihi rajiun" .

Su ne kalmomin da suka shiga fitowa daga bakin mahaifiyar Amira É—in wadda hankalin ta ya yi masifar tashi, lokaci guda kuma ta ji wata irin hajijiya tana shirin kwasar ta, da sauri ta dafe jikin bangon toilet É—in sannan ta fara sulalewa a wajen tana yin zaman Æ´an bori.

Wasu hawaye ne masu zafi suka shiga biyowa ta kuncin ta cikin kuka ta fara magana.

"Shikennan abun da na daɗe ina gudu ya faru ya faru!, Shikennan Amira kema sun kashemin ke!, Ai ni daman tun da naga an kashe aminan ki jikina ya ban ba za'a ƙyale mun ke ba, innalillahi wa'innailaihi rajiun, yanzu wannan wana irin tashin hankalin ne hak, yanzu wana la'annanne ne yake bibiyar ku ɗaya bayan ɗaya shin mai ku ka aikata mishi haka?".

Ta ɗauki tsawon lokaci a zaune a bakin ƙofar toilet ɗin kafin wata zuciyar ta ce mata.

" _Kinga zama bai kama ki ba, kamata ya yi ki tashi ki fita ki duba waje ko Allah zai sa ki ganta_ ".

Aikuwa tana kaiwa nan a zancen zucin nata ta miƙe da sauri sannan ta fice daga cikin ɗakin, Kasancewar dare ne ya sanya bata haɗu da kowa ba a filin makarantar.

Kai tsaye bakin gate ta nufa inda taje ta tarar da jami'an tsaro a tsaitsaye kamar masu jiran ko ta kwana.

Tun da Inspector Rasheed ya hango mace ta nufo inda suke É—in cikin sauri kamar zata kifa da bakin ta jikin shi ya bashi ba lafiya ba.

Gaba É—aya jami'an tsaron ido suka zuba mata suna jiran su ji da wacce ta zo.

Tana isowa wajen ta fashe da kuka sannan ta buÉ—i baki cikin rawar murya ta fara magana.

"Yallaɓai sun sace Amira na tabbatar da cewa a yanzu sun riga da sun hallaka ta kamar yadda suka hallaka sauran ƴan uwan ta, yallaɓai ku taimaka dan Allah nikam ko gawar ta a kawo mun na ganta kaf.......".

Kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon wani kuka da ya ci ƙarfin ta.

Dafe kan shi Inspector Rasheed yayi cikin tsananin tashin hankali, anya kuwa makashin Æ´an mata nan mutum ne?, Idan kuwa har mutum ne to tabbas a cikin makarantar nan yake rayuwa, domin kuwa abun shikam ya fara bashi tsoro ya za'a yi a ce suna tsaye a wajennan ko rintsawa ba su samu damar yi ba amma ace an shiga har cikin Clinic É—in an kashe yarinyar, to amma yanzu kana da tabbacin an kashe ta É—in ne?, Wata zuciyar ta jefa mishi wannan tambayar.

Aikuwa cikin sauri ya kawar da tunanin da yake sannan ya juya ya dubi mahaifiyar Amira É—in da take dirzar kuka kamar ran ta zai fita yace.

"Kin ga ki nutsu ki mun bayanin abun da ya faru da Amira É—in".

Goge hawayen ta tayi tare da sanya bakin hijab É—in ta ta fyace majinar da ta zubo mata sannan ta fara mishi bayani tun daga farkawar da tayi bata ga Amira É—in ba har zuwa yanzun da take tsaye a gaban su.

Hankalin jami'an tsaron wajen ba ƙaramin tashi yayi ba, musamman Inspector Rasheed.

Har ya buɗi baki zai yi magana sai kuma ƙira ya shigo wayar ta shi, ganin wanda yake ƙiran nashi ya sanya ya yi saurin ɗaga wayar tare da karawa a kunnen shi.

*MANGA* ✍️
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_ .

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_ 💀☠️).

_Tsarawa/Rubutawa_

© *SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_.

*Free book*

-------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*010*
____________________________

*Not Edited* .

Shiru Inspector Rasheed ya yi ina sauraran abun da ake faÉ—a mishi a cikin wayar kafin daga bisani naji yace.

"Ok to shikennan ku barta a wajen kar ku barta ta tafi ina zuwa nima akwai ƴar wata matsala ce da ta ta so in sha Allah idan na shawo bakin ta zan shigo zuwa nan da asubah, amma kasan DPO a wannan lokacin ko ka ƙira shi ba samun wayar shi zaka yi ba,so kar ka ƙira shi ka bari mu ga zuwa safiya".

Inspector Rasheed ya faɗa, ban ji abun da aka ce mishi a ɗaya ɓangaren ba sai ji nayi yace.

"Ok to shikennan duk yadda zaku yi dai kar ku ƙyale ta ta tafi".

Yana kaiwa nan a zancen na shi ya katse wayar sannan ya juya ya dubi mahaifiyar Amira da har a wannan lokacin bata daina kukan da take É—in ba.

"Uhmm Mama dan Allah ki daina wannan kukan kiyi haƙuri in sha Allah daga yanzu zuwa safiya zamu yi duk ƙoƙarin da zamu yi domin ganin mun gano wanda yake da hannu a wajen ɓatan Amira ɗin".

Ya ƙarashe maganar cikin sigar rarrashi.

"Yallaɓai ni wallahi a yanzu buƙata ta ko gawar Amira na kalla domin kuwa na tabbatar i zuwa yanzu sun daɗe da hallaka ta,na tabbata ba zasu ƙyale ta ba itama kashe ta zasu yi kamar yadda suka kashe sauran ƴan uwan ta, Allah ya ji ƙanki Amira ya saka muku a kan duk wanda yake aikata muku wannan zaluncin".

Mahaifiyar Amira ta faɗa tana durƙushewa a wajen sakamakon kukan da yaci ƙarfin ta.

Shikam Inspector Rasheed rasa abun da yake mishi daÉ—i yayi wannan bala'in har yaushe, tabbas duk wanda suka kama da hannu a wannan aika-aikar ba zasu mishi da daÉ—i ba,har ya hango irin hukuncin da za'a zartar mishi.

Da ƙyar dai ya lallaɓa mahaifiyar Amira ta tashi daga wajen sannan suka sanya ta a mota suka mayar da ita gidan ta.

*****

Lokacin da suka mayar da ita gidan nata har asubah ta kawo kai domin kuwa a lokacin har ƙarfe biyar ta yi dan haka suna kai ta gidan nata suka dawo wani massallaci da yake ɗan gaba da gidan kaɗan suka gabatar da sallar asubah kafin suka miƙe suka nufi police station ɗin.

Shigar su cikin police station ɗin ne suka yi arba da abun da ya yi matuƙar ba su mamaki.

Amira suka gani a zaune a bakin kanta ta kafe ƙofar shigowa cikin police station ɗin da ido ko ƙiftawa bata yi.

Wata zabura Kofur Bala yayi ya maƙale a bayan Inspector Rasheed yana furta.

"Yallaɓai Fatalwa, innahu min sulaimanu wa innahu bissimillahir rahmani rahim ku kuke ganin mu ba mu muke ganin ku ba, yallaɓai ka ga abun da idanuna suka gane mun kuwa".

Ya ƙarashe maganar yana ƙara shigewa jikin Inspector Rasheed ɗin domin kuwa shi har ran shi yayi tunanin Fatalwa ce kuma yayi tunanin shi kaɗai yake ganin Amira ɗin.

Tsawar da Inspector Rasheed É—in ya buga mishi ne ta dawo dashi daga haukar da yake É—in.

"Wai kai Kofur Bala mai yasa wani lokaci lamarin ka sai a hankali ne, yanzu fisabillillahi ina Fatalwar take a wannan wajen?, Ko kuma an ce maka ita wannan ɗin gawa ce?, Kuma wai a hakan kana iƙirarin kai jami'in Ɗan sanda ne ko?, Dallah ni malam sakar mun kaya".

Inspector Rasheed ya faɗa yana ɓamɓare hannun Kofur Bala ɗin daga jikin shi.

A sannan ne kuma waÉ—annan Æ´an sandan suka fito daga wani É—aki alamar salla suka yi.

"Inspector Rasheed har kun iso kennan?".

Da sauri Inspector Rasheed ya ƙarasa wajen shi yana riƙo hannun shi suka nufo wajen da Amira take rakuɓe sannan ya fara magana fuskar shi da alamun mamaki.

"Asp Sadiq a ina ku ka samo wannan yarinyar?".

Murmushi Asp Sadiq yayi sannan ya nuna Inda Amira take yace.

"Wannan ai ita ce yarinyar da na ƙira ka a kan ta wadda na sanar da kai cewar ta zo tana son ganin DPO".

Wata doguwar ajiyar zuciya Inspector Rasheed ya sauƙe tare da furta godiya a Ubangiji a fili.

Kllon shi Asp Sadiq ya yi fuskar shi da alamar tambaya sannan yace.

"A'a ya naji kana sauƙe numfashi haka ko dai ka santa ne?".

"Tabbas kuwa na santa, ina case É—in da yake hannu na na waÉ—annan Æ´anmatan da aka kashe har guda uku a jami'ar Ahmadu Bello?".

Inspector Rasheed ya faÉ—a yana kafe Asp Sadiq da ido.

"Ƙwarai kuwa na gane,kar fa kace mun wannan yarinyar tana da hannu a cikin wannan kisan da ake yi ɗin?".

Ya ƙarashe maganar cikin zaro ido waje.

"Ko kaɗan ba hannun ta a ciki asali ma yanzu haka rayuwar ta tana cikin haɗari domin kuwa gaba ɗaya waɗanda aka kashe ɗin tana da alaƙa ta kusanci sosai da su,idan ka yi duba da irin zazzafan amintar da take tsakanin su ba wanda bai san irin ƙawancen na su ba,yanzu haka maganar da nake maka mahaifiyar ta tana can hankali a tashe a tunanin ta an kashe mata ƴa kamar yadda aka kashe sauran abokanan ta, to amma abun da ya bani mamaki shine mai ya kawo ta police station ɗin?".

Inspector Rasheed ya faɗa yana kai duban shi inda Amira take rakuɓe wadda har a wannan lokacin idanun ta ba su daina zabur da hawaye ba.

"To gaskiya ni dai ban ba zance maka nasan takamaiman abun da ya kawo ta nan ba domin kuwa lokacin da ta zo ta sanar da mu kawai ita Dpo take son gani".

Shiru gaba ɗaya suka yi kafin a hankali Inspector Rasheed ya ƙarasa wajen Amira da take ta rarraba idanu kamar a ce mata firit ta ruga da gudu.

"Amira".

Inspector Rasheed ɗin ya ƙira sunan ta yana mai tsugunawa a kusa da ita.

ÆŠago ido Amira ta yi ta kafe shi da ido ba tare da tace uffan ba.

"Amira kina jin yunwa a kawo miki abinci".

Saurin jijjiga mishi kai ta yi, wanda sai a wannan lokacin ta samu damar yin magana cikin rawar murya tace

"A'a bana son in ci komai, dan Allah buƙata ta nidai kawai ku haɗani da DPO saboda nasan wallahi nima ta kusa kashe ni, nasan ba zata bar ni ba kashe ni zata yi dan haka tun kafin lokaci ya ƙure ku haɗani da DPO domin na bayyana mishi wata ɓoyayyar gaskiya wadda burin ku shine ku gano ta".

Ta ƙarashe maganar cikin sakin wani irin marayan kuka.

"Kin ga Amira ki nutsu in sha Allah ba wadda zata kashe ki, yanzu ki nutsu ki sha ruwa sannan kimun bayanin abun da yake tafe da ke".

Inspector Rasheed ya faɗa yana tsiyayo ruwa a cikin wani kofi da Kofur Bala ya kawo mishi sannan ya miƙa mata.

Karɓar ruwan Amira ta yi amma bata sha ba sai ma kafe ruwan da ta yi da ido sannan ta ɗago kai daga bisani tace.

"Ina mahaifiya ta?".

Kallon ta Inspector Rasheed yayi cike da mamaki kafin daga bisani yace.

"Mahaifiyar ki tana nan cikin ƙoshin lafiya tana gida".

ÆŠan shiru ta yi kafin tace.

"Ina son kafin na sanar da ku abun da ya faru dan Allah ina son na nemi wata alfarma daga wajen ku".

"Ok to shikennan ki faÉ—a in sha Allah za'a miki ita".

"Ina son dan Allah a ƙira iyayen su Afrah da Azra da Anisa da kuma Anwar domin a gaban su ne kaɗai zan iya bayyana irin mummunar aika-aikar da ƴaƴan su suka aikata har yake bibiyar su".

Kallon Asp Sadiq Inspector Rasheed yayi sannan kuma daga bisani ya mayar da kallon shi kan Amira yace.

"Meyasa sai a gaban iyayen su zaki iya sanar da mu abun da yake faruwa?".

"Saboda hakan ne kawai zai wanke musu raɗaɗɗin kisan da aka yiwa ƴaƴan su, sannan kuma hakan zai sa su gane cewa kowane abu aka yiwa ƴaƴan su su suka janyo, kuma hakan zai sa su daina ganin laifin wanda yake kashe mu su ƴaƴan su daga haka sai su koma ganin laifin ƴaƴan su domin kuwa ko mai ne su suka janyo wa kan su, idan da hali ma ina buƙatar a gayyato ƴan jarida da kuma hukumar makarantar mu domin a samu a yaɗa labari a duniya ko hakan zai sa masu son zuciya irin ta su su shiga hankalin su".

Mamaki ne ya kama su Inspector Rasheed inda suka shiga kallon-kallo da kuma mamakin kalaman Amira É—in.

Duban agogon hannun shi Inspector Rasheed inda ya ga har ƙafa shiga ta gota sannan ya dubi Asp Sadiq yace.

"Asp bari naje gida na yi wanka daga can zan biya ta gidan iyayen yaran can dan na sanar da su ko zasu samu damar zuwa dan mu ji abun da yake tafe da wannan yarinyar".

Inspector Rasheed ya faÉ—a yana mikewa daga tsugunen da yayi da sauri Asp Sadiq ya dube shi yace.

"Ai nima tare zamu wuce domin kuwa kaga jiya ban kwana a gida ba, wallahi wasu yara aka kawo wanda yasa dole aka ƙirani na zo to kuma na zo kennan ban daɗe ba wannan yarinyar ta zo ta".

Asp Sadiq ya faɗa yana bin bayan Inspector Rasheed ɗin inda su kuma sauran ƴan sandan suka tsaya jiran ma su aikin safe su zo su karɓe su suma su tafi.

Sai da Inspector Rasheed ya fara biyawa ta gidan su kasancewar ba shi da aure, wanka ya fara yi kafin ya fito ya je part É—in mahaifiyar shi inda ya same ta zaune ta kammalla haÉ—a breakfast.

Waje ya nema ya zauna a gefen ta kafin ya shiga gaishe ta.

Amsawa tayi sannan ta dube shi tace.

"AbdulRasheed naga kwana biyu wannan case ɗin da ka ke gaba ɗaya ya sa ka fara fita a hayyacin ka, ni dai dan Allah abun da nake so da kai kuma wanda kullum na sha faɗa maka shine ka kula kuma ka riƙe gaskiya da amana kar a baka kuɗi ko wani abu wanda zai sa ka danne haƙƙin mai gaskiya har ka bawa marar gaskiya gaskiya, sannan addu'a kullum ina faɗa ma addu'a ita ce jagaba a komai idan har ka riƙe addu'a to tabbas ka riƙe babban makami wanda zai kare ka daga dukkan wani sharri dan haka ka kula kaji".

Sosai maganar mahaifiyar ta shi ta shige shi inda ya dube ta yace.

"In sha Allah Ummu kamar yadda kika sanni a da to ba zan taɓa sanjawa kuma addu'a ina kan yin ta zan kuma cigaba da yi in Allah yarda".

Bayan sun gama cin abincin addu'a ta mishi sosai kafin kuma ya miƙe ya mata sallama, lokacin ƙarfe takwas da rabi sannan ya fita, duk da irin baccin da yake ji amma haka ya fita, kai tsaye gidan su Afrah ya fara nufa.

A dai-dai bakin gate É—in gidan su Afrah É—in suka ci karo da mahaifin ta da kuma yayan ta Aliyu sun fito zasu tafi wajen aiki.

Gaisawa suka yi da Inspector Rasheed É—in cikin sakin fuska kafin Inspector Rasheed É—in ya dubi mahaifin Afrah É—in ya fara mishi bayanin abun da yake tafe da shi É—in.

ÆŠan shiru suka yi daga mahaifin Afrah É—in har yayan nata kafin daga bisani kuma mahaifin Afrah É—in ya É—ago ya dubi Inspector Rasheed É—in yace.

"To amma Inspector a ganina meye dalilin yarinyar na ganin dole sai a gaban mu zata sanar da komai?".

"To Alhaji nima abun da na kasa fahimta Kennan amma ina ganin ku yi haƙuri mu je idan ya so mu ji abun da yake tafe da ita ɗin".

"To Shikennan Inspector bari na shiga na sanar da mahaifiyar ta sai ta shirya mu wuce".

"To ni dai yanzu idan kun shirya kwa same mu a can police station É—in domin kuwa yanzu haka ma zan wuce gidan sauran iyayen yaran ne".

Inspector Rasheed ya faɗa yana juya sannan ya shiga motar shi ya nufi gidan su Anwar bayan ya karɓi address ɗin shi a wajen Aliyu.

Lokacin da ya je wajen Anwar ɗin bai wani samu damuwa dashi ba, haka a ɓangaren mahaifin Anisa ma inda shima yace zasu shirya su biyo su daga baya.

Daga gidan su Anisa gidan su Azra ya nufa sai dai bai tarar da mahaifin ta a gida ba inda mai gadin gidan ya sheda mishi cewar ya tafi office, wayar shi ya ƙira amma bai ɗaga ba dan haka kawai ya yanke shawarar ya je ya same shi a office ɗin.

Hakan kuwa aka yi inda ya nufi office ɗin Justice Kabir ɗin, bai wani samu matsala wajen ganin Justice Kabir ɗin ba sai dai kuma inda gizo ke saƙar shine Justice Kabir ya daga tsallen aradu yace.

"Ni ai daman na san wallahi makashin ƴata a cikin shegun yaran nan yake,watau sai da ta bisu ɗaya bayan ɗaya ta kashe su tukunna zata wani kai kan ta police station ɗin ai cuta kam an riga an gama cutar mu, dan haka wallahi itama ta shiryawa karɓar nata hukuncin dan kar ta ga ta kai kan ta police station ta yi tunanin cewar hakan zai sa a sassauta mata hukunci, to ba zai yiwu ba wallahi sai ta tafi inda ta aika mun ƴata".

Shi dai Inspector Rasheed haƙuri ya bashi sannan ya lallaɓa shi suka tashi suka nufi police station ɗin.

A zazzaune suka tarar da kowa ya hallara a office ɗin DPO ɗin su kawai ake jira, ga Amira kuma a zaune a gefe ido yayi jawur tun da suka shiga cikin office ɗin DPO ɗin mahaifin Azra yake jefawa Amira mugun kallo ji yake kamar ya shaƙe ta ta mutu.

Gyaran murya DPO yayi bayan kowa ya nemi waje ya zauna sannan yace.

"To yanzu dai Alhamdulillahi mun hallara kamar yadda malama Amira ta buƙata dan haka muna sauraran ki shin mai yake tafe dake?, ga dai iyayen yaran da aka kashe nan a gefe suna sauran ki, ga kuma ƴan jarida kamar yadda ki ka buƙata su ma sun zo, ga wasu daga cikin hukumar makarantar ku su ma sun samu damar halartar wannan wajen, kowa ya baza na zumaye da na mujiyar shi yana sauraran abun da zaki faɗa".

DPO ya faÉ—a yana mai zuba idon shi a kan Amira.

ÆŠago jajayen idanun ta ta yi tare da sanya hannu ta share hawayen da suka zubo mata sannan ta fara magana cikin kuka.

A dai-dai sannan kuma Æ´an jarida suka saita camera É—in su da abun É—aukar sauti a dai-dai fuskar Amira É—in.

*MANGA* ✍️.
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_💀☠️).

_Tsarawa/Rubutawa_

© *SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book É—in gaba É—ayan Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_ .

*Free book*

---------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*011*
____________________________

A hankali Amira ta É—ago fuskarta sannan ta fara magana.

"Kamar yadda na faɗa in sha Allah a yanzu zan sanar da duniya irin cin amanar da aka aikatawa Amrah, tabbas an ci amanar Amrah wadda duk wata mace da aka mata haka an jefa rayuwar ta a cikin tashin hankali inda za'a ja mata tsana da ƙyara daga wajen al'umma, Azra, Afrah,da kuma Anisa sun kasance mutane da zamu iya ƙiran su da green Sneak, su ɗin azzalumai ne ma su bala'in son kan su, ina son kafin na fara baku labarin gaskiyar abun da ya faru ku ɗauki kan ku ku sanya a matsayin Amrah shin idan ku ne wane irin hukunci zaku aikatawa wanda ya aikata muku irin wannan aika-aikar da aka aikatawa Amrah?, Kasancewar Amrah macece wadda bata iya ɓoye sirrin ta ga waɗanda suke tare ba wannan ya sanya babu abun da bamu sani ba game da labarin rayuwar Amrah hakan shi ya bawa su Azrah damar cutar da ita domin kuwa sun yi amfani da irin matsayin mahaifin ta da kuma yadda suka fahimci cewar kaf iyayen su sun fi na Amrah rufin asiri wannan ya sanya ba suji shayin su tarwatsa mata rayuwa ba.Da farko dai bari na fara sanar daku labarin wacece Amrah?, da kuma su waye Azra?, Da kuma irin zaluncin da aka aikata mata duk kuwa da cewar nima ina da kamasho a wajen lalacewar farin cikin Amrah duba da yadda na san gaskiya amma na kasa bayyana ta a lokacin da ya kamata har na bari azzalumai suka yi nasara a kanta, na tabbata idan ku ka ji abun da aka aikata mata daga haka zaku ƙara tabbatar da cewa an cuce ta cuta mafi girma da za'a yi duk wani ɗan Adam.

*FLASH BACK*

*Wacece Amrah* *?*

Asalin sunan ta Amrah Kabir ƴar asalin garin Giwa da ke ƙaramar hukumar Zaria a jahar Kaduna, mahaifin Amrah babban malami ne da ba wanda bai san shi a cikin garin na Giwa ba har ma da wasu ɓangare daga cikin jahar Kaduna an san shi, sai dai su ɗin talakawa ne wanda rufin asirin Allah ne kawai yake riƙe da su. Tun tasowar Amrah Allah ya sanya mata son karatun boko inda bata da wani buri wanda ya wuce ta ga ta zama cikakkiyar likita. Mahaifiyar Amrah ta rasu tun a wajen haihuwar Amrah ɗin Allah ya mata rasuwa to sai Amrah ta ta so a wajen matar mahaifin ta mai suna Sa'adatu sai dai kuma Amrah ta yi dacen kishiyar mahaifiya domin kuwa gwaggo Sa'adatu macece mai kyakkyawar zuciya kuma ta riƙe Amrah tsakani da Allah kamar ita ta haife ta a cikin ta,Amrah tana da yayu maza guda uku ɗaya uwar su ɗaya uban su ɗaya sauran kuma ƴaƴan gwaggo Sa'adatu ne, Hashim,Umar, Sai kuma Usman su ne yayun Amrah ɗin. Mahaifin Amrah mutum ne da mutane suke ganin mutuncin shi da girman shi a cikin garin Giwa ɗin kasancewar shi malami babba kuma ga dattako, gashi shi mutum ne da baya iya danne haƙƙin ƴaƴan shi duk abun da ƴaƴan shi suka nuna suna so yana musu matuƙar abun bai kaucewa Shari'a ba,saɓanin wasu iyayen da zaku ga basa iya baiwa ƴaƴan su dukka haƙƙin da ya rataya a wuyan su inda zaku ga wasu iyayen suna nuna ai kamar su kaɗai su ke da haƙƙi akan ƴaƴan wanda hakan kuma babban kuskure ne da wasu iyayen suke aikatawa dalilin haka sai kuga an zo an haifi ɗa marar ido.

Da gudu ta shigo cikin gidan fuskar ta kana gani kasan ba ƙaramin farin ciki take ciki ba, tana shigowa ta faɗa kan cinyar gwaggo Sa'adatu wadda take zaune a tsakar gida tana gyaran kayan miya.

"To ɓallani hankalin ki ya kwanta kin ji Amrah, ni wallahi ban san sai yaushe zaki girma ba,mutum yana girma kullum kamar ana mai da shi baya, ni ɗaga ni dan Allah kar ki ƙarasa ni".

Gwaggo Sa'adatu ta faÉ—a tana ture Amrah daga jikin nata.

Shagwaɓe fuska Amrah ta yi sannan tace.

"Gwaggo wallahi yau ina cikin farin da ban taɓa shiga ba".

Ta faÉ—a tana ware wata paper da take hannun ta.

"Gwaggo wannan result É—in mu ne na Waec and Neco ya fito duka na cinye ina da nine credit, yanzu saura na jamb zamu jira muga abun da Allah zai yi".

Murmushi gwaggo Sa'adatu ta faÉ—aÉ—a fuskar ta dashi sannan tace.

"Ai ni daman ban taɓa kawo miki faɗuwa ba Amrah kawai dai kece kike ta abun ki, Ubangiji ya sanyawa wannan sakamakon albarka".

"Ameen ya Allah gwaggon mu kice mun kusa mu samu likita a gidan na mu".

Yaya Hisham ya faɗa da yake ƙarasa shigowa gidan yanzu.

"Wallahi kuwa Hisham ga dai result ya fito Alhamdulillahi sai kuma mu jira wancan É—ayan jan yake ko meye ma?".

Gwaggo Sa'adatu ta faÉ—a fuskarta tana faÉ—aÉ—a da Murmushi.

Dariya muka yi gaba É—aya nida yaya Hisham kafin kuma nace.

"Kai gwaggo Jamb fa ake cewa dan Allah meye kuma wani jan kamar a ƙauye".

Hira muka ɗan taɓa kafin kuma lokaci guda su lura da fuskata da ta sanja idanuna suka ciko da hawaye.

"Subhannallah Amrah mai ye kuma haka muna hira zaki ɓata fuska?".

Gwaggo Sa'adatu ta faÉ—a tana janyo ni jikin ta itama fuskar ta da alamar damuwa.

"Gwaggo a duk lokacin da aka fara maganar karatu na sai na dinga jin faɗuwar gaba, a wani ɓangaren kuma gwaggo ina tausayin Abba kasancewar na san bashi da ƙarfin da zai biya mun kuɗi na yi karatu,sannan gwaggo kin san a wannan zamanin karatu ya zama sai ɗan wane da wane musamman ni fannin da nake son karanta, sannan gashi a wannan garin na mu har yanzu ba'a ɗauki ilimin mace da muhimmanci ba inda wasu suke yiwa abun kallo na daban,duk lokacin da na tuna abubuwan nan sai naji duk wani farin ciki na ya koma ciki".

Amrah ta ƙarashe maganar hawayen da take ƙoƙarin tare suna zubowa daga cikin idanun ta.

Shiru gwaggo Sa'adatu suka yi da ita da Hisham cikin tausayin Amrah ɗin,tabbas sun san cewar duk maganganun da ta faɗa gaskiya ne to amma kuma a yanzu su ya kamata su kwantar mata da hankali su nuna mata cewar duk abun da Allah ya tsara a rayuwar bawa shi yake kasancewa da shi. Hisham ne yayi ƙarfin halin duban Amrah ɗin sannan ya fara magana cikin sigar rarrashi.

"Amrah kinsan dai a rayuwa duk abun da Allah ya tsara shi yake kasancewa da bawa,to dan haka ki É—auka cewar idan har kin samu damar yin karatu to Allah yayi zaki yi ne, haka kuma idan har kika ga baki samu damar cika burin ki ba to Allah ne bai yi hakan zai tabbata ba,dan haka in sha Allah ki sa a ranki in dai muna raye burin ki zai cika kuma zaki zama likita da izinin Allah,kuma daga yau ki fara shiri Jamb É—in ki yana fita zaki wuce makaranta".

Wannan kalaman da Yaya Hisham ya yiwa Amrah su suka sanya ta cikin farin ciki wanda har bata san sanda ta saki murmushi ba, sannan ta tashi da gudu ta yi cikin É—aki tana jin wani daÉ—i kamar an cemata gobe zata wuce makaranta.

Da dare bayan malam Kabiru mahaifin Amrah ya dawo gwaggo Sa'adatu ta kawo mishi abinci da ruwa kamar yadda ta saba.

Sai da Amrah ta bari ya ci abinci ya sha ruwa kafin ta fito daga cikin É—akin ta sannan ta zo ta zauna a kusa dashi tare da gaishe shi.

"Mamana (kasancewar sunan mahaifiyar shi gare ta), ya dai yau naga bakin ki kamar gonar audiga ya ƙi rufuwa ga dukkan alamu bakin akwai magana ko?".

Cewar Malam Kabiru É—in, murmushi Amrah ta yi sannan tace.

"Abba Albishirin ka".

"Goro Mamana, goron ma fari tatass".

Ya faÉ—a yana faÉ—aÉ—a fuskar shi da murmushi.

"Abba ga result É—in mu na Waec and Neco ya fito kuma Alhamdulillahi Abba na cinye duka nine credit".

Ta faɗa tana miƙa mishi result ɗin da yake hannun ta.

"Ah ah ah Masha Allah Mamana wannan albishir dole a baki tukwaici".

Ya faÉ—a yana buÉ—e result É—in da yake hannun na shi.

Caraf gwaggo Sa'adatu ta yi tare da amshe zancen sannan tace.

"Ai ba'a isa ba wannan tukwaicin a ni za'a bawa domin kuwa ni na fara maka albishir É—in ai".

Dariya suka yi gaba É—aya sannan Amrah tace.

"To ai gwaggo ko an bani tukwaicin ma kamar ke aka bawa ni da ke ai duk É—aya ne".

"Uhmm kaji Sarkin wayo ko, zata rufe mun baki to Shikennan ai nayi shiru daman haka ki ke so".

Albarka Sosai mahaifin Amrah ya sanyawa result É—in nata kafin daga bisani ya mata addu'a sannan ta tashi ta koma cikin É—aki.

Bayan shigar Amrah É—aki ne Malam Kabiru yayi gyaran murya tare da duban Gwaggo Sa'adatu fuska da alamar damuwa ya buÉ—i baki ya fara magana.

"Wallahi Sa'adatu ranar da nake ta tunanin zuwan ta ne take ta ƙaratowa,kullum da tunanin wannan ranar nake kwana nake tashi ranar da Amrah zata kammalla karatun ta na sani cewar Amrah tana son karatu sosai to amma gashi ni kuma bani da halin da zan sanya ta a makaranta domin cikar burin ta,kin fi kowa sanin halin babun da muke ciki tun da kina gani hakan zan fita yanzu na dawo gidannan hannu wayam wata ran ma sai ke kike taimaka mana,ga Hisham shima yanzu kasuwar ba wata kawo mishi take ba,ga ɗawainiyar shi ga ta iyalan shi, shi kuma Usman karatun shi yanzu haka ya katse sakamakon kuɗin registration da bai biya ba har na semister biyu,mai dama-daman shine Umar to shima yanzu hidimar auren shi ta sako shi a gaba, sannan abu na gaba kin san yadda ƙasar ta mu yanzu ta zama karatu sai kana da kuɗi,ga yadda tarbiyya ta taɓarɓare a manyan makatantu sai a hankali".

Malam Kabiru ya ƙarasa maganar fuska cike da damuwa.

Saurin kallon shi gwaggo Sa'adatu ta yi sannan ta fara magana cikin son ta ƙarfafa mishi gwaiwa.

"Malma na sani duk abubuwan da ka faɗa ba wanda ba dai-dai ba a cikin maganar ka, amma ina son ka san wani abu guda ɗaya duk bakin da Allah ya tsaga ba zai hana shi abinci ba,dan haka kamar yadda Amrah ta kammalla makarantar ta Sakandire lafiya kuma ta samu ta fita da kyakkyawan sakamako to bi'izinillahi rabbi zata cigaba da karatu kai dai kawai yanzu mu mata addu'ar wannan result ɗin da ya rage mata ya fito lafiya kuma ta ci shi,sannan a halin yanzu Amrah ƙwarin gwaiwar mu take buƙata dan Allah ka cire komai a ranka,ko ka manta duk sauran jarrabawar da ta rubuta da kuɗi ake rubutawa kuma an biya mata ta yi to in sha Allah wannan ma ba zai gagara ba".

Sosai Malam Kabiru ya ji daÉ—in maganganun matar ta shi in da ya shiga sanya mata albarka ya kuma godewa Allah da ya azurta shi da mata mai halin kirki irin Sa'adatu É—in.

Bayan wasu kwanaki result ɗin Amrah ya fito na Jamb in da cikin ikon Allah ta ci maki fiye ma da yadda ake buƙata wannan dalilin ya sanya ƴan gidan su Amrah suka ƙara zage damtse wajen ganin an cika mata burin ta.

Yau gidan su Amrah an tashi ana bikin yayan ta Umar in da aka ɗaura aure lafiya aka gama lafiya ba wani ƙarya da aka yi a bikin kasancewar auren ƴaƴan malam Shehu ne daga amaryar har angon.

A wannan bikin ne Amrah ta haÉ—o da sanyin idaniyar ta Anwar wanda ya kasance abokin Umar Sai dai shi a garin Zaria yake da zama.

Tun da Anwar ya ƙyalla idon shi akan Amrah ya ji duk duniya ba wadda yake so sama da ita.

Aikuwa ba tare da yayi ƙasa a gwaiwa ba ya isar da saƙon shi wajen Amrah in da bai wani sha wahala ba ta karɓe shi hannu bibbiyu.

Lokaci guda wata zazzafar soyayya ta ƙullua a tsakanin Amrah da Anwar,wanda Anwar ya mayar da Zaria da garin Giwa kamar unguwa, tun ba wanda ya fahimci abun da yake faruwa a tsakanin su har ƴan gidan su Amrah ɗin suka zo suka fahimta.

Yau Amrah ta tashi da wani irin farin ciki sakamakon Anwar zai zo in da za su shiga cikin garin Zaria da Umar domin a mata siyayyar tafiya makaranta, duk da cewar tafiyar da É—an saura ba'a ma gama registration ba.

A motar Anwar É—in suka tafi inda ya kai su wani babban Mall a garin Zaria É—in.

Suna fitowa a cikin motar Umar ya tsaya yana ƙarewa wajen kallo sannan ya dubi Anwar yace.

"Malam kasuwa fa zaka kai mu ya naga ka kawo mu wannan wajen wanda kai ma kasan waje ne da yafi ƙarfin talakawa irin mu,kaga dan Allah wuce mu tafi kasuwa".

Umar ya faɗa yana ƙoƙarin komawa cikin motar.

Murmushi Anwar ya yi sannan ya dubi Umar yace.

"Umar dan Allah ku zo ku shiga ka sani cewar ko ba wata alaƙa a tsakani na da Amrah ita ɗin na ɗauke ta kamar ƙanwa ta ce,dan haka kar ka damu akwai enough kuɗi wanda zamu yi siyayya a ƙanwar mu,ita ma ta je makaranta ta fantama".

Ya faÉ—a yana kamo hannun Umar É—in suka nufi cikin Mall É—in, siyayya ta gani ta faÉ—a Anwar ya yiwa Amrah inda sai da Umar ya ce mishi ya dakata.

Sosai suka yiwa Anwar godiya har sai da Amrah ta zubar da hawaye ganin irin lodin siyayyar da ya mata É—in, a ciki hadda waya mai bala'in tsada ya haÉ—a mata da ita.

*MANGA* ✍️
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_ .

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_ 💀☠️).

_Tsarawa/Rubutawa_

*©* *SHAMSIYYA MANGA*

*SADAUKARWA* : _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi._

*Free book*

-------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*012*
____________________________

Lokacin da su Amrah suka koma gida Malam Kabiru bayannan sakamakon wata tafiya ta gaggawa da ta ta so mishi ya tafi cikin Kaduna.

A tsakar gida suka zauna inda suka shiga fito da kayayyakin da suka zo da su É—in, ido waje gwaggo Sa'adatu ta shiga bin su da kallo tana mamakin yawan kayan, sannan ta buÉ—i baki ta dubi Umar tace.

"Umar wannan kayan fa haka,ko dai ido na ne?".

Murmushi Umar ya yi sannan yace.

"Gwaggo ba idon ki ba ne wannan kayan duka na Amrah ne,na tafiya makarantar ta".

Kayan Gwaggo Sa'adatu ta shiga É—agawa É—aya bayan É—aya baki buÉ—e.

"Kai Umar a ina ku ka samu kuÉ—in siyo waÉ—annan kayan haka?".

"Wallahi Gwaggo Anwar ne ya yi duk waɗannan siyayyar kuɗin da muka tafi da su ma ga su nan ko taɓa su bamu yi ba mun dawo da su".

Umar ya faÉ—a yana ciro kuÉ—in a aljihun shi yana nuna wa Gwaggo Sa'adatu.

Shiru Gwaggo Sa'adatu ta yi kamar mai nazarin wani abu kafin can ta É—ago tace

"Amma Umar kana ganin hakan ba kuskure ba ne ba kuwa?".

"Gwaggo kuskuren mai Kennan?".

"Kafi kowa sanin halin mahaifin ku, kasan sarai idan har ya ga waɗannan kayyayyakin ran mu ne gaba ɗaya zai ɓaci".

Caraf Amrah ta amshe zancen wadda tun da suka dawo sai yanzu ta yi magana.

"Wallahi nima Gwaggo tun da muka taho abun da yake ta mun yawo Kennan a rai,gashi ba halin mutum ya maka kyauta kuma kace ba zaka karɓa ba, amma ni nasan matuƙar Abba yaga kayan nan sai ya sa an mayar wa da Anwar su,kuma ma Gwaggo kin ga Abba bai san alaƙar da take tsakanin mu da Anwar ɗin ba, nikuma gaskiya da ran shi ya ɓaci gwanda kawai tun kafin ma yazo ya ga kayan kawai a ƙira Anwar ya zo ya ɗauki kayan shi".

Amrah ta faÉ—a fuska da damuwa.

"Hakane Amrah kema kin ce wani abu,amma in sha Allah zan yi ƙoƙari na fahimtar da Abba har ya fahimta, kuma zan sanar dashi ƙudurin Anwar ɗin a kan ki".

Umar ya faÉ—a yana kallon su duka su biyun.

"To Shikennan Umar Allah ya maka Albarka, sai ya dawo É—in muji abun da zai ce".

Gwaggo Sa'adatu ta faɗa tana miƙewa tare da mayar da kayan gefe.

Tashi Amrah ta yi tace

"Gwaggo bari na je gidan Anty Naja (matar Hisham) na dawo jiya tace naje na mata kitso".

"To a dawo lafiya ki gaida ta".

Sai yamma liƙis Malam Kabiru ya dawo, Gwaggo Sa'adatu kaɗai ya tarar a gidan, da fara'a ta tare shi tana mishi sannu da dawowa,sannan ta shimfiɗa mishi tabarma a tsakar gida kasancewar lokacin zafi ne.

Abinci da ruwa ta kawo mishi sai da yaci ya tashi ya shiga wanka bayan ya gama komai ya zo ya zauna, kafin Gwaggo Sa'adatu ta shiga bashi labarin siyayyar da Anwar É—in yayiwa Amrah É—in, har Gwaggo Sa'adatu ta gama zancen da take É—in Malam Kabiru bai cai uffan ba.

Tun daga irin kallon da Gwaggo Sa'adatu ta ga Malam Kabiru É—in yana mata ta sha jinin jikin ta.

Tashi ta yi ta shiga É—aki sannan ta shiga fitowa da kayan da Anwar É—in ya saiwa Amrah É—in.

Ai tun kafin ta gama fito da kayan gaba ɗaya taji ya ƙira sunan ta da kakkausar murya har sai da hanjin cikin ta ya kaɗai.

"Sa'adatu mai nake gani haka?".

Cikin inda-inda Gwaggo Sa'adatu ta fara magana.

"Malam su ne kayan da nake faÉ—a ma yaron can Anwar abokin Umar ya saiwa Amrah wallahi yaron akwai kirki ga.......".

Saurin dakatar da ita Malam Kabiru yayi sannan yace.

"Sa'adatu yaushe hankalin ki da tunanin ki suka fara gushewa ban sani ba?, Eyeee nace yaushe hankalin ki da tunanin ki suka fara gushewa ban sani ba,idan su su Amrah da Umar ɗin basu da hankali ƙuruciya tana ɗawainiya da su ai ke babba ce kuma kin fi su hankali".

Ya faÉ—a yana duban Gwaggo Sa'adatu É—in fuska a haÉ—e.

"Mala.......".

Saurin dakatar da ita yayi ta hanyar É—aga mata hannu sannan ya cigaba da magana

"To tun wuri ma kiyi gaggawar ƙiran Umar ɗin a zo a ƙiran yaron ya zo ya ɗauke kayan shi, kamar yadda na yi alƙawarin zan sanya Amrah a makaranta zan kai ta,idan ina da shi idan bani da shi babu wani ɗan Adam da zan nemi taimako a wajen shi,dan haka ni talaka ne zan yi iya abun da zan iya akan Amrah sauran ta yi haƙuri a hankali idan Allah ya hore mun sai na mata amma a yanzu, a zo a mayar da kayan nan tun kafin ran kowa ya ɓaci,wannan ai salon ku sanya a zage ni ne, to ba zai yiwu ba".

Tun daga ƙofar gida Amrah ta fara jiyo maganganun mahaifin nata, idan ta shiga cikin gidan bakin ta ɗauke da sallama sannan ta ƙarasa wajen da iyayen nata su ke tsaye.

Durƙushewa ta yi a ƙasa tare da fara magana cikin rawar murya.

"Abba dan Allah ka yi haƙuri,in sha Allah ba za'a yi abun da zai sanya ka a cikin ɓacin rai ba, Abba daman ni wallahi ba'a son rai na aka karɓo kayan ba, dan haka ka yi haƙuri wallahi za'a mayar mishi, amma Abba dan Allah kar ka sanadiyar haka ran ka ya ɓaci".

Amrah ta faɗa tana ƙarashe sakin kukan da take riƙewa ɗin.

Tausayin Amrah É—in ne ya kama Malam Kabiru É—in da Gwaggo Sa'adatu, a hankali Malam Kabiru ya dube ta ya fara magana.

"Amrah ko kaɗan rai na bai ɓaci ba, kuma bana fatan Allah ya kawo ranar da zaki zamo sanadiyyar ɓacin rai na,ke ɗin yarinya ce mai biyayya, dan haka ina son ki ɗauki wannan abun da nake shirin yi a matsayin shine dai-dai".

Share hawayen ta Amrah ta yi sannan tace.

"Abba komai ka aikata a garemu shine dai-dai bamu taɓa ɗaukar wani hukunci da ka zartar a cikin gidannan a matsayin ba dai-dai ba,dan haka komai ka zartar zamu karɓe shi ko da bai mana daɗi ba".

Sosai Gwaggo Sa'adatu da Malam Kabiru suka ji daÉ—in maganganun Amrah É—in,inda suka shiga sanya mata albarka.

A daren ranar Malam Kabiru ya ƙira Umar ya sanar da shi a kan hukuncin da ya yanke ɗin,yace kuma maza-maza ya sanar da Anwar ya zo ya ɗebi kayan shi

Duk yadda Umar ya so ya fahimtar da mahaifin na shi akan Anwar yayi hakan ne dan Allah amma ina Malam Kabiru ya ƙeƙashe ƙasa kasancewar shi mutum mai magana ɗaya.

Haka Umar ba dan ya so ba ya ƙira Anwar ya mishi bayanin komai,kuma Alhamdulillahi Anwar ya fahimta inda ya zo ya ɗauki kayan.

Sai dai fa Anwar yana komawa gida ya sanar da mahaifin shi cewar yana so a zo a tambayar mishi izini a wajen mahaifina.

Hakan kuwa aka yi ana saura sati É—aya na tafi makaranta iyayen Anwar suka zo suka nemi izini a wajen Mahaifina, kuma cikin ikon Allah mahaifina yace a bashi kwana biyu.

Kamar yadda mahaifin Amrah ya faɗa hakan kuwa ta kasance a cikin kwanaki biyun da ya faɗa ya ƙira Amrah ya tambaya ta shin ko ina son Anwar,shirun da na yi shi ya bashi damar fahimtar komai inda yace ta tashi ta tafi.

Amrah bata tashi tafiya makaranta ba sai da aka tabbatar da angama komai na maganar auren su da Anwar kawai rana ce ba'a sanya ba,amma dai an bashi ita an gama komai maganar auren akwai ta akan Amrah.

Cikin kwanaki ƙalilan ɗin da suka ragewa Amrah na tafiya makaranta, Malam Kabiru mahaifin Amrah ya yi duk yadda zai yi yayi bakin ƙoƙarin shi inda ya mata siyayyar duk wani kayan buƙata dai-dai ƙarfin talaka.

Gwaggo Sa'adatu ma ta yi iya bakin ƙoƙarin ta wajen ganin ta haɗa mun ɗan abubuwan da ba'a rasa ba, irin su kayan yaji, niƙaƙƙen kayan miya,mai, manja,daddawa,taliya ƴar mirji,yajin borkono,da yajin ƙuli-ƙuli da sauran su dai duk sai da ta tabbatar ta haɗawa Amrah.

Su yaya Hisham ma sun yi iya bakin ƙoƙarin su wajen ganin sun taimakawa Abba an mun siyayya dai-dai ƙarfin talaka ba abun da aka rageni dashi.

Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya, yau ta kama ranar da Amrah zata tafi makaranta.

Tun asubah da ta tashi ta yi salla bata koma bacci ba ta shiga shiryawa, sai da ta sa kaya sun kai wajen biyar tana cirewa ita a dole bata yi kyau,da ƙyar dai Gwaggo Sa'adatu ta nemo mata wata atamfa mai ruwan ganye da hijab har ƙasa, daman Amrah bata sa mayafi.

Ƙarfe Bakwai dai-dai yaya Hisham suka zo shida Umar dan tafiya raka Amrah makarantar inda zata fara karatu a AHMADU BELLO UNIVERSITY ZARIA Fannin Medicine.

Malam Kabiru ne ya aiko ƙiran ta inda ta je ta same shi a cikin ɗakin shi.

Zama ta yi a gefen shi inda Gwaggo Sa'adatu take zaune daga É—ayan gefen.

"Amrah".

Malam Kabiru ya ƙira sunan Amrah ɗin cikin wata iriyar murya da bata taɓa jin shi da ita ba.

Saurin É—ago idon ta Amrah É—in ta yi sannan tace.

"Na'am Abba"

Jikin ta duk ya yi sanyi.

"Amrah yau dai gashi Allah yayi zaki tafi makaranta,nayi iya duk ƙoƙarin da zan yi naga na miki duk abun da ya kamata dan haka duk abun da ki ka gani kawai kiyi haƙuri dashi, sannan abu na gaba Amrah dan Allah ƙawaye ki san irin ƙawayen da zaki yi mu'amala da su saboda a wannan zamanin ƙawaye sai an tona ake samun na kirki, Amrah duk abun da zaki yi kar ki manta da ga gidan da ki ka fito,kar kuma ki manta da ke wacece da kuma matsayin mahaifin ki,mutunci, Amrah ki riƙe mutuncin ki sannan kar ki ringa hangen rayuwar wasu. Kiyi haƙuri da abun da ki ka je da shi kar kice dan wance tana da abu kaza kice kema sai kinyi. Na sani Allah ya sani ga ƴanuwan ki nan shaida ne tarbiya dai-dai gwargwado na baki ita Amrah idan har ki yi watsi da tarbiyyar da na baki Amrah baki mun adalci ba,sannan kin cuci kan ki bani kika cuta ba, dan haka zan ƙara maimaita miki ƙawaye ki kula da su bance kar ki kula ƙawa ba amma dan Allah ki san irin ƙawyen da zaki yi mu'amala da su,Allah Ubangiji ya kare ki,ya baki abun da ki ka je nema ya kuma dafa miki a harkar karatun ki".

Tun da mahaifin Amrah ya fara magana jikin Amrah ya yi wani irin sanyi kamar ruwan fridge,wasu hawaye ne suka shiga biyowa ta kuncin ta ita kam ji ta yi lokaci guda karatun ya sare mata a rai har taji kamar tace ta fasa, a hankali ta sanya hannu ta goge hawayen fuskarta ta sannan ta buÉ—i baki ta fara magana.

"Abba in sha Allah karma yadda ka yarda cewa ka bani tarbiya dai-dai gwargwado Abba na maka alƙawarin ba zan taɓa watsa maka ƙasa a ido ba, Abba in sha Allah zan yi karatu kuma zan zo maka da kyakkyawan sakamako wanda zaka yi alfahari dani, Abba fatana shine kawai ka tayani da addu'a kamar yadda ka ke mun kullum,ba zan taɓa fatali da irin tarbiyyar da ka bani ba Abba wannan alƙawari ne na ɗaukar wa kai na".

Kuka sosai Amrah ta shiga yi kamar an aiko ta.

Rungumeta Gwaggo Sa'adatu ta yi sannan ta shiga bubbuga mata bayan ta alamar rarrashi.

Sai da ta rarrashe ta kafin ta tashi inda suka fice a gidan dan mata rakiya zuwa tasha su hau mota.

Sai dai suna fita suka tarar da Anwar a tsaye a ƙofar gidan a jikin motar shi.

Ba yadda suka iya haka Gwaggo Sa'adatu da Hisham da Umar suka shiga motar bayan an sanya kayan Amrah a bayan motar suka kama hanyar Zaria É—in daga garin Giwa.

Amrah sosai take kuka ga wani irin matsanancin faÉ—uwar gaba da take ji tun da suka kama hanyar zuwa garin Zaria É—in wanda ta rasa gane kan shi.

Allah sarki ashe mafarin tarwatser duk wani farin cikin ki ne Amrah.🥺😫

*MANGA* ✍️
_Comment_
_Share_

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_💀☠️).

_Tsarawa/Rubutawa_

*© SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_.

*Free book*

---------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*013*
_____________________________

*AHMADU BELLO UNIVERSITY ZARIA*

Shine sunan da Amrah ta gani a rubuce a saman makaranta wadda take a matsayin makarantar da zata fara karatu a cikin ta yanzu.

Tun da suka shiga cikin makarantar Amrah take ta kalle-kalle kamar wata ƴar ƙauye.

A dai-dai inda ake parking É—in motoci Anwar ya yi parking É—in motar shi inda suka fito gaba É—aya daga cikin motar.

ÆŠalibai ne ta ko ina idan ka duba kowa yana harkar gaban shi, kun san dai yadda jami'a take ba sai na muku bayani ba.

Tsaye su Amrah suka yi a jikin mota suna tunanin ta inda zasu fara, kallon Anwar Gwaggo Sa'adatu ta yi sannan tace.

"To yanzu Anwar muna tsaye a ina ita Amrah É—in zata zauna"..

Murmushi Anwar yayi sannan yace.

"Ai Gwaggo angama mata komai yanzu É—akin da aka bata zamu tambaya sai ku je ki raka ta".

A dai-dai sannan wata kyakkyawar matashiyar budurwa ajin farko ta zo wucewa har ta wuce sai kuma suka ga ta dawo sannan ta dube su bakin ta É—auke da sallama tace

"Bayin Allah sannun ku".

Amsa mata suka yi sannan ta ƙara duban su tace.

"Da alamu dai ku baƙi ne ko sabuwar zuwa ku ka kawo?".

Ta faɗa tana kai duban ta inda Amrah take rakuɓe har a sannan bata daina kuka ba

"Eh wallahi gatanan ƙanwar mu ce muka kawo".

Ya Hisham ya faÉ—a yana nuna inda Amrah take.

"Eyya sannun ku, hala ba'a bata Hostel ba ko?".

"An bata wallahi to bamu san ta inda zamu fara neman É—akin ba ne shiyasa muka tsaya a nan".

Dariya budurwar ta yi sannan tace.

"Bari muga wana Hostel aka bata".

Ta faɗa tana karɓar takardar Hostel ɗin da aka bawa Amrah ɗin.

"Lah ai Hostel É—in mu ne ma".

Ta faÉ—a tana É—ago kai sannan ta kai duban ta wajen Amrah.

"Ƙawata saki ranki mana, kefa yanzu kin zama ƴar makaranta dan haka kima share hawayen ki yanzu mu ne ƴanuwan ki".

Ta faÉ—a tana kamo hannun Amrah,sannan ta dubi su yaya Hisham tace

"Yawwa ni dai sunana Amira kuma nima sabuwar zuwa ce dan ko sati guda ban fi da zuwa ba, dan haka idan ba damuwa zamu wuce da ita sai ta zauna a ɗakin mu,tun da naga ɗakin da aka bata duk tsofaffin ɗalibai ne a ciki,to ba lalle ta ji daɗin zama da su ba amma yanzu idan a ɗakin mu ne, dukan mu sabbin zuwa ne komai zamu yi tare,wataƙila ma depertment ɗin mu ɗaya, kun ga zata fi sake jiki a cikin sa'anin ta, amma fa idan kun ga hakan bai muku ba,sai na rakata ɗakin da aka bata ɗin".

Har Anwar ya buÉ—i baki zai ce wani abu kawai ya ji Gwaggo Sa'adatu ta yi caraf tace.

"Lah wallahi mun gode sosai gaskiya kina da kirki kuma mun ji daÉ—in hakan, Allah ya miki Albarka ya baku Sa'a a karatun ku".

Kallon Yaya Hisham Anwar yayi suka haÉ—a ido da alama dai su basu so hakan ba amma kuma ina aikin gama ya gama tun da Gwaggo Sa'adatu ta riga ta yi magana.

Godiya suka yiwa Amira sannan Anwar ya zaro maƙudan kuɗaɗe tare da sabuwar waya dal ya miƙawa Amrah wadda ita ma da alama ta ji daɗin haɗuwar ta da Amira ɗin.

Kayan Amrah É—in suka fara shigarwa cikin Hostel, wanda ba zasu iya ba kuma suka yiwa securities magana suka taya su.

Sai da su Anwar suka ga angama shiga da kayan Amrah ɗin kafin suka yi musu sallama suka ce zasu tafi, nan fa sabon kuka ya ce Salama alaikum a wajen Amrah, da ƙyar Amira ta jata suka nufi Hostel ɗin.

ÆŠakin na su suka nufa da sallama suka shiga inda suka tarar da wasu Æ´an mata guda uku É—aya tana girki É—aya tana kwance,É—aya kuma tana gefe tana chat da wayar ta.

"Hi guys mun yi sabuwar ƙawa fa".

Amira ta faɗa tana ƙarasa shiga cikin ɗakin.

Juyowa suka yi baki É—aya suka zuba musu ido,amma banda É—ayar da take zaune tana chart wadda ko kai bata É—ago ba balle su sa ran zata musu magana.

"Sannun ki da zuwa".

Ƴanmata biyun suka faɗa

Kallon Amrah Amira ta yi wadda idon ta ya kaÉ—a ya yi jawur sannan ta ce.

"Amrah ki zauna daga yau mun zama Æ´an uwan juna ki saki jikin ki ki zauna a cikin É—akin nan ki É—auka kamar a gida kike".

Sannan ta juya ta nuna wadda take girkin wadda ta kasance fara ce sosai kuma doguwa, sai dai idan ka kalle ta zaka sanya ta a sahun masu kama da Æ´an Korea saboda yanayin fuskar ta duk irin na su ne.

"Wannan ita ce Anisa,waccan kuma da take kwance kasa ake baki labari in dai wajen bacci ne an sara mata, sunan ta Afrah, sai can da ki ka ga tana zaune tana chart sunan ta Azrah miskila ce da ki ka ganta aka ce wai kafi mahaukaci ban haushi".

Amira ta faɗa tana yi wa Azara gwaliyo dan ta san wataƙila sai ta zage ta saboda ta tsani kalmar miskila ɗin da take faɗa mata.

Afrah da Azra da Amira baƙaƙe ne sai dai kuma suna da kyau irin kyawun da ake ce musu Black beauties,sai dai kuma ko ƙafar Amrah ba su kama a kyau ba.

Sai a wannan lokacin Azra ta ɗago da fuskar ta inda ta jefawa Amrah wani kallo wanda muka kasa gane ma'anar shi, sannan ta miƙe tare da cewa.

"Mutum sai shegen jida-jide da wanda ya kamata, da wanda kafi ƙarfin kulawa da kabi ka dinga kulawa".

Azra ta faÉ—a tana shigewa toilet, ba wanda ya bi ta kanta a cikin mu.

Azra tana da wata cuta wadda mu ke ƙiran ta cutar hassada domin kuwa Azra a rayuwar ta ta tsani ta ga wani ya fi ta,ko ya wuce ta da wani abu, wannan dalilin ya sanya ta na yiwa Amrah kallo ɗaya ta ji bata kwanta mata a rai ba,duba da yadda kafin zuwan Amrah ba wanda ya kai Azra kyau a cikin mu,amma kuma sai ga Amrah ta zo ta kereta, wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da ya sanya Azra bata ƙaunar Amrah, sai dai kuma bata bayyana mana hakan ba.

*****

Washegari ya kama Monday in da muka shirya gaba ɗayan mu cikin shiga mai kyau da ɗaukar hankali, mayafi muka sanya dukan mu amma ban da Amra wadda ta sanya hijab ruwan blue wanda yake har ƙasa kuma ya bala'in yi mata kyau.

Tana gama sanya hijab ɗin Azra ta dube ta sama da ƙasa sannan ta ce.

"Amra mai ki ke nufi?, Ba dai da wannan abun kike nufin zamu fita lecture ba?".

Kallon kan ta Amra ta yi ita a tunanin ta ma wani abu taga ni marar kyau a jikin hijab É—in ya sanya ta faÉ—i haka,sai dai bata ga komai ba daman ta san haka tun da ta san cewa hijab É—in ta sabo ne yau ta fara sanya shi ma.

"Azra wani abu ki ka kalla a jikin hijab É—in nawa?".

Sanya hannu Azra ta yi ta É—akko wani mayafi mai ruwan atamfar jikin Amrah a cikin kayan ta sannan ta sanya hannu ta cire hijab É—in jikin Amra É—in ta ce.

"Haba Malama sai kace wata village girl, duk da nasan Giwa da Zaria da bambanci amma dai ai yanzu Zaria ki ke dan haka ki ajiye hijab a gefe ki sanya mayafi sai ma kin fi kyau.

Murmushi Amra ta yi duk da cewar maganar Azra É—in bata mata daÉ—i ba amma haka ta basar tare da É—aukan hijab É—in ta ta mayar jikin ta sannan ta ce.

"Azra ni fa karatu ya kawo ni ban zo makarantar nan da na yi gayu ko wani ado ba, dan haka ni ban saba sanya mayafi ba,ko dai wayayyu da ku ka saba sanya shi sai ku sa ku yi ta fama".

Sosai Azra ta ɓata rai da maganar da taji Amrah ɗin ta faɗa wanda har muka isa lecture hall ɗin Azra bata kula kowa a cikin mu ba.

Lecture aka mana in da bayan lecturer É—in ya gama ne ya yi tambaya, kuma cikin ikon Allah Amrah ta tashi ta bada amsa gamssashiyya, hakan ya janyo hankulan Æ´an depertment É—in da dama kan Amrah domin kuwa take ta fara shiga ran wasu da yawa kun san dai yadda mutum mai ilimi yake a cikin mutane, to haka Amrah lokaci guda ta yi farin jini a wajen Æ´an class É—in na mu.

A ɓangare guda kuma wanan dalilin ya ƙara dasa tsanar Amrah mai ƙarfi a zuciyar Azra.

Bayan mun tashi a lecture Kai tsaye muka nufi komawa Hostel in da Amrah ta ce ita kam zata tsaya a masallaci ta yi salla da karatu kafin ta dawo Hostel.

"Mtsssswww mun ga mangoperck ma ƙarshen boko kennan".

Muka tsinkayi muryar Azra ta faÉ—a tana mai wucewa ta bar mu a tsaye.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya in da kullum Azra bata da aiki wanda ya wuce ta ga ta baƙantawa Amrah rai.

Sai kuma aka yi rashin Sa'a domin kuwa Amrah bata taɓa nuna ta san ma mai Azra ɗin take ba, idan zata mata abun ɓacin rai guda goma ta ko guda ɗaya Amrah bata ɗauka a matsayin abun da zai sa ran ta ya ɓaci.

Wannan abun ba ƙaramin damun Azra yake ba domin kuwa ita kam bata da buri da ya wuce ta ga ta ƙona ran Amrah ɗin musamman da ta fahimci cewa Amrah ƴar talakawa ce.

A ɓangaren mu kuwa ni da su Afarah ba wani abu mummuna da muke nunawa Amrah na musgunawa kullum cikin jan ta a jiki mu ke, musamman da muka fahimci cewa ta fi mu saurin fahimta da gane karatu.

Duk bayan sati Yaya Umar ko Yaya ko yaya Usman É—aya daga cikin su yana kawowa Amrah ziyara domin su duba ya yanayin karatun na ta.

Shi kuwa Anwar kusan kullum ƙafar shi tana cikin makarantar mu, domin kuwa wata irin kulawa ta musamman ya ke bawa Amrah ɗin ga waya da suke akai-akai.

Sai dai duk zuwan da Anwar ɗin yake har yau wajen wata guda basu taɓa haɗuwa da su Azrah ba, ni kaɗai na san shi, sai dai duk sanda ya ƙira yana yawan tambayar ta ƙawayen ta kuma wani lokacin har ba mu wayar take mu gaisa dukan mu.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya in da yau muke dosar wata biyu da fara karatun mu.

Zaune mu ke a lecture Hall ɗin mu in da kowa ya duƙufa wajen duba takrda sakamakon test ɗin da wani lecture ɗin mu zai mana.

An yi test Alhamdulillahi kuma test ɗin ta yi mugun sauƙi ba kamar yadda muka yi tunani ba.

Kasancewar kowane lecturer da irin method of yadda yake gudanar da abubuwan shi, to wannan ma haka wanda mu ke cewa Prof,a ƙa'ida ba ya bada test sai dai ya kafe sunayen masu highest mark.

"Amira Prof fa ya kafe list É—in wanda suka ci test É—in shi".

Wata ƙawar mu da mu ke ƙira Maryam ta faɗa tana mai ficewa daga hall ɗin.

Da sauri muka miƙe dan mu je mu duba.

Murmushi Azra ta yi sannan ta ce.

"Wanda ya san bai tsinana abun kirki ba ai shi zai É—aga hankalin shi".

Ta faÉ—a tana gyara zaman mayafin ta.

Cikin ikon Allah kuwa muna zuwa muna dubawa sunan mu duka ya fito amma sunan Amrah shine a farko.

Innalillahi ina wuta Azra ta jefa kanta, murna mu ke Sosai tare da rungume Amrah.

Fuuuuu Azra ta juya ta bar wajen cikin tsananin ƙunar zuciya.

*MANGA* ✍️.
Comment
Share
Fisabillillahi

*FANSAR FATALWA*

_Tsarawa/Rubutawa_

© *SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_ .

*Free book*

--------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*014*
____________________________

Kaf cikin mu ba wanda ya lura da yanayin da Azra ta bar wajen,mu kam sai murna mu ke, Amrah ce ta fara farga da cewar Azra bata wajen,kallo na ta yi sannan ta ce.

"Amira Azra fa?".

Sai a sannan muka juya inda muka lura cewar Azra É—in bata wajen.

ÆŠaga kafaÉ—a na yi alamar bansani ba sannan nace.

"Kun ga mu wuce Capteria mu je mu ci abinci dan wallahi yau girki na ne,kuma gaskiya ba zan iya girki ba".

"Haka dai kullum mutum ya iya".

Cewar Afra tana galla mun harara.

Murmushi Amra ta yi sannan ta ce.

"A'a ba za'a yi haka ba mu je Hostel É—in ni sai na girka mana, ga mu da kayan abinci kuma mai ye zamu je mu kashe kuÉ—in mu".

Juyawa muka yi duka sannan muka nufi Hostel É—in.

Azra kuwa tana barin bakin notice board ɗin kai tsaye Hostel ta wuce tana tafiya kamar zata kifa ga zuciyarta da take jin tana mata wata iriyar suya kamar ƙirjin zai ƙone.

Tana isa ɗaki ta dannawa ƙofa key sannan ta cire mayafin ta ta yi wulli da shi gefe kafin kuma ta nemi bakin gado ta zauna tana mayar da numfashi kamar wadda ta yi gudun tsere.

Ta É—auki tsawon lokaci a haka tana zaune kafin ta yi auni ta ji abu mai É—umi a kuncin ta.

Hannu ta sanya ta gogo wajen tabbas idan har ba ƙarya idanun ta suka mata ba wannan hawaye ne yake zubowa daga cikin idonta.

Mai hakan yake nufi?,kuka ta ke saboda waccan yarinyar Æ´ar matsiyatan?.

Azra ta tambayi kan ta a zuciyar ta.

"Ƙarya ki ke wallahi Amra!, Wallahi ƙarya ki ke ki zama dalilin zubar hawaye na a doron ƙasa".

Azra ta faɗa cikin ƙaraji tana miƙewa tsaye tare da fara zagaye cikin ɗakin, kafin ta cigaba da magana.

"Wacece ke Amra?, Ai wallahi baki isa ki zamar mun baƙin ciki ba,ya zamar mun dole na yi gaggawar ɗaukar mataki a kan ki tun kafin lokaci ya zo ya ƙure mun".

Bugun ƙofar da ta ji ana yi ne ya sanya ta saurin shiga toilet ta wanke fuskarta sannan ta fito ta buɗe ƙofar.

Su Amra ta gani tsaye a bakin ƙofar, Saurin kawar da kan ta gefe ta yi sannan ta juya ta koma cikin ɗakin domin tsayuwar ta a wajen dai-dai ya ke da tonuwar asirin ta.

Da ido muka bi ta gaba É—ayan mu cikin tsananin mamaki domin kuwa kallo É—aya muka mata muka fahimci cewa ta yi kuka.

Shiga cikin É—akin muka yi inda na buÉ—i baki tare da duban Azra sannan na fara magana.

"Azra lafiya kuwa?".

Da sauri ta É—ago kan ta tare da duba na irin duban mai ki ke nufi sannan ta ce.

"Mai ki ka ga?, Ko wani abu ki ka ga ni daban?".

Kallon juna muka yi sannan Anisa ta ce.

"Azra ai ba wani abu zaki ce ta ga ba, cewa zaki yi wani abu ku ka ga, Azra alamun ki sun yi kama da na marar lafiya, kuma gashi kamar kin yi kuka".

Ɗan ƙaramin tsaki Azra ta ja kafin daga bisani ta ce.

"Ba wata damuwa fa, kawai É—an kai na ne na ji ya namun ciwo, kuma na sha magani".

Addu'ar samun lafiya muka mata amma nikam ba wai na yadda da bayanin na ta bane.

******

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya kullum ƙawancen mu ƙara ƙarfi yake, duk in da zaka ga ɗaya daga cikin mu to zaka ga sauran, wannan dalilin ya sanya har suna muka sanja domin kuwa idan kaje Hostel ko class ɗin mu idan baka ce Five Stars ba to ba wanda zai gane mu ka ke nema.

Kwance tashi ba wuya a wajen Allah yau mu ke shirin fara jarrabawar mu ta first semester a school.

Kowa ka gani karatu ya ke ba kama hannun yaro.

Mu ma a ɓangaren mu ba'a bar mu a baya ba domin kuwa fafafa mu ke karatu sosai kamar kan mu zai cire.

Cikin ikon Allah mun fara jarrabawa yau kuma Alhamdulillahi exam ɗin yau ɗin ya yi sauƙi.

Haka abubuwa suka cigaba da tafiya in da yau mu ke zana Paper ɗin mu ta ƙarshen a makaranta.

Mun gama jarrabawa lafiya in da kowa kuma ya fara shirin tafiya gida sakamakon hutun wasu Æ´an kwanaki da aka mana.

Amra ma a ɓangaren ta ya Anwar ya zo ɗaukar ta, a sannan ne kuma muka taho da su Anisa da Afra da Amra in da Azra ta ke biye da mu a baya.

Kasancewar duk an zo É—aukan mu, in da kowa motar gidan su ta zo É—aukan shi.

"Lah Afra ga can yaya Anwar a tsaye ku zo mu je ku gaisa".

Amra ta faÉ—a tana sakin murmushi.

"Ah yau zamu ga Yaya Anwar É—in nan dai wanda kullum aka bi aka dame mu da zancen shi"

Afra ta faÉ—a tana kai duban ta in da Anwar ya ke tsaye.

Tun da suka doshi wajen Afra ta kafe Anwar da ido tana jin wani irin baƙon al'amari a tattare da ita.

Murmushi Anwar ya shiga sakarwa Amra in da ita ma ta shiga mayar mishi har suka isa wajen.

"Ga Majnun ɗin Amra ya ƙaraso".

Amira ta faÉ—a cikin sigar zolaya.

Dariya Anwar ya yi sannan yace

"Ai na wuce Majnun a wajen ta domin soyayyar mu ta wuce irin soyayyar laila da Majnun, ta zarce ta romio da Juliet, ta kere ta Ram da Sita, ko ba haka ba Masoyiya".

Yaya Anwar ya faÉ—a yana kashewa Amra ido.

Rufe idon ta Amra ta yi cikin jin kunya.

"Ah lalle ma Watau Anwar ko kunya ta baka ji".

Amira ta faÉ—a tana rufe baki.

Tun da suka tsaya a wajen Afrah ta kafe Anwar da ido ko ƙiftawa bata yi, lokaci guda ta ji guy ɗin ya matuƙar burge ta.

Amrah ce ta juyo tana cewa.

"Afra, Anisa da kuma Amira ga Ya Anwar É—ina".

Turus ta ja ta tsaya ganin irin yadda Afrah ta kafe Anwar ɗin da ido ko ƙiftawa ba ta yi, bata ma san abun da Amrah ɗin ta ke cewa ba.

Cike da mamakin ganin irin kallon da Afrah ɗin ta kewa Anwar Amrah ta taɓa ta tare da jijjiga tana cewa.

Wani irin ƙayattaccen murmushi Azra ta saki wanda ita kaɗai ta san ma'anar shi a ran ta tace.

"Tabbas na samu makami, Tabbas Afrah da ke zan yi amfani wajen cikar muradi na, Afarah ke zaki zamar mun makamin da zan riƙa dan tarwatsa rayuwar wannan ƴar matsiyatan".

"Afrah lafiya kuwa?".

Afrah ta tainkayi muryar Amrah ta daki dodon kunnen ta kamar sauƙar aradu.

Da sauri Afrah ta É—an firgita sannan ta yi saurin basarwa tare da sosa kai alamar rashin gaskiya sannan ta ce.

"Uhmmm Amrah gaskiya ya Anwar É—in ki ya haÉ—u, kuma kun dace sosai wallahi, Ubangiji ya tabbatar da Alkhairi a tsakanin ku".

Amrah bata kawo komai a ranta ba ta saki murmushi sannan ta ce.

"Ameen ya Allah Afrah, yawwa Masoyi ga su Afrah da Anisa fa,waccan kuma ta bayan ita ce Azra da nake baka labarin su, ita kam daman Amira ka santa ai".

Sai a sannan Anwar ya É—ago ya dube su, kallo É—aya ya musu ya É—auke kai a lokaci guda ya ji zuciyar shi ta tsananta bugu wanda bai san dalilin hakan ba.

Haka kawai Anwar ya tsinci kan shi da jin ƙin su Afrah ɗin musamman ma Azra, sai dai ko da wasa bai nuna wa Amra ba dan ya san yadda take ji da ƙawayen nata hakan zai iya sawa su samu matsala.

Sama-sama suka gaisa da su Afarah É—in kafin ya juya ya shiga mota yana cewa.

"Masoyiya ki yi sauri mu kama hanya mu tafi kin ga Æ´an gida suna jiran ki".

Juyawa Amrah ta yi ta kalli in da su Amira su ke sannan suka shiga yin bankwana da juna.

Har Amrah ta shige cikin motar Afrah bata daina bin motar da kallo ba.

Duk abun da Afrah ta ke Azra tana ankare da ita, kuma tunin Azra ta ramfo jirgin da Afrah É—in ta hau, kasancewar Azra mutum ce mai shegen yawo da kaifin basira ya sanya kallo É—aya ta yiwa Afrah É—in ta fahimci in da ta dosa.

*****

Tafe su ke a cikin mota ita da Ya Anwar ɗin, hira suke yi sosai cikin so da ƙaunar juna.

Kallo ɗaya zaka mu su ka fuskanci irin tsantsar shaƙuwa da kuma son da suke yiwa juna.

"Amrah".

Ya Anwar ya ƙira sunan ta cikin wata iriyar murya da ta kasa tantance ta.

ÆŠagowa Amrah ta yi ta dube shi sannan ta ce.

"Na'am ya Anwar".

"Amrah kina so na!?".

Da sauri Amrah ta kalle shi cikin tsananin mamakin tambayar da ya mata É—in.

"Ya Anwar wannan wace kalar tambaya ce hak?".

"Amrah ki bani amsar tambaya ta, kafin ke ma ki jefa mun ta ki tambayar".

Anwar É—in ya faÉ—a yana mai kai duban shi zuwa kan titi.

"Yaya Anwar kalli cikin ido na sai ka maimaita tambayar da ka mun É—in".

"Meyasa sai na kalli cikin idon ki?".

"Yaya Anwar saboda a ido na zaka ga amsar tambayar ta ka, ya Anwar ka sani cewa jinina da naka sun daÉ—e da gauraya sun zama abu guda, sannan ka É—auki kan ka a matsayin jijiyar da ta ke yawo da jini a jiki na, idan aka datse wannan jijiyar mai ka ke tunanin zai faru".

"Mutuwa".

Ya Anwar É—in ya bata amsa.

"To ka sani idan babu kai a cikin rayuwar ta to babu wannan rayuwar, rasa ka a cikin rayuwa ta dai-dai ya ke da a sanya almakashi a datse duk wata jijiya ta jiki na, ya Anwar ina son ka da dukkan zuciya ta da kuma gangar jiki na, ina son ka fiye da yadda na ke son kai na, ko bayan rai na zan roƙi Ubangiji ya ƙara haɗa mu rayuwa a gidan Aljannatul firdaus".

Amrah ta ƙarashe maganar cikin rawar murya.

Sosai Anwar ya ji daÉ—in maganganun Amrah É—in a hankali ya yi parking É—in motar a gefen titi sannan ya juyo ya fuskance ta tare da kafe ta da idanuwan shi har sai da Amrah ta ji gaba É—aya ta tsargu.

"Amrah in sha Allah ni na kine ke kaɗai, an hallice ni ne saboda ke,kema an hallice ki saboda ni, zamu rayu tare sannan ko mutuwa ce zan roƙe Ubangiji ya ɗauki rayuwar mu a tare saboda rashin ki a tare da ni tamkar rashin numfashi ne a tare da ruhu na,Allah ya miki Albarka Amrah nah".

Murmushi Amrah ta yi tana jin wani irin mugun son Anwar ɗin yana ƙara zagaye duk wani sashi na zuciyar ta,wasa ta fara yi da bakin hijab ɗin ta sannan ta ce.

"Ameen ya Anwar".

Jan motar Anwar ya yi sannan suka shiga cikin garin Giwa É—in.

Tun bai gama parking ɗin motar ta shi ba, Amrah ta shiga ƙoƙarin buɗe ƙofar da gudu kuwa ta fice ta shige gidan na su in da ta rungume Gwaggo Sa'adatu wadda fitowar ta Kennan daga ban ɗaki.

Wata irin wawiyar runguma Amrah ɗin ta yiwa Gwaggo Sa'adatu har sai da suka kusa kifawa da ƙasa.

Salati da sallamimi Gwaggo Sa'adatu ta shiga yi tare da cewa.

"Kin tafi kwana biyu muna kewar ki yanzu kuma kin dawo kina shirin ɓalla ni".

"Kai Gwaggo irin ko ki yi murnar dawowa ta ma, to shikennan bari na koma kawai".

Amrah ta faɗa cikin shagwaɓe fuska, hadda su bubbuga ƙafa.

Janyo ta Gwaggo Sa'adatu ta yi jikin sannan ta ce.

"Haba dai Shalelen Gwaggon ta, lale marhabun da dawo wa, ai tabbacin ma cewa na yi farin cikin da dawowar ki na shirya miki abun da ki ka fi so, ke de shiga ki cire ga ruwan wanka zan haÉ—a miki, ki gama ki zo ki ban labarin makaranta".

Shigowar Ya Anwar da yara biye a bayan shi suna shigowar da kayan Amrah ya katse Gwaggo Sa'adatu daga maganar da take.

Gaisawa suka shiga yi kafin kuma ya juya ya fita, bayan Amrah ta mi shi rakiya har motar shi ya kama hanyar komawa Zaria.

Sosai Æ´an gidan su Amrah suka yi farin ciki da dawowar ta, haka aka dinga nan da nan da ita kamar ta shekara bata gidan, abun ka da Æ´ar gaban goshi.

*MANGA* ✍️
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_ .

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_💀☠️ ).

Tsarawa/Rubutawa

© *SHAMSIYYA MANGA* .

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA* : _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_ .

*Free book*

---------------------------------------------

*015*
*Bissimillahir rahmani rahim*
_____________________________

Yau kwanan Amrah Biyu da dawowa hutu gida.

Zaune su ke a tsakar gidan su ita da Anwar suna hira cikin so da ƙaunar juna, in da Gwaggo Sa'adatu ta ke ɗaki tana sauraren radio.

Girki Amrah É—in ta É—aura kasancewar in dai tana gida daman da wuya ta bar Gwaggo Sa'adatu ta É—aura girki komai ita ta ke musu.

Wayar Anwar ce da take riƙe a hannun Amrah ta yi ƙara alamar shigowar saƙo.

Miƙa mishi wayar Amrah ta yi tana cewa.

"Masoyi ga wayar ka an turo saƙo".

Anwar bai karɓi wayar ba sai ma cewa ya yi.

"Duba mana kiga mai aka turo mana".

"A'a Yaya Anwar ba kyau duba sirrin mutum".

Harara Anwar É—in ya jefawa Amrah É—in kafin daga bisani ya ce.

"Lalle ma Watau kina nufin sirri na ba naki bane ba!?".

Marairaice fuska Amrah ta yi sannan ta ce.

"A'a fa Yaya Anwar ba haka na ke nufi ba,wai da naga kamar baƙuwar number ce".

"Eh buÉ—e ki karanta mana ba ni nace ba".

"To Yaya Anwar angama bari na karanto".

Amrah ta faÉ—a tana mai buÉ—e message É—in.

Ƙurawa message ɗin ido Amrah ta yi tana jin wani irin matsanancin faɗuwar gaba sakamakon ganin abun da aka rubutu a message ɗin.

"Masoyiya lafiya kuwa?, Karanto mana ina jin ki".

Murmushi Amrah ta yi sannan tace.

"Kai Yaya Anwar ashe ma message É—in MTN ne".

Amrah ta faÉ—a tana ficewa daga wajen message É—in tare da goge shi gaba É—aya daga cikin wayar, sannan ta É—auki number É—in da aka turo message É—in ta yi seving a wayar ta.

Miƙa mishi wayar ta yi sannan suka cigaba da hira ko kaɗan Amrah bata nunawa Anwar wani abu ba, duk da kuwa yadda take jin zuciyar ta kamar zata fashe ga wani ɗaci da zuciyar take mata.

Sai dai kuma duk yadda Amrah ta so ta ɓoye halin da take ciki ɗin sai da Anwar ya fahimci sanjin yanayin da ta yi.

Amma kuma duk tamabyar duniyar da ya mata cewa mishi ta yi babu, in da daga ƙarashe tace mishi kan ta ne yake mata ciwo.

Shidai Anwar ba wai ya yarda da abun da tace É—in bane, haka suka yi sallama ya wuce ya tafi, ita kuma ta shiga É—aki.

Tana shiga É—aki ta fara dialing number É—in da ta É—auka É—in sai dai kuma abu É—aya ake sanar da ita shine wayar a kashe.

Haka ta cigaba da gwada ƙiran wayar amma haka dai ake ta ce mata a kashe.

Shiru Amrah ta yi tare da zama a gefen katifar ta,sannan dafe kan ta tana jin zuciyarta kamar zata fashe.

Message ɗin da ta ga an turowa Anwar ɗin ne ya shiga dawo mata a cikin ƙwaƙwalwar ta.

" _Barka da wannan lokacin kyakkyawa mai kyawun zuciya,Tauraro a cikin taurari mai haskawa,da farko dai na_ _san ganin message ɗin nan zai sa zuciyar ka a cikin tunani da kuma son sanin ko ni wacec? Sai dai kuma hakan ba abun_ _damuwa bane domin kuwa ka sanni sai dai baka san cewar ni ɗin ce na turo wannan saƙon ba, Anwar ba zan ɓoye ma ka ba wallahi tun kallon farko da na maka a ranar farko na ji zuciyata ta kamu da son ka, ina kuma fatan mu kasance a inuwa ɗaya a matsayin mata da miji, kar dai na cika ka da surutu Anwar ina son ka ina ƙaunar ka,kuma zan jure duk wani irin cin_ _mutunci in dai daga wajen ka ne"_ .

A hankali ta fara jin wasu irin hawaye masu zafi suna biyo wa ta kuncin ta.

Innalillahi wa'innailaihi rajiun ta shiga maimaitawa har ta samu ta ji zuciyar ta ta mata sanyi.

*****

A ɓangaren Anwar kuwa yana isa gida ya cire kayan shi ya shiga wanka, bayan ya fito ya shirya cikin kaya marassa nauyi tare da yin alawlar sallahr magariba kasancewar lokacin ya yi.

Yana cikin zira kayan shi ne ya ji wayar shi ta yi ƙara alamar shigowar saƙo.

Duban shi ya kai kan wayar inda ya ci karo da message da number É—in da aka turo É—azu.

Kallon message É—in ya shiga yi cike da mamakin to waye zai turo mishi irin wannan message É—in?.

Tsaki ya ja sannan ya yi deleting message É—in tare da ajiye wayar ya fice ya tafi massallaci.

Abun mamaki Anwar yana dawowa daga massallaci ya tarar da messages wajen guda biyar kuma duka da numbobi mabanbanta, sai dai kuma message É—in duka iri É—aya ne wanda shi zai tabbatar maka da cewar mutun É—aya ne yake turowa.

Har ya danna number ɗin zai ƙira sai kuma ya basar kawai sannan ya shiga ya yi blocking ɗin duka numbers ɗin.

Haka abubuwa suka cigaba da gudana in da kullum wayewar garin Allah ta'ala sai an yiwa Anwar message na kalaman soyayya a ƙalla sau biyar a rana.

Sai dai Anwar ko dai-dai da rana guda bai taɓa bi ta kan mai tura message ɗin ba, in da ana turo message ɗin zai shiga ya yi blocking ɗin number ɗin sannan ya goge message ɗin saboda gudun kar Amrah ta kalla, duk kuwa da cewar ya san ko ta gani ma ba lalle ta nuna ɓacin rai a gare shi ba amma ya san dole zata ji ba daɗi.

Abu fa kamar wasa tun lamarin yana bawa Anwar mamaki har ya koma bashi tsoro in da ya fara tunanin ko dai ba mutum ba ne yake tura message ɗin ba, Duba da yadda kullum sai an turo kuma ba sau ɗaya ba, gashi idan ya yi blocking number yanzu to anjima za'a sake ƙira da wata number.

Haka Anwar ya cigaba da share lamarin a tunanin shi idan suka ga ba'a kulawa za'a daina turo message ɗin, amma sai dai fa kamar ma ƙara ƙarfafa lamarin ya yi.

*****

Afrah na gani tsaye a cikin bedroom É—in ta sai kaiwa da komowa ta ke, hannun ta rike da waya, kallo É—aya zaka mata ka fahimci cewa tana cikin damuwa.

Turo ƙofar aka yi aka shigo cikin ɗakin in da Afrah ta kai kallon ta wajen ƙofar da sauri.

Anisa ce ta shigo É—akin da alama yanzu ta iso gidan.

Da sauri Afrah ta ƙarasa wajen ta tare da ruƙo hannun ta cikin rawar murya ta fara magana.

"Anisa ina cikin damuwa, Anisa na rasa ya zan yi da rayuwa ta wallahi".

Afrah ta faɗa tana ƙara matse hannun Anisa a cikin nata.

Jan hannun ta Anisa ta yi zuwa kan gadon É—akin sannan suka zauna kafin Anisa É—in ta dubi Afrah ta ce.

"Afrah ba sai kin sanar dani cewa kina cikin damuwa ba domin kuwa kallo É—aya mutum zai miki ya fahimci hakan indai har ya sanki, yanzu faÉ—a mun meye damuwar ki?".

"Anisa wallahi nasan ko na faÉ—a miki damuwa ta ba lalle ki gane ba har ki goyi bayana ba"

Afrah ta faÉ—a tana sanya hannu tare da share hawayen da ya zubomata.

"Afrah ki faɗa mun ko mainene na miki alƙawarin zan goyi bayan ki kuma zan taya ki wajen ganin kin samu".

Shiru Afrah ta yi kamar ba zata yi magana ba,kafin kuma daga bisani ta ja dogon numfashi tace.

"Anisa Anwar na ke so,kuma na ke son aure".

Kafe ta da ido Anisa ta yi tana so ta gano shin daga ƙasan zuciyar Afrah wannan maganganun su ke fitowa ko kuwa dai wasa take.

"Anisa nasan zaki iya cewa baki gane wane Anwar nake nufi ba,to bari na fito na miki bayani ta yadda zaki fahimta Anwar saurayin Amrah wanda zata aura shi nake so, ba damuwa ta bane idan ya aure mu duk mu biyun ni dai fatana shine ya amince kuma ya aure mu É—in".

Ƙaran ƙiran wayar Anisa da aka yi shi ya dakatar da ita daga shirin yin maganar da take son yi ɗin.

Ɗaga wayar ta yi bayan ta duba mai ƙiran nata sannan ta kara a kunnen ta tare da fara magana.

"Hello Azra ya akayi ne?".

Daga ɗaya ɓangaren Azra ce ta amsa da cewa

"Anisa kina ina ne na zo gidan ku ba kya nan kuma kin san da maganar fita unguwar da muka ce zamu yi?".

Kasancewar Azra da Anisa sun fi shiri sosai da kuma kusanci ko a cikin cleaque ɗin na mu, in da nikuma kafin shigowar Amrah cikin mu ya zamana na fi shiri sosai da Afrah jinin mu ya fi haɗu,saboda ni mutum ce da in dai abu ya take gaskiya to sai na faɗawa mutum idan naga yana aikatawa ko da zai ji haushi na,wannan dalilin ya sanya muke ɗan samun saɓani da Azra wani lokacin idan ta yi abu na mata magana sai ta ji haushi na hau ni da faɗa nima sai na hauta.

"Wallahi Azra Anisa ce ta mun ƙiran gaggawa wai tana son gani na, yanzu haka dai ina gidan su".

Anisa ta faɗa daga nata ɓangaren.

"Ok to bari nazo na same ki a gidan".

Azra ta faɗa tana datse ƙiran.

Ba'a É—auki tsawon lokaci ba Azra ta iso in da ta tarar da mu jigum-jigum a cikin É—akin.

Turus ta yi ta tsaya ganin hawaye shaɓe-shaɓe a idanun Afrah ɗin.

"Afrah lafiya kuwa? Waye ba shida lafiya?, Ko mutuwa aka yi?".

Azra ta ƙarashe maganar tana ƙarasawa bakin gadon da su Afrah ɗin suke.

Kwashe duk abun da Afrah ta sanar da Anisa, Anisa ta yi ta sanarwa da Azra sannan ta ƙara da cewar.

"Maganar gaskiya bansan wace irin shawara zan bata akan wannan lamarin ba,domin kuwa gaba ɗaya kaina ya kulle, abu mafi wuya ne a ce Afrah ta mallaki Anwar matuƙar Amrah tana nuna numfashi a doron ƙasa, to amma ban sani ba ke ko kina da shawarar da zaki bata".

Anisa ta faÉ—a tana kafe Azra da ido.

Murmushi Azra ta yi sannan a zuciyarta ta furta.

" _Masha Allah an zo dai-dai gaɓar da nake so_ ".

A fili kuma sai ta dubi Afrah ta ce.

"Yanzu Afrah saboda É—a namiji ki ke kuka?, Mai aka yi aka yi wani Anwar da har zaki zauna kina asarar hawayen ki a kan shi?, To wallahi tun wuri ma ki share hawayen ki haba sai kace ba mace, yanzu faÉ—a mun ya ki ke so a yi?".

Share hawayen idanun ta Afrah ta yi sannan ta dubi Azra ta ce.

"Azra idan da ina da yadda zan yi da ba zan tsaya ina sanar da ku damuwa ta ba, rashin sanin abun yi shi ya sanya har na sanar da ku dan ku bani shawara".

Shiru Azra ta yi kamar mai nazarin wani abu kafin can ta numfasa tace.

"Shikennan yanzu abun da nake so da ke ki fara tura mishi messages mu gani idan har ya yi responding to,duk da ma nasan abu ne mai wuya amsawar tashi amma dai sai an gwada akan san na ƙwarai,sannan kar kice dan kin tura sau ɗaya bai yi reply ba zaki dakata a'a idan zaki tura sau goma bai amsa ba ki cigaba da turawa har a dace,idan kuma wannan hanyar bata yi ba,to ina da wata hanya wadda na tabbata idan muka bi ta kamar kin mallaki Anwar kin gama,amma fa kuma wannan hanyar hatsarin ta ya fi mallakar Anwar wahala,domin kuwa nasan idan har ba wani ikon Allah ba ba lalle ki yarda ba,amma koma mainene yanzu dai a gwada wannan ɗin mu gani, sauran bayani kuma sai mun koma makaranta".

"Amma Azra wallahi zuciyata tana tsoron abun da zai je ya dawo, bana son na ci amanar Amrah, wallahi ina tsoron kar bakin mutane ya yi yawa a kaina har a zo a mun tofin ala-tsine".

Afrah ta faÉ—a tana jin matsanancin faÉ—uwar gaba.

"Ita Amrah ɗin ƙanwar uwar ki ce da ba zaki iya cin amanar ta ba, Dalla malama idan zaki farka ki ajiye wannan maganar a gefe ma to tun wuri ki farka,ita Amrah ɗin sai aka ce miki idan ita ce a matsayin ki ba zata iya cin amanar ki ba?, Da zaki wani ce yenyenyen".

Anisa ta faÉ—a cikin jin haushin abun da Afrah É—in ta faÉ—a.

Tun daga ranar da Azara ta bawa Afrah wannan shawarar Afrah ta shiga turawa Anwar message ba dare ba rana.

Kullum wayewar garin Allah ta'ala sai Afrah ta yiwa Anwar message aƙalla sau biyar a rana da layuka mabanbanta,in da ta sayi layuka sun fi a ƙirga,tana tura message ɗin zata cire layin daga cikin wayar ta sauya wani.

Sai dai ko dai-dai da rana guda Anwar bai taɓa bi ta kan messages ɗin da a ke tura mishi ɗin ba,hakan ko kaɗan bai taɓa damun Afrah ba daman ta yi tunanin kasancewar hakan.

*****

A ɓangaren Amrah kuwa cikin kwanaki ƙalilan ta zabge ta rame duk ta shiga damuwa, tun daga wannan ranar da taga message ɗin da aka turowa Anwar ɗin.

Tashin hankalin da take ciki ba zai misaltu ba, domin kuwa tun da taga message ɗin ta fara jin haushin wani irin yanayi gani take kamar ana daf da raba ta da Anwar ko kamar lokacin rabuwar su ne ya ƙarato.

Ta san Anwar yana son ta sosai amma kuma tana tsoron abun da zai je ya dawo domin kuwa ita ta san halin ƴan matan wannan zamanin matuƙar suna son abu to ba abin da ba za su yi ba dan ganin sun mallaki abun musamman na miji.

Yin duniya Gwaggo Sa'adatu ta yi da Amrah a kan ta sanar da ita damuwar ta amma fir Amrah ta ƙi,kullum idan Gwaggo Sa'adatu zata tambaye ta sau goma to amsa ɗaya ce, shine babu.

Wannan abu ba ƙaramin fara damun Gwaggo Sa'adatu ya yi ba, domin kuwa kullum Amrah ramewa take ƙara yi,duk wanda ya san Amrah a da to kallo ɗaya zai mata a yanzu ya fahimci sauyin da ta yi ɗin.

Har Malam Kabiru sai da Gwaggo Sa'adatu ta samu da zancen Amrah ɗin, inda shima ya ƙira ta ya tambaye ta amma amsar da ta bawa Gwaggo Sa'adatu ita ta bawa Mahaifin nata.

Shikam nasiha ya mata tare da ƙara tunatar da ita duk halin da ka tsinci kan ka to kar ka manta da addu'a sannan ka sani addu'a ba abun da bata magani.

Ni kaɗai Amrah ta ƙira a waya ta sanar da ni abun da yake damun ta cikin kuka ta kwashe komai ta sanar dani.

Haƙuri na bata sannan na ce mata ta dage da addu'a kuma in sha Allah Anwar nata ne ita ɗaya ta ma kwantar da hankalin ta.

Da waɗannan kalaman rarrashin da Amira ta ke yiwa Amrah ya sata ta ɗan fara jin sauƙin damuwar da take ciki.

Sai dai kuma kullum daren duniya fa Amrah da tunanin wannan message É—in ta ke kwana ta ke tashi, sai ta yi kamar zata yi Anwar zancen sai kuma ta fasa.

Yau Anwar ya ƙira Amrah yake sanar da ita cewar zai zo shi.

Wanka ta yi sannan ta É—an shafa powder da lipstick a bakin ta sai É—an kwalli da ta zizarawa idon ta.

Kamar yadda ta saba shiryawa ta yi cikin doguwar riga da dogon hijab har ƙasa, sai dai fa kana kallon fiskarta zaka fahimci ta rame sosai.

Ƙarfe huɗu dai-dai Anwar ya ƙira ta a waya ya sanar da ita ƙarasowar shi.

Tun da ta fito Anwar ya kafe ta ido yana mamakin ramar da ya gani a fuskar Amrah É—in.

Da sallama ɗauke a bakin ta ta ƙarasa wajen Anwar ɗin da yake tsaye a jikin motar shi, ita ma jingina ta yi a gefen motar tare da cewa.

"Barka da isowa ranka ya daÉ—e".

Ganin irin kallon da Anwar ɗin ya ke mata ne ya sanya ta tsarguwa da kan ta in da ta shiga kallon kan ta tana duba ko wani baƙon abu ya gani a jikin nata.

"Amrah mai yake damun ki?".

Anwar ya faÉ—a fuskar shi da alamar damuwa.

Duk yadda Amrah ta so ta ɓoye damuwar ta ta abun ya gagara, in da kamar jira take kawai sai gani Anwar ya yi ta fashe da kuka.

"Subhannallah Amrah meye haka kuma?, Mai yasa ki kuka, dan Allah ki sanar dani in har ba so ki ke nima na yi kukan ba, dan Allah kiyi shiru".

Cikin kuka Amrah ta dubae shi sannan ta buÉ—i baki tace.

"Ya Anwar......".

Sai kuma maganar ta katse sakamakon kukan da ya ci ƙarfin ta.

Anwar kam idan hankalin shi ya yi dubu to gaba ɗaya ya dugunzuma, cikin tsananin tashin hankali ya kamo hannun ta abun da bai taɓa yin attempting ba amma yau saboda yadda hankalin shi yake a tashe sai gashi ya kamo hannun ta, cikin rawar murya ya ce.

"Amrah Dan girman Allah ki yi haƙuri ki sanar da ni mai ya same ki?, Amrah ko ni na ɓata miki rai ban sani ba".

"Ya Anwar dan Allah ko bayan raina ban yadda ka ci amana ta ba,ya Anwar ko da ƙasa ta rufe idona dan Allah ya Anwar kar ka manta da soyayyar mu, kar ka manta da alƙawarin zukatan mu,ya Anwar ina jin wani irin abu a ƙasan zuciyata, ya Anwar ina jin kamar ba zan yi tsawon rai da har zamu cika burin mu ba, ya an........".

Kukan da ya ci ƙarfin Amrah ne ya hanata ƙarasa maganar da ta yi niyya ɗin da gudu kuma ta wafce hannun ta daga na Anwar sannan ta shige cikin gidan su ta bar Anwar tsaye kamar mutum-mutumi.

Faɗin irin tsananin tashin hankali da Anwar ya shiga a wannan lokacin ɓata lokaci ne sakamakon jin kalaman Amrah ɗin.

Wayar shi ya ɗaga ya shiga ƙiran layin ta amma ba'a ɗaga ba.

Innalillahi wa'innailaihi rajiun shine kawai abun da bakin Anwar ya shiga maimaitawa, da ƙyar ya tattaro duk wani sauran ƙarfin halin da ya rage mishi sannan ya buɗe motar shi ya shiga tare da kifa kan shi akan sitiyarin motar, Anwar bai yi auni ba sai jin wasu hawaye masu ɗumi ya yi sun shiga gangarowa ta kuncin shi.

Ya É—auki tsawon lokaci a cikin motar domin kuwa shi kan shi ba zai iya faÉ—in iya lokacin da ya É—auka ba a zaune a motar yana kuka kamar mace.

Kafin daga bisani ya zaro wayar shi ya ƙara dialing number ɗin Amrah ɗin sai dai a wannan karon ma bata ɗauka ba.

*MANGA* ✍️
Comment
Share
Fisabillillahi.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_💀☠️ ).

_Tsarawa/Rubutawa_

*© SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk in da ku ke ina son ku fisabillillahi_.

*Free book*

---------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*016*
______________________________

Da gudu Amrah ta ƙarasa shiga cikin gidan na su cikin kuka ta shige cikin ɗaki ko ta kan Gwaggo Sa'adatu ba ta bi ba da take zaune a tsakar gida.

"Subhannallah mai zan gani haka?, Amrah!, Amrah!"

Gwaggo Sa'adatu ta shiga ƙwala mata ƙira cikin tsananin tashin hankali.

Shirun da ta ji Amrah ɗin ta mata bata amsa ba ne ya sanya ta miƙewa da sauri ta bi bayan ta, tana cigaba da ƙwala mata ƙira, amma shiru Amrah kamar bata jin ta.

Shigar Gwaggo Sa'adatu É—akin ta tarar da Amrah a kwance a kan katifa ta yi ruf da ciki tana dirzar kuka kamar ran ta zai fita.

"Amrah lafiya kuwa?, Mai zan gani haka wai?, Mai ya faru da Anwar É—in?, Ko wani ne ya mutu?".

A lokaci guda Gwaggo Sa'adatu ta jefawa Amrah waɗannan tambayoyin tana ƙarasawa bakin katifar da take kwance ɗin, sannan ta ɗago kan ta ta ɗaura a kan cinyar ta.

Jin shiru Amrah bata da niyyar amsawa Gwaggo Sa'adatu tambayoyin da take mata ɗin ne ya sa ta ƙara cigaba da magana.

"Amrah ki buÉ—e baki kimun magana wani abu ne ya faru da Anwar É—in?, Ko wani ne ya mutu?".

Sai a sannan Amrah ta É—ago kan ta daga cinyar Gwaggo Sa'adatu É—in sannan cikin kuka ta buÉ—i baki ta fara magana.

"Gwaggo ko ɗaya ba wanda ya mutu, sai dai ni kuma da alama lokacin mutuwa ta ya ƙarato dan haka Gwaggo idan na mutu ku bini da addu'a kawai".

Ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka.

Hankalin Gwaggo Sa'adatu idan ya kai dubu to gaba É—aya ya tashi da sauri ta fara magana.

"Subhannallah Amrah wannan wace irin magana ki ke faɗa haka?, A duniya ai ba wani bawa da ya san lokacin mutuwar shi sannan duk wanda ki kaga ya mutu to lokacin mutuwar shine ya yi, dan haka kar na ƙara jin wannan maganar a bakin ki".

"Gwaggo dole nace lokacin mutuwa ta ya zo tun da ana shirin raba ni da rayuwa ta, ana shirin rabani da farin ciki na, Gwaggo wallahi mutuwa zan yi idan aka rabani da Anwar domin kuwa shine rayuwa ta".

Amrah ta faɗa tana ƙara tsananta kukan ta.

"Innalillahi wa'innailaihi rajiun, wai Amrah kan ki É—aya kuwa ki ke waÉ—annan maganganun?, Tukunna ma waye zai rabaki da Anwar É—in?".

Hannu Amrah ta sanya ta share hawayen idon ta kafin ta kwashe duk abun da ya faru a kwanaki biyun can na message ɗin da ta ga an turowa Anwar ɗin ta sanarwa da Gwaggo Sa'adatu sannan ta ƙara da cewar.

"Kinga kuwa Gwaggo dole nace ana shirin rabani da rayuwa ta, Gwaggo nasan halin ƴanmatan yanzu zuciyoyin su tsoron Allah yayi ƙaranci a ciki, kan su kawai su ke so, dan haka ni nasan tun da har aka fara turowa Anwar irin waɗannan saƙonin to ana daf da shiga tsakani na da shi".

Shiru Gwaggo Sa'adatu ta yi tana jin ta har ta dasa ayar tsayawa.

"Yanzu Amrah saboda wannan dalilin ki ka bi ki ka ɗaurawa kan ki damuwa, ki ka hana kan ki sukuni,to wallahi ni dai abun da zan faɗa miki shine duk tsananin da zaki shiga a rayuwa kar ki manta da cewar Allah shi yake bayarwa kuma shi yake hanawa, a yau idan ki ka ga baki auri Anwar ba to daman tun fil'azal Allah ya ƙaddara cewar shi ba mijin ki bane ba, sannan idan har Allah ya ƙaddaro cewa zaku rayu da Anwar a matsayin mata da miji to ba wani rai a doron ƙasa da ya isa ya zamo shamaki ga kasancewar ku ma'aurata, dan haka ki miƙa lamuran ki ga Allah ki dage da addu'a kina faɗa mishi buƙatun ki a sannu bisa hankali zai amsa miki domin kuwa shi baya bacci".

Da waɗannan kalaman Gwaggo Sa'adatu ta samu ta rarrashi Amrah har ta ji zuciyar ta ta ɗan mata sanyi amma kuma duk lokacin da ta tuna da wannan saƙon da ta gani a wayar Anwar ɗin sai ta ji gaban ta ya tsananta faɗuwa, sai dai kuma kamar yadda Gwaggo Sa'adatu ta bata shawara haka Amrah ta miƙa lamuran ta ga Allah ta miƙe tsaye da addu'a ba dare ba rana.

*****

A ɓangaren Anwar kuwa haka ya cigaba da ƙiran wayar Amrah amma shiru ba amsa, ana cikin haka ne Umar ya ɓullo daga hanyar gidan shi ya zo zai shiga gidan na su ya ga motar Anwar a fake a ƙofar gidan.

Ƙarasawa wajen motar ya yi tare da ƙwanƙwasa glass ɗin motar, abun mamaki mai Umar zai gani Anwar ya gani yana kuka ga hawaye shaɓe-shaɓe a idon kamar mace.

"Subhannallah Anwar lafiya kuwa mai ya same ka haka?".

Usman ya faÉ—a yana buÉ—e murfin motar Anwar É—in.

Kallon Umar Anwar ya yi sannan ya sanya hannu ya share hawayen idon shi tare da cewa.

"Umar dan Allah ka taimaka ka dubo mun a wana hali Amrah ta ke ciki, wallahi idan ban san a halin da take ba ba zan iya tafiya na bar ƙofar gidan nan ba, Umar dan Allah ka taimaka mun".

Anwar ya ƙarashe maganar cikin rawar murya.

Kallon shi Umar É—in ya yi cikin tsananin mamakin maganganun na shi kafin ya ce.

"Anwar mai ya faru da Amrah É—in?"

"Wallahi Umar ban san mai ya faru da ita ba, ni dai muna cikin hira kawai na ga ta fashe da kuka sannan ta tashi da gudu ta shige cikin gidan, ƙiran duniya na yiwa wayar ta amma ba ta ɗagawa, dan Allah ka taimaka ka gano mun ita ma idan ni na mata wani laifin wallahi zan je har ƙasa na durƙusa na bata haƙuri".

Umar yana ƙarasa jin abun da Anwar ɗin ya faɗa ya juya ya nufi cikin gidan na su dan gano halin da Amrah ɗin ta ke ciki.

A bakin murhu Umar ya tarar da Gwaggo Sa'adatu in da ya shiga tambayar ta ina Amrah É—in.

Ƙira Gwaggo Sa'adatu ta shiga ƙwalawa Amrah ɗin wadda ta ke kwance a ɗaki.

Jin ƙiran da Amrah ɗin ta ji Gwaggo Sa'adatu tana mata ne ya sanya ta fitowa daga cikin ɗakin sanye da hijabi tana cewa.

"Gwaggo gani".

Da kallo Umar ɗin ya bita domin kuwa shima sai a yau ya fuskanci ramar da Amrah ɗin ta yi kallon ta yake sama da ƙasa sannan ya juya ya dubi Gwaggo Sa'adatu tare da cewa

"Gwaggo, Amrah ta yi rashin lafiya ne hala ko?".

"Hmmm wallahi Umar Amrah ba ta yi rashin lafiya ba, kawai dai wata damuwa ta É—auka ta sanya a ranta marar tushe".

Gwaggo Sa'adatu ta faÉ—a tana ajiyar numfashi.

Juyawa Umar ya yi ya dubi Amrah sannan yace.

"Ki je Anwar yana waje yana jiran ki".

Hasbunnallah shine abun da Amrah É—in ta faÉ—a sannan ta juya ta fice da sauri ga idanu da suka yi jawur.

A bakin motar ta tarar da Anwar tsaye ya kafe ƙofar gidan su Amrah ɗin da ido.

Tana fitowa idon su ya sarƙe da na juna in da suka kafe juna da ido kowa da abun da yake ayyana wa a ran shi.

Sun É—auki tsawon lokaci a haka kafin a hankali Amrah ta fara takawa ta nufi wajen Anwar É—in cikin matsanancin tausayin shi ganin yadda idon shi suka yi jawur alamar kuka ya sha.

"Amrah me yasa ki ke son jefa zuciyata cikin damuwa?,me yasa Amrah?, Kin san irin damuwar da ki ka sanya zuciyata a ɗan wannan ƙanƙanin lokacin?, Amrah wallahi na damu sosai ganin halin da ki ka shiga ɗazu".

Amrah ta tsinkayi muryar Anwar yana magana cikin rawar murya irin ta waɗanda suka yi kuka suka ƙoshi.

"To ka yi haƙuri kaji".

Amrah ta faɗa cikin shagwaɓaɓɓiyar murya tare da sanya yatsan ta ɗaya a baki.

"Me yasa zan yi haƙurin to?".

Anwar ya faÉ—a shima yana kwaikwayon Muryar ta irin yadda ta yi magana.

"To me yasa ba zaka haƙura baaaaaaa?".

"Saboda baki sanar dani abun da ya saki kuka É—azu ba".

Shiru Amrah ta yi tana jin a ranta ba zata iya faÉ—a mishi damuwar ta ba, sai dai kuma wata zuciyar ta ce mata

" _Ki faɗa mishi kawai wataƙila ki samu ƙarin wani bayani daga gare shi, tun da wataƙila an cigaba da tura mishi message ɗin"_.

Daramm gaban Amrah ya tsinke ya faɗi jin abun da zuciyarta ta ta raya mata, a hankali ta ɗaga kan ta ta dube shi sannan ta fara labarta mishi labarin message ɗin da ta gani a wayar ta shi sannan ta ƙara da cewar.

"Yaya Anwar wallahi ina tsoron kar a yi galaba a kan mu, ina tsoron kar a raba zuciyoyin mu, Ya Anwar nasan kana sona da gaske kuma a ko ina zan bugi ƙirji na faɗi hakan, amma ban san meyasa ba tun da naga wannan message ɗin na ji hankali na ya tashi na kasa samun nutsuwa, na kasa danne zuciya ta, na rasa me yasa duk sanda na tuna da wannan message ɗin sai na ji gabana ya tsananta faɗuwa, ya Anwar wallahi ina tsoron ƴanmatan wannan zamanin".

Amrah ta ƙarashe maganar idanun ta suna cikowa da hawaye.

Wani matsanancin tausayin Amrah ɗin ne ya kama Anwar ɗin a lokaci guda kuma ya ji wani son ta ya ƙara mamaye shi, a hankali ya saki murmushi sannan ya dube ta yace.

"Amrah yanzu a kan ɗan wannan abun shine ki ka bi ki ka tayar da hankalin ki har kina ƙoƙarin ki sanya wa kan ki jinya, to ki sha kurimin ki ni Anwar mallakin ki ne kai kaɗai, ba wata ƴa da ta isa ta yi galaba a kai na,sannan kin daɗe da gina fada a cikin zuciyata wadda har abada ba za'a samu wata sarauniya da zata mallaki wannan fadar wadda ta wuce ki ko da kuwa ba kya numfashi a doron ƙasa, fada ta ki ce mallakin ki ne ko kusa da ita sai wanda ki ka ga dama zai je".

Duk da cewar Amrah ta ji daÉ—in kalaman Anwar É—in amma kuma sai ta É—ago ta ce.

"Ya Anwar dole hankali na ya tashi, ya Anwar wallahi na tsorata da yawa,amma kuma yanzu kalaman ka sun kore duk wani tsoro da ya ke a zuciyar ta wa, ya Anwar ina son ka sosai".

Amrah ta ƙarashe maganar tana rufe idon ta.

Murmushi Anwar ya yi sannan yace.

"Matsoraciya kawai ni kuma bana son ki".

Dukan wasa Amrah ta kaiwa Anwar ɗin tare da ɗan bubbuga ƙafa a ƙasa sannan suka yi sallama ya shiga motar shi ya tafi ita kuma ta shige gida.

*****

Yau ta kama ranar da su Amrah za su koma makaranta, tun asubah Amrah ta gama duk wani shirin da zata yi.

Malam Kabiru ma ya yi ƙoƙari in da ya siya mata ƴan abubuwan da ba za'a rasa ba duk kuwa da cewar Amrah ɗin ta ce mishi tana da komai, amma bai ta kan ta ba ya mata abun da ya kamata.

Sai da ya zaunar da ita a wannan karon ma ya mata nasiha mai ratsa zuciya kamar yadda ya yi a ranar farkon tafiyar ta.

A wannan karon ma Anwar ne ya zo ya É—auke ta ya mayar da ita, shima sai da ya mata siyayya ta gani a faÉ—a, amma bai bari mahaifin Amrah ya san da maganar siyayyar ba don ya san zai iya cewa a mayar mishi da kayan,ita kan ta Amrah bata san da maganar siyayyar ba sai da suka isa makaranta ta ga yana fito da wasu kayan daban ba wanda ta sani ba.

Suna cikin fitowa da kayan motar gidan su Afrah ta iso wajen ta yi parking a gefen ta Anwar.

Haka kawai Afrah ta ji wani irin abu ya taso tun daga maƙoshin ta ya tokare ta dalilin ganin Amrah da Anwar ɗin da ta yi a tsaye cikin shauƙin ƙauna.

Afrah bata yi auni ba sai jin wasu hawaye masu É—umi ta yi suna gangarowa ta kuncin ta.

BuÉ—e murfin motar ta yi a hankali ta fito daga cikin ta sannan ta fara takawa ta nufi wajen da su Amrah É—in su ke tsaye, zuciyar ta kamar zata fito.

*MANGA* ✍️
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_ .

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_💀☠️).

_Tsarawa/Rubutawa_

*© SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam, Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_.

*Free book*

-------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*017*
____________________________

Daf da Afrah ta kusa isa inda su Amrah su ke tsaye taji an sanya hannu an janye ta da ƙarfe har tana shirin kifawa da bakin ta.

Cikin sauri Afrah ta juyo da niyyar yin magana sannan taga wana mai ƙarfin halin ne ya dakatar da ita daga abun da tayi niyyar aikatawa.

Azrah ta gani tsaye ta kafeta da idanu cikin kallon ashe baki da hankali.

"Afrah mai kike shirin aikatawa haka?, Ko kin samu kuncewar kaine bamu sani ba?".

Cikin hawaye Afrah ta juya ta dubi inda su Amrah suke tsaye waÉ—anda basu lura da ita ba har zuwa yanzun dai suna tsaye a inda ya gansu,kana ganin su zaka tabbatar da cewa masoyane na gaskiya.

"Azrah mai yasa kika dakatar dani?, Azrah da kin barni naje na bayyana kaina a wajen Anwar kuma a gaban Amrah idan yaso ayi duk wacce za'a yi".

Afrah ta ƙarashe maganar cikin shesheƙar kuka ga wani suya da taji zuciyarta tana mata.

Wani irin kallo Azrah tabi Afrah da shi tun daga sama har ƙasa sannan tace.

"Tabbas na yarda Afrah soyayya ta rufe miki ido tun da gashi har kina shirin ɓallo mana ruwa,to wallahi tun wuri kar ki fara wannan gangancin kin ji na faɗa miki in dai ba so kike kiyi biyu babu ba,ba Anwar sannan Amrah kuma ta fara kallon ki a matsayin maci amana".

Sai a sannan Afrah ta fara dawowa hankalin ta in da ta sauƙe wani nannauyyan numfashi tare da furta.

"Amma yanzu Azra haka zan zuba ido kullum ina ganin su cikin son juna sannan kullum kamar ƙara musu ƙarfin soyayyar ake, nikuma ina nan ina ta fama da ciwon zuciya da dakon so".

Shiru Azra ta yi bata ce komai ba sannan ta ciro tissue a Jakarta ta miƙawa Afrah tace.

"Karɓi ki share hawayen ki,idan kin gama kukan mayi magana tun da naga yanzu kamar hankalin ki ya gushe".

Cikin sauri Afrah ta kamo hannun Azra sannan tace .

"A'a Azra dan Allah ki sanar dani wallahi ina cikin hankalina".

Ta faÉ—a tana sanya tissue É—in tare da share hawayen nata.

Kallon su Amrah Azra tayi waÉ—anda sai a sannan suke shirin yin sallama,juyowa tayi ta dubi Afrah wadda itama su Amrah É—in take kallo sannan tace.

"Afrah da alamu kin manta maganar da muka yi daku a gidan ku,karki manta fa na sanar dake cewar idan mun dawo school zamu yi magana,sannan ni na miki alƙawarin cewar zan nemo miki mafita ki yarda dani kamar yadda na faɗa wallahi Afrah na miki alƙawarin ciki nan da wasu kwanaki ƙalilan za'a shafe babin soyayyar Amrah da Anwar inda za'a kafa naku babin soyayyar,nan da wasu kwanaki ƙalilan za'a koma cewa Anwar ɗin Afrah inda zai tashi daga Anwar ɗin Amrah,amma kuma ki sani komai ba zai tafi yadda muke so sai da haɗin kanki keda Anisa da kuma Amira,sai dai nasan abu ne mai wahalar gaske ace Amira ta yarda da abun da zamu zo dashi ɗin,amma ba damuwa nasan ta yanda zan ɓullo mata".

"Wallahi Azra na miki alƙawarin ko mainene zan amince kuma zan baki haɗin kai matuƙar hakan zai kaine ga mallakar abun da nake so".

Wani murmushi Azra ta sake sannan ta kamo hannun Afrah ɗin suka fito daga inda suke laɓe ɗin,sannan suka nufi wajen da Amrah suke tsaye da Anwar suna sallama.

Da sallama ɗauke a bakin Azra ɗin suka ƙarasa wajen sannan ta dubi Amrah tace.

"A'a kaga masoyan asali,kaga laila da Majnun wadda soyayyar su ta zarce ta romio da Juliet,sannan ta kere ta Ram da Sita,irin wannan shan love haka,to gaskiya ya kamata a bar mana ita haka mu tafi Hostel domin kuwa muma mun yi missing É—in ta".

Azra ta faɗa suna ƙarasa tsayawa a wajen daga yanayin da tayi maganar zaka fahimci cewa da biyu ta yi maganar, amma kuma kasancewar Amrah zuciyarta ɗaya ce ya sanya bata kawo komai a ranta ba.

Murmushi Amrah tayi sannan tace.

"Ai yanzu kuwa zamu tafi dan daman tun ɗazu na dame shi da sai munyi sallama shikuma yaƙi sai jana yake da surutu".

"Gaskiya dai mu tafi, malam Anwar ya gida ko gaisawa ma bamu yi ba".

Cewar Azra É—in tana kallon cikin idon Anwar É—in.

A taƙaice ya amsa mata sannan ya juya ya dubi Amrah ya mata sallama ya shige motar shi ya ja ya tafi domin kuwa shi wallahi bai san maiyasa bai son waɗannan ƙawayen Amrah ɗin ba, musamman Azra mutum ɗaya yake so kuma yake ganin mutuncin ta ita ce Amira.

Ita kam Afrah tsananin mamakin Azra ɗin ne ya hanata cewa ko kanzil domin kuwa abun ya matuƙar bata mamaki.

Sosai Azra ta sakewa Amrah fuska harda tambayar ta ya ta baro su Gwaggo Sa'adatu abun da kuma bata taɓa yi ba.

Haka suka kama hanya suka wuce Hostel,kayan su kuma suka nema aka shigo musu dashi.

Tun daga ranar da suka dawo makaranta Azra bata sake nunawa Amrah wani abu mai kama da ƙyashi ba kullum cikin janta a jiki take wata irin kulawa ta musamman take nuna mata.

Tun abun yana bamu mamaki har ya dawo muka daina mamaki in da muka cigaba da harkokin mu.

Cikin ikon Allah yau aka kafe mana result É—in exam É—in da muka yi na First semester wanda Amrah ce ta yi overall,sannan Azara ta biyo bayan ta sai ni sai Afrah sai kuma Anisa.

Wannan abu ba ƙaramin daɗi ya mana ba inda muka sha murna sosai wani abun mamaki yadda Azra ta nuna tafi kowa taya Amrah murna shine babban abun da ya ɗaure mun kai,domin kuwa ni dai nasan cewa Azra tana da tsananin ƙyashin taga wani ya wuce ta abu amma sai gashi wai yau Azra an kafe result wata ta fita amma ko a jikin ta.

Abun da bamu sani ba shine ashe ta Ciki na ciki domin kuwa Azra inda zaka tsaga zuciyarta a wannan lokacin ba abun da zaka gani sai tsantsar wutar ƙiyayyar Amrah da ta sake ruruwa a cikin zuciyar ta.

Haka ta shiga toilet ta kulle kan ta ta sha kuka kamar ranta zai fita,ba wanda ya sani a tsakanin mu.

*****

Yau ta kama weekend ne inda tun safe muka fita karatu kasancewar ni da Amrah muke karatu tare, sai ya zamana mun bar Anisa da Afra da kuma Azra a É—akin.

Zaune suke a cikin ɗakin in da suke tattaunawa akan yadda zasu ɓullowa lamarin Anwar ɗin.

Azrah ce ta dubi su Anisa sannan tace.

"Afra ki ƙira Anwar a waya ki bayyana mishi abun da yake zuciyar ki a yanzu muji abun da zai ce".

Kallon Azra Afrah ta yi da niyyar yin magana tare da fito da ido waje,sai dai da sauri Anisa ta dakatar da ita tare da cewa.

"Wai Afrah wace irin matsoraciya ce?, Wallahi shiyasa wani lokacin ki ke bani haushi ni idan da nice da tunin an daÉ—e da wuce wannan zancen,da tunin wani zancen ake ba wannan ba,sai kace ba mace ba,haba dan Allah!".

Anisa ta faɗa cikin son ta ƙarfafawa Afra ɗin gwaiwa.

A hankali Afrah ta sanya hannu ta É—akko wayarta da take gefe sannan ta cire sim card É—in ciki ta sanya wani sannan ta nemo number É—in Anwar ta shiga dialing tana jin zuciyarta kamar zata fito waje saboda tsoron abun da zai je ya dawo.

Sai da ta yiwa Anwar ɗin ƙira uku ana huɗu tukunna ya ɗaga,bai yi magana ba ya yi shiru in da a hankali cikin sanyin murya ta furta.

"Hello!".

Daga ɗaya ɓangaren Anwar ya amsa bai jira abun da zata ce ba yace.

"Da wa nake magana pls?".

Shiru tayi bata amsa ba, jin da Anwar ya yi anyi shiru ne ya sanya shi katse wayar domin a tunanin shi mistake aka yi wajen ƙiran.

Sai dai ko dawowa daga zancen zucin da yake bai yi ba ya sake jin wani ƙiran ya shigo mishi cikin wayar, yi yayi kamar ya share sai kuma dai ya ɗaga.

A wannan karon duk wani ƙarfin gwaiwa Azra ta laluɓo ta azawa kan ta sannan ta furta.

"Anwar kana jina".

Ta faÉ—a tana ajiye wayar a tsakiyar su bayan ta sanya ta a handsfree.

"Ina jin ki wacece bangane ba?".

Anwar ya faÉ—a kamar an mishi dole.

"Anwar dan Allah ina son muyi magana idan ba damuwa mana?".

Shiru Anwar É—in yayi kamar ba zai ce wani abu ba kafin kuma daga bisani yace.

"Ok Ina jinki".

Ya faɗa a taƙaice.

"Anwar sunana Afrah shin ko zaka tuna wata number da kwanakin baya ake ta tura maka message?".

Shikam Anwar jin sunan da ta ambata ɗin ko kaɗan bai kawo a ranshi cewar wai Afrah ƙawar Amrah bace,domin kuwa bai taɓa sanyawa a ranshi cewar hakan zata iya faruwa ba,gashi kuma ko muryar ma bai ji ta mishi kama da wacce ya sani ba,duk kuwa da cewar sau biyu ne ko sau uku suka taɓa gaisawa.

"Anwar kayi shiru,ko baka ji abun da na faÉ—a bane?".

Ya tsinkayi muryar Afrah daga ɗaya ɓangaren ta faɗa.

"Eh na tuna"

"Amma kuma shine Anwar ko sau ɗaya baka taɓa mun reply ba?".

Shi maganar ma dariya ta bashi inda har sai da ya dara.

Jin muryar Anwar É—in yana mata dariya ne ya sanya ta kalli su Azra idanun ta suna cikowa da hawaye,sannan cikin rawar murya ta furta.

"Anwar dariya ma na baka?".

Sai da yayi dariya mai isar shi kafin yace.

"Sosaima wallahi, saboda gaba ɗaya maganar taki ne naji ta wani bambarakwai,kawai saboda nine wanda ban san ciwon kaina ba daga ganin message a wayata sai na hau yin reply,to an gayamiki Anwar irin mazan da kika saba turawa message ne marrasa aji irin ki, tukunna ma mai yasa kika ƙirani?".

Hawayen da Afrah ta ke riƙewa ne suka shiga sintiri ta kan kuncin ta,tun da take ba'a taɓa faɗa mata maganar da ta ƙona mata rai irin wannan ba,amma bakomai ko da zai zage ta yau dai zata bayyana mishi sirrin zuciyarta.

"Amma Anwar ina so ka sani duk wanda zai so ka to ai da alkhairi ya nufeka,sannan soyayya bata taɓa zama ƙiyayya, wallahi Anwar ina son ka kuma da gaskiya,ban taɓa ganin wani ɗa namiji da naji son shi irin yadda naji naka ba, pls Anwar dan Allah ka so ni".

Shikam Anwar mamaki ne ya mamaye shi lokaci guda jin wai Æ´a macece take requesting soyayya a wajen namiji,lalle duniya ta lalace.

"Uhmmm wa kika ce ma sunan ki?".

"Afrah"

Ta maimaita a hankali.

"Yawwa Afrah dan Allah zan roƙe ki da girman Allah ki fita a rayuwata domin kuwa ni da kika gani ina da mata,dan haka tun muna cikin ganin darajar juna ki fita a rayuwata sannan kar ki ƙara garajen turamun message ko kuma ki ƙirani saboda ranar na farko kin sanya matata a cikin damuwa dan haka idan kika ƙara yin na biyu wallahi zan wulaƙanta ki duk kuwa da cewar wulƙanci ba ɗabi'ata bace amma kuma idan kika kaini bango zaki sha mamaki dan akan matata Amrah ba abun da ba zan iya ba,kuskuren da zaki aikata wanda zai zamar miki damuwa a rayuwar ki shine sake ƙiran wayata ko kuma ki turamun message".

Anwar yana kaiwa nan a maganar shi ya katse wayar sannan ya danna number É—in Afrah É—in a blacklist.

Wani mahaukacin kuka Afrah ta fashe dashi tare da dafe ƙirjin ta da yake mata suya kamar wuta.

"Innalillahi wa'innailaihi rajiun Azra kunji abun da yace!, Azra ni daman nasan wallahi Anwar ba zai taɓa sona ba matuƙar Amrah tana raye, Azra mutuwar zan yi wallahi matuƙar ban mallaki Anwar ba, Azra dan Allah ku taimaka mun".

Afrah ta faÉ—a tana kuka wiwi harda majina.

Sosai Anisa da Azra suka ji tausayin Afrah ɗin da ƙyar Azra suka rarrashe ta ta sassauta kukan nata, sannan Azra tace.

"Afrah ki daina kuka in sha Allah Anwar zai dawo gareki kuma zaki mallake shi,kuma Amrah tana cikin duniyar nan,sannan in sha Allah ke ba zaki taɓa shiga damuwa ba sai dai Amrah ta shiga, ina mai tabbatar miki nan da wasu kwanaki Anwar zai zama bashi da wata wadda ya tsana kamar Amrah, ke in taƙaice miki labari ma sai Anwar ya dawo ko sunan Amrah baya buƙatar ya ji an ambata balle ya ga fuskarta".

Cikin sauri muka É—ago muka kalli Azra ni da Anisa cikin matsanancin mamakin maganganun nata.

"Azra ta yaya hakan zata kasance?, Ina tunanin a duniya ba abun da zai sa Anwar ya tsani Amrah koda kuwa asiri aka musu".
Wani murmushi Azra ta sake sannan tace.

"Sanin hakan ne ma ya sanya ba zamu taɓa amfani da asiri wajen yi musu farraƙu ba domin kuwa ɓatawa kan mu lokaci kawai zamu yi saboda ba zai yi tasiri ba, amma wannan hanyar da zamu bi tabbas hanya ce da zamu yi nasara".

"To fah! Azra wannan wace irin hanya ce?".

Su Afrah suka tambayi Azra É—in.

"Karki damu zan sanar daku in sha Allah yanzu dai mu bar maganar tun da kinga lokacin dawowar su daga karatu ya kusa, sannan Afrah ina son ki mannawa Anwar ki fita a harkar shi kar ki ƙara neman shi,bayan mun samu nasara a abun da muka sa a gaba sai kuma mu ɗora daga inda muka tsaya".

Wani farin ciki ne ya kama Afra ji take kamar ta mallaki Anwar ta gama.

*MANGA* ✍️.
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_💀☠️) .

_Tsarawa/Rubutawa_

*© SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA* : _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam, Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_ .

*Free book*

---------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*018*
______________________________

Sai dai abun da su Afrah basu sani ba shine duk wani abu da suke shiryawa ina sane da su,domin kuwa yanzu haka ma lokacin da suke waɗannan zantukan ina tsaye a bakin ƙofa ina jin su,a lokacin na dawo zan ɗaukar mana wani littafi kawai naji abun da suke tattaunawa ɗin.

Fasa shiga cikin É—akin namu na yi inda na tsaya na gama saurarar abun da suke faÉ—a É—in.

Tsoro,fargaba,mamaki ne suka dirar mun a lokaci guda,jikina idan banda rawa ba abun da yake yi.

Sai da nagama jin komai kafin na juya na koma wajen karatun namu ba tare da na shiga É—akin ba.

Lokacin da nakoma wajen Amrah ta lura da yanayi na ba yadda na bar wajen ba,hakan ya sanya fara tambaya ta

"Amira lafiya kuwa naga yanayin ki ya sanja ba kamar yadda ki ka bar nan wajen ba?".

Murmushin ƙarfin hali na ƙaƙaro sannan nace.

"Bakomai Amrah wani abu kika gani?".

Kallo na Amrah ta yi irin kallon ban yarda ba sannan tace.

"Haba Amira ya zaki cemun bakomai bayan duk wanda ya ganki ya san yanayin ki ya sanja,kuma da alama ma kamar kuka kika yi?".

Rasa abun da zancewa Amrah na yi inda wata zuciyar ta bani shawarar na sanar da ita kawai abun da naji,wata zuciyar kuma tace kul Amira kar ki fara ki bari muga iya gudun ruwan su.

Da wannan shawarar na yi amfani inda na dube ta sannan nace.

"Da gaske Amrah bakomai ki yarda dani ke kinsan da akwai abun da yake damuna da na sanar da ke,tun da kinsan bana ɓoye miki komai,kawai dai kaina ne ya ɗan fara mun ciwo".

Ji na kawai Amrah ta yi amma alamun ta ya nuna bata yarda ba,kallo na tayi sannan tace.

"Ina littafin da kike je É—akko mana to?".

Sai a sannan Amira ta tuna da abun da taje yi Hostel É—in, É—an sosa kai ta yi alamar rashin gaskiya sannan tace.

"Ai ban ma ƙarasa Hostel ɗin ba saboda ciwon kan yanzu mu ce miki zan yi mu koma kawai".

Na ƙarashe maganar ina miƙewa tsaye domin bana son Amrah ta cikani da tambaya gudun kar a zo a samu matsala ta fahimci halin da nake ciki.

Fuskantar da Amrah ta yi cewar bana son maganar ya sanya ta miƙe tsaye tare da cemun mu wuce,amma ba wai don ta gamsu da abun da nace ɗin ba.

Lokacin da muka Hostel mun tarar da su Afrah har sun shirya mana abinci sannan suka tare mu fuska faran-faran.

Wani ƙullutun baƙin ciki ne ya taso ya tokare mun zuciyata a lokacin da na tuna da maganganun da naji su suna yi ɗazun, fisabillillahi kamar ba sune suke shirin tarwatsa farin cikin Amrah ba amma gashi yanzu suna nuna mata sun fi kowa sonta,alhalin kuma idan za'a tona abun da yake a zuciyar su ba za'a ga da kyau ba,lalle ɗan Adam ba abun yarda bane,tabbas su Azra sun cika masu fuska biyu,na faɗa a zuciyata ina kwanciya a kan gado,tare da juya musu baya domin kuwa a yadda nake jin zuciyata idan har zan zauna na cigaba da kallon su to tabbas za'a samu matsala zan iya zagin uwar su da uban su wanda kuma ba zan so hakan ba domin kuwa ba yanzu nake son na tona musu asiri ba. Sai dai rashin sani yafi dare duhu domin kuwa da nasan abun da zai faru a gaba da nayi gaggawar tonawa munafukan asiri Amrah ta san da su wa take zaune, wannan shine babban kuskuren dana yi wanda har ya sanya su Azra suka yi galaba akan Amrah kuma wanda har yanzu ina danasanin aikata shi.

Muryar Azra da naji tana mun magana akan na tashi muci abinci ita ta dawo dani daga tunanin da na tafi É—in.

Da sauri na runtse idona alamar bacci nake ina jin su suna ta mun magana amma na manna musu,kasancewar sun san halina da saurin bacci ya sanya suka yi tunanin ko nayi bacci ne.

Tun daga wannan lokacin na daina sakewa su Azra fuska domin kuwa gaba É—aya haushin su nake ji, su kuma sun yi yin duniya na sanar da su damuwa ta amma sai dai nace musu Bakomai.

Lokaci guda na zabge na rame duk na zama wata iri dani gashi ko hira na daina sakewa muyi dasu Azra, Amrah ce kawai ban sanja mata ba yadda muke mu'amalar mu ta da to haka muke yanzun ma.

Sai dai fa na sawa su Azra ido sosai domin kuwa nayi alƙawarin sai na tarwatsa shirin su.

Kasancewar Azra tana da mugun wayo ya sanya ta fara zargin ko na gano abin da suke shirin aikatawa ne ya sanya na sanja musu.

Sai dai abun da ban sani ba shine yadda na sawa su Azra ido ashe itama Azra haka ta sanya mun ido sosai, duk wani takuna tana ankare dani.

Wata ranar lahadi da ba zan manta ba, mun fita wajen saloon nida Amrah, mun gama komai lafiya har muka tsaya a kasuwa muka yi siyayya sannan muka kamo hanyar dawowa Hostel a lokacin ma Anwar ne ya kawo mu.

Tafe muke a cikin motar in da Anwar da Amrah suke hira sosai,duk da sun so su sanya ni a cikin hirar tasu amma hakan ya gagara domin kuwa nikam gaba É—aya hankali na ma baya kan su.

Anwar ne yake tambayar Amrah shin ko lafiya nake kuwa.

Amrah amsa ta bashi inda take ce mishi wallahi itama ta kasa gane meye yake damuna cikin Æ´an kwanaki biyun nan.

Tambaya ta Anwar É—in ya shiga yi amma ba wata amsa sabuwa.

Duk wata tambayar duniya sun mun amma amsar dai itace bakomai, ganin da suka yi bani da niyya ya sanya suka ƙyale ni.

A haka muka iso makaranta inda na fita daga cikin motar bayan na yiwa Anwar sallama ciki-ciki.

A mota na ƙyale Anwar da Amrah suna hira inda nikuma na nufo Hostel da kayan da muka siyo.

Har na kama handle ɗin ƙofar zan murɗa na buɗe kawai naji maganganun su Azra wanda suka kusa sanya ni sumewa a wajen.

Muryar Azra naji tana cewa.

"Kamar yadda na sanar daku a baya cewar akwai hanyar da zamu bi dan mu tarwatsa alaƙar da take tsakanin Anwar da Amrah cikin sauƙi, shine kun ga wannan wayar ta daɗe a ajiye a jakata ina jiran zuwan ranar amfanin ta,kuma Alhamdulillahi gashi ya zo".

Ɗan shiru tayi sannan ta dubi Afrah ta cigaba da magana tare da ɗakko wata ƴar ƙaramar Camera.

"Wannan Camera É—in da kuke gani zamu sanya ta a toilet, kun san cewar Amrah itace sarkin yin wankan dare,a rana tana wanka sau huÉ—u ne, to zamu daidaice lokacin da zata shiga toilet sai mu sanya wannan Camera É—in,inda zata mana video É—in Amrah tsirara daga nan kuma sauran bayanan zan muku shi daga baya".

Saurin zaro ido waje Afrah ta yi duk da cewar tana son a raba Anwar da Amrah amma wannan karon sai taji ba zata iya goyon bayan a ɗauki videon tsaraicin Amrah ba,da ƙyar ta ƙaƙalo kuzari sannan ta dubi Azra tace.

"Azra nikam gaskiya a sanja shawara domin kuwa wannan abun ai da cutarwa sosai a cikin sa,ni wallahi ba zan so a ɗauki videon tsaraicin ƴaruwata mace ba,ke ko maƙiyiyata ce ba zan so ba,balle Amrah yadda muke da ita, dan Allah mu sake wata hanyar dan.......".

"Idan har ba wannan hanyar ba to ki shirya haƙura da Anwar domin kuwa in dai baki bi wannan hanyar ba,to ba wata hanya da zamu bi domin ki mallaki Anwar ,ruwan ki ne ki amince ruwan ki ne ki ƙi amincewa,sai dai kuma rashin amincewar ki yana nufin kin rasa Anwar har abada, domin kuwa ba zaki taɓa mallakar shi ba".

Itama Anisa take ta dubi Afra tace.

"Ni a ganina Afra wannan itace kawai mafita idan har kina son ki mallaki Anwar,amma kuma idan kin shirya rasa shi to shikennan ba zamu miki dole ba sai mu ƙyale ki,daman saboda ke zamu yi komai domin mallakar farin cikin ki".

Shiru Afrah ta yi tana nazari ita kam gaskiya zuciyarta bata aminta da wannan shawarar ba.

Kallon Azra tayi sannan tace.

"To Amma mai zamu da videon tsaraicin Amrah É—in?".

"Sanin abun da zamu yi dashi ba wani abun damuwa bane kede kawai ki amince da abun da na ce miki, koma meye daga baya zaki ji".

Innalillahi wa'innailaihi rajiun shine abun da Afrah ta shiga furtawa,wannan shi ake ƙira ga ƙoshi ga kwanan yunwa. Tabbas tana son Anwar amma kuma wannan hanyar ba hanya bace wadda ta dace ba, domin kuwa babu komai a cikin ta sai zallar tozarci,anya kuwa zata amince?. Afrah ta tambayi kanta, gaskiya abun da kamar wuya domin wallahi zunubin da yawa, haƙƙin Amrah ba zai taɓa barin su ba idan har suka tozarta sannan Allah ma ba zai ƙyale su ba,tun daga duniya za su fara ganin sakamako.

Nikuwa da nake tsaye a bakin ƙofa,take ƙafafuwa na suka shiga wata irin karkarwa ban san sanda na zube a wajen ba wani irin gumi ya shiga tsatstsafowa ta kowanne sashi na jiki na,ashe Azra bata da imani har haka?, Ashe Azra zuciyarta baƙar zuciya ce?, Ashe Azra azzaluma ce?, Ashe Azra bata kishin ƴar uwar ta mace?, Yanzu videon tsaraicin ƴar uwar ta mace take son ɗauka?, To mai zata yi dashi, innalillahi wa'innailaihi rajiun wannan wace irin rayuwa ce haka,mai Amrah ta tarewa Azra har haka?.

Tambayoyin da nashiga jerowa kaina Kennan sai dai bani da wanda zai bani amsar su.

Wasu hawaye masu matuƙar zafi ne suka shiga kwaranyowa ta kumatun na, a take wani irin zazzafan zazzaɓi ya rufe ni, wata irin tsanar Azra ce ta kamani take nayi danasanin saninta da nayi.

Saurin ɗan ƙarfin da ya rage mun na tattaro sannan na fara ƙoƙarin miƙewa tsaye duk kuwa da wata irin juya da take ƙoƙarin kayar dani.

A zafafe na ƙarasa miƙewa sannan na kama handle ɗin ƙofar da niyyar buɗewa naje na ci musu mutunci, sannan na nuna musu cewar nasan duk abun da suke shirin aikatawa.

"Amira!".

Muryar Amrah ta dira a dodon kunnuwana hakan ya sanyani dakatawa daga shirin shiga É—akin da nayi.

*Assalamualaikum dan Allah kuyi haƙuri, nayi niyyar yi muku typing da yawa to amma hakan bai* *samu ba sakamakon an kwantar da ƙanwata a asibiti, ɗazu da azahar, wannan typing ɗin ma tun safe na yi shi shiyasa, amma da yau kam ma ba zaku samu posting ba,dan haka kuyi haƙuri kuyi manage har zuwa lokacin da za'a sallamo ta, kafin ta samu lafiya,ina fatan zaku mun* *uzuri* 👏🏻👏🏻.

*MANGA* ✍️.
_Comment_ ,
_share_
_fisabillillahi_

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_ 💀☠️).

_Tsarawa/Rubutawa_

*© SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_

*Free book*

---------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*019*
_____________________________

Takowa Amrah tayi cikin sauri har ta ƙaraso in da nake tsaye ɗin,sannan ta sanya hannu ta juyo da fuska ta muka kalli juna cikin matsanancin mamaki Amrah ta furta.

"Amira kuka!, Amira kuka kike mai ya sameki?".

Duk yadda na so na daidaita kaina amma abun ya gagara inda a maimakon na bawa Amrah amsar tambayar da ta mun ɗin,kawai sai gani tayi na rungumeta tare da fashewa da wani irin kuka mai taɓa zuciya.

"Innalillahi wa'innailaihi rajiun, Amira wai meye haka dan Allah?, Amira ko wanine ya mutu ban sani ba?, Dan Allah ki sanar dani".

Amrah ta faÉ—a cikin matsanancin tashin hankali a lokacin itama har idanun ta sun fara cikowa da hawaye saboda yadda nake rubzar kukan duk rashin tausayin mutum sai ya ji tausayi na domin kuwa zaku yi tunanin cewar ko uwata ce ko ubana wani ya mutu.

Ƙofar ɗakin namu muka ga an buɗe inda muka ga su Azra sun fito daga cikin ɗakin alamar kukan da nake ɗin ne ya sanya su fitowa.

"Subhannallah Amira lafiya kuwa? Amrah mai yasameta haka?".

Azra ta faɗa tana ƙoƙarin kai hannun ta jikina dan ta taɓa ni.

Ai da sauri na É—ago da fuskata da niyyar balbale ta da bala'i, sai dai mai kallon da naga tana jifana dashi ne ya dakatar dani daga abin da nayi niyyar yi É—in, domin kuwa wani irin kallo mai cike da alamar gargaÉ—i Azra É—in ta shiga aika mun,idanun ta kaÉ—ai na kalli na fahimci inda ta dosa da kuma abun da take nufi,watau Amira kar ki fara wannan gangancin domin kuwa zaki yi dana sani.

Wannan kallon da naga Azra tana mun ba ƙaramin tayar mun da hankali yayi ba,take jikina yayi sanyi inda na janye jikina daga na Amrah sannan na shige cikin ɗakin ina tafiya kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki,na bar su Amrah tsaye baki sake.

Sai dai ina shiga cikin É—akin Amrah ta biyo bayana da sauri tana cigaba da jaifamun tambayoyin da tamun É—azun amma shiru nikam ba amsa.

Sai dai a raina na ƙuduri niyyar in sha Allah duk yadda zan yi sai nayi domin na tarwatsa shirin su Afrah ɗin,sannan zan samu Azra ko gobe ne mu keɓe da ita na mata nasiha ko Allah zai sa taji.

Sai dai washegari tun da asubar fari aka ƙirani a gida inda ake mun neman gaggawa sakamakon jikin mahaifina da ya tsananta har an kaishi asibiti.

Cikin tashin hankali na tashi na shirya sannan na sanar da su Amrah abin da yake faruwa,sai dai sun buƙaci na bari su shirya mu tafi tare,ban so su Afrah suka bini ba,amma ba yadda zan yi domin kuwa ina yin wani abu ƙalilan Amrah zata iya fahimtar wani abu shiyasa na ƙyale su muka tafi tare, inda bayan sun duba shi suka dawo makaranta nikuma suka barni a can.

Allah sarki Amrah ashe wannan dawowar da suka yi ita ce mafarin komai.

Bayan tafiya ta da kwana biyu abubuwa sun faru waÉ—anda ban san wasu ba,wasu kuma na samu labarin su daga wajen wasu abokanan karatun mu.

Yau ta kama Friday da wuri su Amrah suka tashi a lecture tafe suke su huÉ—u a harabar makarantar,idan ka kalle su sai sun baka sha'awa domin kuwa zaka iya rantsewa zuciya É—aya suke zaune da juna sai da ta ciki na ciki.

A dai-dai wajen roundabout É—in da zaka nufi hanyar hostel suka ci karo da wata Æ´ar class É—in mu in da tana hango su ta fara musu kirari tun daga nesa.

"Kaga taurari guda biyar a ganku a barku tun daga nesa kuke haskawa,amma kuma gaskiya yau akwai abu É—aya da babu a cikin ku".

"ÆŠayar tauraruwar ce babu, watau Amira".

Anisa ta faÉ—a da sauri.

"Tabbas!, Amma ina kuka baro ta".

"Hmmm wallahi Fiddausi mahaifin ta ne ba lafiya tana gida an kwantar dashi a asibiti".

Amrah ta faÉ—a fuskarta da alamun damuwa.

"Eyya Ubangiji Allah ya bashi lafiya".

Fiddausi ta faÉ—a cikin jimami sannan ta mana sallama ta wuce.

Da Ameen suka amsa mata sannan suka wuce suka nufi Hostel.

*****

A ɓangaren na kuwa a can asibiti yau mun tashi da matsanancin tashin hankali domin kuwa yau jikin mahaifina ya tsananta likitoci ne kawai suke kaiwa da komowa a kan shi.

Sai dai abin da Allah ya nufa ba makawa sai ya faru,ashe jinyar mahaifina bata tashi bace,inda ba'a É—auki tsawon lokaci ba rai yayi halin shi, Allah ya yiwa mahaifina rasuwa.

Wannan rasuwar ba ƙaramin girgiza ni tayi ba dani da sauran ƴan gidan mu musamman ma ni domin kuwa har aka kai mahaifina maƙabarta aka dawo dashi ban san inda kaina yake ba.

Bansan yadda aka yi su Amrah suka samu labarin rasuwar mahaifin nawa ba,sai ganin su nayi gaba É—ayan su a daren ranar har a lokacin ma ban farfaÉ—o ba, sai da na kwana ban san a wace duniyar nake ba kafin bayan gari ya waye na farfaÉ—o inda na tarar da su Amrah da Afrah a kaina suna mun firfita.

Sannu suka mun gaba É—ayan su,amma ban samu damar amasawa ba sai ido da na bisu dashi.

Kwanan su Amrah biyu a gidan mu kafin a ranar na uku suka kama hanya suka koma makaranta bayan sun raka mahaifina da addu'ar samun rahamar Allah.

Tun daga bakin gate ɗin makarantar mu Amrah ta fara ganin wani baƙon al'amari yana faruwa domin kuwa duk inda suka wuce sai taga ɗalibai ana binta da kallo wasu kuwa har nunata suke wanda ta rasa gane dalilin hakan.

A haka dai suka cigaba da tafiya har suka doshi hanyar Hostel, sai dai abun mamaki shine suna isowa daf da wata dabar wasu ƴan mata da samari,kunnuwan Amrah suka jiyo mata wata kalma da tayi matuƙar bata mamaki.

"Kun ganta waccan ta tsakiyar ita ce ai,ku ganta kamar ta Allah ashe munafuka ce kullum cikin hijab ashe na ƙarya ne".

Wani saurayi ya faÉ—a yana nuna saitin inda Amrah É—in take.

"To kai daman Hamza ai kawai ka kalli masu sanya hijab ɗin nan ka ƙyale su,domin kuwa duk munafukai ne,cikin su fal yake da iskanci".

Da sauri Amrah ta kai duban ta wajen samarin sannan ta dubi su Azra a tunanin ta ba da ita suke maganar ba, sai dai tana kallon su taga ita suke nunawa.

"Azra kun ji abun da waÉ—an can suke faÉ—a kuwa?".

"Wallahi na jisu amma share su neman maganane kawai".

Azra ta faÉ—a cikin son ta kawar da zancen.

Haka dai suka ƙarasa Hostel inda suna shiga suka ci karo da Fiddausi ta nufo su hankali tashe, tare da kama hannun Amrah tace.

"Amrah Dan girman Allah idan kin ƙarasa shiga cikin Hostel duk wanda kika ji ya miki wata maganar banza karki saurari kowa".

"Fiddausi lafiya kuwa mai yake faruwa?".

Amrah ta faÉ—a fuska cike da mamaki.

"Bakomai kede kawai kiyi abun da nace".

Fiddausi tana kaiwa nan a zancen nata ta wuce su Amrah da sauri ta bar wajen.

Shiru Amrah tayi cike da mamakin waÉ—annan abubuwan.

*****

A can gidan mu kuwa,cike gidan yake da mutane har a sannan gidan kamar yau aka yi mutuwar. Kun san yadda gidan mutuwa yake a wannan zamanin wanda ya mutu shine dai ya mutu sai kuma Æ´an uwan shi na jiki wanda mutuwar ta shafe su. To haka take a gidan namu ma inda wasu cin abinci ne ya kai su, wasu kuwa gulma ce ta kai su,kowa dai da abin da ya kai shi.

"Ke ƙawata kinga wani video da akayi posting ɗazu a TikTok".

Wata mata ta faÉ—a tana nunawa ta gefen ta wayar tata.

"Innalillahi wa'innailaihi rajiun ƙawata wannan ai yarinyar da suka kwana a gidan nan ne jiya,ƙawar Amira".

Matar ta faɗa tana ƙasa-ƙasa da murya wai gudun kar na jita,sai dai bata san ta makaro ba domin kuwa caraf naji dirar maganar tata a kunnuwan na.

Haka kawai naji gaba ya shiga bugawa,inda naji a raina ina son naji akan abun da suke maganar.

A hankali na tashi sannan na nufi inda suke zaune É—in na zauna a gefen su.

Su kuwa ganin na dawo kusa da su sai suka fara ƙoƙarin sauya zancen da suke ɗin, ni kuwa hannu na sanya na ɗauki wayar da take kan cinyar matar sannan na cemata cikin dasasshiyar murya ta wacce kana ji kasan ta gaji da kuka.

"Nuna mun videon da kuke magana a kai".

Haka kawai matar taji na mata wani irin ƙwarjini take ta karɓi wayar ta shiga TikTok ɗin sannan ta kunna videon.

Fuskar Amrah ce ta bayyana a jikin videon,inda ta shiga toilet sanye da towel sannan ta cire shi ta ajiye a gefe sai gata tsirara haihuwar uwar ta tana wanka.

Wata irin sarawa kaina yayi take kuma wayar ta suɓuce mun a hannu inda na fara ganin dishi-dishi sai kuma cak numfashi na ya datse inda na zube a wajen a sume.

Nan fa mutane aka yo caaaaa a kaina inda kowa ya shiga faÉ—in albarkacin bakin shi, mahaifiya ta ce ta nufo ni cikin tsananin tashin hankali tana kuka.

Waɗanda basu san dalilin sumewar tawa ba,cewa suka fara yi na zama marar tawakkali domin kuwa i zuwa yanzu ya kamata ace na karɓi wannan ƙaddarar da ta same mu nayi haƙuri tun da shikam mamaci ya riga da ya mutu. Haka dai kowa ya shiga faɗin ta bakin sa.

Bayan wani lokaci aka yayyafa mun ruwa na farfaÉ—o, ina farfaÉ—owa da sunan Amrah na farfaÉ—o a baki na,inda na kai dubana wajen waÉ—annan matan sai dai wayam inda suke zaune É—in babu su ba alamar su ashe wai tun lokacin da suka ga na sume É—in suka cika wandon su da iska.

"Ina wayata Umma".

Shine abun da na faÉ—a ina kallon inda Umma na take tsaye.

Kallo na Umman nawa ta shiga yi cikin tsananin mamakin abun da taji nace É—in.

Ni kuwa ganin irin kallon da Umman take mun sannan na lura bata da niyyar bani wayar tawa ya sanya na tashi da gudu na tsallake duk tarin mutanen da suke zaune a wajen sannan na shige cikin ɗakina inda na tarar da wayar tawa a yashe a kan gado. Da sauri na ɗakko ta sannan na shiga dialing number ɗin Amrah sai dai no answer, na mata ƙira ya kai goma a jere amma ba'a ɗagawa, nan fa hankalin na ya ƙara dugunzuma, wayar Azra na shiga ƙira inda ina mata bugu ɗaya ta ɗaga.

"Shegiya munafuka,makira algunguma ina Amrah?".

Duk da bana gaban ta amma sai da na fahimci cewa taji zafin zagin da na mata É—in. Ban damu ba inda na cigaba da magana.

"Wallahi Azra ban taɓa sanin cewa ke azzaluma bace sai a yau,tabbas kin cika shaiɗaniya amma sai dai ki sani wallahi baki yi nasara a kan Amrah ba, domin kuwa sai na tona miki asiri ki jira dawowa ta makaranta ki gani tsinnanniya kawai".

"Sanin hakan da nayi Amira shiyasa na miki babban tanadi,ki sani cewa kin makaro domin kuwa ni Azra murucin kan dutse ce ban fito ba sai da na shirya, Amira ina nan ina jiran ki dan Allah ki tona mun asiri kinji".

Azra tana kaiwa nan a zancen ta ta datse wayar ta bar ni da baki a sake.

Kan kuce kwabo gidan mutuwa ya zama dandalin zancen Amrah domin kuwa cikin ƙanƙanin lokaci aka bi duk wata kafa ta sada zumunta aka yaɗa wannan videon,kafin wani lokaci video ya samu viewers sama da mutum dubu ɗari biyar a TikTok ban da facebook da sauran kafafen soshiyal media ɗin.

Wani abun da zai baku mamaki da kuma zai É—aure muku kai shine duk videon da aka sanya É—in a lokaci guda aka sake su,sannan gaba É—aya sunan Amrah ne akan duk account É—in da aka É—ora videon wannan ya tabbatarwa da mutane cewar Amrah É—in ce da kanta tayi posting videon tsaraicin nata.

Lokacin da labarin wannan videon ya riski Amrah ƙaryatawa tayi sai da ta ganshi ido da ido kafin fa hankalin ta ya tashi inda ta shiga suma tana farfaɗowa,domin kuwa ta suma ya kai sau biyar,ga wasu irin zantuka da ta dinga yi marrassa kan gado kana jin su zaka ce ta zauce.

Duk wanda yake wajen Amrah a wannan lokacin sai da ta bashi tausayi hatta ita kanta Afrah sai da taji tausayin Amrah ɗin take wani irin dana sani ya rufe ta,inda ta shiga rusa kuka itama kamar an aiko mata da saƙon mutuwa.

Wani abin mamaki shine sune Azra sun fi uban kowa shiga damuwa domin kuwa idan ka kalli Afra ta kalli Azra ka kalli Anisa sai ka kasa tantance wacce tafi wani shiga damuwa.

Kafin wayewar gari video ya samu sama da one million viewers likers kuwa ba zasu ƙirgu ba, haka cikin makarantar su Amrah duk inda ka wuce ba zancen da ake wanda ya wuce na videon tsaraicin Amrah ɗin.

*MANGA* ✍️.
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_ .

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_ 💀☠️).

_Tsarawa/Rubutawa_

*© SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam, Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillah_.

*Free book*

---------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*020*
______________________________

"Innalillahi wa'innailaihi rajiun na shiga uku na jama'a ku sanar dani cewa mafarki nake, Amira dan Allah ku cemin mafarki nake ba gaskiya bane abun da na kalla, Wayyo Allah na hasbunnallahu wa ni'imal wakil, Ubangiji Allah kayi gaggawar É—aukar rayuwata tun kafin na gano cewa ba mafarki nake ba".

Amrah ta faÉ—a wadda farfaÉ—owar ta kennan daga suma na shida da tayi Kennan.

Saurin riƙo ta Afra tayi sannan ta sanya hannu ta toshe mata baki,tare da fara magana cikin kuka.

"Amrah dan Allah kiyi haƙuri ki daina kuka, wadannan maganganun duk ba su kamace ki ba a wannan halin da kike ciki, Amrah addu'a ita ya kamata kiyi".

Da sauri Amrah ta É—ago idanuwanta da suka kumbura suka sanja kalla saboda tsabar kuka sannan tace.

"Afra haƙuri!, Haƙuri fa kike ambatar nayi, Afrah da gaske ne videon tsaraicina ne yake trending a social media?", Dan Allah kuyi gaggawar sanar dani".

Anisa ce ta kamo hannun ta wadda itama hawayen take amma na munafurci sannan tace.

"Amrah ki ɗauki hakan a matsayin ƙaddarar rayuwar ki, Amrah ki sani kowane bawa da kalan tashi ƙaddarar kuma ita ƙaddara ba a iya kauce mata,kiyi addu'a kawai Allah ya baki ikon cinye wannan jarrabawar".

"Innalillahi wa'innailaihi rajiun Kennan ya tabbata da gaske ni ce nake yawo tsirara a social media, idan kuwa har haka ne to wallahi banga amfanin rayuwa ta a doron ƙasa ba,gwanda na mutu kowa ya huta".

Amrah ta ƙarashe maganar tana gwara kanta da jikin gadon da suke zaune ɗin take kuwa kan nata ya fashe sai ga jini ya fara ɓulɓulowa daga goshin ta, amma duk da haka Amrah ko a jikin ƙoƙari take kawai taga ta ƙara fasa kanta.

Cikin hanzari Azrah ta miƙe tare da ciro bandage a cikin side drawer ɗin su,kasancewar suna da first Aid Box a ɗakin inda suke ajiye ƴan abubuwan da ba za'a rasa ba,irin su allurai da wasu magungunan haka saboda gudun abun emergency ya faru.

Ƙoƙarin rike Amrah ta fara domin ta samu damar tsayar da jinin da yake zubomata ɗin,amma ina Amrah gaba ɗaya ta fice daga hayyacin ta, lokaci guda ta fara wasu irin buge-buge kamar mai wasu aljanu,kanta kuwa bata daina bugashi a jikin gadon ba,da ƙyar su Afrah suka haɗu suka danne ta sannan Azra ta samu ta naɗe mata kan nata da bandage ɗin tare da yi mata allurar kashe zogi.

BuÉ—e baki Afrah tayi zata mata magana sai dai cikin sauri Amrah É—in ta katse ta sannan ta cigaba da magana.

"Karki cemun komai Afrah, shin maina aikata a duniya wanda na cancanci irin wannan mummunan hukuncin?, Shin waye yake son ganin bayana a doron ƙasa?, Maina aikata musu?, Tabbas duk wanda ya mun wannan cutarwar wallahi wallahi ba zan taɓa yafe mishi ba domin kuwa bai cancanci yafiyata ba".

Jikin Afrah ne ya ƙara yin sanyi jin kalaman da Amrah ɗin take yi,Tabbas sai a yanzu ta fara nadamar abun da suka aikata mata ɗin, innalillahi wa'innailaihi rajiun meyasa na bari shaiɗan yayi galaba a kaina?, Maiyasa na bari soyayya ta rufe mun ido har na manta da muhimmanci ƙawance da kuma zaman tare?, Maiyasa na yadda aka haɗa kai dani aka cutar da baiwar Allahn nan?, Yanzu da wana ido zan kalle ta har na nemi yafiyar ta?".

Kallon ta Azra tayi sannan ta mata wata alama da ido wadda na kasa fahimtar ta mainene.

Turo ƙofar ɗakin namu aka yi aka shigo, inda muka ga wasu ƴanmata ne guda biyar suka shigo tare da neman waje su zauna sannan ɗaya daga cikin su ta dubi Amrah ta ce.

"Subhannallah Amrah ashe abun da ya faru kennan! Ashaaa! Gaskiya abu bai yi kyau ba,bai kuma yi daÉ—i ba,kamar ke yadda kike da ilimin addinin nan amma a wayi gari kin yaÉ—a tsaraicin ki a duniya,gaskiya ilimi bai yi rana ba".

Ta ƙarashe maganar tare da sakin wata shewa ita da abokan nata.

Ai Afrah bata yi wata-wata ba ta tsinke wadda take maganar da wasu irin tagwayen maruka sannan ta nuna ta da yatsa.

"Kefa daman Khadijah baki da mutunci inda mutunci yake ma baki dosa ba,ke a rayuwar ki baki da wani buri kullum wanda ya wuce kiga kin tozarta mu, to kiyi gaggawar fice mana daga cikin É—aki tun kafin mu sauya miki kammanni".

Afrah ta ƙarashe maganar tana sakin wani irin huci.

"Kan bala'i ni zaki mara Afrah to wallahi yau sai dai ko mu ko ku a cikin É—akin nan, dan wallahi yau sai dai ayi kare jini biri jini".

Khadija ta faɗa tana mai yin kukan kura tare da kaiwa Afrah wata irin wawar shaƙa.

Ai fa nan suma sauran Æ´anmatan da suka shigo tare da Khadijah suka mara mata baya tare da rufe Afrah da duka.

Ganin haka ya sanya su Azra ma suka shigarwa Afrah inda take faɗa ya kacame a tsakanin su, duka suke kaiwa junan su ta ko ina ba ƙaƙautawa burin kowa shine yayi galaba akan ɗan uwan shi.

Allah sarki Amrah kuwa baiwar Allah tana zaune a gefe kamar wata mutum-mutumi kamar an dasata.

Hayaniyar da maƙotan ɗakin su Afrah suka jini ya sanya su saurin fitowa tare da nufar ɗakin nasu, sannan aka shiga tsakanin su aka raba su, amma fa kowa sai da taji a jikin ta,duk sun haɗawa kan su jini da majina kowa ka kalla sai huci yake suna aikawa junan su harara.

Haka dai aka samu aka ja su Khadijah aka fitar da su daga cikin É—akin sai aikawa su Afrah da zagi suke ta uwa ta uba.

Su Khadijah wasu clique ne a class ɗin su Afrah waɗanda basu da maƙiya sama da su Amrah ba dan komai ba sai dan yadda su Afrah suka fi su ja a cikin class ɗin wannan dalilin ya sanya suka tsane su musamman Amrah da kowa yake son ta a cikin makarantar daga malamai har ɗalibai burin kowa shine yayi mu'amala da Amrah saboda ƙoƙarin ta da kuma kewawan halayen ta,sunan clique ɗin su Khadijah shine IRON LADIES ko Zafafa shida. A lokacin da clique ɗin su Khadijah suka samu labarin abun da ya faru da Amrah sai da suka ɗauki videon suka ƙara reposting a Instagram da Twitter sannan suka dinga jin kamar su zuba ruwa a ƙasa su sha.

*****

Allah Sarki a ɓangaren Anwar kuwa bai san abin da yake faruwa ba kasancewar shi ba ma'abocin hawa social media sosai ba, domin kuwa shi Whatsapp ma kawai yafi yi Whatsapp ɗin ma ba wani sosai ba. Hakan ya sanya ko Amrah bai barta ta buɗe shafuka a social media ba iya Whatsapp itama ya amince mata take yi. Kuma daman itan ma ba wata ma'abociyar son chatting ɗin bane sosai ba, yawanci idan ka ganta a Whatsapp to group ɗin class ɗin su ta shiga ko kuma irin suna da online class ɗin nan haka, ko kuma Anwar ya ce ta hau su yi video call.

Kwance yake a cikin É—akin shi yana danne-danne a cikin Computer É—in shi, akwai research É—in da yake yi.

Bugo ƙofar ɗakin nashi da aka yi aka shiga da ƙarfi ne ya sanya shi saurin ɗago kai ya kalli wana mai ɗanyen kan ne haka.

Ƙanin shi ya gani tsaye mai suna Nazir yana riƙe da waya jikin shi sai rawa yake.

Kallo É—aya zaka mishi ka fahimci tsantsar tashin hankalin da yake ciki sannan ka gane cewa akwai wani babban al'amari da ya É—aga mishi hankali

"Subhannallah Nazir lafiya kuwa?".

Anwar ya faɗa yana miƙewa tsaye tare da rufe Computer ɗin sannan ya saƙƙo daga kan gadon.

A dai-dai wannan lokacin kuma mahaifiyar shi itama ta faÉ—o cikin É—akin kamar an jeho ta.

"Ina kuwa lafiya, Anwar kai daman ashe karuwa kake shirin auro mana ka kawo mana ita cikin gidan nan bamu sani ba?".

Da sauri Anwar ya dubi mahaifiyar tashi cike da mamakin maganar tata sannan yace.

"Mama bangane karuwa ba!, wacece karuwa É—in?".

"Eh dole kace haka mana tun da an mana rufa-rufa ana ƙoƙarin ƙaƙaba mana karuwa a cikin zuri'a, to wallahi anyi walƙiya mun gano halin kowa munafukai kawai, in dai ina numfashi a doron ƙasa wallahi ba zaka taɓa auren wannan tsinnanniyar yarinyar ba,karuwa wadda ta gama tallatawa duniya jikin ta, kai ko bayan raina ne ban amince daka auri wannan yarinyar ba".

Wani irin sarawa Anwar yaji kan shi yayi lokaci guda ya dafe kan sannan ya fara takawa a hankali ya ƙarasa wajen mahaifiyar tashi sannan ya dube ta yace.

"Mama wallahi kin sanyani a duhu, gaba É—aya maganganun ki sun kulle mun kai, Mama dan Allah ku fitar dani haske".

Kallon shi sama da ƙasa mahaifiyar tashi tayi irin kallon ka raina mun hankali ma tukunna tare da jan tsaki sannan tace.

"Kai Anwar ka kalleni da kyau shekaruna hamsin a duniya dan haka,kar kayi ƙoƙarin wasa da tunani na ka nuna mun cewar baka san abun da yake faruwa ba,to ni dai na faɗa maka wallahi ba Amrah ba ko uwar ta ce, kai zuri'ar su Amrah ma baka isa ka nemi aure a cikin ta ba, shima uban nata ashe munafuki ne kwanta-kwanta ya yiwa mutane ya sanya ake masa kallon allaramma har yake jagorantar mutane ashe munafuki ne, to wallahi Allah ya tona musu asiri, kuma kuɗin mu da suka ci wallahi biyar ba zamu bar musu ba sai sun biya komai ko na maka su a kotu"

Tana kaiwa nan a zancen ta ta fice a cikin ɗakin tare da banko ƙofar kamar zata karyata,ta bar Anwar a tsaye cike da al'ajabin wannan baƙon lamari.

Bayan fitar mahaifiyar ta su daga cikin ɗakin daga Anwar har ƙanin nashi rasa wanda zai yi magana aka yi, sun ɗauki tsawon lokaci a haka kafin dai Anwar ya tattaro duk wani ƙarfin hali da ya rage mishi sannan ya taka a hankali har ya ƙarasa gaban Nazir sannan ya fara magana cikin sanyin murya.

"Nazir ka mun bayani mai yake faruwa?, Jikina ya riga da ya gama bani cewar ba lafiya ba".

Wayar hannun shi kawai Nazir ya miƙawa Anwar bayan yayi playing videon Amrah ɗin yana jin zuciyar shi kamar zata fito waje dan yadda yaji ya tsani Amrah ɗin.

A lokacin da idanuwan Anwar suka sauƙa akan videon ɗin kallo ɗaya ya yiwa videon ya ɗauke kan shi tare da furta.

"Auzubillahi minna shaiÉ—annir rajim"

Ya faÉ—a ba tare da ya lura da fuskar wacece a jikin videon ba, har ya buÉ—i baki zai ce wani abu sai kuma maganganun mahaifiyar shi suka shiga mishi yawo a kunnuwa.

" _Ina kuwa lafiya Anwar kai daman ashe karuwa kake ƙoƙarin auro mana ka kawo mana cikin_ _zuri'aaaaaa. Eh dole kace haka mana tun da an mana rufa-rufa ana_ _ƙoƙarin ƙaƙaba mana karuwa a cikin zuri'a,_".

Haka Anwar ya dinga jin Kalmar Karuwa tana masa yawo a cikin kunnuwa. Lokaci guda yayi saurin zubura tare da ƙara kai duban shi a kan wannan videon a karo na biyu.

Wani irin sarawa kan Anwar yayi a lokaci guda tare da jin wata irin hajijiya tana ƙoƙarin kayar dashi, ga wani irin gumi da ya shigar karyo mishi tun daga tafin ƙafa har tsakar kan shi.

Nazir bai yi auni ba sai ganin Anwar yayi ya zube yashe a ƙasa ko ƙwaƙwaran motsi bai yi ba.

Da gudu Nazir ya nufi kan shi yana ƙiran sunan shi amma shiru, nan fa ya ruga waje da gudu yana ƙwalawa mahaifiyar shi ƙira cikin tsananin ruɗani da tashin hankali.

*****
*GARIN GIWA*

Ba wanda ya san abun da yake faruwa da Amrah ɗin a can gidan nasu, sai dai kafin wani lokaci wasu daga cikin tsirarun ƴan garin sun fara cin karo da videon inda kan kace kwabo har video ya fara yawo a cikin garin tunin rabin ƴan garin sun samu ganin wannan videon rashin kunyar na Amrah domin kuwa har waɗanda basu da waya ma sai da suka ga videon wannan nunawa wannan wannan nunawa wancan haka aka rinƙa fasin-fasin da videon inda magana ta shiga tashi a cikin garin irin ƙananan maganar nan,da yawa take suka shiga yin Allah wadai da wannan halin da Amrah ɗin ta ɗakko,inda wasu kuma suka shiga yin Allah ya ƙara daman ai shi Malam Kabiru laifin shine ba ya dage sai ƴar shi tayi karatu ba,to ai ga irin ta nan tun ba a je ko ina ba ta janyo mishi abun kunya. Wasu kuma cewa suka yi daman kwaɗayin abun duniya ne da kuma son duniya ya sanya shi har ya kai ƴar shi makaranta wata uwa duniya, cikin waɗanda suke waɗannan maganganun hadda manyan abokanan Malam Kabiru ɗin,waɗanda lokacin da suka samu labarin cewar Malam Kabiru zai tura ƴar shi karatu jami'a sun same shi sun bashi shawara akan kar ya kaita ɗin inda suka nuna mishi illar hakan amma sai baiyi amfani da shawarar ta su ba,abun da ba a fiye yi a garin ba shine a kai yarinya makarantar gaba da secondary, yawancin yara daga secondary school an musu aure.

Da yawa daga cikin masu maganar sun fi ganin laifin Malam Kabiru akan laifin Amrah domin kuwa cewa suke da ace bai kai Amrah ɗin makarantar ba da duk haka bata faru ba, sai dai bakin alƙalami ya riga da ya bushe ƙaddara ta riga fata!.

Haka dai kowa ya dinga tofa albarkacin bakinsa kan kace mai duk wani alkhairin Malam Kabiru ya disashe a idon mutane inda aka shiga jifan shi da munanan maganganu saɓanin da da duk wanda zai buɗi baki ya faɗi magana a kan Malam Kabiru ɗin to alkhairi ne zai biyo ba, daga shi har iyalan shi ba wanda yake da wani mummunan aibu a idon mutane, amma gashi yau an wayi gari mutane sun buɗawa idon su toka sun manta da waye Malam Kabiru a wajen mutanen garin dalilin abun kunyar da aka ci karo dashi na ƴar shi.

Hmmmm É—an Adam Kennan!.

*MANGA* ✍️
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_ .

*FANSAR FATALWA*!
( _Horror Story_💀☠️).

_Tsarawa/Rubutawa_

*© SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam, Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_.

*Free book*

----------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*021*
______________________________

Malam Kabiru ne ya fito daga cikin rumfar ƙofar ɗakin nashi,sanye yake cikin babbar riga wanda kana gani shi ka san mutum ne mai cike da dattako da kamala.

Buta ya ɗauka a wajen randa inda ya nufi bayi domin kama ruwa kasancewar lokacin sallahr Azhar ya ƙarato.

Bayan ya fito daga bayin ne ya tarar da Gwaggo Sa'adatu tsaye a bakin rumfa tana jiran shi hannun ta riƙe da asuwaki, tana ganin fitowar tashi tayi saurin ƙarasawa ta karɓi butar hannun shi sannan ta kai mishi wajen alawla sai da ta miƙa mishi asuwakin ya fara yi domin kuwa hakan yana daga cikin al'adar shi in dai zai alawla to sai yayi asuwaki haka bayan ya kammalla ma.

ÆŠan rusunawa Gwaggo Sa'adatu tayi É—in kafin daga bisani tace.

"Malam dan Allah ko zan iya cewa wani abu?".

Zama Malam Kabiru yayi akan dutsen da yake alawlar kafin ya dube ta yace.

"To Shikennan kiyi maganar ki Allah dai ya sa ba doguwar magana bace ba".

"Malam yau É—in ne naga kamar wani abu yana É—an damun ka?, Allah dai yasa lafiya".

Dogon numfashi Malam Kabiru É—in ya ja sannan yace.

"Bakomai, amma idan na dawo daga massallaci zamu yi magana".

Ya faÉ—a sannan ya cigaba da yin asuwakin.

Bayan ya kammalla asuwakin ne ya fara gabatar da alawlar cikin nutsuwa ya idar da alawlar sannan ya yi addu'ar bayan idar da alawla tare da É—aga hannun sama yayi addu'a sannan ya tashi tare da duban Gwaggo Sa'adatu yace.

"To ni zan fita sai kuma Allah yayi dawowar mu".

"To Shikennan Malam a dawo lafiya".

Sa kai yayi tare da ficewa a cikin gidan sai dai mai yana fita ya ji massallacin da yake jan su Sallah har an fara ƙiran sallar, ko kaɗan malam Kabiru bai kawo komai a ranshi ba ya cigaba da nufar masallacin a tunanin shi yayi lattin fitowa ne shiyasa wani ya karɓi limancin duk kuwa da cewar wannan shine karo na farko da hakan ta taɓa faruwa.

Sai dai mai! Tun daga lokacin da ya fito daga cikin gidan nashi ya lura da cewar duk indai ya wuce majalisar mutane sai ya ga ana nuna shi ana ƴan maganganu ta ƙasa-ƙasa. Ƙarin wani abun mamakin ma shine duk inda ya wuce ya musu sallama sai ya ga ana ɗauke kai ana sunkuyar da kai ƙasa, saɓanin da da idan ya nufo majalisar mutane ma tun daga nesa za'a fara ɗaga mishi hannu ana gaisheshi cikin girmamawa.

Kan Malam Kabiru ne ya ɗaure ganin baƙon al'amarin da yake cin karo da shi ɗin,haka dai ya daure ya ƙarasa cikin massallacin amma zuciyar shi tana raya mishi wani abu yana shirin faruwa.

Wasu mutane ya gani tsaye daga gefen masallacin sun idar da alawla suna jiran a yi ƙiran shiga salla su shiga cikin massallacin.

Ɗaya daga cikin mutane aminin Malam Kabiru ne ƙut da ƙut tare suka taso, sannan kuma shine wanda ya ƙira salla a yau ɗin.

Da sallama ɗauke a bakin Malam Kabiru ɗin ya ƙarasa wajen mutanen sannan ya miƙa musu hannu yana cewa.

"Malam ÆŠalha sannun ku dai, da alamu yau nayi lattin fitowa sallar nag......".

Maganar Malam Kabiru É—in ce ta katse ganin cewa duk mutanen da suke tsaye a wajen sun yi gaggawar barin wajen sun shige a cikin massallaci an bar shi a tsaye ba tare da kowa ya tanka mishi ba

Sororo Malam Kabiru ya tsaya tare da bin hanyar da suka shige massallacin da kallo yana jin zuciyar tana wata irin harbawa.

Jin alamar tayar da iƙama da limami yake shirin yi ne ya sanya Malam Kabiru jan ƙafafuwan shi da suka mishi sanyi ya shiga cikin massallacin.

Sahun da yake gaba ya nufa ya tsaya, sai dai nan fa mutane suka shiga darewa suna matsawa daga gefen Malam Kabiru É—in har ya zamana cewar shi kaÉ—ai ya rage a sahun.

Duk da cewa abun ya zamar mishi sabon abu kuma abun ya taɓa mishi zuciya amma sai ya daure ya tayar da kabbarar sallar kamar yadda ya ji liman ya tayar da kabbarar sallar, a ranshi yana ayyana cewar in dai aka idar da sallar zai tsaya ya tambaya ko wani abu ya musu na ɓacin rai wanda bai sani ba sai ya basu haƙuri.

Bayan an idar da sallar sai da Malam Kabiru ya zauna ya yi lazimi kamar yadda ya saba kafin ya shafa addu'ar sannan juyo ya duba gabas da kudu da arewa na massallacin ba kowa sai shi É—aya.

A hanyar shi ta komawa gida yaci karo da Malam Ɗalha ya fito daga shagon wani mutumi hannun shi riƙe da leda alamar abu ya siya.

"Malam ÆŠalha".

Malam Kabiru ya ƙira sunan Malam Ɗalha ɗin ganin cewa shiɗin ya ɗauke kai kamar bai gan shi ba.

Manna mishi Malam Ɗalha ɗin yayi tare da cigaba da tafiya kamar bai ji ƙiran da Malam Kabiru ɗin yake mishi ba, hadda ɗan ƙara saurin tafiyar tashi.

Ganin cewa Malam Ɗalha ɗin bashi da alama ko niyyar tsayawa ya sanya Malam Kabiru ƙarasawa da sauri ya sha gaban shi sannan yace.

"Haba Malam ÆŠalha wai mai yake faruwa ne dan Allah?, Idan ma wani abu na aikata muku ai ba haka addinin mu ya koyar da mu ba, sai ku same ni ku sanar dani amma sai wa........".

Saurin dakatar dashi Malam ÆŠalha É—in yayi tare da fara magana.

"A haka dai kamar na kirki, ga ka nan kowa ya ganka ya ga dattijon kirki amma kuma sai gashi ka kasa bawa ƴar ka cikakkiyar tarbiya inda har ta aikata abun da ko a ƙasar arna haramun ne balle mu musulmai, wai wanda ya kasa kula da tarbiyyar ƴar shi ne ake zaton zai jagoranci al'ummar ta hanyar addini, ai wannan ma ba abun da zai yiwu bane, kayi ƙoƙari ka gyara ɓarakar da ta ɓarke a gidan ka kafin kayi ƙoƙarin gyara rayuwar wasu.Allah dai ya shirya wallahi, ai an yi walƙiya mun gane halin uban kowa".

Malam ÆŠalha yana kaiwa nan a zancen shi ya ratsa ta gefen Malam Kabiru É—in ya wuce ya barshi tsaye cikin kullewar kai kamar an dasashi.

Da ƙyar dai ya ja ƙafafuwan shi ya nufi hanyar gida zuciyar shi sai saƙa mishi abubuwa iri-iri take ga faɗuwar da yaji gaban shi ya tsananta mishi.

Daf da zai shiga gida shine yaji ana ƙwala mishi ƙira daga nesa.

"Malam Kabiru, Malam Kabiru".

Juyawa yayi ya kai duban shi zuwa inda mai ƙiran nashi yake.

"Malam Kabiru Subhannallah ashe abun da ya faru Kennan, gaskiya ka bamu mamaki wallahi ya kamar kai ace an ci karo da videon tsaraicin Æ´arka yana yawo a duniya, dan Allah Malam Kabiru a garin yaya ka bari haka ta faru,gashi nan duk gari ya É—auka ko ina maganar ake".

Ƙarasowar Hisham wajen ne cikin tashin hankali ga idanun shi da suka kaɗa suka yi jawur kamar wuta alamar cewar baya cikin nutsuwar shi ya sanya wannan mutumin da yake tsaye saurin jan ƴan ƙafafuwan shi ya bar wajen daman gulma ce tsantsa take cin shi.

Shikam Malam Kabiru tun da wannan mutumin ya fara magana ya nemi duk wata Æ´ar guntuwar nutsuwar da ta rage mishi ya rasa, maganar duniya Hisham ya mishi amma shiru ba magana gashi ya kasa motswa daga wajen da yake tsaye É—in.

Ganin hakan da Hisham yayi ne ya sanya shi saurin jan Malam Kabiru É—in suka shige cikin gidan.

A tsakar gida suka tarar da Umar da Usman ga Gwaggo Sa'adatu a gefe in banda tsiyayar hawaye ba abun da idanun ta suke yi.

Kujera Hisham ya janyo a gefe sannan ya zaunar da Malam Kabiru É—in.

Da sauri Gwaggo Sa'adatu ta ƙaraso wajen Malam Kabiru ɗin tare da zube duka gwaiwowin ta a ƙasa sannan ta fara magana cikin kuka.

"Malam karka yadda da duk wani abu da ka gani wallahi Malam nasan cewar Amrah ba zata taɓa aikata abun da aka ce ba wallahi sharri kawai aka mata,wasu ne suke son suga sun tarwatsa mata rayuwa, Malam kasan wacece Amrah ka kuma san abun da zata yi da wanda ba zata yi ba Malam wallahi ko kaffara ba zan yi ba ba Amrah bace ta aikata wannan abun ba".

Duk maganganun da Gwaggo Sa'adatu take har ta gama Malam Kabiru ko uffan bai ce mata binta kawai yake da kallo,gaba É—aya kan shi a kulle yake ya rasa inda maganar tata ma ta dosa.

Saurin ƙarasowa inda Gwaggo Sa'adatu ɗin take durƙushe Hisham yayi sannan ya ɗaga ta tsaye tare da fara magana.

"Gwaggo dan Allah ki bar ɗaga hankalin ki akan abun da Amrah ta aikata ni na tabbatar zata yi nadama sannan idan ta yi hakan ne ma dan ta ɓata mana suna wallahi kan ta ta ɓatawa ni dai kam Hisham na cire Amrah daga cikin ahali na ko a lahira na ganta zan nuna ban santa balle a nan duniya".

Hisham yana kaiwa nan a zancen na shi ya juya cikin tsananin jin tsanar Amrah É—in ya fice a cikin gidan.

*****

A can makarantar su Amrah kuwa yau zama hukumar makarantar ta ƙira na gaggawa inda ta buƙaci duk wani malami da ya halarci wannan zaman domin wasu daga cikin malaman makarantar sun shigar da ƙara akan a yi gaggawar dakatar da Amrah daga makarantar domin gujewa sake afkuwar irin abun da Amrah ɗin ta aikata.

Daga wani ɓangare ma Student Union Government da kuma musulim Student society na makarantar suma sun shigar da nasu ƙorafin inda suka buƙaci da ayi gaggawar ɗaukar mataki akan Amrah ɗin saboda hakan ya zamarwa ƴan baya darasi.

Wani babban Conference Hall na gani wanda a ƙalla zai ci mutane sama da Hamsin inda naga wasu mutane a zaune kowa ya mayar da hankali shi a kan abun da wani mutum yake faɗa wanda kujerar shi take a tsakiya da alama shine shugaban taron.

Taro ake inda gaba É—aya Malaman ABU É—in ne a cikin Hall É—in, wannan taron ba akan kowa ake yin shi ba sai akan Amrah.

"Sir ni a ganina bai kamata ace an yi saurin yankewa wannan yarinyar hukunci ba ba tare da an zurfafa bincike ba domin kuwa Sir wallahi wannan yarinyar ko shakka bana yi bata aikata wannan abun da aka ce ba".

"Haba Dr Gana wannan wace irin magana kake haka, bafa cewa aka yi ta aikata ba ra'ayul aini aka ganta ai a ganina ba wani bincike da kuma za'a yi bayan kamata da aka yi dumu-dumu".

"Shine gaskiya kawai"

Gaba ɗaya mutane cikin Conference Hall ɗin suka haɗa baki suka faɗa in ka cire Dr Gana wanda burin shi bai wuce ya nunawa hukumar makarantar cewar Amrah ba zata taɓa aikata wannan abun ba domin kuwa shi kam ya shedai ta.

ÆŠagowa Dr Gana yayi ya kai duban shi kan VC É—in da yake zaune a kan kujerar shi yana saurar duk abubuwan da suke faÉ—a É—in.

"Sir dan Allah ku fahimce ni wallahi wannan yarinyar mutuniyar kirki ce, dan Allah ayi bincike kafin a zartar mata da wannan É—anyen hukuncin da ake son zartarwa, Sir a duba halin da take ciki kar a haÉ—a mata zafi biyu da wanne zata ji ga mari ga tsinka jaka".

Manage it pls wallahi bani da chaji😞👏🏻.

*MANGA* ✍️
Comment
Share
Fisabillillahi.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_ 💀☠️ ).

_Tsarawa/Rubutawa_

*© SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA* : _Wannan book É—in gaba É—ayan_ _shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam_ , _Alkhairin Allah ya kai_ _muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_.

*Free book*

---------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*022*
______________________________

Haka dai aka cigaba da wannan zaman meeting ɗin inda a kaf cikin Malaman ABU ɗin Dr Gana ne kawai yake ƙoƙarin ganin ya kare Amrah ɗin da kuma ƙoƙarin fahimtar da shuwagabannin makarantar cewar Amrah tana da kyakkyawan hali ba zata taɓa aikata abun da ake zargin ta ba.

Hayaniyar da VC É—in ya ji tayi yawa ne ya sanya shi yin gyaran murya sannan a karon farko ya buÉ—i baki ya fara magana.

"To da farko dai duk naji ƙorafe-ƙorafen ku dama duk shawarwarin da kuka bada daman amfanin meeting ɗin Kennan shine domin aji opinion ɗin kowa,Dr Gana bari in fara da maganar ka saboda naga kai kaɗai ne wanda kake kare wannan yarinyar, da farko ina son ka gane wani abu guda ɗaya shine wannan abun fa ba wai zargin yarinyar ake da aikatawa ba a'a hannu dumu-dumu aka kamata da wannan laifin dan haka ba buƙatar a tsaya wani bincike akan lamarin, dalili kuwa shine na farko account ɗin da ka yi posting Videon gaba ɗaya username ɗin ta ne a kai kaga kennnan tabbas tana da alaƙa da account ɗin, abu na gaba shine a cikin toilet a ka ɗauki videon wanda ni dai a iya sanina mutum ɗaya yake shiga toilet yayi wanka dan haka wannan ya nuna cewar da sanin ta da kuma yardar ta aka shiga toilet ɗin aka mata video ko kuma ta yiwa kanta zan ce wannan ya nuna cewa daman tuntuni yarinyar bata gari ba ce ba".

Ɗago kan shi Dr Gana yayi cikin sauri wasu hawaye masu zafi ne yaji suna ƙoƙarin fitowa daga idanun shi inda yayi saurin mayar da su sannan ya buɗi baki tare da furta.

"Amma Sir..........".

ÆŠaga mishi hannu VC É—in yayi sannan ya cigaba da magana.

"Maganar gaskiya Dr Gana dole a zartarwa da wannan yarinyar hukunci, hukunci kuma mai tsauri ko dan hakan ya zama darasi ga ƴan baya masu shawara aikata abu da makamancin nata, a yanzu haka maganar da nake maka manyan malaman addini sun shigo cikin maganar kuma sun buƙaci a yi gaggawar ɗaukar mataki a kan ta domin kuwa wannan abu ne da tun da aka kafa wannan makarantar ba'a taɓa samun irin haka ba,yanzu dai taro zai tashi inda zamuyi zama na gaba a nan ne kuma za'a faɗi hukuncin da aka yanke a kan yarinyar da kuma makomar karatun ta".

VC yana kaiwa nan a zancen shi ya miƙe tsaye tare da ficewa daga cikin ɗakin taron,inda suma sauran Malaman ɗaya bayan ɗaya suka shiga ficewa daga cikin ɗakin taron ya rage daga Dr Gana sai abokin shi Shahid.

"Dr Gana wai mai yasa kake son É—aura damuwar wannan yarinyar a ranka ne?".

Shahid ya faÉ—a yana tasowa daga kan kujerar shi ya dawo kusa da Dr Gana É—in.

ÆŠago idanun shi Dr Gana yayi waÉ—anda suka mishi jawur sannan yace.

"Haba Shahid mai yasa ba zan damu kaina ba, wallahi Shahid ina tausayin Amrah kuma wallahi na tabbatar Amrah bata aikata abun da ake zargin ta ba, Ni na tabbata wasu ne suke san ganin sun ɓata mata suna".

Tun da ya fara maganar Shahid ya kafe shi da ido cikin tsananin mamakin kafiya irin ta abokin nashi.

"Hmmm Dr Gana mai yasa zaka ji tausayin wadda bata tausayawa kanta ba, sannan maganar zargi ka daina cewar ana zargin ta domin kuwa ba maganar zargi a wannan lamarin,dan haka ni dai shawara zan baka a matsayina na abokin ka wallahi ka cire kan ka daga cikin case É—in wannan yarinyar domin kuwa na tabbata ba wanda ya isa ya sanya a hana zartar mata da hukuncin da aka yi niyya,dan haka idan zaka tashi mu tafi ma ka tashi mu wuce kawai".

"Akwai,tabbas! Akwai abun da zai hana a zartar mata da hukunci".

"Waye shi?".

Shahid ya faɗa yana ƙunshe dariyar da yake ji ɗin domin kuwa ya san abokin nashi zance kawai yake.

"Gaskiya! Gaskiya idan ta bayyana zata hana a zartar da hukuncin".

Dr Gana yana faɗin haka ya tashi ya fice daga cikin Conference Hall ɗin ya har Shahid a tsaye sake da baki,yana mamakin ƙarfin hali irin na abokin nashi.

*****

Haka aka jidi Anwar ranga-ranga rai a hannun Allah ko motsi ba yayi, ana isa da shi asibiti likitoci suka taho da gudu suka karɓe shi suka shiga dashi Emergency room domin bashi Emergency Treatment.

Likitoci sun shafe lokaci mai tsawo a kan Anwar É—in amma sun kasa ceto shi daga cikin halin ha'ula'in da yake ciki.

Sun shafe tsawon awanni a kan shi kafin su samu numfashin shi ya daidaita amma kuma yana nan unconscious bai san wanda yake kan shi ba.

Ɗaya daga cikin likitocin ne ya fito wanda da alama shine babban su yana sharce gumi inda ya tarar da mahaifiyar Anwar da ƙanin shi Nazir a waje sai kaiwa da komowa suke hankali a matuƙar tashe.

Suna ganin fitowar likitan suka nufe shi da sauri suna tambayar shi ya jikin Anwar É—in.

Kallon su yayi sannan yace su biyo shi office.

Aikuwa ko gama rufe bakin shi baiyi ba suka bi bayan shi da mugun sauri kamar yadda ya buƙata ɗin.

Bayan sun shiga cikin office É—in kujera likitan ya nuna musu alamar su zauna sannan ya janyo folder É—in Anwar É—in tare da fara rubuce-rubuce a ciki.

Ya É—auki É—an tsawon lokaci yana rubutun kafin ya É—ago ya dubi mahaifiyar Anwar yace.

"Sannu Hajiya, pls ko zan iya sanin maiye alaƙar ku da wannan yaron?".

"Likita ɗana ne nice mahaifiyar shi wannan kuma ƙanin shi ne".

Mahaifiyar Anwar ta faÉ—a cikin rawar murya.

"Ina mahaifin shi fa?".

Da sauri Nazir ya kalle shi sannan yace.

"Kaga Dr duk abun da zaka faÉ—a ka faÉ—a da mu da mahaifin shi duk É—aya ne, dan Allah kayi gaggawar sanar damu abun da yake damun shi".

ÆŠan shiru likitan yayi kafin kuma ya sanya hannu ya gyara zaman glass É—in idon shi kafin kuma ya fara magana.

"To a zahirin gaskiya dai zan iya cewa kuyi haƙuri domin kuwa mun yi duk iya ƙoƙarin mu dan ganin mun ceto rayuwar wannan yaron sai dai abun yana so ya gagare mu sakamakon ya shiga shock ne dalilin gani ko jin wani mummunan abu,yanzu dai Alhamdulillahi mun yi nasarar samu mun daidaita numfashin shi amma kuma har yanzu yaron ku yana buƙatar addu'a, domin kuwa mu dai mun yi iya abun da zamu iya sauran kuma mun barwa Allah,kuyi haƙuri ku cigaba da mishi addu'a Allah ya tashi kafaɗun shi".

Wani irin kuka mai taɓa zuciya mahaifiyar Anwar ɗin ta fashe dashi inda da ƙyar Nazir ya janyo ta suka baro office ɗin likitan,sai kuka take kamar ranta zai fita.

Rarrashin duniya Nazir ya yiwa mahaifiyar tashi amma kamar wadda yake ƙara tunzura ta.

*****

Yau ta kama Monday tun safe na tashi da shirin komawa makaranta kasancewar yau É—in mahaifina har yayi sati biyu da rasuwa kuma gashi saura sati É—aya mu fara exams wannan dalilin yasa zan koma makarantar domin yin karatu gudun kar a zo a kafe result na samu matsala.

Ƙarfe bakwai na safe na fito cikin shirina na tafiya inda na tarar da mahaifiyata har ta tashi ta kammalla haɗa breakfast.

Gaishe ta nayi inda na nufi dining table É—in a tsaitsaye na ci abincin ina ta sauri domin ina son naje na samu lecture gashi duk hankalina yayi kan Amrah so nake kawai naje makarantar naga a wane hali take ciki.

Ina kammalla cin abinci na yiwa Mahaifiyata sallama sannan na fito harabar gidan mu inda na tarar da driver yana tsaye a jikin mota yana jirana.

Shiga motar nayi inda drivern ya tayar da motar muka fice a cikin gidan muka É—auki hanyar ABU É—in.

Bamu yi wata doguwar tafiya ba muka ƙarasa makarantar tamu a parking lot drivern ya sauƙe ni inda nikuma na zari jakata na nufi Hostel.

Da sallama É—auke a bakina na shiga cikin É—akin namu wata mummunar faÉ—uwar gabane ta dirar mun a lokaci guda sakamakon arba da nayi da Amrah.

Kwance take a kan gado ta rame tayi baƙi domin idan har ba kyakkyawan sani ka mata ba to ba lalle ka gane ta ba a yanzun.

Cikin sauri na ƙarasa shiga cikin ɗakin tare da yasar da jakata a tsakiyar ɗakin,a bakin gadon na zauna tare da rungumota ina ambatar sunanta.

"Ya subhannallah Amrah mai zan gani haka!?".

Sai a sannan Amrah ta samu damar buɗe idanunta wadda bata ma san da shigowata cikin ɗakin ba sai da taji sauƙar muryata a dodon kunnenta.

Wasu zafaffan hawaye ne suka shiga zarya a idanun Amrah É—in wanda da alama har sunyi sabo da kuncin nata.

Lokaci guda nima naji wani kuka ya ƙwace mun cikin kuka na fara magana.

"Amrah dan Allah kiyi haƙuri ki yafe mun, Amrah nasan ban kyauta miki amma dan girman Allah kiyi haƙuri naso na dakatar da faruwar wannan abun amma kuma rasuwar mahaifina ita ta dakatar da komai, amma ki sani na dawo a yanzu kuma in sha Allah zan.......".

Maganar tawa ce ta katse sakamakon turo ƙofar da akayi.

Su Azra ne suka shigo cikin ɗakin wani mugun kallo na watsawa Azrah ɗin kafin na buɗi baki da niyyar cigaba da magana domin kuwa na ƙudiri aniyar cewar a yau sai na tona musu asiri a wajen Amrah koma meye zai faru sai dai ya faru sai dai kafin na fara maganar tunin Azra tayi saurin dakatar dani ta hanyar fara magana.

"Lah Amira sauƙar yaushe irin wannan zuwa haka ko sanarwa babu".

Ban kulata ba sai ma juyawa da nayi na kalli inda Amrah take kwance sannan nace.

"Amrah ki sani cewar a wannan zamanin da muke ciki amana tayi ƙaranci,hassada ta cika zukatan al'umma,wanda baka zaton zai ci amanar ka shi yake jefaka a bala'i, Amrah mutane sun zama ba abun yarda ba yanzu dan haka ki bar ganin mutanen da kike tare dasu suna nuna damuwa a kan ki dan abu ya sameki to wallahi kar kisha mamaki sune waɗanda sukayi silar shigar ki wannan damuwar,domin kuwa munafukin ka tabarmar ka sannan makashin ka yana tare da kai sa........".

"Haba Amira a kan wana dalili zaki zauna kina sanar da Amrah karatun da ta daÉ—e da sanin shi,idan darasi zaki mata ai kamata yayi ki mata a kan sabon karatu amma wannan tun yaushe aka daÉ—e da sanin shi,a yanzu lallashi ya kamata ki mata ba waÉ—annan suki burutsin karatun ba ko ba haka ba Amrah?".

Na tsinkayi muryar Azra ta daki dodon kunnena, da sauri na juyo na dube ta inda take ta jefa mun wani kallo mai cike da gagarÉ—i na cewar Amira ina gargaÉ—in ki kar ki fara jefa kan ki a cikin ramin da kika san ba zaki iya fita ba.

Har na buɗi baki zan yi magana sai kuma ga ƙiran gaggawa an yiwa Amrah ana ƙiran ta daga school management kuma da gaggawa.

Wani matsanancin faÉ—uwar gaba ne ya ziyarce mu a lokaci guda daga ni har Amrah É—in.

Tashi tayi tare da ɗaukar hijab ɗin ta ta sanya sannan ta fara tafiya tana tangal-tangal kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki.

Tashi nayi da sauri zan kamata sai dai kafin na ƙarasa inda take ɗin har Azrah ta isa ta riƙe ta tare da cewa.

"Wayyo Allah Amrah kar ki faÉ—i bari na rakaki".

Ba yadda zan yi haka na ƙyale Azrah ta kama Amrah inda muka bi bayan su muka nufi Administrative Block ɗin.

Duk inda muka wuce haka zaka ji ana ƙananun maganganu ana nuna Amrah,wasu kuwa hadda yada baƙar magana amma ba wanda muka kula tun da mun lura daman neman magana mutane suke.

Su Khadijah ne suka zo wucewa Clique ɗin su guda hadda ƙarin wasu maza guda uku, wata iriyar dariyar suka kwashe da ita irin ta rainin hankali nan hadda tafawa sannan Khadijah ta dube su tace.

"Ikon Allah nikam banga amfanin saka hijab ga wasu mutanen ba domin kuwa abun da ake ɓoyewa ɗin mun riga da mun gani duniya ma ta gani,to maiye na ɓoyewar In banda munafurci,Allah dai yayi wadaran wasu mutanen wallahi".

Har na buɗi baki zan tanka musu kawai Amrah ta damƙe mun hannu tare da jijjiga mun kai sannan muka wuce ba tare da mun tanka musu ba.

A bakin Admin Block É—in muka tsaya muna jiran Amrah inda ita kuma ta shiga cikin Conference Hall É—in inda malamai suke tare a ciki ana jiran Amrah É—in.

Da sallama a bakin ta ta shiga duk kuwa da ta san cewa akwai malami Kiristan a wajen amma saboda ta saba hakan bai sanya taƙi yi musu sallama ba saboda ta saba.

Tun da ta shiga Dr Gana ya kafeta da ido cikin tsananin tausayin ta ganin yadda duk ta zabge ta rame wasu hawaye ne yaji suna ƙoƙarin zubo mishi inda ya sanya hannu ya goge gudun kar a gani.

Kujera aka nuna mata ta zauna sannan aka miƙo mata wata farar takarda.

Cikin rawar hannu ta miƙa hannun ta ta karɓi takardar ba tare da ta buɗe ba.

VC ne ya buÉ—i bakin shi sannan ya fara magana cikin harshen turanci.

"Amrah Kabir a madadin malamai da hukumar wannan makarantar muna sanar dake cewar mun dakatar dake daga karatu a cikin wannan makarantar ma'ana a yanzu ke ba ɗalibar mu bace ba, sakamakon samun ki da muka yi da aikata laifin irin wanda tun da aka kafa wannan makaranta ba'a taɓa samun makamancin irin hakan ya faru ba sai a kan ki, wannan dalilin ya sanya hukumar makaranta zauna a kan ki domin zartar da hukunci wanda yayi dai-dai da abun da kika aikata,sannan mun zartar miki da wannan hukuncin ne saboda ya zama darasi ga ƴan bayan ki,domin kuwa mun san cewar akwai masu zuciya irin taki da yawa a duniya to amma wannan hukuncin shi zai sa duk wani mai sha'awar aikata abu kwatankwacin naki to zai tsorata idan ya tuna da irin hukuncin da aka miki ɗin, dan haka zaki iya tashi ki tafi mun sallameki"

Tun da VC ɗin ya fara magana Amrah taji kamar an sanya wata guduma ne an buga mata a tsakiyar kai,kafe shi da ido tayi kamar an dasata a lokaci guda kuma taji kamar an sanya ruwa an wanke mata duk wani ɓacin rai da take ciki,a maimakon tayi kuka kawai sai gani suka yi ta kwashe da wata irin dariya kamar wata zararriya,a lokaci ɗaya kuma tana dariyar hawaye yana fitowa daga idon ta watau kuka da dariya a lokaci guda.

Duk wanda yake cikin Hall É—in sai da Amrah ta bashi tausayi domin kuwa kallo É—aya zaka mata ka fahimci cewa ta zauce.

Miƙewa tsaye tayi ta fara tafiya tana tangal-tangal kamar wadda ta sha giya ta bugu.

Dr Gana ne ya fara ƙoƙarin miƙewa da sauri zai riƙo ta sai dai take Shahid ya ruƙo shi wanda yake zaune a kusa dashi sannan ya shiga jijjiga mishi kai alamar a'a.

Amrah kuwa har ta fito daga cikin Hall ɗin bata daina ɓaɓɓaka dariyar da take yi ɗin ba ga hawayen shima bai daina zubowa ta idon ta ba.

Tun daga nesa na hango ta na tafe tana tangal-tangal,da gudu na tashi inda na nufeta sai dai kafin na ƙarasa inda take ɗin har ta yanki jiki ta faɗi ko alamar shurawa bata yi ba.

Innalillahi wa'innailaihi rajiun, Hasbunnallahu wa ni'imal wakil,shine kawai abun da bakunan mutanen wajen ya shiga furtawa ganin cewa kamar Amrah É—in bata da rai.

Cikin tsananin tashin hankali na ƙarasa kan ta da gudu inda na shiga jijjiga ta ina ƙiran sunan ta.

"Amrah dan Allah ki tashi, Amrah dan girman Allah ki taimakawa ki tashi, Amrah ki tashi wallahi yanzu zan sanar dake gaskiyar da na ɓoye miki, Amrah nasan ba mutuwa kika yi ba, Amrah ki tashiiiiii".

Na faɗa ina sakin wata razannanniyyar ƙara tare da ƙanƙame Amrah ɗin a jikina.

A dai-dai wannan lokacin su Afrah da Anisa da Azra suka ƙaraso wajen da gudu suna ƙoƙarin taɓa Amrah ɗin,sai dai wata irin shaƙa da na kaiwa wuyan Azra ɗin shi ya dakatar da ita daga abun da take shirin aikatawa ɗin.

Cikin wata iriyar murya wadda kamar ba tawa ba na fara magana.

"Na rantse da girman Ubangiji idan har Amrah ta mutu wallahi tallahi sai na kashe ku gaba É—aya sai dai nima a kashe ni tsinnannu kawai waÉ—anda suka kwashe kayan su daga gaban ma'aiki,wallahi sai rayuwar ku ta tagayyara domin kuwa tun a nan duniya na tabbatar Allah ba zai bar ku ba dan wallahi sai kun ga sakayya mafi muni".

Duk irin yadda Azra ta so ta ƙwace kan ta daga irin shaƙar da na mata abun ya gagara,tsananin tsoro da tashin hankali ne ya bayyana a fuskokin su Afrah da Anisa ganin cewar har Azra ɗin ta fara fita a hayyacin ta.

Mutanen wajen ne suka shiga kiciniyar ƙwace Azra daga hannun nawa amma ina! Duk irin yawan mutanen wajen sun kasa ƙwace Azra daga hannuna domin kuwa wani irin ƙarfi nayi ba zaka ce mutum bane da wannan ƙarfin.

Da ƙyar dai aka samu aka ƙwace Azra ɗin a hannun nawa wadda tunin ta daɗe da sumewa.

Nima a take kuma na yanki jiki na faÉ—i tare da sumewa a wajen.

Sosai mutanen wajen suka cika da mamakin wannan al'amarin.

*MANGA* ✍️
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_💀☠️).

_Tsarawa/Rubutawa_

*© SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_.

*Free book*

-------------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*023*
________________________________

Ambulance aka samu inda aka sanya Azra da Amira a ciki,in da ana ƙoƙarin ɗaukar Amrah matasan makarantar suka ce ai wallahi ba za'a ɗauke ta ba gara a barta ta mutu,domin kuwa bata da wani amfani a cikin al'umma.

Nan fa hayaniya ta kware a wajen wasu daga cikin mutanen wajen suna goyon bayan a ɗauki Amrah ɗin a taimaka a kai ta asibitin inda wasu kuwa suka yi tsallen aradu suka ce ba za'a ɗauke ta ba. Sai dai kun san an ce majoraty carry the both wannan ya sanya masu iƙirarin cewa ba za'a kai Amrah asibitin ba suka rinjayi masu cewa a taimaka mata ɗin.

Hakan ya sanya duk yadda wasu suka so a taimaka mata amma abun a ci tura gashi suna kallo rayuwar ta tana tsaka-tsaki domin kuwa a wannan halin da ake ciki ma basu sani ba shin Amrah É—in tana da rai ko kuma ta mutu ne.

Hayaniyar da malaman da suke cikin Conference Hall É—in suka ji tayi yawa ne ya sanya su fitowa da sauri dan ganin mai yake faruwa.

Ganin Amrah suka yi a yashe a ƙasa ba alamar numfashi a tare da ita,ga matasan makarantar kuma sun cika a wajen maza da mata ana ta cece-kuce wasu har suna cewa a basu ita kawai suje su binne ta da ranta,wasu kuwa cewa suke a banka mata wuta kawai ta mutu, kasancewar tun ranar da abun ya faru Amrah bata sake fita koda nan da can ba,duk da cewa ko a cikin Hostel ɗin ma ba tsira tayi tun da wani lokacin har cikin ɗakin su ake shigowa a ci mata mutunci,babu irin baƙaƙen maganganu da ba'a gayawa Amrah ɗin,kullum cikin kuka take karatu kuwa tunin ta ajiye shi a gefe domin kuwa da ace ba'a koreta a makarantar ba to tabbas ta san wannan semester ɗin ba abun da zata iya tsinanawa wataƙila ma a mata repeat.

Dr Gana ne ya ƙarasa inda Amrah ɗin take a yashe ganin shi da ƴan makarantar suka yi ya sanya suka fara darewa suna bashi hanya wajen kuma yayi tsit kasancewar shi yana daga cikin malaman da ɗalibai suke shakka a cikin makarantar saboda baya sakewa kowa fuska balle a raina shi.

Ba wanda ya saurara yana ƙarasawa inda Amrah ɗin take ya sanya hannu ya sunkuceta sannan ya fice daga cikin Admin Block ɗin da ita ya nufi motar shi duk sai idanun mutanen suka dawo kan shi inda ƙananan maganganun suka shiga tashi.

A bayan motar ya sanya Amrah sannan Anisa da Afrah suma suka shiga motar waÉ—anda suka biyo bayan shi a lokacin da suka ga ya É—akko Amrah É—in.

Da gudu ya figi motar sannan ya fice daga cikin makarantar ya nufi babban asibitin da yake cikin garin Zaria É—in da Amrah É—in.

Tsananin gudun da yake shararawa akan titin ya sanya motoci da yawa suka fara kaucewa suna bashi hanya gudun kar ya haɗa da su a tafiya lahirar tun da sun lura kamar wanda yake tuƙin motar baya son rayuwar shi ne.

Kan kace kwabo har ya ƙarasa asibitin, ko parking mai kyau bai yi ba ya fito daga cikin motar da sauri sannan su Anisa ma suka fito.

CiÉ—ak ya É—akko Amrah a hannun shi ya nufi Emergency unit da ita,inda suma su Afrah suka bi bayan shi sai sharar hawayen munafurci suke.

Hango shi da ma'aikatan asibitin suka yi ya sanya su nufo shi da gudu sannan suka karɓi Amrah ɗin suka ɗaura ta akan gadon da ake tura marrasa lafiya suka nufi cikin Emergency unit ɗin da ita.

A dai-dai wannan lokacin aka ƙaraso da su Amira da Azra ma inda suma aka sanya su a ɗakin da yake gefen na Amrah.

Likitoci ne suka duƙufa akan Amrah suna bata agajin gaggawa,sun ɗauki tsawon lokaci a kan ta kafin suka samu numfashin ta ya daidaita, amma sun sha matuƙar wahala kafin su shawo kan daidaituwar numfashin nata.

Drip aka sanya mata sannan aka mata allurai inda suka fice suka barta kafin a ga lokacin farfaÉ—owar tata.

Dr Gana yana tsaye a bakin ƙofar ɗakin da aka shiga da Amrah ɗin sai kaiwa da komowa yake hankali a tashe.

Yana ganin fitowar likitocin ya nufe su da gudu yana cewa.

"Dr ya jikin nata, dan Allah karka sanar dani cewa ta mutu?".

Dr Gana ɗin ya faɗa tare da riƙo hannun likitan,jikin shi sai rawa yake.

"Ku biyoni office É—ina".

Shine kawai abun da likitan ya iya faÉ—a sannan ya nufi hanyar komawa office É—in nashi.

Jiki a sanyaye Dr Gana da su Afrah suka bi bayan likitan gaba É—aya sun gama bayarwa Amrah ta mutu.

Shigar su office ɗin likitan ya nuna musu wajen zama sannan ya shiga musu bayani ba tare da ɓata lokaci ba.

"Maganar gaskiya Dr Gana rayuwar wannan yarinyar tana cikin haɗari,yanzu dai mun samu mun daidaita numfashin nata sannan a kowane lokaci zata iya farfaɗowa daga doguwar suman da tayi sai dai akwai yiwuwar cewa idan ta farfaɗo ta farfaɗo da ciwon hauka domin kuwa, ƙwaƙwalwar ta ta taɓu sannan ya zuciyar ta da itama ta fara kumbura,dan haka a yanzu wannan yarinyar addu'ar ku kawai take buƙata".

"Innalillahi wa'innailaihi rajiun, likita yanzu Meye abun yi,wallahi duk abun da ake buƙata zan bayar matuƙar za'a ceci rayuwar ta,pls Dr do something I beg, dan Allah a taimaka".

Dr Gana ya faÉ—a cikin tsananin tashin hankali da ruÉ—ewa.

Su Anisa da suke zaune a gefe ma take suka ji zuciyoyin su sun shiga bugawa a lokaci guda jin abin da likitan ya faÉ—a, Wannan shine karo na farko da Anisa taji nadama da tausayin Amrah sun shige ta.

"Dr Gana Sorry to say a yanzu kam ba wani abu da zamu iya yiwa Wannan yarinyar domin kuwa duk wani abu da ya kamata mun yi,dan haka zamu jira har zuwa lokacin da zata farka muga a wana hali ta farka,ku yi haƙuri".

Tashin hankali shine abun da Dr Gana ya faÉ—a sannan ya dubi likitan yace.

"Amma likita zamu iya shiga mu ga a wane hali take".

"Gaskiya ba zai yiwu ba,domin tana buƙatar a keɓeta ita kaɗai, a yanzu haka ƙarar abu kaɗan zata iya sanyawa ta farka,mu kuma bama son farkawar tata a yanzu".

Haka Dr Gana da su Anisa suka tashi suka fito daga office É—in likitan fuska cike da damuwa.

A ɓangarena kuwa ba'a wani ɗauki tsawon lokaci ba na farfaɗo inda ina farfaɗowa na juya gabas da yamma naga ba kowa a cikin ɗakin. Cikin sauri na sanya hannu na cisge ƙarin ruwan da ake mun ɗin sannan na tashi da gudu na fice daga cikin ɗakin ko takalmi ban tsaya sanyawa ba,dagani sai ɗan kwali.

Ɗakunan da suke gefena na shiga dubawa inda cikin ikon Allah na hango Amrah kwance a cikin ɗakin da yake tsakiyar namu ni da Azra kamar ka ƙira sunan ta ta amsa.

Da gudu na nufi ɗakin naci Sa'a kuwa ƙofar ɗakin ba'a rufe take ba ina turawa ta buɗe.

Tura ƙofar tawa yayi dai-dai da farkawar Amrah inda kafeni da ido kamar yadda nima nayi ina tsaye a bakin ƙofar ɗakin.

Kamar wadda ta tuno wani abu kawai sai gani nayi ta miƙe da sauri tare da dirowa daga kan gadon sannan ta sanya hannu ta cisge ledar ruwan da ake ƙaramata ɗin.

Da gudu na ƙarasa wajen ta sannan na fashe da wani irin kuka mai taɓa zuciya.

"Amrah nasan an cuce ki,amma kuma tabbas nima na bada gudummawa wajen faruwar hakan, Amrah nasan abun da aka shirya aikata miki amma na ɓoye ban sanar da ke na bari har maƙiya suka yi galaba a kan ki, Amrah dan Allah ki yafe mun, Amrah zan sanar dake duk wani abu da ya faru da kuma waɗanda suka aikata miki hakan duk da nasan cewar faɗar a yanzu bata da amfani".

Nan na shiga sanarwa da Amrah duk abun da su Azra suka shirya mata tiryan-tiryan ban ɓoyemata komai ba,har na gama sanarwa da Amrah labarin bata ce ƙala ba sai dai irin kallon da take mun kaɗai ya Isa ya fahimtar da kai irin halin da take ciki da kuma cewar tana jin abin da nake faɗa ɗin.

Gani nayi ta sanya hannu ta ture ni gefe sannan ta nufi ƙofar fita daga cikin ɗakin.

Da sauri na sha gaban ta ina cewa.

"Amrah ina zaki?, Amrah dan Allah ki tsaya ki saurareni, Amrah ina miki magana da........."

Kallon da naga Amrah É—in ta watsa mun ne ya sanyani shan jinin jikina sannan na tsinci kaina da jan bakina nayi gum.

Ficewa Amrah tayi daga cikin É—akin sannan ta nufi hanyar barin cikin asibitin, ai ina ganin haka nima na shiga bin bayan ta da sauri da sauri har ina haÉ—awa da É—an gudu.

Har muka bar area É—in Emergency unit É—in bamu haÉ—u da su Anisa ba,balle Dr Gana.

Tun da muka fito daga cikin ɗakin duk inda muka wuce sai an bimu da kallo ganin cewar ƙafafuwan mu ko takalmi babu, ga ko hijab babu a jikina daga ni sai ɗan kwali,ita kuma Amrah da hijabi amma itama ba takalmi a ƙafar ta.

A bakin gate É—in asibitin naga Amrah ta ja tunga ta tsaya,hannu naga ta yiwa wani mai mashin ya tsaya,inda ya iso inda muke É—in ba tare da ta faÉ—a mishi inda zai kaita ba naga ta faÉ—a cikin mashin É—in.

Aikuwa nima ban tsaya wata-wata ba na afka cikin mashin É—in ganin har mai mashin É—in yana shirin tayar da mashin É—in.

Tafiya muka fara yi,inda na cigaba da yiwa Amrah magana amma har a sannan bata juyo ta kalleni ba balle ta tanka mun.

Shima mai mashin É—in sai tambayar mu yake inda zai kaimu amma ba wanda ya bashi amsa.

Mun yi tafiya mai É—an tsaye kafin mu kazo wucewa ta wajen tashar da ake shiga motar garin su Amrah.

"Sauƙeni a nan".

Muka tsinkayi muryar Amrah wadda sai a sannan tayi magana, sai dai jin Muryar tata da nayi sai da ya kusa sanya ni na saki fitsarin da ban yi niyya ba domin kuwa wata irin murya naji daban wadda ban taɓa sanin Amrah ɗin da ita ba.

Tana sauƙa daga cikin mashin ɗin naga ta kama hanyar barin wajen ba tare da ta bawa mai mashin ɗin kuɗi ba

"Hajiya kuÉ—i na?".

Kallon Amrah nayi wadda tayi alamar bata ma san yana magana ba.

Da sauri na juyo na kalle shi sannan nace

"Dan Allah ka jirani zaka mayar damu zan baka kuÉ—in".

Ban jira naji abun da zai faɗa ba,na bi bayan Amrah da gudu wadda naga ta nufi wata mota da naji ana ta ƙiran.

"Giwa! Giwa! Giwa! Saura mutum É—aya".

Daf da zata shiga motar na riƙo hannunta sannan nace.

"Amrah dan Allah ina zaki?, Sai magana nake kin shareni?".

Sai a sannan Amrah ta juyo ta kalleni sannan tace.

"Zan tafi gida,amma ina son na baki saƙo ki sanarwa su Azra cewar kar suga sun yi galaba a kaina a yanzu,to wallahi ba galaba suka yi ba faɗuwa suka yi,kuma ki sanar dasu cewa su tsoraci ranar da zan waiwayo gare su, sai na jefa rayuwar su a cikin uƙuba, uƙuba mafi muni,yanzu wasan zai fara".

Har ta fara tafiya kuma sai ta juyo ta dubeni sannan ta buɗe baki cikin shaƙewar murya ta cigaba da magana.

"Amira kin san irin tashin hankalin da na shiga dalili wannan videon da aka mun aka sakar a duniya?, A dalilin haka har yau ƴan gidan mu ba wanda yake ɗaga ƙiran wayana,a dalilin haka ya sanya iyayena da suke ji dani suka juya mun baya domin kuwa tun ranar da abun ya faru har kawo yau ba wanda ya amsa ƙiran wayata a cikin ƴan gidan mu ke daga ƙarshe ma idan na ƙira wayar ma bana samu,a yanzu haka fargabar abun da zanje na tarar nake a gidan namu. A dalilin haka saurayina wanda zan aura shima har yau ban sake samun wayar shi ba,nasan cewar na rasashi rasawa ta har abada. Shin kina ganin ya dace na ƙyale waɗanda suka zama silar tarwatsewar farin cikina?, Shin kina ganin ya dace na bar mutanen da suka yi sanadiyar tarwatsewar burina dana daɗe ina son ya cika?, Wallahi ko wana irin hukunci zan ɗauka a kan su ba zan taɓa goge tabon da suka mun a zuciyata ba,domin kuwa sun mun tabon da har yauma taƙummu Sa'a ba zai goge ba,sun bar wa zuciyata ciwon da mutuwa ce kaɗai zata zama maganin shi".

Tana kaiwa nan a zancen nata ta shige cikin motar ta bar ni tsaye kamar an dasa bishiya.

Ina tsaye a wajen kamar yadda Amrah ta barni har motar su ta tashi ban motsa ba,ta gabana motar ta zo wucewa in da Amrah ta leƙo ta window da idanunta da suka yi jawur sannan tace cikin ɗaga murya.

"FANSA! FANSA! FANSA! su jira dawowa ta ɗaukar FANSAAAAAAAAAA domin kuwa zan wulaƙanta maciya amana zan tozara su,dan illata rayuwar su illa mafi muni,idan har ban yi haka to ba zan taɓa yafewa kaina, ko na mutu sai ruhina ya dawo ya wanzu a doron ƙasa ya ɗauki Fansa,domin kuwa ba zan taɓa samun kwanciyar hankali ba matuƙar na tuna cewar maƙiyana suna rayuwa a doron ƙasa kuma cikin kwanciyar hankali".

******

Yau kwanan Anwar Uku a gadon asibiti ba tare da ya san inda kan shi yake ba.

Mahaifiyar shi ce zaune a gefen shi tayi tagumi idanunta in banda tsiyayar hawaye ba abun da suke domin kuwa tun ranar da Anwar É—in ya faÉ—i tayi sallama da farin ciki inda ta É—aura abota da kuka.

Kamar an ce ta juya ta kalli inda Anwar É—in yake kawai taga ta fara motsi da hannun shi alamar zai farka.

Da sauri ta tashi sannan ta nufi kan shi tana ƙiran sunan shi amma kafin ta ƙarasa gadon nashi taji ya saki wata razannanniyyar ƙara sannan ya shiga ƙiran sunan Amrah inda gaba ɗaya sai da ɗakin ya amsa.

Wata irin jijjiga Anwar É—in ya shiga yi kamar yadda mata masu borin haihuwa suke yi,haka ya shiga daddatse bakin shi gadon da yake kai kuwa take shima ya shiga wata irin karkarwa.

Kan kace mai Anwar ya sanya hannu ya fige robar ƙarin ruwan da ake masa ɗin inda ya shiga ƙoƙarin miƙewa tsaye daga kwancen da yake ɗin.

Shigowar likitoci cikin ɗakin da gudu ne suka danne shi tare da hanashi miƙewar sai dai har a wannan lokacin bai daina ambatar sunan Amrah ba.

Duk yadda likitocin suka so su hana Anwar ɗin tashi amma abun ya gagara haka ya dinga jifa dasu inda ya miƙe kamar wani namijin zaki ya diro daga kan gadon.

*MANGA* ✍️
_Comment_
_Share_
_Fisabillillahi_ .

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_💀☠️ ).

_Tsarawa/Rubutawa_

*© SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S* *ASSOCIATION*

*SADAUKARWA* : _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai_ _muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi._

*Free book*

------------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*024*
______________________________

Har motar su Amrah ta ƙulewa ganina ban motsa daga inda nake tsayen ba,mamaki,tsoro,Ruɗani da kuma tashin hankali ne suka ziyarce ni a lokaci guda.

Ban san adadin lokacin dana É—auka a tsaye a wajen ba har sai da na tsinkayi muryar mai mashin É—in dana bari a tsaye yana mun magana cikin fushi.

"Wai ke Malama wannan wana irin rashin mutunci ne tun ɗazu kin barni a tsaye ina jiran ki kamar wanda kika ajiye bawan ki,sannan tsabar rashin mutunci nazo ina miki magana shine zaki mun shiru kin maida ni mahaukaci ina ta ɓaɓatu ni a kaɗai mutane sai kallo na suke".

Sai a sannan nayi saurin motsawa sakamakon dirar maganar mai mashin ɗin a cikin kunnuwa na da naji,haƙuri na bashi sannan na shiga cikin mashin ɗin muka kama hanyar komawa Kallo ɗaya zaka mun ka fahimci cewa bana cikin nutsuwa ta.

ÆŠago da jajayen idanun ta Amira tayi ta kai duban ta ga mutanen da suke cikin police station É—in wanda sun ci kuka har sun gode Allah, shikuwa Anwar ba'a magana.

Ganin Amira É—in tayi shiru ne ya sanya Inspector Rasheed saurin kallon ta da rinnannun idanun da suka zama kamar gauta saboda ja shi sannan yace.

"Ya zaki katse labari a dai-dai gaɓar da kowa ya matsu yaji ƙarshen labarin,muka jure jin na baya ma balle yanzu da burin kowa bai wuce ya ji yadda ɗaukar Fansar ta fara ba,dan Allah kiyi gaggawar sanar damu mai ya faru da Amrah?, Ya aka yi ta mutu?, Sannan ya aka yi ta fara ɗaukar Fansar?".

Murmushin takaici Amira tayi sannan ta kalli Justice Kabir wanda har a wannan lokacin bai É—ago kan shi ba balle ya iya haÉ—a ido da ita,bata san a wana hali zuciyar shi take ciki ba,amma alamu sun nuna yana cikin matsananciyar kunya da kuma nadama.

"Kun san wani abun mamaki?, A mafarki na Amrah take zuwar mun ta sanar dani duk wani abu da ya faru da ita a lokacin da ta bar makaranta ta koma gidan su,duk wani abu da Amrah zata aikata sai ta zo mun a mafarki ta sanar dani hatta kisan da zata fara yiwa su Azra kaf sai da ta bayyana mun a cikin mafarki na".

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.