Complete Hausa Novels

Fansar Fatalwa Book 1 Complete Hausa Novel

Reading file: FANSAR FATALWA.txt

Chapter 2 of 2

Cigaba da ba wa Æ´an wajen labari Amira ta yi, ga Æ´an jarida da suka kafa kyamarorin su suna É—aukar rohotonni burin su kawai a kammalla labarin su je su sanya a tashoshin su.

Lokacin da Amrah suka kama hanyar garin Giwa har suka isa cikin garin bata tankawa kowa a cikin motar ba haka take zaune gata-gata nan kamar wadda aka dasa ta.

A haka har suka ƙarasa garin su Amrah ɗin,a bakin kasuwa mai motar ya sauƙeta sannan ta fito daga cikin motar ta fara tafiya.

Cikin sauri Condastan motar ya fito tare da shan gaban ta sannan yace.

"Malama ya haka baki bamu kuÉ—in motar mu ba zaki kama hanya ki tafi".

Ko kallon inda yake Amrah bata yi ta juya ta ci gaba da tafiya,hijab É—in ta ya kama sannan yace.

"Ke dalla Malama ki bamu kuÉ—in mu wannan ai iskanci ne,ina miki magana kuma kina cigaba da tafiya, idan baki da kuÉ—i sai ki faÉ—a mana ai kin saba tallan kanki sai ki bamu abun da kika tallatawa duniya mu kwashi na kuÉ—in mu,tun da daman Æ´ar yawon ta zubar ne".

Cak Amrah taja ta tsaya a lokacin da kalmomin bakin Condastan suka daki dodon kunnen ta,a hankali ta shiga juyowa sannan ta kafe shi da ido take idanunta suka kaÉ—a suka yi jawur sai dai a maimakon su ga hawaye a idanun Amrah É—in kawai sai gani suka yi ta bushe wata irin mahaukaciyar dariya tun abin yana bawa mutanen wajen mamaki har ya koma basu tsoro ganin irin dariyar da Amrah É—in take wadda batayi kama da ta masu hankali ba.

Hannun Condastan da ya riƙe mata hijabi ta kalla sannan a hankali ba tare da ce komai ba ta sanya hannu ta cire hannun shi daga jikin hijab ɗin nata sannan ta ƙara juyawa ta cigaba da tafiya har a wannan lokacin bata daina dariyar da take ɗin ba.

Mutane kuwa take aka shiga bin ta da kallo ganin alamun hauka tuburan sun bayyana a tare da ita, ga wuyan hijab a kafaɗa ga ƙafa ba takalmi,ga dariyar da take ita kaɗai.

Haka ta cigaba da tafiya tana ratsa unguwanni duk da irin nisan da unguwar ta su take da ita daga kasuwar zuwa gidan su tafiya ce tuƙuru amma haka Amrah ta yi ta kurɗawa ko a jikin ta.

Sai dai duk inda ta wuce sai mutane su shiga nunata suna aibatata wasu kuwa har madalla suke cewa suna addu'ar Allah yasa ma ta haukace É—in ne da gaske.

A lokacin da Amrah ta sanya ƙafar ta a cikin unguwar su taga tsananin tashin hankali domin kuwa kafin ta isa cikin unguwar ashe har an samu irin tsagerun matasan nan an sanar dasu cewar ga Amrah ɗin ta iso,inda su kuma suka haɗa kwambar yara waje guda tana sanya ƙafarta a cikin unguwar ruwan duwatsu suka fara mata maraba,sauƙar duwatsu kawai take ji ta ko ina.

Mutane suna kallo amma aka rasa samun na ƙwarai mutum ɗaya da zai tsawatar musu ya kuma nuna musu rashin dacewar abun da suke aikatawa ɗin.

Amrah kuwa ko gizau bata yi ba haka ta cigaba da tafiya duk irin sauƙar duwatsun da take ji a jikin ta bata yi ƙoƙarin guduwa ba balle ta nemi mafaka ko ta yi yunƙurin kare kanta.

Daf da tazo zata shiga gida kawai taji sauƙar wani ƙaton dutse a kan ta wanda yayi sanadiyar fashewar kan nata,ji tayi hawaye yana shirin zubo mata amma ta daure domin kuwa alƙawari ta ɗaukar wa kan ta har ta koma ga mahaliccin ta ba zata ƙara zubar da ruwan hawaye ba akan abin da su Azra ɗin suka mata ɗin.

"Kar ki kuskura ki shigar mana gida, ki kama hanya ki koma inda kika fito domin kuwa mun daÉ—e da sallama ki a duniya a yanzu baki da wani amfani a wajen mu da ke da mattaciyyar gawa duk matsayin ku É—aya a wajen mu".

Amrah ta tsinkayi muryar ya Hisham a dai-dai sanda take ƙoƙarin sanya ƙafarta a cikin zauren gidan nasu.

A hankali ta shiga juyawa tana jin maganganun Ya Hisham ɗin suna mata dakan lugude a ƙasan zuciyarta.

Wani irin sarawa kan ta ya mata a lokacin da ta juya suka yi arba da ya Hisham É—in a tsaye a É—an nesa kaÉ—an da ita yana aika mata wani irin kallo mai cike da tsantsar tsana.

A hankali ya shiga takowa har ya ƙaraso inda take sannan ya cigaba da magana.

"Ko baki ji abun da nace miki bane ba,na rantse da girman Allah idan har ƙafar ki ta taka cikin gidan nan sai dai a fito da gawar ki daga cikin gidan, idan kuma ba'a fito da gawar ki ba to tabbas zan miki illa illar da sai kin gwammace mutuwar ki fiye da rayuwar ki, Tun da ke kin zama mugun iri".

*****

Anwar fa lamarin shi ya ta'azzara domin kuwa hauka yake tuburan yana buge-buge.

Ƙoƙarin ficewa yake son yi daga cikin ɗakin amma haka likitocin nan suka sake tasowa suka mishi rub dugu suka danneshi in da aka samu ɗaya daga cikin su ya danna mishi allurar bacci.

Abin mamaki da tashin hankali a maimakon su ga Anwar ɗin yayi relax kawai sai ji suka yi kamar allurar ma wani ƙarfi ta ƙara mishi, domin kuwa haka ya dinga jifa da su yana son sai ya fice a cikin ɗakin bakin shi kuwa bai daina ƙiran sunan Amrah.

Ganin cewa idan har aka kuskura aka bar Anwar É—in ya fita to tabbas za'a samu matsala gaggaruma.

"Anwar ka yiwa girman Allah ka dakata da duk wannan abin da kake yi ɗin, nasan wallahi ƙarya ne da hankalin ka baka haukace ba".

Turus Anwar ɗin ya ja ya tsaya har ya kama handle ɗin ƙofar zai buɗe sakamakon Muryar mahaifiyar shi da ya ji ta mishi magana cikin kuka.

Wasu hawaye ne masu zafi suka shiga zarya a kan kumatun Anwar ɗin a hankali kuma ya shiga sulalewa a jikin ƙofar har ya kai ƙasa.

Wani irin kuka mai cin rai ya fashe dashi sannan ya juya ya dubi mahaifiyar shi da ƙarasowar ta wajen Kennan yace.

"Mama da gaske ne wai videon tsaraicin Amrahn da zan aura na gani yana yawo a social media?, Mama dan Allah ki ce dani bacci nake Mama ki ce dani mafarki nake duk abun da nagani ba gaskiya bane?, Mama wallahi idan har ya tabbata Amrah ce wannan to wallahi mutuwa zan yi domin kuwa ba zan iya rayuwa a duniya ba a yanzu haka ina jin zuciyata kamar zata tarwatse saboda baƙin cikin da nake ciki, Mama in.........".

Maganar Anwar ɗin ce ta katse sakamakon wani uban kuka da ya shaƙeshi, take kuma ya fara wani irin tari ba ƙaƙƙautawa,wani irin baƙin jini ne ya shiga fitowa daga cikin bakin shi inda da gudu likitocin suka yo kan shi ganin idanun shi ya shiga ƙaƙƙafewa.

Kafin su ƙaraso har ya tafi ƙasa ko shurawa bai yi ba.

Wata ƙara mahaifiyar Anwar ɗin ta sake tare da rungumo Anwar ɗin tana ihu.

Da ƙyar likitocin suka samu suka ɓanɓare Anwar ɗin a jikin ta,kafin su duƙufa a kan shi domin bashi agajin gaggawa cikin tsananin tausayin halin da Anwar ɗin yake ciki a wani ɓangaren kuma tausayin mahaifiyar ta shine da fargaba suka dirar mu su domin kuwa suna gudun kar mai afkuwa ta afku,tun da gashi dai rayuwar Anwar ɗin tana cikin tsaka mai wuya

Da gudu mahaifiyar Anwar ɗin ta tashi tare da yin waje a matuƙar gigice, a bakin ƙofa suka kusa yin karo da Nazir wanda ƙarasowar shi asibitin Kennan.

Cikin sauri ya ruƙota ganin kamar mahaifiyar ta su bata hayyacin ta sannan ya shiga tambayar ta.

"Mama ina zaki je kuma mai yake faruwa naga kamar hankalin ki a tashe ya jikin yaya Anwar É—in".

Duk a lokaci guda Nazir ya jefawa mahaifiyar ta su waÉ—annan tambayoyin.

"Nazir gidan su wancan karuwar yarinyar zan je, tsinnanniya wadda take son taga mun Bayan yaro,na rantse da girman Allah ba abun da zai hana yau ban aika yarinyar nan lahira ba,daga ita har munafukan iyayen nata,matuƙar kuwa Anwar ya mutu sai na ƙarar da duk dangin su dan wallahi sai na sa an kulle kaf dangin ta a prison kullewa ta har abada".

Mahaifiyar Anwar É—in tana kaiwa nan a zancen ta ta juya ta kwashi uban sauri ta nufi hanyar barin asibitin domin zuwa gidan su Amrah.

Da sauri shima Nazir ya bi bayan ta cikin tashin hankali domin ya riga da ya san wacece mahaifiyar ta su matuƙar fa ta faɗi abu to tabbas sai ta aikata sannan kuma ba wanda ya isa ya dakatar da ita.

*MANGA* ✍️
Follow my account at Whattpad @Shamsiyyamanga, Arewa books@shamsiyyamanga.
Comment
Share
Fisabillillahi.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_💀☠️).

_Tsarawa/Rubutawa_

*© SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S* *ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_.

*Free book*

------------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani* *rahim*

*025*
_______________________________

Wasu Hawaye masu zafi ne suka shiga kwarara a kan kuncin Amrah É—in duk yadda ta so ta daure kar ta kayi kuka amma abun ya ci tura sakamakon jin kalaman Yaya Hisham É—in.

Durƙushewa Amrah tayi a bakin ƙofar gidan na su tare da fashewa da wani irin kuka mai sauti,zuciyarta ce taji tana mata barazanar fashewa,dafe ƙirjin ta tayi sannan ta shiga wani irin tari ba ƙaƙƙautawa har tana shiɗewa.

A wannan lokacin duk yadda Yaya Hisham É—in ya so ya kawar da kan shi akan Amrah É—in abun ya gagara wani matsanancin tausayin ta ne ya rufe shi a take soyayyar Æ´anuwantaka ta motsa Allah sarki naka naka ne koda kuwa faÉ—a ku ke kullum to in har zai shiga wani yanayi sai kaji a jikin ka.

Ganin irin tarin da Amrah ɗin take ne ya sanya Yaya Hisham saurin ƙarasawa kan ta,tare da ruƙo ta yana ƙiran sunan ta.

Ɗago da kumburarriyar fuskar ta Amrah ta yi sannan ta sakarwa Yaya Hisham ɗin murmushi kafin kuma ta buɗi baki da ƙyar ta fara magana.

"Yaya Hisham kaima ka yarda da abun da mutane suke zargin na aikata ko?, Yaya Hisham kaima baya zaka juya mun kamar yadda kowa ya juya mu?, Yaya Hisham a makaranta kowa ya tsaneni,Yaya Hisham a makaranta kowa ya juya mun baya,ban isa na fita ba sai zagi sai hantara,Yaya Hisham ina jin zuciyata kamar zata fashe. A tunanina idan kowa ya juya mun baya Yaya Hisham ku bazaku juya mun ba,Yaya Hisham hannun ka ba zai taɓa ruɓewa ka yanke ka yasar ba".

Shiru ta yi tare da sanya hannu ta goge jinin da yake fita ta bakin ta a fakaice ba tare da Yaya Hisham É—in ya lura ba,sannan ta kalle shi ido cikin ido kafin ta sakar mishi wani murmushi marar fassaruwa wanda ita kaÉ—ai ta san ma'anar shi kafin kuma ta cigaba da magana.

"Hmmm Yaya Hisham bai kamata kayi saurin yanke hukunci a kaina ba domin kuwa nasan kafi kowa sanin halina da kuma abin da zan aikata da wanda ba zan aikata ba,Duk da cewar shi ɗan Adam a kowane lokaci ya kan iya sanjawa sannan ya rikiɗe amma wallahi Yaya Hisham wallahi ƙarya su ke mun ban aikata ba,Yaya Hisham meyasa ka kasa mun adalci a yanzu rarrashi nake buƙata ba a ƙara haɗamun wani zafin ba.Amma Bakomai Yaya Hisham kamar yadda ka buƙata zan tafi zan bar ku in sha Allah zan bar ku bari na har abada zan tafi ba zan sake waiwaiyar ku ba,ba zan shiga cikin gidan nan ba kamar yadda ka buƙata idan kuma kaga na shiga to sai dai idan gawata za'a shigar,Daga ƙarshe zan roƙi wata alfarma a wajen ka wadda nasan da wuya ka iya mun amma Yaya Hisham dan Allah ba dan ni ba ba kuma dan halina ba ka roƙar mun Abba ya yafe mun nasan ba lalle mu sake haɗuwa ba wataƙila sai dai a lahira,sannan dan Allah ka kuma sanar dashi cewar ban aikata abun da ake iƙirarin na aikata ɗin ba wallahi sharri aka mun,dan Allah ku ma ku yaf..........".

Kasa ƙarasa maganar da take bakin nata tayi sakamakon wani tari da yaci ƙarfin ta nan fa ta shiga yi ba ƙaƙƙautawa in da lokaci guda kuma wasu irin gudan jinnannaki suka shiga fitowa ta cikin bakin nata.

A dai-dai wannan lokacin kuma Gwaggo Sa'adatu ta fito daga cikin gidan tare da Umar sakamakon Muryar Amrah ɗin da suka ji da kuma tarin nata da yaƙi tsayawa.

Fitowar su Gwaggo Sa'adatu É—in yayi dai-dai da tsayawar numfashin Amrah ciÉ—ak take duk wata jijiyar da take harbawa a jikin ta ta daina harbawa,sai dai har a sannan gudan jini bai bar fitowa ta bakin ta ba.

Da gudu Gwaggo Sa'adatu ta ƙarasa kan ta tare da rungumota tana fashewa da wani irin matsanancin kuka, Umar take ya shiga maimaita innalillahi wa'innailaihi rajiun.

Shi kuwa Hisham ja da baya ya fara yi tare da fara jijjiga kan shi yana jin kan nashi kamar zai bar jikin wuyan shi,durƙushewa yayi a wajen tare da ɗaura hannun shi a ka ya fasa wata ƙara.

"Nooooooo Amrah,dan Allah ki taimaka ki tashi,wallahi ƙarya nake miki ba zan iya juya miki baya ba,Amrah ki taimaka ki tashi kar ki tafi ki bar mu,Amrah wallahi muna son ki kawai d.........".

Shima kasa ƙarasa maganar da yake ɗin yayi sakamakon wani kuka da yaci ƙarfin shi,take kuma komai na jikin shi ya tsaya cak sai numfashin da yake ne kaɗai zai tabbatar maka da cewar yana da rai.

Umar ne kawai ya iya ƙarfin halin sunkuyawa ya ɗauki Amrah ɗin tare nufar bakin titi da ita domin ya samu mota ya sanyata a ciki ya kaita asibiti ko akwai taimakon da za'a yi musu.

Suma su Gwaggo Sa'adatu da Malam Kabiru haka suka bi bayan Umar É—in dukan su kamar wasu zarrarru.

Da ƙyar suka iya samun mota a bakin titin inda aka sanya Amrah a ciki aka nufi asibiti da ita.

Suna barin wajen motar su Nazir da Mahaifiyar su tana shigowa cikin layin inda ko bari ba tayi Nazir É—in ya gama parking ba ta fito daga cikin motar saboda tsabar bala'in da yake cinta.

Kai tsaye cikin gidan ta nufa tun daga zauren gidan ta fara surfa ruwan bala'i a tunanin ta gidan da mutane,sai dai shirun da taji ba wanda ya tanka mata ne ya bata tabbacin cewa gidan ba kowa.

Kasancewar bata san Hisham ba shiyasa bata lura dashi ba da yake zaune a wajen da ya fadi tun É—azun ya kasa motsawa.

Shi kuwa Malam Kabiru yana kwance a cikin ɗaki yana jin duk tijarar da mahaifiyar Anwar ɗin take yi,sai dai kasancewar tun bayan labarin da ya riske shi game da abun da Amrah ɗin ta aikata ya zamana ya koma kamar mutum-mutumi komai nashi ya daina aiki sai dai a ɗaga a tayar a kwantar,hatta wanka da alawla da duk wani abu da mai lafiya zai yi to shi sai dai a mishi,idon shi ne kawai yake aiki amma hatta magana ya daina yi,fitsari kuwa da bayan gari ba'a magana haka yake yi a jikin shi. Wannan yana daga cikin babban dalilin da ya sanya Hisham ya ƙara jin ya tsani Amrah saboda shi a ganin shi a sanadiyar Amrah mahaifin su ya haɗu da jinya.

Lokacin da Su Umar suka ƙarasa asibiti sun tarar da layi sosai gashi sai ma'aikatan suka ce lalle sai sun nemo kati kafin a karɓi Amrah ɗin,da ƙyar dai wani babban likita ya ce a shiga da Amrah ɗin domin shi a kallo ɗaya ma da ya mata ya fahimci cewa ta daɗe da rasuwa.

Su kuwa su Umar ba su fahimci komai ba kasancewar basa cikin nutsuwar su.

Wani É—aki aka shiga da Amrah É—in inda likitan ya fara duba ta aikuwa hasasshen shi ya tabbata domin kuwa duk wani bincike da yayi a kan Amrah É—in ya yi inda ya tabbatar da cewa Amrah É—in ta riga mu gidan gaskiya.

Jikin likitan gaba ɗaya a mace ya fito daga cikin ɗakin da Amrah ɗin take bayan yasa an rufe ta da farin ƙyalle.

Ganin fitowar likitan da su Gwaggo Sa'adatu suka gani ya sanya suka tare shi cikin matuƙar tashin hankali inda suka fara tambayar shi.

"Likita ya Amrah É—in take?,Dan Allah zamu iya shiga mu ganta?,Amma dai ta farfaÉ—o ko?".

Gwaggo Sa'adatu ta jefawa likitan waÉ—annan tambayoyin gaba É—aya a lokaci guda jikin ta in banda rawa ba abun da yake domin kuwa tun daga fitowar likitan daga cikin É—akin da Amrah É—in take jikin ta ya bata wani abu ya samu Amrah É—in.

Kallon su likitan yayi cikin matuƙar tausayawa tare da jin nauyin sanar da su mutuwar Amrah ɗin domin idan da ba dan ya zama dole ba sanarwar da ba abun da zaisa ya faɗa musu,duba da yadda alamu suka nuna tsananin shaƙuwar dake tsakanin ahalin,haka dai ya daure ya dube su sannan yace.

"Hajiya ku yi haƙuri kun san cewar daman rai baƙon duniya ne,kuma dukan mu ba wanda ya zo duniya domin yayi gadin ta,yadda muka zo haka zamu barta,Rayuwa ƙarya ce mutuwa kuma gaskiya ce da.......

"Kaga Likita ka tafi kai tsaye zuwa inda ka ke son tafiya ka faÉ—a mana ya marar lafiyar mu take,kunnuwan mu sun gaji da jin wannan dogon sharhin da kake mana".

Umar ya tari numfashin likitan cikin matsanancin faÉ—uwar gaba.

"Ku yi haƙuri Allah ya yiwa marar lafiyar ku Rasuwa domin kuwa zuwan ku da ita asibitin ma tunin ta daɗe da rasuwa sakamakon bugawar da zuciyarta tayi,dan haka ku........".

Ai bai ƙarasa maganar da yake ɗin ba suka ga Gwaggo Sa'adatu ta faɗi rigijib a ƙasa.

Shi kuwa Umar Wata irin shaƙa ya kaiwa likitan tare da gwara kan shi da jikin gini sannan ya fara magana ko lura da halin da Gwaggo Sa'adatu ɗin take ciki bai yi.

"Na rantse da Allah ƙarya kake da zaka wani zo ka tare mu kana sanar damu cewar ƙanwa ta ta rasu,sai dai idan kai kaine ka kashe ta,wallahi baka isa ba yadda ka kashe mun ƴaruwa kaima sai na kashe ka".

Da gudu sauran ma'aikatan asibitin suka nufo kan Umar inda da ƙyar suka ɓanɓare hannun Umar ɗin daga jikin wuyan likitan sakamakon shaƙar da ya mishi ɗin bata wasa ba ce har sai da idanun likitan ya fara fitowa waje.

Ana ƙwace likitan daga hannun Umar ɗin,ya juya da gudu ya nufi kan Gwaggo Sa'adatu yana ƙiran sunan ta tare da zubewa a kan ta ya ɗago ta sannan ya rungumeta tsam a ƙirjn shi tare da sakin wani irin kuka wanda kaf mutanen wajen sai da suka ji tausayin Umar ɗin.

Innalillahi wa'innailaihi rajiun,kullu nafsin za'iƙatul maut, shikennan rayuwar Kennan Amrah ta rasu ta bar wa su Azra duniyar sai mu gani ko su zasu zauna su yi gadin duniyar ne ohoooo😰😰😰😰😰😰😰.

_Yau Ban wani a gida ba wallahi aiki ya mun yawa ban iya muku typing da yawa ba,ga page ɗin yau_ _ɗin da ƙyar na iya ƙarasa muku shi saboda gaba ɗaya maganganun Amrah da suka taɓa_ _mun zuciya_ _ga mutuwar_ _ta_ 😰😭😭😭.

Pls Follow my account .
Whattpad @shamsiyyamanga.
Arewa books@shamsiyamanga.
Comment
Share
Fisabillillah.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_💀☠️).

_Tsarawa/Rubutawa_

© *SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D auta, Sis Amira Adam, Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_.

*Free book*

-----------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*026*
______________________________

A can gidan su Amrah kuwa waje mahaifiyar Anwar ta nema ta zauna a cewar ta ba zata bar gidan ba har sai ta jira taga dawowar Æ´an gidan dan yau sai Amrah ta gwammace kiÉ—a da karatu.

Ta É—auki tsawon lokaci a zaune a cikin gidan domin kuwa sai da ta shafe fiye da awa a zaune a tsakar gidan ba Amrah ba labarin wani nata.

Nazir kuwa yana cikin mota yana zaune yana ganin ikon Allah yana kuma jiran ya ga sai yaushe mahaifiyar ta su zata fito daga cikin gidan.

Gajiya yayi da zama ganin shirun yayi yawa ya sanya shi ya fara tunanin ko ba lafiya ba,fitowa yayi daga cikin motar sannan ya nufi hanyar shiga cikin gidan su Amrah É—in.

Daf da zai shiga cikin gidan ya ji tsayuwar a daidaita shahu a bayan shi ,juyawa yayi sannan ya dubi bayan nashi dan ganin su waye a motar.

Daram ya ji gaban shi ya buga sakamakon tozali da yayi da yayun Amrah Umar da Usman sun fito daga cikin motar kallo ɗaya zaka musu ka fahimci cewa basa cikin nutsuwar su ga idanun su da suka kaɗa suka yi jawur kamar garwashin wuta alamun dai sun sha kuka, bayan sun gama fitowa daga cikin motar ne suka zagaya da driver ɗin motar da ya kawo su suka buɗe boot ɗin motar inda suka fito da gawar Amrah wadda take nannaɗe a cikin wani farin ƙyale wanda kallo ɗaya zaka yi ka gane cewar likkafani ne gaba ɗaya jikin Amrah ɗin a nannaɗe yake a cikin likkafani ɗin sai fuskar ta ce kawai a waje wadda ta ƙara kyau ga wani sheƙi da goshin ta yake yi kamar kace Amrah ta amsa ba zaka taɓa mata kallo ɗaya kace macacciya ba ce ba idan har ba faɗa ma aka yi ba.

Tun da aka fito da Amrah daga cikin motar jikin Nazir yayi sanyi domin kuwa ya tabbatar da cewa ba lafiya ba.

Shi kuwa Ya Hisham da yake zaune tun ɗazu kamar mutum-mutumi ji yayi yana son ya miƙe tsaye amma abun ya gagara domin kuwa ji yayi kamar an sanya igiya an ɗaure mishi duk wata jijiyar gudanar da aiki ta jikin shi,wata irin zuffa ce ta shiga kwaranyowa ta duk wani sashi na jikin shi,gashi dai a haka a zahiri rayayye ne amma kuma fa a baɗani Hisham ya daɗe da mutuwa.

Gwaggo Sa'adatu ce ta fito daga ɗayan ɓangaren na cikin motar Usman ne yayi saurin zagayowa ya riƙe ta ganin tana shirin faɗuwa sakamakon wani jiri da yake son kwasar ta, inda shi kuma Umar suka nufi cikin gidan da gawar Amrah ɗin a hannun su shi da drivern da ya kawo su ɗin da kuma wani mutum da ban san ko waye ba.

Daga Umar har Usman ba wanda ya lura da Ya Hisham É—in da kuma halin da yake ciki É—in ba lalle wani yaje ya kai mishi É—auki.

Ta gaban Nazir aka zo wucewa da Amrah aka shiga cikin gidan da ita da mugun sauri Nazir ya bi bayan su,a zauren gidan suka ci karo da mahaifiyar Anwar da take shirin fitowa sakamakon ƙarar motar da taji.

"Yawwa daman yau nace ko kwana zan yi a cikin gidan nan sai.........".

Maganar ta ta ce ta katse sakamakon ganin Amrah da tayi a cikin likkafani ga kuma su Umar É—in da fuskokin su gaba É—aya ba walwala.

Wani matsanancin bugawa ƙirjin ta yayi a lokaci guda kuma ta kai duban ta kan Nazir da ya shigo cikin gidan a yanzu ya biyo bayan su Amrah ɗin,da sauri kuma ta ƙara kai duban ta kan gawar Amrah da kuma mutanen da suka shigo da ita ɗin a lokaci guda kuma ta ƙare kai duban ta kan Gwaggo Sa'adatu da Usman wadda kallo ɗaya zaka mata ka fahimci yadda ta ci kuka har ta gode Allah.

Ba wanda ya kula ta ba kuma wanda ya tanka mata aka wuce da Amrah ɗin ciki, gani tayi Nazir ma yana ƙoƙarin wuce ta ba tare da ya tanka mata ba.

"Kai Nazir wai Meye yake faruwa ne?, Meye idanuna suke gane mun?, Ko dai gizo suke mun ne?".

Mahaifiyar Anwar É—in ta faÉ—a tana janyo hannun rigar Nazir É—in tare da Zaro ido waje.

ÆŠaga mata kafaÉ—a Nazir É—in yayi alamar shima bai sani ba domin kuwa a lokacin da za'a tsaga jikin Nazir É—in to tabbas ba za'a tarar da jini ba Saboda irin tsananin tsoro da kuma tashin da yake ciki É—in.

Cikin gidan ya shiga inda ita ma mahaifiyar Anwar É—in ta bi bayan shi a ranta tana addu'ar Allah yasa ba gawar Amrah ba ce ba wannan.

"Yanzu abin da za'a yi Usman zamu je a sanar da massallaci mutuwar Amrah ɗin sannan a yi sanarwar jana'izar ta ta nan da zuwa ƙarfe huɗu sai a sallace ta a kaita makwancin ta ko?".

Wannan drivern motar da ya kawo su Usman ɗin ya faɗa wanda har zuwa yanzu ban san waye shi ba,ban kuma san alaƙar da take tsakanin su da su Usman ɗin ba sai dai ga dukkan alamu akwai alaƙa a tsakanin su ganin yadda ya shige musu gaba tun daga asibiti aka bada gawar Amrah ɗin har taimaka musu da yayi a lokacin da Gwaggo Sa'adatu ta suma aka samu ta farfaɗo sannan kuma shi ya je ya ɗakko Usman tare da sanar dashi mutuwar Amrah ɗin har ya kawo shi asibitin suka ɗakko su Umar da Amrah ɗin wadda take gawa a a yanzu.

Kai kawai Usman É—in ya iya É—aga mishi sannan ya juya ya bi bayan shi.

Tabbas i zuwa wannan lokacin ya kamata a ce Mahaifiyar Anwar ta fahimci abun da yake faruwa É—in,amma saboda tsananin ruÉ—ewa da tayi ta kasa gane komai sai ma wajen Umar da ta nufa da kuma gwaggo Sa'adatu ta shiga tambayar su.

"Dan Allah ina buƙatar ƙarin bayani dan Allah mai yake faruwa ne a gidan nan?, Sa'adatu wai mai ya samu Amrah ɗin naji ana wani zance da har yanzu na kasa gane inda ya dosa.

Umar ne ya samu damar da kuma ƙoƙarin buɗe baki ya fara magana.

"Amrah ta riga mu gidan gaskiya, Amrah ta tafi ta barmu cikin duniya cike da kewar ta, Amrah ta tafi ta bar duniya a dai-dai lokacin da muka fi buƙatar ta, innalillahi wa'innailaihi rajiun tabbas da ana ƙaryata mutuwa a yau da sai na ƙaryata mutuwar tillon ƙanwata wadda nake matuƙar so nake kuma jin ta har a ƙasan zuciyata,ban san yadda zan kwatanta muku irin ciwon da nake ji a ƙasan zuciyata ba,ban san y..........".

Kukan da ya taso mishi ne ya hana shi ƙarasa maganar da yake ɗin inda ya shiga raira shi kamar wani ƙaramin yaro.

Wani kuka Gwaggo Sa'adatu É—in itama ta fashe dashi mai bala'in cin rai har shiÉ—ewa take sannan ta fara magana.

"Amrah meyasa?,Amrah meyasa?, Amrah kin san ko da kowa zai guje ki ni ba zan taɓa guje miki ba, Amrah tun ranar da na samu labarin abin da aka ce kin aikata Amrah na ƙaryata saboda nasan wallahi ƴata Amrah mai cikakkiyar kunya ba zata taɓa aikata abun da aka ce ba,kullum idan nayi salla goshina baya taɓa ɗagowa daga sujadda face na kai ƙarar duk waɗanda suka aikata miki wannan aika-aikar wajen mai kowa mai komai kuma mai duka,kullum cikin addu'ar Allah ya tona musu asiri nake Amrah amma kin tafi kin barni cike da kewar ki Amrah m..........".

Sai kuma maganar tata ta katse sannan ta tafi luuu ta sume a wajen.

"Innalillahi wa'innailaihi rajiun,la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minna zalumin,yanzu da gaske Amrah ta mutu?, Yanzu da gaske Wannan gawar Amrah ce?".

Wannan shine abin da mahaifiyar Anwar ta shiga maimaitawa.

*****

A can asibiti kuwa lokacin da likitoci suka duƙufa akan Anwar wasu na'urori aka shiga jona mishi ta ko wane sashi na jikin nashi,hanci da bakin shi kuma an jona na'urar taimakawa wajen numfashi ya daidaita watau (OXYGEN).

Likitoci ne sun fi ƙarfin biyar a kan shi kowa da abin da yake yi manyan su da yaran su, ƙoƙarin kowa shine bai wuce a taimak rayuwar Anwar ɗin ba.

Amma sai dai tun suna yin abin iya ƙarfin su har suka fara galabaita Anwar ko shurawa bai yi ba,nan fa hankalin su ya ƙara dugunzuma suka fara tunanin ko ya mutu ne.

Sai dai kuma ganin cewar jijiyar shi tana harbawa sannan ga na'urar da aka jona mishi tana yi wannan shi ya tabbatar musu da cewar yana da rai.

Wani abu suka ɗakko kamar Iron sannan suka shiga danna mishi a jikin shi ana sawa ana cirewa sai ya zabura kamar zai miƙe,duk sawa ɗaya sai ya zubar da shi da haka dai suka samu ya ɗan fara responding amma ba wani sosai ba.

Ganin da suka yi numfashin ya fara daidaituwa ne suka ƙarasa komai sannan suka fita suka bar shi.

Sai dai alamu sun nuna yana cikin halin tsaka mai wuya halin ko a mutu ko a yi rai a kowane lokaci zai iya tashi sannan a kowane lokaci zai iya mutuwa duba da yadda zuciayar shi take bugawa da sauri da sauri.

*****
Lokacin dana koma makaranta na tarar da Anisa da Afrah a bakin Hostel fuskokin su duk alamar tashin hankali ya bayyana.

Ko kallon inda suke ban yi ba na fara ƙoƙarin shigewa cikin Hostel ɗin sai dai da sauri Anisa ta tare ni tana ce mun ina Amrah.

Wani malalacin kallo na wurga mata sannan na juyo na dube su kafin na fara magana.

"Wacece Amrah a wajen ku?, A ina kuka santa?, Mecece alaƙar ku da ita da har zaku tambaye ta?, Lalle na yarda cewar baku da kunya wallahi ko kaɗan, Anisa har kina da bakin da zaki tsaya a gabana kina tambayata ina Amrah cikin nuna damuwa?, Matar da a yanzu ko da mutuwa ta yi ku ne sila ko tantama bana yi. Hmmmm idan ba ku sani ba ku sani Amrah ta bar mu ku cikin makarantar nan sai ku zuba ruwa a ƙasa ku sha,Anisa Afrah Azra wallahi ba zaku gama da duniya lafiya ba,wallahi wallahi mutuwar ku sai ta zama abar kallo,na rantse da Allah rayuwar ku sai ta wulaƙanta fiye da yadda ta Amrah ta wulaƙanta,domin kuwa ita a duniya ne kawai ta wulaƙanta na tabbata a lahira zata samu kyakkyawan sakamako, amma ku kuwa ina tausayin ku a nan duniya da kuma abin da zaku tarar a lahira".

Ɗan shiru na yi tare da sanya hannu na na goge hawayen da suka zubo mun sannan na tako a hankali na ƙaraso har gaban su na kalle su ido cikin ido bayan na sako wani murmushi mai cike da ma'anoni sannan na cigaba da magana.

"Albishirin ku Amrah ta bani saƙo tace na sanar da ku tana nan dawowa gare ku,ku tsoroci haɗuwar ku da ita a karo na biyu, domin kuwa haɗuwa ce da ba zata yi kyau ba,haɗuwa ce tsakanin maƙiya guda huɗu".

Kallo ɗaya zaka yiwa su Anisa ka fahimci zallar tashin hankalin da ya ke shimfiɗe a kan fuskokin su sakamakon jin abun da na faɗa ɗin domin kuwa ko da wasa Afrah da Anisa ba su taɓa tunanin cewa na san abin da suka aikata ɗin ba in ka cire Azra.

*****

Wani tashin hankali da ya faru da su Usman a lokacin da suka je suka sanar a massallaci mutuwar Amrah ɗin shine limamin massallacin ya dubi ƙwayar idon Usman ido cikin ido sannan yace mishi sam su basu sallaci gawar fasiƙa ba wadda ta nesan ta kan ta daga rahamar Ubangiji dan haka suma kama hanya tun wuri su bar wajen,ai daman sun san cewa Allah ba zai taɓa barin Amrah ba domin kuwa ba zai taɓa barin ana ɓarna a doron ƙasa ba,har da siffanta Amrah da ƴan wuta baƙaƙen maganganu dai haka wannan limamin yayi ta sukar Amrah da su hadda Malam Kabiru daman shi wannan limamin mai suna Malam Ɗalha abokin Malam Kabiru ne ba wanda bai san irin amintar da take tsakanin su ba domin kuwa tun amintar yarinta ne amma kuma a lokacin da wannan abun ya samu Amrah shine mutum na farko da ya fara sukar Malam Kabiru har ya juya mishi baya sannan ya dinga bi wajen mutane yana ƙara ɓata Malam Kabiru ɗin da haka yayi nasarar cusa tsanar Malam Kabiru da kuma ahalin shi a zukatan mutanen garin,shi daman yana nunawa Malam Kabiru su ne kawai a baki amma a zuciyar shi ba shi da wani buri da ya wuce ya ga ya samu abin da zai durƙusar da sunan Malam Kabiru ɗin ƙasa ta yadda kowa zai juya mishi baya .

Innalillahi wa'innailaihi rajiun tun da Usman yake a faɗin duniya bai taɓa haɗuwa da cin fuska da kuma cin mutunci irin wannan ba. Wannan wana irin tashin hankaline daman haka duniya ta zama? Usman ɗin ya faɗa yana mai dafe kan shi da ya ji yana barazanar tsage mishi.

*Kuyi haƙuri na jina shiru da kuka yi jiya wallahi abubuwa ne suka mun yawa,amma dai gashi yau na yi ƙoƙarin yi muku* *typing, tun da ku ko kara ma ba zaku yiwa Amrah ba ku ce Shamsiyya ki bar typing ɗin nan har sai an gama* *zaman makokin Amrah ku nuna mata ƙauna* 😒😞😞.

Follow my account Whattpad @shamsiyyamanga. Arewa books @shamsiyyamanga.
Whatsapp number
07060943991
Phone call
09065779330.
Comment
Share fisabillillahi .

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_ 💀☠️ ).

*Tsarawa/Rubutawa*

*© SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA* : _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi._

*Free book*

-----------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*027*
_______________________________

Tsananin takaici da baƙin cikin maganganun Malam Ɗalha ɗin ne suka sanya Usman ɗin fara ganin wani dishi-dishi duk irin dauriyar da Usman ɗin ya so yayi a wannan karon abin ya gagara. wasu hawaye ne masu zafi suka fara zarya a kan kuncin nashi gilmawar wasu taurari ya gani a idon nashi kafin kuma daga bisani ya tafi luuu zai faɗi, cikin sauri Wannan mutumin da suka zo tare ya tare shi ganin yana shirin kaiwa ƙasa.

Ƙiran sunan shi mutumin ya shiga yi amma ina! Usman bai san ma yana yi ba gashi dai idon shi biyu yana numfashi yana komai amma kuma ya buɗi baki yayi magana ya kasa.

Haka dai da taimakon wannan mutumin ya kama shi suka nufi hanyar komawa gida.

Wani sabon tashin hankali na biyu da suka je suka tarar a gidan shine sun isa suka samu labari mummuna game da Ya Hisham inda ake sanar da su cewar an wata mota ta taka shi a bakin titi inda ko shurawa bai yi ba shi kuma mai motar da ya buge shi É—in ya tsare bai tsaya ba.

Innalillahi wa'innailaihi rajiun gawa biyu a cikin gida ɗaya a lokaci guda tsayawa kwatanta muku irin tashin hankalin da wannan ahalin suka shiga ɓata lokaci ne,domin kuwa Gwaggo Sa'adatu haka ta dinga suma tana farfaɗowa da an zuba mata ruwa da ta farfaɗo zata sake yankar jiki ta suma,ba wanda ya san adadin suman da tayi.

Kaf cikin su daga Umar har Usman ba wani mai ƙarfin hali kowanne ka ganshi kuka yake wiwi kamar ran sa zai fita.

Nazir kuwa da mahaifiyar su gaba ɗaya suma sai da suka shiga tashin hankali har sai da suka yi hawaye saboda tausayin wannan ahalin, ita kam mahaifiyar Anwar ji ta yi duniyar ma gaba ɗaya ta ishe ta,wannan wace kalar mummunar ƙaddara ce.

Da ƙyar dai aka samu wasu tsirarun mutane da basu fi a ƙirga ba a cikin garin suka zo aka gyara gawar Hisham data Amrah aka fara shirin sallatar su.

Duk wannan abin da yake faruwa Malam Kabiru yana kwance a cikin É—aki yana jin komai wasu hawaye ne masu zafi kawai suke zarya a kuncin shi.

Daf da ana shirin fita da gawar su Amrah ɗin ne aka ga Malam Kabiru ya fito daga cikin ɗakin da yake kwance ɗin kamar ba shine ya taɓa wata jinya ba,sannan a hankali ya nufo wajen da gawar take lulluɓe a cikin likkafani,tsugunawa yayi dai-dai saitin fuskar ta sannan ya buɗe fuskar a hankali ya buɗi baki ya fara magana cikin rawar murya.

"Ubangiji Allah ka ji ƙan wannan baiwa taka,Ya Allah ka sa tayi kyakkyawan ƙarshe,Allah nasan wacece ƴata Amrah na kuma san abin da zata yi da wanda ba zata yi ba ya rabbi samawati Wal ardi ka yafe mata duk wani abu da ta taɓa aikatawa sananne da kuma ɓoyayye,Allah ka haɗa ta da mala'ikun Rahma,Allah ka faɗaɗa mata ƙabarin ta ka yalwata mata shi,Amrah ina miki kyakkyawan zato da samun rahamar Allah domin kuwa ni na daɗe da sanin cewa baki aikata wannan mummunan abun da aka ce kin aikata ba,nasani wallahi ƴata Amrah ba zata taɓa aikata haka ba,ina ma ace kina duniya Amrah ina ma ace sai da muka yi ganawar ƙarshe kafin kika tafi amma ina! Ƙaddara ta riga fata, Amrah in sha Allah maƙiyan ki sai sun kunyata a idon duniya in sha Allah nan da ɗan wani lokaci ƙanƙani nasan gaskiya zata yi halin ta a lokacin da kowa zai so ina ma kina da rai gaskiya ta yi halin ta,wasu kuwa kuka zasu dinga yi da idanun su suna so su nemi yafiyar ki amma lokaci ya ƙure musu.".

Daga haka ya dakata da maganar da yake É—in sannan ya tashi ya nufi inda gawar Hisham take shima addu'a ya masa sannan yace a zo a É—auke a je a sallace su.

Duk wanda yake wajen sai da jikin shi yayi sanyi da jin maganganun Malam Kabiru ɗin wasu kuwa har sun fara zubar da hawaye. Daman gidan har ya fara cika da mata da yawa sun zo gulma ne da kuma ganin irin mutuwar wulaƙanci da Amrah ta yi a cewar su sai kuma gashi labari ya sha bambam domin kuwa abin da suka yi zato ɗin ba haka bane.

Sanda aka zo fita da gawar su Hisham da Amrah Gwaggo Sa'adatu sai da aka riƙe ta domin kuwa wasu abubuwa ta dinga yi tana fisge-fisge kamar hauka sabon kamu.

A haka aka fita da su aka je aka sallace su sannan aka miƙa su gidan su na gaskiya,Malam Kabiru da kan shi ya sanya gawar Amrah a cikin ƙabari sannan ya ɗaga hannu sama ya shiga kwararo mata addu'a bayan ya gama ne aka binne ta sannan aka binne gawar Hisham ma daga gefen ƙabarin Amrah.

Lokacin da aka dawo daga binne gawar su Amrah É—in gidan na su tunin ya daÉ—e da cika aka shiga zaman makoki wanda rabi gulma ce da munafurci ya kawo su.

*****

Yau kwana uku da mutuwar Amrah kuma har zuwa yanzu ban san da labarin mutuwar ba abun da na sani kawai shine tun da Amrah ta tafi gida bana samun wayar ta,gashi idan na ƙira wayar Anwar ma bata shiga haka ƴan gidan su Amrah ɗin ma kasancewar duk ƴan gidan su inada number ɗin wayar su, wannan abu ba ƙaramin ɗaga mun hankali yayi ba ya kuma sanya ni na shiga ruɗani, sai dai na yanke shawarar kawai muna samun hutu idan mun gama exam zan shirya naje har garin Giwa ɗin na gano a wane hali Amrah ɗin take ciki kasancewar saura sati guda mu fara exams.

Sai dai cikin ƴan kwanaki biyun nan tun bayan tafiyar Amrah ɗin ina yawan jin faɗuwar gaba da ban san ta Meye ba, sannan kullum idan na kwanta bacci sai na yi mafarki da Amrah a cikin wani kogon rami sanye da farin mayafi amma da zarar na yi ƙoƙarin yi mata magana sai in nemeta in rasa ko kuma na farka.

A ranar da ta cika kwana na uku da rasuwa ne na yi mafarki da ita inda har ta mun magana sai dai abu É—aya ta faÉ—a mun na nemeta na rasa shine ta sanar dani cewa na sanarwa su Azra lokacin É—aukar Fansa yayi.

Ban sanar da su mafarkin ba domin kuwa Tsakanina da su zuwa yanzu sai dai ido domin kuwa tunin na fita a harkar su duk yadda suka so su shiga harka ta hakan baya yiwuwa domin basa samun fuskar hakan, harakar gabana kawai nake yi na fita a ta su harkar.

Yau tun da wuri na dawo É—aki na kwanta sakamakon kai na da yake mun ciwo sosai, ban daÉ—e da kwanciya ba bacci ya É—auke ni.

Su Azrah sai wajen ƙarfe sha biyu suka shigo ɗakin sun tsaya group discussion sakamakon lokacin exam ɗin mu ya kusa.

Azra bata kwanta da wuri ba har ƙarfe ɗaya inda ta tsaya kallo a system ɗin ta daman bata cika kwanciya bacci da wuri ba duk muna rigata yin bacci.

Kallo take gaba ɗaya hankalin ta ya tafi i zuwa cikin system ɗin,ji ta yi kamar ƙarar abu ya gifta ta gefen kunnen ta, a hankali ta waiga sai dai bata ga komai ba.

Juyowa tayi da niyyar cigaba da kallon sai dai abin mamaki shine system ɗin tata ta gani tana yawo a saman ɗakin,bata gama kallon wannan abin tashin hankalin ba ta fara jin wata irin iska mai ƙarfi ta fara tashi a cikin ɗakin inda ta shiga rufe ƙofa da windunan cikin ɗakin tana buɗe su da ƙarfi a lokaci guda kuma wutar ɗakin ma ta fara wata irin fafarniya tana kashe kanta tana kunnawa.

Wani irin kuka ne kuma mai matuƙar ban tsoro ya karraɗe cikin ɗakin sannan kuma aka shiga ƙyaƙyata wata irin dariya marar daɗin ji. Wata zuffa ce ta shiga karyowa Azra a kowane sashi na jikin ta tsoro firgici haɗe da tashin hankali ne suka dirar mata fara ja da baya ta yi in da ta fara ƙoƙarin miƙa hannun ta dan ta tayar da su Afrah,sai dai ba shiri tayi saurin janye hannun nata tare da sakin ihu a lokacin da ya sauƙa a jikin Afrah ɗin sakamakon wasu irin ƙayoyi da taji sun caki hannun nata.

Bata yi auni ba sai ji tayi an É—aga mata sama cak an fara hajijiya da ita a cikin É—akin inda aka shiga gwara kan ta ta kowane kusurwar É—akin.

Ihu Azrah ta shiga yi tana ƙwala ƙiran sunan su Afrah amma ina ba wanda ya san tana yi balle ta sa ran za'a ƙwace ta.

Sai da aka gama galabaitar da ita kafin aka yi jifa da ita ta faÉ—i can gefe guda tana mayar da numfashin wahala,sai dai har zuwa wannan lokacin iska da kuma wutar É—akin ba su tsaya ba ga wannan kuka da dariyar yana nan ba'a daina ba.

Azrah kuwa wata irin azaba take ji a kowane iri sashi na jikin ta kamar ana zuba mata ruwan dalma wani ihu ta shiga yi tana birgima a ƙasa saboda tsananin azabar da take ji ɗin.

Can zuwa wani lokaci wutar É—akin ta tsayar da kan ta kafin kuma komai ya tsaya, itama kuma Azrah ta daina jin wannan azabar.

A hankali Azrah ta shiga buɗe idanun ta sai dai abin da ta yi tozali da shi ɗin ne ya sanyata sakin wata ƙara a lokaci guda kuma wani fitsari ya shiga biyowa ta tsakanin cinyoyin ta sai kuma ta tafi luuu ta sume a wajen saboda tsananin razanar da tayi.

Ba komai Azra ɗin tayi arba da shi ba da ya tsoratata face Amrah da ta gani a tsaye cikin fararen kaya da suka ɓaci gaba ɗaya da jini,harshen ta ya zazzago ga idanun ta da yake zubar da hawayen jini.

Takowa Amrah ta fara yi har ta ƙaraso kan Azrah ɗin sannan ta sanya hannu ta ɗago kan ta wasu zafafan maruka ta shiga kwashe ta da su ta ko ina wanda yayi sanadiyar farfaɗowar Azrah ɗin daga suman da tayi ɗin.

Ihu take tana kururuwa tare da roƙon Amrah a kan ta yi haƙuri amma Amrah ko saurarar ta bata yi ba ba kuma ta da niyyar saurara mata ɗin.

Kan kace kwabo Amrah ta haÉ—awa Azrah jini da majina ta kuma sanja mata gaba É—aya hallitar fuskar tata inda ta kumbura mata ita tayi suntum.

A wannan daren dai gaba ɗayan shi Azrah bata yi bacci ba,saboda tsananin tashin hankalin da take ciki ɗin suma kuwa tayi yafi sau a ƙirga.

Da asubah ni na fara tashi inda na nufi hanyar shiga toilet,sai dai turus nayi na ja na tsaya sakamakon tozali da nayi da Azrah a yashe a bakin ƙofar toilet kamar bata da rai ga fuska a kumbure suntum,gabana ne yayi ta mummunar faɗuwa sakamakon tunowa da nayi da mafarkin da nayi a daren jiya na Amrah da Azrah ɗin.

*Wasan ya fara yanzu fa Azrah an fara girbar abin da aka shuka*.😂💃

Follow my Whattpad account @shamsiyamanga. Arewa books @shamsiyyamanga
Whatsapp number
07060943991
Phone call
09065779330
Comment
Share fisabillillah.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_ 💀☠️).

_Tsarawa/Rubutawa_

*© SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D auta, Sis Amira Adam, Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi._

*Free book*

------------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*028*
______________________________

Har na yi niyyar Ɗauke kaina na wuce sai kuma dai na nufi inda Azrah ɗin take yashe sannan na fara ɗan bubbuga ta ina ƙiran sunan ta,shiru bata amsa ba hakan ya tabbatar mun da cewar a sume take.

Miƙewa na yi na nufi cikin toilet ɗin namu inda na ɗebo ruwa mai sanyi na zo na watsa mata.

Da wani kalar razannannen ihu Azrah É—in ta farka inda ta shiga cewa.

"Dan girman Ubangiji kar ki kashe ni ki yiwa Allah ki ƙyale ni wallahi ban shiryawa mutuwa yanzu ba".

Azrah ta faɗa tana ƙanƙame mun hannu a tunanin ta Amrah ce cikin tsananin firgici.

Ni kuwa abun nata ma dariya ya bani har sai da dariya ta so kufce mun na yi ƙoƙarin gumtse baki na, wai kiji wani ikon Allah wai Azrah ce take furta bata shirya mutuwa yanzu ba.

"Azrah wai lafiya kike kuwa ki nutsu mana, wai mai yake damun ki ne,waye zai kashe ki?".

Na jefawa Azrah waÉ—annan tambayoyin a lokaci guda tare da É—ago kan ta muka fuskanci juna.

Sai a sannan Azrah ta ɗago kan ta sannan ta fara waige-waige a cikin ɗakin, buɗe baki tayi da niyyar yi mun magana amma sai taji komai ya ɗauke mata cak daga cikin ƙwaƙwalwar ta,duk yadda Azrah ta so ta tuna abin da ya faru da ita a daren jiyan abin ya gagara, ƙwaƙwalwar ta kamar an wanke mata ita ko kamar wadda ta haɗu da cutar mantau.

Bata ce komai ba sai ta fara ƙoƙarin tashi tana jin duk jikin ta ya mata tsami,sannan ta shiga toilet ta haɗa ruwan wanka zata yi wanka,sai da ta gama haɗa ruwan wankan ta cire kaya zata fara wankan kawai taga gaba ɗaya ruwan ya koma jini.

Wani mahaukacin ihu Azrah ta sake sannan yanki jiki ta zube a cikin toilet ɗin gaba ɗaya in banda rawa ba abun da jikin ta yake mata,wata irin zuffa ce ta shiga karyo mata,da rarrafe ta nufi hanyar fita daga cikin toilet ɗin amma sai dai duk irin jan da ta yiwa ƙofar ta kasa buɗe ta.

Wannan dariya mai haÉ—e da kukan aka shiga yi kafin kuma abubuwan cikin toilet É—in su shiga tashi suna kewaye Azrah duk abin da ya zo kewaye ta sai an buga mata kan a jikin shi ga maruka da aka shiga zabga mata ta kowane gefe na fuskar ta.

Ihu Azrah ta shiga yi tana bugun ƙofar iya ƙarfin ta tare da ƙura sunan mu amma abin da bata sani ba shine duk wannan ihun da take da buga ƙofar ba wanda yake jin ta a cikin mu balle a kawo mata ɗauki.

A ranar dai Azrah taji a jikin ta domin kuwa tashin hankali ba irin wanda bata gani ba a cikin toilet É—in azaba iri-iri haka ta shata ba wanda ya kawo mata taimako.

Kuka kuwa ta yi shi har sai da hawaye ya daina fita daga idon ta, a lokacin gaba ɗaya Azrah har ta fice a hayyacin ta sannan ta saddaƙar da cewar watan mutuwar ta ne ya kama ,sai da aka ɗauki tsawon lokaci kafin komai ya lafa,sannan ƙofar ma ta buɗe da kan ta.

Haka Azrah ta tashi da gudu ta fice daga cikin toilet tana mai da numfashi.

Kallo muka bita dashi cike da mamaki tare da Zaro ido waje ganin ta fito da gudu sannan bata yi wankan ba,gashi ba towel É—in da ta shiga dashi É—in.

"Azrah lafiya kuwa naga kin fito daga toilet da gudu sannan mai ya same ki a fuskar ki haka naga jini ya taru miki a gefen ido?".

Cewar Anisa tana kawar da idon ta gefe.

Duk yadda Azrah ta so ta tuna abin da ya faru Abu fa ya gagara gashi tana son yin magana amma komai duk wani abu ya É—auke mata,to mai yake shirin faruwa da ita haka?. Ta jefawa kan ta wannan tambayar sannan ta dube mu tace.

"Mai kuka gani mai ya same ni?, Nima ban san abin da ya same ni ba, kawai na farka ne naga fuska ta a kumbure wata ƙila faɗuwa ne jiya ina bacci".

"Azrah da alamu baki san a yadda kika fito daga toilet ɗin ba ko?, Ko dai ƙadangare ne ya koro ki?"

Afrah ta faɗa tana ƙunshe dariyar ta,

Kallon kanta Azrah tayi wadda sai a sannan ta lura da yadda ta fito daga cikin toilet É—in.

Da sauri ta nufi wajen kayan su ta buÉ—e ta É—akko wasu kaya ta sanya.

A ranar dai wankan da Azrah bata yi ba kennnan muka tafi lecture a haka.

Tun daga wannan ranar kullum sai a Amrah ta zo wa Azrah da dare,daga zarar mun yi bacci to ita kuma fa Azrah watan cin uwar ta ya kama a wajen Amrah sannan da zarar safiya kuma ta yi to Shikennan Azrah zata nemi duk wani abu da ya faru ta rasa, bacci kuwa tayi arba dashi.

Lokaci guda Azrah ta rame ta zabge ta fita a hayyacin ta gaba É—aya duk wanda ya san Azrah kallo É—aya zai mata ya fuskanci cewa akwai abin da yake damun ta.

Yau ta kama ranar da zamu fara exams, Alhamdulillahi mun yi paper É—in farko lafiya mun fito sai dai a wajen Azrah fa ba wani abu da ta tsinana domin kuwa duk wani abu da ta karanta tana shiga É—akin jarrabawa take mantawa,kuma daman ba wani karatun ma take samu ta yi ba duba da cewar bata iya karatu da rana sai da dare, sai gashi daren kuma ya zama mata daren tashin hankali a gare ta.

Yau muka gama exam lafiya kowa ka gani cikin farin ciki yake ana ta shirin tafiya gida, Ni kuwa farin ciki na bai wuce zan je naga Aminiya ta Amrah ba wadda na yi kewa.

Kai tsaye ina komawa gida na fara shirin tafiya garin Giwa ɗin bayan na sanar da Mahaifiyata duk wani abu da ya faru da Amrah ɗin domin kuwa bana ɓoye mata komai.

Sosai Mahaifiyata ta tausayawa Amrah É—in sannan tayi Allah wadai da halin su Azrah,sannan ta ce na shirya zamu je tare da ita.

Hakan kuwa aka yi muka shirya Ni da mahaifiyata driver ya É—auke mu sai garin Giwa.

Allah sarki mun isa garin lafiya sai dai mun tarar da labarin da yayi mugun É—aga mana hankali, in da muka tarar da cewar Malam Kabiru da iyalin shi sun tattara sun bar garin Giwa É—in sannan kuma ba wanda ya san inda suka nufa, daman kuma su ba Æ´an asalin Kaduna bane kasuwanci ne ya kawo mahaifin Amrah É—in har ya hayyayafa a garin.

Babban labarin da ya fi girgizani ya kuma É—aga mun hankali bai wuce labarin mutuwar Amrah da na samu ba. Wannan abun ya gigita ni fiye da tunanin mai tunani. Wallahi ni dai ban san yadda aka yi ba sai buÉ—ar ido na yi na ganni a cikin gidan mu a kan cinyar mahaifiyata tana mun fifita inda nikuma nasan cewar mun je garin Giwa ne.

Abubuwa ne suka shiga dawo mun É—aya bayan É—aya,da gaske Amrah ta mutu?, Ita ce tambayar da ta fara fitowa a bakina zuwa kunnuwan mahaifiyata.

Haƙuri mahaifiyata ta bani sannan ta mun nasiha sosai tare da mun kashedin cewar na fita a harkar su Azrah tun da su ba mutanen kirki bane sannan kuma na yi gaggawar neman duk wata hanya domin na fito na bayyana gaskiyar da ni kaɗai na santa ko dan na wanke Amrah a idon duniya.

Na amince da abin da Mahaifiyata ta ce sai dai kuma ta yaya zan fara fitowa na shaidawa duniya wannan ƁOYAYYEN SIRRIN da ni kaɗai na san dashi?, Tabbas akwai aiki a gabana amma fa sai na shirya na kuma yi taka tsantsan.

Haka rayuwa ta cigaba abubuwa sun shuɗe ba adadi, na so na fita daga cikin rayuwar su Azrah gaba ɗaya kamar yadda Mahaifiyata ta buƙata sai dai samuna da Azrah tayi tana kuka ta nuna mun cewar ta yi danasanin komai ya sanya na ɗan ji tausayin ta sannan muka cigaba da rayuwa ,amma fa ina baya-baya da su ba kamar yadda mu ke da ba, domin a da kan ma har ɗaki na so sanjawa sai kuma na fasa.

Kwanaki sun shuÉ—e,Satikai sun zo sun biyo bayan su, watanni sun zo sun shuÉ—e yau wata uku mu ke dosa da mutuwar Amrah, kuma i zuwa yanzu komai ya lafa na daga tsoratarwar da take yiwa Azrah har Azrah É—in ta fara dawowa hayyacin ta,sai dai ashe a wannan karon mai gaba É—aya zata musu.

Ban san yadda aka yi ba da rayuwar Anwar domin kuwa tun bayan da na samu labarin mutuwar Amrah ta daina zuwa mun a bacci ta daina sanar dani komai ban kuma san dalilin hakan ba.

Ban san yadda aka yi ba kawai sai wayar gari nayi na tarar da Afrah sun fara soyayya da Anwar kamar za su haÉ—iye juna.

Wannan abin ba ƙaramin mamaki ya bani ba har sai da na tari Anwar ɗin da maganar sai dai abin da ya sanar dani shi yafi komai ɗaga mun hankali inda yake cemun ai ko da Amrah tana da rai ba haramun bane dan ya so Afrah balle kuma Amrah ta mutu, kuma ko da tana da rai mai zai yi da karuwa wadda ta gama tallatawa duniya kan ta,Allah ya tsari Gatari da saran shuka.

Innalillahi wa'innailaihi rajiun shine kawai abun da na iya faɗa domin kuwa a lokacin in da wani ne yace mun Anwar zai aikata haka a Amrah wallahi ƙarya tawa zan yi amma da idona da kunne na ji, ya Subhannallah.

A ranar na yi kuka sosai irin kukan da rabon da na yi shi tun bayan mutuwar Amrah,na ji na tsani ƙawance fiye da tunanin mutum,na tsani Afrah fiye da yadda na tsani Azrah da Anisa domin kuwa Afrah ita ce silar komai.

A kwana a tashi har magana ta yi nisa tsakanin Anwar da Afrah inda cikin lokaci ƙanƙani aka tsaida ranar biki, sai dai a ranar da za'a ɗaura mu su aure komai ya lalace domin kuwa a ranar Amrah ta kashe Afrah.

Follow my Whattpad account @shamsiyamanga Arewa books @Shamsiyyamanga
Whatsapp number
07060943991
Phone number
09065779330.
Comment
Share fisabillillahi.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_ 💀☠️).

*Tsarawa/Rubutawa*

© *SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_ .

*Free book*

-----------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*029*
____________________________

Shiru Amira ta yi tare da Sunkuyar da kan ta ƙasa wasu hawaye masu ɗumi ne suka shiga zubo mata tana jin zuciyarta kamar zata faso ƙirjin ta ta fito,ji take kamar a yanzu komai yake faruwa bada labarin da ta yi ya fame mata ciwon da bai gama warkewa ba a cikin zuciyarta,da ƙyar ta ɗago fuska sannan ta dubi mutanen cikin police station ɗin wanda sun kasa furta komai.

"Wannan shine a taƙaice abin da ya faru da rayuwar Amrah domin kuwa akwai abubuwa da yawa waɗanda bayyana su ma bashi da amfani,rashin faɗar su shi yafi alkhairi, idan har nace zan farke komai to zan jawa su Azrah baƙin cikin da kaf ahalin su sai ya shafa,duk da cewa a yanzun ma nasan zuciyoyin mutanen wajen nan sun cika da tsanar su. Tabbas! Amrah ta lashi takwabin ɗaukar Fansa tare da ƙudurin hakan a ranta,kuma gashi kamar yadda ta ƙudurta sai da ta aikata ɗin shi daman idan zaka gina ramin mugunta to ka gina shi gajere wataƙila baka sani ba ko kai zaka afka cikin sa. Su Azrah sun yi tunanin zasu tarwatsa rayuwar Amrah su zauna lafiya basu san cewa kwanakin mutuwar su suka janyo ba, Allah Ubangijin ya ji ƙan ki Amrah ya sa kin huta ya kyautata makwancin ki,ya miki sakayya tsakanin ki da azzaluman da suka ruguza rayuwar ki".

Amira ta faÉ—a tana fashewa da wani irin kuka mai sauti.

Tun da Amira ta dasa aya baka jin sautin komai a cikin police station ɗin sai sauƙar ajiyar zuciyoyin mutane,kowa ka kalla a cikin wajen idanun shi ya sanja launi daga fari zuwa ja, Inspector Rasheed ne yayi ƙarfin halin fara magana.

"Tabbas idan nace an zalunci wannan yarinyar ban yi ƙarya ba,Tabbas waɗannan yaran sun zalunce ta zalunta mafi muni,kuma ban ga laifin Amrah da ta ɗauki Fansa da kan ta ba domin kuwa yau idan da bata ɗauki Fansa ba da ba wanda zai tsaya mata a cikin ƙasar nan wajen bi mata haƙƙin ta duba da yadda ƙasar ta mu ta lalace ta zama komai sai ɗan wane da wane,kuma wanann hukuncin da ta musu shine dai-dai da su duk da ma ni hukuncin ya mun kaɗan amma ba komai Ubangiji Allah zai bi mata haƙƙin ta kuma zai saka mata,dan haka wannan ya zama izinah ga masu mummunar zuciya irin ta su Azrah masu kuma sha'awar aikata irin abin da waɗannan ƴanmata suka aikata suma zasu shiga hankalin su,sai dai abin da na kasa fahimta shine ya aka yi Anwar ya warke har ya zo ya fara soyayya da Afrah duk irin wannan soyayyar da yake nunawa Amrah ɗin".

"Wallahi Inspector Rasheed wannan tambayar sai dai shi Anwar É—in ya bamu amsar ta da kan shi domin kuwa ni kaina ban san ta yadda aka yi wannan lamarin ya faru ba,Anwar sai ka sanar da mu yadda abu ya faru".

Amira ta faÉ—a tana kai duban ta inda Anwar yake zaune wanda tun da ta gama bada labarin har zuwa yanzu ya kasa É—ago ido ya kalle ta.

ÆŠago kan shi yayi a hankali sannan ya dubi mutanen da suke wajen kafin kuma yayi saurin kawar da kan shi gefe sannan ya fara magana.

"Amira wallahi nasan duk wani bayani da zan muku ba lalle ku fuskance ni ba duk da ni nasan cewar ban ci amanar Amrah ba kamar yadda ki ke mun kallo. Watau abin da ya faru shine bayan na tashi daga doguwar jinyar da na shafe watanni ina yin ta,domin kuwa lokacin da naji labarin mutuwar Amrah ba wanda ya sa ran zan sake ƙara kwana guda a doron ƙasa saboda yadda na birkice ikon Allah ne kawai ya tashi kafaɗuna,amma an sha jinya jinya mai suna jinya. Wata rana muna zaune da Mahaifiyata falon mu sai muka ji Sallamar wasu ƴan mata har suka shigo cikin falon suka zauna ban kalle su ba,waje Mahaifiyata ta nuna musu suka zauna abin da na lura shine kamar mahaifiyar tawa ta san su domin kuwa cikin sakin fuska suka shiga gaisawa har naji tana tambayar su ya karatu, sannan naga ta tashi ta nufi kitchen ta kawo musu abinci da abin sha haka dai ta shiga nan da nan da su har a wannan lokacin idona a rufe yake ban buɗe ba balle nasan su waye, domin ni haka kawai tun bayan mutuwar Amrah na ji duk wata mace ta fice mun a rai idan ka cire mahaifiyata,kamar a cikin bacci na ji sauƙar Muryar Afrah a dodon kunnena tana gaishe ni.

"Anwar Barka da gida ina yini,ya kuma ƙarfin jiki?".

Ban buɗe idona ba na amsa ciki-ciki sannan su ma sauran ƙawayen nata suka shiga gaishe ni,ni dai ban san adadin lokacin da suka ɗauka ba a gidan suka tafi domin kuwa tashi na yi na shige cikin ɗaki na bar su a wajen.

Bayan kwana biyu da zuwan su Afrah gidan mu kawai sai ga Mahaifiyata ta same ni da wani zance wanda yayi matuƙar tayar mun da hankali shine wai tana so na auri Afrah,da farko dariya na yi wadda rabona da yin ta tun bayan mutuwar Amrah sannan na dube ta nace.

"Haba dai mama amma dai wasa ki ke ko?".

Kallo na ta yi sannan ta ce.

"Ba wasa nake ba Anwar idan kuma kana tsammanin wasa nake to ka kalli cikin idanuna zaka faskara gaskiyar abin da nake nufi É—in".

Nan fa na zaro ido waje sannan na fara ƙoƙarin son naga na fuskantar da Mahaifiyata illar abin da take son sani na aikata ɗin,amma fir Mahaifiyata ta rufe ido ta shafawa idon ta toka tace ta ci alwashin tare da rantsuwa a kan sai na auri Afrah idan kuma har naga ban auri Afrah ba to ɗayan biyu ne ko dai bani da rai ko kuma ita Afrah ɗin bata da rai wannan shine kaɗai abin da zai hana a aura mun ita tun da gawa bata auren gawa. Jin wannan kalaman na mahaifiyata ba ƙaramin tashi hankali na yayi ba domin kuwa nasan halin ta sarai idan har ta furta abu to ba wanda ya isa ya sanja mata ra'ayi.

Ita kuwa Afrah har makarantar su naje na same ta na buga mata warning a kan idan har ta kuskura ta yarda da wannan auren to wallahi ta kuka da kan ta. Sai dai rashin sani yafi dare duhu idan da nasan abin da hakan zai janyo da ban fara zuwa na tunkari Afrah da wannan maganar ba domin kuwa ina gama buga mata warning ɗin ta ƙira mahaifiyata ta kwashe komai ta faɗa mata cikin kuka sannan ta ce ta fasa auren nawa kawai zata haƙura dani,sosai ran Mahaifiyata ya ɓaci inda ina dawowa gida ta ce mun wallahi duk ranar da na kuskura na ƙara sanya Afrah kuka ko na ɓata mata rai Allah ya isa tsakani na da ita bata yafe ba sannan kuma tana so a yanzu na koma na bawa Afrah haƙuri kuma in shirya nan da sati biyu za'a ɗaura mana aure. Innalillahi wa'innailaihi rajiun tashin hankali wanda ba'a sa ma sa rana a ranar na yi kuka kamar raina zai fita na ji kamar na mutu nima na bi Amrah ko na huta a raina,gashi a rayuwa ta ni irin mutanen nan ne masu gudun ɓacin ran iyayen su,haka na juya na je na bawa Afrah haƙuri sannan kuma tun daga wannan ranar na shiga nuna wa Afrah cewar ina son ta alhali kuma ƙasan zuciyata ba haka bane ba kawai ba yadda na iya ne shiyasa na kuma bi umarnin Mahaifiyata.

Tun da Afrah ta samu wannan damar a wajena shikennan ta fara ƙoƙarin ganin ta ƙara cusa mun tsanar Amrah ganin cewa har zuwa wannan lokacin ban yadda da abin da aka ce Amrah ɗin ta aikata ba,sai dai zuwa wani lokaci Afrah ta yi nasarar sanya wa zuciyata yarda da abin da aka ce Amrah ɗin ta yi duk da kuwa cewar wani sashi na zuciyar tawa yana ƙaryata yana kuma ƙara tuno mun da kyawawan halayen Amrah. A wani ɓangaren kuma shine Kullum idan na kwanta bacci sai Amrah ta zo mun tana kuka wanda a da ban fahimci dalilin bayannar ta ta a mafarkin nawa ba sai a yanzu na gane ashe wannan kukan da nake ga tana yi ɗin duk dan ta na so ta nuna mun cewar an zulunce ta ne. A taƙaice dai har an sanya aure na da Afrah kuma sai gashi saboda ba Alkhairi a cikin sa Allah ya kawo ƙarshen abin".

Tun da Anwar ya gama bada wannan labarin ƙananan maganganu suka shiga tashi a cikin police station ɗin kowa da abin da yake faɗa wasu suna ganin laifin Anwar ɗin in da wasu kuma su ke ganin laifin mahaifiyar wadda nima na shiga sahun ma su ganin laifin mahaifiyar ta shi.

A ɓangaren Justice Kabir kuwa kuka sosai ya ke kamar wani ƙaramin yaro tare da Allah wadai ɗin mummunar ɗabi'ar da ya gina ƴar ta shi a kai,Tabbas ya san cewar ƴaƴa amana ce da Allah ya bamu kuma kowane bawa sai Allah ya tambaye shi akan amanar da ya bashi ɗin,yanzu shi da wana ido zai tsaya a gaban Ubangiji ya kare kan shi akan abin da Azrah ɗin ta aikata ya san tana da laifi amma shima yana da kaso talatin cikin ɗari na kamashon abin da ta aikata ɗin,yayi danasani ba adadi wadda zamu iya ƙiran ta danasani a ƙurarren lokaci kuma marar amfani.

Haka suma iyayen su Afrah kowa ka kalla fuskar shi tsantsar nadama ne da kuma danasanin abin da Æ´aÆ´an na su suka aikata.

Ganin hankalin kowa baya jikin shi ga kuma yadda jikin mutane da yawa yayi sanyi ya sanya Inspector Rasheed ya bada umarnin kowa zai iya tafiya.

Hakan kuwa aka yi inda suma ƴan jarida suka kwashi kayan aikin su su ka ƙara gaba,itama Amira Inspector Rasheed ne ya mai da ta gida sannan yace dan Allah idan ba damuwa gobe zai zo akwai abin da yake so zasu ƙara tattaunawa.

Shi kuwa Justice Kabir yana komawa gida ya fara shiri inda ya shirya zai je garin Giwa domin ya binciki inda iyayen Amrah su ke don nemawa Æ´ar shi yafiya daga gare su.

A ranar gidan telebijin da radiyo duk idan ka kunna ba abin da zaka ji sai Muryar Amira tana ba da labari da duk wani mai imani idan ya saurara sai jikin shi yayi sanyi.

*GARIN GIWA*

Samari ne sun fi ashirin zaune a teburin mai sai da shayi,wasu suna cikin rumfar wasu suna ta waje, wata ƙatuwar Radio ce ajiye a tsakiyar su gaba ɗaya hankalin su ya tafi kan Muryar da ake saurara a gidan radiyo ɗin watau Muryar Amira da take bada labari a kan Amrah,duk wanda ka kalli fuskar shi a wannan lokacin ba abin da zaka gani face tsantsar damuwa da danasani ga wani gumi kuma da yake zubowa daga fuskokin wasu daga cikin mutanen wajen.

Malam ÆŠalha kuwa da yake zaune a gefe tunin hawaye sun gama wanke mishi fuskar shi sakamakon tunowa da abin da ya yiwa abokin na shi,gashi a halin yanzu bai san a wace duniyar abokin na shi yake ba gaskiya bai kyauta ba sannan bai cika aboki na gari ba da har ya bari zuciya ta yi tasari a kan shi ya manta da waye Malam Kabiru da kuma ahalin shi.

Har aka gama jin labaran ba wanda ya iya motsawa daga inda yake sai can dai da ƙyar wasu tsiraru daga cikin matasan wajen suka fara tashi ɗaya bayan ɗaya suna barin rumfar mai shayin cikin matsananciyar kunya ga kuma gwaiwowin su da suka daɗe da yin sanyi.

Shi kuwa Malam Ɗalha har aka gama barin wajen aka bar shi ya kasa tashi domin kuwa kaf mutanen wajen sun watse sun bar shi a zaune a wajen kamar an dasa shi, shi kan shi mai shayin a ranar haƙura yayi da sana'ar shayin na shi tun da ba masu siya.

Da ƙyar dai Malam Ɗalha ya iya tashi gwaiwa duk ta gama sakewa sannan ya rarrafa ya shiga gida.

Follow my Whattpad account @shamsiyamanga, Arewa books @shamsiyyamanga
Whatsapp number
07060943991
Phone call
09065779330
Don't forget to share and comment pls.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_ 💀☠️).

_Tsarawa/Rubutawa_

*© SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S* *ASSOCIATION*

Kai jama'a Bari nima na ɗana yin waƙe 💃💃😂. Rayuwa da masoyi a duniya babbar nasara ce ƴan uwa💃💃🫴🏼. Ya Salam gaskiya masoyi yayi a rayuwa ni wallahi ban taɓa sanin haka daɗin masoyi yake ba sai a kan ku masoyana🥲🥳💃. Tabbas naga ruwan ƙauna sanadiyyar wannan jinyar da nayi 😿🥲😣. Jama'a ku bani tissue,wallahi some prayers sai da suka sanyani hawaye😿🥲 . I received a lots of messages from different places and different people,wasu mun yi magana via phones call, wasu sun tura mun message ta Whatsapp wasu ta direct message duk ana tambayar littafin FANSAR FATALWA☺️😇. Ni kaina ban san haka littafin ya karɓu a gare ku ba sai da na yi kwana biyu ban yi posting ba,and hakan ya faru ne sakamakon jinyar da na yi ciwon ido mura da kuma zazzaɓi🥹🥲.To Alhamdulillahi I'm getting much better and better know and Finally I'm back ☺️ 💃💃🥳🥳in sha Allah na dawo zamu ɗaura daga inda muka tsaya godiya buhu-buhu gare ku masu yi mun addu'a wanda na sani da wanda ban sani ba,na fili da na ɓoye Musamman ma ƴan group ɗina na FANSAR FATALWA u people Ina son ku fisabillillahi because kun nuna mun zunzurutun ƙauna wadda masoyan gaskiya ne kawai su ke nunawa ta hanyar yi mun addu'oi🥰😌😘Lots of Love to u guys really appreciate ur concerned towards me🥳🥳🥳. Yanzu dai jiki Alhamdulillahi amma ku yi haƙuri saboda ba lalle na dinga yin dogon
typing ba saboda idona an hanani kallon haske sosai,amma dai zamu lallaɓa a haka in sha Allah 😁🥰😌.

*SADAUKARWA* : _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk in da ku ke ina son ku fisabillillahi._

*Free book*

-----------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*030*
________________________________

Kamar yadda Justice Kabir ya faɗa washe gari kuwa sassafe ya buga sammako inda ƙarfe bakwai a garin Giwa ta mishi sai dai ya bugi gurbi domin kuwa lokacin da ya isa garin yake samun labarin cewar ai iyayen Amrah ɗin sun daɗe da barin garin.

Wannan labari da Justice Kabir ɗin ya tarar ba ƙaramin ɗaga mishi hankali yayi ba domin bai taɓa kawowa a ran shi cewar labarin da zai tarar ɗin ba kennnan.

Haka Justice Kabir ɗin ya kama hanyar komawa cikin Zaria zuciyar shi duk ba daɗi,sai dai kafin ya bar garin ya buƙaci a taimaka mishi da hoton Malam Kabiru ɗin domin kuwa ya ƙuduri niyyar sai ya nemo inda su ke a faɗin duniya domin ya nemarwa ƴar shi yafiya ko hakan zai sa ta samu sa'ida da salama a cikin ƙabarin ta.

Bayan ya isa gida zama yayi a cikin falon shi tare da riƙe kan shi lokaci guda ya fara tunanin hanyar da zai bi domin neman inda Malam Kabiru ɗin yake, miƙewa tsaye yayi sannan ya fara zagaye cikin ɗakin yana nazarin hanyar bi.

Ya ɗauki tsawon lokaci yana kaiwa da komowa a cikin falon gidan nashi domin neman mafita kafin cikin ikon Allah wata zuciyar ta bashi shawarar kawai ya je gidan radiyo ya bayar da sanarwa sannan ya yi Albishirin tukwaici mai tsoka ga duk wanda ya gano inda Malam Kabiru da iyalin na shi su ke. Da wannan shawarar ya yi na'am sannan ya ɗauki hoton Malam Kabiru ɗin ya ɗauka a wayar shi tare da ƙiran wani layi ya sanar da mai layin abin da yake buƙata kafin kuma ya juya ya nufi hanyar barin falon domin zuwa gidan Radiyo ɗin.

Tafe yake a cikin motar shi duk tunanin duniya ya ishe shi dai-dai ya iso wajen danger ne aka tsayar da motar ta shi. Ganin cewa da goslow da yawa a gaban shi ya sanya shi kashe motar sannan ya kifa kan shi da sitiyarin motar.

Har aka fara bayar da hannu motoci suka fara wucewa Justice Kabir bai san ana yi ba,nan fa motocin bayan shi suka shiga zabga mishi horn wasu cikin ɓacin rai har sun fara fitowa daga cikin motocin su domin a tunanin su irin rainin hankali ne kawai irin na wasu masu motar.

"Bawan Allah idan ba tafiya zaka yi ba ka kauce ka bamu hanya mu wuce?, Haba tun É—azu ka kasa gaba ka kasa baya ka tsaya mana a kan titi!".

Muryar da Justice Kabir ya ji ta daki dodon kunnen shi ne ta sanya shi saurin ɗago wa tare da buɗe baki da niyyar yin magana sai dai yin arba da mutumin da yake mishi maganar ta sanya ta shi maganar maƙalewa inda ya kafe mutumin da ido cikin wani irin yanayi mai wuyar ganewa.

Kallon da mutumi ya ga Justice Kabir É—in yana bin shi da shine ya sanya shi cika da mamaki kafin kuma ya jijjiga kai ya koma cikin motar shi yana ganin cewar kamar Justice Kabir ba mai lafiya ba.

Saurin jan motar shi Justice Kabir ya yi tare da komawa gefe sannan ya sanya hannu ya ɗakko hoton Malam Kabiru ya duba nan fa ya buɗe motar da sauri ya shiga duban inda ya ga wannan mutumin ya nufa sai dai ya tarar har mutumin ya shiga motar shi ya tayar yana ƙoƙarin barin wajen , da sauri shima Justice Kabir ya koma cikin motar shi tare da bin bayan motar mutumin amma kuma sai dai sama ko ƙasa ya nemi motar ya rasa ta ɓace mishi.

Hankali tashe Justice Kabir ya shiga bin bayan motoci da gudu amma ko mai kalar motar mutumin bai gani ba.

Hankali tashe Justice Kabir ya koma cikin motar shi sannan ya tayar tare da barin wajen ya na nufar gidan Rediyo É—in,shi kam duk da a hoto ya ga fuskar Malam Kabiru ko shakka ba ya yi wanna mutumin shine mahaifin Amrah. To amma ta ya hakan ta kasance tun da ya san a labarin da Amira ta bayar na Amrah ta sanar da su cewar iyayen Amrah talakawa ne to amma ya akayi yanzu kuma ya ga Malam Kabiru cikin shiga ta alfarma?.

Amsar da Justice Kabir ya kasa samarwa kan shi Kennan har ya isa gidan rediyon zuciyar shi cike da tunani iri-iri.

Yana isa gidan Rediyon ya sanar da su abin da yake tafe da su sannan ya basu hoton Malam Kabiru ɗin tare da cewar duk wanda ya gano inda Malam Kabiru da iyalan shi su ke ya masa alƙawarin kyautar kuɗi har Naira Miliyan guda.

Bayan ya gama komai ne ya fito daga cikin gidan rediyon sannan ya nufi motar shi da niyyar shiga sai dai kuma ƙiran da ya shigo wayar shine ya sanya shi dakatawa tare da ɗaukar number ɗin.

"Hello ya ake ciki ?".

"Ranka ya daÉ—e na samo labarin inda mutumin yake yanzu haka yana Jahar Yobe a cikin garin Potiskum,a wata unguwa da ake cewa Tsohuwar kasuwa,dan haka duk sanda ka shirya sai ka mun magana na raka ka".

Shine bayanin da aka yiwa Justice Kabir a cikin wayar aikuwa cikin zumuÉ—i da murna ya ce gobe za su wuce garin.

Sai dai abin bada ya bashi mamaki to shi kuma wancan da ya gani É—azu fa waye?.

Tambayar da ya kasa bawa kanshi amsa kennan.

*****

Anwar tafe yake a cikin motar shi baka jin sautin komai a cikin motar face karatun Alkur'ani da yake tashi cikin zazzaƙar Muryar Sheikh Sudes cikin ƙira'ar sa mai sanyaya zuciya.

Tun daga nesa yake zabga horn sakamakon kallon mace da yayi a tsakiyar titin tana tafiya cikin ƙwanciyar hankali kamar ta samu cikin ɗakin ta. Wani abin ƙarin haushi da takaici shine bai wuce yadda Anwar yaga ta manna mishi ba duk irin Horn ɗin da yake zabgawa ɗin ta ƙi barin kan titin ko a jikin ta balle ta nuna mishi ta san ma da wanzuwar hallitar shi a wajen.

Sai da Anwar ya iso daf da ita kafin ya ja wani mahaukacin burki ko kashe motar bai yi ba ya buÉ—e murfin motar ya fito a fusace ya fara magana.

"Ke wace irin Æ´ar gadara ce kina tafiya a kan titi kamar kin samu titin gidan ku,ko an gayamiki cewar titi wajen shashanci ne iyee?, Ko ke kurma ce bansani ba".

Sai a sannan wannan matashiyar budurwa ta juyo itama cikin masifa ta fara magana.

"Shin kai makaho ne!?, Ko an gayama an yi titi ne saboda shashashun mutane irin ku masu tsula gudu a kan titi ba bisa hankali ba!, Da zaka dinga gudu a titi sarai na jika kaka mun horn kawai ban yi niyyar kaucewa bane domin ina so na tabbar ko da sauran hankalin ka".

Tun daga juyowar da tayi Anwar ya kafe ta ido ko runtsawa ba yayi har zuwa yanzu da ta dasa aya a maganar da take É—in,tsananin mamaki da ruÉ—ani ya shiga a lokaci guda kafin ya furta.

"Amrah!".

Ya furta a hankali kafin kuma ya ji idanun shi sun fara mishi dishi-dishi ga kan shi da ya sara mishi a lokaci guda sakamakon tozali da fuskar budurwar da yayi fuskar da har ya koma ga mahaliccin shi ba zai manta da mamalakiyyar fuskar ba, cikin rawar murya da hannu ya shiga nuna ta yaba furta.

"Amrah da......ma...n ki.....nna a....Ra...ye..., Amr...ah..da...m..a .n ba ...ki.....mu....tun.....ba?".

Anwar ya ƙarashe maganar yana mai kai hannun shi tare da shafa fuskar wannan budurwar da yake ikirarin Amrah ce.

Wani ihu wannan budurwar ta sake sannan ta make hannun Anwar da yake kan fuskar ta kafin ta zura da gudu tana furta.

"Allah ya isa na wallahi wuta balbal,haka kawai daga ganina zaka hau taɓa mun fuska kana wani ƙiran wata Amrah mugu kawai,wallahi ban yafe taɓa mun fuska da ka yi ba".

Ai shima Anwar da gudu ya bita yana ƙwala mata ƙira yana cewa ta tsaya dan Allah.

Ai ina! ita kuwa ganin ya biyota da gudu ya sanya tsoro ya ƙara rufe ta nan fa ta ƙara kaimin gudun ta haba wa zo ku ga gudu ƙafa mai naci ban baki ba.

_Ku yi haƙuri ba zan dinga dogon typing ba saboda_ _idona_ .

Follow my Whattpad account @shansiyyamanga, Arewa books@shamsiyamanga.
Whatsapp number
07060943991
Phone call
09965779330
Don't forget to share and comment pls.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_💀☠️ ).

_Tsarawa/Rubutawa_

© *SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA* : _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_ .

*Free book*

-------------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*31-35*
_______________________________

Haka Anwar da wannan matashiyar budurwar suka cigaba da gudu a kan titi kasancewar titin ba irin public titi bane ba sannan gashi unguwar ba mutane shiru. Sai da suka kusa ƙure titin kafin ya ga ta sha wata kwana inda tana sha ta nufi wani gida wanda shine na uku a cikin layin sannan ta shiga buga gate ɗin gidan kamar zata ɓalla shi.

Da sauri mai gadin gidan ya buÉ—e gate É—in ko jira bata yi ya gama buÉ—ewa ba ta hankaÉ—e shi ta shige cikin gidan da mugun gudu, mamaki ne ya cika mai gadin ganin halin da ta shigo cikin.

Leƙawa waje yayi ya ga ko lafiya kuwa inda kuma a dai-dai sannan Anwar ya ƙara so bakin gate ɗin gidan yana ƙoƙarin danna kan shi cikin gidan .

Da sauri mai gadin ya tare shi yana cewa.

"Malam lafiya kuwa?, Ya zaka zo ina bakin aiki na ba magana kawai zaka fara ƙoƙarin ture ni ka shiga gidan mutane".

Sai a sannan Anwar ya dawo hayyacin sa ya lura da abin da yake shirin aikatawa ɗin, kan shi ya shiga sosawa sannan ya fara bawa mai gadin haƙuri.

"Dan Allah kayi haƙuri bawan Allah, Amrah na biyo kuma ta san da zuwa na".

Kallon shi mai gadin ya yi sheƙeƙe sannan yace

"Wacece haka kuma?, Wacece Amrah?".

"Amrah dai ta gidan nan mana wadda ta shiga yanzu".

Anwar ya faɗa yana cigaba da leƙa cikin gidan.

"Kaga Malam gidan nan ba wata Amrah ina ganin ka yi ɓatan kai ne".

Mai gadin ya faɗa yana ƙoƙarin juyawa zai mayar da gate ɗin ya rufe.

Da sauri Anwar ya sanya hannu ya riƙe gate ɗin tare da cewa.

"A'a dan Allah bawan Allah ka tsaya na maka bayani, Amrah fa ta cikin gidan nan wadda ta shiga yanzu,da idona na ganta ta shida cikin gidan kuma kace mun ba Amrah a gidan nan".

"Oh wai Farida ka ke nufi!, to ai wannan sunan ta ba Amrah ba sunan ta Farida".

"Kamar ya wace Farida kaga nifa Amrah nagani ba wata Farida, dan Allah ka ƙyale ni na shiga mu yi magana".

"Kai Malam wallahi ba inda zaka shiga ya ina faɗa ma magana kana mun musu ni da nake aiki a gidan nasan kowa a gidan ba wata Amrah a cikin gidan nan, dan haka kauce ka cire mun hannun ka a jikin ƙofar nan zan rufe ƙofa".

Ai Anwar yana jin abun da wannan mai gadin ya faɗa ya yi saurin zube gwaiwowin shi a ƙasa tare da riƙe ƙafar shi yana mishi magiya akan ya taimaka ya bar shi ya shiga.

Shi kam mai gadin mamakin wannan lamari ya shiga yi,inda ya shiga kiciniyar ƙwace ƙafar shi daga hannun Anwar ɗin, a dai-dai sannan kuma wata mota ta ƙaraso ƙofar gidan tare da yin horn a mai gadin.

Da gudu mai gadin ya ƙwace ƙafar shi a hannun Anwar sannan ya buɗe gate ɗin gaba ɗaya inda mai motar ya kunna hancin motar shi zuwa cikin gidan.

Ai Anwar yana ganin haka da gudu shima ya miƙe tare da rufawa motar baya shigar Anwar cikin gidan yayi dai-dai da tsayawar motar inda matuƙin motar ya ziro ƙafafuwan shi waje tare da fitowa.

Ɗaga ƙafar shi Anwar yake ƙoƙarin yi amma ya kasa sakamakon tozali da fuskar mutumin da yayi.

Wani matsanancin bugawa ƙirjin shi ya shiga yi a lokaci guda kuma wata zuffa ta shiga karyo mishi.

Innalillahi wa'innailaihi rajiun wannan ai mahaifin Amrah ne to amma ya aka yi hakan ta faru?, yaushe ya zama mai kuɗi? Sannan ya tabbata Kennan Amrah ba mutuwa ta yi ba ko mai hakan yake nufi?, Ko dai gizo suka fara mishi domin kuwa a labarin da mahaifiyar shi ta ba shi ta sanar dashi cewar a gaban idon ta aka kawo gawar Amrah sannan a gaban idon ta aka ɗauke ta aka sallace ta a taƙaice ma ƙanin shi Nazir a gaban idon shi aka sanya gawar Amrah a cikin ƙabari. Sannan shi dai ya san tun da aka kafa duniya Allah ya hallici mutanen cikin ta ba'a taɓa mutuwa an dawo ba.

*****

Yau Justice Kabir suka kama hanyar garin Yobe domin zuwa ya haɗu da iyayen Amrah kamar yadda ya ƙuduri niyya.

Kasancewar garin Yobe da Zaria akwai tafiya sosai domin kuwa a ƙalla zai ɗauki mutum tsawon awanni shida kafin ya isa jahar Yobe ɗin.

Lokacin da suka isa garin Potiskum É—in basu wani sha wahala ba wajen neman unguwar da aka ce musu Malam Kabiru É—in yake, Kasancewar Tsohuwar kasuwa tana É—aya daga cikin manyan unguwanni kuma daÉ—aÉ—du a cikin garin.

Da tambaya da komai aka kawo su har ƙofar gidan Malam Kabiru ɗin inda suka tarar da shi zaune da wasu mutane manya guda huɗu yana ƙara musu karatu.

Waje suka nema suka zauna a gefe suka jira har Malam Kabiru É—in suka dasa aya sannan ya juyo ya dube su cikin sakin fuska yana musu maraba.

Suku wa waÉ—annan mutanen tashi suka yi tare da yiwa Malam Kabiru sallama suka É—auki littafan su suka tafi.

Bayan tafiyar mutanen ne Malam Kabiru suka shiga gaisawa sannan ya tashi wani yaro da yake zaune a gefe yace ya shiga cikin gidan yace a bashi ruwa yayi baƙi.

Ƙofi mai tsafta aka zubo musu ruwan a ciki,ruwa mai sanyi kamar na fridge.

Sai da suka sha ruwan sannan Malam Kabiru ya dube su yace.

"Maraba sannun ku da zuwa hala baƙi muka yi?".

Murmushi Justice Kabir É—in ya yi sannan yace.

"Eh alah gafarta Malam fatan mun same ku lafiya?".

"Lafiya lao Alhamdulillahi amma sai dai ban gane ku ba?".

Malam Kabiru ya faÉ—a yana mai tattara gaba É—aya hankalin shi zuwa kan su.

Mukhtar ne wanda suka zo tare da Justice Kabir ya dubi Malam Kabiru yace.

"Eh Malam daman balalle ka gane mu ba domin kuwa baka san mu ba, baƙi ne mu daga Zaria mu ke".

Tun da kalmar Zaria ta dira a kunnen Malam Kabiru gaba É—aya yanayin fuskar shi ya sanja daga fara'a zuwa haÉ—e fuska, su kan su su Justice Kabir É—in sai da jikin su yayi sanyi.

"Bayin Allah to mai ya kawo ku waje na?, Ku yi ku faÉ—a domin inada abun yi".

Malam Kabiru ɗin ya faɗa yana kawar da kan shi gefe domin tun bayan barin su garin Zaria ya ji ba ya sha'awar ko sake waiwaiyar abin da ya shafi Yamma ma balle kuma wata Zaria,har zuwa yanzu yana jin abin da mutanen garin suka mu su a ƙasan zuciayar shi sannan ba zai taɓa mantawa da wannan abin ba har ya koma ga mahaliccin sa.

"Malam daman mun je garin Giwa ne neman ka sai kuma mu ka bugi gurbi muka samu labarin cewar kun bar garin, shine na sanya aka bincika mun sai ake sanar dani cewa kana Jahar Yobe. Malam idan ba damuwa wata alfarma na zo nema a wajen ka dan Allah ka yi haƙuri ka saurare ni ka kuma duba girman Allah ka mun wannan alfarmar".

Justice Kabir ya faɗa yana Sunkuyar da kan shi ƙasa,shi kam Malam Kabiru shiru yayi bai tanka ba sai dai zuciyar shi kuma da yaji tana buga mishi da sauri da sauri kamar zata fito waje.

Jin Malam Kabiru ɗin yayi shiru ne ya sanya Justice Kabir ya cigaba da magana inda ya buƙaci a mishi iso cikin gidan domin maganar da zai faɗa ɗin yana buƙatar ace duk wani makusancin Amrah yana wajen.

Da farko Malam Kabiru bai amince ba amma kuma jin sunan da Justice Kabir É—in ya ambata na Amrah ya sanya ya musu iso cikin gidan.

A tsakar gida suka zauna inda Gwaggo Sa'adatu ta shimfiɗa musu tabarma sannan ta sake kawo musu ruwa a ƙaton kofi da abinci a kwano.

Sosai Justice Kabir ya ji daÉ—in irin karamcin mutanen duk da sun kasance basu da wani arziki amma akwai wadatar zuci,gashi dai basu san su ba amma kalla yadda suka karramma su.

Usman ne suka shigo cikin gidan dashi da Umar da matayen su da alama Malam Kabiru ne ya ƙira su,waje suka nema suka zauna sannan suka gaishe da su Justice Kabir ɗin.

Sai da suka gama gaisawa sannan Malam Kabiru ya dubi su Justice Kabir yace.

"Bayin Allah muna jin ku mai yake tafe da ku?".

Shi kam Justice Kabir tun da ya ga yadda ƴan uwan Amrah ɗin suka taru sai gaba ɗaya yaji wani tsoro haɗe da fargaba sun rufe shi har yaji ya rasa ƙwarin gwaiwar da zai fara sanar da su abin da yake tafe dasu ɗin.

Da ƙyar dai ganin duk sun zuba mishi ido ya sanya shi buɗe baki sannan ya fara magana inda ya shiga sanar da su abin da yake tafe da su.

*****

Daga Farida har iyayen ta kuka su ke sharɓa sakamakon labarin da Anwar ɗin ya sanar da su na Amrah duk da daman sun riga sun san labarin a gidan Rediyo.

Daman tuntuni mahaifin Farida ya yiwa Anwar iso har cikin gidan saboda tun lokacin da Anwar ya ƙira shi da wani suna jikin shi ya bashi cewar lokacin daina kukan shi ya iso.

Kallon Anwar mahaifin Farida ya yi da idanun shi da suka yi jawur sannan yace.

"Yanzu a ina kake ganin zan haÉ—u da mahaifin Amrah?".

Shiru Anwar yayi na É—an lokaci kafin daga bisani ya ce.

"Eh to a gaskiya yanzu sun bar garin Giwa sai dai na samu labarin cewar suna jahar Yobe a wani gari wai Potiskum, sannan na samu labarin hakan ne ta wajen abokina Umar wanda har gobe muna tare sannan duk wani hali da su ke ciki ina samun labarin hakan ta wajen shi".

"Idan ba damuwa ina son gobe ku shirya zamu tafi Yobe, idan har kai Anwar kana da wani uzuri to zaka iya tafiya amma mu dai gobe zamu tafi zamu yi sammako".

Cewar mahaifin Farida É—in yana kawar da kan shi gefe sakamakon yadda yake jin zuciyar shi tana mishi zafi.

"Ai ba wani uzuri Dad in sha Allah gobe dani za'a yi wannan tafiyar Ubangiji Allah ya kaimu kawai da rai da lafiya"

Da Ameen suka amsa gaba ɗaya kafin Anwar ya miƙe tare da mu su sallama zai tafi.

A hankali ya saci kallon gefen da Farida take inda take suka haÉ—a ido ita ma shi take kallo.

Follow my Whattpad account @shamsiyyamanga,
Arewa books @ shamsiyyamanga
Whatsapp number
07060943991
Phone number
09065779330.
Don't forget to share and comment pls.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_💀☠️).

_Tsarawa/Rubutawa_

*© SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi._

*Free book*

------------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*36-37*
_______________________________

Tiryan-tiryan Justice Kabir ya shiga bawa su Malam Kabiru labarin duk wani abu da ya faru da Amrah kamar yadda Amira ta sanar da su ba bu wani abu da ya ɓoye musu,sai dai bisa mamakin shi a maimakon yaga tashin hankali ko ɓacin rai a tattare da ahalin Amrah ɗin sai ya ga saɓanin haka domin kuwa kaf ɗin su ba wanda ya nuna alamar damuwa a tatare dashi sai yaga alamar ma kamar labarin bai zama sabo a gare su ba.

Wani murmushi irin na dattako Malam Kabiru ya sake kafin kuma ya É—aga hannu sama tare da furta.

"Alhamdulillahi Ubangiji Allah na gode daka nuna mun zuwan wannan ranar dana daɗe ina tsunamayi Allah na gode ma daka bani ikon ganin wannan ranar ba tare da na koma gareka ba, dukkan godiya ta tabbata ga Ubangiji da ya tsamo gaskiya ya bayyana ta a idon duniya a lokacin da idon mutane ya rufe da ganin gaskiya!, A lokacin da mutane suka sanya ƙafa suna ganin gaskiya suka take ta. Amrah ina ma kina duniya kiga wannan ranar!, Amrah Ubangiji Allah ya miki Rahama duk da cewar jikina yana bani kina cikin rahamar Ubangiji".

Magana Malam Kabiru ya kasa cigaba da yi sakamakon zuciyar shi da ya ji tana mishi zafi,wasu hawaye ne masu zafi suka shiga ƙoƙarin zubo mishi sai dai tunin ya sanya hannu yayi saurin goge wa.

Ita kuwa Gwaggo Sa'adatu duk yadda ta daure sai da abin ya gagare ta bata san sanda ta fashe da wani irin kuka mai taɓa zuciya ba duba da yadda aka famo mata ciwon da yake zuciyarta wanda ya kasance ɗanye bai gama warkewa ba.

"Dan Allah alfarmar da nake nema a wajen ku shine ku taimaka ku yafewa ƴata abin da ta aikata wa ƴar ku saboda ba ita kaɗai ta cutar ta sanya a cikin matsala ba harda ku ma ta ɗauki haƙƙin ku,amma dan girman Allah ta ci albarkaci na ku yafe mata. Na sani cewar abin da wahala sosai domin kuwa ko kun ce ba zaku yafewa Azrah ba ba zan taɓa ganin laifin ku ba dalili kuwa shine an cutar da ku an muku tabon da ba zaku taɓa mantawa dashi ba sannan Azrah bata cancanci yafiya ko tausayawa daga gare ku ba,amma ku yi haƙuri ba dan halin ta ba ba kuma dan ni ba dan Allah nake neman wannan alfarmar a wajen ku".

Justice Kabir ya faɗa yana haɗe hannayen shi waje guda alamar neman afuwa tare da Sunkuyar da kai ƙasa.

Wani irin kallo Umar ya watsawa Justice Kabir wanda na kasa fahimtar na menene kafin daga bisani yace.

"Kai ko kunyar haɗa ido da mu baka yi ba da sunan kana nemawa azzalumar ƴarka yafiya?, Kar ka manta irin cin amanar da ƴarka ta aikatawa Amrah wadda ko a lokacin jahiliyya sai an tona kafin a samu wanda zai iya aikata abin da ƴarka ta aikata. A sanadiyyar ƴarka muka rasa ƴar uwar mu mafi soyuwa a gare mu!, A dalilin ƴar ka muka zo mu ka rasa ɗan uwan mu wanda mu ke so!, A dalilin ƴar ka mu ka rasa martaba, ƙima, mutunci da duk wata daraja da mahaifin mu yake da ita har ta kai ta kawo mun yi nisa da garin da mu ke so mu ke jin daɗin zama a cikin shi,lokaci guda masoyan mu suka rikiɗe suka koma maƙiyan mu duk ta dalilin ƴar ka, ta ya kake tunanin zamu manta da wannan azzalumar? ta ya ka ke tunanin zamu iya yafewa wadda ta cutar da mu tare da sanya mu a cikin irin waɗannan matsalolin dana ambata?, To bari kaji har abada idan nace har abada ina nufin har gaba da abada ba zan taɓa yafewa ƴar ka ba ko da kowa ya yafe mata to nikam ba zan yafe mata ba,kai in taƙaice maka labari ma ko da Amrah zata dawo duniya idan har ta yi niyyar yafe maka sai na hana".

Umar yana kaiwa nan a zancen na shi ya miƙe da niyyar barin gidan saboda yadda yake jin zuciyar shi tsaf zai iya maƙure wa Justice Kabir wuya saboda kallon shi yake kamar Azrah ce a gaban su take zaune tana neman su yafe mata.

Muryar Malam Kabiru da yaji ya ƙira sunan shi ne ya dakatar da shi daga shirin ficewa daga gidan da yake yi ɗin.

"Umar dawo ka zauna".

Shine kawai abin da Malam Kabiru É—in ya furta.

A hankali Umar ɗin ya juyo ya dawo ya zauna a gefen Usman wanda shi kam har a wannan lokacin bai ce ƙala ba.

"Umar ka yi haƙuri ka sassauta zuciyar ka kasani Ubangiji Allah yana son bayin shi masu haƙuri da yafiya,dan haka mu yi haƙuri wannan yarinyar ta ci albarkaci mahaifin ta da ya taso takanas ya zo har garin nan domin neman yafiyar mu,sai kaga dalilin yafiyar da muka mu su Allah ya kawo mana wani abin alkhairin, sannan ita rayuwa da ka ke gani kullum nasha faɗa muku duk wanda zai zo neman alfarma a wajen to ku yi ƙoƙari ku mishi wannan alfarmar idan har kuna da halin yi domin kuwa shi Alkhairi da ku ke gani danƙo ne baya faɗuwa ƙasa banza,yau idan ka taimaki wani to kai ma baka sani ba wataƙila gobe shi zai taimake ka".

ÆŠan shiru ya yi kafin daga bisani ya Juya ya ya dubi gefen da Justice Kabir É—in su ke zaune sannan ya cigaba da magana.

"Bakomai kamar yadda ka taso ka zo nemar wa Æ´ar ka yafiya mun yafe mata Ubangiji Allah ya yafe mana gaba É—aya,yanzu zaku iya tashi mu tafi massallaci tun da kun ga magariba ta gabato".

Allah Sarki Justice Kabir ɗin jin kalaman Malam Kabiru ɗin bai san lokacin da ya zube duka gwaiwowin shi a ƙasa ba tare da fashewa da wani irin kuka na nadama. Tabbas Malam Kabiru ya cika mutum sannan samun irin shi a duniyar mu a yau sai an tona domin kuwa ya tabbata yau idan da shine a matsayin Malam Kabiru aka yiwa ƴar shi Azrah haka sannan mutumin da ƴar shi ta aikata musu haka yazo neman yafiya wajen shi to wallahi sai ya sanya karnuka sun yi mishi yaga-yaga da naman mutumin. Amma yanzu duba ikon Allah yadda Malam Kabiru ya tarbe shi sannan ko musu bai yi ba yace ya yafewa Azrah.

Haka suka tashi duk suka yi alawla suka nufi masallaci itama Gwaggo Sa'adatu tashi ta yi sannan ta haÉ—a musu abinci dare wanda ta gama tun É—azu ta ajiye mu su tana jiran su dawo.

*****

Kamar yadda Mahaifin Farida ya faÉ—a yau tun asubar fari suka gama duk shirin su na tafiya garin Yobe É—in, daman daren ranar gaba É—aya mahaifin Farida bai iya wani isasshen bacci ba gani yake daren ya mishi tsawo da yawa ya kasa wayewa gashi ya rasa wani irin hali yake ciki murna ne ko kuma akasin haka.

Ƙarfe Shida dai-dai suka fito cikin shirin su na tafiya sai a sannan na ƙara ganin tsantsar kammannin ta da Amrah.

Sanye take cikin wata sea green É—in abaya wadda ta fito da tsantsar baiwar kyawun da Allah ya mata.

A dai-dai wannan lokacin Anwar ya ƙaraso gidan Wayyo zo ku ga idon Anwar a lokacin da ya yi arba da Farida,take kewar Amrah ta dawo mishi sabuwa haɗe da ƙaunar ta.

Kafeta yayi da ido har bai san cewar mahaifin ta ya lura da hakan ba sai da ya ji sauƙar hannun shi a kafaɗar shi yana cewa.

"Malam Anwar mu je ko kar mu makara daman kai kaÉ—ai muke jira".

ÆŠan sosa kai Anwar yayi yana jin wata kunya ta rufe shi sannan suka nufi motar suka shiga suka bar gidan. Anwar ne yake jan motar inda Farida da mahaifiyar ta suke baya mahaifin ta kuma yana gefen Anwar a kujerar gaba.

A haka suka kama hanyar jahar Yobe ɗin sai dai mu musu fatan sauƙa lafiya.

*****

Washe gari sai wajen ƙarfe sha ɗaya su Justice Kabir suka fito cikin shirin su na komawa Zaria.

Har wajen motar su Malam Kabiru suka fito suka raka su.

Tsayaawa yin sallama suka yi Umar kuwa yana da tsaye a gefe sai cika yake yana batsewa tare da aikawa Justice Kabir harara.

A dai-dai wannan lokacin motar su Anwar ta tsaya a gefen motar su Justice Kabir a ƙofar gidan Malam Kabiru ɗin.

Tun da motar ta tsaya Malam Kabiru ya kafe motar da ido a lokaci guda kuma yana jin zuciyar shi tana matsanancin bugawa.

A hankali aka buÉ—e murfin motar aka fito.

Mahaifiyar Farida ce ta fara fitowa sai Farida da Anwar sai kuma mahaifin Farida da ya fito a ƙarshe.

Wata irin sarawa kan mahaifin Farida ya yi a lokaci guda shima Malam Kabiru ya ji haka sakamakon sarƙewar da idanuwan su suka yi a cikin na juna.

Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin su Umar da Farida kowa da abun da yake saƙawa a ƙasan zuciyar shi inda Umar da Usman suka shiga kallon mahaifin su sannan su juya su kalli mahaifin Farida sannan su kalli Farida cikin matsanancin mamaki.

Haka a ɓangaren Farida ɗin ma kallo ta shiga aikawa mahaifin nata da Malam Kabiru ɗin cikin tsananin mamaki domin kuwa duk yadda Anwar ya basu labarin kammannin da mahaifin nata yake da Malam Kabiru sai taga ashe ma wancan labari ne yanzu ne taga gaskiya ra'ayul aini.

Allah mai iko Ubangiji Mai hallita, tabbas Allah abin godiya ne lalle Allah shi kaÉ—ai yake yadda yaso a kan bayin shi a kuma lokacin da ya so ku ga tsantsar kammanni.

Ita kuwa Gwaggo Sa'adatu kallon Farida da ta yi sai da numfashin ta ya É—auke na wucin gadi domin kuwa duk a tunanin ta Amrah ce.

Follow my Whattpad account @shamsiyyamanga.
Arewa books @shamsiyamanga.
Whatsapp number
07060943991
Phone call
09065779330
Don't forget to share and comment pls.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_💀☠️).

_Tsarawa/Rubutawa_

© *SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA* : _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku, Anty Hadiza D Auta, Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_.

*Free book*

------------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*38-39*
________________________________

"HASSAN ashe daman da rabon ruhikan mu zaku sake kasancewa a inuwa ɗaya?, Ashe daman akwai rabon mu sake rayuwa tare? Hassan ashe daman mutuwa ba zata ɗauke mu ba ba tare da mun sake kallon juna ba?, Allah na gode maka bisa wannan ƙudira da ka nuna a kan mu!, Mun ɗauki tsawon shekaru bama tare da juna amma sai gashi lokaci guda Allah ya sake haɗa fuskokin mu".

Wannan su ne kalmomin da suka shiga fitowa ta bakin mahaifin Farida take kuma hawaye ya shiga sintiri ta fuskar shi sannan ya zame a ƙasa kan gwaiwowin shi kafin kuma ya saki kuka mai sauti,yana kai goshin shi ƙasa ya yi Sujuddu shukriyya.

Malam Kabiru ne ya tako da sauri ya ƙaraso har inda mahaifin Farida ɗin yake durƙushe sannan ya sanya hannu ya ɗago kafin kuma ya rungume shi tsam a jikin shi,yana jin wata sabuwar soyayyar shi tana ratsa duk wani ɓargo da ƙashi na jikin shi.

Kuka sosai Malam Kabiru da mahaifin Farida su ke yi kuka kuma irin mai sautin nan da taɓa zuciya,duk wanda yake wajen sai da ya tausaya mu su domin kuwa abin da mamaki da kuma tausayi a ce manyan mutane irin su Malam Kabiru gasu durƙushe a ƙasa suna kuka kamar wasu ƙananan yara.

Farida kuwa da mahaifiyar ta da Gwaggo Sa'adatu suma tunin suka fara kukan duk da basu san dalilin kukan su Malam Kabiru É—in ba.

Justice Kabir kuwa da mukhtar motar da basu iya shiga ba Kennan suka tsaya suma suna ganin ikon Allah.

Shi kuwa Anwar da yake tsaye a gefe tun da suka fito a motar yaga mahaifin Azrah ya cika da tsananin mamakin abin da kawo mahaifin Azrah É—in wajen mahaifin Amrah sannan ya ma aka yi ya san inda su ke.

Ganin da Usman ya yi cewar har mutane sun fara taruwa a wajen su Malam Kabiru É—in sun zama kamar Tv kasancewar unguwar irin unguwa ce ta mutane da yawa duba da yadda ta kasance tsohuwar unguwa. Wannan ya sanya Usman É—in saurin zuwa ya É—aga mahaifin na shi sannan ya yiwa mahaifin Farida da su Anwar iso cikin gidan.

Haka suka ɗunguma gaba ɗaya suka shiga cikin gidan harda su Justice Kabir domin kuwa tafiyar da ya ji ya fasa yin ta gaba ɗaya yana son ya ji alaƙar Malam Kabiru da wannan mutumin.

A tsakar gidan aka baje musu wata ƙatuwar tabarma duba da yadda gidan yake da fili gashi akwai bishiyar maina ƙatuwa a tsakar gidan.

Umar ne ya fita waje inda ya nufi wani shago ya karɓo lemo masu sanyi guda shida da kuma ruwan leda na pure water ya nufo gidan dashi ashe ma shagon na Umar ɗin ne.

Gidan ya ƙara nufowa ya kawo mu su ruwan sannan ya nemi waje ya zauna tare da gaishe da su sannan ya musu barka da zuwa.

Abinci Gwaggo Sa'adatu ta tashi ta zubo musu daman bayan abincin da take matan su Umar da Usman suna kawo mata shiyasa wataran abincin har yawa yake musu.

Abincin suka shiga ci inda Farida ta kasa shiru ta É—ago ta dubi mahaifin ta sannan tace.

"Dad nifa kaina ya kulle, Dad Dan Allah ku fitar damu daga cikin wannan duhun da ku ka sanya kawunan mu, Dad ashe daman ku ƴan biyu ne shine bamu taɓa sannin hakan ba?, Dad ko da wasa baka taɓa sanar damu cewar akwai wani ɗan uwan ka na jini da yake raye ba saboda kullum idan mun tambaye ka sai kace mana ƴan uwan ka duk sun rasu,tun muna tambaya har mu ka daina tambaya, Dad ashe daman kana da ƴan uwa ka barmu ba tare da mun san su ba balle ka nuna mana su, yanzu Dad da halin mutuwa ya kasance ya zamu yi haka zamu mutu ba tare da mun san dangin ka ba,a yanzu ma ba dan albarkacin Ya Anwar da ya zo gidan mu ya sanar da kai cewar ya ga mai kama da kai ba da shikennan nake ga har mu mutu ba zamu taɓa sannin su ba. Dad mai yasa?".

Farida ta ƙarashe maganar cikin rawar murya ga hawayen da suka shiga zarya a kuncin ta.

Sunkuyar da kan shi mahaifin Farida yayi ƙasa sannan ya tsame hannun shi daga cikin abincin da su ke ci ɗin, kafin ya ɗago da kan shi ya dube su yace.

"Farida ki yi haƙuri wallahi ni kaina ban san dalilin da ya sanya na kasa sanar da ku asali na da kuma dangi na ba, ki sani kullum burina bai wuce na yi ido huɗu da ɗan uwa na ba amma kuma ban san dalilin da yasa na kasa neman shi ba".

Ya ƙarashe maganar tare da sanya hannu ya goge da suka zubo mishi.

"HUSSAIN ka sani ni kaina ban san mai yasa ban taɓa jin ina son na nemeka ba duk kuwa da cewar na daɗe da sanin cewa kana raye kuma har unguwar da ka ke a cikin garin Zaria da gidan ka na sani amma kuma ban taɓa sha'awar na nemeka ba".

"To amma Malam ni wannan abin ya bani mamaki to wai shin ta ya aka yi ku ka rabu ma da É—an uwan na ka?, Sannan kana nufin Malam Umaru mai almajirai ba shine asalin mahaifin ka ba"

Usman ya faÉ—a da fuskar mamaki.

Murmushi Malam Kabiru ya sake wanda kana gani kasan cewa yaƙe ne wanda yafi kuka ciwo sannan yace.

"Tabbas Malam Umaru ba shine asalin mahaifin na ba in taƙaice ma bayani ma ban san shi ba sai dalilin zuwa na Nigeria,bamu da wata alaƙa da shi ta ƴan uwan taka sai dai ta musulunci sannan kuma shi ɗin malami na ne. In sha Allah a yanzu zan sanar da ku asalin mu da kuma inda mu ka fito".

*WAIWAYE*
*SHEKARU HAMSIN BAYA DA SUKA SHUÆŠE.*

Asalin mu mutanen ƙasar Nijar ne a wani gari da ake cewa DAMAGARAM mahaifin mu buzu ne fari kyakkyawa ga gashi kamar balarabe. Mahaifin mu ba wani mai kuɗi bane sai dai kawai rufin asirin Allah sai dai akwai wata baiwa da Allah ya yiwa mahaifin mu shine duk wata irin cuta idan tana damun mutum to da zarar an kai shi wajen mahaifin mu to da izinin Allah idan ya mishi addu'a ya tofa a ruwa ya bashi ya sha to zai warke. Sunan mahaifin mu Malam Hamisou shahararren Malami ne da ba iya garin DAMAGARAM ba hatta garuruwan da suke kewaye da namu an san shi,Allah ya zuba mishi ilimin addini sai dai bai yi karatun boko ba duba da cewar a zamanin su karatun boko ɗin ba kowa ya damu da shi ba,amma ilimin addini kuwa tun bai fi shekara goma sha biyu ba a duniya ya sauƙe alƙur'ani mai girma. Da wannan ilimin da Allah ya bawa mahaifin mu ya sanya shi ya shahara sannan ya zamana ya na samun alkhairi da yawaa daga wajen mutane mabanbanta. Mahaifin mu da mahaifiyar mu wadda sunan ta NAJIDATOU ƴan uwan juna ne ƴaƴan Baffanu su ke wannan dalilin ya sanya tun tana ƙarama mahaifin ta ya bayar da ita a mahaifin mu kuma daman a gidan su mahaifin mu ta tashi bayan ta kai munzalin aure aka aurar da ita a mahaifin mu inda suka fara rayuwa mai cike da so da ƙaunar juna. Sosai mahaifiyar mu take nunawa mahaifin mu kulawa sannan tana bashi girma da darajar shi a matsayin shi na mijin ta. Bayan auren su da wasu wattanni ta samu cikin mu sai dai cikin tun lokacin da ta same shi gaba ɗaya ta fara shiga damuwa domin kuwa sosai cikin yake wahalar da ita lokaci guda ta rame ta koɗe ta fice a hayyacin ta wannan dalilin ya sanya aka buƙaci ƙanwar ta mai suna Hafsatou data dawo gidan da zama. Sai dai fa Hafsatou kwata-kwata zuciyar ta bata da kyau amma ba wanda ya taɓa sanin haka a fuska tana nunawa duniya cewar tafi kowa son Najidatou amma kuma a zuciyar ta ba haka bane domin kuwa idan akwai babban maƙiyin Najidatou to bai wuce Hafsatou ba gashi dai uwar su ɗaya uban su ɗaya asali ma Hafsatou ita take bin bayan Najidatou. A haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya har cikin Mahaifiyar mu ya shiga watan haihuwa inda cikin dare naƙuda ta kama mahaifiyar mu gadan-gadan haka Hafsatou ta kama ta suka nufi wani asibiti mafi kusa ko mahaifin mu bata sanarwa ba a cewar ta kar ta tayar mishi da hankali Aikuwa suna isa asibitin ba su kai ko Minti goma ba Allah ya sauƙe ta lafiya inda ta haife yaron ta kyakyawa sak mahaifin mu, murna sosai Hafsatou ta shiga yi inda ta fito da sauri ta nufi hanyar gida domin zuwa ta sanarwa mahaifin mu tun da gashi lokacin ba waya,sai dai bayan ta isa gidan ta sanarwa mahaifin namu sai ta tarar da shi a ƙofar gida ya fito hankali a tashe ganin bai gan su a cikin gidan ba da murnar ta ta ƙarasa wajen shi sannan ta sanar da shi cewa Najidatou ta sauƙa, aikuwa ko gama rufe bakin ta bata yi ba ya juya da sauri ya nufi hanyar asibitin inda ita ma ta mara mishi baya, sai dai lokacin da suka isa murna ta ƙaru domin kuwa sun tarar da yara biyu jere reras a gefen mahaifiyar mu wannan yake nuni da cewa ƴan biyu ta haifa wannan abin ba ƙaramin daɗi ya yiwa mahaifin mu ba har sai da ya zubar da ƙwalla haka dai cikin daren aka sallamo su mahaifiyar mu suka dawo gida kasancewar an duba ana ga bata da wata damuwa. Wani ikon Allah shine lafiya-lafiya mahaifiyar mu ta haife mu sai gashi cikin dare jini ya ɓalle mata kamar an kunna famfo cikin tashin hankali mahaifin da Hafsatou suka ɗakko ta aka ƙara mai da ita asibiti duk yadda likitoci suka so su tsayar da jinin da mahaifiyar ta mu take zubarwa abin ya gagara gashi sun rasa abin da ya janyo mata zubar jinin su kan su likitocin sai da hankalin su ya tashi. Sun yi iya bakin ƙoƙarin su dan ganin sun ceci rayuwar mahaifiyar mu amma kuma Allah bai so hakan ta kasance ba domin kuwa komai sai da yardar shi haka suna ji suna gani mahaifiyar mu ta cika ta ce ga garinku innalillahi wa'innailaihi rajiun Tabbas! Rai baƙon duniya ne kuma mutuwa gaskiya ce maganar Allah ce ko wane mai rai sai ya ɗanɗani ɗacin mutuwa to gashi dai ita kam mahaifiyar mu tata ta ƙare. Faɗar wanda yafi shiga cikin tashin hankali tsakanin mahaifin mu da Hafsatou ɓata lokaci ne domin kuwa kaf cikin su ba wanda zaka iya kwatancen irin halin tashin hankalin da ya shiga. Haka Hafsatou ta dinga suma ta na farfaɗo wa Tabbas sun shiga tashin hankali amma kuma ba yadda su ka iya domin su basu isa su dawo da ita ba. Haka suna ji suna gani aka sallaci mahaifiyar mu aka danganta ta da gidan ta na gaskiya. Su kuma jaririn da ta tafi ta bari akwai matar ƙanin Malam Hamisou sai aka bata tana shayar da su tun da a lokacin itama shayarwa take. Bayan wani lokaci iyayen su mahaifin mu suka zauna suka yanke shawara akan za'a haɗa Hafsatou aure da Hamisou kawai tun da itan ƴar uwar mahaifiyar mu to zata riƙe mata ƴaƴan ta da amana. Sai dai ashe basu san cewar wannan shine babban kuskuren da zasu aikata ba domin kuwa wannan haɗa auren da suka yi shi yayi sanadiyar tarwatsewar farin cikin dangin mahaifiyar mu da kuma mahaifin mu. Lokacin da aka sanar da Hafsatou cewar zata auri Hamisou ta maye gurbin ƴar uwar ta Aikuwa take ta daka tsallen aradu tace ita fa wallahi bata san wannan maganar ba kuma ba wanda ya isa ya sanya ta ta auri Hamisou,Haka aka shiga tafka drama da Hafsatou inda shi kuwa mahaifin ta ganin tana so ta maida shi mutumin banza ya sanya shi ya yi rantsuwa da Allah sai ta auri Hamisou wannan maganar da Hafsatou ta ji daga bakin mahaifin ta ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba domin kuwa ta san halin shi sarai idan har ya furta magana to wallahi ba wanda zai sanya shi ya sanja saboda shi irin mutanen nan ne masu kaifi ɗaya. Haka tana ji tana gani aka ɗaura auren ta da Hamisou ranar ta yi kuka tayi kuka kamar ranta zai fita har ta godewa Allah,sai dai fa ta ƙuduri mummunar manufa a ranta na musgunawa Hamisou da ƴaƴan shi kuma ta yi nasara domin kuwa tun daga ranar da ta sanya ƙafar ta a cikin gidan Hamisou ya nemi duk wani farin ciki a cikin gidan shi ya rasa domin kuwa Hafsatou da gaske take ta shiga gidan da muguwar manufa.

Follow my Whattpad account @shamsiyyamanga.
Arewa books @shamsiyyamanga.
Whatsapp number
07060943991
Phone call
09065779330.

*FANSAR FATALWA*
( _Horror Story_ 💀☠️).

_Tsarawa/Rubutawa_

*© SHAMSIYYA MANGA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*: _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku Anty Hadiza D Auta Sis Amira Adam Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda ku ke ina son ku fisabillillahi_.

*Free book*

-------------------------------------------------
*Bissimillahir rahmani rahim*

*040*
________________________________

Tun daga ranar da Adda Hafsatou ta sanya ƙafar ta cikin gidan mu ta fara nunawa mahaifin mu tsantsar ƙiyayya duk wani salon rashin mutunci Adda Hafsatou ta tsiro shi a cikin gidan nan haka mahaifin mu ya zama shi da gidan shi bashi da wata walwala domin kuwa dai-dai da ruwan gidan sai da Adda Hafsatou ta mishi shamaki da shi balle kuma a zo ga gandun abinci wanda shi zai nemo amma kuma cin abincin yafi ƙarfin shi. Sai dai ko da wasa mahaifin mu bai taɓa ɗaukar ɓacin ran Adda Hafsatou ɗin ya sanya a ranshi ba kullum addu'a yake ma ta da fatan shiriya,tun daga sannan ya ƙara tabbatar da cewa ya rasa Najidatou rashi na har abada. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yau fari gobe baƙi sai dai a ɓangaren mu mahaifin mu kullum baƙa ce domin kuwa i zuwa yanzu ranshi mutuncin Adda Hafsatou ɗin ya ninka na da a da tana barin shi ya kwana a cikin ɗaki amma a yanzu ta rantse ba zai ƙara kwana mata a cikin ɗakin ba haka dare yana yi zata tiso ƙeyar shi a gaba duk tsananin sanyi da damina haka zai yi shimfiɗa a tsakar gida ya kwanta,gashi wani ikon Allah kamar an kulle mishi baki duk wannan abin da take mishi ɗin bai taɓa buɗar baki yace mata kanzil ba. A ɓangaren mu kuwa muna wajen matar ƙanin mahaifin mu wadda take gidan tana shayar da mu sai dai ƙofar su daban. A lokacin da muka cika watanni sha biyar a duniya sai Adda Hafsatou ta shiga har ƙofar Sajida ta buƙaci ta bata mu zamu koma wajen ta da zama da farko Sajida ta so mata musu amma tunowa da alaƙar da take tsakanin ta da mahaifiyar mu ya sanya bata musa mata ba ta ba da mu. Tun daga ranar da muka dawo hannun Adda Hafsatou sai ya zamana ƙiyayyar da take yiwa mahaifin mu ta shafe mu domin kuwa Adda Hafsatou rufe ido ta yi ta manta da wacece mahaifiyar mu a wajen ta inda ta shiga gana mana azaba iri-iri mun sha wahala matuƙa a hannun Adda Hafsatou domin kuwa ni na tabbatar tsawon rai ne kawai ya kawo mu zuwa wannan lokacin inda ace cuta tana kisa to da ta daɗe da hallaka mu. Lokacin da mahaifin mu ya fahimci halin da mu ke ciki a wajen Adda Hafsatou sai ya mata magana domin kuwa Allah ya gani yana son mu ba zai taɓa barin wani abu ya cutar da mu ba,buɗar bakin Adda Hafsatou a lokacin da ya mata maganar sai tace idan har yana son mu yana kuma son ya cigaba da ganin mu a tare dashi a raye to kawai ya sake ta, Shikennan idan ya yi haka wallahi zata ƙyale mu amma muddin zata cigaba da zama a gidan to wannan ma kaɗan mu ka gani. Ko kaɗan mahaifin mu bai ɗauki maganar ta da wani muhimmanci ba domin kuwa shi a tunanin shi duk barazana ce ashe kuwa da gaske take. Lokacin da muka cika shekara biyu a duniya na fahimci cewa Hussain yana da wata irin zuciya inda duk irin muguntar da Adda Hafsatou ta mana to fa sai ya zamana ya riƙe ta a ranshi daga kallon da yake mata kaɗai zaka fahimci cewa Hussain ya tsane ta tsana mafi muni.
Bayan Shekara biyar a lokacin mu kuma mun cika shekara Bakwai a duniya abubuwa da dama sun faru a tsakanin waɗannan shekarun wanda faɗin su ma bashi da amfani domin wataƙila idan kun ji ku ɗauki tsanar Adda Hafsatou ku dasawa zuciyar ku ni kuma ba zan so haka ba tun da ko ba komai ita ɗin kamar mahaifiyar take a wajena. Wata rana da ba zan taɓa mantawa ba mahaifin mu ya tafi wani taro na malamai a cikin Nijar Adda Hafsatou ta zo ta same mu da dare, domin kuwa lokacin ƙarfe goma har ta wuce sannan tace mana mu zo zamu rakata wani waje, tun a sannan jikina ya bani wani abu amma sai ban nuna mata ba muka fito muka bi bayan ta kai tsaye wata unguwa ta nufa da mu inda ta tsaya a ɗan wani lungu bamu daɗe sosai da tsayuwa ba sai ga wani mutum ya zo inda mu ke tsayen sannan suka yi magana cikin Yaren buzanci ƙasa-ƙasa yadda ba zamu ji mai su ke cewa ba, kafin ya ciro wani abu a cikin wata leda da yawa a dunƙule kamar kuɗi sannan ya miƙa mata bayan ta karɓa ne ta ƙudundune a cikin hijab ɗin ta kafin ta juyo ya dube mu ta ɗakko wani abu fari a ƙulle a leda ta busa mana a fuskar mu take kan mu ya sara a lokaci guda sannan mu ka ji gaba ɗaya kamar ana hura mana wutar ƙiyayyar ƙasar Nijar ɗin a cikin ran mu. Mutumin nan ne ya kama hannayen mu sannan ya nufi marabar da ake shiga jirgin ruwa a shigo ƙasar Nigeria lokacin da mu ka isa bakin tekun mun tarar da har an lodawa wani jirgi kaya irin wanda ake Safarar su daga Nijar zuwa Nigeria,ba mutane a cikin jirgin daga matuƙin jirgin sai shi wannan mutumin sai kuma kaya a cikin buhuna wanda bamu san ko Meye ba,isar mu bakin jirgin ke da wuya sai wannan mutumin ya hankaɗa mu cikin jirgin sannan shima ya shiga kafin matuƙin jirgin ya kaɗa igiyar jirgin mu fara tafiya. Ban san adadin lokacin da muka ɗauka muna tafiya ba domin kuwa ana sanya mu a cikin jirgin kamar abun haɗin baki muka ɓingire mu ka fara bacci ni da Hussain bamu tashi farkawa ba sai daf da asuba shima iskar asubah ce ta hura mu sai dai abin mamaki ina farkawa na ga wannan mutumin da ya taho da mu a yashe a gefe an mishi yankan rago daga shi har matuƙin jirgin na mu nan fa hankali na ya tashi sai dai wannan bashi ne abin tashin hankalin ba face buɗe ido da na yi na ga ba Hussain ba alamar shi a tare dani, innalillahi wa'innailaihi rajiun haka na tashi ina kuka na shiga ƙwalawa Hussain ƙira amma shiru ka ke ji wai malam yaci shirwa na ɗan yi tafiya mai ɗan tsayi kafin na zo bakin titin da ban san ina bane,zama na yi a gefen titin na cigaba da shirga kuka ga yunwa da nake ji kamar naci babu tun da rabona da abinci yau kwana biyu Kennan sai zallar ruwa da yake cikina. Daga nesa na hango wata mota tana tahowa lokacin garin ya fara haske tashi na yi inda na fara ɗagawa motar hannu har mai motar ya wuce sai kuma naga ya dawo da baya, tsayawa ya yi a gefe na sannan ya leƙo kan shi daga cikin motar ashe ma motar kasuwa ce tare da tambaya ta ina zan je, ƙarasawa na yi jikin motar ban yi magana ba domin kuwa ban san inda zan ce mishi zan je ba,ganin na yi shiru ne ya sanya shi fara ƙoƙarin tayar da motar zai bar wajen, sai dai da sauri ɗaya daga cikin fasinjojin motar ya dakatar da shi sannan ya fito ya ɗakko ni ya sanya ni a cikin motar kafin ya cewa direban motar su tafi. Bamu yi tafiya mai tsayi ba muka shigo cikin wani gari inda aka sauƙe mu a tasha. ZARIA shine sunan garin da naji an ambata.Rarraba idanu na shiga yi ina kallon duk mutanen da su ke kai kawo a cikin kasuwar, ji na yi an dafani da sauri na juya inda na yi arba da wannan mutumin yana mun murmushi. Kama hannu na yayi sannan mu ka bar wajen mashin mu ka hau inda mu ka nufi wata unguwa mai yawan mutane kai tsaye wani gida mu ka shiga mai zauruka har guda uku ga almajirai nan zaune a ƙofar gidan suna karatu wasu kuma a cikin gidan sai kaiwa su ke tsakanin cikin gidan da zauren gidan. Abin da na lura dashi shine duk inda mu ka wuce almajirai sai sun tsuguna sun gaishe da wannan mutumin wannan shi ya mun nuni da cewa malamin su ne, a cikin gidan mu ka yada zango a bakin rumfar wani ɗaki, wata mata ce ƴar dattijuwa ta iso tare da kawo mana ruwa sannan ta zauna gefen shi tana mishi sannu da dawowa Sai da mu ka ci abinci sosai na buɗe ciki na cinye abinci tass sannan mutumin yace a bani ruwa na yi wanka Aikuwa wannan matar da na lura matar shi ce ita ta haɗa mun ruwan wankan sannan ta kai mun banɗaki kafin ta shiga ta wanke ni tas, bayan mun fito ne aka kawo mun wasu kaya na sanya sannan mutumin ya dube ni yace daga ina nake, shiru na yi domin ina gudun kar na sanar dashi ya ce zai mayar dani garin mu ni kuwa ban san komawa,shirun da yaga na yi ne ya sanya shi sake mun tambaya sai dai take nace mishi nima ban san garin mu ba,iyayena kuma sun mutu sannan ban san ta yadda aka yi na zo wannan wajen ba,sosai wannan mutumin mai suna Malam Umaru da matar shi Talatu su ka tausayamun tun daga ranar suka riƙe ni tare da haɗa ni da ƴaƴan shi sannan ya sanya Ni a Makarantar boko shi kuma ya shiga koyamun karatun Addini. A haka na taso gidan Malam Umaru inda ba zaka taɓa kallo na kace bashi ya haife ni ba saboda yadda ya ke kula dani fiye da yadda yake kula da ƴaƴan shi na cikin shi, a haka har na sauƙe littattafai da dama na addini karatun boko ma Alhamdulillahi na yi shi ba laifi inda har na kai matakin Diploma a sannan ne kuma Malam Umaru ya haɗa mu aure da ƴar shi mai suna Amrah mun haifi Hisham da ita ne kuma haihuwar ta tsaya mata gaba ɗaya domin kuwa har Hisham ya kai shekaru bakwai a duniya Amrah bata sake ko ɓatan wata ba,da haka na roƙe ni alfarmar dan Allah na ƙara aure da farko naƙi yarda amma da mahaifin ta ya sanya baki sai na auri Sa'adatu mutuniyar kirki domin kuwa bata ɗauki Amrah a matsayin kishiya ba tana bata girman ta sosai sannan suna zaman lafiya fiye da tunanin mai tunani. Sa'adatu bata rufa shekara ba sai da ta haifamun yaro Namiji inda na sanya mishi suna Umar sunan mahaifin Amrah,bayan haihuwar Umar da shekara biyu ta sake haihuwar ɗa Namiji inda na sanya mishi suna Usman mai sunan mahaifin ta, tun daga wannan haihuwa ita ma Shikennan haihuwa ta tsaya mata sai da muka shafe shekaru ashirin a haka ba'a sake mun haihuwa ba kafin daga bisani Amrah ta samu ciki mai bala'in wahalar da ita, ciki ya cika wata tara inda ta zo haihuwa ta haifi ƴar ta mace kyakyawa mai m
Kama da ita sak sai dai tana haihuwa da wasu ƴan mintuna Allah ya karɓi rayuwar ta na yi kuka Sa'adatu ta yi kuka iyayen Amrah sun yi kuka har mun gode Allah, ranar suna kuwa Yarinya ta ci sunan mahaifiyar ta. Alhamdulillahi a ko ina zan yabi Sa'adatu kuma ina sanya mata albarka domin kuwa ta riƙe Amrah tsakani da Allah kamar ita ta haife ta domin dai-dai da tsawa ban taɓa jin Sa'adatu ta yiwa Amrah ba har zuwa ranar da Amrah ta koma ga mahaliccin ta. Daga baya ne kuma na gano cewar Hussain yana cikin garin Zaria har unguwar da yake na gano amma kuma duk ranar da na yi niyyar zuwa inda yake sai naji komai ya ɓace mun ko kuma naji kaina ya kama mun matsanancin ciwo. Sunana kuma ya sanja daga Hassan zuwa Kabiru ne a lokacin da nazo gidan Malam Umaru inda ya tambaye ni sunana shima na nuna mishi ban sani ba,wannan dalilin ya sanya ya sanja mun suna na koma Kabiru.
ÆŠago kai Malam Kabiru yayi sannan ya dubi É—an uwan shi Hassan wanda idanun shi yayi jawur kafin ya juya ya dubi mutanen da su ke wajen suma ido yayi jawur yace.

"Wannan shine kaÉ—an daga cikin abin da ya faru da rayuwa ta bayan Adda Hafsatou ta rabamu da mahaifar mu".

Kuka sosai su Gwaggo Sa'adatu su ke da mahaifiyar Farida, su ma su Umar gaba ɗaya idanu yayi jawur sai ajiyar zuciya su ke sauƙewa.

"To Amma Dad kai ya aka yi kuka rabu da É—an uwan ka?".

Farida ta faÉ—a cikin rawar murya.

Ajiyar zuciya mahaifin ta ya sauƙe kafin ya buɗi baki ya fara magana.

"Maganar gaskiya ban san yadda aka yi mu ka rabu da Hassan ba kawai Ni dai buɗar ido na yi na ganni a kan gadon asibiti ga wani mutum da matar shi da kuma ƴar shi wadda bata fi shekara uku ba gefen su,kallon su na yi inda na kasa furta komai sai sunan Hassan, ƙoƙarin tashi na shiga yi inda mutumin suka riƙe ni tambaya ta ya shiga yi ya sunana amma shiru sai kuka kawai da nake ɗirka. Sai da muka kwana biyu a asibiti kafin aka sallame mu bayan an sallame mu ne suka wuco dani gidan su da yake cikin garin Kaduna, lokacin da muka zo gidan ɗaki guda aka bani matar ta shi ta shiga ta mun wanka ta bani kaya na sanya aka kawo mun abinci na alfarma sunana suka tambaye ni inda na sanar da su sunana Hussain kuma ni ɗan ƙasar Faransa domin kuwa ina yawan jin sunan garin a bakin mahaifin mu sai dai na sanar da su cewar iyayena sun mutu inda su ka tausayamun su ka rike ni har na girma na yi karatu tun da ta matakin primary har high institution duk wannan mutumin mai suna Alhaji Sani shi ya biya mun kuma Alhamdulillahi na kammalla inda na yi karatu a fannin likitanci na auri ƴar shi mai suna Halima muna da yara biyu da ita ɗaya na miji mai suna Khamis yana ƙasar Bahrain yana karatu sai kuma Farida wadda gata nan a zaune. Aiki shi ya dawo dani garin Zaria domin kuwa yanzu haka ni lecturer ne a cikin jami'ar Ahmadu Bello da take garin Zaria lokacin da incident ɗin Amrah ya faru bana ƙasar ina Egypt na tafi ƙarin karatu shiyasa ban santa ba ban kuma taɓa ganin ta ba".

Shiru wajen ya ɗauka aka rasa wanda zai ce uffan kowa da abin da yake saƙawa a cikin zuciyar shi, da ƙyar dai Justice Kabir ya buɗi baki ya fara magana.

"Gaskiya duniya marrassa tsoron Allah sun yi yawa a cikin ta yanzu ƙanwar mahaifiyar ku ita ta ta yi sanadiyar rabaku da mahaifin ku saboda kawai son cimma wata manufa Tata,ya Allah ya Ubangiji ka ƙara buɗe mana idanun mu wajen fahimtar gaskiya da gane banbanci tsakanin duhu da hask, Tabbas duniya ta zama abar tsoro yarda da amana sun yi ƙaranci wanda baka tunanin zai ci amanar ka a wannan lokacin shi yake cin amanar ta ka,shin ko mutane sun manta cewar akwai ranar sakamako akwai ranar da kowa zai tsaya a gaban Ubangiji ya kare kan shi a kan abin da ya aikata?, Ita ce ranar da baki ba zai magantu ba wajen bayar da shaida sai dai wasu sassa na jikin ka, Tabbas yanzu mutum ba abin yarda bane labarin Amrah da kuma labarin ku da naji ya sani na ji ba zan ƙara yarda da kowa a duniya ba,domin kuwa wanda yafi kusanci da kai shine yafi saurin cin amanar ka. Kaico rayuwa Azrah kin cuci kan ki ni ma kuma na cuce ki da na kasa baki tarbiyya wadattaciya".

Justice Kabir ya faɗa yana fashewa da kuka,haƙuri Malam Kabiru suka shiga bashi sannan Malam Kabiru ya dube shi yace.

"A'a Kabiru kar ka ce haka domin kuwa ba duka mutanen duniyar bane aka taru aka zama ɗaya ba,a ko ina akwai na gari akwai na banza,kawai dai amanar ce ta yi ƙaranci amma akwai masu tsoron Allah masu amanar sai dai kuma a zahirin gaskiya ba su da yawa,abin da yafi sauƙi kawai shine mutum ya zamana mai riƙe sirrin shi sannan kar ya zamana yana sakewa da kowa sosai gudun abin da kan je ya dawo, Allah Ubangiji ya shiga tsakanin mu da maƙiyan mu ya kuma bamu ikon riƙe amanar duk wani wanda ya yarda damu".

Da Ameen su ka amsa gaba ɗaya kafin daga bisani su ka tashi su ka ce bari su je su yi sallar azahar. Bayan sun yi sallar sun dawo ne Justice Kabir ya ce wa Malam Kabiru zasu wuce Zaria a yanzu Malam Kabiru ya so ya ce mishi su bari sai gobe amma kuma ya ƙi yarda yace yana da abubuwan yi a gidan. Haka su ka raka shi motar shi ya shiga ya tafi bayan ya ajiyewa Malam Kabiru ɗin maƙudan kuɗaɗe.

Su kuma su ka koma cikin gida da shirin nan da kwana uku za su tafi Nijar gaba É—ayan su, shima Anwar washe gari da safe ya musu sallama ya koma gida.

Cikin kwanaki ukun da Malam Kabiru su ka shirya su ka tafi Nijar ɗin da ƙyar su ka iya gane unguwar su saboda sanje-sanje da aka samu na zamani. Zuwan bai mu su daɗi ba domin kuwa sun tarar da labarin cewa mahaifin su ya daɗe da rasuwa, sai Adda Hafsatou da suka tarar wadda ta tsofe ta yi wata iri da ita,Allah sarki rayuwa ta haɗu da cutar hawan jini inda gefen jikin ta ya shanye bata iya komai kana dosar cikin ɗakin da take wani wari ne haɗe da zarni zai ziyarce ka sakamakon fitsari da kashin da take a jikin ta,gashi bata taɓa haihuwa ba,balle wani daga cikin ƴaƴan ta ya taimaka mata,mutane kuwa ba wanda yake zuwa inda take cikin gidan ma can daga gefe aka ware mata ɗaki irin na langa-langa ɗin nan kamar wata Akuya. Sosai su Malam Kabiru su ka tausaya wa halin da take ciki wai hausawa su ka ce naka naka ne take Malam Kabiru ya sanya aka ɗauke ta aka kai ta asibiti,sai dai asibitin sun ce ba zasu iya mata magani ba sai dai su tafi cikin Nijar, Hussain cewa yayi kawai su mayar da ita gida ta mutu amma Malam Kabiru ya hana haka ba dan ran shi ya so ba su ka wuce da ita Nijar ɗin domin kuwa shi kam Hussain har gobe haushin ta yake ji. Nan ma asibitin Nijar ɗin da ƙyar da su ka karɓe ta sai dai cikin dara Allah ya karɓi rayuwar ta bayan ta gama iface-iface tana ƙiran sunan Hamisou da ƴaƴan shi akan su yafe mata. Shikennan rayuwa duniya ba mattabata ba gashi dai Hafsatou ta rasu a lokacin da ta gama wulaƙanta kowa ya guje ta su waɗanda ta wulaƙanta ɗin su ne dai su ka dawo su ka taimake ta.

*BAYAN WASU SHEKARU*

Abubuwa da dama sun faru ciki har da auren Farida da Anwar da aka yi , Amira kuma da Inspector Rasheed a lokacin har Amira ta haifu ƴaƴan ta biyu duka mata inda ta sanya mu su suna Amira da Amrah. Su ma a ɓangaren Anwar da Farida sun haihu sun haifi ƴar su ɗaya kyakyawa sak Farida ita ma taci sunan Amrah. A ɓangaren Justice Kabir ku garin Giwa ya je inda ya gina makaranta guda mai sunan AMRAH MEMORIAL SCHOOL. Sannan bayan haka ya nemawa Usman aiki a wani Company da yake cikin Kaduna na yayan shi. Shi ma Malam Kabiru yanzu rayuwa ta sanja musu domin kuwa yana ta samun cigaba ta ko ina ga shi ɗan uwan shi Hussain sosai yake kulawa dashi sai dai har zuwa yanzu Malam Kabiru ya ƙi komawa garin Zaria yana Potiskum a cewar shi tafi mishi daɗin zama. Sai dai yana zuwa jifa-jifa wajen iyalan Malam Umaru tun da shi kam ya rasu. Komai dai Alhamdulillahi sai godiyar Allah kawai.

*Alhamdulillahi Lazi bini'imahi tattimmu salihat, a nan na kawo ƙarshen littafi nan nawa mai suna FANSAR FATALWA, Allah na gode maka da ka bani ikon kamalla wannan littafin lafiya kamar yadda na fara lafiya,abin da na faɗa dai-dai Ubangiji ka bani ladan shi kuskuren da nayi a ciki Allah ka yafe mun. Dan Allah duk wanda ya karanta wannan labarin ya yi koyi da kyakyawan halin ciki sannan a yi fatali da munanan halin ciki. Ina ƙara miƙa godiya ta ga duk masoya wannan littafin nawa na FANSAR FATALWA waɗanda na sani da waɗanda ban sani ba musamman* *ma ƴan group ɗina da kuma ƴan sauran groups na gode sosai da addu'oin ku a gare ni Ubangiji Allah ya saka mu ku da mafificin alkhairi. Na gode da nuna soyayyar ku ga wannan littafin son so fisabillillahi. Sai kuma mun sake haɗuwa a sabon littafi na wanda* *zai zo mu ku immediately ana yin sallah,fata na shine ku karɓe shi kamar yadda ku ka karɓi wannan. Na gode sosai. Domin gyara ko sharhi ƙofa ta* *a buɗe take domin karɓar gyararrakin ku zaku iya magana da ni kai tsaye ta number ɗin da take* *ƙasa* .

Follow my Whattpad account @shamsiyyamanga.
Arewa books @shamsiyamanga.
Whatsapp number
07060943991
Phone call
09065779330

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.