Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 15 of 15
SHAFI NA SHA BIYAR
Masarautar Zulwara
Tun Sarki Dikko yana jin ruwa mai sanyi yana mamaye shi, har ya ji yanayin ruwan ya fara sauyawa zuwa mai ɗumi-ɗumi. Wata irin tsawa ya ji ta tashi a cikin kabarin Sarauniya Humaira, ɗakin kabarin ya fara girgiza tamkar ƙasarsa za ta rushe ta haɗiye shi. Duk taurin zuciya irin ta Sarki Dikko, sai da ya ji wani matsanancin tsoro ya kama shi. Har ya fara saddaƙar da shi kansa tasa rayuwar ta zo ƙarshe, saboda ji ya yi ruwan da ya shanye shi ya daskare ta yadda ba zai iya motsa koda ɗan yatsansa. Yana cikin wannan yanayin, sai ya ji ruwan ya fara yin ƙasa. Wutar cikin ɗakin ta dawo kamar yadda take ci da farko, sai dai a ɓangare ɗaya ji ya yi jikinsa ya yi lakwas har da ƙyar yake iya motsa ƙafarsa. Ganin ya samu kansa, Sai Sarki Dikko bai daddara ba. Ya fara jan jiki a sanyaye ya tunkari wurin da littafin yake, yana miƙa hannu ya ji gabansa ya yanke ya faɗi. Amma haka ya yi ta maza ya miƙa hannunsa na hagu da zummar ya ɗauka. Wani irin sagewa mai haɗe da yin sanyi ya yi masa, ya janye hannunsa da ƙyar ya miƙa hannun dama a nan ya samu nasarar ɗauko littafin. Sai dai yana duba littafin ya ji daga bayansa an ce.
"Mutuwa, Rayuwa, Hatsari da Rai."
Da sauri ya waiga, sai dai bai ga komai ba, cike da mamaki ya sake maimaitawa.
"Mutuwa, Rayuwa, Hatsari da Rai. Me hakan yake nufi?"
Ya wurga wa kansa tambaya ba tare da hango wurin da amsar take ba.
Cikin ɗakin ne ya cigaba da girgiza tamkar ƙasar ciki za ta faɗa ciki, don haka cikin sauri Sarki Dikko ya fice daga ɗakin sannan ya sake biyo siriryar doguwar hanyar da ya shigo. Sai da ya ƙasara cikin turakarsa, sannan ya rungume littafin a ƙirjinsa ya runtse ido cike da tsananin farinciki.
"Haƙiƙa na yarda rayuwa kasada ce, cimma buri jajircewa ce. Duk wanda ya yi tseren agali tilas ɗayan biyu zai faru, kodai ya mace murus kuma ya kai ga hawa turbar tudun tsira."
Sarki Dikko ya furta cike da farinciki yana sake ƙanƙame littafin kamar wani zai ƙwace masa. Har ya kai hannu zai buɗe littafin, sai kuma ya saki murmushi ya nufi ɗakin da tsoho Babagana yake zaune. Sai da ya zauna a kujerar da ke fuskantarsa, cikin izza, isa da ƙasaita ya ɗago masa littafin.
Cikin tsananin mamaki Babagana ya É—ago a hargitse yana kallonsa, Sarki Dikko ya saki malalacin murmushi mai É—auke da manufa da izgilanci ya ce.
"Babagana na sha sanar da kai ni mai nasara ne! Duk wani abu da na saka a gaba sai na same shi."
Babagana ya kawar da mamakin fuskarsa, don kada Sarki Dikko ya fahimci lagonsa ya ce.
"Kana da nasara a wurin da nasarar da ma can taka ce, Sarki Dikko kada wannan nasarar da ka samu ta sa ka fara jin ka a matsayin mai nasara."
A ɗan harzuƙe Sarki Dikko ya ce. "Me kake nufi?"
"Ina nufin kai ba komai ba ne, domin wannan abin da ka yi kowanne mai numfashi ma zai iya."
Babagana ya furta, duk waɗannan maganganun yana yin su ne don ya dasa wa Sarki Dikko wasu-wasi a zuciyarsa. Domin har a cikin ransa yake jin tsoro da shakkun makirci da taurin zuciya irin ta Sarki Dikko. Miƙewa tsaye Takawa ya yi, ya kalli Babagana ya bushe da wata mahaukaciyar dariya, wacce ta sake kaɗa hanjin cikin Babagana.
"Matuƙar wannan littafin shi ne zai ja mini gora zuwa ga ɗan uwanka Tsoho Sulaimanu da Dattijuwa Kursum. Ina mai tabbatar maka da nesa ta kusa zuwar mini kusa, haka zalika ina gab da mallakar manyan kundin da kowanne basarake yake fatan samu musamman Sarki Gambo da Sarki Giɗaɗo."
Sarki Dikko ya yi furucinsa yana sake sakin dariyar ƙeta, duk da kalamansa sun sayaya jikin Babagana hakan bai dakushe masa ƙwarin gwawa ba. Cikin yanayin jikin tsufa ya dafa bangon ɗakin ya miƙe, sai da ya yi taku biyu ya matsa gaban Sarki Dikko sannan ya ce.
"Na ji daɗi da rashin sani ya zama babban duhu ga kowanne mai numfashi. Ba zan ce maka uffan a kan maɓoyar Kundi uku ba, haka kuma ba zan dakatar da kai daga bulayin nemansa ba. Sai dai zan ce maka ga wani abu a kan matar sarki da ace da ido da tuni ta gani. Ko kuma na ce maka da magani a gonar yaro, amma rashin sani ya sashi bai sani ba." Babagana ya saki dariyar mugunta. Da sauri Sarki Dikko ya waigo ya ce.
"Akwai abin da ka sani Babagana, ka hanzarta sanar da ni tun ban É—auki mummunan mataki a kanka ba.
Babagana ya gyaɗa kai ya ce, "Tabbas ina da masaniya, ina da sani mai zurfi game da wannan Kundin. Amma ba a yanzu ne lokacin ya dace na motsa ba, hukuncinka kuma a shirye nake da na karɓe shi kowanne iri ne. Amma ka sani, koda ka kashe ni na rantse da sarkin da ya busa mini numfashi. Ba za ka dakatar da wacce take ƙoƙarin ceton rayuwata daga nakasa taka rayuwar ba. Abu ɗaya zan ce maka Sarki Dikko, ita ɗin ta jima da yi maka illa, don ta kowacce fuska ta shammace ka. Ba za ka fuskanci haka ba sai a nan gaba, na tabbata ko ba na raye za ka tuna da kalamaina."
Shiru Sarki Dikko ya yi yana nazari, cike da sanyin jiki ya ce.
"Wace ce ita? A ina take? Me ya sa ban santa ba? Ko a binciken bokayena me ya sa ba su hango mini ita ba?"
"Saboda ita ma ba ta fito ba sai da ta shirya, ta kasance tamkar ingarman dokin da ke gudu a dokar dajin sahara. Ta kasance wuta mai laƙume duk wani makamashi, ita ɗin zakanya ce mai ɗauke da zuciyar gawurtattun zakuna dubu..."
"Ya isa!"
Sarki Diko ya katse Babagana daga maganar da yake yi, cikin ƙufula ya ce.
"Duk hatsabibancinta sai na tsamo ta da hannu."
Babagana ya saki murmushi ya ce.
"Ina maka fatan alheri."
Daga haka Sarki Dikko ya fice daga É—akin cikin takaici.
Sarki Dikko zama ya yi a kan ƙasaitacciyar kujerarsa, ya ɗago littafin da aka buga bangonsa da fatar tsohon jemage. Daga ƙasan litttafin akwai wani gashi, wanda duk wanda ya san gashin ɗawaisu yana gani zai gane shi ne. Daga sama kuma wani gashi ne, wanda duk wani maharbi yana gani zai san gashin jelar zaki ce. Daga tsakiyar bangon littafin cikin rubutun ajami an rubuta 'RUWA A WUTA' Sai waɗansu ƙananan rubuce-rubucen ajami, wanda sai ka ƙura ido sosai za ka gane abin da aka rubuta. Ganin zai wahalar da kansa, ya sa shi buɗe shafin farko ba tare da ya karanta ba.
"Duk kalma É—aya da ka tsallake daga cikin littafin nan, daidai take da gayyato masifar da ba ka yi tsammani ba a kundin rayuwarka."
Ya ji an furta da wata irin murya, wacce yaka jin kamar ya taɓa saninta. Yana sauke idonsa don ya cigaba da karatu ya ji sallamar Shamaki a bakin ƙofa, da sauri ya rufe littafin. Ya ƙarasa can ƙarƙashin gado ya zaro wata tsohuwar akwati ya zura a ciki. Sai da ya koma mazauninsa, sannan ya ba wa Shamaki izinin shiga.
"Allah Ya taimake ka, Allah Ya ƙara maka lafiya. Jakadiya ce take neman iso idan ka lamunce mata ranka shi daɗe." Shamaki ya furta yana sunkuyar da kai ƙasa.
"A ba su dama."
Sarki Dikko ya furta a taƙaice. Cikin girmamawa Shamaki ya ce.
"A huta lafiya ranka shi daÉ—e."
Miƙewa ya yi ya fita bayan Takawa ya ba shi izini, yana fita Jakadiya ta shiga. Sai da ta zube ta kwashi gaisuwa bayan ya amsa mata ta ce.
"Allah Ya taimake ka, Fulani Asiya ce take son ganawa da kai ranka shi daÉ—e."
Murmushi ta ga ya suɓuce masa, cike da annushuwa ya ce.
"A cewa Fulani muna nan zuwa gare ta, mun hutar da ita da zuwa wurinmu."
"Allah Ya ja zamanin amale, Allah Ya taimaki fari mai farar aniya. Garnaƙaƙin dutse kake, kowa ya yi faɗa da kai shi zai faɗi. Hadari mai zubar da ruwa, ƙasa mai karɓar shuka idan an gume ki rumbu ya kwana da yunwa. Ina gwanin wani ga nawa, ina wanda yake iƙirarin shi sarki ne ya zo ga ubangidansa. Sai ka yi gajimare mai ɓoye wata, sai ka yi damuna mai zubar da ruwan alheri. Sai ka yi ko da tsiya ko da ƙarfin ikon Allah."
Murmushi Sarki Dikko ya yi ya ce, "Kulawa da yabawa Jakadiya."
Cike da jin daÉ—i Jakadiya ta yi masa jinjina ta ce.
"Idan mai martaba ya lamunce zan iya tafiya?"
Amsa mata ya yi sannan ta yi masa godiya ta fita.
Da fitar Jakafiya babu jimawa Sarki Dikko ya kira Shamaki, ya sanar da shi zai ziyarci sashen matansa wurin Fulani Asiya. Sai da ya koma ya shirya cikin shigar ƙasaita, ya yi kyau sosai sai baza ƙamshi yake yi. Sabuwar alƙyabba ce ya saka ta, wacce ta sha adon jajayen duwatsu. Fitowa ya yi yana dogara sandarsa, fadawa da Dogarai suka shiga yi masa kirari suna take masa baya. Har sai da suka je sashen matansa, sannan ya dakatar da su. Ya tura ƙofar ya shiga, sashen Fulani Aisha ne a farko, sai sashen Fulani Halima, Sashen Fulani Hauwa kulu na ƙarshe shi ne sashen Fulani Asiya. Da yake a jere kamar yadda suke uwargida da mabiyarta har zuwa amaryarsa Fulani Asiya.
Duk a tsammaninsu zai leƙa sashensu ya fara ganim lafiyarsu, amma ga mamakinsu sai suka ga ya wuce wurin Fulani Asiya.
Fulani Hauwa kulu tana daga ɗaki ta ga giftawarsa, mamaki da takaici ya kamata. Tana nan zaune ta ga ya fito har zai fita ta yunƙura ta fita wurinsa.
"Ranka shi daÉ—e barka da hutawa."
"Barka!"
Ya amsa mata a daƙile, duk da bata ji daɗin abin da ya yi mata ba. Amma sai ta saki murmushi ta ce.
"Ranka shi daÉ—e idan ba za ka damu ba mu shiga daga ciki..."
"Duk abin da za ku faÉ—a, muna sauraronku ba sai mun shiga ba."
Ya furta fuska a haÉ—e, ajiyar zuciya ta sauke tana haÉ—iyar yawu mai É—aci ta ce.
"Ranka shi daɗe haihuwa fa na yi, na aika Jakadiya ta sanar da kai ɗan babu rai, amma har aka binne shi ba ka zo ba. Kuma ba ka ga jaririn ba, sannan yanzu ka shigo ba ka leƙo ka ga lafiyata ba. Amma idan na yi kuskure ka yi haƙuri ranka shi daɗe."
"Tun da muka ji shiru ai kuna cikin ƙoshin lafiya, haihuwa kuma tun da babu rai mene ne amfanin ganinsa? Muna da magada masu yawa, don haka ku yi haƙuri idan ma kun haifa sun mutu. Domin tun asali mun fi son jinin Fulani Asiya ya gaje mu, kuma hakan ce ta faru tun da kwalliya ta biya kuɗin sabulu."
Cikin murmushi mai É—auke da manufa ta ce, "Amma muna fatan waÉ—annan tagwayen su lafiyayyu ne da za su iya kula da sha'anin mulki?"
Da mamaki Sarki Dikko ya dube ta, sai Fulani Hauwa kulu ta cigaba da cewa.
"Amma kada ka sa a ranka su ne kaɗai za su iya zartar da mulkin masarautar nan. Wataƙila akwai wani jinin naka da zai shammaci magadan da ake tsammani."
Tana gama faɗar haka ta faɗa ɗaki, cikin ƙasa da murya ta ce.
"Sarki Dikko ka yi kuskure da kake tsammanin ni Karima zan lamumce maka, kuma ka yi ganganci da kake tsammanin tagwayenka za su mulki masarautar nan. Batul! Ita kaɗai ce za ta gaji karagar nan, ni kuma zan cigaba da yaƙi har na samu nasarar fitar da Babagana daga ƙangim bautarka."
Tana rufe baki Sarki Dikko ya É—aga labulen É—akin ya ce, "Me kuke faÉ—a haka?"
Fulani Hauwa kulu ta saki murmushin ƙeta ta ce. "A sauka lafiya ranka shi daɗe."
Masarautar Kajjura
ÆŠan É—agowa Sarki Gambo ya yi, ya zuba wa Fulani Sadiya idanu ya ce. "Matsalar da zan sanar da ke a kan su Hasana ne."
"Ni ma matsalarsu ce take tafe da ni, Sarkina akwai gagarumar matsala. Ka gafarce ni ranka shi daÉ—e, amma a yadda na lura da su Hasana kamar ba su da wadatacciyar lafiya."
"Ba kama ba ce Fulani..."
Nan take Sarki Gambo ya zayyane mata duk abin da ya faru, Fulani Sadiya ta kawar da kai gefe tana sakin murmushim ƙeta. Amma sai ta danne ta ce.
"Mene ne mafita Sakina, domin ba na son magauta su fahimci rauninmu. Ko kuma Malami ya kawo maka wata mafitar?"
GyaÉ—a mata kai ya yi sannan ya sanar mata da bayanin Malami, sun jima suna tattaunawa. Sai da Fulani Sadiya ta kwantar da kai ta gama jin sirrin Sarki Gambo, sannan ta shiga nuna masa kulawa cike da soyayya.
Fulani Zainaba
A bayan ɗakunan bayi suka keɓe suna tattauna, cikin shigar ɓadda kama ta ce.
"Wanzam na kira ka ne domin na sanar da kai na san duk wani tuggu da kuke kitsa wa kai da Ciroma, kuma kai ka sani idan har na buɗe baki a wurin Takawa taka ta ƙare."
Wanzam da cikinsa yake kaÉ—awa ya ce, "Tuba nake ranki shi daÉ—e."
Murmushin cin nasara ta yi ta ce, "Idan ka ga wannan maganar ta mutu, to tabbas ka samar mini da jinin Sarki Gambo a gobe Alhamis idan za ka yi masa aski. Idan ba haka ba kuwa, tabbas zan bankaÉ—a masa sirrinka. Sannan na sanar da shi tuggun da kuka binne a cikin turakarsa."
Cikin sauri ya zube a ƙasa ya ce.
"Tuba make uwar ɗakina, zan yi duk abin da kike buƙata."
'A Gobe war haka na tabbata na samu nasarar ganawa da tsoro Sulaimanu tare da Kursum.'
Zainaba ta raya a ranta, daga can bayan bishiya Jakadiya da ke laɓe ta gyaɗa kai ta ce.
"Ƙarshenki ya zo Fulani Zainaba, na rantse da girman Allah sai na yi sanadin da Sarki Gambo zai tarfa ki a ɗakin."
A nan na zo ƙarshen book 1 na KUNDI UKU mai son karanta 2&3 zai tura 700 zuwa ga Aisha Adam 3090957579 shaidar biya ta nan 07062062624 idan littafi ya kammala zuwa doc 1k
Sarki GiÉ—aÉ—o ga shi da jaririya Batul, Sarki Gambo da Fulani Zainaba ga Jakadiya a gefe. Sarki Dikko ga Babagan ga Fulani Hauwa kulu/ Karima. Ba sai na ce komai ba, kun san dai akwai Æ™ura.👌ðŸ»
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.