Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Kundi Uku Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 5 of 15
SHAFI NA BIYAR
Masarautar Zulwara
Kasancewar duk ranar asabar ita ce ranar bikin gaida abin bautarsu, ya sa iyalai da dama suke shirya ƙwai da kwarkwarta domin halartar wurin bauta. Kusan tun asuba ilahirin mutanen ƙauyen suke zuwa bakin kogin, saboda kowa burinsa ya isar da bukatarsa domin Allahnsu da suke bautawa ya yi gaggawar amsa musu.
Kogin Sutturu shi ne kogi ɗaya tal da yankin Zulwara suke bautawa, kasancewar akwai wata murgujejiyar bishiyar kukar da ke gaban kogin. Dalilin da ya sa suke bautawa kogin da kuma bishiyar kukar, kasancewar a shekaru masu tsayi da suka gabata. Ita wannan bishiyar an wayi gari da ta faɗi a cikin ruwan, da mutanen yankin suka yi yunƙurin tsamo ta daga ciki saboda wucewa a kwale-kwale, sai ya zamana duk wanda ya shiga kogin ba zai fito ba sai da wata nakasa. Ko dai idanunsa su makance, ko ƙafa ta shanye da hannu, wasu ma sai dai a tsame gawarsu daga ciki. Tun daga lokacin mutane suka daina shiga wannan kogin, a hankali sai kuma ruwan cikinsa ya dinga janyewa. Har ta kai ga ruwan kogin ya ƙafe tas. Bishiyar kukar da ke kwance ta ƙone ƙurmus, sai aka wayi gari shuri da gidajen turuwawa sun kewaye wannan bishiyar kukar. Ana cikin haka sai Boka Ɗan Asabe ya yi mafarki, a cikin mafarkin an ce ya je ya ɗebi ƙasar wannan kogin ya yi wa wani ɗansa mai nakasa magani. Idan ya warke sai ya cigaba da bayar da magani, da farko ya ji tsoro. Amma da ya tuna a mafarkin nasa an ce za a ɗaukaka shi, kuma za a ba shi ƙarin ilimin bokanci sai ya yi ta maza. Ya tara mutanen gari ya sanar da su abin da ya faru, mutane da dama ba su amince da kalamansa ba. Saboda suna ganin kamar yawo da hankali ne a ce su bar bautar rana su koma bautar ƙonanniyar bishiyar kuka. Boka Ɗan Asabe cikin fargaba ya tunkarin ƙonannan kogin ya ɗebo ƙasa, ga mamakinsa sai ya ji ƙasar ta yi sanyi sosai kamar ya ɗebo ta daga cikin kogi mai ruwa. Bayan ya ɗiba ya karyi itacen bishiyar, ya fito daga ciki ya haɗa wa ɗansa magani ya shafe masa ƙafafuwansa. Ko sa'a guda ba ta shuɗe ba, ɗansa ya miƙe garau ya samu lafiya.
Wannan dalilin ya sa mutane suka fara gasgata maganar Boka Ɗan Asabe, musamman da wasu nakasasun suka dinga zuwa yana warkar da su. Sai ya zamana duk umarnin da bokan ya ba su tamkar wahayi haka suke amfani da shi, na zartarwa su zartar na aikatawa su aikata. Ana cikin haka Boka Ɗan Asabe ya ce kowanne magidanci ya ɗauki dabba ɗaya daga cikin gidansa ya kaita wannan ƙonannan kogin, da sunan godiya ga sabon abin bautarsu bisa ni'imar da ya fara yi musu. Jin yadda boka Ɗan Asabe yake ƙara samun ƙwarin gwiwa, maganarsa take karɓuwa. Ɗaukakarsa ta tumbatsa ya sa sarkin wancan lokacin ya aika har gida aka hallaka shi, saboda yana ganin idan aka cigaba da tafiya a haka al'ummarsa za ta daina ba shi girma da matsayin da yake kai. Tun da sai abin da Bokan ya faɗa ake zartarwa, saɓanin idan shi da yake sarki ya bada umarni ake tantama a kai.
A ranar da Boka Ɗan Asabe ya mutu, a daren ranar Sarki Nomau ya makance. Tun ana nema masa magani har abin ya ci tura aka haƙura, daga ƙarshe aka naɗa ɗansa ya zama sarki.
A ranar da Sarki Isa ya hau kan karagar mulki, a ranar kuma ƙoramar da suke bautawa ta fara tsattsafowa, bishiyar kukan da ta shafe sama da shekaru masu yawa ta miƙe. Haka mutane suka dinga turuwa suna ganin abin al'ajabi, ana cikin haka sai Damina ɗan Boka Ɗan Asabe ya gaji mahaifinsa a fannin bokanci. Sanin abin da ya faru ga tsohon sarki ya sa sarki mai ci bai yi yunƙurin kashe shi ko illata shi ba. Haka suka cigaba da tafiya ana zaman doya da manja tsakanin Sarki Najume da Boka Damina. A haka har girma ya cin musu, ajali ya riski sarki Najume bayan mutuwarsa aka naɗa ɗansa Sarki Dikko.
Abu na farko da Sarki Dikko ya fara yi a ranar da ya hau kan karaga shi ne rushe tsibirin Boka Damina. Ya sa aka kawo masa shi a gabansa a fada, ya zare takobi a gaban jama'a. Sannan ya bayar da umarnin daga ranar babu wanda zai sake bayar da wani umarni idan ba shi ba, ganin abin da ya faru da Boka Damina ya sa jikin mutane ya yi sanyi. Tsoro ya mamaye su, sai dai a ɓangare ɗaya suka shiga dakon ganin mummunan yanayin da zai faru da Sarki Dikko kamar yadda ya faru da kakansa tsohon Sarki Nomau. Abin da ya sake ba su mamaki da tsoro jin shiru babu wani al'amari da shi, don dama tun hawansa mulki suke jin raɗe-raɗin ana cewa shi ma Dikko hatsabibin kansa ne. Tun daga wannan lokacin suka bayar da kai bori ya hau, suka zame masa tamkar raƙuma da akala saboda yadda suke yi masa biyayya sau da ƙafa. Shi kuma Diko ya cigaba da murza kambumsa yana yin sarauta yadda ya ga dama, saboda hatta dattawan ciki fada shakkarsa suke yi.
Babban tashin hankalin da Sarki Dikko ya fara fuskanta akan haihuwa ne, ba don ba ya haihuwa ko iyalinsa ba sa haihuwa ba. A lokacin da uwar gidansa ta fara haihuwa sai ya zama duk yaran da take haifa masu nakasa ne, daga makafi sai masu shanyewar ƙafa da hannu. Waɗansu kuma masu taɓin ƙwaƙwalwa ta yadda ba za su mori ba. Da farko sai ya yi tsammanin daga ɓangaren uwargidansa ne, don haka ya ƙara aure sai dai ita ma tana zuwa ta haifo masa jariri mai shanyewar jiki.
Amma duk waɗannan al'amarun da suke faruwa, Sarki Dikko bai taɓa bari labarin haihuwar masu nakasar da yake yi ya fita ba. Saboda killace yaran yake sa wa ayi, tare da yi wa masu tsaronsu bazaranar matuƙar zancan ya fita sai ya hallaka su. Da al'amarin ya fara ci masa tuwo a ƙwarya, sai ya sa amintaccansa wato Waziri. Da ya nemo masa hatsabiban bokayen da su iya warware masa matsalarsa, kuma duk ƙiyayyarsa da addinin kiristanci sai ya amince da a kira malaman addinin a sirrance domin su kawo masa ɗauki. Amma kowanne da ya jarraba maganinsa sai ya ga aikin bai ci ba, don haka ya cigaba da bada ƙarfi a ɓangaren addininsa na gargajiya. Aka cigaba da nemo masa bokayen da ke aiki da ruhin magabata, amma sai lamarin ya girme wa tunaninsa.
Sarki Dikko (1835)
Cikin damuwa yake duƙurshe a gaban tsohuwar bukkar da aƙalla za ta kai shekara hamsim, Waziri da ke gefe ya sunkuyar da kai cikin damuwa. Hatsabibin bokan ne ya ratso ta jikin dutsen da ke kallon bukkar, sannan ya ƙarasa gabansu ya zaune a kan shurin da ke fuskantarsu. Waziri ya ɗan russuna ya ce, "Ran boka ya daɗe, fatan shekaru masu yawa irin na dabino. Ina mai ja da aikinka ya zo a nuna masa ƙarshensa, ba don ka hana a bauta maka ba da babu mahalukin da ya isa ya hana mu fara bauta maka ya kai boka Tsumbur."
Jin irin kirarin da Waziri yake yi wa Boka Tsumbir ya Takawa jin É—aci a zuciyarsa, saboda shi mutum ne mai tsananin kishi. Don ba ya san ko kaÉ—an ya ga al'umarsa na fifita wani fiye da shi.
"Ya kai shugabana, a yau tare nake da Sarkin masarautar Zulwara..."
"Sarkin da yake ƙyashin fifikon wani a kansa, sarkin da yake gabana amma yake jin ban isa a ba ni matsayin da ka ba ni ba. Sarki da yake fama da matsalar haihuwar masu nakasa, kuma a yanzu ma kun zo gabana domin na taimaka muku a kan haihuwar masu nakasar da aka yi masa da asubar yau."
Boko Tsumbur ya furta yana ƙura wa Sarki Dikko idanu, a sanyaye Sarkin ya sunkuyar da kai ƙasa. Duk sai ya ji kunya ta kama shi, don duk a kalaman bokan babu wanda ya yi ƙarya a ciki. Saboda lokacin da Waziri yake masa kirari ji yake kamar ya ƙarasa ya shaƙe shi, Waziri ya katse masa tunanin da cewa.
"Tuba yake uban kowa, tuba yake mai taimakon kowa."
Boka Tsumbur bai tanka masa ba, ya miƙe a gabansu ya saki fitsari a saman shurin da yake zaune. Sai kuma ya mayar da ganyen jikinsa ba tare ya yi tsarki ba, ya ya ɗebi kasar shurin da ta jike da fitsarin ya miƙa wa Sarki Dikko. A tsantsance Sarkin yake kallonsa, Boka Tsumbur ya zuba masa daƙwa-daƙwa idanunsa sannan ya ce.
"Ka yi imani da wannan ƙasar shurin ita ce mai rayawa kuma mai kashewa. Sannan ita za ta sa na taimaka wa duk matsalar da kake ciki, kuma sai ka yi imani da wannan shurin ya fi abin bautar da kake bautawa."
Jim Sarki Dikko ya yi, cikin sauri Waziri ya ce.
"Ya amince tabbatacan boka."
Sarki Dikko kallon Waziri ya yi, ya fakaici idon Boka Tsumbur ya matsa hannunsa alamar ya ce ya amince. Cikin muryar takaici da ganin gazawarsa Sarki Dikko ya ce.
"Mun amince."
Wata mahaukaciyar dariya Bokan ya saki sannan ya fara yi wa kansa kirari, "Sai ni bokan da har gobe babu wanda ya kai ni, sai ni Tsumbur jikan maguzawa masu abin mamaki. Sai ni waraka ga duk wanda ya raɓe ni, sai ni mai abin bautar da babu wanda ya kai ni." Sai ya waigo ya dubi Sarki Dikko ya cigaba da cewa.
"Matsalar 'ya'yanka ba daga matsalar iyalinka ba ne, wannan matsalar tana da alaƙa da kisan da ka yi wa Boka Damina. Don haka ko yanzu matanka suka tara da wani namijin za su haifi lafiyayyun yara."
"Zafin kishina ba zai bari na saki mace ta yi wani auren ba, babu wanda ya isa ya aikata wannan mummunan aikin a kan macen da na santa."
Sarki Dikko ya furta a fusace, murmushi Boka Tsumbur ya yi ya ce.
"Ƙarfin zuciyarka yana matuƙar birge ni Dikko. Sai dai ka sani daga nan har ka mutu ba za ka taɓa haihuwar lafiyayyun 'ya'ya ba."
A razane Sarki Dikko yake kallonsa, Boka Tsumbur ya cigaba da cewa.
"Sai dai waÉ—annan jariran da aka haifa maka za mu iya warkar da su."
"Ka taimaka mini Boka Tsumbur, wallahi ina cikin tashin hankali domin a yanzu babu ɗa ɗaya ƙwaƙƙwara da zan ɗaga wanda zai gaji karagata."
Boka Tsumbur ya ɗebi ƙasar shurin ya watsa a wutar da ke ci a gabansa, sannan ya ce.
"Za su warke matuƙar ka lamunce da sharaɗin da za mu kafa maka."
Cike da rashin dogon nazari Sarki GiÉ—aÉ—o ya ce.
"Kowanne irin sharaÉ—i ne a shirye nake da na tunkare shi. Na amince da sharaÉ—inka Boka Tsumbur."
"An haifa wa Sarki Gambo tagwayen mata, adaidai gaɓar da iyalinka ta haife maka tagwayen yaranka mace da namiji. Macen da aka haifa maka makauniya ce, shi kuma namijin ƙafafuwa da hannuwansa a shanye suke."
Sarki Dikko ya sunkuyar da kai ƙasa cikin takaici, boka Tsumbur ya cigaba da cigaba da cewa.
"Don haka za mu musanya lalurar 'ya'yanka zuwa kan 'yan tagwayen da Sarki Gambo ya haifa."
"Amma me ya sa sai Sarki Gambo? Boka Tsumbur ko ka san ni da Sarki Gambo kamar wuta da ruwa muke, idan har sarki Gambo yana ƙaunata. Ko kuma idan ina ƙaunar Sarki Gambo to zan ƙaunaci mutuwata, ta yaya 'ya'yana za su yi amfani da surar 'ya'yan maƙiyina?"
Boka Tsumbur ya yi saurin katse Sarki Dikko da cewar.
"Saboda ba ka san jinin wace ce a jikin 'ya'yan Gambo ba, da ace ka san wace ce mahaifiyar yaran nan. Na tabbata da ka zabarce ta cikin rayuwarka tun kafin mutuwarta, kamar yadda wani ƙudurin Sarki Gambo ya sa shi aurenta ba don yana sonta ba."
Ajiyar zuciya Waziri ya sauke, ya yi ƙasa da murya yana yi wa Sarki Giɗaɗo raɗa.
"Ranka shi daɗe ka ajiye batun gabarku a gefe, ka fuskanci abin da yake gabanka. Wannan wata dama ce ta idan ta kuɓuce ba lallai mu sake samun ta ba, kada ka manta ranka shi daɗe. A ƙalla yau shekara biyar kenan ina bibiyar Boka Tsumbur a kan ya ba mu damar ganinsa, amma sai yau ya ba mu wannan damar." Shiru Sarki Giɗaɗo ya yi yana nazari, cikin zafin nama ya ce.
"Mun amince Boka Tsumbur."
Dariya Bokan ya saki marar daɗin sauraro, sai ya saka hannunsa a cikin wutar gabansa. Ya ɗauko wani allon farin ƙarfe, ya soka a jikin shirun sannan ya fara biya ɗalasiman tsafi, yana kiran sunayen manyan aljanun da suke yi masa aiki. Wani ruwa mai kamar jini da ke tafasa ya ɗiba ya watsa a kan allon, nan take hoton jariran Sarki Gambo da ke kwance Unguwar zoma tana yanke musu cibi suka bayyana. Daga gefe kuma jariran Sarki Dikko ne kwance a saman gadon mahaifiiyarsu, ruwan ya sake watsa musu lokaci ɗaya jarirai huɗun suka fashe da kuka jikinsu yana wata irin karkarwa. Har sai da Sarki Dikko ya tsorata da ganin abin da yake faruwa da su, Boka Tsumbur ya ɗago ya dube su ya ce.
"A yanzu haka duk irin tawaya da nakasar da ke jikin jariranka, sun koma yaran Sarki Gambo. Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba."
Da sauri Sarki Dikko ya dube shi yana shirin yin magana suka ji tsibirin ya yi wata irin tsawa mai razanarwa.
*Ummmou Aslam Bint Adam*🌚
07062062624
[24/11, 15:59] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.