Mairo Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: MAIRO 1.txt
Chapter 1 of 4
*♡... MAIRO ...♡*
*BY*
Â
  *_KHADEEJA CANDY_*
*1*
"Na rantse da Allah yau sai an biyani ni babu ruwana"
rik'e take da kunkuru tana marmaÉ—en ido da murguÉ—a baki jikinta sai rawa yake wai ita ga matsifaffeya.
yaron dake gabanta ya risina har k'asa yana bata hak'uri
"dan Allah Mairo ki yafe min wlh ba zan kara ba ni naga kinje wani gurin ne shiyasa na cika miki ban san ba kyaso ba"
sai a lokacin ta kalleshi cikin matsifa tace "saka nayi cewa nayi na cika min kai mai hegen salo yau ko saika busar dashi ko na maka hegen duka"
wata dattijuwa take wanki gefen kogin ta kalleta tace "ke Mairo wai miyasa baki jin magana ne yanzu miye laifin yaron nan dan ya cika miki tulu?"
harara ta watsa mata ta murguda mata baki "ke kuma tsohuwa ina ruwanki dake nake yi ne da zaki samun baki ko sashi nayi da zai cika min tulu wannan ai rainine"
"ke fa baki da kirki Mairo daga magan zaki wani taso min kamar wata warinki"
"mtsssss yau daman kin san ba warinki nake ba kika samin baki a magana dan neman tsokana"
daidai nan Almu ya iso da jakinsa da jalkunan É—inba ruwa.
yana kallon Mairo yasan matsifa ce take ganin yadda take marmaÉ—en ido tana rawar jiki
murmushi kawai yayi ya gaida dattijuwar
"inna ina kwana?"
"lafiya kalau Almu an tashi lafiya?"
"Alhamdulillah inna"
kallon mairo yayi "ke lafiyarki kike wannan harare2?"
banza ta masa ta cigaba da karkada jiki.
inna ta taɓe baki
"ai haka take indai rashin kunya ne ta iya ga yar banzar matsifa"
juyowa mairo tayi kanta "wai ke ina ruwanki dani kinga ban hega saggarki ba ki fita tawa bana son shinshigi"
da marmaÉ—e2 ta ksrasa maganar tana murguda mata baki.
   mari Almu ya kai mata ya fizgota ya jefar
"ke wai miyasa rashin kunya yayi miki yawa kamar inna zaki tsaya kina faÉ—awa irin wannan maganar sa'arki ce?"
wani ihu mairo ta saki ta shiga murk'ususu cikin kasa tana jan gashin kanta
"wayyo na shiga uku ya kashe ni wayyo Allah ya kare ni wayyo gwaggo"
tsoro Almu yaji ganin yadda take ihu duk'awa yayi ya rikota "tashi mu gani?"
wani mugun cizo ta kai masa a hannu saida ya saki kara ya saketa da sauri.
inna ta rike baki "oh ni hajjo wannan wace irin masifaffiyar yarinya ce haka?"
Almu dai shiru yayi yana murzar hannun dan ba karamin cizo tayi masa ba,
ya dade a haka kamin ya nufi kogin ya shiga cika jalkunansa.
    ihunta ta cigaba dayi tana murje2 daga Almu har inna babu wadda ya sake bi ta kanta.
Almu na daf da cika kayansa halilu ya iso gurin yana ganin mairo yayi saurin ta data "ke lafiya miya faru?"
langaɓe masa tayi ta cigaba da kukan
nan ya kalli inna da Almu ya shiga tambayar su ba'asi "wai miya sameta ne haka?"
inna tace "babu kawai rashin kunya tayi min Almu ya É—an zungureta shikenan fa ta faÉ—i ta shiga koke2"
cikin kuka Mairo ta É—ago "wlh karya suke itace ta fasa kuka tace masa na zageta shi kuma ya É—aga ni sama ya jefar na kare"
tana kaiwa nan ta saki wata kara kamar wadda aka sokawa wuka.
rik'e baki inna tayi jin irin karyar da Mairo ta zagga
Halilu ya kalli Almu "haba Almu ya zaka mata haka kamar wata warinka ko namiji"
Almu yayi murmushi "haba dai Halilu sai kace bakasan halin Mairo ba wlh karya take"
Halilu yace "wai minene mafarin wannan masifa?"
inna tace "É—iban ruwa tazo fa saita eje tulun ta tafi yawonta shine haruna ya dauka ya cika mata shine data dawo tace sai ya biyata shine ya zubar da ruwan daya zuba kuma duk da haka tace wai saiya busar tulun yadda yake shine ya shiga bata hak'uri taki hak'ura wai ita saita dake sai natibmata magana shine fa ta shiga fada min magagganu har Almu saida tayi masa rashin kunyar"
Halilu yace "daman shine kawai take yiwa wannan kuka?"
"shine kawai babu wani abun da akayi mata"
cewar inna.
kai halilu ya kaÉ—a ya Nufi ecen dogon yaro ya k'allo ya juyo gurin mairo cikin zafin nama ya watsa mata ita,
mairo najin saukar bulala ta tashi da gudu ta nufi gida tana uhu.
***Â Â ***Â Â ***
da ihu ta isa gida tana murxa gurin da Halilu ya buga mata bulalar.
da sauri gwaggo ta tare ta "lafiya Mairo miya sameki?"
rumgumeta tayi "wayyo gwaggo zasu kasheni gwaggo basa sona sun min taro suna ta duka na"
gwaggo ta dagota "su waye Mairo faÉ—a min uban wa ya taba ki cikin garin nan?"
cikin kuka ta shiga yima gwaggo k'arya data saba "tsohuwar gidansu hajara ce tace wa Almu wai na zageta shine shi kuma ya daga ni sama ya jefar gwaggo ya k'arya ni na bani mutuwa zanyi"
da sauri gwaggo ta zaunar da ita ta shiga duba ta tana matsifa "wannan wace irin k 'etace haka wlh duk suka karyaki sai munyi shari'ah dasu mugayen mutane azzalumai"
gwaggo na taɓa mata k'afa ta saki wani mahaukacin ihu "wayyo na shiga uku gwaggo nan gurin Halilu ya buga min ecce"
gwaggo tayo waje da ido "ecce kuma yaushe mi kika masa?"
"ban masa komai ba daga zuwansa suka fada masa k'arya shine ya dauko k'aton ecce ya buga min gwaggo basu sona na shiga uku"
tashi gwaggo tayi ta shiga É—aki ta É—auko mayafinta ta nufi kofa.
 Â
    '''
NOTE'''
*_Assalamu Alaikum ina bawa fans É—ina hak'uri bisa ga rashin ganin cigaban novel É—ina mai suna LAMARIN DUNIYA na k'are novel É—in gaba É—aya kamin na fara posting sai phone É—ina ya samu matsala kuma wadda nayi publishing a blog É—ina blog É—in ya samu matsa. ta dalilin matsalar da phone É—ina ya samu amman ana kan gyara blog É—in da zarar an kare zanyi muku C & P Insha Allah ko kuma na baku blog address ku karanta bayan haka dan Allah ina rokon duk mai novels É—ina ko wane iri ya turo min ta wannan number_*
+2348036126660
*_taku har kullum Khadeeja Candy_*
© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:37 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
Â
  *_KHADEEJA CANDY_*
*2*
gwaggo na k'ok'arin fita halilu na k'ok'arin shigowa sukaci karo nan taci kwalarsa ta k'asara shigowa dashi tana masifa "ashe baka da hankali halilu dan kana magu zaka sa ecce ka bugawa Mairo bancin bugun da Almu yayi mata wai mi ta tare maka ne?"
kai ya girgiza "haba gwaggo wai miyasa duk tazo tayi miki k'arya saiki yarda ya za'aiyi na buga mata ecce fisabilillahi?"
"ai halinka na sani ba sonta kake ba zaka iya mata komai"
kallon mairo yayi da tayi shiru tana kallonsu kamar wata munafuka yace "ke dukanki nayi?"
kai ta daga ta turo baki tana matsar kwallah.
"eh gurin da Almu ya karyani ka buga min ecce"
gwaggo ta kara ciyo kwalarsa "mugu yanzu abunda kake ya kamata kenan a gaban idonka ka bari Almu yayi mata wannan illar wai miyasa baka son yarinyar nan ne halilu?"
"ohhh gwaggo haba haba wane irin illa Almu zaiyi mata rashin kunya fa tayiwa tsohuwar mutane shine ya dan zingureta fa"
gwaggo tace "tho ina ruwansa ya zingureta haihuwarta yayi kuma karya kake karyata yayi"
"haba gwaggo yarinyar da aka karya zata iya kawo kanta gida har ta iya faÉ—a miki an karya ta ai saidai a kawo miki ita"
saki kwalarsa gwaggo tayi ta nufi Mairo ta shiga duba k'afar.
aiko nan mairo ta k'ara marairaicewa tana "wayyoh k'afata" gwaggo ta duba bata ga alamun kariya a k'afarta ba ko alamun jimuwa babu barre karaya ta data gwaggo tayi tsaye "tashi kiyi tafiya na gani"
nan ta lak'e kafar "wayyo bazan iya takata ba gwaggo ta riga ta karye"
cikin dabara halilu ya cire takalminsa ya jefa mata iya karfinsa aiko da gudu ta faÉ—a É—aki tana ihu.
matsowa yayi kusa da gwaggo ya É—auki takamin yana faÉ—in "yanzu wadda aka karya zata iya wannan gudun?"
shiru gwaggo tayi halilu yace "gwaggo wata rana saita saki kunya matukar duk abunda tazo ta faɗa miki kina yarda dashi tho ko zaki ɓata da kowa"
tsaki gwaggo taja "mtsss tho sai mi dan na ɓata da kowa akanta so kake na zuba ido ina kallon ana cin amanarta? ko kai ka taɓa ta saina taɓa ka bare wani can"
halilu bai kara cewa komai ba banda kan da ya girgiza ya fice ya barta tana masifarta.
saida Mairo taji fitarsa sannan ta fito tana kukan munafurci.
nan gwaggo tayi cikinta ta masifa "Allah mairo in kina zuwa kina min karya saina ɓata miki rai kuma na ɓata dake na fita harkarki"
  kwantowa tayi jikinta tana kukan shgwaɓa "tho ai ba karya nake ba Almu ya dakeni kuma Halilu ya zaggamin bulala"
tureta gwaggo tayi "amman ai cemin kikayi shiya buga miki ecce Almu kuma ya karyaki"
turo baki tayi
"eh karya nake amman dai sun dakeni dukansu"
"tho miyasa kika min karya kuma halilu yace ai tsohuwa kikayiwa rashin kunya"
"tho gwaggo ai itace ta samin baki a magana kuma tace min masifaffiya"
"amman ai kinsan na hanaki rashin kunya da karya ko ni daga yau babu ruwana dake"
kuka ta shiga rerawa "na daina gwaggo dan Allah kar kiyi fushi dani ba zan kara ba"
gwaggo bata so kuka mairo ko kaÉ—an janyota tayi jikinta "shi kenan bazanyi fushi dake ba amman ki daina kinji ba kyau kuma bana so"
"na daina daga yau ni ko kallon mutane bazan sakeyi ba"
gwaggo tayi dariya tace "rufe da ido zaki rika yawo kenan?"
"eh bazan sake kallon mutane ba bare suce nayi musu rashin kunya"
gwaggo ta shafa kanta "a'a kawai ki rika jin magana kibar rashin kunya yayi basai kim rufe idoba"
dariya mairo tayi "ai wasa nake miki gwaggo ya za'ayi na rufe ido kina son na fada rijiyane ko rame?"
dundu gwaggo ta kaimata a baya tana dariya "oh baki daina karyar ba kenan ko?"
"na daina Allah yanzu ko zanyi kaÉ—an zanyi"
gwaggo ta girgiza kai "a,a ki daina gaba É—aya dai wai ina kika baro min tulu?"
"yana can kogi ni gaskiya gwaggo daga yau bazan kara zuwa É—iban ruwa ba kullum ni nake zuwa kuma yar k'ank'anuwa dani shi halilu da yake k'ato bazai jeba sai ni shiyasa suke dukana sunga ni banida girma"
cike da shagwaɓa take maganar tana son yin kuka.
gwaggo ta shafa bayanta "shikenan bazaki sake zuwa ba halilu ne zai rik'a É—ebowa"
rumgumeta mairo tayi tana murna.
'''Â Â Â Â * * *'''
_2:13pm..._
gwaggo ta kare dahuwar giÉ—ar ta ta zuba a gwango.
ta kwalawa Mairo kira da sauri ta fito tana É—aurin É—ankwali rabin fuskarta duk fodace da bata shafu ba.
"na'am gwaggo kin kare?"
saida ta kare lisafin sannan ta É—ago ta kalleta tace "ta É—ari biu da arba'ince"
ɓata fuska mairo tayi "gaskiya gwaggo saidai ace ta ɗari biu da talatin dai dan gaskiya zan ɗauki ɗaya"
gwaggo tace "É—auki ko nawa kike so mairo waya isa ya hanaki?"
murmushi tayi ta duka ta É—auki turen tana faÉ—in "yau duka zan siyar"
"tho Allah bada sa'ah amman dai hodarki bata shafu ba mairo"
turo baki tayi "nidai gwaggo bana son haka bani na shafa ba nidai haka zanje"
hannu gwaggo ta É—aga mata "jeki jeki Allah bada sa'ah inda yanzu kuma ban faÉ—a miki ba ki hauni da masifa"
batace komai ba ta É—ora turen samsn kai ta nufi kofa.
gwaggo ido ta sakar mata a ranta tana _Allah ya shirya minke mairo ya tsare_
© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
Â
  *_KHADEEJA CANDY_*
*3*
tafe Mairo take É—auke da turenta na giÉ—a saman kai tana yan wakewakenta.
saida tayi nisa da tafiya sannan ta tuno da ɓanɓaramar da tayi jiya da sauri ta chaja hanya harda haɗawa da ɗan gudu tana waigen bayanta.
saida taga ta shanye kwana sannan hankalinta ya kwanta tafiya ta rik'ayi a hankali tana kwanÉ—alar giÉ—ar tana ci.
kashe kunne tayi tayi gefen dashi tana son ta tabbatarda abunda kunnuwanta suke jiyo mata.
wak'ar india ce _ghajiniguzarish_ ke tashi cikin wani kiÉ—an taushi mai daÉ—i
taɓe baki tayi "tho wai wayasa wannan kiɗan mai ɗaɗi cikin ɗaji kodai buki ake?" magana take tana kallon giɗar dake hannunta kamar wata taɓaɓɓiya.
kara kasa kunne tayi har ta gano gefen da sautin ke tashi dariya tayi "Allah buki ne ake bari na leka na gani amman ba zan daÉ—e ba sai na dawo"
haka ta kunna kai daga wani ɓangare na hanyar ta rika tafiya tana bin inda taji sautin wakar na tashi harta iso wani guri mai kamada lambu.
tsayawa tayi tana kallon etacen dake gurin "lahhh ashe ma haka gurin yake ni kan ban taba zuwa ba sai yau"
rabon ido ta shigayi saida ta kare kallon gurin sannan ta cigaba da tafiya.
a hankali ta fara hango wasu mutane sanye da wani yadi kala É—aya.
da sauri ta laɓe gefen ecce tana lekensu ,
duk kansu sanye suke da yadi kala É—aya mai ja da kore (red and green) kana gani kasan fadawa ne in banda mutun biu dake zaune saman wani k'aton carpet na alfarma É—ayan sanye yake da riga da waddo na turawa É—ayan kuma sanye yake da riga doguwa mai kamada jalabiyar fakistan _golden color_ Mai kyau sai kyali take.
ya dora wani É—an kyale saman wuyansa daya sauko har saman rigarsa.
gashin kansa ya kwanta lum kamar balarabe ya lankwashe kafafunsa wata rekoda na gefensa tana bada sauti shi kuma yana fuskarta É—ayan suna karta ko wannensu kuÉ—i yake azawa in aka cinye ya kara wasu.
    sosai abunda suke ya burge Mairo aje turen giɗar tayi tayi zaune tana kallonsu tana dariya amman baki rufe dan kar suji
ta daÉ—e a haka can dai taji bazata iya jurewa ba ta É—auki turenta ta nufosu tana Murmushi.
"Assalamu alaikum"
sallama tayi musu tana k'ok'arin k'arisawa kusa dasu
  da sauri suka tare wadda ke zaune saman carpet ɗin wasu kuma suka nufota rik'e da takobi.
tsaye tayi tana kallonsu kamar hoto har suka karaso kusa da ita,
wani zarare cikinsu ya ɗaga takobi zai sara mata ɗayan yayi saurin rikewa yana faɗin "Yarima yace a dakata"
da sauri ya janye takobin yayi baya.
É—aya daga cikin fadawan ya fisgota da karfi har giÉ—ar dake saman kanta ta watse ya nufi gurin yarima da ita.
yana tsaye yana kallonsu har suka iso da ita kallo É—aya yayi mata ya gane bata cikin hayyacinta ganin yadda idonta suka k'afe kuma bata motsi.
  ido ya ɗan tsura mata sannan ya bada umarnin a zuba mata ruwa,
da sauri bafaden ya dauki ruwan gora ya watsa mata
sai a lokacin ta matsa alamar ta dawo hayyacinta zubewa tayi zaune ta É—aga kai tana kallonsu
suma ita suke kallo har yarima saida ta kare kallonsu É—aya bayan É—aya sannan ta saki wata irin kara iya karfinta mai shiga cikin kwakwalwa faÉ—uwa yarima yayi zaune ya dafe kunnunwansa shida wadda ke kusa dashi.
mari daya daga cikin fadawan ya watsa mata saida ta faÉ—i can gefe ta fashe da kuka
   ɗagowa yarima yayi ya watsa masa wata mugunyar harara da sauri bafaden ya faɗi kasa "Allah ya huci zuciyarka Yarima banyi dan ranka ya bace ba"
kawarda kai yayi yana sauraren sautin kukanta dake tashi tare da sautin waka
ya daÉ—e a haka sannan ya É—ago cike da isa yace "kashe sautin nan" da sauri ya tashi ya nufi rikodar sa hannu ya kashe ya dawo ya risina gaban Yarima yana faÉ—in "Allah karawa Yarima martaba na kashe"
ba tare daya kalleshi ba yace
"jeki ka rarrasheta"
"am gama Yarima" tashi yayi da sauri ya nufi gurin Mairo.
tirgewa Mairo ta karayi tana kuka tana kiran gwaggo tana murza hannayenta da kafafunta cikin kasa,
yayita rarrashinta har ya gaji tak'i tayi shiru sai ma karawa take.
ganin tak'iyin shiru yasa Yarima yayi mata alamar tazo da hannun tashi tayi ta share hawayenta ta nufoshi tana murmushi kamar ba ita ba.
kallonta yake harta karaso kusa dashi tun kamin yayi mata magana ta zauna saman carpet É—in kusa dashi.
    da sauri ɗaya daga cikin bafaden ya unkuro zai mata magana Yarima ya ɗaga masa hannu nan dukansu suka ja baya kowa ya shiga harkar gabansa.
kallonta yayi a natse cikin isa yace
"ya sunanki?"
washe masa hauru tayi
"Mairo"
"Mairo?"
"eh sunana Maryam amman Mairo ake cemin kaifa ya sunaka?"
bai amsa mata ba ya jefa mata wata tambayar "an garin kike?"
"eh kai amman dai É—an birni ne ko?"
nan ma wata tambayar ya sake jefa mata batare daya amsa mata ba
"mi kikazo yi nan?"
"talla nake zan wuce sai naji kiɗi na ɗauka bukine ake shine nace bari nazo na gani saina koma shine na ganku sai na taɓe"
shiru ya ɗanyi yaɓa kallonta sannan yace
"tho miyasa kika fito?"
abunda ke gabansa ta É—auka ta nuna masa "wasan da kuoe da wannan abun ya burgeni shiyasa na fito"
bai sake ce mata komai ba ya janyo wayarsa ya shiga danne2
sai a lokacin Mairo ta tuno da giÉ—arta
hannu ta É—ora saman kai ta fasa kuka
"wayyo na shiga uku giÉ—ata"
wani mugun tsaki wadda ke kusa da Yarinan yaja yana hararta.
a hankali Yarima ya É—ago kai ya kalleta
"ina giÉ—ar take?"
"nima ban saniba É—azu dai kamin nayi bachi nasan tana saman kaina"
kallon rashin fahimta yayi mata "bachi kikayi?"
"eh É—azu da suka nufoni da takobi ba sai naji bachi dana farka sai naganni nan kuma banga giÉ—ar ba"
murmushi yayi dan ya gane suma take nufi da bachi.
É—aya daga cikin fadawansa ya kira da sauri yazo gabansa ya risina cikin isa Yarima yace
"ina giÉ—ar Yarinyar nan?"
"gata can kusa da ecce ta zubar"
"jeki ka É—auko mata"
tashi yayi da sauri ya nufi gurin yana faÉ—in "am gama Yarima"
kallon Yarima tayi tana dariya "na gode"
kai kawai ya É—aga mata
ta sakar masa murmushi tace
"kai baka fada min sunanka ba?"
yi yayi kamar bai jita ba ya mai yarda idonsa wani gefen
nan mairo ta ɓata fuska ta buro baki
"ni inna tambayeka saika kyaleni nima amsar da na baka ban yafe ba lafira saika biyani"
cikiciki take maganar amman hakan bai hanashi ji ba
dariya ce tazo masa da sauri ya mayarda ita murmushi ya kara kawarda fuskarsa.
*© Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
Â
  *_KHADEEJA CANDY_*
*4*
suna haka nafaden ya kawo mata turen giÉ—arta ya aje yana faÉ—in "gashi Yarima Allah ya kara maka daraja"
hannu ya É—aga masa bafaÉ—en ya tashi.
kallonsa Mairo tayi "na gode"
banza yayi mata kamar bai jita ba sun daÉ—e a haka sannan ya juya ya kalleta yace "amsar da kika bani zan biyaki lahira?"
shru tayi tana kallonshi dan batayi zaton yaji ba can tace "eh mana tunda kai baka banu amsar tambaya ta ba"
shiru ya É—anyi sannan yace "mi kike tambayeni?"
"ba nace ka faÉ—a min sunanka ba"
ya É—an daÉ—e kamin ya bata amsa "sunana Yusuf Usaini"
dariya tayi harda sa hannun baki "lahhhh shiyasa kake da kyau daman masu suna Yusuf suna da kyau"
murmusawa ya É—anyi ya É—auki enabi yakai bakinshi.
yatsa É—aya Mairo ta É—aga masa "sauran tambaya É—aya"Â
kai ya É—aga mata yana tsusar enabi kamar mai shan minti.
tsaki kawai na kusa dashi keja haushi ya isheshi
harara Mairo ta watsa masa ta kalli Yarima tace "amman dai É—an bunni ne ko?"
murmushin gefe yayi ya É—aga mata kai alamar 'eh' waje tayo da ido ta shiga shafa mishi riga "lahhh nikan daman nace dan bunni ne kai inason yan bunni kuma..."
"ke! mahaukaciya"
bata karasa maganar ba na kusa dashi ya katsa mata tsawa saida ta razana
hmda sauri Yarima ya É—aga mishi hannu yana kallon fuskar Mairo data k'ara rik'e masa riga tana kallon mutunen.
tsaki ya k'ara ja ya kalli Yarima "haba Yarima ya zaka..."
dakatar dashi Yarima yayi ba tare daya kalleshi ba yace "enough yahuza plz excuse us"
tashi yayi cike da bachin rai ya nufi wta bishiya ya zauna.
sai lokacin Mairo ta turo baki tayi kwafa "tho an taɓa shi zo kayi abunda zakayi mai k'aton kai"
murmushi Yarima yayi yace "baki tsoron ya dakeki?"
kai ta kaÉ—a "ni wlh bana tsoron duka nifa ko sheÉ—an bai kaini masifa ba"
faÉ—aÉ—a murmushinsa yayi "gaskiya ne tho tashi zaune"
tashi tayi zaune ta É—auki ruwan dake gansa "insha ruwan bunni?"
kai ya ɗaga mata yana kakkaɓe rigarsa data bata da k'asar hannunta.
saida ta shanye ruwan kofin gaba É—aya sannan ta dire kofin tana dariya tana faÉ—in "wlh na sha ruwan bunni"
"birni ake cewa ba bunni ba"
ya gyara mata
washe hakora tayi ta sake cewa "bunni"
murmushi yayi yace "waya shafa miki hoda?"
"nice na shafa É—azu da zanje tallah"
ta karasa maganar tana gyaran É—ankwalinta.
can ta É—auki abunda ke gabanshi ta kalleshi tace "minene kuke da wannan abun É—azu naga kuna wasa dashi?"
saida ya É—an daÉ—e sannan yace "chachace muke zakiyi?"
da sauri ta matso kisa dashi tace "eh zanyi dan Allah"
"tho mi zaki aza?"
"kamar ya mi ake azawa"
"duk abun mutum kr so yana azawa bakiga yadda muke yi ba ni kuÉ—i nake azawa"
kalle2 ta shigayi tana neman abunda zata aza can ta kalli giÉ—ar ta da sauri ta É—auko k'waya É—aya ta aza "to ga giÉ—a nan na aza"
shafa kansa yayi yayi murmushi ya sa hannunsa aljihu ya ciro dalar amerika É—aya ya aza.
bata fuska Mairo tayi ta turo baki "ni dai bana son wannan takardar da kuke da ita saida ka aza kuÉ—i ko wani abu mai daÉ—i"
ta karasa maganar tana lek'en lemun dake bayansa.
ido ya tsura mata yana mamakin wayonta wato shi ya aza (É—ora) kudin data sani ko abu mai daÉ—i ita kuma ta aza kwaya É—aya ta giÉ—a
cikiciki yayi murmushi yace "ai kuÉ—i ne ba takarda bace in kika chaja kuÉ—i da yawa za a baki"
lak'e kafaÉ—a tayi "ban yarda ba kuÉ—i bane ai da na sansu saidai ka aza kuÉ—in k'warai"
"ba nida wayan can kuÉ—in da kika sani wannan ne kawai in kuma ba zakiyi ba shi kenan"
shiru tayi tana son masa musu shima shirun yayi yana kallonta.
da taga babu sarki sai Allah yasa ta kalleshi tace "na amince"
kai ya kaÉ—a mata ya É—an daÉ—e sannan ya gyara zamansa suka fara.
yin kawai suke tana masa shirme dan bata iyaba ci kusan 10 yayi mata sai haushi take ji dak'er ta samu tayi masa ci biu koshi danya nuna mata yadda zatayi ne.
aiko murna kamar ta kasheta sai dariya take kwasa harda hawaye.
shidai kallonta kawai yana shakkun hankalinta.
da taga ya kara mata ci biu ta ɓata fuska tace
"nidai na daina kuma saika bana giÉ—ata"
shiru yayi yana kallonta kamar ba zaiyi magana ba saida yaga ta fara turo masa baki sannan yace
"ni kuma kuÉ—ina dana baki fa?"
ɗaukar kuɗin tayi ta kikkiresu tayi musu guntu guntu baiyi unkurin hanata ba saida ta k'are ta watsar ta kalleshi tace "ni bana sonsu"
"mi yasa kikayi haka bakisan ba kyau yaga kuÉ—i ba?"
"ai ba kuÉ—i bane takardace nidai bani giÉ—ata"
banza yayi mata ya ɗauke kansa saida yagata soma yi masa kuka sannan ya ɗauki giɗar ya mik'a mata ta da sauri ta karɓa tasa a ture ta tashi ta karkaɗe jikinta ta ɗora turan saman kai tayi masa murmushi ta kama hanya.
har tayi nisa sai kuma tayi juyo ta nufoshi.
kaÉ—an kaÉ—an take tafiya tana turo baki har ta karaso kusa dashi ta sauke turen ta aje masa ta fashe da kuka.
kallon kawai yake tun tana kuka ba hawaye harta fara hawayen tana shureshuren kafafunta cikin k'asa sai kallonshi take,
shima ita yaƙke kallo yana tsusar baki kamar mai mai shan minti.
sunfi karfin minti 30 a haka ita taki tayi maganar sai kuka take shina yaki yayi mata magana fadawansa sai satar kallonsu suke yahuza ko yasa earphone a kunne dan kar haushi ya kasheshi.
saida yaji ta kara buÉ—e baki tana kiran Gwaggo sannan ya matsa ya rik'o fuskarta ya sakar mata manya idonsa yace "mi kike yiwa kuka?"
cikin kukan tace "ba kaine ba ka jani da wasa har lokacin komawa gida yayi ban siyar da giÉ—a ba kuma Gwaggo bazata bani kuÉ—in sawa asusu ba"
murmushi yayi yasa wani bafaden sa ya kira masa yahuza.
haka ya iso gurin yana hararar Mairo.
Yarima ya kalleshi yace "kuÉ—in nageriya nake so"
hannu yasa aljihu ya ciro yan dubu dubu ya aje masa gabansa.
nan ne yaga kuÉ—in da Mairo ta yaga kallon Yarima yayi yace "wayayi wannan aikin?"
kallon Mairo Yarima yayi bai bashi amsa ba hakan ya tabbatar masa da itace 'uhmmm' kawai yace ya watsa mata harara ya koma gurin zamansa.
Yarima ya kalli Mairo yace "É—auki ko nawa kike so"
da sauri tasa hannu ta dauki dubu uku tana dariya tace "na gode"
kai ya É—aga mata "sun isheki?"
"eh na gode amman dan Allah ka bani wacan abun"
juyawa yayi yana kallon apple É—in data nuna masa.
hannu yakai ya dauki ɗaya ya mika mata tana karɓa takai baki "lahhh daman haka goribar bunni take?"
murmushin gefe yayi ya girgiza mata kai "ba goriba bace apple ne"
"minene apple?"
"tuffa"
"minene tufa?"
shiru yayi dan yanzu kam baisan mi zai ce mata ba.
kamin yayi mata wata magana ta sake rokonsa
"dan Allah karamin É—aya na kaiwa Gwaggo"
kara É—auko É—aya yayi ya mika mata dariya tayi ta kara rok'onsa "na gode amman É—an Allah kara min É—aya na kaiwa k'awata jummalo (MANIRA Lol.) da Halilu hannu yasa ya sake É—aukowa ya mika mata.
bata bar gurin ba saida ta lisafa masa mutum takwas ya bata sannan ta tashi ta É—ora ture tana dariya tayi masa godiya tare da sallama ta nufi hanyar fita gurin tana waigensa tana É—ago masa hannu shidai kallo kawai ya bita dashi da murmushi harta fice.
© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
Â
  *_KHADEEJA CANDY_*
*5*
tana tafe saman hanya tana cin apple É—in tana É—ariya.
koda ta iso gida taci kusan guda 4 É—ayan ma da giÉ—a ta haÉ—ashi ta ci a kofar gida ta tsaya ta karasa na biyar É—in sannan ta shiga tana watsar hak'ora
Gwaggo na zaune k'ark'ashi ecce durumi taɓa jan carbi Mairo ta shigo
"fuwan (gafaran) kudai masu gida"
murmushi Gwaggo tayi jin yau abunda Mairo ta shigo dashi sabanin sallamar data saba.
kusa da ita Mairo ta zauna ta eje mata turen giÉ—ar gabanta ta zuba mata ido.
Gwaggo saida ta kai karshen carbin ta shafa sannan ta kalli Mairo da fuskar damuwa tace "yanzu Mairo tun fitar da kikayi giÉ—a É—aya kika siyar?"
É—ariya tayi ta É—auki apple takai bakinta tace "É—ayar ma cinta nayi ba siyarwa ba"
kai Gwaggo ta girgiza "yayi miki kyau yanzu ai saiki ce na baki na sawa asusu ko na siyen wani abu"
fashewa tayi da dariya harda buga k'afa ta É—auki apple É—aya ta mikawa Gwaggo "Gwaggo karbi ki ci goribar bunni"
banza Gwaggo tayi mata ta kara hade fuska.
nan Mairo ta ciro kuɗin dake lak'ame a k'ugunta ta ajewa Gwaggo
"nidai ga kuÉ—inki nan har ma sun ninka na giÉ—ar"
buÉ—e baki Gwaggo tayi tayo waje da ido "Mairo ina kika samu wannan kuÉ—in mai yawa haka?"
"wani É—an bunni ne ya bani harda wannan goribar shine ya bani kuma fa kuÉ—in da yawa ne nice na É—ebo kaÉ—an"
kallon tsoro Gwaggo tayi mata "ina kika haÉ—u dashi Mairo"
kwantayi tayi saman k'afafunta ta soma bata labari tun farkon fitarta.
   Â
Mairo na kaiwa karshe Gwaggo ta É—ora hanu bisa kai tana salati
"Hasbunallahu wa ni imal wakil innalillahi wa inna ilaihi raji'un Mairo mi ya kaike mi yasa bakisan ciyon kanki ba Mairo mun shiga uku da wannan 'ya mai ya kaiki shiga can?"
Tashi Mairo tayi zaune tana kallon Gwoggo gabanta soma faduwa.
“minene hala Gwaggo?â€
“Mairo kinyi gamo miya kaiki Mairoâ€
baki Mairo ta saki “gamon me Gwaggo?â€
kamin Gwaggo tayi magana sukaji sallamar Halilu da sauri Mairo ta shige cikin Gwaggo tana fad'in “Gwaggo karki fad'a masaâ€
koda ya karaso Mairo yake kallon ganin yadda ta ahige cikin Gwaggo dan yasan ruwa baya tsami banza gashi kuma Gwaggo na kuka.
“Lafiya Gwaggo miya faru kike kuka?â€
da sauri Mairo tace “bata da lafiya ne shine take kukaâ€
risinawa yayi yana fad'in “Subhanallah mi yake damunki?â€
Mairo tace “ciyon kai ne da ciki yake damunta ko Gwaggo?â€
Kai Gwaggo ta girgiza Alamar 'ah ah' nan cikin Mairo ya duri ruwa hannu tasa ta toshe bakin Gwaggo tana fadin “dan Allah Gwaggo karki fada masa dan Allahâ€
tsawa Halilu ya katsa mata “jaye mata hannunki kona miki duka yanzuâ€
da sauri ta janye hannun idonta cike da hawaye.
hannu Gwaggo ya rike yana fadin “dan Allah Gwaggo ki fada min abunda ya faruâ€
cikin kuka ta soma fada masa abunda ya faru.
raku6ewa Mairo tayi gefe tana hawaye.
Halilu ya juyo yana harararta yace "ashe haukarki Mairo har takai kiyi wannan kasadar?"
Gwaggo tace "ni tsoro ma nake ji in basu shige mata ba"
Halilu yace "wane irin shige mata Gwaggo aini bako ta aljanu nake ba ya mutanen nan nake yan yankan kai ko yan iska tunda zamani yanzu ya chaja babu babba babu yaro inma aljanune ai da sauki"
sai a lokacin wannan tunanin ya zowa Gwaggo kallon Halilu tayi tace "kana da gaskiya Halilu tunda kaga harda goribar burni ya bata wata kila akwai abu a ciki"
Kallon apple É—in dake saman ture Halilu ya kalla "ragowarce nan?"
"eh itace taci guda shida tace koma minene ai ta cinye shikenan"
da kuka ta karasa maganar.
Ayatul-kursiyu Halilu ya karanta sannan ya É—auki sauran biu da suka rage ya jefar bayan gida ya juyo gurin ecce durumi ya kallo ya hau Mairo da duka.
ihu take tayi ko ina ana jinta babu wanda take kira sai Gwaggo tana faÉ—in kasheta zaiyi.
wannan karon kan Gwaggo ba tayi unkurin hanashi ba dan itama ta tsorata da lamarin Mairo
mak'ota ne suka shigo suka caceta koshi daker dan mugun rik'o Halilu yayi mata saida bulalar ta kwanta mata a jiki.
kowa tambayar yake dalilin dokan da akayi mata Halilu dai baice komai ba ya fice Gwaggo ce take cewa kuÉ—in tallah ta zubar kuma an sata aiki taki tayi
wasu dai basu yarda ba dan sunsan yadda Gwaggo take son Mairo duk abunda zaisa ayi mata wannan dukan ta kyale batayi magana ba ba karami bane.
haka suka fice kowa da abunda yake faÉ—a,
         '''*  *  *'''
kuka kan Mairo ta shashi har ta gaji tun tana iya É—aga murya har ta koma kiran baba.
tausayinta ne ya kama Gwaggo tana cikin É—aki ta fito ta nufi ta tadata zaune tana kaÉ—e mata jiki "dan Allah Mairo ki rika jin magana ki gyara halinki ki daina wannan halin"
kai Mairo ta É—aga mata tana shisshekar kuka kamar zuciyarta zata fito idonta sunyi mugun ja.
hannunta Gwaggo ta rik'a suka shiga banÉ—aki wannanka tayi mata sannan suka fito,
Mairo na shiga É—aki ko kaya bata saba ta faÉ—a saman gado ta soma wahalallen bachi
_8:15pm..._
gwaggo ta tashe ta taci abinci.
da ciyon kai ta tashi saboda kukan da tasha gashi kuma tayi bachi hannunta Gwaggo ta riko suka fito.
saida ta wanke mata ido sannan ta nufo tabarma.
Halilu dai kallonsu kawai yake yan mamakin irin son da Gwaggo take yiwa Mairo
saida ta zauna sannan ta zaunar da ita saman cinanunta (cinyoyi) ta shiga bata abincin da hannunta.
kai Halilu ya girgaza yace "Gwaggo kinga irin wannan sagartar da kike nuna mata shi yasa take kara lalacewa tana rashin jin maganar nan"
tsaki Gwaggo taja ta watsa masa harara sai yanzu take jin haushin dukan da yayima Mairo.
bai sake ce mata komai ba harta kare bata abinci ta bata ruwa kamar wata jaririya ta zaunar da ita saman tabarma tana k'ok'arin tashi Mairo ta rik'o hannunta tace "Gwaggo kin daina sona ko?"
dawowa tayi ta zauna tana shafa fuskarta tace "ina sonki Mairo inban so kiba wazan so halinki ne bana so koshi kuma na rashin jin nan da kikene ina sonki Mairo"
saida ta kalli Halilu dake kallonta sannan ta sake kallon Gwaggo tace "tho miyasa kika bari Halilu ya dakeni É—azin?"
"saboda abunda kikayi baki kyauta ba kuma inason ya zamo miki dalilin da zaisa bazaki sake irin abunda kikayi ba ko makamancinshi"
jikinta ta shiga nunawa Gwaggo da ko ina kwancin bulalane "amman Gwaggo ai kwarai dakeni dubi jikina kuma inata kiranki ki ceceni kika kyaleni"
"na daina Mairo daga yau babu wadda zai sake dukanki bazan bari ba kiyi hak'uri kinji"
kai ta É—aga mata tana hawaye.
Gwaggo tace “amman fa ki rika jin magana kinji?â€
“na daina daga yau bazan sake ba Gwaggo har na mutuâ€
tashi Halilu yayi ya nufi kofa yana faÉ—in “indai dukane tho yanxu kika fara shanshi har sai ranar da kikayi hankali†kukan shagwaÉ“a ta shigayi “Gwaggo ce ya kyaleni bana sonsaâ€
“a a ki daina cewa baki son sa amman dai dukakan bazan bari ya sake miki shi baâ€
kai Mairo ta É—aga mata tana share hawaye.
© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
Â
  *_KHADEEJA CANDY_*
*6*
tun daga lokacin Gwaggo bata sake bari Mairo ta fita ba.
tallar da take É—ora mata ma bata sake ba kullum tana gida ko fita zatayi saida tare da Gwaggo,
tun abun baya damun Mairo har ya fara damunta
tunani take ko ta saci hanya ta fita in kuma ta tuna da dukan da Halilu yayi mata saita tsorata duk da yake tasan Gwaggo tace mata ba zata sake bari ya dake taba.
tana zaune ta raffka uban tagumi tana tunanin karyar da zatayiwa Gwaggo da zata sa ta kyaleta ta barta fita,
can wata dabara tazo mata
tashi tayi ta koma kofar É—akin gwaggo ta fasa kuka tana murgemurge
da sauri Gwaggo ta fito tana tamabayarta “lafiya Mairo mi nene?â€
“ni gidansu Jummala nake son zuwa ba tada lafiyaâ€
shiru Gwaggo tayi tana kallonta dan tasan rigimar ce ta tashi
“nidai babu ruwana kinsan halin Halilu in yanxu yazo bai ganki ba faÉ—a zaiyiâ€
“tho ai ba daÉ—ewa zanyi ba kuma ai ba zaki faÉ—a masa baâ€
Gwaggo bata sake cewa komai ba ta nufi tabarma ta zauna.
Mairo na ganin haka takara É—aga murya tana ihu
cikin faÉ—a Gwaggo tace “tashi kije kuma duk kika daÉ—e babu ruwa daga can kuma karki biya ko inaâ€
tashi tayi tana dariya daman kukan kawai take ba hawaye.
“amman dai zan biya giÉ—an tsoho ko tunda kusa neâ€
“nidai ba ruwana keda Haliluâ€
“eh na yardaâ€
da gudu ta fita gidan
bata tsaya ko'ina ba sai gidansu jummala wuni sukayi suna shiririta basu can basu nan.
sai da bayan magariba sannan ko wannensu ya nufi gida
da fargaba ta shiga gidan tana lek'e2
bakin k'ofar É—akin Gwaggo ta hango Halilu zaune farin wata na haskashi.
faÉ—uwa gabanta yayi É—an tasan ita yake jira zagi ta shiga zabga masa cikin ransa.
_hege mai katon kai mai kamada zabarmawa ni dai wlh ka takuramin Allah kasa ma ya mutu mai idon mage (mussa) mai kan ɓera_
ta daÉ—e gurin tsaye tana kallonsa wai ko zai tashi amman sai kara gyara zama yake.
kamar ta fasa kuka ta shiga kwalawa Gwaggo kira _Gwaggo Gwaggo Gwaggo a dawo_
É—agowa Halilu yayi yana kallon k'ofa yace “to shigo mana aike ake jiraâ€
k'in shigowa tayi ta cigaba da kwalawa Gwaggo kira “Gwaggo ke ki taho mana ganiâ€
ta daÉ—e tana kiranta sannan ta fito sanye da hijab da alama sallah ta k'are,
har kofar gida tazo ta kama hannunta suka shigo.
tashi Halilu yayi yana k'ok'arin rikota Gwaggo ta tare “kyaleta Halilu ni na aiketaâ€
“Gwaggo ki daina goya mata baya tana k'ara lalacewaâ€
“tho mi nayi da zakace na goya mata baya bana son raini fa Haliluâ€
“wane irin aikene zaki mata tun da maraice sai dare zata dawoâ€
Mairo ta turo baki tana watsa mata harara “ai bada maraice bane da rana neâ€
buge mata baki Gwaggo tayi “ke yiwa mutane shiru dake ake neâ€
kai Halilu ya girgiza “yayi miki kyau ai kamaki zanyi saiki faÉ—i wadda ya aikekeâ€
kuka Mairo tasa “Gwaggo kinji ko dukana zaiyiâ€
“ba zai dakeki ba bani na aikeki baâ€
“hmmm Gwaggo ina miki tsoron wata rana ki daina goyawa Mairoâ€
“wai miyasa ka rai nanine Halilu karya zan maka kenan na faÉ—a maka aikenta nayiâ€
taɓe baki yayi ya girgiza kai ya fice.
kwafa tayi da taga ya fice “kai mugu bakin azzalumi to zo ka dakeni É—inâ€
sakin hannunta Gwaggo tayi ta shiga mata masifa “ban rabaki da rashin kunya ba kuma kinsan saida mukayi dake bazaki daÉ—e ba kikaje kika zauna har dareâ€
turo baki tayi “to ba shine daren yayi saurin yi ba kuma kinsan na daÉ—e ban fita ba kuma...â€
bata karasa maganar ba Gwaggo ta katsa mata tsawa “ke dan Allah rufe min baki 'yar rashin ji kuma ki wuce kije kiyi sallah kici abinciâ€
da ture2 ta nufi É—aki tana gunguni.
_Washe gari..._
tun safe Mairo tasa Gwaggo gaba tana rokonta tayi mata giÉ—ar siyarwa,
sai faman rantsuwa take mata wai bazata sake yin abunda tayi ba.
sam Gwaggo kin yarda tayi duk da magiyar da tayi ta mata
Mairo na ganin haka ta sawa Gwaggo kuka ba k'akkautawa harda su shak'ewa tana murje murje cikin kasa duk ta bata kayan jikinta.
banza Gwaggo tayi da ita duk da bata son kukanta amman ta daure.
haka ta wuni tana kuka ta kuma yi sa ah Halilu bai dawo gidan ba tun fitar da yayi da safe.Â
     saida ta gaji dan kanta ta shi ta dawo kusa da Gwaggo dake tukin tuwo ta zauna tana ajiyar numfashi,
  Gwaggo saida ta gama kwashe tuwon ta kai ɗaki sannan ta riko hannunta suka shiga banɗaki tayi mata wanka.
har suka fito bata daina ajiyar zuciya ba idanuwanta duk sun kunbura sunyi ja
saman gado Gwaggo ta zaunar da ita ta É—auko doguwar rigar atamfa tasa mata,
ta kwantar da ita saman jikinta tana shafa bayanta
lafewa Mairo tayi in banda ajiyar zuciya babu abunda take sauke
sun daÉ—e a haka Gwaggo sai buga mata baya take tana son tayi bachi ita kuma taki tayi bachin sai faman sauke wahalallen numfashi take.
kai Gwaggo ta girgiza tace “ni kan Mairo kina bani mamaki ace bakida aiki sai kuka sai ja magana sai masifa haka kawai ki wahallarda kanki dubi yadda kika wuni kina kukaâ€
nan sabon kuka ya zo mata “to bake bace kika ki yarda kimin giÉ—a ba kuma na faÉ—a mki bazan sake baâ€
da in'in niyar kuka take maganar tana numfashi da karfi kamar zuciyar zata fito
bubbuga bayanta Gwaggo ta shigayi tana faÉ—in “halinki nake tsoro Mairo karkije ki sake yin wani abun kuma kina ganin yadda Halilu ya sa miki ido jira kawai yake kiyi wani abun bama hHlilu kaÉ—ai ba harda makota jiraye suke dake Mairo ke kuma gaki baki jin maganaâ€
É—agowa tayi idonta cike da hawaye tace “wlh Gwaggo na daina na faÉ—a miki bazan sake ba in kuma na sake Allah yasa na mutuâ€
rufe mata baki Gwaggo tayi “Subhanallahi Mairo miye haka karki sake faÉ—an irin wannan maganar kinjiâ€
kai ta É—aga mata “na daina Gwagho zaki doramin ko gobe zakimin giÉ—ar?â€
shiru Gwaggo tayi tana tunani dan tasan Halin Mairo in kuma bata dora mata ba wata sabuwar masifa ce.
kallonta tayi tace “kinmun Alkawari bazaki sake ba bazaki yi abunda zaisa a dake kiba?â€
da sauri tace “eh nayiâ€
“shikenan zn dora mikiâ€
“gobe ko Gwaggo?â€
“eh Allah ya kaimuâ€
“aminâ€
rumgumeta tayi “na gode Gwaggoâ€
“Allah yayi miki Albarkaâ€
“amin gwaggo zaki sayamin hancin ligidi?â€
“eh shi kike so?â€
“ehâ€
“to bari na bada a siyo mikiâ€
kwantar da ita Gwaggo tayi ta nufi kafit (wadurup ta da tsohuwar yayi) ta bude fanteka (kwala) ta É—auko kuÉ—i ta sa hijabinta ta fice.
© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
Â
  *_KHADEEJA CANDY_*
*7*
_Washe gari..._
tun da asuba Mairo ta tashi tana yin sallah ta shiga karatun gajerun surorin data iya inta kare ta sake maimaitawa har rana ta fito.
_8:14pm..._
Gwaggo na motsa kunu (koko) Halillu ya shigo gaishe ta har lokacin Mairo karatu take.
mamaki yayi sosai bayan sun gaisa da Gwaggo yace “yau yarki abun k'warai akeji?â€
murmushi Gwaggo tayi “ai daman tana abun k'warai indai karatu ne ai kasan Mairo ba baya baâ€
“a makarantan ba agida yaushe rabon da tayi irin wannan karatum tunfa da asuba nake jinyo ta É—akinaâ€
“to ai daman Mairo abunda take ai kuruciya ce data girma dainawa zatayiâ€
“ai da girmanta Gwaggo yanxu inta kara kaÉ—an ai aurarda ita za'ayiâ€
kuka Mairo ta fara wadda ba hawaye ta daina karantun “wlh Gwaggo bana son aure ba zanyi baâ€
dariya Halilu yayi “au daman ba karatu kike ba kunnenki na kanmu ai daman nasan karatun munafirci neâ€
kamar ta fasa kuka ta kalli Gwaggo “kice ya kyaleni ya tashi ya bar miki É—akinkiâ€
kofi Gwaggo ta janyo ta zubawa Halilu ta mika masa “karÉ“i ga kununka kosai na can gindin murhu a kwanoâ€
dariya yayi bayan ya karÉ“a yace “dan tace ki koreni shine zaki koreni Gwaggo?â€
“to naga fitina kake son jami muna zaman mu lafiyaâ€
“ai ni gaskiya ce na faÉ—a kuma Mairo da kike gani aurene kawai zaiyi mata hankali ta daina abubuwan nan da takeâ€
haÉ—ashi da Allah Gwaggo ta shiga ganin Mairo nason yin kukan da gaske daker ta samu ya fita.
juyawa Mairo tayi zata cigaba da karatu Gwaggo ta shafa bayanta “taso haka yar Gwaggo ki karya (breakfast) ai kinyi karatun da yawaâ€
murmushi tayi “to gwaggo aI zaki mun giÉ—ar ko?â€
“sosai ma ai dole nayi miki bana miki alk'awari ba anjima kaÉ—an zanyi mikiâ€
daɗi ne ya lumluɓe Mairo da sauri ta ɗauki kayan karatun ta aje gefe ta kwanto jikin Gwaggo ta soma bata kunun tana sha cike da jindaɗi.
_2:00pm....._
Mairo ta fita tallar giÉ—ar k'inbi tayi hanyar da tabi ranar duk da zuciyarta na raya mata ta É—an lek'a taga ko yana nan gashi har k'anshin goribar birni takeji tana tuna yadda take cinta.
haka dai ta daure ta nufi bakin kasuwa gurin data saba zama tana siyarda giÉ—ar. wata yarinya na zaune a gurin tana ganin Mairo ta tashi da sauri ta koma gefe dan tasan halin Mairo indai matsifa ce saida ka barmata balle yau da fuskarta take a haÉ—e kamar anyi mata mutuwa.
koda la'asar tayi Mairo siyar da bakin rai ta nufo gida tana tureture baki kamar ta fasa kuka sai wata tafiya take kaÉ—an kaÉ—an.
haka ta ido gida ko sallama babu tun a bakin kofa tayi jifa da turen ta ta karaso idonta ciki da kwallah ta zauna kusa da Gwaggo dake Sallah,
tana sallamewa ta kalleta “lafiya Mairo waya taÉ“a ki?â€
soshe soshe ta shiga yi tana tunano karyar da zatayi “ni..ni...ni....É—an ta malele zan siya?â€
shafa kanta Gwaggo tayi tana murmushi “haba Mairo sai kace wani abu harda su kwallah? É—auki kuÉ—i kije ki siyo ki haÉ—a da kifi yadda zaki jidaÉ—in cinsaâ€
kai ta É—aga “tho amman sai in zanje makarantaâ€
“tho inkin huta ki watsa ruwa sannan kije makaranta kinjiâ€
kai ta É—aga mata ta mika mata kuÉ—in giÉ—ar.
“eyeee Mairo yau duka aka siyar gaske naji kin jefar da ture tun kofaâ€
murmushi Mairo tayi “yau nawa zaki ban?â€
“hamsi zan baki ashiri kisa a susu talatin ki siye É—an ta maleleâ€
ta karasa maganar tare da mika mata 50 É—in.,
da zumuɗi ta karɓa ta tashi ta nufi ɗaki da guɗu yau an sami abun sawa a susu mai tsoka.
  '''*** *** *** *** *** ***'''
   tun daga lokacin kullum sai Gwaggo tayiwa Mairo giɗa ita kuma bata fashin zuwa gurin siyarwa so ɗaya ta je gurinda aka bata goribar birni koda taje bata tararda kowa ba tsoro taji sosai babu abunda take rayawa a ranta sai aljani ne
“kai aljanine wannan mutunen da gaskiyar Gwaggo tunda gashi ban sake ganinshi ba kuma duk goriba karfine da ita amman tashi taushi ne da ita kuma na riga naciâ€
a fili take wannan maganar can ta tsaya tana tunani “inda ba aljani bane ai bazai zo cikin dajin nan ba har ya zauna kuma fa....â€
bata karasa maganar ba ta watsa da gudu saboda motsin da taji cikin itacen dake gurin tana faÉ—in “karku biyoni na daina bazan sake zuwa ba wayyoh Gwaggoâ€
ihu take tayi da kuka tana gudu rabin giÉ—arta na zubewa,
har tabar gurin bata daina kuka ba dan gani take kamar sun biyota saida ta isa baki kasuwa sannan ta É—an natsu ta soma numfasawa daidai,
tun daga lokacin bata kara tunanin zuwa gurin ba
duk ta É—auko tallar giÉ—arta sai dai ta nufi bakin kasuwa inta siyar ta tayi ta shiririta ita da abokanin talla ko inta dawo ta biya gidansu jummala suyi gantalin da suka saba daman haka take so,
fagen neman magana da matsifa ba babba ba yaro kowa ta raina musamman inta ga ta girmeka ko kana tsoronta,
    Gwaggo in banda goya mata baya babu abunda take.
Halilu yayi faÉ—a harya gaji amman a banza kamar ma kara turata yake,
gashi Gwaggo ta hana ya daketa sai in ya faki idonta ko ya haÉ—u da ita can waje.
harta saba inta ganshi saita chanja hanya haka suka rika wasan ɓoya ita dashi.
*_3 months later....._*
yau da wuri Mairo ta siyarda giÉ—arta kuma yau bata jin wasa saboda dukan da Halilu yayi mata jiya dan yanzu har bakin kasuwa yake zuwa da ya tarar tana wasa ya fatattaketa da duka har gida,
duk yadda abokanin shashacinta sukaso ta tsaya kiyawa tayi dan tsan sai yazo gurin kuma Gwaggo tace mata da ta siyar ta dawo gida dan kar halilu ya daketa,
sallama tayi musu badan sunso ba dole suka kyaleta wasu kuma suka wuce gida dansu inba da Mairo ba basa jindaÉ—in wasa,
_Aysha adon gari ga Hajara adon gari ni Maryam adon gari inba ni ai ba gari Khadija Abubakar nake Candy kunji laqani gani tafe da'ayari yan mata a dandali_(MY UP COMING SONG INSHA ALLAH)
Mairo na tafe tana rera wak'a mak'ale da turenta na giÉ—a.
tunda kamin ta k'araso ta hango wata kafirar mota baqa mai shek'i fake kofar gidansu yara sun zagayeta sai shafa suke.
© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
Â
  *_KHADEEJA CANDY_*
*8*
da gudu Mairo ta karaso gurin ta shiga korar yaran duk da bata san mai motarba É—an kawai ta ganta kofar gidansu ne kuma taga yara sun zagayeta suna shafa ita yar neman masifa,
shafa motar itama ta shigayi tana dariya tana kallon kanta ta madubin motar harda zira halshe tana lasa glass tana tale idanunta (fitar da ido)
tafi kafin minti 3 ahaka sai fana dariya take kamar wata taɓaɓɓiya,
yaran sai kallonta suke suna son su kwakwayeta suna tsaron tayi musu masifa tunda taɓa motar ma ta hana su.
can ta juyo ta kallesu ta hade rai taja tsaki “mtssss ku dan Allah ku ba mutane guri kauyawan banza kawai kowa ya bar mana k'ofar gidan mu ko naa muku hegen dukaâ€
maganar take tana wani É—ageÉ—age da marmaÉ—en ido.
     duk ja yaran sukayi da baya dan sunsan halin Mairo indai masifa ce ba baya ba
yarinya É—aya aka bari tana watsawa Mairo harara harda kai hannu ta shafa motar tana faÉ—in “an shafa kema ai yar kauyece da hegen kankiâ€
kai Mairo ta girgiza tana dariya “hee ni kike faÉ—awa wannan maganar zaki ko ci ubanki yanzuâ€
É—ankwalinta ta cire ta k'ulle kuÉ—in giÉ—ar dake hannunta ta É—aura É—an kwalin a k'ugunta (kwankwaso) tayi cikin yarinyar suka hau faÉ—a da juna,
kaye huɗu yarinyar tayiwa Mairo dan ta fita girma kuma k'arfi ba ɗaya ba gashi daman can Mairo ba wani k'arfi ne da itaba sai yar banzar masifa.
É—ukan k'warai Mairo tasha a hannun yarinyar tun tana iya jurewa har takai ga fasa kuka tana faÉ—in “azzaluma wlh sai naci ubanki hegiya-â€
Mairo bata rufe baki ba yarinyar ta kai mata wani mugun shuri.
nan Mairo ta faÉ—i ta fashe da kuka
da gudu yarinyar tabar gurin gudun kar Gwaggo ta ji ta fito.
kuka Mairo tayi tayi tana kallon kofar gidan ganin babu wadda ya fito yasa dole ta tashi rik'e da É—ankwalinta a hannu kanta kuma duk k'asa ta shiga gida,
da kuka ta shiga gidan ta nufi gurin Gwaggo dake bakin murhu tana eza wuta.
da sauri ta É—ago ta rikata “lafiya Mairo Halilu ne ko?â€
kai ta girgiza mata ta shiga faÉ—a mata abunda ya faru,
É—ankwalinta Gwaggo tasa tana share mata hawaye “haba Mairo miye na wani korar yara dansun taÉ“a mota kuma in banda fitina inake ina faÉ—a da wannan yariyar?â€
turo baki Mairo tayi ta ɓata fuska kamar ta fasa kuka
“shigar mata kikayi ko Gwaggo?â€
“a'a wani nan na shigarwa wata na bar Mairo dukan da ta miki ne ban jidaÉ—ibaâ€
“kuma harda wani mugun shuri tayi mun ina jin zafi har yanzuâ€
“barta da Allah kijinâ€
kai ta É—aga “Gwaggo motar wace kofar gida?â€
“yan birni ne suka zo ganin gidaâ€
kusa da ita Mairo ta matso “yan bunni Gwaggo gurin wa sukazo ina sukeâ€
“sun tafi ganin sauran dangiâ€
“lahh daman Gwaggo kina da yan uwa yan bunni?â€
“eh kema ai en'uwanki ne tun kima karama marabinsu da nanâ€
risinawa Mairo tayi zatayi magana sukaji Sallama.
Gwaggo ce ta amsa masa Mairo kan ido ta sakar masa kamar bata taɓa ganin mutane ba,
harya karaso tsakar gidan shi take kallon tana masa dariya shidai kallon kawai yake kamin ya kalli Gwaggo yace “Sannu da aiki Gwaggoâ€
“yauwa sannu qasin kai kaÉ—ai ka dawo?â€
“eh ina gabansu ne suna hanya sumaâ€
tabarmar dake shinfiÉ—e k'arkashin ecce ya nufa ana k'ok'arin zaunawa yayiwa Mairo magana
“ke baki eya gaida mutane ba?â€
tasowa tayi da gudu tazo kisa dashi ta zauna.
“na eya ina wuni?â€
“lafiya kalau ya sunaki?"
saida tayi dariya sannan tace “Mairo sunana Mairoâ€
murmushi yayi ya kalli Gwaggo “Gwaggo ni bansan wannan yarinyar ba yar gidan nan ce?â€
daga can Gwaggo ta amsa mishi “eh gidan nan take ear uwarka ce ai yar wajen margayi ceâ€
“wane margayi?â€
“malam tanimu wadda koda kukazo gaisuwarsa bakayi aureba ita kuma tana k'aramaâ€
shiru yayi yana kallon Mairo data washe masa hak'ora,
“na ganeta Gwaggo daman ke kike rik'onta?â€
sallamar dasu Abbah sukayine ya hana Gwaggo amsa masa tambayarsa.
“amin wa'alaikassalam alhaji harku dawo?â€
“eh wlh kinga kara mu kama hanya da wuri tunda munga dangiâ€
momi ce ta amsa mata.
bayan sun xaune Gwaggo ta nufosu tana faÉ—in
“ai nikan ban yaba miku ba ace mutum shekara ds shekaru rabonsa da gida amman yazo É—ai rana ai kamata yayi ace kuzo ko sati É—aya kuyi ko biuâ€
É—ariya sukayi Abbah yace “har yanzu dai Jamila baki chaja ba halinki nanan na masifaâ€
“yau ni wani haline dani daga faÉ—ar gaskiyaâ€
momi tace
“karki damu jamila insha Allahu zamuzo muyi sati anan yanzu bamuzo.da shirin kwana ba kuma kinga sauran yara suna makaranta sai anyi hutu tukunaâ€
taÉ“e baki Gwaggo tayi “nidai nawa idone ai rana bata karyaâ€
dariya suka sake yi har Mairo sai a lokacin ta gaishesu.
duk suka amsa Abbah ya shafa kanta “Maryam am girma ko?â€
“ashe zaka iya gane ta ai É—aukar ka mantaâ€
cewar Gwaggo
murmushi yayi yace “haba dai yar tawa zan manta ko yanzu da mukaje gurin tsoho saida mukayi maganartaâ€
mansura ta kalleta tana murmushi tace “oh Abbah itace yarinyar da ake maganaâ€
momi tace “eh itace yar marainiyaâ€
“Allah sarki Allah ya jikan mahaifaâ€
duk suka amsa da Amin.
sun É—an juma suna fira daga bisani Gwaggo ta kawo musu abinci.
gudun masifar Gwaggo yasa dole suka ci badan sunso ba koshi kaÉ—an sukaci dan tuwon dawane ba wani sonshi suke sosai ba.
kuÉ—i Abbah ya ciro aljihunsa masu É—an É—ama ya ajewa Gwaggo “gashi ayi wata lalurarâ€
“haba Alhaji bancin abin alkharin da aka kawo?â€
“babu komai jamila a daici da hak'uriâ€
godiya sosai Gwaggo tayi masa momi da mansura sukayi mata sallama.
suna shirin fita Mairo ta laqe kafaÉ—a ta bata fuska ita saita bisu.
Gwaggo ce ta shiga lallasarta “haba Mairo wane irin binsu kuma bunni fa zasujeâ€
“eh ina son zuwa bunni nidai saina bisuâ€
“kinason ki daina ganina?â€
“a a ai dawowa zanyiâ€
Abbah ne ya dafata “kiyi hakuri Mairo kinga Jamila bata so kije ki bari har wani lokacin inmun dawo sai muje dake kinji?â€
kuka ta fasa “a a ni saina biku yanzuâ€
Qasin ya kalli Gwaggo yace “Gwaggo ki bari aje da ita tunda tana son zuwaâ€
faÉ—a Gwaggo ta soma “babu inda zataje ita kenan ina ganinta ina jindaÉ—i saiku É—auke ta to baza taje baâ€
juyowa Gwaggo tayi gurin Mairo ana lallasarta ba
aiko.kamar tana kara turata sai uhu take kaar wadda aka yiwa wani abu.
Abbah tsaye yayi yana lallaɓata shima
duk yadda Momi taso su tafi kiyawa yayi dan bayason barin Mairo tana kuka gashi Gwaggo ta hana aje da ita.
suna Halilu ya shigo aiko da gudu Mairo ta tashi tayi bayan Gwaggo tana kuka,
nan ya shiga tambayar abunda akayi mata momi ce ta faÉ—a masa,
nan ya hau Mairo da masifa “Allah in baki yiwa mutane shiru ba saina miki shegen duka yar iskar yarinyaâ€
kara buÉ—e baki Mairo tayi tana kuka kamar wata karamar yarinya,
Gwaggo ta kalli Halilu “kaga ko ana neman tayi shiru kaxo kana mata masifa koâ€
“to Gwaggo in tana son xuwa ki barta taje mana in kuma ba zataje ba su su kama hanya kar dare yayi musuâ€
“to waya hanasu tafiya ai sune suka hure mata kunne tace saita bisuâ€
Qasin yace “a a Gwaggo karkiyi zargin kowa itace kawai dan kanta tace saita bimuâ€
momi dai haushine yasa ta fice ita da mansura suka bar Abbah da Qasin.
Halilu yace “ni wlh da kina yarda da kinbarta taje su da kansu zasu dawo da ita dan mugun halintaâ€
kin yarda Gwaggo tayi saida taga su Abbah zasu wuce gashi Mairo na kuka kamar ranta ya fita sannan ta amince.
aiko Mairo kamar ta zuba ruwa k'asa tasha da gudu ta nufi É—aki ta shiga haÉ—a kayanta cikin bakko (ghana most go).
© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
Â
  *_KHADEEJA CANDY_*
*9*
bayan Amimcewar Gwaggo saida akaje gurin tsoho tare da Mairo aka faÉ—a masa shima kin amincewa yayi saida yaga abun na Mairo bana wasa bane sannan ya yarda sosai Abbah ya jidaÉ—i daman tun rasuwar kanensa yaso a bashi ita Gwaggo ta hana,
sai goshin magariba (kusan magariba) suka kama hanya
so huɗu ana tsayawa Mairo nayin amai jikinta sai rawa sanyi yake nan da nan zazzaɓi ya rifeta saida aka kashe ac ɗin motar,
*_9:37pm....._*
suka isa Sokoto koda Qasin yayi farkin Mairo na rungume jikin momi tana bachi.
saida kowa ya fita sannan momi ta tasheta
a firgice ta fito motar tana É—aga kanta hankes ya cika mata ido,
gidan sama ne mai hawa É—aya ko ina an manna gulof murza ido Mairo ta shigayi dan gani take kamar mafarki take.
bayan momi ta fito Qasin ya rufe motar shida Mansura suka nufi part É—insu daman Abbah tuni ya wuce nashi part É—in,
Mairo na tsaye tana kalle2 momi ta rik'a hannunta zasu shiga ciki Mairo tayi tsaye tana kallon kofar farlon da alama tsoro take ji,
faÉ—uwa gaban momi yayi tana tsoron kar kuma tace bazata shiga ba.
“lafiya zomu shiga ciki manaâ€
shiru Mairo tayi ta lakkafe kafaÉ—a
saida Momi ta maimaita sannan tace “nan ne gidan?â€
“eh nan ne zo mu shiga cikiâ€
tsaye tayi kamar bazata shiga ba
momi bata bi ta kanta ba taja hannunta suka cigaba da tafiya.
jiki a sanyaye Mairo ta shiga farlon tayiwa hannun momi mugun rik'o Usman na kwance saman doguwar kujera yana bachi siraj kuma na kallo,
shine ya taso ya tari momi da far'ah “sannu da zuwa momiâ€
“yauwa sannu siraj baka kwanta ba?â€
kayan dake hannunta ya k'arÉ“a yana faÉ—in “eh ban kwanta ba wacece wannan momi?â€
kallon Mairo momi tayi “qanwarka ceâ€
“daga can aka zo da ita?â€
“eh bari na shiga cikiâ€
Up stairs momi ta nufa Mairo na rik'e da hannun Momi,
suna shiga bedroom Momi ta faÉ—i zaune saman bed ita da Mairo,
har lokacin tana rike da hannunta
bayan sun É—an huta Momi ta nunawa Mairo tawel “jeki ki É—auki ga tawul can ki É—aura sai kiyi wanka kici abinci ki kwantaâ€
kai Mairo ta girgiza “a'a nidai Gwaggo wanke min kafafu kawai take in zan kwanta bata min wankaâ€
“to mu wanka muke in zamu kwanta tashi ki cire kayankiâ€
tashi Mairo tayi ta nufi gurin da Momi ta nuna mata.
itama Momi tashi tayi ta shiga cire kayanta
saida ta gama wanka sannan ta kira Mairo tayi mata
tare suka fito Mairo bata tsaya jiran komai ba ta faɗa saman bed
Momi kuma ta nufi waduraf tasa kayan bachi ta É—aura zane sama bayan tasa hijab ta kabbarta sallah.
koda Momi ta gama sallah Mairo tayi bachi.
tana cire hijab É—inta ta nufi down stairs.
bata daÉ—e ba ta shigo É—akin da plate din abinci a hankali ta shiga tada Mairo amman hakan bai hanata farkawa a firgice ba.
“k'arÉ“i ga abinci kici saiki kwantaâ€
kin k'arɓa tayi ta tsurawa Momi ido can kuma ta mayarda su gurin abinci.
sakwarace da miyar agutsi da namomi hannun tasa ta k'arÉ“a “ni bazan iya cinyewa duka baâ€
“ci kibar sauraâ€
kusa da ita Momi ta zauna tana amsa waya.
saukowa Mairo tayi kasa ta hau cin abinci
cikin yan mintuna ta kare ta tashi tana suɗar miyar dake plate ɗin duk ta ɓata gurin da miya kamar mai ɓararen baki.
nunawa Momi hannunta tayi “na kare ina zan wanke hannuna?â€
toilet Momi ta nuna mata
tana gyaran É—aurin tawul ta shiga toilet É—in
koda ta fito Momi ta gyara gurin tana mopping
tsaye tayi har momi ta kare ta nuna mata gado “hau ki kwantaâ€
ba musu ta hau Momi taja zanen rufa ta lulluɓa mata.
ta kashe wutar É—akin ta kunna ta bedside lamp ta nufi kofa,
Mairo na ganin zata fita ta tashi da sauri “ni kaÉ—ai zaki bari nan?â€
Momi daga gurin da take tsaye tace “tsoro kike jine?â€
“eh bazan iya kwana ni kaÉ—ai baâ€
“babu abunda zai sameki ki kwantar warki kiji?â€
“aa ni bazan yarda baâ€
saukowa tayi ta nufo Momi.
Momi tace “to bari na kunna miki wutar saiki kwanta kamin nazo yanzu zan dawo jeki kwantaâ€
lake kafaÉ—a tayi “a a ni bazan yarda baâ€
tsawa momi ta katsa mata “wuce kije ki wanta naceâ€
jiki na rà wa Mairo ta faɗa saman gado ta ɗanne fuskarta cikin katifa,
Momi na ganin haka ta taja kofa ta fice
kuka Mairo tayi tayi kaÉ—ankaÉ—an kuma ta kasa É—ago kan dan tsoron kar taga wani abu har bachi ya É—auketa.
*_washe gari....._*
tunda asuba Momi ta tada Mairo
a firgice ta farka jikinta sai rawa yake hannun momi ta rika suka shiga banÉ—aki tare sukayi alwala.
bayan sun fito Mairo ta nufi yar zakarta ta zazzage ta É—auki wata atamfar kauye tasa tare da hijab ta fara sallah,
tana sallamewa komai bata tsaya yiba ta koma bachi.
sai 8 da minta ta farka koshi dan siraj ya tada tane.
da murje murjen ido ta tashi tana mik'a idonta a lumshe tana soma kiran gwaggo.
“ke tashi momi na kiranki naceâ€
‘to’ tace tana turo baki kamar ta fasa kuka
shidai bai tsaya jiranta ba ya fice,
saida ta gama gunguninta sannan ta tashi ta nufi kowa duk jin take bata son gidan,
tana fitowa ta hango farlo down stairs.
wani irin ihu ta saki saboda juwa data gani tayi bayabaya tana kiran “na shiga uku wayyo Gwaggo na bani mutuwa zanyiâ€
duk kai suka É—ago sun Kallonta daga dining area siraj ne ya fara tambaya “lafiya?â€
cikin kuka tace “na bani bazan iya saukowa ba na shiga uku Gwaggoâ€
duk fashewa sukayi da dariya banda siraj da yaja tsaki sai kuma Momi data hau mata faÉ—a “ke wai wane irin iskancine dake haka haka kawai zaki rika yiwa mutane uhuâ€
Qasin dake tsaye ya kalli Momi yana murmushi “tsorone taji momi kinsan yar kauye ceâ€
“to dan taji tsoro sai tayiwa mutane ihu iskancin da takeyi can kauye nan bazan É—auke shibaâ€
tea cup É—in dake hannunshi ya aje ya nufi up stairs.
hannunta ya riko ta rumgumeshi iya karfinta ta kulle ido gam sannan suka sauko.
har suka isa dining bata buÉ—e idon ba saida taji an zauner da ita sannan ta buÉ—e ido tana kare musu kallo,
da Qasin ta fara sannan Usman, Siraj sai kuma ta juyo gun Nura.
kofin tea Momi ta aje mata idonta cike da hawaye ta É—auka ta kai baki
bata ajeba saida tasha rabin kofin Siraj da Nura da Usman sai dariyarta suke Qasin Murmushi yayi ya kalli agogon hannunsa yace “Momi ni bari na wuce gurin aikiâ€
“to Allah ya tsareâ€
“Aminâ€
saida ya kara kurɓa tea ɗin sannan ya fice.
Usman ya kalli Mairo yana driya yace “bakison bredin hala?â€
banza ta masa har Momi ta kare cin abincinta da Usman suka tashi.
sannan ta É—auki bredin tana hawaye ta rika somawa kamar turo da miya tana ci.
© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
Â
  *_KHADEEJA CANDY_*
*10*
Siraj dai sai kallonta yake can yaji bazai iya zurewa ba yace “wai mi kike yiwa kuka?â€
cikin kukan tace
“ni gida nake soâ€
dariya yayi “gida?â€
“ehâ€
“mi aka miki to?â€
“bana son gidan nan bana son gida a sama kuma mumi faÉ—a take minâ€
fashewa sukayi da dariya Nura yace “hala baki taÉ“a ganin gidan sama ba?â€
“eh nidai bana sansaâ€
tashi nura yayi yana faÉ—in “amman gaskiya kauyancinki yayi yawaâ€
k'ara turo baki tayi kuka nason fito mata fili Siraj dai kallonta kawai yake har ya kare cin abinci ya tashi,
Mairo tasowa tayi ta dawo kusa da doguwar kujera dake parlour ta zauna har lokacin hawaye take.
jin tafiyar momi yasa ta É—ago kai tana kallon up stairs “lafiya kike kuka?â€
fuskar momi a haÉ—e take mata tambayar
“gida nake so gurin Gwaggoâ€
murmushi momi tayi “karya kike yi ai ke kika dage saikin biyomu jiya jiya muxo yau kice a kaiki gida babu yadda bayiba akan ki zauna kika kiâ€
hannayenta ta haÉ—e tana rokon momi
“na daina mumi bazan sake cewa a zo dani baâ€
“uhmm tashi muje kicin kiyi wanke wankeâ€
lake kafaÉ—a tayi “ni ban iya wanke wanke baâ€
kunneta momi ta kamo “ke bari kiji na faÉ—a miki iskancin da kike can kauye nan bazaki min shibaâ€
kuka Mairo tasa sai kiran Gwaggo take.
haka momi taja hannunta suka nufi kicin.
gurin wankewanke momi ta nuna mata ta “oya sa hannu ki wanke†kallon momi tayi idonta cike da hawaye tace “wlh ban iya wanke wanke baâ€
“dukanki dai kikeso nayi kamar zakice baki iya wanke wanke ba kuma rikon kauye ba birnin ba koki wanke shi ko na miki dukan tsiya†momi na kaiwa nan ta juya tabar kicin ɗin,
haka Mairo ta hau wankewanke tana kuka
sama take wankewa dan har ga Allah bata iya ba tunda Gwaggo bata sata aikin komai inba sharaba koshi inta ga damane take yi.
haka ta wankesu samasama kofukan da akasha tea ma É—aurayisu kawai tayi ta aje,
koda ta kare ta fashe tea cup ɗaya kuma duk ta ɓata gurin da ruwa ɗan kwalinta tasa ta goge ruwan ta jefashi bayan firjin.
jikinta a sanyaye ta nufo parlour tsaye tayi tana kallon momi dake zaune saman kujera.
ganin bata kula taba yasa ta karaso kusa da ita “na kareâ€
sai lokacin momi ta kalleta “to wuce kiyi wankaâ€
“ina?â€
“inda kika ga na miki jiyaâ€
lake kafaÉ—a tayi tayi baya baya “ni bazan hau sama ba gaskiyaâ€
taɓe baki Momi tayi ta cigaba da kallon tv.
*****
ranar Mairo wuni tayi tana kuka saboda faÉ—an da momi tayi mata kuma ta hana mata abincin rana saboda takiyin wanka.
da magariba Mairo na gefen kujera zaune Momi ta nufi kofa da sauri Mairo ta tareta tana “ni ki bani abincina yunwa nake jiâ€
tureta momi tayi saida ta faÉ—i wani mahaukacin ihu ta saki momi saida ta rufe kunnuwanta ta hau shurenta.
“lafiya?â€
Qasin na shigowa abunda ya fara tambaya kenan
momi ta nunata da yatsa “rainin wayo ne da ita so nake na gyara mata zamaâ€
karasawa yayi ya tada ta “mi tayi momi?â€
“iskancin da take can kauye ne take son tamunâ€
kallon Mairo yayi “mi kika mata?â€
cikin kuka Mairo tace “ban mata komai ba muguwace azzaluma Æ™k'atuwar banza kuma ban yafe miki b-â€
da sauri Qasin ya rufe mata baki “ke karna sake ji ba mamanki baceâ€
kai ta girgiza tana hawaye “ni ban sonta ba mamana baceâ€
kwafa momi tayi “aiko kashinki ya bushe cikin gidan nanâ€
“wai minene mafarin wannan abun ne momi?â€
momi tace “rantsuwa nayi duk batayi wanka ba bazan bata abinci baâ€
kallon Mairo yayi “ke mi ya hana miki wanka maryam kin fi son ki zaina da k'azanta?â€
“a a itace tace saina hau saman sama sannan nayi wanka ni kuma tsoro nake jiâ€
kallon momi yayi yana murmushi “kinji momi tsoro take ji kinsan ko É—axun saida aka saukarda itaâ€
“ba wani tsoro iskancine kawaiâ€
“ba iskanci bane ko?â€
ya tambayi Mairo kai ta É—aga yace “bata hakuri sai kuje tayi miki wanka kuma karki kara rashin kunya kinjiâ€
saida ta daÉ—e sannan ta kalli momi kasa2 tace “yi hakuri bazan sake baâ€
da ita da dashi duk tsurawa momi ido sukayi sunajiran abunda zatace
saida ta watsa masu harara sannan ta fixgi hannun Mairo suka nufi up stairs.
kankame momi Mairo tayi ta rumtse ido nan momi ta sakar mata hannu “wuce da kankiâ€
kuka tasa nan momi ta katsa Mata tsawa dole ta rike karfen ta rika hawa da rumtsen ido har ta haye.
momi ce tayi mata wanka Mairo kan ana mata wanka tana tunanin yadda za ayi ta tsera ta gudu ta bar gida,
bayan sun fito momi ta wulgo mara kayanta ta sauka downstairs ta É—ebo mata abinci.
*_washe gari....._*
tun asuba momi ta tada Mairo bayan sunyi sallah bata barta ta koma bachi ba suka nufi kicin.
tare suka haÉ—a komai na breakfast ranar momi batayi mata faÉ—a ba dan tare sukayi komai duk da ba wani iyawa tayi ba daman momi abunda bata so ta saka aiki kaki da kuma kuka.
*_8:30am....._*
suka kare hada komai momi ta nunawa Mairo gurin da zata jera.
ba musu ta rika jera abinci badan ranta yaso ba sai dan gudun matsifar momi aranta kan É—ebima momi albarka kawai take tana aiban ta'ta.
Mairo ce ta fara zama bayan ta jere breakfast É—in sannan momi,
Usman da Nura dake zaune saman kukera suka nufo dining.
Siraj sai janta yake ita kuma ta wani haÉ—e fuska kamar ta fasa kuka .
momi da kanta ta zubawa Mairo breakfast su kuma suka shiga zubawa kansu.
Nura ya kalli Momi yace “yau yaya ba zai karya nanba ?â€
momi tana k'ok'arin zuba ma kanta tace “zaizo mana ai kasan nan yake karyawa kila bai tashi bachi baneâ€
kamar daga sama sukaji an banko kofar parlour duk juyawa sukayi suna kallon Qasin daya shigo fuska a haÉ—e.
yana karasowa momi tace “lafiya?â€
takardun dake hannunsa ya nunawa momi cikin zafin rai yace “kwangila ce Yarima yakai a kanfaninmuâ€
murmushi momi tayi “wow...-â€
tare numfashinta yayi ya juyarda fuska “haba momi kamar bakisan Yarima ba he just want to ruin my life kuma deal ne between me and him saina gani tsakanin ni da shi who is going to be loserâ€
tashi momi tayi ta daga hannunta da niyar yi masa magana sai kuma ta kasa jefarda takardun yayi ya fice cike da bacin rai.
*HAPPY JUMMA'AT MUBARAK.*
_i Really Need Your Prayers fans Ina Ciyon Zuciya_
© *Khadeeja Candy*
[11/10, 2:12 PM] ‪+234 806 053 5947‬: © *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
Â
  *_KHADEEJA CANDY_*
*11*
sanyi jikin momi yayi ta kasa kai komi bakinta Nura da Usman ne kawai suke cin abinci shima Siraj ya damu sai kallon momi yake,
tashi momi tayi ta nufi gurin daya watsarda takardun ta shiga haÉ—awa.
saida ta haÉ—esu guri É—aya sannan ta kalli Siraj daya juyo yana kallonta tace “Siraj jeka kiran min yayankuâ€
kai kawai ya É—aga mata ya tashi ya fice.
Mairo dai sai satar kallonsu take tana tsomen beredi,
guri momi ta samu ta zauna dafe da kai kamar mai mata ciyo.
tana haka Qasin da Siraj suka shigo dining Siraj ya nufa Qasin kuma ya nufota yana faÉ—in “gani momiâ€
kujera momi ta nuna masa har lokacin tana É—afe da kai.
bayan ya zauna ta kalleshi tace “Qasin ka rika hakuri kasan da wadda kake zama Qasin ni bana tunanin saboda É“ata maka suna ko karyarda kai Yarima ya É—auki kwangila ya bakaâ€
kawar da kai yayi alamar bai jidaÉ—in maganar ba.
ganin haka yasa momi ta taso ta dawo kusa dashi ta zauna “Qasin ni a ganina kamar ma Yarima yana son É—aukaka kanfaninku neâ€
juyowa yayi ya kalleta “a a momi so yake ya karya ni kawai kuma bazan taÉ“a yarda da wannan kwagilar ba ba zai taÉ“a cinma burinsa a kaina baâ€
dafashi momi tayi “ban sanka da zuciya haka ba bana son ka runtse ido ka yanke hukuncin da zai zamar maka nadama nafison ka yanke hukunci ido a buɗe
bana son abunda zai saka cikin matsala Qasinâ€
kallon momi yayi yana nazarin kalamanta can ya lumshe ido ya sauke ajiyar zuciya ya sake buÉ—e idon yace “momi banida mafita sai wannan momi bana son Yarima yayi nasara a kaina momi ki duba min plzâ€
itama Momi ajiyar zuciya ta sauke tace “baka ganin mayarda kwangilar zai zame maka matsala?â€
“zai iya zama kan dan lokacin da zai bada kwangilar tare da yan jarida yazoâ€
“to karka kuskura ka mayarda kwangilar zai zubar muku da mutuncin kanfaniâ€
“momi ba nida wata mafita sai wannanâ€
“haba Qasin sai kace kai ba namiji ba kai bakasan yadda zaka sarrafashiba ka bashi kunya ka taka abunda ya taka Qasin ka zama gawurtaccen namiji ba rago baâ€
Siraj da tunda ake maganar hankalinsa na gurin tasowa yayi yana faÉ—in “yes yaya kaima namijine ka ya k'eshi ks kara É—ags martabar kanfaninka kabi shawarar momi plzâ€
ajiyar zuciya Qasin ya sauke a karo na uku ya kalli momi “momi ba hannuna da nasa ya bani kwangilar ba PA É—ina yaba kuma banida tambas dan zai iya haÉ—a kai dashi ya cutar daniâ€
Siraj yace “ka chanja PA kawaiâ€
“haba Siraj how many PA I have to change just because of him? PA 4 na chanja akanshi bazan sake chanja wani ba not anymoreâ€
cikin faÉ—a yake maganar jijiyar wuyansa na tashi da sauri Usman da Nura suka juyo suna kallon su, Mairo kara sakin baki tayi tana kallonsu daman hankalinta yana gurin,
dafashi momi tayi “ga wata shawara Qasinâ€
kai ya ɗaga mata ba tare daya kalletaba ‘uhmm’
“mi zai hana ka karÉ“i kwangilar kayi da kanka?â€
murmushi yayi mai cike da jin haushi “haba momi ai zubarda kai ne daÉ—i zaiji na k'arÉ“i kwangila da hannuna masaâ€
“ba faÉ—uwa kayi ba Qasin cigabane a gareka da kuma É—aga darajar kanfaninkuâ€
kai ya girgiza “momi ba zaki gane baâ€
“kaine baxa ka gane ba Qasin idan kayi haka mutane zasu yaÉ“eka suce bakada girman kai sannan kodan kwangilar tayi ya kamata kayi haka kuma idan tayi kyau zaka jawowa kanka customers ayaba maka ka kara samun É—aukakaâ€
Siraj yace “gaskiya ne yaya ka É—auki shawarar momiâ€
ya daÉ—e zaune gurin kamin ya É—ago kai ya kalleta “shi kenan momi zanyi yadda kikaceâ€
murmushin jidaÉ—i Momi tayi ta shafa kansa “Allah ya maka albarka ya shige maka gabaâ€
shida Siraj suka amsa da ‘amin’
tashi yayi ya nufi kofa yana sauke ajiyar zuciya,
da gudu Mairo ta taso ta nufo shi tana faÉ—in “dan Allah ka je dani yawo inson fitaâ€
fuska a haɗe ya shafa kanta yace “ba yanzu ba†ɓata fuska tayi idonta suka cika da hawaye shirinta na guduwa ya rushe .
juya tayi tana kallonsa har ya fice.
tashi momi tayi ta nufi up stairs tana faÉ—in “Maryam in kuka k'are ki haÉ—a kayan ki kai kicin ki wanke kuma ki share parlour nan ki gogeâ€
kara ɓata fuska Mairo tayi abunda ta rsana kenan hawayen dake makale a idonta suka zubo.
© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
Â
  *_KHADEEJA CANDY_*
*12*
bachi Mairo take saman kujera ta wani turo baki sai numfashi take da k'arfi,
Momi na saukowa ta tadata “ke ke ke Maryamâ€
a firgice ta farka ta kara turo baki fuskartar momi ta rik'o “kinyi wanke2?â€
kai ta É—aga tana murza ido momi tace “tashi kije kiyi wankaâ€
tashi tayi kamar ta fasa kuka ta nufi up stairs zuciyarta cike da tsoro,
rik'e k'arfin tayi ta rumtse ido tana tafiya a hankali har ta haye.
    '''* * *'''
Momi na kicin tana girki taji uhun Mairo da sauri ta aje robar dake hannunta ta nufi up stairs.
tsakiyar É—aki ta tararda Mairo sai juye2 take tana kuka jikinta ba kaya kikata momi tayi “ke lafiya miya faru?â€
kasa magana tayi sai toilet take nunawa momi tana tuma,
da sauri momi ta nufi toilet É—in,
kalle2 ta shiga ta rasa dalilin dayasa Mairo kuka hankalinta bai kai gurin shower da take kunne ba sai gab da zata fita sannan idonta suka kai gurin juyowa tayi ta nufi shower da niyar kashewa,
nan hannunta ya taɓo ruwan dake zuba da sauri tayi baya baya da yar k'ara saboda ta fasasshin ruwan da suka taɓa mata hannun,
ta daÉ—e tsaye cikin toilet É—in tana duba hannunta,
sannan tasa hannun hagu ta kashe shower.
koda ta fito duk'e ta tararda Mairo sai faman kuka take tana kiran ta bani ta shiga uku ta data momi tayi tana faÉ—in “sannu Mairo ni wlh na manta da yadda shower take mantawa ma nayi na haÉ—a miki ruwan da kai na yi hakuri kinjiâ€
kai ta É—aga tana kuka tace “ni a kaini gida gurin Gwaggoâ€
hakuri momi tayi ta bata daker tayi hakuri momi ta haÉ—a mata wasu ruwan tayi mata wanka ranar har kanta saida momi ta wanke,
da suka fito momi ta rasa kayan da zata saka mata dan ita bata ga wasu kayan kwarai da zata sa mata ba haka dai momi ta É—auko wata tsohuwar a tamfa tasa mata,
momi ta kalleta tace “hau gado ki kwantaâ€
da sauri ta nufi gadon ta faÉ—a rub da ciki,
momi na gab da wucewa Mairo ta É—ago da jajayen idanunta ta kalli momi “mumo ko zaki aikeni?â€
juyowa momi tayi “aike kuma Maryam kamar ya?â€
tashi tayi zaune “in siyo miki wani abu ko aikeâ€
murmushi momi tayi tace “a a ni babu abunda za'asiyo min koma abu zan siya saidai na aiki direba ko yara su siyoâ€
komawa tayi ta kwanta tana zubarda hawaye.
kai kawai momi ta girgiza ta fice.
Mairo tunda ta kwanta take wahalallen bachi sai uku da rabi ta farka koshi dan momi ta tadata ne.
hannunta Momi ta riko ta suka nufi bathroom kin shiga tayi ta lak'e kafaÉ—a “ni bazan shiga baâ€
“yi hakuri ni zan haÉ—a miki ruwan ba zakiji zafi baâ€
daker momi ta lallaɓata ta yarda suka shiga,
brush momi tasa tayi tare da alwala sannan suka fito,
tsareta momi tayi saida tayi sallah sannan ta riko hannunta suka nufo downstairs.
zaune suka tararda Qasin yana cin abinci laptop na gefensa yana aikin danne2.
tsaki momi taja bayan ya jama Mairo kujera ta zauna,
É—agowa yayi yana kallon Momi “lafiya dai momi?â€
saida ta zauna sannan tace “hala baka ci abincin ba?â€
sosa kai ya É—anyi yayi murmushi “indomi ce ta É—afaâ€
taÉ“e baki momi tayi “to Allah ya kyauta ya sawwakeâ€
kasa amsawa yayi saima kallon Mairo da yayi yace “bakida lafiya ne hala?â€
kin masa magana tayi saima faman cin abincinta da take tana sauke ajiyar zuciya,
momi ce ta kalleshi tace “k'onewa tayi da ruwan zafi shine take fushiâ€
“ayyah sorry kijin injin bata jimu ba?â€
“bata jimuba zafin daine ya raÉ“etaâ€
kanta ya shafa “sannu kinji?â€
kai ta É—aga masa tana aika lomomi,
suna haka Usman ya fito É—akinsa ya nufi kofa.
kiransa momi tayi “Usmanâ€
“na'am Momiâ€
“dan Allah jeka É—aki ka É—auki ATM É—ina kaje nan Damary plaza ka siyo ma Maryam kayan sawaâ€
“owk momiâ€
da sauri ya nufi upstairs.
tashi Mairo tayi jikinta na rawa tace “zan bishi mumo ina zuwaâ€
momi kamar tasan plan É—inta ta zauner da ita “a a ba yanzu ba ba kasuwa zaije kuma ba daÉ—ewa zaiyi baâ€
da kuka tace “thomâ€
ta sunkuyarda kanta tana hawaye.
Qasin ya shafa kanta yana murmushi “yi hakuri bari ranar da nake free sai muje yawo ko ki zaga gari?â€
kai ta É—aga mishi ba tare data kalleshi.
murmushi momi tayi ta kalli Qasin tace “Qasin ya akayi da batun kwangilar?â€
“na karÉ“a ni da kaina zanyi kuma baza a samu matsala ba insha Allahâ€
daÉ—i sosai momi taji “Allah ya taimaka ya shige maka gabaâ€
tashi Qasin yayi ysns faÉ—in “Amin momi bari naje part É—ina nayi wani aikiâ€
kai kawai momi ta É—aga mishi ya fice rik'e da laptop.
© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
Â
  *_KHADEEJA CANDY_*
*13*
da É—are Usman ya kawoma Momi kayan (tufafi) data aikeshi ya siyo,
aiko murna gurin Mairo ba'a magana sai tsalle take tana wani shafar tufafin tana jefasu sama tana rawa.
duk wani bachin rai dake ranta ranar gushewa yayi sai faman godiya take yima momi.
tun abun naba Momi dariya har ya koma bata tsoro ganin irin murnar da take kamar zata haukace sai faman uhu take, tana daredare harda hawaye,
momi dai da taga ba kanta baro mata É—akin tayi ta sauko k'asa,
nan ta tararda Qasin yana aikin rubuce2,
guri ta samu ta zauna suka soma fira.
Mairo na jin muryarsa ta kwaso tufafin ta nufo downstairs da gugu tana faÉ—in “Qasin kaga tufafina da-â€
kasa karasa maganar tayi saboda wani mugun kaye da tasha saman tile aiko nan kuka ya chaja salo ta koma yin na gaske,
dariyace tazo ma Qasin haka ya matseta ya nufeta ya tadata tsaye yana bata hak'uri yana murza mata gurin data gimu.
momi kan faÉ—a ta hau yi mata “yarinya ba kai sai bak'ar hauka tun É—azu take murnar tufafin nan kamar mahaukaciya kekan kauyenciki yayi yawa Maryamâ€
Qasin na dariya yace “haba momi koni ai murna zanyi inna samu sabon tufafi zuwa fa tayi ta gwada min ko?â€
kai ta É—aga masa tana kuka, handkerchief É—insa ya ciro yana share mata hawaye.
“ya isa haka jeki gwada tufafin mugani suna miki kyauâ€
da ininniyar kuka tace “thomâ€
ta nufi É—aki.
tana shiga ta cire kayan jikinta ta É—auki wata diguwar riga tasa da gudu ta fito ta nufo parlour.
bata tararda shiba sai momi dake zaune saman kujera tana kallon tv,
gurinta ta nufa tana nuna mata kayan, koɗata momi tayi tana yaba yadda kayan suka karɓeta nan dariyarta ta dawo ta rik'a tsalle tana mulmula a k'asa saida momi ta soma yi mata faɗa sannan ta tashi ta nufi ɗaki.
    ''' *  *  *'''
tun daga lokacin Mairo bata k'ara saka tufafinta na kauye ba saidai wayanda momi ta siya mata,
kuma ba laifi Usaman ya iya zaɓi dan duk tufafin data saka saisun yi mata kyau sun k'arɓi jikin ta,
kyau ta ma ba laifi da farinta sai kara fitowa yake ga gashin kanta kullum sai momi ta gyara mata shi,
taci maikyau tasha maikyau tasa maikyau wasa wasa cikin wata 2 tayi bulbul kamar ba itaba,
aiki kan yanzu Mairo ta É—an fara sabawa dan kullum tare da momi suke haÉ—a breakfast kuma duk wani karamin aiki ita momi take sawa tayi tun tana fushi har ta gaji ta daina sai in taje É—aki ta rika kuka tana zagin momi da cire mata albarka,
zancen guduwa yanzu ta daina tunda taga momi bata bari a fita da ita kuma in zata fita bata zuwa da ita babu yadda batayi ba momi tak'i yarda duk wata dabara ta ta saita rushe ta daina ma yima momi zancen ta hakura,
*_3 months later....._*
yau da far'ah Mairo ta tashi saboda tayi markin Gwaggo,
koda Momi ta shigo ta tasheta zaune ta tararda ita harma tayi alwala tana sanye da hijab,
da mamaki momi ta shiga bathroom bayan ta É—oro alwala ta fito ta nufi waduraf tana faÉ—in “Maryam ya akayi yau kika rigani tashi?â€
carbi ta nunawa momi tana wani gyaran murya kamar wata babbar mace wai ita mai tasbihi ba a magana,
“hmm Maryam manyaâ€
momi ke faÉ—ar haka tana k'ok'arin É—aura zane,
hijab tasa ta shimfiÉ—a carpet ta rik'a carbin tana salati har aka tada sallah sannan suka bi zan'in masallacin dake kusa dasu,
suna karewa bayan suyi yan addu'o'e suka nufi kicin.
*_8:45am_......*
Mairo ta shiga jera breakfast a dining sai tsaki take tana faÉ—in “mumo yau munyi ranaâ€
tsayawa tayi tana kallon agogn dake manne gefen gurin tana tunani yadda momi ta koya mata,
ta daÉ—e a tsaye tana kallon agogon ganin bata tuna ba yasa ta shiga shirmen ta “kinga fa mumi har wannan mai laulaye tayi (8) da mai k'afa É—aya (4) da mai kai sama (9) gaskiya munyi rana yauâ€
da dariya momi ta fito kincin ta nufo dining tana faÉ—in “waike Maryam yaushe zaki daina wannan shirmen naki ne? ke kullum ana koya miki abu amman kamar kara toshe miki k'wak'walwa akeâ€
turo baki tayi ta nufi kujerar data saba zama ta zauna,
momi bata sake cewa komai ba ta shiga zuba mata abincin harsu Usman da Nura da Siraj suka fito suka nufo dining,
bayan sun zauna kowannensu ya shiga zubama kansa,
har suka fara ci Mairo bata ci nata ba sai kunbure2 take tana harararsu duk da momi ce take son ta harara amman ba dama.
babu wadda ya tanka mata sai Siraj dake k'ok'arin zaunawa,
“waike lafiya kike hararar mutane?â€
saida tayi kwafa sannan ta kalleshi tace “ina ruwanka daniâ€
tashi yayi da niyar ya doketa momi ta tareshi “ai tace maka ina ruwanka da ita bai isaba?â€
“tho momi baki ganin yadda take hararar mutaneâ€
“ba da kai take ba ni take son harara bata da dama saboda nace bata gane agogoâ€
komawa yayi ya zauna yana dariya “LOL yarinya aike kullum liki minandak'u ce kulli yaumin É—ifÉ—ifâ€
kifa kanta tayi da dining tana kuka,
momi ta kalleshi da siffar masifa “wai Siraj mi yasa kake wasa da ita ne bafa tabashiyarka bace mahaifinta da naku uwa É—aya uba É—aya sukeâ€
hannu ya É—aga “tho momi kice ta daina wasa daniâ€
“ai kai ka soma wasa da ita gashi har sauran suna son yiâ€
jan zib yayi a bakinsa alamar bazai kara cewa komai ba,
© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
Â
  *_KHADEEJA CANDY_*
*14*
sai a lokacin Mairo ta É—ago kai ta soma cin abinci,
_GOOD MORNING EVERYONE_
yau da abunda Qasin ya shigo dashi kenan fuskarsa É—auke da murmushi ya ware hannayensa hannunsa É—aya rike da wasu file.
duk juyowa sukayi suna kallonsa rabon da suji muryar irin wannan ta farinciki daga gareshi harsun manta,
wani sanyi ne ya ziyarci zuciyar momi dan tasan duk yadda akwai abun farincikin daya faru,
yana karaso ya mika ma momi file É—in yana faÉ—in “lafiya kuke kallona hakane?â€
murmushi sukayi suka ci gaba da cin abincisu dan sun san ko minene dole a fasa kwai suji,
a rikice momi take karanta har tana tsalleke wasu saboda daÉ—i tana kare karantawa ta mike tsaye ta rumgumeshi idonta cike da hawaye
“ai daman na faÉ—a maka Qasin duk ka É—auki hawarana bazaja taÉ“a jin kunya ba kuma ka ganiâ€
rumgumeta yayi yana dariya “haka ne momi naâ€
ko wannensu kasa cin abincin yayi sai murna suke suna yaba masa suna rumgumarsa,
Mairo kan ido ta sakar musu kamar tana cin abincinta dan ita mahaukata ta É—aukesu tunda bata gane abunda suke yiwa murna,
saida tayi tsaki sannan suka tuna da tana gurin
É—agata momi tayi saboda murna ta tsayar da ita saman dining tana faÉ—in “me kike yiwa tsaki yata? yau ranar farinciki cefaâ€
“to ba duk kunata murna ba kuma kunk'i ku faÉ—a min daliliâ€
“ayyah to yi hakuri bari na faÉ—a miki yayanku ne yaci nasara akan kwangilar da aks bashi har mutumen ya yaba masa da kalamai masu daÉ—iâ€
“to minene kwangila?â€
“sashi akayi yayi gini sai kuma yayi sa'ah shine muke murnaâ€
fashewa tayi da dariya “hahaha nima Qasin nayi murnaâ€
“to ai ba haka akeba uhu ake ana tumaâ€
aiko kamar jira take ta soma yin sama tana yin kasa saman dining,
juyawa momi tayi tana kallon Usman da yayi maganar “kasanfa bana son iskanci dan ba hankaline da ita baâ€
juyowa tayi ta sauke Mairo tana faÉ—in “ke kuma kinsan na rabaki da kiran sa Qasin ko to daga yau karna sake jiâ€
bata fuska Mairo tayi ta soma kuka,
dafata Qasin yayi “haba momi miyasa zaki sata kuka yaufa ranar farinciki ceâ€
share mata hawaye ya shiga yi yana faÉ—in “yi hakuri yi shiru kinji?â€
makkale kafaÉ—a tayi “ni bazanyi shiru baâ€
“aiko in bakiyi shiru ba ba zanje dake yawo ba kindai san kinfi kowa son yawo ko kina so naje dake?â€
kai ta É—aga tana share hawaye.
Qasin yace “good to ysu zanje dake kodan farinciki danakeâ€
da far'ah tace “yanzu ko?â€
“a'a sai an jima inna shirya harda tufafi ma xan saiya miki kiyita tsalleâ€
wata irin dariya ta saki tana tunowa da momi yasa ta karasa ba ta rufe baki,
É—agowa yayi yana murmushi ya kalli momi “thank you more. momiâ€
“ur welcome Qasin nafika farincikiâ€
“momi ai har a tv aka nuno dan da yan jarida yaje dan yayi zaton zan to zartaâ€
“kwata2 yau bamu kunna tv ba bamu gani baâ€
“ai tun jiya ne da dare aiâ€
hannu momi ta daga “oh nidai Alhamdulillah ai tunda anyi nasaraâ€
   ''' *  *  *'''
ranar wuni sukayi suna farinciki momi harda rabon kuÉ—i ta rikayi ko abincin rana ma kasa ci tayi saboda farinciki,
*_2:30pm......_*
Qasin ya shigo sanye da kananan kaya,
zaune ya tararda Mairo tasha doguwar rigar fakistan momi ta mata farkin É—in kanta kamar wata balara sai É—an gyale na abayar da take rike dashi,
ta wani hakinci kamar wata princess ga bakinta yasha mai yar girace kawai momi batayi mata ba,
tsayawa yayi yana kallonta kamin ya kai hannu yaja hannunta su taÉ“e “eyye yarinya haka momi ta gyara ki?â€
da sauri ta tashi tsaye “eh daman kai nake jira tun É—azuâ€
murmushi yayi “to yayi kyau bari naga momi sai muje kinji?â€
kai ta É—aga masa ya nufi stairs.
bai daÉ—e ba ya fito ba mairo ta mika masa hannu ya rika suka fice yana yaba kwaliyarta,
suna kaiwa parking space ya buÉ—e mata giÉ—an gaba ta zauna shi kuma ya shiga driver seat. yayima motar key suka fice,
wuni sukayi suna yawo duk gurinda suka ga wani abun kwadayi sai ya tsaya ya siya,
Qasin yasha dariya saboda Mairo take murna kamar wata taɓɓabiya.
*_4:52pm....._*
suka nufo gida Mairo sai surutu take masa shidai tun yana dariya harya koma murmushi,
daf ta zasu shiga gida ta tuno da Alkawarin da yayi mata na siya mata kaya,
aiko nan tasa mai kuka dole ya juya ya nufi Dubai mall. suna isa ta shiga k'ok'arin rigansa fita amman ta kasa dan bata san yadda ake buÉ—ewa ba,
saida ya fita sannan ys buÉ—e mata kofar ta fito sai dariya take tana yaba kyaun gurin,
suna shiga ta nufi wani gurin saida ya riko hannunta suka nufi sashen yara,
sannan ya saketa ya É—auki basket ya mika mata ya riko kunnenta “karki kuskura wuce É—auko kala uku uku kawai zaki É—auko kinji ni ai?â€
kai kawai ta É—aga mishi badan ta fahimci mi yake nufi ba dan hankalinta nacan gurin kayan data gani,
haka ta nufi kayan tana wani leko harshe kamar karya tana shafa kayan.
tafi karfin minti 20 tana duba kayan sannan ta É—auko kala biyar ta nufoshi tana dariya “duba kaga suna da kyau sosaiâ€
É—aya bayan É—aya ya rika dubasu “haba Maryam har huÉ—u keda nacewa uku?â€
“nidai su nake soâ€
“a rage kinji?â€
lake kafaÉ—a tayi “a a nidai dukaâ€
bai sake cewa komai ba ya nuna mata gurin biyan kuÉ—i “ɗauki ki kai canâ€
da sauri ta É—auki kayan ta rigashi isa,
ana cikin lissafi ta É—auko wata riga ta É—ora “harda wannan inasoâ€
bakin baki Qasin yayi yana kallonta can dai yaji tsoron ta sake É—auko wani abun ya nuna mata kofa “Maryam jeki gurin mota ki tsaya harna fito kinji?â€
ba musu ta fice ta barshi,
tsaye tayi jikin motar tana wasa da hannayenta duk wadda zai shiga saita faÉ—a masa akwai kaya masu kyau a ciki,
wasu basa kulata wasu kuma suyi ta dariyarta,
tana haka Yarima yazo shiga cikin wasu tufafi na alfarma fadawansa na take masa baya,
nunashi Mairo tayi tana faÉ—in “kai ma kayi sa'ar zuwa nan kayan suna da kyauâ€
kwatakwata bai lura da itaba sai a lokacin ya juyo ya kalleta a ransa yana _wani sabon tsari suka samune nasa yara sunayiwa mutane welcome_
suna haÉ—a ido Mairo tayi waje da ido “lahhhh kaineâ€
kayanshi ta shiga shafawa tana É—aga masa gira.
can ta shaa nata kayan tana juyi tana rawar kai “ni ka gani yanzu kaya masu kyau nake sawaâ€
shikan kallonta kawai yake yana tunanin gurin daya santa. dan jikinshi yana bashi ya santa,
saidai ta É—an kwanta masa lumshe ido yayi yana tsusar hot pink lips É—insa faÉ—awansa dai sai kallonsa suke da k'warorin mutanen dake guri
bai buÉ—e idon ba sai da ya tuna da murmushi ya rika fuskarta “ya akyi kikayi kyau haka? waya kawoki nan?â€
saida tayi dariya sannan tace “yaya kuma momi ce tamun kwaliyaâ€
“wane yaya?â€
kamin ta bashi amsa Qasin ya fito ya nufosu fuskarsa É—auke da mamaki.
nunashi Mairo tayi “gama shi nanâ€
kai ya É—aga mata yana wani shu'umin murmushi.
Qasin na karasowa Yarima ya mika masa hannu “thanks to yhu once again My Men for the contractâ€
kallon hannun kawai Qasin yayi fuskarsa babu yabo ba fallasa ba tare daya amsa ba yace “ur welcome the perfect oneâ€
murmushin fuskar Yarima ne ya kara faÉ—aÉ—a,
Qasin bai saje kylashi ba buÉ—ewa Mairo mota “ke shiga mujeâ€
da sauri ta shiga tana É—agawa Yarima hannutana sama byebye.
da wani irin karfi Qasin yaja motar har saida Mairo taji tsoro,
Yarima yayi tsaye yana kallon motar har suka bace masa.
© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:40 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
Â
  *_KHADEEJA CANDY_*
*15*
tunda suka shiga motar Mairo kasa magana tayi saboda tsoro saima rike bel É—in motar da tayi,
shima bai tanka mata ba saida suka kusa isa gida sannan ya soma magana ba tareda ya kalleta ba “ina kika sanshi Maryam?â€
shiru tayi kamar ba zata amsa ba saida ya sake maimai tawa sannan tace “can gida na sanshi harda kuÉ—i yake bani da goribar bunni ba na taba faÉ—a maka wani yaban goriban bunni ba?â€
kai ya É—aga mata “eh ina ya haÉ—u dake?â€
“can gidaâ€
“gida ina?â€
daidai nan suka iso gida yana yin parking ta yinkura zata taji bazata iya buÉ—ewa ta juyo ta kalleshe “buÉ—e min zan fitaâ€
yana kallon kallon fulawoyin gidan yace “sai kin faÉ—a min gurin da kika sanshi?â€
kamar ta fasa kuka tace “bana ce maka can gida baâ€
sai a lokacin ya kalleta “to ai baki min bayani yadda zan gane baâ€
ganin babu sarki sai Allah dole tasa ta faÉ—a masa tun farkon haÉ—uwarsu,
“to tun daga lokacin baki sake ganin shi ba sai yanzu?â€
“eh nidai buÉ—e min na fitaâ€
“to ya akayi ya ganeki?â€
“nidai ba shine ya ganeni ba ni ban sanibaâ€
bai sake ce mata komai ba ya buÉ—e motar ya fita,
ya zagayo gefenta ya buÉ—e mata ta fito da guÉ—u ta nufi parlour. bayan ya rufe motar ya rufa mata baya,
parlour suka tararda momi da gudu Mairo ta faÉ—a jikinta “kinga yaya ya simin mai kyauâ€
dubawa Momi ta shigayi tana yabawa “eyyye yar yayanta duk ke kadai?â€
“eh ni kuma na zaÉ“o kuma mukaje yawoâ€
“amman gaskiya yana ji dake to injin kin masa godiya?â€
“eh na masa ko yaya?â€
kai ya É—aga mata yana murmushi
“eh kinyi bama iyakaâ€
“naji je É—aki ki ajeâ€
“toâ€
tashi tayi tana dariya ta nufi É—akin.
momi ta kalli Qasin tace “magana nake son muyi dakai Qasin mai muhimmanciâ€
agogonsa ya kalla “owk momi amman fa kamar lokacin Sallah yayiâ€
agogon É—akin momi ta kalla “inaga ma an soma sallar wani gurin jeka masallaci kawai nima bari na tashi nayi sallah gobe mayi maganarâ€
‘to’
kawai yace ya tashi ya fice jiki yake baya son maganar duk da bashi da masaniya akan abunda zasu tautauna,
*_washe gari....._*
da safe Qasin bai lek'a part É—in momi ba ya wuce gurin aiki,
bai shigo gidan ba sai dare part É—insa ya fara wucewa saida yayi wanka ya sauke gajiya sannan ya nufo part É—inta,
zaune ya tararda momi tana hamma Mairo na kasan carpet tana bachi Usman da Nura ma duk bachi suke saman kujera,
ta dasu Qasin yayi yana faÉ—a “momi sai ki rika barinsu suna miki bachi saman kujera manya dasu kuma mazaâ€
“ai nasha musu magana har na gajiâ€
masifa Qasin yayits musu da suka farka basu dai ce masa uffan ba daya kare suka tashi kowane ya nufi É—akinsa,
tsaki yaja ya zauna yana faÉ—in “shi yasa Siraj yake burgeni wlh shi halinsa da ban yakeâ€
momi tace “ai Siraj yasan kansa gadai wata nan da take son biye musuâ€
kallon Mairo yayi “gaskiya momi ya kamata asa maryam makaranta dan inaga Gwaggo ba k'arÉ“arta zatayi baâ€
“eh ai inaso ma maka maganar daman jira nake naga yadda zaman zai kasance dan kar asata daga baya tace abata yarta amman kaga yanxu tunda bata tambaya ba ai sai a sakataâ€
“ina gafa Gwaggo fushi ne tayi kinga ai ko waya bata kira duk da son da take yiwa Maryamâ€
“fushi kan ai da ganiâ€
momi na yunkurin tashi Qasin yace “momi wace magana ce kikace zamuyi jiya?â€
da idon bachi momi ta kalleshi “bachi zanyi ba wani magana yanzu yau ma ko leko nan bakayi ba bakayi breakfast ba ka fitaâ€
“eh kirana akayi shiyasa kuma tunda naje nake aiki sai da magriba na samu kainaâ€
“to nidai bachi zanyi kuma ko gobe bani da time dan gobe abbanku zai dawoâ€
tashi yayi yasa hannayensa aljihu yana faÉ—in “Allah kawoshi lafiya ni bari naje na kwantaâ€
“to saida safe ta damun maryam kamin ka wuceâ€
É—aki momi ta nufa tana hamma,
a hankali Qasin ya shiga data ita ganin bata motsaba yasa shi girgiza ta. ciki magagin bachi ta rika faÉ—in “mumi kinga Siraj koâ€
“ba Siraj bane nine tashi kije É—aki ki kwantaâ€
sake komawa tayi bachi haka yasashi data ita tsaye yana girgizawa “ke momi tace kije É—aki ki kwantaâ€
“aa barni ni nan zan kwantaâ€
girgizata ya rikayi da karfi daker ya samu ta buÉ—e ido aiko tana ganin shine ta kara zube masa, dole ya É—auketa ya kaita É—akin yayiwa momi saida safe ya fuce.
*_4:21pm....._*
momi na zaune ita da Siraj suna fira sukaji an buga k'ofa. kofar momi ta kalla tace “waye?â€
shiru akayi ba amsa nan ta kalli Siraj “jeka dubaâ€
tashi yayi ya nufi kofar yana buÉ—ewa yaga Yarima tsaye cikin kananan kaya yasa hannayensa ciki aljihu sai kanshin turare yake fuskarsa na kallon wani gurin.
kasa masa magana Siraj yayi shima kin juyo fuskar yayi ya kalleshi,
juyowa Siraj yayi ya nufi É—akinsa tambayarsa momi ta shiga “lafiya wanene?â€
yana gaf da shiga É—akin yace “gashi nan waje nima ban sanshi baâ€
tashi momi tayi ta nufi kofar, yadda Siraj haka ita ta tararda shi tsaye murmushi momi tayi tace “Yarima ne yau a gidan?â€
sai a lokacin ya juyo ya kalleta shima fuskarsa É—auke da murmushin “nine Momiâ€
“kuma ka tsaya a wajeâ€
“to ai ba amin iso baneâ€
kai momi ta girgiza “Yarima ai naga gidan ba bakonka bane gidan nan ai gidanku ne tunda kai É—ana neâ€
momi na cewa haka ta juyo ta dawo cikin parlour.
kai ya É—aga yana karewa bakin kofar kallo kamar sannan ya taka kafarsa ya shiga cike da takama,
yana zaunawa momi ta dire mishi drinks.
“yau Yarima an tuna damu? kodai wani abun ne ya kawoka?â€
da kanshi ya shiga zuba drinks É—in yana faÉ—in “ziyara ce na kawo muku momiâ€
momi tayi dariya “aiko ka kyauta ya aiki to ya kuma gida?â€
saida ya kurÉ“a drinks É—in kusan so uku sannan yace “Alhamdulillahâ€
kallon parlour yake ta ko ina kamar mai neman wani abu.
can ya kalli momi yace “gaskiya momi Siraj bashi da tarbiyaâ€
ko kaÉ—an momi bata jidaÉ—in maganar ba amman haka ta haÉ—iye tayi murmushi “yayan zamanine sai hakuri kannen nakaâ€
taɓe baki yayi ya juyarda fuskar wani gefe.
momi zatayi magana Mairo ta fito kicin rike da abu a hannu tana faɗin “mumi kinga ni duk na wanke shuwakar kuma ta fita†maganar take tana kallon kujerar da Yarima yake zaune dan bata gane ko wanene ba,
momi tace “thom naji jiki gani nan zuwaâ€
yana juyowa suka hada ido murmushi ya sakar mata.
waje Mairo tayo da ido ta buÉ—e baki ta nufoshi da gudu rike da shiwakar da sauri momi ta tashi tsaye kamin ta rikota ta rumgumeshi har cup É—in dake hannunshi ya faÉ—i.
[11/10, 2:12 PM] ‪+234 806 053 5947‬: . MAIRO ...♡*
*BY*
Â
  *_KHADEEJA CANDY_*
*16*
fisgota momi tayi ta jefar k'asan carpet “lallai Maryam baki da hankali daga ganin mutun baki san inda ya fito ba ki wani rumgumeshi dubi yadda kika bata masa rigaâ€
momi ta kalli yarima “dan Allah Yarima kayi hakuri hankaline bata daâ€
cikin kuka Mairo tace “nida hankalina niba mahaukaciya baceâ€
hannu momi ta É—aga zata É—aketa Yarima ya rik'e “no momi plzâ€
hannu yasa ya É—ago Mairo yana bata hakuri,
kuka Mairo tace yanzu ta fara daman mai nema a duhu balle an yada duk yadda yaso tayi shiru k'iyawa tayi.
fuskarta ya kama da hannayensa biu ya rik'e iya karfinsa ta kasa juya fuskarta shi kawai take kallo.
“yi shiru kinji in kina son na baki apple da abu mai daÉ—iâ€
kai ta É—aga “to na dainaâ€
“good girlâ€
handkerchief ya ciro ya share mata hawaye ya cire mata majina,
juyawa tayi tana hararar momi k'asak'asa ta gefe Yarima yayi murmushi ya rika hannunta ya “muje ki raka niâ€
lakkame masa hannun tayi “ba kace zaka bani abun daÉ—i baâ€
baice mata komai ba ya kalli momi yana murmushi yace “ni ban wuce momi in Qasin yazo ki gaishe shiâ€
fuska a sake momi ta amsa mishi “to zan faÉ—a miki mun gode a gaida gidaâ€
kuÉ—i ya ciro masu É—an dama ya aje mata sannan ya fice rike da hannun Mairo.
motarsa ya nufa harya buÉ—e rike yake da hannunta yana zaunawa ya kama É—ayan hannum ya rike “faÉ—a min miye dan gantakarki da gidan nan?â€
turo masa baki tayi “to ni nasan mi kake nufi neâ€
shiru yayi yana tunanin yadda zai mata ta gane “faÉ—a min momi mamar suwa ce?â€
kai ta É—aga sama “maman yaya da Siraj da Usman da Nura su kenanâ€
“good ke kuma ina mamanki?â€
“mu bamuda mama sai dai Gwaggo tana can gidaâ€
“yauwa to faÉ—a min ya akayi kika zo nan gidan?â€
“da sukaje can suka zo dani nan gidanâ€
“to faÉ—a min Qasin yace miki wani abu da ya gamu tare?â€
“a a baice komai baâ€
banÉ—ir É—in 500 ya ciro ya dora mata saman hannu yana faÉ—in “karki faÉ—awa kowa munyi wannan maganar dake kinjiâ€
da karfi tace “to bazan faɗa ba†tana wani kallon kuɗi tana dariya.
har kasa ta duka tana masa godiya,
kunnenta ya kamo yana faÉ—in “duk kika faÉ—awa wani saina É“ata dake kuma bazan sake miki komai baâ€
É—agowa tayi tana kallonsa “wlh ba zan faÉ—a ba ko za a kasheniâ€
murmushi yayi “yauwa jeki kar moni taga kin daÉ—eâ€
tashi tayi da gudu ta nufi cikin gida.
saida yaga shigewarta sannan yayi ma motarsa key.
kaura suka tashi yi da Qasin daya kunno kai cikin gidan shi kuma yana k'ok'arin fita da sauri Qasin ya bashi hanya dan yasan shi ba jaye mishi zaiyi ba, saida ya fita sannan Qasin ya karaso parking space a ransa yana mamakin abunda ya kawo Yarima yanzu,
da sallama ya shigo parlour momi ta amsa masa Mairo ta nufeshi da gudu tana nuna masa kuÉ—in “yaya ka gani Yarima ya bani duka kuma ni kadaiâ€
kuÉ—in ya karÉ“a ya duba yana kokarin zaunawa yace “momi miya kawoshi yanzu kumaâ€
“jiyara ta kawoshi kuma yace a gaishe kaâ€
“a gaishe ni? yanzu fa kasa bari yayi na shigo saida na kauce masaâ€
momi tace “to ai kasan halin kayan kaâ€
Mairo ta riko hannunsa “yaya kuma harda mumi yaba kuÉ—i masu yawaâ€
lakatar mata hanci yayi “ke wai ba ance miki momi ake cewa ba ki daina cewa mumiâ€
turo baki tayi tana kallon momi “to kuma yaya momi tace mun banida hankaliâ€
kamin Qasin yayi magana momi tace “ai ba kida hankaline Maryamâ€
kara É“ata fuska Mairo tayi “kaji ko?â€
Qasin yayi dariya yace “haba momi Maryam fa nada hankalinta komai na hankali take dan Allah ki daina ce mata mahaukaciâ€
“Allah ni bana mata É—aukar masu hankali kaga abunda tayiwa Yarima yanzu?â€
“mi ta masa?â€
“bata fa sanshi ba daga ganinshi ta tazo a guje ta rumgumeshi ga hannayenta ba kyau har cup É—in hannunshi ya faÉ—iâ€
Qasin ya kalleta “amman ya dakeki ko?â€
momi tace “bai mata komai ba dama zan daketa hanani yayi inajin yan k'aurai ne bisan kai harda fa kuÉ—i ya bataâ€
murmushi Qasin yayi ya shafa kan Mairo.
yace “ya santa ne shiyasaâ€
“ina ya santa?â€
nan ya bata labari kamar yadda Mairo ta faÉ—a masa da kuma haduwar da sukayi Dubai Mall,
Momi tace “shiyasa kika rumgumeshi ni ai nayi mamaki yadda naga ya sakar mata fuska harda share mata hawayeâ€
uhum kawai Qasin yace yana kallon siraj dake saukowa downstairs.
“Maryam faÉ—a min mi Yarima yake ce miki daya rike miki hannu?â€
wani irin É“ata fuska tati ta É—ago tana kallonshi “ni baice min komai ba kawai yace yace yace yana siyomin kayan daÉ—i kuma kuma yana in yana gaida momiâ€
taÉ“e baki yayi “aikin banzaâ€
momi tace “kaga halin nan naks Siraj sam bana sonsa ai kodan girmanka da yayi yaci ake ka gaisheshi amman kakiâ€
“wlh momi matukar bai sauke wannan girman kan dake tare dashi ba to baza mu taÉ“a haÉ—a hanya baâ€
cikinsa momi tayi da faÉ—a “bana fason shashanci Siraj bai girmeka miye abun girman kai a ciki mutun ya tako kafarsa har nan cikin parlour nan ka kasa yi masa magana kaifa da kanka ka buÉ—e masa kofa ina ruwanka da girman kansaâ€
murmushi yayi ya nufi kofa “Sirajâ€
kiran Qasin ne ya juyo dashi “na'am yayaâ€
“nasan bai fika da komai ba amman ka rika masa magana tunda momi bata soâ€
kai É—aga masa ya fice.
candynovels.wordpress.com
© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
Â
  *_KHADEEJA CANDY_*
*17*
tsaki momi taja “da gaskiya Yarima da yace Siraj bashi tarbiyaâ€
kallonta Qasin yayi “shi yace haka?â€
“ehâ€
“shi Yarima har ya iya buÉ—e baki yace Siraj bashi da tarbiyaâ€
momi tace “ai da gaskiyarsa ace murun ya shigo ka kasa masa mana dama fa na tambayeshi cemun yayi baisan ko wanene ba jifaâ€
“haba momi duk abunda Siraj ai baici ace gaban idonki ya furta bashi da tarbiya ba shi har ya isa yayi miki wannan maganar gaban idonki duk fa wadda ya aibanta maka abu kaiya aibanta babu wadda zai buÉ—e baki kaf duniyar nan yace yayan gidan nan basu da tarbiyaâ€
cikin faÉ—a yake magana cike da jin zafin maganar.
momi tace “miye na wani tada jijiyar wuya akan wannan maganarâ€
tashi yayi tsaye yana faÉ—in “hmm iskancin Yarima yayi yawa sai yayi nadamar furta wannan kalaminâ€
tashi ita momi tayi tsaye “Qasin bance kayi rigima da shiba wannan maganar kuma ta wuce karka kuskura ka masa wani akan wannan maganar kaji na faÉ—a makaâ€
tana kawai nan ta nufi upstairs.
Mairo tayi war da ido ta rufe baki “tho momi tayi fushi kuma kaineâ€
murmushi yayi ya shafa kanta ya fice.
saida momi taji ficewarsa sannan ta fito tun kamin ta karasa saukowa Mairo tace “momi yaya yasa kinyi fushi ko?â€
momi ta karasa saukowa tana faÉ—in “a a ni banyi fushi baâ€
“to mi yasa kika masa faÉ—a kuma kika shige É—aki saida ya fice kika fito?â€
basarda maganar momi tayi “muje cikin mu karasa girki kar babanku ya dawo bamu kare baâ€
da sauri ts nufi kicin momi ta rufa mata baya,
*_washe gari....._*
tara saura Qasin ya shigo part É—in momi zaune ya tararda ita tana kallon aljazeera news saida yaÉ—an kalleta sannan ya zaina kusa da ita yana gaisheta,
juyowa tayi ta kalleshi fuskarsata ba yabo ba fallasa bayan ta amsa tace “ga abun breakfast É—inka can inka kare zamuyi maganaâ€
faduwa gabansa ya É—anyi jin harsun karya basu jirashi ba,
su jiki a sanyaye ya kalli momi yace “ke har kun karya ne?â€
“eh yau tea kawai nayi su Usman da Nura sunci nasu sun tafi makarantaâ€
“ke fa momi?â€
“ni tun part É—in babanku na karya nida Siraj maryam ce kawai bata tashi bachi baâ€
bai sake cewa komai ba ya tashi ya nufi dining.
ruwan tea kawai ya zuÉ“o ya dawo kusa da momi ya zauna “momi wace magana ce?â€
shiru momi tayi na É—an wani lokacin kamin ta kalleshi tace “akan maganar matarka neâ€
faduwa gabansa ya É—anyi “momi wani abun ne?â€
“a a ba wani sabon abu bane kawai dai na gaji da dafa maka abinci kana ci,
matarka na kwance tana yadda taga dama da aurenka ace kullum sai kazo nan kaci abinci kaci na rana kaci na dare banda na safe tu na maka wannan lokacin da baka da aure yanzu kan bazan maka gaka baâ€
Qasin jim ya É—anyi sannan ya kalli momi yace “momi bata saba bane kota girka ba wani daÉ—i yake baâ€
“to ta rika girka maka haka nan ko ruwa ne ta rika dafa maka kana sha daga yau dai bazan sake aje maka abinci ba kodai kayiwa kanka abun kunya kaci na kasuwa ko kuma ka cilasta mata ta girka makaâ€
“to momi a bamu maryam saita ri..-â€
hannu momi ta É—aga mishi “dan Allah karka soma na baka maryam ita da bata san zafin gikinta ba ko? kai da ka iya kare mata in anyi magana ka iya kareta ita yar masu kuÉ—i yar boko bata iya komai ba sai hutu ko to nadai faÉ—a maka kuma bazan bada maryam ba in yar aiki zaka É—auko ya rage nakaâ€
kansa na kasa har momi takai aya,
ko kaÉ—an bai jidaÉ—in maganar ba.
    “shikenan momi zan san abun yi shine kawai matsalar?â€
kai ta É—aga mishi tana kallon Mairo dake saukowa sanye da kayan bachi.
murmushi ya sakar mata “maryam kin tashi?â€
“eh momi ina kwana yaya ina kwanaâ€
“lafiya kalau kin tashi lafiya?â€
kusa da momi ta zauna tana “kalau momi yau ba ayi kari ba?â€
“anyi kinga naki can kan diningâ€
zata tashi Qasin yace “momi nafa nema wa Maryam makarantaâ€
sai lokacin momi ta É—an sakar masa fuska “amman kuwa daka kyauta gaskiya a ina?â€
“nan tudun wada Alex international school makarantar nada kyau kuma suna karatu sosaiâ€
wani daÉ—i Mairo taji ta riko hannunshi “yaya da gaske?â€
“da gaske mana ina miki karyane?â€
“a a kuma zanje?â€
“eh yau zamuje su tantanceki in aka shirya komai saiki fara zuwaâ€
tashi tayi ta shiga rawa tana taÉ“i da hannu momi tayi dariya “yau fa abun nema ya samu sai a dage ayi karatu in yaso sai a samu wadda zai rika miki lesin kina É—an karawaâ€
Qasin ya tashi yana faÉ—in “nima haka nake sonyi yadda zatayi ssurin fahimta da kuma islamiya sai a nema mata ta na kusa kidai shirya mata kamin 11 sai muje ayi komaiâ€
“to saika fitoâ€
Mairo ta kalleshi “yanzu zamuje?â€
“a a saikin karya kinci abinciâ€
“to bari nayi sauriâ€
da gudu ta nufi dining shi kuma ya fice yana murmushi,
'''Â Â *Â Â *Â Â *Â Â '''
tunda suka fita sai basu dawo ba sai dare Qasin na rike da hannunta suka shigo parlour.
Siraj ne ya taresu yana zolayar Mairo “eyye yar kauye an sata makaranta eyye aiko za a ga kauyanci kaiâ€
murguda masa baki tayi “eh naji koma minene naji mai k'aton kaiâ€
momi tayi dariya “a a maryam kan yar birni ce ko?â€
nan Mairo ta nufeta “eh momi kuma karantar nada kyau kuma gidan sama ce har sun bani kayan makarata kuma momi wlh suna ta turanci harda yan yaraâ€
Siraj yace “ke kan harki kare bazaki gani komai ba sai shinkafaâ€
É“ats fuska tayi “momi kin jishi ko?â€
momi ta shafi fuskarta “ke kyaleshi xuwazuwa kema zaki iya ai da tambaya akan zama malamiâ€
dariya tayi ta kwanta jikin momi tana rufe ido,
momi tana kallon Qasin tace “an kare komai ko?â€
“eh anyi komai sunce monday zata iya fara zuwa ga uniform nan sun bata na biya kuÉ—in scul bos zata rika zuwa 7:30am tana É—aukar ta in kuma suka tashi zata kawo taâ€
“to Allah ya taimaka abbanku ma ya jidaÉ—i sosaiâ€
murmushi yayi ya tashi “bari naga abbah naje na kwantaâ€
kai momi ta É—aga mishi Mairo ta É—ago tana kallonsa “baza kaci abinci ba?â€
kallon momi yayi dake kallonsa,
can ya É—auke kai yace “bana jin yunwaâ€
ya sun kuyarda kai ya fice.
candynovels.wordpress.com
© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
Â
  *_KHADEEJA CANDY_*
*18*
wasawasa Mairo ta fara karatu a'na mata lesin a gida na makaranta ma Qasin ya sakata.
in kuma lokacin islamiya yayi momi ta tura bata samun zama inba weekend ba da dare ma Siraj ne yake tisa mata ko Usman,
*_2:30pm..._*
schools bus ta sauke Mairo.
da gudu ta shigo parlour tana faÉ—in “momi yauâ€
bata karasa magabar tayi shiru ganin Yarima zaune saman kujera.
ware mata hannaye yayi yana murmushi kaÉ—an kaÉ—an ta karaso tana kallon upstairs.
saida ya mata kiss a goshi sannan ya rumgumeta,
da sauri ta É—ago tana masa magana kamar mai raÉ—a “ina momi?â€
schoolbag É—inta ya shiga cirewa “bata nan nima ban tararda ita baâ€
“tana É—aki ko tana kicinâ€
kai girgiza mata “bata nan ta fitaâ€
“a a bari dai na dubaâ€
kicin ta nufa ta fara duba bata ga kowa ba nan ta nufi ɗakin momi nan ma bata nan haka ta fito ta nufoshi hannu a baki ta ɓata fuska,
hannu ya mika mata yana murmushi “zo nan bana faÉ—a miki bata nan baâ€
ba musu tazo kusa dashi ta zauna hannu yasa ya cire mata takalmin makaranta da safa ya kara janta kimusa dashi ya riko mata fuska,
“pretty gal wani sirrin zanyi dakeâ€
shiru tayi sannan tace “na minene?â€
“bazaki faÉ—awa kowa ba?â€
“wlh Allah ni bazan faÉ—a ba kofa wannan da kace karna faÉ—a har yanzu ban faÉ—awa kowa baâ€
hannunsa yasa yana taÉ“a lips É—inta “da gaske kodai kin faÉ—a?â€
“wlh ban faÉ—a baâ€
“yauwa haka nake so wannan ma karki faÉ—awa kowa kuma karki bari kowa ya gani kinji zan baki abun daÉ—i da kuÉ—i kinjiâ€
“tho amman ka xaka kawo min kayan daÉ—i da gaske harda ice cream da madara kuma kaje dani yawoâ€
hannunsa yasa yana shafa gefen fuskarta “zan miki duk abunda kike so matukar zaki mun abunda na sakiâ€
da sauri tace “zanyi minene?â€
“zan fada miki zaki daiyi ko?â€
war tayi da ido “eh da gudu maâ€
murmushi yayi ya shiga mata chakulkuli tana dariya saida tayi mai isarta ya jata jikinshi ya rumgumeta yana shafa bayanta,
“Maryam....â€
kamar daga sama taji muryar Qasin da sauri ta É—ago tana ganinshi jikinta ya shiga rawa Yarima kuna bai fasa shafa bayanta da yake ba koma É—agowa baiyi ya kalli Qasin ba saima haÉ—e fuska da yayi yana wani tsusar baki da yake na salon iskancin.
tsawa Qasin ya katsa mata “mi kike nan?â€
tashi tayi tsaye cikin rawar murya tace “momi bata nanâ€
“bashi na tambayeki ba?â€
razana tayi sosai tayi bayabaya tana son yin kuka zatayi magana Yarima ya tari numfashinta ba tare daya kalli gurin da Qasin yake ba “ba komai take ba miye matsalarka?â€
kara haÉ—e fuska Qasin yayi yace “I thought da ita nake Maganaâ€
tashi Yarima yayi tsaye yasa hannayensa Aljihu ya nufi Qasin cikin wata tafiya ta isa da tak'ama,
saida ya isa daf da fuskar Qasin ya sakar masa wani shu'umin murmushi yace “don’t put words into my mouth. I have got plenty to sayâ€
wani kallo ya watsa masa tun daga samansa har kasa ya É—auke kai ya fice.
wani kallo Qasin ya bishi dashi cike da jin haushi can ya juyo ya watsama Mairo wata muguwar harara,
aiko jikinta ya kara shiga rawa kamar mai jin sanyi.
cikin tsawa Qasin yace “baki san wanene Yarima ba ko miya tsayarda ke gurinshi?â€
kasa masa magana tayi babu abunda zuciyarta take nuna mata saita shige cikin ɗaki ta kulle karya ɗaketa duk da bai taɓa dukanta ba amman haka zuciyarta take nunama ganin yadda yake harararta,
hankalinta bai kara tashi ba saida taga ya nufo gurinda take,
sakar masa ido tayi saida ya kisa kawowa kusa da ita ta watsa da gudu,
cikin zafin nama ya kaÉ—e mata k'afa ta faÉ—i.
gashinta ya riko Æ´ya tada ita tsaye “ina zaki ba tambayarki nake ba?â€
fashewa tayi da kuka tana rokonsa “dan Allah kayi hakuri ka yafe min bazan kara ba wayyo Gwaggo momiâ€
saida ta kira momi ya tuna da ita da sauri yaja hannunta suka nufi kofa.
tana masa ihu ya buge mata baki yana mata alamar tayi shiru ba shiri ta rufe baki tana son mayarda kukan,