Complete Hausa Novels

Mairo Book 1 Complete Hausa Novel

Reading file:   MAIRO 1.txt

Chapter 2 of 4

part É—insa ya nufa da ita wani emptyroom ya nufa da ita.
saida suka shiga sannan ya sake mata hannu ya kulle ɗakin ya zare bel ɗinsa ya buɗe mata ido “mi ya kaiki kwanta masa a jiki?”
baya tayi tana kuka ta kasa mace masa komai,
matsowa yayi yana faɗin “duk na sake ganin kin rumgumeshi saina miki shegen duka na rufeki cikin ɗakin nan babu wadda ya isa ya ceceki”

sai a lokacin ta soma magana “dan Allah yaya kayi hakuri bazan sake ba wayyo momi”
bel É—in ya É—aga sama kamar zai buga mata wani irin ihu ta saki tayi cikinshi ta rumgume mishi kafafu tana kuka,

“lafiya Qasin miya faru?”
mansura ce take masa tambayar tana jijjigar kofa.
nan Mairo ta koma kiranta “anty mansura zoki ceceni”
ɗagota “aya rufe min baki”
da sauri tasa hannu ta toshe baki tana É—aga masa kai.
juyawa yayi ya buɗe kofar ya dawo parlour bel ɗin dake hannunshi mansura ta rika kallo kamin ta kunno kai cikin ɗakin tana duɓe duɓe,

bata ga komai ba sai Mairo take tsaye rufe da baki tana shawaye.
rikota mansura tayi suka fito gurin Qasin ta nufo tun kamin ta karaso ta jefa masa tambaya “mi kayi mata Qasin?”
ba tare daya kalleta ba yace “mi kike tunanin zanyi mata?”
“ka bani amsa ta kawai Qasin ya zaka saka ta cikin ɗaki harda zare bel zaka ɗaketa mi tayi maka?”
wani dogon tsaki yaja ya tashi fuska a haÉ—e ya fisgi hannun Mairo suka fice.

tunda suka fito Mairo take masa magiyar karya daketa,
yana shigowa parlour ya jefarda ita saman kujera yana kiran momi.
jin shiru yasa ya nufi upstairs. bai jima ba ya fito ya nufi kicin nan ma bai jima ba ya fito ya nufi gurin Mairo dake kuka,

da sauri ta tashi zaune tana share hawaye sai wani numfashi take kamar zai É—auke,
“ina momi?”
“ta fita koda na dawo ban ganta ba Yarima kawai na isko”
cikin rawar muryar kuka take masa maganar,

ido ya tsura mata tayi kasa da kanta hawayen na zuba.

candynovels.wordpress.com

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*
 
    *_KHADEEJA CANDY_*

*19*

ajiyar zuciya ya sauke ya ciro handkerchief ya kama fuskarta yana share mata hawayen “yi hakuri kinji bazan sake ba daina kuka”
kai ta É—aga masa tana wani wahalallen numfashi,
kwantarda ita yayi saman kujera “wanta kiyi bachi?”
harta kwanta sai kuma ta ɗago ta kalleshi “yaya karka faɗawa momi kaji?”
kai ya É—aga mata ya tashi ya fice.

takura kanta tayi saman kujera ta matse guri É—aya kamar wadda aka cilasta tana matsar kwallah har bachi ya É—auke ta,

'''   *   *   *   '''

*_2 hours letter..._*
can cikin bachi taji muryar momi da Siraj,
    da sauri ta tashi tana soshe2.
Momi na kallonta taja wani dogon tsaki “haba Maryam ace mutum kana girma kana cin k'asa kamar ki ace inkin dawo makaranta ba kisan ki cire uniform ba saidai ki samu guri ki kwanta dubi kiga har lokacin islamiya ya wuce kuma baki san ki saka uniform kije ba”

ɓata fuska tayi “to momi ba fita kikayi ba kika barni”
nan momi kasa ce mata komai tayi dan takaici in banda tsakin data sakeyi ta nufi kicin,

momi na shigewa Siraj yaja mata kunne “ba wani daman baki son makaranta yar kauye”
fashe masa tayi kuka ta tashi tana aika masa mugayen duduna tana son huce haushinta akansa.

tsawa momi ta katsa mata “wuce ki cire uniform ɗin nan kiyi wanka kila ma ko abinci baki ciba?”
kai ta É—aga
Momi tace “Allah ya shiryaki maryam wuce kije kiyi wanka duk kika sake yin abunda kikayi yau saina miki shegen duka”
kamar ta fasa kuka ta nufi stairs Siraj na zolayarta,

ta kusan minti 30 toilet É—in tana wasa ruwa saida taji motsin momi a bedroom sannan ta fara wanka,
koda ta fito momi na zaune saman kujera tana duba wasu matirial da atanfofi.
     kallonta kawai Mairo tayi ta nufi waduraf ta ɗauko wata atamfa red colour riga da saket tasa ko mai bata shafa ba ta janyo k'aton hijab ɗin momi tasa ta shimfiɗa carpet ta soma sallah,

momi na kalle da ita saida ta rama azahar sannan tayi la'asar.
bayan ta sallame ta cire hijab É—in ta jefar saman bed ta nufi kusa da momi ta zauna,

    “momi kayan waye?”
kyaleta momi tayi saida ta kare danne2 wayar da take sannan ta kalleta “na siyarwane”
shafa kayan ta shigayi “wlh momi suna da kyau suma siyarwa zakiyi?”
momi bata amsa ba ta kama hannunta ta kira sunanta a natse “Maryam”
dariya tayi “na'am momi”
“magana zamuyi ki bani hankalinki kinji banason kisa wasa ki daina dariya kinji?”

wani haɗe fuska tayi saida tasa momi murmushi sai kace wani cartoon ta wani tada kafaɗu “thom ina jinki?”
a natse  momi ta soma mata magana yadda zata fahimta “maryam ki daina abunda kikeyi kinji ba kyau kinga kara girma kike ba ragewa ba ya kamata ki rika sanin ciyon kanki ki daina abunda kike”

“tho ni kuma momi mi nayi?”
ajiyar zuciya momi ta sauke “yanzu fa saida kika rama azahar sannan kikayi la'asar kina ganin kin kyauta?”
kai ta girgiza alamar a a momi tace “tho kingani wadda fa yake haɗa salloli azaba ake masa ba kyau ki daina kinji?”
nan ta ɗaga kai “kuma kinga in kika dawo makaranta maryam basai nace ki cire uniform ba ki rika cirewa duk abunda kika san aikin kine ki rikayi basai nace kiyi ba kinji? ki zama yarinyar kirki”
wata dariya ta rikayi tana kallon momi tana tsutsar leɓenta na kasa,
can dai ta kawarda fuska tace “tho momi na gane koma minene kike nufi”
shafata momi tayi “yauwa yata haka nake so kuma ki dage ki rika karatu ba wasa banda faɗa ko jan magana kinji?”
nan ma kan ta ɗaga ta tashi tsaye “nidai bari naje naci abincin yunwa nake ji”
bata ko tsaya jiran abunda momi za taceba ta fice.

tana saukowa downstairs Qasin na shigowa.
suna haɗa ido ta juya da sauri zata koma hannu yakai ya rikota “ya haka ina zaki?”
upstairs ta rika nunawa “ɗaki zan kwanta ne”
murmushi yayi yaja ta suka nufi kujera bayan ya zauna ya zaunarda ita “baki san ba kyau bachin maraice ba?”
“eh ni ban saniba”
“tho ba kyau ki daina karki sake bachi da maraice”
“tho na daina bazan sake ba”
idonta a kasa take amsa masa dan tsoron kallonsa take.
lura da hakan yasa ya sakar mata hannu yace “tsorona kike ko maryam?”
shiru tayi tana wasa da hannayenta fuskarta ya riko “faɗa min mana tsorona kike ne?”
ɓata fuska tayi ta soma magana “nidai bana son duka in mutun yana dukana tsoronsa nake sosai”

murmushi yayi “tho na daina bazan sake ba ai ban dakekiba”
“eh amman ai kaso ka dakeni dan dai anty mansura tazo ne ka kyaleni”
tana maganar tana wani langwashe langwashen kai da turo baki,

dariya yayi tace “ai ba mansura ce ta ceceki ba daman ba dukanki zanyi ba”
harara ta watsa mishi “kai wlh karya ne tho miyasa ka ɗaga dankon zaka buga min?”
“minene sanki?”
rufe ido tayi tace “wannan wadda kaso ka dakeni dashi”
“bel?”
kai ta ɗaga tana kara matse ido dariya yayi yace “ki yarda maryam bazan iya dukanki ba kawai dai horaki nayi”
kwanta masa tayi saman jiki tana dariya,

“wlh karya ne dukana kaso kayi”
kunnenta riko ya rika murɗawa “ni nake karya?”
dariya ta rikayi tana faɗin “na daina ba kaiba”
haka ya rika wasa da ita soma masa kuka sannan ya saketa ta nufi kicin shi kuma ya fice.

washe gari tunda safe Mairo ta shirya kanta duk abunda momi ta saba mata ita tayiwa kanta,
sosai momi ta jidaÉ—i da schoolbus É—insu tazo har bakin gate momi ta rakata ta buÉ—e mata motar ta shiga.
hannu ta rika É—agoma momi har suka fice,

*_2:30pm..._*
ta shigo gidan da sallama ta shiga parlour momi ta amsa mata da fa'ah “wa'alaikissalam yar mama an dawo?”
kai ta É—aga mata tana cire takalmin makaranta,

daga gurin da take zaune ta jefasu gurin da aka tana da dan ajeye takalmin tana faɗin “momi yau Yarima ya kai mana ziyara a makaranta”
Usman dake zaune kisa da momi yace “da gaske?”
“eh wlh harda chocolate ya raba mana”
momi tace “gurinki yaje ko makaranta gaba ɗaya”
“a a makaranta dai kofa jiya yaje kuma yazo gidan na-”
shiru tayi ta kasa karasawa sai rabon ido take. momi tace “jiya ya zo nan? bayan fitana ko?”
wata dariya tayi “ke momi na tuna mafarkine nayi ba gaske bane”
tashi tayi da sauri ta nufi upstairs “bari naje nayi sallah nayi shirin islamiya”
  tanayi tana waigo momi harta shige.
momi kan daÉ—ine ya isheta tana gani ta fara samun kan Mairo.

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*
 
    *_KHADEEJA CANDY_*

*20*

washe gari ma Mairo ita ta shirya ma kanta komai bayan ta saka safa ta riko schoolbag É—inta ta nufo downstairs.

da dariya ta sarasa saukowa ta rumgume Qasin dake zaune saman kujera rike da laptop,
aje laptop ɗin yayi yana murmushi ya zaunar da ita saman kafafunsa “maryam har kin shirya?”
ɗagowa tayi tana murmushi “eh kuma ni na shirya kaina”
saukar da ita yayi jin motar makarantarsu ya karɓi jikar hannunta yasa mata,
da sauri momi ta fito kicin rike da kular abincinta tana faɗin “oya karɓi ga abincin ki naji motar ku”
da gudu ta karɓa ta nufi gurin da takalminta suke ta saka harta fice sai kuma ta dawo ta tsaya bakin kofa “momi ba zaki bani komai ba?”
“mi zan baki?”
shiru tayi tana bugun kofar parlour.
hannu Qasin yasa aljihu yana cirowa ya mika mata É—ari biyar,
wata dariya ta saki jikina na rawa ta karɓa tana masa godiya “na gode yaya” kai ya ɗaga mata ta fice da gudu.

ɓata fuska momi tayi tace “Qasin bana so karka sake ka ɗauki kuɗi har ɗari 500 ka bata”
hannu ya ɗaga “shi kenan na daina amman naga kamar bada yawa bane”
cikin faɗa momi tace “tho na dai faɗa maka bana so duk kyautar da ita karta wuce 100 zuwa k'asa”
tana kaiwa nan ta nufi kicin,
da sauri Qasin yace “owk momi yi hakuri ai ya wuce zo kiga wani abu?”
yi tayi kamar bata jishi ba shige kicin É—in saida ta kare abunda take sannan ta fito.
har lokacin yana zaune Æ´yana danne2 sa,
kujerar dake kusa dashi ta zauna “gani ya akayi?”
ɗagowa yayi ya kalleta “momi ɗan ruwan tea ma bazan samu ba?”
taɓe baki momi tayi “au daman jiran kake na ɗauko maka breakfast? inma shine dalilin zamanka nan tho tashi ka koma part ɗinka dan kasan munyi ba'ada dakai tun farko”
dariya yayi “a'a momi bashine ba abu zan nuna miki”
laptop ɗin ya ɗauko ya ɗora saman jikinta “kinga wani design ɗin wata kwangila da za'ah ba kanfaninmu”
duba momi ta shigayi tana faɗin “amman kan abun da girma sosai mi za a gina haka?”
“wani kanfani suke so a gina musu na sarrafa motoci _JAMES GLOBAL AUTOMOBILES_ sunan kanfanin shine na farko da zai kafa branch a Nigeria”
momi tace “aiko dasun kyauta muma mu ɗan samu cigaba kuma matasan mu su samu aiki”
“sosai ma momi kinga in aka ginashi mutun kusan ɗari biyar zasuyi aiki karkashin su kinga ai an ɗan rage kuma kanfanin sun iya motoci ana son motocinsu sosai sune zakiga J.G.A mutunin ɗan amerika ne”
momi tace “amman naji daɗi to kai zaka gina musu gurin ne?”
“tho haka ake tunani amman dai ba ni kaɗai bane mu uku aka kaimusu zasu zaɓa ne saisu bada kwangilar ga wadda suka yarda da aikinsa amman dai mutane da yawa ni suke cewa saboda kanfanin fitaccen kanfanine kuma muna aiki babu kissa ciki”
murmushi momi tayi “tho ai haka ake so Allah ya taimaka yasa ka samu”
“amin momi dan gaskiya zamu samu kuɗi masu yawa”
“to Allah ya yarda ya taimaka”
“amin”

tashi yayi rike da laptop ɗin yana kallon “bari naje can na karya”
kai momi ta ɗaga mishi “da yafi”
murmushi yayi ya fice.

*_7pm..._*
Mairo na zaune parlour kasan carpet ita da Siraj yana duba littafanta na makaranta sai zolayarta yake tana masa kuka yana sa ta karanta gurinda bata iyaba yayi mata dariya ita kuma ta buga masa fillo. suna haka sukaji an taɓa kofa duk juyawa sukayi suna kallon kofar,

cike da takama Yarima ya shigo ba tare da yayi sallama ba ya nufo gurinda suke,
wani irin haɗe fuska Siraj yayi kamar bai taɓa dariya ba,
wannan karon Mairo batayi unkurin tarboshi ba ido kawai ta sakar masa tana dariya.
da murmushi ya karaso kusa da ita tashi Siraj yayi tsaye da niyar tafiya tunowa da magagganun momi yasa ya kalli yarima yace “sannu da zuwa”

banza ya masa yana tsutsar lips É—insa.
juyawa Siraj yayi cike da bachin rai ya fice,
            hannu Mairo ya riko yana murmushi ya nufi kujera suka zauna tare.
     
kallonsa tayi tace “ba kaji Siraj yana mska magana ba?”
lakatar mata hanci yayi “na jishi bana jin amsa masa ne”
murmushi tayi gyaÉ—a masa kai,
wasa ya shigayi da hannayensa yana faÉ—in
“pretty gal ya maranta?”

“lafiya kalau”

“ina momi?”

“tana ɗaki na kirata?”

hannu yasa yana taɓa lips ɗinta “a a karki kirata”
saida ya ɗaga kansa ya kalli upstairs sannan ya kalleta yace “gurinki nazo kinsan munyi dake zan saki abu ko?”
kai ta ɗaga “eh kuma kace zaka bani kuɗi kuna kace zak-”
rufe mata baki yayi da sauri jin motse saukowar mutun downstairs,
saida yayi mata alama da tayi shiru sannan ya juya da murnushi yana kallon momi.
“Yarima yanzu ake tafe?”
“eh momi ya wunin gidan?”
taka kokarin zaunawa tace “lafiya kalau maryam baki ɗauko masa abun sha ba?”

war tayi da ido tace “lahh mantawa nayi bari na ɗauko”
tana sauka ya riko hannunta ya tashi tsaye “a a momi barshi kawai yanzu zan wuce”
“da wuri haka?”
“eh kinga an kira sallar isha kuma daman biyowa kawai nayi naga Maryam”
da ɗan mamaki momi tace “owk tho a gaida gida”
hannu yasa aljihu ya ciro dubu 20 ya aje mata “ayi hakuri da wannan momi”
murmushi momi tayi “Yarima kenan Allah dai ya amfana”
baice komai ba yaja hannun Maryam suka fice,

motarsa ya buÉ—e mata ta shiga bayan ya rufe ya zagayo shima ya shiga.
“ina zamu?”
tambayar data fara jefa masa kenan tana kallonshi,

baice mata komai ba yasa hannu baya ya ɗauko laptop ya ɗora mata saman jiki “kinga wannan abun?”
“eh”
“kin taɓa ganinta?”
“eh sunanta kwanfuta”
mirmushin jindaɗi yayi “good wa kika taɓa gani da irinta?”
“malamin makarantarmu da yaya”
“tho kinsan mi nake ao dake?”
kai ta girgiza “a a”
“ta yaya nake son ki ɗauko min”

da sauri tayi waje da ido ta rufe baki “kaikai nidai babu ruwana baya so fa ina taɓa mishi kaya”
“ke mayarwa zanyi kawai inason na arane na ɗanyi wani abu sai na baki ki mayar”
lake kafaɗa tayi “a a gaskiya saidai nace ya aro maka”
haɗe mata fuska yayi “a a karki kuskura kice masa haka bazai bayar ba kuma inma yaji dukanki zaiyi kuma nima na ɓata dake”

hannu yasa ya ɗauko wata leda dake bayan ya mika mata “kinga kayan daɗi nan na siyo miki kuma gobe zan karo miki wasu kullum zan rika siyo miki kuma na baki kuɗi amman fa sai in kin aikata abunda nace”

shiru tayi tana tunani kamar ta fasa kuka ta kalleshi tace “amman inna ɗauko cewa zaiyi mi zanyi da ita”
“no ai bazaki bari ya gani ba a boye zaki ɗauko karki yarda kowa ya gani koda kuda ne”
“tho inna ɗauko ina zan ɓoye?”
shiru yayi yana kallonta kamin yace

“ke bakisan gurin da zaki ɓoye ba?”

“eh duk gurinda zan ɓoye gani za ayi”

“tho ki kaɗa rijiya”
“kai rijiya?”

“eh koki jefar wani gurin innazo sai ki faɗamin na ɗauko”

“ba zai lalace ba?”

“ba zaiyi komai ba kinji”
kai ta ɗaga mishi sosai yaji daɗi ya shafa kanta “good pretty gal”
“amman mi zakayi da ita”
idonsa ya shiga susa kamar wadda abu ya faɗawa “am zan ɗan ɗauki wani abune a ciki na cofa sai na baki ki mayar kinga bazai gane ba ko?”
da mirmushi ya karasa maganar itama tayi masa murmishin karfin hali,
kuɗi ya ciro masu yawa ya mika mata “gashi ki siye duk abunda kike so amman kinsan bazaki faɗawa kowa munyi wannan maganar dake ba ko”
“eh bazan faɗa ba”
“good kuma tsakanin gobe sa jibi nake son ki ɗauko min ita”
kai ta É—aga mishi,

daga nan ya mika hannu ya buÉ—e mata motar shima ya buÉ—e suka fito tare.
Qasin na tsaye bakin kofa yana kallonsu yana rumgume da hannayensa fuskarsa a haÉ—e,
faɗuwa gaban Mairo yayi da sauri ta juya ta riko hannun Yarima ta soma kuka “nidai bazan iya zuwa ba ga yaya can yana kallona”
mirmushi yayi yaja hannunta suka nufi kofar parlour.

har suka isa Yarima bai kalli gefen da Qasin yake ba,
ita kadaice ke masa kallon tsoro jikinta har wani ɓari yake, da kansa ya buɗe mata kofar data shiga yayi mata byebye yana murmushi hannu itama ta ɗago mishi sannan ya rufe kofar,

yana juyowa Qasin yace “ka bani kunya ka kuma zubar da girmaka momi bata taɓa yiwa yayanta gurɓatacciyar tarbiya ba kuma bana tunanin za'a samu matsala a maryam dan haka ta banbanta da sauran matan da kake gani.
maryam karamar yarinya ce in zakayi sama kayi kasa ba za ah aura maka itaba balle baka daman lalata mata rayuwa dan haka banga abunda zai haɗaku ba”
yana kaiwa nan ya juya ya shigewarsa parlour.

kasa tafiya Yarima yayi sosai maganganun suka ɓata masa rai sai wani busar da iskar baki yake,
_É—an iskane ni Qasin na karshe har yanzu baka gama sanina ba zan nuna masa true color na_
a zuci yake wannan zancen yana wani kashe ido.

candynovels.wordpress.com
[11/10, 2:12 PM] ‪+234 806 053 5947‬: © *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

_na gode Sosai da k'auna yan *perfect women's*👌🏻 Allah barmu tare 😍 kaina a kasa maman husna & mrs tijjani much love😘_

*21*

Mairo na zaune kusa da momi tana nuna mata kuÉ—in,
Qasin na shigowa ta tashi tsaye da sauri tana masa kallon tsoro gabanta sai faÉ—uwa yake ganin yadda ya haÉ—e fuska,

yana karasowa kusa da ita ya fisgota ya jefar kasan carpet ya cire bel É—insa ya watsa mata,
wani ihu mairo ta saki ta durkushe guri É—aya,
da sauri momi ta tashi ta rik'e "lafiya Qasin miya faru?"
kallon momi yayi rai a bace yace "bata jin magana ne momi so nake nayi mata dukan da in taga Yarima ko kallonsa ba zata sake yiba"
bel ɗin momi ta karɓe "miya faru wani abu tayiwa Yarima?"
"ba wani abu tayi masa ba shi daine yake son yayi mata illah"
kallon mamaki momi tayi masa "wani abun yayi mata ne?"

"momi kinfi kowa sanin halin Yarima ba mutunin kirki bane taya zaki rika barinshi yana keɓanta da maryam?"
sai a lsokacin moni ta gane inda ya dosa kallon maryam "Ke Tashi Kije É—aki"
tashi maryam tayi ta gudu ta nufi stairs tana kuka.

saida ta shige sannan momi ta kalli Qasin tace "mi yasa kake da zafin zuciya haka ne Qasin?"
"ba zafin zuciya bane momi ina tsoron abunda zaije ya dawo ne kinfi kowa sanin halin Yarima saboda mi zaki barta ta keɓanta dashi ba ɗan'uwanta bane ba wani nata bane hasalima bashida wata alaka da ita ta dalilin mi zai rika bata kuɗi haka masu yawa kuma ki zuba ido kina kallo keda kanki kika ce bakison ina bata kuɗi mai yawa saboda karta lalace to akanmi zaki barta da Yarima?"

cikin faÉ—a yake maganar har jijiyar wuyansa na tashi,
kai momi ta girgiza tace "bana tunanin haka Qasin nasan waye Yarima"
wani murmushin jin haishi Qasin yayi ya fice,

a hankali momi ta kai zaune saman kujera tana nazarin kalamansa.
sai a lokacin wani tunanin ya soma bijiro mata,
ta kusan awa biu a haka sannan ta tashi ta shiga É—aki.

*_washe gari..._*
Qasin na zaune garden ya wani aiki a computer yaji an dafashi,
a hankali ya É—ago suka haÉ—a ido da mairo da gefen fuskarsa ya kunbure,
murmishi ta É—an sakar masa tace "yaya"
shima murmushin yayi mata yaja mata kujera ta zauna a kusa dashi "maryam kin tashi?"
"eh tun É—azu"
"eh kaima kaci?"
kai ya ɗaga mata yana yana taɓa gurin daya kunɓurar mata "dukan da nayi miki jiya ne?"
taɓa gurin tayi "eh shine yaya karkayi fushi dani"
laptop É—insa ya matsar gefe ya kara matso da kujera kusa da ita "ba zanyi fushi dake ba maryam dukan jiya ma rai nane ya bace kiyi hakuri kinji?"

hawaye ne suka zuɓo mata "yaya ni banma ce ya bani kuɗi ba shine ya bani kuma bance ya sani mutarshi ba shine ya sani"
cikin kuka ta karasa maganar,

tausayinta Qasin yaji duk sai yaji ba daÉ—i hannunsa yasa yana share mata hawayen "ya isa daina kukan haka kinji bazan sake dukanki ba"
É—agowa tayi ta kalleshi "kayi alk'awari?"
"eh nayi"
saida taja majina tace "malamin mu yace ba kyau saɓa alk'awari"

dariya yayi yace "maryam kwan wayo na yarda amman sai in kin min alkawari nima kin yarda"
"eh minene?"
ido ya tsura mata yayi shiru yana mata murmushi,

ganin haka yasa tace "yaya lafiya?"
ajiyar zuciya ya sauke yace "kalau kesan mi nake so dake?"
"a a saika faÉ—a"
"so nake karki sake kula Yarima duk abunda ya baki karki sake karɓa"
shiru tayi "koda kuÉ—i ne yaya"
"eh koma minene"
kai ta É—aga mishi "tho bazan sake ba"
murmushi yayi ya rumgumeta yana faÉ—in "yauwa maryam É—ina"

"yaya mi yasa baka shiri da Yarima?"
daidai kunnensa tayi masa tambayar.
É—agota yayi yana murmushi ya tashi ya rufe laptop É—in ya mika mata "jeki ki kaimun É—aki"
tashi tayi tsaye jikinta na rawa ta karɓi laptop ɗin tana kallonsa,
juyawa yayi ya nufi part É—in momi ya barta nan tsaye.

laptop É—in ta tsurawa ido tana shafawa maganganun Yarima suka rika mata yawo akai tunawa zuciyarta ta shiga mata zance biu akai akai takan kai duba gurin rijiyar dake gefen gurin sai faman haÉ—eye yawu take,
dukan da Qasin yayi matane ya faÉ—o mata rai nan da nan sai tsoro ya shigeta,
da sauri ta juya ta nufi part É—inshi.

''' ***************** '''
*_6:15pm..._*
Qasin ya shigo part É—in momi da sallama yana murmushi,
Nura da Usman suka amsa masa Maryam kuma ta tashi da gudu ta tarɓoshi "oyoyo yaya"
shafa kanta yayi "maryam oyoyo bita kikeyi?"
sakinshi tayi tana faÉ—in "eh kuma yaya iya"
zaunawa yayi yana sauke gajiya "yayi kyau haka nake so ina momi?"
"tana É—aki bari na kirata"
da gudu ta nufi É—akin tana kwalawa momi kira,

tare suka fito tana rike da hannun Mairo da murmushi ta zauna tana kallon Qasin "injin anyi nasara?"
dariya yayi yace "anyi momi saidai fa akwai yar matsala"
nan da nan yanayin fuskar momi ya chanja "wace irin matsala kuma?"
"wai sunce zasu min interview gobe bance wadda suka min yau"
"daman abun harda interview akeyi sai kace É—aukar aiki"
ajiyar zuciya ya sauke "nima abunda yaban mamaki kenan momi kuma kinsan wani abu?"
"a a minene?"
"Yarima ne zai min interview É—in kuma wai sai nazo da laptop É—ina sunga irin aikin da nayi"

lumshe ido momi tayi "oh ni har ka faÉ—armun da gaba wannan tho ai ba wani abun É—aga hankali bane sai kaje da ita ka nuna musu kuma duk abunda suka tambayeka ka basu amsa"
"momi bakiji mi nace ba Yarima fa zai mun"
"tho minene a ciki ai baka kirsa cikin aikinka ko kaÉ—an bana fargaba akan aikin da za'ayi maka"
"momi tsoron nake kar Yarima yayimin wani abun kinsan halinsa"
"karka taɓa saka wannan a ranka ka yarda da kanka Qasin karka bari damar nan ta wuce ka kaifa kmda kanka ka faɗa min kuɗine masu yawa"
kai ya É—aga mata yana kallon maryam,

Usman yace "yaya ya akayi Yarima ya zama shine zaiyi maka interview É—in"
Qasin yace "nima ban saniba amman dai kasan yana hulda da motocin kasashen waje kuma kasan tunda Illustrator ne inajin shiyasa"
"Allah dai ya baka nasara yaya"
duk suka amsa da 'amin'
sun É—an jima suna fira saida aka kira sallar magriba sannan kowannensu ya tashi momi da maryam kuma suka nufi É—aki dan sallah.

*_Monday @10:30am..._*
cikin nasara akayiwa Qasin interview duk yadda Yarima yaso ya samu matsala Allah bai yarda ba duk abubuwan da suka bukata saida ya nuna masu Yarima yayi mamaki sosai ganin laptop É—in,
bayan fitarsa akayiwa mutun 3 duk basuji sun gamsu dasu ba kamar yadda sukaji da Qasin sun daÉ—e suna ttaunawa kamin su yanke hukunci sosai Yarima yaso a bawa wani ba Qasin ba amman suka ki yarda dan sun lura da gwarewarsa nesa ba kusa ba,

*_2 hours letter..._*
suka aika aka kira Qasin daya shigo suka sake yi masa wasu tambayoyi,
ya amsa musu fiye da yadda suke tunani nan suka kara jindaÉ—i Yarima suka bawa files É—in cike da jin haushi ya mika masa,
Qasin na murmushi ya karɓa yayi sign fuskarsa a sake ya mikawaƳYarima files ɗin yana murmushi yace "thank you"
murmushi Yarima wadda bai kai zuci ba "ur welcome Men"
hannu suka rika mikawa Qasin sunna masa congrats,

'''**********************'''
cike da jindaÉ—i Qasin ya shigo gida kai tsaye part É—in momi ya nufa tun daga sallamarsa ta gane haka bata masa magana ba saida ya zauna "an daiyi nasara ko?"
dariya yayi ya mika mata jakar dake hannunshi "anyi momi sun bani"
ba karamin daÉ—i momi taji ba saida ta gama duba laptop É—in sannan tayi ma Allah godiya "Alhamdulillah Allah mun gode maka haka nake so Alhamdulillah Yarima yaje?"
"eh tare dashi akayi komai shima ya bani files É—in nasa hannu"

"masha Allah Allah ya tayaka riko"
"amin momi kinga fa ko breakfast banyi ba"
maganar yake yana wani sosa kai,
taɓe baki momi tayi tace "zakaci albakacin wannan ranar zan baka na yau"
murmushi yayi "aiko momi da kin kyauta"
tashi yayi ya nufi dining yana faÉ—in "yau momi gidan sit ba kowa"
"to ai kasan yau monday wazai zauna nima anjima kaÉ—an fita zanyi"
"tho bari na daukeki dan nima fitar zanyi"
taahi momi tayi ta nufi upstairs,
"bari na shirya wani abin kamin ka kare"
"owk momi"

kujera yaja ya zauna ya hau cin abincin har wani sauri yake yana lumshe ido raban da yaci abinci mai daÉ—i haka har ya manta kullum cikin siyen takeaway yake gashi abinci inba na momi ba baya jindaÉ—inshi,

kusan plate biu yaci yasha zoɓon da momi ta haɗa ya tashi yana hamdallah,
part É—insa ya nufa bai daÉ—e ba ya fito ya sake nufo part É—in momi bayan ya É—an watsa ruwa ya chanja kaya, zaune ya tararda ita tana jiranshi,
"momi har kin shirya?"
"eh so nake nayi saurin dawowa kar maryam ta dawo gidan ba kowa"
agogon hannunsa ya duba "gashi ko sun kisa dan 12 ta kusa"
tashi momi tayi ya É—aukar mata jekar dake gabanta suka fice.

*_2:34pm..._*
Mairo ta shigo gida kamar ta fasa kuka ta nufo parlour dan tun gate maigadi ya faÉ—a mata momi bata nan,
jefa tayi da jakarta tsakiyar parlour ta nufi upstairs,
tana shiga ta cire uniform É—inta ta É—auki tawul ta É—aura ta shiga bathroom wanka tayi tare da alwala sannan ta fito sai wani tureturen baki take tana matsar kwallah,
wadurof ta nufa tana buÉ—ewa taji an kira amsawa tayi duk da bata san mai kiran ba ta rufe wadurof É—in da sauri ta nufi kofa.

candynovels.wordpress.com

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*22*

da sauri ta sauko stairs tana rabon ido dan bata ga kowa ba har ta nufi kofa taji an rikota,
juyowa tayi da sauri suka haÉ—a ido da Yarima sosai ta razana ganin fuskarsa a haÉ—e gashi batayi tsamaninsa,
kokuwa ta shigayi dàshi tana son kwace kanta jikinta har wani rawa yake.
iya karfinsa yayi wurgi da ita saman kujera cikin jar fuska yace "mi yasa kika karya alkawarin?"
tashi tayi zaune tana kuka tace "yi hakuri dan Allah karka dakeni"
risinawa ya shafa gefen fuskarta "baki son na dake ki miyasa kika ki aikata abunda na saki? mi yasa maryam?"
shiru tayi tana kallonsa hawaye na mata zuba.
hannu yasa yana share mata wayarsa tayi ringing,
saida ta kusan katsewa sannan ya É—auka banji mi akace masa ba saidai naji nace "Gret mun faÉ—i sai dai mu tari gaba... owk sai na ganka"
yana aje wayar ya tashi tsaye yana tafiya bayabaya fuskarsa É—auki ke da murmushi saida ya kai kofa sannan ya juya ya fice,

ajiyar zuciya ta sauke ta kawanta saman kujera dafe da zuciya.
ta kusan minti 20 a haka sannan ta tashi ta nufi É—aki,
cikin kankanen lokacin tayi shirin islamiya ta É—auki littafanta ta nufo downstairs.

cike da tsoro ta sauko sai leke2 take har ta samu ta fita parlour,
har ta isa harabar gidan bata daina jin tsoro tana kisan isa gate motarsu momi ta kunno kai,
Qasin nayin parking mairo ta nufi momi ta rumgumeta idonta cike da hawaye.
murmushi momi tayi ta rumgumeta "maryam kin dawo?"
kamar tayi kuka tace "eh momi ki daina fita kina barina"
"tho na daina maryam jeki islamiyar karkiyi latti"
kin É—agowa tayi saida taji an ja mata kunne sannan ta juyo da fuskar ta kalli Qasin,
murmushi ya sakar mata ya buÉ—e mata mota "shiga na kaiki"
ba musu ta shiga bayan ya rufe ya shiga mazaunin direba yayi ribas suka juya momi kuma ta nufi cikin gida.

tukin yake yana kallonta ita kuma kanta na kasa sai murza yatsunta take tana haÉ—iyar yawu,
A'hankali ya rage gudun da yake ganin haka yasa ta É—ago ta kalleshi suna haÉ—a ido yace "mi yake damunki maryam?"
shiru ta É—anyi sannan tace "babu komai"
Qasin yace "kinsan ba kyau karya ko?"
kai ta É—aga mishi
"tho faÉ—a min miya ke damunki?"
"nace maka babu komai"
"Yarima yazo?"
batace masa komai ba har yayi parking daidai gate É—in makarantar saida ta buÉ—e motar zata fita sannan tace "eh yazo"
da sauri ta rufo motar ta nufi cikin makarantar,

saida ya daina hangota sannan yayima motar key da sakesake ya iso gida yana tuna yadda mairo ta rumgume momi,
har ya nufi part É—inshi wani tunanin ya dawo dashi gurin maigadi ya soma masa tambayoyi bayan sun gaisa "Sadiqu bayan fitarmu waya shigo?"
"babu wadda ya shigo inba Yarima ba"
"ya jima nan?"
"a'a bai jimaba ya fita"
kai Qasin ya É—aga mishi "owk na goÉ—e"
ya juyo ya nufi part É—in momi,
da sallama ya shigo saidai bai samu mai amsa masa ba dan babu kowa parlour.
guri ya samu ya zauna yana sauke ajiyar zuciya sai kallon parlour yake ta ko ina kamar wani bako,
ya daÉ—e haka sannan ya tashi ya nufi part É—inshi.

*_washe gari..._*
*7am* Qasin ya shigo part É—in momi,
momi na kicin tana aiki taji shigowar mutum hakan yasa ta nufo parlour,
Qasin na ganinta yace "an tashi lafiya momi?"
"lafiya kalau"
"masha Allah maryam tqa tashi?"
da É—an mamaki momi tace "eh tana ciki shirin makaranta take yi lafiya dai"
murmushi yayi ya nufi stairs "lafiya kalau momi abu zan bata"

a hankali ya tura kofar ya shiga tana zaune tana saka safa tana ganinshi ta saki murmushi "yaya ina kwana?"
"lafiya kalau maryam kin tashi lafiya?"
"lafiya kalau"
zaunawa yayi kusa da ita yana faÉ—in "shirin makaranta kikeyi?"
"eh"
"yayi kyau"
kafarta É—aya rika yana saka mata safar "maryam jiya da Yarima yazo mi yayi miki?"
ɓata fuska tayi "nidai ba nace maka bai min komai ba bai min komai ba"
"tho miya yace miki?"
"nidai baice komai ba kawai yace gurin momi yazo kuma bata nan harda kuɗi ya bani amman ban karɓa ba sai yayi tafiyarsa"
tana maganar tana wani ɓalɓal da ido karya gano karya take.
daɗi Qasin yaji sosai da kanshi ya saka mata jikar makarantar yana murmushi yace "yauwa maryam daɗina dake jin magana kin kyauta da baki karɓi kuɗin nan ba"
rufe ido tayi ta fashe da dariya da gudu tabar É—akin,

'''***********************'''
tafiya yake yana shewa (fito) hannayennsa na lakkame a bayansa.
duk gurin da yabi sai sun gaisheshi jiki na rawa amman ko kulasu ba yayi bare ya amsa gaisuwar sai wani rangashi yake har ya iso maidaidaicin parlour,

guri ya samu ya zauna bayan ya gaisheta ya É—ora kafa É—aya saman É—aya yana wani lumshe ido,
tsakin da yaji tayi ne ya sashi É—ago kai ya kalleta yana kalkatar dariya "haushi nake baki ko hajiya?"
taɓe baki tayi "Yusuf na gaji da maka magana na gaji da saka maka ido haba Yusuf sai kace wani yaro karami kullum ayita faɗar abu ɗaya ana maimai tawa"

rufe baki yayi kamar wani mai jin hamma "sorry hajiya komai ya kusa zuwa karshe na samu wadda nake so jira kawai nake ta karasa girma"
kallon rashin fahimta Haiyar tayi mishi "ban gane ba?"
murmushi yayi "na samu wadda nake so saidai karamace amman idona na kanta data girma zan É—auke abunta"
maganar yake yana wani ɗaga hannu sama yana taɓe baki kamar wadda yasha wani abu,
kai Hajiya ta girgiza "Yusuf lafiyarka kuwa ban sanka da wannan halin ba"
dariya yayi yace "nayi miki kama da yan shaye2 ko kinfi kowa sanin bana shaye2"
"tho mi yasaka cikin wannan halin?"
"tsabar bakin ciki ne kawai"
"bakinciki kamar ya?"
kafaÉ—unsa ya É—aga ya tashi tsaye yana faÉ—in "barshi kawai hajiya kona faÉ—a miki bashi da rana"
cikin rashin jindaÉ—i tace "Allah ya sauwake"
dariya yayi yace "amin bari naje ciki"
kofa ya nufa yana saida ya kusa fita sai kuma ya juyo ya kalleta yace "wlh hajiya bana shaye2 kuma ba wani abun na shaba karki saka wannan a ranki kinji dai na rantse wannan abun da nake tsabar bakincikine da kuma yunwa"
a jiyar zuciya ta sauke iya Tabbacci tana dashi akan Yarima baya shaye2 ko babu komai yakan yi mata irin haka wani lokacin saidai ba kamar na yau ba.
a kasale ta kalleshi tace "na yarda dakai Yusuf baka taɓa aikata irin wannan amman mi yasa ka bakinciki haka?"
yana rike da kofa yace "wani abin na sawa gaba kuma ban cima masara ba shiya ɓata min rai har na kasa cin abinci tun jiya amman karki damu yanzu zan koma daidai dan na hari gaba"
"Allah ya yaye maka ko minene Yusuf na yarda da kai"
murmushi ya sakar mata "good mother"
saida ta masa murmushin sannan ya fice.

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*23*

yanzu hankalin mairo a kwance yake dan ta daina ganin Yarima ba tada wata matsala inba ta jarabawar da suke ba dan momi bata barinta ta zauna data dawo gida kullum ciki karatu take banda wadda ake mata a makaranta da kuma wanda Siraj yake tisa mata Qasin ma wani lokacin yakan mata,

'''*********'''
yau Mairo da far'ah ta tashi ita ta da shi kowa na gidan tare suka shiga kicin da momi aikin komai tare sukayi,
bayan sun kare ta shiga jerawa a dining tana wakewake momi na zuba mata abinci a kula tace "maryam yau far'ah me kike haka?"
fashewa tayi da dariya "oh momi kin manta yau muke kare jarabawa shikenan sai hutu"
momi ta rufe kular tana faÉ—in "o na ganoki shiyasa kika tashi tun safe haka tho Allah yasa a kara muku wata har 8"
da fuskar zolaya momibta karasa maganar
mairo ta marairaice fuskar "Allahumma a'a Allah karka amsa momi wlh bana son haka"
dariya momi tayi tace "tho na daina amman dai kinsan ta É—aya zaki É—auko mana ko?"
dariya tayi ta rufe ido "momi dan kinga ban iya ba ko?"
"a a kin iya maryam Allah dai ya bada sa ah"
"amin momi kin san kince in an mana hutu zaki kaini gurin Gwaggo ko?"
"eh anyi haka tho bari a muku hutun"
rumgume momi tayi cike da jindaÉ—i kamin ta sake ta ta É—auki kular makarantar ta fice dan tuni motar makarantar ta iso,

*_2:37pm..._*
ta shigo gida uniform É—inta duk ya bace da k'asa tafarta ma babu kyau gani,
tafiya ta rikayi laɓalaɓa har ta isa kofar parlour ta shiga leke.
cikin rashin sa'ah ta hango momi zaune ita da Siraj da sauri ta koma baya,
can kuma ta sake lekowa momi kamar wadda aka tsikara ta waigo suka haÉ—a ido.
"lafiya maryam kike laɓe?"
kara laɓewa tayi ta yadda fuskarta kawai ake gani tace "momi uniform ɗina duk yara sun lalashi"
"kamar ya? shigo mana"
"kasa suka samin kuma nidai banma yi qasan kasa ba sune suka samin"
"tho shigo"
"bazaki dakeni ba?"
"eh shigo"
daker ta shigo parlour tana wani kakkaɓen2 muna furci.

ɓata fuska Siraj yayi "yanzu maryam da girmanki zakiyi wasan kasa haka?"
harara ta watsa masa "ina ruwanka nida momi nake magana bada yara kananuba"
dariya Siraj yayi momi kuma tayi murmushi hakan yasa ts ɗan saki jiki ta matso kusa da momi "momi ni yarane suka ɓata uniform ɗin harda kular suka fasa marfin kawai suka barmin"
sai a lokacin momi ta lura da murfin kular dake hannunta,
Siraj yace "karya kike kedai kika fasa da kanki ai nasan halinki"
kamin mairo tayi magana momi ta tari numfashinsa "tho ai babu komai sai a siya mata wata aini tunda tana karatu komai zan iya yimata"
gwalu tayiwa Suraj tana daddalomai ido "yaee an bashi red card"
shikan inbanda dariya babu abunda yake ganin abun nata ba mai karewa bane yasa momi ta riko tace "kyaleshi haka jeki wanka kiyi sallah sai muci abinci"
saida ta kara masa gwalon sannan ta nufi stairs.

da dare mairo na zaune parlour ita da Qasin suna game Siraj ya shigo,
aiko daman neman tsokana yake haka yasha mur yace "ke tashi muje kiyi karatu"
juyowa tayi ta kalleshi tayi mai fari da ido "kai dan Allah ja can yaro ba sauran karatu mun kare jarabawa hune kawai zayi mana yaro"
dariyace ta suɓucewa Siraj Qasin ya kalleta yace "Siraj ɗin ne yaro?"
"eh yaro ne man baka ga ka girme shiba"
"tho ai shekara kaÉ—an na bashi"
"eh duk da haka dai yaro ne"
maganar take tana wani war da ido tana jujjuya baki,
fashewa Qasin yayi da dariya Siraj ma da dariyar ya nufi dining.

game É—in Qasin ya kashe ya rika hannunta "tashi muje muci abinci"
ɓata fuska tayi ta taɓe baki "yaya bamu gama game ɗin ba fa kuma momi bata zoba barre muci abincin"
hancinta ya lakkata "momi yau ba nan zata ci abinci ba kisan abbah yana nan g(me kuma gobe zamuyi tunda ba makaranta tashi muje"
tashi tayi yana rike da hannunta suka nufo dining saida yaja mata kujera ta zauna sannan shima ya zauna ya soma zuba mata abincin"
Siraj dai kallonsu kawai yakeyana cin abincinsa yana murmushi saida suka fara cin abincin sannan yace "yaya kasan momi tace ka daina ci mata abinci fa"
harara Qasin ya watsa mishi "tho momi ka gani nan ne"
rufe baki mairo tayi tana dariya "lahh yaya Allah sai na faÉ—a mata"
dariya Siraj yayi Qasin ya haÉ—e fuska
"kaga bana son iskancin nan fa Siraj ina ruwanka"
Siraj yace "gaskiya ce ai ace mutum da matarsa amman kullum sai yazo gurin momi yaci abinci"
banza Qasin yayi mishi ya cigaba da cin abincinshi,
Mairo kan dariya kawai take tana kallon Qasin.

can ta dafe ciki ta koma kuka kamar ba ita ba "na bani cikina ciyo yake"
duk suka kalleta Qasin yace "ciki kodan kinyi dariya ne?"
"a a tun safe yake min ciyo kuma sosai"
Siraj yace "kinsha magani?"
"a-"
waje tayo da ido tunowa da bata son magani da sauri tace "eh na sha momi ta bani magani mai shegen É—aci"
wani ya mutse fuska tayi kamar da gaske
Qasin yace "tho ci abincin sai kije ki kwanta"
kuka tasa masa
"ni bazan iya ciba Allah ciyo yake sosai"
"owk jeki ki kwanta"
tashi tayi da sauri tana yiwa Siraj É—ageÉ—age,
har ta kama hanya sai kuma ta dawo ta nunashi da yatsa ta maida baki gefe tace "kai kuma yaro kayi sauri ka cinyeshi duka"
juyawa tayi ta cigaba da tafiyarta tana wani rausaya kamar wata tsohuwar karuwa,
Siraj kai ya girgiza yana dariya,
murmushi Qasin yayi ya bita da kallon har shige.

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*24*

*_washe gari..._*
9 da yan mintuna mairo ta nufo downstairs sanye da kayan bachi fuskarta babu annuri,
duk É—agowa sukayi suna kallonta harta zauna momi nakai wainar kwai tace "maryam lafiyarki kuwa?"
kara ɓata fuska tayi "momi cikina ne yake ciyo sosai tun jiya"
Siraj ne ya gwaleta "dan Allah can ji kanta"
"kai yaro wlh ka kyaleni"
dariya yayi "Allah momi in bata daina cemun yaro ba dukan gwarai zanyi mata"
momi na mika mata cup É—in tea tace "karma ka soma ka daketa bakai ka fara wasa da itaba"
gwalo mairo tayi mishi "ance yaro yaro yaro yaro yaro yaroooooo"
Usman yace "ba cikinki ke ciyo ba kenan?"
nan ta rike cikin ta langwashe "momi ni ko tea nan bazan iya shaba ciyo yake sosai"
momi tace "wani abun kika cine?"
"a a ni banci komai ba"
Qasin na kurɓa tea yace "bakince kinsha magani ba ko karya kike?"
soshe2 ta shigayi yana son kawarda maganar "uhm momi kinsan kince yaya bazai kara ci miki abinci ba ko jiya yaci kuma yau yana ci"
kallonshi momi tayi "tho yana iya da abunda yafi k'arfin wuta inji kishiyar k'onanna"
dariya yayi yace "Allah momi abinci inba naki ba bana jindaÉ—inshi"
momi zatayi magana Siraj yace "nidai duk ba wannan ba dan Allah momi karki barta taje ki hanata"

mairo da Qasin suka kalli momi mairo ce ta riga tambaya "minene momi wa za a hana?"
da fork Siraj ya nuna ta "ke mana ke za a hana"
"ina zataje?"
Qasin ya tambaya,
momi badan taso ba ta soma masa bayani "jiya ne bayan fitarka Yarima yazo wai yana son maryam ta rakashi wani taro da za ayi na buÉ—e wata kungiya ta taimakon yara"
ɓata fuska Qasin yayi ya taɓe baki "tho saboda mie sai ita zata rakashi miye haɗin ta ta kungiyar?"
Siraj ne ya karɓa mishi "wai shine zai kaddamar da abun kuma yana son yaje da yarinya da zatayi jawabi a maimakonsa jifa"
momi tace "tsarin ne yazo da haka dan haka aka tsara komai har ma abunda maryam zata faÉ—a a rubuce yake"
tsaki Qasin yaja "aikin banza maryam ce kawai yarinya ai yana da kanne mata da maza yaje dasu mana babu inda zata je"
momi tace "yafa riga ya bada abunda zata karanta har kayan da zata saka ya kawo"
tashi Qasin yayi tsaya yana faÉ—in "tho a mayar masa da kayansa momi dan Allah karki barta taje"
momi bata ce mishi komai ba sai maryam take kallo data ɓata fuska kamar ta fasa kuka,

tana ganin ya fice tace "momi nidai zanje inason nayi jawabi"
Usman da Nura dai kallonta kawai suke basu ce komai ba
kai momi ta É—aga mata "ai zaki je inma kike kare zan baki takarÉ—ar kiyita bita kamin assabar kin iya"
daÉ—i sosai mairo taji za a rika Microphone ayi jawabi.
baki sake Siraj yace "momi kina nufin barinta zakiyi taje duk magangganun nan da akayi"
shima banza momi tayi dashi mairo nata watsa masa harara harya kare cin abincin ya fice.

'''***'''
koda 12 tayi mairo na zaune ɗaki tana karanta takardar da taji motsi ta ɓoye dan kar Siraj ko Qasin ya shigo ya gani,
haik'an ta É—auki abun ta rika tarewa a É—aki duk abunda da bata gane ba ta tambayi momi,
islamiya ce kawai take tasa ta aje idan ta dawo ta cigaba,

a waya Yarima yake kiran momi tabawa mairo yana jin yadda take karantawa dan yasan zuwa gidan ba zai masa daÉ—iba kuma daman momi tayi dashi akan komai zasuyi ayi a waya karya zo gidan inba weekend ba ranar da zasu tafi,

kullum Qasin da Siraj cikin nanatawa momi suke akan karta barta taje. a fili momi nuna musu take bazata barta ba dan karsu dameta,
mairo har zumuÉ—i take taga assabar É—in tayi duk wani ciyo da take ji daina faÉ—awa momi tayi dan karta hana ta zuwa,
cikin kwana biu mairo ta haddace abunda yake fefar kasancewar ba wani jawabi ne mai yawa ba,

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*25*

*_Saturday morning..._*
_8:24am_ Qasin ya shigo part É—in momi cikin kananan kaya,
parlour ya tararda su suna karyawa.
momi na ganinshi gabanta ya faÉ—i a haka ta É—aure ta amsa gaisuwar da yayi mata "lafiya kalau ya naganka cikin shiri haka?"
yan duba agogon hannunsa yace "wlh meeting ne wai zamuyi da wasu kuma basu faÉ—a min ba sai jiya da maraice gashi anjima zasu wuce balle nayi cancle É—inshi"
wani daÉ—ine ya jiyarci zuciyar mairo da momi mairo kasa jurewa tayi saida tayi dariya,
cup É—in tea momi ta aje mishi "xauna ka karya mana"
É—aukar tea yayi a tsaye yana sha "bani da time É—in tsayawa ina Siraj ne?"
"yaje birnin kebbi"
fuskar mamaki yayi birnin kabbi gurin mie?"
"nima ban saniba baba hajara ce ta aiko tana nemansa tun da 7 ya tafi"
iskar bakinsa ya busar "owk maryam tashi ki chanja kaya ki rakani"
da sauri momi ta kalleshi "gurin meeting É—in zata rakaka?"
"eh momi ban yarda da barinta cikin gidan nan ba"
faÉ—a momi ta taso masa dashi "tho bazata ba in baka yarda da magana naba sai kayi abunda zakayi nifa na haifeka Qasin ba ni ka haifa ba"
kasa yayi da kansa yana sauke ajiyar zuciya,
duk sai yaji ba daÉ—i ganin yadda ranta ya bace haka ya juya jiki ba kwari ya fice.

*_9:41am..._*
motar Yarima tayi parking,
ya kusan minti uku ciki motar sannan ya fito ya nufi parlour.
da sallama ya shigo mairo ta amsa masa tana murmushi,

tsaye yayi yana kare mata kallo ganin yadda tayi masa mugun kyau doguwar rigace jikinta golden colour sai É—an karamin bakin hijab da momi ta saka mata da da jan janbaki sosai tayi kyau,
a hankali ya karaso kusa da ita ya risina ya kai hannu ya taɓa gefen fuskarta yana haɗiye yawu,
murmushi ta sakar masa "ina kwana"
bai amsa mata ba
ya mayar mata da murmushin yana mata wani kallo,

jin an taɓa kofa ya sashi tashi ta sauri ya matsa baya yana kallon momi data nufo downstairs.
"Yarima ka iso?"
"eh momi naga har kin shiryata"
"eh kasan kace mun 9:30 zaka zo"
agogon hannunsa ya kalla "bari muje momi kar muyi african time"
"owk tho Allah ya kiyaye"
hannunta ya rika suka fice tana yiwa momi byebye.

murmushi momi ta bita dashi har ta fice ko kaÉ—an momi bata son tafiyarta dan dai babu yadda zatayine tunda tana ganin inta hana mairo zuwa bata kyautawa Yarima ba,

'''*************'''
Qasin ne tsaye tsakiyar É—aki yana kai da kawo kana ganin yanayin fuskarsa kasan ransa a bache yake.

momi ma zaune take saman kujera dafe da kai lokaci lokaci takan kai dubanta gurin agogon dake parlour.
wannan karon *9:21pm* ya nuna hankalinta ne ya kara tashi,
da sauri ta janyo wayar dake hannunta tana kiran number Yarima duk sakamoko É—aya ake bata kamar É—azun wayar a kashe,
juyowa Qasin yayi ya kalleta "kinga ni ko momi saida nace miki karki barta taje kika ki yarda da magana na gashi yanxu abunda ake yiwa gudu"
numfashinsa momi ta tara "babu abunda zai samesu insha Allah kawai dai bana son sukai 10 ne"
magana take kamar abun bai dameta ba saɓanin cikin ranta dake cike da tashin hankali,
kai Qasin ya girgiza "hmm ace tun safe mutun ya fita har yanzu babu labarinsa"

da karfi Mairo ta turo kofar parlour ta shigo idonta zurun zurun.
duk juyowa sukayi suna kallonta babu wadda ya iya taɓuka komai harta karaso kusa dasu,
lumshe ido Qasin yayi yana sauke ajiyar zuciya.

da fata momi tayi tana kallon bayanta "ina Yarima?"
"yana can basan inda yake ba sawa yayi a kawoni"
magana take muryarta na rawa kana gani kasan tsoro take ji sai waiga bayanta take,

juyowa Qasin yayi da ita "maryam mi yasa kuka daÉ—e?"
shiru tayi tana haÉ—iyar yawu "ba ba babu komai"
tsawa Qasin ya katsa mata yana girgiza ta "faÉ—amin min gaskiya tun safe ku fita sai yanzu ki dawo kice mun babu komai faÉ—a min miya faru?"
matsawa tayi ta rike momi tana kuka "yace duk na faÉ—a sai ya kasheni"
sanyi jikin Qasin yayi momi kuma tsigar jikinta ta tashi,
a hankali momi ta rika zata zaunarda ita kin zama mairo tayi ta ɗan ɗaga rigarta cike da tsoro tace "momi kayana duk ya ɓata dubi jini na min zuba"
da sauri Qasin da Momi suka kalli jinin dake bin k'afarta.

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*26*

waje Qasin yayi da ido cikin rawar murya yace "maryam..-"
da sauri ta kalleshi itama idon nata a tsaye.
zai rikata momi tayi saurin rika hannunta "muje ciki"
janta momi tayi suka nufi stairs jikinta babu karfin,
Qasin ma haka yake kallonsu jiki ba kwari har suka shige sannan ya faÉ—in zaune yana kallon gurin da jinin ya zuba,

sai kusan 10 da wani abu ya tashi ya nufi part É—inshi tafiya yake kafafunsa na masa nauyi zuciyarsa sai bugawa take da karfi,
baiyi sallama ba ya shigo parlour.
har ya zauna bai lura da mansura dake zaune saman kujera ba
dafe kanshi yayi ya kulle idonsa gam yana cizon baki,
jin an dafashi yasashi É—ago kai ya kalleta.
tashi hankalinta yayi yanayin yadda taga idonsa yayi ja tasan ba lafiya ba,
tana shafa gefen fuskarsa tace "Qasin lafiya na ganka haka?"
janye mata hannun yayi "babu komai jeki kwanta"
"kamar ya naje na kwanta bayan kai hankalinka ba-"
cikin tsawa ya tari numfashinta "nace miki kije ki kwanta babu komai"
tashi tayi tana masa wani kallo kamin ta juya ta nufi É—aki,

dafe kai yayi ya sake rumtse idon abunda ya faru É—azu ne ya rika dawo masa,
jin yayi bashi da natsuwa yaji wani irin abu ya tsaya masa a zuciya da sauri ya tashi ya nufi firij yana buÉ—ewa ya É—auki gorar ruwa ya kafa a baki,
kaÉ—an yasha ya É—ire ta saman firij É—in yana maida numfashin,
ya daÉ—e tsaye a gurin sannan ya juya ya nufi kofa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.