Mairo Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: MAIRO 1.txt
Chapter 3 of 4
part É—in momi ya sake nufowa yadda yabar parlour haka ya tarardashi kai tsaye upstairs ya nufa,
tun kamin ya karasa hawa yayi tsaye jin shinshikar kukan momi wani abu yaji ya tsikareshi tun daga É—an yatsan kafarsa har tsakiyar kansa karfen stairs É—in ya rike da karfi ya matse hannunsa ciki yana dantsar hakora,
jin bazai iya jure tsayinba yasashi zaunawa a gurin,
lumashe ido yayi saida yaji abunda ke zuciyarsa ya É—an kwanta sannan ya tashi ya nufi É—akin momi,
a hankali yakai hannu ya tura kofar É—akin.
tsaye yayi yana kallon mairo dake saman gado kwance tana bachi kamar gawa.
ɓachin ransa dake ransa ya karu saurin ɗauke idonsa yayi ya mayar gurin momi dake zaune kusa da ita hana sharar kwallah,
cikin dakisasshiyar murya yace "momi kuka kikeyi?"
ba tare data kalleshi ba ta girgiza masa kai alamar a'a,
kai ya É—aga "itama naji kukanta É—azu"
sai a lokacin momi tayi gyaran murya tace "eh ina tambayar tane ko yayi mata wanin abun ne shine nace zan daketa inbata faÉ—a ba shine take yiwa kuka"
saida ya É—anyi jimmm sannan yace "mi tace momi?"
ita shirun ta É—anyi kamin ta bashi amsa "ina jin menstruation ne Qasin dan banga wata alama data nuna yayi mata wani abun ba kuma ita bata faÉ—a ba"
sai a lokacin ta kalleshi
murmushi yayi "yes momi menstruation ne saida safe"
bai tsaya jiran mi zata ce ba yayi baya baya yaja mata kofa daman can bai karasa shiga cikin É—akin ba,
cikin wani yanayi ya nufo downstairs yana tafe hawaye na masa zuba har sauko.
saman kujera ya zauna saida yaji hawayen sun tsaya masa sannan ya tashi a kasale ya nufi part É—inshi,
*_washe gari..._*
Mairo na zaune saman gado tana wasa da kafafunta Qasin ya turo kofa ya shigo fuskarsa É—auke da murmushi,
tana É—ago kai suka haÉ—a ido murmushin da ta gani a fuskarsa ya hanata jin tsoronsa tun kamin ya karaso tace "yaya ina kwana?"
saida ya risina kisa da ita sannan ya amsa mata murya kasakasa "lafiya kalau kin tashi lafiya?"
"lafiya kalau"
"ina momi?"
"tana kicin"
hannayenta ya riko "faÉ—a min maryam mi Yarima yayi miki?"
"ni bai min komai ba yaya"
shiru yayi ya soke kai
can ya É—ago kai ya kalleta "jinin dake miki zuba har yanzu yanayi ko ya daina?"
"a'a ya daina koda na tashi da safe bai min zuba ba"
da sauri ya lumshe ido bugun zuciyarsa ya karu.
"ba abunda kake zargi bane Qasin jikina bai bani haka ba kuma na bincike ta banga haka ba"
momi ce take maganar lokacin da ta karaso kusa dashi.
sakin hannunayen nata yayi suka tashi tsaye tare shida Mairo,
wani irin faÉ—uwa gabansa yayi lokacin da ya juyo suka haÉ—a ido da mansura dake tsaye bakin kofa rike da kofar É—akin.
cikin rashin ta karasa shigowa tana faÉ—in "miya faru da maryam?"
da sauri momi ta tari numfashinta "babu abunda ya faru da ita gimuwa ne tayi da kuma ciyon kai"
karasowa tayi kusa da mairo "gimuwa a ina?"
nan mairo ta soma mata bayana "a a jiya ne da-"
tassssss Qasin ya wanke mata fuska da mari saida ta faÉ—i tun bata kai ko ina a zancen ba,
da sauri mansura ta kalleshi "Qasin mi-"
marin itama ya watsa mata saida tayi baya ta dafe kunci.
*©Khadeeja Candy*
candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
_dedicated this page to maama Hajiya Zainab Kano kakar yan biu 🙈 LOL_
*27*
da sauri momi ta riko Qasin da fuskarsa ke É—auke da bachin rai tace "mi yake damunka Qasin mi suka maka?"
kallon kawai ya rikayi ba tare daya amsa mata ba,
sun minti 10 haka É—akin tsit sai shehsekar kukan Mairo ke tashi.
mansura ce tayi karfin halin sake yin magana "momi mi yake damunsa ne tun jiya na kasa gane kansa?"
nan momi ta saki Qasin ta matsa kisa da mansura "abunda ya kawo ki kenan? daman nasan baki taɓa leko part ɗina ba sai a wata bukatar kanki ta taso"
kasa tayi da kanta har alokacin tana dafe da kuncinta hawaye na mata zuba,
"indai har abunda ya kawo ki kenan tho ki juya ki barmin É—akinki ai mijinki ne kinfini sanin hanyoyin da zakibi ki fahimcin abunda yake damunsa"
kamar *HAWAINIYA* ta soma tafiya kanta a kasa har ta fice,
juyawa momi tayi ta nufi mairo ta tashe'ta tana share mata hawaye cikin sanyayyeyar murya momi ta soma magana da Qasin ba tare data kalleshi ba "bana son kowa yasan da maganar nan Qasin koda Siraj ne"
nan ma baice komai ba ya kaÉ—a kai ya fice,
mairo sai taga ya fice sannan ta kalli momi cikin muryar kuka tace "momi minayi masa?"
"baki masa komai ba maryam"
"amman momi ya mareni haka da zafi"
murmushi momi tayi "baya son idan manya na magana yara su saka baki"
shiru mairo tayi tana shafa gurin,
momi ta kwanto ta ita jikinta "maryam"
cikiciki ta amsa "na'am"
"duk wadda ya tambayeki mi akayi miki kice komai karki kuskura kice Yarima yace in kika faÉ—a sai ya kasheki ko kice ranar jini yayi miki zuba kinji?"
"tho momi"
"koda fa can ne kauye karki faÉ—awa kowa kinji?"
"tho bazan faÉ—a ba"
"yauwa Maryam É—ina yar albarka tashi muje muyi breakfast"
"tho"
da sauri ta tashi momi ta rika hannunta suka fice,
parlour suka tararda Qasin zaune saman tree-setter rike da cup din tea.
da kallo ya bisu yana kurɓa tea a hankali har suka zauna sannan ya tashi ya nufi kofa,
"yaya yau ba dakai za ah karya ba?"
Siraj ne yake masa maganar yana kokarin saka T-shirt É—in dake hannunsa ya nufi dining.
kai kawai ya É—aga masa ya fice,
haÉ—e gira yayi ya kalli momi "lafiyarsa kuwa?"
momi tace "lafiyarsa kalau saidai ko in wani gurin aka taɓoshi"
kafaÉ—unsa ya É—aga alamar bai damu ba yaja kujera ya zauna yana tsokanar mairo,
"miya kunbura miki fuska haka yar kauye?"
turo baki tayi ta kalli momi "momi kingan shi ko?"
kai momi ta girgiza "oh Siraj dan Allah ka rabu da ita bana son fitinar nan dan Allah"
murmushi yayi ya noce kansa ya soma cin abincin.
lokaci lokacin ya kan É—ago dasun haÉ—a iÉ—o da mairo yayi mata gwalo ita kuma ta murguÉ—a masa baki,
daga ita har momi ba suyi wani cin abincin kirkiba suka tashi daman ita Siraj ya tsangwameta
*_2:55pm..._*
Qasin ya shigo part É—in momi saida ya karewa kujerun parlour kallo sannan ya kalli momi dake tsaye dining yace "Yarima yazo?"
kallon mamaki momi tayi masa "Yarima? mi zaya maka?"
jijiyar kansa ce ta tashi jin yayi kamar ya ɓalɓalowa momi masifa amman ba dama dan mahaifiya ce. dole tasa ya tausasa harshensa "magana nake son miyi dashi momi na ɗauka ta shigo ne"
"tho bai zoba kuma in har akan maryam ne karka kuskura masa magana kaji na faÉ—a maka"
kallon rashin fahimta yayi mata "momi karfa ayi masa magana kikace"
kallonshi tayi ido cikin ido "eh nima mahaifiyarta ce ina tunanin ko ni kaÉ—ai nayi magana dashi ya isa"
wani murmushin ban haushi Qasin yayi ya juya ya fice,
Gardem ya nufa yana tafe yana tunanin hali irin na momi,
wakewaken Mairo ne suka É—ago da hankalinsa yakai gareta
tana zaune karkarshin bushiyar mangoro rike da gwallon gwaiba tana ci,
sai a lokacin ya soma jin tausayinta nn d nn idansa suka cika da kwallah wata irin tsanar Yarima yaji ta taso masa a ɗayan ɓangaren kuma yana son ganin laifin momi,
ya daÉ—e yana kallonta zuciyarsa sai wani tunani take kawo masa saida ya fisgi kansa sannan ya samu karasa kusa da ita,
da sauri ta tashi tsaye ta jefarda gwaibar tana masa kallon tsoro.
risinowa yayi ya É—an sakar mata murmushi "maryam..."
da sauri ta amsa "na'am yaya"
hannu yakai ya shafa gefen fuskarta kamin ya jata jikinshi ya rumgume,
_'ya lalata miki rayuwa Maryam ya cutar dani yayi miki taɓon ds zakiyi bakinciki nan gaba amman zan nuna masa kuskurensa sai yayi nadamar abunda ya aikata'_
a zuciyarsa yake wannan maganar yana cige da lips.
kalamanta ne suka dawo dashi daga tunanin da yake,
"wlh yaya kaci arziki yanzu na daina fitsara na shiryu da baka isa ka mareni na kyale kaba"
hannu yasa ya ciro handkerchief ya share hawaye da suka zubo masa ya É—ago yana murmushi yace "da gaske?"
"Allah wlh kai hmm"
gefen fuskarta ya lakata "ashe ke matsifaffiya'ce ko?"
dariya tayi ta rufe ido "a'a ni mai lafiya ce"
dariyar yayi shima "mai lafiya ai sunan wani ne"
wannan karon rumfumeshi tayi tana dariyar
"yaya zaka bimu kauye?"
"yaushe zaku je?"
"da anyi hutu ranar juma ah za ayi mana hutu"
saida ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "zanje Allah ya kaimu"
rawa ta rika masa "yauwa yaya na gode ina sonka sosai"
murmushi kawai ya shafa bayanta,
can ta É—ago "bari naje nayi shirin islamiya kar momi tayi faÉ—a"
kai ya É—aga mata ta masa byebye ta nufi cikin gida da sauri.
*©Khadeeja Candy*
candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
*28*
Mairo na zaune parlour gaban tv tana buga game Siraj ya shigo,
da far ah ya karaso kusa da ita yana ya zauna,
kallonshi tayi taja tsaki ta matsa nesa dashi tana harararsa.
hannu ya kai ya kashe game É—in ya ja mata hanci,
tashi tayi tsaye ta É—auki fillon kujera ta rika buga mishi iyakar karfinta.
rikota yayi ya fisge fillon yayi ya jefar ya shiga kokuwar zaunar da ita,
daker ta zauna koshi dan ya rike mata hannayene haka ta rika kokuwar kuncewa ganin bazata iya bane yasa dole ta hakura ta zauna kurum,
bakinsa ya É—ora daidai kunneta yace
"plz maryam magana nake son muyi dake ta fahimta ba faÉ—a"
banza tayi masa ta kara turo baki ta É—auke fuska.
murmushi yayi "haba my sis plz"
"tho ka faÉ—a mana ai kunne ne yake ji kuma ka sakeni"
sakinta yayi ta zauna daidai tana fuskartarsa "maryam kinga yau aka muku hutu kuma momi tace kauye zata kaiki dan Allah in kukaje karki yarda a baro ki kice ke bazaki zauna ba"
wani kallo tayi masa ta É—aga baki sama "saboda mie?"
"kinga can ba daÉ—i kuma ba abinci mai kyau irin wannan ba gurin bachi mai kyau ba daÉ—i kinsan ai kauye ba daÉ—ine dashi ba"
"nikan inaso a haks zan zauna har hutun mu ya kare inason naga gwaggo da tsoho da kawayena da kowa da kowa"
"oh maryam bazaki gane ba yanxu fa in kikaje can bazaki sake ganinmu ba sai anyi hutu"
tashi tayi tsaye "eh naji nidai ka kyaleni"
kallo ya bita dashi har ta haye stairs tana masa gunguni.
*_6:30pm..._*
momi na zaune ita da Usman,Nura da Mairo Qasin ya shigo da sallama,
da gudu mairo ta rumgumeshi tana murna momi bata kulashi ba Nura da Usman ne suka rika kallonsa har ya zauna,
gefensa Mairo ta zauna tana rike da hannunsa "yaya mi yasa ka daina zuwa nan gurin momi?"
shiru yayi yana kallon fuskar momi data ki ta kalleshi,
nan mairo ta sake jefa masa wata tambayar "kuma yaya ka daina cin abinci nn?"
sai a lokacin ya kalleta yana murmushi yace "aiki ne ya mun yawa bani da time É—in kaina shiyasa kika daina ganina"
kai ta girgirza tana dariya,
juyawa yayi ya kalli momi "momi an wuni lafiya?"
amsa mishi tayi still bata kalleshi ba "lafiya kalau Qasin ya aiki?"
"Alhamdulillah"
bai sake cewa komai ba in banda wasa da yake da yatsun mairo momi ma ko kallonsa batayi ba barre ta sake ce masa wani abu,
suna haka aka kira sallar magariba haka ya sashi tashi yana kallon momi "bari naje nayi sallah an kira magariba"
sai a lokacin ta kalleshi "ka shirya ranar assabar zamuje kauye"
kai ya É—aga "owk momi har da mansura"
"a a daga ni sai kai sai maryam zamuje"
"owk Allah ya kaimu"
"amin"
kallon su Usman yayi "ku ba zakuyi sallar bane?"
tashi sukayi ko wane na sosa kai suka nufi kofa, nn ya juyo gurin mairo "kema je kiyi sallah"
"tho"
da sauri ta tashi ta nufi stairs saida ta shige sannan ya maso kusa da momi ya risina hakan yasa momi ta kalleahi cikin sanyayyiyar murya yace "momi fushi kike dani ko?"
"mi zai sa nayi fushi dakai Qasin mi kayi min?"
shiru yayi yana kallonta kamar mai tunanon abunda zaice,
tashi momi tayi "nikan bari na shiga ciki nayi sallah"
bata tsaya jiran mi zai ceba ta nufi stairs saida yaga shigewarta sannan ya tashi ya fice.
*_washe gari..._*
tun 7am Qasin ya shigo part É—in momi ya tare a parlour murna gurin mairo ba a magana haka ya sake jikinshi kamar ba shiba momi dai sai kallonshi take.
tare sukayi breakfast sai kusan 10am ya koma part É—insa bai daÉ—e ba ya fito cikin shiri ya yabar gidan.
da dare ma nan ya ci abinci ya rika jan momi da fira tun tana shareshi har ta gaji ta sake jiki, saida dare ya raba sannan yayi mata sallama ya nufi part É—inshi,
haka Qasin ya rikayi duk wani bachin rai dake ransa dannesa yayi ya barshi a ranshi saidai duk lokacin daya kalli mairo sai yaji ba daÉ—i,
da sallama ya shigo kaya nuki nuki a hannunsa banci wa yanda Siraj da Usman suka riko,
gaban momi suka É—ire kayan nn da nn mairo ta shiga budewa "momi kayan waye?"
É—an kwalin dake kanta Siraj ya cire yaja mata gashi saida tayi uhu,
da sauri Qasin ya kalleshi "kai mi yasa kake son mata keta haka ne?"
mairo ta watsa masa harara "mugune shi mai katon kai ai gobe ba zaka gannin ba"
murmushi yayi ya kalli momi yace "dan Allah momi karki baro ta"
shafa kanta momi tayi "a a can zan barota sai taga gari sannan a dawo da ita"
gwalo tayi masa tana masa rawar kai,
dariya Qasin yayi yace "gobe mirna gurin Gwaggo ba a magana"
momi tace "lallaikan an kwana biu ba a ga mairo ba"
rufe baki Siraj yayi "momi mairo kike ce fa"
"eh ai haka suke ce mata can kauye"
aiko nan ya hau kiran suna nata yana fashewa da dariya tun bata kulaba har ta soma tsarguwa ta tsuke baki "tho sai miye dan kace Mairo ai sunane haka ake kirana"
gwalo yayi mata "ai ba mairo yake ba mero yar kauye"
fashewa duk sukayi da dariya haka yasa ta haÉ—e fuska kamar ta fasa ta turo baki,
nn Qasin ya sake fashewa da wata dariyar yace "Siraj shi yasa ta raina ka ka cika mata shinshigi da yawa"
"ba shinshigi bane Allah mero ne sunan"
da fata momi tayi "ke kyalesu tashi kije ki kwanta kinsan gobe sammako zamuyi"
tasgi tayi kamar ta fasa kuka ta nufi daki.
*©Khadeeja Candy*
candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
*29*
*_washe gari..._*
koda 8am tayi mairo tayi shirin tafiya kasa yin breakfast tayi saboda murna ruwan tea kawai tasha ta tare saman kujera tana kallon su momi dake karyawa,
can taja tsaki ta kalli agogon dake hannunta "mts momi duk kun ɓata min lokaci har 9tayi"
juyowa Siraj yayi ya kalleta "eyye yar kauye an waye yanzu kin iya agogo ko mero?"
kawarda fuska tayi ta masa banza momi ta tashi tana faÉ—in "bari naje na shirya muje na kaiki gurin Gwaggo ki huta da matsalar Siraj"
kallonta Siraj yayi "momi dan Allah karki baro mana Maryam wlh miss É—inta zamuyi"
kallonta kawai Qasin yayi ya kara kurɓa tea dake gabansa ya tashi ya fice,
mairo ta kalli momi "nidai kije ki shirya momi kar ki daÉ—e"
Usman yayi dariya yace "yau Maryam har gudun mu akayi ne dan zakije kauye"
Siraj kamar mai tsira ya hau tsokanarta "kaji fa wai kauye babu ma daÉ—in faÉ—in"
taɓe baki mairo tayi ta kalli momi "momi kije dan Allah ki shirya muje"
stairs momi ta nufa tana faÉ—in "tho yar gidan Gwaggo"
itama tashi tayi tana rufawa momi baya tana hararar Siraj,
*✧*
sha É—aya da yan mintuna suka kama hanya,
mairo na front-seat Qasin na driving momi kuma a gidan baya surutu kan mairo shi tasawa gaba inta ɗauko wannan ya ɗauko wannan momi dai saurarenta kawai take inta kai gana dariya ba ta tamata saɓanin Qasin da fuskarsa take haɗe hankalinsa ma a wani gurin yake,
hannu Mairo takai ta taɓoshi da sauri ya kalleta "ya maryam mi kikace ne?"
murmushi tayi masa "bance komai ba naga dai kayi shirune baka magana kuma ka ɓata fuska"
sakin fuskar yayi "ina tunanin wani business nawa ne"
"tho ka ka daina haÉ—e fuska"
murmushi yayi yace "na daina Auntie"
dariya tayi ta kwanta tana kallon t-t,
motocin dake wucewa ta rika lisafawa har bachi ya É—auketa.
'''*************'''
tsayawar da motar tayi da karfine yasa ta farka a figice tana rabon ido,
rana ne zagaye dasu sai tsalle suke suna ambatar mairo.
da sauri ta fita motar tana uhu suka shiga rumgumar juna ita dasu suna tsalle² ta gina wasu matan aure suka rika lekenta,
tuni momi da Qasin suka kunna kai cikin gidan,
ita kan saida suka gama ɓata mata kaya da kasa sannan ta shiga cikin gidan. da gudun ta karasa ta rumgume Gwaggo dake zaune saman tabarma tare dasu momi, idon Gwaggo cike da hawaye ta soma ture mairo "ni ɗagani ai guduwa kikayi kika barni"
kara rumgume tayi "Gwaggo ni ba guduwa nayi ba ai daman nace miki zan dawo kuma ba gashi na dawo ba ni babu inda zanje"
momi tayi murmushi tace "haba aiko duk kika kori mairo baki mata adalci ba dan kullum zancenki take ita dai Gwaggo ta dai"
Qasin yace "Gwaggo yar matsifa ke kullum matsifarki karuwa take ba raguwa ba"
nn Gwggo ta dawo kansa "eh ai daman kaine ka hure mata kunne tunda kazo taki ta samu matsuwa sai ta biku"
dariya yayi "tho Gwaggo ba gata yanxu mun dawo da ita ba da nan fa da can duk É—aya ne tunda duk abu É—aya ne"
momi ta karɓa masa "duɓe ta ki gani na gyare miki ita ta zama yar zamani"
gaban Gwaggo mairo ta dawo tana jujjuyawa kamin ta fashe da dariya ta faÉ—a jikinta ta rumgumeta,
*_two hours letter..._*
"kingani ko Gwaggo mairo ta sami lafiya ai daman nasan cikin biu sai anyi É—aya kodai a maidota dan mugun halinta ko kuma ta chanja hali"
Halilu ne ke maganar yana kai lomomin shinkafs da wake bakinsa,
taɓe bag Gwaggo tayi "ai daman ba wani mugun haline da ita ba kaine dai ka bi ka matsa mata"
halilu yayi dariya yace "Allah Gwaggo in zaki faɗi gaskiya kema kinsan mairo ta chanja jifa har take bari yaran na su taɓa ta inda ne ai basu isaba ballan tana ma ta dawo daga birni"
"gaskiya kan ya gashi yanzu har girma maryam tayi kuma tayi hankali"
maganar momi take tana kallon fuskar Gwaggo,
Gwaggo ta taɓe baki "ai dole tun Allah kaɗai yasan hawalar da kuke gwada mata ai duk abunda zai sa mairo ta zama haka ba karamin abu bane"
Halilu ya tashi yana faÉ—in "Gwaggo ai ba zasu dai yi mata abunda kike nufi ba"
momi tace "ai muna zuwa duk wani abu da tasan bana Gwarai bane zubarwa tayi kuma muka saka ta a makaranta"
juyowa Halilu yayi da far'ah "harda makaranta kuka saka ta momi gaske dai ta kara chanja wa tayi kyau yanzu"
dariya momi tayi "kaji Halilu shi boko har sawa yake mutun yayi kyau?"
"Allah kuwa momi kinga ai yanzu ta natsu kuma ta waye ba kamar daba daman burina kenan naga mairo a makaranta kuma cikin rayuwar jindaÉ—i"
harara Gwaggo ta watsa masa "kuma can da kake dukanta?"
"yau ai saboda bata jin maganane shiyasa kuma kinga dan ta dainane ake mata haka"
"hmm tho chanjawa tayi ne ai babu irin dukan da bata a hannunka ba"
dariya yayi ya aje kwanon dake hannunsa "ai ba zaki gane ba Gwaggo ni dai bari naje Qasin na jirana mu zaga gari"
momi ta kalleshi "kar kuyi nisa halilu yanzu zamu je gidan tsoho mu koma gida dan ba daÉ—ewa zamuyi ba"
"tho momi bari na faÉ—a masa"
hannunsa ya É—auraye bayan yasha ruwa ya kurkure baki ya fice.
*©Khadeeja Candy*
candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
*30*
momi ta kalli Gwaggo tace "wai halilu ya daina karantun da yaje ne"
"wane karatu?"
"ba nasan da yana zuwa can sokoto gurin karatu ba"
Gwaggo ta taɓe baki "karatu kan ai yasha kashi tunda babu kuɗin karasawa"
"ayyah haba nijan kasan yana karatu a da digiri yake ne ko mie?"
"karki tambayeni ni sanin nayi yadda abun yake ne can dai su suka sani"
dariya momi tayi tana gyara É—aurin É—an kwalinta,
abincin dake gaban momi Gwaggo ta kalla tace "kema bazaki ci abincin ba ko Qasin ma yace ba zai ciba ku yan birni baza kuci na kauye ba"
"a a aini kinfi kowa sanin ba haka nake ba tun kamin mu baro gida saida muka ci abinci kuma ni bama abincin ne a gaba na ba"
"ko a siyo miki wani abun ne kici?"
"a'a ai inason shinkafa da wake ni wata magana nake son muyi dake Gwaggo"
kara juyowa Gwaggo tayi tana fuskarta "wace magana ce hauwa?"
"cewa nayi wai mi zai hana ayi haÉ—in gida"
"haɗin gida kamar ya kiɓfito kiyi magana tunda ba kunyata kike jiba kuma ba bakuwarki nake ba"
dariya momi tayi ta matso kusa da Gwaggo "ina nufi auren gida a haÉ—a Maryam da Qasin"
faÉ—aÉ—a fuskar Gwaggo tayi da far'ah "masha Allahu hauwa kin kawo magana daman abunda aketa magana kena a gari wai mun bayarda mairo can birni dan kwaÉ—ayi mamakon muyi mata aure ai kara lalacewa zatayi magagganu kalakala babu daÉ—in ji
shekaran jiya fa tsoho yake cewa shidai cewa zaiyi a maido da mairo ya huta har nace nidai ba zanyi magana ba indai ba garin kukazo"
dariya momi ta girgiza kai "ai koda man munce fushine kikeyi"
"ai babu yadda halilu bai yiba kan yaje ya ganota na hana amman gaskiya naji daÉ—in maganar nan kin kawo shawara tho amman kunyi magana da Alhaji?"
"da haÉ—in bakinsa nake wannan maganar saida muka tattauna komai dashi kuma ya aminci shi da kanshi yace in nazo nayi miki magana ke kuma kiyiwa tsoho magana kinga duk yadda kukayi in muka dawo sai muji"
"tho insha Allah haka za'ayi abu mai sauki"
sosai momi ta jidaÉ—i dan batayi zaton zata samu goyon bayan Gwaggo ba,
abincin taja ta fara ci suna fira da Gwaggo, daf da zata kare Qasin ya shigo tare halilu.
zaunawa yayi kusa da ita yana kallon agogon hannunasa yace "momi tashi muje gurin tsoho so nake muje gida da wuri mansura tace nayi baki"
banza momi ta masa saida ta gama cin abincin sannan ta tashi suka nufi gidan tsoho,
''' * * * '''
sai bayan la'asar suka dawo gidan Gwaggo har lokacin mairo bata dawo gida ba,
sosai momi taso ta ganin mairo kamin su wuce.
amman ba dama dan halilu yayi nemanta har ya gaji baiga inda ta shiga ba, haka yasa dole momi tayiwa Gwaggo sallama. godiya Gwaggo tayi ta musu ita da halilu suna É—sgs musu hannu har suka daina hango su,
sannan suka koma cikin gida.
kuÉ—i halilu ya ciro aljigunsa ya mikawa Gwaggo "ga naki kason"
da far'ah ta karɓa "yayi ɗan albarka abun ya samu"
yana dariya yace "Qasin ne ya bani É—azun da muka fita"
zaunawa Gwaggo tayi tana faÉ—in "ai yaron nan yana da albarka wlh shiyasa ni na jidaÉ—i sosai da haÉ—in auren na da za'ayi shida mairo"
faÉ—uwa gaban halilu yayi nn da nn yanayin fuskarsa ya chanja tsigar jikinshi ta tashi a kasali ya kalli Gwaggo yace "aure za a haÉ—a mairo da Qasin?"
"eh abunda muka tattins da hauwa kenan kuma alhaji ne ya aikota yace a faÉ—awa tsoho kuma ni wlh nafi kowa farinciki wannan abun da za ayi ksgs ms mun huta da tsegumin mutane-"
da karfi halilu ya haÉ—eye yawu duk sai yaji maganar ta cika masa kunne, ya juya jiki ba gwari ya nufi kofa, kallo Gwaggo ts bishi dashi baki sake har ya fice,
tsaki taja ta taɓe baki "ai daman kai bason mairo kake ba kafison ka rika gwada mata azaba kamar haihuwarta"
'''***************'''
cikin dare su momi suka shiga sokoto _Rahama Restaurant_ momi tasa Qasin ya biya sukayo takeaway sannan suka iso gida,
Qasin nayin parking ya nufi part É—insa, momi ma a gajiye ta nufi nata part É—in,
*_washe gari..._*
sai kusan 10 momi ta kare haÉ—a breakfast saboda gajiyan tafiyar jiya gashi kuma mairo maitaimaka mata bata nan,
Nura ne ya taimaka mata gurin jera abincin a dining, Usman yayi dariya "ayyoh Allah momi har nayi miss É—in mairo"
momi na shirin zaunawa tace "ai nice nayi miss É—inta yanzu haka ita nake tunani aikin nan duk sai naga yayi min wata kala"
Qasin yayi murmushi "ai momi ko ita sai tayi miss É—inki balle ma can da nan ai ba É—aya ba"
Siraj ya kalli momi "Allah momi da ba dan wani abu ba dasai nace Allah ya kara ai saida nace karki barota kika ki É—aukar shawara ta"
"ai dole na barota wata nawa bata ga gida ba sai yanzu bamabfa shi kaÉ—ai ya kaini ba"
Siraj yace "tho miya kaiki momi?"
tana buÉ—e marfin filas tace "auren maryam naje nemawa Qasin..."
kamar daga ssma sukaji maganar da sauri Qasin ya tashi tsaye yana kallonta
Usman da Nura ma duk ita suke kallo Siraj baisan lokacin daya saki tea cup É—in dake hannunshi ba.
*©Khadeeja Candy*
[11/10, 2:13 PM] ‪+234 806 053 5947‬: candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
*31*
"aure fa kika ce momi?"
Siraj ne yake maganar yana mata wani kallon rashin fahimta,
murmushi momi tayi "aure mana miye abun tada hankali a ciki?"
Qasin da tun É—axu ya kasa fahimtar ta yace "kamar ya momi nifa naji kin anbata?"
É—ago kai momi tayi ta kalleshi "eh kai na nemawa inason ka auri Maryam ne"
a hankali ya zauna yana kallonta "saboda mi momi nifa ban fahimta ba?"
"bari mu gama cin abinci sai muyi magana"
juyawa tayi gurin Siraj "zauna mana Siraj"
zaunawa yayi yana kallon wainar kwan dake gabansa momi ta sake haÉ—a masa wani tea ta mika masa,
Qasin kasa cin komai yayi shidai moni kawai yake kallo zuciyarsa cike da tambayoyi,
Siraj ma cin abinci kawai ba dan yana jidaÉ—insa ba
wayarsa nayin ringing kamar mai jira yayi sauri tashi tsaye ya ciro ta a jihu ya kara a kunne ya fice,
momi saida ta kare cin abincin tsaf sannan ta tashi ta nufi stairs ko minti uku ba tayi ba Qasin ya rufa mata baya,
gefen gado ya samu ya zauna yana kallon momi dake tsaye gaban madubi yace "momi kefa nake saurare nama kasa fahimtar abun kike nufi?"
zaman kujerar mirrow momi ta zauna "kasan me nake nufi Qasin auren maryam nake so kayi"
"saboda mie momi?"
"saboda inason ka kara aure"
"ban gane na kara aure ba mansura fa momi?"
"mansura ba mata bace Qasin so nake ka auri matar da zaka san kayi aure kasan waye kai"
kai ya girgiza "momi ni ban shirya kara aure yanzu ba haba momi ni bazan iya zama da mata sama da É—aya ba"
leme baki momi tayi
"soboda mi baka san macce hudu Allah ya halitta maka aure ba?"
"na sani momi amman gaskiya ni ban shirya kara aure yanzu ba"
momi tace "ban fahimceka ba Qasin baza iya ba kamar ya?"
shiru yayi ya maida dubansa wani gurin fuskarsa É—auke da damuwa,
ido momi ta tsura masa tana jiran amsar da zai bata.
ganin bashida niyar magana yasa tace "ina saurarenka faÉ—amin dalilinka?"
juyowa yayi ya kalleta "momi da wane ido zan kalli mansura bama zata fahimta ba momi inma gwadanine kike dan Allah ki daina"
"mansura..." momi ta faÉ—a "itace ta faÉ—o maka a rai ko baka kada wata matsala sai ita. kar dai ranta ya bache kana gudun bachin ranta amman ita bata gudun naka"
kallon mamaki yayi mata "momi muna zaine lafiya da ita fa ba muda wata matsala"
a hankaɗe momi ta kalleshi "na faɗa maka mansura ba mace bace Qasin har yaushe zaka san waye kai ne tunda mansura tazo gidan nan bata taɓa girka maka na safe da rana da dare kaci ba saidai ka siye takeaway koka zo nan kaci, wata hidima ta dangi bata taɓa tashi ta wanke kafarta taje ba bata taba shiga familinmu ba wani daga familinmu bai taɓa zuwa gurinta tayi masa kyakyawar tarba ba bata taɓa tako kafarta tazo nan part ɗina da sunan tazo gaidani ba matarka bata son haihuwa duk wannan bai taɓa damunka ba bai taɓa bata maka rai ba?"
da karfi momi take masa faÉ—an saida ya rumtse ido,
"mi yasa son mansura ya rufe maka ido haka Qasin? miyasa baka ganin laifinta baka son bachin ranta wanyannan abubuwan dana lissafa nasan suna damunka amman ka ɓoye saboda kar ranta ya bachi thobin kai ka jure ni bazan iya jurewa ba umarnine nake baka ba neman shawara ba kuma mun riga mu yanke shawara da babanka maryam zaka aura"
kallonta yayi da raunanniyar fuska "momi naji amman fisabilillahi a rasa wadda za a ce na aura sai maryam"
"kamar ya sai maryam
maryam ba mutum bace?"
kamar ya fasa kuka yace "momi kankanuwar yarinya ai kowa ma yaji dariya zai mun"
"kwarai za'a maka dariya kan tunda ka auro dodo ko aljana kamar maryam kake cewa kankanuwar yarinya shekara goma sha?"
tashi yayi tsaye yana kallonta yace "momi am more than 30 now taya kike ganin zan auri yarinyar da bata kai shekara ashirin ba?"
"tho abun kunya kayi ko saɓawa addini kayi Annabi (S.A.W) ya auri nana Aysha tana da shekara 6 aka kaita gidansa tana yar shekara 9 auren duk kuma abunda Annabi ya aikata Sunna ce ba akanka aka fara ba barre a kare kanka dan haka ni maryam nake son ka aura"
lumshe ido yayi ya buɗe "amman momi kona sureta hankalina ba zai taɓa kwanciya da ita ba ba zan taɓa samun natsuwa ba"
momi tace "saboda mi Qasin baka son tane?"
ya daÉ—e kansa a kasa kamin ya bata amsa "inason ta momi ina sonta sosai amman-"
shiru yayi ya kasa karasawa,
tashi momi tayi tana murmushi tace "ka zamo min ɗa Qasin bana son ka bani kunya mun riga mun kate magana da babanka kuma na sanar a kauye amincewarsu kawai muke jira mansura zaɓinka ce Qasin kasan ko kaɗan bana son aurenta amman na hakura saboda ka samu farinciki dan na fahimci kana sonta sosai tho nima inson ka farantamin ka auri maryam"
baice mata komai ba ya sauke ajiyar zuciya ya fice.
*©Khadeeja Candy*
candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
*32*
*_K'auye..._*
taliya É—aya É—aya Mairo take É—auka tana kaiwa baki tana kallon Halilu Da Shima Taliyar Yake Ci Tana Dariya,
"wai lafiyarki mairo mikike dariya haka?"
Gwaggo ta tambaya cikin dariyar Mairo tace "Halilu ne yake bani dariya"
É—agowa yayi ya kalleta "dariyar mie nake baki mairo?"
nan ta ɓata fuska "ni dan Allah ku daina cemun mairo nan a birni fa maryam ake cewa yafi daɗi"
Gwaggo tayo dariya "lallai mairo yanzu fa an waye ko É—an zuwan nan da kikayi tho ai nan k'auye duk mai suna maryam mairo ake ce masa"
"ni dai gaskiya ku daina cemun mairo haka fa jiya su hawwa damary suka rika cemun mairo duk naji haushi"
Gwaggo tace "lallai xuwa birni yayi miki daÉ—i mairo an fara chanjawa ga kiba ga fari ni har maganarki naji ta fara chanjawa"
"ai dole Gwaggo kullum fa da nama muke karya wa da rana ma muci da dare ma haka ga kwai ga madara ga komai na daÉ—i ai dole nayi kiba"
wani guntun tsaki Halilu yaja "Gwaggo sai kace marar ido yanxu dan Allah ina kibar da mairo tayi nan daman can ai tanada É—an jikinta saida kice tayi fari da É—an girma koshi ba sosai ba"
leme baki Gwaggo tayi "ai kai daman ba son kake a ambaci abun alkharin taba"
murmushi yayi ya É—auke kai
Mairo ta watsa masa harara tace "aiko Halilu duk wadda ya gannin sai yace nayi kyau nayi fari nayi kiba"
Gwaggo tace "ke fita harkarsa ai shi haka yake baya kaunar a ambaceki da alkhari saidai abunds zaisa ya rika dukanki yana shuri kamar an aiko shi"
mairo tace "aiko Gwaggo kinga É—ana je can ba duka ba komai"
ta karasa maganar tana yiwa Halilu gwalo,
hartatarar ta yayi "dan Allah gafara can ai bazaki koma ba"
"ai wlh sai na koma da hutun mu ya kare zan koma birni na barka nan dan yaro"
kwafa yayi "gani kike kamar wasa nake ko tho bari ki gani bazaki koma ba kowa yayi miki tsaye"
ganin da gaske yake yasa Gwaggo ta kallonshi tace "kamar ya bazata koma ba?"
"babu komai kawai dai bazata koma ba"
"koma warta aiko yanzu ma take dan mai dalilice za'ayi sai in abunda ake son k'ullawa bai yiyu ba kuma bama fatar haka"
ɓata fuska Halilu yayi "tho karma ku soma Gwaggo wannan haɗin da kuke son yi ba zaifa haɗu ba"
Gwaggo ta leme baki "sannu baba ba zai yiyu ba tunda kai ka haifeta wai miyasa baka son mairo ne Halilu? mita tare maka?"
"Gwaggo ba wai bana son cigaban mairo bane ko kaɗan babu wannan a zuciyata hasalima nafi kowa son cigabanta amman Gwaggo ina son ki duba wannan lamarin da kuke son haɗawa kwata² bashi da wata ma'ana"
rike baki Gwaggo tayi "bashi da ma'ana kamar ya nifa ban gane inda ka dosa ba?"
matsowa yayi kusa da ita ya sassauta murya "dan Allah Gwaggo karki yarda da abun nan dasu momi suke son hadawa wata kila ma wata cutace zasuyi ya za ace kamar mairo Qasin ya aure ta haba Gwaggo ki duba fa"
Gwaggo tace "ban fa gane maka ba Halilu ka fito fili kamun bayani yadda zan fahimta mana mi kake nufi ne?"
"Gwaggo taya za ace kamar Qasin yace yana son mairo? mairo tashin yaushe ce kuma yar kauye yaushe mairo tayi wayewar da har zaice yana sonta shifa digirine dashi kuma mai kuÉ—i É—an birni.
kuma fa har yana da mata haba Gwaggo ki duba fa"
"tho in banda abunka Halilu minene aciki Qasin ɗan'uwanta ne ka kuma san inda wani abun cutane babu yadda za ayi babansa da mamarsa su amince har suzo tambayar in an basu kuma fa muma abunda muke nemane ya samu tunda kafi kowa sanin abunda uan garinnan suke cewa anki ayiwa mairo aure an kaita birin minene² kananan maganganu anyi kara anyi ice tho yanxu dan an bashi aurenta ai ba wani abun bane tunda ko ba shiba dole ne ai ne ayi mata aure"
"th tunda har haka ne ai kinga kara ma a aura mata wani É—in ko É—an gujewa masu cewa dan kwaÉ—ayi aka kaita birni kinga yanxu ai sai su kara cewa wani abun in aka haÉ—a auren"
Gwaggo tace "babu fa abunda zai sa mu fasa haÉ—a auren nan duk kuma uban da bai zagemu ba bai haihuba dan an zagemu zagin lake mana zaiyine maganar banza"
da tsaki Gwaggo ta karasa maganar cike da bachin rai.
Mairo ta aje kwanon abincin ta matsa kusa dasu tana musu kallon rashin fahimta tace "mi kuke yiwa faÉ—a Gwaggo?"
tashi halilu yayi tsaye fuskarsa babu yabo ba fallasa yace "aure za'ayi miki mairo Qasin za'a aura miki"
da sauri ta nuna kanta tana kallon Gwaggo "ni?"
"eh ke aure za ayi miki mairo ai kinsan kin kai munzalin aure ai"
kamar ta fasa kuka tace "ni wlh Gwaggo bana son aure ni yar k'ank'anuwa dani za'ayi mun aure ga yan mata nan a birni manya dasu ba ayi musu aure ba sai ni"
hannunta Gwaggo ta riko ta zaunar da ita kusa da ita "mairo nan kauye ne ba birni ba kuma kinga mutane sai gulma suke suna faÉ—in anki yi miki aure"
"tho ni ina ruwana dasu nidai ma bana son hutun na fasa a mayarda ni gurin momi"
halilu yace "momi itace ta kawo wannan shawarar tace a aura miki Qasin"
shiru mairo tayi tana tunani, Gwaggo tace "karki ji komai mairo alkharine ake nema miki ba sharri ba kinga ma sai kiyi ta zamanki can birni kina yin yadda kike so, ko bakyaso?"
kai ta É—aga "ina so Gwaggo amman nidai ina jin tsoro"
idonta cike da hawaye ta ke maganar.
nan Gwaggo ta shiga tallaɓata tana kwantar mata da hankali
ido halilu ya tsura mata kamin ya sauke ajiyar zuciya ya fice.
'''*****'''
"dan Allah Momi ku nemawa Nura admission a A.B.U Zaria nidai ganibnake kamar can yafi"
Usaman ne ke maganar yana kallon Momi dake zaune saman tree-setter tana cin abinci,
Momi saida tasha ruwa sannan tace "ni bana ra'ayin A B U nan nafi son State University nan da aka buÉ—a ance ana karatu sosai kuma kaga nan garin ne hankalina yafi kwanciya iddan yayana suna kusa dani"
dariya yayi yace "momi ni da nake É—an fodio fa?"
"eh tho ai duka É—aya ne tun cikin sokoto take nidai bana son ayi nesa ne kawai irin gari haka ko wata kasa"
"amman momi ai kinga yaya ba nan yayi karatu ba shi har kasar ma ya bari"
kafin momi ta bashi amsa aka turo kofar parlour,
juyowa sukayi suna kallon Yarima daya shigo cikin wata bugaggiyar shadda sky blue.
ba tare da yayi sallama ba ya nufo gurinda suke zauna hannayensa sanye cikin aljihu yana tsosar baki kamar mai shan sweet.
*©Khadeeja Candy*
candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
*33*
Saida ya kusa kawowa kusa dasu sannan yayi sallama Momi ta amsa mishi da Usman,
kujerar dake kusa da Momi ya zauna yana yiwa Usman wani kallon raini ciki² Usman ya gaisheshi, ba tare daya amsa ba ya kalli Momi yace "sannu Momi an wuni lafiya?"
da far'ah Momi ta amsa masa "lafiya kalau Yarima kana nan?"
"no shekaran jiya na dawo dan naje Uk ne tun ranar da muka fita da Maryam"
"Allah sarki tho ya gida ya da kowa²?"
shiru ya É—anyi kamin ya bata "Lafiya kalau kowa yake"
juyarda fuskarsa yayi gurin tv, Momi ta cigaba da cin abincinta Usman ya tashi ya fice,
daf da zata cinye ya juyo ya kalleta "Momi ina Maryam?"
"Maryam ta tafi Kauye kasan anyi hutu ta tafi ganin gida"
shiru yayi ya ɗan ɓata fuska "yau kwananta 6 tun ranar asabar taje sai kuma hutu ya kare"
gefen fuskarsa ya shafa "oh Momi nako yi mata tsaba na É—auka tana nan"
"da yake baka cikin garin shiyasa baka sani ba"
tashi yayi tsaye yana murzar zabban hannunsa "ni zan wuce kuma Hajiya tace na faÉ—a miki tana son ganinki"
Momi ta kalleshi "lafiya dai ko?" wani murmushi yayi "yo ni momi ya za ayi na sani sai dai kinje zakiji"
"tho shikenan sai gobe zanzo insha Allahu ka gaisheta"
kai kawai ya É—aga mata ya fice yana kallon upstairs,
*_7:12pm..._*
"Assalamu Alaikum"
a hankali momi ta ɗago kai ta kalleshi tare da amsawa ciki² "Amin wa'alaikassalam"
suku² ya nufi kujera ya zauna kansa a kasa yace "Momi an wuni lafiya?" momi fuska babu tabo ba fallasa tace "lafiya kalau ya iyali?"
saida ya haÉ—eye yawu sannan ya amsa mata "lafiya kalau Momi"
gyaran murya momi tayi tace "Qasin in baka aikin komai inason ka kaini gidansu Hajiya yanzu ta aiko tana nemana ɗazu naso na ɓari har gobe kuma dai hankalina bai kwantaba nafi son yanje naji koma minene"
"wace Hajiyar Momi?"
kallon mamaki momi tayi masa "Auntie Hasana mana"
"Yarima yazo nan ne?"
"eh shine ya faÉ—a min ai"
tashi yayi tsaye yana faÉ—in "bari na kiran Siraj sai ya kaiki akwai inda nake son zuwa"
haɗe fuska momi tayi cikin tsawa tace "babu wani gurin da zakaje Qasin kawai ka fito fili yace baka son zuwa gidan iya isa ba sai kayi min nuku² ba"
lumshe ido yayi ya dafa kai "oh Momi baki fahimceni ba-"
hannun Momi ta ɗaga mishi tana tari numfashinshi "na fahimceka Qasin na san abunda kake nufi amman karka amta wannan Yarima ɗan'uwanka ne kuma inason ka sani bazan taɓa yardar maka ba ka ɗauki kiyayyah ka ɗora masa babu wani dalili nayin haka koba ɗan uwanka bane ai ba abun kwaraine bane ballantana ɗan uwa mi yasa baka da tunanine in kaje gidansu Yarima faɗuwa kayi shi da yake tako kafarsa har nan gurina fa,
ya fika sanin muhimmancin yan'uwan taka Qasin ya fika iya siyasa dan ko kiyayyah ce Yarima bai taɓa fitowa fili ya nuna maka ba ballantana ni har a zuciyata nasan Yarima baya kiyayyah dakai"
komawa yayi ya zauna ya kama hannayen Momi ya rike cikin sanyayyiyar murya ya shiga mata magana "bana kishin Yarima ko kaɗan Momi bana kishinsa kawai dai halayensa ne banaso kuma momi bazan taɓa yarda na faɗa a gadar zaren da yake kullamin ba momi kinfi kowa sannin waye Yarima kinsan duk inda ya ganni ko yaga wani dags cikin familinmu sai ya musguna masa kodai ya faɗa masa gana mara daɗi ko kuma yayi masa wani abun na bachin rai ni kuma na tsani haka momi saboda babu abunda Yarima zai nuna min
sannan momi kin hana na rama momi kince Yarima ɗan'uwana ne nasani shiyasa ma nake ɗaga masa kafa amman momi kinsan Maryam ma yar'uwata ce ko kuma duk abunda ya sameta ya sameni bazan taɓa mantawa ba"
lumshe ido momi tayi ta sauke ajiyar zuciya a ranta tana _...ba zaka taɓa ganewa ba Qasin..._
can ta buÉ—e idon ta kalleshi tace "naji zaka iya tafiya"
"momi ki shirya na kaiki mana"
"a'a sai goben kafin ka fita"
"momi kar kimun rashin fahimta bana nuf-"
numfashinsa ta tara tare da tashi tsaye "a a Qasin na fahimtace ka karka damu gobe zaka kaini"
bata tsaya jiran mi zai ce mata ba ta nufi stairs,
Momi na shiga ta tararda wayarta saman madubi tana ringing da sauri ta karasa ta É—auka Hajiya ta gani a screen kamin ta É—anna picking ta kara a kunne,
_"Amin wa'alaikissalam Hajiya ya gida?"_
banji mi akace mata ba na daiji tace _"eh ina gida lafiya dai?"_
_"tho sakin iso"_
sauke wayar tayi gabanta na É—an faÉ—uwa tana mamakin abunda yasa Hajiya take son ganinta haka.
*_© Khadeeja Candy_*
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
*34*
*_9:35pm..._*
Hajiya ta iso gidan tun kamin ta fito mota momi ta fito ta tareta cike da far'ah, rumgume juna sukayi kowane na dariya suka shigo parlour,
momi bata barta ta zauna ba suka nufi bedroom drinks kala² momi ta jere mata da kayan ciye² bayan ta zauna suka ɗauko firar yaushe gamo,
can momi ta kalli Hajiya tace "nifa Hajiya ina mamakin zuwan nan naki haka kawai"
murmushi Hajiya tayi "ba zuwan haka kawai bane maman Nura É—azu ai nayiwa Yusuf sako ya faÉ—a min kince sai gobe zaki zo shiyasa ni kuma na kasa hakura har goben nace bari nazo yau"
"nima ai na tashi zuwa É—azun bayan magriba sai kuma nace bari dai na bari har goben lafiya dai ko?"
Hajiya ta dafa momi "lafiya kalau É—anki ne yaga wata yarinya yace yana so"
farincikine ya bayayyana a fuskar momi duk da faÉ—uwar da gaban ta yake "masha Allahu ba dai Yarima ba?"
"shifa ai nima farinciki kasa ɓuyiwa yayi a gareni kuma yace nazo na tambaya masa shine fa nace tho ya kira min daya faɗa min kince sai gobe ni kuma na kasa hakuri"
momi tace "ai dole abunda aka ta jira shekara da shekaru nima ai na jidaÉ—i sosai"
Hajiya tace "yace yarinyar tana nan gidan ke kike rikonta yace mun sunanta maryam"
wani irin gaÉ—uwa gaban momi ya karayi shiru momi ta É—anyi kamin ta haÉ—e yawu tace "maryam Hajiya?"
yanayn yadda tayi maganar yasa Hajiya ta kalleta "eh ita koda matsala ne?"
"a'a ba wata matsala kawai dai naga yarinyar karama ce dan bazata wuce 13 ba"
murmushi Hajiya tayi "kar wannan ya dameki ys faÉ—a min daman karamar yarinyace har yake cemin kiyonta yake sai ta girma tukuna tho shekaran jiya nida Mai Martaba muka sashi gaba muna masa faÉ—a mishine fa yake faÉ—a min shi babu yarinyar da yakeso inba ita ba sai kinga yadda mahaifinshi yayi murna"
momi jiki ba kwari tayi murmushi tace "ai dole kan abunda kowa yske mafarki nimaai nayi farinciki"
Hajiya tace "ina kika sani nima daÉ—in nake ji kamar me shine babbah yanzu kingaya kamata ace yanzu yayo aure kanensa na biu fa yanzu za ayiwa aure shi yasa ma ai abun ya damu mai martaba yasa yayi masa haka dan cewa yayi im bashi wadda yake so tho shi zai mema masa duk wadda yaga dama shine fa sai ya faÉ—a mana ita kaÉ—ai kawai yake so dafa duk akayi magana sai yace shi bai samu wadda yake so ba kinga sai yanxu Allah yayi"
ajiyar zuciya Momi tace "kinsan komai yana da lokaci wata kila sai yanzu Allah ya kaddaro za ayi saida fs hajiya wani hanzari ba gudu ba"
kallonta Hajiya tayi "ina jinki minene?"
"its maryam É—in yar kauye ce kuma ba tsyi wani karatu ba dan zuwannan ma da nayi da ita Qasin ya sata makaranta"
"kar wannan ya dameki duk ba matsala bace tho da dai har yace yana so ai duka É—sys muke gurin Allah babu wadda yafi wani"
lumshe ido momi tayi ta buÉ—e ta kallii hajiya tace "shikenan zanje kauye sai nayi masa magana dan yarinyar ma tana can hutun na da akayi sai na kaita ganin gida"
"wai yar insce?"
"wlh kanwar su Qasin ce yar kanne mahaifinsu da mukaje kauye sai muka zo da ita......"
"tho yanzu dai kije kauyen ki nema masa"
cikin karfin hali momi tace "insha Allah haka za ayi"
hajiya tace "ki faÉ—awa mai gidanki dan ni cikin satin nan nake son aje inma ta kama har dani duk sai muje koda da Mai Martaba ne"
"a a ni ma ai ns isa na nema masa ba sai kunjeba inma dolene kuje ai sai na faÉ—a muku amman sai in babansu ya dawo dan yayi tafiya"
murmushin jindaÉ—i Hajiya tayi "ai ba matsala bace Allah ya dawo dashi lafiya ana nan anata harkokin business É—in ko? ba hutu"
"eh ai shi koyaushe baya samum zama gida neman kuɗi kawai aka sawa gaba ba a nan ba a can zamansa gida kaɗsƙan ne kuma a koma"
"tho mai sa akan ai daman bai gaji zamaba musamman in akwai iyali"
haka momi tayi ta smsa mata firarda suke kamar marar lafiya sai kusan 11 da wani abu ta bar gidan,
daren momi kasa bachi tayi tana tunsnin yadda zata billowa lamarin, har a ranta Qasin take son maryam ta aura sai kuma yanzu dabo biu ziciyarta take mata akan maganar da hajiya tazo da ita dan Hajiya ba tada wani farinciki sai na yarima taya zata yarda Qasin ya aureta ga yarima in kuma ta yarda Yarima ya aureta rigima ce ba yar kaÉ—an,
kai ta dake ta zauna gefen gado _...oh ni mi yasa ban faÉ—awa hajiya anyiwa maryam miji ba..._ sai yanzu take jin haushin,
_...amman kuma in har taji Qasin ne ai zata iya cewa ya barwa Yarima kuma gashi har na rig na faɗa a kauye Qasin yana sonta yanzu kums si sai su ga ɓayi musu magana biu..._ busarda iskar bakinta tayi ta lumshe ido.
*_© Khadeeja Candy_*
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
*35*
*_washe gari..._*
_10:47am_ Qasin ya shigo part Äin momi zauna ya tararda ita a dining area,
a kujerar daya saba zama ya zauna yana kallonta "momi ina kwana?"
a hankali ta kalleshi kana ganin fuskarsa kasam tana Äauke da damuwa "lafiya kalau ka tashi?"
"eh momi ke kaÄai kike karyawa?"
"a a duk sun karya sun tafi makaranta ne kai ka daina karyawa nan ko?"
Äauke fuska yayi ya Äauko wani zancen "momi ya maganar tafiyar so nake na kaiki sannan na wuce dan yau zan wuni busy"
tea momi ta k'urɓa tace "ai tazo tun jiya"
kallon mamaki yayi mata "nan gidan laifiya dai ko?"
"lafiya kalau wata magana mukayi"
"tame momi?"
"sirrice"
"kamarbya momi nasan duk abunda zai sa Hajiya tazo gidanna ba karami bane dan Allah ki faÉ—a min minene kodai wani abun aka cene?"
momi bata ce masa komai ba ta tsura masa har tsargu ya tashi dan kanshi ya nufi kofa da tunane²
"Qasin..." murya kasa² momi ta kirashi da sairi ya juyo ya dawo "gani momi"
"ka faÉ—awa matar maganar aurenka?"
kasa yayi da kansa ya daÉ—e kamin ya bata amsa "a a momi ina tsoron abunda zai biyo baya ne kinsan ba fahimta zatayi ba"
ajiyar zuciya momi ta saike tace "yayi kyau zaka iya tafiya"
kallonta yayi kamar yace wani abu sai kuma ya juya ya fice,
dafe kai momi tayi tana nemawa kanta mafita sa kusan minti 30 haka sannan ta tashi ta nufi stairs,
''' * * * '''
kusan isha'i Siraj ya shigo part Äin momi ganin ba kowa parlour yasa kai tsaye ya wuce Äakinta, zaune ya tararda ita ta rafka uban tagumi tana kallon windo,
"lafiya momi?"
a sanyaye ta kalleshi da murmushin karfin hali "lafiya kalau Siraj ka shigo"
yana k'ok'arin zaunawa kusa da ita yace "momi gaskiya ba lafiya ba dan tunda safe naga damuwa a fuskarki akwai abunda yake damunki momi"
batace komai ba ta sauke ajiyar zuciya ganin haka yasa yace "barin kashi a ciki baya maganin yunwa momi babu kuma wadda ya dace ki fafawsa sirrinki irina hankalina bazai taɓa kwanciya ba momi matukar naki bai kwanta ba dan Allah ki faɗamin abunda ƴake damunki"
kallonshi tayi "kona faÉ—a maka Siraj ba magani zaka mun ba"
"naji nidai dan Allah ki faÉ—amin momi indai ba so kike nima na shiga damuwa ba"
momi ba dan taso ba ta fayyace masa komai,
Siraj ya daÄe yana jinjina al'amarin kamin ya kalleta yace "yanzu momi mi kike gani shine fita?"
"nima ban saniba Siraj ita nake ta nema na kuma kasa samu"
Siraj yace "tho momi ga wata shawara..."
kallonshi momi tayi "ina jinka"
"momi mi zai hana kik'i yarda Qasin ko Yarima ya aureta"
"saboda mi?"
juyo yayi yadda zata fuskanceshi da kyau yace "kinga yanzu in kika bari Qasin ya aureta Yarima zai yita ganin laifinki shida mahaifiyarshi kuma otama zata taga kin mata cin fuska kinki bari Yarima ya aure kika bawa Qasin ya yaje ɗanki kimsan Hajiya bata tada wani Farinciki sai na Yarima tunda shi kaɗai ta haifa zata iya ɓatawala da kowa akansa kinga in kika mata haka ba zata taɓa mantawa dake ba kuma kinga zata ga baki tashi aurawa Qasin ita ba har saida Yarima ya ganeta yace yana so tunda baki riga kin faɗa mata kin nema masa ita ba kuma itama ba ganewa zata yiba sannan kinga shima yaya sai naga kamar bayason maryam sosai kuma kinga yana kaunar matarsa ko auren maryam yayi za suyita samun matsala,
in kuma kika yarda Yarima ya aureta nan ma baki tsira ba dan kinsan yaya bazai taɓa yarda ba kuma nima bazan yarda ki aura masa ita ba dan zai iya musguna mata kodam ganin daga falinmu take kuma kodan muji haushi zai iya yi mata hakan koda yana sonta dan kinsan halin Yarima ishesshen kanshine ko yanzu baki san dalilin da yasa yace sai ita kaɗai yake so ba tunda akwai yan mata da yawa a garinnna kuma suna sonsa dan babu wadda zaice yana so ta kishi kodan dukiyarsa balle ga mulki ga kyau amman ya nace shi sai maryam bakisan abunda yake shiryawa ba kuma kinga duk ya cuceta mudai ba kyalewa zamuyiba kauye kuma dake za suyi kuka dan haka ni abunda nake ganin mafita shine kawai ki bari can kauye ayi mata aurenta duk wadda suka ga damar haɗa shi da ita sai su aura mata"
gyara zama momi tayi tana nazarin kalamansa,
"ka kawo shawara Siraj amman kuma har yanzu da saura in har haka ta faru ita hajiya mi zan ce mata suma kauye dana riga nace Qasin na sonta ya zance musu har yanzu da sauran rina a kaba"
murmushi yayi "no momi kawai ki samu baba ku tattauna sai a warwar zancen auren Qasin ni da kaina zan kaiki kauye in yaso sai kice musu daman bakiyi shawara da Qasin ba kuma yanzu yaji bai amintaba kuma matarsa yar matsiface dan haka kina tsoron abunda zaije ya dawo dan haka a bar zancen aure kawai duk wadda suka dama su aura mata ita kuma hajiya in kika dawo saiki faÉ—a mata an riga anyiwa maryam miji alkawarine tun tana karama dan haka iyaye sunce bazasu tada ba koda tace ki kaita kauyen karki yarda kikaita dan zata iya zuwa ta rokesu ta nuna musu kuÉ—in koma shi Yarima da kanshi dan a yarda a aura mishi kuma kinga ko aura mishi ita akayi wahala zata sha dan kinga karamar yarinya ce sannan ba wani tsayawa zai kikayi yana bata hakkinta ba kuma zai iya ganinta tankar kaunarsa koma yarsa da ta masa abu ya daketa koma karki faÉ—a masu har sai an É—aura aure, kawai momi wannan shine abunda nafa ya dace kiyi"
murmushin jindaÄi momi tayi ta shafa kansa "ka kawo shawara Siraj haka zanyi Allah yayi maka Albarka"
shima murmushin yayi yace "amin momi shikenan damuwa ta wuce ko?"
kai momi ta É—aga masa ya tashi tsaye yana faÉ—in "tho muje kici abinci dan nasan bakici abincin dare ba"
"jeka gani na zuwa"
"owk"
juyawa yayi ya fice cike da farinciki.
*_©Khadeeja Candy_*
candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
*36*
A waya Momi ta kira Abbah sukayi magana dan kasa hak'uri tayi ganin ta samu mafita sosai yaso ta bari har ya dawo suje tare amman tak'i dan yadda Hajiya ta matsa mata kullum cikin kiran wayarta take,
ranar alhamis tun da safe Siraj ya fitarda motar da zasu shiga suna karyawa suka kama hanya,
*_K'auye..._*
ajiyar zuciya Gwaggo ta sauke tace "wannan magana ai kamar anyi sara akan gaɓa ne"
Momi tayi mata kallon rashin fahimta "mi kike nufi wani abun ne?"
Gwaggo tace "akan maganar nan ne wai Halilu yanzu ya fito wai sonta yake bai tashi magana ba saida yaga anyi wannan maganar kiji mun rainin hankali"
Momi ta rik'e baki "yanzu Halilun ne yace haka?"
Gwaggo tace "ai kum` bAki san wan) abun haushi b� wlh tsoho yaYi tsaye shi sai Ialilu zai aurasa"
"amman tsoho"yaji da Qasin ne ake sof`haɗa(a�2en?"
"wlh yaja kinsan matsalapda aka samu? 9a rigani zuwa yayi magaNa dan oi a y`dda na yanKe sai an ȗan kwanc biu kusaf zata komc sannin nsyi maganar kin'a koma mhnene amsar in iukaje sai kuji aiko yana j�n haka saI kawci`yajg ya fcɗaWa tsoho wai shi softa yake ni kuma da naji haka sci naje nima nace ga abunda kike �e aiko tsoho k'hn yarda yayi"ya dinga gani� laifi ya�e nice nake son juyarda abun haka ai da kunwo shi!zaku samu kuyiua magana ba niba wai shi daman yana son {a haɗasu amman yana �soh/ cmmao yanzu tunda`har haka ta feru shm+ena ti kwana gidan sauki shi Halilu zai bawa babu yadda banyi ba amman yayi tsaye shi lallai sai Hadilu balle nasan ya kwashi k
arya da gasjiye ya faÉ—a masa"
Momi tace "tho inji. ita Maryam É—in tana sonsh)"
2ehmmm aifa kinJi inda matsala0 take nan itakan tayi tsaye wlh bata s'nshi yanxu hAka in kikayi mata maganar kuka zatayi"
"dank'ari aiko akwai matsala tho ba'a faÉ—awa tsoho bata soba?"
"hmm ai sai kiyi abunda tsoho yake nema ai shine ya tsaya kai da fata wai ko bata so sai anyi shi daman ya yanke shawarar aurarda ita dan ya gaji da tsegunmi mutane"
Momi tace "amman kuma Gwaggo ai naga kamar shi Halilun bashi da wata matsala"
"aiko shine da matsa nifa na rik'ashi tun yana k'arami yanzu haka ganin da kike masa baya noma tho É—sn k'auye in baiyi noma ba mi zaiyi sannan babu sana'ah babu aikin fari babu ma bak'i in kinmai magana yace shi karatu zai bazai iya rayuwar k'auye ba kuma karatun nan bai wani yi zurfi ba balle ace aiki kuma ance aikin nan fa ko a can birni wahala yake tho ina wani abun k'aurai tunda babu abun ci da mata"
Momi ta jinjina kai zatayi magana taji an rumgumeta da karfi,
dariya tayi jin Mairo ce tace "tun É—azu mukazo ban ganki kiba kina can gurin yawo ko?"
dariya Mairo tayi ta k'ara rumgume Momi "a'a Momi tunda kukazo naga Siraj yaje dani yawo sai yanzu muka dawo Momi nayi mesage É—inki"
"missed ake cewa yar boko"
Gwaggo tayi dariya tace "haka muke da ita abu kaÉ—an sai turanci ita yar boko"
Momi ta juyo da ita ta zauna daidai "ina kukaje yawo wato kings shigowa amman da kiks gs Siraj sai kiks shareni ko?"
"a'a Momi yawo fa mukaje da mota ko'ina sai kallonmu ake"
ta karasa maganar tana wani marmarÉ—en ido,
Gwaggo tace "kin samu abunda kikeso ko kiyiwa mutane kuri tho ina kika baroshi ko ya sake fitane?"
"a'a waya yake yi yanzu zai shigo"
kallon Momi tayi "Momi kinci abinci?"
da murmushi Momi tace "a'a Gwaggo ki bata bamu ba amarya"
nan da nan Mairo ta ɓata fuska kamar ta fasa kuka "Momi bana so ki daina"
Momi ta dafata "ai dole kiso kedai tashi ki É—auko mana abincin"
matsawa tayi gefen ta takure kanta ta haÉ—e rai, Siraj na shigowa ta rushe da kuka.
da sauri ya karaso kusa da ita "lafiya mi akayi mata"
Momi tace "wai dan nace mata amarya shine take kuka"
"kamar ya auren za'ayi mata ne?"
"eh Halilu za'a aura mata wai ita kuma bata sonshi"
murmushi yayi ya shiga tallaɓata yana bata hak'uri, daker ya samu tayi shiru ta tashi ta nufi ɗaki,
gurinsu Momi ya nufo yana faÉ—in "wai yanxu daga yin magana har anjuyarda abun zuwa ga Halilu?"
kamin ya zauna Momi tace "a'a daman rigimar da aketayi kenan wai shi sonta yake...................."
nan Momi ta labarta masa komai,
Sosai Siraj yayi mamaki ya kalli Gwaggo yace "mi yasa bakison auren Gwaggo? Halilu bashida hallin k'waraine hala?"
Gwaggo tace "a' wlh yana dashi nina rik'ashi tun yana k'arami gaskiya bashi da wani mugun hali"
Siraj yace "tho mi yasa bakison ya auri Maryam ni aganina ba wani abu bane kinga shima ai É—an'uwane kuma duk duniya bana ganin akwai wadda ya dace ya aureta sama da shi kefa kika reneshi Gwaggo ya tashi a hannunki yanzu dan yace yana son Maryam in kikak'i baki ganin xai iya shiga damuwa? ni aganina koda ahi baiyi magana ba kema ya kamata ki haÉ—asu ballantana har yayi gaskiya Gwaggo in kikak'i goya masa baya baki masa adalciba kuma kin nuna masa ke bake kka hafeshi ba"
shiru Gwaggo tayi tana nazarin maganar.
"amman fa Sirajo ita Mairo bata sonshi fa"
"karma ki kawo wannan Gwaggo Maryam k'aramar yarinyace bata san soba ko a birni ksmar Maryam za'a iya aura mata wadda akaga dama balle k'auye kune kuke k'ara sa tana cewa bata sonshi kawai kibar ma wannan zancen inta girma gidansa a babu zance k'i"
dariya Gwaggo tayi "kuma fa haka ne Sirajo da maganar ka Allah dai ya zaɓa mana abunda yafi zama alkhari"
duk sukace 'amin'
Siraj yace "amman dai Gwaggo ba zaku raba ta da karantunta ba ko?"
Gwaggo ta leme baki "karatu kan ai yasha kashi tunda in an mata aure ai tarewa zatayi kaga ko babu zancen karatu"
"amman gaskiya Gwaggo ku barta tayi makarantar ta koda anyi auren ne inta k'are sai ta cigaba da zamanta na aure"
ido Gwaggo ta nuna masa "kaga nawa ni yanzu kuma fa ako auren akayi nan zatayi ta zama dan bashida gurin ajeta sai yayi gina"
shiru Siraj yayi ya nuce kai bai sake magana ba,
can Momi tace "wai ins wadda taje É—auko mana abinci?"
Gwaggo tace "aifa sai kiyi bafa zata É—auko ba da nan fushine take dake"
Momi tayi dariya "in banda abinki Maryam daga faÉ—ar gaskiya sai cibi ya zama k'ari"
Gwaggo ta tashi ta nufi É—aki tana faÉ—in "bari na É—auko miki indai wannan ce saiki shekara"
tashi Siraj yayi "ni bari naje bakin kasuwa kamin ki k'are cin abinci"
"kai ba zaka ciba?"
"kai Momi kinsan ni kan bazan iya cin abincin nan ba bari dai naje can ko zan samu abunda zanci"
kai Momi ta É—aga mishi ya saka hannayensa aljihu ya fice.
*_©Khadeeja Candy_*
candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
*37*
kai tsaye Siraj bakin kasuwa ya nufa daman É—azu da suka wuce ya hango gurinda Halilu yake zaune,
Halilu na hangoshi ya ɓata fuska aransa yana _babu wani magiya da zaka mun na barma ku ita wlh boko dai nima nayi dan haka baka fini wayeba_,
Siraj ya k'arasowa kusa dashi yayi masa sallama tare da mik'a masa hannu, ciki² ya karɓa ya juyarda fuska,
murmushi Siraj yayi ya zauna saman teburin da yake zaune yana faÉ—in "kai kaÉ—ai kake zaune?"
"eh ina hutawane"
Siraj ya kalleshi "Halilu ka saki jikinka dani bana nufin cutarda kai ko cilas taka yin abunda baka tashi ba ni shawara nazo na baka kuma inason kayi nazari ka É—auki shawarar karka kalleni a matsayen É—an'uwan Qasin inason ka kalleni a matsayin É—an'uwanka"
juyowa Halilu yayi ya kalleshi "wace shawarace?"
dafashi Siraj yayi yace "naji ance ka fito kana son Maryam ita kuma bata sonka kuma kaga yayana ma yana sonta banci shi kuma akwai wadda yake sonta can birni sannan naji ance baka kada sana'ah ba kama da gurin ajeta tho kuma yanzu naji tana zance sai ta bimu birni tho abunda nake so da kai shine kayi sauri ka matsa a É—aura muku aure koda baka da gurin ajeta É—in dan in kayi sake tho rasata zakayi kaga in ka aureta koda tace sai taje birrin kana iya kyaleta taje tayi karatunta amman fa da aurenka kaga kamin ta k'are kai kuma ka samu aiki kayi gidan ajeta ni zan iya taimaka maka ka cigaba da karatunka amman karka yarda wani sati yayi ba'a É—aura maka aure da ita ba"
ido Halilu ya tsurawa Siraj yana son tantance abunda yake faÉ—a,
_ta yaya zai yi masa wannan shawarar bayan shi É—an'uwan Qasin ne miyasa yake son shi ya aureta sama da Qasin can wata zuciyar tace amman kuma fa gaskiya ya faÉ—a min tunda banida gurin ajeta balle abun ciyarda ita kuma nasan yanzu Mairo bazata yarda ta zauna k'auyen nan ba tunda nama ji ta fara zancen sai ta bisu kuma gashi har yace zai taimaka min na k'arasa karatuna inhar da gaske yake kuma fa inna aureta na huta koda taje can birrin wani ya ganta yana so na dai riga na aureta......_
dafashi da Siraj yayi yasashi dawowa daga duniyar tunanin daya tafi,
Siraj yace "ka yarda da shawarata Halilu shine kawai mafita a gareka"
ajiyar zuciyar Halilu ya sauke yace "maganganunka abun dubawa ne Siraj saidai na kasa ganewa taya zaka goya mun baya na auri Mairo bayan yayanka ma yana sonta?"
murmushi Siraj yayi yace "shiyasa tun farko nace karka ɗaukeni a'matsayen ɗan'uwan Siraj ka ɗaukeni a'matsayin ɗan'uwanka Halilu bana nufi cuta a gareka nayi haka ne saboda shi Qasin yana da mata sannan kuma zuwan da Maryam tayi birni ne ya ganta yace yana so saɓanin kai da tun tana k'arama kake sonta ko ɗazu na faɗawa Gwaggo babu wadda ya dace da Maryam irinka,
Halilu nifa bance dole ka É—auki shawarta ba kawai in tayi maka shikenan in kuma batayi maka ba duk É—aya ne"
ya karasa maganar tare da tashi tsaye. Hannu halilu ya mik'a masa "na gode sosai Siraj zanyi tunani a kai"
"nima na gode da bani lokacinka da kayi Allah ya shige mana gaba"
nan sukayi sallama Siraj ya nufo gida,
''' * * * '''
bakin k'ofa ya tararda Mairo zaune rik'e da É—an karenta tana zane a k'asa,
da murmushi ya fito motar ya nufota, saida ya kusa kawowa kusa da ita sannan ta É—ago ta kalleshi ta wani turo baki wai ita gamai fushi,
sai da ya zauna kusa da ita sannan yace "fushin mi kike Maryam?"
"wai Momi ce tace bazata je dani birni ba"
"tho ai hutunku bai k'areba kuma kinga aure za'ayi miki babu ma zancen komawa birni gaba É—aya rayuwarki ta dawo nan kenan"
da sauri ta kalleshi "ni wlh ba zan zauna ba kuma ni bana son aure wlh bana son halilu"
da kuka ta k'arasa maganar,
saida Siraj ya duba yaga babu mai kallonsu sannan yace "in baki shawara?"
kai ta É—aga mishi
yace "karki yarda a aura miki Halilu kinga É—an k'auyene kuma duk wani abun daÉ—i da kikasan kinaci da kin aureshi kin daina cinsa kenan kuma kings babu ke babu karatu babu zuwa birni nan zakiyi ta zama kina daka da zuwa daji kina É—ebo kara shikenan kinyi bankwana da jindaÉ—i muma ba zaki sake ganinmu ba har Momi"
k'ara fashewa tayi da kuka da sauri ya rufe mata baki yana kallon k'ofa "shinnnnn kar sujiki kina son na baki wata shawara?"
nan ma kan ta É—aga yace "koda an É—aura miki aure da Halilu karki yarda ki zauna kice ke gurin mu kikeso kiyi ta musu kuka kice kesai an barki kinyi karatu in kikayi haka nasan za'a iya barinki ki bimu amman inba haka ba shikenan ba zaki k'ara jindaÉ—i ba kinji"
cikin muryar kuka tace "tho Gwaggo zanyiwa ko tsoho?"
"dukansu har Halilu kice indai yana sonki yabarki kije kiyi ta musu kuka kina murje² in kikaga sunk'i yarda sai kice ke sai kin kashe kanki...."
maganar yake yana wani kalle² kamar wani munafiki,
ita ko sai kai take É—aga mishi, hannunta ya rik'o "Maryam kimin alk'awari komai akayi bazaki faÉ—a ni nace kiyi haka ba"
"nayi wlh bazan faÉ—a ba"
murmushi yayi "yauwa ai inma kika faɗa ɓatawa zanyi dake dan haka karki faɗawa kowa kinji share hawayenki"
hannu tasa tana share hawaye yana tayata saida ya goge mata fuska sannan ya rika hannunta suka shiga cikin gidan,
*_©Khadeeja Candy_*
candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
*38*
biye² Momi tayi dan duk inda wasu ɗangi suke na kusa saida takai Siraj,
da shine bai san dangi sosai ba sai kusan magariba suka dawo gidan Gwaggo danyi mata sallama, tana zaune tana tuki tuwo suka shigo Mairo na genta,
"Assalamu alaikum" Momi ce tayi sallamar Gwaggo ta amsa mata "amin wa'alaikumussalam ku wayannan sai yanzu?"
momi tace "tho ya muka iya Siraj ne ai ya tsayarda mu yanzu kan ai sai kama hanya"
"a'a zaku tsaya kuci abinci kan"
Siraj yace "a'a Gwaggo k'ara mu wuce kawai bason tuk'in nan na dare nake ba koma can ai munci abinci"
tashi Gwaggo tayi tana faÉ—in "kai ai da yayanka daman bason cin abincina kuke ba Allah dai ya kiyaye hanya"
dariya yayi ya ciro kuÉ—i aljihunshi ya mik'a mata "ga daishi a siye goro"
karɓa tayi tana godiya nan ya sake sa hannu ya ciro dubi kusan 5 ya mikawa Mairo, k'in karɓa tayi idonta suka ciko da kwallah "a'a nidai zan biku bama son nan"
hannun Momi ta rike ta fashe da kuka,
lallasarta Momi ta shigayi "haba Maryam ki bari har hutunku ya k'are sannan kinji kinga ko yanzu tsoho saida yayi ta mana masifa akanki kinga in mukaje dake faÉ—a zaiyi"
"nidai kije dani haka inaso Momi dan Allah karki bari"
risinawa Momi tayi ta dafata "tho ya isa daina kukan haka kinji ki tambaye Halilu in ya yarda sai na aiko a É—aukeki amman fa sai inya yarda da zarar ya yarda kisa a bugamin waya kawai zam aiko mota aje dake?"
lak'e kafaÉ—a tayi "a'a nidai kije dani yanzu dan Allah Momi"
kuka ta ringa rusawa tana k'asa tana sama duk sai Momi taji ba daɗi babu irin lallaɓar da basuyi mata ba amman ta k'iyin shiru,
har bakin k'ofa ta biyosu tana jan gyalen Momi, nan Siraj ya shiga lallaɓata shida Gwaggo ganin abun nata na gaskene, k'in daina kukan tayi nan idanuwan Momi suka koma kwallah. daker ta samu tayi musu sallama suka kama hanya,
'''*****'''
cikin dare suka iso gida bayan Siraj yayi parking Momi ta fito rai ba daÄi ta nufi part Äinta
palour ta tararda Qasin zaune yana kallon k'ofar data shigo, gyara zamansa yayi yana faÄin "sannu da zuwa Momi"
wani irin haushinshi Momi taji ciki² ta amsa mishi "yauwa sannu"
saman kujera ta zauna tana sauke gajiya, Qasin ya kalleta yace "Momi yau ina kukaje haka tun safe naga kun fita kuma sai yanzu ka kuka dawo lafiya dai ko?"
"lafiya kalau k'auye mukaje"
Siraj ne ya bashi amsa yana k'ok'arin zaunawa kusa,
Qasin yadda yaji gabanshi ya faÉ—i yaji bazai iya k'ara tambayasu wani abu ba tashi yayi yasa hannayensa aljihu yace "sleep tight Momi saida safe" bai tsaya jiran amsarta ba ya nufi k'ofa,
saida ya fice Siraj ya kalli Momi yace "gaskiya Momi Maryam taban tausayi sosai banji daÄin da muka barota ba"
wani guntun numfashi Momi taja tace "tho ya muka iya tunda haka suka zaɓa mata kuma kasan indai ba Halilu ya aminceba ba zasu bari muzo da ita ba"
"eh ai naga haka amman ya kamata a masa magana ya barta ta dawo nan kamin ya kammala shirye² kinga ta ɗan k'ara samu illimi"
"tho ai sai yaga dama tunda yanzu shi zai aureta"
taɓe baki yayi ya tashi yana faɗin "saida safe Momi"
"Allah ya tashemu lafiya nima ai bari na shiga ciki nayi sallah"
har zai fice Momi tace "amm.. Siraj gobe ma ka shirya muje gurin hajiya na mayar mata da amsa"
murmushi yayi yace "In'sha Allah" ya juya ya fice,
'''*** *** ***'''
*_3:47pm..._*
wani uban ta gumi Hajiya ta rafka wadda ya rufe mata fuska da kuma hanci,
cikin yanayin damuwa Momi tace "Hajiya babu yadda zanyi ne na buga na buga sukace ina su sam bazasu chanja zaɓin ds sukayi mata ba babu yadda banyi ba amman suka k'i aminta wai tun tana k'arama mahaifinta yayi wannan alk'awarin na haɗasu aure dan haka su bazasu tada ba"
saida Hajiya ta sauke ajiyar a'zuciya sannan ta kalli Momi tace "kin kuwa faÉ—a musu wanene yake sonta?"
"hmm Hajiya babu abunda ban faÉ—a musu ba inma baki yarda ba sai ki kira Siraj kiji komai dan tare mukaje ke in takaice miki labari magagganu babu daÉ—in ji nima ai kamar kar naje sai kin gani"
kai Hajiya ta girgiza "ni yanzu bansan yadda zan cewa Yarima ba ba fahimta zaiyi ba kuma yanzu yana iya cewa inba ita ba saidai ya fasa aure"
Momi tace "ni wlh dama zaki É—auki shawarata a nema masa wata tunda yan'matan ne gasu nan kuma kyawawa"
Hajiya tace "ai inda matsalar take yace yana so É—in"
dafata Momi tayi "ki yarda dani Hajiya In'sha Allah wannan sai yace yana so dan babu abunda akeso ga ‛ya mace wadda Allah bai bata ba babu wadda zai ganta yace baya sonta 'yar k'awata ce kawai ki bari mu haɗa shi da ita muga kuma abunda Allah zaiyi"
shiru Hajiya tayi kamin tace "tho yanxu mi kike ganin zance sa game da wannan yarinyar ta k'auye?"
"karki faÉ—a masa anyi mata miji dan inyaji haushin haka zai iya rufe mishi ido yak'i son wannan kawai ki bari inna kirata yaje ya ganta kinga in yace yana so sannan ki faÉ—a masa Maryam anyi mata miji kinga babu wani shan wahala nasan zai amince da wannan"
sosai Hajiya ta jidaÉ—in shawara daman mafita take ta nema,
da fira Momi ta jata sai kusan biyar ta baro gidan,
*_©Khadeeja Candy_*
candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
*39*
*_K'AUYE..._*
tun tafiyar Momi Mairo bata kara walwalah ba duk tabi ta takura kanta kullum cikin kuka take tana kiran Momi duk tabi ta rame dan bata cin abinci ga ɗan banzan ciyon kai da take fama dashi wadda ya sakar mata zazzaɓi sanaɗin kukan da take, Gwaggo babu irin rarrashin da batayi mata ba har ta gaji ta zura mata ido,
yau ma kamar kullum tana zaune saman ta barma tana rusa kukanta data saba Halilu ya shigo,
tana ganinshi ta juyarda fuska ta k'ara fashewa da kuka,
saman tabarmar ya zauna yana bata hakuri. maimako tayi shiru sai abun ya k'aru Gwaggo ta tabe baki tace "aifa sai kayi ai duk kasan matsalar yarinyar nan ka barta taje birni kak'i ka dai riga kasan halin Mairo tun ba yau ba ba daina kukan nan zatayi ba dubi yadda duk tabi ta rame dan Allah ko abincin kirki bata ci amman baka tausayinta shiyasa mani nake tsoron auren nan naku wlh kar kaje can kayi ta gallaza mata daman ka saba"
Ajiyar zuciya ya sauke ya dafe kanshi,
_ba nida wata mafita sai wannan inhar na barta taje birni tho na rasata kenan dole ne na É—auki shawarar Siraj dan itace kawai mafita agareni_
kallon Gwaggo yayi dake ta masa masifa yace "shikenan zan barta taje birnin amman sai in an Äaura mana aure ta tafi da aurena inma karatun zatayi taje tayi in yaso daga baya sai ta tare"
kafin Gwaggo tayi magana Mairo tace "da gaske halilu?"
kai ya É—aga mata yana murmushin da baikai zuci ba "da gaske Mairo tunda naga kina son zuwa birnin"
k'ara matsowa tayi kusa dashi "yanzu ka yarda gobe naje?"
"a a sai an É—aura aure"
"tho a É—aura mana ni na Æ´yarda a É—aura sai naje"
bakinta Gwaggo ta buge ta kalli Halalu tace "indai har da gaske kake tho kaje ka sanarda tsoho duk abunda yace shikenan"
kai ya É—aga "In'sha Allah haka za'ayi anjima zan sameshi mu tattauna"
da sauri Mairo ta rumgimeshi tana masa godiya,
fisgeta Gwaggo tayi ta jefar tana mata faÉ—a wai bata da kunya, Halilu kan daÉ—i yaji dan gani yake yanzu Mairo na sonshi tunda ta daina kukan aurenshi sai na a barta taje birni,
'''*** *** *** *** ***'''
cikin satin nan aka saka ranar É—aurin auren, murna gurin Mairo ba'ah magana ko yar kunyar nan da yan matan k'auye suke yi ita batayi ba,
duk wadda yagani sai yayi zaton son Halilu take itakan bata ma kulaba murnar zuwa birni take, a'waya aka sanarwa da su Momi dama duk wasu dangi da suke nesa,
duk wannan abun da ake Qasin bai saniba dan ya daina zuwa part Äin Momi indai ba wani abun zaiyi ba Momi kuma ta fita sabgasar,
ana gobe É—aurin aure Abbah ya dawo dan Momi ta faÉ—a masa ranar laraba za'a É—aura,
*_2:45pm..._*
Momi na shirye² kaima Abbah abinci Qasin ya shigo rike da wata leda a hannu,
saman kujera ya dire kayan yana faÉ—in "gashi inji Abbah yace na kawo miki"
ba tare data kalleshi ba tace "shaddodin ne?"
"eh sune"
"ok barsu harna tashi amm ka shirya gobe zamuje É—auri aure k'auye"
haka yaji maganar kamar wadda aka jefowa abu daga sama da k'arfi ya haÉ—eye yawu ya kalleta yace "auren wa Momi waza'ayima aure?"
tsayawa Momi tayi ta kalleshi "Maryam za a É—aurawa aure amman bada kai ba da É—an'uwanta Halilu"
a hankali ya kai zaune saman kujera "Momi ban gane abunda kike nufi ba?"
kusa dashi Momi ta dawo ta zauna tace "Qasin na fahimci baka son Maryam kuma kana tsoron matarka dan haka nake ganin inna aura maka ita na cilas maka na kuma shiga tsakaninka da matarka shiyasa nace musu ka yanje zancen nemanta su kuma sukace koda kai ko ba da kai ba su daman aire zasuyi mata dan haka suka zaɓa mata Halilu a matsayen miji gobe ne ɗaurin aurensu na sani ko ba yau ba wata rana kai da kanka zaka nemi k'ara auren"
kai ya girgiza baki na rawa yace "wlh Momi ina sonta Momi na shirya bin umarninki kodan na faranta miki miyasa kika yi haka ba tare da kinyi shawara dani ba haba Momi"
"aikin gama ya riga ya gama Qasin sannan banida tabbacin kana sonta ko a'a bazan iya kai Maryam gurinda nasan zata cutu ba inason ka shirya gobe ka halarci É—aurin aurenta"
kasa ce mata kamai yayi ya tashi idonsa cike da hawaye jiki ba gwari ya fice.
da dare Qasin kasa bachi yayi haka yasa ya dawo parlour,
_tunani fal a ransa jin yake bai kyautawa Momi ba da kuma zuciyarsa dan harga Allah yana son Mairo saidai natsuwace bayaji a tare da ita haka yasa sai kuma yaji daÄin yadda Momi tayi dan yana ganin hakan kamar mafitane a gareshi tunda yanzu tayi aure ai dole ya daina sonta_ juyawa yayi daga kwancen da yake, ya lumshe ido.
*_WASHE GARI..._*
tun 6 na safe Qasin yabar gidan, kuma ya kama duk wayoyinsa ya kashe,
haka su Momi da Abbah suka Kama hanya ba dashi ba Siraj dai inbanda dariya babu abunda yake yana faÉ—in wai Qasin kishi yake.
*_©Khadeeja Candy_*
candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy ðŸ§: *♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
*40*
*_K'ARFE 2:30PM..._*
aka É—aura auren Mairo da Halilu babu laifi anyi taro saidai wasu yan'uwa na nesa basu samu halarta ba ango kan baki har kunne sai murna yake,
gudumuwa kan ya samu sosai musamman gurin Abbah.
ɓangaren Mairo ma farincikin ba baya ba dan ita zuwanta birni ne kawai a gabanta, da su Momi zasu dawo lak'ewa tayi sai ta biyosu daker aka samu aka lallaɓata bayan an aje ranar da Momi zata aiko a'je da ita.
'''*** *** *** ***'''
"miya hana ka zuwa É—aurin auren nan Qasin?"
zaune yake saman kujera kansa a k'asa Momi kuma na tsaye kansa tana masa magana, a hankali ya É—ago kai ya kalleta yace "wani meeting ne mukayi da wasu chenis shiyasa na fita da wuri"
taɓe baki Momi tayi tace "tho Allah ya kyauta daman zancen karatun Nura ne inason ka nema masa admission a state University tun kamin lokaci ya k'ure"
"abun yana raina Momi nayi magana ai kuma In'sha Allah gobe zanje makarantar ma"
"Allah ya kaimu"
"Amin"
haka ya tashi ransa a jagule ya fice,
*_4 DAYS LETTER..._*
ruwan sama ake kamada bakin k'waya harda k'ank'anra,
Qasin na zaune parlour sanye da k'ananan, laptop na gabansa yana yan danne² sai cup ɗin drink dake gefen laptop ɗin. a hankali yaji ana shafashi ɗagowa yayi suka sakarwa juna murmushi "daman ba bachi kike ba?"
"a a idanuna huÉ—u baka jin sanyi dear kake zaune parlour?"
murmishi ya sake sakar mata "tho ya na iya so nake na k'are aikin nan kamin gobe dan-"
ihun daji yasashi kasa k'arasa maganar ya tashi da sauri ya nufi windo,
yana ɗaga labulen gabansa yayi wani dakan uku² ganin Mairo na gudu cikin ruwa tana son kama lema. kasa tantance abunda yake gani yayi mamaki ya rik'ayi yana tunanin abunɗa zai kawo Mairo gidan cikin wannan lokacin haka ya rik'a k'acce² wai ko idonsa ne suke masa gizo,
gani haka yasa Mansura ta karasa kusa dashi tana kallon windom tana ganin Mairo ta ɓata fuska ta taɓe baki "mts miye abun kallo gurin wannan mahaukaciyar ai daman ni nasan sonta kake"
juyowa yayi yana kallonta fuskarsa ɗauke da mamaki kwata² baya jin abunda take faɗi dan hankalinsa na can wani guri har ta k'are surutanta ta shige ko ɗaya kunnensa bai ɗauka ba,
*****
"gaskiya ni har yanzu sanyi nake ji sosai"
Mairo ce take maganar tana sanye da atamfa red colour da hijab tana saukowa downstairs,
Siraj dake zaune saman kujera ya kalleta yace "ai dole duk fa ruwan nan da akayi saman kaki suka k'are"
"tho ba lema naje kawowa ba sai suka jik'ani" "tho dan kinje kama lema sai akace ki tsaya cikin ruwa kiyi wanka?"
dariya tayi ta zauna saman kujera tana k'ank'anme jiki "kai kuma Siraj ba murna nake nazo birni ba saida fa nayi ta kuka sannan aka barni nazo"
rigar sanyin dake jikinsa ya cire ya mik'a mata yana faÄin "ai naga duk kin rame k'arÉ“i wannan rigar ki saka"
saida ta k'arɓa sannan tace "kaifa?"
tashi yayi ya nufi stairs "bari na É—auko wata"
kai ta É—aga mishi ta shiga saka rigar,
takan mata yawa sosai saida kuma ta fitar mata da kyaunta sosai tana jan zip taji an buga k'ofa, da sauri ta nufi kofar tana buÉ—ewa ta sako idanu "lahh Yarima"
"na'am pretty gal"
da murmushi ya amsa ya kai hannu ya shafa gefen fuskarta, sannan ya shigo.
hannunta ya rika suka nufi kujera Siraj na tsaye yana kallonsu da murmushi har suka zauna, sannan yace "ke Maryam tashi daga nan yanzu ba kamar da bane"
da sauri ta koma a É—ayar kujerar Yarima ya É—ago yana masa wani wulakantaccen kallo, can kuma ya É—auke kai yana kallon Momi dake saukowa dwnstairs,
saida ta zauna sannan suka soma gaisawa "Yarima yau kaine a gidan namu da maraice haka?"
saida ya daÉ—e kamin ya bata amsa
"eh an faÉ—a min Maryam tazo ne"
mamaki ne fal a fuskar Momi "waya faÉ—a maka?"
"mutum..."
a takaice ya bata amsa yana kallon zoben hannunsa,
murmushi Momi tayi zatayi magana Siraj yace "Momi ya kamata yasan halin da Maryam take ciki yanzu Level Äinta ya chanja ba"
kallon Momi Yarima yayi alamar bai fahimci abunda Siraj ke faÄi ba,
cike da tsoro Momi tace "Yarima...Marya...m fa yanzu ..matar..aurece.. satin da ya wuce aka É—aura mata aure"
wani kyakkyawan murmushi ya saki wadda ya kara fitar da kyauwunsa yace "kidding me it's funny Momi"
Siraj yace "ba wasa ake maka ba yanzu Maryam igiya uku ce a kanta in kuma kana shakku kaje ka tambayi Hajiya ko kuma ita Maryam É—in gata nan"
kallon Maryam yayi dake kallonshi tana dariya da rufe fuska, ya sake kallon Momi kai Momi da gyaÉ—a mishi tace "wlh an É—aura mata aure Yarima kaji kuma na rantse"
tashi yayi tsaye ya wani yarfarda hannu "ohhh Momi inma gwadani ne kike tho ki daina bazai taɓa saɓuwa ba bindiga a ruwa bari kiji na faɗa miki tunda hajiya ta haifeni ban taɓa neman abu na rasaba wht ever I luff is my nd my only inason ki rubuta ki aje Maryam tawa ce no mttr wht dan haka in so kike ki gwadani k'ara ma ki daina in kuma so kike ki aura mata wani tho ki janye wannan tunanin..."
yana kaiwa nan ya karkaÉ—e rigarsa ya fice,
lumshe ido Siraj yayi yana _k'arya kake Maryan tawa ce duk wannan plan É—in nawa ne tunda har yayana baya sonta tho mine mijina ba kaina she s my_ a zuciyar yake wannan zancen yana wani lafiyayyen murmushi.
[11/10, 2:13 PM] ‪+234 806 053 5947‬: *_©Khadeeja Candy_*
candynovels.wordpress.com
[11:27PM, 3/17/2017] Khadeeja Candy: ​*♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
Candynovels.wordpress.com
_How can I begin to say I am sorry akan rashin ganin post's d'ina akan Lokacin I didn't mean to upset you hakan yafaru ne akan wasu yan dalilai I didn't mean to do what I did,_ _Naga sak'wanninku da kuma calls d'in_ _wasu daga cikinku na gode da jajanta min wayanda ban samu damar yima reply ba my apologies please, and thanks to you all kuma KHADEEJA CANDY na alfahari daku and to my Cooperate writers na gode sosai da irin kulawar ku agareni Allah bar zumunci._
'''I DEDICATED THIS EPISODE TO ALL MAIRO FANS AND READERS.'''😘