Mukaddari Ne Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: MUƘADDARI NE DAGA ALLAH.txt
Chapter 2 of 3
Cigaba da kallon sa yake Raj din abun yanata bashi mamaki, shi kuma Siddarth kokari yake yaga yabar kan benan,
Mutani da yawwa suna yabon Siddarth sbd ya gwada jarumta anan gun gaskiya wannan jarumi ne sosai mutani suke yabon sa, shi kuma Siddarth haka yata bin katangan benan har Allah yabashi sa'a saukowa kai tsaye yanufo gurin motar sa da ita shiga da ita cikin moton yayi ya dauko ruwa mai sanyi yazuba mata akan fuskan ta, doguwar ajiyar zuciya ta sauke tana mai numfashi sama-sama kallon ta Siddarth yakeyi cikin sanyi muryan sa yace fita mun amoto na, idanuwa tabishi dashi tana sake numshewa ina miki magana nace kifita amoto na idanuwa kawai takafa masa bata ko kiftawa, numshe idanuwan sa Siddarth yayi yana kallon ta aran sa yana cewa wannan yarinya akwai raini atattare da ita ok dan taga nataima kamata ko shikadai yake magana cikin zuciyar sa,
Suha ne take bubuga moton tana kiran sunan yar uwan ta Sana Sana kina jina kifito mutafi gida, Siddarth fuciko hannu Sana yayi fito da ita daga cikin moton sa ya koma ciki, Raj yashiga yaja motar yabar gurin baki daya, kuka Sana tasaka sosai kuka mai jin rai taji zafi azuciyar ta taji radadi aran ta taso tayi masa magana ko da godiya ce kukan ya hadu kashi biyu shin ina zata sake ganin sa har tamasa magana itafa lokaci guda yatafi da zuciyar ta kuka take sosai irin sosai dinan, Suha ne taje tazauna kusa da ita tafara mata magana haba Sana kitashi mutafi gida tundazu ina miki magana kina kuka kima gode Allah wannan mutumin yazo yacece ki da yanzu ba wannan labarin akeyi ba
Sana riko hannayen Suha tayi cikin dacin zuciya tafara magana ina zan gan sa ina zan sake ganin sa lokaci guda naji yashiga raina wallahi ina son sa Suha itai maka mun karna rasa sa idan narasa sa mutuwa zanyi, sosai Suha take kallon ta tana mamakin Sana Sana nan da aduniya idan kana son ganin bacin ranta too kamata magana nan namiji kokace mata wani yace kana son ta too fa anan ne zaku samu matsala da ita
Bazata taba mantawa ba wani lokaci da suka samu matsala da ita akan takawo mata magana nan wani matashin saurayi yagan ta a school nasu yace yana son ta shine fah yasamu Suha yafada mata akan dan Allah ta taimaka tafadawa yar uwan ta yana son ta kuma tashawo mata kan ta
Suha ne tashiga dakin Sana alokacin Sana tana chatting da kawayan ta tana cikin nishadi sosai Suha tashiga dakin kusa da Sana tasamu guri ta zauna tana kallon ta ita kuwa Sana ko kallon yadda take batayi bare tasa ran zata mata magana Suha ne tace ina son magana dake dan Allah kiban aron lokacin ki, kallon ta Sana tayi tace ina jinki wayan hanunta ta ajiye agefen ta tace ina sauraron ki,
Magana Suha tafara da farko dai sako akaban nabaki, Sana tace sako dagawa, Suha tace sako daga masoyin ki aman, Sana ta anbata suna abakin ta Aman ehh Suha tace mata tace yace infada miki dan Allah ki saurare sa kuma yaban sako nikuma zan isar da ita zuwa garki yace mun infada miki abun farin ciki nazuwa ne yayin da yasamu abokiyar rayuwar sa yace mun yar uwan ki akwai shiga rai kina da komai da yake dauke hankalin mutum dan Allah kikarba soyayyan sa dan Allah
Bata karisa rufe bakin taba taji saukan fari akan fuskan ta hakan yasaka Suha ware manya-manya idanuwan ta akan Sana tana mai mamakin marin ta tamata ae kuwa fada yakauce tsakanin su wanda yakai dambe ne yashiga tsakanin su sosai har takai sai da mom taraba su, saida sukayi kwana kusan goma basa magana akan wannan amma wai yau Sana take cewa wai tana son wani mutum kodai dan yataima keta ne amma kuma ae gayen Allah yazuba masa ruwan kyau sosai take kuka akan ita ina zata sake ganin sa lallabata Suha tayi ta tace mufara zuwa gida sai mufadawa mom itace zata san abunyi da haka Suha tashawo kan Sana har suka nufi gida,
Siddarth gabaki daya ran sa abace yake yanajin zuciyar sa na masa zafi sosai ganin halin da Siddarth yashiga ne yasa Raj bai ko masa wata magana ba, wayan Siddarth ne tafara ruru ae kuwa yaga daddyn sa ne ke kiran sa ae kuwa da sauri ya dauka da sauri yakai kun nan sa yace Assalamaalaikum daga bangaran daddy amasa wa'alaika musalam my son fatan kana lapiya, lpya kalau daddy ya ummi da Arjun da Aawa suna lapia kalau, dady yafara magana cikin sanyi murya yace masa jikin Alhaji kaka yatashi sosai yanzu haka muna asibiti kuma yace yana son ganin kowa gobe dan haka yau kabi jirgin dare kadawo
Siddarth yace insha Allahu daddy Allahu yabashi lapiya
************
KAUYEN GUMA
Washigari da safe Alili da kaka suka shirya domin tafiya asibiti kaka yadobi Alili yace wani asibiti yaka mata muje ne Alili yace kaka muje asibitin haske haka kuwa sukaje,
HASKE HOSPITAL
Doctor ne ya dumi su Kaka da Alili yace duk kwaje-kwajen da yakamata mumasa mun masa kuma mun gano brain din sane yasamu matsala kodai yasamu accedet din da yabuga kan sa kodae wani abu yasame sa akai dumin iya binciken mu mungano komai na brain din sa yamanta wato komai tunanin sa da kwakwalwan sa yamanta shi bazai iya tuno komai ba amma kuma zai iya tunuwa idan ana tuno masa da rayuwar sa na baya, yanzu zaina abu kamar karamin yaro kuma mungano wani abu game dashi akwai firgici da tsoro atattare dashi abu kadan zai zai sashi zubar da hawaye, zai kasan ce kamar yaro dan goye wanda yanzu zai sabada mutani kamar uwa da tahaifi dan ta ae yaro da uwan sa yake fara sabawa kafun baba da sauran su to haka wannan majinyacin zai kasance yanxu zamu daurasa akan magani insha Allahu zai samu lapiya kuma kuna yawwan tuno masa da rayuwar sa ta baya hakan ma zai taimaka sosai, sosai likita yabasu shawarwari mai amfani,
Amma kaka Alili sunshiga cikin damuwa sosai taya zasuna tuno masa rayuwar sa na baya bayan basu sansaba basu taba ganin saba basu san daga ina yakeba bare har suna tuno masa da rayuwar sa nabaya kuma shine abunda zai taimaka masa har yadawo cikin haiyacin sa, wannan abun yasa su arudani kuma sosai, saida likita ya dan taba tebur gin gaban sa tukun na suka dawo cikin duniyar da ta aura tunanin su insha Allahu zamuyi abunda kace likita,
Bayan sunsiya magunguna da akarubuta musu ne suka nufo kauye guma Khalil da ayanzu suka sakama sa sauna da garkuwa shine atsakiyan su, haka suka dawo gida suka daura sa kan maganin sa akoda yaushe yana manne da Bintu,
Bushar ne yasaka Bintu agaba duk wannan abun da yake faruwa bai san labarin ba sakama kon tafiyar da yataso masa kai tsaye, duban Bintu yayi yace tafiya takamani zuwa birni abu mai mahimmanci ne yataso mun dan haka ina fada miki ina fada miki ina fada miki Bintu wallahi karna dawo kauye nan nasamu wata labari dan kin san akan ki zan iya komai innace komai ina nufin komai dan haka kifita harkan kowa kuma nace karki raga wa Jummai wallahi tamiki kimata nafadami dai fatan kingane sannan kuma ina dawowa aure zamuyi babu wata bata lokaci sosai yake mata fada kamar wata yarsa ita kuma sai girgiza kai take amun tana fahimta, wannan tafiyar tayi matukar dadiwa Alili dan sun samu daman da Bintu zatabawa garkuwa lokacinta sosai,
Wata sanyanyiyan shakuwace tashiga tsakanin Khalil da Bintu shakuwa ce wace mutanin kauyen guma suke matukar mamakin ta shakuwace wanda akoda yaushe Khalil yana tare da Bintu ba iya Bintu ita daya ba kowa yana son mu'amala da Khalil domin Khalil yarasa tunanin sa na baya amma kuma gabaki daya abun da yashafi fannin adinin sa babu abunda ya manta, amma asanda yake da hankalin sa yasha babban da haka domin alokacin abaton Allah wahala take masa sosai amma yanzu wai Khalil ne ke yawan yi wa mutani garin nasiha insunyi abunda bai kamata ba Khalil tunanin sa nabaya kawai yamanta amma ta bangaran adini kam masha Allahu,
Yadauki Alili tamkar dan uwan sa wanda suka fito ciki daya dan shi azaton sa ma uwa daya uba daya suke kaka kuma kaka ne agun su, saidai wani abunda yake damun su da Khalil abu kalilan zai sakashi kuka bashida juriya ko kadan ne mutum ne mai saurin kuka da raunin zuciya,
Baffah zaune adakin sa Bintu agaban sa yayin da Khalil agefan sa, Baffah yadubi Bintu yace ina jin tsoron wani abu yasamu yaro nan Bintu yaro nan dake kawai yake sakewa har yayi wa mutani magana ina tsoron Bushar yadawo yasamu labari nan ya illata yaro nan wallahi tun farkon ganina da yaron nan naji hankalina ya kwanta akan sa gashi da adini Bintu dan Allah karki bari wani abu yasame sa, Bintu tace insha Allahu Baffah dama nikam bason Bushar nake ba kawai takuramun yake ni wallahi Alili nake so Baffah, Baffah yace tooo ae Alili akwai hankali insha Allahu zanyi abunda yakamata dan bazan bari amiki auran dole ba, sosai Bintu taji dadi, Baffah idanuwa yazubawa Khalil da yake ta sauke murmushi yana kara matsowa kusa da Bintu girgiza kai kawai Baffah yayi
Inna Jummai ne tashigo gidan babu koda sallama ne magana tafara ke yar tsutuwa fito nan karuwa mai bin maza duk namijin da tagani saita manne masa ae wlh sai kinwaso cikin shege magana take tana daukan muciya dakin Baffah ta nufa tana zuwa kan Bintu tayi tana dukanta da muciya sosai take dukan ta Allah sarki Baffah bai isa yayi magana ba tadawo kan sa,
Khalil kuka yake sosai yana cewa kibari kibar dukan ta kidaena, Inna Jummai ne tajuya tadawo kan sa kai karka sake mun magana dan wallahi yanzu zandawo kanka dan ba imani nake dashi ba, ae kuwa Khalil yafita adakin da gudu yanufi tsakar gida yana y'an dube dube adaidai lokacin da Alili yashiga cikin gidan ae kuwa Khalil bai ko lura da Alili ba yanufi ice dake ci da wuta kai tsaye ya koma dakin shigan shi keda wuya kuwa yazubawa Inna Jummai ice nan mai ci da wuta ae kuwa radadi da zafi lokaci guda yazuraci fuskan ta, bata sanda muciya nan yafadi ahanun taba, magana yafara mata cikin kakauran murya maicike da gargadi wallahi wallahi wallahi Allah dayane daga yau daga yau daga yau karki kara shiga tsafgar mimi dan zan iya komai akan ta dan haka nafadami tare da mikawa Bintu hannun sa akan tazo
Ae kuwa Bintu zuba masa idanuwan ta tayi tana kallon sa yayi matukar burge ta duk da yana gargadin Inna Jummai akan tadaena dukan ta yana kuka yana magana abun yabata mamaki sosai
Khalil kallon Bintu yayi yace tashi mutafi shuru ta tsaya kallon sa shikuma Alili idanuwa yazuba musu yana son ganin yadda zata kare wannan draman,
Bintu kallon hannun Khalil tacigaba dayi bata mika hannun taba, wani uban tsawa yadaka mata saida ta girkiza nace to zuciya ta mutsa, wani uban burkice Bintu ta mike, yatsa khalil yanuna mata ya soma magana.........
Khalil magana yafara mata cikin tsawa da tsantsan bacin rai wanda duk iya tsawon rayuwar sa da Bintu bata taba ganin sa cikin wannan yanayin ba magana yake mata da babban murya MIMI kin san matsayin ki arai na kuwa? kinsan mai aeke nufi da so kuwa? yadan numfasa kana yadaura dace wa bakin sannan yadda nake jinki cikin wannan zuciya tan ba? ko ina miki son da nikaina banayiwa hakui dukan ki akeyi amma ajikina nake jin dukan Mimi yakuma daura da tsawa karshen magana nan sa! amma shine ina miki magana kizo mutafi kina kallo na! Yakarisa magana sa cikin tsawa,
maida duban sa yayi kan Inna Jummai yafaramata magana "wallahi wallahi wallahi Allah daya narantsemiki da Allah daga yau daga yau idanuwa na suka sake ganin kin dauki hannayen ki kin duki Mimi na wallah narantse dawanda raina ke wajan sa sai na yanke hannu idan kuma kina ganin hakan baizai faru ba kikara, "
Yakuma komawa bangaran Bintu yace ke kuma daga yau karna sake miki magana kishare kumakina jina kimun shuru ba amun haka dan haka karki kara wallahi hannun ta yafincika ya jata da karfin da Allah yabashi yafitar da ita acikin gidan, kai tsaye wajan kaka yayi da Bintu Alili bayan sa yabi, yayin da Baffah yayi shuru yafada duniyar tunin da sake-sake acikin zuciyar sa,
Kaka kaka kaka Khalih yake kwala masa kira kaka arude yafito daga cikin daki, arude yana duban Khalil da yake tasoke numfashi kamar wanda aka biyu sa da gudun mutuwa ga kuma Bintu rike da hannun sa , kaka binsu yayi da idanuwa da ko kiftawa bayayi, kariso wajan sa yayi Khalil magana yafarayiwa kaka "kaka ina son ka aura mun Mimi ina son ta bana son rasata kai daya zaka goyamun baya wajan ganin na aure ta babu bata lokaci, " Kaka kallon sa yakeyi cikin rashin fahimta, Khalil kuma ganin Kaka yazuba masa idanuwa yasa shi fashewa da kuka tare da riko hannun Kaka yana masa magiya, "
Kaka yace haba Khalil meye na kuka kuma bayan kasan Kakan ka zai goya maka baya akan dukan abunda kasa agaba ina dai Bintu kake son aura to ka kwantar da hankalin ka insha Allahu zan samu mahaifin ta da maganan kaji sosai Kaka ya kwantarwa Khalil hankali,
Khalil yajidadin maganan Kaka dan haka yace "nagode sosai Kakana Allah yasaka maka da alakhairi Allahu yashiga cikin lamarin ka kamar yadda kafaran tamun Allah ya faran tamaka kakana" sosai Khalil yayiwa Kaka addu'a,
Khalil yamai da idanuwan sa kan Bintu yace Mimina ina daf da samun ki arayuwata Mimi ina miki son dani kaina banayiwa kaina dan haka kije gida anjima zanzo fira dare, Bintu kawai girgiza kanta tayi gabaki daya hankalin ta atashe yake bawai dan Khalil bai mataba bakuma dan Khalil bashi da kowa ba a'a saidan Bushar tasan bazai bar Khalil yasame taba wata kila ma yakashe sa duk tashiga cikin rudani ahaka ta nufi gida,
Zaune suke adakin su dama dakin su daya ne Khalil da Alili, Alili yaduba Khalil yace masa ina son namaka wasu yan tambayoyi, Khalil cikin farin cikin da Kaka yasa shi yace nabaka dama kamun kowata tambaya nikuma insha Allahu zan baka amsa idan nasani,
Alili duban sayayi tare da soma magana ina son kafada mun sunan tauraro wanda kasani cikin rayuwar ka, dan jam kadan Khalil yayi kafun ya furta cewa Fatima zarah, abirkice Alili yadube sa yace wace Fatima zarah, Khalil yayi murmushi yace masa Mimi mana, Alili yace Mimi kuma bayan da sunan da kake kiran ta dashi kenan Mimi banta jin ka ambaci Bintu ba bayan kaf gari nan da Bintu ake ce mata,
Numfasawa Khalil yayi yace "ae sunan danaji nafada mata kenan Mimi amma nasan sunan ta kenan Fatima zarah, "
Sosai Alili yashiga cikin mamaki akan lamarin wannan bawan Allah anya ba lafiyan sa kalau ba yana abu cikin hankali da tunani, cikin sanyi jiki Alili yace gaskiya kana son ta, sosai Khalil yace, Alili yadaura dacewa sai tambaya nagaba, ina jin ka Khalil yace yana gyra zaman sa,
Alili yace fadamun sunan macen da kasani, Khalil yace "hallou dai Fatima zarah ce, cikin mamaki yace masa gaskiya kana ji da zarah, Khalil yace sosai ma kuwa, " Alili yace sai tambaya tagaba, Khalil yace ina jin ka
Alili yace fadamun abu daya dakake so a rayuwar ka,
Murmushi Khalil yayi yace "Fatima zarah itace kadai nake so arayuwa ta , "
Alili ya numfasa yadaura dacewa fadamun abu daya dakake tsoran rasawa arayuwar ka,
Khalil yanumfa sa yace "tsoro na daya ne shine narasa Fatima zarah, "
Alili yace fadamun bukata daya dakafi rokon Allah,
Kahili ya numfasa yace "shine Allah kabani Fatima zarah, "
Girgiza kai Alili yayi yace gaskia kana son Fatima zarah amma kuma banajin akwai alaman zaka aure ta, cikin firgici Khalil yamike yana fadin babu abunda zai hanani auran Mimi na babu shi, Alili kire hanun sa yayi yace zauna namaka wata bayani, zama Khalil yayi,
Duban sa Alili yayi yace kasan maiyasa namaka dukan wadanan tambaya, girgiza kai Khalil yayi yace a'a Alili yace saboda infada maka akwai kalubali daywa agaban ka idan harkana son kasamu Bintu too dole sai kadage saboda akwai wani mutum daya sunan sa Bushar yana masifan son Bintu arayuwar sa kuma babu wani matashi agari nan wanda yaisa yace yana son Bintu, yana da matukar hadari arayuwar sa, mutum ne mai amfani da tsafi ajikin sa, idan kana son Bintu dole sai kadage da addu'a duk dana san kanayi,
Sosai Khalil yashiga tashin hankali yana girgiza kai yana fadin indai yafi karfin mutani to ae baifi karfin Allah ba dan haka daga yau zan dage da addu'a ae Allah yafisa, sosai Khalil yayi wa Alili godya,
Tunda daga lokacin da Khalil da Alili sukayi wannan maganan Khalil yadage da addu'a Allah yabashi Mimin sa,
Soyayya shakuwa da fahimtar juna tazauna atsakanin Bintu da Khali wanda ayanzu kaf garin guma kowa yasan da wannan soyayya, idan kaga Bintu tofa tabbas zakaga Khalil suna rayuwa cikin farin ciki,
Babu bata lokaci Kaka yasamu Baffa Bintu da magana nan, bayan Kaka sun zauna da Baffah Bintu Kaka yafara magana dama akan wannan mutumin da Alili yatsuto sa ne adaji kuma harmuka yi jinyan sa cikin iko na ubangiji Allah yasamu lapiya harya kai yamanta koman nakan sa baya iya tuno kamai nasa kuma mun kai sa asibiti likita yatabbatar mana zai iya samun lapiya idan ana tuno masa da rayuwar sa nabaya amma kuma bamu san waye shiba, amma nayarda da hankalin sa idan zaka iyabashi auran diyar ka dan Allah kashi yana son ta mutum ne mai addini nasan tabbas zai irike diyar ka cikin mutunci da mutumtawa koda kuwa ya dawo cikin haiyacin sane dan haka dan Allah idan zaka iya, sosai Baffah ya girgiza kai yace mai zai hana idan harya na son ta kuma kunyi na'am da hankalin sa dan haka nabashi ina fatan yazamo sanadiyar samun iyayan ta da kowa nata dan haka na amince nabashi Allah yasa alkhairi ciki, sosai Kaka kaji dadi kuma yamasa godiya
Har yamike zai tafi Baffa yatare sa da wata magana amma nasan kasani kowa yasan Bushar nason Bintu dan haka ina son kafun Bushar yadawo daga tafiyan da yayi amusu aure idan babu damuwa, sosai Kaka yaji dadin hakan, Kaka yace wannan hakane kaga kuwa idan yadawo yatarar da Bintu tayi aure dole ya hakura ne dahaka suka tsayar da rana sati uku,
Kaka yasamu Khalil da Alili ya sanar musu dukan magan-ganun da sukayi da Baffahn Bintu suji dadi sosai da sukaji ansanya ran auran Bintu da Garkuwa duk saboda Bushar, kaka yace to yanzu sai kufara ginin wanancen filin saboda kar lokaci yagure mana, haka kuwa akayi suka shiga gini sosai,
Gini yayini sa yayin da sauran kwana auran Bintu da garkuwa saura sati daya kowa yasan da zance auran agarin domin kuwa har gulma aekyi duk saboda Bushar ae baya nan ne hakan tafaru wasu sunyi murna haka yayin da wasu suke cewa ae dama Bintu yar tsutuwa ce dan haka babu laifi dan dan tsutuwa ya aure yar tsuwa,
Yau garin antashi ne da wata iska mai dadin shaka gamida sanyi sosai yayin dawani hazo-hazo yayiwa garin rumfa sosai, Bintu ne da Garkuwa awani bakin rafi iska sai kadasu yakeyi gawasu furanni yakewaye su kananu da manya kasama yayi jaa alamun dai ruwa yana daf da saukowa, garkuwa ya dubi Bintu yasoma magana cikin zakin muryan sa maidadin sauraro yace Mimina yau saura kwana uku rak kizamo malakina uwar y'ay'a na, muna aure zakidaena komai nine zanyi komai abinci ibo ruwa komai fah, murmushi Bintu tayi tace bazantaba barin mijina ya wahalaba dan haka babu abunda zakayi mun idan kuma kace dole sai kamun toofa tabbas saidai muyi tare, sosai Garkuwa wato Khalil yayi murmushi yace gaskiya banzan bari iyiba Allah, Bintu tace Allah zakabari muyi tare tafada cikin shagwaba ae tuni takashewa Garkuwa jiki to naji zamuyi tare amma kuma daka sanda kika samu ciki nine zanyi komai, cewar Khalil ae Bintu idanuwan ta ta rufe sosai suke hirar su gwanin ban sha'awa da nishadi
Adai-dai wannan lokacin kuma wani ganka ake dokawa acikin gari anawa ka ga ga Bushar yadawo ga Bushar yadawo ahaka har akawuce gidan Kaka da wakar, alokacin Alili suna fantin dakin amarya, yaji sunan da aka ambata kamar diran mikiya.........
Ganga ake dokawa ana waka ana cewa ga Bushr ga Bushr, Alili da suke ta panti dakin amarya yaji saukan sunan kamar diran mikiya sosai ya shiga cikin razana da furgici kai tsaye cikin gari yayi domin niman Khalil gabaki daya baya cikin haiyacin sa,
Khalil da Bintu da suke zaune abakin rafi da basusan abunda yake faruwa ba acikin gari sosai suke shan soyayyar su cikin farin ciki da fahimtar junan su
Bintu tace kasan me Khalil yace sai kin fada ae zan sani, sauke numfashi Bintu tayi ta soma magana cikin muryan ta maidadin sauraro tace atareyata dakai Saudauki na na ilimantu da wasu abubuwa masu yawa hakan ne yasa nakejin babu wani tamkar ka ina maka son da nidaina ban san adadin hakan ba zuciya ta babu wani tamkar ka zanciga ba da hidimtawa soyayyar ka har ranan da Allah zaisa kazamo mijina ina maturkar kaunar ka annurin raina ina son ka sosai Khalil yaji dadin maganta kuma yake jinkan sa babu wanda yakai sa sa'a awannan duniyan
Bintu tace inama muna aure dani dakai mubar wannan garin mai cike da masifa agaremu,
Khalil adan razane yace masifa kuma Mimi,
Bintu tace ehh masifar Bushar koda yadawo munyi aure bazai barmu muzauna lapiya dakai ba ina jin tsoran ya cutar mun dakai, Khalil yace karki damu ae Allah yafisa, sosai suke cikin nishadin su,
Alili ko ina yaduba bai ga Khalil ba dan haka yayi tunanin yana can gunda suka saba zama dashi da Bintun sa dan haka kai tsaye rafi yanufa cikin tashin hankali,
Numfashi yake ta saukewa yana kara saukewa Khalil yafara ganin sa cikin wannan yanayin yazo gare shi yafara masa magana Alili meyafaru kake ta sauke numfashi haka fadamana Alili yadubi Khalil yace ka gudu ka gudu zai kashe ka yadawo yadawo yadawa abunda Alili yake fada kenan kawai
Khalil yace kanutsu kafadamun maiyakw faruwa, Alili yace Bushar yadawo, daga Khalil har Bintu tsaya sukayi cak zuciyar su tana bugawa ,
Bintu tace shikenan nashiga uku na kashe mun kai zaiyi yanzu yazanyi kuka take sosai kamar wanda aka mata mutuwa yo ae mutuwar ce ae Bushri babban mungu ne kuma matsafi ne
Tashin hankali wanda ba asama rana kenan Alili yace mufi daya ce shine Khalil ya bar gari nan, shine kawai zamu kare sa daga azabar Bushar, Khalil da tun farkon da Alili yafada musu cewa Bushar yadawo bai sake magana sai yanzu dayaji abunda Alili yafada masa cewa ae ya gudu,
Girgiza kai yakeyi yana fadin a'a babu inda zan tafi na bar Mimisaidai mutafi tare da ita cikin kuka yake fadin haka babu inda zan tafi nikam ae Mimi ce rayuwa ta idan har bada Mimi zan bar garin mahaifa na ba too wallahi zan tsaya ne duk abunda Bushar ya mun zan jure, sosai Khalil yake sun batu cikin fitar haiyacin sa,
Alili yace garkuwa dole ka gudu guduwa yazama dole, maida kallon sa yayi kan Bintu ya fara magana cikin sanyi murya mai cike da tsoro yace Bintu kibi sa wata kila Allah yahada ki da iyayan ki nikuma zanyi wa Baffan ki bayani yadda zai fahimta, kinji,
Cikin kuka Bintu tace too dan Allah ka kulamun da Baffah na sosai Alili yana kuka yana cewa insha Allahu zanyi hakan nidae fatana watara na kudawo gida,
Khalil yace bazan taba manta gida ba dan haka dole nadawo gida sosai suke kuka abun yataba zuciya ta, Khalil Bintu Alili dukan su kuka suke kamar wanda ace idan suka tafi bazasu kara ganin junan suba.
Dukan tattaunawan dasu Khalil sukayi duka akunnan iro aboki ga Bushar kai tsaye yayi cikin gari domin sanarwa abokin sa.
Sosai iro yake sauri dan zuwa sanarwa Bushar cewa fa Bintu zata gudu da wani mutum suje can suyi rayuwar su,
Bushar zaune akan kujeran sa da akoda yaushe yake zama ga mukarrabon sa sun kewaye shi cikin tsoron son fada masa fa Bintun sa yau saura kwana uku kacal auran ta, iro da gudu yazo yasame sa yana haki yana fadin oga Bushar wanda babu kaman sa akaf kauyan guma nakawo maka babban labari, Bushar kada kai yakeyi yana fadin ina jinka fadamun, iro yace Bintun ka matar ka tana shirin gudu da wani acan bakin rafi, mikewa yayi da sauri yana haki yana yacewa a'a karya kake babu wanda ya isa yashiga gona ta, Iro yace wallahi Allah dagaske ne Bintu matar ka zata gudu da wani ae labarin komai Iro yabashi bayan tafiyar sa da abunda yafaru kaf yafada masa kuma yau saura kwana uku auran su
Ina karya ne babu wanda isa ya aura Bintu ina duniyan nan ya numfasa kana yadaura dacewa Alili da kai da Kakan ka da shi kan sa Baffahn Bintu sunshiga ukun su wallahi basu isa ba, kai tsaye yayi bakin rafi domin hana su Kahlil guduwa kuma yajene da niyan kashe Khalil da Alili idan har yatarar da su agun,
Khalil hannayan Alili yarike yana kuka yanacewa bazan iya tafiya nabar kuba kaka idan yasamu labarin tafiya ta bazaai jidadi ba kuka sake sosai mai karya zuciya Alili yace Garkuwa kutafi dan wallahi rayuwar ka tana cikin hatsari Khalil yana kuka yana nafasa tafiyan ae Alili fincike hannuwan sa yayi yace naroke ka kabar gun nan fatan samun nasara awanna tafiyar na ku sosai Khalil yake kuka yarike hannun Bintu sukabar gun,
Alili hango su Bushar yayi suna tahowa acikin zuciyar sa ya futa Alhmdullah yasamu wani gu yaboye, kari sowa Bushar yayi da mukar rabon sa bakin rafi nan amma babu kowa agun Bushar yadubi Iro yace masa kace sunan amma banga kowa ba, Iro yace bashaka basu jima da barin nan gun ba ina da tabbacin basu kai fita daga cikin dajin nan ba ae kuwa Bushar ya kwashe da dariya yana fadin ae wannan dajin malaki nane dan haka ko ina kuka shiga sai nasamoku namuku hukunci mai tsanani, ya fashe da dariyan marasa imani,
Sosai Alili yashiga cikin tashin hankali jin abunda Bushar yafada ae kuwa addu'a yafara cikin zuciyar sa,
Bushar yace mutafin ku muni mosu ae kuwa cikin dajin sukayi dan nimo Khalil da Bintu, Bintu da Khalil gudu suke yi sosai kamar wanda suka ara kafa, Khalil yace Mimi nagaji mu huta ae kuwa suka zauna agaban wata bishiyar mango ro wanda ganyan ta yarufe ko ina na cikin bishiyar ne zai iya ganin na wajan ta, suna zaune suna sauke numfashi kamar ance Bintu ta daga idanuwan ta, tasauke su akan Bushar ae kuwa riko hannun Khalil tayi magana tafara masa cikin hankali tace gashi nan sun biyo mu ae aburkice Khalil yariko Bintu yana fadin shikenan kashe mu zasuyi ko, kuka yafara sosai kamar karamin yaro ae kuwa Bintu tayi saurin tushe masa bakin sa dan kar ajisu,
****************
BIRNIN TAREYA ABUJA
MANGA FAMELY
Alhaji Kaka kwance awani babban asibiti sai fitar da numfashi yakeyi kadan-kadan yayin da yaran sa baki daya sun kewa ye sa, matar Alhji Kaka nae ageban sa wanda ita ce mahaifiyan Sadar wato mahaifin su Arjun wanda tun kwana kin baya Allah yayi rasuwa wa ummu Safiyya wanda uwace ga uncle musa, musa Abubakar da kuma Sadar da maijidah kanwa agare su wanda tayi aure a Bauchi yaran ta biyu Nusaiba sai Bahijah
Yaran sune age fan su
Abdulkadir dan gidan uncle musa kanwan sa ummi salam
Sai yaran uncle Abubakar Mansoor da Sagir
Sai yaran sadar wato mahaifin,
Siddarth da Arjun da Araw gabaki daya manga famely sun kewaye sa yayin da babu jikan sa daya wanda yafi kauna agun Siddarth wanda jirgin sa yana daf da sauka
Karfe 10:00Am dai-dai Siddarth ya sauka a manga Hospital kai tsaye cikin room din da Alhaji kaka yake yanufa bayan sun gai-gai sa da su uncle din sa wanda matar uncle musa wato hajia Laila take tafan hada rai, Alhaji kaka ganin jikan sa yasa yafara yun kurin tashi daga kwanciyar da yake taimaka masa yaran sa sukayi bayan ya mike yafara mika hanu wa Siddarth ae kuwa Siddarth yafika hannuwan sa yaje gare sa hajia Laila kamar ta muta mai yasa dan ta ba'a jansa ajiki bayan kuma shine babba agabaki daya familyn,
Alhaji Kaka magana yafara yana kuka yana cewa duk nine silar tarwatsewar familyn mu ina da kanne har biyu wanda bansa yadda suke ayanzu ba Muhammad da Sulaiman, gabaki daya yabasu labarin abunda yazamo sanadiyan raba su, dama su uncle musa sunsan magana yaran sune basu sani ba sosai suga shiga cikin mamaki da ban al'ajabi, Aaraw harya fara zumudin kagani yan uwan sa shi mutum ne mai son mutani, Alhaji. Kaka riko hannu Siddarth yayi tare dana Abdulkadir yace dan Allah kutaima ka kunimu su sanan kuje suyafe mun ninasan bazan kara ganin suba, sosai sugashiga cikin tashin hankali, Siddarth yace insha Allahu zaka samu lapiya zaka warke da yardan ubangiji Allah,
Rai bakon duniya Allah yayiwa Alhaji kaka rasuwa, wayyo zokaga tashin hankali agun manga family amusu mutuwa mai karya zuciya rayuwa kenan,
Bayan ankai sane Siddarth yafara bin hanyan dazai gano yan uwan su wanda Alhaji kaka yadaura masa nauyin hakan,
Dalilin mutuwar Alh. Kaka ne yasa Arjun mai tafi kauye guma ba wannan kenan
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*******************
INDIA
Har yanzu jikin momy yanan yadda yake saidai ma muce ciki kara tsanani yake Abba yashiga tashin hankali sosai, Abba samun Doctor yayi kamar yadda Dr. yabukaci hakan Doctor yadubi Abba yafara masa magana cikin harshen turanci, Alhaji gaskiya matar ka ba jinyar asibiti yaka mata da itaba dan wanna jinyar kamar bana asibiti nane dan haka zan baka shawara kadauke matar ka zan hadaka da wani malamin addini dan kasar Saudia ina da tabbascin zaku dace agun da yardan Allah sosai Abba yamasa godya, akadauki momy wanda ayanzu batama zan yadda kanta yakeba zuwa Saudiya,
💕💕💕💕💕💕💕💕💕
*********************
AMERICA
Suha cikin parlo suka shiga rike da Sana mom datake zaune a parlo tamike tana tambayan meyake faruwa da ita haka rike da hannu Suha tace mom zauna nabaki labari, kaf abunda yafaru da Sana, Suha tabawa mom, mom girgiza kanta tayi nata cewa ae kuwa ngd masa sosai, Sana kuka tafarayiwa mom din ta tana fadin mom wallahi ina son sa kitaimaka mun karna rasa dan wallahi idan narasa mutuwa zanyi, sosai take kuka kamar ranta zai bar gangan jikinta
Mom Suha mamaki duk ya mamaye zuciyoyin su yau Sana take cewa tana son wani mutum lalai kam abun mamaki ne wannan, Sana burgima take sosai, Sultan ne yashigo parlon yana magana a mom meyafaru da sweet sister na take kuka, Sultan mutum ne da sam bai dauko halin mom din saba yana matukar son su Sana yadauke su tamkar Sukaina, Sukaina ne dai tadauko bakin halin mom din su,
Ae Sana tana jin muryan Sultan tamike daje wajan sa tarike hannuwan sa tana kuka tana fadin bro dan Allah kataima kamun karna rasa shi wallahi ina son sa lokaci guda naji kaunar sa yashiga cikin zuciya ta, Sultan yace sister nutsu kimun bayanin komai yadda zan fahimta kama hannuwan ta yayi ya zaunar da ita kan kujera yace too yimun bayanin komai yadda zan fahimce ki kinji blood sister na Sana kuka take tana masa bayanin komai sai da tagama basa bayani tayi shuru,
Sultan idanuwan sa yakafe ta dashi cikin sanyi muryan sa yace ki kwantar da hankalin ki my lovely one indai wannan zan taimaka miki kuma zan iya bakin kokari na wajan ganin kinsa mesa kuma nasan shima zai so ki ae kin caccanci aso ki wata kilama shima yanata fama da son ki acikin zuciyar sa,
Sosai Sultan ya kwantarw kanwar sa hankali, yabata abinci abaki yanata fada mata magana mai dadi sosai da sosai
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
**********************
KAUYE GUMA
Bintu "tace kayi shuru kar sujimu Khalil ya gabaki daya baya fahimtar da cikin muryan sa na kuka yace zai rabani dake Mimi ban son rabuwa dake, " Bintu tace ae ba rabuwa zamuyi ba, "amma idan kayi kuka zasu jimu kuma suraba ni dakai kadae na kuka kaji Bintu takari sa magana nan kamar karamin yaro,
To nadaina cewa Khalil kamo hannuwan sa Bintu tayi suka mike suna tafiya ahankali-ahankali har suka bar wannan bishiyar mangoro nan batare da su Bushar sun gan suba, tafiya suke har suna hadawa da gudu sai da sukayi nisa sosai ne kafun Khalil yace Mimi nikam nagaji muhuta anan, murmushi Bintu tayi tace shikenan samun wuri sukayi suka zauna, Khalil yace Mimi ina jin yunwa, kallon sa Bintu tayi tace "Hmmm to yanzu yakake so nayi Sadauki, " takarisa cikin tausayin sa, mutsu-mutsu yayi da fuskan sa kamar karamin yaro na shirin kuka, yace nikam yunwa nake ji Mimi, Bintu tace karkayi kuka kaji kayi hkr mukari sa cikin gari duk da akwai dan nisa amma bansan yadda zan sama maga abinci ba, da lalama Bintu ta lalaba Khalil har yadaina mata kukan yunwa,
Bushar ya kalla yaran sa yace baza muta komawa cikin gari ba batare da Bintu na ba dan haka mukara gaba ina da tabbacin zamu gan su, haka kuwa sukayi sukara shiga cikin dajin dan niman Bintu da Khalili,
Yau kwanan Khalil da Bintu biyar acikin daji........
Yau kwana nan Khalil da Bintu biyar acikin daji, gabaki daya sunfita cikin haiyacin su musamman ma Khalil gaba ki daya yafita haiyacin sa gawata bakar yunwa sumaci sa'a ne acikin tafiyar su Allah yahada su da bishyar mangoro sukaci, da tuni Khalil ya sumewa Bintu
Rayuwa kenan yau Khalil cikin daji Khalil wanda sai yazaba abincin da zaici amma yau Khalil abunda zaici ma yana masa wuya Allah ya kyau ta
Yauma cikin tafiya suke yayin da Khalil yafashewa Bintu kuka cikin kukan sa yace dan Allah Mimi muhuta anan nikam nagaji ga yunwa nake ji sosai Bintu tace haba Sadauki na ka kara hakuri mana niban san mai zanba ka kaciba, kayi hakuri mana mukara gaba ko Allah zaisa musamu wani abunda zamuci, ae kuwa Khalil ya barke baki yafara kuka yana kuka yana fadin nikam yunwa nake ji, Bintu ma gani Khalil yana kuka itama ta farke da kuka ae kuwa dukan su suka farke da kuka babu mai rarrashin wani cikin su, kuka suke sosai kamar wanda aka musu mutuwa,
Bushar suka tusa kansu sukeyi cikin dajin sama-sama suke jin kuka kamar na mutani tsayawa cak sukayi, suna suraron kukan, Bushar yace kamar kuka nake ji, ae kuwa suka kara kai kan su gurin da suka ji kukan,
Khalil "yace Mimi maiyasa kike kuka kidaina kuka ban son ganin ki kina kuka dan Allah kidaina, taya zandaina bayan kuma Jarumina yana kuka idan kana kuka kana karya mun zuciya ta ina jin zafi acikin zuciya ta, too nadaina kema kidaina kinji sosai Khalil yake rarrashin ta, gabaki dayan su sundai na kuka suka fada duniyar soyayya Khalil yace Mimi na idan munkasance mata da miji ko too tabbas zan jiyar dake ruwan soyayya zaki kasance mai halfahari dani sosai idan Allah ya so, sosai Bintu taji dadin, kalama, sa, harta wani rausayar da kanta tsaban murna, har tabude baki zatayi magana kawai sai ganin mutani sukayi sunke waye su, ae kuwa da sauri Bintu ta mike tana rarraba idanuwan ta cikin tsoro, Khalil kuma bayan Bintu yaboya yana kuka kamar karamin yaro yanacewa Mimi kiboye ni kamani zasuyi,
Bushar fashewa yayi da dariya yana fadin ashema macce yake son ki Bintu ya kuma fashewa da dariya na marasa imani, ya kuma juya fuskan sa yadubi yaran sa yace kar kuma sa komai ku dauka mun shi mukoma guma ya kuma fashewa da dariya, ae kuwa Khalil ya kankame Bintu yana kuka yana fadin "Mimi kiboye ni dan Allah karki bari sumun komai dan Allah Mimina, "
Allah mai iko yau Khalil shiyake boyewa
abayan macce akan wani mutum wai dan karya duke sa rayuwa kenan harna tunu fadan sa da Billyboy tabbas Khalil bashi da lapiya na tabbata yau😞
Yaran Bushar suka nufo Khalil domin kamashi ae kuwa Bintu tasha gaban su tare da ware hannayen ta tana magana cikin tsawa wanda shi kan sa Bushar sai da abun yabashi mamaki yayin da Khalil yasake razana yakara kankame Bintu ajikin sa, Bintu tace wallahi kar ku kuskura ku taba shi narantse da Allah idan hanunku yataba jikin sa to wallahi saina muku abunda bakwatinani takarisa magana nan cikin zare musu idanuwar ta, Bushar yace taya baza aso mace kalan wannan ba mace jaruma gaskiya ina son ki Bintu na kuma dole sai na aure ki yafashi da dariya kana ya daura dacewa kubarshi kada kutabashi, haka yasaka su agaba kai tsaye suka nufi kauyen guma, Khalil amakale da Bintu,
Alili yazo gurin kaka aguje yana magana cikin haki kaka kaka shikenan Bushar yadawo kaka yace Alili katsaya kafadamun abunda yake faruwa yadda zan fahimce ka, Alili yace Kaka Bushar ne yadawo daga tafiyar da yayi yau din nan gabaki daya Alili yakwashe komai yafadawa Kaka ae kuwa Kaka yashiga cikin rudani, fada yafarayiwa Alili yace kasan mutum ba lapiya gare shiba amma ka goya bayan yagudu sbd mace bayafa cikin haiyacin sa amma kuma kace ya gudu gaskiya Alili kayi ganganci anan gun, sosai ran Kaka yabaci, kai tsaye gurin Baffahn Bintu yayi ya sanar dashi komai akan gudun Bintu da Khalil, Baffah yashiga cikin damuwa sosai da jin labarin gudun diyar sa Bintu yashiga matukar damuwa too yakamata mubasu dan niman su dan baika mata mubar su ba, ahaka suka kare magana nan sbd bazasu iya barin suba wannnan kenan
Haka Bushar ya tura su Khalil da Bintu agaba kai tsaye gun mai garin garin sukayi, suna isa Bushar yafara magana cikin zafin nama yace, maigari dakai za'a ahadabaki, auran mun da mata dan anga bana gari ko too baka isaba ina son atara kowa nagari nan akwai magana nan danake son yi da su, maigari ya aike dan aike domin yasanar da mutani cewa kowa da kowa ana bukatar su afada, haka kuwa dan aike yasanar da kowa da kowa, bayan yagama sai kuma yanufi dayan aikan da maigari yasa shi ae kuwa yace yasanar da Kaka da Alili da kuma Baffahn Bintu,
Baki daya sun gama taruwa afadan sarki kowa yayi shuru yayin da suke jira suji tabakin maigari, maigari duban Bushar yayi yace kai muke sauraro ae kuw kowa yafara zare idanuwan sa, Kaka da sai yanzu ne idanuwan sa ya sauka akan Khalil da ke kamma me da Bintu Kaka taba Alili yayi yana nuna masa yadda Khalil da Bintu suke, Alili sosai yaji tausayin su,
Bushar yace da farko anan mun laifi agarin nan kuma sun san kan su kuma wallahi sai na dau hukunci akan ku amma yanzu bazan fara ta kan kuma, yadago fuskan sa yadaura akan maigari kana yadaura dacewa, maigari acikin garin ka kuma kana gani za'a aurar mun da matar da zan aura amma kayi shuru, kuma kasan zan iya daukan hukumci dakai na amma meyasa nazo gare ka, Bushar ya numfasa kana ya daura dacewa duk hukumcin da na zantar akan ku ya zauna amma kuma banyi ba sbd da ina da dalilin yin hakan kana ya kuma fashewa da dariya, na marasa imani, kana yadaura dacewa anriga da ansaka auran Bintu na da wani mutumin da ba musan waye shiba dan haka kar ace nayi son kai nayanke wani hukumci wanda kowa zaiji dadin hukumcin da nayanke,
Bushar yace hukumcin da nayanke shine kowa yasani ina son Bintu kuma ina son auran ta, bayan tafiya ta nazo nasamu ansaka bikin ta da wani, too magana nan gaskiya tunda dukan mu biyu muna son Bintu kar na dage akan sai na aura Bintu da karfi na yasa nayanke hukumcin dani da wannan mutumin zamuyi gasa akan ta duk wanda yaci gasan too shine zai aura Bintu, yakarisa magana yana murmushi,
Maigari yace "too munji maganan ka kuma mun amin ta dashi amma baka fadamana wani kallan gasa ne haka, Bushar yace " Shadi zamuyi shadi dani dashi duk wanda yayi hawaye yafadi, "
Kaka Baffah Alili dukan su mekewa sukayi atare baki dayan su.............
Bushar yace "kunsan bashi da lapia zaku aura masa mata? ae duk mutum da zai rike mata too tabbas zai iya shadi, maida kallon sa yayi kan mai gari kana yadaura dacewa, tabbas wannan shine abunda za'ayi dan kar ace nayi son kai dan haka idan kuna son zaman lapiya too wallahi ku amince da wannan gasan saboda idan har bazan ayi gasan nan ba zankashe wannan mutumin domin wannan shadin shine zan gwada masa cewa niba asa'an saba ne, shine zai sa yagane bakai yashiga harka taba amma idan kunce baza ayi ba too kuma kunsan zance, "
Bushar yace Baffah yakace ka amin ce, Baffah kan sa yadaga yadaura akan Kaka, hada idanuwa sukayi Baffah da Kaka, kaka ya girgiza masa kai alamun ehh, Baffah yace ehh na amin ta da batun ka, Bushar yamaida fuskan sa kan Kaka yace kai fa, Kaka yace na amin ta, Bushar ya maida fuskan sa kan mai gari kana ya daura dacewa, duk wanda ake bukata ya amin ce ya amin ce dan haka sai asaka ranan da za'ayi, budan bakin Alili yace ae shi wanda za'ayi dashi bai amin ta ba, ae kuwa kallo yadawo kan Khalil, mai gari ya maida kallon sa kan Khalil yace ka amince da wannan gasan da za'ayi,
Kallo fa yadawo kan Khalil kowa so yake yaji mai Khalil zaice,
Khalil hannun Bintu ya kama gam yana zare idanuwan sa hawaye fal cikin idanuwan sa, magana yakeyiwa Bintu "Mimi na zai rabani dake ko hawayen cikin idanuwan sane suka zubo, " Bintu tace Sadauki ka kwantar da hankalin ka kaji ka nutsu kaba su amsar da take cikin zuciuar ka kai tsaye, " Khalil yace ban fahimta komai ba da suke cewa, Bintu tace "gasa zakuyi da kai da Bushar na shadi bulala 100 duk wanda yayi kuka to shine yafadi kuma bazai same ni ba, shine suke tambayan ka ka amince, " tsayawa yayi cak yana kallon Bintu, Bintu ta daura dacewa nasan kana sona Sadauki bazaka so karasani ba ko? girgiza kai Khalil yayi yace ehhh, Bintu tace yawwa to fada musu amsan su, kuma kai tsaye daga cikin zuciyar ka,
Khalil ya dago kan sa ya daura akan mai gari yace "na amince" Alili kamar yayi kuka dan yasan Khalil ba iyawa zai yiba, Bushar yace to shima ya amince dan haka ansaka kwana uku rak,
Bintu ta mike tace nima aminta amma gasan nan zai fara ne akan Sadauki, Bushar dariya yayi na irin na marasa imani nan yace na amin ta,
Bayan gama taro afada kowa ya kama gaban sa, Alili da sauri yazo wajan Khalil ya fara masa fada cikin bacin rai "Khalil kana cikin hankalin ka kuwa kasan waye Bushar kasan mai yake takama dashi da zakace ka aminta da batun sa, gabaki daya shifa babu Allah acikin zuciyar sa amma kana cewa wai kai ka aminta, tabbas idan bai kashe kaba too zaimaka ila da bazaka iya komai ba, arayuwar ka, " Khalil rike hannun Bintu yayi gam yana kuka yana cewa kasan me Alili bakasan yadda nake jin Mimi cikin rai na kuwa hmm yadan numfasa kana yadaura dacewa Alili ina son Mimi zan iya bada rai na fansa akan ta dan haka koda Bushar zai kashini ne yau daya kam saina gwada jarumta na akan Mimi, kasan yadda tasha wahala akai na kuwa acikin daji nan ya karisa maganan sa cikin kuka,
Sosai jikim Alili yayi sanyi kana ya fara girgiza kan sa yana cewa addu'a itace kawai abunda zan taya ka tashi, Baffahn Bintu ne ya cafke zancen da cewa insha Allahu zamu taya ka da addu'a baki dayan mu, haka ma Kaka ya fada, sosai Khalil yaji dadi daganin dukan su sona son shi kuma suna masa fatan alkhairi cikin rayuwar sa, da haka kowa ya nufi gidan sa, yayin da Bintu tabi Baffahn ta kana Kaka Alili sai kuma Khalil suma sukayi gidan,
WASHI GARI
Bushar a kofar gidan su Bintu yana jiran fito wan ta, babu bata lokaci sai ga Bintu ta fito, fuskan ta ahade kamar wanda aka mata mutuwa, Bushar ya fara magana "ae dama nasan basona kikeyi ba, Bintu nikum ko ina sona ko baki sona sai na aure ki babu wanda yafi karfina awannan garin dan haka kima sani dole sai nadawo miji agare ki, Bintu da tagama sauraron sa tace " Allah yafika Bushar ayanzu bana jin tsoron ka kuma kasani Allah baya barci kuma yace murokesa zai amsa mana, ni Allah ne gatana kuma dashi na dogora kuma washi zankai wa kukana, kuma ina da yakinin zai amsa mun da yardan sa, "
Bushar yafashe da dariya kana yadaura dacewa, kinga wannan abun shi zai nuna muku karfin ikona akan ku keda ragon mutumin da kike son sa Bintu zan nuna miki nafi karfin kowa awannan duniyan, Bintu tace ae idan kafi karfin mu bakafi karfin Allah ba kuma Allah daya ne abun bautan mu kuma baya barcci, tayi tsaki tabangaje shi tashege cikin gidan kai tsaye dakin da take kwana tayi, kuka take sosai barci ba rawo ne kawai yasace Bintu,
Bintu 3:am dai-dai Bintu tashi futa adakin tayi kai tsaye bayi tayi tayi fitsari bayan tagama tayi alola, takoma d'aki wani kodaddan sallaya tashin fita ta da kafbara sallah tafara bayan ta idar hannayen ta sama tad'aga tafara zuba addu'a Bintu tace "ya Allah ya ubangiji na babu abin bautawa dagaskia sai kai Allah ya Allah dan wanda kayi duniya kayi lahira domin sa ya Allah dan wanda kace idan mun bisa za mushiga aljanna nan ka, dan Amina da Abdullahi Annabi Muhammad (saw) Allah nagawo kukana zuwa gare ka Allah ina rokon ka kazaba mun abunda yafi zama alkhairi awaje na,"
Tabbas Allah Allah ne kuma maji rokon bayin sa Bintu magana take da ubangijin ta kya kace tana ganinsa, tabbas shi yana ganin ta amma zuciyar ta yana hasko shi buwayi gagara misali, Bintu ta daura dacewa ya ubangiji kai ka halice ni bani da kowa bani komai
sai kai kuma da kai kadai na dogara, kai ne kace muroke ka zaka amsa mana, Allah katsaya mun da kanka, kada kabarni da iyawa ta dai-dai da kiftawan ido na bazan iyaba, Allah idan har wannan bawan naka alkhairi ne agari ne ina rokan ka da katabbar mun dashi amatsayin mijina, Allah idan har shi ba alkhairi baine kazabamun mafi alkhairi agarini, Allah zabin ka nake so, Allah kazabamun miji nagari wanda zai kula da rayuwata, sosai Bintu take addu'a tana kuka tana rokon Allah,"
Yayin da Bintu take addu'a haka ma Baffan ta shima yake addu'an wa yarin yar sa Allah yabata miji nagari wanda zai kula da rayuwar ta, haka ma Kaka da Alili ba abar so abaya ba,
Fada ya cika makil kowa soyake yaga wannan gasar da za'ayi da Bushar, wasu sunyi Allah wadai da wannan mutumin da yace zaiyi gasa da Bushar shin shi bai da hankali ne, wasu sunyi Allah wadai da Kaka, da kuma Alili, fada tacika kowa wanda yakasance dan kauyen guma ne yazo fada dan bawa idanuwam sa abinci da maza da mata, kowa yasa aran sa cewa fa wannan mutum da zasuyi gasa da Bushar shine zai fadi,
Angama cika y'an gasa kawai akejira domin fara wasa, Bushar yafito filin gasar yayin da Khalil yake gifen fili yana taraba idanuwan sawa Bintu dan gabaki daya atsorace yake, kama hannun sa, tafara masa magana cikin ruwan sanyin ta, Sadauki na kaman ta alkawarin da kamun nacewa yau zaka zamo jarumi wanda hawaye bazai taba fita daga cikin idanuwan saba? girgiza kai Khalil yashigayi kamar karamin yaron dayake daf da fashewa da kuka, yancewa ban manta ba ina sane Mimi, ya daura dacewa Mimi tsoro nakeji kigani fa bulalan da take hanun sa kuma dashi zai duke ni har guda dari jikina bazai iya dauka ba idanuwa na bazasu iya jure rashin fitar hawaye ba idan har aka zuba mun wannan bulalan ajikina, wallahi Mimi tsoro nake ji, yakarisa magana yana mai fashewa da kuka maicin rai wanda duk wanda yagan sa agun sai ya tausaya masa,
Bintu kama hannuwan sa tayi tace nasan Sadauki na jarumi ne wanda zai iya jure komai akaina idan nace komai ina nufin komai, numfasawa tayi kana ta daura dacewa ehh tabbas jikin ka bazai dauka ba amma zuciyar kafa, nuna kirjin sa tayi da yatsan ta tana cewa tabbas nayarda da matsayin da nake ciki ciki awannan zuciyar taka nasan zatayi komai akaina daga ciki harda hana idanuwar ka zubar da kwala, Sadauki kasan yadda nake jin ka acikin zuciya ta kuwa? Hmmm to inbaka sani ba yanzu zan fada maka, kana da matukar shiga rai, kana da komai, komai da yake dauke hankalin mai kallon ka Sadauki na, babu wani yanayin da za'ariske ka face sai anga wannan yanayin yada d'an kara maka fito da kyawun ka, Sadauki , numfasawa Bintu tayi yayin da hawaye ke zuba daga cikin idanuwan ta tadaura dacewa
Murmushi, damuwa, kunci, ko kuka duka afuskan ka ababen murmushi ne amma kuma yau bana bukatar hawayan ka, nasan kowa yana son ganin ka dan ganin wannan gasar bakai ne zakaci wannnan gasar, haka kowa yake fada, amma nikuma nasan wannan jarumin mazan shine zaici kasani fa idan har hawaye yazubo daga cikin idanuwan ka tabbas karasa ni dan haka dan Allah karkabari hawaye sufito daga cikin idanuwar ka.
Sosai Khalil yashiga cikin da muwa da yaji labarin idan har hawaye suka fita acikin idanuwan sa zairasa Bintu dan haka yace Mimi tabbas yau zaki kasance mai alfahari dani, tabbas hawaye bazasu fito daga cikin idanuwa taba haka Khalil yana ta, zan saka juriya acikin zuciya ta, sosai, bazanyi kuka ba addu'a kawai nake bukata,
Mekira ne ya fara magana dayan bangaran yazo saura dayan bangaran shuru har yanzu kodai yaji tsoro ne ya gudu, ae kuwa mutanin wajan suka fashe da dariya har anfara surutu ana cewa ae dama bazai iyaba matsoraci ne dama wazai iya da Bushar fili yaciki da surutun mutani, shikuma Bushar saiwani wage baki yake dajin anyaba masa, Bushar duk atunanin sa yazata gargadin da yayiwa Khalil ne yasashi guduwa, kawai bazatao ba tsammani sai ganin Khalil sukayi atsakiyar fili babu riga ajikin sa kamar dai Bushar, ae kuwa fili yasake fashewa da surutu.
Saida me magana yafara magana asaurara yanzu gasa zata soma dan haka kowa yazauna shuru yayi kallon gasa zamuga atsakanin Bushar da Garkuwa wazaiyi nasara, sosai mutani sukayi shuru suka nutsu danganin wannan gasar yadda zata kayya,
Kaka Alili Baffah gabaki dayan su basa cikin haiyacin su atsorace suke sungama sadaukarwa cewa Khalil yafadi sbd kafun sufito gidama kuka yake duk jikin su yayi sanyi,
Za'a fara cewar mai gabatarwa Bushar matso ae kuwa Bushar ya matso dawani uban bulala ahanun sa yana jujuyawa idanwan Khalil nae yadawo kan mutani ae tuni jikin sa yadau rawa, yayin da mutani sukaga wannan bulalan suka fara magana kasa-kasa suna nuna bulala ae wannan bulalan ko daya aka maka sai kayi kuka bare kuma dari haka mutani suke ta magana,
Mai gabatarwa yace wannan gasar takunsa abu biyu, dafarko Bushar zaiyi bulalawa Garkuwa har guda dari, idan har Garkuwa idan yayi hawaye kuma shikenan yarasa Bintu, idan kuma baiyi hawaye ba to nan da sati guda mako kenan za'asake dawowa domin gasar amma kuma akan Bushar shima za'a masa bulala dari, idan shima baiyi hawaye ba tofa tabbas za'acigaba da wannan gasar har sanda daya daga cikin su zaiyi kuka, dan haka mai gabatarwa ya kirawo Bushar yace zan kirga uku kacal, ina kamawa sai afara gasar,
Bushar tunkar Khalil yake da wata uban bulala ahannun sa, ae kuwa Khalil ganin wannan bulalan hanun Bushar yashiga cikin dimuwa harta kai ga yana kokarin barin filin baki daya, kamar akun nuwar sa yaji magana nan Bintu"koda jikin ka bazai dauka ba amma nasan zuciyar ka zata dauka nasan matsayin da nake dashi acikin wannan zuciyar taka, " ae kuwa Khalil yatsaya cak dumin yanajin maganar Bintu kamar yanzu take masa,
Mai gabatarwa kuma yafara kirgan sa, daya, biyu, uku, afara aekuwa, ae kuwa Bushar yadago bulalan nan yazubawa Khalil bawan Allah, adai-dai lokacin da Bushar yazubawa Khalili adai-dai lokacin Kaka, Alilil, Baffah suka runtsa idanuwan su dan ganin kar idanuwan su ganin halin da Khalil zaishiga, awannan lokacin kuma Bintu addu'a kawai takeyi yayin da Khalil addu'a yake tayi cikin zuciyar sa, tabbas Khalil yaji bulalan nan amma idanuwan sa sunyi jaa runtsa su yayi, babu alamun kuka attare dashi, saida Bushar yayiwa Khalil bulala biyar kamun ya tsaya dan duba idanuwar Khalil ko yayi hawaye amma kuma abun mamaki aduba idanuwar Khalil babu ko alaman hawaye aciki,
Ae kuwa mai gabatarwa yace aradu idanuwar Garkuwa babu ko d'igon hawaye ciki dan haka acigaba, ae kuwa Bushar yashiga cikin damuwa meyasa Khalil baiyi hawaye ba, amma kuma ae da saura da yawa, Bushar yacigaba da bulalawa Khalil har yana hadawa da mugun ta, saida yayi bulala ashirin kafin Bushar yatsaya dan duba idanuwar Khalil, dasuke aruntse mai gabatarwa ya zakayo wajan fuskan Khalil dan ganin ko Khalil yayi hawaye amma kuma har yanzu Khalil babu ko hawaye cikin idanuwar sa, ae kuwa, ae kuwa mai gabatarwa yace "aradu idanuwar sa ko ruwa babu, " ae mutani suka fara magana gaskiya yaburge ni jarumin gaske ne, a fuska kamar bazaiyi jarumta ba, mutani da yawa suka fara yabon sa suna zagin Bushar, dama tun can bason sa suke ba tsoron sa sukeji, amma kuma yau sunga wanda yafishi jarumta, kuma babu wata sihiri ajikin sa hakan ya matukar burge su,
Bushar kuma yashiga cikin tashin hankali sosai haka yacigaba da bulalawa Khalil har akagama bulalan batare da digon hawaye yazuba acikin idanuwar saba, ae kuwa fili yakafce da surutu da hayaniya sosai, anata yabon Khalil kai tsaye akanufa Khalil akayi sama dashi sai gidan Kaka jikin sa sai futar da jini yakeyi, yayin da mai gabarwa yana cewa tabbas Garkuwa ya gwada jarumta anan shima wata sati za'ayi nashi, Bushar bai tsaya sauraran duk wata magana nan da'akeyiba kai tsaye ya nufa wajan Bokan sa,
Khalil gabaki daya asume yake baima san yadda kansa yake ba, Bintu sujjad tayi tagodewa ubagijin ta, saida Kaka yayi maganawa mutani akan suyi hkr zasuyi maganiwa Khalil dan ayanzu yana bukatar maganin ae kuwa suka tsaya akofar gidan Kaka damuwar su Khalil ya farka dan yanzu cewa suke sunsamu jarumi agarin su wanda bashida sihiri ajikin sa, magani sosai agashigayiwa Khalil
Bushar zaune agaban Boka sai masifa yakeyiwa Boka, kace haba haba Boka kaifa da kanka kafadamun cewa tabbas sai yayi kuka idan har nazane sa da wannan bulalan amma kuma yau munyi gasar amma kuma ko kuka baiyi ba, Boka yadobi Bushar yace "tabbas shima wannan mutumin da kukayi shadi dashi naga abubuwa da yawa ajikin sa amma kuma ka kwantar da hankalin ka karka damu ba wata sati nakaba kabari idan har akayi naga akagama too zan fadamaka wata gasar daza ka sauya da wannan shadin dan haka ka kwantar da hankalin ka sosai Boka yake ta maganawa Bushar dan kwantar masa da hankali ae kuwa yayi nasara akan sa,
Alhmdullah jikin Khalil yad'an samu sauki har yana iya fita kofar gida, Alili yadubi Kaka yace Kaka bamusamu daman fadama cewa fa ran da mukaje daukan bulalan nan munga Bushar dashi da wani mutumin da gabaki daya ba'a iya kallon fuskan sa, munji tattaunawar su suna jayya da Bushar akan dole sai yayi amfani da bulalan da mukaje daukawa amma shi Bushar yace sam bazaiyi amfani da wannan bulalan ba, Kaka tsayawa yayi cak yana tunanin wanene wannan mutumin haka, gabaki daya kaka yafada duniyar tunani damuwan sa yagano wannan mutum, can kuma ya numfasa kana yadaura dacewa bakuga fuskan saba? Alili yace ehh kaka ae kuwa Kaka yace nifa ina ji ajiki na Kakan Bushar ne indai kuma takasance haka to tabbas akwai babban kad'ubali agaban mu dan Kakan Bushar babban matsafi ne, tabbas kuyi kokari kuma kudage danganin kunsamu wannan bulalan, dan wannan bulala tabbas zata taimaka muku,
Kaka yanumfasa kana yadaura dacewa kunsa masifar dake tattare da wannan mutumin Kakan Bushar, Shehu to tabbas akwai babban aeki agaban mu damuni muyi shadi dashi amma Allah yabani narasa akan sa, Alili yace insha Allahu Allah zaibamu nasara akan sa, yanzu haka zamusharya domin dauko bulalan nan kuma zamu dauko ta da yardan Allah, yau saura kwana uku gasar dan haka yau da dare zamuje, fatan alkhairi Kaka yamusu dafatan nasara,
SIDDARTH
_________________________________________
Siddarth wata daya yayi a Negeria yakoma Amireca domin kamala karatun sa abubuwa sunyiwa Siddarth yawa ga nauyin da Alh. Kaka ya daura masa ga kuma Zoey a wannan lokacin tana addaban rayuwar sa akan dole sai ya aure ta shikuma baiga abun so ajikin Zoey ba,
Zoey zaune ita da kawan ta mecol suna magana akan Siddarth mecol tace "Zoey ai tun farko nabaki wannan shawara amma kince ke bazakibi shawaran ba to yanzu yakike so nayi miki, " Zoeya tace mecol bazan wajan ki dan jan magana ba kuma banzo dan nabi shawaran kiba kawai nazo gunki, nazo gunki ne dan kisake bani wata shawara, nafuskan ta Siddarth shi mutum ne wanda kyalekyale bashi gaban sa kuma naga shi mutum ne wanda yakeson taimako, shine nazo kiban shawara akan abun da zan jawo hankalin sa gare ni, dan jam kadan mecol tayi kana tace kin san wani abu kawo kunnan ki infada miki,
Sana ce tafio daga loyala beach sanye cikin wando palazzo black colour da shirt riavy blue tayi rowling wani veil navy blue akan ta, tana rataye da wata yar bag black colour dayan hannun ta kuma na dama cup ne na coffe rike a hannun tafiya take tana shan wannan coffen tana lumshe idanuwan ta da sukayi jaa saboda kukan rashin wannan mutumin da yataemake ta yauma tagaji da kukan ne tacewa mom dinta zata fita shan iska ita dayan ta tafito babu Suha sai direba dake jiran ta a moto,
Siddarth ne yau gabaki daya baya cikin haiyacin sa tafiya yake cikin moton sa gawanu uban yunwa dayake ji dan rabon sa da abinci tun jiya parking yayi dai-dai loyola beach domin yana bukatar sha iska, fitowa yayi daga moton cikin shigar jamfa amma babu hula akan sa suman kan sa duk yabaje masa agadon bayan sa kai kace mace ne tafiya yake kamar wanda bai son taka kasa,
Sana tana shan coffen ta tana lumshe idanuwan ta gashi kuma tafada duniyar tunanin da ayanzu ya aure ta tuninin wannan mutum takeyi bata ankara ba da wani babban tudu dayake gaban taba tudun da idan tafada ciki to tabbas sai dai muce Allah yajikan ta gangara take kawai bata kula da gaban taba, mutani sai magana suke mata amma ina, bata jinsu dumin bata cikin haiyacin ta dai-dai lokacin da Siddarth yakai idanuwan sa gunda aketayin surutun mutani daura idanuwan sa yayi akan ta datake dafda fadi ai kuwa da sauri da gudu Siddarth ya nufo wajan ta rumgumata yayi sukayi kasa turmusu suka farayi akasa, wannan ya haukan wannan hakama wannan har suka isa bakin wannan tudun kuma Sana ne tayi kasa, rike hannun ta daya Saddarth yayi yana mata magana cikin zazzakar muryan sa mai dadin sauraro "karki sakeni kirike ni sosai tarike hannun sa yayin da dayan hannun yana lilo akasa da dukan jikin ta rikon da Siddarth yamata ne kawai ya hanata faduwa, kasa da tuni ta fada kasa magana yake mata cikin muryan sa karki sake hunnuna insha Allahu bazaki fadi ba, idanuwan ta tazuba masa babu ko kiftawa sosai take kallon sa kamar tasamu tv bataki su tabbata a haka ba miko dayan hunnu yayi akan tarike sa ai kuwa da tema kon Allah sai ga Sana tamiko janta yake har ya fito da ita daga ciki zubewa sukayi akasa yayin dashi yafadi dabaya ita kuma da ruf da ciki gashin kanta duk yarufe musu fuskan su sai da su sai da sukayi minti kusan goma kafun Siddarth yacilla ta gefe kana yadawo kusa da ita hunnun sa ya daga ya zafga mata mari kana yaja laben bakin ta ya kuma jaa yafara magana cikin sanyi muryan sa, "meyasa kike son kashe kanki, " abunda yafada mata kenan yabar gun,
Kallon sa take har yabar gun sai da tadaina kallon sa kafun tadawo haiyacin ta, bin bayan sa tayi amma kuma har yabar gun, kuka take tana surutu da sumbatu gabaki daya tafita haiyacin ta, direban ta haka yazo yasame ta, "madam lapiya wani abu yafaru dake ne" direban yake mata magana sam bata cikin haiyacin ta
Saddarth
_________________________________________
Haka Sana take ta kuka tana fadin nikam bani da sa'a acikin rayuwata kuka take da sumbatu, haka direban tama yanaata magana amma sam batasan yanayi ba,
Siddarth kai tsaye gida yanufa damuwa fal acikin zuciyar sa meyasa wannan yarinyar takeson kashe kanta tabbas zangano, dalilin ta, yana shaga parlo yatar da Raj, Raj magana yama fara masa ina kashiga ne bro ina tajiranka baka dawoba lapiya ko, samun guri Saddarth yayi yazauna, magana yafarayiwa Raj, "Raj ina son sanin gidan su, ina son sanin dalilin kashe kanta, meyasa take son kashe kanta, Raj kaine zaka nimomin ita, Raj dayashiga damuwa yacewacce haka wanda kakeso, nanimo maka ita haka Siddarth yace wanda nataemaka mata daga saman bene, yauma taso kashe kanta badan nazoba da kuwa tarasa kanta, tabbas jikina yana bani akwai abunda yake damun ta, dan Allah Raj ka nimomin ita, Raj yace insha Allahu karka damu,
Mom Razia zaune a parlon ta Suha agefan ta, suna dan firan su, kwai sai ga Sana tashigo da dugu tana kuka, kai tsaye gun mom dinta tayi tafashe mata da kuka, mom Suha duk sunshga cikin damuwa sosai sai tambayan ta suke, Sana nutsu ki mana bayani, Sana tana kuka tana fadawa mom dinta duk abunda yafaru tsakanin ta da Siddarth, sosai mom ta tausayawa yarinyar ta kuma rarrashin ta tashigayi, "ki kwantar da hankalin ki kisaka nutsuwa cikin ranki, tabbas idan alkhairi ne cikin rayuwar ki tofa tabbas da kansa zaizo gareki, haka Suha ta kwantarwa yar uwata hankali,
Tun daga wannan lokacin mom da Suha sukashiga kula da Sana basabarin ta ita daya, fadan dayake tsakanin Sana, da Suha yakoma shakuwa,
Sana ce zaune agaban simun full tasaka kafafuwan ta cikin ruwan, gashin kanta kuma gabaki daya yabazo mata akanta, magana takeyi ita dayan ta, hakika idanuwa ta sun rufe akan ka, haka zalika nazamo kurma akan ka, nayi nisan da bana jin kira akan ka bansan kaba, aduk sanda nake bukatar taimako kawai sai nagan ka amma kuma ka kasa taimakon zuciya ta, tabbas zuciya ta daftake da bugawa, tabbas zuciyata takusa daina aiki, wayyo so meyasa so zakimun haka? meyasa so zakishe geni? alokacin da banshirya ba? meyasa so zakishiga zuciyata? wayyo Allah tabbas so baki kyauta mun ba, taya zakiso wanda bai san inayiba baisan da zamata awannan duniyar ba, Sana kuka take sosai tana sumbatu baki daya tafita haiyacin ta,
Suha ne tazo gun tsayawa tayi cak tana kallon ta tabbas Sana tana bata tausayi sosai, Sana da soyayya bai da meta ba amma yau itace take kuka akan mutumin da baisan tanayi ba, inama inada daman mallaka mata shi da kuwa tuni nayi hakan, hannaye ta sama tad'aga tafara addu'a Allah ga baiwar ka nan Allah kashiga cikin lamuran ta Allah idan har wanda take so cikin zuciyar ta alkhairi ne Allah kamllaka mata shi, tana hawaye tana addu'a, share hawayen ta tayi, tanufi gun Sana
magana tafarayiwa Sana "haba yar uwata kidai na kuka, idan kina kuka tabbas zakija makan ki ciwo ne kuma zakisa mom din mu cikin damuwa tabbs ko wani mutum akwai yadda tashi son take kasance masa to kiyi hakuri mucigaba da addu'a tabbas idan har shi akhairi ne agare ki zaizo ne, idan kina kuka zakija makan ki ciwo ne, idan kuma abu yasame ki nikuma fa yazan yi, tabbas idan mukarasa ki nima tabbas sarani za'ayi, idan kuma dukan mu bamu nan ya mom dinmu zata sakan ta yanzu ma bata farin ciki ga damuwar Abbi ga kuma kullum kina cikin kuka kinsan yadda takeji cikin zuciyar ta kuwa? Sana kiyi shuru dan Allah yar uwata.
Sana tace Suha dole nayi kuka baki san yadda nakeji cikin zuciya ta bane zuciya ta tana mun zafi ina jin tamkar narasa wani bari ajiki na, Suha soyayya tasani arudani tabbas so bai kyauta mun ba, Suha ina jin kamar kwaniki na sun kusa karewa, kuma tabbas soyayyar wannan bawan Allah ne, yashiga cikin rai na ya zauna ta ko ina ina jin sa, ina jin sa ajikina, ina jin sa, akunnuwa ta, ina jin sa a komai na, Suha idan nace komai ina nufin komai, kuka dukan su biyu suke kamar wanda akamasusu mutuwa, babu mai rarrashin wani acikin su.
Suna cikin kukan su ne sukaji hayaniya a part din su ai kuwa gabaki dayan su, sukayi part din su danganin meyake faruwa,
Abbi ne da Ammi sunsaka Mom agaba suna mata fada kamar y'ar su, Abbi yace wallahi Razia kifita acikin idanuwa ta zan iya koran ki cikin gidan nan kece kike goyawa yaran ki baya suna abunda sukeso ko, tam kifada mayaran ki cewa aurar dasu zanyi nan da sati biu, kuma sadakan su zanyi dasu, kuka sosai mom Razaia takeyi takasa magana, haka zalikama su Sana, sai kuka sukan suna ganin rayuwa meciki da bakin ciki da tashin hankali, tabbas kowa da kallan tasa kaddaran sa, sukan nasu ahaka tazo, haka Abbi da Ammi suka tayin fada suka bar parlon,
Suna barin parlon Sana da Suha sukayi gurin mom din su suna kuka mai karya zuciya, tabbas suna ganin jarabawan rayuwa, gabaki dayan su suka kwanta ajikin mom din su, suka fara mata magana "mom kiyi hkr kiyi shuru Allah shine zai saka mana duk abinda Abbi yake mana" Mom Razia tace "damuwa na ku aure sukace zasu muku kuma ni gaskia bazan bari amuku auran dole ba, zanyi iya bakin kokari na wajan gani basu muku auran dole ba, Suha tace mom ki kwantar da hankalin ki babu wanda ya isa yama na auran dole, idan har ina raye haka Suha tafada, tadaura dacewa mom to mubar musu gidan su mana, Sana tace bazamu nar wannan gidan ba, kinmata gidan nan da komai mallakin mom din mune, dan haka bazamu bari ba Allah yafisu, mom batace musu komai ba kawai kallon su take tana tunani acikin zuciyar ta.
KAUYE GUMO
_________________________________________
Yau garin antashi da zafi sosai iskan bazara sai kadawa yake, alamun ruwa zai iya saukowa a ko wani lokaci, Khalil ne zaune agaban Bintu, Bintu tace tabbas Sadauki na kasani farin ciki, zuciya ta bazata iya musulta maka yadda nakeji cikin zuciya taba wai yau kai kai Garkuwa na wanda nake fatan yazama alkhari acikin rayuwa ta yau shine akayi shadi akama sa duka har guda dari amma idanuwan sa babu ko alamun hawaye acikin su, tabbas ina alfahari dakai ina rayuwa dakai ina son ni nakasance uwa tagari gurin y'a y'an ka, kaima kazama uba nagari gurin su tabbas zuciya ta ta yarda dakai kuma nayi maka alkawari idan har nakasance mata agare ka zanyi maka biyayya kuma zan kula dai nawan, Khalil ya dubi Bintu ya numfasa kana yadaura dacewa "Mimi yanzu duk wannan kallaman duka ni daya, tabbas nine nayi sa'a acikin rayuwa, tabbas Mimi komai ki kaga yalalace tofa yarasa uwa ne to mema za'a kira da gidan da babu uwa acikin sa? Kango fa kenan, ko wani gida daya amsa sunan gida yana da uwa acikin sa, Mimi kinsan menene gidan? girgiza kai Bintu tayi tace bansani ba, Khalil ya numfasa kana yadaura dacewa wannan gidan kece Mimi uwar gida sarautar gida na, farin cikin gidana sirrin gida na, Mimi kefa gani nan bari ne sirrin tskar gida na, idan anmiki daya ta arziki tofa sai kin masa goma ta arziki, Khalil ya numfasa kana yadaura dacewa, ke tadaban ne kin hada komai Mimi idan nace komai ina nufin komai Mimi ke mai hakuri ne da sanin yakamata taya bazan jure komai akan kiba, ga kuma sanin yakama ta, Mimi ina son ki anan duniya har da lahira ina fatan dani dake mukasance tare agidan Aljanna tare da yaran mu ina alfahari nazamawa yarana uwa tagari, a ko wani irin lokaci inana matukar son ganin fuskan ki Mimi na,
Hmmm ina rubuta ina tunanin anya Khalil tunanin sa baidawo ba irin wannan kallaman haka,
Bintu tsaban dadin kalaman da Khalil yamata har rasa yadda zatasa kanta tayi, Khalil yadube ta yace tabbas idan har Bushar baiyi kuka ba nadau miki alkawarin jure ko wani gasan da zamuyi Mimina nidai fatana addu'an ki kuma yau da dare zamuje daji mai hatsari domin dauko wannan bulalan dan Allah Mimi ki kara mun addu'a akan wanda kika saba, dan Kaka yace dajin akwai hatsari acikin ta.
Bintu tace tabbas nayi sa'a acikin rayuwa ta kuma insha Allahu zan cigaba dayi maka addu'a Allah zai shiga cikin lamuran ka Allah zai tai make ka duk abunda kasa agaban ka nawam, Allah ya Allah ga wannan bawan naka Allah kashiga cikin lamurun ka Allah yasaka nasara agaban ka da bayan ka Allah Allah Allah ya ubangiji na Allah wannan bawan kaine mai kaunar ka da maka biyayya Allah yamaka jaroga aduk inda kasa kan ka nawan, Amin Amin Amin Khalil yace yana mai zubawa Bintu riki tattaun idanuwan sa tabbas yaji dadin wannan addu'ar da Bintu tamasa, Bintu ta numfasa ta daura dacewa, "kasan wani abu kuwa? nawan, girgiza kai Khalil yayi yace sai kin fada matar Aljanna, Bintu tace "nifa akan ka na yarda soyayya gaskiya ce, nayarda hakika soyayya taha hauka ta mutum, nashiga cikin rudani a lokacin sadin nan zuciyata ta karye idanuwa na duk sunfito waje, tun daga lokacin da kashigo rayuwa ta komai sabo take zuwa mun, ka cancanci na son ka, Allah yabaka komai, kai kyakyawa ne, gason addini hmmm Allah nagode maka da kahadini da wanna bawan naka,
Sosai Khalil yaji dadin kalaman Bintu har yasa mai zace mata, hawaye ne yashiga zubowa daga fuskan Bintu, arude Khalil yake tambayan ta lapiya wani abu namiki? girgiza kai Bintu tayi tace dan Allah idan mukayi aure mufita katayani niman iyayena tabbas ina son ganin su bawai dan banso Baffah bane sai dan ina son ganin uwata da ta haifeni kuma tafadamun dalilin yardani da tayi, kama hannayen ta Khalil yayi yace Mimi na ki kwantar da hankalin ki muna aure bada jimawa ba zamu fita niman iyayan ki, sosai Bintu taji dadi kuma a zuciyar ta sai kara godewa Allah take da Khalil yashigo wannan kauyen har yakawo mata agaji, tunwa tayi da lokacin da Inna Jummai take dukan ta, Khalil yana ce tabari amma taki haka yafita yadauko bakin wuta yazafga mata ajikin ta, tsabar farin ciki bata san lokacin da ta kwanta asaman kafadan saba, tana furta masa kalamai masu dadin sauraro da sanyayya zuciyar masoya,
Khalil Alili dukan su durkushe agaban Kaka duk sunshiya da alama dai lokacin tafiyar su wannan dajin dauko wannan bulalan da Kaka yafada musu yayi, Kaka magana ya fara musu, tabbas wannan dajin sai kun kula sosai dan awai hatsar aciki sosai, nasake binciko dajin kuma tabbas nagano wani abu agame da wannan dajin, kuna shiga dajin zakuga hanya takasu kashu uku ne, akwai hanyar da amike take, akwai kuma hanyar da take dama, akwai kuma haryan datake hagu, hanyar data meke wannan hanyar ba kowa bane yake shigan ta ko shima kansa Bushar din bazai shiga ba, hanyar mace ce kawai zata iya shiga idan har tashiga wannan hanyar babu tabbas zata iya dawowa da ran ta, wannan hanyar ya kunsa abubuwa da yawa, kamar bishiyoyi masu furan ni da kyawun gani, idan mutum yashiga wannan wajan to tabbas zaiyi matukar burge sa, amma kuma akwai abubuwan ban tsoro acikin ta, akwai manya-manya Aljanu wanda su mutani ne kawai abincin su, duk randa bil Adam yashiga wannan daji to tabbas zaiyi wuya yadawo, bayan haka akwai majizai, akwai kuma namumin daji kamar su, Damisa, Zaki, da sauran su tabbas akwai hatsari acikin ta, Allah ma yataimaka wannan bulalan batacikin wannan dajin bayani nake muku yadda zaku fahimta kuma karku sake kushe ta dan bata da kyau ko kad'an.
Numfasawa Kaka yayi yadaura dacewa "hanyar hagu kuma itama akwai hatsari amma kuma bai kai sauran ba, domin hanyar, mayu masu cin naman mutani su suke zama agun, amma har yanzu basu gano akwai mutani a wannan kauyen namuba, dan haka kukiyaye fatan kuna fahimta na,
Girgiza kai sukayi alamun ehh sukace " muna fahimtar ka Kaka, kaka yadaura dacewa, hanya dama kuma itace hanyar da zakubi amma kuma akwai hatsari kafun ku uce waje uku da zaikai ku gurin bulalan, hanya tafarko sai kun wuce taikun ruwa wato kogi, wannan kogin akwai abubuwa da yawa ciki sosai dan haka sai kun kiyaye, hanya ta biyu kuma zakuyi fada da Aljani guda biyu dukan su zasufito muku asufar mutum ne kuma masu kama daku, daya zaiyi kama dakai, yanuna Khalil, daya kuma zaiyi kama dakai yanuna Alili, zakuyi fada tsakanin ku, amma yadda matsalan take shine karku ta fada da junan ku kuzata Aljanun ne domin gabaki dayan su asufar ku zasu fito, dan haka mekewa Kaka yayi yadauko wani ruwa acikin gora, yamika musu yace wannam ruwan zam-zam ne zai taima ke ku sosai wajanwa inna bakaken Aljanun, guna ganin sunfito gaban ku sai ku watsa musu da sauri to tabbas zakushiga lapiya, sai hanya ta uku akwai kananun abubuwa masu cutarwa dan haka sai kun kula sosai, tabbas idan anshiga wannan dajin ko ayi nasara ko kuma mutum bazai dawo ba.
____sosai Kaka yayi wasu Khalil bayani yadda zasu fahimta daga karshe ya musu fatan alkhairi da fatan nasara acikin tafiyar su,
Fita sukayi daga cikin gidan kai tsaye hanyar dajin nan suka nufa suna tafiya babu wanda ya tamkawa d'an uwan sa kowa da abun da yake sakawa cikin zuciyar sa,
Sun iso bakin dajin tsayawa sukayi cak wannan ya kalli wannan haka suka ringayi daga karshe suka yanke hukuncin shiga ciki,
Alili yace "mushaga Garkuwa" haka kuwa sukashiga da Bismla, suna shiga sukaga hanyar kashi uku kamar dai yadda Kaka yace musu,
Hanyar kashi uku ne kamar yadda kaka yace musu, amma kuma ganin ta yafi jinta gefe-gefen hanyar furanni ne sosai suncika gun masu kyau da kamshi tabbas idan kadaura idanuwan ka awanan gun bazaka taba yarda akwai abun cutarwa agun ba, furani ne kyawawa kananu da manya, ga bishiyoyi sunyiwa gun k'awanya, ganyan bishiyoyin kyawawa masu kashi jiki, furan ni gasan gun kuma kyawawan k'ananun furani ne masu kyau da kawata kallon wajan,
Khalil kashim wannan furannin ne sukayi tasirin acikin zuciyar sa sai yanajin ina ma shida Mimin sa ne agun,
Gabaki dayan su sunsha galtu da kallon gun domin ya matukar burge su, kukan tsuntsaye ne dasuke ta yawo atsakanin wannan furan ni ne ya farkar dasu daga shagaltuwa da kallon wannan dajin mai cike da kamshi,
Alili yace "yakamata mushiga fa kaga lokaci yana kure mana" Khalil duban sa yayi yace gaskia wannan wajan ya matukar burge ni sai nake jin dama ina tare da Mimi na ana wajan" Alili yace "kadaina wannan tunanin dan nawajan akwai hatsari sosai cikin ta, yakamata muyi abunda yakawo mu mubar nan wajan tukafin wani abu yasame mu",
Haka kuwa sukayi gabaki dayan su suka bi wannan hanyar da Kaka yace musu,
Suna shiga suka tsaya cak ashe basuyi kallo ba, kogi ne babba mai fadi sosai ga tsayi gabaki daya furan ni ya kewaye wajan gawasu bishiyoyi masu kyau da haske yabaza gun da kyau, nace wow wow wow daga wani waje gabai dayan ta bishiyoyi ne suka kewaye gun y'ay'an bisiyoyin sunfiffito ajikin bishir ga bishiyar sai haske take kamar wanda akasaka masa wutan lantarke haske yagama gauraye wajan, wasu kyawawan furan ni ne wanda yanayin jikin sa kamar zanan love, wow masu karatu sai kunga gun yayi matukaryimun kyau sosai,
Khalil yadubi Alili yace ta ina zamu hai wannan kogin, Alili yace ae kuwa Kaka bai fada mana ba, tsayawa sukayi suka zubawa sarautar Allah ido dan sunsa koda giya sukasha basu isa subi wannan kogin ba , batare da wani taimako ba,
Wani gefe guda kuma wata kofa ce wanda gabaki daya furan ni sun fure gun sai ka lura sosai kafun kagane gun akwai kofa, Khalil ne yakai idanuwan sa gun kuma Allah yanufe sa daganin kofar haka kuwa Khalil yace "Alili kaga wata kofa acan wata kila musamu abunda zai hayarda mu wannan gun, "
Ai kuwa Alili yace muje haka kuwa sukayi, tunkaran wannan kofar sukayi tafiya suke har Allah ya isar dasu wannan gum,
Wani haske ne ya cika musu idanuwan su haske ya mutu ya kunnu haka haske yake tamusu Alili da yagama tsorata har yafara jada baya yana magana "Garkuwa nifa Allah tsoro nake ji kar wani abu yacutar damu, " Khalil yace "Alili ka kwanatar da hankalin ka insha Allahu babu wani abunda zaicutar damu, "
Alili kama hannuwar Khalil yayi kam suna tunkarar wannan kofar da gabaki daya furan ni sun rufe gun ga kuma wannan hasken yana ta walwal,
Murya suka faraji sama-sama ai kuwa Khalil Alili suka rumguma junan su, suna kam-kamme junan su, gabaki dayan su sun tsorata da magana nan dasuke ji amma kuma basa ganin mutumin, magana yake musu amma kuma basa ganin sa, yace musu "kunutsu zan muku bayani yadda zaku fahimta, ai kuwa tsayawa suka yi cak duk da haka jikin su bari yakeyi,
Mukullin wannan kofar yamika musu yanace musu, " wannan mukullin itace zatakai ku yadda zakusamu abunda zai tsallake ku daga wannan kogin",
Dif suka daina jin magana nan mutumin, Khalil ne ya dauke wannan mukullin, suka tunkara wannan kofar mai cike da fulawowin nan, suna isa suka fara kokarin bud'e kofar da taimakon Allah suka bude kofar, kutsa kansu sukayi ciki, kukan tsutsaye suka ji yana kewaye gun, kananu-kananun furan ni ne jajjaye maso kyawun gani sun kwan-kwanta akasa gefe guda kuma fararan furanni ne atsatsaye sun kewaye gun, abun shawa,
Khalil, Alili, tsayawa sukayi cak sunrasa yadda zasu nufa, sunrasa abunyi babu wanda yake magana wa d'an uwan sa cak kuma sukaji wani abu a saman kan su ai kuwa Khalil Alili kayin su, suka daga sama dan ganin abunda suka ji asaman kayin su,
Wata jirgin ruwa ne mai kirar zinare take sakowa, ai kuwa idanuwa suka zuba mata har ta sauko kasa, dai-dai gaban suta tsaya cak, kujera guda biyu acikin ta kasan jirgin kuma furar ni ne aciki, gabaki daya gurin yayi ma Khalil kyau sosai,
Muryan wannan mutumin sukaji yana ce musu kushiga shine zai hayar daku wannan kogin, duk da jikin su yana bari amma kuma sai da suka shiga cikin jirgin,
Still muryan mutumi nan suka sake ji "kurufe idanuwar ku, ae kuwa suka rufe kam, tare da kamkamme junan su,
Haka jirgi nan ta rufe su gam, kai tsaye jirgin tayi sama da su kogi nan tayi kai tsaye tana zuwa tadawo kasa, kuma still idanuwan su arufe take basu yarda sun bude ba duku da yadda aketa wena su amma kuma basu bude ba, jirgin ne tayi kasan ruwa da su, ai kuwa ruwa ya lulube su, basu sanda suka bude idanuwan suba, ganin su sukayi cikin ruwa, ga kuma kifaye masu hadiye mutum, ga kuma kada masu cin mutum abubuwan ruwa wanda suke cutar da mutum babu wanda babu cikin wannan kogin, Alili harda fitsari a wandon sa, yayin da Khalil duk addu'ar da tazo bakin sa shiyakeyi,
Kwan nan su daya cikin ruwan nan sunga, tashin hankali har sun fida rai da rayuwa, har sun sadakar mutuwa zasuyi dayake kwa nan, su yana gaba da taima kon Allah sai gashi sunfito amma gabaki dayan su basu cikin haiyacin su, abakin kogin jirgin takifar da su, tajuya abunta,
Sam basu masan sufito daga cikin kogin ba, gawani uban yunwa adadde su,
Muryan wannan mutumin sukaji yana musu magana, "lokaci yana kure muku fa akwai sauran k'alubali agaban ku fa"
Kamar a mafarki suke jin maganan nan ai kuwa da sauri suka tashi sai ganin su sukayi abakin kogin, gaggara mekewa sukayi hancin cikin su sai murda musu yake tsabar yunwa, abinci suka gani agaban su, magana suka sake ji kuci abincin nan lokaci yana kure muku, ai kuwa suka faracin abincin nan sai da suka ci suka sha ruwa, mekewa sukayi suna jiran abasu umarni dan basu san ta ina zasubi ba,
Muryan mutumin nan sukaji yana magama saura tsallake ta biyu kuma nasan kunsani dan Kaka yafada muku dan haka ni taima kon da zan muku shine kawai nunamuku hanyar, ai kuwa haka yayi kawai ganin su sukayi agaban wata hanya, ai kuwa sukashiga kallon junan su wannan yaga wannan haka
Wata kofa suka gani tana mutsi, ai kuwa suka kam-kame jikin su, gabaki dayan su atsorace suke kowa da abunda yake rayawa acikin zuciyar sa,
Ai basuka tashin hankali ba sai da sukaga kofar nan ta bude ai asannan maganar Kaka ta dawomu su hanya uku ce na farko kogi ne ta biyu kuma Aljannu masu kaga dasu, ai gabaki dayan su suka rake junan su,
Basu gama tunani ba sukaga Aljannu nan masu kagama dasu sak sunfito ta wannan kofar, wayyo Allah na zo kaga yadda Khalil Alili suka shiga cikin rudani, ai ruwan zam-zam din da Kaka yabasu agani ba ai kuwa Ajannu nan suna tukaran su, sukuma suna ja da baya, gabaki dayan su arude suke basuka ruwan zam-zam din nan ba ga kuma suna daf dasu, sun sadakar shikenan taso takare, ai bazato ba tsammani sai ganin ruwan zam-zam dinan sukayi agaban su alokacin Aljannu nan suna daf dasu, ai Khalil yana ganin ruwan zam-zam dinan akasa, yayi kasa yadauka yawatsa musu, lokaci guda suka bace, Alili duk bai san abunda yake faruwa ba sai da Khalil ya tabashi ai kuwa atsorace ya bada kai duk atunanin sa wannan Aljnun ne sukayi nasaran kamashi, amma shurum da yaji ne yabashi daman bude idanuwan sa, babu su babu alaman su, ai sauke ajiyar zuciya yashigayi, gabaki dayan su suka zube akasa suna mai da numfashi,
Sai da suka gama sauke numfashi kafun Alili ya tambaye Khalil maiya faru ne meyasa wannan Aljanun suka rabu dash, gabaki daya abunda yafaru Khalil ya fadawa Alili, Alhmdullh kawai Alili ya iya furtawa,
Gabaki dayan su sunmanta aikwai, wani aiki agaban su barci mai dadi ne ya dauke su, sai daf yamma suka tashi ganin duhu sukashi ga tashin hankali baki dayan su,
Suna tunanin da ina zasubi kuma yanzu, ae basuka gama tunanin suba suka ji muryan mutumin dazo nan yana musu magana,
Tabbas lokaci ya kure muku dan saura kwana daya shadin ka amma kuna zaune anan kuna bacci kuma kunsan akwai wani tafiyan agaban ku ko to tabbas kutashi tsaye zan nuna muku hanyar ta karshe sai ku kula dan nasan Kaka yafada muku akwai namumin daji wanda tabbas a yunwace suke musaman idan dare yayi kuma dole kutafi da daran nan saboda gobe ne wannan gasar, taku,
Ganin su sukayi awani katafaran daji mai duhu sosai, gabaki daya kukan namomin daji suke ji ya kewaye dajin ku ina suka bi kukan sukeji, tsayawa sukayi cak suna tunanin ta ina zasuyi kuma ta ina zasu ga wannan bulalan,
Bazato batsamani kawai ganin zaki sukayi tayi kansu, ai kuwa gabaki dayan su, suka rasa yadda zasu nufa Alili fisari yafara Khalil kama hannun sa yayi suka fara gudu, suna gudu zakin nan yana bin su, ai kuwa sauran abubuwan cikin dajin sukaji ai gabaki dayan su suka nufe su suka hau bin su,
Tashin hankali da ba'a saka masa rana kenan Khalil tuntube yayi yazobe akasa gashi wannan namomin dajin suna daf dasu wayyo Allah Alili kokarin sa yataimaki Khalil amma kuma yakasa dan gabaki daya a tsorace yake shima,
Da taimakon Allah Khalil ya mike yayi gaba gudu suka cigaba dayi, gudu gabaki dayan su sunfita haiyacin su,
Gudu suke sosai da sosai duk yadda kafan su tanufa dasu haka suke bin gun,
Wani babban kofa ne mai kiran zinare gabaki daya guri jajayen furani ne komai nagun launin jaane, Khalil Alili tunkaran kofar sukayi suna tunkaran ta kofar tana buduwa, suna kariso bakin gun kofar ta budu gabaki daya, ai kuwa suka shiga da gudu, kirif kofar ta rufu,
Sauke numfashi suka shigayi, gabaki daya dakin launin jaa ne acikin d'akin komai na d'akin launin jaane,
Tsayawa sukayi ta ina ne zasuka bulalan, Alili yace "taya zamuga wannan bulalan kuma jina yana bani anan ne bulalan take",
Khalil yace " Kamar yadda Kaka yafada mana cewa bulalan tana cikin wani kwanu ne, mai murfin roba, dan haka buduba duk kwanu mai murfin roba na cikin d'akin nan",
Ai kuwa haka sukayi duk kwanu mai murfin roba sukashiga dubawa,
Wani kwanu mai launin jaa kiranta kiran maciji ne murfin roba, Khalil nufan gun yayi ai kuwa yana zuwa yana addu'a, hannun sa yakai kan murfi da bismila ya bude murfin wata zufgegiyar bulala ne aciki, dauko bulalan yayi kana ya daura idanuwan sa agan ta bulalan babba ne sai sheki takeyi sosai irin sosai dinan,
Alhmdullahi Khalil yace ya duba Alili dashima yake tafaman furta Alhmdullh haka kuwa suka ta murna sosai,
Kofar ce tafara rufewa ai kuwa murna ta koma ciki sukayi kofar da gudu dan karta rufe dasu aciki,
YAU RANAR SHADI
_________________________________________
__fada yacika makir kowa ya halata a fada dan ganin yadda wannan gasar zata kasance yau tsakanin Garkuwa da Bushar,
Bushar yace yasamu Bokan sa yabasa wani magani yace masa yashafa ajikin sa, dan idan yashafa ajikin sa to tabbas bazaisan ana dukan saba,
Dan haka gabaki daya Bushar yashafa maganin nan ajikin sa, da wuri yazo fada dan yana cike da farin ciki ya kosa dan ganin yau anyi wannan gasar, dan yacanza wata gasar daza'ayi,
Kaka gabaki daya acikin rudani yake yarasa yadda zaisa kansa dan babu alamun su Alili gashi kowa yazo dan ganin gasar nan
Bintu tashiga rudani , kai tsaye tayi gun Kaka dan tambayan sa ina su Khalil suke,
Bintu tasamu Kaka tace "Kaka ina su Alili har yanzu basu dawo bane Kaka, "
Kaka yace "har yanzu basu dawoba ina jin tsoro kardai wani abu yafarau dasu ne shiyasa basu dawo ba, sosai suka shiga cikin damuwa, Bintu kuka take sosai,
Idanuwan Kaka yayi jaa sosai sam baya cikin haiyacin sa,
Fada kowa yazo mai gaba tarwa ne yafara magana " Kowa yazo ina Garkuwa, ina Garkuwa, ina Garkuwa, ina yaje tabbas idan Garkuwa baizo ba yabata wasan sa, kuma tabbas Bintu zata aura Bushar,
Zan kiraka sau uku idan bakazo ba to tabbas, gasa takare daga nan tunda kai kayi wasa da gasar.
Ina Garkuwa daya, ina Garkuaa biyu, ina garkuwa uku kafun yarufe bakin sa sai ji sukayi ganin,
BARIMU KOMA BANGARAN MANGA FAMILY
________________________________________
Arjun kwace a bedroom dinsa jikin sa ya dau zafi zazzabi ne yayi mungun kamashi, kwance yake a kan bed din sa,
Aaraw ne yashigo bedroom din sa, zama yayi akusa dashi kama hannayen sa yayi yafara masa magana cikin sanyin muryan sa wanda yanzu tunani ya gama gauraye rayuwar sa akan brother sa yana matukar tausayin d'an uwan sa,
Magana yafara masa "haba dan uwa na karege damuwa cikin zuciyar ka katashi muje muyi breakfast, ummi da daddy suna jiran mu a parlau,
Arjun yadubi Aaraw yafara magana " Aaraw ina cikin damuwa sosai narasa yadda zanyi kaina ya dau zafi sosai narasa ina zansaka kaina,
Kullum idan na kwanta barcci sai nayi mafarkin ta, zuciya ta tana matukar son ta, ina son ta sosai irin sosai dinan,
Aaraw yace nasani Arjun amma yanzu muje parlau muyi breakfast kaji, haka suka fito parlou,
Ummi da Daddy duk suna jiran fitowar su, bayan sunfito kai tsaye dining area suka nufa bayan sun zauna, Arawa yace "morning ummi na"
Morning haw are u autana, cewar ummi turabaki Aaraw yayi, ummi kina mai dani Auta fa, haba my son idan ban mai dakai Auta ba towa zai zamo auta na,
Turabaki yayi kamar zaiyi kuka, Daddy yace ni kuma bazaka gaishe niba ko, turabaki yayi yace ai ina jiran nagama da ummi na ne sai nadawo kan daddy na gabaki dayan su sukayi murmushi,
Arjun yace barka da safiya uwa tagari fatan kin tashi lapiya, ummi tace "lapiya kalau d'an albarka, Alhmdullh" masha Allahu Arjun yace kana yadaura idanuwan sa akan daddyn sa, abun alfahari na fatan katashi lapiya,
Daddy yace Alhmdullh natashi ina kaunar ku Allahu yacika rayuwar ku da farin ciki, sosai sukaji dadi kuma suka amsa da Amin,
Daddy yace "yawwa dama ina son magana daku baki dayan ku, fuskan sa yadaura akan Arjun kana yasoma magana Arjun zakatafi india,
Arjun yace " daddy India kuma meyafaru wani abu yafaru ne?
Ummi ma tace wani abu yafaru da su hajjo ko? gabaki dayan su sun rude, daddy yace babu abunda yafaru sai Alkhairi, kana ya daura dacewa Arjun zaije ganin yar uwa jan yayan ki ne Sima,
Arjun Aaraw suka mai-mai ta sunan abakin su Sima yarinyar da bata da kunya ko kadan,
Daddy yadaura dacewa tajima tanason Arjun, mahaifin ta yajima da mun magana amma kuma nace mubari bayan zuba sai nan gaba, yadan numfasa kana yadaura dacewa jiya kuma nagano matsalan da take damun Arjun naciwon mara tabbas yana bukatar mata, shiyasa nayanke hukunci tunkafin abun yafi karfin mu,
Mai da idanuwan sa yayi kan Arjun yace nasan zakaji dadin Sima saboda tana son ka sosai dan haka kafara shiri zakatafi India,
Ummi gabaki daya tashiga cikin rudani dan tasan yaron ta yana son wata yarinya amafarkin sa,
Aaraw har yabude baki zaiyi magana, Arjun ya katsae sa, ya kalla daddyn sa yace "yaushe kake son natafi,"
Daddy yace "duk sanda kashirya,
Bayan kamala breafst kowa yabar daning din yayin da daddy yayi office,
Ummi ta dubi yaran ta tasoma magana cikin tausayin Arjun din tace " Arjun mai yasa baka fadawa daddyn ka kana da wanda kake soba? bayan nasan bazai maka auran dole ba,
Arjun yace ummi na har yaushe zanta dakon soyayyar da babu ita, ummi bantaba ganin ta azahiri ba, sai amafar ki na kawai, ummi zanyiwa daddy biyayya, zan aura Sima insha Allahu duk da atsarin rayuwa ta bana da ra'ayin auran mace sama da daya amma kuma duk abunda Allah yatsara dai-dai ne,
Ummi tace Allahu yanuna maka wannan yarinya gabaki dayan su suka amsa da Amin,
Sun tausayawa Arjun sosai, Arjun sai shirye-shryen tafiya yake,
AMERICA
_________________________________________
Mom Razia zaune a parlou, gabaki dayan su, suna cikin damuwa sosai, Sana tace "mom yanzu yazamuyi",
Mom kallon su tayi tasoma magana cikin tausayin yaran ta, " ina son ku sani duk wata matsala da tasame ku, kada kuyi kokarin guje mata kutun karai ta kusa aran ku ko ina nan ko bana nan zaku magance matsalan ku y'a y'a na tabbas kowata matsala akwai maganin ta, ina ji ajiki na duk wannan abunda yake faruwa damu watarana zai zamo labari, "
Dan haka kujigaba da addu'a tabbas addu'a tana canza kaddara, kuma kusani duk abunda yasamu bawa to fah tabbas MUKADDARI NE DAGA ALLAH,
Sosai mom Razia tayi nasihawa yaran ta, cigaba da tattaunawa sukayi akan yadda zasu fuskan ta matsalan su,
Mom Ninah ne zaune a parlou ta waya take da kawan ta Maro, tattaunawa suke akan wata magana, mom Ninah tace "nafadamiki nagaba da Sana dan zan hadata aure ne da wani mutum talaka ne sosai, Suha ne bansan yadda zanyi da itaba tana da taurin kai,
Dayan bangaran Maro tace ita kasheta zamuyi dan haka zamu nimo mutani da zasu gama da ita, Mom Ninah tace wannam gaskiya ne dan haka zuwa gobe ita zamu gama da ita Sana kuma bayan rasuwa Suha sai na aura mata wanna talakan, sosai Mom Ninah tayi na'am da shawaran da kawan ta tabata,
Gabaki daya wayan da Mom Ninah tayi akunna nan Sultan ne, bai bari Mom din sa tagan saba yabar parlon kai tsaye part din su Mom Razia yayi,
Suna cikin tattaunawa saiga Sultan yashigo abujajan kamar wanda aka biyosa, sai haki yakeyi, Mom Razia ne tameke ta nufi gun sa, kama hannun sa tayi tazaunar dashi akujera tadauko ruwa mai sanyi tabashi sai da yasha kafun nutsuwa tafara dawo jikin sa bayan, nutsuwa tagama gauraye jikin sa,
Ya fuskan ta Mom Razia yasoma magana "Mom yakamata Suha tabar gari nan tabbas idan bata bar gari nan ba komai zai iya faruwa da ita, "
Mom Razia tace ban fahimta ba ka nutsu kamun bayani yadda zan fahimce ka, Sultan gabaki daya abunda kunuwan sa sukaji masa agun Mom dinsa yafadawa Mom Razia, ai gabaki dayan su suka shiga cikin rudani sosai,
Sana tace "mom yanzu maiyi abunyi ina Suha zataje ",
Shuru Mom Razia tayi tana tunanin, gabaki dayan su zubawa Mom idanuwa sukayi, yayin da Suha take fara rayawa cikin zuciyar ta babu inda zataje ai yanzu Mom dinta tagama fada mata duk matsalan da tashafi kai karkace zaka guje mata ka fuskance ta, to tabbas zan fuskance wannan matar, kuma lokaci yayi da yakamata ta nuna mata ita ba tsoron ta take jiba,
Mom Razia ta numfasa kana ta daura dacewa "Suha zata tafi India akwai gida na acan kuma tabbas Suha zata ji dadin zaman gun dan gidan agefen kankara ne wanda yake sakowa daga sama kuma ga abubuwan more rayuwa agun,
Sulatn Sana, Alhmdullah suka fada baki dayan su, yayin da Suha ta tashi tsaye tana magana ina bazai yayyu ba intafi nabar ku cikin hatsar ni babu inda zanje wallahi, mom yanzu kika gama fada mana duk matsalan da ta tukaro ka karkayi kokarin guje mata amma kuma yanzu zakije natafi wani waje, Mom kibarni kawai na tunkara matsala ta,
Mom Razia mekewa tayi takama hanun Suha kana tasoma magana cikin sanyi murya wanda kana jin muryan ta zaka gane yanzu Mom Razia an kure ta sosai, magana take hawaye yana zuba cikin idanuwan ta "tabbas yarinya ta duk matsalan da ta tukaroka karkayi kokarin guje mata ka tunkare ta amma wannan ba yanzu ba maiyasa bance Sana zata bar guna ba sabda ita ba kashe ta za'ayi ba ina son ki sani magana nan kisa tayi dan haka yazama dole kitafi dan Allah ina son rayuwar ku sosai kunake gani naji dadi dan Allah Suha kitafi ai zaki dawo yayin da komai ya lafah,
Suha da hawaye yagama wanke mata fuska tace "zantafi mom insha Allahu zantafi, " Sosai Mom taji dadi kana ta daura dacewa, "Suha zaki ji dadin tafiyan nan sosai,
Addu'a sosai Mom tamusu kuma tagodwa Sultan,
Mom Razia da Sana sai shirye-shiryen tafiyan Suha India suke gabaki daya sun hada mata kayan ta, saboda suna son tafiyan ta yakasance yau ne,
Suha ne tasamu Mom din ta da kuma Sana a parlou tafara musu magana " Mom Sana zan tafi yau kuma zan barku gaskiya zanyi kewar ku sasai da sosai,
Sana da hawaye yagama bin fuskan ta tace ni kuma gaskia bazanyi kewar kiba, Suha tana hawaye tana murmushi ai dama nasan bazakiyi kewata ba gabaki dayan su suka fashi da kuka mai cin rai, Mom Razia ma kuka tafashi dashi yayin da taje ta rumgume su tabayan ta, kuka suke sosai basu masan lokaci ya kure ba,
Sultan ne yashigo d'akin ya soma magana yakamata kutashi kubarta tashirya lokaci na kure mana haka kuwa sukayi gaba ki dayan su, suka rabu da ita yayin da hawaye nazuba daga cikin idanuwan su, shima kan sa Sultan din hawaye ne cikin idanuwan sa yayi Allah wadai da halin mahaifiyar sa,
Suha tafito sak India dan shigar India tayi gashin kanta bazashi tayi abayan ta yayin da ta dauko rigan sanyi babba tasaka ajikin ta,
Tana fitowa parlou taje da gudu ta rumgume Mom din ta hawaye sai zuba suke cikin idanuwan ta yayin da Sana kuka take kamar ranta zai fita daga gaggan jikin ta zuwa tayi ta rumgume su tabaya tana fadin bazanyi kewar kiba Suha, ita kuma Suha tana cewa zanyu kewar ku kullum zan kasance cikin kewar ki sosai suke kuka kamar wanda akace musu rabuwan su kenan yayin da Sultan hawaye sai fita suke daga cikin idanuwan sa,
Gyran murya yayu ya furta lokaci yana kure mana fah, haka kuwa suka rabu badan suna suba shi kuma ya raka Suha har filin jirgi,
INDIA
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
_________________________________________
Suha saka kafar ta tayi akasa yayin ta ta lumshe idanuwan ta tana shakar iskan kasan India wanda gabaki daya garin ya matukar burge ta wannan ne zuwan ta nafarko,
Idan Suhaima Abdulkadir tana kusa bata bar nan wajan ba tazo ta amsa bag din ta, abunda ake ta mai-maitawa kenan Aripot dinan
Juyawa Suha tayi dagudu tana bingefe-gefen mutani tana wuce su dan tagama mantawa da bag din ta sai yanzu dataji ana niman ta tukuna ta tuna,
Arjun sakowan sa kenan daga jirgi ya manna waya akun nan sa da alama waya yake, waya yake da Aaraw, Aaraw yace bro yakaji garin yama kuwa, Arjun ya lumshe idanuwan sa kana yadaura dacewa "wallahi tunda nasaka kafana akasan nan nakejin bugun zuciya, bugun zuciyar danake ji cikin mafarki na wallah kara tsanan take ye,
Aaraw yace gaskia Allahu ya nuna maka wannan yarinyar idan ba Aljanna bane kabar kasan kama bazata narka ka huta ba, Allah har nafara tsanan ta,
Arjun baice masa komai ba sai tsakin tayai, tsaki yatayi akai-kai, Aaraw ne ya tambaya sa lapiya kake tsaki ko dan nace natsana wannan yarinyar datake damun mun d'an uwa,
Arjun yace wallah wata yarinya ce wai Suhaima Abdulkadir tamanta bag din ta shine ake ta cika kun nan mutani wajan niman ta, inbanda rashin kamun kai taya mutun yazo tun daga wata kasa kuma ace yamanta bag dinsa daga gani zatayi rawan kai,
Aaraw murmushi yayi baice komai ba suka canza firah,
Suha gudu take gashin kanta yana bin bayan ta, dai-dai lokacin da Arjun yasha kwana yana cigaba da waya da Aaraw, bugun zuciyar sa sai karuwa take, sosai Suha bangaje Arjun tayi batarai da tasani ba yayin da wayan tafadi kasa shi , Arjun dago kansa yayi dan ganin wata yarinya ce tamasa ta'asa haka,
Suha hartayi gaba, idanuwan sa yazubawa gashin kanta, juyowa Suha tayi ta dan hada hannayen ta biyu tace kayi hkr, 🙏
Sumewa Arjun yayi atsaye yarinyar da yake gani mafarkin sa, yau itace agaban sa, kafun yayi wani yunkuri yani maita yarasa,
INDIA
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
_________________________________________
____Arjun tsayawa yayi cak yarasa abunda zaiyi, yunkura yayi zaibi bayan ta amma kafun ya isa gare ta har tabace wa ganin sa, gabaki daya gurin babu yadda Arjun bai duba ba dan kawai yagan ta amma babu ita babu alaman ta,
Arjun yashiga tashin hankali sosai, wani ciwon kai ne mai zafi yakama sa, lokaci guda, adaddafe ya isaka gurin da akaturo masa, direba yashiga cikin moton,
Kai tsaye aka kaisa gidan daddyn sa dake mumbai gidane madai-daici dan uncle din sa yaso ya sauka gidan sa dan susaba da Sima amma kuma Arjun yanuna kin abincewar sa akan hakan,
Kai tsaye d'akin da ako dayau shi idan yazo India yake sauka, yashiga kai tsaye toitel yashiya ruwa yasakar wakan sa sai da yayi awa guda ruwa yana sauka akan sa kafun yayi wanka ya daura alola yafito, jallabiya yasaka ajikin sa tauzauna kamar dama ajikin sa akayi, kyau sosai tamasa masha Allahu kai tsaye masallaci yanufa, bayan ya idar da sallahn sa ya koma gida kai tsaye jikin windon d'akin sa yaje yatsaya,
Zubawa furani idanuwa yayi ga iskar datake kadawa, duniyar tunani yafada, yanzu kam zuciyar sa tagama yarda masa cewa wannan yarinyar Aljana ce,
Yanzu magana nan da Aaraw yafada gaskia ne, tabbas koda ita Aljana ce tabbas zan zauna da ita,
___Arjun duniyar tunani yafada, wayar sa dake kan bed ne tafara ringtone ne ya katsai masa tunanin sa, komawa yayi kan bed din ya dauki wayar ganin sunan Aarawn ne yasashi daukawa,
Aaraw jin Arjun ya dauka sai da yasauke numfashi wanda sai da Arjun ya jisa, Aaraw yace "ina kashiga ne tundazo damuke waya ta ktsaye, kuma inata kiran ka baka dau waya taba fatan kana lapiya ko? mai yafaru naji wayarka ta katsaye?
Nufasawa Arjun yayi cikin cool voice Arjun ya furta " nagan ta Aarraw"
Kaganta wakagani kardai yarinyar mafarkin ka? Arjun yace "ita" kana yadaura dacewa "Aaraw wannan yarinyar ba mutum bane Aljana ce Aarae zuciya ta tana mun zafi shin dagaske idan ita Aljana ce bazan kara ganin taba,
Zuciyata tana mun d'aci kaima kasan yadda nake son ta da kaunar ta ina son ta sosai Aaraw kataima kamun dan Allah, Arjun yakarisa magana nan cikin dashashiyar murya wanda yake daf da fashewa da kuka,
Aaraw yafurta " kuka zakayi Arjun?
tabbas nisheda ne akan son ta amma meyasa tazabi kai bayan tasan kai dan Adam ne babu aure a tsakanin ku nidai shawar da zan baka itace kullum nake fada maka, itace addu'a kacigaba da addu'a insha Allahu komai zai wuce addu'a tana maganin komai brother na dan haka zantaya ka kaji,
Sosai Aaraw ya kwantar wa d'an uwan sa rai kuma yamasa alkawarin zai cigaba da tayasa da addu'a har sanda aljna nan zatafi ta daga rayuwar sa, dan a yanzu Arjun ya yarda da itadin Aljana ce, amma kuma yasaka aran sa cewa fa koda ita Aljna nace sai ya aure ta yayi rayuwa da ita, dan yadda yake jinta nan bayacin zai iya hakura da ita,
Bayan sun gama wayar ne yakira ummin sa, amma bai sanar da ita abunda yake faruwa ba, bayan gaisawa kawai ta masa fatan nasara cikin rayuwar sa,
Daddyn sa yakira bayan kammala waya da ummin sa sun jima suna fira, kana sukayi sallama,
Babban yayan sa Siddarth yakira awaya, Siddarth yana daukan wayar Arjun ya gaishe sa kana yafurta "nayi kewar ka yayana kullum cikin kewar ka nake, Siddarth daga bangaran sa yafurta" nima nayi kewar ka sosai ya India fatan kaji dadin zuwa gun ko? girgiza kai Arjun yayi kamar yana ganim sa, yafurta ehh sosai, lumshe idanuwan sa Siddarth yayi kana yadaura dacewa "Alhmdullahi naji dadin hakan" Kana yadaura dacewa Arjun katayani da addu'a akwai abunda nasa gaba fatan Allah yaban nasara akai, Arjun yace insha Allahu yayana Allahu yashiga cikin lamarin ka, bayan sun kammala wayar ce Arjun ya koma kan bed din ya kwanta, yacigaba da tunanin da yazamo masa dole a rayuwar sa, ehh dole mana tun yana ganin ta a mafarkin sa gashi yanzu tana masa gizo,
Suha tana karban bag dinta tazzi tashiga ta nufi gidan da mom dinta tace ta sauka agun, a parlou ta sauka gabaki daya kayan ta agun tabari ta kwanta agun, tayi barccin ta suhaima kenan
Karfe 10pm ta tashi da wani yunwa da ya murde mata cikin ta, gashi babu komai a gidan dama itace zatayi siyayar komai idan tazo tunda babu wanda yake zama cikin gidan,
A parlou tabar bag dinta wanka tayi tasaka doguwar riga yamata kyau sosai kai tsaye gurin cin abinci tayi dan bazata iya barcci bataci abinci ba,
Arjun mekewa yayi ya nufi gun cin amincin dake kusa dashi dan shan coffi da shima babu wani abunci agidan sa,
____Suha bayan tashiga gun cin abinci tazauna akan kujera, list din abinci waiteres takawo mata tafara dubawa zaban abincin da zata iyaci tayi, bayan ankawo mata, faraci tayi ahankali tanaci tana lumshe idanuwan ta da alama dai bakad'an abinci yamata dadi ba,
Bayan tagama cin abincin tabiya kudin tamike ta nufi gidan ta dan gabaki daya agajiye take sosai, fita tayi tafara tafiya akasa dan babu wani nisa tsakanin gidan ta da gun cin abin cin,
Tafiya tayi mai d'an nisaka, sosai wata moto ce tasha kwana fitilan moton ce ta haska fuskan ta gabaki daya hasks moton yakashe mata idanuwar ta gashi bata ganin wanda yamata haka,
Magana tafara cikin masifa da nuna fa duk wanda yamata haka to tabbas kar yabari idanuwan sa suyi tozali da nata dan tabbas wallah Allah daya ne bazata barshiba,
Shikuma Arjun da yake cikin moton gabaki daya ya fita cikin haiyacin sa idanuwan sa kawai yazuba mata kallon ta yake sosai babu ko iftawa,
Suha kaucewa tayi daga hasken moton kai tsaye wajan mazaunin direban ta nufa, kwan-kwasa kofar tayi, zuge gilashin moton yayi zuwa kasa, kafe ta da idanuwan sa yayi yana kallon ta,
Suha tana hada ido dashi ya mata kwarjini amma hakan bai hanata magama ba tana magana zuciyar ta yana bugawa sosai, nunashi tayi da yatsa tafara magana cikin tsawa da nuna abunda kamun ya batamun rai "kai makaho ne ko baka gani ne kodai kai kurma ne kodai babu hankali ajikin ka ne, da zaka haska mun cikin idanuwa ta kuma nasan kasani amma kuma kacigaba da haska mun fuskata tabbas magana nan dake fada gaskiya ne akan ku, ku y'an India kuna da giraman kai da wulakanci danuna kuna da kyau, okayy dan ga ganka mai kyau ko, to karkayi tunanin haka nake to ba haka nake ba, taja tsaki tawuce abun ta tabar sa agun zaune kamar gunki,
Saida tabace wa ganin sa kafin yadawo cikin hai yacin sa, dukan kansa yakeyi kamar wani mahaukaci yana tambayan kan sa shin maike faruwa dani ne naganta kuma ta kubuce mun, mai take nufi da karnayi tunin haka take ita ba haka take ba, tunani yakeyi sosai, fasa shan coffi din yayi ya koma gida da fatan sake ganin ta koma yaya ne.
Arjun shigan sauie yayi yama sa kyau sosai, fita yayi a parlou yayi kai tsaye waje yayi sai gashi sa masu aikin gidan sukeyi yana amsa musu babu yabo babu fallasa, motar sa ya nufa ya kunna ta yabar gidan baki daya,
SIMA
___Sima wata rigace ajikin ta duguwa jaa sosai ya mata kyau futowa tayi tace Ammi na yayi mun kyau kuwa?
Wanda ta kira da Ammi ta numfasa kana ta daura dacewa haba Auta saunawa zaki sauya kayya ajikin ki tabbas karki sauya wannan rigan dan tamiki matukar kyau sosai Autana,
Sima tace Ammin ina son nayiwa sweet Arjun dina ne kyau sosai, Ammi tace ai kinyi kyau sosai,
WAYE SIMA
⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐
Mahaifin Sima DR Sulaim yana da mata Azara DR sulaim yaya ne agun Hajia Sarah wato mahaifiyar Arjun haifuwan Dr. Sulaim uku amma dukan su basa zuwa da rai, Sima ce kawai Allah yabasu tazauna sun dauki son duniyar nan sun daurawa Sima suna son farin cikin ta, sunsar garta ta komai tace suna mata,
Suna kaunarta shiyasa duk abunda take so suna kokarinyi mata,
CIGABAN LABARIN
_________________________________________
Abu ne yafito daga d'aki yana magana daughter na gaskia ke yarinya ce kyakyawa ai dole ma Arjun ya rikece miki yana ganin ki, murmushi Sima tayi tace "Allah ko Abuna" sosaima kuwa daughter na,
Komai da Arjun zai bukata agama hada masa jiran sa kawai akeyi,
Kafe 9:30Am dai-dai Arjun ya isa gidan tun daga ged Sima tazo da gudun ta tana masa oyoyo nufoshi tayi zata rumgume sa, yayi sauki kaucewa yafurta "hayanzu baki sauya ba ko" kama hannun sa tayi tana murmushi tana cewa "har yanzu bazaka gane yadda nake son kaba ko" Bai ce mata komai ba,
Bayan sunshiga parlou ne suka za zauna akan kujera ya gaishe da uncle din sa tare da Ammi bayan sun gai-gai sa suka fara cin abince, sosai Arjun yaci dama akwai yunwa atattare dashi, sai da suka gama cin abinci aka dawo parlou suka cigaba da tattaunawa,
Suna cikin tattaunawa Sima ta mike gabaki dayan su suka mai da kallon su kanta, Ammi tace ya ana cikin tattaunawa kuma naga kin mike, Sima tace "wallahi Ammina so nake mufita shan iska da swwet Arjun dina,
Abu yace " hakan ma yana da kyau sosai"dan haka sai kundawo,
Magana nan gaskia Arjun bai jidadin wannan fitan ba shiyasa bai so shiyasa bai son zuwa India saboda abunda su uncle din sa sukeyiwa Sima komai tace tana so suna mata, babu yadda zaiyi haka ya tashi yabita suka tafi,
Suha sai karfe goma tayi wanka tashirya cikin rika da wando, tayi kyau sosai kamar ka dauke ta ka gudu da ita, gashin kanta kuma zubashi tayi abayan ta farin gele ta dauka ta rataya akan ta tafito sak baturiyan ta, Suha badai kyau ba bag dinta ta dauka tafita daga cikin gidan baki daya,
Tsayawa tayi cak a kofar gidan tana tunanin ta ina zata je tafara siyayyar, acikin zuciyar ta kuma tunani take anya bazataje cin abinci ba, yanke shawaran fara zuwa cin abinci tayi, ai kuwa tana zuwa taga gun cin abincin arufe, tambaya tayi ko mai yasa masu gurin cin abinci nan basu fito ba? wanda ta tambaya yace mata ae basa fitowa ranan sunday, bata jidadin hakan ba ga kuma yunwa da yake damun ta sosai haka ta juya ta nufi gurin da zata je,
Arjun zaune cikin motar sa gabaki daya gurin da sukazo da Sima gurin yarane sai wasan furere sukeyi na omo ga wata iska tana kadawa mai dadin shaka, lumshe idanuwan sa yayi yana kara tunano yarinyar nan da take a daddaban tunanin sa, wanda duk sanda zai kwanta tofah tabbas sai yagan ta a mafarkin sa,
Suha ne ta yanko gun da Arjun yake shi da Sima, Arjun yana cikin moton yayin da kuma Sima tana waje tana siyan sweet,
Idanuwar Arjun a lumshi zuciyar sa tana bugawa a dai-dai lokacin da kuma Suha takusa daf dashi, kamar anjewa Arjun ya bude idanuwar sa, kawai ya fara bude su a hankali-hankali ganin kamar gizon ta yakeyi, ai bai san sanda yakara kwangale suba, domin tabbatar da ita yagani, ai kuwa ita yagani tana tunkaran sa, gefen sa ta wuce gilashin motan sa ya saukar dan ganin kara ganin ta, ai kuwa itadin ce ya furta haka cikin zuciyar sa,
Wasu yara ne kananu suka kewaye Suha suna watsa mata fure, ita kuma tana saka hannun ta tana bebegewa tana murmushi, wayyo kuzo kuga yadda Arjun ya rude sosai, bai masan da ya fito daga cikin moton ba yazuba mata idanuwan sa mai riketa mata.
___Arjun tsayawa yayi yazubawa Suha idanuwan sa masu rikitar da mata, yayin da Suha sai murmushi take cikin yaran tana bibbige hannun ta, sosai ta kashe Arjun da wannan murmushin ta,
Sima ce tazo gurin Arjun kanta ta kwantar a kirjin Arjun tace "swwet Arjun mutafi nagama siyan sweet din Arjun baima san Sima tana masa magana ba, sai da Sima tadan buga kirjin sa tana tura baki tukuna Arjun ya dawo cikin haiyacin sa yafara magana cikin yake " kingama mutafi ko" ehh nagama cewar Sima,
Haka Arjun yana ji yana gani yabar gun bai samu yayiwa Suha magana ba datake tafaman wasa cikin kananun yaran nan,
KAUYE GUMA
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲
_______________________________________
__Khalil yace gani nan ai kuwa kallo yadawo kansa baki daya mutanin wajan suka fara sauke numfashi, Bintu wani wawan juyi tayi jin muryan sahibin ta Alhamdullahi ta furta yayin da Kaka kuma fuskan sa ta sauya da murmushi, gabaki daya gurin kowa furta Alhmdullah yakeyi,
Mai gabatarwa kuma yace "kazo amakararan lokaci amma yanzu ma bai baciba zamu iya fara gasar,
Kamar yadda Bushar yayiwa Khalil wancen lokacin haka mai gabatarwa ma yafara yayi bayani, Bushar hankalin sa kwance damuwar sa wannan gasar a fara kuma agama ta dan ya sauya wata gasar wanda yana da tabbacin zaici wannan gasar,
Bushar rigan sa yaci rai kamar dai yadda Khalil yayi wancan lokacin, mai gabatarwa ya fara magana yace zan fara da daya, zuwa uku sai a fara haka kuwa akayi, mai gabatarwa kuma ya fara "daya, biyu, uku, a farah haka kuwa Khalil ya fara gasar,
Bulalan da su Khalil suka dauka ne a hannun Khalil ya tunkara Bushar dashi, Bushar sai sake murmushi yakeyi, dan shi so yake agama wannan shadin ga maganin da yashafe jikin sa dashi sai sheki yakeyi
Bulalan Khalil ya daga ya zubawa Bushar runtsa idanuwan sa Bushar yayi tabbas yaji zafin bulalan nan amma kuma ya sake murmushi gai kana ganin murmushi nan kasan na karfin haline, sai da akayi guda biyar kafun Khalil ya tsaya da bulalan dan aduba fuskan Bushar aga ko yayi hawaye, amma kuma fuskan Bushar babu hawaye, mai gabatarwa yace acigaba fuskan Bushar babu alamun hawaye, budan bakin Bushar yace kar abar bulalan sai angama, mai gabatarwa kuma yace ai ba haka tsarin gasar yake ba, idan kayi kuka fah, Bushar yace koda nayi kuka kar kubari kucigaba dan nasan bazanyi kukan ba, haka kuwa aka cigaba da bulalan, guda 50 akayiwa Bushar sai ga hawaye ya cika idanuwan sa, Khalil cigaba yayi da bulalan Bushar kuma yana kuka kamar karamin yaro daga karshe ma fita yayi afilin da gudun sa dan bazai iya juran bulalan nan ba mai shegen zafi sosai ba, ai kuwa mutani suka fara dariya wasu harda rike ciki wasu kuma harda kwanciya, sama mutani sukayi da Khalil sunata juya sa suna fadin munsamu jarumi a kauye mu, Bintu tsabar farin ciki rasa yadda zatayi tayi, sujada tayi kamar dai wancan lokacin, Kaka kuma farin ciki har yakasa rufe bakin sa,
Bayan kowa ya nutsu mai gari ya fara magana cikin jin dadi dan gabaki daya garin sun ji dadin nasaran da Khalil yasamu dan dama Bushar ya gundiri kowa agarin, mai gari ya fara da "Alhmdullh Allah shine abun godiya tabbas komai tsanani yana tare da sauki yanzu kam Allah yakawo mana saukin annoban wannan mutumin Bushar dan haka Allah zamu gode da yakawo mana wannan mutumin cikin kauye nan, mai gari ya mai da kallon sa kan Baffah Bintu yace kamar yadda muka tsara duk wanda yaci wannan gasar shine zai aura Bintu to yanzu nan za'a aurawa Bintu da Garkuwa fatan gabaki dayan ku kun amince Baffah yace na'amince Allahu yabasu zaman lapiya gabaki daya gurin ya kauce da Amin Amin
Mai gari ya dubi Khalil yace kaje kashirya karfe 3:30pm za adaura maka aure da Bintun ka, Khalil tsaban murna rasa yadda zaisaka kansa yayi shi da Alili suka mike har da Kaka, yayin da Baffah ma ya mike zaije yashirya dan zuwa daurin auran yarinyar sa, farin ciki cikin zuciyar Baffah ba'a magana
Bayan Kaka yadawo gida ya saka Khalil da Alili su fada masa mai yasa basu dawo da wuriba,
BARI MUJI YADDA SU KHALIL SUKA FITA A DAKIN NAN
Khalil suna ta murnan samun bulalan nan suna tsaka da ganin bulalan kofar ta fara rufuwa ai sukayi kofar da gudun su dan karta rufe dasu amma kuma ina kofar ta rufe dasu, sun shiga cikin tashin hankali sosai da sosai gashi sunyi nasaran samun bulalan amma kuma babu da man fita daga cikin d'akin dur kusawa sukayi a kasa agun Alili kuka yake harda hawaye Khalil ma haka kuka suke kamar babu gobe sun fida rai da sake ganin nasu Alili kuka yake yana furta wayyo Allah na Kaka shikenan bazan kara ganin kaba wayyo rayuwa ta shikenan na banu na lalace sosai suke kuka a haka har barci ya dauke su, iskar asubahi ne ya tashe su daga barcin da sukayi mai cike da munanan mafarkai ganin yadda suke ne yasake basu da man kuka sosai, suna cikin kukan ne suka ji murya a saman kan su, muryan mutumin da yake musu magana ne kuma yanuna musu hanya har takai sun samu bulalan, wannan karon kam ya fito musu amma basu iya ganin fuskan sa, magana yafara musu a tsaye yace "tabbas lokaci ya kure muku kuma dama wannan hanyar ba'a fita idan anshigo ta dan haka zan nuna muku hanyar fita to amma kuma akwai bakin Aljani Kahu agun tabbas bazan iya dashi ba amma kuma zan nuna muku idan kunyi nasaran wuce hanyar to tabbas wannan gasar kai ne zakayi nasara akan ta, amma kuma wani sa'in idan ya kwanta barcci baya sanin akwai mutani a gurin da yake domin bai cika barcci sosai ba, idan kunci sa'a yayi barcci to shikenan zaku waje dan haka kutashi nanuna muku hanyar lokaci yana kuraiwa, haka kuwa sukayi gabaki dayan su suka tashi, hanyar da ya nuna musu suka bi, sunsha wahala sosai domin hanyar tsiririya ce Allah ne kawai ya taimake su suka yi nasaran fita a hanyar kuma sukaci sa'a Aljani Kahu barcci ya dauke sa, numfasawa Kaka yayi da ya gama jin labarin yace Allah ya taimake ku yanzu kutashi kushirya kar lokaci ya kure, haka kuwa suka mike suka dau haraman shiyawa domin daurin auran Khalil da Bintu,
BUSHAR
Bushar kai tsaye wajan Bokan sa yayi domin a wannan lokacin da niyar kashe sa yaje gun, yana isa kokon Bokon ya hau dukan Bokan nan sai da yamasa jina-jina kafun yarabu dashi kuma yabashi umarni yabar garin baki daya idan kuma ba haka ba zai kashe sa, haka kuwa Bokan nan yabar garin badan ran sa yaso ba sai dan yana tsoran Bushar idan yace zai aikata abu to tabbas zai aikata, Bushar ihu yasaka mai cin zuciya yana furta bazan barka ba nine nan zan kashe ka kazo gari na kuma karabani da abar sona kuma kayi nasara akai na kowa a garin nan yana jin tsoro na amma kuma yau kasa kowa ya rabu da tsoro na sai na kashe ka nine zan kashe ka ya kuma ihuu yana magana cikin fitar haiyaci,
BINTU
Yau take sallah agun Bintu daga gurin gasar kai tsaye gida tayi domin yau tana cikin farin ciki zata aura zabin ran ta, tana shiga cikin gida ta tarar da Inna Jummai a tsaye a kofar gida tare da muciya a hanun ta, Bintu tana ganin Inna Jummai da muciya ahanun ta taja da baya dan bata son yau ataba lapiyar jikin ta yau auran ta guda, Mero ne tazo tarike hannun Inna Jummai tafara magana cikin sanyi murya "haba Inna ke baki jindadi idan baki dauki hannu ki kinduki Bintu ba haba haba Inna wallahi abunda kikeyi baki kyau tawa Inna Jummai tace Mero ki matsamun yau na kashe yarinyar nan bazata taba aure ina da rai ba, yarana biyu dukan su babu wanda yayi aure sai ke yar tsutuwa wallahi Allah bazakiyi auran nam ba matsamun Mero!! Mero tace "wallahi Inna bazaki duke taba idan kuma kin matsa sai kin duketa to tabbas saidai kifara dukana dan Allah bazan bari kiduke taba, zainab tace Inna meye abun duka anan dan zatayi aure bayan dan tsutuwa ne zai aura yar tsutuwa dan haka Inna ta karki wani damu kanki, ajiye muciyar Inna Jummai tayi dai-dai lokacin da Baffah yashigo gidan, harara Inna Jummai ta gallamasa tare da tsaki ta wuce d'aki abun ta Mero ne tayi masa barka da dawowa yawwa kawai yace kana yafito da kudi ya mikawa Mero yace "ayiwa Bintu lalle yau auranta, sosai Mero tajidadin hakan , lalle akafarayiwa Bintu da kitso tafito sak Amaryan ta Bintu kyakyawace sosai akamata kwalliya irin ta Amaryan kauye sosai Bintu tayi kyau abunta,
Alili bayan yashirya yafito yasamu Kaka da kuma Khalil yace nizan fita Khalil yace ina zuwa haka Alili yace jarumin garin mune fa zaiyi aure dole naje nayi sanarwa kowa yasani dan namu ai ba irin nasuba ne, murmushi kawai Khalil yayi Kaka kuma yace kadawo da wuri fa insha Allahu Kaka cewar Alili, haka Alili yace yakarba abun magana sifika yana tafiya a cikin gari yana sanar da auran Khalil da Bintu,
Alili yace "aure kofar shiga duniyar so da kaunar juna damba kuma foundation naginin shakuwa mai daurewa Aure masamar dukan wata alkhari wannan ne yasa Garkuwar mu jarumin mu da Amaryan sa Gimbiya Fatima Bintu daurin auran su da za'a daura a yau dinan sakamakon yin nasara akan Bushar dan haka kowa da kowa ana bukatar sa wajan daurin auran nan, fatan azo lapiya, gabaki daya mutani sunata jin-jinawa Khalil yayin da Alili yadaura dacewa kuma akwai shagalin dazamuyi da dare bayan ankawo amarya gidan ta Allahu yabawa kowa ikon zuwa,
Gabaki daya magana nan Alili akunan bushar ne sosai Alili yasake fusata Bushar,
Khalil yasha jamfan sa da hulan sa faran yadi masha Allahu yafito sak angon kauye hmmm yau auran Khalil da Bintu abun mamaki nace Allahu yabasu zaman lapiya, Kaka Khalil Alili suka tafi wajan daurin aure kuzo koga farin ciki da annashuwa atattare da Khalil kyc,
Dubin al-uman mutani ne suka sheda auran Bintu da Khalil bayan kammala daurin auran ne kowa yazo yana taya Khalil murna, da fatan zaman lapiya auran Khalil ya dauru yayin da kuma Bushar yake can da bakin cikin a cikin zuciyaar sa da kuma sake-saken abunda zaiyiwa Khalil
Bintu sosai take kuka agaban Baffahn ta nasiha yashigayi mata, "Bintu yau kinzama mace wanda ko wata mace wannan ranan take jira Bintu kinta so cikin wahala a cikin gida nan amma yanzu zakitafi gidan y'anci amma hakan baya nufin iyi abunda ranki yakeso saboda kinga gidan kiba Bintu tabbas nasan duk wanda ya aure ki yayi sa'a a cikin rayuwar sa wajan samun mata tagari dan haka kibi mijin ki sauda kafa duk abunda yace miki kimasa dan Aljanna nan ki tana gare sane kisani yardan Allah yana tare dake tunda har kika samu yarda na Bintu duk abunda kikayi azaman auran ki dayan biyu sakamako zai bayar inma dai jinjjinawa tarbiyar ki da kuma wanda suka tarbiyar dake ko kuma akasim haka Baffah ya numfasa kana ya daura dacewa kiyi kokarin karai martaba na kamar yadda nakarai martabar naki Bintu duk dana sancewa banyi wani abunda zo agani a cikin rayuwar kiba
hakika babu wanda zai miki alkawarin farin ciki mai daurewa amma kuma tabbas hakur, da kuma juriya, da kuma addu'a zasu baki Bintu ki martaba auren ki kamar yadda zaki so a martaba auran y'ay'an ki Bintu, Aure ibada ne dukan ibadah kuma tana zuwa da kalubale daga shed'an Bintu karki bari shed'an yayi galaba akan ki Aure gida ne mai zaman kansa wanda daga shi kuma ake zarcewa gidan Aljanna mata tagari dole sai tayi hakuri kafin tazamo tagari Bintu, kisaka gskiya cikin al'amuran ki Bintu kije Allahu yashiga cikin lamuran auran ki, addu'a zatabaki sa'ar yiwa shed'an bara'a
Sosai Bintu take kuka babu abunda ta iya furtawa haka aka dauketa akaita gidan ta saidai mu musu fatan zaman lapiya tare da samun zuriya masu Albarka,
Dandali auran Khalil da Bintu wakokin soyaya aketa sakawa mc ne yabukaci amarya da Ango afilin dandaki dan sununa farin cikin wannan ranar, ai kuwa sunfi to wakar soyaya akasaka musu masu sanyaya zuciya wakar Sadiq Sale Khalil kama hanun Bintu yayi suka fara juyawa, mutani kauyan suka fara magana kasa-kasa wakar Sadiq Sale wanda yakecewa
Natafi kuma nai nadawowa kuma ban komaba indai zakimun soyayyar gaskiya tare dake muyi zaunawa zama mai daurewa masu fada su fada mudai muyi dauriya narasaki zanyi shekewa karyi musawa nafi bukatar mu haka kai muzama tsitsya kanki bana iya jurewa wasu sukushe ki zan ma tubin daka dan daka makiya nidai kece, nanace maitsace ke natattance kyayawace bazaku gane dalilina ba,
Macen matace "sona gare ni zalama ne alkhari ne inna gujeka za'akirani tsinaniya shima masoyin ka abun sone makiyin ka abun kine idan naganka da wata y'a zamuyi yar watattiya koda sonka jaraftace na toshe kunne zan gada kai har nayi dariya zana tsaya inkakame inbibbine kai nagani acikin taro zanafada dole nafada kaine zabina
Kosufada kokarsu fada dai nidai sai kai sake ko sunki kaine kaine koda sunki gabaki daya taro bikin Khalil da Bintu yani shadantar da mutani kuma anyi farin ciki sosai daga karahe akai amarya dakin ta,
Bayan ankai amarya d'akin ta agefen gaton ta Khalil yazauna ya furta "Alhmddullahi yau dai burina yacika wajan zauran mace tagari farin cikin rai na Khalil yace Bintu mamaki yakama Bintu dan tasan a iya zamantakewar su baitaba kiran ta da Bintu ba amma kuma yau Khalil da Bintu ya kirata, gani tazuba mishi idanuwan tane yashi daga mata gira yace muje muyi alola muyi sallah godewa Allah haka kuma sukayi bayan sun kammala sallah ne Khalil yacirai rigan sa a lokacin Bintu tana karshen gado, kusa da ita Khalil yayi babu komai ajikin sa sai gajeran wando Bintu makuraiwa tayi ajikin gadon shi kuma Khalil sosai ya matseta ajikin sa ta yadda tanajin dumin jikin sa sosai magana yafara mata cikin kunnuwan sa, Bintu na wannan kyakyawan suna ne da yasamu daman radawa kyakyawar yarinya, darajan ki takai yanda babu wanda wani abun da za'a ya cewa kinyi sa'ar samu sa sai dai ace yayi sa'ar samun ki dan haka nine nayi sa'ar samun ki cikin rayuwa ta tun daga hijabi riga gyale wando da dankwali babu abunda zaki saka ace yayi miki kyau face kika masu kyau da kara hasken su Bintu ke ko acikin mata ke tamusaman ce ko a cikin kyawawa ta daban ne hakama ko acikin abubuwa masu daraja ke mafi darajan cikin su ne nikaina ba daga nan ba yanzu dana sameki Bintu, komai nawa yadawo kan saiti ina matukar son ki Bintu, ina burin kasancewa dake a cikin rayuwa ta Bintu ina son ki Bintu irin sosai dinan fatana Allahu yabamu zaman lapiya mai daurewa
Sosai Bintu tashiga cikin tsananin murna da kuma fargaban kar wata rana tarasa shi tabbas arana nan zata iya mutuwa domin tana matukar son sa
Wata sanyayiyar shakuwace tasake shiga azaman auran Bintu da kuma Khalil sosai suke bawa junan su kulawa musamman ma Khalil baya kaunar Bintu tayiwani abu idan ba yazama dole ba akoda yaushe suna manne da junan su Khalil shiyake taya Bintu komai, babu idan da Khalil yake zuwa sai da yayi kusan sati biyu kafun Alili da Kaka suka zauna sukayi magana akan yakamata fah Khalil yaringa wani abunda kodan saboda rikon gida, haka Kaka da Alili suka hadawa Khalil kudi domin yafara wani kasuwanci dan yafi zaman dayakeyi agida, haka kuwa Alili yasamu Khalil har gida yadan kamasa kudin sosai Khalil yajidadin kudin kuma yayi musu godiya,
Khalil ya nima shawara agun Alili akan abunda yakamata yafara siyarwa, Alili yace idan har babu wata damuwa kafara saida kayan miya kamar su ataruhu da albasa da kuma tumatur, Khalil yace babu wata damuwa hakan ma yayi, Alili yamike yace to ni zan tafi sai idan Allah yakai mu gobe zan shigo da wuri domin zuwa sarin kayyan miya dan haka kashirya da wuri, insha Allahu zan shirya cewar Khalil haka sukayi sallama Alili yatafi Khalili yashige cikin gida,
Bintu tana zaune abakin murhu tana aza wuta dan tana sauri taga tagama abinci dan kar Alili yatafi baici abinci ba Khalil yashigo gidan, Bintu batama san Khalil yashigo gidan ba,
A hankali sadaf-sadaf Khalil yake zuwa gare ta batare da Bintu ta lura dashi ba ai kuwa adai-dai lokacin Bintu ta mike tsaye tana cewa "yawwa yanzu abinci na zaiyi yaa Alili yaci afin yatafi" batakai da karisa magana nan ba kawai taji anyi sama da ita kamar yar babyn roba, saura kadan Bintu tasaka ihu taji muryan Khalil yanacewa matsoraciya nine nan sahibin ki,
Sauke ajiyar zuciya Bintu tayi a dai-dai lokacin da kuma Khalil yana sauke ta kasa, ai kuwa yana sauke ta kasa ta juya ta fuskan cesa ta kama wuyan sa da dukan hannayen ta tatusa kanta a faffadan kirjin sa tana tace wallahi Allah katsoratar dani dan haka karar rasheni tafada tana mai dako kanta daga kirjin sa, tana tura masa baki , Khalil kama bakin yayi yajaa yace ai kuwa sai na ciza wannan bakin naki,
Kukan shagwaba Bintu tafara ai kuwa da sauri Khalil yakama kunnuwan sa yanacewa agafarce ni ayi hkr dan Allah bazan karaba nine ko to mijin ki ya tufa, ya kuma hada hunnuwan sa alamun yana niman afuwa a gare ta, sosai Bintu tashagala da kallon sa tana jin wani soyayyar sa da kaunar sa yana sake shigan ta, bude baki Bintu tayi tace to shikenan na hakura, sosai suka shiga kallon soyayya sun manta ma da abinci akan wuta, zaida yafara konewa tukuna suka ankara da abinci ai da sauri Bintu ta katsai kallon ta koma kan abincin,
Sai da tasauke abincin akafi, tajuyo ta kalli Khalil tace ina yaa Alili? d'aga mata gira Khalil yayi yace "sai yanzu ne zaki tuno da yayan naki ko to yatafi, tura baki Bintu tayi tace " mai yasa zaka barshi yatafi bayan kasan na kusa gama abinci, Khalil yace sauri yakeyi dama yazo mutattuna ne akan abunda yakamata nafara siyarwa, gabaki daya Khalil ya kwashe duk abunda sukayi da Alili yafadawa Bintu sosai Bintu taji dadin hakan kuma takuma jin jina-jinawa Alili da kuma Kaka akan kokarin dasukeyiwa Khalil, tabbas samun mutani kamar su Alili a wannan zamanin akwai wahala,
Abincin Bintu ta zuba musu sukaci tare bayan san kammalaci ne Khalil yashiga wanka da yau suna son zuwa ziyara gidan Kaka da kuma Baffah,
Gabaki dayan su sangama shiri suka fito sunyi kyau sosai masha Allahu Khalil da Bintu badai kyau ba, dama Bintu farace sol sosai yayin da kuma Khalil baki ne ba sosai ba,
Gidan Kaka suka fara zuwa suka gaishe sa sosai sukayi fira Khalil yayi godiyawa Kaka harda dan hawayen sa, Kaka yace "haba babu komai dan nayiwa jikana abu basai yamun godiya ba, sosai sukayi fira daga bisani kuma sukayi sallama da su Kaka da Alili, suka nufi gidab Baffah,
Sallama sukayi suka shiga cikin gidan Baffah suka tarar a tsakar gidan shikadai yana wankin kayyan Inna Jummai, da sauri Khalil yaje gare sa ya fara masa magana " haba Baffah wanki da kanka kuma ai da ka aika anki rawoni ni sai nayi wanki amma ace kana damu kai kuma kana wanki!
Daga cikin d'akin Inna Jummai tayi magana tace idan bai yi awanki ba uban wakake so ya masa, Baffah yace Garkuwa kar ka tamka mata karabu da ita tun ran da Bintu ta tafi nina dawo nake komai a gida nan, garama wani sa in Mero tana fakan idanuwar Jummai tana tayani amma kar ku damu kan ku komai mai wucewa ne,
Bintu tun sanda suka shigo cikin gidan ta tarar da Baffah ta yana wanki tazube agun ta fashe da kuka mai cin rai, sosai take kuka Baffah ne ya shiga rarrashin ta da k'ar yasamu tayi shuru, Khalil ne ya karisa wanki bayan yagama ne kuma suka koma d'aki suka fara fira sun tattauna sosai kana sukayi sallamawa Kaka suka koma gidan su,
Tun da suka dawo gida Bintu batawani farin ciki Khalil ya lura da hakan amma kuma baice mata komai ba sai da yadawo daga masallaci, kafin yasaka Bintu a gaba dan ko abinci takici, "Mimi nasan meke damun ki tun damuka dawo daga gurin Baffah kika shiga cikin damuwa kuma nasan sanadiyan ganin Baffah cikin wannan yanayin da muka ganshi ne, tabbas Baffah yana cikin da muwa amma kuma Baffah addu'an mu yake bukata dan ya hadu da mata maral imani amma kuma kisani addu'a itace take sauya komai dan haka kicirai damuwa aran ki kuma insha Allahu zan kawo karshe abun da yardan mai duka,
Bintu kwanciya tayi ajikin Khalil ta kuma fashewa da kuka tana sake tusa kanta a kirjin sa tana magana, "Baffah na shi ne komai na shine gata na ina matukar kaunar Baffah na tabbas Inna Jummai bata da imani amma kuma kamar yadda kace mijina addu'a itace gaba da komai to zanci gaba Allahu ya wace mana gabaa, Allah nagode maka da yaban kai amatsayin mijina tabbas kai alkhairi ne a cikin rayuwata kuma zanci gaba da maka biyayya Allahu yaba mu zaman lpa,
Khalil sosai yaji dadin maganganun Bintun sa kuma yakara godewa Allah da yabashi mata kamar Bintu, kara kwanta da ita yayi ajikin sa, sunfi awa guda a haka suna jin dumin jikin su, kana daga karshe Khalil ya dauki Bintu yayi d'aki da ita, kan gado ya nufa da ita kwantar da ita yayi shima ya haukan gadon sukayi barci rumgume da junan su,
Karfe uku na dare dai-dai Khalil ya farka daga barccin sa fita yayi a d'akin mand'aki ya shiga daura alola bayan ya kammala ya koma cikin d'akin Bintu ya tarar tayi ruf da ciki, yasha ganin Bintu tayi irin wannan barccin sai dai ya gyra mata amma kuma har yanzu tanayi dan haka yayan ke shawarar tashin ta daga barccin dan yafada mata ilar ruf da ciki,
Mimi kitashi a barcci nan akwai magana nan da zan fada miki, idanuwar Bintu a lumshe tace "haba Sahibi na kabari mana sai gari yawaye" a'a Mimi ki tashi kawai babu yadda ta iya ta tashi daga kwanciyar tazauna,
Khalil jawota yayi kirjin sa yasaka tsakakanin kafafafuwan sa ya kwanta da ita a kan kirjin sa yafara mata magana cikin sanyin muryan sa wanda zatayi saurin fahimtar sa,
Mimi na zan fadamiki illar kwanciyar bacci akan ciki (Rub da ciki)!!!
Mutane da dama suna wannan kwanciya ta rub da ciki wanda mafi yawa suka mai dashi a matsayin kwanciyar da tafi musu dadi ba tare da sun san cewa kwanciyar ce wacce Allah baya so kuma Annabi (saw) yayi hani akan hakan ba wasu daga ciki kuma sun san cewa ba kyau, amma suna yin irin wannan kwanciyar ba tare da sun damu ba, "
Nufashawa Khalil yayi ya kara kwantar da kan Bintu a kirjin sa, kana yadaura dacewa, "haka nan akwai wadanda daga anyi magana akan wannan kwanciyar ta rub da ciki sai suce ai camfi ne (ma'ana maganganun mutane) ne kawai,
To a hakikannin gaskiya babu maganar chamfi an samo hadisi ingantacce daga hanin manzon Allah (swt) akan ita wannan kwanciya ta rub da ciki kamar haka
Idanuwar Bintu Khalil ya duba ko tana sauraran sa hada idanuwa sukayi tayi lamo a jikin sa Khalil yace "Mimi na kina jina kuwa? Bintu tace ina jinka miji nagari,
Khalil yace ai nazata kin koma bacci ne, numfasawa Bintu tayi tace ai kaima kasan bazan iya bacci ba yayin da mijina yana fada mun magana masu daraja wanda zasu amfani ni dan haka ina jinka miji nagari,
Numfashawa Khalil yayi kana ya daura dacewa, " Annabi (saw) yace ita dai kwanciyar (rub da ciki) kwanciya ce ta yan-wuta kuma kwanciya ce da Allah yake fushi da ita (Abu dawud ne ya ruwaito shi da isnadi ingantacce)
Haka nan hadisi ya inganta cikin sunani Abu Dawud ta Turmizhi daga ya'ish Bn duhful gifari (RA) daga baban sa cewa wata rana Annabi (saw) yazo wucewa ya same ni a masallaci ina kwance rub da ciki sai ya zungureni da kafar sa yace kadai na irin wannan kwanciyar saboda kwanciya ce da Allah yake fushi da ita,
Khalil yasake rumgumar Bintu yaci gaba da magana,
Haka nan masana bincike sun gano cewa rub da ciki wajen bacci yana da matukar illa ga kashin gadon baya,
Mimi na nasha ganin kina wannan baccin ina gyra ki amma kuma har yanzu kinayi shiyasa nace bari na fada miki babu kyau dan Allah kidai na nasan da wuya kadaina abun da kajima kanayi amma dan Allah kikokar ta kinji Mimi na
Numfasawa Bintu tayi tasake kwanciya a jikin sa hannu ta ta tusa a cikin kashin kirjin sa tace "insha Allahu zan gyra Allah nagode naka da kaban miji mai tattaku mai jan matar sa a jikin sa naji dadi kuma ina alfahari dakai masoyina,
Tace nagode nagode sosai ina son ka, Khalil ya kalle ta yace nice da godiya ai yanzu mutashi muyi sallah kafin asubahi tayi, kinsan yau zamu shiga kasuwa da Alili kuma yace mun inshirya da wuri, Bintu tace haka ne kam suka mike sukaje sukayi alola har da Khalil din
Da safiya Bintu tagama hada musu abun karyawa bayan sun yi wanka Khalil ya kira Bintu yace tazo suyi addu'ar safiya kamun su karya haka kuwa sukayi
Ayatu kursiyyu sukayi sau uku, sai sukayi Qul huwallahu Ahad shima sau uku, sai Qul a'udhu rabbil falaq sau uku sai Qul a'udhu bi rabbin naas sau uku
Addu'o'i Khalil ya yacigaba dayi Bintu tana cewa Amin Khalil yace Allah ya ubangiji mu mai rahma kashiga cikin lamuran mu kamana jagora akan duk abunda mukasa gaba na alkhairi ya ubangiji Allah karemu da kariyar ka kadaura mu akan makiyar ka, Bintu tana tacewa Amin
Bayan sun kammala addu'an suka karya suna gama karyawa Alili yazo, Khalil yayiwa Bintu sai mun dawo, dawo lapi Bintu ta musu baki dayan su suka tafi,
BUSHAR
Bushar yaran sa gabaki dayan su sunkewaye sa, Bushar yace yau zamu kashe wannan mutumin da yarabani da Bintu na naji na labarin zasu tafi kasuwa shi da wannan yaron Alili to yau gabaki dayan su zamu gama dasu amma sai da yamma zamuje hanya mujirasu mugama dasu yaran Bushar sunyi na'am da batun sa kuma sun tsayar da cewa yau zasu kashe mutum nan da kuma Alili,
Khalil da Alili sunshiga kasuwa asa'a atake suka sara kayyan miya kuma suka siyar agun sai daf da bangari ba suka sake saran kayyan miyyan wanda Khalil zai siyar akofar gidan sa, khalil ya siyawa Bintu abubuwa da yawa natsaraba suka nufo gida,
Bushar da yaran sa kuma sunkewaye hanya dan yau basuga abunda zai hana su kashe Khalil,
Bintu tayi wanka ta tashirya tana jiran mijin ta dan gaskiya yau tayi kewar mijin ta tamasa abinci sa mai dadi wanda yafi so sosai Bintu tagama abunta dan tarban mijinta,
Bangaran Khalil ma yayi kewar matar sa sosai suna cikin koma kauyen guma motan amalalke ta samu matsala gabaki dayan su suka fito a cikin motar sai da sukayi kusan tara na dare akafu aka gyra suka dau hanya,
___Khalil tafiya suka cigaba dayi cikin moton amalanke, mutani da yawwa suka gani akwance a kasa duk jini yabata musu jikin su wasu kam ma babu rai a jikin su, tsoro da firgici duk yagama gauraye zuciyoyin su Khalil addu'a kawai suke fatan su Allah yakai su gida lapiya,
Bintu duk tashiga cikin rudani da damuwa narashin jin mijin ta, takasa zama kuma takasa tsaye duk a cikin damuwa take fatan ta Allah yasa gabaki dayan su suna lpa,
Har kusan goma na dare Khalil bai shigo gida ba anan ne Bintu tagama rudewa, hijabin ta tadauku zata tafi gidan Kaka taji ko lapiya, saka hijabin tayi ta nufi kofar gida dan zuwa gun Kaka, har tasaka kafar ta a kofar gidan taji karo da Khalil sai sauke numfashi yakeyi,
Kamashi Bintu tayi tana kuma tambayar sa lapiya mai yafaru dakai kake haki wani abu yafaru daku ne, ina yaa Alili fatan kuna lpa gabaki daya tajero masa tambayan lokaci guda kuma duka tambayan ta babu wanda tasamu sa'ar amsa mata dan Khalil sai sauke numfashi yake,
Kama shi tayi ta nufi d'aki dashi zaunar dashi tayi abakin gado tafita a d'akin ruwan zafi sosai ta hada masa takai masa bayan gida, komawa tayi d'akin tace na kai maka ruwan wanka idan kayi wanka jikin ka zai warar-ware, Khalil sam baya cikin haiyacin sa da alama dai yau ciwon sa ya motsa ne, ganin hakan ne yasaka Bintu nufar wajan sa takama shi suka nufi toilet kayan jikin sa tayi kokari taci rai masa tafara masa wankan da ruwan zafi sosai ta masa wankan kana takama shi suka koma d'aki tazau nar dashi abakin gadon mai, tasha famasa bayan tagama ne kuma tasaka masa kayya mai sauki
Ta hada masa koko mai zafi tabashi yasha bayan yasha ta kwantar dashi akan gadon ai kuwa bacci ne tayi awun gaba dashi, itama kwantar da kanta tayi a kirjin sa bacci ya dauke ta,
Da a suba Khalil yafara mutsu-mutsun dube idanuwan sa da suka masa jaa sosai firgicin yanzu babu sai dai kawai kasala abunda yafaru dasu ne yafara dawo kan sa,
Suna cikin tafiya sukaci karo da mutani a kwance a kasa gabaki daya jikin su duk jini yabata musu, kafin subar wajan sai sukaji muryan mutani suna fadin kuka masu gasu nan,
Kewaye su Khalil sukayi suka saka su a tsakiya Bushar yafito, akasa masa kujera yazauna ga bindigar sa agefen sa ya daura kafa daya kan daya ya dubi su Khalil ya soma magana "kai ne karaba ni da zabin rai na ka aure ta to yau zan rabaka da duniyar baki daya kuma na aura matar ka, kai kuma Alili dan gidan Kaka kai tun farko kafara kawo sa wannan kauyen to yau gaba ki dayan ku zan kashe ku,
Tsoro da firgici gabaki daya ya lulube su Khalil zufa sa tsa-tsafo musu yakeyi gabaki daya sun fita haiyacin su,
Mikewa Bushar yayi yana kewaye su yayin da bindigar tana kan kujeran, cigana da zagaye su Bushar yakeyi, Khalil idanuwan sane suka sauka akan bindigar nan da bara yakeyi yana zuwa gun bindigar a wayo dan yadauko ta, ai kuwa da taima kon Allah sai ga Khalil ya dauka wannan bindigar ya nuna Bushar dashi yana cewa "kabar mu mutafi idan ba haka ba sai na kashe ka "
haka kawai Khalil yake fada sai da ya harba bindigar kafin Bushar ya juya aguje kowa ya kama gaban sa shi kuma Khalil cigaba da harba bindigar yakeyi kamar babu gobe Alili da sauran mutanin duk sun gudu Khalil ne kawai yarage agun bai gudu ba,
yagama fita hai yacin sa yafara tafiya tai makon Allah ne kawai yakawo sa gida,
Bayan yagama tuno duk wata abunda ya faru dasu sai karan bindigan nan tadawo kan sa kamar yanzu ake harba ta rike kansa yayi sosai hawaye suna fita daga cikin idanuwan sa, da sauri Bintu datake gefan sa tamike tana mana magana "kana lpa kuwa? amma ina Khalil baisan tanayi ba, kuka yake sosai kamar karamin yaro kuma yarike kan sa kam............
Kuka yake kamar karamin yaro, Bintu kuma sai tambayan sa take amma kuma Khalil bai bama san Bintu tana tambayar saba gani Khalil yaciga da kukan ne yasa Bintu itama tacigaba da kukan, kuka suke sosai kamar babu gobe, sosai suke kuka Bintu ganin kuka bazai musu maganin komai ba yasa tamike ta dauka mayafin ta tasaka tafita a ɗakin taja,komar ɗakin gabaki daya gidan tabari, gidan Kaka tanufa dan sanar masa cewa fah tun jiya Khalil yake kuka,
sallama ta ringayi a kofar gidan amma kuma shuru babu amsa, dan haka takusa kanta cikin gidan amma kuma babu kowa a tsakar gidan ɗakunan gidan tafara dubawa amma kuma gabaki daya babu kowa a ciki ruɗani tafara shi amma kuma sai tace bari tazauna tajira zuwa anjima wata kila sun je daji dan nimowa mutani magani duk da akwai tunanin sahibin ta a ranta,
kusan la'asar amma kuma Kaka da Alili basu dawo gida ba dan haka tamike dan komawa gida dan tabar Khalil shikadai kuma bawani ishashen lapiya gare sa wani bangare kuma na zuciyar ta yana fada mata cewa su kaka anya suna lapiya,
Lokaci guda wani hadiri ne ya hadu gabaki daya garin yayi bakikirin sosai ko tafin hannun ka baka iya gani sosai garin yayi bakikirin haka Bintu tarin gabin bango dan komawa gida dan batasan awani hali Khalil yake ba taimakon Allah ne kawai yakawo Bintu gida tana shiga gida ɗaki tanufa dan ganin awani hali Khalil yake, amma kuma babu Khalil ko ina Bintu taduba amma babu Khalil hankalin ta yatashi sosai gabaki daya ta fita cikin haiyacin ta tazama kamar mahaukaciya duk yadda yakamata da duba taduba amma kuma babu shi ai kuka tafashe dashi mai cin rai koka take sosai tana fadin nashiga ukuna ina kake Sadauki ina katafi wayyo Allah bazan iya rayuwa babu kai ba kadawo gareni dan Allah kadawo idan wasa kake mun dan Allah kabari sai sumbatu take tana kuka ga kuma ruwan sama da yasako kamar da bakin kwarya,
haka ruwan nan yacigaba da dukan ta agun tana zaune a tsakar gida ruwa yana dukan ta tana kuka har ruwa ya dauke tana tsakar gida ganin ruwar ya dauke ne yasa tasa fita agidan baki daya da kuma jikan kayyan ajikin ta,
gidan Kaka tasake komawa amma kuma har yanzu babu su a cikin gidan, sake shiga cikin wata rudani tayi da kuma tsoro yasake shigan jikin ta rasa yadda zata nufa taji sanyi aran ta tayi ko ina zafi wannan shi ake kira da rana zafi inwa kuna,
saike komawa gida tayi tazauna a tsakar gida ta fashe da kuka mai karya zuciya tana kuka tana sumbatu,
SAUDI
_________________________________________
Har yanzu jikin momy kara gaba yakeyi babu wani sauki atattare da ita momy yanzu bata gane kowa batasanin waye akan ta
Haka Abba ya dauke ta yadawo da ita gida Negeria su Khairat ne masu kula da momyn su domin yanzu aiki ,yayiwa Abba,tabbas idan kasauke idanuwan ka akan momy sai ka tausaya mata tuni Mahaifinta mai martaba sarkin Bauchi yasaka adauko masa ƴar sa amma kuma Abba ya nuna ƙin amincewar sa akan hakan,
umma ce akan komai ita take kullawa da ita gabi daya gidan ya koma babu wata farin ciki haka suke rayuwa adaddafe,
AMERACA🇬🇧
💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝
Sana da mom sundawo zaman gidan yana musu wahala kullum sai Abbi yazo ya zzzagamu su fada yana tambayar su ina Suha amma kuma magana daya Mom take fada masa nima bansan yadda take ba,
haka kullum rayuwar su take Sana ce tashiya cikin doguwar riga after the rest tayi kyau sosai samun mom tayi akasa tazo ta rumgume ta ta sumbace ta akumatu tace to nikam mom natafi school, mom tace adawo lapiya kuma ki kulla sosai Allau yakai ki lapiya sannan kuma yadawo dake lapiya, Amin Amin mom dina sai na dawo,
motan ta tashiga aka bude mata get tafita a gidan tana cikin tafi tana sauraran waka mai dadi tana tunanin kalbin ta kwai moton ta tafara jakin da alama dai wani abu acikin motar yasamu matsala,
parking tayi agefen hanya ta sauka a moton gashi ita ba gyran moto tayi ba tsyawa tayi cak tana tunanin abunyi wayar ta tafara ringing tana dubawa kuma Suha tagani ai da sauri ta dauka wayar takara a kunnan ta suka fara magana,
Suha tace ai daman kince bazaki kewata ba kuma ashe da gaske kike nikuma nayi kewar ki shiyasa nace bari nakira wanda batayi kewata muyi fadan da muka saba dan ajima bamuyi ba tun kafin natafi,
murmushi Sana tayi tace "Suha rigirma fatan kina lapiya bata jira amsata ba ta daura dacewa ai dana zata bazanyi kewar kiba ashe ba haka abun yake ba kewarki yagama shiga cikin jinin jikina kullum sai nayi kukar rashin ki akusa dani,
murmurshi Suha tayi Allah sarki rabin jiki fatan yanzu kin daina tunanin wannan mutumin ko?
murmursshi Sana tayi tace ai tunanin sa sai kara shiga cikin rai na yake kullum sai nayi kuma ince Allah sarki ƴar uwata da yanzu tana nan da itace zata rarrashe ni gabaki dayan suka fashe da dariya,
Suha tace sai yanzu nagano dalilin yin kewata ashe saboda haka ne ,
Murmanshi Sana tayi tace Suha sarkin rigima,
waya suke cikin nishadi har Sana ta hau kan titi batare da tasani ba,
Siddarth cikin jamfa da hula yayi matukar kyau sosai yana tafiya cikin moton sa, idanuwan ya sauke akan Sana da take waya akan titi dafa kan sa yayi yana girgiza kan sa yana furta "mai yasa yarinyar nan take son sa rayuwar ta cikin hadari,
wata babban moto ne tayi kan Sana bata rai da ta ankara ba Siddarth ganin hakan yasaka ya fito a moton sa yana furta keee keee, juyowa Sana tayi ta kafesa da idanuwar ta tana kallon sa,
shi kuma Siddarth alamu yake mata da hannun sa akan ta bar gun amma ina Sana bata fahimta ba kallon sa kawai takeyi
bangaran Suha kuma sai HELLO take tacewa,
a aguje Siddarth yatun karo Sana yana haki yana daf da ita moto nan yana karisowa gunta ai daguun sa ya zo gare ta ajefata agefan sa tayi gefen titin shima yayi gefen titin,.................
_____bangaje ta Siddarth yayi tayi gefe shima yayi gefen titin..
Suha datake dacewa Hello Hello daga karshe kuma sai taji wayar taka tse.
Siddarth da gudun sa yakari so gun Sana yafara mata magana cikin fada "fadamu mai yake damunki yasa kike kai kan ki cikin halaka.
Shuru Sana tayi ta zuba masa idanuwan ta tana kallon sa, hannu ta Siddarth yakama yazo,daf daita yana mata magana yana zare mata idanuwan sa kifadamun nace ko mai yake damun rayuwar ki amma kuma kin mun shuru bazaki bani amsa ba.
okay bazaki mun magana ba shikenan tsaketa Siddarth yayi yabar gun yana mai ji ran sa sai yanimo abunda yake damun wannan yarinyar.
Sana ganin mutum da take mutuwar kauna awannan karon zai sake kufce mata yasa ta tashi tabisa da gudun ta, yana daf dashi ga moto Sanna ta rumgume sa tabaya ta fashe masa da kuka mai jin rai,
tsayawa Siddarth yayi cak shi bai yi kokarin hana taba kuma baice mata komai ba kawai tsayawa yayi yana sauraran kukan ta,
kuka sosai Sana take tana kara tusa kan ta a tsakiyar bayan sa,
sai da yaji alamun tadan sauko da kukan tan yasa ya juyo da ita suka fuskan ta junan su, zuba idanuwa sukayiwa junan su suna kallon juna su sun shafi lokaci mai dan tsawo kafin Siddarth ya katse kallon yaja hannun Sana yasaka cikin moton sa shima yashiga yazauna, shi bai ja moton ba ya tsaya agun,
sai sukayi kusan minti na 30 kafi Siddarth ya lumshe idanuwan sa kana ya dubi Sana yace kin shirya fadamun abunda yake damun ki kenan?
Girgiza kai Sana tayi alamun ehh,
Ina jin ki cewar Siddarth ya mai da idanuwar sa akan ta kana kuma ya lumshe idanuwan sa alamun dai ina jinki,
Sana rasa yadda zata masa magana tayi gabaki daya idanuwan sa da yazuba mata yagama burki tata duk sai yama kwarjini,
Shuru tayi da zuba masa idanuwan ta tana kallon sa tana ji aran ta ina ace sutabbata ahaka,
kin zuba mun idanuwa kina kallo na kuma kinsan ke kadai nake sauraru Sana ta tsinka ya muryan sa kamar bashi yayi magana nan ba domin idanuwar sa arufe suke
Sana ta gyra zama tafara fai yace masa abunda take ji aran ta kuma akan sa,
sai da tagama magana tukuna Siddarth yafurta tun yaushe kika fara jin kina sona,
tun lokacin da kataima keni daga saman bene, cewar Sana
saboda haka kikaji kin fara sona? girgiza kai tayi alamun ehhh
Bude idanuwar sa Siddarth yayi yace "tabbas kina so nane saboda na tai makeyi kuma saboda kyawun da Allah yabani ko kuma saboda kudina ko?
girgiza kai Sana tayi tace a'a ba saboda haka bane,
Siddarth yace to saboda me kike sona yan numfasa kana ya daura dacewa idan ma saboda kyawu na kike sona tabbas kinyi gangganci arayuwar ki dan ni ban son mace wanda zata soni saboda kyawuna idan kuma saboda kudi ne ni bani da komai a cikin rayuwa ta dan kar kiga wannan moton kizata nawa ne na mai gida na nee ya kuma numfasawa kana ya daura dace idan duk saboda haka ne bana bukatar ki kifita mun amoto kuma na tsana macce da zatace tana son namiji na tsana irin wannan matan..
___Tsawa Siddarth ya doka wa Sana yana kuma maimai ta mata cewa shi yatsana mace kallan ta kifita mun a moto na ku baki jin ina magana ne.
Kuka sosai Sana takeyi tana hada hannayenta waje guda tana bashi hakuri kuma tana kukarin ganin ta fahimtar dashi ba duk saboda haka take son shi ba ita sabda Allah take son shi kuma lokaci guda son sa da kaunar sa tashige ta,
Amma kuma Siddarth bai ma tsaya ya saurare taba barai kuma ya fahimce ta,
kifita mun a moto na bana son mace irin ki wanda take iya zuwa gaban namiji ta furta masa kallaman soyayya kifita nace ko,
haka Sana tafita amoton badan ranta yaso ba,
KAUYE GUMA
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Bintu gabaki daya tafita hai yacin ta babu wani nutsuwa a tattare da ita tabbas Bintu tana cikin wani hali,
wani baƙin hadari ne yasake,taso sosai haka Bintu ta zauna babu wani alamun zata tashi agun domin Bintu yanzu jikin tane kawai yake motsi amma bata cikin haiyacin ta
ruwa ne ya sauko kamar da bakin kwarya sosai ruwan har yafi ɗazo dan sosai ake ruwan har da ƙankara akeyi ,
fitsari ne ya matseta sosai tashi tayi cikin ruwan ta nufi banɗaki har ta tsuguna zatayi fitsari kawai idanuwar ta ya sauka akan Khalil dayake wance sai bari yakeyi da'alama dai tun ruwan farko har na yanzu akan sa ya sauka
Fitsarin da batayi ba kenan ta nufi gun sa tana masa magana cikin rudani da tashin hankali, "sadauki na mai yasa kazo nan tun ɗazo nake niman ka duk nashiga cikin tsoro a she kana nan naje gidan Kaka gabaki dayan su basu nan
katashi mutafi ɗaki ruwa yana maka duka anan gun,
sam Khalil baya cikin hai yacin sa gashi kuma Bintu bazata iya daukan sa ba saboda akwance yake,
itama Bintu zama tayi agun ta fashi da kuka maicin rai da kuma fitar hai yaci
haka ruwan sama yayi musu duka agun
ALILI
Alili tun da Khalil ya harba bindigar nan yabir kice yafitahai yacin sa ya ruga aguje baima san yadda yake saka kafar saba,
A dai-dai lokacin da kuma Kaka yazo gun sakama kun jin labarin da yayi cikin gari wai ƴan fashi sun tare ƴan kasuwa shine hankalin sa yatashi ya nufi hanyar kasuwa tofa yana zuwa gun ne yacikaro da Alilin sa jikan sa yayi daji shine yabi bayan sa dan yasan Alili yana da tsoro da kuma firgici,
wannan abun ne yasaka Bintu bata ga kowa a cikin gidan ba,
Khalil gabaki daya baya cikin haiyacin sa yayin da Bintu kuma take gefen sa amma yanzu tabar kukan sai dau sauke ajiar zuciya,
kusan tara dai-dai Khalil kamar an mitsi ne sa yatashi yana rike kan sa datake sara masa,
Ganin Khalil ya mike ne yasaka Bintu itama mikewa tarike hannun sa,
fincike hannun sa yayi yana kara rike kan sa hawaye suna fita a cikin idanuwan sa,
sosai Bintu tashiga cikin damuwa itama ta fashe da kuka tana sake rike hannun sa,
shikuma Khalil yana sake fisgewa da kuka, yana rike kan sa
Bintu jansa take tana son ta fitar dashi amma kuma inaa takasa,
cikin kuka Bintu take masa magana "kaga fa halin dakake ciki amma kuma kazauna a bayi sai kuka kake idan wani abu ya cutar akai ya kake son nayi idan abu ya faru dakai ya kake son kaka yayi da kuma Alili gabaki dayan mu muna son ayuwar takasance cikin farin ciki da annashuwa sadauki,
Numfasa Bintu tayi kana ta daura dacewa kai ne farin cikin mu abun alfaharin mu dan Allah kazo mubar nan gun muje ɗaki kar wani abu ya cutar mana dakai,
Sosai Bintu ta kama hannun sa tana jansa da taimakon Allah ne kawai yasa Bintu takai Khalil ɗaki,
bayan tashi gar dashi ne ta fara kokarin cire masa jiƙankun kayan jikin sa bayan tagama cirai masane ta dauki wani a cikin kayyan sa mai saukin sawa ta saka masa ruwan shayi ta hada masa mai zafi sosai tabashi dakan ta yasha bayan yagama shane ta kwantar da shi akan gado,
bayan ta kwantar dashi ne tame ke tacire kayyan jikin ta bayan tacirai ne tasha sauran shayin da yasha tana gama sha kuma daje kusa da Khalil ta kwantar da kanta a ƙirjin sa tunani tashigayi inasu kaka sukashiga haka,
tana cikin tunani ne taji Khalil yarike mata hannu ita fah duk a tunanin ta Khalil yayi barcci ne,
jawota yayi zuwa ƙirjin sa ya matse ta sosai ajikin sa fara sauke ajiyar zuciya yayi akai-kai,
rigan jikin ta yafara cirewa Bintu batayi kokarin hanashi ba tabarshi yacigaba da cire mata
gabaki daya yarabata da kayan jikin ta yafara sumbatar ta ta ko ta ina
fita nayi a ɗaƙin naja musu kofa,
washi gari da safe Alhmdulilahi Khalil yatashi babu wannan raza nan a tattare da shi,
amma kuma wani sa'in yana dan razana
Bintu tamusu abun karyawa bayan sum gama cine Bintu takaiwa Khalil ruwan wanka mai zafi,
Khalil yana zaune akan gado Bintu tashigo ɗakin kusa dashi ta zauna ta kwantar da kanta akan ƙirjin sa tace na hada maka ruwan wankan yakamata kaje kayi wankan,
hannayen ta Khalil yarike yace "sai dai muje tare Mimi na,
To tashi muje cewar Bintu haka kuwa suka je amma taki aminta tashiga bayin
Duk yadda Khalil yaso Bintu tabishi har bayin amma taki haka yabar ta badan yana soba,
Yana shiga bayin ya fara wanka bayan ya kammala wankan kawai sai kashi ya fara sara masa kamar ana dakawa da guduma sosai ya rike kan yana kuka kamar karamin yaro yana son tunu abu amma kuma inaa yakasa tun komai
Sosai yake ihu da kuka yana kara kama kan nashi,
Ihun sa Bintu taji adai-dai lokacin da Kaka da kuma Alili suka shigo cikin gidan duk sunyi wani iri,
Haka khalil yaciga ba da ihu yana kuka kamar karamin yaro
Ai da sauri Bintu ta nufi bayin bata masan kaka da kuma Alili sun shigo cikin gidan ba,
Samun Khalil tayi reke da kan sa sai ciza bakin sa yakeyi ai kuwa da sauri Bintu ta nufa wajan sa tana kokarin kama sa amma kuma inaa
Khalil bai bari hakan ta faru ba kara kama kan sa yayi yana wani surutun da Bintu bata fahimta
Kaka da Alili kuma sun tsaya cak akusa da bayin dan bazasu iya shiga ba
Sosai Bintu takari so wajan sa yana rike da kan sa haka tayi kokarin saka masa kayya bayan tasaka masa ne ta fashe da kuka mai karya zuciya,
Kaka ya dubi Alili yace yaka mata fah kashi ga,
Haka kuwa akayi Alili yashiga ae da sauri ya fito yace ya sanarwa kaka haka suka shiga ciki bayin ganin khalil yana kuka rike da kayin sa ne yasaka Kaka furta "Alili yaka mata mutafi asibiti haka kuwa akayi da sauri Alili ya fita ya ɗako keken amalan ke,
Bayan Alili ya dawo ne gabaki dayan su kashiga keken suka nufi HASKE HOSPITAL
bayan likita ya gama ƴan dube-duben su na likitoti ya dubi suka kaka wanda yabukaci ganin su a office din sa,
DOCTOR ya dubi su kaka yace "amm Baba kwana ki na fada maka akan cewa wannan majin yaci duk abun da yashafi rayuwar sa na baya yamanta har nace muku kuna kokarin ganin ya tuna komai kamar kuna kokarin tuno masa da rayuwar sa na baya to mun bincika kuma munga no Alhamdulilah yanzu cikin kaso ɗari mun samu kusan kaso saba'in gaskia anna samu cigaba, likita numfasa kana ya daura dacewa a yanzu kuma mun gano akwai wani abu da yasakashi firgici sosai har yana razana to insha Allahu zamuyi maganin abun kuma zamu sake daura sa akan magani domin samun lapiyan sa kuma ina mai muku albishir ako wani lokaci zai iya tuno koman sa kudai kawai kubi shawarwarin dana baku,
Sosai likita ya musu bayani ya kuma daura bayanin sa bayan ya numfasa yace tabbas wannan firgicin yana yawan tsora tashi har yakai yana kuka da idanuwan sa da alama dai akwai wani abu da yataba ko dai akwai wani firgici da kuma tsoro da yataba samun sa daga rayuwar baya kodai wani abun amma karku damu kan ku zaiji sauki a ko wani lokaci,
ɗan numfasawa likitan yayi kana ya daura dacewa,yau insha Allahu zan salame ku Allah yabashi lpa,
GAbaki daya maganga nun likita ya kashi masu kaka jiki wani gurin sunyi farin ciki da jin Khalil zai samu lapiya wani gurin kuma sun shiga cikin damuwa idan khalil yanuna bai sannu ba amma kuma babu komai sukace,
Godiya sukayiwa likitan kuma yabasu takardan sallaman,
ALHMDULLH Khalil zaune a gadon a sibiti jikin sa yayi sauki ba kamar yadda suka kawo shiba zaune yake yarike hannun Bintu gam yana murzawa babu wanda yayi mawani magana,
Haka Kaka da Alili suka shigo suka musu bayanin asalla me su haka suka tattara komai nasu sukayi gida,
Bayan sun koma gida ne suka zauna a tsakar gidan Khalil.
Bintu tace kaka jiya naje gidan ku amma baku nan ina kukaje ne haka gabaki daya nashiga ruɗani duk abun da yafaru jiya Bintu ta zaiyawa kaka da kuma Alili,
Numfashawa kaka yayi kana yace wallahi hankali na yatashi sosai da nafita cikin gari naji labarin ƴan fashi suntare mutani a hanyar kasuwa kuma gashi gabaki daya jikokina sun tafi kasuwa shine na nufa hanyar kasuwar kuma ina zuwa nasamu anyu harbin bindiga kuma naga Alili yayi hanyar daji shiyasa hankali na yatashi nabi bayan sa,
Kakaa ya numfasa kana ya daura dacewa kwana daya har da wuni tukuna Allah ya hadani da Alili shine muka dawo gida muna dawowa kuma nace muzo nan saboda muga a wani hali Garkuwa yake ciki,
Shine muka samai sa cikin wanan halin
Kaka ya mai da idanuwan sa kan Khalil yace dan Allah daure kashenye magani nan saboda muna bukatar lapiyar ka ,
Khalil ya dubi Kaka ya kama hannayen sa yace insha Allahu zansha kuma nagode sosai da kulawan ku agare ni sosai sukaji dadi,
Sallama suka masa dan da Kaka da kuma Alili gabaki dayan su suna bukatar hutu,
Bayan tafiyar su Kaka ne Khalil ya mike ya dubi Bintu yace kinsan wani abu kuwa?
girgiza kai Bintu tayi tace ban sani ba amma kuma ina jin ka mijina,
Kama hannayen ta Khalil yayi ya mikar da ita jawo ta jikin sa yayi ya kwantar da ita akan ƙirjin sa hannayen sa kuma ya daura akan kugun ta har zai fara magana kawai sukaji sallaman Alili,
Sake ta Khalil yayi yace shigo mana Alili,
Shigowa Alili yayi yazauna ya dube su yace duk kuzauna akwai magana nan da zamuyi daku,
Gabaki dayan su suka zauna suka zuba masa idanuwa da alama dai shi suke sauraro,
Duban su Alili yayi ya dauko wata jaka ya ajiye musu agaban su,
Ya fara musu magana yadda zasu fahimce sa jakar ya fara budewa gabaki daya abun dayake cikin jakar yafito dashi ya ajiye musu agefen sa,
Wayace Android Khalil ya zubawa idanuwar sa,
Kai hannun sa yayi kan wayar ya kura mata idanuwan sa yana kallon kamar yataba ganin irin wannan abun amma kuma ainaa
Alili zubawa Khalil idanuwa yayi yana kallon sa tabbas Alili yayi haka ne daman dan yayi kokarin tuno rayuwar sa nabaya duk da yana son sutabbata ahaka dan sunyi matukar shakuwa da juna nan su,
Amman inaa iyayen sa suna bukatar ɗan su a wani hali iyayen sa suke a yanzu wata kilama sun dauka ɗan su ya mutu
Yakamata yadawo cikin haiyacin sa dan yaje gare su
Shiyasa duk wani abunda zai dawo masa da hankalin sa yasaka wani a kauyen su dazeje birni ya ɗan haka kudi n din sa yaba shi akan ya siyo masa abubuwan da ƴan birni suke yawan amfani da ita,
shine fah yau yakawo masa shi kuma Alili baiyi kasa a gwiwa ba yakawo masa,
Alili yace wannan kyauta ce na auran ku da ban samu na muku ba a lokacin auran ku fatan kunyi farin ciki da haka,
Khalil ya ɗan numfasa kana yace to shi wannan meye?
Alili yace "waya ce wanda zakunayi video da hoto da sauran su,
Bintu tace "yaa Alili yazamu na amfani dashi?
Alili yace bari nanu na muku haka kuwa akayi yanunawa Bintu dan shima ba iyawa yayi ba wannan wanda ya siyo tane ya koya masa,
Khalil bayi kokarin koyaba sai dai zuba wa wayar idanuwa yayi,
Alili yace lapiya kuwa Garkuwa?
Khalil yace wallahi ina ji kamar nasan wani abu game da wannan abun amma kuma nakasa tunowa,
Mekewa Alili yayi yaje gun sa ya dama kafadan sa yace kayi kokarin tunuwa kaji,
DA fa kansa Khalil yayi amma kuma yakasa tuno komai,
fuskan sa ya dago ya daura akan fuskan Alili yace nakasa tunowa,
Alili ya bubuga kafadun sa yace karka damu zaka tuna aduk sanda Allah yaso ya mai da idanuwan sa kan Bintu yace to ni zan wuce sai zuwa anjima zan zo naci abinci dare,
too yaa Alili cewar Bintu sai kazo,
bayan Alili ya tafi ne Bintu taje wajan Khalil taka hannayen sa tace fadamun abunda zaka fadamun yanzu,
mikewa Khalil yayi yace Mimi bana jin dadi ne zan kwanta
idanuwa Bintu tabishi dashi shikuma ya wuce ɗaki,