Mukaddari Ne Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: MUƘADDARI NE DAGA ALLAH.txt
Chapter 3 of 3
cigaba da aikin gida Bintu tayi tana tunanin mai yafaru da mijin ta lokaci guda ya sauya,
shi kuma Khalil daukan wayar yayi ya kunna video batare da sanin saba ya fito daga É—akin ya ajiye wayar akan windo,
alokacin hadiri ya hadu sosai, ganin Bintu tana aiki ne yasa ya nufi gun datake,
atsaye take tana shara shine ta mike tana rike kugun ta alamun ta gaji kawai sai ji tayi anrugume ta ta baya,
tace sahibi na har katashi daga barccin?
Sake rumgumo ta yayi ajikin sa yace ai nakasa barcin ne saboda baki kusa dani,
Murmushi Bintu tayi tace mijina kenan ina son ka,
Khalil yace kin san wani abu kuwa?
Girgiza kai Bintu tayi tace ban sani ba amma kuma ina jinka mijina
Khalil yasake rumgumo ta a jikin sa sosai ya fara magana,
"A duk sanda rayuwa tasakani kukaðŸ˜
sai ganin ki yasakani dariya😄
yayin da na fitar da rai na daga duniyaðŸŒ
sai soyayyar ki kuma da kulawan ki subani saraiðŸ˜
haka kuma idan damuwa ta mamaye zuciya ta da fuskana😊murmushin ki kadai ya isa ya musanya wannan da murmushi☺ina son ki Mimi na ke rayuwa ce agare ni wacce bazan iya batare dake ba ina matukar sonki acikin rayuwa ta😠ina son ki
Bintu tsaban dadi sake rungumo Khalil jikin ta tayi tace wayyo Allah dadi ina son ka ka kashe ni da kalaman ka ina son ka sosai suka shagala da wasan soyayya,
Ruwan sama lokaci guda yasauko ai gabaki dayan su suka fara wasa cikin ruwan wannan yawatsa mawan haka ma wanan,
sunshiga cikin nishadi sosai kamar kar wannan rana ta wuce agare su, rawa suka fara acikin ruwan sai tsalle suka tayi cikin ruwan kamar kananun yara
BUSHAR
____Sunan mai dadi Arjun yafurta mikawa Sima foffi yayi yace mata ina É—an zuwa, bai jira amsan taba yabar gun,
Bayan Suha yatabi kuma yaci sa'a gida takoma Alhndullh ya furta ganin Æ´anda take kusa dashi ne dan haka sake ya koma wajan Sima farin ciki fal cikin zuciyar sa,
Sai tara na dare ya koma gida gabaki daya ya gaji amma kuma hakan bai hana sa dauko pen da takarda ba yafara rubutawa sahibar sa sako kamar haka,
Barka da dare sahibata fatan kina cikin koshin lapiya,
Baki sanan waye niba amma kuma nina san waye ke tun a mafarki na idanuwa ta suka hasko mun ke zuciya ta da tunani na suka isa zuwa gare ki tukafin idanuwa ta sugan ki a zahiri zuciya ta ta hasko mun ke cikin mafarki na bana iya komai ban san komai ba sai zallan son ki da kaunar ki,
zuciya ta ta fada soyayya da mai irin siffofin ki tun kan ido ya kai ga ganin ki tun a cikin mafarki na dalili kenan dayasa da kallon farko idanuwana suka gane ki zuciyata ta kamu da kaunar ki domin dama can dakon ranar zamowar mafarki na gaskiya suke
SUHAI ba lallai nazamo na farko ba amma ina son nazamo na karshen da sunan sa zai rubutu a littafin soyayyar ki zan so nazamo mutumin da a kullum zaki sami farin ciki da nutsuwar zuci da dorewar murmushi a sanadin sa zanyi burin shimfida rayuwa ta domin kitaka zuwa ga cimma burikan ki na rayuwa
SUHAI kin zamo fitila wacce ta haske duhun zuciya ta soson data wanke dattin zuciya ta hakama wacce ta bawa rayuwa ta alkibila
Idan nace ina son ki iya kalmomi uku nayi amfani da amma manufar dake kunshe cikin su yafi karfin abunda lissafi zai iya kewayewa ina son ki ba babu ranar dainawa
Ina kaunar ki Suhai yau kinyi matukar kyau fushi akan fuskan ki kuwa yana miki kyau kiyi fushi kar kiyi dariya,
Fatan barcci mai dadi
SUHAIMA
Ya fito daga cikin gidan sa ya nufi gidan Suha tare da furen da ya siyau mata a dai-dai kofar gidan ya ajiye furan tare da wasikar yaÉ—an labe awani waje ya tsaya jiran ta
Wayar Arjun ne tara ruri dubawa yayi ganin Aaaraw yasa bai É—auka kiran ba ya cigaba da kallon kofar gidan yana ta addu'a cikin zuciyar sa Allahu yasa tafito ya ganta kuma taga wasikar sa,
Suha gabaki daya yau bata da niyar fita dan yau wani kasala take ji dan haka tayi wanci yanta abun ta,
Arjun da yakusan awa guda agun dayake bai ga alaman Suha zata fito ba yasashi lapiya badan ranshi yaso ba ga kuma Aaraw yana ta kiran wayan sa
Yana shiga gida ya kira Aaraw a waya
Aaraw yace haba bro ina ta kiran ka waya baka dauka ba fatan kana lpa ko
Numfasaw Arjun yayi ya lumshe idanuwar sa kamar dai Aaraw yana ganin sa ya furta Allah dagaske nagan ta kuma ba Aljana bace mutum ce gabaki daya abubuwan da ya faru tsakanin su ya fada masa,
Aaraw ya numfasa kana ce kamar yadda ta adabe ka acikin baccin ka tunanin ka kai haka zaka mata ta hanyar wasika da kalamai a ciki masu sanyaya zuciya,
Sosai Aaraw ya kwantarwa É—an uwan sa hankali sukayi sallam,
Arjun bacci barawo ne kawai ya dauke sa da asubahi yatashi yayi alola ya tafi masallaci bayan yadawo ne kuma ya dauki pen da takarda yasake rubuta ma sahibar sa wasika kamar haka,
Arjun ya fara rubutun sa
Barka da wannan kyakkyawar safia duda nasa batakai akirata da kykkyawa ba agaban ki domin idan akace kyakkyawa bana tunanin wata ake nufi wacce ba keba ke kadai kika cancanci wannan sunan dan haka nakeyi miki SUHAI
Ina son ki fatan kintashi cikin daddan yanayi mai cike da farin ciki dan naji hakan ajinin jikina da kuma bugun zuciya ta
Bana son kiyi murmushi ko dariya a fushi nake son ganin ki dan haka kiyi fushi nagan ki kinji Suhai na
Yadauka ya nufi gidan da Suha take kamar yadda yabar wasikar jiya haka yazo ya gani alaman dai bata fito ba har yanzu
É—an shuru yayi kodai ba ita daya bace agidan nifa a tunani na kamar school ne yakawo ta garin nan,
Shuru yayi yazubawa wasikar idanuwa kawai bazato ba samma ni yaji karan nan bude kofa ai da sauri yabar gun ya boye awani gun yana kallon ta,
Sanye take cikin kayyan barci gashin ganta duka abaje abayan ta bakin ta kuma ature da alama acikin fushi take
Har tasa kafarta zata sallake wasikar batare da tagani ba kawai idanuwan ta yasauka akan wasikar zuba masa idanuwa tayi tana kallon wasikar har guda biyu,
_____tsu gunawa tayi ta dauki wasikar ta koma ciki zama tayi akan kujera tafara karan tawa sai data takaran ta baki daya cikin mamaki tamike tsaye tana magana waye wannan haka waye yasani a kasan nan haka har da tura mun sako amma waye wannan dan jim kadan tayi kana takoma tazauna gabaki daya tashiga cikin rudani da tsoro sosai,
Shima Arjun ganin ta dauki wasikar ta yasaka komawa gidan sa yana mai sauki numfashi yana ji kamar ya sauke wani abu akan sa,
tunani yashiga wani abu zaiyi wa Sima dan gabaki daya baya son yafita da ita yau
ai kuwa yana cikin tunani wayar sa ta fara ruri dubawa yayi ganin Sima yayi tsaki gami wurgar da wayan
sai da Sima tama 10 missed call kafi ya dauka
Tana jin ya dauka ta fara zuba mishi shagwaba har da kuka tana magana haba ina takirn ka amma kuma baka duka ba ina ka ajiye wayar ka?
Numfasawa Arjun yayi yace yanzu duk wannan tambayoyin duk nine zan amsa miki kuma lokaci guda, kinsa ban son tambayoyi dan haka idai na,
Kayi hakure cewar Sima tace da naki raka ne na fada maka nashirya kai nake jira zakazo ka dauke ni ne ko nine zanzo na dauke ka?
Lumshe idanuwan sa Arjun yayi kamar tana gaban sa kana ya numfasa yace yau bana jin dadi ne Sima yau muhuta kawai a gida,
Cikin damuwa da nuna tsatsan tausayin sa tafara jero masa tambaya mai yasa ke?ina ne yake maka ciwo bari nazo yanzu,
Sai da Arjun ya gama saurarun ta kana yace kar ki damu kanki bawani ciwo bane kuma karkice zaki zo waje na kinsan banson haka dan haka yanzu ina bukatar hutu zan huta kat ya kashe wayar sa ya ajiye ta agefan sa ya fara tunanin abunda zai tuwa wa Suhai din sa na barka da rana dan yana son sai ya gama kashe ta da soyayyar sa ne afin ya fito masa da kan sa a lokacin tagama aminta da soyayar sa,
Zama yayi da bairo rike a hanun sa yana rubuta mata sako kamar haka
Barka da rana my Suhai fatan kina cikin koshin lapiya fatan kin kasance da mamakina acikin zuciyar ki na waya miki wannan wasikar ko to nine Aljanin ki kuma mai son ki
HMMM
Kinsan wani abu kuwa ?
Mafi dadin sauti a duniyar nan muryar ki ne ina jin dadin sauraran ta musaman idan kina cikin fushi bana son kina yawan murmushi
A kowace dakika ta rayuwa ta sautin muryar ki a kullum yana kara tuna mun da cewa har yanzu akwai ragowar farin ciki a duniya
Mafi kyawun abunda ido yake son kalla shine fuskar ki idan zan fadi abunda nafi jin dadin yi a rayuwata to kallon kyakkyawar fuskar ki ne ina jin dadin hakan,
SUHAI ina so nayi farin ciki amma taya farin ciki na zai yayu idan babu ke?
NI tamkar fitila ne kece makunnin idan kika so zan kasance a cikin haske idan kuma kika juyan baya zan dawwama ne a cikin duhun da babu saran wani haske a gaban sa
SUHAI idan zan jaraba hanyoyi dubu da zan sakaki farin ciki dari 999 suka ki aiki ta cikon duhu tayi murna zanyi kamar ba gobe kowace hanya matukar dai tana kaiwa ne ga farin cikin ki ne to kuwa zan bita
Burina nasa murmushi ya zamo abokin fuskar ki amma kuma ina son kallon fushin ki dan yana miki kyau Suhai daurawa zuciyar ki aure da farin ciki na kuma kulla zumunci mai karfi tsakanin ki da ni
Ina son ki sossa irin sosai dinan my SUHAI na
Fatan idan kin gama karan ta sako na kiyi fushi kar kiyi murmushi
ABAR kauna ta
Yana gama rubutawa ajiye agefan sa yana jiran 12:30pm yayi ya kai mata har gidan ta amma wannan karan kam sai yayi nocking,
Suha ta shiga cikin mamaki matuka amma hakan bai hanata nishadi ba dan ita tama mance komai girki ta daura tana sauraran waka tana rawan ta abun ta bayan tagama cin abin cin ta tayi wankan ta tazauna dan yau kam tayi niyar agida zata zauna babu wani abunda zai saka tafi ta,
Karfe 12:30pm tayi anayi mata nocking tana ji amma kuma tayi shuru dan ita gabaki daya bata son ta kura a cikin rayuwr ta sai da akayi nocking kusan sau biyar kafin ta tashi tana jan tsaki tana kananun magana a cikin bakin ta na irin nifah anta kura mun,
Kofar ta bude amma kuma babu kowa sai wasika tagani kamar dai na É—azo wayege-wayege ta fara ko zata ga wanda yayi mata haka but bataga kowa ba,
Daukan wasikar tayi ta koma cikin tazauna ta fara karantawa tana karan tawa tana murmushi wani gun kuma ta tura baki wani wajan kuma ta lumshe idanuwar ta
Sai da tagama karantawa kuma tashiga duniyar tunani wai nikam waya mun haka ne waye shuru tayi amma kuma sai wani tsoro ya kamata da ta tuna cikin wasikar nasan baki san waye niba to Aljanin ki ai tsoro yasata tamike tashirya badan taso ba tafita a gidan kai tsaye kogin ganga tayi domin shakatawa da shan iska dan wallahi gabaki dayan ta atsora ce take,
Tafita agidan baki daya daya ke kogin gangan babu nisa yasaka ta tafiya da kafar ta,
Tafiya take abakin ruwan tana tunani shin waye waye wannan mutumin da yasanni har haka shuru tayi tana bin bakin kogin a hankali, kwai jitayi kamar ta ya guce tayi cikin ruwan kashi bata iya ruwa ba
Arjun yashiya yayi kyau yau haka kawai yaji yana son tafiya a kan doki dan haka ya hau kan doki yana ta tsula gudu kai tsaye ya nufi kogin ganga dan yau yana son shakar iskan wajan dan gabaki daya yana cikin farin ciki sosai yau dinan da yaga sahibar sa har sau biyu,
Suha datake ta faman mutsu-mutsu cikin ruwan mutani duk sun kewaye bakin ruwan anrasa wanda zai take maketa,
Arjun ne ya yanko da dokin sa gun da mungun gudun sa ganin mutani a bakin kogin ganga yasashi sauka daga kan dokin ya nufi gun dan yaji mai yake mafuwa,
Tambaya ya fara mai yake faruwa anan mutanin da suke tsaye agun lokacin da abun ya farune suka sheda masa cewa fa wata yarinya ce ta fada cikin ruwan kuma da alama dai bata cikin haiyacin ta,
Arjun sarki tai mako bai tsaya sauraran wani zance ba ya fada cikin ruwan, lalume ya fara cikin ruwan ta ko ta ina ya duba bai ganta amma a hakan bai sarai ba yacigaba da dubawa da taimakon Allah sai ga Arjun yaga Suha ama asume take babu alamun numfashi ajikin ta
Fito da ita yayi akafadan sa har yanzu baiga fuskan taba sai da ya kwantar da ita akasa dan dubawa ko tana numfashi sai yadaura idanuwan sa akan nata ,sosai ya razana yafara jijigata yana mata magana gabaki daya yagama rike cewa wata matace tazau kan sa ta fara masa magana kahura mata bakin ta sai ka matsae mata cikin ta ruwa da tasha gabaki daya zai fito,
Dago fuskan sa yayi ya daura akan fuskar matan yafara magana yace ai mutuwa tayi gashi du bata matsi matan tace to ka kaita asibita ni inajin kamar bata mutu ba ,
haka kuwa akayi Arjun yasaka baleta abayan sa ya sakata akan dokin sa yayi a sibiti da ita,
tu kafin su isa hospital din Suha ta bude idanuwan ta jitayi kamar tana tafiya akan wani abu lumshe idanuwan ta tayi kana ta fara tunano duk wani abunda ya faru da ita tun daga fitan ta daga cikin gida har zuwa kogin ganga har fadawan ta kogin sai da tuna amma kuma yaya akayi ta ganta anan yun kura tayi zata tashi kawai sai jinta tayi kamar tana tafiya akan doki ai kuwa da sauri ta mike ta zauna dai-dai kai idanuwan ta tayi kan fuskan Arjun tayi dai-dai lokacin da shima ya daura idanuwan sa kan nata,
ae kuwa tafara kokarin saukowa daga kan dokin ganin zata iya jin ciwo ne yasa ya tsayar da dokin sauka tayi akan dokin,
Ta matsu daf dashi ta nuna sa da yatsan ta,
Waye kai kake bibbiyan rayuwa ta mai nakeyi akan dokin ka kai waye da har zaka hada jikina da naka waye kai da har zaka dauki ni kasakani akan dokin ka okay kai muharami nane kodai haka kuke to bari kaji duk da ni maturiya ce amma kuma a gidan mu anan tar biya mai kyau dan haka karka kara kuskura ko kadan ne kaso kataba jiki na banza kawai tayi tsaki ta juya abun ta,
Zuba mata idanuwa yayi har ta bacewa ganin sa sai yabar ganin tukun na ya daga idon sa akan ta yayi murmushi yace Suhai rigima ina son ki,
Kai tsaye gida tayi tana datasanin fita dan dama yau bata da niyar fita amma kuma wannan mutumin da ya dage da tura mata wasikar nan ne yasa duk haka ta faru tsaki tayi tace n tsaneka ko kai waye ne,
Wanka tay tabi lapiyar gado ta wanta dama ba salla takeba
Sai kusan mangari ba ta tashi da wata yunwa sosai indomei tayi taci abunda da bata da niyar fita agidan yanzu
Tana gamawa tasake wanka ta saka kayan bacci ta zauna a parlo tana kanllo awayan ta tana shan sweet,
Nocking taji anyi amma kuma ta share tacigaba da kallon ta sake nocking akayi amma kuma shuru tayi tacigaba da kallon ta sai da akayi nocking kusan 20 kafi tayi tsaki tamike tace wayene taje ta bude kofar amma kuma babu kowa sai wasika tagani hakan yasa tasake tsaki kamar zata dauka kamar bazata dauka ba kawai ta yanke shawaran daukawa ta wuce ciki abun ta sai da tagama komanta kafin ta dauka tafara karantawa kamar haka
Fatan kina lapiya sarkin fushi na amma fa kuma fushi yana miki kyau sosai tabbas ke ta musammance kuma ke rayuwa tace ina son ki sosai
Kinsan wani abu SUHAI?
Ba ina son ki bane dan na rayu dake ina son ki ne domin hakan ne kadai zabin da rayuwar tawa takeda shi
Bazan iya tina halin dana kasance ba a cikin ba kafin sani ki amma zan iya fadar halin rayuwa ta zata kasance anan gaba idan rabuwa tashigo tsakanin mu
Kiyi min alkwari bazanmu rabu da juna ba kuma kicika min alkawari komai rintsi da tsanani bazaki rabu dani ba idan ba mutuwa ce tadau raina ba
Idan kin dauka mun alkawari too ka number waya ta gobe zan nuna miki kaina
Ina jiran gani reply din ki my SUHAI ta
____Shuru Suha tayi tana tunanin ta masa reply ne ko kuma ta rabu dashi amma kuma koma waye ne bana bukatar sanin sa dan haka ta ajiye wayar ta agefe tayi baccin ta
Arjun ganin har yanzu baiga messages ya shigo cikin wayar sa ba yasa shi numfasawa ya gyra kwanci yar sa ya furta ai nasan taurin ranki bazai sa ki mun reply ba,
KAUYE GUMA
_________________________________________
Khalil da Bintu suna rayuwar farin ciki kowa so yake ya farantawa É—an uwan sa idan kaga rayuwar Khalil da Bintu sai rayuwar su tabaka sha'awa Alhmdllu a dauki azumi lapiya dan yau har ankai 20 har anfara shirye-shiryan sallah, Khalil yasiya wa Mimin sa duk abunda zata bukata a sallah hata kaka da Baffah ma bai bar su abaya ba duk abun da yasan zasu bukta iya karfin sa yayi musu har da Alili ma yayi masa duk Alili ya nuna kin amincewar sa akan hakan amma Khalil ya dage akan sai ya bashi babu yadda Alili zaiyi haka yakarka kuma yamasa godiya.
Khalil da Bintun sa kwance akan gado Bintu ta daura kanta akan kafafa fun sa yayi da shi kuma Khalil ya mike kafaffun sa dago Bintu Khalil yayi ya jawo ta jikin sa yafara magana cikin nuna soyayar sa agare ta, Mimin idan Allah ya kai mu gobe zamu hada duk wani abun da zamu bukata zamu tafi wannan dajin mai ciki da dadin zama dan agun nake so muyi sallah, saboda haka ne ma yasa gabaki daya abunda zamu bukata nakai mana batare da sanin kiba fatan kinyi farin ciki da hakan,
Sosai Bintu ta kwantar da kanta akan ƙirjin sa hannayen ta kuma akan fuskan sa tace "gaskia samun miji kamar ka abun farin ciki agun duk wata ƴan mace gaskia nikam nayi sa'a acikin rayuwa ta kuma ina kara godiyawa Allah da yakawo mun kai a matsayin miji ina son ka sosai sahibi na,
Sosai Khalil ya jawota jikin sa yana kara kwantar da ita akan ƙirjin sa suka shiga duniyar soyaya mai cike da dadi,
Washi gari Bintu ta tashi da zazzabi mai zafi ajikin ta dan ko azumi bata dauka ba sai amai kawai takeyi haka Khalil ya samu Kaka ya she da masa cewa yau Bintu ta tashi bata jin dadi sai amai take,
Kaka ya dube sa yace gaskiya ni ban kwarai tanan fanin ba amma kuma shawara katashi ka kaita a sibiti sai kaji duk abunda yake damun ta dan haka zansa Alili ya raka ku ,sosai Khalil ya ji dadi kuma yayi na'am dan haka yayiwa Kaka sallama ya fita agidan kai tsaye gida ya koma ya sanarwa Bintu tashirya zasu tafi asibiti dan duba lapiyar ta haka kuwa akayi suka shiya suka tafi asibiti harda Alili,
HASKE HOSPITAL
Bayan likita yagama gwaje-gwajen da yakamata ya dube su yace ina tayaka murna matar ka tana dauke da ciki har na wata guda, wani uban tsalle Alili yayi tare da rungumo Khalil yajikin sa Bintu kuma duk kunya yagama rufe ta Khalil sujada yayi na nuna godiya wa ubangijin sa yayi matukar mun na har yarasa abunda zaiyi, likita yace zan rubuta muku magani sanan kuma ya kamata a kula da ita sasai abun da yakamata taci kamar su ganyaya ki su fruit kifi kwai da kuma nama ya kuma daurawa da basu shawarwari gurin kula da mai ciki kana kuma ya sallame su,
Khalil tunda suka koma gida ya kafe ya tsare akan babu wani abunda Mimin sa zatayi shine zaiyi komai gabaki dayama yadankaw Alili ragamar kasuwancin sa ya dauki Bintun sa suka koma dajin da zama shiyake mata komai
Wata irin kulawa Khalil yake bawa Bintu shakuwa da soyaya tasake shiga tsakanin su,
Anga wata gobe ne sallah kowa sai murnan sallah yakeyi amma kuma banda Bushar da yanzu duk hankalin shi ya gama tashi komawa wajan Bokan sa yayi dan yaji mai yasa har yanzu Khalil bai fada rashin lapiya ba,
Bokan yace ka kwantar da hankalin ka yanzu komai ya zo karhe kwanan zakaji kyakyawan labari dan haka kaje duk sanda wani labari mai dadi ya riske ka akan wannan mutumin sai kadawo gare ni haka Bushar yatafi badan zuciyar shi ta amin ta da hakan ba sai dan kawai babu yadda zai yi ne
Yau take sallah kowa yayi wankan sallahn sa danzwa eid hakama mangaran Kaka da Alili sunyi kyau masha Allahu mangaran BAffah da Inna Jummai da yaran su Miro da kuma Hauwa suma sunyi kyau sosai masha Allahu gabaki daya sukatafi sallah eidi
Bintu tayi matukar kyau sosai yayin da Khalil yake bayan ta dukan su sanye cikin fararan kaya sunyi matukar kyau suka tafi masallacin eidi
Alhamdullh anyi sallah lapiya sai gaishe gashe akeyi yayin da Khalil ya dauki matar sa sukayi gidan Kaka suka masa barka da sallah daga nan kuma sukayi gidan Baffah shima haka babu laifi Inna Jummai ta sake musu sun É—an samu tarba agun ta daga nan kuma sukayi gidan su wanda suka koma yanzu wannan dajin kenan,
Suna shiga Khalil ya kama hannun ta yajawo ta jikin sa ya fara mata magana cikin kunuwan ta
Rayuwa nada ma'anoni dayawa dogaro da yanda kowa yake fassara ta a gurina cikakkiyar ma'anar rayuwa shi ne samun haske da babu duhu a bayan sa haske ba irin na rana ba domin yana wucewa ba kuma irin na farin wata ba domin yana dishewa haske dai irin na halittar da ko baccin ta haske ne ba iya murmushin ta ko hasken idanuwan ta ba
Barka da sallah sahiba ta Allahu ya maimai tamana insha Allahu idan muna cikin rayayu wata sallah tare da yaran mu zamuyi ina son ki matana
Bintu bata masan abun ta zata masa ba dan yayi farin ciki kamar yadda yasaka ta kawai tafara sumbatar sa ta ko ta ina tun suna tsaye har suka fada kan gado daganan kuma sukashiga wata duniya nikuma na fita aÉ—akin
Kusan awa guda na koma É—akin gani nayi har sun sake wanka Bintu tafi to ta daura musu girki gidan ya cika da kamshi ga kuma kamshin furan ni sosai gidan yayi wani irin dadin zama wa masoya,
Bayan Bintu tagama komai nata ne ta koma É—akin ta fara bubbuka kafadan sa amma kuma taji shuru babu alamun mutsi magana tafara masa katashi muci abinci nagama komai amma kuma ina shuru duba fuskan sa tayi taga idanuwan sa sun kafe bakin sa na fitar da wani farin ruwa mai warin gaske ai salla ihu! Bintu tayi tana jijiga sa amma kuma Khalil ko motsi baiyi ba...........
___jijiga shi tafara yi tana masa magana akan yatashi amma kuma shuru babu alamun ma ya jita hankalin ta yatashi sosai tarasa yadda zatayi dan taga ya tashi amma kuma inaa shuru ne ai kuwa ta fashe da kuka mai cin rai da tashin hankali sai suru rai takeyi tana sumbatu tana fadin nashiga uku na ina zan saka kai na mai yake faruwa da miji na yanzu yana lapiya kalau amma kuma gashi nan babu alamun numfashi ajikin sa wayyo Allah na nabanu na lalace Allah kai ne gata na kashiga cikin lamarin wannan bawan naka kuka take sosai kamar babu gobe zama tayi a gurin bata ko iyace komai kukan ma yanzu ta dai na sai zuba masa idanuwan ta da tayi,
A haka suka wuni tana zaune agaban sa ta zuba masa idanuwan ta tana kallon sa babu ko kiftawa rayuwa kenan kana naka shi kuma Allah ya kama nashi É—azo fa Khalil lapiyan shi kalau har yana fadawa Bintu sa kamamai masu dadi amma kuma yanzu gashi nan shi kamar gawa akwance babu ko motsi atattare dashi oh Allah
Alili tun É—azo gaban sa sai faduwa yakeyi kamar dai wani mummunan abu yafara haka yake ji ajikin sa kuma gashi tare da Kaka lapiya kalau sai firan su sukeyi mikewa Alili yayi ya dubi Kaka yace "Kaka zan je na duba Khalil na jisa shuru kuma yace mun zai zo muje wani waje dan haka zan je na duba sa, da to kaka ya amsa masa shi kuma Alili yayi gidan khalil, sallahma ya ringayi acikin gidan amma kuma shuru babu wanda ya amsa masa dan haka ya kusa kan sa cikin gidan a tsakar gida ma yana ta sallama amma shuru tsoro ne yasake shiga cikin zuciyar sa kardai wani abu ya faru dasu dan haka ya yanke shawaran shiga cikin É—akin ai kuwa yana shiga yagan su a kwance kamar babu rai ajikin su, gaban sa ne yayi mummuna faduwa yayin da yasake zuba musu idanuwan sa akan su dan ya kara tabbatarwa kan gadon drect ya nufa yafara duba Khalil idanuwan sa duk sun kafe yayin da kuma wani farin ruwa mai warin tsiya yana fitowa daga cikin bakin sa, araza ne Alili ya fara jijigashi amma kuma babu wani alamun motsi atattare dashi ari kice yayi kan Bintu dan ya dubata amma itama a sume yasa meta rasa yadda zaiyi yayai tashin hankali wanda ba asaka mata rana rayuwa kenan ai da gudu Alili ya fita agidan drect gida ya nufa dan yasanarwa Kakan sa cewa fah Garkuwan su da kuma Bintu baki dayan su sun mutu, a mungun firgece yashigo gidan sai sauke numfashi yakeyi yayin da kuma hawaye sai fita daga cikin idanuwan sa suke yi sai nuna hanya yakeyiwa Kaka yana sauke numfashi,
Kaka kama hannun sa yayi ya zaunar dashi ya dauko ruwa ya kafa masa abaki sai da yashanye tass kafin Kaka ya dube sa ya fara magana to yanzu nutsu kamun bayani yadda zan fahimce ka kafadamun mai yake faruwa har kunce yadda zakuje din kai da Garkuwa mai ya faru acan din kadawo kana haki haka, fashewa da kuka Alili yayi yana furta gabaki dayan su sun mutu basu motsi basu numfashi sun tafi sun bar mu, kaka yace nifa ban fahimce abunda kake cewa ba kayi muna magana ta fahim ta waye suka mutu waye suka tafi suka barmu Alili da hawaye ya gama cika masa idanuwan sa sai zubowa suke kan kumatun sa ya furta "Kaka Garkuwan mu da shi da Bintu dukan su , sun mutu babu wanda nasa mu acikin su suna numfashi,
Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana Kaka yace kamar ya sun mutu bayan yanzu suka bar nan Allah sarki Kaka tsabar ruÉ—ani ya matan ikon Allah akan bawan sa, Alili yace wallahi Kaka basu numfashi, Kaka bai tsaya sauraran suba yabar gun kai tsaye ya nufi gidan su Khalil yana tafiya yana hada hanya babu wani nutsuwa a jikin sa duk wanda ya kalli Kaka sai yasan yana cikim tashin hankali sosai, Alili yabi bayan sa,
____________A firgi ce Kaka ya shiga cikin gidan ko sallama babu kai tsaye É—akin yayi ganin su a kwance ne yasa shi da fa bango yana jin jiri-jiri yana É—iban kan sa idanuwan sa kuma sunyi jaa lokaci gudu tsayawa yayi dafe da bango kusan mintuna kafin yayi kan Khalil da yake kwance kamar gawa jijigashi ya shikayi yana ambaton sunan sa amma kuma ina babu alamun zai farka Kaka komawa yayi kan Bintu itama yafara jijigata shuru itama zama yayi yayi shuru ya zuba musu idanuwan sa da gabaki dayan su, sunyi jaa sosai ko kiftawa bayayi, Alili ne yashigo É—akin ganin kakan sa yayi zaman dirshin yasa shi wani irin razana sosai zuciyar za sai bugawa takeyi kardai mutuwa sukayi dagaske, ganin kakan sa babu wani abun kirki dazai iya ne tunda yana cikin rudani yasashi tunkaran wajan mai gari dan yasanar masa abunda yake faruwa ko Allah zaisa yataimaka masu,
Sauri-sauri har yana hadawa da gudun sa dan ya isa gurin mai gari shima kan sa Alilin karfin haline kawai amma zuciyar sa zafi take masa sosai, afigice ya isa gun mai gari sai sauk numfashi yakeyi na huci zama yayi ya fara zai yana masa duk abunda yake faruwa bayan mai gari ya gama saurara ne yasaka liman yayi masa jagora izuwa gidan Khalil din, liman da Alili suka dau hanya sai gidan Khalil yadda Alili ya tafi yabar Kaka haka sukazo suka samai sa a yadda yabar shi, liman ganin duk karfin zuciya irin na Kaka a irin wannan halin sai da jikin sa yayi sanyi mutum mai yarda da kaddara duk yadda tazo masa mutum min da yake fadawa mutum idan wani abu yasa mu bawa tofa tabbas wannan MUKADDARI NE GADA ALLAH amma yau shine a zaune haka, gyra zama liman yayi ya fara raira karatun alkur ani mai girma sosai yake karanta suratun bakara, a hankali-a hankali kuma kaka nutsuwa tafara shiga jikin sa ya fara sauke numfashi sai da nutsuwan sa ta dawo jikin sa kuma sai yafashe da kuka yana magana cikin kukan sa, "wannan yaron ya gara jarabawa a rayuwar sa shikam haka Allah ya kaddara masa naso wannan bawan Allah aje tunanin sa yadawo ya je wajan iyayan sa dan nasan suna matukar mukatar sa amma kuma haka Allah yatsara abun sa wannan yaron bazai koma cikin dangin saba, rayuwa kenan Allahu yajikan ka Allah yama rahama, liman ya amsa da amin yayi da Alili kum hawaye yagama wanke masa fuskan sa,
Mikewa liman yayi ya nufi gun da Khalil yake yafara kokarin fara masa addu'an mamaci kafin kuma asalla ce sa akai sa gidansa nagaskiya kawai idanuwan sa ya sauka akan yatsan Khalil ya yake ta motsi yana ai kuwa da sauri yake furta bai mutu ba yanan da ran shi ai daga Kaka har Alili awani figice suka mike suka nufi gun Khalil suka fara jijigashi suna magana suna murmushi tare da sauke ajiyar zuciya duk da halin da Khalil din yake amma sunji dadin ganin shi yana raye wannan yayi matukar faran ta musa, Alili ya dube Kaka yace Kaka yakamata mukai sa asibiti Kaka ya dube sa yace "kana ganin wannan jinyar ta asibiti ne aa wannan jinyar bata asibiti bane daukan sa zamuyi muje gida amafara masa jinya har Allah yasa yasamu lapiya,
A figice Baffah yashigo gidan yana ambaton sunan Bintu Bintu sai asanan Kaka ya tuno da Bintu datake kasa itama kamar wanda rai yayi halin sa, ai da sauri Kaka ya nufi gun da Bintu take ya dauko ruwa ya watsa mata a fuskan ta dagon ajiyar zuciya tasauke amma kuma idanuwan ta suna rufe bata bude ba ida dai fatan ta Allah yasa mafarki take, Baffah kanta yana nufa hawaye idanuwan sa yana jijigata akan ta tashi amma kuma Bintu idanuwan ta arufe suke gam, Kaka ne ya bada mumar ni akan su dauke su sukai sa gidan su haka kuma akayi gabaki dayan su suka dauki su sai gidan Kaka,
Bayan ankai su Khalil gidan Kaka agashiga masa magani sosai amma kuma babu wani cigaba Bintu na batsa dantse wajan kula da mijin ta Alili da Kaka su suke kai Khalil toilet Bintu kuma ta masa wanka kullum Bintu ita take mamatsa jikin mijnta tare da masa addu'oi yau kimani wata guda kenan amma har yanzu babu wani jigaba mutanin kauyen guma kuma ko albaracin bakinsa yake fada akan jinyar Khalil yayin da Bushar yake cikin farin ciki da labari yasame sa har yafara shirye shiryen raba Khalil da Bintu da kawai yaga ya aure ta,
Kaka yau da sassafe ya nufi daji dan nimo maganiwa Khalil duk maganin da yashafi na tsihiri sai ya nimo anyiwa Khalil amma kuma har yanzu abun daya ne shine babu wani cigaba a tafiya nimo magani,
Kwanaki na tafiya lokaci kuma yana shudewa yau takama Khalil yana da wata uku akwance yayin da cikin Bintu kuma wata hudu da kwana uku jikn Khalil sai gaba-gaba yakeyi babu wani sauki a tattare dashi dan haka Kaka yasake shiga cikin wata duniyar tunani ganin yamuwar lapiyar Khalil, amma har yanzu shuru, Kaka yasamu Baffah da magana akan Bintu akan ko zata dawo gida ne tunda ba ita daya bane yanzu kuma tana shan wahala sosai, Baffah yace to muji ta bakin ta, haka kuwa akayi suka saka Bintu agaba da magana nan akan ko zata koma gidane dan ta huta saboda cikin jikin ta, ai kuwa Bintu ta fashe musu da kuka mai cin rai tana cewa ita fa abarta tayi jinyar mijin ta babu wani abunda zai sa arabata da mijin ta jin hakan ne yasa Kaka da Baffah suka barta suka kuma saka mata albarka,
A hausa sukace dare ma hutun bawa amma kuma ban da kaka dan yanzu zaune yake yana tunanin maganin da baiyiwa Khalil ba tunini ya tsuguba ciki amma kuma har yanzu shuru babu wani abunda yasamu, tashi yayi yayi sallah bayan ya idar kuma ya fara zubo addu'a na samun lapiyawa wa Khalil yashafa ya kwanta,
Cikin barcin kaka yayi mafarkin khalil yasamu lapiya sanadiyar wani ganyen bishiya afirgice kaka ya tashi duk zufa ta wanke masa fuskan sa zama yayi yana tunan mafarkin sa tabbas yasan wannan bishiyar amma kuma zuwa gun ta akwai hatsari sosai dan haka washigari da sa ssafe ya kira Alili da kuma Bintu bayan gabaki dayan su sun zauna yafara zaiyana musu duk mafarki n da yayi jiya da dare shuru yayi bayan yagama fada musu, Alili yace Kaka muna jin ka kuma kayi shuru Kaka ya gyra zaman sa kana ya dan numfasa ya daura dacewa wannan bishiyar akwai hatsari zuwa gunta Alili yace wata irin matsa kuma Kaka, kaka ya numfasa kana ya daura idanuwan sa akan Alili yace idan bazaka manta ba lokacin da zaku dauko bulala na fada muku akwai hatsari sosai a cikin wannan dajin har nake fada muku hanya uku ne daya wannan hanyar zallan mayu ne masu cin naman mutani, dayan hanyan kuma sai mace ce kawai zata iya bi to wannan bishiyar a cikin wannan hanyar take kuma kaga babu wata mace da zata iya bi, Bintu datake hawayen farin ciki tace kaka ni fah mai yasa bazan jeba bayan kuma mijina ne bashi da lapiya, Kaka ya dube ta yace Bintu bazaki iyaba saboda cikin da yake jikin ki kuma wannan dajin idan anshiga babu wagen baya duk wanda yashiga wannan hanyar tofa tabbas bazai waga bayan saba sabda mutuwa akeyi duk wanda ya waiga bayan sa dan haka ke bazakije ba,
Fashewa da kuka Bintu tayi tana roko Kaka akan yabar ta taje dan babu wanda zai iya zuwa idan ba itaba dan haka dan Allah Kaka barni sosai Kaka yaji tausayin ta ya kuma numfasawa yace ni bazan ce komai ba sai naji tabakin mahaifin ki dan haka anjima zanje nasame sa dan gurin akwai hatsari sosai, da to Bintu ta amsa masa dan tasan Baffahn ta zai bar ta
Kaka yace yasamu da Baffah da magana nan bayan sun gama gaisawa sai yasanar masa abunda yakawo sa kuma ya fada masa duk yadda sukayi daBintu bayan Baffah yagama sauraran sa sai ya numfasa kana yace ai nikam babu wata damuwa Allah yasa tafiyar ta yazamu silar warakan sa, Amin kaka yace kuma yaji dadin abunda Kaka ya fada masa bayan sun gama tattaunawa kuma suka yi sallama kai tsaye gida ya nufa yasanarwa Bintu duk abunda suka tattauna dan haka Bintu ta haushirin tafiya dan nimawa sahibin ta lapya.........
Bintu tashirya tsaf dan zuwa wannan dajin dan nimowa mijin ta magani Kaka Alili sun mata fatan alkhairi da fatan nasara, Bintu nufar hanya tayi ita dayan ta ga ciki a jikin ta tana tafiya tana addu'a cikin zuciyar ta,
Har Allah ya iso da ita lapiya hanyar da Kaka ya fada mata shi tayi tafiya take babu waye-waye kuma dama kaka ya fada mata bishiyar ita daya ce atskar dajin gabaki daya Bintu a tsorace take duk addu'an da yazo bakin ta shi takeyi a gida ma su kaka da Baffah sai addu'a suke matana masha Allahu Bintu tayi nasarar samun ganyan bishiyar kuma ta ciro sa, ta nufo gida kuma tadawo gida lpya tana zuwa kaka ya daddaka maganin yasaka cikin tukunya ya daura akan wuta ya dahu sosai ya hada masa ruwan wanka akayi masa wanka kuma akabashi yasa suka gyra masa kwanciya suna jiran ko Allah zai sa adace,
Har kusan goma na dare Khalil bai farka ba haka Kaka da Alili sukayi sallamawa Bintu suka tafi É—aki dan dare yayi sosai Bintu bar ci ne ya dauke ta kusan asuba Khalil ya fara bude idanuwan sa yana kara kallon cikin É—akin Mimi yake furtawa a kasan makoshin sa kina ina kizo kimun magana ko zanji sanyi cikin zuciya ta, Mimi kinsan ina son ki ina son ki,kamar amafar ki Bintu taji muryan sahibin ta da saurin ta ta je gare sa tafara masa magana
"Sadauki katashi? Mimi kitai maka mun abunda Khalil kawai yake fada Bintu fita tayi a É—akin ta nufi É—akin da su kaka suke ta sanar musu cewa Khalil fa ya farka ai kuwa da saurin su suka nufi É—akin samun sa sukayi a zaune ya mike kaffamun sa, yana ganin su Kaka ya mika hanun nuwan sa wakaka alaman yazau gare sa, dasauri Kaka yashe kare sa ya kwantar da kan Khalil a kirjin sa magana Kaka yafara masa"ya jikin ka Allah yabaka lapiya,
Khalil yadago fuskan sa daga kwancen da yake ya dauka akan Kaka yace "Kaka mai yasame ni" Kaka yace rashin lapiya kayi shine kajima akwance amma yanzu komai ya wuce tunda kasamu lapiya sosai Khalil yasake wantar da kansa akan Kaka yace Kaka ina Mimi,
Bintu da hawaye ya cika idanuwan ta tazo wajan sa tace gani gani Sadauki gabaki dayan su suka kwanta akafadar Kaka rayuwa ta musu dadi kuma sunkara jinjinawa Bintu.
.......Sosai kwanaki suke shudewa yayin da wata shakuwa tasake shiga tsakin ma aura ta biyu Khalil da Bintu yayin da cikin Bintu yanzu yana da wata shida aduniya, sosai Khalil yake kula da Bintun sa komai tare sukeyi
Bushar sosai yashiga tashin hankali da yasamu labarin Khalil yasamu lapiya ransa sosai yaɓaci dan haka yasake sabon shiri akan Khalil
Yau garin da zafi aka tashi Khalil ya dubi Bintu ya fara mata magana cikin sanyin jiki dan yau haka kawai yake jin sa wani iri kallon ta yayi yace zan fita Mimi amma zan dawo da wuri kuma ki kulamun da kanki gabaki daya yau jikina wani iri yake mun bana jin dadin jikina dan Alili ya matsamun dole na fito ne da bazan fito ba amma ina zuwa ina gama abunda zanyi zan dawo, Bintu ta ce babu komai Allah ya tsare mun kai ina son ka mijina sosai tamasa addu'a shikuma ya fita,
Khalil yana cikin tafiya yaji ansha gaban sa tsayawa yayi yana kallon wanda suka shagaban sa har Khalil ya bude baki zaiyi magana kawai yaga Bushar a gaban sa, Bushar ya kalle sa ya sake kallon sa bai ce masa komai ba kuma bai furta komai ba kawai suka hau dukan sa da kota ina dukan sa suke babu gaggautawa wani katoton ice Busher ya dauka ya kwadawa Khalil a tsakiyar kansa,
Wari razanana ihuu! Khalil yayi tare da nadi agun sumama me ganin baya motsi ne yasa gabaki dayan su sukabar gun
Bintu tagama koman ta girkin ta tana jiran mijin ta amma kuma shuru babu shi babu alaman shi hakan ne yasa tafara tsoro sosai,
Alili ya jira zuwan Khalil amma ganin baizoba sai ya hada komai nashi ya nufi gida yana cikin tafiya yaga muta ne da yawa sunkewaye wani waje haka yake tazuwa har ya isa gun ya fara tura mutani har yasamu ya kutsa kansa cikin gun idanuwan sa da gangan jikin sa ne sukashiga cikin rudani gani abunda suke gani kamar Garkuwa zuciyar sa bata gama yanke hukunci ba kawai ya tsinka muryan wani daga cikin mutanin yana cewa yauwa ga Alili nan Alili zubawa Khalil idanuwa yayi kamar babu gobe tabbas shine amma kuma waye ya masa duka har haka? kafadun sa wani aciki yataba yace yakamata mukai sa wajan Kakan ka dan zai iya rasa rayuwan sa,
A zahirin gaskiya Alili suke gani amma kuma gangan jikin sa ne kawai a gun zuciyar sa ta jima da daina aiki, ganin Alili yatsaya ne yasa suka dauki Khalil suka nufi gun Kaka dashi wani bawan Allah ne a ciki ya kama hanun Alili suka bi bayan mutani da suka dauki Khalil din
Kaka yana zaune a kofar gida sai yaka mutani sunyi kan sa a tunanin Kaka wani bashi da lapiya aka kawo masa shi dan haka ya meke ya shiga cikin gida ya bude É—akin dake maganiwa mutani aka shigar dashi bayan sun kwantar da Khalil ne Kaka ya fara ko karin masa magani kawai idanuwan sa ya sauka akan Khalil tsayawa yayi cak yafara tunani amma kuma sai yaga tunani babu wani abunda zai masa kawai sai yafara addu'a yana kuma masa abunda yakamata tabbas wannan mutumin yana gani jarabawa saida kaka yama sa duk abunda yakamata bayan gabaki daya mutanin sunwatse kawai sai wannan mutumin da ya kama hanun Alili gabaki daya abunda yafaru ya fadawa Kaka suma sun gan sane kawai akwance babu numfashi ajikin sa, sosai Kaka ya masa godiya shi kuma ya musu sallama ya tafi abun sa
Kaka kama hanun Alili yayi ya fara masa nasiha sosai kuma nasihar tashiga jikin sa, haka ya umar ce sa akan yaje yasanarwa Bintu kuma suzo tare bayan Alili yazo wajan Bintu sai da yafara mata nasiha da tunatar da ita akan duk wani abun da yasa mu bawan sa tabbas MUKADDARI NE DAGA ALLAH yamata nasiha sosai kafin yafaÉ—a mata abunda yafaru da Khalil abun mamaki Bintu cewa tayi Allahu yabashi lapiya haka tafi Alili
Rayuwa kenan yau Khalil watan sa guda bai san yadda kan sa yake ba sosai cikin Bintu yayi girma sosai kuma hakan bai hanata kula da mijin taba
Yau garin antashi da wani tashin hankali na mayu masu cinye naman mutani wanda suka shiga kauyen kunkar kusa da kauyen guma kuma gabaki daya sun gama da kauyen Kunkar sun tunkari kauyen Guma, yau tun safe Kaka yatafi daji dan nimowa Khalil magani Alili kuma ya É—an fita kauye ya har gitse dan mayu nan sun shigo kauyen Guma sun fara daga farkon garin
Dai-dai lokacin da Khalil ya fara bude idanuwan sa a hankali ware idanuwan sa yayi gabaki É—aya a cikin É—akin zubawa É—akin idanuwan sa yayi yana kallon gun, bude bakin sa yayi yana furta MIMI MIMI MIMI kar ki mutu kibar ni a'a dan Allah kubar ta kar kuka she ta tashi yayi a firgice dai-dai lokacin kuma Bintu tashigo É—akin da sauri tazo waja sa ta kama hannun sa tana masa magana "SADAUKI katashi? zuba mata idanuwan sa yayi yana kallon ta yana magana cikin zuciyar sa wannan kuma daga inaa haka sake kama hannun sa tayi tana kai hanun ta akan cikin ta tana cewa kaji yaron mu shima yana murna katashi dama kullum sai yayi kukan rashin ka,
Wacece ke? nan ina ne ? mai nakeyi anan? gaban ƙirjin tane yabuga tashi ga cikin ruɗani amma hakan bai sa tayi shuru ba tace "matar kace Mimin ka kaga har da cikin ka ajiki na, mekewa Khalil yayi yace mata na ɗaya ce a duniya ita ce INJILA MIMINA bayan ita babu kowa banga je Bintu yayi ya fita a ɗakin ai da gudun ta Bintu tabi bayan sa ta rugume sa ta baya tana fadin dan Allah kar kabar ni wallahi ni matar kace kuma sahibar kace, bai bari ta karisa magana nan ba yawani ture ta ajikin sa yasa kafa yataka yatsan ta na hanu yana murzawa yana magana WALLAHI WALLAHI WALLAHI ko a hanya kika ganni kikace ni mijin ki ne kuma har da ciki jikin ki kuma wai nawa sai na kashe ki mtss yaja doguwar tsaki yabar gun baki daya, yabar Bintu tana furta "kar katafi kabar ni wallahi ina son ka, tana kuka sosai tana sumbatu,
A haka Alili yazo ya same ta afirgice yashigo gidan yana haki yana furta Bintu kitashi mu gudu mayu masu cin naman mutani suna daf dashi gowa gidan nan kitashi ni zanyi kokarin na dauki Garkuwa mugudu, Bintu tace yatashi kuma yatafi, Alili yace wani irin yatashi kuma ya tafi ina yaje? gabaki daya abunda yafaru Bintu ta sanar masa, Alili zama yayi a gun zaman dishin ya fashe da kuka ya manta da mayu nan gabaki dayan su kuka suke,
MAYYUN nan masu cin naman mutani ne suka shiga gidan ganin Bintu da Alili a wani hali yasa su suka kauce da dariya sukaye sukace mata da miji kukan baza mukashe kuba sai matar ka tahaifu zamu tsaka yaron agaban ku gafin mukashe ku............
_________________________________________
ALHMDULLAH
ALHMDULLAH
ALHMDULLLAH
ANAN NAKAWO KARSHEN MUKADDARI NE DAGA ALLAH TAKUN FARKO SAI KUBIYON A TAKU NA BIYU
TABBAS YANZU ZA'A SHIGA SARƘAƘIYA DA KUMA RUDIN KAUNA
ZAKUJI YADDA KHALIL YA NUFA DA KUMA YADDA BINTU DA ALILI ZASUYI DA MAYYUN NAN DA KUMA WAYE INJILA A GUN KHALIL KUDAI KUBIYO NI DAN JIN LABARIN WANNAN YARINYAR DA TABUGAWA KHALIL MOTO
SAI KUN BIYONI ZAKUJI
BY
SUHAIMA ABUBAKAR SHEHU +2349168176464