Complete Hausa Novels

Zuciya Da Kuna Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Zuciya Da Kuna Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 1 of 10

ZUCIYA DA ƘUNA..

By Billy S. Fari & Nana Hadiza
@nanadiso10 | Arewabook

PAGE 1

Daren Paris ta kasance cikin sanyi mai kaifi a ranar Litinin, iska mai ɗan ƙarfi tana kadawa a kan babban titin Boulevard Périphérique, ɗaya daga cikin hanyoyin da suka fi cunkoso a birnin. Sararin sama ya ɗauki launin toka, gajimare sun lullube hasken rana, yayin da motoci ke tafiya cikin sauri suna ketare juna kamar yadda aka saba a rayuwar birni mai cike da hanzari.

Sai dai a wannan safiyar…komai ya sauya. Wani mummunan hatsari ya afku a tsakiyar titin motoci uku sun yi mummunan karo da juna cikin wani irin tashin hankali da ya sa mutane suka tsaya cak. Ƙarar birki, fashewar gilashi, da ihu sun gauraya a lokaci guda, lamarin da ya jefa duk wanda ke wurin cikin firgici. Cikin ‘yan daƙiƙu kaɗan, mutane suka fara taruwa.Wasu suna kiran taimako, wasu suna ƙoƙarin ceto waɗanda ke cikin motocin. Jini ya ɓata titin, hayaniya ta mamaye wurin, yayin da ƙarar siren na motar asibiti ke ƙara kusantowa daga nesa.Ba tare da ɓata lokaci ba, aka fitar da waɗanda hatsarin ya rutsa da su, aka shimfiɗa su cikin gaggawa, aka ɗauke su zuwa Hôpital Européen Georges-Pompidou, ɗaya daga cikin manyan asibitocin Paris.

A can ne aka fara gwagwarmayar ceton rayukansu.Likitoci da masu jinya suka shiga aikin gaggawa, kowanne yana ƙoƙarin yin abin da zai iya.Amma…
ƙaddara ta riga ta zartar da hukunci.
Bayan ɗan lokaci, wata likita ta fito tana kallon mutanen da ke jira. Cikin nutsuwa amma da nauyi a muryarta ta sanar “Sun rasu…” Kalmar ta sauka kamar dutse.Duka Babu wanda ya tsira…sai jariri guda ɗaya.Shi ma yana cikin rauni hannunsa ya samu mummunan rauni, amma yana numfashi. A take aka fara duba wayoyinsu, ana neman wani makusanci…wanda za a sanar.

A ɗaya ɓangaren birnin Paris, a unguwar Neuilly-sur-Seine, cikin wani katafaren gida mai cike da alfarma da nutsuwa, shiru ya mamaye ɗakin kwana mai faɗi.Haske mai laushi daga bedside lamp yana ba ɗakin wani irin dumi mai kwanciyar hankali. A kan gadon alfarma…Haroon Kareem na kwance cikin nutsuwa, bacci mai nauyi ya rufe shi, kamar wanda babu damuwa a rayuwarsa. A gefen gadon, wayarsa na ci gaba da ringing…sau ɗaya… sau biyu… sau uku…har ta zarce sau ashirin.

A kusa da shi, Fatima na zaune a kan sallayarta. Ta kammala sallah, amma idanunta sun kasa rabuwa da wayar da ke ta haskawa a cikin duhun ɗakin.
A hankali ta miƙe.Ta ƙaraso kusa da gadon, ta taɓa shi a hankali.“Haroon… your phone has been ringing since.”
Ya motsa a hankali, yana buɗe idanunsa. Cikin kasala ya kai hannu ya ɗauki glass ɗinsa daga gefen gadon, ya saka. Murmushi mai sauƙi ya bayyana a fuskarsa.
“Subhanallah… Fatima, you’re still awake?”
Ta ɗan yi murmushi, amma cikin murmushin akwai ɓoyayyen ciwo. Ta share ƙananan hawaye da suka taru a gefen idanunta. Haroon ya lura.
Cikin tausayi ya shafa kanta. “Fatima… ki daina damun kanki. Haihuwa nufin Allah ne. Mun yi addu’a, mun yi iya ƙoƙarinmu… idan shiru ya zo, to hakan ne mafi alheri a gare mu.” Ya ɗan tsaya.
“Please…” Kukanta ya ɗan ƙaru.
“Toh… na daina, Habibi…”

Ya ɗauki wayarsa. Idanunsa suka sauka a kan screen Umar. Kiran ya shiga sau da dama.Cikin firgici ya miƙe tsaye.
Ba tare da ɓata lokaci ba ya kira.
A ɗaya ɓangaren aka ɗaga. “Sir… muna bukatarka anan asibiti.” Kalmar ta tsaya a kunnensa. Bai san lokacin da ya ɗauki mukullin mota ba. Fatima ma ta biyo shi a firgice. Suka fito daga gidan cikin gaggawa. “Security..” Da sauri aka kawo masa key. Ya shiga mota.Ba tare da bata lokaci ba suka fice cikin tashin hankali, motar tana yanke titunan Paris cikin gudu. Da suka isa asibitin…cikin ya cika da mutane. Hayaniya,Kuka,Firgici.

Haroon bai san lokacin da ƙafafunsa suka kasa ɗaukar shi ba.Hawaye suka zubo. “Umar…?” Aka nuna masa. A can yake. Shi da matarsa…a kwance, Ba numfashi, Ba motsi. Duniya ta tsaya masa.Kuka ya fashe da shi kamar yaro.
Fatima ma ta kasa jurewa ta rufe baki tana kuka. “Muyi haƙuri, sir…”muryar likita ta faɗo.v“Akwai jaririnsu… bai rasu ba.” Suka nuna musu ɗaki. Jaririn yana kwance… yana kuka.Hannunsa ɗaya ya ji rauni. Fatima ta yi saurin ƙarasa, ta ɗauke shi cikin hannunta.
Kukanta ya ƙaru. Ta kalli jaririn… sai zuciyarta ta karye. Haroon ya tsaya yana kallon su ya rasa abin yi. A rana ɗaya…ya rasa ɗan uwansa. ya rasa matar ɗan uwansa.ya rage sai jariri…
wanda bai san komai ba game da duniya.

Asibitin Hôpital Européen Georges-Pompidou ya cika da wani irin shiru mai nauyi, irin shiru da ke ɗauke da kuka da ba a furta ba. A cikin corridor mai tsawo, hasken farin wuta yana haskakawa a bango, yayin da ƙarar na’urorin asibiti ke fita a hankali kamar suna bada labarin wani abu da ya riga ya faru. Haroon Kareem ya tsaya a wuri guda kamar wanda aka dasa, idanunsa sun yi ja, hawaye suna sauka ba tare da izini ba. Fatima na tsaye kusa da shi, tana riƙe da jaririn da ya rage ƙaramar rayuwa da ta tsira daga mutuwar da ta shafe komai. Jaririn na kuka a hankali, muryarsa tana raɗaɗi kamar yana jin abin da ya faru duk da cewa bai fahimta ba. Hannunsa ɗaya an ɗaure shi da bandeji, jinin da ya ɗan fito ya bushe a gefen yatsunsa. Fatima ta rungume shi sosai, jikinta yana rawa. “Ya Allah…” ta furta a hankali, “why this child?” Haroon ya rufe idanunsa na ɗan lokaci, numfashinsa ya yi nauyi. Likita ya ƙaraso kusa da su, ya yi musu magana cikin nutsuwa, “We are sorry for your loss, sir… we tried everything.” Kalmar we tried ta tsaya a zuciyar Haroon kamar wani abu mai sosa rai. Bai amsa ba. Ya ɗan juya, ya ɗauki wayarsa, hannunsa na rawa. Ya fara danna lambobi daya bayan daya. “Hello… Aslam? Please… come to the hospital… something happened.” Bai jira amsa ba ya katse. Wani number ya kira. “Uncle Musa… we lost them…” kalmarsa ta karye. Daga can aka ji ihu. Wani kiran ya shiga. Wani kuma. A cikin mintuna kaɗan, labari ya fara yawo kamar wutar daji. Family, friends, acquaintances… kowa ya fara jin abin da ya faru. A cikin awa ɗaya, asibitin ya fara cika da mutane. Wasu suna kuka, wasu suna girgiza kai, wasu suna tsaye cikin shock. “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…” kalmar ta mamaye wurin. Fatima ta zauna a kan kujera tana riƙe da jaririn kamar ba za ta sake shi ba har abada. Wata mata ta zo ta ce, “Ki bani shi ki huta…” Amma ta girgiza kai da sauri. “No… I can’t… please…” muryarta ta cika da tsoro. Ta ƙara rungume jaririn, yana kuka yana motsi, kamar yana neman wani abu da ya ɓace. Haroon ya kalli wannan scene, zuciyarsa ta ƙara karyewa. Wannan jariri… ɗan uwansa ne. Jinin su ne. Amma yanzu… shi ne kawai ya rage. Bayan wasu lokuta, aka shirya fitar da gawar. An rufe su cikin farin zanen asibiti. A hankali aka ɗauke su, aka saka su cikin motar gawa. Mutane suka bi motar cikin nutsuwa, wasu suna addu’a, wasu suna kuka. An kai gawar gida a Neuilly-sur-Seine, inda gidan ya riga ya cika da mutane. Maza a waje, mata a ciki. Kuka ya mamaye gidan. “Umar… Umar…” wata murya ta riƙa kira. Fatima ta shigo da jaririn a hannunta, idanunta sun kumbura. Ta zauna a gefe, ba ta shiga hayaniyar kuka ba, amma zuciyarta na fashewa. A ciki, aka fara shirya wankan gawa. Maza suka ɗauki Umar, suka shiga da shi. Ruwa mai ɗumi aka tanada, aka wanke shi cikin tsari na Musulunci, aka sanya masa turare, aka lulluɓe shi da farin likkafani. A ɗaya ɓangaren, mata suka yi wa matarsa wanka, suna kuka a hankali, suna furta kalmomin addu’a. “Allah ya jikanki…” “Allah ya sa aljanna ce makomarki…” Bayan komai ya kammala, aka fito da gawar. Aka shimfiɗa su. Mutane suka tsaya suna kallonsu ba su motsi, ba su magana. Duniya ta ƙare a gare su. Lokaci ya yi na jana’iza. Aka fita zuwa masallaci. A waje, sanyi yana kadawa, iska na busawa, amma babu wanda ya damu. Kowa yana cikin wani yanayi dabam. Aka jera su. Aka yi sallar jana’iza cikin nutsuwa. “Allahu Akbar…” muryar liman ta ɗaga. Mutane suka bi. Kowa yana addu’a a zuciyarsa. Bayan sallah, aka nufi makabarta. Aka haƙa kabari. Aka sauke su a hankali. Aka rufe. Ƙasa ta rufe komai.

A gida, Fatima har yanzu tana riƙe da jaririn. Babu wanda ya iya karɓar shi daga hannunta. “Please… leave him with me…” ta faɗa a hankali. Zeynab ta zo kusa da ita. “Sis… ki huta mana…” Amma fatima ta girgiza kai. “No… he needs me…” ta kalli jaririn. “He has no one now…” kalmarta ta fito da rauni. Jaririn ya yi ƙara kaɗan, yana motsa hannunsa da aka ɗaure. Fatima ta ɗan sumbace goshinsa. “It’s okay… I’m here…”

_Hmmm wasu labarai ba sa farawa da farin ciki. Suna farawa ne da rauni... ku biyo mu muje

ZK2026
08081005693
07040402435.
ZUCIYA
          DA ƘUNA

By Billy S. Fari & Nana Hadiza
@nanadiso10 | Arewabook

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.