Zuciya Da Kuna Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuciya Da Kuna Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 5 of 10
PAGE 5.
Cikin wannan lokaci ne gidan Haroon Kareem ya sauya gaba ɗaya zuwa wani sabon yanayi na farin ciki da nasara,kasuwancinsa ya bunƙasa sosai, sunansa ya shiga cikin jerin manyan attajiran da ake girmamawa a birnin, kamfanoninsa suna aiki a fannoni daban-daban real estate, importation, luxury investments duk inda aka ambaci Haroon Kareem, ana magana ne da girmamawa, ana kallonsa a matsayin mutum mai hankali da hangen nesa, amma duk da wannan arziki da daukaka, akwai abu guda ɗaya da ya fi komai muhimmanci a gare shi iyalinsa. Rayyan… wanda aka haifa cikin hawaye, ya girma cikin soyayya.
Tun yana ƙarami, Fatima bata taɓa barinsa ya ji wani irin rashi ba, duk abin da yake buƙata tana nan, amma ba kaya ba ne kawai, ba abinci ba ne kawai soyayya ce, kulawa ce, da wani irin attachment da ya wuce misali, duk wanda ya ga yadda take mu’amala da shi zai rantse cewa ita ce ta haife shi, tana kiran sa “My Rayyan…” yana amsa da “Mom…” cikin wani irin laushi da ke sa zuciya ta narke.
Da safe, kafin ya tafi makaranta, Fatima ce ke shirya masa komai, uniform dinsa mai kyau, shoes dinsa masu tsabta, tana gyara masa gashi a hankali tana cewa “Stand still… you’re always moving” shi kuma yana dariya yana rungumeta “Mom you worry too much…” Haroon na tsaye a gefe yana kallon su da murmushi, yana jin wani irin cikar zuciya.
Rayyan ya zama yaro mai hankali sosai, a makaranta yana daga cikin top students, teachers suna yabonsa, abokai suna girmama shi, yana da nutsuwa amma yana da confidence, yana magana cikin ladabi amma akwai wani irin ƙarfi a cikinsa da ke fitowa lokaci zuwa lokaci, kamar yana ɗauke da wani abu daga baya da bai sani ba.
Ranar wani school event, aka kira iyaye domin ganin yadda yara ke gabatar da ayyukansu, Fatima da Haroon suka halarta, suna zaune a cikin hall mai kyau, yara suna gabatarwa ɗaya bayan ɗaya, sai aka kira suna “Rayyan Haroon” ya tashi cikin nutsuwa, ya hau stage, ya fara magana cikin English mai kyau, confidence dinsa ya fito fili, kowa ya kalleshi, Fatima ta dafe zuciyarta tana murmushi da hawaye a lokaci guda, “That’s my son…” ta faɗa a hankali, Haroon ya kalleta ya ɗan riƙe hannunta “He’s doing great…”
Bayan an gama, mutane da yawa sun zo suna gaishe su, suna yaba Rayyan, suna cewa “You raised him well” Fatima ta ji zuciyarta ta cika da alfahari, ba ta san lokacin da ta rungume shi ta sumbace shi ba “I’m so proud of you…” shi kuma ya ce “I did it for you Mom…” kalmar ta shiga zuciyarta sosai.
A gida kuwa, Rayyan ba ya rabuwa da Haroon, suna yawan fita tare sometimes business meetings, sometimes just drive around the city, Haroon yana koya masa abubuwa, yana nuna masa yadda rayuwa take, yadda ake yanke hukunci, yadda ake zama mutum mai daraja, Rayyan yana sauraro da nutsuwa, yana ɗaukar komai a hankali. Wata rana suna zaune a office dinsa mai girma, gilashi a ko’ina, ana kallon Paris daga sama, Haroon ya kalli Rayyan yana cewa “One day… all this will be yours” Rayyan ya kalle shi cikin mamaki “Really?” ya ɗaga masa kai “Yes… but you have to earn it” ya ɗan murmusa “I will” Amma a bayan wannan farin ciki, akwai wasu idanu da ke kallon su da wani irin yanayi, Zeynab ba ta taɓa mantawa da abin da ya faru ba, a duk lokacin da ta ga Rayyan tare da Fatima, zuciyarta na cika da wani irin abu, wani abu da ya haɗa hassada da ƙiyayya, tana jin kamar an ƙwace mata wani abu da ya kamata nata ne, sauran family ma ba duka ne suka amince da wannan haɗin ba, wasu suna yin gulma a ɓoye.
Amma duk wannan bai shafi Rayyan ba.
Shi rayuwarsa guda biyu ce kawai Mom da Dad A wurinsa, Fatima ita ce komai, ita ce duniya, ita ce zuciyarsa, yana son ta ba tare da shakka ba, yana kare ta kamar yadda yaro zai iya kare uwa.
A daren wani rana mai sanyi, bayan Rayyan ya kwanta, Haroon da Fatima suna zaune a balcony, suna kallon hasken Paris, iska mai laushi na kadawa, Fatima ta jingina da shi a hankali “Look at him… he’s grown so fast…” Haroon ya ɗan rungumeta “Because you gave him everything…” ta ɗan yi murmushi “No… we did” Ya ɗan jawo ta kusa da shi “I couldn’t have done this without you…” ta kalli idanunsa “And I couldn’t live without him…” ya ɗan murmusa “Or me?” ta ɗan yi dariya “You too…”Ya sumbaci goshinta a hankali.
Daren Paris ya sauka cikin sanyi mai kaifi, iska na kadawa a hankali a waje, bishiyoyi na rawa kamar suna faɗin wani sirri, a cikin katafaren gidan Haroon Kareem kuwa, shiru ne mai nauyi ya mamaye komai, fitilun corridor suna haskakawa da laushi, amma a cikin ɗakin Rayyan… babu nutsuwa, yana kwance a kan makeken gadonsa mai faɗi, duvet mai laushi ya rufe rabin jikinsa, amma jikinsa ba ya jin daɗin kwanciyar, yana juyi daga gefe zuwa gefe, numfashinsa na fita da sauri, hannunsa na riƙe cikinsa kamar wani abu na cinsa daga ciki, wannan ba sabon abu bane a gare shi, sau da yawa yana jin irin wannan ciwon, amma ba su taɓa gano dalili ba, doctors sun yi bincike, tests, scans… komai normal, amma ciwon yana dawowa lokaci zuwa lokaci, wani lokacin ma har yana faduwa kamar matacce, hakan yasa ya saba ɓoye wa Fatima, saboda ya san idan ta sani… zata shiga wani irin hali, hali na tashin hankali da kuka da tausayi wanda yake karya masa zuciya, shiyasa yau ma bai gaya mata ba tun da ya dawo daga Islamic school dinsu, makarantar da ta koya masa abubuwa da dama addini, nutsuwa, da kuma wani sabon yanayi na jikinsa da yake fara fahimta a hankali, girma na zuwa masa, amma tare da shi akwai wannan ciwo da ba a san asalinsa ba. Yau kuwa… ya yi tsanani.Jikinsa ya fara rawa. Sanyi ya ratsa shi. Ya miƙe a hankali daga kan gadon, ƙafafunsa suna rawa, ya sauko ƙasa, ya durƙusa yana riƙe cikinsa da ƙarfi, “Ahh…” ya furta a hankali, amma muryar ta fito da rauni, jikinsa ya fara kakkarwa, idonsa ya ɗan rufe, numfashinsa ya rikice, kamar zai faɗi. A daidai wannan lokacin, ƙofar ɗakin ta buɗe. Fatima ta shigo da plate a hannunta abinci da ta kawo masa kamar yadda take yi kullum. “My Rayyan…” ta fara magana da murmushi, “sweetheart… it’s been two good hours, baka zo gurina ba… so kake zuciyata ta tsaya?” ta ƙarasa tana ɗan dariya.
Amma dariyar ta mutu a leɓenta. Plate ɗin ya faɗi daga hannunta. Ƙarar yaɗuwar abinci a ƙasa ta cika ɗakin. Idonta ya sauka kansa.
Rayyan na ƙasa. Jikinsa na rawa. Yana riƙe cikinsa kamar zai mutu. “Rayyan!!!”
Ta yi ihu da ƙarfi. Ta garzaya gare shi, ta rungume shi, jikinsa ya yi sanyi, hannunsa na kakkarwa, numfashinsa ya rikice. “My baby… what is this… what is this???” ta riƙa faɗa cikin firgici, hawaye sun zubo ba tare da izini ba. Ta ɗaga kai cikin tashin hankali, “JOHN!!!” ta ƙwala kira. Da sauri ɗan aikin gidan ya shigo, “Ma’am!” “Call the driver! NOW!!”
“Ma’am, I’m here, I’ll drive!” Ba tare da ɓata lokaci ba suka ɗauke Rayyan kamar wanda ya sume, jikinsa ya yi laushi a hannunta, ta rungume shi da ƙarfi kamar ba za ta sake shi ba har abada. Kuka take.bKuka mai karya zuciya. “Rayyan please… don’t leave me… please…” ta riƙa maimaitawa. Suka fita daga gidan cikin gaggawa, sanyi na bugun su amma babu wanda ya damu, motar ta tashi da gudu cikin daren Paris, fitilun titi suna wucewa a gefensu, amma a cikin motar… sai kuka da addu’a. “Ya Allah ka taimaka… please Allah…” Fatima ke maimaitawa.
Haroon baya ƙasar. Wannan ne ya fi bata tsoro. Ta ɗauki waya da hannu mai rawa, ta kira Dada. “Dada… Rayyan… he’s not well…” kuka ya katse mata magana. Ta kira Didi.
Ta kira Aslam. John ma ya riga ya sanar da shi. Aslam ne ya iso asibitin kafin su.
Da suka isa emergency, ba tare da ɓata lokaci ba aka karɓe su, aka ɗauke Rayyan zuwa cikin gaggawa, nurses suna zagaye da shi, likitoci suna ba da umarni. “BP check” “Get the IV ready.” “Monitor him” Fatima na tsaye a waje tana kuka kamar ranta zai fita, jikinta na rawa, zuciyarta na bugawa da ƙarfi.
“Aslam…” ta kira da muryar da ta cika da tsoro.“Please… do something…” Aslam ya riƙe hannunta, “Calm down… he’ll be fine…”
Amma shi ma zuciyarsa na bugawa. Bai san me ke faruwa ba. A cikin wannan tashin hankali… Fatima ta ji duniya na juyawa.
Idonta ya duhu. Ta faɗi. “Fatima …” Aslam ya kama ta kafin ta bugi ƙasa. Aka ɗauke ta cikin gaggawa. A wani ɓangaren… Zeynab da Meme suna zaune a gidansu. Labari ya iso musu. Amma ba tausayi bane a fuskarsu.
Sai wani irin yanayi. “Hmmm…” Zeynab ta ce.
“Daman ya mutu.” Meme ta ɗaga kai.
“Kai da naji dadi…”Saboda duk wannan arzikin da Haroon ke ciki…Rayyan ne gadonsa. Rayyan ne komai. Kuma hakan ba ya musu daɗi.
A asibiti… Fatima na kan gado, an yi mata allurar bacci. Fuskarta ta nuna wahala.
Rayyan kuma… ya fara dawowa.
Numfashinsa ya daidaita. An haɗa masa drip.
An yi masa allurai. Yana kwance a hankali.
Aslam na tsaye kusa da likita.
“What happened to him?” ya tambaya.
Likitan ya ɗan ɗauki lokaci kafin ya amsa. “We ran all the tests…” ya ɗan girgiza kai. “Everything is normal.” Aslam ya ɗan rikice. “Then what is causing this?” Likitan ya ce a hankali, “It might be something his body reacts to… maybe food… maybe internal sensitivity… we still need to monitor him.” Kalmar ba ta ba su amsa ba. Sai ƙarin damuwa. A cikin ɗakin… Dada na zaune. Kowa cikin shiru. Rayyan ya motsa kaɗan. Ya buɗe idanunsa a hankali. “Mom…”
ya kira da muryar da ta yi rauni. “Mom… where are you…”Aslam ya matsa kusa da shi.
“Hey champ… Mom is fine…” ya yi murmushi.
“Don’t worry.”Amma Rayyan ya girgiza kai.
“I want my Mom…” kamar ƙaramin yaro.
Aslam ya kalli Dada. Ya san idan suka gaya masa tana kwance… zai sake shiga tashin hankali. “She’ll be back…” ya faɗa. “Just rest.”
Sa’o’i suka wuce. A hankali…Fatima ta farka.
Abu na farko da ta faɗa “Rayyan…” Ta miƙe da sauri, jikinta ba ƙarfi. “Aslam… where is he???”v“Relax… he’s okay…” Bai gama ba… ta riga ta sauko daga gadon.Ta nufi ɗakinsa.
Da ta shiga…ta gan shi Yana kwance.Idonsa a buɗe. “Mom…” ya faɗa da murmushi mai rauni. Ta garzaya gare shi. Ta rungume shi da ƙarfi. Kuka ya kwace mata.“My baby… don’t scare me like that… please…” Ta sumbaci kansa,Hannunsa,Fuskarsa.
Shi kuma ya riƙe ta.
Daren Paris ya yi sanyi mai laushi, iska na kadawa a hankali tana motsa labulen ɗakin su, fitilun birni suna haskakawa daga nesa suna bada wani irin golden glow da ke shiga cikin ɗakin, Fatima na tsaye a gaban madubi tana cire ‘yan kayan kwalliyarta a hankali, gashinta ya sauka a bayanta cikin nutsuwa, jikinta sanye da riga mai laushi wacce ta ƙara fito da kyawunta cikin salo mai tsafta, tana kallon kanta amma zuciyarta tana wani wuri daban, tana tunanin rayuwarta, yadda komai ya sauya, yadda soyayya ta shigo rayuwarta ba tare da tsammani ba, a hankali ta ji wani zafi mai laushi a bayanta hannun Haroon ne ya zagayo ya rungumeta daga baya, jikinsa ya manne da nata, numfashinsa ya bugi wuyanta, ta lumshe idanu na ɗan lokaci kamar tana jin daɗin wannan kusancin da bata gajiya da shi, “You look beautiful…” ya faɗa a hankali cikin muryar da ke shiga zuciya, ta ɗan yi murmushi ba tare da ta juya ba, “You always say that…” ta amsa cikin laushi, ya ɗan sunkuya ya sumbaci wuyanta a hankali, ta ɗan ja numfashi, jikinta ya amsa wannan taɓawar cikin nutsuwa, “Because it’s always true…” ya ƙara faɗa yana kallon ta a cikin madubi, idanuwansa suna nuna wani irin so mai zurfi, Fatima ta juya a hankali ta fuskance shi, idanunta sun haɗu da nasa, na ɗan lokaci babu wanda ya yi magana, sai kallon juna, kallon da ke ɗauke da shekaru na fahimta, na jurewa, na ƙauna, ta ɗaga hannunta ta taɓa fuskarsa a hankali, “You’ve done so much for me…” ta faɗa da murya mai laushi, ya girgiza kai kaɗan yana murmushi, “No… we did this together…” ya riƙe hannunta ya sumbace shi a hankali, ta ji wani irin sanyi ya ratsa jikinta, ta ɗan matsa kusa da shi, “Sometimes I wonder… what I did to deserve you…” ta faɗa cikin gaskiya, ya ɗan ja ta zuwa jikinsa, “You stayed… when everything was broken… that’s more than enough,” kalmarsa ta sauka a zuciyarta, ta jingina da shi tana jin bugun zuciyarsa, ɗakin ya yi shiru sai numfashinsu kawai, ya ɗaga haɓarta a hankali ya sa ta kalle shi, “Fatima…” ya kira sunanta cikin nutsuwa, “I love you…” kalmar ta fito a sarari, ba tare da ƙoƙari ba, amma cike da gaskiya, idonta ya ɗan cika da hawaye, amma wannan karon na farin ciki ne, ta ɗan yi murmushi, “I love you more…” ta amsa, ya ɗan yi dariya kaɗan, “That’s not possible…” ta ɗan turo baki, “It is…” kafin ta ƙarasa ya sumbaci goshinta a hankali, sannan ya sauka zuwa kuncinta, sannan ya tsaya a leɓenta na ɗan lokaci ba tare da ya yi gaggawa ba, kamar yana ba ta lokaci, kamar yana tabbatar da komai yana cikin nutsuwa, daga nan ya sumbace ta cikin salo mai laushi, ba tashin hankali ba, ba gaggawa ba soyayyarsu ce kawai, mai tsafta, mai zurfi, mai cike da mutunta juna, ta riƙe shi da ƙarfi kamar tana jin tsoron rasa shi, ya ƙara rungumeta yana shafa bayanta a hankali, a waje iska na ci gaba da kadawa..
ZK2026
08081005693
07040402435.
ZUCIYA DA ƘUNA
By Billy S. Fari & Nana Hadiza
@nanadiso10 | Arewabook