Zuciya Da Kuna Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuciya Da Kuna Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 8 of 10
PAGE 8.
Misalin Ƙarfe 1:40 na dare a Paris, lokacin da gari ya ɗan yi shiru, amma zuciya ta fi yin magana saboda raguwar hayaniyar motoci da kuma surutun jama'a, Tun farkon dare da Rayyan ya kwanta har zuwa wannan lokaci bacci ya ƙaura daga idanuwansa, banda juye-juye babu abinda yake faman yi a saman katafaren gadon nasa, tun yana tunanin zuwan sauƙi daga azababben ciwon cikin da yake ji har ya fara galabaita haɗe da fidda rai saboda yadda yake tsananta masa acikin kowane sakan ɗaya, numfashi ya fara saukewa da ƙarfi saboda gangar jikinsa da zuciyarsa sun fara gajiyawa daga ƙarfin halin da yake tilasta kansa yi tare da kasa jurewa, a hankali yake kiran sunan Allah da bakinsa kaɗai ne ke motsawa ya kasa bayyana hakan a zahiri. Nishi mai ƙarfi ya shiga saukewa yana fitar da iska ta baki ko zai ji saukin raɗaɗin dake damunsa, hakan ya yi dai-dai da turo ƙofar Mom dake shigowa tana dariya Dady na biye da ita a baya, tun da yaga ta miƙe zata baro part ɗin nasa shima ya miƙe ya biyo bayanta “Indai ɗakin Rayyan zaki je to mu tafi ƙafata ƙafarki duk da nasan ya riga yayi bacci yanzu ba zaki jima ba zaki dawo, na rasa me kika ɗauki yaron nan naki da har yanzu bazaki rage yawan duba sa ba cikin dare†"Baka ji meka faɗa ba? Yarona fa kace taya zan rage basa kula bayan har yanzu shi ɗin yarona ne." “Shi yasa nake so yai aure yaje matarsa taci gaba da kula dashi ni kuma yabar mun tawa matar ta huta.†Wannan zance na Dady yai shi yaba Mom dariya wanda yai dai-dai da lokacin da suka iso ɗakin na Rayyan.
Da sauri Mom ta Æ™arasa bakin gadon Dady na rufa mata baya ganin halin da Rayyan É—in ke ciki, hankali a tashe ta zauna bakin gadon ta jawosa duka a cjikinta tana girgiza shi “Oh my God, my son! What’s happening to you? Please talk to me, what’s wrong? Why are you like this? Can you hear me? Say something, please! Rayyan." Ganin ya kasa magana numfashinsa na Æ™ara wahalar fita yasa ta kalli Dady da shima hankalinsa ya tashi ya kasa magana sai bin shi da kallo yake yi tamkar mai son gano yanayin da yake ciki "Dady...†Ta faÉ—a a É—an ruÉ—e tana sake maida kallonta ga Rayyan kamar wanda take tsoron tsayawar lumfashinsa, a hankali take furta sunansa tamkar mai koyo “Rayyan, My Rayyan!†Nan ma Rayyan ya kasa cewa komai sai riÆ™e ciki yake yana lumshe idanuwa kafin can taga ya rufe su hannunsa dake rike da cikinsa ya faÉ—i, girgiza sa tai da É—an Æ™arfi tace “Noooo…My son..Stay with me, don’t close your eyes! can you hear me? Please, open your eyes… talk to me, what’s wrong? Don’t do this to me… please!â€
Ganin haka yasa da sauri Dady ya fita yana ƙwalawa cikin securities kira suka shiga cikin gidan tare, ɗakin Rayyan ɗin suka haura Dady ya tallabosa daga jikin Mom data soma kuka suka riƙasa hankali a tashe suka fita dashi, suna fita Dady ya nufi wajen ɗaya daga cikin motocinsa, driver na ganin haka da sauri shima ya taso ya buɗe motar suka saka shi, hannu Dady ya miƙa masa ya karbi key ɗin motar, dama akwai mayafi ajikin Mom ta faɗa cikin motar itama Dady ya ja da ƙarfi suka fice daga gidan, ganin haka yasa cikin sauri securities ɗin suma suka ɗauki mota ɗaya suka bi bayansu. Daga Mom har Dady duka hankalinsu a tashe yake, yi suke suna juyowa suna kallon yanayin da ɗan nasu ke ciki tamkar wanda babu rai ajikinsa, babu abinda wannan yanayi ya tunawa Dady sai lokacin da Mom ta samu cikin Nayla yadda wani dare ya ɗauke ta rai a hannun Allah, saboda cikin ya matukar bata wahala sosai dan babu wanda ya zata ma zata rayu ko haihuwar abinda ke cikin nata cikin ƙoshin lafiya, kauda wannan tunanin yai tare da ɗan dukan steering wheel ɗin motar yana sake taka wuta, a Clinique Ambroise Paré dake kusa da Neuilly-Sur-Seine ya nufa bai tsaya nufar asibitin da suke ganin likita ba saboda gani yake yi kafin sukai komai zai iya faruwa, private hospital ce mai kyau da tsari yana zuwa yai parking a harabar wajen da gudu nurses suka fito suka ɗauki Rayyan, cikin sakonni kaɗan ɗakin da aka shiga dashi likitoci suka hau kanshi, Mom ta kasa zaune ta kasa tsaye, zagayen ƙofar ɗakin ta shiga yi tana ji tamkar ta kutsa kanta ciki ta shiga taga halin da yaronta ke ciki, Dady yasan shaƙuwa da irin soyayyar da takewa Rayyan, a hankali tana kawowa kusa dashi ya riƙo hannunta ya janyo ta zuwa jikinsa ya rungume “Calm down, I’m here with you. Everything will be okay, by God’s grace.†“bana so wani abu ya sami Yarona" “The doctors are doing their best, and we will keep praying, in Sha Allah ba abinda zai samesa." “Hopefully amma kasan bazan iya jurar wani abu ya sami yarona ba, I can't†“i know! But you are a strong mother, and I’ll stand by you Saboda haka ki kwantar da hankalinki kin ji ko?†bata iya amsa shi ba ta ɗaga masa kai kawai, ita kadai tasan me take ji a ranta, tana son Rayyan har cikin zuciyarta, batasan wane irin ciwo ne haka ke damunsa ba, ta rasa wace irin matsala ce haka, da tana da iko da tun a shekarun baya tayi masa maganinta.
A jikin wata kujera ya jata suka nufi gun ya zaunar da ita yana ci gaba da rarrashinta, bayan mintina ashirin da biyar likitan daya jagoranci dubasa ya fito tare da sauran likitoci kowane ya wuce office ɗinsa, shi kuma ya yi masu izinin dasu biyo shi a office, bayani yayi masu akan ba wata matsala ke damun ɗansu ba su kwantar da hankalinsu yanzu haka sun bashi taimakon duk daya dace ya samu yin bacci, tare suka sauke ajiyar zuciya Mom ta kalli likitan tace “Please help me, I’m really worried about my child, is there anything urgent we need to do right now?, Please doctor ka faɗa mun ko me yake damun ɗana zan iya fitar dashi ƙasar nan where he can receive the best treatment idan har kana ganin abun yafi ƙarfinku.†Murmushi doctor ɗin yai "No need for that Hajiya, Babu wata matsala dake damun yaronki idan har zaku yi masa aure, i think this is the best treatment daya kamata kufara bashi." Dady ya gyara zamansa yana kallon likitan “Likita kana ganin wannan shine maganin matsalarsa? Saboda tun years back wannan ciwon ke damunsa mun kashe kudi sosai amma abinda likitoci suka tabbatar mana babu abinda ke damunsa, and da mun san wannan ne damuwar tun farko ai da mun yi masa abunda ya dace.†"It's not too late ranka shi daɗe ko yanzu, ina baka tabbacin in sha Allah matukar zai yi aure to wannan matsalar zai rabu da ita, na ma yi mamaki matuka da saurayi irin wannan a shekarunsa zai zauna cikin wannan matsala ba tare daya nemawa kansa mafita ba duba da yadda zamanin ya sauya." “Alhamdulillahi Indai wannan ne damuwar zamu nemo masa maganinta nan kusa bada jimawa ba.†Mom bata iya sake cewa komai ba har suka gama maganar sannan likitan ya sallame su, jiki ba kwari Mom suka shiga ɗakin da aka kwantar dashi, tausayinsa ne yarufeta tasa hannu ta shafa kansa tana kallon fuskarsa, tabbas dole ta amince da haɗin da Dady ke son yi masa da yar abokinsa, zata saka a fara yimata bincike akanta in sha Allah da zarar ya samu sauƙi, murmushi Dady yai yana sauke ajiyar zuciya "Yanzu hankalinki sai ya kwanta kin ji dai ba abinda ke damun yaronki, ɗago kai tayi ta kallesa ta maida kallonta ga Rayyan tana jin wani abu aranta data kasa misilta ko meye, ajiyar zuciya ta sauke itama, Dady yace "Yanzu muje gida gobe sai mu dawo zasu kula da komai.†"No I can't kawai ka tafi bazan iya barinsa anan shi kaɗai ba." Dady ya ɗan jima kafin yatafi yabar Mom kamar yadda ta buƙata saboda yaransu dake gida.
Kwana ɗaya Rayyan yai washe gari da marece aka basu sallama, wata irin kulawa Mom keba Rayyan tamkar shine jaririn ɗanta, gaba-daya ta hanasa yai komai da kansa, da kanta ta haɗa masa ruwan wanka ya shiga yayi tasa Nayla ta kawo masa abinci, ta gyara masa ɗakinsa da kanta ta fidda masa da kayan da zai saka, bayan ya fito ya shirya cikin kaya marasa nauyi ta zauna da kanta ta bashi abincin abaki har sai daya ci ya koshi, kallonsa tayi "akwai abinda ke damunka yanzu? Ya kake ji?†Ta tambaya cike da kulawa, Rayyan da tunda aka sallamo shi wani irin nauyin Mom yake ji duk da bai ga wani sauyi a fuskarta ba dake nuna tasan ainahin matsalarsa, amma sai yake ji a jikinsa kamar wannan karon ta fahimci komai, Nayla ce ta shigo ita da Suhayla "Ya Rayyan afternoon how was your body?†"Alhamdulillah." Ya faɗa yana kallon yadda ta caɓa kwalliya, ta fahimci dalilin kallon da yake yi mata, don haka tayi murmushi cike da son neman izini tace “Yaya dan Allah zan je gidan Uncle Usman Amnah was invited me since 2days ago, jiya naga baka jin daɗi shiyasa ban tambayeka ba Please ya." Tai maganar dan tasan zai iya hanata, Mom Rayyan ya kalla ta kauda kanta gefe “Baza ki je ba." Ya faɗa ba tare daya kalleta ba, Nayla kamar zatayi kuka ta matso inda Mom take ta zauna kusa da ita “Please Mom dan Allah." Ta ɗora kanta a saman kafadar Mom, Mom ta ture kanta daga kafadarta, ta mike tana cewa "Ba ruwana wannan tsakaninki da yayanku ne idan ya amince." Matsowa Nayla tayi zata fara yimasa sakalci ya ɗaga mata hannu yana kallonta "zaku iya tafiya ke da Suhayla amma after 5 na marece ki tabbatar kin dawo gida, zan kira John ya sauke ku.†Gefen pillow ya ɗauko wallet ɗinsa ya ciro kuɗi ya miƙa mata, cike da farinciki ta karɓa tana godiya duk da taji haushin cewa da Suhayla zata je.
Cinkin farin ciki Nayla suka shiga gidan Uncle Usman tana ƙwalawa Amnah kira, Amnah tafito da gudu suka rungume juna “Ke yar air na ɗauka baza ki zo ba fa da ban ganki ba jiya." Amnah ta faɗa suna riƙe da hannun juna ita da Nayla, Suhayla kuwa can gefe ta nufa inda ta hango su Mahbub da Ikramah ana yi masu lesson dan sune sa'anninta musamman Mahbub da suke matukar shiri dashi, dariya Nayla tayi “Bari kawai Amnah kin san Yayanmu ba lafiya jiya aka sallamosa daga asibiti shiyasa baki ganni ba." “Hmm ai na ɗauka ma shiya hanaki zuwa tunda baya son zumunci kuma yana hanaku.†" Laaa.. wallahi kin masa sharri ba haka bane." Nayla ta faɗa tana kallon gun da akewa su Mahbub lesson jin wata murya data tafiyar mata da hankali na dukan dodon kunnenta, idanuwanta ne suka sauka akan Uncle Sajid dake yiwa Ikramah faɗa kan rashin maida hankali, a ɗaya ɓangaren kuma yana taya yan uwanta yi mata dariya yadda yai mata wani question ta kasa amsawa. Lumshe idanuwa Nayla tayi ta sake buɗe su akansa, lokaci ɗaya taji wani abu mai ƙarfi ya dira a zuciyarta akansa, wani yanayi da bata taɓa tsintar kanta aciki ba ya ziyarceta, ƙaƙƙarfan wani irin sinadari taji kai tsaye na tasowa daga cikin idanuwanta mai kama da wutar lantarki yana neman isar da wani saƙo ga mutumen da bata taɓa gani ba, bai santa ba itama bata san shi ba, gaba-daya ta rikice ta kasa tsayar da natsuwarta sai juyowa take yi tana kallonsa. “Ke Nayla lafiya kike?" Muryar Aunty Zeynab data zo gidan zata tafi suka kusan cin karo ta faɗa fuska a ɗaure, da sauri ta dawo hayyacinta daga duniyar data tafi ta wucin gadi, sai dai har yau maganaɗisun dake kokarin janta wajen sanin ko waye wancan mutumen data gani bai saketa ba, "Wlh Amnah na rikice.†"Da akai uwar me? Ko rashin ganin girman mutane ne da kika gado wajen uwarki zaki nuna mun, har ina miki magana kina cewa kin rikice." Aunty Zeynab ta faɗa a ɗan hasale cikin ɓacin rai, maganar ta daki zuciyar Amnah, ta ji rashin jin daɗin kalaman a zuciyarta, amma bata ce komai ba, a yanzu ba lokaci ne da take fahimtar komai ba saboda zuciyarta ta tafi wani gun, gaida ita tayi tana bata hakuri, tsaki zeynab ta ja tana ci gaba da masifa da faffaɗar maganganu marasa daɗi akan Mom, Nayla na kin zafinsu amma ta saurara saboda ba yadda zata yi, haka Aunty Zeynab ta ƙarasa masifa ta tafi tana jin haushin Nayla ɗin, taso ta tanka mata ta nada mata shegen duka a gidan, so take ta rage zafin mahaifiyarta dake zuciyarta na tsawon shekaru amma ta rasa ta wace hanya zata iya yin hakan, Nayla nada hankali, duk yadda aka zagesu a cikin family ko aka ci zarafin Mahaifiyarsu, zata ji zafin har tana ji kamar ta rama amma bazata taɓa zuwa ta sanar da ita ba, takan sha damuwar ita kaɗai wasu lokutan saboda bata son su ci gaba da musgunawa mahaifiyarta idan har taje ta faɗa wani abun ya faru.
Zeynab ko dama a hasale take da Mahaifiyarsu Amnah ke sanar da ita rashin lafiyar Rayyan da Uncle Usman ke sanar da ita ɗazu daba kowa ya ji ba, kasa hakuri tayi har ta isa gida akan hanya ta kira Mom tayi mata tas “bamu san kin fimu son Rayyan ba sai kin cire jininmu dake jikinsa kin musanya da naki jinin, waya sani ma ko ke kike neman ajalinsa kike so ya mutu ku gade dukiyarsa shi yasa kikai kane-kane kika hana kowa ya raɓesa, ai wallahi kin ji haushi kuma indai Rayyan ne sai mun nuna miki mun fiki karfi akansa dan zai dawo hannunmu dole, wawiya mai raba zumunci kin dai ji kunya saboda you're after his money.†Mom na zaune a falo ne tana kallo Zeynab ta kira wayar ta ɗauka, duk abinda take faɗa Rayyan na jiyota daga cikin wayar, shigowarsa kenan falon yazo ya zauna akusa da mom ɗin, sosai ransa yai mugun ɓaci da kalaman ƙaunar mahaifin nasa, idanuwansa suka kaɗa sukai jajir, zuciyarsa tayi zafi tamkar ana tafasata da sauri ya miƙe ya wuce ɗakinsa, ba'a jima ba ya sauko cikin shiri riƙe da makullin motarsa ya nufi kofar fita, bayansa Mom da zuciyarta ke lulluɓe da kunci tabi tana kiran sunansa cike da son dakatar dashi, sai dai ko data isa harabar gidan har ya tada motar da karfi ya fizgeta yabar gidan “Ya Salam." Ta faɗa tare da komawa ciki ta dauki wayarta tana kiransa, amma sai taji karar wayar ya barta anan falo…
_Aunty Zeynab da alama yau kin taro match É—in da baza ki iya bugawa ba, mu dai munce Rayyan karka yimata da sauki amma ya kuka gani ku?_
.
ZK2026
08081005693
07040402435.
ZUCIYA DA ƘUNA
By Billy S. Fari & Nana Hadiza
@nanadiso10 | Arewabook