Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel By Hafsat Bature
Reading file: ABBAN SOJOJI 1.txt
Chapter 14 of 51
Page 25-26
Ita kaÉ—ai take ta faman wannan aika ce aikacen saboda azmi bata jin daÉ—i headache ke damunta dama ta sanar da ita, zata sha magani ta É—an kwanta,
tunanin ta ynx yadda za ta goge waɗannan long stairs ɗin kullum wahalar su take ji, bin wurin tayi da kallo, wasu irin tagwayen bene ne masu double starcase ɗin nan, a zagaye suke, left & right , in kabi na hannun haggun zaka iya zagayo wa ka sauko ta hannun daman ka, a tsakanin su akwai space, a space ɗin nan zaka iya shiga ta tsakankanin benayen ka miƙi hanya anan zai kai ka bedrooms ɗin su Ayaan waɗan da ke a down kenan,
In kuma ka hau saman É—aya daga cikin stairs É—in zai kai ka , upstair in da ke akwai hanyoyin da zasu sada ka da jerin É—akunansu junaid, a kalla bedrooms É—in dake a gidan totally da wanda ke akwai mutane da wanda babu zasu kai 30,
Falo kuwa akwai manyan manya sunkai 9, kuma kowanne an ƙawata shi da attractive & expensive furnitures,
Amma babban cikinsu shine wanda kana shigowa ciki zaka fara cin karo dashi, main palour É—insu kenan
Ni nasan duk yadda zan kwatanta haÉ—uwar gidan nan ba kowa bane zai gane ba saini dana shirya kuma na gabatar
don hka just imagine it like the one u used to see in your dream, 🙅
tasha wahala sosai wurin gyara gyatan ɗakunansu don ma ba ɗauda kawai iya bedsheet ne zaka samu an yamutsa, sai kaya in an cire kaga anyi wurgi dasu ƙasa, wani ma don iyayi kayan nasa a saman mirror ta same su,
Bayan ta kammala dukan aiyukan, gajiya ta saukar mata bagatatan, ɗaki ta koma cike da jin ƙyanƙyamin jikinta,
Maballin rigar ta ciccire ta zame ta duka ta ajiye ƙasa, cire wandon tayi shima, sannan tasa hannu ta cire naɗin mayafin kanta, kafin tasa hannu ta 6an6are abunda take matse ƙirjinta dashi, tana ciresa taji wata irin iska na shigarta, gaba ɗaya boobs ɗinta a mugun taƙure suke, ba abunda ya same su, amma ƙan nipples ɗinta ba ƙaramin hurting ɗinta ya ke ba,
Ita kanta tausayin kanta taje ji, yadda ƙiri~ƙiri ta canza kanta daga mace zuwa namiji, duk tabi ta takure halittarta, hannu tasa ta cire ɗan gashin bakin da take mannawa, ɗago dashi tayi tana kallonsa tana matuƙar son ainihin halittarta ta mace,
gaban dressing mirror taje ta ajiye shi, toilet ta shiga tasakarwa ƙanta shower, ta haɗa hada hairs ɗinta ta wanke saboda ya fara tashi, gashi tana buƙatar tayi shaving, batasan ya zata yi, sauƙin bata da gashin armpit amma can under ɗinta kuwa akwai sosai,
ta gama yanke shawarar zata É—ebo shaving cream É—in junaid taga hada set na shaver gare sa, dama shine marainin wayan ta,
ganin cewa babu kowa gidan daga ita sai azmi wadda ke can kwance tana sharar bacci, hakan yasa ta yanke shawarar cewa yau zata sakata ta wala, don haka ta shirya tsaf cikin riga t-shirt white colour da black trouser, sai da ta tabbatar ta matse ƙirjinta kamar yadda ta saba, sannan ta aza gashin bakin da take sawa, lalubawa tayi cikin jakar kayanta dayake ba duka kayan ta zuba cikin wardrobe ɗinba, anan tasamu hular da hajjaju ta siya mata, irin wannan hular da ake kira da tashi da kwakwa,
sai da ta tabbatar ta naÉ—e gashinta cikin ta cunkushe ta matse shi sannan ta kifa hular a saman kanta, sai gashi ta fito fes kamar É—an saurayi,
Ita kanta ba ƙaramin daɗin jikinta taji ba, fitowa tayi ƙafarta sanye da takalmi roba na maza,
Kama hanyar É—akin junaid tayi, cikin sauri take tattaka matattakalar stair É—in, a gajiye ta iso É—akin tura sa tayi ta buÉ—e ta shige,
Komai tsaf a tsanake dama ita ce tayi gyaransa, cikin jin daÉ—i ta wuce cikin toilet É—insa, agaban bathroom cabinet ta tsaya, anan taga jerin tsaddun mayukansa, duk wani abu na gyaran jiki akwashi kai kace na macene ba na namiji ba,
Tsawa tayi tana tunanin me yakamata ta ɗauka, tunani ta shiga yi " kodai kawai na tsaya anan nayi shaving ɗin inyaso in na gama in tsaftace masa wurin yadda bazai gane ba sai in samu in lalla6a in fi ce, saboda in na ɗaukar masa zai iya gane wa, ƙarshe ya kamani a matsayin 6arauniya, ya zanyi ni," ta fada tana ƙarewa wurin kallo
hannu tasa ta É—auko roban shaving cream É—in ganin yana da kusan guda uku yasa ta yanke shawarar ta É—auki É—aya bazai gane ba, sai ta haÉ—a da shaver guda biyu, tun da taga yana dasu dayawa a cikin ledarsu,
ruƙo su tayi a hannun ta saboda haɗama irin tamu ta bil'adama zuciyarta ta raya mata cewa mai zai hana ki haɗa da shampoo saboda wanke kai ga kuma sabulai masu ƙamshi sannan kina buƙatar turare na fesawa a jiki,
Murmushi tasaki jin wannan zancen na zuciyarta,
A fili tace "abun sai na samo wurin da zan zuba su baxan iya É—auka ba a hannu na,
Fitowa daga bathroom ɗin tayi ta shiga neman wurin da zata sa kayan, a nan tasamu wata shopping bag, ƴar jakar nan ta siyayya, komai cikin sauƙi take ganin sa,
Komawa cikin toilet É—in tayi ta shiga jidar kaya tana zurawa aciki, Sam bata tunanin cewa sata take yi ita ina gani take kamar ta zama Æ´ar gida in ta É—auka halal ne.
A gajiye ya shigo cikin gidan jikinsa sanye da kayan kwallo riga da gajeran wando, yellow colour ba ƙaramin kyau sukayi masa ba, hannunsa riƙe da kwallo yana ɗan bugata a hannunsa, kafin ya rungumo ta a ƙirjinsa, cikin sauri ya haye upstair yana isa kofan ɗakinsa, yasa ƙafarsa ya harba door ɗin ta buɗe,
Saboda tsananin firgice sai da tasaki kayan dake rungume a ƙirjinta, zo kaga tashin hankali, daga cikin toilet ɗin take jin shigowarsa, tuni ido ido ya raina fata musamman da taji tabbas shine ɗin dai ya shigo, ana dara ga dare yayi 🙉
"Nashiga ukuna junaid ya dawo tafaru ta ƙare " ta faɗa ido luhu-luhu, tuni jikinta ya fara rawa, matsawa tayi jikin kofan tana leƙansa,
samun shi tayi yana cire takalmansa, ganin he's trying to takeoff his clothes,
Hakan yasa ta fargaba, koma wa tayi ciki tasa tafin hannunta tana bugun goshin ta, tuni Æ´an matan hawaye sun bayyana, sintiri hawayen suka soma yi suna sauka a kumatunta, tashin hankalinta kada junaid ya ce zai cire kayansa saboda shi baisan da human being aciki ba,
Kuma tana da tabbacin cewa yadda ya dawo a gajiyen nan, wanka zai buƙaci ya fara yi, cikin tsananin tsoro ta furta "ae shikenan waman ƙadarallahu hakka ƙadrihi,"
wayyo Allah na there's no way out, ya Allah ka kawo min mafita, ni nasan alhakin satar dana zo yi masa ne Allah ya kamani, hannu ta ɗaga sama tana addu'a tana cewa Ya Allah bazan ƙara ba ya Allah kafi kowa sanin cewa ni ba 6arauniya bace wlh sharrin shaɗain ne da kuma zuciya 😥
Ashhhh ! a wani irin yanayi yayi wannan sautin yayin da yake cire rigarsa da alama something is hurting him may be he gets wound,
Wurgi yayi da rigar saman bedmatress É—insa, hannu yasa yana shafa gefen cikinsa wurin yayi jawur abunka da kalar madara, ciwo ne wurin amma is not much,
A gefen gadon ya zauna yana sauke ajiyar zuciya,
Leƙo shi sehrish ta ƙarayi ganin sa zaune yasa taji sanyi aranta, zuba mishi na mazurin ta tayi tana kallonsa
A wani irin yanayi yake lumshe kyawawan idanuwnsa, teeth ɗinsa ya ɗansa yayi biting red lips ɗinsa, kai ka ce wanda ke cikin shauƙi ne,
hakan ba ƙaramin feelings ya sa sehrish ba, ita da ke leƙensa ta cikin toilet,
Mayar da kanta ciki tayi tana tunanin dabarar da zata yi masa ta samu ta fice, ranta ne ya bata cewa kawai ta fauze tayi kamar wanke toilet É—in take yi tunda ita house maid ce tana da damar shiga ko'ina,
Murmushi tasaki tuna wannan dabarar, acikin zuciyarta ta ce ashe hakanan nake wahalar da kaina gaskiya kan kifi ne dani, bana gane komai cikin sauƙi
wurga idonta rayi kan kayan da ta zubar, ji tayi bazata iya barin shaving cream ɗin nan ba, koda zata mayar masa da sauran, matsawa tayi wurinsu da ta zubar da kayan, ta zuƙunna ta kwashi robar shaving cream ɗin da shaver guda ɗaya,
Cikin aljihunan wandon jikinta ta sanya su, amma robar tayi ɗan zumbuɗi tayi tayi amma taƙi idasa shiga haka tabarta,
Sauran ta tattara su ta mayar masa a cikin bathroom cabinet É—in,
cikin sanɗa ta tura kofan ta fara zuwa kai tana leƙansa, ganin idonsa rufe ya tabbatar mata da cewa junaid fa bacci yayi awon gaba dashi don haka ta soma tafiya cikin sanɗa maimakon ta wuce ta fice cikin salama,
Amma hango jerin turarurrukansa da tayi agaban mirror yasa ta tsayawa, koma wa tayi a hankali ta cafko kwalbar turare ɗaya, ƙiris ya rage kwalbar ta faɗi kasa saboda ta kusa ta zame daga hannunta,
Wani irin bugun zuciya taji amma ganin ta same ta raÉ—au a hannunta ysa ta sauke ajiyar zuciya,
"na tsira" ta faÉ—a alokacin da ta samu ta fice cikin sa'a ,
Sam sehrish batayi tunanin cewa yaya Qarfin ƙamshin turaren yake ajikin mutun ba ! Kunsan turaren maza da ƙamshi,
cikin jin daÉ—i ta wuce bedroom É—inta, jera su tayi agaban mirror É—insa, ran ta fal da farin ciki ganin itama yau ta fara jera abu a gaban mirror,
junaid
Bacci yayi na ɗan wani lokacin sai wuraren asr prayer ya farka, ƙarar shigowar message a wayarsa ne ya tayar da shi, a ɗan firgice ya tashi hannu yasa tare da shafa face ɗinsa yana sauke ajiyr zuciya,
Idonsa yakai kan well clock ɗin dake manne, hadaddiyar gaske ƙarfe 3:59 dai dai time haryaso ya goce masa,
Cikin kasala ya tashi kamar wanda ke shirin yin kuka, faÉ—awa cikin toilet yayi ya jagwalgwala wanka ya fito,
Closet É—insa ya bude riga da wando ya dauko, t-shirt É—in ja wandon black colour,
Hannu ya kai ya dauki wayarsa dake gefen fillow É—insa, buÉ—e wayar ya yi tare da karawa a fuskarsa nan take security É—in wayar ya buÉ—e,
buÉ—ewa yayi ya fito daga room nasa, a natse yake tafiya yana daddana wayarsa message É—in ya buÉ—e ya soma karantawa kamar haka
"Sister kwana biyu naji baki kira kin tambayi ya ya jikin mu ba, anyi mana aiki cikin nasara, naji sauƙi sosai husanna ma taji sauƙi sai dai hanyarzu akwai sauran mentel illness akanta, sunanki kawai take kira sehrish sehrish dan Allah ki kira mu muji voice ɗinki,"
tsayawa ya yi cike da tsananin mamakin ganin wannan saƙon a wayarsa a fili yace wacece kuma sehrish da husanna ! A wayata kuma !! me hakan yake nufi, wani namin amfani da wayata ne shin wai ma wanene wannan sehrish ɗin !!!
Kansa ya gama ɗaure wa, a hankalin ya idasa saukowa daga saman stair ɗin, ransa ne ya basa cewa kawai wasu ne sukayi kuskuren hada numbarsa, don haka ya share lamarin da cewa in ya samu lokaci zai kira number ɗin ya sanar dasu cewa its a wrong number, tunda yaji maganar rashin lafiya ce tana da mahimmanci kwara su son cewa basu sa number dai dai ba. 😳
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•
*_Hafsat Bature_*
~(Boss Lady)~
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.