Trending Hausa Novels

Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel By Hafsat Bature

Reading file: ABBAN SOJOJI 1.txt

Chapter 20 of 51

Page 37 to 38

Shiru su kayi na É—an wani lokaci wani irin kallo yake binta dashi confidence É—inta na basa mamaki ita ala dole namiji ce,
"Can u make a choculate cake for me,'?
Ya tambaya yana kallonta
ɗan zaro ido tayi hakan ba ƙaramin kyau tayi masa ba,
Cikin en ina tace" choculate cake kuma ranka shi daÉ—e banda lafiya,' ta faÉ—i hakan tana É—an dafe waist É—inta alamar akwai ciwo wurin,.
yar dariya yayi kafin ya ce "naso ace zaka iya haɗamin da nayi ko browsing ne a wayata sai na baka ka ga yarda akeyi saboda ina buƙatar cin.....'
tun kan ya idasa ta katsesa "zan iya tsaf in ka ban wayr zan ga yadda ake yi sai nayi....
abun yaso yasa shi darawa dama dagangan yayi mata haka saboda ya gane cewa ita ce ke satar masa waya tana kiran yan uwanta, yayi hakan ne don ya haÉ—a ta da Æ´an uwanta dake nemanta,
tayi tunanin ita ce tayi masa wayau batasan cewa shine yayi mata wayau ba domin yasa recording da za'rar ta fara wayar recording É—in zai soma yana so ya ji meke damun Æ´an uwan nata,
Bayan ya bata wayar ya fi ce daga gidan, jikinta har rawa yake yi ta samu nama,6oyewa tayi a wani corner ta danna wa su husanna kira,
A lokacin jahad bata kusa sun fita amsar wani tallafi da ake rarrabawa a gidan wani É—an majalissa ita da tsohuwa sun bar wayr a gida,
wayau su kayi ma husanna don ta zauna suka bata wayar tayi game sannan suka datse ta a É—aki da key gudun kar ta fita kar kuma wani ya shigo ya cutar da ita tun da ba kofa a gidan buhu ne kamar labule,
da tagama buga game É—in taji shiru gidan ba kowa ta kwakkwala masu kira kawai sai ta kama rera kuka tayi mai isarta ta koma ta kama bacci,
Ringing É—in wayar ne ya tayar da ita har sai da ta tsorata saboda ta ajiye wayar a saitin kunnan ta,
Cikin sauri tasa hannu ta É—aga wayar tana sauraran jin muryar wanene,
Sehrish ta gyara murya tare da cewa"assalamu alaikum yar uwa ni ce pls kiyi mgna da sauri ya jikin naku ya husanna taji sauƙi ko har ynx da haukan nan akanta ?
ta tambaya tana jiran amsa
Sautin kuka taji tunda taji hakan ya tabbatar mata da cewa husanna ce ta É—auki wayr saboda ta tsani ace mata tana hauka ita bata yarda ba har yau !
"Subhanallahi kash ! husanna ke ce..? ta tambaya kamar tana a gabanta,
Cikin muryar kuka tace "ni ce! shine kika tafi ki ka barmu ko ? cikin wahala da bakin talauci kullum ba abinci sai mu jera kwana 5 muna cin É—umamen tuwa....'
Jin wannan maganar yasa kwalla ta taru a idon sehrish ci gaba da sauraronta tayi
"ni nagaji dan Allah ki dawo ko kizo ki dauke ni wlh bana jin daÉ—i, ko isasshen bacci bana samu ga sauro ga yunwa ko kayan sawa babu kullum wasu tsummo karai tsohuwa take bamu muna sawa ni nagaji gsky,'
Sehrish batasan lokacin da kuka ya 6arke mata ba, sam tagaza magana tuni jikinta ya soma jijjiga kamar wadda sanyi ya buga
"Kinyi shiru baki ce komai ba ? kin manta oumman mu tace duk runtsi duk wuya karmu rabu da juna amma kika tafi ko ? baki sona ko ? So kike na mutu ko, to shikenan zan je na kashe kai....'
tsawa sehrish ta daka mata wanda hakan ya dakatar da ita daga magana " ya isa ! Ya isa! ya kike so nayi? saboda ku nake zaune a nan husanna, bashi ne na dubu É—ari tara akaina how can i pay it ? i dont ave anything dole na tsaya nayi musu aiki na tsawon shekara É—aya da rabi,saboda ku !
daker ta ƙarasa maganar tana share kwalla,
Jin yadda sehrish ke faman shesshekar kuka yasa jikin husanna yin sanyi ta ce "kiyi hakuri in na 6ata miki rai bansan ran ki zai 6ace ba,'
dakyar sehrish ta tsaida hawayen ta gyara wayar a kunnanta tace" rai na be baci ba ina kuka ne saboda ku halin da kuke ciki, amma karki damu kinji ƙanwa ta in na samu kuɗi zan tura muku insha Allah ki tayani da addu'a,'
cikin sanyin murya husanna tace" ina miki addu'a kullum bana mantawa,'
Murmushi sehrish tasaki kamar suna kusa da juna tace"I love u so much shashasha,'
tana jiyo muryar husanna ta cikin wayar tana tiƙar dariyar saboda ta tuna mata da wani abu,
daga nan sehrish tace "zan ajiye waya send my regards to jahad & tsohuwa,'
husanna tace"insha Allah zasu ji"
daga nan ta katse wayar ranta fal saboda taji muryar husanna, cikin koshin lafiya,
nan fa ta soma tunanin yadda zata haÉ—a masa chocolate cake ita hasalima a suna kawai tasan cake É—in,
Wuri ta samu saman ta zuƙunna ta shiga lalubar masa waya instead taje tayi aikin daya sata,
Gallery ɗinsa ta shiga madaddalar hotuna, na fa ta fara ganin haɗaɗɗunan pictures ɗin samarin familƴ ɗinsu hada waɗanda su kayi a ƙasashen waje,
A nan ne taga hotonan wannan haÉ—aÉ—É—en matashin saurayin mai shegen kyan nan, shi da junaid su kayi hoton a cikin jirgi da alama privet jet ne mallakinsu saboda su biyu ne acikinsa, sunyi hugging É—in junansu fuskarsu É—auke da murmushi,
wuce wa gaba tayi next picture nan fa ta ƙara ganin hotonsa cikin dandazon sojoji suna sara masa,
Ƙasa tayi ta shiga videos nan fa ta gane wa kanta zahiri,
Videos É—insa tagani kamar hauka da alama junaid na yinsa sosai,
ran ta yana bata cewa wannan ba kowa bane face BABBAN YAYA wato surgeon general RAFAYET,
ta jinjina wa matsayinsa ganin kowane video zakaga dubban sojoji ne turawa kewaye da shi suna taka masa baya, ko suna sara masa ,
tana cikin wannan laluban wayar ta soma ringing bin hoton da ya bayyana a calling É—in tayi ,
zaro ido waje tayi tare da buÉ—e baki alamar mamaki, mutumin da take bibiya ynx haka shine ke kiransa a waya,
tunani ta soma yi ta yi É—aga ko kar ta É—aga ? katse wa kiran yayi wani kuma ya sake antayo wa wayr ta ci gaba da ringing,
Cikin tsananin tsoro da jin fargaba ta É—aga tare da karawa a kunnanta bata ce komai ba, tayi shiru tana sauraronsa
abun da ya É—aure mata kai shima bai ce komai ba ! hasalima alamu sun nuna cewa ya manta daya danna kiran saboda tajiyo hayaniya mutane ta cikin wayar alamar tattauna wa ake,
katsewa kiran yayi, janye wayar tayi daga kunnan ta ta zuba ma number ido da sunan da aka a jiki "My everything"
ta jima wurin zugudun tana kallo kamar daga sama taji muryar junaid
"An kammala haÉ—a min cake É—in"
A firgice ta tashi zaune tana kallonsa tayi wuri wuri da ido tana mazurai,
Murmushi ya saki tare da miƙa mata hannu ya ce "Gimme my phone,"
cikin rawar murya tace"am..umm..dama ynx nake am..:
hannu yasa yayi mata alamar tayi shiru kafin yace its ok ba damu zan sa a kawo min ne kawai,'
ya faÉ—i hakan tare karban wayar ya shige ciki binsa da kallo tabi shi har ya 6ace wa ganin ta,
A cikin waɗannan kwanakin wata irin shakuwace ta shiga tsakaninta da junaid tarasa dalilin dayasa yake kyautatamata sannan abunda ke ɗaure mata kai ynx baya bari ta shigo ɗakinsa musamman inda ga shi sai shorts (gajeran wando) a jikinsa, abunda bata sani ba shine ya gane cewa ita macece da cen abunda yasa yake sakin jiki bai kunyar yin komai a gabanta saboda a tunaninsa namiji ce, ga shi kullum sai ya bata aron wayarsa ya ce ta buga game, waɗannan abubuwan na matuƙar ɗaure mata head,
Ba ƙaramin daɗin hakan taji ba, kullum sai sunyi waya dasu jahad da husanna, kullum sai tayi mata complain akan ta turo musu kuɗi sun gaji da talauci, tai ta faman basu hakauri akan su bata lokaci,
bata samun matsala da kowa ynx, tana taka tsantsan akan duk wani abu da zai sa a kore ta daga gidan, Mutunci tsakanin ta da azmi sai ƙara habbaka yake abun ba'a magana ta maida ta kamar auntyn ta ita ma haka azmi ta maida ta kamar yar cikinta ko nace ƙanwarta komai na tafiya dai dai,
A 6angaren su husanna kuwa dake cikin mawuyacin halin kamar kansu farau talauci, suna buƙatar agajin gaggawa domin maganungunan da doctor ya ba ta sun ƙare dole sai an samu ƙuɗi an siya mata wani,
don haka jahad ta yanke shawarar turama sehrish saƙo, a lokacin da message ɗin ya shiga wayar na hannun junaid,
Karantawa yayi kamar haka" sister maganin husanna fa sun ƙare akwai matsala tazama wata zararriya ta hana mu sakat pls ki taimaka mana,"
Koda junaid ya karanta message É—in sai ya tura masu da "Send me your account number,'
ganin wannan saƙon cikin zumuɗi jahad ta zari hijabi don tashiga gidan makwabtansu saboda yarinyar gidan nada account number su nan basu dashi,
kafin ta dawo husanna tafarka daga bacci saboda cikinta daya katsa, ta soma laluben waya saboda toilet ɗin akwai duhu irin na gargajiyar nan ne ginin ƙasa, nan ta samu yar nokia ɗin da jahad ta ajiye a saman jakar kayansu taɗauka ta shiga da ita toilet ɗin, to ka'ida in ta kunna fitilar wayar ta zukunna sai ta fara buga game tana sukuni,

Tana cikin zuƙunno nan wani ƙaton kyankyaso mai fiffike yayi tsalle sai saman kanta, cikin firgici ta tashi a razane nan take wayar dake hannunta ta sulale daga hannunta ta faɗa cikin ramin masan Subhannallah,
Can ance a turo account number nan kuma wayar da suke da ita kwalli kwal ta faÉ—a cikin masai,

Zaro ido tayi tare da buÉ—e baki saboda tsoro, taji haushin kyankyasan nan har taji cewa bazata kyalesa ba dole ya mutu,
Nan suka shiga sintiri ita dashi shidai wings ke gare sa, ita kuma da ƙafa take binsa sai faman tashi sama yake yake yi tana binsa da gudu, hada ɗauko takalmi tana kokarin kwaɗesa,
Baki a washe jahad ta shigo ta samo account number É—in yarinyar ta rubuta mata a farar paper,
ɗakinsu ta shiga tana neman waya, sama ko ƙasa babu ita ta shiga lalube ko'ina babu, tashiga mamakin ina aka kai wayar bayan babu,
tunawa tayi da cewa tabar husanna a kwance tana bacci tabbas tana wurinta , fita tayi cikin saurin tsakar gidan
Adai dai lokacin Husanna tafito tana sauke ajiyar zuciya tace"wash Allah da ace ban kashe shi ba dana binne kaina,'
"Husanna ina wayar nan take"?
jahad ta jefa mata tambaya ita bama ta lura da ita ba sai da tayi magana, nan fa tashiga wurga ido na mara gaskiya shiru tayi tana kallon ƙasa,
hakan ba ƙaramin tayarwa jahad da hankali yayi ba, saboda akwai abunda ko ba'a faɗa maka ba zaka fahimta ne ta yanayin mutun,😿*🔥ABBAN SOJOJI🔥*

*writer* *HAFSAT BATURE*

~Boss Lady~

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.