Auren Bauta Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bauta_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 1 of 2
Compiled by Umar Dalha Funtua.
🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
*AUREN BAUTA*
ðŸ·ðŸ½ðŸ¥›
👩ðŸ½â€ðŸ³~(the amazing cook)~👩ðŸ½â€ðŸ³
ðŸ³ðŸœðŸ¥˜ðŸ²ðŸ›ðŸðŸ¥—🌯ðŸ¢ðŸ¥ ðŸ¥ðŸ¤ðŸ£ðŸ±ðŸ²ðŸ¡
By mmn walid and walida (mrs aliyu)
Marubuciyar
*tawa kaddarar*
*dangin sa*
*uwata*
*rabo na ce* to be continued in shaa Allah
Page 1🌹
"Sai yanzu kika dawo ƴar iska tun ɗazu da aka aike ki ɗebo ruwan sai yanzu kika ga daman dawo wa kuma kina ji na nace miki sanwar wake da shinkafa zan ɗaura da ruwan shine kika je kikai zaman ki don kina min baƙin cikin kuɗin da zan samu ko, shegiya da fuskar kamar ta aljan"
Duk wannan faÉ—an da inna harira bata taimakawa Æ´ar yarinyar da take É—auke da ruwa akan ta, duk kuwa da ganin cewar yarinyar ta gaji sosai
sai da tayi ta gama sannan ta sauke,
"kuma kije gonar malam ki wo min in kin ga dama ki daÉ—e kamar kinje lahira gaida iyayen ki"
ÆŠan É—ankwalin da take É—auro karar ta É—auka tayi waje da shi, directly gonar ta nufa wanda bashi da nisa da gidan ta É—ebo karar sannan ta kama hanyar gida tana yi tana nishi daga gani yunwa ce da kuma gajiya a tattare da yarinyar
Da sallamar ta ta shiga gidan ta ajiye karar sannan ta zundumi ruwa a randa ta É—an sha kaÉ—an bata san ta cikawa cikin ta ruwa
"shiga madafi ki ɗauko ragowar ɗumame ki don yadda kike zaro min idandinan nan naki a cikin wannan baƙar fuskar taki ai wannan sai in mummunan mafarki"
Abincin ta É—auko zata fara ci kenan inna harira ta kuma saka ta aikin hura wuta na wake da shinkafar da take saidawa
A bakin murhun ta zauna tana hura iccen tana cin sandararran tuwon dawan da idan aka jefe ka da shi sai kaji ciwo saboda tsabar taurinsa
Sai da ta gama girka wake da shinkafar tsab sannan ta kwashe a Æ´ar fantekar da ake kwashewa sannan ta gayaws inna harira ta gama
"lantana lantana", inna harira ta kira ƴar ta da ke yi mata talla don kuwa asmau bata da kan inna harira tace yadda fuskar ta take baƙa haka ma kwakwalwar take sam babu haske a tattare da ita
Asma'u ce ta É—au fantekar inda lantana ta shige gaba suka tafi tallan haka suke yi kullum ita lantana itace me kan talla amma ban da asma'u
Sai bayan sallah la'asar sannan suka dawo inda suka tarar da inna harira da baƙuwa a zaune a tsakar gida akan tabarma
Ƙwalawa asmau kira tayi ta ƙarasa inda take sannan ta nuna wa matar asmau
"hjy kina ganin zatayi, don ni ƴar nan babu abinda take min anan, kullum sai dai taci tayi kashi kan talla babu shi yanzu in ta tashi aure wazai mata kayan ɗaki, ga shegen baƙi kamar kwalta"
Matar da aka kira da hjy ta dubi asmau sannan tace
"to ba wai baza tayi ba kamar yadda na faÉ—a miki abuja ni fa nake kai yara aikatau, wannan kuma kamar yarinya ce"
"ahap haka kike gani ai wannan in ta kama aiki kamar jaka haka take, reno shara wanki wanke wanke duk ta iya"
Hjyr ta kuma kai duba asmau wacce kan ta yake a ƙasa sannan ita sam bata fahimci inda zancen su ya dosa ba
"ni dai da waccen ce" ta faÉ—a tana nuna lantana Æ´ar inna harira, inna harira sai tayi dariya irin ta basarwan nan
"haba bazaki so kiɗau wannan ba ai alanƙosa ake ce miki indai lantana ce ba abunda zata iya, yanzu tallan wake da shinkafar da take kai min ma tace zata dena tunda ɗan me gari yace yana sonta shi yasa nake neman hanyar da kuɗi zasu dinga shigo min, ga bikin lantana ban ajiye ba ban ba wani ajiya ba, kuma auren ɗan me gari kashe kuɗi gare" ta faɗa tana ajiyar zuciya
"to shike nan indai kince wannan ɗin zatayi ai shike nan, amma idan na tafi da ita kuma aka ƙi ɗaukar ta zan dawo miki da ita"
"na yadda amma kice su fara gwadata tukunna kafin su yanke hukunci da wannan ɗan ƙaramin jikin nata shine yake sawa mutane suna yi mata kallon yarinya ce"
Sukai sallama kan kashegari da asuba zata zo É—aukar asmau zuwa garin abuja aikatau
***********************
Asmau sunana na kasance ni kaɗai a wajen iyaye na babana ɗan nan garin ne azore wanda yake a ƙaramar hukumar minjibir ta jihar kano,
Garin fulani ne sosai don gida tsilli tsilli zaku dinga gani in kun shigo sannan sai kuma gonar mutum a jikin gidan sa, irin dai ginin fulani, in kaga gida É—aya sai kayi tafiyar mill kafin kaga wani
Ban san iyaye na ba kasancewar sun rasu, mahaifiyata ta rasu lkcn haihuwar ƙanina, inda aka rasa aka rasa ɗan,
Shi kuma mahaifina sai da na É—an tasa kaÉ—an sannan Allah yayi masa rasuwa, sai kulawata ta koma hannun wan mahaifina
Inda yake min rikon sakainar kashi, don kuwa babu ruwan shi da duk wani daya shafe ni duk abinda matar shi zatai min baya cewa komai wannan shine taƙaitaccen tarihi na
******************
Da sassafe hjy ta zo mukai sallama sannan muka kama hanya inda naci karo da wasu Æ´ammata waÉ—anda zamu tafi da su, amma duk sun girme ni don ni sai na zama kamar wata Æ´ar tsana a ciki su
Sai da muka je gezawa sannan muka samu ƙaramar mota inda zata kaimu abuja, haka aka cunkusa mu a motar nan kamar dabbobi inda ita kuma hjyr ta zauna a gaba ita kaɗai
Tafiya ce kamar ta yada shege ba ƙaƙƙautawa sai da muka je kaduna sannan direban ya tsaya muka fito muka ɗan huta, sannan muka kama hanyar abuja
Lfy ƙalau muka isa abuja inda muka sauka a kubuwa, anan gidan hjy yake, ɗaki ta bamu guda, tace duk mu sauke kayan mu
Ni dai kamar an min duka haka nake ji don kuwa a gajiye nake, kwanciya nayi sai bacci, inda Æ´ammatan da muka zo da su kowacce take ta buri tare da fatan irin gidan da za a kaita, ni dai tunda na samu bacci ya kwashe ni sai nace saba'ul khairi
👩ðŸ½â€ðŸ³ menu of d day👩ðŸ½â€ðŸ³
*wake da shinkafa served with local salad & zobo drink*
🲠```wake da shinkafa```ðŸ²
```ingredients```
```wake```
```shinkafa```
```gishiri```
```man gyaÉ—a```
```haÉ—in salad```
```method```
1) bayan kin gyara waken ki saki ki wanke ki É—aura akan wuta, sannan ki bishi da ruwan kanwa (optional)
2)sai waken ya dahu, sannan ki É—auko wankakkiyar shinkafar ki ki zuba ki juya ki saka É—an gishiri sannan ki rufe
3) idan ya dahu sai ki sauke ki yi serving da soyayyan man gyaÉ—a, ko tankwa, da yaji sai kiyi ganishing da salad aci lfy
*LOCAL SALAD*
```ingredients```
cabbage
lettuce
carrot
cucumber
green pepper
lemun tsami
man gyaÉ—a
maggi
```method```
1) ki wanke lettuce, cabbage, cucumber, green pepper É—inki, ki barsu su tsane sannan sai ki yanka su irin yankan da kike so
2)ki kankare bayan carrot sannan ki wanke shi daga nan sai ki gurza shi
3) ki É—auko kayan haÉ—in da kika yayyanka ki haÉ—a da carrot sannan ki haÉ—e su waje É—aya, ki É—auko lemun tsami ki É—iga kaÉ—an ba dagawa ba yadda dai zai miki sannan ki zuba mai ki zuba maggi ki juya sai ki juye a salad bowl sai ci
*zobo drink*
```ingredients```
Ganyen zobo
Citta
Kanunfari
Abarba
Cucumber
Sugar
Flavour
```method```
1) ki ɗauko zobo sai ki wanke shi ki zuba masa ruwa ya sha kansa sannan ki ɗaura a wuta, tare da citta, ɓawon abarba, sai dakakken kanunfari ( ```sirrin daka kanunfari shine ƙamshin shi ya fi fitowa idan an daka shi akan a watsa shi haka```)
2) idan zobo ya tafasa ya dahu sai ki sauke shi ki juye a babban mazubi yadda zai sha iska, kafin ya huce kuma bari mu haÉ—a ragowar
3) ki fere yanka abarbar da cucumber ki ƙanana yadda dai zasu miki daɗi wajen blending sai ki markaɗa su kina yi kina tacewa kina ƙara markaɗawa har dai a samu yadda ake so
4) sai ki É—auko wannan zobon naki ki tace ki É—auraye ganyen ki kuma tace wa har sai maa shaa Allah, sannan ki haÉ—a da ruwan cucumber & abarbar nan
5) ki zuba sugar, flavour ki zuba a jug a saka shi a fridge yayi sanyi sai shaa
👩ðŸ½â€ðŸ³ *Bon appetit*👩ðŸ½â€ðŸ³
*ASMA'UN SABIT*
🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*
ðŸ·ðŸ½ðŸ¥›
👩ðŸ½â€ðŸ³~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩ðŸ½â€ðŸ³
ðŸ³ðŸœðŸ¥˜ðŸ²ðŸ›ðŸðŸ¥—🌯ðŸ›ðŸ¢ðŸ¥
Ê™Ê á´á´É´ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (á´Ê€s ᴀʟɪÊá´œ)