Complete Hausa Novels

Auren Katin Kasa Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Katin_Kasa_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 3 of 10

Chapter 55

Tunda salima ta tashi yau take tsoron daukan wayan don charging bazaikai mata dare ba zai mutu haka yasa tayi dialing number amra, lokacin da kiran ya shugo amra na tare da haifa suna duba patients, jin kiran yayi yawa yasa ta zaro wayan sannan tadan koma gefe ta daga ta fara Magana ‘’hello who’s this?”.. jin an daga wayan yasa salima fashewa da wani matsanancin kuka tace ‘’addaa adda nice ki kirani’’ jin muryar salima yasa amra saurin cewa ‘’salima salima kece salimaaa’’’da sauri ta kashe wayan sannan ta sake kiran layi, da sauri salima ta dauka ta fashe mata da wani matsanancin kuka tace ‘’adda nice, adda muna cikin mawuyacin hali, adda ki taimake mu, ciwon salim ya dawo, adda kizo ki daukemu ki dawo damu wajenki dan Allah’’ jin hakan yasa amra tsugunnawa anan mutane kuwa me zasuyi banda kallonta don duk ta furgice, cikin shesheka amra tace ‘’salima meya faru daku, meya sameku innalillahi,’’ kittt wayan yamutu sakamakon chargi daya kare,
hankali atashe amra ta soma cewa ‘’salima say something salima!!!!! Jin shuru yasa ta duba wayan taga call din yayi ending hakan yasa tayi sauri sake kira amma me switch off, hankali atashe ta daura hannu aka ta fashe da kuka, haifa wanda sai yanxu hankalinta ya dawo kan amra yasa tayi sauri zuwa gaban ta tace ‘’amra what’s wrong’’ innalillahi kawai amra ke furtawa dakyar haifa ta jawo ta suka wuce office suka zauna, saida ta bata ruwa sannan ta fara dawowa dai dai, anatse ta soma Magana ‘’haifa siblings dina, suna cikin mawuyacin hali, ashe sune suketa kirana da wani line over a month now, I’m so stupid for not recognising them, bazan taba yafema kaina ba idan qannena suka shiga cikin matsala, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, na shiga uku haifa”…saida haifa ta kwantar mata da hankali tukunna ta dawo dan daidai, babu abinda kwakwalwarta ke tariyo mata sai maganan salima da take cewa ‘’adda kixo ki taimake mu ki tafi damu, muna cikin matsala, ciwon salim ya dawo gadan gadan, runtse idonta kawai tayi don bazata iya jurewa ba kwata kwata.

Aikin da basuyiba a ranar Kenan ba, koda ta koma gida number ta dunga kira amma switch off, aranar dai amra batayi bacci ba kwata kwata.
Bangaren salima hakan ta kasance, tayi kuka harta godema Aallah, karshe dai alwala kawai tayi domin kai kukanta wajen Allah, salim kuwa da yanxu rabin rayuwar shi kamar mattace kullum sai barci yake ta kalla, tausayinsa duk yagama lullubeta.
 
Washe gari, kwata kwata amra ta susuce, bata cikin nutuswarta, koda taje aiki babu abinda ta iya yi kwata kwata, gashi ayyukan sunyi mata yawa don hafiza tunda ta tafi bata kara dawowa ba, haifa ce kwai ke taimakonta sosai wajen wasu abubuwan, yanxu kam ta yanke hukuncin duk yanda za ayi saita san yanda tayi ta kawo qannenta kusa da ita kuma zatabi ko wace irin hanya ce.

 Zama sukayi ah café, wanda kwata kwata amra ta kasa cin komi sai haifa ce take dan turawa itama bata cikin kwanciyar hankali ganin yar uwarta cikin damuwa, hakan yasa ta zuba mata ido kawai sannan tace ‘’ámra I have a solution but I don’t know if its going to work,(inada shawara saidai bansan ko zata yiwu ba), kinga dai visa ki saura shekara biyu kuma kince baki gama tara bashin uncle ba ko?..girgiza mata kai amra tayi tana fuskantarta da nutsuwa .. anatse haifa ta cigaba ‘’babe why not ki nemi katin kasar nan sbd ki kawo kannenki kusa dake’’ jin wannan batu yasa amra yin shuru chan tace ‘’wannan ce kadai hanyar da zan iya kawo su kusa dani haifa??’’’girgiza mata kai haifa tayi sannan ta cigaba ‘’but babe samun katin kasa ah uae shine abu mafi hatsari musamman ma ke mace yar Africa domin hanyoyin da akebi asamu are not legal, kuma akwai risk babba’’..kallonta amra tayi don a yanxu kam bata jin akwai abinda bazatayi ba akan qannenta, gyara zama tayi sannan tace ‘’haifa all the risk are not important to me now, ni yanxu damuwa na qannena ne, so I can go to any extent don na taimaka masu, kuma wannan katin kasar shine kawai solution ayanda nayi tunani yanxu.

Nunfasawa haifa tayi sannan tace ‘’okay idan har kinga zaki iya ni kuma zan taimaka maki, akwai wata secretary data tabaa aiki karkashin abu na, itama kusan issues dinku daya saidai ita iyayenta ne wanda suke cikin mawuyacin hali wanda hakan yasa tayi AUREN KATIN KASA…’’jin haka yasa gaban amra faduwa ana wata ga wata, dakewa kawai tayi ta cigaba da sauraron haifa, ‘’yanxu zan kira abu don ya bani number nasan yana dashi har yanxu, idan na sameta zan roki ganinta sai muyi fixing date between yau da gobe don mu ganta yanxu dai ki kwantar da hankalin ki komai zaizo da sauqi kinji’’
Saida haifa ta gama tukunna tadanji sauqin zafin da ranta keyi mata sannan sukaci abinci suka koma office. ✍️✨***Auren Katin Kasa ***✨✍️
(Unexpectedly falling❤️🇦🇪)

Story and written by:
QueenMarh👸🏼

Paid book 📚

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.