Complete Hausa Novels

Budurwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Budurwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 12 of 16

*Page 15*

Bugu daya ya d'auka Yana "Kasan kuwa yanzu nake Shirin kiranka inata Kiran Lubna dan na hadata da Aisha su gaisa bata d'auka ba halan bata kusane"?

"Hmmm Abdul Ina cikin matsala"

"Subhanallahi wani abune ya faru"?

"Abdul idan na fada ma nasan zaka ji haushina amma.kasa kanka a matsayina ko kaina zaka iya kwafsawa"

Mahfuz kasa ma bashi labarin yayi ya cigaba da kame kame sai daya ga Abdul zai kashe wayar ya bashi labarin abinda ya faru ya Kara da "Bansan Mai ya hau kaina ba banyi tunani ba Sam,wlh Hadeeza kanainayeni tayi,na kasa yakice mata gashi yanzu lubna tayi fushi tunda nake da ita wlh ban taba ganin ta yi irin Wanan fushin ba"

"Allah ya Isa tsakanina da Kai Mahfuz baka kyauta min ba yanzu dama yarinya nan budurwa ka ce Taya zaka aikata irin wanan danyen aikin,daka tashi abinka hada dani, wlh Azeem da nasan budurwarka ce ko kallonka bazanyi ba yanzu wane kallo kake San lubna ta ringa min kasa kanka.a matsayin ta yanzu ta kawo maka Saurayi gida ka ringa.kuma hidima da saurayin zaka ji Dadi,ka cutar da ita,wlh ka zalinceta"

"Wai dan Allah Abdul ka barni naji da daya Mana yanzu na kiraka dan.na samu kwanciya hankali da mafita Kai Kuma sai Kara maganganu kake"

"Toh Mai kakeso nace maka a lokacin da zaka yi abinka kayi shawara dani, wlh Ina Jin labarai naka ya banbanta idan ma holewar zakayi da ita ka kaita hotel mana why zaka kaita gidanka tsakani da Allah kace bazan maka.magana ba yanzu ka jawomin bakin jini a gurinta kenan,yanzu zata dauka da hadin bakina aka kaita gidanka a gaskiya banji dadin abinda kamin ba

Yace cikin tsananin b'acin rai kafin mahfuz yayi magana ya kashe wayarsa

Mahfuz yabi wayar da kallo,shi kansa Abdul din bai tab'a jinsa cikin bacin rai kamar haka ba,sake kiransa yayi,bai d'auka ba.

Haka yayi ta Kira a karshe yaji ya kashe wayar.

Mahfuz haka ya rike wayarsa Yana tunanin mafita Abdul kadai yake tunanin zai iya rokon lubna ta sauko sai gashi yak'i sauraransa.

Ammi Kuma yasan ko zai mutu ya dawo bazata saurare shi ba,karshe dai sai yayyensa sun Shiga maganar nan dole su zasu shige Masa gaba wajen shawo Kan lubna.

Zurfin da yayi a tunani yasa Sam bai san dare yayi ba sai muryar Ammi yaji a kansa tana "Wai uban me kake a daki tundazu baka koma asibitin ba"?

"Bana Jin dadi Ammi nima ban wuce a kwantar dani ba bazan iya komawa asibiti ba"

"Sabida ka rabu da Yar dabba Yar gwal ko"? shine zaka kwanta rashin lafiya,Kaine ka dauki yarinya Nan ka Kai gidanka matarka ta kusa kasheta badan Allah yasa tana da tsawon rayuwa ba,shine dan wulakanci zaka barta da shemau kawai a asibiti,idan ma dan ita lubna kake duk abinan toh kayi a banza dan ka gama Zama da ita dan yarinya nan Sam ba matuniyar arziki bace,Sam bansan tana da boyayyen Hali ba sai da abinan ya faru,har ni ta kalla ta zaga a gaban idonka ta ringa yiwa mutane hauka a gida,taya zaka dawo da ita ma Haram lubna ba matar da zaa zauna da ita bane"

"Ammi dan Allah dan annabi ya kike haka nifa na cutar da ita tsakani da Allah kema kinsani tunda Hadeeza ta dawo rayuwata ta kanainayeni ta hanani sukuni,bansan da manufa a ranta ba ashe so take ta tarwatsa min gida,Ammi Kamata yayi ki shige min gaba muje har gidansu mu basu hakuri bawai ki ringa ganin laifinta ba"

"Bakada hankali bazan tab'a taka kafata naje gidansu wata lubna ba Kai da kaga zaka iya da ita sai kaje tunda ka nace amma ka sa a ranka wlh tallahi sai ka Kara aure kurkusa ma kuwa bari yarinya nan ta warke"

"Wacce yarinya Ammi"?

"Wacce ka Kai gidanka Mana ko ka dauka ka samu abinda kakeso bazaka aureta ba,ai ka gama aurenta ka gama tunda har ka iya Kai ta gidan ka ta zauna kaga kuwa aurenta dole badani zaa cuci Yar mutane ba,wanan zalincin da lubna ta Mata ba abinda zaa saka Mata dashi sama da aurenta,dalla tashi kaje asibiti ka dubata."

"Bakin ciki ne ma ya hana shi ce Mata komai yaso ya kwana a gidan nasu,dan ji yayi Sam bazai iya kwanan gidansa ba lubna ba.

Amma da takurar Ammi gwara yaje gidan nasa ya kwana.

Koda ya bar gidansu gidansa ya nufa da isarsa d'akin lubna ya wuce,da wayarta ya fara cin Karo a side bed kafin ya bi koina da kallo Yana Jin inama mafarki yake ace duk abinda ya faru ba gaske bane yaso da wayarta ta tafi da yau bazai bacci ba text zai kwana Yana tura mata na ban hakuri,sai a yanzu ma yake dana sanin biyewa Hadeeza dan tunda ga lokacin daya Santa yaji kamar ba budurwa bace yaji zuciyarsa na Masa rawa akanta,ta Masa Abubuwan da dama daya sa yake zarginta dan ko a ranar ma dayaje d'akin nata bada zumar wani abu ya Shiga tsakanin su ba yaje,yaje ne suyi hira su dan yi romance Kamar yanda ta fara sabar mai,sai dai Yana shiga yaga taci mahaukacin sleeping dress da babu marabarsa da tsirara a matsayinsa na namiji lafiyayye tuni yaji zuciyarsa ta harba ga wani irin fitinannen kamshin da take, gashi ya kwana biyu rabonsa da lubna hakane yasa Koda suka fara romance ya zarce Romance din ta Kuma bashi hadin kai dan kafin ma yayi wani abu da ita sai da ta kusa haukata shi dan da kanta ta zame wandonsa ta hau tandarsa Kamar ta samu alewa,Yana balain so ita Kuma lubna nada kyankyami ko zata Masa sai yaga tunda ranta bayaso shima ba wani Dadi zaiji ba,da hannu biyu ya damke bakinsa sabida Kar yayi ihu kasan zuciyarsa Kuma balain mamakinta yake taya.akayi ta iya ita da ba Aure ta tabayi ba ko aure kayi indai ba koya ma akayi ba taya ta kware haka,tuna wayayya ce kila bf ta kalla da wanan tunanin ya cire zargin ta a ransa har sai daya kusanceta Kuma yaji Kamar ba budurwa.bace dan lubna ya fara sani a rayuwarsa daga shi har ita ba karamar wahala Suka Sha ba,sai da lubna ta tafi wata uku ma kafin ta fara sabo dashi,Amma Hadeeza Kam Kamar kwararriya dan ta bashi hadin kai kwarai,dan gamsuwa Kuma ya gamsu dan kawai bayaso lubna ta tashi tazo ta Kama su.

Ya koma d'akin kamar bai komai ba.

Sai jiya da ya Kara komawa kafin su wayi gari yau da wanan tashin hankalin,Sam Hadeeza batazo masa da alheri ba,ba abinda yasa Hadeeza ta Kara fice Masa a rai sama da asirinsu duk da ta tona musu,har da alherin da tayiwa Ammi,yanzu lubna zatayi tunanin shi ya dauketa ya kaita gidansu Hadeeza ta Kara dagula Masa komai.

Juyi kawai ya ringayi ya rasa mai ke Masa dadi addua kawai yake Allah yasa Lubna ta sako da wuri.

Kowane gida ana shirye shiryen sallah gobe Banda shi da yake cikin tashin hankali da yanzu.

Bacci rabi da rabi yayi washegari Koda ya fita.massallaci Suka hadu da Hamisu mijin mmn Iman bai wani sakar Masa fuska ba suna gaisawa ya wuce Kamar ba mutumin dake jansa da hira ba kila haka mutuncinsa ya zube a idon duk Wanda yasan ya kawo budurwar sa har gidansa.

Koda ya koma gida daga massallaci Kaya ya canza ya dauki wayar lubna yasa a aljihunsa Yana so anjima kad'an yaje gidan yaga ko zai dace da ganinta.

Gidansu ya wuce acan ya hadu da yayyensa dan haka suke haduwa a gida su tafi sallah idi,daga nan su dawo suci tuwon sallah su Kuma bawa Ammi barka da Sallah dan idan har ka hanata haka zatayi ta mita tana bawa mutane labari wane bai bata barka da Sallah ba.

Yana k'ok'arin gaishe da Ya Ali da ya kasance shine baba sai Usman mai binsa sai Kuma Mahfuz.

Dukansu sunyi aure da matansu kannensu Mata uku suma sunyi Aure,Yar autarsu shemau kadai ce ta rage batayi Aure ba.

"Mahfuz ashe abinda ka aikata kenan kanka daya kuwa taya zaka dauki budurwarka ka kaita har gidanka"?

Mahfuz najin haka yasan Ammi ce ta fada musu,fada Suka rufe shi dashi Kamar zasu dake shi sai Ammi ce ta tsawatar musu tana "kuka san dalilin dayasa ya kaita gidansa ni abinda yasa na fada muku sabida kuji irin dibar albarkar da yarinya nan tayi mana idan haka ta kasance sau tari mace tagari rufawa mijinta asiri take,amma.yarinya nan haka ta Tara Mana jamaa a yanzu nasan kowa yasan mai ya faru yarinya nan Sam ba matar rufin asiri bace sai kunga yanda ta canzawa yarinyar kamani"

"Haba Ammi ya zakice haka wlh duk Wanda akayi wa haka dole ya dau matakin da ta d'auka har gida fa ya Kai budurwarsa dan bashida mutunci ,a madadin ki Masa fada shine kike k'ok'arin fito da laifinta bansan Mai yasa bakya san laifin yayanki ba yanzu da shemau ko Amina akayi wa haka wlh nasan kece gaba wajen cewa Baki yarda ba"

"Fito kawai fili ka dura min ashar Aliyu Kai dama ai bakada mutunci tunda kayi aure kunnuwaka Suka Kara fadi kamar na matarka,nama manta Kai waye na tsaya Ina fada muku na manta bazaku bi bayan dan uwanku ba ai bance muku yayi daidai ba abinda yayi Amma abinda ita lubnar tayi yayi yawa yanzu da auren sukayi da yarinya nan halan haka kishi zai saka ta zuba Mana hauka"?

Duk sun Riga da sun San halin Ammi dan yanzu nan ma sai laifiin Kuma ya koma Kan matansu da suka San hakuri suke da ita hakane yasa Suka ja bakinsu suka tsuke har ta gama ta fice kafin suma suyi waje gabad'aya dan su tafi massallaci mahfuz na dab da fita Ammi ta tsayar dashi tana "Ka tabbata daga massallaci ka jeka ka gano yar mutane idan an sallameta a yau ta dawo nan din ta zauna kafin Iyayenta su dawo"

"Aaa Ammi dan Allah idan an sallameta na bata kudin mota ta tafi wajen danginta ba dai a gidan nan ba yanzu dan Allah idan lubna taji labarin tana gidanmu wlh bazata ji dadi ba zan Kara jawowa kaina matsala ne a wajenta.

Mahfuz Anya haka.yarinyar nan ta barka kuwa"?

"Mun tafi massallaci Kar mu makara yafice daga gidan da sauri yabi bayan yayyensa.

Suna fitowa daga massallaci,Mahfuz cikin kwantar da murya da biyyaya ya hau neman taimakon su ya Alin akan su shige Masa gaba wajen zuwa bawa lubna hakuri,Ya Ali tsaki yaja yayi tafiyarsa Yana ba inda zaije.

Sai Ya Usman ne yayi ta Masa fadan abinda yayi a karshe yace "yarinya nan daka Kai gidanka Sam Bata da tarbiyya karka soma aurenta domin ka aureta wlh sai kayi matukar nadama Taya mace zata biyo namiji har gidan aurensa wanan yarinya sam bata da kamun kai, idan ma so kake ka aureta ka gaggauta fasawa Ina laifin matarka yarinya Mai hankali dududu yaushe ma kayi auren dan masifa.

Sharrin shaidan ne Yaya tsaki Ya Usman din yayi Yana "Ka fara zuwa asibitin ka dubota karfe uku kazo ka sameni a gida sai mu tafi Allah ya kyauta"

Mahfuz machine dinsa ya hau ya nufi asibitin Ya Usman Kuma yaje ya hau motar ya Aliyu suka tafi.

Hadeeza.

Bakin ciki kamar ya kasheta data ga mahfuz baizo ba,Koda ta ce shemau ta Kira mahfuz taji Yana Ina ce mata tayi ta kirasa bai d'auka ba.

Ko baccin bata koma ba har gari ya waye tunani kawai take Yana can kila ma Yana rarrashin Lubnar da ta kusa kasheta ko'ina na jikinta kuwa ciwo yake mata, idan kanin mahaifinta ya dawo sai dai tace Masa hatsari tayi,lubna bata daki banza ba insha Allahu sai ta rama dukan da ta Mata idan ta auri mahfuz sai ta fitar da ita daga gidan,cikin kirsa zata saka Mahfuz ya saketa,dan ta gano logon Mahfuz.

Wajen sha daya taga mahfuz ya shigo fuskarsa a daure.

Shemau na gaishe shi ta mik'e tana "Wlh dama na gaji Yaya ko sallah idi yau bansamu zuwa ba bari naje gida"

Yana Jin idon Hadeeza daya balain kankancewa sabida kumburin da yayi a kansa,ko kallonta baiyi ba dan haushinta Yake ji bashida burin daya wuce ya yakice ta ta barshi ya sarara "Nima ai ba dadewa zanyi ba ai inaga ba wani matsala sallamarta kawai za'ayi yanzu dan na biya ta wajen likita yace ba wani matsala"

"Toh nidai na tafi Yaya sai kun fito"

Tayi waje da sauri sai a lokacin ya kalli ya Hadeeza da take zubar hawaye fuska a had'e yace "Ya jikin naki"?

"Mahfuz sai a yanzu zaka zo wajena"?tun jiya da kuka kawoni mahfuz baka Kara waiwayata ba, kaga yanda matarka ta min lahani kaga fuskata mahfuz duk halin nan da nake ciki matarka ce jefani a ciki amma shine baka zauna dani a asibiti ba sai a yanzu kazo"

"Kinsan halin da Kika jefani a ciki ko Hadeeza kin zubar min da mutunci Hadeeza wanan wane irin rashin hankaline taya zaki saki baki ki fadawa lubna komai har dasu Ina zuba mata magani a lemo dan nazo dakinki Kika ce mata kin bawa Ammi atamfa wane irin rashin hankaline wanan"?

"Mahfuz mutuwa na gani Kai yanzu damuwarka abinda na fada ba lafiya ta ba haba mahfuz matarka kiris ya rage ta kasheni da ban fada mata ba ba abinda zai hana ta kasheni fada ya Kamata kazo kana min Ina cikin wanan halin tsakani da Allah Mahfuz"

"Komai zata miki bai Kamata ki fada mata komai ba kinzo kinsani nayi Abu mutuncina ya zube lubna tayi fushi ta koma gidansu,kin jefani cikin tashin hankali Hadeeza nifa Ina kaunar matata bance Miki bana Santa ba,badan kin dawo rayuwata ba ni ta isheni rayuwa bana bukatar wani Karin Aure Kuma na fada Miki"

"A yanzu Kuma fa"?
Tace tana zubar da hawaye

Mahfuz ya d'auke kansa Yana

Hadeeza bari na karbo takardar sallamarki idan an sallameki sai na raka ki tasha na biya Miki kudin mota zan nemeki idan komai ya daidaita"

"Taya zanje gida a haka bayan na fada maka ba kowa,can gombe ma ba kowa sai dai naje gidanku"

"Hadeeza baza kije gidanmu ba wanan wane irin masifa ne Taya zakije gidanmu da wane Ido kikeso dangina su kalleki a kin gama zuwa gidan aurena kin zauna kin zauna Kuma a gidanmu Zan aureki,sai kace a kudu,a kudu nasan ake haka,mace zata je ta zauna a gidansu saurayi,wannan ba al'adar bahaushe bane Sam,dan haka bazaki zauna a gidanmu ba gidanku Zaki tafi"

Yayi waje a fusace Hadeeza tabi shi da kallo baki a sake,sam bata tab'a tunanin zai Mata haka ba,lailai idan batayi dagaske ba Mahfuz bazai aureta ba,da alama duk Haushin tona musu asiri da tayi yake ji anya Haka lubna ta barsa ba asirice shi tayi ba.

Mintuna da fitarsa sai gashi ya dawo da likita.

Likitan ya duduba ta ya tambayeta inda ke Mata ciwo ta fada Masa kanta ne har yanzu yake balain ciwo.
Yayi rubuce rubuce a takarda ya bawa mahfuz akan a siya Mata magunguna Yana karba yace tazo su wuce su tafi

A wajen tashin haka tayi ta cicije lebbe tana faduwa da gangan taga ko zai taimaka Mata amma ko kallonta baiyi ba har ta saka takalminta ta fara tafiya a hankali tana binsa a baya.

Ta d'auka gidansa zai kaita ta kwaso kayanta tana so taje taga ko Lubnar na nan, sai dai suna zuwa ya tsayar da abin hawa akan ya kaita gidansu zai aiko Mata da kayanta yaki bari ma ya kalleta ganin Yana k'ok'arin tafiya yasa ta ruko hannunsa tana "Ya zancen Aurenmu mahfuz"?

"Allah ya Mana zabin daya fi alheri"

Yace tare da fusge hannunsa daga nata......

Kuringa hakuri dani wajen posting din Daren da nake a lokacin nake da time

Don't share my novels plc
Are you guys looking for where to buy ur skincare product @ mg's skincare is the best plug for you🤗
Do you wish to have that flawless skin that's free of all skin prblm
Do you wnt to achieve that milky skin that turn heads wherever you go😉
Try mg's product nd I assure you you'll never use any other product except mg's product✅
Mg's will gv you the best out of all
With mg's product ur skin is 💯 clear,fresh,smooth nd ur skin will absolutely glow all day💃
We have herbal whitening black soap now nd beauty set available
Nd both the soap nd the beauty set is for all skin type everyone can use it🤗
Just gv it a try now nd see wonders✅
Chat:08062991549
07046881166
Call:08064532391
Soap price:3k
set:11k

Follow us on
Instagram@glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare

what are you guys waiting for hurry nd grab urs💃 now is the time to glow🧖‍♀️
Pamper ur skin🦵
Shine like a bride 👰
be part of the glow team karkubari abaku lbr
Just chat 08062991549 to plc ur orders😘

Do not forget to follow us👆
Like nd comment pls dearies😘
Patronize us🙏
mg's always serve you the best✅❤️

*WANAN NOVEL DIN NA KUDINE BIYA 500 zuwa 2029764071 first bank nafisa Nuhu sai a tura shaidar biya zuwa ga lambar Nan 08033719070 ko katin mtn mutanen Niger Airtel Kika min sharing idan bansanki ba Allah Yana kallonki na barki dashi*

*Bm*

*Na Sadnaf*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.