Budurwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Budurwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 2 of 16
*PAGE 2*
Bansan tsawon lokacin dana d'auka a durk'ushe a kasa ba,zuciyata Kamar an cinna Mata wuta ban tab'a sanin haka nake da tsananin kishi ba kawai Ina hararo irin so da kaunar da mahfuz yake gwadamin ya fara gwada wa wata,har ta d'auke Masa hankali a kaina akanta ya cemin wawiya Mara hankali waya sani ma ko zance yake zuwa wajen tsininiyar yarinya da ta Kira mahfuz da sugar,har san da yake Mata ya Kai Muna kwance ya baroni a daki ya fito Palo dan kawai yayi waya da ita.
Ko dan na samu ciki hallitar jikina ya canza yasa mahfuz ya fara ganin munina
Tunanin daya darsu a raina yasa na m'ike a hankali na nufi wajen da mudubi yake na fara karewa kaina kallo tunda ga saman goshina tare da shafa fuskata.
Tunda na samu ciki wani irin kananan pimples suka feso a fuska ta suka Sakani Muni,siririn lebbena yayi kauri.Haka hancina da bai fiye tsini ba ya doke nasan cikin nan yasani muni ba kadan ba fari dai na Kara tunda ni fara ce.Baza'a sakani a sahun masu tsayi da kyau sosai ba akan dai mahfuz za'a sakani a sahun masu kyau duk da mace sai ta dan yi kwalliya kyaunta ke Kara fitowa.Kwalliya da nake yi yasa ake ganin kyauna sosai. mutum tara yake bai cika goma ba abinda na rasa shine nono banida cikar kirji Sam idan na ga mace mai kirji sai naji Kamar na sace ko dan mahfuz da sai da muka yi aure na fahimci Yana balain san no-no,kafin na samu ciki indai Muna zaune hannunsa na saman kirjina Yana shafawa wai idan ana yawan shafa shi Yana fitowa.Bansan Yana san nono ba sai da naga ya fara siyomin duk wani cream ko supplement akan na ringa Sha zai taimaka wajen fitomin da nono.Ba abinda banyi amfani dashi dan nono ya girma ko dan na farantawa mahfuz rai amma abin ya gagara daya ga na fara matsawa kaina ya ce min na daina takura kaina duk da haka burina na samu nono na ya girma idan na d'auke nonon ba wani abu a jikina da baya burge mahfuz.Idan ya dawo bashida wajen kwanciya sai a jikina ya gwadamin kaunar daya narkar dani a kogin Sansa burina bai wuce nayi abinda zan faranta Masa ba Koda bana so har na samu ciki banga canji a wajensa ba duk da mitar da nake akan cikin ya sani muni hakan na iya sawa mahfuz ya rage ji dani.Idan na ce masa nayi muni dariya yakemin yace shi bai gani ba ai cikin nan yasa kirjina ya ciciko,bamu tab'a fushi da juna ba,bamu taba sa'insa ba,bai tab'a gaya min bak'ar magana ba sai gashi wata Yar iska tana neman juyar min da kwakwalwar miji bansan adadin tsinuwar da nayiwa macen da ta Kira shi ba.Gajiya nayi da tsayuwa agaban mudubin na koma Kan gado na kwanta Ina sak'e sak'en yanda zan biyowa mahfuz ni nasan idan ya dawo dole ya bani hakuri dan baya iya dogon fushi dani dole na nuna Masa bacin raina na Kuma jawo shi jikina na binciki wayarsa nayi blocking din Yar iskar yarinya da take kiransa,da Wanan tunanin na samu nayi wanka abincin ma da kyar naci sabida b'acin rai,sai duba wayata nake naga ko zai kirani ko zaimin text,har watsapp na hau naga ko ya ajiyemin sako duk shiru,hakan kuwa ya Kara saka min Jin haushinsa na tanadi masifar da zan Masa idan ya dawo.Kamar bazan yi girkin dare ba na daure na dafa jollof din shinkafa na hada Masa zobo.Nayi kwalliya kamar yanda na Saba na zauna zaman jiransa raina a had'e.Mahfuz bai dawo gidan ba sai goma da rabi na dare Ina Jin sa ya shigo da machine dinsa.Ciki ciki yayi sallamar ya hade rai da leda a hannunsa bai Kuma Kalli inda nake ba.Baki sake nabi shi da kallo har ya shige daki mamaki da bakin cikin halin ko inkular da ya nuna min ya rufeni,Mai mahfuz yake nufi dani yamin laifi ya nade tabarma da kunya a zuciye na tashi zan bishi har d'akin.
Kafin na isa d'akin na tsaya Ina bin umarnin zuciyata dana watsar dashi zai nemeni da kansa.
Da wanan tunanin na nufi daya d'akin da idan ba baki muka yi ba ba Mai kwana a ciki.Nan na shige zuciyata na balain tafasa
Duk abinda nayi dan na samu zuciyata tayi sanyi duk a banza kofa kawai nake kallo ko zanga shigowarsa yazo bani hakuri ga yunwa da nakeji amma bana jin cin abincin.
Watsapp na hau sabida na samu nayi hira da Yan uwana da muke grp daya ko zan samu na rage bakin ciki dake Raina sai dai Ina hawa na duba mahfuz naga Yana online,wato ba abinda ya dame shi ni nasan da Yar iskar yarinya yake hira.Ban iya hakuri ba na rubuta "Mahfuz yanzu nice abar wulakantawa a wajenka ko,"?
Bai bud'e sakon da wuri ba na fara k'ok'arin Kara rubutu naga ya bude ya turo "hmmmmm"
Bakin cikin bazai iya bani hakuri ko ya biyoni daki ba yasa na kashe data na wurgar da wayar,Idona akan agogo har karfe daya na dare sai juyi nake ba alamar bacci zai daukeni sai tunani daya cike min zuciya tunda mukayi Aure bamu taba raba shimfida da mahfuz ba sai gashi a sanadin haduwa da wata nayi fushi dashi bai ma kalleni ba.
Hawaye kawai ke zubomin Ina tsinewa macen da ke san Shiga tsakanina da mahfuz har ta samu matsayi haka a wajen mahfuz da zai k'i nemana a kanta sai da cikina ya tsufa mahfuz ya fara daga min kafa amma ko yayane sai ya nemeni ko period nake sai na Masa dabaru har hirar na tab'a yi da wata aminiyata take cemin namijin da baya iya daga ma kafa ba karamin gamsar dashi ake ba.Amma mahfuz yamin laifi akan Ina kishinsa bai iya bani hakuri ba,nifa yayi wa laifin nan amma shine ya kasa bani hakuri.Har tunani na Kara yi a tsanake dan naga ko dai zaginsa nayi cikin fushi batare da nasani ba sai dai banda karya tashi da nayi na zagi tsinaniyar da ta kira ban Masa komai ba.Zuciyata raya min kawai yake akan naje d'akin na sameshi wani b'ari na zuciyata na hanani akan shi yamin laifi shi ya Kamata ya nemeni.Haka na kwanta zuciyata kamar tayi bindiga dan bakin ciki sai biyu da wajen rabi na dare bacci yayi awon gaba dani. Ban tashi bude Idona ba sai wajen bakwai da minti goma Sha biyar.Na Mik'e da sauri Ina sallati na tsani naga sallah asuba ta kubcemin.Da balain sauri na fada bandakin na daura alwala na fito.Sai dai banida hijabi a dakin bana san zuwa dakina naga mahfuz sai dai ya zama dole tunda ba hijabi a d'akin.Fuskata a had'e na nufi dakina a hankali na tura k'ofar na shiga.Bangan shi a dakin ba na dai jiyo motsinsa a bandakin da alama wanka yake.
A madadin na d'auko hijabi na wajen da na hango wayar sa a saman bedside drawer na nufa da sauri na dauki wayarsa na fita daga dakin na koma daya d'akin na saka key na zauna a saman gado hannuna sai rawa yake.Ko da na bud'e wayar ajiyar zuciya na sauke da naga ba password.Message dinsa na fara shiga SR da na gani ta turo message da bai bud'e ba yasa na bud'e message din jikina na balain rawa Message ta turo.masa wajen biyar na asuba da alama reply ta Masa "Kayi hakuri sugar banga kiranka ba sai yanzu kasan jiya ban kwanta da wuri ba how was your night my love zaka biyo d'in I missed you"Hannuna rawa kawai yake kirjina Kamar ya fado ji nake ma dakin na juya min"Lubna ki bud'e min k'ofar nan sabida Mai zaki zo ki dauki wayata?Wai me yake damunki ne"Najiyo mahfuz a bakin k'ofa Yana jijjiga k'ofar.Rawar da jikina keyi yasa ban ma iya mik'ewa ba na nemo lambar SR na fara kiranta a wayarsa bugu daya ta d'auka murya can kasa tace "Sugar ka iso ne"?"Kutumar bura ubanki tsinanniya ya iso wajen ubanki shegiya laananiya"Kit naji ta kashe wayar na Kara kiranta bata d'auka ba,ban hakura ba na cigaba da kiranta Mahfuz kuwa sai jijjiga kofa yake Yana kwalla min Kira akan nazo na bud'e k'ofar na bashi wayarsaGanin tak'i d'aukar wayata yasa na m'ike jikina na rawa naje na bud'e k'ofar mahfuz ya fado dakin da sauri ya fusge wayarsa daga hannuna idonsa ya Kada yayi jajjur cikin k'ak'ausar murya yace "Daga yau karki Kara tab'a min waya lubna wlh Kika Kara sai ranki ya b'aci kinji na fada miki"Ya fara k'ok'arin juyawa ya bar dakin na Sha gabansa da sauri hawaye na zubomin
"mahfuz mai na maka da na cancanci haka daga wajen ?Mahfuz jiya baka san a ya na kwana ba amma ka kira wacce ba matarka ba dan kaji lafiyarta Kuma har zaka biya ka ganta kafin kaje wajen aiki, Mahfuz Kaine kamin laifi Ina gefenka ka fita Palo dan kayi waya da mace dan na tambayeka da wa kake waya ka rufeni da fada ka kirani wawiya mara hankali laifine dan nayi kishin ka har yaushe muka yi auren da zaka min haka?Ina duk alkawarikan da kayi min a baya Koda zaka kula mace mahfuz bazaka kwantar min da hankali ko dan cikin jikina ba? kayimin adalci kenan"?
Na karashe hawaye na zubomin
"Lubna kina da matsala shikenan dan kinji.ina waya da mace sai ta zama budurwa ta,kinsan ya muke da ita da zaki zageta ne?wajen aikinmu daya da ita kuma ba komai a tsakanina da ita sai Yar tsokana amma sabida balai kin dorawa kanki kishi,har kina Neman zagina,wane bayani kikeso na miki?
Mamakin maganar sa ya sa na kasa motsawa na zuba Masa Ido har ni zai cewa ba budurwarsa bace shi kuwa ganin ban magana ba yace "ba wani abu a tsakanina da ita ke kikesan ki dorawa kanki abinda ba haka ba,abinda yasa jiya ban waiwayeki ba naji Haushin karyatani da kikayi bai dace na miki magana ki karyatani ba har kina neman zagina kina nufin baki yarda dani ba kenan,nidai zanje wajen aikii dan na makara daga haka ya ratsa ta gefena nabishi da ido har ya shige ko minti biyar baiyi ba ya fito daga d'akin ganin Ina hawaye Ina Kuma tsaye ban motsa ba ya iso wajen da nake tsaye yana "Kina nan a matsayin da Kika sanki a zuciyata ba Wanda ya Isa ya kwaceni a wajenki gwara ki kwantar da hankalinki daga haka ya sunkuyo yamin kiss a kumatu ya juya Yana "Sai na dawo"
Lumshe idona nayi Dana shaki kamshin turarensa kukan da nake dannewa ya kwacemin har ga Allah ni nasan Mahfuz soyayya yake yi da wata amma yake San raina min hankali Ina balain San mijina dama yarinya nan ta barni da mijina ta nemo wani nayi nadama da ban dauki lambarta a wayarsa ba.
Ban tab'a tunanin mahfuz zaimin haka ba
A daddafe nayi Sallah na dumama abincin da mahfuz baici ba naci dan yunwa nakeji.
Sai da na gyara ko'ina nayi wanka na zauna Ina tunanin hanyar da zan bi na raba mijina da SR dinan da take neman d'auke min hankalin Miji.
Kiran aminiyata farinciki rayuwata abokiyar sirrina ce ta katse min tunanin da nake mahaifiyata banida wacce tafita duk duniyar nan ba abinda nake boye mata a haka na taso sabida yanda take jana a jikinta ba Kuma Ni kadai ba haka duk kannena,koda na tashi aure ajiye kunya tayi a gefe ta karantar dani rayuwar aure da yanda zan kula da mijina.
Mahaifiyata a waye take dan nurse ce bama na iya boye mata komai.
Ina sallama na hau gaisheta bata amsa ba tace "Mai yake damunki Lubna"?
Kamar Mai jiran kiris na fashe mata da kuka.
Sai da naci kuka na na koshi bata hanani ba ba ta kashe wayar ta ba Jin na tsagaita tace "Ina jinki lubna mai yake faruwa"
Tiryan tiryan na kwashe komai na gaya mata ba abinda na cire har yanda mukayi da Sr din da bansan sunanta ba sai da na gama tsaf ta sauke ajiyar zuciya tana "Wlh bansan bakida wayo da tunani ba sai yau,Lubna waye ya gaya miki ana yiwa namiji haka,waye ya gaya miki ana fada da budurwa Miji a waje,salon ki jawowa kanki raini,daga lokacin da Kika d'auko wanan hanyar kin kashe kanki da kanki ai komai dan wayo ne da dabara wlh na raina wa wayon ki Lubna,ai kiyi fushi da mijinki ko kiyi gaba dashi dan kin gano Yana da budurwa ba shine mafita ba dan kin nisanta kanki daga wajensa ne kin kusanta shi da budurwar tasa dan su maza haka suke Abu kad'an ka d'auke musu hankali,daga lokacin da Kika fara wanan haukar fita zaki nayi a zuciyarsa ya fara ganin aibunki,waccen kuwa dama burinta ta samu ta kwace shi, karki sake wanan gangancin yanzu damara zaki daura ki jawo mijinki jikinki cikin kirsa ki rabashi da wancan yarinya cikin ruwan sanyi,ki rubanya kyautatawarki a gare shi.
Ai ke mijinki ma Yana shakarki tunda a boye yake Mata waya kinsan akwai mazan da agaban matansu zasu yi wayar sai dai ta hadiyi zuciya ta mutu.
Ki nesanta kanki da tab'a wayarsa ko da Kinga an turo masa text an Kira karki sake ki nuna Masa kingani cikin salo zaki rabashi da ita, kiringa kai zuciyarki nesa kishi hauka yake sawa da tarin nadama, kifita a zuciyarsa yaji ma gwara yayi auren kawai tunda kin k'i ki kwantar masa da hankali,ba dai text take tura masa ba kema sai ki dage wajen tura masa,Yana fita ki kirasa kiji lafiyarsa sau uku kafin ya dawo anan zaki ga hankalinsa ya fara rabuwa gida biyu har kiyi nasarar dauke masa hankali akan wacce yarinya ki fito da salo salo na soyayya da bai sanki dashi ba kiga ikon Allah"
Sai da muka shafe awa daya mahaifiyata na bani shawara na Kuma ji dadin shawarawarin da ta bani duk da ba k'aramin dauriya zanyi ba dan Ina da tsananin kishi bana iya controlling kaina idan ya motsa min.
Koda muka gama waya wacce take min lalle na Kira akan tazo tamin na Sha damara dawo da hankalin mahfuz kaina insha Allahu sai na raba shi da SR dinan
MAHFUZ
Allah Allah yake ya isa gidansu Hadeeza dan ya bata hakuri tunda ya fito daga gida yake kiranta a waya taki d'aukar wayarsa.
Koda ya iso k'ofar gidansu ya cigaba da kiranta a waya bata dauka ba sai da ya mata text akan ya iso Yana waje ta fito Yana jiranta.
Sai da aka kwashi mintuna wajen goma Kafin ya fara shako kamshin turarenta daya saka shi lumshe Ido ya bud'e Idonsa a hankali ya zuba Mata tana daga bakin k'ofa a tsaye ta harde hannayenta a kirjinta ta had'e Rai......
*mg's skincare*
Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Then @mgs skincare gat you covered 💯
Now is time to glow😍
Pamper ur skin🦵
Shine like bride👰🏻♀
Glow🧖♀️
💯 tested nd trusted🤝
Guarantee
Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166.
*BUDURWAR MIJINA*
*NA SADNAF*
*E.W.F.*
*PAID BOOK*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.