Complete Hausa Novels

Budurwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Budurwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 8 of 16

*PAGE 8*

Koda isarsa a karamin palon gidan da suke zance yayi zamansa Yana jiranta,tun kafin ta iso palon ya fara jiyo kamshin turaren ta, Hadeeza ba baya ba wajen saka turare a ransa Yana so ya nuna mata rashin Jin dadinsa da zuwa gidansu da tayi baya san garajen nan da takeyi yafisan su bi komai a hankali yasan Yana santa amma har ga Allah da san zuciyarsa ne babu bukatar wani Karin Aure,Sam baiji dadin yanda lubna duk ta dago halin da yake ciki da Hadeeza ba tun a jiyan ya daura damarar canzawa wajen iya takunsa sam bayaso ta ringa Jin kamar ya daina santa,yasan tana iya k'ok'arin ta wajen faranta Masa

Sallamar da Hadeeza tayi cikin takunta najan hankali ya katse masa tunanin da yake ya dago idonsa Yana kallonta har ta samu waje ta zauna ta sakar Masa murmushi,dayasa ta kashe Masa jiki kwana biyun nan tana shigar dake dan bayyana surarta.

"Sai yanzu ka tuna dani,jiya ko bacci banyi ba dan banji muryarka ba"

"Lubna ta haihu fa an samu bby girl shiyasa Sam jiya ban bi ta Kan waya ba"

Sai da ta dau tsawon lokaci kafin ta daure ta saki murmushi dan Addu'a tayi a ranta dama mutuwa lubnar tayi da tazo haihuwar

"Masha Allah Allah ya Raya mana ita kace na samu takwara"

"Sunan lubna na saka Mata zaa ringa kiranta Mimi ashe kinje gidanmu dazu"?

Kamar ya watsa Mata ruwan zafi dayace sunan lubna ya sawa yarsa dan taji labarin idan har miji yasa wa yarsa sunan matarsa ba karamin kaunarta yake ba,bata so ta nuna Masa rashin Jin dadinta yak'e tayi tana "Eee dazu naje na gaida mama tunda baka tab'a cewa muje na gaisheta ba"

"Dama kinsan gidanmu ne"?

"Tunda har nasan gidanka sanin gidanku bazai min wahala ba Mama nada kirki wlh tayi min tarb'a Mai kyau da dukan alamu na samu karbuwa a wajenta ba nida wani fargaba"

"Hmmm ai da kinn fada min zakije kila akwai shirin da zanyi kafin kije din amma tunda kin riga da kinje shikenan tace na miki godiya"

"Ba wani damuwa ai nima mahaifiyata ce"

"Hadeeza"

"Naam"

"Magana nakeso muyi mai mahimmanci Ina fatan Kuma Zaki fahimceni"

Gaban Hadeeza yanke wa yayi ya fadi duk tunani take mahfuz cewa zaiyi tayi hakuri bazai iya aurenta ba bata iya cewa komai ba ta zuba Masa Ido

"Kinsan dai Ina sanki Ina Kuma kaunarki,fatana Allah ya mallaka min ke Babu yaudara a tsakanina dake,da ace bana kaunarki bana Jin zan tsaya na ringa b'ata Miki lokaci ina b'atawa kaina,saura wata hud'u na samu shekara biyu da aurena,kafin ki dawo rayuwata wlh banida wani plan din auren Mata biyu a nawa tsarin mace daya ta isheni rayuwa sai dai idan Yana cikin kaddara ta sai na Kara Aure,Hadeeza Kamar yanda Kika sani a baya ni ba wani shahararren Mai kudi bane da na tada kai,rufin asiri gareni rayuwa ta a saukake nake yinta,kina kallo ko mota har yanzu bani dashi,dama burina bai wuce idan lubna ta haihu na fara tunanin yanda Zan samu motar ba,banida wani gida daya wuce Wanda Lubna ke ciki sai wani fili da na siya nida wani abokina Abdul komai a rayuwa sai kana tsarawa yanda bazaka yi abinda zai takura ka a yanzu nauyi ya Kara hawa kaina.tunda na fara tara iyali,Hadeeza abinda yasa nake Miki wanan maganar naga kin matsu kina so ko a yayane na turo muyi aure, inaso kisan komai sai da plan bana so muyi gaggawa ko garaje,inaso mubi komai a hankali a yanzu da Allah ya kaddara Zan aureki Zan fara shirye shiryen yanda Zan zauna da Mata biyu,dan haka zanzo na samu Abban naku yasan da maganar auren a bani lokaci na samu mu tsara komai,na biyu ba zancen Ina tsoron matata bane ko wani abu,inaso mu canza taku yanda ba zaa ringa saurin dago mu ba,wayar daren nan da mukeyi inaso mu hakura da wanan wayar,
Idan na fito daga gida Zan Kira ki da kaina.

kema kinsan Ina samun sarari Ina baki lokaci sosai a wajen chatting wanan shine maganar kawai dafatan Kuma zaki fahimceni"

Ba karamin dauriya tayi ba wajen danne zuciyarta cikin yak'e tace "Na fahimceka wlh ba wani damuwa zan daina kiranka idan kana gidan kamar yanda ka bukata amma inaso kasan cewa wlh ba sharri a zuciyata bansani ba ko matarka wani abu tace maka kazo kake min maganganun nan"

"Aaa wlh ba abinda tace min kawia naga ya dace yanda nake baki lokaci itama na ringa bata lokacinta Kinga bai dace na ringa shiga hakkinta ba ko"

"Eee hakane kuma"

Tace cikin yak'e tana "yaushe zanzo barka ne kaga ya Kamata naje naga 'yata"

"Kai aaa Zan kawo Miki ita idan ta fara wayo"

"Kasan kuwa next week su Abba zasu tafi umara wlh dukansu har da yaran ni Kuma wai na koma gida idan sun dawo sai na dawo"

"Allah sarki kice zanyi missing dinki"

"Tab ai ba Inda zani bazan iya kwana biyu banganka ba wlh"

Dariya mahfuz yasa Yana "toh ya zaayi kenan"?

"A jaka zan saka ka mu tafi can"

Hira kawai suke mahfuz Sam baima San lokaci ya ja ba sai da aka fara Kiran sallah magriba yaso daga massallaci ya wuce gida Hadeeza ta hana shi har sai daya ci abincin dare a gidan.

A lokacin daya isa gida har Lubna tayi bacci.

Zainab da Aunty Sa'a kanwar mahaifiyar lubna kuwa Suna daya d'akin Yana jiyo hirarsu.

Wanka kawai yayi yazo ya kwanta ganin Lubna na bacci yasa ya kunna data Suka hau chatting da Hadeeza da ta ajiye masa message rututu na irin kaunar da take Masa ta hada da ya turo mata hotunan baby.

Sai da ya fara Jin bacci yayi Mata sallama ya kashe wayarsa.

LUBNA

Ba laifi naga canji daga wajen mahfuz tunda na haihu,ban sake ganin yayi wayar dare ba,idan ya dawo gida baya sake fita har a raina naji dadi Inda na ringa addua Allah yasa ya dore a haka Allah yasa ya rabu da wanan tsinaniyar budurwar tasa,har bincike nayi a wayarsa na shiga message dinsa da watsapp banga alamar lambarta ba a wayanda yake Hira dasu yafi hira da Abdul na Kuma ji dadi sosai.

Ba laifi ya min dinki masu dan kyau da tsada daidai karfinsa duk da mummy ta riga da tamin dinkin fitar suna haka ma ta kusa cikowa mimi akwati da kaya.

Hankalina kwance muka Sha Suna a ranar sunar ba inda Mahfuz yaje Yana nanike dani,Muna ta hotuna.

Ko kunyar mutane bayaji da suka cika gidan,har anko mukayi dashi na wani blue shadda munyi kyau sosai Koda ba'a fada ba.

Zuwan mahaifiyarsa Hajiya Ammi da ta had'e rai tana dan harararsa yasa ya bar wajena yayi waje.

Koda na gaisheta Mimi kawai ta karba daga hannuna ta amsa gaisuwar ciki ciki nakan yi mamakin yanda take min,Banda matan yayyen mahfuz nace min haka halinta yake da nace sona ne batayi.

Yan uwana sai da suka tayani kintsa koina Kamar ba'ayi taro a gidan ba kafin suka tafi Aunty Sa'a Dai sai ta Kara kwana biyu kafin ta tafi.

Mahfuz

Yaji dadin hadin Kan da Hadeeza ta bashi wajen daina damunsa a waya suna gama chatting yake gogewa gudun kar Lubna ta masa bincike a waya ta gani yafiso ta dauka sun rabu da Hadeeza Sam bayasan ta ringa zarginsa tana dagawa kanta hankali.

Ranar suna da Mai kwalliya tazo ta rangada wa Lubnarsa kwalliya ba karamin kyau ta masa ba hakane yasa yayi ta zuba musu hotuna a wayarsa da mimi.

Hotunan dayafi kyau ya zab'a ya Dora akan status da rubutun "Allah ya Raya mana Mimi ya baki lafiyar shayarwa Rabin Raina

Ko minti biyar baiyi da sawa ba sai ga Kiran Hadeeza a wayarsa.

Bai kawo komai ba ya daga wayar

Kukanta ne ya karade wayar

Sam baisan Mai yasa ta kuka.ba hakane yasa a rude ya hau tambayarta lafiya mai ya faru bata ce masa komai ba ta cigaba da rusa kuka.

Katse wayar yayi ya haye machine dinsa yayi gidansu dan bata tab'a kiransa tana rusa uban kuka haka ba.

A lokacin daya iso gidansu sai daya dade Yana jiranta kafin ta fito idonta ya kada yayi jajjur.

Mik'ewa yayi da sauri dan ya d'auka ko wani ne ya mutu da sallati yace "Lafiya kuwa Hadeeza Mai faru

A wajen kafarsa ta zauna ta Kara fashewa da kukan

Ya zauna da sauri.yana "Hadeeza wai Mai yake faruwane"

Dagowa tayi kafin ya ankara ta jawo hannunsa ta manna a kirjinta "kaji zuciyata Mahfuz kaji yanda yake bugawa,Ina da kishi mahfuz hotunan nan daka dora ya daga min hankali mahfuz anya kana Sona kuwa"?
Tunda muke da Kai baka tab'a dora hotona ba"

"Wai wane hotone ya daga Miki hankali hoton nida Lubna ko me"?

"Gyada Masa Kai tayi har lokacin Tana kankame da hannunsa ba hotunan da sukayi tare da mahfuz ne ya daga Mata hankali ba bata kawo Lubnar ta kai haka kyau da haduwa ba,bata ga abinda zata Gaya wa Lubnar ba,sai taga ma kamar ta girmi Lubnar Sam ta kasa danne kishinta har sai data Kira mahfuz din,gani take mahfuz na iya kubce Mata kowane lokaci,tundaga lokacin daya kafa mata sharadin kiransa a waya,ta tsorata dashi,dan taga dagaske Lubna nada wani irin matsayi a wajensa abu.kadan na iya sawa mahfuz yace ya fasa aurenta.

Tsananin mamakin Hadeeza yasa ya saki baki Yana kallonta kallon Anya ma tana da hankali kuwa hoton lubna ne bataso ya dora ko me

"Yanzu ke kishin lubna kikeyi har dasu kukan ki yanzu laifi ne dan nayi hoto da matata matata ce fa ba wata ba"?

"Mahfuz bazaka gane ba nidai dan Allah kayimin alkawari bazaka rabu dani ba duk runtsi duk wuya"

"Wai duk hoton namune ya rudaki haka,lailai kinma fi lubna kishi to bakya so muyi hoton ne ko me"

"Ni ba haka nake nufi ba"

"Toh Mai kike nufi"

"Nidai kayimin alkawari bazaka rabu dani ba"

Girgiza Kai mahfuz yayi Ya hau dariya dan dariyar ma ta bashi biye mata yayi yace yayi alkawari kafin ta yarda ta cika Masa hannu tace Masa tana zuwa.

Bayan minti goma sai gata ta dawo cikin kwalliya ta Sha shadda pink mai duhu ta kashe dauri,

Da ido yake binta har ta zauna a gefensa kafadarta na guga nashi ga kamshin turarenta nan ya bade ko'ina.

Bai san mai take nufi ba sai da ta d'auki wayar ta tana "nima hotunan zamuyi naji dadi dama bamu tab'a hoto ba tace tare da daga wayar murmushi kawai yayi ta hau yi musu hotuna har tana dadafa shi kamar irin couples dinan da basu Dade da Aure ba.

Shi dai biye mata yayi sukayi tayi har da su videos sai daya gaji ya kwace wayar daga hannunta yana ya isa haka.

Jera hotunan ta hau yi status sai duk yaji hankalinsa bai kwanta da dorawa da tayi ba duk da yasan Lubna ba saninta tayi ba yanzu idan ya ce ta cire sai ta masa wani fassarar.

Yanda take wani nanarke Masa tana neman daga Masa hankali a banza yasa ya mik'e yace Mata zai tafi.

Sai da ta raka shi har waje ta Kara komawa ciki ta d'auko leda mai dan girma ta bashi tana ya kaiwa yarta.

Yakan yi.mamakin Inda take yawan samun kudin da take kashewa haka,duk da yasan shima Yana tura Mata kudi Dan Yana da acct number dinta sai dai kudin daya ke tura Mata bai Kai yawan hidimar da take dashi ba har dinkin shadda ta Masa da agogo da turare mai tsada lubna duk ta d'auka shi ya siyo da kudinsa.

Godiya yayi Mata bayan ya roketa da daina dorawa kanta wahala haka.

Koda ya isa gida a zaune ya tarar da Lubna tana shayar da Mimi yanda ta zubo Masa Ido yasa yaji duk ya tsargu sai yake ganin kamar zata gane wajen Hadeeza yaje.

"Ina ta gwada wayarka tundazu Ina ka shiga ne"?

Nace Ina Kare Masa kallo nidai duk da ban Kara Kama shi Yana waya ba idan har ya dan Dade a waje sai naji kamar zance yaje.

"Ina can gida mun hadu da Yaya Mustapha"

Ya mik'o min ledar hannunsa "ga Kaya nan inji wani abokina"

Karba nayi na bud'e na fara fito da kayan ciki,kayane masu kyau da tsada wajen kala biyar sun balain yimin kyau

"Wane abokin naka ne ya Mana abin arziki haka"?

"Baki San shi ba a wajen aikinmu yake"

"Aikuwa ya kyauta sosai kayi Mana godiya"

Kai kawai ya gyada min ya hau Wasa da mimi.

A yanzu dai Zan iya cewa banida wani matsala Ina samun kulawa sosai a wajen mahfuz, tuni hankalina ya fara kwanciya dan da alama yanzu baya tare da yarinya data so saka min hawan jini sau tari na Sha Masa bincike ban ga alamar bakon lambar da bansani ba.

A yau da nasamu sati biyu da haihuwa baifi saura kwana shidda ayi babbar sallah ba bayan fitar mahfuz wajen aiki ya kirani a waya akan Abdul Yana hanya zai zo ya shigo garin na tanade shi.

Nasan yanda Abdul yake a wajen Mahfuz aminan juna ne Yana da balain kirki Nima Ina matukar ganin mutuncinsa,baya Wasa da duk wani abu daya shafi Mahfuz duk da baya garin na haihu sai da ya hada kayan barka ya aiko Mana dashi.

Kitchen na Shiga da kaina na fara k'ok'arin dafa fried rice a cikin awa daya na kamalla komai na gyara gidan zainab bata Nan taje gida ta dawo.

Wajen karfe biyu naji sallamarsa tare da bugun k'ofar gidan.

Hijabina na saka har kasa,naje na bud'e k'ofar fuskata d'auke da murmushi.

Tsokanata ya fara yi Yana "Uwargida sarautar mata"

"Dagani ba kari insha Allahu na karashe Ina "toh ashe da amaryarka kake tafe aa lalle marhaban shigo shigo.

Nace Ina bawa macen dake biye dashi a baya fuskata washe ita kuwa sai wani sunkuyar da Kai take hannunta janye da dan madaidaicin trolley.

Suna Zama na dauko musu ruwa da lemo Ina satar kallon budurwar Abdul din bana iya ganin komai na jikinta dan hijabi tasa har kasa fuskarta ce kawai a waje kyakyawa ce ba laifi.

Mimi kuwa na hannun Abdul Yana ta mata Wasa "wato ka gaji da gorin auren da muke ma kenan"

Nace ina tsokanar Abdul daya gyarawa Mimi Zama a jikinsa Yana "Tukunna dai wlh har yanzu ban samu wacce ta kwanta min ba wanan ai 'yar babar yayar mu ce da suke zaune a Lagos inaga mahfuz ya tab'a baki labarinta lokacin dayaje can Lagos din ko"?

"Kwarai kuwa ya tab'a bani labarin yayarka ta Lagos"

"Toh wanan yarta ce ta fari.

Ta shigo garin nan ne zatayi wani training na kwana goma,shine nace bari na kawota nan ta zauna idan ba damuwa"

"Haba haba ba wani damuwa wlh ai an Zama daya fatana dai ta saki jikinta Nan ma gidane ai"

Muka hada ido da ita ta sakar min murmushi tare da sake sunkuyar da Kai,nikam yanayin ta ya burgeni da alama tana da nutsuwa da kamun Kai.

Sai da suka ci abinci na Kai mata akwatin ta daya dakin.

Muka dan tab'a hira da Abdul kafin yamin sallama.akan goben nan zai koma ya ajiye min kudi Mai yawa na hau yi mishi godiya har bakin k'ofa muka raka shi nida ummi bakuwar da mukayi sabida tsiya irin na Abdul Ashe bai fadawa mahfuz zai kawota ba Wai Idan ya dawo na fada Masa.....

Wanan novel din na kudine a page 10 zamu gama free pages biya 500 dan ki samu kicigaba da karatunki cikin sallama tura 500 ta 2029764071 first bank nafisa Nuhu ko ta wanan 0000551222 Taj bank nafisa Nuhu turo da shaidar ta wanan lambar 08033719070 ko katin mtn ta wanan layin 08033719070 karku bari a barku abaya.

KAYAN MATA

Assalamualaikum kina mace hadaddiya komi kincika ama kinada nakasu tawurin dadadawa miji?

Shin kinkai kin isa kina gogayya d sauran mata Amma tafannin ozaroom mishkila tasamu?

Shin sanyi y addabeki tayanda Baki iya gamsarda miji kullum kina makalemai yana kauda Ido?

Shin minene matsalar?
Kinshiga ko Ina kinnemi magani bawani chanji?

Tosaurara yar uwata aminiyar arziki, ubangiji yakawo mikini har inda kike,kizo kiji qawata,

Inada maganin sanyi me fatattakar kowani irin sanyi duk fitinarshi d izinin ubangiji seyabarki,

Munada magungunan mata masu matuqar kyau,hadaddu gangariya kizama t gaban goshi,komi kikace oga yace don, 🥰 kikerewa sa'o'i, kizama abun riritawa abun tarairaya a kudi qalilan,karki cuci kanki kizauna kina cewa ayni nasan kaina,a inadin? Wallahi ko kanada kyau qara d wanka Kisha kiyi qattt kigigita oga,

Munada tsumi nau'i nau'i
Gumba ta madara,ridi,gyada,dabino,kwakwa,dasauransu
Akway ruwan jaraba
Ruwan Dadi
Hadin minannas
Hadin dafa kaza(manta uwa)
Hadin yar gaban goshi,
Turarukan mallaka.

Duk a farashi mesauqi.

Serious buyers call, WhatsApp 07046881166

Senajiku kusiya kuyi godiya Kuma kumin addua❤️nagode
*BUDURWAR MIJINA*

*NA SADNAF*

*E.W.F.*

*PAID BOOK*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.