Complete Hausa Novels

Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 5 of 8

*Shafin nakune my aunties Aunty Maijidda musa tare da aunty jamila gombe, sosai nake godia da karamcinku gareni Allah yabar k'auna Amin.lallai kusani Inaji daku ainun acikin ruhina*❀😘

*11~12*

Suna shiga Addawiyya tana sakkow abisa gadon. atare suka rungumeta suna ta jera kalaman godiya ga Allah mad'aukakin sarki daga dawo musu da gudan jininsu zuwa garesu batare da zato ka tsammani ba.

Ita kam Addwaiyya sai kuka takeyi tana qara k'amk'ame su ummi zuwacan ta dawo ta rungume Salma, cikin fizgan magana irin namai kuka tace "Adda nayi kewarki sosai wallahi, inna tuna daku nayita kuka bamai rarrashina.

Itama Salma kuka takeyi har da sheshsheka ta amsa "nima nayi kewarki sweet Addawiy, har suma nayi tayi danaji kin bace, ashe zakidawo gare, kai wallahi Allah shine abin godiya, Allah mun gode maka, Allah kak'ara tsare dukkan musulmi da afkawa irin wannan yanayi.
"Amin, su Abb suka amsa atare.

Cikin k'ank'anin lokaci yankin k'auyen labari ya bazu na anga Addawiyya, ta dawo gida batare da ko rauni ba. Kafin kace me gidansu Addawiyya yacika taf da al'umma masu zuwa tayasu murna tare da ganin ya Addawiyya tadawo.

Hatta ard'o dakanshi ya tako yazo ganinta.
Atsakiya suka sakata suna tayi mata tambayo na ya'akayi ta bace kuma aina tasami mafaka ta boye akayi ta xuwa nemanta batare da anganta ba?

Cikin sanyi tace dasu "sanda su hisqilu suka kamani nasamu na kufce sai nayi ta gudu har nafad'a inda mucijiya take kwana, tako biyomu tarw dasu, nasamu na tsira ahaka nayi ta rayuwa cikin daji innaji yunwa sai na ci a kayan itatuwan dajin haka innaji k'ishi sai inqarasa awata rafi nasha ruwanta sannan nayi arollah in sallah inna fahimci lokaci yayi,, nakan bata lokaci ina addu'ar Allah yakawomin mafita, to ahaka dai harna kwashe wasu kwani ina rayuwa ni d'aya batare da wani abin citarqa yasameni ba.
Nasoma bin hanya domin indawo cikin mahaifana to cikin ikon Allah sai gashi d'azun da sanyin safia na iso gida.

Cike da al'ajabi mutanen wurin sukayita hamdalah suna kumayi mata sannu, ita dai sai murmushi takeyi tana kallon gefen damarta wanda tun sanda tasoma basu labarin take kallon wurin bako k'iftawa.

Bayan kwana biyu.
Addawiyya ce tare da Salma suke hiransu cikin nishad'i zuwa can Addawiyya ta dubi salma tace "Adda ashe jikin micijai sanyi yake dashi kamar k'anqara? Idanu waje Salma take dubanta takasa tankawa, ita kam tacigaba dacewa "uhmm ai wallahi har yanzu inajin sanyin jikinta a fatata kuma hasken dake idanunta yakasa bacemin afuska, kai Allah yayi halitta awurin kam, Adda bakiganta ba wata qatuwa gaske kamar tayan babban mota kalanta fara tare da rod'i rid'in golden,, wallahi bantaba ganin micijiya mai kalantaba sai a mufarkina naran nan sai kuma lokacin dana nemi wurin tsira daga sharrin su hisk'ulu.

Jadabaya Salma tasomayi har tamatsa sosai sannan tamiqe ta kwasa da gudu tashige bukkan Abbi, tabe baki Addawiyya tayi tana mai furta "matsoraciyar banza kawai.

"Abbi wallahi Addawiy tana tare da matsala domin taboye muku gaskiyan abinda yafaru da ita.
"Kamar nami ba? Cewar ummi.
"Allah ummi yanzu take bani labarin wai jikin micizai yana da sanyi kamar k'anqara.

Azabure ummi ta jababaya tana kallon Salma tace "banson sharrinki fa yarinyar malam.
"Wallahi Allah ummi kuje ku tambayeta kuji.
"Tam munji kiramana ita, Abbi ya umurceta, wanda shima yasoma tsorata dajin labarin, dama can shi bai gamsu da yarda tayi musuba bayanin bacewan nataba yadai kyaletane kawai.

Daga nesa da ita Salma ta tsaya tace "Addawiy kizo inji Abba, harara ta wullamata sannan ta miqe tace da k'arfi "ga miciji nan ya nad'e miki k'afafu. Aiko wani tsale Salma ta daka ta fad'a bukkan Abbi da uban gudu tana ihu.
Me Addawiyya zatayi inba dariyaba, hartana kwanciya aqasa ta dafe cikinta hawaye da majinu suna ta zirara don tsaban dariyan mugunta.

Cirko2 su ummi sukayi suna kallonta tana d'agowa ta dubi Abbi tace "laaa! Gashinan ajikin Abbi zai shige mishi aljihu.
Wayyo zo kuga wani wuntsilawa da tsohon yayi ya fad'i ya k'asa ya miqe arud'e yayi hanyar waje da gudu. Ummi kam ai tuni takai cikin bukkanta ta kulle qofa dama ita kam Salma bata fitoba tunsanda tashige bukkan da gudu.

Addawiyya kam don tsaban dariya saida tasaki fitsari awando, haka yake gudu ajikinta ya wanke mata qafafu.

Abbi ne yadawo yana mazurai Addawiyya ta dubeshi ta kuma kyalkyalewa da dariya tace "Abbi wallahi duk kanku nafiku jarumta nida naga micijiyan da idanuna har natabata banyi irin wannan rud'ewanba amma ku daga ina muku wasa shine duk kuka zure haka? gama Adda Salma can cikinta yana murd'awa tana son kaiwa ma'aikatan sarrafa kashi (msk) ziyara.

"Rabi'a kinci gidanku nace, wato kinmaidamu kakan ninki ko? Girgiza kanta tayi tare da barin dariyan ta tsunu kamar ba itace ke kyakyacewa ba. Jan hannunta Abbi yayi zuwa cikin bukkanshi.

Salma naganinta ta miqe ta fice hannunta dafe da cikin, a makewayi tayada zanzo ji kake fatsatsatsa!!! Burrrr!! Burr!! Burrrriririii!!.

Tana share zufa ta shigo bukkan, Addawiy ta dubeta ka kama bakinta tana qunshe dariya.

timmm!! Salma ta timawa Addawiyya duka a baya zata qara mata wani ummi ta riqe hannunta tana hararanta, cike dajin haushi ta zauna gefen Abbi tana wullawa Addawiyya harara, ita kam sai murmushi take dokawa tare da kanne mata ido 1.

Gyara murya Abbi yayi ya sauke dubanshi kan Addawiyya yace "Rabi'a muna saurarenki da kifad'amana gaskiyan abinda yafaru dake sanda kika bace.

Zama Addawiyya tagyara ta jingina jikin ummi tasoma basu labarin da ta sanu har zuwa falkawan datayi ta ganta agadon umminta.

Baqaramin al'ajabi suka fad'aba sanda sukaji wannan sirad'i da tsallake musanman na wurin rijiyan kugu.

Salma ta matso ta kama hannunta tace "amma Addawiy taya kika tsara labarin nan sanda su ard'o suka tambayeki kuma miyasa kika boye musu gaskiyan lamarin?

Shiru tayi taqi cewa komi.
Ummi ta dafa kanta tace "autana abin alfaharina kuma haskena yi magana mana.
Quri tayi tana kallon rifin tsoron d'akin zuwacan ta gyad'a kai tana mai amsawa da "tam.

"Alokacin fa wannan mutumin ne daya tai makeni yazo ya bud'emin tafin hannunshi ina karanta dukkan bayanin danayi sabida yacemin bakowane zai yarda da abinda zan fad'aba kuma wasu zasu iya mai dani 'yar mai ganye sunazuwa suna cewa inbasu magani alhalin bansan komi akan cutarsu ba.

Jinjina kai sukayi dukkansu cike da gamsuwa da bayaninta.

Abbi ya numfasa yace "hakikanin gaskiya Rabi'a kinga abubuwan al'ajabi kuma tabbas kin had'u da aljannun musuncine, lallai nagode musu da Allah yabasu ikon taimakonki, Allah yasaka musu da Alkhairi. Suka amsa "Amin.
"Abbi dama a aljannu akwai masu kirki haka? "Sosaimakuwa Salma, dasu kuma wasun suma sun mafimu tsoron Allah sabida su d'in suna ganin mala'ikun Allah kuma suna jure bautan Allah mad'aukakin sarki fiye damu bil'adam illadai Allah mad'aukakin sarki ya tabbatar da munfisu matsayi da d'aukaka ta ko ina sabida masoyinsa habibinsa d'angatansa ma'aiki SAW ajinsinmu yafito.

"Allahu Akbar!! Suka fad'a atare.

Addawiyya tace "to Abbi miyasa ake samun azzalumai macuta cikinsu alhalin sunfimu ganin ilmomin Allah SWA quru k'uru?

"Haka Allah yake wanzar da k'udinsa da iradanshi kuma asanda yaso, kisani yarda mukammu bi'adama cikinmu akwai azzalumai marasa imani koda kuwa suna musulmai to suma haka yake a cikin jinsinsu.

"Aikam indai hakane to micijiyan nan data biyomu itadin azzalumace kuma tana daga jinsun junnu domin daganinta ba normal micijiyabace kuma hakik'a itace tayi azajalin su ilya sabida inajiyo kurukuwansu sanda ta kamasu.

"Biri yayi kama da mutum kam don koni nayi zargin ba micijiyan kyau bace

Allah bata kyau bace Abbi, bakaga idanunta ba zar haske kamar fitila kuma wallahi haskensu sunqi bacemin a cikin idanuna.

"Auta dayardan Allahu zakibar ganin gizon da idanun su ke miki kinji? "Tam ummi, Allah yasa hakan "Amin.

Salma ta wulla mata harara zatayi magana Addawiyya ta rigata tace "madam Salma matar mr. Mushaffa'u to be insha Allah minayi miki kuma da kike hararata?

"Wallahi ummi kirabi da autanki ko yanzu in sanza mata kamanni tam.

Kallo Addawiyya ummi tayi tako kwashe da dariya tana cewa "ummi Allah nagama fahintar adda Salma tana da mugun tsoron jin labarin aljannu tare da micizai ne shiyasa na walata d'azun sai kuma Gashi ashe ba ita kad'aice maijin tsoronba har da ke.
Murd'e mata kunni ummi tayi da k'arfi, tako kwalla k'ara Abbi ya toshe kunninsa yana cewa "kai zuwaira kibari kada ki yi mata illaman "barni da ja'ira malam wato sabida kin maidamu abokanan wasanki shine zaki wana mu ko? To dad'in abinma ubanki yafi koqa tsorata tunda shi waje yayi da gudu kamar goyon barewa.

Duk sukasa dariya, Salma harda kwaciya.
"Su Adda anji mugunta anata dariya to gashinan zawo zai zubo miki dai, aiko da gudu Salma ta tashi ta fice zuwa bayi tasoma zugawa ba k'aqk'autawa.

Me Addawiyya zatayi inba dariya ba, Abbi ya miqe cike da dariyan qaran fitar zawon Salma da suke jiyowa daga inda suke yace "Rabi'a biyoni kinji in harbo mana zabon daza ayi mana miya dashi anjima.

Cike da zumud'i tabiya bayanshi tana cewa "yawwa Abbi aharbosu da yana sabida isowar dasu mama Ramlat zasuyi anjima sannan kuma yakamata ace angabatar da walimar dawowata gida cikin qoshin lafiya shima. Kaga kenan sai ayi amfani dasu wurin taron ko?

Shiru Abbi yana mamakin lamarin Addawiyya kamar wato 'yar duba wani karon take dawo mishi domin lokuta da dama inta fad'i abu sai ya tabbata dad'in abinma natama bata fad'an na sharri kuma iyakarta agine zancen nata.

Ilai kuwa suna cin abincin rana saiga su hajiya Ramlat tare da yaranta dukkansu.

Cikin murna suka tarbesu yayin dasu kuma duk suka rungume Addawiyya suna murnan bayyanarta.

Bayan sunci sun qoshi aka bud'e babin Hira tare da maida zancen abinda yafaru sannan suka cike da addu'ar Allah yaqara tsare musu zuri'a daga k'ara afkawa mummunar kaddara irin wannan.

"Yawwa malam to yanzu kenan tunda Addawiyya ta bayya kayi watsi da qudurinka na tashi daga mahaifar naka kenan? Hajiya Ramlat ce take tambayarshi sabida tun sanda Addawiyya tabace da kwana uku yasoma saida wasu daga cikin tabbobinshi yace zai bar yankinsu yayi nisa da jaharsu sosai koyin haka zaisa ya rage mishi rad'in rashin Addawiyyarsa.

Amsawa yayi "maganar tananan Ramlatu, domin ko yau zan Koran wasu zuwa kasuwa kuma harna turawa aminina Alhaji gambo kud'i masu kauri dayasaya min fili ko ginannen gida mai d'an girma sabida nafiso da zarad na isa garin in zauma acikin muhallina.
"To Allah yatai Mata "Amin.

Mushaffa'u yana sosa kai yace "to Abbi amma dai baza kayi misa damuba ko? kuma zaka auramin Salma kafin lokacin tashinnaku naku yayi amma.

"La'ilaha'illallahu!!! Mushaffa'u baka da ta ido she bansani ba?

Cikin sosa kai yace "Allah mama ni dai kibari Abba ya amsamin tambayata kawai, duka hajiya Ramlat takawo mishi ya goce, hindu dake gefenshi ta rankwasheshi a kai yayi saurin taba warin yana hararanta, itama Salma ta tura baki tayi tana hararan Hindu tagefen idanu, aikan Addawiyya tana ganin haka tasoma tafi tana cewa "masoyan zamani ooo, Abbi wallahi ka d'aura musu auren nan yau kawai gobe sai su wuce tare da ita sabida dama tuni sun shirya tunqaranka da zancen ita da shi.

Idanu waje Salma take dubanta zatayi magana tamatsa da bakinta daf da kunninta tace "Allah kina musawa zan fasa kwai, domin kisani nasan yana latsa miki nono in har yaritsaki a inda babu idanun mutane kuma sarai kinajin dad'in latsawan ko?

Ahaukace Salma tasoma kai mata duka, ira kam tashi tayi ta gudu zuwa d'akinsu tana dariya tako rufa mata baya iyayennasu suka bisu da kallo cike da sonjin abinda Addawiyya ta fad'ama Salma a sirrince.

Da yammaci ranar suka fita yawon shan iska cikin rigagen fulanin dake zagaye dasu tare da leqawa yankin da dikkawa tare da kammabari suke gabatar da al'adunsu.

Basu dawo gida ba sai daf da magariba.
dukkansu arollah suka d'auro Abbi yajasu Sallah, koda suka idar anan suka zauna suna jiran zuwan lokacin isha'I tayi su d'ora.

Sai jan chasbahansu sukeyi yayin da Addawiyya ce kad'ai ta bud'e Alqur'anin karim tana karantawa cikin zuciyarta zuwa can ta tsinkayi wani qamshin turare mai dad'i yana busowa ta gefenta kallon tabi wurin dashi ta hangoshi tsaye gefenta yana murmushi itama murmushin ta maida mishi zata yi magana ya girgiza mata kai tare da jan hannunta ya nufi wata bishi datake bayan bukkokinsu.
abin mamaki suna isa ya amshi qur'anin ya ajiye agefe sannan suka zauna abisa wasu kujeru masu kyalkayali.

Kallonshi tayi tace "uncle yau banji sanyi ajikinka ba kamar ranan nan. "Dariya yayi kad'an yace badai ki lura bane amma sanyi yana tare da ni ako da yau she sabida nid'in iyayena a tsibin mafi sanyi suke rayuwarsu nikuma nakanyi tawa rayuwar ak'asan ruwa, sannan mud'in jinsinmu haka Allah yayi rayuwarsu gaba d'aya cikin sanyine kinga bayarda za'ayi sanyi yarabi dani.
K'uri tayi mishi da idannu bako kifatawa ya hura mata iska taja numfashi da sauri tare da lumshe idanunta ta bud'esu tace "uncle wai miyasa ni kad'aice nake ganinka agidanmu? "Sabida kece kad'ai idanunki abud'e sakamakon bud'e miki danayi tun kina 'yar shekaru biyar a duniya kinga yanzu kimanin shekaru tara kenan da watanni uku tare da kwanaki goma sha d'aya da awa biyu da mitoci arba'in tare da sakonni tara cif.

Baki bud'e take kallonshi ya gyada mata kai alamar gamsarwa.
"To har karatun danaji ranan awurin itaciyar tumfafiyar nan wai duk kaine ka bud'emin kunnin naji? "Eh, nine mai babban suna, kuma karatun da kikaji ranar anayi a wurin to makarantarmu ta haddar al'qur'ani ce awurin, kema in kinaso sai kin bud'e miki wurin kiriqa zuwa d'aukan karatu amma fa kisani zakiga halittu kala kala awurin damasu kyawun sura da munana da farare da baqaqe harma da jinsin micizai duk zaki riga gani amma bazasu cutar da keba Sam.

Dafe qirjinta tayi tace "banaso uncle.
"Tam kwantar da hankkinki bawanda zai kaiki, mai babban suna.
Murmushintayi tana maijin dad'in sunar datake kiranta dashi ainun.

"Amma wai uncle intambayeka man, shin kai mutum ne ko aljani?
Dariya yasaka sosai yace "mai babban suna kece zaki lalubo amsar da kanki domin ma naji Abbinki yayi sharhi akanmu rannan sosai.

Shiru tayi tana son tunano abinda Abbin yafad'a zuwa can tace "au natunama kai junnu ne kuma musulmi mai tausayi.
Gayda mata kai yayi ta kuma cewa "oh to ita wanna micijiyan wanda idanunta yaqi bacemin a maganaina fa? Shin muguwace ko?

"Eh, muguwace ta kyau kuma musulma ce "to yanzu da na ina kuma miyasa nakasa mantawa da ita?
"Tana can yankinsu a tsubirin sanduluna sannan brain d'inkice take da riqe abubuwa sosai wanda batacika mantuwa ba shiyasa kika kasa manta hasken idanunta.

Shiru tayi sai kuma tace "uncle to ya akeyi ajinsunku ake samin micizai?

Haka Allah yayosu mucizai wasu kuma komawa sukeyi dakansu kamar yarda micijiyan data biyoki takeyi inzatayi zalunci.

"Tafd'ijan, to Allah ya shiryata "Amin mai babban suna, hakan takwaranki sayyada rabi'atul Addawiyya take, komi akamata na zalunci sai ta nemawa mutane shiriya wurin Allah.

"To aina itad'in kenan take? Itad'in jinsun kuce ko namu?

Gyara zama yayi yana murmushinsa mai kyau ya amsa "Wata baiwar Allah ce mai tsananin tsoron ilahu da gudun duniya sannan ajinsinku bil'adama take.

Cike da zaquwa tace "to uncle bani labarin nata man insha.

Miqewa yayi yace "Yanzu dai tashi kitafi ki sanja arollah kibi 'yan uwanki sallar isha'i nima zantafi inyi tawa, zuwa dare ko cikin barcinki zan fad'amiki taqaitaccen tsoron Allah nta.

"Amufarki kuma uncle? "Eh, acan fa kuma zanfad'a miki wacce take yawan janmiki tsaki sanda kike zauna ad'akin nan sanda kika bace. Da magen dayi tazuwa miki cikin barci
"To uncle, amma dai da kazomin azahirine zaifi ba a cikin barci ba "tam hakan za'ayi mai babban suna, yau in kowa yayi barci ki fito zuwa wurin bishiyar gwaiban dakike yawan zama sai muyi hiranmu ko?
"Eh zanzo kuwa indai har banji tsoro fitowa ba.

Ya jinjin mata hannu ya zama haske ya bace ita kuma ta ganta tsaye gefen randarsu sai kawai ta d'auki buta ta shige bayan gida abinda hankakinta kwance kuma bako tsoron komi dataji na ganinta tsaye alhalin tasan itad'in a zaune take awurin bishiya.

Tana arollah tana qudurtawa aranta lallai anjima kuwa zata tambayeshi dalilin dayasa take gaininta awuri batare da itace tayi tafiya takawo kanta wurinba.

Bayan sallame sallarsu sai kowa yatashi ya gabatar da shafa'i da wutri sanna suka zauna cin abincin dare cike da nishad'i.

Addawiyya kam kad'an taci tuwon ta tsame hannunta taje ta wanke ta dawo ta zauna gefen Hindu tare da leqa agogon dake d'aure a tsintsiyar hannun ta sai kuma taja tsaki tana cewa "kai haba wannan wani irin barci ne yazomin da farkon dare haka, duka2 fa qarfe tara saura kwata ne yanzu amma don tsiya jibeni dakyat nake bud'e idanuna kamar wacce tasha maganin barci.

"To Addawiy tafi kije ki kwanta man.
"aikam yazamamin dole kuwa aunty.

Tayi sallama dasu ta tafi zuwa bukkansu ta fad'a masar katifansu tana ta sakin hamma, cikin 'yan seconds barci ya d'auketa.

*mrs j moon*
[12/29/2017, 3:00 PM] Asma'u Seema1: *RABI'ATUK ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

*Wannan shafin na duk wata mai suna RABI'ATUL ADDAWIYYA ce, gashi nan kyauta nabaku domin jin dad'inku sannan kuma kuyi alfahari da sunar sabida sunane mai matuk'ar daraja. Inasonku a ruhina takwarorin Addawiyya*❀.

*23 ~ 14*

Miqa tayi tana hamma ta dubi gefenta ta hango wani kujera fari ta roba ta jawo ta zauna qasan bishiyar gwiba tana ta waige2 zuwa can tajiyo qamshinsa ta miqe cike da zumud'i har zata kamo hannunshi sai kuma ta nok'e tana kallonshi fuskanta d'auke da murmushi.

"Mai babban suna kenan bakyason jin sanyin jina ko? "Eh wallahi uncle kuma kagama hakan baida kyau a addinin islama "hakene kam, yarinya k'arama da sanin yakamata, lallai kinkerewa Adda nki Salma ta ko ina.

"Yawwa uncle wai da gaske ne yaya mushaffa'u yana latsa mata jiki? "Tabbas gaskiya ne amma ita d'in bata son haka hasalima tsoronshi takeji sabida har yanzu takasa manta wuyar da mariyan yarannan suka bata.

"To amma miyasa bazata hanashi ba? "Shammatanta yakeyi kuma koshi iyakar ita yake tabawa sabida yana da k"yank'yami sosai kuma yana da yana da tsoron Allah illa iyaka yana son kasancewa da ita ne ainunn kuma yana cikin jinsi masu qarfin buk'atuwa.

"Miye shi buk'atuwan uncle? Wani kallo yabita dashi sai kuma ya kauda maganar yace "Mai babban suna gyara zama insoma yi miki bayanin wacce keyi miki tsaki da kuma magen datake sanja miki launi a cikin barcinki da farken ki.

"Tam ina jinka mai kyau. "Murmushi yayi yace "kinfini komi ai mai babban suna "nikam banyarda ba "uhmm kedai bari kiji "sanda na cetoki daga zalinci 'yan uwana junnu sai na ajiyeki afilin da kikasha ruwa kika kwanta sai nakuma cetonki a hannun micijiya nan sai na d'aukeki nakaiki gidana dake k'asan teku to sanda na kaiki lokacin shiga halwata yayi sai nacewa qanwata da ta kulamin dake to shine fa take tajin haushi wai nakawo musu bi'adama cikin yanki gashinan kindameta da kukan shagwaba sabida ita ta tsani hayaniya balle sautin kuka shi yasa baruwanta da yawo ballantana ta had'u da bil'adama iyayen gajen hak'uri da hayaniya,, cewarta fa amma.

Sai ita kuma magen ta kasance matar dazan aura ce.

Da sauri Addawiyya ta katseshi tana zare idanu tace "magen!!? "Eh da ita aka had'amu amma ita ba mage bace ta dai koma mage ne don ra'ayinta in kuma taso sai ta dawo irin jinsinmu.

"Taf d'ijan, uncle lamarinku yana da ban mamaki gaskiya.

Dariya yayi yacigaba "takan biki cikin barcinki don ta tsorataki kuma ta kan fito miki azahiri sannan itace ke gilgilma miki duk domin ta tsorataki wai ita tana kishi da ke ne sai ni kuma na fidda miki jin tsoron komi aranki.

"K'uri tayi mishi tana aikin kallonshi, hura mata iskan bakinshi yayi a fuska taja numfashi ta lumshe idanunta ta bud'esu tace "uncle amma matan nan taka so kuwa ce, ta k'arshe, to ta yaya zata soma kishi dani ni ba matarka ba.

"Mai babban suna kenan, yanzu dai kinji wad'anda kika zauna tare dasu.
"Eh naji su amma baka fad'amim sunayensu ba "ita mai yi miki tsaki sunarta khadija, budurwata kuwa sunarta mabaruka.

"Kai kuma sunarka wane? "Habibullah (masoyin Allah)

"amma kam yana da dad'i sunar.
"Ni kuma nafi jin dad'in naki sunar sabida k'arfin imanin mai sunar taki da kuma jajircewan ta.

"Yawwa uncle bani labarin nata dakacemin zaka bani. 'Daga kanshi yayi ya kalli sama itama ta tabi inda yake kallon sai kawai taga wasu abubuwa masu girma kamar mutane gasu da fuka fukai suna ta shawagi kamar tsuntsaye.

'Dan matsawa kusa dashi tayi tace "uncle miye su? "Halittun Allah suke harkan gabansu kamar yarda mukeyi ni da ke.
Sai taga ya bud'e yatsunsa biyu ya nuna samar atake suka bace ya dawo da dubanshi gareta, ta matso zatayi magana ya d'aga mata hannu yace "mai babban suna kinfiye sonjin k'wam, amma nasan abinda zan miki kibari "bata rai tayi tace "nidai ina jinka bani insha.

"Kad'an zan fad'a miki k'arfin imaninta
"tam inaji.

"Ita d'in mace ce mai tsoron Allah tare da son ma'aikinsa sosai kum har cikin ruhinta son nasu ya nashe domin wata rana tana tafiya sai ta taradda da wani bawan Allah yana kiran sallah, bayan ya idar da kiran sallan sai tace da mutanen wuri wannan mutumin bai kira sallan nan domin Allah ba, sabida in yakira domin Allah to wancan dandamalin da yahau yayi kiran bazai d'aukeshi ba.
Sai mutanen wurin suka cika da mamaki maganarta ganin haka sai tace bari kugani ni inkira kuga ikon Allah aikam sai ta tafi zuwa dandamalin ta hau tasoma kiran salla batako idar da kiran sallan ba dandamalin ya watsar da ita gefe duk ta ji rauni ta miqe tace dasu kungani ko, jinjina mata sukayi suna mai cike da mamakin lamarin.

Haka nan wata rana tana sallah mak'iya Allah da mazonsa suka zuba mata micizai da kunamu sukayi ta cizonta suna harbinta amma ko gezau batayiba bama tasan anayiba sabida zuciyarta gabaki d'aya yanaga Allah ne, sahi kad'ai takeji dani lokacin don haka dakansu suka kwashe kayansu suka barta tana cigaba da ibadarta.

Tace badan aure sunar mai k'arfi bane to dabaza tayi aure ba domin bata da lokacin kula da miji sabida yawan ibadarta amma hakanan tayi aure domin ANNABIN ALLAH yayi alfahari da ita ranar sakamako.

Magabata na kwarai sunyi ittifa'k'i cewa da ace Allah SWA zai bawa mace Annabta to da Rabi'atul Addawiyya zata zamo daga cikinsu.

Kinji tak'aitacce tsoron Allah n mai sunarki.

"Allahu Akbar kabiran, lallai inada suna mai girma da matsayi, Allah nagode maka, Allah yabamu danshin Sayyada Rabi'atul Addawiyya.

"Amin ya rabbi mai babban suna.

"Nazamo tare dake ne domin k'aunar danakema mai sunarki kuma sunar kakata ce wacce ta haifi maihaifina.

"Ikon Allah, uncle to kai waya baka wannan tarihin? "Kakana na biyar shine yabani domin yayi zamani da ita lokacin
"Dafe qirji tayi zata kuma tambayarshi ya katseta da cewa "kinason sanin yarda akeyi kike samun kanki a wuri batare da kinyi tafiba ko?
"Eh inason sani "to ilmine wanda Allah yahore mana mu junnu kuma ko da nabud'e miki tunanki bazai iya da'auka ba don haka kibarshi asirrinmu ne kawai.

"Tam uncle, amma wata rana inajin maganarka akunnina kuma kana fad'amin abinda zai faru kafin ya afku, to ya akayi kasani "shima sirrine, sai dai in kuma kina son komawa cikinmu sai in fad'a miki.
Wani zabura tayi tajita tim tafad'o asamar katifan da ta kwanta.

Ta tashi zaune tayi tana matsa hannunta data bige sai kuma tasoma tunano maganganun da sukayi da unlce d'inta, dasuri tamik'e tana kallon agogon dake rataye awani k'usa taga 5:00am.
ta duba gefenta ta hango Hindu tana ta sharan barcinta ta kuma duba inda Salma take taganta kwance duk ta mamaye wurin ta turota bakin katifan aikam ta zabura zata doketa.

"Kul mai babban suna, ba kyau tashin barci da duka, ware idanunta yayi tace "uncle.

"Fito ki arollah kiyi sallah nima masallacin makka yanzu zani, yin sallah.

Da qarfi ta ambaci "Makka!!

Sai jitayi an hura mata iska ta tafi luuu.

Koda ta farka sai ganin su Abbi tayi zaune sunyi jigun jigun sun sata atsakiya, suna gani ta miqe suka soma yi mata sannu ita kam mamaki ne ya cikata tace "waye baida lafiya? "Kece auta, kin suma tun subahi sai yanzu da hantsi kika farfad'o.

Jikinta tabi da kallo taganshi duk ya jiqe d ruwa almun tasha kwara ruwa kenan.

sai tasoma tunanin mi ya sumar da ita kuma? Ganin tagaza samo amsa sai tamiqe tayo tsarki tayi arollah tagabatar da sallah safe.

Nata nan zaune ummi ta kawo mata abinci ta ci sosai tasha ruwa tayi hamdalah ga Allah sannan ta miqe tafice zuwa wurin su Salma.

*Mrs j moon*
[12/29/2017, 3:00 PM] Asma'u Seema1: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

Affuwan sisters ansami matsala a last page inda amaimakon 13~14 sai nasa 23~14. Dafatan za'ayimin kuziri.

*Ina kike mum Abdul (Bahijja, bebeelo) Wannan page naki ne domin jin dad'inki kuma Addawiyya tace tana gaisheki sosai tana sonki da qawa😝. Lallai kisani Kina zaune daram a cikin ruhina ainun*😍😘

*15 ~16*

Tana isa inda suke zaune suna ta hiransu cike da nishad'i sai ta zauna kusa da Hindu ta dubi Salma ta tabe baki ta amida hankalinta wurin mushaffa'u tace "yaya bani tarihin mai sunana inka sani inji.

"Amfaninmi tarihin zai miki? "Kai dai in kasani kabani insha kawai "nasani amma na manta sabida tun ina islamiyya aji uku wani yaro yayi tambaya sai aka fad'ama a tare.

"Uhmm to Allah yayima sauqi "Amin dai kam, hindu ta amsa tana hararan mushaffa'u.

Sosa kansa yayi ya ja tsinin hancinshi yace "to aunty da inyi mata karya ai gara in fad'amata gaskiya ta.

"To fad'amin miye buk'atuwa? "Tofa yau Rabi'a da tambayoyi kika farka kenan.

"Nidai amsamin tambayata kawai.
"bazai amsaba 'yar rainin wayau, kintafi can wurin rawar maitanki kindawo zaki damemu da fi'ili.

"Adda nice mayuwan? Ta fad'a haka idanunta cike da kwalla "Eh kefa, sabida da k'arara d'abi'unkin yanuna irin ta mayune.

"Aunty kinajinta tana son laqamin alkaba'i ko?

"Salma banson wasan banzan nan, kinko san illar maita kuwa? To Allah naqarajin kinkirata da hakan sai na saba miki.

"Tam aunty bazan qaraba "hakan shi yafi kam.

Addawiyya ta watsawa Salma harara tace kinjama kanki yau kamar na tona asirin da ke boye,;kuma kinfi kowa sanin hukuncin da Ummi zatayi miki, ciki ma harda hanaki ko...
"dalla!! banza kawai wacce bata da sirri sam, bata san rufamawa d'an uwa asiri ba, Salma ce takatseta cikin hargagi.

Dariya Addawiyya tasa tana cewa "zakiyi bayani ne in Ummi tasa kaki aloko.

Fuuuu Salma ta tashi tabar wurin, tana cewa "wallahi kika fidda zancen nan fili Allah na lahira sai yafiki jin dad'i.

mushaffa'u yabi bayanta yana kiranta amma taqi tsayawa.

Ita kam Addawiyya sai dariya take kyal kyalawa, hindu ta dubeta tace "wani sirri zaki tona na Salma? "Aunty share kawai walata nakeyi sabida tacemin mayya amma babu wani sirri.

Jan kunninta hindu tayi tace "Autan ummu baki jin magana ko? "Washh aunty wallahi inaji magana sosai, kawai Adda ce tafiye jata da fad'a, shine nikuma nake tsikananta. sakin mata kunninta tayi ta janyo kwaryan damammiyar fura dake gefe tasoma sha.

Gyara zama Addawiyya tayi tace "aunty mijinki fa yana nan bisa hanya yau zaizo neman qarin bayani akan cikin jikinki amma inaga sai gobe da hantsi zai iso nan inyasami kabarin kuna nan garin, kuma gashi naga alamar baki d'auke da komi.

Tarine yasark'e Hindu tayi tayi har saida ta amayo furan data sha.
Sai sannu Addawiyya keta jera mata, ita kam sai gyad'a kai takeyi tana cigaba da kwaro amai.

Bayan tagama Addawiyya ta d'ibo mata ruwa ta wanke bakinta da fuskanta, ita kuma ta zuba qasa ta rufe aman.

Jan hannunta hindu tayi suka fita zuwa wani wurin wata bishiya dake nesa da bukkansu.

Zama sukayi a manyan jijiyojin bishiyar, Hindu ta kama hannun Addawiyya ta runtse tace "waya sanar da ke Adnan zaizo yau?

Shirub Addawiyya tayi kamar ba ita ake tambaya ba.

"Autan Ummi kefa nake sauraro.

"Aunty jiyane nayi mufarki zaizo yau kuma nasan tabbas zaizo sabida wata rana mufrkina yana zama gaskiya.

K'uri hindu tayi mata d idanu zuwa can taja nufashi tace "nafahinceki amma hak'iqanin gaskiya autan Ummi lamarinki yasoma bani tsoro.

"Kidainaji tsoro komi aunty baiwace kowa da irin nashi

"haka ne kam.

"Autan ummi amma fa inaji ajikina inyazo da matsala.

"Eh wallahi aunty ba mutunci zaizo kuma yasan kina da cikinsa d'an wata d'aya koda kuka rabu, yanzu kuma yana tunanin ya kai watani biyar kenan.

"Ya ilahil alamina!! Ni hindu yazanyi? "Aunty ki tubure mishi ke bakida komi tunda ko su mama basu san kin zubda cikin ba.

Idanu waje Hindu take duban Addawiyya, cikin rawar baki tace "autan Ummi wai wayake fad'a miki sirri mutane ne?

Abarcina naganki tun sanda kika aikata abin domin ma har kwanciya kikayi a asibiti na kwanaki biyu, to nad'auka shirmen mufarki ne, sai yanzu nagano da gaskene don naga adnan din yana ta kuri sai kindawo gareshi kodon abinda zaki haifa amma fa bata lalama zaibi ba ta tsiya da tijara wai ganinshi kece kika cuceshi da kika gudu da aurenshi kika kumayi biris da lamarin shi.

Ahankali Hindu tace "autan Ummi baki da wayon dazan fad'a miki abinda yasa na guji zama da Adnan amma inamai tabbatar miki shine ya zalunceni yayimin qarya alhalin shid'in mara asaline wanda bawanda yasan inda iyayenshi suke kuma rayuwarshi gaba d'aya sabon Allah ne.

"Aunty rabuwarku shine mafita kuma gara da kika zubda cikin domin had'a zuri'a da irinshi hatsari ne, kuma yanxu koda yazo ki rufe idannu kici masa qaniya ta haka zaiji shakkan sake tunqaranki kuma atake zai baki takardanki ki huta da shegen aurenshi.

Cike da mamakin basiran yarinyar Hindu tace "autan ummi wai shekarunki nawa yanzu?

"Goma sha hud'u da watanni.
"Ok, amma fa kina da azancin iya magana gashi wayonki ya girmi shekarunki.

Kwantar da kanta tayi a cinyar Hindu tace "haka mutane ke fad'i, hatta Abbi yafiso yayi shawara dani fiye da Adda Salma.

"Aikam Salma sokuwa ne ba wayau sai uban iya fushi, abu ba abu ba tayi ta hawa kamar garin kwaki.

Dariya Addawiyya tasa tana cewa "kuma kinsan fa abincin Adda ne kwaki, sosai take son shanshi dayin qosanshi.
"Nima na shaida hakan, tunda gashinan mushaffa'u yakoyi cin qosan, kamar wasu dikkawa.

Dariya sosai sukayi sannan suka cigaba da hiransu amma lokaci2 Addawiyya sai duba gefen damarta ta gyad'a dai, ita kam hindu batama san tanayi ba.

Washe gari suna shirin tafiya motar Adnan ta iso bakin bukkan su Addawiyya, baiko gyara parking ba ya kashe motar ya fito yasoma tsula rashin mutuncimshi.

Duk tsayawa sukayi cirko2 suna kallonshi cike da ta'ajibin dalilin faruwan hakan alhalin sune suke jiranshi dayazo yayi musu bayanin abinda kefaruwa tunda ita Hindu taqi cewa komi duk tsawon lakacin da ta kwashe zaune agida.

Zuwa can mushaffa'u ya shammaceshi ya d'agashi sama ya soka da k'asa yayi ta bugu.

Mutanen qauyen suka sami abin kallo, saida yahad'a mishi jini da majina sannan Abbi yayi nasaran rabasu.

Atake Adnan ya rubuta takardan saki ya cillawa Hindu ta d'auka ta shige ciki tana kuka.

Abbi ya matsa domin yabashi haquri ya tureshi kad'an yarage bai fad'i ba.

Mushaffa'u ya zabura zai kuma dukanshi mama ta riqeshi tace
"wandama kayi mishi ya isa, barshi ya wuce duniya ce.

Afusace yaja motarshi ya wuce, bakinsa tare da hancinshi zai zuban jini yakeyi sannan aqasan zuciyarshi kuma tunanin abinda zaiyiwa mushaffa'u yakeyi.

Aciki kuwa Hindu kuka take tayi kamar ranta zai fita.

Addawiyya dake zaune gefenta ta soma share mata hawaye tana cewa "kyaleshi aunty kansa yayi mawa kuma yanzu haka yana tace da masifa tunda garin yawon banzanshi yaje ya kwaso k'anjamau.

"Nashiga uku, yasamin kenan yanzu? "A'a aunty ke bakya tare da cutar komi domin sanda ya aureki lafiyarshi lau, bayan kin barshine ya kwaso abinsa.

Shiru hindu tayi tana mai cike da mamakin lamarin Addawiyya, yarinya kamar goyon aljannu.

Dariya Addawiyya tasaki tace "nikam wallahi goyon bin'dama ne.

Idanu waje Hindu tace "nashiga uku, ko dai maganar Salma zai tabbane da tace ked'in rabinki mutum ne rabinki junnu.

"Au wai sai yau kika fahimci Addwiy tana da matsala aunty?

Cikin tsiwa ta tari gaba Salma tace "waya kasa dake?

"Yanzu zan zubarmiki da haqora wallahi, kindai sanni sarai bana d'aukan rainin wayonki.

"Eh na sanki kam, amma a fannin kare martabanki baki iya tsinana komi sai tura baki kina wani cewa "banso2 kamar wata sakarya.

Afusace tayo kanta tayi saurin maqalewa a bayan Hindu tana yimata kwalo.

Ficewa Salma tayi tana cewa "mai rabani da yarinya yau sai wanda yabusan numfashi.

"Kedai tafi wurin mijinki, kud'ora daga inda kuka tsaya jiya.

Afusace Salma ta dawo ta fizgota abayan Hindu tayi d'akinsu da ita, hindu tabiyo bayansu Salma ta kulle qofan.

Daga ciki Addawiyya tace "yi tafiyanki aunty na isheta riga da wando domin ba'abin da zata iyayimin duk tarin burgane.

Hindu dai dariya tayi tabar qofan ta nufi inda su Abbi suke zaune. Inda sukayi ta bata baki tare dayimata tuni akan yarda da k'addara.

Sai bayan la'asar suka sami tafiya wanda har da Addawiyya suka wuto sabida takafe ita sai ta koma makaranta aranar, sabida an wuceta sosai akaratu.

Ita suka fara saukewa a school tana ta kuka dakyat suka shawo kanta tayi shiru sanna suka k'arasa cikin gari.

Washe garim ranar Salma da Mushaffa'u ne zaune cikin garden suna hiransu ta masoya.

Ya rungumeta a jikinshi yana lalibenta, kamar yarda yasaba.
Cikin fushi ta kwace jikinta tasoma magana "wallahi yaya bana sin abinda kakemin ko don kasanni d'in ba virgin bace shiyasa kakemin haka?
"Honey mi yakawo wannan maganar kuma? Nifa ke nakeao da k'auna ba jikinki ba.

"To indai kayarda da haka kabar tabani har sai shedu sun shaida na zama mallakinka, in kuma kacigaba damin haka zan fasa auren muhaqura da junaid.
"Nabari honey wallahi, inkuma kinga naqara kimin duk hukuncin da kikaso.

Murmushi tayi tana mai jinninawa qanwarta Addawiyya databa wannan shawaran.

Haka ko yafaru domin tsawon kwanakin da suka biyo baya ya kame gabbanshi daga lata mata jikinki saima yasoma azumi donmin samun kariya daga afkawa cikin sha'awar datake yawan taso mishi wanda bai samun sauqi har sai ya kai hannunsa jikinta,sannan ya qagara su Abbi su iso ko atsaida lokacin bikinsu ya Hutu.

Ita kam Salma hakan yayi Mata mugun dad'i tunda gashi har yamaida hankali da bautan ubangijinsa ta hanyar yin azumin nafila. Sai takuma qara jinjiwa Addawiyya da kuma godemata sabida ita ce sanadin tsamosu ga fad'ama sabon Allah SWA.

**** Bayan sati biyu su Abbi sukayo parking din kayansu sukayi ban kwana da mutanen garin jangaba suka nufo kwantagora amma kafi su isa sai suntsaya a makarantar su Addawiyya sun d'auketa domin ason ran Abbi kwana 1 zasuyi agarin su d'uki hanyar birnin kano don tuni ansama musu gidan dazasu zauna.

*TUNA BAYA* (Nasabarsu)

*mrs j moon*
[12/29/2017, 3:00 PM] Asma'u Seema1: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

*Ina kuke 'yan mata Adon gari, ga page d'inku nabaku shi kyauta.*
*Maryam Rano*
*Maryam Kaumi*
*Ummiey Ahmad*
*Fatima kaka malam*
*Khady kd (my inlaw)*
*Aisha gombe*
*Pretty (meena)*
*Exclusive (zainab)*
Allah ya kaimu lokacin bikinku musha bidiri bired'e AmeenπŸ‘πŸ»πŸ˜Š

*17~18*

Malam Yusuf shine cikakken sunar Abbi? Haifaffen garin jangaba ne, mahaifiyanshi tare da k'anninshi uku biyu maza d'aya mace wutane ta yi ajalinsu lokacin shi yana can cikin garken shanu yana gad'insu, wutan ta tashi kokafin akawo agaji wutar ta lashesu sanadin haka mahaifinshi yakamu da ciwon zuciya shima bai jimaba yace ga garinku nan sakamakon haka sai yataso maraya.
ga dukiya ubanshi yabari sosai amma 'yan uwanshi sukace nasune yake yi musu kiwo kuma bawanda ya musanta hakan a garin sabida haka suka k'wace komi su bar mishi wata tsohuwar saniya wai ladan kiwon da yariqa yi yayi kuka har yagode Allah kawunshi yayan mahaifiyarshi daya rage mishi shine yayi tabashi baki ya nuna mishi wuta sukaci kuma da yardan Allah bazai amfanesu ba.

Haka nan yacigaba da rayuwanshi a gidan kawunshi ya kuma jefa karsanan shi cikin garken kawun duk da suma basu da yawa domin basufi bakwai ba.

Bayan shera saiga sanuwa ta haifi 'yan maruk'qa biyu suna isa yaye suka saida uwar suka bar 'ya'yan sabida ta tsufa.
suka sayo wasu mata biyu suma shekara na kewayowa suka haihu 'yan bibiyu.

abufa yayi albarka sai gashi a cikin shekaru uku shanun yusufa suntasarma kusan ashirin banda tumaki da raguna ga kaji tare da zabbi.

Ganin haka sai yacewa kawunshi zai shiga duniya neman ilimi sabida ilimi Addin yayi qaranci sosai ayankinsu, bai hanashi ba saima addu'a daya bishi dashi.

Ya soma isa garin kwantagora a inda yahad'u da wani matashi mai suna Abubakar ya taimakeshi ganin yana tare da k'auyenci, ya kaishi gidansu ya kwana washe gari ya kaishi tasha ya sashi amotar garin Zaria birnin ilimi sabida yasanar mishi cewa ilimin addini yafito nema shine yaga ba inda zai samu mai nagarta irin birnin zazzau.

Ya iso garin zaria daf da la'asariyya, ranar ya nemi gidan shehin malamin dazai soma karatu, wani mutum yayi mishi jagora zuwa gidan lamamin mai suna Alhaji malam Haruna mai riguna. yanemi iso atake kuma akayi maraba dashi domin gidane na karamci da nagarta, kowa nasune domin irin adalcin mai gidan, yasa ake karrama bak'o kodaga ina yazo sabida yakance shima ai zuwa yayi gashi har yazama wani abin wanda har ake zuwa wurinshi.

Anan yusufa yasamu karatun AL-QUR'ANI dawasu littafai na addina sai yakoma gida amma akwantagora ya sauka.
Abokin shi Abubakar yayi ta mamakin ilimin da yasamo.
Washe gari yayi misu bankwana ya nufo qauyensu kafin ya shiga mota yaji wani yana bawa abokinshi labarin ya kosa yakoma kano yacigaba da sa'arshi.
Sai yayi tsam da ranshi atake kuma yaji bazai koma garinsu baida komi ahannumshi ba sai kawai yanufi wurin saurayin nan yayi masa sallama ya fad'a mishi intafiya zaiyi to zai bishi, atake saurayin mai suna gambo ya amince suka shiga motan kano.

Ya shigo garin kano da qafar dama sabida a shera 1 yasami alkhairi mai tarin yawa, fad'i yake lallai tacika tumbin giwa.

Sai ya shirya yayiwa abokinshi Gambo bankwana ya nufo gida.

Koda kawu ya ganshi bai ganeshi ba sabida yazama magidanci sosai mai tarin natsuwa daka ganshi kaga cikakken mai ilimi, gashi dama farine sai farin yakuma qaruwa.

Shikuma yayi mamakin irin shanun da kawu yanuna mishi yake nashine domin sunkai garke biyu banda tumakai da kaji tare da zabbi ga kuma kud'in kwan zabbin da yake saidawa insumyi sai ya ajiye mishi, ya tara mishi kud'I masu yawa.

Take yaraba komi biyu yabawa kawu kyauta, dakyar kawun ya amsa, saida yayi tayi mishi magiya.

Dangin mahaifinshi hankakinsu yatashi dasuka ganshi da wannan dukiya sabida nasu dasukaci zalin duk sun kare basu ka komi sai wahala, sai suka nemi da ya auri y'a'yansu yanuna shi baitashi yin aure yanzu ba.

Ya rushe kangon gidansu yayi sabbin bukkoki guda biyar kuma manya.

Yacigaba da zamanshi aciki shi kad'ai wata rana kuma ya leqa wurin kawunshi, ahaka yasoma koyar da yaran garin ilimin addini kuma ba laifi suna ganewa sai dai yaran makwaftansu sunfi zuwa akan na yankinsu.

Bikin abokinshi Abubakar ne yatashi ya kuma zo har dajinsu ya gaiyaceshi shikuma ya shirya yatafi bikin tun ana saura sati 1, komi dashi akayi sabida sosai ya waye ya kuma iya karatun hausan boko da yakoya tun kafin yayi saukan qur'ani.

Bayan angama biki ya komo garinsu yacigana da hidimomin shi.

Watanni biyar baya abokinshi Abubakar yazo misho da zancen qanwarshi zuwairat taface sai shi domin wai tunda taganshi a bikin dayazo takamu da dasonshi.

Bai watsawa abokinsa k'asa a ido atake ba ya amince da soyayyar qanwar tashi sabida shima tun a lokacin yakamu da sonta amma ya boye abinne sabida yaga tana birni bazata dawo qauye ba.

Ba'adauki lokaciba akasha biki aka kawota gidan mijinta.

Rayuwa suka gudamar mai kyau da tsari ga kuma so da qaunar juna da yayi musu jagora.

Sai da ta kwashe shekaru shida sannan ta haifi danta na miji amma kwanarshi biyu ya koma.
Ta kuma haihuwar wani d'an shima ya koma aqalla saida ta haifi 'ya'ya hudu dukannsu maza suna rasuwa sai da kyat Salma ta tsaya kuma sai bayan shekaru biyar da wata biyu sannan ta kuma haihuwar Rabi'atul Addawiyya.

Tunda aka haifi Addawiyya arzikin Abbi yaketa qara habbaka fiye da da, har ya kaima yana da shago a cikin gari na saida kayan masa rufi ya danqawa abokinshi gambo amana kuma yariqe amana domin sosai riba yake samuwa a cikin lamarin.

Sosai yake fatantawa iyalinshi bai gagyesu da komi ba komi sukesu yanayi musu baima bari sunema zai kawo musu.

Abubakar matarshi Ramlat 'yar kano ce shima biki yaje kano suka had'u har sukayi aure.
Ta haifa mishi 'ya mace mai suna Hindatu sai mushaffa'u ke bi mata amma da shekaru tsakaninsu da juna bayanshi ta haifi Aliyu da mudansir.

Tun salma tan 'yar shekaru hud'u Abbi yake d'aukanta akeke ya kaita gari makarantar boko sabida ya qudiri aniyar yaranshi sai sunyi karatun zamani.

Sanda yasoma kai salma makaranta garinsu ya d'auka wai zai maida yaranshi karuwai, musanma d'angin mahaifinshi dama sun tsani matarshi wai itama karuwa ce dukdon tazama y'ar boko kuma 'yar birni gashi kuma tana adawa da al'adarsu ta yawon gudun amare ta kance jahilcine wannan abin.

Duk sukan dasuke ta kawowa Abbi akan boko baikoji d'arba tunda yasami goyon baya a wurin kawunshi.

Sanda Salma ta gama primary lokacin aka saka Addawiyya kuma a shekaran kawunshi ya koma ga mahaliccinshi, gashi kuma dama baya d'a bare jiki sai mata hud'u yabari.

Sosai Abbi yaji mutuwarshi, bayan gama zaman makoki aka raba gado aka bawa Abbi nashi sabida shikad'ai yaragewa mamacin d'an 'yar uwanshi ciki d'aya, ya amsa tare da maidawa matan kawum nashi kyauta yace suqara,, Allah yajiqan kawu mamman yabashi aljanna mad'aukakiya, suka amsa Amin.

To tun a lokacin Abbi yaso barin yankin amma sai ummi tace a'a ya barzancen kawai kowa ai da mahaifanshi yake tunqaho.

Ahaka rayuwa tayi ta tafiya har Salma tagama makaranta hajiya Ramlat ta d'auketa takoma da ita wurinta da zama, wai bazatayi aure a qauye ba, sudai su Abbi nasu idanu kawai suka zuba.

A lokacin kuma Addawiyya ta soma karatuta a boarding school ake garin zuru.

K'addaran dayasami Salma yafarune awani xiyara data kawowa mahaifanta ta cinma ana bikin qawarta tako bisu yawon gudu anan hisk'ilu tare da abokanshi suka yagamata martaba cike da rashin tausayi.

Sanda aka dawo da ita gida baqaramim tashin hankali su Abbi suka shigaba.

Hajiya Ramlat data zo tace sai tayi qaran yaran tare da iyayensu amma Abbi ya hana dole ta haqura ta d'auketa suka tafi akayi treatment d'inta sosai sabida raunin datasamu.

To tundaga lokacin su ummi ke taka tsantsan da Addawiyya amma duk da haka saida azal ya kusa afka mata, Allah ya kareta da fad'awa ciki.

Mushaffa'u yasoma son Salma ne tun kafin qaddarar ya afkamata kuma yacigaba da sonta ahaka sabida yace bayin kanta bane qaddaran Allah ne bawanda ya isa ya hanashi afkuwa.

Iyayensu sosai sukayi tasa mishi albarka akan jarumtar da yanuna tare da taimakon jininshi da yayi.

Hindu kuwa bayan ta kammala karatunta na degree a jami'a minna sai tayi aure da abokin karatunta Adnan suka tare a cikin minna amma zamansu na jin dad'I na sati uku ne katsal yasoma bullo mata da iskanci kala2 inda anan tagane iyayen qarya yayi amafani dashi suka zo amsar mishi aurenta, domin shi d'in baya da cikakken asali karatunma da yayi a jami'a wata magajiyan karuwaine ta d'auki nauyinshi.

Zaman lafiya yayi qaranci a tsaninsu don haka tunda tagane tana da shigar ciki d'an wata 1 sai ta gudu wani asibitin kud'i suka mata allura na zubewan ciki lokacin watansu hud'u da aure.

Takosha wuya sosai domin saida ta kwanta na kwana biyu a asibitin, kuma duk mijinta bai saniba sabida ya lula wani ajon karuwai a garin kaduna.

Aranar da aka sallameta ranar tabar garin minna zuwa kwantagora kuma taqi fad'an dalilin zuwan nata sam.
Har zuwa sanda minjn nata yazo yayi rashin mutuncinsa, mushaffa'u yagyamishi zama.

Yanzu Salma ta kusa kammala school of nursing yayin da ita kuma Addawiyya take ss1.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.