Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 8 of 8
Part d'in Hajiya karima aka fara kaita.
Tana jinsu taqi fitowa har suka gaji Hindu tace "sufito su tafi ai anfita hakkinta.
Suna fita khairi ta fad'a bedroom d'in nata cikin kuka take fad'i take "ni kika wulaqanta momy ba kowaba, masifa ta rufeta dashi wanda yasa dole tafice bashiri domin taga inta tsaya zata bata na gidan bread.
A part d'in Hajja sun sami tarba mai kyau inda tanemi da Abar mata ita da kanta zata sadata da d'akin mijinta, atakeko suka barta suka koma akabarta tare da qawayenta.
Misalin tara saura Hajja ta umurceta data shiga wanka, ruwan zalla turare irin tasu na kanuri tazuba mata acikin ruwan wankar, bayan ta fito ta zuba mata wani na tsugun.
Cike da kunya ta tsuguna, wani d'an ubansun swiss lace ta fito mata dashi bayan ta sata ta mulke jikinta da had'in su humra da kulacca.
Koda tafito wurin su maryam duk miqewa sukayi suna yaba kyawunta Hajja tayi ta fad'in Tubarkallah masha Allah.
Suna shirin kaita part d'inta Hameed ya shigo afujanjan.
"Kai lafiya kuwa? Hajja ta tambayeshi cike da rud'ani.
Dariya yasoma batare da ya amsata ba ya nufi inda Addawiyya take ya kai hannu zai kamata ta noqe, Hajja ta qaraso wurin ta dima mishi duka abaya ya ja baya yana fad'in "Kai hajja mugunta dai bai da kyau, kuma zuwa nayi na d'auki Amaryanmu lokacin zuwa dinner zai qure.
Cikin fad'a Hajja ta amsa "Uban dinner za'a nace, ficemin dagani ko yanzu ranka yabaci.
"Hajja don girman Allah kada kiyi mana haka, kibani ita kada ayi ta jiranmu.
"Hameed kaficemin anan ko ranka ya baci, dinner banza da wofi, to bata zuwa ko qofa ta kashi kaji dai na fad'a maka.
Cike dajin haushi ya fice, ta dubi 'yanmatan tace "irin wannan bidi'ar yake kwashe karamar aure don haka sai ku kiyaye habbaka shi.
Suka amsa da "to cike da yabawa hangen nesa irin na tsohuwar.
A ta qaice dai a part d'in Hajja suka kwana duk don kada ta kaita atafi dinner aboye.
Da yamacin ranar akayi bud'an kai inda Alhaji muktar ya mallaka mata wani gidan hayarsa mai d'auke da parts shiga.
Wayyo zo kuga yarda hankalin h. Karima yatashi, khairice tayi ta lallabata kada taraba abin fad'a qarshema sai tajata kawai suka bar wurin, tana mai cike da qunar rai agame da d'abi'ar mahaifiyarta.
Taro yawatse lafiya qawayenta duk sun tafi sai maryam tare da khairi kawai suka rage.
Qara gyara gidan sukayi, ya d'auki qamshi.
Salma tashigo ta shiryata cikin wata koriyan atamfa mai tsad'a da kyau, ta kuma amsheta sosai d'inkin yayi mata cif2 ajiki, ta yafa gyale kalar atamfar, tafesheta da perfumes masu taushin qamshi.
A gefen gado ta zaunar da ita tace "jirani inzo yanzu my Addawiy, gyad'a mata akai tayi.
Maganganun isowar abokan Ango ya ankarad da ita wayau Salma tayi mata, gudu su kayi suka barta, atake idanunta suka kawo ruwa alokaci d'aya kuma taji gabanta ya bada sound dam!!!
Murd'a handle d'in yayi tare da sallama, can qasar maqoshi ta amsa, tsaye yayi yana qare mata kallo zuwa can ya tako a sannu ya yaye gyalen data rufe fuskanta dashi ya d'ago kanta, tayi saurin kulle eyes hawayen dasuka maqale suka zubo ya sunya sosai ya zaro harshenshi ya lashesu.
Cikin hanzari ta bud'e idanun ya sakar mata murmushi tare da furta "shine cikar so da qauna.
Kayda fuskanta tayi gefe, ya juyo dashi tare da miqar da ita ya gyara mata zaman gyalen sosai ya rufe mata jiki sannan yaja hannuta suka fito parlor inda abokananshi suke jiransu.
nasiha tare da addu'o,i sukayi musu sannan syka ajiye mata kayan siyan baki kamar dai yarda al'adar mafi aka sarin hausa fulani yake.
Sunagama fita ya kulle qofar parlon ya dawo ya cimmata inda yabarta.
Zama yayi a gabanta samar carpet ya zuba tagumi yana aikin kallonta.
Tura baki tayi tare da sakar mishi hararan love tace "miye kuma? "Uhmm uhmm qaunar kice ce zata maidani kurma.
Bata san sanda dariya ta kufce mata ba ganin yarda ya kwaikwayi voice d'in mata.
"Masha Allah ya furta da qarfi tare da d'agata cak kamar baby, bai sauketa ko ina ba sai cikin bathroom, yace "oya muyi arolla sai muyi sallah domin nuna godiyarmu ga Allah.
Bayan sun idar da sallah ya d'au ledar da suka shigo dashi yace "bismillah, girgiza kai tayi alamar ta qoshi. Ture ledar gefe yayi ya miqe yashiga wanka bai jimaba yafito yazo ya zauna gabanta yace "ehem fara aikin ladarki tun yanzu,kallon qari batani tabishi da shi, ya miqa mara cream "shamamin zakiyi, kauda fuska tayi gefe, ahankali tace "niban iyayiwa gato shafa ba, "yau zaki koya zuwa gobe kisoma da koyon yarda ake wanke gato.
Ganin da gaske yakeyi yasa ta marairaice fuska takoma kalan tausayi tace "ya Ali nidai kazo kaci abinci tukunna "in har baza kiciba nima na haqura, shiru tayi tana kallonshi.
"Mai babban suna tun safe baici komi ba don haka ki lallabashi yaci.
Haran gefen da sautin yafito tayi, murmushi mai sauti yaka saki tare da cewa "affuwan Amarsu ta ango yanzu zan wuce dama sallan godiya ga Allah na tsaya binku jam'i amma ba burina naga sirrin kuba.
Da sauri tasoke kanta qasa cike dajin kunyar qarshen Ancen shi.
"Asuba tagari mai babban suna, motsa bakinta tayi alamar amsawa sai kuma ta juyo wurin Haydar taga har yagama shafanshi ya sanya night wear, turare yake fesawa.
Tashi tayi ta d'auko plate ta juye kazar ta zuba fresh milk a cup tazo gabanshi tasoma bashi abaki saida ya qoshi sanna yabata taci kad'an tace taqoshi.
Miqewa tayi tashiga toilet, yabita da kallon tausayi, gamace har mace amma lafiyar mijinta sai a slow, abinda yake ayyanwa a zuciyarshi kenan.
Kansa bisa qirjinta yake wasa yakeyi da sumarta, sai hira yake mata kad'an kad'an ita kam gabanta sai bugawa yakeyi sam bata fahimtar inda hiran nashi ta dosa.
Cire kanshi yayi a bisa qirjinta ya kwance zaren gaban riganta ya tura hannunshi ciki ta rutse idanu, yace "mi yasa gabanki yake beating haka? Tak'i cewa komi, sai da yakuma tambayarta ta amsa ahankali "bakomi barci nakeji kawai, shafa fuskanta yayi ya kai bakinsa daf da ear d'inta yasoma hura mata iska yana mai furta "yi barcinki my life, "uhmm uhmm to kabar huramin iska nan zata iya hanani barci "ohk na bari, ya rumgumeta tsam tsam yana ceqa muyi addu'ar shiga barci tukunna, suna shafawa ya kuma cewa "to asuba tagari kayan Haydar, murmushi tayi tare da kulle idanunta.
ASUBA TA GARI ADDHAY๐
*Mrs j moon*
[1/24, 9:09 PM] Mrs J Moon๐: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*
NA
SAFIYYA.
*39*
Qamk'ameshi tayi sosai, ita kuma sai qoqarin rabasu takeyi tsawon lokaci takasa yin nasara akansu sai ta ja baya ta koma kura bakinta yana fidda wuta ta nufosu ko kafin ta iso iska yazo yayi sama dasu tabisu ta gudu haka sukayi ta keta dazuka kamar walkiya tana biye dasu cikin siffarta na kura awani fili mai yawan itatuwa iskan ta saukesu, ita kuma kuran tuni hasken wurin yasa ta daina gani sai juye juye takeyi tana tsala ihu mai firgitarwa, zuwa can tabace bat.
Jin nishinsa nafita da qarfi kamar mai tsere, shiya ya falko da ita.
Har yanzu yana kwance bisa qirjinta shafa kanshi tayi tana mai cewa "ya Ali lafiya kuwa? Shiru bai motsaba saima qara cukumeta da yayi yana magana wanda bata fahimtar miyake cewa.
Addu'a tasoma tofa mishi afuska zuwa can yaja ajiyar zuciya ya tashi firgigit.
Da lalube yayi turn on d'in globe haske ya gauraye d'akin.
Kallon kallo suka somawa junarsu, ta matsa jikinsa ta miqa hannu tasoma share masa sweat d'in daya jiga mishi face har zuwa jikinsa.
Da sauri ya rungumeta yana sunsuna wuyarta zuwa qirjinta sai kuma ya d'ago ya kama face d'inta ya had'a da nashi yacigaba da sauke numfashi.
Da kyat ta iya motsa bakinta tace "wai mike faruwane mijina?
Muryansa na rawa ya amsa "mufarki nayi mai ban tsoro naga wasu mutane masu girma zasu jefaminke cikin rami mai zurfi ga duhu shine nake ta dambe da su inason na kwaceki amma nakasa daf da zasu jefaki naga kin kwace kin zama iska mai qarfi iskan ya turasu cikin ramin su duka take wani baqin hayaqi ya turnike wurin a dai dai nan na falka.
Shiru tayi tana auna mufarkin da irin wacce tayi yanzu.
Voice d'insa ya katse mata tunani inda yake cewa "Rabi'atu wallahi ni bancika yin mufarkin ababen tsoroba haka ba inko kikaga nayisa to abin zai iya zama azahirance shiyasa yanzu duk na rud'e kada wasu suzo su sacemin ke, yaqara rungumeta yacigana dacewa Allah in hakan ya kasance bansan halinda zan fad'aba, ya saketa daga rungumar da yayi mata ya d'aga hannayenshi sama yace "Ya Allah yasa na mutu nabar matata Addawiyya ba wai ta mutu ta barni ba.
Da sauri ta amsa "ba Amin ba, Allah ka d'auki ranmu atare ya amsa "A'a indai mutu nabarki ki rainar mana yaran dazan bari inhar ina da rabon barin kwaina a duniya.
Kuka ta fashe mishi dashi sosai, zai kamota tayi hanzarin sauka tafice zuwa parlor.
Amfani yayi da inda sautin muryan kukanta yafitowa qasa qasa ya isa wurin sabida parlon babu haske.
Rungumeta yayi tasoma kicikicin kwacewa ta kasa.
Jin yarda yake sauke numfashi kamar mai shashshekan kuka yasa ta d'auke nata kukan bashiri tasoma magana "wayyo Allah natuba kayafemin nasa mijina kuka a darenmu ta amarci, don Allah ya Ali kada kayi fushi dani na fad'a cikin fushin Allah tare da tsinuwar mala'iku akan kukan dakakeyi, don Allah badan niba kayi shiru.
Cak ya d'ata zuwa bedroom ya zaunar da ita bisa cinyoyinsa ya kai hannu cikin riganta yana latsa mata tumbi yace "kezan bawa hakuri akan sakaki kukan danayi amaimakon nishad'i, sannan ki rubuta ki ajiye Ni Aliyu kami kikayimin tundaga yau har izuwa ranar da za'azaremin rai na koma ga mahaliccina nayafe miki.
Cikin muryan kuka ta soma magana "banson haka ya Ali, banson zancen mutuwa, banson haka, yazaka tasani agaba da tsawon darennan kayi tamin maganar mutuwa, agaskiya bana so.
Yana shafa sumar kanta alamar rarrashi yace "affuwan my heart beat bazan qaraba insha Allahu kinji? Tura baki tayi taqi amsawa, yayi saurin kai lips d'insa kan nata.
Da kyat tasamu ya saketa ta ruga toilet da gudu yabi bayanta.
Arollah suka d'auro yajasu sallar nafia raka'a 4 bayan sun idar kowa ya bud'e alqurnin kareem yasoma karantawa cikin ransa.
Sai da suka sallaci subahi sannan suka koma barci.
Aunty Hindu tayo aike yakai sau 3 da break fast d'insu amma sai adawo ace mata anyi nocking basu bud'eba dan haka sanda taga 11am tayi sai ta fito da kanta Salma nabiye da ita abaya, bugu d'aya tayi Addawiyya tazo tabud'e mata, rigan barci ne ajikinta kanta ba d'an kwali sumarta duk ta yamutse sai hamma take zubawa alamar junya takeji.
Idanu waje Salma tace "ke Addawiy kina da lafiya kuwa? Jibi yarda kike amma kika iya zuwa bud'e door, to da wasu canne kumafa ba muba?
Yamutsa fuska tayi ta amsa "nasan daga ku saiko su khairi zasu zomin part da safen nan "au 11am kike kira safia? "Uhm nifa yunwa yataso dani ina daf da shiga kitchen naji ana nokin nataho na bud'e.
Hindu taja hannunta ta zaunar tace "akul nakuma ganin kin fito bud'e qofa a haka, kuma yanzu kije kiyi wanka sai kizo ga break d'in kunan tun 7am na aiko muku dashi sai adawo acemin kuna barci.
Amsawa tayi "tam, mungode sosai Allah yabar zumunci "Amin suka amsa tare da miqewa suka fice ita kuma ta nufi ciki.
Atare suka fito da Haydar cikin shigar shadda coffee colour sunyi mugun kyau sai qamshi suke zubawa, direct dining suka zarce sai da sukayi nak sannan yaja hannunta suka nufi part d'in Abba.
Sosai yaji dad'in ganinsu, yayi musu nasiha mai ratsa jini da jijiya tare da samusu albarka ya miqo keys guda biyu yace "amsa Haydar motoci ne kai d'aya ita d'aya, cike da murna sukayi masa godiya da adduar Allah yajiqan magabata.
Daganan part d'in Hajja sukayi itama tayi ta samusu albarka, anan suka zauna har lokacin sallar azuhur tayi, haydar ya nufi masallaci ita kuma tayi tare da Hajja.
Da dare suna zaune a parlor yanata aikinsa cikin laptop d'insa ita kuma tana yanka mishi fruits.
Hira suke ahankali kamar masu rad'a,
"uhmm ajiye computer nan kasha fruits inka gama sai ka d'ora"ohk angama beauty.
Abaki tabashi yasha sosai sai da yaqoshi sannan yariqe mata hannu ya janyota ya bud'e qafafunsa ya sata ciki, ta zabura zata miqe ya maidata da sauri yace "oya open ur mouth aramawa kura aniyarta.
Kulle eyes dinta tayi "no ya Ali am ok kasan bandad'e dagama cin super ba"uhmm kinsan Allah kozakiyi amai ne sai kinsha.
Kwabe baki tayi cikin shagwaba tace "Allah inkasani amai kai zaka kwashe kayi mopping d'in wurin "eh naji bud'e dai kigani.
Tas ta shanye tana lasan lips.
Dariya yasa mata ta shammaceshi ta mannawa cinyarsa cizo ta ruga da gudu yako mara mata baya yana fad'in "la la la la laaa kika cijenni to sai na rama.
Tana qoqarin kulle qofa ya danno tasaki ta ruga toilet nan ma kafin ta kulle ya shigo.
Cak ya d'au kota, tasoma yi masa ihu yayi sauri rufe mata baki da nashi, tuni ta natsu tasoma amsar saqon.
Satin ta biyu ta koma school inda shi yake kaita ya kuma d'aukota, baya damu dako yana da aiki a office.
tarairayanta yakeyi kamar egg, itama tana qoqarin bashi kulawa sosai, rayuwa mai cike da inganci suke gudanawa.
Su maryam suyi tayi mata tsiya wai yanzu ta koma mara kunya tunda agabansu takeyiwa Haydar fari da shagwaba don iskanci acewarsu har rumgumeshi takeyi da zarrar sun tashiga cikin motar in yazo d'aukanta, takan ce dasu "adaiji tsoron Allah arage liqamin sharri ko asami na cin exam, su kanyi dariya in sunji tace haka.
Yau ma kamar kullum qarqarfe 3pm ta fito hole d'aukan darasi.
Cike take da gajiya ga kuma maranta data matsa mata da ciwo akwanakin nan wanda tasa dalilin ciwon tadai san 2 days kenan dagama mensuration period d'inta don haka bazata danganta ciwon da shiba.
Zaune suke ita su maryam suna ta hiransu ita kuma tayi shiru tana jin wani feeling yana damunta cije labbanta tayi tare da qamqame jikinta wuri 1.
Khairi ta dubeta cike da kulawa tace "ya dai kayan ya Haydar? Banza tayi da ita, maryam ta dafata tace "baki da lafiya ne ko har mun kusa zama mummies ne?
Kallonta tayi da eyes d'in wanda suka sanza launi da kyat tace "dadies zaku zama dai. Dariya suka sa mata, ta miqe ahankali ta nufi inda ta hango Haydar yana gyara parking.
Daf da zata isa ta hango gimbiya zuhfa zaune a back seat suna had'a idanu ta sakar mata murmushi taji muryanta cikin kunninta tana cewa "yau mun hole da masoyina don haka wannan dire data tasomiki nice sanadinta kuma haka zakiyi ta fama da ita har ajalinki yariskeki sannan romancing danabarku kunayi itama narasa yarda zanyi na hana kune shiyasa nasamo mafita kinga yanzu nike da nasara akanki kenan.
Kallonta tayi sosai tako jinjina mata kai alamar tabbatarwa fuskanta d'auke da walwala, wani maqaqin abu taji yataso ya tokare mata numfashi wanda tabbas ta san zafin kishine ya taso mata, adaidai kuma lokacin Haydar ya iso gabanta ya d'an sunkuya yana gyara mata zaman shoes d'inta.
Ya d'ago face d'insa yayi cike da murmushi yace "sannu haskena, ya karatu? Kallonshi tayi abirkice sai kawai taga yayi mata wani baki kamar tukunyar data shekara 10 ba'a taba wanke bayarta.
Cike da fushi ta tureshi kad'an yarage bai kai qasa ba, ko kulawa batayi ba tanufi motarshi kamar zata tashi sama.
Kokafin ta isa makirar tuni ta bace bat sai sautin dariyanta takeji yana mata amsa kuwwa cikin ears.
Tsaye tayi tana gyada kai sai kuma ta juyo face d'in sake kamar ba ita ba.
"Uhmm mijina zo mutafi kaga 'yan matan jami'a sai kallacemin kai sukeyi.
Cike da sanyin jiki ya yaqaraso ya bud'e mata qofa tashi ya rufe, ya shiga yayi key suka bar wurin zuciyarsa cike da tarin tambayoyi.
Ita kam kwanciya tayi sosai a seat d'in sai gyada kai takeyi tare da sakin murmushi lokaci zuwa lokaci bisa ga dukkan alamu sako take amsa.
********Watansu uku da aure aka sawa su khairi rana sati hud'u,
Khairi zata auri d'an yayar momynta namiji yayin da Hameed zai auri budurwansa Zuhuriyya 'yan boko wayayyiya mai kayan alatu cewarshi.
Addawiyya da Haydar zaman su lafiya sai dai matsalar rashin kuzarinsa fa har yanzu babu alamar nasara kuma yaqi sanar da Addawiyya komi akai haka uncle sai boye mata yakeyi yaqi bata haske akai, yadai bata shawaa da tabar yin mafani da maganin da ummie takawo mata haka nan tabar shan wanda Hindu take bata domim suke kawo mata yawan jin ciwon mara.
Tuni ta bari kuma ciwon maran yayi sauqi sosai amma dai abinda takasa fahinta shine wai ko Haydar namiji ne? Amsar datake son sani kenan kuma kunya ta hanata tambayarshi.
matsalar junnj zuhfa kuwa yanzu kam sai tarihi sabida taji ruwan ayoyin Allah da Addawiyya tayi taja mata alqunut dasu sai gashi dakanta ta bayya mata tana kuka wai tabarsu har abada dama mamanta bata son abinda takeyi, tuni Addawiyya ta yafemata tare da neman mata shiriya na Allah yasa tayi tuban na har abada kenan.
Yau bata da class don haka a part d'in Hajja ta yini.
tana cikin kitchen d'an wake takeyi mata sai tajiyo muryan Haydar qasa qasa yana ma Hajja bayani abinda taji ne yayi mugun tada mata da hankali ta dafe qirji, tuni hawaye sungama wanke mata fuska fad'i takeyi "wh zakayimin haka ya Aliyu, sirri yana da dad'i ai.
Wani qarin rud'ani kuma sai ji tayi yana cewama Hajja "nariga da nagama yanke shawara zan saketa kawai amma dai yanzu miye shawaranki akan hakan?
Dafe qirjinta tayi dake barazanar barewa biyu, ta jingina jikin da cabinet sabida jirin dayasoma bilayi da ita, ahankali take ta maimaita hailala hawaye yanata cigaba dayi mata sintiri a fuska.
*mrs j moon*
[1/26, 10:42 PM] Mrs J Moon๐: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*
NA
SAFIYYA.
*40*
Shiru shiru ko zataji amsar da Hajja zataba shi amma bataji komi ba da alamar ma sun bar parlon.
Cikin rashin karsashi ta tsame d'anwaken ta wanke tare da zubawa a kula, dama tuni tagama had'a kayan had'in daza'aci dashi sai kawai ta d'aukesu ta kai dining ta jera, duk abinda takeyi bakinta bai yanke da ambaton sunar Allah ba, shi yasa asannu tariqajin natsuwa yana shigarta tare da kuzari.
Koda ta kammala komai sai zuciyarta tayi ta ingizata datayi wucewarta kawai batare da tayiwa Hajja sallama ba har ta kai bakin qofa zata fita sai kuma ta dawo da baya ta nufi bedroom d'in Hajjar inda take zaton tana zata sameta.
Saida ta saita kanta sosai ta boye halinda take ciki sannan tayi nocking daga ciki Haydar ya amsa mata, ta shiga kanta a qasa ta matsa jikin Hajja ta d'an kwanta sannan cikin sigar wasa tace "komi yayi ready 'yar tsohuwarmu ke yake jira kizo kiyi ta jifan yunwa dashi.
Cike da dariya Hajja ta shafi kanta ta amsa "nagode sosai d'iyar albarka, Allah ya sa ki gama da iyayenki lafiya ya kuma baki zuri'a d'ayyiba.
Sunne kanta qasa ta kumayi ta amsa "Amin can qasar maqoshi ko Hajja datake kusa da ita bataji mi ta ceba.
Haydar kam cike da zumud'i ya amsa "Amin da qarfi.
Kallonshi tayi ta watsa mishi harara ya zaro idanu ta kuma watsa mishi wani harara tare da jan siririn tsaki wanda iyakarshi lips d'inta ya tsaya.
Ganin ya yunqura zai iso wurinta tayi hanzarin miqewa ta nufi hanyar fita tana cewa Hajja "bara na watsa ruwa kafin akira magrib, batajira amsawarta ba tafice da sauri har da had'awa da gudu.
"Kagani ko Ali, yanzu mace kamar wannan mai tarin nutsuwa da hankali ga girmama manya, uwa uba kuma maccen sirri ita ce zaka nemi yin nesa da ita don rashin tunani, to wallahi summa billahil azim akul nakuma jin zance makamancin wannan daga gareka, kaji ko?
Cikin sanyi ya amsa "naji Hajja kuma insha Allah zanbi shawaranki na sanar da ita lamarin "tam haka babu laifi, Allah yayi muku Albarka "Amin.
Koda yashigo part d'insu bai ganta cikin parlor ba sai ya zarce cikin bedroom d'inta, nanma bata ciki.
Wasa wasa ya duba ko ina bata nan, tuni hankalinsa yasoma tashi ya fito compound yana ta waige waige, juyowar da zaiyi ya ganta abayarshi riqe da hannun hussain.
Wani ajiyar zuciya ya saki wanda sai da tajiyoshi amma baisa ta d'aga kai ta kalleshi ba, tayi wucewarta ciki.
Cike da wasi wasin laifin da yayi mata take fushi dashi yabi bayanta.
Tana shiga room d'inta ta kulle qofa koda ya murd'a handle d'in yajishi gam sai ya wuce room d'inshi, arollah ya d'auro yafito ya ja hannun hussain suka nufi masjid.
Addawiyya kam tadad'e cikin toilet tana kuka har sai da taji kanta yasoma yi mata ciwo sannan tayi wanka tare da d'auro arollah ta fito.
doguwar riga kawai ta zira ta tada sallah, bata bar wurinba sai da ta sallaci isha'i ta kuma gabatar da shafa'i da wuttiri.
Cream ta shafa tayi simple make up ta sanya wata riga mai gajeren hannu tsawonta bai gama kai laps d'intaba, ta fesa turare sosai sabida zamowarta ma'abociya son qamshi ne sosai.
Direct kitchen ta zarce ta tayi worming food d'in datayi before taje part d'in Hajja.
A dining ta shiryasu ta d'auki qaramin cup ta had'a tea wanda yaji garin titta tadawo parlor ta zauna tana kurba kad'an kad'an.
Haydar ya shigo d'auke da sallama ta amsa mishi dakyat ya iso ya zauna gefenta ya qurawa cinyoyinta idanu yanajin wank abu na kai komo cikin jikinsa, hannun yakai samar cinyarta ya latsa tayi wani zabura ta miqe tsaye ta sanja kujera baki a ture, cikin sanyi jiki yabita.
Tun kafin ya iso ta miqe ta shige room d'inta da sauri ya bi bayanta yana cewa "wai meke damunki ne haka beauty? Bata amsa shiba.
tana shiga ta murza key ta zame jikin qofar ta saki kuka fad'i take why kayimin haka? Ina alkawarinmu da juna na cewa duk wuya duk rintsi muna tare da juna haka matsalarmu tare zamu warwareshi, amma duk ka watsar, sai ta kuma fashewa da kuka, ni kai nakeso ba wai ka... Sai ta kasa qara sawa ta sunne kanta tsakanin cinyoyinta cewa take "in narasaka ya Ali bansan wani irin hali zan fad'aba, wash Allah na qirjina zafi yakemin kamar zai fashe,,, tafad'a hakan cikin kuka mai cin rai.
"Don girman Allah heart beat ki bud'e door d'in nan, kibar kukan nan haka, ki fito ki sanar dani laifina kinji? wallahi bansan laifin danayi miki ba, ki bud'e ki sanar dani dan Allah. tana jinsa ko motsi taqiyi.
Yafi 30 minutes yana aikin yi mata maqiya ta bud'e amma taqi bud'ewa haka nan yagaji ya koma parlor ya had'e kai da gwaiwa yana son tunano laifin da ya aikata mata haka da zafi.
Ko dai taji zancen danakewa Hajja ne d'azun? To in kuma taji ai tsayawa zatayi muyi magana na fahinta ba fushi ba, to wai ni minayi mata ne?
Abubuwan da yayi ta saqawa kenan cikin ransa har dare ya tsala batare da yasani ba.
Ranar dai kowa room d'insa ya kwana cike da kewar juna sun kasa rintsawa tsawon lokaci sai juye juye suketayi. Bawanda yasan sanda barci barawo yasaceshi, sai kawai farkawa sukayi sukaji anata kiraye kirayen sallar subahi.
Koda tafito taduba dining taga komi bai taba ba sai kaji ba dad'i, d'auka tayi ta zubda wanda ya lalace wanda bai lalaceba ta kai kitchen.
Tsaye tayi a kitchen d'in tarasa mizatayi sai kawai ta dafa ruwan zafi ta juye a fulas ta soya eggs kad'an dai dai cin mutum 1 sabida yarda takejin bakinta baza ta iya cin komi ba yanxu, d'imama ferfesun kayan cikin datayi jiya tayi ta kawosu dinning ta jera.
Daf da zata shiga room d'inta shi kuma yafito cikin shirin zuwa office kallon kallo sukayiwa juna, tayi saurin janye idanunta shi kuma ya wuceta batare da yace da ita kanzil ba. Sosai yayi mata kyau cikin shigarsa ta dogayen kaya na wani yadi milk, sai tasami kanta ta binsa da murmushi.
Daf da zai fice parlon ta daure tace da shi "ya Ali, cike da mulki ya juyo batare da ya amsa ba, had'iye yamu tayi bakinta na rawa sabida yayi mata mugun kwarjini tace "bakayi break fast ba, kamar mai ciwon hak'ori ya amsa "naqoshi daga haka yasa kai ya fice.
"Kam bu!!!! Mi guy d'innan yake nufi ne? Wato tabarman kunya da hauka ake nad'eta kenan? Uhmm zanko nuna mishi ni Autan ummi nafi gaban wulaqanci, kuma wallahi kadawo yayita ta qare in auren aure in kuma rabuwan rabuwa, kai bama zan iya zama da kai ba ehee!!!! Tafad'a cikin qaraji, fuuuu tashige room d'inta sai kai da kawo takeyi tana jan tsaki.
"Mai babban suna ba'ayi haka ba, kiyi haquri, zaman aure sai da hakuri, kuma dama ance zo mu saba zo mu zauna, rayuwa bata taba inganta sai tare da qalu bale cikinta don haka nake roqonki da kiyi haquri ki saurari bayaninsa.
"Uncle!!!! Yau banaji kuma bana gani dan haka kayi tafiyarka kawa kawai kabarni domin kaima mun bata da kai tunda kasan komi ka boyemin.
Iska mai qarfi yasoma kad'awa, sanyi yasoma shiga jikinta tunk tasoma rawar sanyi bakinta na rawa tace "please uncle stop doing dis, i'm begin u, washhh!!! Shikenan nazama iceeeeeee sai ta tafi luuu zata fad'i Haydar yayi saurin tareta ta fad'a jikinsa.
Manage ๐๐ป
Momyn sadiq this page is for you๐๐ Allah yabar zumunci ya raya mana su sadiq rayuwa mai cike da ni'imomi. Amin
*mrs j moon*
[1/27, 4:18 PM] Mrs J Moon๐: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*
NA
SAFIYYA.
*41*
K'amqameshi tayi bakinta yana karkarwa cewa take "Ya Ali katai makeni sanyi nakeji kamar ina cikin snow.
Taba wuyarta yayi yaji babu alamar sanyi saima dumi da yaji.
"Washhh!!!!! Banso nace, kabari don Allah, zan mutu wayyyo ummie sanyi zai mashe ni, sai kuma maganar ta daina fita sai motsa baki takeyi jikinta yana rawar saniyi hak'oranta sai had'uwa da juna suketayi.
Haydar iya rud'ewa yayi yama rasa mizaiyi sai kawai ya d'auketa akafad'arshi ya isa inda ac yake yayi switch d'insa ya kuna ta dumama d'aki, duk tana qamqame dashi, ya koma ya shimfid'eta a bisa gado, ya tube kayan jikinshi yarage dagashi sai vest da boxer.
Ya d'agota ta kufce ta cure wuri d'aya sai kiran sanyi sanyi take tayi cikin muryanta dabata fita sosai.
Da kyat yasamu ya cire mata rigan barcin dake jikinta yarage daga ita sai pant.
Boobs d'inta suka bayya baiko lura dasuba hankalinshi yana kan ganin ta dawo normal.
Vest d'in jikinsa ya kuma cirewa yaja blanket ya rufesu ruf ya rungumeta sosai yana ta murza skin d'insa da nata yana kiran "sorry sorry, sorry my angel yanzu zan ragemiki jin sanyin, haka qaddaranmu take, ki yafemin dan Allah.
Ita kam sai tura kamta takeyi cikin qirjinsa tana kuma jin sanyin yana raguwa kad'an2.
Tsawon lokaci ya d'auka yana abu 1 kuma cikin ikon Allah sai tadaina jin sanyi, tayi lamo a jikinsa ganin haka yasa ya bud'e su kad'an, yaga tayi barci sai lokaci ya lura da kayan ruwanta a fili suke, jim yayi yana qaremusu kallo cike da sha'awar su, ya kai hannunsa kansu yana shafawa asannu sannu tare da lumshe idanunsa.
Afili ya furta "Allah kabani lafiya na biyawa wannan cikakiyar yarinyar buqatarta, donshi tunaninsa dire ce ta dameta har ta fad'a cikin wannan yanayin.
Xuwa can ya koma ya kwantar da face d'inshi tsakanin boobs d'inta tare da lumshe idanu yana mai jin wani yarrr yarrr cikin jininsa, bai jimaba shima barci yayi gaba dashi, bako tuna saqon da Abba ya turoshi d'auka ba, shine daliline ma dawowarshi har zai wuce yaji yana son ganin beauty d'insa duk da bata mishi rai datayi daren jiya, ashe da rabon zai risketa cikin halin damuwa ne haka.
"Uncle haka dama kake da iya cin zalin? Tafad'a cike da shagwaba.
Dariya yasaka mata sosai ta bata rai tayi bakinta a ture ta kuma cewa "inaga kasheni kasoyi da sanyi, bakaji yarda nakejin dhigarsa ba har cikin bargona kamar ana bud'esu ana ziraramin ruwan qanqara.
"Mai babban suna kin batamin rai ne sosai, tayarda inayi miki magana kina maidamin da martani cikin tsawa har dacewa baruwanki dani shine na yanke shawaran bari na horaki koda nan gaba in kin tuna baza ki kumamin haka ba.
Kamar zatayi kuka tace "to kayi haquri insha Allah bazan qaraba fushin abinda ya Ali yayimin ne ya shafeka.
"Nima bazan kuma cutar dakeba mai babban suna kiyimin affuwa, wannan ma danayi duk yabi yadameni ga khadijata nan sai fushi take dani wai nayi mugunta abinda ba halina bane kuma wai narasa inda zanyi sai akanki.
Shiru tayi tana kallon inda yake nuna mata da hannunsa can ta hango wata budurwa zaune akujera wasu mata gewaye da ita da alama fadanci sukeyi, suna had'a idanu da ita tasakar mata murmushi tare da d'ago mata hannu, itama hakan ta maida mata da martani sannan tajuyo tace da uncle "yaushe zakuyi aure ne da juna?
"Ankusa mai babban sun, dafatan zakixo bikinmu ko? "Uhmm kanaso acigaba da cemin jinsin junnu kenan? "Eh, inaso indama da dayarda zanyi ki koma jinsinmu ai da tuni nayi kinkoma cikinmu da zama.
Wani zabura tayi tare da miqewa tana cewa "uncle inaga yanzu kadaina bani kulawa kamar da.
Dawo da ita yayi ya zaunar, ta fizge hannunta tana hararanshi murmushi ya saki yace "affuwan matar Aliyu Haydar.
murmushi ta saki tare da gyara zama tace "uncle sanar dani gaskiyan zancen danaji Ya Ali yanayi da Hajja.
"Uhmm mai babban suna kinfayi alqawarin bazaki kuma tambayata maganar laluran Ali ba.
Dafe goshinta tayi tana mai furtan"oh!! sam na manta, to barshi kawai.
"Anqi a barin sai nafad'a, kafeshi tayi da idanunta tare da baza ears.
Ya koma serious sosai sannan yasoma magana "mai babban suna abinda kikaji yana fad'a hakane tabbas baya da qarfin dazai iya saduwar aure dake kuma shine yasa kakarsa ta matsa sai yayi aure sabida ya sanar da ita laluranshi abinda yayi ta boyarshi tsawon lokaci, duk don ya gane ko abin da gaskiya ne.
Bari kiji yarda yakejin laluran... halittanshi ne yake komawa qarami ya kuma sirance sannan wata zubin ya nad'e ya kom ciki to in yayi haka shine yake yawanjin ciwon mara da kuma son kasancewa da mace. Ada nayi tunanin gimbiya zuhfa ce take maida mishi da halitta haka sai gashi yanzu bata tare dashi amma still yana fuskanta hakan.
Cikin zubar hawaye tace "uncle to baije hospital bane? Yaje mai babbn suna sai dai har yanzu basuyi nasara ba kuma kakarshi tana amso mishi na gargajiya shima bawani sauqi sai na Allah.
"Ikon Allah sai kallo, to yanzu uncle miye mafita? Jim yayi yana tunani zuwa can yace "zan nemi gimbiya zuhfa na tuntubeta naji intana da sa hannu cikin lamarin to ta taimaka tacire ko yasami lafiya in kuma haka Allah ya halicceshi to bamu da mafita sai abinda Allah SWA ya wanzar donmin shi cuta lokaci d'aya yake shigar bawa amma warakarsa sai a sannu, to muna fatan samun warakar cikin amincin Allah.
Nisawa tayi jikinta duk yayi sanyi tace "Allah yakawo mana mafita cikin lokaci qanqani
"Amin mai babban suna, uhmm wata yarinya ta qosa tafad'a cikin kogin amarci, yafad'a hakan cike da zolaya.
Saurin rufe fuskanta tayi tana mai cewa "wallahi banson haka uncle "to nabari, yanzu dai sai ki daina fushi dashi "uhmm Allah uncle sai nayi, sabida tun kafin muyi aure yakamata yasanar dani "mai babban suna yana gudun kada kiqi amincewa dashi ne lokacin "to lokavin da mukayi aure fa? "Shima tsoronsa kada kiqi zama da shine "uhmm to yanzu da yake son rabuwa dani fa "bazai iyaba fad'a kawai yakeyi ganin kamar yana zalintarki na rashin baki hakkinki da yagaza yi.
Kauda face d'inta tayi gefe tana qunquni.
Dariya Habibullah yayi sosai yace "kinganki ko? baza ki daina fad'amin magana bako? Cike da shagwaba tace "cewa fa nayi banson zance kwanciyar nan, kabari "to nabari shi kenan ko? Nodding kanta tayi tana dariya qasa qasa.
Mai babban suna koma duniyarku kinji nima natafi tamu duniyar, yana gama fad'an haka yazama haske ya bace.
Asannu tasoma bud'e idanunta har ta bud'esu tar, jin kamar qirjinta yana mata zafi yasa tamiqa hannunta ta sauke shi bisa kan Haydar d'an zabura tayi abinda ya hayfar da farkawarshi ya zuba mata idanu tayi saurin kulle nata murmushi yayi kad'an ya d'ago ya kai face d'insa daf danata yace "ya sanyin hope yabari yanzu ko da saura?
Tura bakinta tayi taqi cewa komi, fidda finger d'insa 1 yayi yasoma zagaye mata baki da sauri ta bud'e idanunta tare da tureshi daga jikinta tana cewa "ni ka d'agani duk kabi ka taramin gajiya.
Dariya ya saki tare da sauka daga gadon, itama saukan tayi tana miqa ganin ya kafeta da idanu yasa ta dubi kan ganin ta zir sai panta ta kwalla qara ta fad'a bed tare da rufe jikinta ruf da blanket.
Dariya abin yabashi sosai, cikin dariyan ya shige bathroom, har yafito tana qudundune shirya wa yayi ya fice batare da yakuma kulata ba amma tanajin sautin dariyarshi qasa qasa.
Yana fita ta diro tamurza key a qofarta ta isa gaban mirror tana kallon kanta sai kuma tayi saurin duqawa qasa ta tura kanta tsakanin cinyoyinta, "ya ilahi yariga da yagama ganina tsaf yan,, ta furta cike dajin kunya.
zuwa can kuma ta miqe ta nufi toilet da gudu.
Yinin ranar a d'aki tayi shi taqi fitowa parlor wai ita kunyar kada su had'u da haydar takeyi, kuma tana da aji ranar amma taqi zuwa sam.
Haka tayi tajin motsinsa don bai kuma fita ko ina ba shima, ga yunwa tanaji amma taqi fita tasami abinda zara ci, sai bayan la'asar taji fitarsa sannan tafito sad'af2 kamar wata mai laifi tanufi part d'in Hindu, acan taci abinci kuma bata baro part d'in ba sai bayan sallar isha'i.
Tana fitowa zata koma part d'inra taci karo da Hameed, qin tsayawa tayi duk da tanaji yana yi mata magana.
bayanta yabiyo suka iso har cikin parlor n tare.
Haydar suka samu zaune yana cin take away, kallansu yayi na 'yan daqiqa sannan yace "haskena zo kiyi aikin lada, kallonshi tayi ya gyada kai "oya taho kiyi feeding d'in mijinki, cikin dibara ta cilla mishi harara yana 'yar murmushi yataso ya kama hannunta ya zaunar samar cinyarshi tare da kai bakinsa daf da kunninta yana yimata magana.
Kunya kamar me taji tana son tashi amma ya saka hannunsa a qugunta ya riqe gam, hakanan ta zauna amma takasa kallon inda Hameed yake tsaye.
"Uhmm yayi masoyan asali, to kuyi abinku nima nan da 1 week zan wuce gori ai. Hameed yace dasu haka.
Harara haydar ya cilla mishi yaja baya yana dariya tare da nuna Addawiyya yace "Allah sai kinsani in muka had'u, wato kinsan soyayya kike muradi yin shine ina yimiki magana kika mai dani washa hana gashin baki ba geme ko?
Sauke kanta tayi bisa kafad'an Haydar ta amsa "baruwanmu dakai tunda aure yasoma sanja ka, ace mukwana gida 1 mutashi amma baza muganka ba sai dace irin haka.
Zama yayi yana sosa kansa cike da jin kunyarta yace "ayimin affuwa hidmace tayimin yawa wallahi kitambayi mijinki kiji.
Kallo Haydar tayi ya kashe mata 1 eye tare da d'aga mata gira, da sauri ta sauka daga jikinsa tanufi room d'inta daf dazata shiga ta juyo tace "kada kadamu d'an qanina na yi maka uziri, tashige ciki da sauri domin gujewa kallon dake cikin idanun Haydar wanda yake saukar mata da kasala sosai.
Duk dariya suka kwashe dashi mara dashi, tanajinsu itama dariyan tayi tana mai furta "Allah ka barmu tare da juna har izuwa qarshen rayuwarmu.
Haydar da Hameed kuwa tare suka qarasa cin food d'in sannan suka d'ora da zancen yarda bikin zai kasance, sai after 10pm Hameed yayi masa ya fice.
Tana kwance cikin kayar barcin mai laushi riga da wando, chatting takeyi dasu maryam tana ganin ya shigo tayi sauri rufe data.
zaunawa yayi gefen bed tare da kamo hannunta yasoma muzawa ahankali, rintse eyes d'inta tayi tana maijin wani abu yana hawo bisa kanta zuwa dukkanin parts d'in jikinta.
ganin yanayin data shiga sai yayi saurin sakinta ya sunkuyar da kansa qasa yana maijin wani d'aci cikin maqoshinsa, sosai take bashi tausayi yasan duk sanda ya rabeta tanajin feeling amma domin adalci irin nata bata taba nuna mishi rashin yarda ba, "Allah kabani lafiya in ina darabon samunsa.
Can qasan maqoshi ta amsa da "Amin ya rabbi.
Kallon mamaki ya sauke mata sai kuma ya haye bed d'in sosai ya kamota ya miqar zaune ya mannata da qirjinsa tare dayin gyaran murya yasoma magana a natse....
*mrs j moon*
[1/28, 8:39 PM] Mrs J Moon๐: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*
NA
SAFIYYA.
*42*
"Rabi'atul Addawiyya kimin affuwa don Allah, ki agazamin ki zauna dani, kada ki gujeni, inkika gujeni tabbas zuciyata zata buga, ina roqonki domin soyayyarki da fiyayyan halitta Annabin rahama S.A.W Ki haquri da matsalata ki zauna dani kinji?
Shiru tayi masa tana aikin kallonshi bako qiftawa.
Cike da fargaba ya had'a hannunsa da nata ya qamqe gam ta saki 'yar qara kad'an, duk da haka bai sake taba ya kuma matse yatsun nata sosai, "washh Allah!! ta furta da qarfi, sai lokacin ya saketa tare da zamewa ya kwanta rigingime kansa na kallon ceiling.
Asannu ta matsa ta kwantar da kanta bisa qirjinsa cike da sanyin murya tace "mi ke damunka? Daga kwancen ya kallota ya kai hannu bisa sumarta yana shafawa ahankali yana mai bata amsa "bana da kuzarin irinta ko wanni cikakken d'a namiji, bazan iya yin sunnar aure da keba ataqaice dai bana da kwazon da zan iya biya miki buqatarki.
Had'e rai tayi kamar bata san komi ba a kai tace "kasan hakan mi yasa kaqi sanar dani tun kafin muyi aure ko sai bayan aurenmu kasami laluran?
Tashi zaune yayi ya tallabo face d'inta da hannayenshi yace "ina gudun kiqi aure nane lokacin, gashi ni kuma ina tsananin sonki bazan iya barinki ba sannan tun da na soma mallakan hankalin kaina nafahimci ina da matsalar.
Shiru tayi tana kallomsa sai kuma sauke kanta qasa ta kuma cewa "amma mi yasa kaqi sanar dani sanda mukayi auren?
"Tsoron kada kice naci amarki ne ko ki tubure kiqi zama dani shiyasa nayita boye miki.
"uhmm to yanzu kana da yaqinin cewa bazan yima bore ba ne komi?
Shiru yayi zuciyarsa na kai komo, yakasa bata amsa.
Jan numfashi tayi tare da d'agowa ta kalleshi tace "to kuma miye na zuwa kana tona sirrinka wurin Hajja alhalin kasan ta soma tsufa ba komi ne yanzu zata iya dannewa ba, baka tunanin sanin matsalar zai iya jefata cikin damuwa?
"Wallahi tunanin haka sam baizomin ba beauty "uhmm to yayi amma miye nane man shawaran son rabuwa dani alhalin kasan bazaka iya ba?
Dafe kansa yayi cike da nadama domin yanzu yagama gano tsaf taji zancenshi da Hajja, wataqila shine yahaifar da fushin data keyi dashi.
"Ina sauraron ka mr Haydar, tace dashi cike da tsiwa.
Had'a hannayensa yayi wuri 1 yace "affuwan one's again haskena kuma sirrina, lallai nasan na kusa in tafka aikin dana sani sai Allah ya nufeni da rahama yadawo dani cikin natsuwata amma kisani billahil azim ko daidai da second 1 bantaba tunanin zan iya jure rashinki ba sannan abinda kikaji nasanar da Hajja na fad'ane kawai inji ra'ayinta akai sai gashi tayimin wankin babban bargo wanda dakyat nashawo kanta ta sauka kema ina qara neman affuwanki daki yi haquri ki yafemin duk abinda nayi miki wanda yajefaki kicin bacin rai.
Tura baki tayi tana d'an hararansa tace "ni komi ya wuce sai dai banson ka kuma fad'ama wani matsalarka irin haka donshi d'in sirrine.
"Tam bazan sakeba heart beat.
D'an murmusawa tayi tace "Ya Ali, ya amsa "na'am kayana, ta mintsili cinyarsa yasaki qara cikin wasa, ta gyara zama tace "ina son ka rubuta aranka cewa ni Rabi'atul Addawiyya zan rayu da kai acikin ko wani irin hali ka tsinci kanka har izuwa ranar maha'shar, zan zamo mai boye maka sirrinka har izuwa sanda lafiya zai wadaceka haka zan dage dayima ka addu'ar samun sauqi wurin mai duka sannan kasani koza mu dawwama ahaka ne ina tare da kai domin ban mance alkawarin damukayiwa juna ba a cikin garden, don haka kacire duk wani damuwa tare da wasi wasi kawai mucigaba da fadama Allah matsalarmu insha Allahu zaimana maganin komi kaji kayan Addawiyya, ta qara fadan haka tana kashe mishi 1 eye tare da sakin mishi wani murmushi mai kwantar da hankali.
Wani runguma ya kai mata, ya soma sunsuna ko ina na jikinta yana shafawa cike da nishad'i kuma da hanzari yake aika mata da saqon.
Gani zai jefata awani hali yasa tayi dibaran janyewa tana sauke mumfashi da sauri da sauri.
Kallonta yayi cike da tausayawa ya kuma yanjota jikinshi tana qoqarin kwacewa yace "a'a my angel kibari inbaki hot romances yarda zaki sami relief.
"Uhmm ya Ali tafi kayi wanka sai kazo inbaka labari mai dad'i "ya maqe kafad'a kamar wani yaro yace "a'a naqi wayon salon kafin indawo kinyi barci ko?
"Allah bazanyi ba, zan jiraka "ohk tam zomuje kitayani.
Idanu ta zaro tana girgiza kai, lakace mata hanci yayi tare da miqewa yana cewa "matsoraciya kawai, very soon zan soma yi miki wankan ai kuma tas zan wanke komi nawa da kyau nakuma zo na liliyeshi da mai.
Da sauri ta kauda kanta gefe cike dajin kunyar zancensa, yana dariya ya shige cikin bathroom zuciyar cike taf da qaunarta domin hakika tayi mishi bazata data yarda zata zauna da shi ahaka d'auke da lalura.
Kwanakin dasuka biyo baya zamane sukeyi mai cike da tsafta tare da tsantsar bawa junarsu kulawa wanda yake bawa mutanen dasuke tare dasu sha'awa ainun.
Bikin su Hameed da khairi yazo don gashi har nan da kwanaki biyu masu zuwa d'aurin aure, hidima yayi ma Addawiyya yawa sabida Aunty Hindu dazata shige gaba akan abin tana fama da laulayi mai wahala don haka sai itace ke gudanar da komi tare da taimakom Hajja domin Hajiya kareema Alh. Muktar yaqi sakar mata ragamar hidimar har kuwa da abinda yashafi 'yarta khairi yaqi aminta da lamarinta, tayi ta haukanta har tagaji.
Ita kam khairi ko a gyalenta indai tabata kayan gyara na Amare tana sha amma data kawo mata qorafin anyi kaza da kaza zata bar mata wurin sabida tasan tana tofawa to tsiya zata bita dashi.
Da yammacin alhamis suka gabatar da walima mai kyau da tsari.
Ranar gajiya mai suna ita kam Addawiyya tayi ta, don haka tana idar da sallar isha'i ta bingirea wurin ko wanka bata samu tayi ba. Koda su maryam sukazo tabasu gift d'in da khairi ta samu awurin qawayenta zata kaiwa momynta, sunyi2 ta tashi ta kasa saima layi take musu suna haka Haydar yashigo ya korasu suka fice cike dajin haushi, shi kuma ya ragemata kayan jikinta ya d'agata cak sai toilet.
Ita dai tajitane kawai cikin ruwa mai zafi sosai ta zabira tare da sakin qara.
Dariyan dataji yana mata ta fahinci wanka zai mata tako soma mishi shagwaba ita bataso yabarta zata iya da kanta, bai kula taba saida ya sulleta tsaf ya nad'ota kamar baby.
Koda yagama shiryata sai ya shiga nashi wankar kafim yafito tuni takuma lulawa duniyar barci. Rugumeta yayi yana cike da yabawa kwazonta ayayin aiwatar da hidimar bikin hae barci shima ya lula dashi.
Washe gari bayan sakkowa daga sallar juma'a aka d'aura auren khairi da angonta kabir sannan aka wuce aka d'auro na Hameed da Amaryanshi zuhuriyya wacce yabata sunar masoya wai riyya.
Taron biki yayi armashi sosai, qawayen Amarya khairi a part d'in Addawiyya suka tare, sai hidimarsu sukeyi cike dajin dad'i.
Da hayaniya yayiwa Addawiyya yawa sakamakon ciwon da kanta yake mata tun safe sai ta shige room d'in Haydar ta kwanta.
Kwanciyarta ke da wuya ta tsinkayi maganar babibullah yana cewa "sannu mai babban suna, ta amsa "yawwa uncle.
"Mai babban suna nacika miki alkawarinki na tambayo gimbiya zuhfa tace min ba sa hannunta cikin lamari, k'addarar daga Allah ne, zata dai tai maka da addu'a insha Allahu zai sami lafiya yazamo kamar ba'ayiba.
"Tam uncle Allah yasa hakan ya tabbata "Amin Amin.
"Bari nabarki ki huta amma kada kisake kiyi barci a irin wannan lokacin kinji? "Tam bazanyi ba, nagode da samuwarka arayuwa sosai, Allah yasaka maka da alkhairi "Amin.
Yana bacewa ta lumshe idanun face d'inta d'auke da murmushi ta furta "rayuwa kenan mai cike da qalubale, Allah kabamu ikon cinye wannan jarabawar.
***bayan kwana biyu duk 'yan biki sun watse sai gidan yakoma kamar da, tsit bakajin hayaniyar komi sai nasu hussain shima sai ranakun hutun qarshen mako.
Awani safiya Haydar tare da Addawiyya suke matsa jiki sanye suke cikin sport wear suna ta tsale kad'an kad'an a filin dake gefen garden, in tagaji ta duqa, ya miqar da ita su cigaba.
Da dai tagaji sosai sai ta kwanta tana maida numfashi ya iso ya d'ora kanshi bisa ruwan cikinta ya kai hannunsa bisa boobs d'inta yana cewa wai mi kike sha haka ne suke qara cika?
Ture hannunsa tayi cike danshagwaba ta amsa "ba kaine ka damesu da yamutsa ba, ai dole suyi ta kumburi kamar fanke.
'Yar dariya ya saki tare da matsasu da qarfi kuma alokaci d'aya yana mai mannawa cibiyarta kiss ya zarce zuwa samar qirjinta yana qoqarim d'aga mata riga xai tura kansa ciki tayi sauri tureshi tamiqe da gudu ya bita suka soma zagaye filin suna dariya.
Koda yayi nasaran kamata baiyi wata wata ba ya had'e bakinsu wuri 1 sai son kwacewa takeyi amma ta kasa, sai da yagaji don kansa sannan ya saketa tayi baya kamar zata fad'i yayi saurin tareta, idanunta lumshe ta motsa bakinta kad'an tace "Ya Ali yanzu in wani yashigo yaganmu haka mizamu ce?
Mai makon ya amsa mata sai kawai ya kuma had'e bakinsa da nata, ahaka yayi mata d'aukan jarirai ya nufi ciki da ita, ita kam sake maqalqaleshi tayi domin ji tayi kamar zai yar da ita.
Wano uban tsuka taja tare da furta "Wallahi nayi mugun tsanar ki Addawiyya kike koma wa oho.
"Eh dole kice kin tsani 'yar mutunci d'iyar mutanen arziki.
Cike da kad'uwa ta juyo tana kallo Hameed wanda yake tsaye abayanta tun sanda take leqen su Haydar kuma duk yaga abinda ya wakana.
"Mi yakawo wannan maganganun kuma my AH?
"Kinfi kowa sani sannan mi Addawiyya tayi miki da zafi da har kika tsaneta?
Banza tayi dashi zata raba ta wuce ya fisgota ya sakar mata mari yana huci yace "sai kin fad'amin maza nawa sukayi hawan daba akanki kafin in aureki?
Agigice taja baya tana mai jifarshi da wani mugun kallo, acikin ranta kam tsoro ne cike fal domin bata taba zaton wannan ranar zata risketa ba.
"Zaki amsamin ko sai na karya miki wuya kin mace na huta daganin ragowar wasu? Banza kawai karya mai fuska biyu, wato kinsan baki da gaskiya shiyasa kikayitamin zille2 ko? To wallahi kisani bazan zauna da keba harbsai natabbatar da ingancin lafiyarki sabida haka wuce kishirya inje abinkikamin ke ciki da bai don bazanyi da kaina ba.
Zuhuriyya kuka ta fashe dashi mai cin rai, ko kallo bata isheshi yasakai yashige room d'insa yana maijin tsanar kanshi da kanshi duk da bai bi kyalkyala banza ba da haka bai sameshi ba, yanace shi sai mai nonuwa da duwawu to ga irinta nan ya kwasowa kanshi ta kaici, shiba mazinaci ba amma gashi ya auro mazinaciya.
*Hattara dai 'yan mata budurcinki 'yancinki ako ina*
This page is for you Aisha manumfashi, inajin dad'in soyayyarki ga Addawiyya sosai Allah yabar zumunci ๐๐ป๐ sannan tace inbakibar ce mata dangin aljanu ba sai ta kai samar dutsen rafin cigogo kinkwana acan ๐ lol
*mrs j moon.*
[1/30, 9:18 PM] Mrs J Moon๐: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*
NA
SAFIYYA.
*43*
Koda ya fito a inda yabarta tana risgan kuka nan ya sameta, shiru yayi yana kallomta ransa abace, doguwar tsaki ya ja tare da daka mata tsawa ta miqe bashiri ya nuna mata hanyar room d'inta yana mai bata umurni "dalla wuce kishirya tun ban sauke hushina akanki ba, cikin rawar jiki ta wuce tana mamakin bala'i irin na Hameed, ashe dai haka yake da tijara? Tambayar da tayiwa kanta kenan cikin ranta.
Ahanyarsu ta zuwa hospital kowa yayi shiru, sai saqe saqe sukeyi cikin zuciyoyinsu, ya d'an juyo ya kalleta har yanzu bata bar zubar hawaye ba ga kumatun ta nan inda ya mareta har ya tasa kauda kansa yayi yana mai jin tausayinta cikin ransa sabida sosai yake sonta da gaskiya.
Anyi binke iya bincike kuma antabbatar da lafiyarta lau haka shima sumul yake, koda suka dawo gida baibi ta kanta ba room d'insa ya shige ya kwanta yana ta tunanin wannan lamari abinda sam baiyi zatoba sabida dubi da irin tarbiyyan gidan data fito ashe duk ta bogine, uhmm lallai shi natsuwa ba'a fuska takeba dace ne kawai abin.
Sosai lamarin da ya risketa yabashi mamaki in bai mantaba yataba riqe mata hannu tayi ta mishi masifa wai ita ba 'yar iska bace waye2 amma ji yarda yasameta kamar qofar gari, dafe kansa yayi zuviyarsa tayi masa nauyi atake yasoma kiran sunar Allah cikin lokaci qanqani yaji sanyi yana ratsa mishi zuciya.
"Abdul hameed don soyayyarka da ma'aiki SAW kayimin affuwa, maganarta ya doki cikinn ears dinshi.
Kallonta yayi sai daga kwancen sai tausayinta yanemi karya mishi zuciya.
Janyota yayi jikinsa yace "fad'amin gaskiya miyasa kikayi yawon ta zubar?
Lafewa tayi jikinsa cikin muryan kuka tasoma magana "ba'ason raina na aikata ba, sharrin qawayene wata rana a skul qawarmu tayi birthday shine muka had'a party domin tayata murna to anan suka samin abin maye ya bugar dani mazan wurin sukayi watandensu dani, lokacin dana fahimci haka nayi kuka mara adadi sannan naja musu Allah ya isa yafi cikin Duran, baya kwana biyu sai na fad'a halin son kasancewa da d'a namiji abinda ya kaini da nemansu da kaina to tundaga nan na sami abinyi lokaci zuwa lokaci nake aikatawa, kuma agida bawanda yasani domin Abu yana da tsanani kuma yayarda dani ainun shi yasa na boye musu halin dana ke ciki tun farko don gudun jefasu cikin tashin hankali.
Ranar wata littini da bazan manta da shiba arayuwata, na sawo kai kenan cikin hostel sai naji qawayena suna gulmar wai zubamin magani mai tada dire sukeyi shi yasa nakejin son kasancewa da d'a namiji, jin hakan hankalina yayi mugun tashi na koma da baya don kada suganni.
To kundaga ranar na koma gida daga can nake zuwa skul sannan tuni na na d'aukewa qawayen nawa wuta baruwana dasu har xuwa yanzu banayi musu magana don ko bikina ban bari sun sani ba.
Ta fashe da kuka mai qarfi tana buga kanta aqirjinsa, riqeta yayi cike da tausayi yace "ya isa hakanan riyya Allah zaiyi miki sakaiya, qarshensu bazai kyauba, sannan nayafe miki Allah ya yafe mana baki d'aya.
Cike da matsanancin kuka ta qamqameshi, shima qamqametan yayi tare da cewa "fad'amin abinda Addawiyya tayi miki da zafi da har kika tsaneta?
"Uhmm ni batayimin komi ba haka kawai naji bansota sam.
D'aure fuska yayi ta mau ya nunata da yatsa " banson sakejin makamancin wannan maganar abakinki, ina ruwarki da ita da zuciyarki zata tsaneta? To kisani ita mai kyawun mu'amalace ga kowa kuma lashakka babu nasan bata damu da keba bama tasannkalar kiba tunda har yau nasan bata shigo part d'innan ba, kota shigo?
Girgiza kanta tayi tare da amsawa da A'a "to kinga tabbacin bata saki aranta ba kenan, don haka ina son kisama ranki sonta kuma ki bita tunda itace babba dake a aure duk da kin girmeta a shekaru, dafatan kin fahimceni?
"Eh, ta amsa ahankali "tam Allah ya had'amana kanku "Amin ta amsa amma aqasan ranta sam batajin sonta kuma tarasa dalilin hakan. Daganan suka koma kamar wani abu bai faruba sai dai Hameed yasaka mata idanu sosai don gudun kada azo tubar mazuru tayi.
Awani dare Haydar ne zaune yana aiki a computer.
Addawiyya ta iso wurin cikin shigar barci, ta zira kanta a kafad'arshi tana leqen abinda yakeyi kallonta yayi ta hasken computer n tare da shafar fuskanta "my angel barci yazo ko? "Uhmm ta amsa tare da kai hannunta cikin rigarsa tasoma wasa da sumar dasuke kwance aqirjinsa, kuma kallonta yayi yaga idanunta kulle kashe computer n yayi ya janyota ta dawo samar cinyoyinsa "ya akayi ne beauty? Murya can qasa ta amsa "wani kewa nakeji yana baquntata wanda narasa ta miye, ina fatan Allah yasa ta alkhairi ce dai "to Amin haskena.
Miqa tayi tare da hamma yabita da kallo yanajin tausayinta sabida yasan bakomi ke damunta ba sai dire amma ita da alama bata gano hakan ba.
"Tashi muje na ragemiki kewar dake damunki.
Kallonsa tayi kad'an ya kashe mata ido 1 tura baki tayi tace "kai ya Ali ni bawannan abin ne ya daniba kawai ji nake kamar zanyi rashin abu mai mahinmanci arayuwata, wata qila Ummie ko Abbie zan rasa. Sai saka mishi kuka sosai.
Shima sai jikinsa yayi sanyi eyes d'insa ya kad'a ji yake kamar ya tayata kukan amma yasan in yayi haka zai jagula komi don haka sai ya d'agata cak ya nufi bedroom da ita, da kyat yayi nasaran rarrashinta ta daina kukan barci ya kwasheta sai sauke ajiyar zuciya take tayi. Washe gari haka ta tashi ba walwala kuma taqi zuwa skul duk kuwa da test d'in dakake dashi don haka 12pm Haydar yataso daga office ya d'auketa suka nufi gidan su Abbie, acan suka yini sai dare duka dawo tuni ta kawo normal suka cigaba da shinfid'a rayuwarsu mai cike da nagarta.
Lamarin zamansu da zuhuriyya kuwa ba yabo ba fallasa domin tuni Addawiyya ta gano tsanarta atare da ita don haka sai ta fita shirginta tabawa banza ijiyarta inba sun had'u part d'in Hajja ba har mantawa take da wata halitta zuhuriyya.
Al'amura suna ta tafiya cike da nasarori yanzu haka matar Hameed zuhuriyya ta haihu tasami baby girl ansamata sunar ummansu suna kiranta da ummul bait haka itama khairi ta haihu ansami takwaran Abba suna kiranshi da Abbul bait.
Aunty Hindu dama ita ta rigasu haihuwa twins ta kuma sinbulowa duka mata yayin da Adda Salma itama ta kuma samun qaruwa yanxu yaranta uku biyu maza mace d'aya.
Addawiyya ce dai tun suna saran ganinta da ciki har sun haqura sun duqufa fad'ama Allah itama ya bata intana da rabo.
Karatunsu kuwa tuni har yazo gaba goshi ita da khairi maryam ce dai ake ta fafatawa don karatun medicine sai anjajirce.
Hajiya karima angamu da iftila'i domin tana zaune taji tasa tashi kafin ace me qafafunta sun kunbure suntom, anyi maganin asibiti har saudi an kaita amma ba cigaba illa dai anyi nasaran kunburin ya baje tafiya dai ne bata iyawa dole aka bata keken guragu take amfani dashi.
Ranar da ta hau tayi kuka mara adadi har tabawa kowa tausayi, atake kuma nadama yazo mata tayi ta fad'an dukanin tuggun datayi ta had'awa tun tuni tare da roqon gafararsu musanman Hindu wanda taso hala kawa 'ya'ya Addawiyya ta cecesu sai lokacin kowa yaji abinda tayi akayi ta mamaki lamarin kuma hakanan suka yafe mata tana hawaye tana yi misu godiya.
Abba yasamo wata dattijuwa dazata riqa kula da ita domin danginta kowa yaqi yarda yazo sabida sanda take da lafiyarta sunce bata tsinana musu komiba sai mulki da gadara.
*uhmm duniya kenan mai abin al'ajab kuma rawar 'yan mata na gaba ya koma baya, Allah kasa muyi kyakykyawan qarshe*
Yau da jin soyayya Haydar ya tashi domin duk inda Addawiyya tayi yana laqe da ita yana aikin latsata gashi aiki takeyi na snacks d'in birthday d'in su hassan, duk yabi ya takurata yana hana mata aikin yayi sauri.
Agajiye taja ta tsaya tana hararanshi "Ya Ali don Allah kabarni haka nan, ingama aikin dake gabana sai kayimin koma miye bazan hanaka ba.
"Kintabbata? "Eh wallahi zanma duk abinda kake so "tam gama kuwa in kasheli da love.
Siririyar dariya ta saki tace "wai ba kamar gaske "au haka kikace? To zan ko shayar dake mamaki kam "uhmm nidai naji matsa kagani inyi ingama lokaci yana tafiya.
Sa hannu yayi yasoma ta yata har suka mammla da komi suka gyara inda za'a gabatar da party n sannan sukayi wanka tare wurin shiryawa da kyat yabarta tagama yin kyalliya.
Yara sun taru sosai na dangi da makwafta.
Abin kuma yayi kyau sosai, Addawiyya ce ja gaba sai photos ake tayi misu da videos.
Daf da za'a watse taro zuhuriyya ta baiyana d'auke da yarinyarta mai kama da ubanta sak.
Addawiyya na ganinsu ta soma hararan su cikin wasa tace "akoma bama so tunda kuna gidan amma sai amakare za kuzo tayamu murnan.
Kallon tsana ta cilla mata tana murmushi, amma cikin kissa yarda ba kowane zai gane hakan ba.
Addawiyya kam tsaf tanago inda ta dosa sai kawai ta saki murmushi itama mai d'auke da matsalarki ce.
Hannu ta miqa don tabata ummul bait amma sai ta noqe ta wuceta abinda yayi mugun jefata cikin jin kunya ta sauke kanta qasa tana wasa da yatsun hannunta.
Azuciye Hameed yazo ya fincike yarinyar ya iso inda Addawiyya take tsaye ya miqa mata ita tare da cewa "ni Hameed indai nine mahaifin ummul to daga yau nabaki ita kyauta na har abada, yanzu kece uwarta kuma banson kiyimin musu akai indai na isa nayi miki kyau ki amsa.
Tsit wurin ya d'auka kamar mutuwace ta gifta.
Muryan Hajja ya katse shirun "Hamidu lallai wannan kyauta ta faran tamin rai sosai kuma Rabi'atu ta amsa ta gode ainun Allah yata yata riqo.
"Amin mutanen wurin suka amsa, ta d'ora sai dai ina roqon abarta zuwa sanda za'a yayeta sai ta amshi kayanta.
"Hakan zance Hajja, cewar Haydar.
Hameed ya jinjina kai ya amsa "tam ai abin kamar gobe ne in muna da rai.
Cike da murna Addawiyya ta d'aga ummul sama tace "Allah ya albarkaci rayuwarki 'yata, ina sonki sosai, jama'a kushaida.
Sai addu'ar Allah tayata riqo ake tayi mata, yayin da zuhuriyya tuni tabar wuri zuciyarta cike da jin zafin mulkin mallakan da Hameed yayi mata batare da shawaranta ba.
Daren ranar Haydar yazo mata da wani baqon lamari wanda yagigi tata, domin daga romances sai ya zarce, tuntana d'auka lamarin wasane sai ga abu ya tabbata lafiya tasamu gareshi.
Taso ta d'aure amma ta kasa sai kawai ta saka mishi kuka tana bashi haquri amma ina Haydar yayi nisa bayajin kira, ya fad'a wata duniya da bai taba zaton da ita ba.
Koda yadawo natsuwarshi sai kawai ya fashe da kuka yana jera godiyarsa ga Allah subbahanahu wata ala da ya jarabbeshi da lalura kuma gashi ya yaye mishi alokacin dabaiyi zatoba.
Shi ya taimaka mata ta gyara jikinta sannan ya d'aukota ya shifed'e bayan ya fidda bedsheet d'in daya baci ya sanja wani, tsarkake jikinsa yayi shima ya zo ya rungumeta yasoma magana "Rabi'a Allah yasa kigama da iyayenki lafiya, Allah yayi albarka arayuwarki, Allah yacika miki dukkannin burukanki na alkhairi Allah yasa murayu da juna in da rabon haka, Allah yasa kece matata cikin aljanna, wallahi ina sonki Addawiyya, bana son inbarki, Allah yasa sanda zamu koma ga mahaliccinmu a tare da juna za'a zare ranmu.
Can qasar maqoshi ta amsa "Amin.
Bayan sun sallaci subahi Haydar yace mata kansa yana ciwo abu kamar wasa sai gashi yasoma fizge fizge duk tabi ta rud'e.
Number Hameed ta kira qara biyu yayi ya d'auka cikin kuka tace "Hameed kazo ya Ali zai tafi yabarni, ai bai gama jin metace ba yafito da gudu zuhuriyya tana tambayarshi bai ma san tanayi ba.
Tai makon gaggawa yasoma bashi har numfashinsa ya dawo normal sannan ya d'aukeshi suka nufi hospital dashi.
Addawiyya tun tana kuka da hawaye har ya komo hawayen ya qafe, ga jikinta da batajin dad'isa sam, abu dai duk yataru yayi mata yawa, takasa zaune ta kasa tsaye sai kai kawo takeyi.
Hailala tare da istiggifari take ta ambata afili, addu'ar Allah yabashi lafiya kuwa tayisa har tabawa uku lada, cikin 'yan awanni har tayi wani mugun rama.
*mrs j moon*
[1/31, 4:54 PM] Mrs J Moon๐: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*
NA
SAFIYYA.
*44*
Zaune take bisa kujeran roba a gaba gadon dayake kwance ta sarqe hannunta da nashi tare da kwantar da kanta samar qirjinsa idanunta lumshe, fatarsu duk ya kumbura da alama barci ne ya d'auketa ahakan.
Can daga d'an nesa take hangoshi cikin shigar sutura masu kyau tare da kyalkyali har suna kashe idanu don walqiyarsu.
Tafiya tasomayi don ta isa wurinsa amma sai taga yana mata nisa sai ta soma gudu gudu kad'an nanma dai takasa isa inda yake sai kawai ta soma kuka tana kiranshi tare da falfalawa da matsanancin gudu, yana dai ta cigaba dayi mata nisa tare da yi mata murmushi yana kuma d'aga mata hannu ita kam sai gudu takeyi don ta isa wurinshi amma sai taga kamar ana janta baya ahaka har ya bacewa ganinta ta zubbe bisa guiwoyinta a filin mai cike da ciyayi kwance lufluf tare da kalla mishi kira da qarfi "Ya Alee!!!!!.
Kiran da yayi amsa kuwwa cikin room d'in tare da haddasa farkawanshi a firgice sabida amsa kuwwan da sautin yayi cikin kunninsa, bakinsa d'auke da salati.
Shafa kanta yayi ahankali tare da kiran sunarta, tabud'e idanunta wanda suke cike da hawaye sai sauka sukeyi bisa quncinta.
Hannu ya kai yasoma share mata hawayen tare da girgiza mata kai face d'insa cike da annuri.
Kallonsa takeyi kamar yau tasoma ganinsa sabida sai taga yaqara mata kyau sosai kamar bashine aka kawo rai a hannun Allah ba, agefe 1 kuma zuciyarta cike take taf da mamakin mufarkin da tagama yanzu.
Shin ko me hakan ke mufi?
" beauty bani ruwa insha maqoshina kamar zai kama da wuta.
Maganarshi ta katse mata tunanin data afka ciki.
Jikinta ba kwari ta motsa domin d'auko mishi ruwan roba.
Tana shirin bashi ruwan kenan Hameed ya shigo tare dasu Abba.
Hameed yayi hanzarin cewa "A'a Addawiyya kar kibashi bari na dubashi tukunna.
Komawa tayi ta zauna ahankali tana rintse idanu sabida zafin datakeji kad'an2 aqasarta har yanzu sai kuma tayi saurin zamewa ta sunkuya ta gaishe da Abba tare da aunty Hindu suka amsa suna tambayarta mai jiki "yaji sauqi ta amsa.
Hameed ya dubashi tare zare mishi drip d'in sannan ya bashi ruwan da kanshi.
Ya tambayeshi "yanzu ina yake mishi ciwo? Ya amsa "ba ko ina, naji sauqi sosai.
"To Allah ya qara lafiya, cewar Abba suka amsa "Amin.
Aunty Hindu ta had'a mishi tea sabida koda zaiji karfin jikinsa.
Ita take bashi abaki fitar Abba da Hameed yasa ta miqawa Addawiyya ta bashi ba musu ta amsa tasoma bashi har yasha rabi sanna yace "haskena shanye sauran don nasan kema bakici komi gashi kuma bakya da lafiya.
"Mike damun autan ummin? Hindu ta tambayeshi.
Murmushin qarfin hali yayi sannan yace "aunty tana buqatar kulawa dan Allah kitaimakeni tasamu.
Had'e rai tayi tana zabga mishi harara ya saki 'yar dariya kad'an tare da janyota jikinsa tayi sauri tashi ganin haka Hindu ta fice d'akin yarage daga ita sai shi.
"Haskena wurin yabaryi miki zafi ko? Banza tayi mishi, ya matse ta ta saki 'yar qara, ya sake cewa "yabari ko kuwa? "Eh, yabari "da gaske? "Eh "to madallah sannu kinji na wahalar dake jiya ko?
Kauda kanta tayi gefe sannan tace "Ya Alee kabar yawan surutu kasan kana buqatar hutu inji doctor ko?
"Uhmm beauty to nayi shiru amma d'an matsamin qafafuna jinsu nake kamar ba nawaba.
Cike da tausayawa tasoma matsa mishi qafafun shi kuma yayi mata quri da idanu yana aikin kallonta bako qiftawa.
Suna a haka zugan su ummie suka shigo, tayi saurin komawa samar kujera ta zauna suka kayi tayi masa ya jiki yana amsawa cike da murna. Ita kuma ta gaishe dasu cikin ladabi.
Yafito aunty Hindu yayi da hannu ta matso daf da bakinsa ganin yana tunata yasa tayi saurin barin d'akin sabida tasan maganar d'azunne bai bariba.
Koda tafito gefe ta samu ta zauna tazuba uban tagumi.
Hameed ya qaraso wurin ya zauna gefenta yace "yakamata ki cire damuwa aranki haka nan ko don ingantuwan lafiyarki.
"Uhmm kawai tace.
Ya gyara zama yana qare mata kallo cike da mamaki, donmin ya kauda zarginsa sai yace "amma kamar qafafunki sunayi miki ciwo ko?
Kallons tayi tama rasa mizatace mishi.
"Nagano hakan ne tayarda kike tafiya kamar ba dai dai ba.
Kauda fuskanta tayi cike da yabawa rashin kunyarshi wato amatsayinsa na doctor yariga da tuni ya gano komi kenan amma don tsaban rainin wayau tare da fitsara shine zai zo yasata agaba da tambayar wofi.
"Kaga malam banason sharhi, ni lafiyata lau don haka sai ka barni naji da abinda ke damuna.
"Uhmm "aunty Addawiyya kenan daga zan tai makeki sai ki hauni da masifa, to Allah yabaki lafiya amma dai ina cikin mamakin yar da abin yakasance haka alhalin kun wuce 3yrs da aure yanzu.
Tsaki taja tare da miqewa tayi gaba tana qoqarin dai daita tafiyarta tun kafin wasu sa'idanawar su gani.
Murmushi yayi tare da shafan sajensa ya furta "kin canci asoki da girmamaki, ina tayaka murna brother da samun 'yar albarka.
Tana shiga Hindu ta kama hannunta tayi qasa da murya "autan ummi mike damunki Haydar yaketa jaddadamin cewa in baki kulawa bakyajin dad'i?
Kallon inda yake kwance tayi yako sakar mata murmushi ta wulla mishi harara tareda tura baki ya yafitota ta kaqe kafad'a.
Ita dai Hindu sai kallon ikon Allah takeyi, ganin sunqi daina maganar kuramen sai taja hanunta zuwa bakin gadon tana mai cewa "ku sanar dani ko laulayin ciki takeyi dama naga tayi rama ta kuma qara haske.
Cike da shagwaba tace "aunty abar kaza cikin gashinta kawai amma dai nasan ni banda komi.
"To ai shikenan tunda bakyason musani muyi addu'a akai.
Zama tayi gefen gadon taqi kuma cewa himdu komi.
"Kaiko Ya Alee burinka ka tona mana sirri ko? "A'a haskena, inadai son abaki kulawa ne wanda rashin layar nan tahana in baki "to bana so nace, kabari kana sani jin kunya "tam nabari hajiyata, d'an murmushi tayi tana jifarshi da hararan wasa.
Kwanaki biyun da yayi 'yan uwa da abokan arziki sai tururuwar zuwa dubashi suketayi kuma alhdulillah yasami lafiya sosai.
A yammacin daya cika kwanaki hud'u yana zaune ya d'ora qafafunsa bisa cinyoyin Addawiyya wacce take yanke mishi farce da cut nail hira sukeyi qasa qasa xuwa can ya ja numfashi mai qarfi tayi saurin dubashi ya sakar mata lallausan murmushi yace "yanzu ace in na mutu wazaki aura?
Wani kallo tacilla mishi fuska ahad'e tace "banson zancen mutuwanan fa ya Alee
"uhmm heart beat ai kam zancen mutuwa tazama dole sabida ko kana so ko baka so dole sai ka d'and'ani d'acinta don haka amsa min tambayata kawai.
Cike da fushi ta miqe tana cewa "daga kai nagama aure don haka sai ka daina kiran mutuwa in kuma kaqi Allah yau bazan kwana da kaiba, gidan Abbie zan tafi sai da safe nadawo.
A'a zo kusa dani matata, bazan sake maganar ba.
Matsawa tayi ya sun kuyo daf da kunninta yafad'a mata wani magana wanda yasa ta zabura ta ja baya sai kuma tafice tana zubar hawaye.
Tana fita taci karo dasu maryam, khairi tare da zuhriyya da fara'a ta tarbesu tana boye musu hawayen da tafito dashi tare suka dawo d'akin.
Hira suke tayi cike da raha har da zuhriyyan yayin da ummul ta maqale mata taqi yarda dako mamarta ta amsheta.
Tanaji ajikinta idanun Haydar yana kanta amma taqi duban inda yake sabida bata huce zancen takaicin ya yayi mata d'azun ba.
Kwanarsa shida aka bashi sallama suka nufo gida.
An sallamoshi da kwana biyu da hantsi tana cikin kitchen taji ya kwalla mata kira ta kashe stove da hazari tare da amsawa.
Afalo ta cinmashi ya takure wuri d'aya yana rawar sanyi ta sunkuya tana tambayarshi "sanyi kakeji? Kai ya gyada mata tare da yanyota ta fad'o kanshi yayi mata wani runguma kamar zai ballata fad'i yake "ina sonki Rabi'a.
Bakin na rawa itama tace "nima ina sonka sosai ya Alee.
"To in haka ne ina son ki amince da zancen da nayi miki ranan a hospital.
"Ya Alee bazan iya bane.
"Zaki iya my angel Allah zaki iya. Yafad'a hakan cike da kwarun guiwa.
Tureshi tasomayi tana fad'in sakeni in tafi wurin ummie tunda ka gaji dani neman kai kale dani.
Gam yariqeta ya hanata kufcewa yana fad'in am sorry am sorry abin alfaharina nabari Allah nabari.
Zuwa can tace "to sakeni in samowa abinda zakaci.
"Bazanci komi ba "sabida mi? "Hakanan kawai "to tashi muje ciki ka kwanta tunda kabarjin sanyin
"uhmm Rabi'a ni kad'ai nasan minakeji acikin jikina, kawai tafi ki kiramin Abba tare da aunty da kuma Hameed.
Gabanta ne ya wani yanke ya fad'i rass!! Bakinta narawa tace "mizasuyi maka?
Shafa fuskanta yayi cike da juriya ya amsa "kada kidamu ganinsu kawai nake son yi.
"Ohk to bara nakira aunty ta waya sai ta sanar a Abban, hameed shima kiransa zanyi "badamuwa kirawomin su d'iyar albarka, wallahi komi kikayimin tuni na yafe miki kema kiyafeni.
Banza tayi dashi don tasan neman magana yake da ita tunda yasoma zancensa mai kama da wasiyya,, tasoma dialing numbers.
Cikin mintoci biyar duk sun taru cike da fargaba suna zaton ko jikin ne amma sai sukaga sabanin hakan.
Addawiyya kitchen takoma tacigana da aikinta har ta kammala komi tana shirin fitowa dasu zuwa dining ta tsinkayi salatin da Hindu ta kafka da qarfi aibata san sanda ta iso wurin ba ta zube gaban Haydar wanda yake jikin Abba kwance.
Jijjigashi tasomayi tare da kiran sunarshi taji bai amsa ba ta d'ago cike da fargaba tace da Hameed "mike faruwa ne? Mai makon ya amsa mata sai kawai yafice yana kuka, juyowa tayi tace da Hindu "Aunty badai nayi rashin ya Alee ba?
Sauke kanta Hindu tayi qasa ta kasa kallon Addawiyya.
Sallallamin Hajja tare dajin kalmar "Allah yagafarta maka Aliyu shine ya tabbatar mata da cewa ya Alee ya barta har abada.
k'ara ta kwalla mai qarfi bakinta d'auke da Kalmar innalillahi wa inna ilai.... Bata qarasa fad'aba ta sulale qasa babu numfashi.
Abba ya miqe arikice d'auke da Haydar a hannunsa yana mai cewa Abdul "d'auko Rabi'atu mukaisu asibiti, ke kuma Hindu biyomu amma Hajja kijira mudawo yanzu.
*I'm sorry readers please*๐คฆ๐ปโโ
*mrs j moon*
[2/1, 3:45 PM] Mrs J Moon๐: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*
NA
SAFIYYA.
*45*
Suna isa hospital aka amshe su bajimawa wani doctor yafito ya sanar dasu Haydar yajima da rasuwa amma ita matarsa doguwar suma tayi wanda zata iya d'aukan lokaci mai tsawo kafin tafarfad'oba, wata qila ta d'auki kwana 1 ko 1wk koma fiye da hakan.
Tashin hankali kenan wanda ba'asami rana ga dai jimamin rasuwar Haydar ga kuma firgicin lalurar da Addawiyya ta afka ciki duk alokaci d'aya.
Bayarda suka iya da hukuncin ilahu sai haquri tare da addu'ar Allah yabasu ikon juriyan wannan k'addarori dasu afko cikin rayuwarsu.
Allahumma Amin.
Anyiwa Aliyu haydar sutura dibbannin mutane suka miqashi zuwa makwancinsa na gaskiya suka baroshi daga shi sai halinsa sai kuma abinda ya shuka.
Mutuwar ta gigita duk kanin d'aukakin al'umman gidan musanma Hameed wanda ko maqabarta bai iya rakashi ba, tunda yadawo daga asibi ya kulle kansa cikin room d'insa sai da ya kwana ya yini bai bud'e kansa ba, anyi ban bakin har an gaji yaqi bud'ewa sai da Abba ya tako dakansa zuwa part d'in, yasaka mishi kuka abakin qofar sannan ya bud'e tare da fad'awa jikin Abba yana fad'in "Abba yanzu brother yatafi yabarni kenan?
Tambayar da ta kuma saka kowa dake wurin kuka kenan, Abba baibashi amsa ba illa wucewa da yayi da shi zuwa part d'insa yayi tayi masa nasiha tare da bashi misalai har yadawo natsuwarshi yasoma yi masa addu'a yana mai zubar hawaye wanda yarasa yarda zaiyi ya tsaidasu.
Hajja kam sosai tabawa kowa mamaki domin itace mai rarrashin duk wanda yazo da kuka tayi ta cewa addu'a yakeso ba zubar jurwaye ba.
Salma da Hindu kuwa baka gane wanda yafi wani fad'awa ciki firgici cikinsu, suke zaune wurin Addawiyya.
Anyi anyi subar ummie ta zauna sunqi.
Khairi da maryam suma sai da suka sume sanda zancen ya samesu, sunyi kuka har sun gode Allah.
Duk wanda yasan Haydar sai da yayi jimamin rasuwarshi hatta da abokanan aikinsa sunshiga rud'anin rashinsa.
Kowa yayi mishi shaidan arziki baya da abokin fad'a sam, shi bai damu da shiga shirgin da ba'a kasa dashi ba, duk abinda zaiyi to mai ma'ane gashi da riqon gaskiya da amana.
Lallai yasami yabo ta ko ina don haka akeyi masa kyakykyawan zato.
To koma dai miye Allahn da yafimu sonshi ya amsa abinsa sai dai fatan Allah yajiqansa da rahama in kuma tamu tazo Allah yasa mucika da imani, Amin.
Yau kwanar Addawiyya goma sha d'aya batare da ta farfad'oba lamarin da yadagula zuciyoyin dangi babba da yaro.
Ranar da tacika sati biyu na'urorin dake kewaye da ita suka soma tsuwwa alamun ta farfad'o.
Cikin qanqanin lokaci doctors suka kewayeta zuwa can dasuka tabbatar da bugun zuciyarta ya dawo normal sai suka sanja mata d'aki tare da yima mata alluran da zai taima ka ta kuma dawowa cikin natsuwarta.
Asannu tasoma bud'e idanunta wanda suka yi mata nauyi har ta bud'esu tar.
Quri tayiwa gefe 1 tana kallo zuwa can ta motsa bakinta ahankali ta furta "da gaske ya Alee ya tafi yabarni cikin wannan duniyar mai cike da rud'ani?
Jin maganarta ya ankarada da mutanen d'akin farkawanta.
Sannu sukayi ta jera mata amma takasa amsa ko 1.
Salma tana hawaye ta dafa goshinta tace "my Addawy kiyi magama mana muji muryanki.
Kallon salman tayi tare da motsawa tace "kamani in tashi zaune bayana ciwo yake yimin.
Kama tayi ta zaunar tare da kara mata filo ta baya.
Hindu tashigo tare da doctor ya dubata yayi umurni da abata abu mai ruwa ruwa kamar tea sannan sai dawo ya bata magani.
Tunda ta falka take tambayarsu da gaske Haydar yatafi ya barta? Amma an rasa wanda zai amsa mata, data matsa da tambayar sai duk suka saka mata kuka ita dai da ido take binsu, suna haka ummie ta iso ita da Hajja da kuma mama don bata koma kwantagora ba tun datazo ta'aziyyan tace sai taga farfad'owar Addawiyya tukunna.
Fad'a ummie tasoma yiwa su Hindu kamar zata'ari baki wai akanme zasu tasata a gaba suna kuka alhalin sun san batagama dawowa daidai ba.
Hajja ce ta daka tar da fad'an tare da matsawa ta janyo Addawiyya jikinta tayi qasa da murya ta soma yi mata magana "Rabi'atu ki zamo mai tawakkali, mai yarda da kaddara khairan ko akasinta kinji ko?
Gyad'a kanta tayi, hajja tacigaba "Aliyu dai yarigamu gidan gaskiya yau satinsa biyu kenan da rasuwa kamar yarda kema satinki biyu yau kina cikin halin doguwar suma, don haka abinda nakeso dake ki jure kada kiyi masa kuka domin add'arki yafi buqata a yanzu ba kuka ba, kinaji nako? Gyad'a kai ta kuma yi wasu hawaye masu zafi suka zubo mata ta qamqame Hajja tare da sakin kuka mai cin rai, muryanta can qasa take fad'in "kuka yazamamin dole Hajja, bazan iya daurewa ba, kibarni inyi kada ciwon zuciya ta kamani.
Kukan datakeyi yayi mugun karyawa kowa zuciya har kuwa da Hajjan, itama kuka takeyi sosai, kukan dabata samu tayiba sanda abin yake d'anye.
Haka Addawiyya ta qara kwana biyu sannan aka sallameta kuma har lokacin hawaye yaqi qafewa a idanunta, duk kuwa yarda taso ya tsaya amma yaqi.
Gidan mijinta aka wuce da ita, anso barinta a part d'inta amma ganin suna doso part d'in ta tafi luuuu ta sume musu yasa dole aka sakata amota zuwa gidan Abbie bayan anyi nasaran ganin ta farfad'o.
*****Rayuwa kenan kana naka Allah na tasa kuma na Allah itace gaskiya.
Gashi har Haydar yayi arba'in ya tasarma watanni na biyu.
Addawiyya kuwa yanzu ta koma shiru2 kullum tana cikin d'aki, duk tabi ta rame sai uban qashin wuya da kayan boobs da d'uwaiyu ga kuma wani haske da taqara tar tar kamar atabata jini ya tsillo.
bata cin komi sai pineapple kad'ai ta maida abincinta sai kuwa ruwa.
Ummie sosai take bata tausayi, haka Abbie duk in yafita ya dawo d'akinta yake soma shiga ya zube mata duk abinda yazo dashi amma bata taba komi ciki sai Abarba, sunyi sunyi ta riqacin abinci taqi in sun matsa sai taci sai taka musu kuka tana kiran "ya Alee katafi kabarni da kewarka gashinan su ummie suna ta matsamin, da sunji haka sai su soma rarrashinta, don haka yanzu sun daina matsa mata da sai taci abinci, Abarba dai agidan ko gonarta sai haka, abinda hakan yayi mata mugun dad'i.
Kwance take tayi rigingine fuskata na kallom ceiling eyes d'in kulle kamar mai barci, wayarta kife samar qirjinta.
Daf da ita taji qamshinsa ta bud'e idanunta tare da kallon inda qamshin yake fitowa.
'Dan bata rai tayi tare da kwabe fuska cikin sonyin kuka tace "uncle wannan ita ce amana ko? Ace ya Alee ya rasu kaqi zuwamin gaisuwa ko? Tam nagode.
Sai ta koma ta kulle idanunta, tanaji yanayi mata magana taqi kulawa zuwa can taji fitar iska ta window ta bud'e idanu tare da bin window nda harara sai kuma ta fashe da kuka mai tsanani, muryan Alee taji yacewa "addu'arki itace abar da nafi so da qauna ba wannan kukan da kiketayi ba haskena.
Miqewa tayi azabure tana waige2 can ta kumajin ance "mai babban suna nine ba Alee ba nayi miki muryanshi ne don kisan nima nayi kewarsa kuma natayaki jimamin rashinsa, kisani mai babban suna, rayuwa bata taba inganta sai taci karo da qalubale haka cikakken mumuni ne Allah yake jarabtarsa da k'addara domin ya gwada qarfin imaninsa don haka ki zamo cikin bayi nan nagari masu yawan godiya ga Allah in k'addara tazo musu.
Tana kuka ta amsa "tam uncle nagode, Allah saka da alkhairi da tunatarwa.
"Bakomi mai babban suna daga haka yabace ita kuma tamiqe ta fito zuwa kitchen inda ummie take had'a lunch.
Hakan yayi ummie dad'i sosai wanda takasa boyewa sai da ta furta "masha Allah autana tasoma dawowa cikin farin cikinta.
D'an murmushi tayi tare da cewa "uhmm ummiena kenan.
Ranar tayi hira sosai tare dasu kuma taci abinci kad'an, abinda yayi mugun faranta musu rai ainun.
Awani yammaci tana zaune a compound hannunta riqe da Alqur'ani tana bita, sam hankalinta yayi nisa cikin karatun datakeyi sabida yanzu shine aikinta kuma sosai take samun natsuwa da sanyi cikin zuciyarta duk intana karatun.
AL-QUR'ANIN KAREEM KENAN MAGANIN DUK KAN WANI CUTA.
Allah ta dawwamar damu cikin bitarshi Amin.
Kamar daga sama ta tsinkayi muryan su hassan suna kira sunarta "aunty Adda tare da rungumeta suna kyalkyala dariyar murnan ganinta.
Cike da murnan ganinsu itama ta rungumesu tare da cewa "ku dawa kuka zo?
Atare suka amsa mata da "mu da yaya Hameed da kuma ummul bait, yace ma wurinki yakawo miki ita kyauta, mamanta tana ta kuka sanda muka barota Hajja nata bata haquri.
Cikin bargaba ta dubi parking lot ta hangoshi jingine jikin motarshi sabe da ummul bait.
Sai taga yakoma mata Haydar sak, hatta kallon dayake mata hak irin ta haydar.
Rintse eyes d'inta tayi ta sake bud'ewa sai taga ya koma mata biyu gashi sabe da ummul ga kuma Haydar tsaye gefensa yana yi mata murmushi da qarfi ta miqe tana furta "ya salam!!.
"Mai babban suna zuciyarki ce take hasko miki photon Alee amma shi tuni yadad'e da koma ga mahaliccinmu don haka ki cire tunanin zai kuma dawo. Muryan uncle kenan yake tunatar da ita.
Jiki a sanyaye ta koma ta zauna tare da rungume su hussain hawaye yana bin fuskanta.
*mrs j moon*
[2/2, 9:49 PM] Mrs J Moon๐: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*
NA
SAFIYYA.
*Assalamu Alaikum fans ina mai jinjina muku abisa comments d'inku daya riske ni ta ko ina agame da rasuwar Alee, hakan ya dad'a tabbatarmin dacewa kuna tare dani sau da qafa, to ina godiya sosai. Sannan ina son kusani ita rayuwa ko ya take tana tafiyane cike da qalubale haka duk abinda kakeso to tabbas wata rana sai yayima nisa ko kai kayi masa nisa. K'addara ita sikeli ce ta ma'aunin mizanin imanin mummunan bayi, don haka rashin Alee shine k'addarar Addawiyya. Aqarshe ina mai bawa fans wad'an da suka taya Addawiyya kukan rashin Haydar dama wad'an sukayi juriya basu zubda jurwayeba da duk kanin masoya labarin hak'uri, kuma wannan shafin na sadaukar muku dashi kyauta kuyi yarda kukaso da shi bamai hanaku domin nakune*๐ ๐ LOVE YOU ALWAYS FANSโค๐๐
*46*
Hucin saukan numfashinsa taji daf da ita yasa ta waiga da sauri.
Subbahallahi!! Ta fad'i cikin ranta, sai kuma tayi sauri miqewa tsaye tana jifarshi da wani kallo wanda yarasa gano ma'anarshi.
Ahankali yace "wannan kukan baya da amfani agareshi illah azaba da yake qaramishi don haka nasan kin sani wata qila mugunta ce yasa kikeyin hawayen don yayi ta qonashi.
Afusace ta wulla mishi harara tana mai point d'insa tace "Hameed ya isheka tijaran da kazo yimin har cikin gidanmu kuma kasani kada kaga wai uwa 1 uba 1 kuke da ya Alee kayi tunanin kafini sonsa tare da jin zafin rashinsa, to wallahi ko kwatan2 abinda nakeji game dashi kai bakaji sabida haka kada kasake cemin inayi masa mugunta ehe, ta qarasa cike da tsiwa ga kuma kwalla yataru cikin idanunta sai qoqarin maidasu takeyi don bata son su zubo.
Shiru yayi yana binta da kallo fuskasa cike da murmushi.
Ganin ya maidata sauna sai tamiqa hannu ta fizgo ummul wacce take ta sharan barcinta bisa kafad'arsa, tayi gaba sai kuma ta juyo fuska a had'e tace "nagode sosai da kyauta amma kasani bana son yawar bibiya inkana son ganin 'yata sai kanasar dani in ina da lokaci domin bazan lamunta ka riqa zuwamin baqatatan ba, dafatan kajini da kyau?
Shafa kwantarcen sajensa yayi cike da mishad'i sannan ya amsa "naji hajiya Rabi'atul Addawiyya matan malam badamasi.
'Dan sakin fuska tayi batare da ta kuma magana ba tawuce ciki su hassan suka rufa mata baya.
Yajima duqe a wurin yana sake sake zuwa can ya miqe ya isa wurin motarsa ya bud'e boot ya d'auko akwati biyu d'aya babba sosai d'aya kuma d'an madai daici, yayiwa falon tsinke.
Ummie ya tarad zaune tana bitan wani littafin addu'o,i.
Har gabanta ya isa ya zauna sannan ya gaisheta, ta amsa cike da fara'a tare da tambayarsu mutanen gidan ya amsa "suna lafiyalau.
Kallonsa ummie ta kuma yi tace "Hameed haka akeyi ka d'auki mutum sukutum kayi kyauta da shi? Baka tunanin ita uwar yarinya wani hali zata fad'a saka makon rashin gudar jininta kusa da ita?
Sauke kansa qasa yayi kuma cike da ladabi ya amsa "babu komi ummie, ai ni da Addawiyya duk 'ya'yan kune kuma nasan zuhuriyya bazata taba bijirewa umurnina ba haka babu halin dazata fad'a don bata tare da ummul hasalima anrage mata d'awainiya ne sabida yanzu haka batajin dad'i bata iya hidimar ummul sam, nike mata dukkan wani abun da yashafi raino, ga aikina ga hidimarta sai kawai nayanke shawaran bari na cika alkawarin dana d'auka kawai.
"Tam yayi Allah yatayata riqo ya kuma raya ummul cikin ni'imar Allah.
"Amin, ya amsa.
Hira sosai suka sha da ummie, inda ta tashi da kanta ta kawo mishi kayan motsa baki, yanaci suna hira har lokacin sallar magrib tayi.
Ummie tamiqe ta shige room d'inta dake qasa don ta gabatar da sallah.
Yana ganin haka ya haye upstair da sauri.
Koda ya hau sai yatsaya yana nazarin wani room zai shiga, qasa qasa yake jiyo dariya sai ya doshi d'akin kai tsaye, tabawa yayi yajita bud'e don haka sai ya saka kansa kawai batare da neman iziniba.
Su hassan yagani zaune tsaliyar bed d'inta duk sunyi caka caka da chocolates tare da biscuits suna ta aikin sha, sunsa ummul a tsakiyarsu in sun bare nasu sai su bare mata su miqa mata ta amshe.
Ingina da qofar yayi yanata aikin kallonsu cike da jin dad'i, kuma cikinsu bawanda yalura da zuwarshi.
Motsin fitowarta daga toilet yasa ya zubawa qofar bathroom d'in idanu.
Fitowa tayi d'aure da guntun towel wanda iyakarshi cinyoyinta ya rufe.
Ba tare data lura da shi ba, ta isa gaban mirror tasoma shafa mai, ta matso lotion zata shafa a qirjinta ta tsinkayi maganarsa inda yace "kai kai!!! Jira infita tukunna basai kin nunamin kayan ruwan naki ba.
Zabura tayi wanda kad'an yarage towel d'in bai sunbule qasa ba, sabida sosai ta firgita dajin muryanshi don batayi zaton da mutum ba.
Kallonsa tayi kamar zatayi kuka tace "kasan Allah in har nacre bamyafe makaba sai Allah yafitarmin da hakkina da ka d'auka ta hanyar tsoratani.
Kashe mata ido 1 yayi tare da matsowa inda take tayi sauri d'aga mishi hannu tana mai cewa "kul ka taka shari'a kuma kaficemin a room tun ban saukema kwadon rashin matunci ba.
Matsowa ya kuma yi a fusace ya kama dantsen hannunta ya matse da qarfi tako kwalla qara don azaba yasa qafarsa ya take mata yatsu tare da murzawa ta rintse idanunta cike dajin azaba ta dubeshi tace "sakeni Hameed banson irin wannan bad'alar.
Mai makon ya saketa sai kawai ya kai bakinsa daf da kunninta yana mai cewa "kinsan Allah in har kikace tsiwa zaki tsiromin dashi to ni kuma zan soma baki wuya kala kala don haka sai ki kiyaye kinsanni bana d'aukan wargi musanman kan mace, macenma kwaila irinki, yafad'a hakan tare dabin jikinta da kallo.
Da qarfi ta fizge daga riqon da yayi mata, tayi saurin janyo hijab d'inta ta saka ta nuna mishi hanyar qofa tana mai bashi umurni "malam kaficemin a d'aki nace, bana da lokacinka.
Wani damqan ya kawo mata tayi sauri fad'awa cikin su hussain tana ihu, aikam yaran da tun dazu suke kallonsu suka saka mata dariya hassan yace "laaa yaya Hameed yafi qarfin Aunty Adda, hussain ya amshe da "eh, Allah yafita, bakagani ba har yakusa sata kuka, sai suka kuma kwashewa da dariya har da Hameed d'in.
Wani uban tsawa ta daka musu take sukayi shiru suna mazurai, yayin da baby ummul ta fashe da kuka don taji tsoro.
Hameed wanda yake ta kyal kyala dariyan zancen su hussain yayi hanzarin kai hannu zai d'auketa, tako buge mishi hannu tare da cewa "dalla malam kar ka tabamin 'ya, baya yaja yana dariya qasa qasa ta kuma bata rai tace "wai ka soma mensuration ne halan da kanajin time din prayer zai wuce amma katsaya d'aukan magana kamar nid'in ba auntynka bace?
Kallonta yayi kamar zai yi magana sai kuma ya miqawa su hassan hannu suka kama ya d'agasu suka fice batare da yakuma kallon inda take ba.
Tsaki taja mai sauti tare da cewa "iskancin banza da wofi kawai, yawani zo duk ya dagulamin lissafi har yana wani cemin kwaila a'a kwanso ce ba kwaila ba.
Tare dashi da Abbie sukaci dinner, su kuma su hussai sukaci tare da ummie ita kuwa Addawiyya ta qule cikin d'aki da 'yarta tana aikin bata priso.
Tana cikin gyarawa ummul kwanciya ya kuma shigowa ta d'ago tare da cilla mishi harara bai kulata ba illa iyaka yamatsa kusa da 'yarshi ya manna mata kiss daga haka ya fice tabi bayanshi da harara kamar kwayar idonta zai fad'o.
Ummie ce ta shigo da kanta ta tasata a gaba duka sakko don tayi sallama da Hameed.
Baki ature ta isa wurin ta miqawa su hussain ledar chocolates tace dasu "kugaidamin da momynku, dadynku, hajiyarku tare da tsohuwar kirki Hajjanmu, atare suka amsa da "to aunty adda.
Juyawa tayi tabar wurin batare da ta dubi inda Hameed yakeba.
Da sauri ya biyo bayanta ya kama hannunta yace "bakice a gaida my heat riyya ba, da sauri ta amsa mishi "a'a zanba zance agaisar ba riyya ba, ta fizge hannunta tayi gaba bud'e murya yayi da qarfi yace "gudan jininta dai tana hannunki don haka akul kika soma kishi da ita tun zuciyar mijinta bai gama tantance zancen ba.
Wani juyowa tayi afusace, ya kwasa da gudu ya fad'a motarshi yafice a 100 yana ta kyal kyalan dariya domin sosai yau rigimarta yajefashi cikin mishad'i.
Ita kam zubewa tayi awurin tana maimaita kalmar kishi cikin ranta, "kardai ace ya Alee shima yayi mishi maganar da yataba yimin a hospital ne? To inko yayi masa ita lallai ina cikin matsala,, Saita dafe kanta cike da rud'ani takuma cewa "To ma wai duka duka yaushe ne ya Alee yarasun da har Hameed yasami kuzarin da zai soma min zancen banzan nan? Ganin bata san amsarba sai tamiqe jiki ba kwari ta shige ciki tana aiyana abinda zatayiwa Hameed duk randa yakuma zuwa inda take.
Kamarko yasani sai ya d'auke qafarshi tsam daga gidan baima ko kiran wayarta balle yaji irin tanajin da tayi masa.
Baby ummul kuwa sunyi mugun shaquwa da Addawiyya,, batayi mata rigimar komi,, sosai takejin dad'in zama da yarinyar, sai su qulle cikin d'aki suyi ta ifece ifacen su, hakan kuwa yana faran tawa ummie da Abbie rai sosai sakama kon zuwan yarinyan sun fahimci ya tafi mata da damuwarta sama da kaso 80 cikin d'ari, shi yasa kullum suke godewa Hameed da samishi albarka.
Cikin sauri tagama shiryawa ta d'auki ummul itama ta shiryata cikin kayan sanyi masu laushi ta ratayo bag d'inta maroon ta sauko downstairs, ummie ta taradda zaune bisa dinning tana yin break fast, qarawa tayi ta zaumar da ummul bisa cinyar ummie tace "ga rainonan nakawo miki kema kisami ladan.
"Tam auta na amsa, tad'ora da cewa "sai ina kuma yau haka da sassafe?
Sai da tayi gaba sannan ta amsa "skul zani.
Cikin mamaki ummie ta mai maita skul kuma? "Eh, ummie nayanke shawaran komawa ne domin nafahimci kuna son haka, "tam hakan yayi kyau auta, Allah ya tai maka, "Amin ta amsa tare da d'agawa ummul hannu itama hannun ta d'aga mata tana tsalle jikin ummie.
Driving takeyi ranta fal da tunanin mafarkin datayi da Haydar daren jiya, lokaci zuwa lokaci sai tasaki murmushi cike dajin dad'i.
Ta mirror ta lura da wata mota tana binta abaya, hakan tacigaba da tafiyarta tana tunanin ko waye wannan dake bin nata?
Daf dazata shiga get d'in skul motar tazo ta wuceta da gudu tuni bace bat kamar walqiya.
Tabe baki tayi tare da shigewa ciki tana mai furta "can ta matse ma koma waye a matse matsin matsalar shi.
*mrs j moon*
[2/4, 10:37 PM] Mrs J Moon๐: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*
NA
SAFIYYA.
*47*
parking tayi a qasar wata bishiya tayi jim kamar baza ta fitoba zuwa can kuma sai ta bud'e qofar ta zuro santala santalan qafafunta waje tana qarewa students d'in dake kai kawo a harabar wurin kallo, caraf idanunta suka had'u dana wani malaminsu yako kafeta da idanu quri, da saurin ta koma ciki ta kulle door din ta kwanta sosai ta d'aga kanta sama ranta abace.
Qaran shiqowar message taji cikin phone d'inta ta d'ago ta fiddota cikin bag ta duba.
Baquwar number tagani qin bud'ewa tayi tare da yin cilli da wayar cikin jikka, ta koma ta kuma kwanciya tana tuno yarda taga Haydar cikin mufarkinta.
Qiba, haske, jin dad'i duk sun bayyana ajikinsa ga wani qamshi da yake fitarwa mai dad'in shaqa, hatta wurin da yake zaune abin kallo ne, ni'ima mai dad'i yake ta fitarwa sai ta qamqame jikinta cikin jin dad'i tana mai furta kalmar "Alhamdulillah a fili sai kuma ta d'ago ta kife kanta samar sitiyari tayi shiru kamar mai barci tsawon lokaci ta d'auka ahaka sannan ta lalibo phone d'inta ta duba saqon daya shigo d'azun.
*kwailata lallai kinyiwa kanki qiyamun laili tunda kin koma skul amma da yau na yanke zanje nasameki insa ki koma ko tatsiya ne sai gashi kin hutashshe dani, don haka inayi miki fatan samun nasarori masu yawa ki kulamin da kanki sosai Allah yadawo dake lafiya, Abu ummul bait ne mijinki bada jimawa ba da yardan mai duka*
Wani dogon tsaki taja tare da furta "iska na wahalar da mai kayan kara, kuma asannu zan gyarama zama indai har baka bar kirana da kwaila ba, ai wannan ma sunan rainin wayau, fuska a had'e ta fito waje ta kulle motar batare da ta kuma kallon inda taga mayen kallon ba sunar da tabawa malamin kenan ta doshi wurin dasuke zama dasu maryam tun can da, sabida tasan kotace zata shiga class yanzu lokaci ya qure sun kusa fitowa.
Zama tayi tare da juyawa mutane baya ahaka maryam ta qaraso wurin sakamakon hangota datayi tun sanda ta fito daga mota.
Cikin mamaki ta zauna gefenta tare da dafata tace "qawalliya dagaske ke nake gani a cikin skul yau?
Bata ta juyoba ta amsa mata da "eh, nice ya kike dasu mamie?
Sai da ta miqe ta dawo gabanta ta duqa sannan ta amsa "muna lafiya lau.
"Masha Allah.
Shiru sukayi Addawiyya taqi d'ago kanta ta dubi maryam ita kuma taqi tashi daga tsugunon datayi a gabanta, zuwa can ta sa hannun ta tureta aikan abazata ta ganta qasa zaune, dariya tasaka mata irin ta mugunta, maryam bata ce komi ta koma ta zauna agefenta ta ta aikin kallonta, ganin haka tuni ta gintse fuska sai abin yabawa maryam dariya kuma.
Qawayensu ne sukayi ta zuwa suna yi mata ta'aziyya tana amsawa ita da maryam ganin sunqi qarewa masu zuwan yasa ta miqe tana mai cewa maryam "besty bara na koma mota kafin lokacin shiga ta lecture yayi domin naga mutanen nan so suke su sani kuka kuma alhalin nayiwa ya Alee alkawarin nadai yi masa kuka sai addu'a.
Biyo bayanta maryam d'in tayi tana cewa "hakan shi yakamaceki dashi dama, Allah dai yaji qansa da rahama "Amin.
Atare suka isa wurin motar suka shiga.
Maryam ta dubeta tace "amma besty ya akayi kika sanja ra'ayinki kika dawo skul?
Tana murmushi ta amsa "wallahi tunda na falka misalin 3 daren jiya naji jin son komawa skul ya d'arsu azuciyata kuma inajin duk don ganin ya Aleen danayi ne a ciki mufarkina cikin shiga mai kyau da jin dad'i da alama yasa mi kyakykyawan makoama sannan maganar da mukayi dashi ita ce ta karatu na, to inaga shine yahassa samin son komowata.
"Uhmm yayi kyau hakan amma inajin junnu uncle d'in kine dai yafito miki a siffarshi shine kike ganin kamar ya haydar ne.
"To nidai koma waye nasan mufarkin ya jefani cikin nishad'i haka nan yakasa wucemin arai.
"To Allah yacigaba da sadamu da mufarkan Alkhairi "Amin.
Koda zata koma gida wannan motar data biyota ita ce tayi mata rakiya har bakin get sannan ta juya.
Cike da saqe saqe tayi parking ta mufi ciki.
yaran Salma tare dana Hindu tayi arba a falon suna ta iface ifacen su da ummul.
Cogewa tayi a qofa tana ta kallonsu cike da jin dad'i.
Dama ace Allah ya k'addara cewa ya Alee yabar gudan jininsa a jikina fa, uhmm lallai da nafi kowa jin dad'i da kuma wata rana da shi ko ita za'ayi wasar nan.
Cikin zuciyarta take wannan tunanin, atake kuma sai hawaye suka soma zubo mata tayi sauri sharesu tana mai furta "affuwan ya Alee, bayin kaina bane zuciyata ce takasa manta ka.
Muryan ummie taji kusa da ita yasa tayi saurin fad'awa jikinta tana ta sauke ajiyar zuciya.
Shafa kanta ummien tayi2 har ta dawo natsuwarta sannan tayi qasa da murya tace "nasan damuwarki haydar ne to don Allah ba dan niba ina son duk sanda kikaji ya fad'o miki arai kiyi mishi addu'a ne ba kuka ba, kinji?
Gyad'a kai tayi tare da janye jikinta ta qarasa wurin yaran suna ganinta suka soma ihun murnan ganinta ta durqusa tayi ta manna musu kisses cike da murna.
Washe gari da sassafe tafita don ko ummul bata tashi barci ba.
Misalin 10am ta fito daga lecture.
Tafiya suke ita da maryam suka tsinkayi muryan khairi tana kwalla musu kira atare suka juyo ta qaraso tana dariya harara addawiyya ta cilla mata ta kuma saka dariya tana cewa "ke madam ashe dai kin dawo skul ne bako sanarwa.
"Yo ai yanzu idanunki yaga ne miki, dalla kina tawani kwallawa mutane kira kamar wata yarinya, girma yariga hankali zuwa dama ai.
Dukan wasa ta kawo mata tayi sauri gofcewa duk suka sa dariya.
Cikin motar maryam suka shiga sunata yi mata murna tare da addu'ar Allah ya tsare ya ka tsone idannun maqiya sai amsawa take da Amin Amin, da yammacin jiya Abbanta ya danqa mata key d'in motar.
Sosai Addawiyya ta mai da hankali akaratunta sabida komi yazo daf da qarshe, a tsawon lokaci data d'auka nata zuwa uncle d'inta shi yayi ta fitowa a mutum yana zana mata duk kannin wani tests da exams da akayi da bata nan shi yasa komi yazo mata cikin sauqi.
Mai binta abaya dai ya bari kuma har lokacin bata san ko waye ba haka taqi tambayar habibullah sabida bata son ya tado mata da zancen aure sam.
Su Abbie kam yarda ta dawo real Addawiyyanta sosai hakan yake faranta musu rai, shi yasa tunda suka fahimci bata son zancen aure sai suma sukay biris da ita amma hakiqa akwai abinda suke shiryawa agame da aurenta.
Tafiya take cikin jin dad'i ta kunna begen Annabin Allah mai taken murna muke da zuwan shugaba d'aha...... Akan hanyar ta na zuwa saloon sai gyad'a kai takeyi tayi tare da bin begen,sai da tayi nisa da gida sannan motarta ta bata matsala gangarawa tayi gefen hanya ta gyara parking tayi shiru tarasa yarda zatayi gashi tayi nisa da gida.
Har ya wuce sai kuma ya dawo da baya ya iso dai dai inda take yayi parking tare da fitowa.
Nocking yayi mata ta d'ago tare da sauke glass ta zuba mishi idanu, murmushi ya sakar mata tayi saurin kauda fuska tayi tana maijin wani tashin tsiyar jiki yarrrr, yace "matsala kika samu ne?
Banza tayi mishi sabida taya zai ganta anan wuri amma ya tsaya yi mata tambayar rainin wayau irin haka.
Tanajin murmushin da yasaki mai sauti ya matsa gaban motar ya bud'e yayi 'yan tabe tabensa sai ya koma motarshi da sauri ya dawo yacigaba da abinda keyi duk tana jinsa kuma taqi motsawa zuwa can ya dawo wurinta yace "d'anyiwa motar key mugani, bata musaba tayi ai kam cikin sa'a sai gashi ta tashi.
Cike dajin kunya ta fito ta russuna tace dashi "nogode, nawa zan biya? "Kai kai haba mai kyau ai banyi don ki biyani ba.
Murmushi tayi batare datace komi ba tashiga tayi gaba tana ganin yana tsaida ita amma sai tayi kamar bata ganshi ba tayi tafiyarta tana fad'in wahalalle kawai cikin ranta.
Shikan mutumin dariya yasaki ya isa wurin motarshi ya dafata sai kawai ya bace bat.
Agajiye ta dawo hannunta d'auke da babbar leda dagani kayan zaqi ne ta yowa ummul bait tsaraba.
Tana sawo kai taga mutane cikin falon zaune kallonsu tayi sosai sai tagano kamar idanunsu sunyi kama da mage, atake kuma taji fad'uwar gaba yazo mata, tasbihi taja cikin ranta sannan ta qaraso cike da sanyin jiki ta gaishe dasu suka amsa ta nufi room d'in ummie can taga Salma, Hindu tare da maman su ubaiyu suna kus kus daga ganinta sai sukayi shiru cike da zargi take kallonsu sai kuma ta sunkuya ta gaishesu tare da cilla musu tambayar "suwaye nagani afalo?
Mama ce ta amsa mata "iyayen mus'ab ne "waye haka kuma? "Au wai mufinki baki sanshi ba dama ya turosu mana wad'ancan matan su nema mishi aurenki?
Tafe qirji tayi bakinta na rawa tace "wallahi ni ban taba jin sunar da yayi kama dashi ba sam.
"Ikon Allah, to muma muna zaune suka iso wai ya turosu ne neman musu aurenki shine fa muka cika da mamaki naganin mata da zuwa neman aure, zaman damu kayi ma anan jiranki mukeyi kidawo muji ya abin yake.
Zubewa tayi ranta in yayi dubu ya baci, to wai yaushe ta tsaya da wani da har zata bashi izinin zuwa wurin iyayenta? Tambayar da ta rasa amsarta kenan sai kawai ta miqe fuuu tanufi falon suka rufa mata baya amma sai me suna fitowa suka nemi matan suka rasa babu su babu san matan su duk sai suka shiga rawar jiki ita kam komi batayi ba illama wucewa datayi upstairs ta barsu nan tsaye cike da rud'ani.
Tana shiga ta zaune gefen bed tafad'a kogin tunani.
"Mai babban suna warning yayi miki na ya tai makeki amma sai kika wulaqantashi ta hanyar qin tsayawa alhalin kinagani yanayi miki magana kikayi biris dashi.
"Wayyo Allah ni Addawiyya wai mike bibiyata ne haka daga wannan sai wannan kai wallahi rayuwar duniya cike take da rud'ani.
"Haka ne amma banson kiqara yiwa wanda ya tai makeki irin haka, kinji "eh, to amma shi waye? "D'an uwa nane nina turoshi da ya tai makeki donmin shi d'in engineer ne na motoci manya da qanana.
"Tofa!!!, wai uncle shin kuna sana'a ne kamar yarda mukeyi tare da karatu? "Sosai ma, komi da kukeyi munayi wata ranama tare daku muke hada hada kasuwanci da karatu musanman ta nasara.
"Taf d'ijan, to ace yayi haquri bazan sakeba "ai tuni yayi ya dai yi miki haka ne don kigane ba kowwa ne yake cikin jinsin bil'adama ba don haka sai ki kiyaye ba kyau wulaqanta kowa ka gani koya yake sabida dawani mugu ne sai ya nemi cutar dakai musamman jinsinmu na junnu.
Tam nagode bazan sake ba da yardan Allah "Allah yasa "Amin, amma yanzu ya zanyi da su ummie in sun sake neman qarin bayani agareni?
"sharesu kawai ai tuni yasa musu mantuwa zancen ya bar zuciyarsu sai dai Hindu ce ya kasa tasiri mantuwan akanta.
"To sabida mi? "Sabida taga kofato dake qafafun 1 cikinsu, shine abin yaqi tasiri akanta, yanzu haka zata zo kuyi magana akai dama kuma akwai maganar da yakawota wurinki.
"Ohk tam uncle bari na shiga wanka kafin tazo "aha bye in kin fito wanda ke binki baya in zaki makaranta yana nan tafe anijma sai ki shirya tarbanshi.
"Bazan fita ko inaba don haka ma ka tsai da shi can bisa titi yayi ta garararanba kamar leda.
"mai babban suna bansonki da haka, kifito ki saurari batunsa kuma bayanshi biyu sunan tafe zasuzo da buqatar son aurenki.
"Na boni uncle haja ce ni da za ayi tazuwa tayawa haka?
Dariya yasaki yace "farin jinin da Alee yayi miki katanga dashi ne yanzu yake fitowa fili.
"Mi kake nufi da cewa hakan uncle?
"wata qil nan gaba inyi miki bayani amma ban d'au alqawariba, yanzu dai wanda zaizo sunarsa dr. Suwaid'i kuma wurin aikinsu d'ya da Hameed ata qaicema photonki yagani a cikin office d'in Hameed yaji bawanda yakeso sai ke sannan ubaiyu zai dawo da qarfinsa haka lecuran ku Salim yana ciki ga kuma shugaba Hameed kai mai babban suna kin had'a jarumai fa. Yana gama fad'an haka ya bace bat.
Komawa tayi ta zauna hannunta bisa goshinta kamar zata sa kuka, ahaka Hindu tashigo ta sameta ta zaun gefenta tace "autar ummie natsuwarki nake buqata dafatan zan samu? Gyad'a mata kai tayi tare da zuba mata manyan eyes d'inta tana sauraronta.
*Readers ayi ta haquri da Safiyya wlh uzurirrika nake dasu sosai*๐คฆ๐ปโโ
*mrs j moon*
[2/5, 11:35 PM] Mrs J Moon๐: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*
NA
SAFIYYA.
*48*
Autan ummie ina son kisanar dani gaskiyar zancen agame da zuwan wad'ancan mutanen sabida tun zuwarsu nagane ba mutane ba ne domin da idanuna naga d'aya cikinsu na d'auke da fafafun doki.
"Eh aunty h. Hakika ba mutane bane laifi nayiwa wani d'axun... Ta fada mata duk yarda sukayi dakuma abinda uncle yafada mata.
"Uhmm lallai kam biri yayi kama da mutum, to Allah yaqara tsarewa "Amin.
"Kuma autan ummie kikiyayi wulaqanci domin a irin haka ake had'uwa da masifu iri iri masu wuyar magani, duk inda kikaga mutum to ki rabi dashi lafiya sabida wasu ba mutane bane kamar dai yarda kika had'u da wannan.
"tam aunty ai nabari
"To hakan yayi kyau.
Ta murkuta kad'an ta kama hannun Addawiyya tace "Sai kuma maqasudin zuwana wurinki shine Abban Hameed ya aikoni da inzo na tambayeki shin ke kika amincewa Hameed ya fito neman aurenki? Sabida yasameshi da zancen shine yace ya dakata yaji daga gareki.
Da sauri ta amsa "a'a "ohk, to Abbansu yace yana neman alfarmarki daki amince ki kuma zamowa surukarshi akaro na biyu, dafatan baza ki watsan qasa a idanu ba?
Shiru tayi zuwa can tace "ni ba aure zanyi yanzu ba hakanan kuma banjin zan yi aure a lokaci kusa.
"Eh, mun sani dama wai in kin amince dashi ne sai abari har sai sanda kika kammala karatunki sai ayi bikin.
"Aunty ni dai nace bazanyi aureba kuma Hameed baya cikin 'yan kayana, bai min ba, yatafi can ya qarata da matarsa.
Hindu zata kuma magana tayi hanzari tashi ta shigewa toilet tare da murza key.
Baki sake Hindu tabi qofar toilet d'in da kallo kai ta jijjina tana mai cewa "ina nan zaune har sai kinfito naji gamsasshiyar amsa sannan zan kyaleki.
Koda tafito bata zaciga zata tadda Hindu ba don haka sai ta coge a jikin bayin ta tura baki fuska a murtuke, Hindu yi tayi kamar bata gantaba tacigaba da latsa wayarta, tsawon lokaci ta d'auka tsaye ganin bazata kulata ba sai ta isa gaba mirror ta murza lotion tare da jira rigan shan iska mai gajeren hannu ta zo ta zauna gaban Hindu ta marai marai ce murya tace "aunty don Allah ki fahimceni ni bason Hameed ne banayi ba a'a nadai harantawa kai na auren shi ne duk da burin ya Alee kenan bayan ransa in auri d'an uwarsa Hameed ni kuma atun sanda yake fad'amin haka nace bazan auri qanin mijina ba, kuma banson zancen don haka yanzuma banson kinamin zancen don Allah.
"Shikenan hujjanki? "A'a "ok tam ina sauraronki "aunty matarsa zuhuriyya ta tsaneni alokacin ina matsayin matar wan minjinta balle kuma ace yanzu na zama abokiyan zaman, ai kinga sai ta kyes samin ashana kuma.
"Autan ummie ni dai koma miye ina son kice kin amince kawai, zancen bakyason zancen duk bakison zancen ba.
"Allah aunty bazan auri Hameed ba sai dai abisa k'addara.
"Uhm to yayi miki kyau amma ki sani tuni su Abbie sun amince amsar ki kawai suke jira kuma yanzu zantafi nasar dasu amincewarki don haka sai ki shirya zama Amaryan Hameed nan bada jimawa ba kuma kishiyar riyya.
Tamiqe ta barta durqushe tarasa bakin magana.
Leqowa ta kumayi tace "indai da Amana abinda yafi shine kiso jinin Haydar kuma kiyi biyayya ga cikar burinsa ta hanyar auren jininsa kamar yarda yakoma ga mahaliccinsa da burin hakan a ransa.
Runtse idanunta tayi tare da toshe kunninta, Hindu tasaka dariya tace "ki saurari kiran su Abbie kuma in har kika qaryatani to wallahi babuni babu ke ehe, ta buga mata qofar da qarfi tayi gaba.
Bata san tsawon lokacin data d'auka a zube bisa carpet ba tana aikin tunani, ita dai jin muryan Salma tayi akanta tana cewa "ummie tace in sanar miki kifito kici abinci tun bata iso da kanta ba.
Bata tanka taba ta miqe ta rufa mata baya ranta abace suna saukowa mai gadi yana kwad'a salma ko bari a amsa mishi bai yiba yacigaba "Hajiya ummie, wani yazo neman hajiya Rabi'atu.
Caraf tace "jekace masa ina zuwa, takoma upstairs da sauri ta d'oro abaya abisa kayan jikinta, koda ta dawo falon ummie kadai ta kalla tace "natafi kiran, cikin murmushi ta amsa "adawo lafiya kada ki dad'e dai auta "aha ummiena bye tafice da sauri ganin Hindu tana daf da fashewa.
Zaune ta taddashi samar motarshi yana waya cikin harshen fulatanci.
A sannu ta qare mishi kallo, farine tas mai kama da larabawa ko kuma india, muryanshi ce zata tona asirin ko daga wani jinsin ya fito wato jjnsin fulani, hakiqa yana da kyau amma sam batajishi cikin ruhintaba.
Bata san ya sauko ba sai jin maganarsa tayi daf da ita tayi saurin ja baya tana tura baki, dariya yasaki kad'an sannan ya russuna cike da barkwanci yace "ina yini, nasameki lafiya?
"Lafiya ta amsa masa ataqaice, ya ce "Addawiyya d'anyi mana wuri zama man yarda zanji dad'in yin maganar data kawoni.
Batace qalaba sai tayi gaba zuwa wurin wasu kujerun roba dasuke jere cikin wani rumfa.
Uhmm ๐ด๐ด๐ด
*mrs j moon*
[2/6, 8:15 PM] Mrs J Moon๐: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*
NA
SAFIYYA.
*Where are u d best friend of Addawiyya,, Maryam Rano, this page is belong to you, u can do what so ever u want do with it, don abin nakune mrs ustax mai tsefaffen geme* ๐๐ ๐
*49*
"Sunana Doctor Garzali Baffa ard'o, abinda yasoma cewa da ita kenan sanda suka zauna, yacigaba "ni haifaffen garin jalingo, Taraba state, ai kine ya kawoni garin Kano, ina aiki a general hospital.
nasoma ganin photonki a office d'in Dr. Abdul Hameed tun da jimawa kuma nayi ta nacin daya had'ani dake sai yasanar dani wai kina da aure to sai gashi kwatsam kwanaki nayi cikibus dake har nabi bayarki naga kinshiga buk shine nadawo nayi bincike akanki aka tabbatarmin dacewa lallai kintaba aure amma mijinki Allah yayi masa rasu.
Jan numfashi yayi tare da kallonta yana murmushi.
ita kam shiru tayi tana nazarin surutu irin nashi daga zuwarshi na farko.
Yacigaba "ina miqo ta'aziyyata na rashin Aliyu damu kayi Allah qansa da rahama ya kuma yabashi aljanna mad'aukakiya.
Cikin mugun fara'a ta amsa da "Amin, kamar ba itace fuskanta yake d'aure ta mau ba, ta qara da cewa "nagode sosai da addu'a.
Shima fara'ar ya saki cike da gano lagonta ya amsa "bakomi sayyada Rabi'a.
D'an sauke kanta tayi qasa cike da jin kunya, gyara zama yayi yace "da fa qarfina nashigo fagen dafatan zan sami ticket d'in shiga gasar?
D'agowa tayi idanun su ya had'u tayi hanzarin kauda nata.
"Ehm inajinki mai babban suna,yace hakan ahankali.
Ahanzarce ta kuma kallonshi zuciyarta na bugawa.
Kardai ace shima junnun ne? Zancen datayi cikin zuciyarta kenan.
"Sunar ki 1 da wacce ta goyani ita d'in matar wan babana shine Baffan danake amfani dashi a sunana.
Cikin ranta ta cewa ikon Allah yau Allah ya had'ani da suda fad'i ba'a tambayeshi ba radio mai jini.
Ahankali ta sauke numfashi tace "ohk, kace nid'in maman ka ce?
Yana dariya ya amsa "hakk'un mai babban suna.
"Uhmm ta furta tare da miqewa tace "zanshiga daga ciki sai wata rana.
Miqewa yayi shima ya matso daf da ita yace "a'a ya haka, zaki tafi batare da kin bani amsa taba?
Tabatare da ta tsaya ba tace "banshirya yin aure yanzu ba haka kuma bansa lokacin yinsa ba don haka sai dai ince Allah ya sadamu da alkhairi amma fa lallai kasani bance inaqin kaba haka kuma bance inajinka araina ba.
Dai dai sanda ta iso qofar shiga falo taja ta tsaya, shima tsayawar yayi cike da dumuwa yake dubanta domin zancenta yana kama da bigtin.
murmusawa tayi tare da cewa "doctor kayi haquri dani domin nasan anriga da an zartar da hukunci akaina, na wanda zan aura shiyasa na sanar dakai gaskiya kada in boye maka daga baya kaji kace na yaudareka, dafatan yanzu kafahinci inda nadosa?
"Eh, na fahimta amma kisani bashine zaisa na yanje daga gareki ba, zancigaba da gwada k'wanjina har sai naga abinda yaturewa buzu nad'i sabida nasan ba mijin akayi miki ba kawai kora da hali ne kike son yimin, ni kuma naqi koruwa.
Ya qarasa zancen cikin sigar qasa.
murmushi tayi kawai batare da ta kuma ce mishi komi ba ta sakai cikin falon tabarshi anan tsaye.
A zuciyar mamakin hukuncin datace anzartar akanta take tayi "Allah na tuba, ta furta a hankali.
Sai bayan Sallar isha'i Abban su Hameed yazo d'aukan Hindu wacce take ta fishi da Addawiyya taqi kulata tun sanda tadawo daga wurin dr. Garzali.
Salma kam 'yan baruwan muce sai zolayar addawiyya take tayi wai taga taqara qibane komi nata yaqara cika ko dai Alee yabar mata ajiyar shine ba'a sani ba tazo ta duba ta, da harara Addawiyya keta binta dashi amma taqi bari saima sake lalibo abin neman magana take tayi da ita har saida ummie tashiga tsakani sannan ta sarara mata.
Ita kam kwana zatayi a gidan sabida mushaffa'u yayi tafiya sai kuma yayi sati zai dawo shine tazo gida wai bazata iya zama ita 1 a gidanta ba tsoro takeji.
Washe gari a skul tana cikin bawa su khairi labarin zuwar dr. Garzali da yarda sukayi, sai dariya suke tayi mata barinma khairi datake ta mai maita sunarsa wai Garzali.
Ita ma sai yanzu sunar yake bata dariya, ita kuwa maryam cewa tayi taji ya kwanta mata arai kuma sunarshi special ne don bakowa yake dashi ba.
Cike da zolaya khairi tace "ato shi kenan su Garzali anyi kasuwa to ke mrs AH sai kibar mata shi kiriqe Ah d'inki zam zam dama ni team d'insa nake don hausawa sunce so so ne amma son kai yafi, ga gida ana so ai ba'abawa dawa ba.
Wani duka Addawiyya ta taska mata acinya wanda yasa ta kwalla ihu hankalin students ya dawo kansu, tana liliya wurin tace "wallahi bashi kikaci don kamar narama ne.
Gwalo tayi mata tace "warning nayi miki next time kika kuma had'a da yayanki sai nayi miki mafiyinsa kinsan dai karonmu dake ba dad'i.
"Eh, nasani kam amma kisa dai yanzu bada bace sabida komi ya sanja sinadarin aure ya nusheni yagama ratsa jini da jijiyata nayi karfi fiye da doki don haka kibini asannu kada in ji miki targad'e.
Dariya suka saka su dukansu, zuwa can maryam tace "khairi gabaki d'aya kin lalace tunda kikayi aure kika soma sakin zance bako jin kunya, fari tayi ta amsa "lokaci nane yayi kema kina shiga daga ciki zamujiki bulum buqui kunya tayi gefe 1 atare da ke.
"Uhmm badani ba kam, kedai da kike kayarshi Allah ya yaye miki.
"Amin, yayaemana baki 1, "kudai amma nikam tuni dama ina da kunyata ras,
"uhmm addawy kenan, Allah ina tausaya miki in ya Hameed ya danqeki wallahi baya da wasa kinsan zuhuriyya 'yar gida tace, to tasha sanar dani lamarin ya hameed to anan nafahimci shid'in jarumi ne, kinga in kika shigo zaki raina kan... Fas tabuge mata baki abunda yahanata qarsa zancenta, ta nunata da yatsa tana mai cewa "wallahi khairi zan shuka miki rashin mutunci inabaki bar had'ani da wannan mutumin ba tam.
Afusace khairi ta kaimata duka a baki itama tayi saurin kaucewa tako sakar mata dukan a qirji, tafe wurin tayi idanunta sukayi raurau sabida ba qaramin duka tayi mata ba.
Maryam ce tasoma magana "wai miye haka kukeyi ne kamar yara? Banza sukayi mata ta kuma cewa "ke khairi tunda bataso kina danganta ta da shi man basai ki bari ba, haka kema Addawiyya kirage saurin hannu yanzufa bada bane, hankali da girma duk sun wada cemu don haka we r ol mature enough, sabida haka kamewa itace ta kamace mu ba wasan yara ba.
Duk sukayi shiru kowa da abinda yake saqawa aranshi.
Wata budurwa ce ta iso wurinsu ta katse musu shirun ta haryar duban Addawiyya tace "kizo malam Salim yanakiran ki yace kisameshi a office d'insa, tana gama fad'an haka tayi gaba fuuuu.
Tabe baki su kayi atare, zuwa can Addawiyya ta miqe tace don Allah kuzo ku rakani, miqewa sukayi tare da amsawa "tam.
Tafiya suke anatse mai cike da class har zuwa bakin office d'in masa sannan sukaja suka tsaya ta dubesu don neman qarin bayani, khairi ce tace "nan zamu tsaya har ki fito sabida baida mutunci yana iya tijaramu abanza inya ganmu tare, maryam ta d'ora "wannan shine za'ayi don haka ki shiga kawai munamiki fatan jin alkhairi amma ki kula da kanki domin kurane shi indai akan mace ce.
Gyad'a musu kai tayi tare da kwankwasa qofar daga ciki ya amsa da "yes come in.
Tura kai tayi ciki tana maijin fad'uwar gaba atake kuma tasoma jan addu'ar tsari.
Tunda tashigo yakafeta da idanu har ta qaraso bai d'auke idanunsa akanta ba.
Atake taji tayi mugun jin tsanarsa dama can tasan mayen kallo ne ita kuma bata shiri da mai yawan kallo shiyasa ta tubure akan Hameed don tuntuni tagama fahimtarsa yayi degree a kallon mace.
Maganarsa taji cikin kunninta "Rabi'atu zauna mana kya tsaya haka ai sai ki gaji, kallonsa tayi a fakai ce sannan ta russuna tace "Good afternoon sir.
Washe baki yayi yana wani kashe mata ido 1 ya amsa "lafiya lau, ya karatu? "Alhamdulillah "tam haka akeso, masha Allah.
Shiru yabiyo baya na wani lokaci, ta katse shirun ta hanya cewa "Sir, ance kana kirana "eh, dama wata magana nakeso muyi amma zaifi da na sameki agida dai, don haka sai kibani time dazan zo insameki kada kidamu da bani address d'in gidan domin sanishi bamai wuya bane agareni.
"Uhmm malam inhar magana bata tawuce 30 minutes ba kawai kasanar dani insha Allahu ina tare da amsarta.
"Ohk tunda kinfison ayita anan ai shikenan.
Shiru tayi masa kanta aqasa tana ta nazarin d'abi'unsa, domin d'an zamanda sukayi har tagano mutum ne mara kunya dubi da yarda yake mata magana yanajan yaji.
"Dama ina son muqulla wata alaqa ce ta zumunta wanda nake fatan ta kaimu har zuwa aure.
D'agowa tayi tare da qare mishi kallo, bakine har yana qalkiya amma yana da kyau ainun sai dai kallo da'ya zaka kayi masa kagano d'an barike na bugawa a mujalla.
Katse mata tunani yayi ta hanyar tasowa ya dawo ya zauna gefenta har yana shafar mata kafad'a da hanzari ta miqe tayi hanyar fita yayi sauri tareta yana wani langabar da kai "haba kekoh miye haka? Kallonsa tayi sai kuma tayi saurin kauda fuskanta gefe sannan tace "Kayi hakuri don Allah malam domin ban tsaida lokacin aureba gaskiya ayanzu, tana fad'an haka taraba gefensa ta wuce sauri, biyota yayi yaga har tayi nisa ita da qawayenta cije labbansa yayi yana mai furta "Allah sai kinsoni koda ta bayan gidane, bari in bar office tun yanzu na dangana da wurin malam halee nasanar dashi tun lokaci bai quremin ba.
Direct inda ta perker motarta suka nufa ta bud'e motar suka shiga ciki.
"Ya kukayi dashi? Maryam ta tambayeta, "uhmm tatsuniyar gizo ai bata wuce ta qoqi kalmar so dai ya jaddamin ni kuma nace a'a.
Dariya khairi tasa sosai zatayi magana maryam rayi hanzarin rufe mata baki,Addawiyya ta dubesu ta tabe baki ta kwanta tana cewa maryam "don Allah besty yi driving dinmu mu sauke wannan 'yar neman fitinar a gidanta ko nasamu kaina yabarmin ciwo, wanda neman maganarta ya haddasamin.
"Eh, na daiji kuma dole ya Hameed yayi winning ehe.
Banza tayi da ita, tako kwashe da dariya, girgiza kai maryam tayi tare da yiwa motar key suka fice daga cikin skul d'in.
Abin kamar had'in baki tana shan kwanar shiga layinsu bayan maryam ta sauka agidansu sai tacikaro da ubaiyu tsaye a get din wani gida ko kallonsa batayi ba ta wuceshi da gudu, tana mai dad'ajin haushi.
Ita kad'ai take cewa "ni haja ce halan da kowa zai soma son samuna? abinda ban fuskanta a zamanin 'yan matancina ba shine yanzu zai zamemin qalubale?
Amsar da take buqatan sani kenan amma ta kasa samowa.
A tsiyace tayi parking ta fito afusace ta tasarma ciki.
Tana shiga parlor tayi turus kanta yakuma sarawa kamar zai tsage biyu, hannu tasa ta dafe goshinta tare da zubawa Hameed idanu wanda yake zaune a gaban ummie da ala magana mai mahinmanci sukeyi dubi da yarda ya sunyar da kanshi kamar mai d'aukan ilimin addini ga malaminsa.
Quri yayi mata shima yana kallonta tare da nazarto tarin damuwa a face d'inta.
Sallamar Ubaiyu shi yasa tayi saurin isa wurin ummie ta kwanto da kanta a bayanta tana cewa "ummie yimin addu'a kaina ciwo kamar zai rabe biyu.
Sai da suka gama gaisawa da ubaiyu sannan tayi mata addu'ar, ta miqe ta nufi upstairs, ummie tace da ita "auta bakiga Hameed da Ubaiyu bane halan dabaki gaishe dasu ba?
Dawowa tayi cikin rangaji mai nuni da alamun gajiya atattare da ita tace "sannunku ya aiki da iyalanku?
Bata tsayajin amsarsu ba ta haye sama da d'an gudunta, tana shiga room d'inta ta kife ruf da ciki samar bed ta lumshe idanunta tana jin wani mai dad'i yana kad'a mata suma kuma tana jin shigarsa cikin jikinta abinda ya haifar mata dajin kasala, tayi lamo, acan qasan zuciyanta kuwa tunani ne fal har ta rasa wanne zata kama sai kawai tasoma istiggafari, bata jimaba tanayi barci yazo yayi awon gaba da ita.
*mrs j moon*
[2/7, 10:22 PM] Mrs J Moon๐: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*
NA
SAFIYYA.
*50*
Barci ne tayishi mai mugun dad'i wanda ya d'auketa lokaci mai tsawo don sai bayan magrib ta farka, miqa tayi tare da salati sai kuma tayi jim tana tunanin wannan wani irin barci ne tayi shi haka gashi har duhun dare ya shigo, d'an tsaki taja tana mai furta "ummie bata son inayin irin wannan barci amma yariga da ya zamemin jiki.
Hannayenta ta d'aga sama tace "Allah kayaye min shi cikin amincinka, ta amsa ma kanta da "Amin.
Wanka tashiga tabata lokaci sosai cikin bathroom sannan ta fito, shiryawa tayi tsaf sai qamshi take ta zubawa, asannu ta taka ta isa wurin d'an qaramin freeze d'in dake d'akinta ta bud'e ta d'auko babban kwalin hollandia drink ta zauna gefen bed ta bud'e kwalin ta zuba a wani glass cup mai d'an girma tasoma sha tana lumshe idanu, sosai take son duk abinda ya dangainci milk.
Wasa2 sai da ta kusa shen kwalin drink d'in dika sannan ta tsagaita ta d'aga kwalin ta girgiza sai kawai tasoma dariya ita d'aya tare da kai hannu tana shafa cikinta tafurta "waya gayamin barno gabar take, ai dole 'yan hanji sunemi abincinsu, tun safe kwankwani maltina kad'ai yake cikina fa, uhmm wallahi yunwa bata da kyau, Allah ubangiji kanesan tamu da ita alfarman Annabin Rahama, Amin.
Falon qasa ta sauko direct dinning area ta nufa, ta soma bud'e kulolin dake wurin, tuwon shinkafa ne da miyar agushi taji namar saniya sai qamshi yake tashi, sai soyayyen naman jabbi sunji kayan qamshi da kunun aya mai sanyi.
Bata rai tayi domin ita kam ta tsani tuwo arayuwarta gashi kuma tanajin k'yuyar shiga kitchen, da ta dafa ko noodle ne.
Hakanan ta d'iba tuwon kad'an ta saka cinyar naman jabbo 1 ta d'auko ruwan roba ta dawo cikin parlorn ta zauna, sosai taji dad'in food d'in domin sai da ta cinye shi duka ta kora da ruwa, ta d'au kayan ta shiga kitchen ta wanke ta kife sannan ta dawo falon ta kwanta samar doguwar kujera, tunani ne yake son zuwa mata arai amma taqi barinsa yayi galabar zuwa.
Tananan kwance ummie tafito d'auke da baby ummul sai kuka take ta tsalawa, da sauri ta tashi zaune ta miqawa ummie hannu tana cewa "ayya my sweetheart kinyi kewata ko? to zuwa muji d'imin juna.
Tanako amsarta yarinya tayi tsit ta kwanta lamo a jikinta.
Dariya Addawiyya ta saki tana kallon ummie tace "aha yarinya taji d'umin momma nta tayi tsit, anyama kuwa ummie ba mintsilinta kikayi ba? Ta qarasa maganar cike da zolaya.
Cikin hararanta ummie ta amsa "Eh, mintsilinta nayi, 'yar nema kawai, kuma kisani daga yau duk inda zaki da 'yarki zaki tafi don bazan iya da rigimarta ba.
Cikin marai raita tace "Ayi haka kuwa ummie? "Sosai ma kuwa, yi yazama dole ai "uhmm muna neman affuwan ummienmu baza muqara yi miki kukan banza kinji?
Qin kulasu tayi ummien.
Ganin haka sai ta kuma rungume ummul sosai tana sunsuna wuyarta tace "yarinya 'yar gatan ummie sai qamshi takeyi kamar fure, kyal kya lewa da dariya tayi ummul kamar taji mi akace.
Tsillata sama tayi cike da jin dad'i tace "kai inajin sonki 'yata har cikin tsokar zuciyata, Allah yasa ina da rabon ganin aurenki dai.
"Amin, ummie ta amsa tare da cewa "zauna ina son muyi maga dake, "tam ta amsa tare da zaunawa a gaban ummien ta zuba mata idanu yayin da ummul tuni ta sauka tasoma wasanta dama kukan rigimar son ganin addawiyya takeyi.
"Auta shin abinda kikayi d'azun kin kyauta kenan?
"Minayi kuma ummie? "Au kin manta irin gaisuwar asharuwan tsintsayen da kikayiwa Hameed da Ubaiyu d'azun?
Sunkuyar da kanta tayi qasa tana sosa tsinin hancinta, taqi cewa komi.
Kallonta ummie tayi sosai tana son gano damuwarta amma bata gano komi ba sai kawai ta cigaba da cewa "lallai hakika d'azun raina ya baci kuma naji kunyarsu sosai sabida ina ganin qimarsu fiye da tunaninki don haka banason sake ganin kin maimaita hakan koda abayar idanuna ne.
Ahankali ta amsa "tam ummie bazan sakeba ayi min affuwa, nadawo ne da matsanancin ciwon kai shi yasa.
"Allah ya sauwaqa to "Amin.
Miqewa tayi sabe da ummul wacce tasoma gyangyad'i.
"Koma ki zauna bangama maganar ba ai.
Kallon ummien tayi taga babu wasa sam atare da ita sai ta koma ta zauna gabanta yana fad'uwa.
*Ayi haquri da wannan don Allah*
*mrs j moon*