Complete Hausa Novels

Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 7 of 8

*Shafin na masoya ne dake dukkanin lungu da saqo, ku sani sosai nakejin dad'in yabawarku tare da addu'o,in ku agareni, domin haka shi yake qaramin qarfin guiwa, godiya nake agareku sosai fans. Allah yabar kauna, luv u always* 😍😘

*30*

Turus Hindu tayi sanda ta fito daga toilet ta cimma Addawiyya zaune hawaye jage jage a fuskanta.
Cikin rawar jiki ta isa inda take zaune ta dafa kad'anta tace "autan ummi mi aka miki?
Mai makon ta amsa mata sai ta fashe da kuka mai sauti.

Gaban Hindu ya yanke ya fad'i rass!!! Ta zauna gefenta jiki ba k'wari ta kamo hannunta ta rintse qam tace "fad'amin damuwarki Addawiyya, ko bakiso nasami qaruwan twins bane?

Da sauri ta girgiza kai tana jan hanci tace "tunani nake da ace hussain ya rasu ko ya zakiji aranki.

Cikin daburcewa Hindu tace "autan ummi wani abu ya farune? "Eh, ta amsa mata tare da bata labarin tundaga sanka taji uncle Habibullah yayi mata magana zuwa sanda ta ceci jaririn ahannun hajiya karima ta d'ora da cewa "amma ina mai roqonki dan Allah tare da manzonsa kada kisanar da kowa zancen, ita da kanta zata fad'a da bakinta intaji azaba.

"Autan ummi kinaganin rashin d'aukan matakin ba zai kuma bata dama wata rana tadowo ta cutar dasu ba?

Jim tayi tana nazari "bana tunanin zata kuma samun kuzarin sake cutar dasu, sabida yanzu haka tana cikin rud'anin kamata danayi tare da fargaba kada Alhaji yaji kuma tana mugun tsoron 'yan sanda, tana can ana fetsa yawo. Tagarasa maganar cike da dariyan mugunta, hawayen daya maqale yazubo a fuskanta ta sa hannu ta share tana cigaba da dariya.

Kama kunninta Hindu tayi tace Allah shiryamin ke Addawiy "Amin.

" Allah yacigaba dabamu kariya gabaki d'aya.
"Amin.aunty shine addu'ar da yadace muyi tayi kawai domin ita kaddaran Allah wanzarciya ce inta tashi zuwa babu tsimi babu daraba sai ta ilahu.

Atare Salma da Ummi suka iso, sai murna sukeyi suna hamdalah ga Allah.

Addawiyya tun shigowarsu dasun had'a idanu da Salma sai ta sa dariya.
Ummi ta dubeta tayi mata daquwa "kinci gidanku auta, yazakisa mutane agaba kiyi tayi musu dariya kamar wata mai tanbotsai.
Dariya takuma kwashewa dashi har da riqe ciki, ummi ta zabura tayo kanta ta kwasa da gudu tabar room d'in.

"Ummi kibarni da ita, nasa abinda take ma dariya kuma zanci mutuncinta inbata kiyayeni.
"Oh to kunfi kusa ai, nawa idanu.

Hindu ta sauke kallonta bisa tumbin Salma ta kauda kanta gefe tana dariya qasa2 tace "eh dole autan ummi tayi ta dariyan murna ashe mun kusa samun wani qaruwan ne.

Cike dajin kunya Salma ta miqe ta fad'a toilet, suka bita da dariya.

"Allah yaraba lafiya, "Allahumma Amin umminmu.

Mugun karo sukayi da juna ta kwalla qara ta zube aqasa, domin tayi mugun tsorata da ganinsa abazata, cikin hanzari ya d'agata yana kiran "sorry sorry, ta zame jikinta hannunta dafe da qirjinta, tafiya soma yi da baya da baya eyes d'inta yana kanshi har ta shige cikin kitchen.

Ya dafe kansa tare da cije labbanshi, ya saki murmushi mai sauti "i really luv u pretty, yafurta ahankali sai kuma ya yamutsa fuska "uhmm Allah kin wuce pretty akomai my heart, beauty zaifi dacewa dake my kwaila sai yasaki dariya ya dungule hannu ya naushi iska yana mai furta"amma fa Hameed d'an air ne, yanzu wannan zankad'ed'iyar budurwan yake kiranta da kwaila?

"Eh, Nakiratan mi za'ayi? Kai kwanso ma sunarta daga yanzu. Muryan Hameed ne ya doke kunninsa, ya juyo yana jifanshi da harara.

"Mantawa kayi fara ce.
"Eh, hakan ma yafi dad'i, naushi ya kai mishi ya kauce da sauri yana dariya. "Zan gyarama zama Allah "uhmm mr love ina saurare.

Bai kuma kula shiba ya shige bedroom d'in Hindu d'auke da sallama, Hameed yabi bayanshi yana tsokanar shi.

Addawiyya tana shiga cikin kitchen ta jingina da bango idanunta lumshe sai murmishi take dokawa tamotsa labbanta kad'an tace "he is very charming guy, uhmm ina son.... Sai kuma tayi saurin bud'e eyes d'inta ta tafe bakinta tana girgiza kai, jin motsin za'a shigo yasa tayi saurin bud'e qofa tafice ta baya ta nufi part d'in Hajja.

Khairi ta cimma zauna tana kallo bata dubi inda takeba ta wuce kitchen inda takejin motsin ana aiki da alama hajja ce.

Dogon tsaki khairi taja tace "shishshigi ba kwarjini, banza 'yar maula ka wai.

Bataga dawowar ta sai jin saukan mari tayi a face d'inta tassss!!!! Ta dafe wurin tana laliben hanya sabida ganinta ne ya d'auke na wucin gadi, tana ko samun hanya ta d'iba karce har tanajin tuntube yatsarta ta fashe amma ko dubawa batayi ba, burinta ta kawai taga ta tsira daga shan maru kan Addawiyya domin har yanxu bata manta da artabun suba na kwanaki ba.

Dariya ta saka har da dafe ciki tana nuna hanyar da khairi tabi da gudu.

Hajja ce ta fito d'auke da babban kula, ganin Addawiyya na dariya yasa ta koma kitchen da hamzari jikinta yana kyarma sabida ji tayi sautin dariyar wani iri kamar ba na muta ne ba.

Shigowa kitchen d'in tayi anatse hajja taja baya.
"Uhmm hajja dariyan nawane yabaki tsoro ko mi? To bara kiji abinda yasani dariya.

Tana gama bawa Hajja labari itama tasoma dariya tace "amma Rabi'a kinyi mugun tsorata min qawar hirata.
Cikin dariya ta amsa "gyara mata zama nakeyi, kuma yanzu muka soma buga game d'in har sai ta dawo cikin natsuwarta zan sarara mata.

"Lallai hakan yayi kyau d'iyar albarka, Allah yabaki sa'ar saita mana tunanita ta bar yiwa mutane fitsara.
"Amin hajjajunmu.

*****Ranar suna yara suka amsa sunarsu hassan da hussain.

Anyi barin naira, mutanen arziki sukayi ta zuwa suna kwasan gara.

Hajiya karima kam kamar zata had'iye zuciyarta don tsaban baqin ciki da yayi mata yawa gashi Addawiyya takasa ta tsare ta hanata halaka su kotaji dama dama, sabida dazaran ta doso part d'in Hindu sai wani hucin zafi ya dameta akan dole zata koma tana tsinewa Addawiyya, taje wurin malamanta sun kasa gono dalili afkuwar hakan, hakanan tanaji tana gani aka gama taron suna cike da masara.

Alh. Muktar ya biyawa Abbie, ummi, Addawiyya, mushaffa'u, Abba, mama, tare da Salma kujerun makka, yayin da zarar Hindu ta gama wanka yace zasu wuce umrah kuma baza su dawoba har sai sunyi aikin hajji wanda yanzu saura kimanin watani shida asoma tafiya.

Labarin yayi mugun jefa hajiya karima cikin rud'ani wanda atake jininta yayi mugun hawa ta yanke jiki ta fad'i aka kwashe sai asibiti, dakyat doctors sukayi nasaran ceto ranta amma fa taji jiki sosai, khairi sai kuka takeyi gunin ban tausayi.

Kakan su Hindu mahaifiyar maman su itace take kula da ita tare da yaranta.
Hajjama ba'abarta abayaba, ga ummi tana yimata soqo akai akai nakayan gyara da samun ruwa nono sabida Alh. Muktar yace baza'abama yaranshi madara ba nonon uwa yafi komi inganci ajikin jarirai.

Ita kam Addawiyya kuwa ta tarewa tayi agidan, islamiyya da computer school duk tana take zuwa ta dawo, ummi tayi mitan har tagaji na tadawo gidan yayi mata girma ita d'aya amma taqi.

Sunyi mugun shaquwa na ban mamaki da Hameed yayin da duk sanda suka had'u da Haydar ko taji muryanshi sai gabata yafad'i ga kuma wani tausayinshi datakeji acikin ranta.
zuwa lokacin tagama ganewa ta afka kogin son shi abinda take ta boyewa kada kowa yasani domin aganinta baqaramin zubda aji bane mace ta fidda soyayyarta fili ga namiji.

Shi kam Haydar yaqi sanar da ita ne sabida ganin yayi kamar tanajin tsoronsa yafiso su saba da juna sosai kamar yarda ta sake da Hameed.

Yau tana zaune cikin garden laptop ne agabanta tanayin assignment, gefenta had'ad'd'iyar phone d'inne take ta sauraren cool music, sai gyada kai takeyi abinta cike da nishad'i.

Yana zaune a balcony yana aikin kallonta yana doka murmushi, zuciyarshi sai azalzalanshi take da ya isa wurinta amma miskilanci ya hanashi motsawa. Ya kulle eyes d'inshi yana tasbihi cikin ranshi.

Hango khairi yayi zaune suna fuskanta juna da alama wani abu take koya mata computer, dubi da yarda yaga take d'agowa time to time tayi mata magana.

Mamaki ne ya cikashi, "yaushe khairi tayi hanakali haka da har suka zama qawayen juna? Lallai gaskiyan Hajjace da tace yarinyar tana da tare da wank baiwa wanda bakowa zai gane hakan ba sai tazauna awuri koda na kwanaki biyu ne.

Yana nan zaune yana ta aikin kallonsu, wutar qaunarta yanacigaba da ruruwa a ruhinsa, zuwa can yaga sun miqe atare, Addawiyya ta ruga da gudu ta rungume wata budurwa da alama qawarta ce, sai murna sukeyi ita da budurwan, ko kafin ya ankara sun shige cikin gida.

Saukowa yayi bi bayansu cike da k'warin gwaiwa.

So yake yau su soma qulla alaqa ta abota inyaso da zarar sun saba da juna sosai sai ya samu hanyar sanar da ita sirrin zuciyarshi.

*mrs j moon*
[1/15, 4:48 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATU ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

*Aunty maijidda musa keta dabance agareni kisani kullum comment d'inki yana jefani cikin nishad'i ainun kuma yana qaramin kwarin guiwa sosai. Ina alfahari dake, thanks* 😍😘

*31*

Yana shiga parlor n dai dai ta fito daga kitchen d'auke da tire madaidaici shaqe dakayan motsaba baki.

Gabanta taji ya fad'i, jikinta yasoma rawa ta tsaya tsak, kanta aqasa, tasan Ali ne yazo wurin tunda taji jikinta ya sanja, baki ta tura tare da d'ago kanta ta dubi qofar shigowa, ta sauke eyes boll d'inta akanshi ya coge tare da hard'e hannayenshi bisa qirjinsa ya zuba mata idanu bako qiftawa, sai ta qara daburcewa gabanta nacigaba da fad'uwa, tayi saurin tasake yin qasa da kanta.

Takowa yayi asannu har ya iso inda take tsaye ya miqa hannu ya amshi tire d'in ya matsa daf da kunninta yace "halan ni dodone da kike jin tsorona har jikinki yana rawa haka?
Wani yarrrr taji ajikinta, tayi saurin ja baya qara matsowa yayi zata gudu ya take mata qafa ta rintse idanunta dan azaba, ya saki murmushi mai sauti ta bud'e idanun tana hararanshi.

"Waww beauty kinfi kyau ahaka, tura baki tayi ta ma rairaice face tace "d'agamin yatsu kada kajimin ciwo.
Da sauri ya d'aga mata yana kiran "am sorry bazafi ko?
Wani kallo ta sauke mishi tayi gaba yabiyo bayanta yana dariya qasa qasa.

Zama tayi gefen maryam tana wani yamutsa fuska, sai tayi mishi mugun kyau ahaka, ya ajiye tire d'in akan table dake gabansu yana qoqarin bud'e robar coke tayi saurin riqe mishi hannu sai kuma ta saki da hanzari tana yarfe yatsunta.

Murmushi yayi mai burgewa, yaja baya ya zauna akujeran dake kallonta, ya kai dubanshi inda khairi take zaune, wacce tumd'azu ta sake baki da hanci tana kallon abin al'ajabi, wai ya Haydar ne yake nuna soyayyarshi a zahiri haka bako kunya.

"Ke tashi kibawa mutane wuri, kina wani kallon mutane idanu biyu. Maganarshi ya katse mata tunani.

Da sauri ta miqe tabar wurin tana dariya, cije labbansa yayi yana bin bayanta da harara.

"Uhmm qawarmu kin iso lafiya? Yace da maryam, ta amsa "lafiya lau, ya office da ayyuka? "Alhamdulillah amma ba dad'i kam.
"Ayya to Allah tai maka "Amin, thanks.

Addawiyya wacce take saurarensu ta motsa sannu cike da class ta soma zubawa maryam drink ta miqa mata sannan ta bud'e container mai d'auke da danbum nama azuba ta tura gabanta tana satan kallon Haydar wanda yayi balance ya zuba mata manyan idanunshi.

"Godiya nake aminiyata, maryam tace da ita.
Murmushi tayi mata batare datace qalaba.

Sosai ta takura da zamanshi a wurin, duk motsin daza tayi eyes d'inshi na kanta, tana son gudu amma ta kasa tashi.

Hira suke tayi da maryam kamar sun dad'e da sanin juna, ita dai komi takasa cewa koda kuwa sun sakota cikin hiran iyakarta gyada kai ko girgizawa, tazama kurman qarfi da yaji.

Shigowar Hameed yasa ta tashi da sauri tashige bedroom.

Dariya Hameed yasa yana nuna Haydar yace "waww nawa yasoma bada assignment kenan, tam Allah yasa ayi nasara.

Had'e fuska Haydar yayi tare da wulla mishi harara yace "kaifa banza ne wallahi, gashi nan da zuwanka ka kora mana abokiyar hira ko qawarmu?

Murmusawa maryam tayi tare da gyad'a mishi kai.

Tabe baki Hameed yayi yamufi dinning area yana cewa "kadai tsaya kallon ruwa kwad'o yayima qafa.

***** "Qawata mi yake faruwa?
"Kamar na mi fa? "Tsakaninki da guy d'incan Haydar mana.
"Oh babu komi illah zumunci a matsayinshi na d'an mijin aunty Hindu.
"Ba wannan nake son jiba, tunda kinfi kowa sani nasan hakan.

Miqewa tayi zata shige toilet maryam ta fizgowa ta zauna bashiri.
"Miye haka Rano? "Mele ne "uhmm yau dai da jin fad'a kikazo kenan? "Bansani ba.

Shiru sukayi kowa da abinda yake saqawa aranshi.

Addawiyya ce ta katse shirun tahanyar dafa kafad'an maryam tana cewa "kiyarda dani qawalli Allah babu komi a tsakaninmu hasalima bama magana sam da juna yaune naga yana son kawo qarshen 'yar shariyan dake tsakanmu ni kuma banjin zan iya sakewa da shiba kamar yarda na sake da d'an uwarsa Hameed ba.
"Ko akanmi yasa baza ki iya ba?
Shiru tayi zuwa can tace "forget kawai qawata.
"Uhmm dole kice haka man, tunda kinsan baki da gaskiya "ya salam my Rano minayi kuma? "Boyemin sirrin zuciyarki da kikayi "uhmm ke nifa bangane inda kika dosa ba kam "zakigane yanzu yarinya, xuciyarki ta kamu da sonshi, koba haka bane?
Kauda kanta tayi gefe ta amsa kamar mai ciwon hakori "eh, haka ne amma nasan nice nake sonshi, shi bai san inayiba dan haka naboye abin araina sabida gudun kada yagane ya wulaqanta ni, haka nan naqi sanar da kowa ne dan bana son yaji class d'ina ya zube, dafatan kinfahimce ni yanzu.
"Eh, na fahimta amma dai ina da qorafi "tami ba? "Ta yarda baki d'aukeni da mahinmanciba, kikayi ta boyemin sirrinki alhalin ni nawa bana iya boye miki, kadafa kimanta kece ta farko da nasoma sanarma had'uwata da my ustaz kuma kika bani shawara mai kyau gashi yanzu inata cin moriyarta, soyayya mai tsabta ya kankama a tsakaninmu dashi.

"Am so sorry my lovely friend, bazan qara hidden miki komi nawaba daga yanzu.
"Uhmm Allah yasa, "wallahi kinji na rantse bazan kuma ba "tam nayarda "aha thanks besty.

Qasa tayi da murya tace "qawata yanzu miye mafita, abinfa yana son zamamin chronic.
Dariya maryam tasa sosai har da kwalla zuwa can ta tsagaita tace "aini hakan yayimin sweet ainun, dama na dad'e inayi miki addu'a Allah ya saka miki so mai zafi kiji abinda mukeji ko kyabar mana iskanci akai.

Duka ta kawa mata, maryam ta miqe da sauri ta nufi hanyar fita tana cewa "bara naje na sanar dashi, shine kawai bafita.

Aguje tabiyo bayanta tana son kamata amma ina harta fice compound.

Dawowa d'aki tayi ta dafe kanta tana furta "wayyo ni Rabi'atul Addawiyya nagama yawo, sai kuma ta miqe da sauri ta hau had'a kayanta tana gamawa ta fito parlor janye da trolley d'inta.

Rurus taja ta tsaya tana kallon maryam tare da Haydar durqushe gaban aunty Hindu kamar masu neman gafara.

Maryam ce tasoma ganinta ta sakar mata murshi tare da kashema ido d'aya ta motsara baki ta furta wata kalma.

Harara Addawiyya ta dalla mata, ta saki 'yar dariya ta miqe ta iso inda take tsaye ta kai bakinta kusa da kunninta tace "qawata d game is over, munyi winning dan haka yana cewa kule kice cas.

Wani hararan ta kuma doka mata tare da Janye jikinta zata koma ciki "hindu ta kira sunarta ta tsaya batare da ta juyo ba "ki shirya Haydar yanemi alfarka zaki rakashi unguwa yanzu, ga maryam nan sai ku sauketa agida daga nan.
Juyowa tayi cike da shagwaba tace "ni gida zan koma yau, nagama had'a kayana yanzu zan wuce, yanemi khairi ta rakashi.
"Autan ummi nice zanbaki umurni kikawomin taki na daban? To yayi miki kyau, wuce ki tafi ga hanya nan.
Ganin ran Hindu ya baci yasa ta saki trolley d'in qasa ta qarasa gabanta ta zube tahannayenta bisa guiwoyinta, muryanta na rawa tace "don Allah kiyi hak'uri Aunty banufina in bata miki ba, sai dai ina neman alfarma da yayi hakuri zuwa gobe sabida yanzu baifi nan da 10 minutes za'akira sallar magrib, kinga koda zamu dawo sallar ta wucemu kuma maryam kwana zatayi dan mami ta hanata tafiyan dare.

Dafa kanta Hindu tayi tana murmushi tace "nafahimceki autan ummi.

Dafatan Haydar zaiyi hakuri zuwa goben? "Eh' aunty zanyi, da yau da goben ai duk 1 ne, Allah yakaimu da rai da lafiya "Amin, maryam ta amsa.

Sai da yayi nasaran kallon kwayar idanunta ya sakar mata murmushi sannan ya miqe ya fice, tabi bayarshi da kollo tana murmuhin gefen baki.

"Uhmm autan ummi angirma ko? Da gudu ta tashi tashige d'akinta, suka saka mata dariya, kaka Abu ta fito daga kitchen tana tayasu ita ma duk da bata san abinda suke dariya akai ba.

****Shaquwa mai tsanani yashiga tsananin Addawiyya da Aliyu, abinda yayi mugun bawa mutanen gidan mamaki sabida shi mutum ne mai wuyar sha'ani ba'agane kanshi sam amma sai gashi cikin d'an lokaci soyayya ta sanjashi sosai kuma har lokacin yaqi furta mata kalmar ina sonki, ita kuma tsaf tagane imda yadosa so yake ta bara da kanta, abinda ko bazai samuba kenan koda zasu shekara ahaka in har bai furtaba itama baza ta ce ci kanka ba.

Hameed kam dariya yakeyi musu yana mamakin wannan salo tasu abinda ko amufarki bazai iyaba, shi in yana son abu ba boye boye zai fad'a, he was very frank about any things shiyasa yafi Haydar rashin sirri.

Yau Hindu tagama wanka kuma yau zasu maida kaka Abu gida daganan su wuce gidan Abbie su yini, dan haka Addawiyya tana fitowa wanka ta tsaya ka tsara kwalliya mai kyau da burgewa ta sanya wata super d'inkin riga da zani ta kafe d'aurinta ya zauna d'as akanta ta yafa gyale kalan atamfar ta sanya hill shoe kalan da yadace da kayanta tana cikin fesa turare taji iska ya shigo bata juyaba ta cigaba da abinda takeyi dan tasan uncle babibullah ne.

"Uhmm mai babban suna angirma ansoma soyayya ko?
Tura baki tayi tana kallon shi tace "uncle mi yasa kayi watsi dani?
"Sabida kin girma yanzu, bakya da lokacin kanki.
Idanu waje tace "nid'in? "E, "to aikin mi nakeyi? "Ta tunanin masoyinki Ali.
Kauda kanta tayi cike da jin kunya, ya saki 'yar dariya yace "Allah yabarku tare, shima yana sonki sosai amma akwai jarabawar rayuwa azamanta kewarku, ina yi miku fatan cinyewa da kuma samum sakamako mai amfani, yaja numfashi yace "sorry mai babban suna, daya yau zanyi nesa dake agame da ganina dakikeyi azahiri amma dai zakiriqa jin maganata lokaci zuwa lokaci.

Idanuta ya ciko da kwalla zatayi magana ya rigata "kada ki damu mai babban suna ina tare da ke ako ina, bye.
Ko kafinta tayi magan ya bace bat.

zaunawa tayi jiki asanyaye tana son gano inda maganganun uncle d'inta ya dosa amma ta kasa gano komi.
Jarabawa wacce iri kenan? Ganintana batawa kanta lokaci yasa ta miqe ta fito parlor ta tadda duk sun shirya ita suke jira.

Haydar ne zai kaisu, yana ganinta yayi saurin bud'e mata front seat sai da ta zauna sannan ya bud'ewa su Hindu back suka shiga, khairi tace "ya Haydar mata tafi uwa ko?
Ahanzarce ya juyo yana kallonta ta gyad'a kai tana cewa "eh'man kana ganin aunty amma sai da kayiwa Addawiy wuri sannan ka tuna da ita.

Kauda kai yayi yana murmushi su kaka Abu suka saka mishi dariya itama Addawiyyan dariya tasa tayi qasa da murya tace "abin boye dai yau yafito fili.
Mintsilin cinyarta yayi ya amsa "muna isa zakiyimin bayanin me zancenki yake nufi.

Cikin kwabe fuska kuma cike da shagwaba ta ture hannunshi tace "Mugunta dai baya da kyau.

"Haydar ko mufita mubaku wuri ne, ku gama soyayyar?

Cike da jin kunya ya shafi sumar kanshi yace "uhmm aunty gyara zama takeyi fa, banza tayi mishi, ya waiga ya watsawa khairi kallon zakisani ne yarinya sannan ya yiwa motar key suka fice.

*mrs j moon*
[1/16, 4:02 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

*Pape d'in nakine sis Barakah, Allah yabar so da k'auna, inajinki sosai aβ€πŸ‘ˆπŸ»πŸ˜˜ kuma Addawiyya tace ki saurari zuwanta garin barno don duk sai ta tone asirrin boye da masu bama bamai suka binne maku* πŸ˜…lol.

*32*

Kaka Abu suka soma saukewa agidanta, sun cikata da kayan arziki sosai sai godiya take tayi tare da samisu albarka.

A gidan Abbie ummi tarasa inda zata sakasu tayi don murna, ta d'auki hassan ta koma ta d'auki hussain sai kiran "masha Allah takeyi cike da murna.
Addawiyya sai dariya take mata tare da tsokanarta tace "su ummi anga yara masu kalan larabawa duk anbi an rud'e to kisani dai ko yaye baza mu baki su ehe.

Ta amsa cikin wasa "nima banso, kuyita riqe 'ya'yanku nawa sun isheni.
Suka saka dariya su dukansu.

Anan suka yini sai bayan la'asar Haydar yadawo d'aukansu.

Yana shigowa idanun shi ya hango mishi Addawiyya zaune da wani suna hira sai dariya takeyi, wani abu yaji ya sokeshi azuciya yasami kanshi da kasa fitowa bayan da yagama gyara parking.

Addawiyya kam Sarai taga isowarshi, tayi kamar bata gani ba, ta cigaba da sauraren hiran Aisha wanda ubaiyu yake mata.

Afusace ya fito ya wucesu zuwa ciki, bayanshi tabi da kallo tana murmushi.
Ubaiyu ya dubeta "Addawiy ko shine wanda ya kasani? "Uhm tace tana sunkuyar da kanta qasa.
Ah lallai yaciri tuta kam, Allah yabar so da qauna mai nagarta, ta amsa Amin cike dajin kunya.

"Abinda yaja kenan nafad'a tarkon sonki a baya, wato kunyarki da natsuwarki.
"Uhmm Allah yabaka wacce tafini komi ai, gata babba ba yarinya kwaila kamata ba.
"Kece kwailan? Aikam Ko makaho ya laliba yasan kinfi qarfin akiraki da kwaila.

kauda kai gefe tayi ta nunashi da yatsa "kaikoh? Baka da dama ya ubaiyu Allah.

Dariya ya saki yana sosa gemunsa ya miqe yayi gaba sannan ya juyo "tafi wurin mijinki kada yazaci muna soyewa ne.

"Uhmm kafa samu abinyi tsokanata kenan yanzu, to a inkaje kagai damin da Aisha kasanar da ita zanzo cikin satinnan muga juna.
"Zataji, amma ni zanzo nayi mikk jagora ko? "Ai kasan nasoma makanta hqr nasoma shelan neman d'an jagora.
Dariya yasa sosai yana nunata da yatsa, "a'a bance ba autan ummi, harara da dalla mishi tace "banson jin sunar nan abakinka tam.
Sai da ya russuna ya dunqule hannu yayi mata jinjina sannan ya amsa da "angama ranki shi dad'e.
Baqaramin dariya abin yabata ba, tana cikinyi ta hango fitowar su Hindu, ta d'agawa ubaiyu hannu alamar bye tayi ciki da sauri.

Qarasawa yayi wurin su Hindu ya gaishe da ita yaga su twins ya fidda kud'i mai yawa ya miqawa khairi yana cewa "asayawa su twins pampers.
Godiya Hindu tayi mishi, ya juya tare da miqawa Haydar hannu sukayi musa baha, ya shige motarsa ya fice yana jin jina lamarin Haydar ganin yarda ya amsa mishi sallamar kamar baya so.

A bisa hanyarsu ta komawa gida sai harara yake ta wullama Addawiyya, ita kam sai murmushi take sakar mishi da zarar sun had'a idanu abinda ya qara tunzira zuciyarshi yaji kamar ya tsaya ya fiddata a cikin motarshi.

Suna isa tayi saurin ficewa tayi ciki harda had'awa da gudu.

Cije labbanshi yayi yana jijjiga kai, yana ayyana irin hukuncin da zaiyi mata in suka had'u.

Wasan 'yar buya suka soma, duk inda tasan yake bazata je wurinba haka nan da zarar ya shigo part d'in Hindu ko Hajja indai tana ciki bazata bari ya ganta ba.

Yashiga cikin damuwa sosai, har yaji ya tsani kansa, da ace bai nuna mata yana qumunta ba da duk haka bai faru ba. "Yau ko ta tsiya sai naganta, ya furta tare da miqewa yafad'a toilet.

"Khairiyya wallahi inbaki fita shirgin 'yar banzan yarinyar nan ba mai siffan aljannu ba zanci mutuncinki.

Tura baki khairi tayi tana qunquni.
"Fito fili ki zageni kawai khairi ba ki tsaya yimin gunaguni ba.
"Ni ba zaginki nake yiba momy kawai cewa nayi nakusa komawa gaba d'aya part d'in aunty Hindun ma, sabida can yafi nan dad'i kuma mutane suna kai da kawo sosai fiye da nan part d'in, ba'a zama shiru kullum cikin nishad'i ake, muyi karatunmu tare da ita, muyiiwa su twins wanda mu shiryasu mu goyasu har suyi barci sannan acan nakoyi abu buwa masu yawa wanda ke kika kasa koyamin kamar girmama babba, girki mai dad'i, sallah cikin time d'in tare da koyon had'a baqin ajami wanda mugun gatan da kika nunamin yasa bansan komai ba akai amma yamzu alhamdulillahi taraiyata da Addawiyya nasami abu buwa masu tarin alfanu wanda ada nagaza samunsu don.... Saukan marin da Hajiya karima ta falla mata yasa take maganarta ya cinke ba shiri.

Baya taja tana kallon uwar nata idanu waje hannunta dafe da quncinta.
"Momy ni yau kika mara? "Eh, kuma ina daf da lakad'a miki dukan kawo wuqa indai har baki rabi da wad'ancan harsabiban muta nen ba.
Ja baya takuma yi tana girgiza kai, hawaye tuni yagama wanke mata fuska tace "billahil azim bazan rabu da mutanen kirki irin su ba, koda kuwa zaki zamo ajali nane.

Salati hajiya karima tasaka tana tafa hannayenta, ta nuna qirjinta tace "wato kina nufin nid'in mutumiyar banza ce kenan ko khairi?
Muryanta na rawa ta amsa "a'a momy baha nake nufiba.
Ta soma matsowa inda take tana ja baya "to ya kike nufi fad'amin inji sallamammiya wacce aka gama bata rubutun kashe zuciya ta shanye.

"Momy kibar fad'an haka baya da kyau don shine ake kira zato zunubine koda yakasance gaskiya ne.
"Yau nagama ganin Ikon Allah mai mana ruwa, ni karima nagata kaina, wato wa'azi suka turoki kiyimin kenan? "A'a momy nadai san hakan ne ayayin had'uwata da Addawiyya dan ita mai tarin ilimi ne sosai musanman na islama, to ita take koyamin da zarar mundawo daga islamiyya kuma ina ganewa sosai don haka ina roqonki dan girman Allah da manzon sa kidaina aibata su kije kigode musu na dawo miki da 'ya dAsu kayi hayya miqaqqiya amai makon da datake aband'are.

Wani marin ta kuma sauke mata ta fizgota tayi cikin bedroom d'inta da ita, sai ihu take tana kiran wallahi ina tare dasu koda zaki zama ajalina ne.

"Bazan zama ba amma zaki gane kurenki yau, sai naga uban da yatsaya miki agidan nan.

Afusace aka banko qofar aka shigo Hameed ne yashigo cikin fushi ya kwaceta ahannunta, da gaggawa khairi ta koma bayarshi ta lafe tana maida numfashi.

"Uban wa yabaka izinin ka shigomin part.
"Ubana, mari ka kawo mishi ya tare yana zare mata idanu ta zabura zata kamota abayarshi ya daka mata tsawa "wallahi kibar ganin ke kika haifeta to bashi zai hana in faffalla miki mari akan taba.

"Ni d'in zaka doka Hameed?
Gyada mata kai yayi tare da juyawa ya kama hannun khairi yace "muje ki kwashe kayarki daga part d'in nan ki koma na aunty kuma koda lokacin tafiyarsu yayi gidan su Addawiyya zaki tafi har sai sundawo.
Ta amsa mishi da "to jikinta duk yayi sanyi.

Duk jaraban da hajiya karima take musu bai sa sun tsaya da abinda sukeyiba, khairi ce ma tayi qasa da murya tace 'ya Hameed momy fa tana sona kada intafi hawan jininta ya tashi.

Shima murya can qasa ya amsa "walata zamuyi ai, wata qila zata san Allah d'aya ne.
"Ohk nafahimta.

Ranar haukane kawai batayiba gashi har yanzu part d'in Hindu baya shiguwa mata balle taje ta d'auko 'yarta, haka dai tayi ta zage zagenta bawanda ya kulata hattako da 'yar nata khairi.

Hajja ta kaiwa qara itama ta goyi bayan Hameed inda tace "da part d'inki dana Hindun ai duk d'aya ne.
Cikin fushi tabaro part d'in tana jiran Alh. Yadawo daga tafiyar da yayi qasar Germany ayi wacce za'ayi sabida bazata taba lamunta ba arabata da 'yarta d'aya tilo.

"Khairi miyasa kikayi haka? Ba'a fad'a in fad'a da mahaifiyya, girma ake bata koda aya take, inkina son dawo da ita hanya ai asannu zaki bita, ko yanzu kinsan kuwa kina cikin fushin Allah sabida tayi fushi dake, kuma hakan zai iya shafan karatunki burinki na son kiyi saukan alqu'ani zaki iya rasarashi, don haka tashi maza in rakaki ki bata haquri.
"Addawiy baza ta haqura ba, zata dokeni ne.
"Ba hujja bace hakan khairi, tashi maza autan ummi tayi miki jagora, insha Allahu baza tayi miki komi ba.
"To aunty, nagode da kulawarku gareni, Allah yasa da khairan.
"Amin.

Sun cimmata zaune ta tsokala d'ankali gaban goshi, ture kaga tsiya kenan sai huci takeyi ita 1.

"Kuficemin a parlor tun banji muku ciwo ba!! Tace dasu cikin tsawa.

Juyawa khairi tayi a tsorace zata fita Addawiyya ta kamo hannunta tana girgiza mata kai, suka iso gabanta suka russuna "momyn khairi kiyi haquri bazata qaraba kinji?
Kallon banza ta saukewa Addawiyya, zatayi magana ta kafeta da idanu, atake tayi shiru tana jan wa'innahu sulaimanu acikin zuciyarta dan gani tayi idanunta sun koma mata kamar bana muta ne ba, anya 'yannan cikakkiyar mutum ce kuwa?
Tambayar da tayi cikin zuciyarta kenan kuma tagaza lalibo amsarshi.

Murmushi addawiyya ta sakar mata ta tashi ta koma samar kushin ta zauna tana ci gaba da kafeta da idanu.

"Momyna ki yafemin ba burina na bata miki ba, sharrin zuciya ne yasa nayi sa'insa dake amma ina roqon affuwarki don Allah badan halina ba.

Kamo khairin tayi ta rumgume tana shafa bayanta tace "Nayafe miki 'yata amma bisa shara'in zakidawo part d'ina "zan dawo momy "ohk tam komi ya wuce "thank you my momma.

Sai kuma ta zame jikinta ta zauna tare da lankwashe qafafunta ta soma magana "ina son don Allah momy ki cire tsanar da kikayiwa su aunty Hindu aranki domin sud'imuta nen kirkine, kinga wannan tanuna Addawiyya da yatsa tacigaba Allah sanadi ita ce silar komawata mai hankali amai makon mara shi, mai matsuwa amai makon mara tarbiyya, mai ilimi amai makon jahila, mai kwarjini amaimakom mai bakin jini, mai ibada amai makom mai wasa da sallah, nasamu abubuwa da dama atarayyana da dasu na 'yan lokaci qanqani duk kuwa da ada nayi ta zaginta amma dayake Allah yasoni da shiriya sai tayi galaba akaina batare da nasani, don haka ina roqonki da ki daure ki cirekomai aranki muzauna lafiya dasu, kinji ko momyna?

"Uhmm naji, kutashi ina son yin runani akai, sukayi mata godiya suka fice, ta tabe baki tana mai cewa "ba shiri atsakaninmu har abadan abidina, kedai da suka mallake kiyi ta zama dasu amma ni kam ina kan bakana sai naga qarshensu har iyayensu.

*nikam nace uhmm wanda yayi nisa baijin kira sam*

Daf dazasu shiga part d'in Hindu, Addawiyya taji caraf an damqe mata hannu ta juya atsorace tayi arba da Haydar,ta tura baki tare da qoqarin kwace hannunta, yaja ta da qarfi zuwa part d'insu batare da yace da ita kanzil ba.

Khairi tasoma yimusu dariya har suka bacewa ganinta, ta d'aga hannuta sama tace "ya ilahu kasadani da mai sona da qauna mai tsafta kamar yarda ya Haydar yake son Addawiyya.

*mrs j moon*
[1/17, 4:07 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

*33*

Sai da ya zaunar da ita abisa cushion sannan ya saki hannu.
Miqewa tayi da sauri zata fita yayi hanzarin shan gabanta ya miqa hannu zai riqota taja baya tana hararan shi "Ya Ali wallahi banson haka.
Shiru yayi mata ya koma ya zauna, batare da ta kalle inda yake bas ta nufi hanyar ficewa.
"Don Allah kada kitafi, magana nakeso muyi dake.
Tsayawa tayi cak, ya tako zuwa wurinta ya dafan kafad'anta tayi saurin zamewa ta had'e rai tace "nace kabar son tabamin jiki, baya da kyau hakan sam a cikin addininmu.

Rungume hannayensa yayi aqirjinshi ya langabar da kai ya motsa labbanshi kad'an yace "Sorry my heart bazan qaraba.

Kallon shi tayi sosai bako qiftawa, ya gyada mata kai murmushi d'auke afuskanshi, itama mirmushin ta saki tana mai kauda fuskanta cike dajin kunyar kallon data yi mishi na ido cikin ido.

"Uhmm my angel zo kizauna in bud'e miki asirin zuciyata yau, maqe kafad'a tayi kanta qasa, "au bakya sonjin sirrin kenan? Ta girgiza kai, "uhmm kinsoma azumin rashin magana ne? "Eh ta amsa, yasa dariya sosai ya saita voice dinsa cikin serious yace "Rabi'a zo nan magana nakeson muyi dake mai mahinmanci.

"To kazo muje garden sai muyi maganar acan.
Kallonta yayi na 'yan daqik'u kamar zai zanyi magana sai kuma yayi shiru tare da miqewa ya doshi qofar fita tabiyo bayarshi.

Zama sukayi samar kujerun roba dasuke cikin wata madai daiciyar rumfa a cikin garden d'in.

"Rabi'atu bakiyar dani bako? Kina tunanin zan iya cutar dake ko? Yace da ita cikin sanyin murya.
Amsawa tayi itama cikin sanyi "A'a ya Haydar banufina kenan ba ina dai qoqarin ganin mun kiyaye haqk'ok'in addininmu ce ta islama, inda ya tabbatar da cewa duk inda mace da namiji suka kebe su biyu musanman baligai to shed'anne na ukunsu, alokacin komi zai iya faruwa atare dasu koda kuwa sud'in kamilallu ne domin sharrin kaidin shed'an la'ananne saninsa sai Allah kad'ai ba mutum ba, don haka naga ya dace muyi taka tsantsan da hakan, amma in hakan baiyima dad'i ba ina neman affuwarka please.

Jan doguwar nufashi yayi yace "lallai ked'in tadabance Addawiyya, duk yarda zakiyi magana sai ilimi ya fita cikinsa, sosai naji dad'in samunki arayuwata, nafahimce ki kuma bakiyin komi ba, Allah yacigana da karemana gabbanmu daga sharrin shed'an da afkawa barna.

"Amin ya rabbi yayana.

Sosai sukasha hiransu ta masoya inda kowa aranar yanunawa d'an uwarshi irin matsanancin son da yake danqare cikin ruhinshi.

Basu sukayi haramar barin wurinba sai daf da magriba.
Ta dubeshi cikin murmushi tace "Ya Aliyu lokaci salla ta gabato, yakamata mutashi hakanan.

"Ya salam!! Beauty namanta banyi sallar la'asar ba gashi har lokacin magrib ta shiga.
"Ya ilahi, affuwan mantawa nayi ban tuna maka ba don ni ina fashin sal....tunawa da tayi dawa take magana yasa tayi saurin rufe fuskanta da tafukan hannayenta ta kwasa da gudu tabi ta qofar kitchen tashige ciki.

Murmushi ya saki mai sauti ya furta "kunyarki tana dad'a jefani cikin sonki tare da begenki ainun, i luv u wit ol my herat.

Sai da yabatar da sallar la'asar sannan ya nufi masallaci don yabi jam'in magrib.

Bashi yabaro masjid ba sai da ya sallaci isha'i kuma yaga batar da shafa'i yabar wuttiri sai yazo kwanciya.

Yana shigowa get ya hango Hameed yaci uban kwalliya zai shiga car d'insa.

Da sauri ya qaraso wurin ya kama kunninsa ya murd'a da qarfi yako saki 'yar qasa don yaji zafi sosai.
"Hameed mi yasa har yanzu hankali ba zo maka ba? "To minayi kuma Abbana. Yace cikin fushi tare da fizge kunninsa yana liliyawa.

"Kafi kowa sanin abinda nake nufi, yanzu ace ga baki ga hanci amma ka kasa zuwa bin jam'in sallah masjid?
" kai bros ya sayyidi, Kadai san sanyi akeyi don haka na had'a arollar sallar magrib da isha'i nakeyi nayisu lokaci d'aya.

"Ya rasulillahi!! Hameed yaushe zaka daina wasa da ibada ne wai? "Uhmm kai ne kake ganin ina wasa da ita amma ni kam nasan inayinta yarda ta dace.

" uhmm ko? To kasani Wannan abin da kakeyi baka da hujjar kare kanka ranar gobe qiyama a gaban Allah don haka ka hanzarta dawowa bisa hanya na kwarai tun kafin lokaci ya qure maka, don mutuwar fuji'a yanzu ake yayin yinta kuma ita alamar tambaya ce gawanda ta riska.
"Allah ya tsaremu da ita dan alfarman Annabi SAW. "To Amin, adai gyara kaji ko? "Tam Allah yabani iko "Amin.

"Uhm yanzu da ka kasa zuwa masjid sallah sabida sanyi to yanzu kuma ina zaka?

Sai da yasaki lafiyayyiar murmushi ya wani kwanbare sannan ya amsa "gidan su heart d'ina, sabida gidansu ba'a wuce 9:30pm ana hira so shine zanje da wuri kafin tym d'in nasan abinda na yaga.

Idanu waje Haydar yace "mi zaka yaga Hameed?
Sirrin tsaki yaja yace "kai dalla malam ba abin ashsha zanyi ba kawai hirace ta ma'abota k'auna zan yarfar mata itama ta yarfomin shine ma'anar yagowar.

"To Allah ya shirya ka, inka isa kace ina gaishe da ita.
"Amin bros, insha Allahu zataji.
Yana tsaye har ya fice, ya juyo jikinsa a sanyaye saka makon tuno mahaifiyarshi da yayi.

Tun suna yara ummansu hajiya Rahmatu take yaqi da Hameed akan sallah har suka soma mallakan hankalinsu tana aikin abu 1, baya son juwa jam'i haka bayayinta cikin lokacinta sai yaga dama, bayan rasuwarta Alh. Muktar ya d'ora akai, kullum sai yazo dakanshi ya tashesu zuwa masallaci sallar subahi amma Hameed baya zuwa sai Abban yayi da gaske, dakyat aka samu yake zuwa batare da qorafin shi barci bai isheshi ba, sanyi yakeji.
Amma sauran sallolin kuwa wannan agida ko office yake yinsu baya yinsu cikin jam'i suma wata rana rankasu yakeyi, Haydar kullum fad'a yake yi masa ya bar wanna d'abi'ar ta ranka salloli amma yaqi dai nawa.

Matsar dake damunshi kenan amma inbanda ita shid'in mutum ne mai kirki da tausayi ga iya barkwanci, kowa nashi ne haka nan baya shashanci da 'yan mata sam, soyyar shan minti bata cikin tsarin shi, bar shi dai da iya yiwa mace kallon qurillah in abokanshi sunyi masa qorafin kan hakan sai yace abarshi ya tantance d'iri, sura, siga tare da class d'inta sabida anan zai gano wacce zai bawa kyautar ruhinshi.

**cikin sati d'aya da bayanawa junarsu sirrin zuciyoyinsu, sukayi wani mugun shaqu na ban mamaki, basa gajiya da hira duk in haydar yana gida haka in yatafi office suna maqale da waya ana zubawa juna kala man soyayya.

Abin da yayi mugun bawa Hameed mamaki, ai ko ya hana Haydar saqat da tsokana ya kance "sumumu kasau ashe munafunci ne da kai haka, da kayi ta wani noqewa kamar sufi nan ko majnun ne.
Aduk sanda yaji haka sai dai ya bishi da murmushi kawai bai iya ce mishi komi.

Lokacin tafiyar su Hindu yana zuwa suka yi bankwana da dangi suka tafi tare da Addawiyya da khairi sabida rainon su twins.

Hajiya karima taqaraci jarabarta ta haqura.

Haydar duk sai yaji kamar yabisu, badan aikin office yayi mishi yawaba ba tabbas da dashi za'ayi tafiyar.

Kewa tayi mugun daminshi duk sai yadawo shiru2 kamar yarda yake ada can, jin dad'in shi 1 shine kullum dare sai sunyi video call da juna.
Yayi tazuba mata shagwaba tana biye mishi.

Lokacin aikin Hajja yana zuwa su Abbie suka tashi atare dukkansu, acan suka had'u dasu Addawiyya wa d'anga qasa mai tsarki ta amshesu suka saje da larabawa.

Duk inda Addawiyya tayi idanun Salma na kanta har ta tsargu ta matso jikinta ta kwantar da kanta akafad'arta tace "Adda mai tulelen ciki na sanza miki ne halan?
Duka ta faska mata a cinya ta zabura taja baya tana tura baki "Allah kinci albarkacin takwaran ummi dake cikinki da sai na rama ko mi za'ayi.

"'Yar buhu zokirama mana "uhmm nidai fad'amin mi jikina yayi kike tabina da kallo kamar wata mayya.

"Ohk kinrama ke nan ko? Dariya tayi ta amsa "eh'man ban mantaba ai har yanzu
"to yayi miki kyau, matso kiji abinda nagani atare da ke.

Matsowa tayi ta kanga kunninta daf da bakin Salma.
"Addawiy wallahi kin qara girma, haske, wayewa sannan uwa uba komi najikinki yaciko kin zama big lady mai kayan alatu ainun, anya kuwa Haydar zai ganeki in kuka had'u?

Da gudu tafice daga d'akin tana cewa "Allahumma yahadiki Adda Salma. Dariya duka d'akin su kasa, Hindu tace "bakwa gajiya da shiririta duk in kun had'u da juna ko Salma? "Aunty wasan saqo da saqo kenan ai.

Haqiqanin gaskiya Addawiyya tayi mugun sanzawa, duk alamun cikan 'yan matanci sun bayyana gareta, har abin sai da yabama Hindu tsoro ta tsareta sai ta fad'a mata abinda take sha da boobs d'inta tare da ships d'inta suka koma haka, sai da tayi ta rantsewa sannan ta yarda, kuma khairi ta tabbar mata da ba abinda takesha tunda duk inda zasuje tare suke zuwa, sai tabar abin alokacin zuwansu ne yayi, haka itama khairi ta cika ba laifi don tafi yarda tazo.

Cike da nasara suka kammala aikin hajjinsu suka nufo gida Nigeria cike da d'okin ganin dangi.

Addawiyya kam d'okin ganin bubby nta takeyi kawai, ji take kamar tayi tsuntsu ta ganta gabanshi.

Jirginsu ya sauka lafiya, duk abinda za'a anyi angama suka d'auko kayansu suka fito inda su Haydar suke jiransu.

Abin mamaki Addawiyya takasa kallon inda Haydar yake sam, kuma koda akazo tafiya sai shiga motar ubaiyu amai makon tashiga na Haydar, suka nufi gidan Abbie.

Haydar kamar zai kwalla ihu awurin amma sai yayi ta maza ya daure yashiga motarshi yaja suka tafi gidan amma inransa yayi ya baci.

*mrs j moon*
[1/18, 10:24 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

*34*

Kwance take cikin bedroom d'in Ummi ta rufe jikinta har zuwa samar kanta da qaton bargo amma duk da haka sai rawan sanyi takeyi.
A qalla ta d'auki mintoci 20 sannan tasoma zufa alamar zazzabin dake damunta zai sauka.

K'ara gyara blanket d'in tayi tare da jan siririyar tsaki ta furta "duk da ban kyauta mishi ba ai tunda na kira phone d'insa sai ya d'auka yaji uzirina ba wai yayi watsi da niba, takuma jan wani tsakin cike da d'acin zuciya.

Wani sarawa taji gefen kanta yayi mata ta dafe wurin tana matsan kwalla.
"Wai dama haka fushin masoyi yake? Ta tambayi kanta afili.

Lallai in haka abin yake masoya suna shan azaba, "wash ni Addawiyya, Allah kakawomin mafita, ka karkatomin da hankali ya Ali ya bar fushi nan ko nasami sa'ida a ruhina.

Kimanin kwanaki uku kenan da dawowarsu amma ko sau d'aya Haydar baizo gidansu ba kuma bai kirata a waya ba ita ce ta kirashi ranar da suka kwana biyu da dawowa yaqi d'agawa abinda yayi mugun bata mata rai har ya haifar mata da zazzabi mai zafi kuma tunda lokacin bata sake kiranshi ba duk da muradin son jin muryanshi da takeyi kamar me.

Sai bayan azuhur ta falka saboda barci da ya kwasheta bata sani, da hanzari ta shige bathroom, tana fitowa ta shimfid'a sallaya ta hau, bayan ta idar ta miqe ta shafa lotion ta zura wata doguwar riga roba mai d'auke da qananar stones golden ta yane kanta da qaramin gyale shima golden tafito parlor.

Gyefen ummi ta zauna a kasalance tace "Ummi barka da war haka, nabarki da aiki ko?
Cike da kulawa ta amsa "Alhamdulillahi auta, yajikin naki, kin warware ko dai nakira miki Salma ko Hameed wani yazo ya dubaki?

"A'a na warke, kasala ce kawai taragenmin yanzu kuma itama zata bari.
"Tam Allah yaqara lafiya "Amin.
"Ga abinci can a dining kije kici zakiji qarfin jikin, "ohk tam ummina.

Tura abincin takeyi kawai kamar tana cin magana sabida gaba d'aya zuciyarta taqi yi mata dad'i ga bakinta ba d'and'ano sam.

Tana gamawa ta gyara wurin ta dawo ta zauna ta bud'e data,, wata qila zatasami abin d'ebe mata kewa.

Ganin Maryam a online yasa ta tura mata saqo.
'''Ki turomin document d'in Babban goro (khadeeja candy) da cigaban Gidan k'unci (bebeelo) da kuma document d'in Wata uwar (Haemeebrah) ke da dai novels masu dad'i.
Yana shiga ta duba Haydar taga yana online, kamar zatayi mishi magana kuma sai ta fasa ta wank had'e fuska tana hararan wayarta kamar shine agabanta.
Tana shirin sauka taga ya turo mata da massage da sauri ta duba *malamansu kicire photo nan dake dpnki now* quri tayiwa gajeren saqon kamar wacce ta warke makanta cikin tura baki ta shiga setting tayi remove ta sauka da sauri batare da ta duba massage d'in maryam da taga ya shigo.

Haydar ganin ta sauka yaja tsuka. "Wato tafi qarfin ta amsamin kenan? Uhmm to ko sabon saurayi tayi balarabe, shi yasa tasomamin wulaqanci irin tasu na mata? Wani shashi na zuciyar shi ya amsa mishi "kaima baka kyauta mata ba Ali, komi tayi maka ai ka nemeta ka saurari uzurinta ba wai kayi ta fushi da babu gaira babu daliliba.

"Yesss!!!! Ya amsa da qarfi ya miqe ya zari key d'in motarshi yafice har yana had'awa da gudu.

A parking lot ya had'u da Hameed yace "ya haydar sai ina zuwa haka kuma? "Inda ka aike ni, ya masa mishi bai kuma jira cewar shiba ya shige motarshi ya fizgeta da qarfi, get man ya wangale mishi get ya fice.

"Allah yayi maka sauqi kai kam, Hameed ya furta cikin tabe baki.

Tana kwance a bisa cushion, suna hira da Ummi ta tsinkayi sallamarsa, Ummi ce ta amsa mishi ya shigo a natse ya russuna ya gaida ummi ta amsa cikin fara'a tare da miqewa ta bar parlor n.

Kallon kallo sukayiwa juna sai taga yarame mata amma yayi mata kyau sosai.

Shima kallo daya yagano ta rame sai dai yana cike da mamakin girma da cikan da tayi wanda sam bai lura da suba sanda suka had'u airport.
Itace ta soma janye idanunta, cike da yanga ta motsa lips d'in tace "ina yini, ya office?

Bai amsa mata ba illah idanu ya kuma bud'ewa yana qare mata kallo, kamar yau yasoma ganinta.

Wani matsanancin kunya ne ya kawo mata jiyara domin ta tuna rigan jikinta ta kamata tsantsan gyalenta bai rufe mata komi ba.

Cikin shagwababbiyar murya tace "please ya Ali d'an jirani a sitting room.
Ko motsi baiyi ba balle ta saran zai tashi.
Tashi tayi ta haya upstairs cikin sarsarfa don ta sanyo hijab.

Murmushi ya saki mai sauti yana mai furta "komi naki mai kyau da burgewa ne Rabi'atu,ya Allah ka mallakamin ita da sauri.

*sleep*πŸ˜΄πŸ€¦πŸ»β€β™€

*mrs j moon*
[1/19, 11:10 AM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

*35*

Koda ta sauko tuni yabar parlor n, wani sanyi takeji yana sauka mata cikin heart ta runtse idanunta ta daka tsalle ta soma rawa tana d'iban shaky tana juyi cike da nishad'i tana waqan soyyaya soyayya.

Sautin dariyan Ummi taji abayanta yasa tayi saurin dakatawa da rawar ta juyo cike dajin kunya sai kuma ta diba da dugu zata fice.

"Auta zo ki tafi mishi da wani abu mana, juyowa tayi kanta aqasa ta shige kitchen, tana jera drinks tare da snacks tajiyo ummi na fad'in "uhmm auta dai da qarfi da yaji taqi yaron nan ubaiyu, to Allah yasa haka shine mafi Alkhairi.

Can qasan maqoshi ta amsa da "Amin sai kuma ta rufe fuskanta wai taji kunya, haka ta fito kanta a qasa taqi kallon inda Ummi take, rankwashi Ummin ta kai mata tana mai cewa "kunyar qarya ba, bacin yanzu kika gama cashewarki har da d'iban shaky.

Da sauri tafice tana dariya mai sauti, itama ummin dariyan tasa ta furta "auta hoo ita dai abinjin kunya bayayi mata wuya sam.

'Dauke da sallama ta shiga sitting room d'in, ya amsa mata can qasa, ta qaraso ta d'ora tire d'in bisa table ta tsiyaya mishi lemon mango with apple data had'a da hannunta, ta miqa mishi mai makon ya amsa sai ya damqe hannunta yana son su had'a idanu ita kuma ganin haka ta qara soke kanta qasa murmushi ya saki mai sauti yace "kinsan Allah idan har baki d'ago kin kalleni ba sai dai mu kwana ahaka.

Taqi motsawa ya matse hannunta da qarfi ta ritse idanu, jus d'in dake hannunta yasoma zubeqa sabida rawar da hannunta yasomayi.
miqa hannun nata yayi zuwa bakinshi ya kafa kai yana tsotsan jus d'in eyes d'insa bisa kanta, tana jinsa duk abinda yakeyi amma taqi d'ago kanta ta kalleshi.

Sai da ya shanye tas sannan ya saketa ya koma ya lafe cikin cushin yana tsotsan labbanshi cike da nishad'i yace "oya hajiya Rabi'atu sami wuri ki zauna haka nan kada qafafunki yayi tsami, miqewa tayi ta zauna nesa dashi kanta qasa tanayin wasa da ya tsun hannunta.

"Uhmm sarkin jin kunya sai kisaki jikinki hakan ko maji dad'in yin hiran yaushe gamo duk da nasan yanzu batani kikeyi ba kinsami kyakykyawan d'an balarabe tuni ya sace miki zuciya.

Da sauri ta d'ago idanu waje tace "inji wa? "Inji ki.
Ta langabe kai cike da marairaita tace "kai ya Ali yaushe mukayi haka da kai? Shima langabe kan yayi ya amsa "ranar da kuka dawo daga saudi a airport kika tabbatarmin da bana gabanki sam yanzu.

"Uhmm ya Haydar kenan baka rabo da zolaya.
"Allah ba zolayanki nakeyi ba pretty, kece da kanki kika nunawa duniya bakya yayina tunda ko darajan kallon arziki samuba ba daga gareki, ya qarasa zance cikin dacin rai.

Tuni idanunta ya kawo ruwa ta dawo gabanshi ta zauna ta soma magana "wallahi Allah ya Ali ba abinda kake tuna akai shine ba, kawai kunyar yima magana naji agaban su Abbie amma sosai ranar naji dad'in ganinka.

Ya amsa adaqile "Uhm naji, kallonshi tayi sosai tace "don Allah kayarda dani ba wanda ya sace maka heart d'inna, wallahi taka ce har abada bata taba son waniba sai kai kuma bazata qara son waniba bayan kai, kayafe min dan girman Allah kaji my life.

Murmushi ya kufce mishi ba shiri ya jinjina kai ya amsa "komi ya wuce sweetie.
"Aha thank you habibi.

Sosai suka sha hiransu ta masoya kamar wani abu bai taba faruwaba.

Suna tsaka da hira Addawiyya ta had'e rai tayi shiru, jikinsa yana bari yasoma magana "beauty mi nayi kuma? Sai da taja lokaci sannan tace cikin shagwaba "jiya nakiraka kaqi d"auka, kasa zazzabi ya kamani ya wahalar dani nakasa hassala komi nayi ta kuka har hawayena ya kusa d'aukewa.

Dariya yasaki mai sauti tabishi da kallo cike da so da qauna, ya kanne mata ido d'aya yace "ramawa nayi, kuma Alhamdulillah kinji abinda naji dafatan nan gaba zaki kiyaye yimin hakan.

Cike da mamaki ta jefa mishi tambaya "da gaske wai kayi kuka da hawaye kaima? "Yes, ya wuce wai hakik'a nayi kukan zucci wanda yafina na zahiri zafi da rad'ad'i,kad'an yarage heart d'ina bata tasami attack ba.

Zamewa tayi bisa gwaiwoyinta muryanta na rawa tace "don girman Allah da manzonsa ka yafemin bansan zaka fad'a mawuyacin hali haka ba da tuni nayakice kunyar gefe na kula ka.

Shima zubewa yayi gabanta yace "hakan yayimin dad'i sannan qimarki ta qaru sosai ya ruhina, lallai ina alfahari da samun mace mai kunya da kawaici tare da hangen nesa irinki, azancinki yana qaramin jin sonki har namanta da kaina.

Miqewa tayi ta koma mazauninta tana murmushi mai cike da kunya wanda yin hakan yariga yazama d'abi'arta.

Sai da Abbie ya dawo suka gaisa sannan ya wuce gida cike da annashuwa.

A parlor ya zauna dirshen bisa carpet ya zuge zip d'in d'an madai daicin akwatin data bashi sanda zai wuto tace tsarabarshi ne ciki.

Kayan barci ne masu laushi sai vests d boxes masu kyau da wasu littafan addu,o'i sai wata qaramar leda mai kyalli ya bud'eta ya fiddo wani box ya bud'e agogone mai uban tsada tare da zobben azurfa mai kyau, cike da jin dad'i ya zura zobben a yatsrshi nagefen qaramar ya tsarshi yayi mishi cif kamar angwada shi, subba ya kaiwa yatsar ya lumshe idanunsa ya furta "i really love you my angel.

"Uhmm soyayya ruwan zuma, in ansha aba masoyi oooo.
Bud'e idanunsa yayi da sauri ya watsama Hameed harara, yako sheqe da dariya har na buga qafa sai kuma ya matso ya soma duba kayan tare da cire night wear biyu vest da boxer bibiyu ya kwasa ya nufi room d'insa yana waqar "shi zumunci yana qarfafa son 'yan uwa.

Murmushi Haydar yayi tare da tattare sauran kayan ya nufi room d'inshi da su, yana shiga ya hango phone d'insa yana haske koda ya duba yaga Addawiyya ce ta kirashi har 3 miss call da hanzari yayi back call yanajin yasoma ringing yahaye bed d'insa yakwanta hanunshi d'aya cikin sumarsa.

***** Addawiyya tasoma karatunta na pharmercy a BUK duk medicine taso sai suka bata parmacy yayin da Maryam kuma suka bata medicine amai makon choice d'in na pharmacy, ita kuma khairi abinda tanema shi suka bata wato mass communication.

Sosai suka maida hankali akaratunsu amma fa Addawiyya tafi son medicine aranta don haka kullum Haydar yazo sai tayi mishi qorafi ita fa yasan yarda zaiyi a maidata medicine burinta ya cika inyaso sai maryam ta koma pharmacy d'in.

Yauma da yazo da shi tasoma yi masa maraba, ganin yaqi ce mata komi ta soma kukan shagwaba har da hawaye, baice mata kanzil ba har tagaji tayi shiru baki a ture.
Jan bakin yayi tayi sauri gyarashi yayi qasa da murya yace "Addawiyya ki zamo mai godiya ga Allah akan dukkanin abinda yazamo qaddaranki, ki amshi wannan qaddara tako da hannu bibiyu kicigaba da neman zabin Allah tare da nasaranshi sannan ina roqonki daki maidahankali sosai akan karatunki kada kiga ba choice d'inki bane shi ki soma shiririta, dafatan daga yau zakibar qorafi akai.

"Insha Allahu bazan kuma ba sannan nayi maka alqawarin dagewa sosai abisa karatuna.

"That's good my heart.
Idanu ta kad'amishi face d'inta d'auke da murmushi, tayi ihu kad'an ya kwanta baya tare da dafe qirjinsa ya furta "washhh!! Mashin so ya sokeni a ruhi, wannan irin fari ai sai a d'au gawata yanzu.
Dariya tasa tana mai kulle idanunta da tafukan hannayenta.

******* 11:00am at school.
Addawiyya, maryam tare da khairi suna zaune a wurin love garden suna ta hirasu na qawaye cike da nishad'i.

Qamshi turarenshi taji ya doso wurin sai kuma iska mai qarfi ta tashi agefenta tabi wurin da kallo uncle habibullah ne ya baiya a zaune bisa kujeranshi mai d'aukan idanu.

Addawiyya ta juya ta kalli su maryam taga sai hiransu suke tayi da alama basu ganshi ba.

"Mai babban suna tashi ki matsa wurin bishiyar mango d'incan magana nazo miki da ita mai mahinmanci.
Batare da tayi magana ta miqe ta nufi wurin mango tree d'in yayin data ga su maryam sun juya musu baya suna ta hiransu basu ko lura da tashinta a wurin ba.

"Mai babban suna aurenki yazo, za'ayishi nan da kusa kwanaki arba'in masu zuwa, to abinda nakeso dake shine da zarar magabatanki sunzo miki da zancen ki amince batare da gardama ba domin baki san me Allah ya boye ciki ba kamar yarda nima ban san komi akai ba, dafatan kin fahimceni da kyau.

Muryamta na rawa tace "a'a uncle nakasa gane inda zancenka ya dosa, wai kana nufim ni Addawiyya autan Ummi zanyi aure ciki qanqanin lokacin nan? "Eh mai babba suna. Idanu waje tace "to waye miji nawa "Aliyun kine "uhmm uncle ya Ali fa ya tabbatarmin sai na kammala karatuna har zuwa sanda zan gama service sannan zamuyi aure.
"Inkinje gida kinji zancena ya tabbata sai mucigaba da magama, bye sai nazo tayaki hira abarcinki yau.
Kokafin tayi magana ya bace bat.

Jikinta ba inda baya rawa, ta qaraso wurin su maryam ta d'auki purse tare phone d'inta tayi gaba batare data ce dasu qalaba.

*mrs j moon*
[1/20, 4:40 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*
NA
SAFIYYA.

*36*

Ko kafin su maryam su iso inda take tamuza key ta fizga motar da gudu ta ta nufi get d'in fita.

Khairi tuni ta hassala tasoma fad'a, "ai wannan iskancin banzane tana ganinmu amma takasa tsayawa jiba yarda mutane ke kallonmu suna dariya.
Maryam da dubi mutanen ta tabe baki ta dafa kafad'an khairi cikin sigan rarrashi tace "Uhmm share kawai sis basa da aikin yine zo mukoma inda muka taso kafin nan da 25 minutes yaqarasa na shiga lecture.

Bata ce da ita komiba suka juya. Saida suka zauna tace "Maryam mi kika sani agame ta ficewar addawiyya cikin fushi?

"Wallahi bansan komiba khairi.
"Ok, let me call her muji. Tace tare dasoma dialing number ta.

Addawiyya kam driving takeyi kamar zata tashi sama, ikon Allah kawai yakawota gida lafiya.
Tana shiga harabar gidan taci karo da motoci gabanta yana bugawa ta sami gefen bishiyar umbrella tayi parking ta kife kanta bisa Stereo ta rasa meke mata dad'i.

Kiran khairi ya kuma shigowa tana kallo har ta tsinke batayi picking ba.
Kira na biyar kenan tayi mata tana kallo har ya tsinke amma taqi d'auka.

Khairi ta dubi maryam hankalinta atashe tace "bara na bita inajin ko lafiya.
"Ohk, ni inna fito class zan biyo inji mike faruwa"tam sai kinzo, ta qarasa parking lot taja motarta ta fice tana zancen zuci.

Jin maganganun su Abbie yasa ta d'ago tana hangensu daga inda take, Abbie, Abban su ubaiyu, Abban su Hameed tare da wani dattijo mai kama da Haydar sosai ta hango faces dinsu d'auke da fara'a, jikin wata mota babba suka tsaya zuwa can sai ga Hajja, Ummie tare da umman su ubaiyu sunyo mata rakiya.
Tana isowa suka shiga mota suka wuce Abbie da Abban su ubaiyu sukayi ciki tare da su Ummie.

Hakanan sai taji jikkinta yayi mugun sanyi, tasaka fitowa saima ta kuma gyara kwanciya a seat d'in data kwantar baya ta lumshe idanunta kamar mai barci nan kuwa tunanine ya baibayeta kuma tarasa wanne zata kama ciki.

Qaran bud'e get dataji yasa ta bud'e idanunta wanda suka koma red color.
Kusa da ita khairi ta parker motarta, bayan ta kulle ta fito tanufi ciki batare da ta lura da Addawiyya.

'Dan tsaki taja sanda taga su Ummie sunfito suna dube dube, tasan sarai ita suke nema donmin tasan khairi ta riga da ta kai gulma.

Kafin su qaraso wurinta ta fito tanayin murmushin yaqe, aqoqarinta na ganin ta boye halin da take ciki.

Umma ce ta kamo hannunta cike da kulawa tace "Ayya Rabi'atu mike faruwa kika boye kanki cikin mota alhalin kin jima da shigowa gidan?

Sai da ta saita muryanta sannan ta amsa "kaina yakemin ciwo ga kuma kasala yana damuna shine na zauna ciki amma yanzu dama zan shigo.

"Ayya sannu, Allah yaqara lafiya.
"Amin umma.
Juyawa tayi ta kalli inda ummi take tsaye ta zuba musu idannu, da aurin ta d'auke kanta sakamakon kallon tuhuma dataga ummin tana binta da shi.
Jan hannunta umma tayi suka nufi ciki, khairi ta matso daf da kunninta tace "madam Haydar mushiga ciki ki fad'a misu abinda kika boye mana amatsayinmu na qawayenki.

Harara ta wulla mata, itama hararan nata tayi ta kuma bud'e murya tace "dole dai kifad'a musu duk boye boyenki ehe.

Abinci umma ta matsa mata taci sannan ta bata magani tasha, ta umurceta data tafi ta kwanta, intasami barci zataji tadawo normal.

Koda ta shiga room d'in mai makon ta kwanta sai kawai tashige bathroom ta sakarwa kanta shower.

Bata jimaba ta fito ta tadda khairi zaune bakin bed tana aikin yi mata bincike a cikin phone, ko kulata batayiba ta qarasa gaban mirror tayi 'yan shafeshafenta ta sanya inner wear tare da zira english wear na riga da sket masu santsi ta tako asannu ta haye bed ta ja blanket ta rufa ruf har zuwa face d'inta.

Da hanzari khairi ta janye blanket d'in tayi jifa da shi gefe.
A fusace ta tashi zaune tana doka mata harara tace "wani salon iskanci kenan haka khairi? "Salon iskancin da kika koyamin ne.
Kallonta tayi na daqiqa ta girgiza kai tare da komawa ta kwanta tana mai dafe goshinta da left hand d'in.

"Malama tashi zakiyi ki sanar da ni abinda ke damunki ba wai kiyi ta cin magani ba.

"Wai ina ruwanki da lamari nane da kikabi kika takurawa kanki dole sai kinji matsalata?

"Au haka kikace? Tam yayi kyau haka kuma nagode, tamiqe cikin fushi har ta kama handle zata murd'a Addawiyya tace "am sorry qawata dawo kiji matsalata, ko juyowa batayi ba tayi ficewarta cike da fushi.
tabe bakinta Addawiyya tayi tana mai cewa "jikin ya motsa kkenan? sarakan fushin sun matso kusa, to Allah ya saukeku lafiya.

"Mikike cewa? Dariya ta saka ta amsa "abinda iska yakawo miki, wato labe kika koma ko? "Bansani ba, nidai Abbie yace kizo, dafe qirji tayi idanu waje tace "wayace kice mishi idanuna biyu? "Au qarya kike nufin zanyi mishi ko mi? "Bamsani ba dalla magananyi kawai, ta furta cike da jin haushi.

Dariya khairi tasa mata sosai tace eh, din nadai ji alamaun ilimi kenan. "Uhmm ni kirabi danj tam.
"To momy sai kisami da tashi ko nakoma nasanar dashi kince sai yazo da kamshi don dama ina fita naci karo dashi zaizo kiranki da kanshi shine nace bara na kira mishi ke.

"To kin kyauta ai, sai kibani hanya in wuce, duk kinbi kin isheni da uban surutu kamar parrot.
Gwalo tayi mata takoyo kanta da sauri ta kwasa da gudu tayi downstairs ta rufa mata baya.

**** Hajja bakya ganin in akayi haka ba'a tauye mata hakki taba?
"Aliyu kasani yin haka shine zai baka damar sanin lafiyarka sannan shi aure, haihuwa, mutuwa tare da k'addara duk in lokacinsu yayi bawanda ya isa ya tsaidasu sai ikon Allah.
"Haka ne Hajja, amma dai ina duba alkawarin danayi mata ne nacewa sai ta kammala karatunta har tasoma aiki sannan zamuyi aure.

"Uhmm Ali ka kwantar da hankalinka ka natsu ka ajiye wannan zancen agefe, ka d'auka cewa haka Allah ya tsara baza ta kammala ba zakuyi aure.

Nisawa yayi ya amsa "tam Hajja Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi "Amin Amin Ali gadanga qusar yaqi, murmusawa yayi tare da miqewa yafice.

Cike da jin tausayi Hajja tabi bayamshi da kallo ta d'aga hannunta sama tace "Allah kabawa bayanka Aliyu lafiya alfarmar manzon rahama.

**** Cikin parlon Abbie Addawiyya ce zaune ta lankwashe qafafunta kanta duqe a qasa, ta daiyi zama irin ta ladabi.

Sai da Abbie ya dubi gefensa inda ummie take zaune ya sauke ajiyar zuciya ahankali sannan ya soma da cewa "Alhamdulillahi ala kulli halin, yayi jim zuwa can yace "Rabi'atul Addawiyya, tad'ago kanta da hanzari tayi tana dubanshi, yayimata murmushi ta koma da kanta qasa ta amsa "Na'am Abbie.

"Rabi'a ya kuma kiranta akaro nabiyu,, ina mai baki haquri abisa katse miki cikan burinki da zanyi dafatan zaki gafar ceni?

Muryan na rawa ta amsa "Abbie tsakanin iyaye da abin ikonsu wato 'ya'yansu, babu abinda zasuyi musu indai bai sabawa shari'aba ace zasu tsaya roqonsu gafara, don haka bakayimin komiba kuma baza kataba yimin shi ba sabida nasan kai d'in uba nagari ne mai hangen nesa kafin ya aywatar da komi.

Tana rufe baki suka had'a baki wurin cewa "Allah yayi miki albarka har izuwa qarshen rayuwar.
"Amin ta amsa fuskanta yana mai nunajin dad'in addu'ar.

"Rabi'a bakomi bane illah d'azun na amshi sadakin aurenki da Aliyu wurin su Alh. Muktar sannan har mun tsaida lokacin biki nan da sati biyar masu zuwa, dafatan baza ki bani kunya ba.

Ahankali ta amsa "insha Allahu zaka sameni mai ladabi da biyayya a lamarin zamantakewar aurena.
Sai kuma tamiqe tafuce da gudu don sosai maganar ya jefata cikin jin kunyar su Ummie.

"Auta hoo, jibafa kunya wai taji, ya amsa "hakan shi yanuna tana maraba da lamarin kena, "eh, malam dama ai nace maka bazata qiba sabida tana sonshi sosai, "to Allah ya barsu tare da karesu cikin amincin Allah "Amin.

Koda ta shiga room d'inta khairi da maryam tasamu suna cin food, suna ganinta suka sa shewa ta had'e rai ta zauna suka kuma sakin dariya maryam tace "munji komi abakin Adda Salma ai.
"Adda Salama fa kuka ce? "Eh ita "to yaushe tazo gidan?
"Inanan tun bitarki zuwa school baji mawa, don haka agabana akayi komi Abbie ya kyautarwa Haydar dake.

"Malamandu gyara zancenki akadai neman mishj aurena.

Yeeeee!! Tafad'i da bakinta, su Amaren Ali kenan manya, maryam tace.
Ficewa tayi da gudu tana cewa "magul matan banza kawai sai kuyi da wata ai ba ina ba.

Tana jiyo dariyan dasuke kyalkyalawa tashige kitchen ta fice zuwa garden tasami wuri ta zauna ta kulle eyes d'inta tace "Haydar yana tare da lalura ko ta miye?
Saukam Iska taji agefenta ba tare da ta bud'e idanunta ba tace "sanar dani lamarin uncle.
"Kasheki zanyi yanzu kowa ya huta.
Wata murya mai bantsoro ta amsa mata.

*mrs j moon*
[1/22, 3:47 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

*37*

Arazane ta kai dubanta inda sautin voice d'in yafito, wani zabura tayi sakamakon yin arba da wani halitta da tayi shi ba mutum ba bakuma dodo ba, yana d'auke da fuskan mutane kanshi na rago jikinsa na jaki har da bindi dogo qafafunshi na mutace.

Bud'e baki tayi zata kwalla qara raji an hannu ya kulle mata baki tare daijn shigar wani sanyi cikin qirjinta, cikin second tasami kanta cikin jarumta na rashin jin tsoro.

Komawa tayi ta zauna ta had'e fuska cikin kaurin voice kamar banata ba ta dubi halittan tace "to bissmillah, gani kamiqani barzahu, tunda kai ka halicceni.

Wani zaro idanunshi halittan yayi cike da kid'ima sabida yazaci firgicin ganinshi zaisa ta suma yarda zaiji dad'in sheqawa da ita qiyoma.

"Kana batamin lokaci fa, kallonta ya kumayi sosai, atake yagano wani baqon lamari cikin idanunta, yasoma ja baya tana biyoshi bakita na motsi alamar addu'a takeyi.
Ganin burinta ta damqeshi da hannunta yasa yayi girgiza ya zama qaton shaho ya bud'e fuka fukanshi yayi sama.

Abin mamaki sai da tabari ya lula sosai sannan ta bud'e bakinta ta hura iska sama atake shahon ya fad'o tim, ya saki razananniyar qara, yaja baya ya kuma girgiza ya koma kura yayo kanta kamar walqiya ta bace bat zuwa can wani qosasshen zaki ya bayya, yayi kan kurannan suka soma fafatawa wani baqin hayaqi ya rufesu ruf, tsowon lokaci suna abu d'aya zuwa can farin haske ya bayyana.

Habibullah ne zaune bisa chair d'insa mai ruwan gold fuskansa kamar dare don rashin walwala.
Ya dubi kuran da take yashe aqasa bakinta da hancinta sai zuban jini yake, yasa qafa ya shureta tayi wani sama sama sannan ta fad'o tim iska ya tashi ya rufeta, koda ya baje saiga wata mata baqa qirin fuskanta kamar na gorilla, zubewa tayi gaban Habibullah tana yin wani yare kamar na 'yan China.

Wani tsawa ya daka mata ta zabura ta koma wata budurwa mai mugun kyau.
Kallon sosai yayi mata yace "waya aikoki wurin kayana? "Kayimin rai ya kai adalin shugaba.
"Tambayarki nayi, kuma amsa nakeso ba ban haquriba.
"Matar Aliyu ce, wani Aliyun? "Wanda zai auri jaririyanka Addawiyya.
"Uban wa ya d'aura musu aure?
Shiru tayi ya kuma tambayarta saitayi qasa dakanta, taqi cewa komi.

Shiru yayi kamar bazai kuma magana ba zuwa can yace "tashi ki tafi amma inamai gardad'inki kada ki kuma zuwa domin cutar da mai babban suna.

Zubewa tayi gabanshi tana godiya, d'agamata hannu yayi atake ta bace bat.

Kallon wata bishiyar itaciyar tumfafiya yayi saiga Addawiyya ta bayyana sai zare idanu takeyi.
Dariyansa taji agefenta yasa ta juyo ta kama hannunshi bakinta na rawa tace "uncle naga abin tsoro yanzu anan wurin har yana cewa yazo kashe ni ne, don Allah sanar dani mike faruwa.

"Mai babban suna, hakiqa rayuwarki tana gamuwa da ababen ban al'ajabi, don haka nakeso ki dage da yawan ibada da tsayuwar dare tun daga yanzu har izuwa gidan mijinki.
"Tam uncle zan dage dayinsa daga yau in Allah yaso.
"Madallah, yanzu shiga ciki.
"A'a uncle sanar dani labarin wannan halittan dana gani da kuma matsalar Ya Ali danaji d'azun a parlon Abbie kacemin na amince dashi shid'in mai raunine domin lafiya bata isheshi ba.

"Mai babban suna tabbas Aliyu baya da qoshin lafiya sosai, ada bansan miye matsalarba sabida hijabi da abin yake dashi amma bayyanar wannan halitta agareki nagano komi don haka kibar sonjin komiyeshi, ki dai zamo mai yawar addu'a Allah yana tare da mai yawan miqa lamuransa gareshi.

"Idanu ta zuba mishi taqi cewa komi.
Iska ya hura mata, lumshe idanu tayi tare da jan ajiyar zuciya tace "shikenan uncle nabar sake matsa maka akan sai naji ko miye amma don Allah kasanar dani waye wannan halittan?

"Baiwace ta wata basarakiya, anturo tane domin ta cutar dake abisa dalilin banza da wofi na sarauniyar, atunaninta nayi nisa dake sabida taji nace zanyi tafiya to shine ta turo a kasheki sai gashi Allah ya kareki.

"Uncle miye had'inta dani? "Kaddaran maganar aurenki ya had'aku.
"Kamar ya? "Kamar yar yawan bincike baya da kyau sam.

"Uhmm Uncle wallahi ban fahimce kaba.

"Dama bana son ki fahimceni yanzu sai nan gaba.
Zata kuma magana ya rigata "tafi ki shirya tarban zuwan masoyin Haydar.
Yana fad'an haka ya zama haske ya bace.

Barin wurin tayi jikinta duk yayi sanyi.

Adaren ranar Haydar yakawo mata ziyara.
Cikin parlor suka zauna yayin dasu ummie sukabar musu wurin.

Haydar yasha mamaki jin batayi masa qorafin ya daqile mata karatu ba sam, shi kuma baitada zancen ba.

Bai bar gidansuba sai bayan ten na dare.

Daren ranar Addawiyya bata rintsaba sai bayan da ta sallaci subahi.
Anan bisa sallaya ta bingire barci mai dad'i ya kwasheta.

Hiran soyayya sukeyi cike da nishad'i wanda ya shagalar dasu suka manta inda suke.
Qaran zuwar wata ququwa ce ta dawo dasu hankalinsu.
Guguwar na zuwa tayi sama da Haydar ganin haka Addawiyya ta bishi zuwa saman, haka suke gudu cikin girgije, guguwar tana qoqarin tsere mata ita kuma tana qoqarin kamota ta kwace Haydar wanda tuni iska yayi mishi yawa har ya suma, cikin ikon Allah Addawiyya ta cukume guguwar bakinta d'auke da ayatul kursiyyu.
Atare sukayo qasa koda suka sauko sai wata budurwa fara sol mai kyau ainun ta bayya ta nuna Addawiyya da yatsa "wallahi sai kin barmin mijina ko ta halin qaqa ne, wato in raini abina tun yana tsumman goyo sannan tun da naga yafara gima na fidda mishi sha'awar ko wacce mace aranshi, shine ke cikin lokaci qanqani zaki aureminshi duk kuwa da adalcin danayi miki na barin zuciyarshi ta soki, to narantse da karagar mulkin Abbuna baki isaba, kinyi kad'an ki shiga tsakanina da masoyina.
tanagama fad'an haka ta bace bat.

Afirgice Addawiyya ta falka tana share sweat daya jiqa mata fuska har yana d'iga.

Kalmar innalillahi wa'inna ilaihin raji'un take ta ambaata har tasamu natsuwarta yadawo.

"Shine dama labarin da uncle yake boyemin kenan? Shine dalilin da yasa tun kafin in had'u da Ali nakejin tausayinsa? To wai ma miye hakan kenufi? Shin wannan budurwa mutum ce ko aljan?

Tambayoyin datake ta jerawa kanta kenan afili kuma tarasa samo ko amsa d'aya daga cikinsu.

Hakanan ta tashi jikinta ba kwari ta shirya ta wuce school ko break bata samu damar yiba.

Eleven dai dai tafito direct motar ta nufa, tashiga ciki ta kulle kanta ta lume cikin seat ta d'aga kanta sama tana maijin wani maqaqin d'aci a maqoshinta.

"Ya ilahil alamina badai kishi nake da wacce banda tabbaci akan zancentaba?

Baki isaba, kinyi kad'an ki rabani da masoyina.
Shine kalmar datafi tsaya mata arai.
"Ooo ni Addawiyya minyasa junnu suke bibiyata ne haka?

"Mai babban suna kiragewa kanki tunani tun kafin ciwon kai yasoma hanaki karatu.

"Uncle katai makeni man, kafad'amin amsar tambayoyina don Allah.

"To mai babban suna, mufarkin da kikayi duk yana daga cikin sharrin shaid'an don haka kiyi watsi dashi gefen sannan budurwan da kike tunani akanta itad'in d'iya ce ga sarkin aljannu mai mulki ayankin larabawa amma ina son ki sani kece zaki galaba akanta sai dai abinda zai faru ne bayan afkuwan nasaran Allah bai lamuncemin sanin shiba amma tabbas abin yana da rud'ani.

"Uhmm uncle mufarkina dai ya tabbata tunda gashi kabani labarin budurwan data ta dagulamin lissafi.

"Mai babban suna kibi abinda nace kawai kinbarshi a sharrin mufarki ne kawai.

"Tam, Nagode uncle Allah yabiyaka da Aljanna mad'aukakiya.
"Amin, Allah yabawa dukkanin musulmai masu imani daga dukkanin cikin jinsin mutum da aljan. "Amin ya rabbi.

Sosai suke ta hiransu da uncle kuma tuni ta nemi quncin da yadameta ta rasa, suna haka phone d'inta tasoma ringing, ganin sunar Haydar bayyane a bisa screen d'in ta kulle idanunta da hannayenta, wai tanajin kunyar uncle.

Musmushi yayi mai sauti ya bace, jin fitar iska ta window yasa ta d'auki wayar wacce aka kira akaro na biyu.
Cike da salon yanga tare da shagwaba ta furta "mijinaaaa.

*Mrs j moon*
[1/23, 11:50 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

*38*

Amsawa yayi cikin hanzari, jin yarda ya amsa tasa mishi dariya.
"Uhmm my angel dariya kikemin ko? Cigaba tayi da dariyan, shima dariyan yasa.

Sun d'auki fiye da 1hr suna hiran qauna, inda yayi ta tsokanarta da zancen jin kunya ita kuma tayi ta mishi shagwaba wai yabari ko tasa mishi kuka, sosai ta sashi cikin nishad'i yayi ta biyemata zuwa can sukayi sallama badon sunsoba sai don time d'in shiga lecture d'inta yayi.

Sauke phone d'in tayi bisa qirjinta ta lumshe idanu ahankali ta furta "lallai duk wanda yace zai rabani da ya Ali ya tabowa kansa transformer mai tartsatsin wuta kam.

Wani dogon tsaki akaja agefenta, ta kalli wurin da sauri, abin mamaki budurwan nan datagani cikin mufarkinta d'azun ita ce yanzu ta kuma gani azahiri zaune gefenta fuska ahad'e.

Tsakin ta maida mata da martani, tad'ora da cewa "malama ficemin a car ko yanzu in koya miki hankali.

Wani dariya mara dad'in amo budurwan tasoma, sai da tayi mai isarta sannan ta gintse fuska tace "motar banza, in kikai wasa Allah yau sai na batar dake tare da motar kuma inkince qarya cigaba damin tsiwa.

Cike da fushi Addawiyya ta d'auko kwalbar red musk ta bud'eshi ta yarfa mata afuska take ta kwalla qara ta bace, ita kuma ta koma ta kwanta tana maida numfashi tare da bin kwalbar musk d'in da kallo, asannu ake janshi har aka d'agashi sama aka fice dashi ta window.
Murmushi ta saki tana mai furta "thank you uncle.

Abu kamar wasa budurwan junnun nan ta hana Addawiyya sukuni domin duk inda take tana biye da ita, kuma duk in tasoma yi mata bara zana sai taga kwalbar musk agefenta tako d'auka da watsa mata afuska ko jiki take zata bace tana kururuwa, sanan takasa sanar da kowa lamarin.

Agefen Haydar kam, abubu sosai suka soma yi masa yawa ada dai rashin jin kuzarinsa na d'a namiji ne yake damunshi wanda yake yawan sakashi zazzabi da rashin karsashi to kuma yanzu cikin kwanakin nan harda ciwon mara yake damunshi sai ya danganta abin da dire ce tayi masa yawa jin yarda yake jin son kasan cewa da mace sosai kuma Addawiyya ce take zuwa mishi arai sai yayi ta hango surarta cikin shigar daya soma ganinta a gidansu, sannan sam halittanshi baya motsawa yanzu yakumankoma kamar na yara, abinda yakuma tada mishi da hankali kenan yayanke shawara zai je yaga doctor dai akan matsalar in kuma yaga ba'a samu nasara ba sai ya tumtubi Hajja ta soma amso mishi taimako na gargajiya. Shi yasa time to time sai yayi ta tunanin kamar ya cuci Addawiyya, anya zamansu zai yiwu kuwa?
Tambayar datake mugun d'aga mishi hankali kenan, sabida sosai yakejin mai rabashi da ita sai Allah.

Zaune suke su 3 qawayen juna cikin parlor n aunty Hindu, ko wacce hankalinta yana bisa laptop d'inta da alama browsing kowa keyi na assignment, dubi da yarda sukayi shiru bakajin komi sai sound of chewing gum d'in da khairi keta qas qara qas qas!!!! dashi.

Cike da gajiya maryam ta d'ago ta dubi khairi tace "don girman Allah sis khairi ki fidda gam d'in nan koma masami sauqin takuramun da kikayi mana da qaransa.
Fiddawa tayi ta tare da kwallawa hassan kira ya iso da gudu ta miqa mishi "kaishi cikin dustbin yaron ya amsa ya fice da gudu.

Addawiyya ta saki murmushin gefen baki taceb"su hassan sun girmafa yakamata Aunty H tayo musu qanni.
Caraf khairi ta mashe "jiranki takeyi kizo sai kuyi tare.
Wani dariya maryam tasaka har da riqe ciki tana kallan mood d'in Addawiyya wacce tayi mugun bata rai tana zabgawa khairi harara ita kuma taqi kallonta balle tasan abinda ke faruwa.

Afusace ta miqe d'auke da laptop d'inta tashige bedroom d'in Hindu, suka kuwa sake kyalkyale da dariya tare da tafawa.

Biki dai ya matso sai hidima ake tayi ta kowanni part.

Ana saura sati biyu aka kawo lefe nagani na fad'a domin babu ne kawai ba asakaba.

Addawiyya kam tarewa tayi gidan Hindu kuma duk kwakwan Haydar Hindu ta hanashi ganinta sai dai suyi waya ko su raba dare suna hira a online ananma yayi yayi da ita ta turo mishi pictures d'inta ya ganta sai ta fake dacewa wayar bata da camera alhalin tuni yagano aunty ce ta hanata, abinda ya rasa dalilin yimasa hakan.

Ana jibi d'aurin aurin Hindu ta maidata gidan Abbie.

Ummie sai kallonta takeyi kamar wata baquwa sabida gaba d'aya ta sanja mata sakamakon gyaran jikin da akayi mata, abin bana wasa bane, komawa tayi kamar fure don kyau da qamshi.
Dariya tayi tama ummie ganin yarda taketa murza idanunta tana kuma kallonta.

Haka nan suma su maryam sukayi ta yaba gyaran tare da tsokanarta. Ita kam iyakarta murmushi take tayi domin ita kanta tasan fatarta tasanja ainun.

Daren ranar ta fito wanka kenan ta tsaya gaban mirror tana qoqarin bud'e robar lotion ta tsinkayi maganarta abayanta qin juyowa tayi tacigaba da abinda ke gabanta sabida yanzu ta daina kulata komi zatace da ita tun sanda uncle yace tabar bi ta kanta kada ta maidata mahaukaciya domin ya fahimci burinta kenan sabida bata fito mata yanzu sai tana cikin mutane.

"Uhmm jaririya kina son jefa kanki awahala ko? Tacebda ita. Tayi mata shiru "zan maidake abi kwatance in har kika bari aka d'aura miki aure da abin sona. Nanma ko qala bata ce mata ba, haka tacigaba da tsoratata da kalamai masu nuni da gargad'i amma ko kalma 1 taqi tofawa.
Tana gama shirin barcinta ta soma Addu'a atake junnun ta bace tana mai jin haushin yarda take kasa yiwa Addawiyya komi duk in ta bayya gareta alhalin da mugun nufi take zuwa.

Addu'a Addawiyya tayiwa mugun riqo sannan ako da yaushe bakinta bai rabo da ambatar addu'ar da uncle ya fad'amata ta kariya daga sharrin muguntar junnu.

Yau dai aka d'aura auren RABI'ATUL ADDAWIYYA da Angonta ALIYU HAYDAR wanda dubbannin manyan mutane suka halarta halartar harda su Baffa jatau wanda yaragewa Abbie kenan cikin dangin mahaifinshi, yazo tare da 'yayan baffannisa da matarsu, yanzu babu wanda sukeso kamar yusufu wato Abbie sabida yanzu sunga babu mai arziki kamarshi duk cikin qauyensu.

Sanda aka sanya bikin Addawiyya ne ummie ta matsa mishi yaje danginshi ya sanar dasu, dakyat ta shawo kanshi ya tafi sai gashi sunzo tun ana gobe d'aurin aure.

Cikin tsanaki aka gabatar da taron biki.
Qawayen Amarya sunsha kyau sosai sai raha suke da junarsu kamar yarda dai aka san 'yan matan amare sunayi duk in taron biki ya had'asu.

Da la'asar Addawiyya ta zame jiki ta nufi garden ta zauna bisa kujeran roba.
Kallo d'aya zakayi mata kasan tana cikin rud'ani, a hankali ta bud'e baki ta furta "uncle gani, mizaka fad'amin?

"Nasiha zanyi miki da kuma ban haquri.

"Rashi ne za'amin ko mi? "Babu ko d'aya amma ita rayuwa dole sai da haquri musanman ke da kike fuskanta barazanar gimbiya zuhfa.

"To pa!! Sunarta kenan? "Eh "to wai uncle ita d'in tafi qarfinka ne dabaza karabani da ita ba?
"A'a bata isheni komai ba sai dai kisani komi na duniya yana da iyaka inkin cire ikon Allah shikad'ai ne wanzajje bawanda yasan qarshensa sai shi kad'ai. "Hak ne kam "to don haka iyakar ce bai zoba amma Allah yabani iko nayi miki katanga da ita tayarda koda tazo domin cutar dake baza ta iya yi miki komi ba "tam nagode uncle sosai.
"Bakomi mai babban suna.

"Sai kuma ina so ki kula da Ali sosai ki maidashi tamkar yaron da yake buqatar kulawa, kiyi haquri da halin dazaki riskeshi ciki, shine jarabawar rayuwar dana taba fad'a miki zai riskeku amma in kinyi haquri zai wuce kamar ba'ayiba.

"Tam uncle Allah yabamu ikon cinye jarabawar.
Ya amsa "Amin.
Zata kuma yin magana ta tsinkayi muryan khairi agefenta inda ta kai mata duka tana cewa "kefa wata kalan mutumce ayi ta nemanki arasa sai kace wacce taci eggs d'in makwarwa.

Kallon uncle tayi, ya sakar murmushi yace "itama ta kusa aure ita da d'an uwarta hameed za'asha bikinsu bada jimawa ba.

Dariya ta saki tana kallon khairi, sai kuma tamiqe tayi gaba ta juyo tace "bye, gyada mata kai yayi tare da bacewa.

Khairi ta waiga taga bataga kowa ba tace "kefa aljana ce inaga, ke da qaye kike bye.
"dake nakeyi koba ki fahimci narigaki barin wurin ba ne? "eh haka ne "yawwa yarinyata, duka ta kawo mata ta gofce tana cewa "hattara dai yarinya domin Amarya dai tsautsayi gareta, ki lallabani ko yanzu in sume miki.

"Duka takuma kawo mata tace "oya mace man man, kuma Allah haka nan zamu kaiwa ya Haydar ya more sadakinshi.

'Yar buhu kawai, banza wanda batsa yayiwa zubar 'ya'yan kanya a baki kawai.

Dariya khairi tasa sosai ta amsa "naji dai, kuma zuwa jibi kamar yanzu wata yarinya tagama zama ragowa.

Afusace takaima bakin khairi duka takauce tare da fallawa da gudu tana dariya.

Murmushi tayi ta furta "uhmm drama kenan ni Addawiyya a bed d'in aure, sai tasoma kyalkyala dariya, ahaka Hindu ta sameta ta janyo hannunta ta suka fito zuwa d'akin Abbie.
Daf dazasu shiga tace da ita "hala uncle d'inki ne yazo miki sallama yasakaki wannan dariyan kikayi tayi kamar sabuwar kamun almatsutsai?

Qince mata komi tayi har suka shige parlor n d'auke da sallama, gaban Abbansu ta kaita ta zaunar ita kuma ta dawo gefen ummie ta zauna.

Nahisa sosai Abba yayi mata sannan Abbie ya d'ora da tasa, mama tayi irin nata, ummie tayi kai hatta da Salma saida ta tsoma baki kuma sosai tayi magana mai cike da natsuwa da shiga jiki.

Addawiyya sai kuka takeyi, tanajin wani irin kewa yana shigarta.

Ana idar da sallar magrib motocin d'aukan Amarya suka soma layi wanda dukka daga abokan Ango ne suke.

Tana kuka kamar ranta zaifita mama ta sakata a cikin motar Hameed tare da babban qawarta Maryam wacce itama kukan take tayi kamar itace Amaryan.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.