Trending Hausa Novels

Yar Kwalliya Book 1 Complete Hausa Novel

Reading file:   Yar Kwalliya cmplt By ECCELLENCIY.txt

Chapter 1 of 2

WRITING BY HIS ECCELLENCIY NOVELS GROUP..

'YAR
KWALLIYA
Page 1-5
March 07, 2018
'YAR KWALLIYA ..

Bismillahirrahmanir
Rahim
.
Wannan kirki raren labarine
nayi shi dan fada karwa da
nisha dan tarwa ban yishi dan
wani ko wata ba Written by Jabeer..
.
Wata yarin yace 'yar shekara
15 kafa fururu komai babu
fuska kuma tasha Jan baki da
hoda harda gazal ta fallo da
gudu kanta daukeda tulo
tadebo ruwa a guje ta fada
gida Tana shiga ta saki tulun
yafadi ya fashe Nidai gaskiya
bazan yar daba hikenan ni
banda kata bus hine fa ya bini
har inda zan debo ruwafa
inna yana cemin *YAR*
*KWALLIYA* kafa ba mai
fuska tasha ado hine
nakamahi da danbe na fasa
mihi baki hine dan bahida
kunya ya biyoni gida Yasin
bazan yarda ba inna kalli
yanda bakina yake zubar jini
inna Abu muguwace wlh Kayi
hakuri kaji kaima da naka ina
ruwanka da tsokanar ta kuma
kasani sarai bazata barkaba
Au abinda zaki ce kenan to
shi kenan zan turo me rama
min Kayi hakuri mana kai
baka jin hakurine Ina
kotsayawa beyiba yatafi Inna
ki barhi ki barhi nace kaje ka
kawo bindiga karhe kenan
Yanzu Abu Wannan rayuwar
kika zaba to shikenan
zandena tsare miki wlh tinda
ke bakida hakuri yanzu
Wannan gabjejen kato kika
kama da fada Inna hinefa ya
nemi tso kanata fa Yanzu
ruwan da kika debo ma gashi
kin fasa tulon kaini inna ina
zansa kaina Inna Wannan fa
laifin tulun kine ina ruwanhi
dani nan naso na ajiye hi hine
ya fadi ya fahe sai hakuri
Kamarya sai hakuri Abu girkifa
zan Dora yanzu ya kikiso ayi
To ni kome ma za ayi ayi
tuludai yafahe nikuma na gaji
bazan iya komawaba
.
Kin isa komawa kamar kinyi
kin gama ga wani tulun can
jeki dauka kidebo wani
ruwan Kai inna kinemo wani
ya debo kinga janbaki da
hudana ya kare sonake na
zagaya baya na siyo I dan har
baki debo ruwan nan ba ba
inda zaki Abu kin jini da kyau
hikenan zan debo Abu ta
dauki tulun tatafi Rake
yauwa bari naga maya finda
ke daure a kugunta ta kwance
ta Ciro Hamsin ta mika wa me
rake Yabata rake da canji
tana tafe tana sha harta
karasa rafi Yauwa wana
kama wato jiya kika watsa
min kasa kika gudu ko yanzu
wana kama cewar Abu Ke
Abu kinga diban ruwa aka
turoni ba fada ba matsa na
wuce cewar binta Ke binta
me kike nufi ni wasa aka
turoni kenan bari kiga wasa
cewar Abu Hannu tasa ta
ture tulun dake kan binta
yafadi kasa yafashe Yauwa
kinga wasa nan nafasa banza
ko kinada abinyi ne Kaiiii ni
kika fasawa tulu wallahi kinyi
karya saina rama Abu kome
kike takama dashi kin tara kin
samu ni binta saina gyara
miki zama Binta na gama
fada tasa kafa ta daki tulun
Abu yafashe Nanfa Abu ta
daka tsalle ta dire ta kamo
wuyan Binta suka kama fada
da kyar aka rabasu Aina fada
miki Abu ni Binta nice dai dai
ke saina gyara miki zama
Tohi kenan idan baki gyara
min zamaba nizan gyara miki
kuma saikin biyani tuluna
kona daka ki a gurin nan
wlh Allah ko Abu bazan biya
ba kiyi abinda kika gadama
koda me kika zo ni Binta na
fiki haka kikace ko to
hikenan Kallon ta Abu take
tana gyada kai da buga kafa
Banga wanda ze fi karfinaba
ni Abu wai saiwata banza
bazara iskar damuna binta
wlh kintarowa kanki aradu da
ka Hannun ta Abu ta kama
ta sakar mata cizo dagudu
tabar wajan Binta tabi
bayanta da gudu haka suka
yanka cikin unguwa dagudu
harzuwa gidansu Abu Abu ta
boye a bayan inna Inna ki
matsa Wannan fadan ba naki
bane kimiko min Abu na nuna
mata abinda binta zata iya ni
kika ciza dai ko cewar Binta
Yar gidan marasa tsoro
mekikeyi a bayana aina fada
miki ni nadena bada hakuri
kinga Binta gata nan zoki
mata abinda kike so cewar
inna Gadan gadan Binta
tataho Kinga Binta tsaya Abu
ina ruwan dana aikeki kidebo
cewar inna Inna asara kika
aika dankuwa ni Binta nice
nan na fasa tulun *'YAR
KWALLIYA* tafasa min nawa
shine nima na rama wata
tsiyarce cewar Binta Ahh
babu bakomai kinyi daidai
yanzudai kiyi hakuri Binta
kibari idan tafito kuyita takare
mutuwama tana tsoron idon
ma haifi cewar inna Inna
kenan kince haka ko to ina
waje ba inda zanje kekuma
Abu zaki fito kisameni hoda
bawanka kidinga Wanka idan
zakiyi kwalliya Binta tajuya ta
fita Inna ki matsa kibar ni da
ita kina jin metake cemin
Karya tayi Abu gaskiya tafada
yau kwananki nawa rabonki da
kwanka Inna batun wankan
nan kibarhi aikyan kwalliya
kayihi batateda wankaba
gawani kamhin turare na
musamman dayake tahi a
jikina gahi turaren babu a
kasuwa me yafi raina shine
zan tsaya inta batawa kaina
lokaci wajan yin kwanka Dalla
rufemin baki kazamar banza
kazamar hufi ina kyau Anan
*HODA BA WANKA* Baki
tabude ta gir_giza kai ta
dunkule hannu inna harda ke
yasin duk wanda yasake ce
min hoda ba wanka na dena
raga mihi yasin cewar Abu
Yanzu da kika dunkule hannu
damben zakiyi dani nima
cewar inna Jifa tayi da
takalmin kafarta ta debo
kayan Kwalliya ta zube a
gabanta tadauki Wannan
tashafa ta ajiye takalli kanta a
madubi tayi dariya
.
Inna jiya da naje dan dali aka
dinga tambaya waye yafesa
turare nayi shiru tsabar kanhin
turaren jikina hanci suka
toshe Niko kayan nan ma
bacanzasu zanyi ba Wanka
kuwa nadena Kaza kankida
motsi afakaice suka zageki
baki saniba ba abinda kikeyi
sai bugawa kitemaka ki ajiye
kayan kwalliya kiyi Wanka
kekanki zakiji dadi Tab tab
aaah waii saidai wata Abun
badai niba wanka nida hi
munyi hannun Riga inna kifara
sabon lissafi daga nan
harranar sallah nida Wanka
Haka kikace to Allah
yashigoda yayanki da malam
su insun isa dake Sa saki kiyi
tinda ni kin rainani dan Allah ji
yanda kika cika mana gida da
tsami cewar inna Kinji ko
inna kinji irin kamhin turarena
ko hakama wani saurayi yajiyo
kamhin yace yana sona nace
bana son hi ni fako inna har
bana son fita dik inda nabi
ansan nice saboda turturarena
cewar Abu Waiyoo waiyoo
tasa kafa tayi koli da kayan
kwalliya inna ban fada
mikiba yau ake cin kasuwar
gangare natafi Tayi fice
warta Badan Allah yasa akwai
sauran ruwa agidan nan ba da
Abu ta gama dani cewar Inna
Tafiya take a hankali tana
tafiya tana yanga acewarta tafi
kowa haduwa ga turaren
jikinta yafi na kowa kanshi
tana tafe tana cin gyada
hannun takuma rikeda sandar
rake ga wuwar danmara tasha
a kugunta binda na labe tana
kallon ta Abu nakara sowa
inda Binta take Binta tariketa
Wana kama yasin saina
dagargaza bakinki zan kyaleki
yanzu ina inna take balle
kibuye a bayanta cewar Binta
Yasin Binta kanki baya aiki
kalli yanda kika rike min Riga
a gaban mutane gasamari a
gefe kalan ki zubarmin da
mutunci a idonsu haba kidena
abinda kuda zebiki Karsan
kuda nice mangoro kobakijiba
cewar Binta Janyota tayi
zata daka bashiri ta saketa
tatoshe hanci Abu
dagaskene abinda ake fada
kenan Wannan warin daga ina
lallai kinci sunan ki huda ba
Wanka sammin raken mana
Abu taraba shi2 ta bata
Yauwa nagode gyadar fa
Tadiba tace Gahi kibarni zaki
rakani cewar Abu Eh ni yanzu
kawarkice gaskiya kinada
hankali Abu Dariya tayi tace
ko nasani suna tafe suna
shirme harsuka siyo suka
dawo
.
Atare suka shiga gidan Inna
na ganinsu ta fara salati Abu
mekika kuma yiwa Binta
cewar inna Inna ai yanzu
Binta tazama kawata cewar
Abu Ina baze yiyuba ban
yardaba wlh dama ya kike
bare ankaraki da binta waye
besan bintaba cewar inna
Kinga Binta jeki gida zanzo na
same ki cewar Abu To inna
sai anjima cewar Binta
Sallama Alaikum inna ina
wuni Lpy kalau Nura sannu
dazuwa kaga Abu tayi
sabuwar kawa mara aji irinta
Ke Abu yatoshe hanci inna
meya yake bugawa haka
cewar Nura Wacce inbanda
*'YAR KWALLIYA* Fari Abu
tayi da ido tareda
juyawa New writer's
Taku husba'ahfama
.
Yaya Nura a hekaima kaji
kanhin tiraren nawa Dalla
kanshi ko wari kazama kawai
dubi yanda gidan nan yadauki
warin jikin ki Wari karyama
kenan Yasin kanhi kaji cewar
Abu Yau sai kinyi Wanka
bazan iya zama dake kina
wariba wlh inna bani ruwan
nan na kusa dake cewar
Nura Banga abinda zesa nayi
wanka ba Yasin kalan kanhin
turarena ya tafi Nura ya
dauki ruwan yasa a bandaki
yakai mata soso da sabulo ya
karyo bulala yarike Shiga kiyi
wanka Yaya Nura ina ganin
gir manka fa cewar Abu
Yadaga bulala bashiri ta fada
bandaki tayi zamanta Kayi ka
gaji yaya ba wankan da zanyi
cewar Abu Tana tawasa da
ruwan kamar tana wanka
tawanke fuska da kafa da
hannu Kate makeni ina
fitowa zan cika fukata da
KWALLIYA na raka Binta tallar
gurjiya hahhh Tabude ta fito
ta harareshi tashige daki tayi
KWALLIYA ta tafi gidansu
Binta taje tasamu Binta ta fito
tallar gurjiya A hanyarsu na
tafiya Abu tayi ido4 dawata
taci ado da KWALLIYA tayi
kyau sosai harta bace Abu na
kallon ta Ke mekike kallo
cewar Binta Kinga yanda tayi
kyau tafi yanta kayanta komai
yayi Nanfa Abu tashiga yin
irin tafiyar Kibar Wannan abin
Abu kinsan daga ina take
cewar Binta A'a cewar Abu
Daga birni take haka suke
tasu KWALLIYAR dasa kaya ba
irin nakiba HODA BA WANKA
.
Yasin yanzun nan bakinki
zeyi jini Binta nizaki cewa
haka nifazanyi fada da duk
wanda ya kirani da Wannan
sunan kowaye hi cewar Abu
Maida wukar nataba zuwa
birni sau1 yanada kyau ginin
su ba irin namuba kinga baze
yu nabaki lbr ba saikin gani da
idon ki cewar Binta Kai nima
inaso naje zaki kaini dan Allah
cewar Abu Inna inna ce
matsala Abu damunje yasin
cewar Binta Kinga bawata
matsala ki kaini kawai inzaki
kaini ya kika ganni zanyi kyau
a birni ko cewar Abu Ehhh to
ban saniba saikinje tukunna
saboda gaskiya tsoro zaki
basu kalle kifa tab cewar
Binta Waike hikenan bakida
magana sai kice na kalli kaina
me zan gani kodai ciki baki
kike min ne cewar Abu Ko
daya KWALLIYAR takice abin
tsoro ga kafarki Fari fat
gaskiya bazan kaikiba saikin
waye cewar Binta Abinda
Binta tafada yabatawa Abu rai
yasa tayi gaba ta barta a
baya
.
Wani yarone yazo siyan
gurjiya gun binta Binta zuba
min gurjiya Karki zuba mai
cewar Abu Tinda na ganka
nadawo mekace min jiyama
Meka ce mata Eh cewar
Binta Shiru yayi yakasa cewa
komai saida ya gano
yayanshi yace ' *YAR
KWALLIYA* nace Ohh me
dadtin dankwali itace *'YAR
KWALLIYA* cewar Binta
Barshi dani yanzu nanuna
masa kalata Yasin harni zaka
tsokana ka gudu anhi kudin
nahi Binta cewar Abu Binta ta
ansa tace kuma bazan siyar
maka da gurjiyan ba na
karfine Gaya mihi binta waihi
Wannan dame yake dakama
ne naga saiwani jijjidakai
yakeyi cewar Abu Kasa ta
diba ta watsamai a ido Binta
tasamai kafa ya fadi suka
rufeshida duka abin mamaki
kato a kasa mata na duka
abinda mutane ke cewa
kenan Yayan shina kara sowa
ya daka musu tsawa Suka
bar dukanshi suna Harar shi
Lpy kaikuma meya kawo ka
kasan muko suwaye cewar
Abu Suwaye Ku inbanda
kucakai marasa hankali dalla
dubeki kafa furu furu komai
be ganiba dubi kayan jikinki
fuska saikace Aljana waike
kinyi KWALLIYA Ap abanza
yafi na tsohuwa kaga ka
gaggauta barin gurin nan inba
hakaba kuma hmmm cewar
Binta Karkusake suce zaku
yimin haukan da kuka saba
danni bazan daukaba wlh Ko
Binta mu gwadamai aiki dan
nakula saimun koya mishi
hankali cewar Abu Waige
Binta tafara can ta gano dutsa
tace haryanzu bakinka be
mutuba ko tsaya ka gani
Dutsen ta dauko da buga
mishi a kai Banza a banza
cewar Abu Jini ya fara zuba
a kanshi Abu da Binta suka
zuba a guje suka wuce
gidansu Binta Umma ga
gurjiyar ki yau an hana talla
inji me gari cewar Binta Ke
Binta waya fada miki cewar
umma Umma Nifa ganauce
ba jiyauba Gashi can ya baza
yan *DOKA* A gari cewar
Abu Kunga bana son shegan
taka waca tsiyar kuma kukayi
na sanku da kyau cewar
umma Wani ne ya nemi tso
kanar mu hine muka fasa mai
kai cewar Binta Eh banjiba
naji kamar kince fasa kai
Allah na gode maka daka bani
Binta nidai shikenan bakina
baze zauna shiru ba saboda
inada Binta cewar umma
Kofar gidan su Binta aka siga
duka da karfi Kufito mana
dasu ko mushigo yara sun
gagari kowa wlh yau zamu
sharewa kowa hawaye kufito
dasu cewar mutanan da suka
zo Kuna jiko yara kunzama
dan kuka mejawa uwarsa jifa
Umma kinga jeki kiji dame
suka zo idan da sulhune
kusulhunta idan kuma akasin
hakane kikira womu katkenan
cewar Abu Kushiga ciki bari
naji dasu
.
Wai baza a fito dasu bane Eh
mumafa yan zama nine kofar
suka bude suna kokarin
shiga Haba dan samari gidan
matan aure ne fa Nasani ina
'ya'yan Allah banin nan suke
Binta da Abu Basa nan sun
fita Karyama kenan ina ganin
su suka shiga gidan nan dan
haka ki fito dasu kawai mu
baza mu hakuraba dan
uwanmu suka fasawa kai
gashinan sai zubar jini yakeyi
yanzu haka yana Asibiti Allah
yabaku hakuri kuje idan sun
dawo nida kaina zan kawo
muku su cewar umma Eh to
na yarda dake saidai be
kamata mu tafi haka ba bari
mu bar miki sheda idan sunzo
ki nuna musu Yadaga gora
ze sauke mata dagudu tabar
gurin ta shige gida tarufo
kofa Yauni umma naga ikon
Allah ina kuke Umma sun
bar miki sheda banzaye
sokaye sun yarda ba ma nan
gamunan muna jinsu kuma
cewar Binta da Abu Au kujin
dadin kune a bar min sheda
saboda kun amsa sunan Ku
Binta da Abu ko Allah yate
makeku suna nan suna jiranku
kuna fita sai abinda hali ya
yiwu cewar mama Basu isaba
yanzuma ba barinsu zamuyiba
narike muryar su zan ne mesu
1 bayan 1 cewar Abu Umma
kawo mu kai miki dan dali
cewar Binta Gashi nan kutafi
amma dan Allah karku nemi
tso kanar kowa kuma Ku
canza hanya karsu ganku
cewar umma To sai mun
dawo suka fada gaba dayansu
suka fita
.
Suna fita umma taji wani
hadeden wari Umma taja
dogon nun fashi Wannan
wani sabon yayi ne kuma Abu
irin Wannan bugawa haka
nida Allah yasa kar Binta
tadau Wannan halin na rashin
Wanka Suna tafiya suna
waka suna ciye ciye suna
neman tso kana Abu ta gano
bishiya tace Binta ajiye
gorjiyar nan muhau bishiya
kinga yanzu basu fara zuwaba
zuwa anjima sai muje dan
dali To muje suka tarar da
yara a jikin bishiya suna
wasa Kubar gurin nan Abu
da Binta sunzo ko sokuke jiki
yayi tsami cewar Binta Tinkan
Binta ta karasa magana yaran
suka bar gurin dan sunsan
halin Abu da Binta Suka cire
takalmi suka haye bishiya
suna wasa kamar yara Wasu
yan mata suka zo wucewa
suka gano Binta da Abu suka
kwashe da dariya Abu na
ganin su ta sauko Binta ma
sauko wa tayi Wakuke wa
dariya Eh daku nake magana
Abu ta fada tana dungure
musu kai Karki sake dun
guremin kai kinsan kowaye
babana kuwa A garin nan
.
koma waye hi beda meniba
abinda yasa kika kallemu
shine yanzu ze Ja miki dukan
tsiyama kuwa cewar Binta
Jiki ko kayama baki iya
sawaba ji hodar fukarki
janbakin ma tsohon yayi ne
amatse ciki asai sabo cewar
Abu Kaji wai harkurace zata
ce da kare maye jiki kalli
kafarki kalli fuskarki ji wani
wari mara dadi da kikeyi
gaskiya kinci sunan ki HODA
BA WANKA Nanfa Abu tayi
kukan kura ta rufesu da duka
Binta nadukan daya Abu ma
na dukan 1
.
Duka sukai musu bana wasa
ba harda yaga riga Cikin
muryar kuka yarinyar tace
saina nuna miki bakida wayo
Saikin ga gatana Abu tace
Jeki turo duk wanda kika
gadama ni Abu ina jiran hi
banza qazama Eh nice
qazama idan ni kazamace ke
kuma fa fada min cewar yarin
yar Bakinki be mutuba ko
Abu saimun zubar mata da
hakwara tukun na cewar
Binta Kuyi duk abinda kuke
so lokacin kune yanzu nima
lokacina nanan zuwa cewar
yarin yar
.
Tana gama fada ta mike ta
debi takal manta a hannu ta
kalli kawarta da suke tafe
tare Tace 'YAR KWALLIYA
suka zuba da gudu
Matsoratan banza kawai harni
zakibawa tsoro da baban ki
Wannan kalmarta zakiga me
rama min yazama tamkar
tatsoniya a gurina ni Abu naci
dubu sai ceto Sukayi dariya
Kinga dauki tallar mu karasa
dandali yanzu kowa yazo
zamusha kallo kai ni harnaji
ma bana son zuwa cewar
Abu Binta tace meyasa
Tiraren jikina Akoda yaushe
shine matsala ta dana je
dandali daga kallo sai tohe
hanci a gurin sama ri cewar
Abu Binta tace dagaske kike
Abu warin najan hankalin
samari Abu tace bana son
wula kanci binta wayace miki
warine kanhidai nibama nason
irin kallon da sama rin suke
min nasani nafi matan dandali
kyau da kanhin tirare sosai ma
nice kadai nasan sirrin
Nanfa Binta ta tafi tuna ni Ke
tina ninme kikeyi Abu gaskiya
nima zan fara fashin Wanka
konima turaren jikina zefito
kwana nawa zanyi banyi
wankaba Abu tace yauwa yar
gari kinga bake ba Wanka
indai kinaso tiraren yazauna
tareda ke duk inda kika higa
ansan kin higo Binta tace To
hi kenan nagode kawata
Tadauko farantin gurjiya tace
debi kici iya San ranki aikin
bani sirri babba Abu tace
Bakomai yiwa Kaine Binta
amma ya zakiyi da umman ki
idan tagane kin dena kwanka
Kibari kawai nikaina bansan
abinyi ba mutafiko kinga
yamma tayi kar a fara
bugawasa bama nan Abu
tace ga aiki zan saki indan
mun higa dan dali ki ki zuba
ido kiga abin mama ki gurin
sama rida yan mata To
hikenan muje Abu
Suka je dandali hakan kuwa
akayi Abu nazuwa masu toshe
hanci nayi masu dariya nayi
Abu harda sake tafiya
Kawata Abu gaskiya nima na
rike sirrin nan hannu 2
Sukayi dariya suka tafa
Suka sha kallo sukayi tsokana
iya son ransu suka koma
gida Daga ina kike Waye
Wannan Abu tace tana daga
kai taga Nura Daga dandali
nake Yariko hannunta
yawuce da ita ciki ya watsar
da ita kamar kayan wanki
Nura ya fara shin shine shin
shine Yace Inna bana
tunaninda Abu ta shigawanka
tayi Inna tace Ko hmm zata
aikata nasani Wannan nan
gaba kadan nizan fara yimata
Wanka da kaina
.
Abu tace Waaa niii tab
bawanda ya isa dan bakin ciki
turaren nawama rabani dahi
za a yi Nura ya Wanka mata
mari tafashe da kuka Inna
abinda ya dace kenan kifara yi
mata da kanki tinda ita bata
yi Nifa bawanda zemin wanka
Nifa yaya anyi walkiya na
ganka bakin ciki kawai ka keyi
dani dakaji kanhin tirarena
saika dinga yamutse fuska
saboda bakin ciki Tirare ko
wari kinga kidena shiga cikin
mutane kina kiran waikin fesa
tirare dariya zasu miki
Wannan warine warinma mara
dadi qazama cewar Nura hi
kenan Inna kina jinhi ko ni ya
kira qazama tafara timami
akasa Nura yace Inna kice
mata ta tashi kokuma yanzu
jikinta ya fada mata Bashiri
ta mike tana gunguni harya
fito fili tace nagaba yayi gaba
kanshi kuma nayi bawanda ya
isa yakwace Ehhhe Waye ze
kwace inbanda Wanka Inna
duk sanda kika tashi wankar
*'YAR KWALLIYA* kitanaji
kwalin sabulu saboda tsoro
Inna saida safe Yana fada
yayi fice warsa Allah
yakaimu Inna kinji shi ko
Yasin yaya kajawa budur
warka Allah ya hadani da ita
Kinga Abu bana son neman
tsokana karki sake kitaba
musu 'ya kisamu wanda
yamiki badai itaba ki kwanta
saida safe To Inna Allah ya
kaimu WASHE GARI DA
SAFE Abu ta fito tana
hamma
.
Inna Allah dai yasa kin gama
abinci dan yau yunwa
nakwaso abaccin Bagai
suwa ba komai sai Neman
abinci baza kiciba saikin goge
baki kinyi sallah tukunna
cewar Nura Tamatso kusa
dashi tace yaya a gidan nan
kaine kwai matsalata yanda
sauran suka tafi suka barini
kaima zaka tafi ko ince kagaji
kabarni Yatoshe hanci tinda
tafara magana harta gama
Nura yace Wai Wannan bakin
naki Abu ai sai ya kashe me
rai yaushe rabonki da goge
baki AF anzo wajan nikaina
na manta gawayin da gihirin
na ban wuya Yasin hiyasa na
dena wankewa yawan goge
baki na kahe hakori Nura
Yana nesa da ita yanda bazeji
warin bakin ba Injiwa Yau
saikin goge baki yaushe
rabonki da sallah dan Inna
tace rabonda taga kin kalli
gabas harta manta cewar
Nura Eh hakane yaya hadasu
nakeyi hiyasa bata ganina
Hadasu kamarya Abu Nasati1
nakeyi a rana1 sauran
ranakun kuma ina hutu tafada
tana dariya Nura yace Abin
ma dariya yabaki ko Abu
amma kin dena zuwa isilamiya
ko Tab tsohon zance tin
yauhe nadena zuwa bari kaji
laifi nayi yace ze dakeni
nikuma nace be isaba shine
yasa yara suyimin waka
waini *HODA BA WANKA*
hine na sace mai tayar keke
hine fa yake ne mana ruwa a
jallo
.
Tana fada tana Sosa kai da
jikin ta Inna haka lamarin Abu
ya kara lala cewa cewar Nura
Inna tace kaji da kunnan ka
kakuma gani da idonka yazu
kuma abin zekara finnada
tinda ta hadu da Binta Ido
yazare yace Binta gagare Ita
dai yanzu kawartace sosai
duk inda Abu take zakaga
binta Cewar inna Dole nakara
samiki ido Abu jeki kwanke
baki kiyi Alwala kizo kiyi sallah
a gabana kuma ma inbanda
rashin hankali irin na Abu a i
na akace miki hada sallah a
keyi kowacce ana yinta akan
lokacin ta kina jiko cewar
nura Abu tace Yashiga tanan
ya fita tanan bayan kai ba
malami bane me zaka fada
min nayarda bayan sanin ma
nafika Na yarda jekiyi alwalar
kizo Taje tayi ta zo
gabanshi tace yaya na hutar
dakai dama yau nake hadesu
guri guda barima nayi ka gani
Nura yace Ke bana son hauka
fa sallar Asuba raka'a
nawane Lallaima yayan nan
nawane inbanda 2 Sallama
Alaikum Nura yajiyo sallama
daga kofar gida girgiza kai
kwai yayi yatashi yatafi Nura
ya Inna taku Lpy kalau cewar
nura To Alhamdulillah
megarine yace kuzo dakai da
inna dakuma Abu Allah
daiyasa lpy cewar nura
Ehhhhhto lpy ba lpy ba saidai
koma meye idan kazo fada
kaji To gamu nan zuwa yace
yakoma ciki Inna yarinyadai
tasake ballo ruwa megarine
yake Neman mu To Bakomai
bari ta idar da sallah saimu
tafi cewar Inna Abu tace Inna
Nifa ba inda zani idan banci
abinci ba Ehhhhe Waiba
sallah kike yiba Abu cewar
Inna Abu tace Inna kwantarda
hankalinki na idar bani na
bawa cikina tukunna Inna ta
bata ta ansa tana hannu baka
hannu kwarya harta gama
Tasha ruwa Tace Inna saura
kwalliya idan banyiba bazan
iya sa kafata wajeba Nura
yace kin isa waye ze zauna
jiranki Inna tace kai kanka
kasan hakan baze yiyuba
kabarta tayi mutafi Abuta
baje kayan KWALLIYA tayi
kamar yanda ta saba fukarnan
kamar Aljana Inna mutafi
naga ma Warin bakinta yadoki
hancin Nura Kaiiiiiii Abu baki
wanke bakiba ko Eh ban
wankeba bakina ko naka
.
Tayi gaba abinta sukuma suna
binta a baya harsuka karasa
fada kowa na gaida megari
amma banda Abu Megari
yace Ke Abu me yarin yata tai
miki kika daketa jiya tareda
bakuwar gidana Tawatsawa
yarin yar harara tace kuma na
dake ta nadaki banza ba uwar
dayasa tace min HODA ba
Wanka Ke Abu baban nawa
kike fadawa haka cewar yar
megari Anfada mihi ubanki
ubanane cewar Abu Kaji
yarinya mara kunya me garin
kike fadawa haka Ayi hakuri
yarin yace cewar Inna Abu
tace Inna saboda ni karki fara
karya niba yarinya bace
hekarata goma shabiyar Inna
nayimata alama tarufe baki
amma ina zance kwai Abu
take saki..
Writing By Jabeer Rabiu Idris..
Whatsap Number..
07034488635...

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.