Romantic Hausa Novels

Zafin So Book 1 Complete Hausa Novel

Reading file: (00)ZAFIN SO COMPLT-1-1.txt

Chapter 2 of 3

Page5⃣to6⃣
Na Amrah
☘🍁☘
🍁

Da shigar shi gida bai jira komai ba ya kwanta kan wata tabarma dake shimfide a bakin qofar d'aki, NAWWAF dai sai bin babanshi yake da kallo ganinshi da yayi sukuku, "Abba sannu da zuwa", ya ansa da "yauwa NAWWAF, ina umman taka?",,,,," tana daga ciki ina jin, Ummah!", "ga ni nan, zuwa fa, aahhh lale marhaba da mutan birni, sannu da hanya" ummah ta fada tare da fitowa daga daki.

Wasu irin zafafan hawaye suka fara ambaliya a fuskar Abbah, duk hankalunsu ya tashi ganin abbah na kuka, a rude NAWWAF yace "abba wai me ya faru ne? Tunda kazo naga kana da damuwa a zuciyarka, ka fada mn matsalarka wlh na dauki alqawari indai ina da maganinta".
Ummah tace "malan meke faruwa da kai, kuka fa kakeyi, tunda nake dakai ban taba ji ko ganin kayi kuka ba, amma da mamaki sai gashi yau kana yi har idonka yayi jaa".

Sun d'auki tsawon lokaci shiru basu samu ansa daga Abbah ba, jin bashi da niyar basu ansa ne yasa Ummah tayi qarfin halin cewa "ka watsa ruwa malan ka kwaso rana sai kaci abinci". Baice mata komai ba ya miqe jikinshi na rawa ya nufi toilet. Da gamawarshi ya fito, abinci kawai yaci ya kwanta bacci yayi gaba dashi.

NAWWAF duk abn duniya yabi ya dame shi, sai zaman tagumi yake har abba ya farka yaga Ummah zaune kusa dashi tana hawaye, ga NAWWAF ma zaune a gefen Ummah, ganin su cikin wannan halin yasa shi cewa "kuyi haquri, bana son na fada maku abnda zai saku bacin rai ne shi yasa naqi fada maku, amma tunda kuna son ji yanzu zan fada",,,,,,,,,,nan ya hau basu labarin duk abnda ya faru tun farko har qarshe.

Zumbur NAWWAF ya miqe tsaye yace "Abbah ka bar naje Katsina na samu jakar yarinyar nan, wlh sai naci mutuncin ta kamar yanda taci naka mutuncin, kawai qaramar yarinya ta kiraka da tsohon banza, munafuki, Subhanallah! Abbah yau yau din nan zan tafi". Bai jira komai ba ya tafi dakinshi da nufin canza dressing.
Tsawa daya abbah ya mashi dole ya tsaya, abba yace "na saka ne? Wau kai NAWWAF yaushe zaka rage wannan ZAFIN zuciyar taka ne? Ya kamata fa kasan ka girma, kuma nace kabarta da duniya, duniya zata bida ta, ai laifi na ne da naje gidansu da aiki, kaga inda ace banje ba ai da bazata ci min mutunci ba, amma yanxu da nabar gidan ba shikenan ba? Sai kuma tayiwa wani ai".

Ummah tace "hakane malan, tou amma yanxu idan ka dawo gida ka zauna ya zamuyi da abincin da zamuci? Shi NAWWAF bai iya ko wace sana'a ba, shidai karatun boko kawai ya tasa a gaba, ni fa yanxu kusan shekarar shi biyu kenan da gama degree dinshi, har service ya gama amma babu wani aikinyi kullun sai zaman qofar gida yake, sai matacciyar zuciya kawai".
NAWWAF da hawaye ya wankeea fuska yace "Ummah indai hakane zan nemi kudi insha Allahu, neman kudi kuma ta tsaftatacciyar hanya, zan nemi halal insha Allahu ko ta hanya mafi wahala ne".

Dedicated to Rerbee'art sk msh❤

Princess Amrah😘
[7:07pm, 11/04/2016] 💓Princess✍🏼: [5:48pm, 11/04/2016] 💓Amrah💓✍🏼:

☘🍁☘ZAFIN SO☘🍁☘
🍁 🍁

☘🍁☘
🍁

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.