Romantic Hausa Novels

Zafin So Book 1 Complete Hausa Novel

Reading file: (00)ZAFIN SO COMPLT-1-1.txt

Chapter 1 of 3

[8:50pm, 30/03/2016] ๐Ÿ’“Princessโœ๐Ÿผ: โ˜˜๐Ÿโ˜˜ZAFIN SOโ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ ๐Ÿ
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ
1
Na
Amrah
๐Ÿ”† GHW๐Ÿ”†
Da
Haneefa Usman
NWA

GARGADI:
Bamu yarda wani/wata suyi copy and paste na wannan labarin ba, duk wanda ya aikata hakan mun barshi da Allah mai kowa mai komai.

KALAMAN GODIYA:
Duk kan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki, ka qara tsira da aminci ga manzon tsira annabin mu Muhammad (SAW) tare da alayensa, godiya ga duk kan masoyan mu maza da mata aduk inda kuke, duk da wannan shine farkon rubuta novel din mu nida Hanee, muna fatan ku kasance tare damu a wannan labarin, karku bari a baku labari.

โ˜˜๐Ÿโ˜˜SHIMFIDA๐Ÿโ˜˜๐Ÿ
Wannan labarin ya qunshi labarin wata yarinya matashiya wadda ta tashi a cikin gatan iyaye, sai dai kuma kash! Tayi amfani da wannan damar data samu ta hanyar wulaqantar da duk wanda yake qasa da Ita, wanda a sanadiyyar hakan ne zata samu dana sani daga qarshe.

'Yan uwan mu musulmai! Ku sani kar kuga Allah ya baka lafiya, dama, lokaci da kuma dukiya, kayi amfani dasu ta hanyar nuna rashin godiya da ya baka su, ku sani! Akwai dubban mutane da suke neman lafiya, dama, lokaci da dukiya amma basu samu ba, tou dan me kai/ ke kun samu wannan damar sai ku lalata su? Muna roqon Allah daya qara shirya mana zukatan mu, ya bamu ikon amfani da lafiya, da dama da Allah ya bamu.

COMING SOON................โœ๐Ÿผ

Haneefah and Amrah
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ
[7:26pm, 2/04/2016] ๐Ÿ’“Princessโœ๐Ÿผ: โ˜˜๐Ÿโ˜˜ZAFIN SOโ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ ๐Ÿ
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ

Na Amrah ๐Ÿ”†GHW๐Ÿ”†
Da Haneefah NWA
page1โƒฃ-2โƒฃ
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ

Tafiya muke nida Hanee ko waige bama yi, da abn yayI nisa ma har gudu muka koma yi duk dan muga mun tarar da wannan hamshaqiyar yarinyar, bamu muka tsaya ba sai bakun wani qayataccen gida wanda da ka ganshi gasan na wani mai muqami ne, a daidai vakin gate yarinyar ta tsaya da motarta qirar range rover ash colour, horn tayi amma shiru ba'a bud'e gate ba, sai bayan kamar minti biyu ta qara wani horn d'in amma shiru gate man bai bud'e gate d'in ba. A fusace ta fito daga mota ko jakarta bata d'auka ba ta bar motar bud'e ta shiga gidan. Koda shigarta ta samu gate man d'in kwance yana rawar sanyi alamar baida lafiya, bata ko duba yanayinshi ba ta d'aga hannunta ta wanke shi da mari, dafe kumatunshi yayi wani zazzafan hawaye na saukar mishi, kafin ya ankara ta qara d'auke shi da wani marin, sai a lokacin tace "kai uban waye da zanyi maka horn har sau biyu amma ka kasa bud'e min gate? Bayan kuma kasan bisa ga d'abi'ata horn daya kawai nakeyi ko sallah kake dole kabarta kazo ka bud'en gate in shigo gida, mtswww wawan banza!".
Fita tayi bata koma takan motar ta dake waje ba, tayi tafiya mai nisa kafin ta isa inda farfajiyar gidansu take, shiga tayi kai tsaye babu ko sallamah. Ta samu momy kishingide ana mata matsar qafa, fad'awa tayi jikinta tana mayar da numfashi, a firgice momy ta miqe zaune tana fad'in "na shiga uku, auta me ya faru dake na ganki kamar ba'a hayyacinki ba?". Kyakkyawar budurwar tace "momy wai waye ta kawo mana wancan wawan a gidan nan?", momy tace "wa kenan?", a shagwa'be tace "gate man d'in can mana". Momy tace "ai! Wai baba faruku? Dady da kanshi ya kawo shi wai yana tausayinshi ne, me ya miki ne auta ta?", "momy wai har sau uku ina horn amma yaqi bud'en gate, motar ma tana can na bari a waje har da key d'in yana jiki ban cire ba tsabar takaici", miqewa tsaye momy tayi tace "auta! Baki da hankali ne? Baki gudun a sace ta ne? Kin san fa jiya aka kawo ta, waccan d'ayar ma ajiyeta kikayi fa aka sace miki a gidan biki". Kamar tana jira momy ta gama maganar aikuwa ta fashe da kuka tana fad'in "momy! Yau nice kike yiwa fad'a har da nuna min yatsa? Momy tunda nake baki ta'ba yi min haka ba, a dalilin wancan wawan tsohon gate man d'in? Tou barin je inda yake, wlh sai yabar gidan nan, ko uban wa ya tsaya mashi".

Haneefa Usman
Princess Amrah๐Ÿ˜˜
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ
[6:58pm, 7/04/2016] ๐Ÿ’“Princessโœ๐Ÿผ: โ˜˜๐Ÿโ˜˜ZAFIN SOโ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ ๐Ÿ
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ

Na Amrah๐Ÿ”†GHW๐Ÿ”†
Da Haneefah NWA
Page3โƒฃto4โƒฃ
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ

Fita tayi ko dan kwali babu a kanta, bata ko nemi takalmi ba ta kama hanyar d'akin me gadi, ta same shi still yana rawar sanyi wadda tafi yanda tabarshi d'azu. Bara jira komai ba ta fad'a d'akinshi, finciko shi tayi ta jefar waje, ta duba bakin katifar shi taga wata qaramar Ghana most go, dauko ta tayi ta jefa mashi a daidai isowar momy wurin, fitowa tayi daga dakin tace "a dalilinka momy na tayi man fad'a harda nuna ni da yatsa tayi, wlh yau sai kabar gidan nan, tsohon banza zaka nemi takurawa rayuwata, sai ka koma qauye aci gaba da cin tuwon dawa ai, mtsww" taja tsaki tare da barin wurin.
Abn haushi wai momy ta kasa ce mata komai, har tayi nisa da qyar tsohon nan me gadi yace "SAFNA!!! Ni kika wulaqanta haka? Ni kike kira da tsohon banza? Ko da yake banga laifinki ba, laifina ne da na qasqantar da kaina nake bauta a gidanku, hmmm!! Neman halak kenan, insha Allahu yanda na nema gareku kina wulaqanta ni bayan kuma nayi jika dake, ina roqon Allah ya kawo ranar da kema zaki nema a wuri na...." ya qarasa maganar cikin kuka da ban tausayi.

Da sauri ta dawo wurinshi ta sake wanke shi da mari tace "ba amin ba tsohon NAJADU!! Allah ya fika, kuma ni bazan ta'ba nema a wurinka ba, babana yana da kud'in da ko bayan ranshi zanci har in kyautar wa mabarata irinka" ta tofar da yawu qasa tace "tir! Da MUMMUNAN FURUCINKA".
Barin wurin tayi da gudu saboda qunar da zuciyarta ke mata. Momy bata ce komai ba sai bin bayan 'yarta da tayi tabar me gadi nata goge hawaye. Bayan kamar minti biyu yaja Ghana most go d'inshi ya fita. A hankali yake tafiya dan yana tsananin jin zazza'bi.

Da qyar ya samu yaje tasha ya hau motar qauyensu BAGARUWA, d'an chanjinshi ya biya kud'in mota ya isa. Ya samu Nawwaf na zaune qofar gida ya buga tagumi, koda yaga babanshi tuni ya tashi ya nufI wurinshi ya kar'bi jakar suka qarasa ciki yana mashi sannu da zuwa.

Haneefah Usman
Princess Amrah๐Ÿ˜˜
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ
[6:58pm, 7/04/2016] ๐Ÿ’“Princessโœ๐Ÿผ: โ˜˜๐Ÿโ˜˜ZAFIN SOโ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ ๐Ÿ
โ˜˜๐Ÿโ˜˜
๐Ÿ

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.