A Wani Gida
Reading file: A_WANI_GIDA.txt
Chapter 1 of 6
[4/2, 10:05 PM] nabilalady5: π‘π‘ A WANI GIDAπ‘π‘
πππ
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Part 50 β© 55
JINJINA GA DUKKANIN MASOYA LITTAFIN A WANI GIDA, HAKIKA INA MATUKAR JIN DADIN YANDA NAKE SAMUN SAKON NIN GODIYARKU DA KUMA GAISUWA ZUWA GARENI. NAGODE DA ADDU'ARKU AGARENI, ALLAH YABAR ZUMUNCI.
INA MIKA JIN JINA GA 'YAN GROUP DIN NABEELERT LADY 1&2, HAKIKA INA JIN DADIN ADDU'ARKU DA KUMA GWARIN GUIWAR DA KUKE BANI, TARE DA COMMENTS DINKU AGARE NI. ALLAH YABAR ZUMNUCI AMINππ»π.
Zaune suke gaba dayansu a falo, Fahad da Farouk se bata rai sukeyi saboda an dawo Faskari, ba kamar Farouk saboda shi agarin yake karatu. Bayan sun gama cin abinci kowa yayi wanka Malan yace kowa ya kawo result dinshi.
Faisal da Fatima ne suka fara shigowa falon, amma sauran seda suka dade kafin su dawo, sosai Malan yaji dadin yanda result din Fatima yakasance, gaba daya Excellent sun fi yawa, Good dinta biyu.
Hakama result din Faisal, na wannan karon yafi na koyaushe, domin yasamu grade me kyau, hannu ya mika ya karbi result din Farida, kallonta yayi yana fadin wannan ai ba rubutun malaminku bane.
Kuma duk wanda ya kalli score dinki ko be yi total ba yasan be isa ace kin samu wannan mark din da average din ba. Mama tace kamar ya? Kasande Farida ai tana da kokari. Murmushi Malan yayi yace to ai koni ba Malamin makaranta bane ya isa ingane abinda kikayi.
Kuma da alama ga wani bakin lalle nan daya zuba adede kan ai nihin total dinki da average dinki, ya akayi hakan tafaru? Ciccira ido Farida ta fara tana fadin muna kunshi ne yazuba akai.
Dariya Malan yasa yace lallai wannan lalle akwaishi da lura, wato daya tashi zuba seya zuba adede inda rubutun yake, kuma daga nan be kara matsawa ba ya tsaya adede wajen. Hmmm Farida kada ki bata mani rai.
Wannan rubutun ba na malami bane. Farida tace wallahi Malan bani ce na rubuta ba, haka Malamin mu yabani shine ya rubuta. Malan yace to inajin shine yayi kuskure wajen total din.
Amma zan sake total in fidda mark din kuma da average din. Kinga idan zaku koma se inje insameshi, ya kamata anuna mashi kuskurenshi. Saurin dago kai Farida tayi kamar zatayi kuka tace dan Allah Malan ka kyaleshi.
Hannu Malan yasa ya dauketa da mari wanda gaba daya falon seda suka firgita, Mama kuwa saurin tashi tayi tana kallon Malan cike da mamaki. Sosai ranta yabaci, wani irin ihu Farida tasa tana birgima akasa.
Cike da bacin rai Malan ya jawo dorinarshi yafara dukanta, duk yanda Mama taso ta kwaceta kasawa tayi, tun Farida tana kuka da karfi har ta dena. Seda yayi mata dukan dabe taba mata shiba ya saketa.
Hankalin Fahad ne yatashi, domin ya gane dalilin da yasa Malan ya doki Farida, saboda tayi mashi karya. Hannu Malan yadora abaki yana fadin rufe mani baki, idan na kara jin kukanki sena kara maki.
Komawa Mama tayi tazauna ranta abace, sede sam babu wanda ze iya gane hakan. Farouk ne yayi saurin mika nashi result din, sosai yakara jan baya, kallonshi Malan yayi fuska a daure yace kana JSS3 amma kana kawo mani wannan result din.
Babu abinda zan ce maka, domin yanzu ka girma, duk abinda kayi dede da kai ne, idan kuma akayi maka repeating banida matsala, kuma wallahi seka maimaita ajinka. Kallon Fahad yayi yana fadin ina naka? Ja da baya Fahad yafarayi yana fadin nawa faduwa yayi.
Saurin cafkoshi Malan yayi, haka ya zaneshi yana tambayarshi inda ya kai nashi, ihu kawai Fahad yake yana kiran Mama, seda Malan yayi mashi dukan tsiya ya fasa mashi jiki sannan yace yaje yadauko mashi result din.
Da gudu yafita se gashi yadawo dashi duk ya dukun kune, karba Malan yayi yana dubawa, gaba daya result din beyi kyau ba, gashi wajen teachers comment malamin yakawo karar Fahad na rashin jin da yakeyi.
Kuma baya zama a class, sosai ran Malan yabaci, kallonshi yayi yace ka kyauta, ai dama tunda naji ka fadi haka nasan bakayi abin kirki ba, kuma gashi Malaminku yace ba ka zama aji, gidan Uban wa kake zuwa? Cikin Kuka Fahad yace wallahi ina zama.
Malan yace irin wannan halin ka dorama kanka ko? To kasani wallahi duk wanda yaja aka koreshi daga makaranta ni babu ruwa na, sede yadawo yazauna agida, bazan kara bata lokacina da kudina wajen nemar maka makaranta ba.
Mutanan banza, gashi de daga farko kamar kune mutanan arziki amma daga karshe kune mutanan banza, wadan da nake ganin kamar sune zasuyi irin halinku gashi sun bani kunya, dan Allah kalli result din su Faisal.
Ke kuma babbar munafuka, kina karamarki har kin iya yin munafurci, JSS 1 kike amma kinsan ki canza rubutun da malaminku yayi, wai ni zaki fadama lallae ne ya zubar maki. To kisani sena kaima malaminku result din, idan yaso seya nunaki agaban 'yan ajinku kuma shima ya zaneki dan hakan yazama darasi ga sauran yaran.
Kutashi kubani waje. Saurin tashi Farida tayi tana kuka, tasan idan Malan yakai ma malaminsu result dinta dariya za'ayi mata, kuma zatasha kunya. Tashi su Faisal sukayi, Fatima se kunshe dariya takeyi, shiko Faisal se murmushi yakeyi.
Mama se binsu take ta wani irin kallo, tsanarsu ta kara shiga ranta, haka suka fita, shima Fahad se hararar Faisal da Fatima yakeyi, haka ma Farida, Farouk kuwa se dariya yake masu.
Suna fita Mama ta matso kusa da Malan tana fadin kayi hakuri, kasan halin yarinta kowa da irin tashi, wata rana se labari. Malan yace labari marar dadi ba. Murmushi Mama tayi tana fadin haba Malan ya zakace haka? Kada kamanta fa maganarka me dadi da marar dadi zasu iya yin tasiri akan yaranka.
Addu'a ita kadaice abinda yafi kamata kayi masu, amma ni nasan akwai abinda yake faruwa da yarana. Kukan munafunci tasa tana fadin kaima sheda ne akan yarana, duk unguwarmu babu wanda yafisu kokari, amma lokaci guda ace yarana sunja baya.
Wallahi na dade ina zargin wani abu, ai koda zasu ja baya be kamata ace su duka sunja baya ba, kalli Farouk, yaron da sam karatu baya mashi wahala, kalli irin kyaututtukan dayake amsa, amma tunda yashiga wannan makarantar shikenan komai ya lalace.
Uhm, ninasan dama Inne bazaki barni haka ba, waye besan halin 'yan gidanku ba, saboda tsabar asiri uwarta harta tsufa bata bar mijinta yayi aure ba, so nawa yana zuwa neman aure se maganar ta yi karfi kawai ta lalace.
Yanzu kuma gashi nima Allah yahadani kishi da jinin asiri ni wallahi dama nice tayimawa na bar gidan, inbar mata yaran tarike matukar zata barsu da kokarinsu. Kana kallon yanda Faisal yake wani irin murmushin mugunta. Yaron da ko dariyar kirki baya yi agabanka.
Ai ni tun da Farouk yashiga makaranta Inne take bashi wani abu aboye kuma tace kada yafada maka nasan ba abun arziki bane, duk idan ze tafi seta daka mashi yaji da kuli tabashi se kace yaron mayu, haka ma Fahad da zasu tafi shima abinda tabashi kenan, ashe dama akwai abinda ta kulla. Na dauka kawai tanayi ne dan Allah, shiyasa tace base anfada maka ba, ni kuma ganin abun arziki ne yasa bana fada maka, dan ba'aso dan mutum yayi abu se an fada.
Kuma ka kira Farida ka tambayeta, tunda kuka dawo tace zata fada mani wata magana akan Inne wai taje makarantarsu, sede bata gama fada mani ba ka kirawo mu nan, idan gaskiya ne me Inne zataje yi makarantarsu Farida.
Jikin Malan ne yayi sanyi kuma lokaci guda fuskarshi ta canza, kalon Mama yayi yana fadin kin tabbata Jamila taje makarantarsu Fatima? Mama tace ni ban gama jin labarin ba, amma ka kirawo Farida da Fatimar zakaji komai.
Jinjina kai yayi yace biri yayi kama da mutum, ai nasan irin bakin halin Jamila zata iya yima yaran nan wani mugun abun, gashi nan yanzu yaranta ne kadai suke kokari a gidan nan, yanzu kuma ta koma zata bata mani yara.
To wallahi duk da inajin kunyar Alhaji Mansur zanja mashi layi tsakaninshi da yarana. Tashi ki kira mani su. Saurin tashi Mama tayi cike da farin ciki tafita. Kafin suzo seda tace ma Farida ta fadi duk abinda tasani harma dana kari duk ta fada.
Ai ko suna zuwa Malan ya tambayi Farida akan zuwan Inne, tsaf Farida ta kwashe duk abinda ya faru harma da kari tafada masu. Daga karshe tace kuma da naje wajensu Inne koro ni tayi, bata bari naga abubuwan data kawoma Fatima ba, sede kawai Fatima takawo mani wasu kaya.
Lokacin da naci wani abu da tayo mana seda nayita amai, har clinic seda aka kaini, kuma tun daga lokacin idan ana koya mana karatu se inji nagaji da class din kuma bana gane komai, amma farkon zuwanmu har kyautar kudi malamin mu yana bani idan na bada amsa.
Salati Mama ta farayi tana tafa hannu, jawo Farida tayi tana duba idonta, tana fadin nide tunda kuka dawo nake kallonki, gaba daya naga kin canza, kuma Fatima tayi wata irin kiba ashe da abinda kikaci.
Kallon Fatima Malan yayi wadda tayi kasa da kanta yana fadin ke da gaske Uwarku tazo makarantarku? Cikin Kuka Fatima tace e tazo amma wallahi duk abinda takawo mani shine na dibar ma Farida, kuma mu da mukaci babu abinda ya samemu.
Tsawa Malan ya daka mata yana fadin rufe mani baki, yarinyarki karama amma kin iya hali irin na Uwarki. Kallon Faisal yayi wadda gaba daya ya hade rai, kai Faisal Mamanku taje makarantarku? Kanshi yana kasa yace e taje ta duba ni.
Zufa ce kawai take zubo ma Malan, jinjina kai yayi yace ku tashi kubani waje. Bayan sun tafi Mama tace kaji da kunnanka ko? Ai nafada maka, wallahi Inne ba ta sonka da yaran nan, kaga yanzu tunda suna boarding zata rika zuwa tana hure masu kunne, tunda mijinta me kudi ne zata rika saya masu abubuwan da baka siya masu.
Idan suka ga haka dole sufara tunanin komawa wajenta, kuma kaga yarana sune abaya, domin iyakar abinda kasiya masu dashi kadai zasuyi amfani, su kuma sunacin kashi 2. To wallahi seka dauki mataki, idan kuma baka dauka ba, nizan dauka saboda kare yarana.
Bazan zauna ta nakasa mani yara ba, yanzu gaba daya Fahad ya kangare, yaro me nutsuwa me kunya amma yanzu beda ita, ga rashin kokari, haba ai abun yayi yawa. Malan yace kiyi hakuri, seyanzu na fahimci komai.
Kuma nayi dana sanin dukansu, kuma zan basu hakuri, tabbas ba laifinsu bane, daga yanzu bazan kara dukansu ba, ita kuma ita da mijinta zan dauki mataki akansu, idan sukayi wasa wallahi daga Fatimar har Faisal din zan maidosu Day anan garin.
Kinga bazata kara ganinsu ba. Kiyi hakuri zan dauki mataki sosai, bazan bari wannan karon Jamila taci nasara akai na ba. Sosai Mama taji dadin abinda Malan yace, aranta tana fadin yanzu naji batu, amma kawai ka kama yarana kana jibgarsu, kuma wallahi sena saka ka doki Fatima Da Faisal kamar yanda ka doki yarana.
**** ****
Bayan kwana biyu da faruwar haka, malan yakira Farida da Fahad ya basu hakuri kuma yace surika yawan addu'a saboda sharrin makiya. Haka Mama ta sasu daki tana tambayarsu dalilin da yasa basa kokari? Fahad ne cikin gungunai yace kawai Mama yanayi ne.
Mama tace to inaso ku kara dagewa, nasamu nayima Malan dabara daga yanzu baze kara ganin laifinku idan bakuyi kokari ba. Fahad yace Allah Mama sena rama dukan da Malan yayi mani akan Faisal, kinga yanda yake mani dariya shida wannan munafukar.
Mana tace kabarni dasu, kasan de Faisal yafi karfinka, yanda Malan ya dokeku haka zansa ya dokesu. Farida tace wallahi Mama bakiga mijin Inne ba, kudi gareshi, kinga acikin motar da sukazo, kamar wani gwamna.
Yanzu Fatima ta samu wata kawa 'yar gidan 'yan gayu ko kallona batayi amakaranta. Bakiga uban naman da Inne takawo mata ba, amma seda ta bani, niko ban bata nawa ba, kema Mama kirika zuba mata idan kin dafa mani.
Mama tace Farida kenan, ke yarinya ce, Fatima tafiki wayau, kada kiyarda da duk abinda zata maki, so take ta fiki kokari idan tazo wajenki kidena kulata, banaso ta koya maki mugun hali. Murmushi Farouk yayi yace kema de Mama kin cika wata magana.
Taya Fatima zata koyama Farida mugun hali? Duka nawa suke su duka, kede kawai baki son su ne. Hannu Mama takai ta bige mashi baki tana fadin wallahi kashiga hankalinka dani, wai meyasa kakeso ka rai nani ne? Dama fa nasan kai baka bin bayana.
Fahad da Farida su kadai sukeson suga farin ciki na, bakasan irin bakar wahalar dana sha awajen Inne bane shiyasa, lokacin da aka aurota kai kana yaro bakasan komai ba.
Shine yanzu kake goyama yaranta baya. Farouk yace koma menene ai yanzu bata gidan, be kamata kirika nuna masu haka ba, kinga ita Farida bata ba ta abincinta ba, amma ita Fatimar ta bata.
Kuma kinga yanzu Innensu zata rika je mata visiting da kaya masu yawa wanda sukafi na Malan, ai ba zakiji dadi ba idan Fatima ta hana Farida ko? Mama tace tashi kabani waje, kuma daga yanzu kada ka kara zama akusa dani matukar zaka rika kawo mani irin wannan maganganun. Banza wanda be kishin Uwarshi.
Tashi Farouk yayi yana murmushi yafita. Fahad yace ai dama wannan Yayan yafi goyon bayan Faisal, ko muna kwance adaki sekiji yana bashi labari amma banda ni. Mama tace ka kyaleshi, kaide kada ka biye mashi, banaso ka sakarma Faisal fuska. Kutashi muje kitchen.
**** ****
Amira ce take ta kuka wai se an kaita wajen Yaya Faisal, su Munnir, Abba da Saddik se dariya suke mata, Maman Saddik har ta gaji da lallashi. Da sallama Baban Saddik yashigo yana fadin wai me akayima Mamana ne? Saddik ne yace wai wajen Yaya Faisal take. son zuwa.
Kuma munje gidansu a kulle. Zama yayi yana fadin zo muji abinda kikeso. Bade wajen Yaya Faisal zakije ba? Kai ta daga tana goge idonta. Baba yace karki damu zamuje ki ganshi kinji.
Murmushi tayi, tana fadin to yaushe zamuje? Baba yace se ranar da babu islamiya se muje, ai tunda yanzu kina kokari amakaranta duk abinda kikeso zanyi maki. Kinga yanzu ke kadai ce a Primary, Saddik yatafi ya barki.
Amira tace nima to akaini Secondary Baba. Dariya suka sa Mama tace to ai yanzu ajinki 4 damma sunga kina kokari yanzu shiyasa suka maidaki can, ki bari idan kika shiga aji 5 se akai ki JSS 1.
Baba yace ai nayi matukar mamakin kokarin Mamana, ban taba tunanin Mamana zatayi kakori a makaranta ba, amma kuma kome akace Allah angama magana, shiyasa na fada maki bana dana sanin kashe mata kudi.
Saboda haka zan nema mata Secondary din makarantarsu, duk da sunyi first term kawai su dauketa haka, ai Mamana ta zaunu a Primary, ki duba fa Saddik kaninta ne, amma yanzu yana JSS 1.
Idan mukace seta gama Primary lokacin fa Saddik yashiga JSS 3, dama me akeso, ta gane abinda ake koya mata, kuma alhamdulillah, yanzu babu abinda Mamana bata sani ba, matsalarta daya har yanzu akwai yarinta ajikinta.
Wannan kuma bawani abu bane, duk ranar da tayi aure hankali zezo mata. Dariya Mama tasa tana fadin kaji Baban Saddik da wata magana, wai aure? Baba yace emana, kinsan yawancin masu irin wanna matsalar silar aure tana kawo masu sauki.
Shiyasa nake rokon Allah yabata miji nagari. Mama tace yanzu de maganar makaranta akeyi, yarinyar da ko Primary bata gama ba kake maganar miji. Baba yace ai dole inyi. To naji, yanzu de kinji abinda nace.
Allah gara ta tafi secondary haka nan, amma bazan kaita boarding ba, gara tazauna a private dinsu, ta saba da malaman su, kuma sun san matsalarta duk da yanzu wasu malaman zata samu amma yafi ace inda tasani ne.
Mama tace hakan ma yana da kyau. Allah yasa su amince. Baba yace zasu amince ma, private ce kudi kawai sukeso, kuma sun san yanda ta dade amakarantar ba zan sha wahalar amincewarsu ba.
Kuma kinga karin dadin amakarantarsu zan barta. Kallon Amira yayi yace Mamana kema wannan term din zaki shiga JSS 1. Tsalle Amira tayi tana murna hada rawarta tana ma Saddik gwalo. Su Abba se dariya suke mata.
Turo baki Saddik yayi yana fadin gaskiya Baba ba zamu zauna aji daya da ita ba. Dariya Baba yayi yace ai kai boarding kakeyi, ita kuma Day zatayi, kaga ba makaranta daya ma zaku zauna ba. Murmushi yayi yana fadin ai de baza arika maki provision ba.
Amira tace wai haka Baba? Baba yace rabu dashi, kullum se an saka maki biscuit acikin kwandon makarantarki, gwalo tayi mashi, ze kara magana Mama tajawoshi tayi mashi rada. Murmushi yayi yana fadin iye, Amira 'yan JSS 1.
Zulai ce tashigo tana ta sallama, da sauri Mama tafito tana amsawa, dariya tayi tana fadin ashe kece, ina ciki ina fama da yara na sasu aiki. Zulai tace aifa yara sun dawo hutu se hayaniya.
Mama tace kishigo mana, zaune suke afalo suna fira Fatima ta fito da kayan miyan data gyara tana fadin Mama nagama akawo kudin markadan. Harararta Mama tayi tana fadin atsaye zaki mun magana, kuma bakiga bakuwa ba? Dukawa Fatima tayi tana fadin ina kwana.
Zulai tace lafiya lau, ke kam baki dago kai kike sunne kai kamar wata munafuka? Mama tace ai itace, kema kenan da baki santa ba, gashi daga zuwanki har kin ganota. Zulai tace kadde itace Fatimar? Mama tace itace fa me hali irin na Uwarta.
Tabe baki Zulai tayi tana fadin sannu da kokari Maman Farida. Naaira 20 Mama ta wurga ma Fatima tana fadin kuma kimun sauri kizo kidora girkin kada Malan yadawo yasamu ba'a gama ba.
Bayan ta fita Zulai tace ita ce take maki girki? Mama tace to mezatayi? Ai duk aikin gidan nan itace takeyi ita da Yayanta, domin Uwarsu ta sangartasu, komai itace take masu shiyasa yanzu nake horar dasu.
Zulai tace wallahi kinyi dabara, ai dama rikon Dan daba naka ba, sekayi da gaske, domin idan ya lalace kai za'a zarga, gara aga kana matsa mashi ayi gulmarka da kyau, duk ranar daya zama mutum za'a gane abinda kake nufi.
Mama tace kema de kya fada, damma ina taka ma Malan burki akansu, ai da yanzu yarana sun koma baya, kinsan duk yaran da aka ce Uwarsu bata gida Uba yafi sonsu, gani nayi yana so ya maida mani yara Saniyar ware yasa nima na bullo da nawa makircin.
Shewa Zulai tasa tana fadin shiyasa nake sonki, baki barin seta kwana, wallahi ina bayanki, me ake da Dan kishiya, wallahi duk yanda ka rikeshi banza kake awajenshi, ke koda tun yana jariri kika rikeshi ida ya girma yagane ba kece kika haifeshi ba, wata rana seya yi maki butulci.
Bare su da aka barsu da wayonsu. Ai se kinyi da gaske sannan ki kwaci kanki. Mama tace ke damma na iya allo na awajen Malan ai da tuni nazama abin tausayi, yana bala'in daukar maganata, domin nidin bakin ganga ce.
Zulai tace duk inda aka buga zakin daya ne. Dariya suka sa, Faisal ne yafito fuskarshi a daure, dan duk abinda suke fada yaji, ko kallon inda suke beyi ba ya nufi hanyar waje. Mama ce ta daka mashi tsawa tana fadin gidan Uban wa zakaje? Tsayawa yayi amma be jiyo ba.
Mama tace ba magana nake maka ba? Kuma bakaga bakuwa ba zaka wuce ta babu gaisuwa ko haka Uwarku ta koya maku? Kwalla ce tacika idon Faisal bece komai ba ya nufi waje. Da sauri Mama ta tashi ta fisgoshi ta baya harseda rigarshi ta yage.
Zulai tace lallai Maman Farida kin sake ma yaran nan, kamar wannan abun har ya isa kiyi magana ya kyaleki? Hannu Faisal yasa yana fadin ki sakar mani riga. Farouk ne da Fahad da Farida suka fito jin hayaniya.
Suna fitowa Mama tafara fadin dani zakayi fada Faisal? Faisal yace ni yaza'ayi nayi fada dake, kawaide nace ki sakar mani riga. Hannu yasa yakara kama hannunta. Kukan munafurci Mama tasa tana fadin yau naga ikon Allah.
Ni kake zagi Faisal? Kokarin kwace jikinshi yakeyi, ita kuma Mama tana kara matsowa jikinshi kamar masu shirin dambe. Fahad da zuciya ta gama ciyoshi yace kai Faisal bakada hankali da Mamar zakayi fada? Faisal yace ina ruwanka.
Ko nasa da kai? Sosai wannan maganar ta batama Farouk rai, matsowa yayi ya wanke Faisal da mari, Mama ma ta kara wankeshi da mari. Dun kule hannu Faisal yayi ya kaima Farouk naushi, tsautsayi yasa hannunshi ya sauka a idon Mama.
Wani irin ihu tasa tare da dukewa kasa. Ganin haka da Farouk da Fahad suka rufarma Faisal da duka, shima haka yarika dukansu ta ko ina, amma dayake Farouk yafishi karfi kuma gasu su biyu hakan yasa sukafi karfinshi.
Zulai da taga abin yaki karewa tayi saurin fita takira wani namiji yazo ya rabasu da kyar, duk an fasama Faisal baki, shima kuma yaji masu ciwo. Mama kuwa tana gefe ta dafe idonta da yayi Ja lokaci guda.
Fita Zulai tayi tana fadin se anjima Maman Farida zuwa gobe zan dawo. Wucewa daki Faisal yayi yashiga bandaki yana wanke jikinshi, Fatima ce tashigo, ganin kowa yayi shiru yasa ta wuce kitchen, bayan ta aje nikan ta nufu dakinsu Faisal.
Zaune ta sameshi yana ta kuka, saurin karasawa tayi tana fadin Yaya waya dukeka? Hannunta yakamo yabata labarin abinda yafaru, cikin kuka Fatima tace wallahi nima haka tayi mani, kayi hakuri Yaya Allah ze saka maka.
Faisal yace wallahi ba dan ke ba da yau katsina zan tafi, Fatima tace a'a Yaya kayi hakuri, kasan Inne tace muyi hakuri da duk abinda za'ayi mana. Kaga nima yanzu girki Mama tasani, Faisal yace zauna bazakiyi ba.
Bugo kofar dakin akayi, suna daga kansu sukaga Mama ce, wajen da Faisal ya bigeta har yayi baki gaba daya zagayen idon. Kallon Fatima tayi tana fadin bazaki tashi kidora girkin ba sena sa kema an zaneki? Ai ni wallahi naji dadi.
Daga yanzu bazan kara bata bakina akanku ba, tunda Allah yasa yarana sun kawo karfi sune zasu cigaba da rike gidan nan, kuma dani kuke magana, kujira dawowar Malan. Ke kuma kada kije kidafa abincin.
Fita tayi tana masifa, tashi Fatima tayi tana kuka, rikota Faisal yayi yana fadin wallahi ba zakije ba, ko kinje kinyi aikin seta hadamu da Malan, gara ki kiyi tafada da hujja. Fatima tace nide Yaya ina tsoron Malan, kuma kaji tace zatasa adukeni. Kwace hannunta tayi ta nufi kitchen. Kara fashewa Faisal yayi da kuka, yana matukar tausayin Fatima.
Zaune suke gaba dayansu afalo, Mama se kuka takeyi tunda Malan yashigo, gashi yaga idonta yayi ja kuma gefen yayi baki, tambayar abinda akayi mata yayi, Farida ce tace Yaya Faisal ne ya nausheta a ido dan tace ina zeje.
Saurin kallon Faisal Malan yayi, shima ga bakinshi nan afashe. Cikin kuka Mama tace tunda nake da kai ban taba bata maka rai ba, narike maka yara tsakani da Allah, amma yau nice yaranka zasu hade ma kai, shi Faisal ma hada naushi na.
Ita kuma Fatima na sata aiki tace bazatayi ba. Allah yasani nayi iyakar yina, bazan iya zama ana cimani mutuncina da girmana ba, domin nima na haifa, kuma babu wani Dan da zega ana dukar Uwarshi ya kyale.
Badan ina zaune da yaranka lafiya ba, Allah kadai yasan abinda zaka dawo ka iske a gidan nan, domin nice na raba fadan da akai tsakanin Fahad da Faisal, domin Fahad baze iya ganin ana dukana ya kyale ba, shima Farouk dan na hanashi ne.
Amma wai har Fatima tasan tashigar ma dan uwanta, wannan wace irin rayuwa ce haka, gaskiya idan har baka dauki mataki ba wallahi sena bar maka gidanka, idan yaso seka zauna da yaranka ni kuma in koma gidanmu.
Malan yace haba Hauwa meyayi zafi haka? Ai ko dabba inde ta gidan nan ce zata iya bada shedar yanda kike zaune da yaran nan, kuma ni ba sakaran Uba bane, bazan lamunci irin wannan rashin tarbiyar agida na ba.
Kallon Faisal yayi yace kaji abinda tace, anyi haka ko ba'ayi ba? Mama tace karyata ni kake ma? Malan yace niba karyataki nakeyi ba, inso ya amsa da bakinshi ne. Ina tambayarka? Shiru Faisal yayi hawaye ne kawai suke zuba a idonshi.
Cike da bacin rai Malan ya wanke shi da mari, tashi yayi yadauki dorinarshi, haka yakama Faisal da Fatima ya zanesu, Fatima se kuka takeyi tana boyewa bayan Faisal, shiko se kara kareta yakeyi.
Malan kuwa dukansu yake yana fadin yara kanana daku har kun isa ku raina matata, wato Uwarku taje wajenku tayi maku mummunar hudu ba, shiyasa da kuka dawo kukazo da sabon rashin kirki.
Ada ai ba haka kuke ba, se yanzu da taje wajenku, to wallahi zan iya maido ku Day ba damuwata bace, bazan zura ido ina gani abata mani yara ba. Ganin dukan da yake masu yasa mama tace kabarsu haka nan ai sun daku.
Wurgar da bulalar yayi yana fadin gobe ma ku kara. Sosai suka bama Farouk tausayi, domin yasan ba gaskiya Mama ta fada ba, kawai de baze iya karyata ta bane. Sosai jikinsu ya fashe, Fatima se shashsheka takeyi.
Mama tace kayi hakuri nasa ranka yabaci, abun ne naga kada yayi yawa shiyasa na fada maka, amma ba wannna bane karo na farko da suke mani rashin kunya, kawai banason yawan kawo karar sune, domin suma yarana ne.
Amma na yau yayi yawa shiyasa na fada maka, gashi nan ranka ya baci abanza. Malan yace ke zan bama hakuri, kuma daga yau bance ki kara boye mani duk abinda sukayi maki ba, shi icce tun yana danye ake lankwasa shi.
Nan gaba bamusan abinda zasuyi ba, nagode da irin kaunar da kike nuna mani. Kuma zan kira Alhaji Mansur ince yajama matarshi kunne, idan kuma taki zan maidosu Day. Kutashi kubani waje, yaran Banza kawai.
Ruwa Mama takawo mashi tana fadin dan Allah kasaki fuskarka, banaso ina ganin bacin ranka, da na san haka ne ma daban fada maka ba. Murmushi Malan yayi yace shikenan yawuce, amma zamuje chemist aduba mani idonki, dan banzan yaro ze bata mani fuskar mata. Murmushi Mama tayi tana fadin ai yarinta ce, aranta tana fadin burina yacika tunda ka dokesu.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[4/3, 5:38 PM] nabilalady5: π‘π‘ A WANI GIDAπ‘π‘
πππ
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey