Trending Hausa Novels

A Wani Gida

Reading file: A_WANI_GIDA.txt

Chapter 4 of 6

Part 65 ⏩ 70

Zaune su Farida da Fahad suke adakin Mama, da ka kalli fuskar Mama kasan ranta abace yake. Dago ido tayi ta kalli Farida, gyaran murya tayi tace Farida tashi kije gidan Maman Sultan kice ta bani kayana da na bari jiya agidan ta.

Bayan Farida ta fita Mama ta kalli Fahad, dama bata son tayi mashi magana agaban Farida ne shiyasa ta aiketa. Fahad! Dago jajayen idonshi yayi ya kalleta, ganin fuskarta babu alamun wasa yasa yakara nutsuwa.

Meya sami idonka yayi ja haka bayan kuma baka da ciwon ido? Dukar da kai kasa yayi yace wani abu ne ya fada mani a ido. Mama tace bana son karya, kafada mani abinda kake sha? Fahad yace yoni me zansha.

Mama tace kwanaki kuna makaranta kun hadu da Farouk? Saurin dago kai yayi yana kallonta. Tambayarka nakeyi kun hadu? Fahad yace E, awane waje kuka hadu? Mama makarantar mu yaje fa.

Amma ba cikin makaranta ya ganka ba. Shiru Fahad yayi yana zare ido. Fahad irin rayuwar daka daukar ma kanka kenan ko? Yanzu ba kajin kunya su Faisal su san halin da kake ciki? Bakasan zasuyi mana dariya ba.

Me kake tunani idan Malan yaji wannan magana? Kuma kasan yana jin haushinka saboda yanzu baka maida hankali akan karatunka ko? Yanzu Fahad duka shekararka nawa da zaka fara shaye shaye? Kuma ba sigari kadai kake sha ba.

Bakasan kwakwalwarka zata iya samun matsala ba? Kuka Mama tasa tana fadin so kuke bakin cikin ku ya kashe ni? Kai ka fada shaye shaye, ita kuma Farida ta fara bin maza. Haba Fahad, kai ne wanda kafi kowa sona duk cikin yara na.

Meyasa yanzu kuma zaka zamo wanda zesani cikin damuwa? Dan Allah Fahad ka rufa mani asiri kadena wannan halin banzan, idan baka sani ba nasan kana mani dauke dauke. Fahad yace ni gaskiya Mama bana sata.

Mama tace bana son gardama, idan ma ba kayi to kasani shaye shaye babu abinda baya sawa, kuma se yanzu na gano dalilin da yasa kake da zafin zuciya yanzu, halinka ya canza Fahad, ka daure ka canza wannan halin.

Kuka Mama takeyi sosai. Fahad yace Mama kiyi hakuri daga yau na dena duk abinda nakeyi. Mama tace Allah yasa Fahad. Tashi kaje kuma bazan fada ma Malan ba, banaso ya kara jin haushinka. Dadi Fahad yaji jin tace bazata fada ma Malan ba, aranshi yana fadin da sauki ma.

Bayan Fahad ya tafi Farida ta dawo daga aiken da akayi mata. Haka Mama ta sata gaba tana tambayarta metayi amakaranta, Farida Kamar zatayi kuka tace Allah Mama babu abinda nayi. Mama tace amma ya akayi Malaminku ya aiko da takarda abama Malan? Farida tace wallahi ba wata takardar daya bani.

Mama tace ai Fatima yaba, kuma Farouk ya karanta mani duk naji abinda kikayi. Farida tace wai fa Mama daga yazo same mu nida kawata a class munje wajen wani dan ajinmu bayan antashi daga pref muka tsaya ya nuna mana aikin da aka bamu shine fa Malamin yazo yace wai iskanci mukeyi.

Mama tace kenan bake daya bace? Farida tace mu 3 ne fa. Kuka Farida tasa tana fadin kin gani ko za'a jamani sharri, dama Malamin ya tsaneni yafison Fatima saboda wai ni bana mashi magana.

Tsaki Mama tayi tana fadin ai dama nasan karya ne, na sanki bazaki iya aikata abinda akace ba, dama Fatima akace zan yarda domin ba tada abokan wasa se yan gidansu Amira.

Kuma ba tajin kunyar taba namiji. Farida tace damma bakiga yanda sukeyi da mazan ajinsu ba, wai se su zauna suce karatu sukeyi basa komawa daki da wuri. Mama tace ki rabu da ita, in Allah ya yarda seta debo ma Malan da Inne abin kunya.

Bade ita yakeso yanzu ba, kibarshi ai duniya zata koya mashi hankali. Abinda nakeso dake ki kara dagewa kada kibari wannan karon akara maidoki baya. Farida tace zan dage sosai, itama Fatimar ai kawarta ce take bata satar amsa. Mama tace kirabu da ita ai duk nasan komai, ba kokarin ta bane.

Zaune Faisal da Farouk suke a kofar gidansu saman benci suna fira, Farouk yana ta bama Faisal labarin makarantarsu. Faisal yace ai nima idan nagama makaranta duk makarantar dana samu tafiya zanyi.

Kaga yanzu ka huta, nasan akwai abokanka da yawa da suke zaune basu tafi makaranta ba saboda basu sami wadda suke so ba. Farouk yace da yawa ma. Shide Mannir yaci sa'a ya samu Federal University Dutsinma, muna haduwa dashi wani lokacin.

Faisal yace haka Abba yake fada mani, bakomai kowa da rabonshi, kuma kasan kowa yana tafiya da sa'arshi, se kaga wani yafika da wani abun kaima kuma seka fishi da wani abun. Farouk yace hakane. Amma gaskiya ko na gama makaranta zanyi kokarin neman aiki a katsina.

Faisal yace meyasa? Farouk yace kawai ni banajin dadin zaman gidan nan yanzu. Jinjina kai Faisal yayi yace amma kana ganin Malan ze barka? Kuma ma a Katsina wajen wa zaka zauna? Farouk yace kaide Allah ya kaimu in gama, amma gaskiya bazan zauna garin nan ba.

Kaga wannan dinkin hular da nakeyi ba karamun samu nake ba, kuma tun yanzu nafara tara kudi, kafin ingama insha Allah nasan zan tara kudade masu yawa. Faisal yace Allah yasa, amma ko ni bazan zauna garin nan ba.

Fahad ne yataho yana wani cika yana batsewa, domin tunda Mama tace Farouk ne yafada mata abinda yake aikatawa yake jin haushinshi, kuma ko da yafita daga gidan seda yaje yayo shaye shayenshi sannan, yanzu haka daga can yake.

Ko kallonsu beyi ba yashige cikin gida. Girgiza kai Farouk yayi bece komai ba. Faisal ne yace Yaya nikam akwai abinda na dade inaso in fada maka, sede bansan yanda zaka dauki maganar ba. Farouk yace maganar Fahad ce ko? Faisal yace E.

Murmushi Farouk yayi yace nima nasani, domin agaban idona nagashi yana shan wiwi, Faisal yace bayan sigari yanzu har wiwi yakesha? Farouk yace to wama yasan iyakar abinda yakesha, nide abinda nasani kenan.

Faisal yace amma Yaya ai be kamata ace anyi shiru ba. Farouk yace nayi mashi magana, kuma na fadama Mama kuma tace zatayi mashi fada. Faisal yace amma baka ganin yakamata Malan yasani? Farouk yace Mama tace kada afada mashi.

Kuma kasan halin Malan ze iya zaneshi kuma yace babu ruwanshi dashi. Faisal yace haka ne, Allah ya kyauta. Farouk yace amin. Faisal yace yaushe zaka koma Yaya? Farouk yace gobe. Tashi Faisal yayi yana fadin bara inje gidansu Amira kafin akira sallah. Farouk yace kai da Amira kode? Murmushi Faisal yayi yace kawai de mun saba da ita ne. Farouk yace to Allah yatemaka.

***** *****

Haka hutunsu yakare sam Fahad be dena abinda yakeyi ba, sema karuwa da abun yayi, dan da an bata mashi rai to seya sha, kwata kwata yadena zama gidan sosai, komai yace yatafi gidan Hajiya, itako inde yaje seta bashi kudi.

Gashi yanzu son kudinshi yayi yawa, ga roko duk inda abokan Malan suke seyaje ya gaishe su, sata kuwa sede idan ba'a aje ba. Malan tun yana mashi fadan kai dare awaje har yadena, domin duk lokacin da yayi mashi fada to aranar se sunyi fada da Mama.

Farida ma babu abinda ya canza sema abinda yayi gaba, haka suka shirya suka koma makaranta, danshi Faisal daga wannan dawowar sede yazo sallah amma se sun gama zasu dawo gaba daya.

Lokacin daya koma makaranta shida Nura haka Saleem ya sashi gaba yana ta tambayarshi Fatima, Faisal se yanga yake mashi yana fadin seka bani cin hanci zan fada maka.

Seda Saleem yayi kamar zeyi kuka sannan Faisal ya bashi wani zobe da Fatima ta bada akawo mashi Saleem yace dan rainin wayau, Faisal yace wallahi zan anshe. Faisal yace ina Lubna fa? Saleem yace nima bansani ba.

Faisal yace kada kasani, Nura yace Saleem Amira zaka tambayeshi, dariya Saleem yayi yace ka kyaleshi, mun rasa ma wane fanni yake, maganarshi dama bata wuce Fatima, Amira se Lubna.

Faisal yace ai dole in fadesu domin su 3 suna da matukar muhimmanci agareni. Fatima de kanwata ce wadda duk duniya babu wanda nakeso sama da ita, kai kanka saboda yanda kake nuna kulawarka akanta yasa na amince maka.

Amira kuwa jini na da nata ne a hade, bansan irin shakuwar da mukayi da ita ba. Lubna kuwa itace wadda ta debema Fatima kewa kuma ta nuna mata yanda rayuwa take. Wannan dalilin ne yasa nake son su gaba daya.

Nura yace kila de Mata biyu zak aura. Dariya sukasa Faisal yace kutashi mutafi masallaci an kusa kiran sallah. Saleem yace tunda anyi maganar aure ai dole kace atafi masallaci, bayan saura minti 15 akira sallar. Faisal yace E naji koma me zakuce.

Zulai ce ta kira Mama tana tambayarta ina ne gidansu gata tazo Mani, cike da Farin ciki Mama tace da gaske? Zulai tace wallahi da gaske nakeyi, biki mukazo katsina ni kuma na tambaya akace mani babu nisa shine na taho.

Mama tace yanzu kina ina? Zulai tace gani nan an sauke ni atasha, Mama tace samu me mashin ki bani shi. Bayan Zulai ta samu me mashin ta bashi wayar. Kwatancen gidan Mama tayi mashi yace yasan gidan, dan babu wanda besan Malan ba.

Da sallama Zulai ita da wadda suke tare suka shiga gidan Mama, fitowa Mama tayi tana fadin sannunku da zuwa, ashe ma ku biyu ne? Zulai tace wallahi kuwa nida kanwata ne. Mama tace kushigo.

Bayan takawo masu ruwa da abinci sunci nan suka fara gaisawa. Mama tace amma naji dadin zuwanki Zulai. Ban dauka zaki zoba. Zulai tace ai nafada maki sena rigaki zuwa, ke kam tunda kuka dawo nan ai nasan bazaki kara zuwa Faskari ba.

Dama kuma baki taba zuwa ba. Mama tace wallahi inda wani abu babba ya faru da ke da kin ganni, Zulai tace sede haihuwa ko biki, kuma babu wanda zanyi. Mama tace kai Zulai bazaki kira mu zuwa suna ba.

Zulai tace rufa mani asiri, dama ni ba wasu yara gareni da yawa ba. Mama tace ai kin huta, ya sunan kanwar taki? Zulai tace Suwaiba, itace autar mu. Mama tace Allah sarki ba tayi aure ba kenan? Zulai tace kinsan itace auta seda tayi karatu sannan.

Mama tace ai taji dadinta, yanzu se aiki ko? Zulai tace tana aikin ma, ai agidan Yayanmu take zaune anan Katsina, to anan tasamu aikin koyarwa. Mama tace Allah yakawo miji nagari to. Zulai tace amin.

Wai ya naji gidan shiru ina yaran suke? Mama tace ai duk suna makaranta. Zulai tace haka fa, amma ai Farouk ya gama ko? Mama tace yagama har yatafi wata makarantar. Zulai tace lallai Maman Farida kin kusa hutawa, ace babban danki har yashiga jami'a.

Wane gare yake? Mama tace na'am, E, a jami'ar Ummaru Musa yake. Zulai tace lallai ya more, kinga nan da wani lokaci kema zaki fara cin albarkacin 'ya'ya. Murmushin yake Mama tayi tace ai kuwa.

Sam ba taso Zulai tasan Farouk ba Jami'a yake ba, dan bataso a rai nata. Zulai tace ina kuma su Fatima? Mama tace munafuka tana makaranta, Zulai tace amma yanzu takara girma ko? Mama tace sosai ma, baki gantaba, yarinya tun bata gama secondary ba amma ta koma kamar wata uwar mata.

Sam bata da kirar mata, ni tsoro ma nakeji kada afara tanka mana gida, kuma gashi Malan yace se sunyi karatu zasuyi aure. Zulai tace kada taje tajawo maku abun kunya fa.

Mama tace wallahi kamar kin sani, yanda take ganin ta girma tazama budurwa se shige ma maza takeyi, shiyasa yanzu na hana Farida taje kusa da ita dan yanzu zata iya canza mata hali.

Zulai tace kede ki kula da diyarki, idan ta kwaso abun kunya ki korama uwarta ita. Mama tace dama waze zauna a juye mashi abun kunya agida. Mama tace amma de Zulai nan zaku kwana ko? Zulai tace dama cewa nayi kwana zamuyi musha fira.

Mama tace amma naji dadi, sallamar Malan ce ta katse masu firar da sukeyi. Tashi Mama tayi tana fadin sannu da zuwa Malan, murmushi yayi yace yauwa baki mukayi ne? Mama tace wallahi Zulai ce da kanwarta suka kawo mana ziyara.

Tazo biki Katsina shine tazo, nan ma zasu kwana dan sun gama bikin. Malan yace lallai ta kyauta, muje mugaisa ko. Malan yana shiga suka hada ido da Suwaiba, seda gabanshi ya fadi, lokaci guda yaji ta burgeshi.

Zulai ce tace Malan sannu da zuwa, zama yayi yana fadin yauwa Zulai sannunku da zuwa, tace yauwa ina wuni? Yace lafiya lau, ya megidan naki? Tace lafiya lau yana gaisheka.

Ai suna cewa sunyi kewarka. Suwaiba ce ta dago kai tace ina wuni? Murmushi Malan yasaki yana fadin lafiya lau, kunzo lafiya? Tace lafiya lau. Mama tace autar su Zulai ce, itama malamar makaranta ce.

Malan yace da kyau, Allah yatemaka, a Faskarin take itama? Zulai tace a'a a Katsina take, Malan yace Allah sarki, acan take aure ko? Mama tace ai batayi aure ba karatu tagama.

Murmushi Malan yayi yace yayi kyau, tun da angama karatu har ana aiki ai se ayi aure ko, Zulai tace kaima de ka fada, har yanzu Suwaiba taki tsayawa ta fitar da miji. Washe baki Malan yayi yace to ai aure ba'ayi mashi gaggawa, gara ta tsaya tafitar da wanda ranta ya kwanta dashi.

Mama tace wannan haka yake, domin abunda yake kawo yawan mutuwar aure hada rashin tsayawa a gama fuskantar juna. Tashi Malan yayi yace bara inje indawo, yau muna da manyan baki ai dole mu karramasu.

Ai mijinki Zulai mutumin kirki ne. Mama tace ai dagashi har ita haka suke, shiyasa duk a unguwar munfi shiri da ita. Zulai tace mungode. Mama tace baza kaci abinci ba sannan? Malan yace bara indawo. Tashi Suwaiba tayi tana fadin zanyi sallah.

Mama tace to kishiga ciki dauki kayan akwai bandaki aciki. Tana tafiya suka cigaba da firarsu, sam babu wanda yatashi domin yin sallah.

*** ****

Washe gari tunda safe Malan yace ma Mama zeje katsina, Mama tace lafiya de? Malan yace inaso inje induba wani abokina da aka kwantar a asibiti. Mama tace to ko su Zulai su shirya kawuce dasu, kaga nima se inje mu duboshi kada kutafi ku kadai nasan bazakaji dadi ba tun da baku saba ba.

Malan ya daure fuska ganin zata rushe mashi plan, danshi saboda Suwaiba ya shirya wannan tafiyar. Mama tace dan Allah Malan katafi dasu kaga zasu rage kudin mota. Malan yace sede inbasu kudin mota.

Mama tace toshikenan hakan ma yayi. Saurin kallonta yayi danshi latsa ta kawai yayi dan kada taga yayi saurin amincewa. Harta juya yace naga kamar kin bata rai? Mama tace wallahi ni ban bata rai ba. Malan yace wallahi kin bata rai, Mama tace a'a.

Ai nasan halinka ba kason tafiya da matan da baka saba dasu ba, shiyasa nace inshirya mutafi tare. Malan yace a'a kiyi zamanki, zan tafi dasu kawai dan kawarkice, kuma sunzo har sun kwana.

Murmushi Mama tayi tace amma nagode. Malan yace kice su shirya. Tana fita ya saki ajiyar zuciya, aranshi yana fadin zan jama kaina, an mun tayi ina wani sharewa.

Haka Mama ta bama Suwaiba turare Zulai kuma ta bata barkono da kuka. Godiya sukayi mata suka tafi, sede Malan cema Mama yayi su shiga baya dan bayaso adauka wasu ya dauko, seda Mama taji dadi daya fadi haka.

Shiyasa suna fita ta bude masu baya tace su shiga, sosai Zulai tayi mata godiya, haka suka tafi zuciyar Malan cike da farin ciki.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[4/9, 1:34 PM] nabilalady5: 🏡🏡 A WANI GIDA🏡🏡
😭😭😭

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.