Trending Hausa Novels

A Wani Gida

Reading file: A_WANI_GIDA.txt

Chapter 6 of 6

Part 75 ⏩ 80

Malan ne ya fito daga gida yana shirin tafiya sabon shagonshi da aka gama ginawa domin ya duba aikin da akayi, Mama tana biye dashi abaya tana ta masifar seya fada mata dalilin da yasa yanzu baya kulata, kuma baya sakar mata fuska.

Shikam yayi banza da ita bayan ya fitar da motarshi ya koma domin rufe gate din. Mama tace Malan da fa kai nake magana. Malan yace ina ganin kin fara samun tabin hankali, domin babu wata mace me hankali da mijinta zefita ta biyoshi da irin wannan haukan da kike yi.

Ina a gidan nan na kwana? Me ya hana tun jiya da dare idan kina son magana da ni bakizo dakina kikamun ba? Saboda kina tashen iskanci shiyasa kikayi kwanciyar adakinki dan kina tunanin idan na damu dake dole in biyoki.

Se kuma yanzu dan rashin hankali zan fita ki biyoni har bakin gate kina daga mun murya. Idan kece kike iko dani dan Allah kicigaba da yimani irin wannan iskancin wallahi zakiga matakin dazan dauka.

Mutuniyar banza wadda duk kissar da take takama da ita irin ta jahilan mata ne. Gate din yarufe yabar Mama da sakin baki. Har zeshiga mota yaga School Bus ta Dutsinma tana karasowa.

Maida murfin motar yayi ya kulle, tsaye yake har suka karaso, haka nan yaji gabanshi se faduwa yakeyi. Vice yafara ganin yafito hakan yasa yasaki murmushi, shima Vice din murmushi yayi se kuma duk yaji babu dadi.

Sanin abinda yakawosu. Malan yace ikon Allah kaga mutanan Dutsinma, yau kaine da safen nan. Sauran malaman ne suka fito se kuma ga Fahad yafito yana dauke da jakarshi se katifarshi a kulle.

Fuskarshi duk a kumbure take, jikinshi duk datti sannan ga sahun bulala awuyanshi da hannunashi. Kurama Fahad ido Malan yayi jikishi duk yayi sanyi, bayan sun karaso Vice ya kalli Fahad yace shiga daga ciki.

Hannu yabasu suka gaisa Malan yana fadin kushigo daga ciki mana. Vice yace kai bama se mun shiga ba, Malan yace haba ai bazamu tsaya anan ba, dan Allah kushigo. Zaune suke afalo Malan yasa Mama takawo masu ruwa dan ita bama tasan Fahad yashigo ba, dan yana shiga yayi part dinsu yana Kuka.

Bayan ta gaishesu ta tashi zata fita Vice yace ai Hajiya da kin zauna wajenku mukazo gaba daya. Malan yace to Vice Allah de yasa lafiya, dan ban gamsu da ganin da nayima Fahad ba, gashi kuma se gobe ne hutu yan Fedaral ne kawai zasuyi hutu yau.

Yanzu ma fitar da nayi zanje shago ne daga can inwuce in daukosu kuma se gaku? Gyara zama Vice yayi gaba daya kunyar sanar da Malan abinda danshi yayi yake, amma babu yanda ya iya haka ya zayyane mashi duk abinda yafaru har zuwa hukuncin da makaranta ta dauka, kuma ya nuna masu hoton daya dauka.

Kuka Mama tasa tana fadin wallahi bazan taba yafe maki ba, muguwa azzaluma me bakin hali, gaba daya kin gama lalata mani yarana. Malan da zufa ce kawai take zubo mashi ya daka mata tsawa yana fadin tashi kibar wajen nan.

Saurin tashi Mama tayi tana kuka ta nufi bangaren su Fahad. Malan ya dade beyi magana ba, da kyar ya iya bude baki yace Innalillahi wa inna ilaihirraji'un. Sosai yabama sauran mutanan da suke falon tausayi.

Vice ne yace Malan kayi hakuri, nasan kai babban Malami ne, asalima karike mukamin Principal, nasan kasha haduwa da irin wadannan laifukan har ma da wadan da suka fisu, na tabbata ko kai ne iyakar abinda zakayi kenan.

Kayi hakuri dama haka duk wasu iyaye suke fuskanta musamman idan akace sun tara zuri'a, dole se sunyi hakuri da duk wata kaddara tazata fado masu. Inde mutum yana da yara dole seya hada da addu'a musamman yaran zamanin nan.

Tunda har Allah yasa yana SS 2 abinda zefi ka maidashi Day, koba komai kullum agabanka ze tashi kuma ya kwana agida, zakafi samashi ido fiye da idan baya gabanka, kuma kada kace zaka dauki mummunan mataki akanshi.

Domin irin wadan nan ba'a juya masu baya alokacin da suka kauce hanya, alokacin ma yakamata afi jawosu ajiki, idan Allah yaso sekaga sun shiryu, amma idan aka watsar dasu wallahi abinda zasuyi se yafi na baya.

Yawanci manyan barayin da muke dasu da yara masu shaye shaye idan kaduba karuwar lalacewarsu hada sakacin iyayensu, domin wani Uban daga inda akace ya kama danshi da wani mugun hali shikenan se ya dora mashi karan tsana.

Wasu korar yaran suke daga gidansu, wasu kuma shikenan daga ranar yaran sun zama abun kyama da kyara agaresu, gaba daya se su fara nuna masu banbanci tsakaninsu da sauran yaran gidan, ko shawara za'ayi basa kiran su.

Gaba daya se kaga sun zare hannunsu daga kansu, idan karatu ne bazasu tsaya su kula da sunje ko basu je ba, yawanci Iyaye mata sune kadai zaka samu suna janyo masu irin wannan hali ajiki, domin Uwa tafi Uba tausayi.

Daga irin haka kuma se asaka ma yaron wani tunani na daban, idan be shan wani abun ma dalilin banzatar dashi da akayi se yaje yakara haduwa da wasu mugayen abokan sukara koya mashi wani abun.

Kuma shima daga lokacin daya fahimci an cireshi daga layin sauran yara shikenan shima baze kara shiga cikin sauran 'yan uwanshi yazauna ba, daga lokacin ze fara kebe kanshi, se kuma tunani kala kala yarika shigarshi.

Kadaici se yafara damunshi, idan ba'ayi sa'a ba yafara shan kwaya shikenan kuma ya gama kashe kanshi, ga damuwar abinda aka mashi, ga kuma aikin kwaya, shikenan se kaga yaro ya kangare, daga karshe idan be koma babban barwo ba, to kwakwalwarshi zata tabu.

Kaga duk abinda yaje ya aikata dan gidan wa za'ace? Dole akira sunan mahaifinshi ko mahaifiyarshi, kuma har ya mutu baza 'a cireshi daga cikin gidansu ba. Haka zalika duk iyayen daka ga wai yaransu yana cikin irin wanna halin sun ce sun manta dashi wallahi karya ne.

Kai koda tafiya yayi yabar gidan har abada bazasu taba iya cireshi daga zuciyarsu ba. Kaga kuwa babban rigakafin da yakamata iyaye suyi shine surika kokarin jawo yaransu masu irin wannan hali ajiki.

Hakan zesa yaro yarika jin kunyar aikata wani abu marar kyau. Kasan Allah, akwai wani abokina dana sani Allah ya hada yaronshi da wasu mugayen abokai, haka suka koya mashi shaye shaye na fitar hankali.

Kasan matakin daya fara dauka daga lokacin daya kama yaron yana shaye shaye? Makarantar da yakeyi yafara cireshi, dama makarantar kwanace, Day ya maidoshi, kuma duk inda zeje tare yake zuwa dashi matukar baya makaranta.

Wani lokacin ma shi yake aike zuwa wani wajen, kuma koda yaushe suna tare agida, haka idan dare yayi baya barinshi yafita yawo idan ma shima Uban baze zauna gida ba, haka yake jan yaron sufita waje.

A hankali se yaron yadena shan abubuwan dayake sha, domin koda yaushe suna tare da uban, kuma gatan da yake nuna mashi ada seya linkashi, idan wata shawara zeyi to seya sakoshi aciki.

Koda sauran yaran kowa yafadi ra'aryinshi sekaji Uban yace ajira wane yazo. Irin wannan abubuwan da ake mashi sune suka kara sashi farin ciki, kuma yaga babu wanda yake tsangwamarshi saboda yana shaye shaye.

Wallahi Malan cikin ikon Allah wannan mutumin yana addu'a kuma shima yana kokari wajen temakon yaron Allah yasa yaron yashiryu.

Yanzu haka maganar da nake maka yaron ya gama karatun degree dinshi a fannin likitanci, idan ba an fada maka ba bazaka taba cewa ko goro yasha ba. Kaga me yajawo haka? Saboda iyayenshi basu banzatar dashi ba.

To bare kuma kai, duka Fahad shekararshi nawa? Kasan wani lokacin kowa da irin yarintarshi, wasu manyan mutanan idan da za'a tono yarintarsu wallahi abun baze fadu ba, dan haka ina rokon ka kada kabari zuciya ta debeka kayanke danyan hukunci wanda ze saka danasani nan gaba.

Yana da kyau ka nuna mashi fushinka, amma dan Allah kada kazamo kamar sauran wasu iyayen. Ka kokarta kayi da jikinka, kamika ma Allah sauran, Allah yana karbar addu'ar bawansa aduk lokacin da yarokeshi.

Allah yashirya mana zuri'a baki daya, kuma yabamu ikon tarbiyantar dasu. Se alokacin hawaye suka zubo ma Malan, sosai yake kuka kamar karamin yaro, haka suka yita bashi hakuri. Wayarshi ce tayi kara, yana dubawa yaga wani malaminsu Fatima ne yakirashi.

Hannu yasa ya goge idonshi sannan ya daga wayar, bayan sun gama gaisawa Malamin yace dama yarane sukaga haryanzu ba'azo daukarsu ba, kuma sauran yaran duk sun tafi. Malan yace dan Allah Malan kamun wani temako, bansani ba ko suna da kudin mota a hannunsu.

Nima har nashirya zan taho wata matsala ta tsaidani, amma idan suna da kudi ka temakeni kadorasu a motar Mashi, nasan idan sukazo zasu iya kowa kansu Mani. Malamin yace badamuwa, idan ma basu da kudin za'a basu. Malan yace to nagode.

Kallon Vice yayi yace nagode da irin bayanin da kayi mani. Kuma tabbas koda nine nasamu irin wanna case din to irin matakin da kuka dauka zan dauka, babu abinda zance sede ince Alah yasaka da alkhairi, kuma Allah yashirya mana yaranmu.

Kuma insha Allah zanyi amfani da shawarar daka bani. Tashi sukayi suna fadin Allah ya tsare gaba, godiya Malan yayi masu suka tafi. Kasa fita yayi haka ya koma ya kwanta yanajin wani bakin ciki yana shigarshi.

Dama shi yadade da zargin Fahad yana shan wani abu, sede yanda Mamarshi ta dage akan babu abinda yakesha hakan yasa ya kyaleta. Tashi yayi ya nufi dakin Mama domin yaga Fahad din.

Yana saka kafarshi afalo yaji Mama tana kuka tana fadin, haba Fahad, yanzu seda kajawo mani abun kunya ko? Duk irin gargadin danayi maka baka jiba ko? Ai na dauka tunda Farouk ya kamaka kana shaye shaye yazo yafada mani nayi maka fada kuma nace bazan fada ma Malan ba nasan yana iya tsanarka zaka dena.

Ashe daka koma makaranta ma se abun yafi na da, yanzu ya kakeso inkasance acikin unguwar nan? Kasande ba kai kadai bane dan garin nan a makarantarku, karewa ma hada dan unguwarku a makarantar.

Kuma dole gobe wannan maganar ta fasu a garin nan har ma da unguwar nan, shikenan kasani jin kunya,ko wata sabga akeyi bazanji dadin shiga cikin mutane ba, duk inda nashiga haka za'a rika nuna ni.

Dama kowa yasanni da iya yada magana idan aka samu yaron wata yayi wani abun, se gashi yau Dana ne aka kama wai yaje sata, kuma yana shaye shaye, daga karshe kuma an koreshi daga makaranta.

Haba Fahad baka kyauta mani ba, meyasa duk yanda nake kokari wajen kareku daga fadan Malan baka gani? Bani da wani buri agidan nan kamar inga cewa kune asaman kowa, kuma kune nagaban goshin Malan, amma kai baka gani.

Dama yanzu Malan baya sona, kaga yanzu ka kara debo wata mganar shikenan komai akai na ze kare, duk yanda naso ace yaran Inne sune suke cikin irin halin da kuke amma abun ya gagara.

Ka duba lokacin daka jima Faisal ciwo, saboda in kareka daga fadan Malan nasa shi yace faduwa yayi, ko lokacin da Malan yace mun yana zarginka tabbas nima alokacin naga alamun shaye asheya a wajenka, amma saboda banason laifin ka haka na rufe ido nace banyar da ba.

Kalli yanda aka maida maka jikinka kamar wani jaki. Cikin kuka Fahad yace dan Allah Mama kada kibari Malan yakara dukana, wallahi jikina ciwo yakeyi, bulala 20 akayi mana, kuma da katuwar dorina.

Mama tace niyanzu banida bakin magana, amma insha Allah baze duke ka ba, sede nasan tabbas daga yanzu kai ne ja baya acikin yaranshi, yanzu Faisal ze amshe ragamar gidan shida Fatima.

Fahad yace shikenan yanzu Malan baze kara sona ba? Mama tace bazan taba bari hakan yakasance ba, kamar yanda Inne ta lalata mani kai, nima sena saka tsanar Faisal da Fatima a zuciyar Malan.

Idan yana tunanin kai kadai ne wanda yake shaye shaye, to shima Faisal din zamu san yanda zamuyi Malan yasamu wani abun ajakarshi, kaga koya rantse mashi baya sha baze yarda ba. Ita kuma Fatima nasan sharrin da zan ja mata.

Ka kwantar da hankalinka babu abinda ze faru da kai, idan ma tsanar ce to sede ya tsaneku ku 3. Tashi kaje kayi wanka kazo kaci abinci kasha magani se in shafa maka magani ajikinka.

Murmushin takaici Malan yayi seya fasa shiga dakin kawai ya juya ya koma falonshi, aranshi yana tunanin wane irin hali Hauwa take dashi haka? Mace kamar wadda bata da tunani, ashe dama tasan Fahad yana shaye shaye amma ta boye mashi.

Shima Farouk ya sani amma yayi shiru. Ko dayake ba laifinshi bane, dama dole ita ze fara fada mawa, kuma duk umarnin da tabashi dole yabi. Amma tunda haka ne ze kyaleta dashi.

Kuma baze taba yimata maganar Fahad ba, idan kunya ne se ta fishi jin kunya tunda itace take shiga cikin mutane, shikam yasan babu wanda ze tareshi da maganar, idan ma za'ayi maganar sede bayan idonshi.

Kuma shi dama bame shiga cikin jama'a bane. Murmushi yayi daya tuna sharrin da takeso tajama Faisal da Fatima, aranshi yace wannan kuma tsakininki da Allah ne, domin kin cutarsu dasu da yawa, kuma Allah baze barki ba.

Idan kuma kina tunanin Malan din da kika sani ne ada wanda baya bincike to kin makaro, Allah ya kaimu lokacin da zaki ja masu sharrin, dadin abun ma Faisal baze dawo hutu ba, Fatima kuwa da nayi aure tabar dakin ki.

Se wajen azahar su Fatima suka iso, Farida da gudu tashiga gida tana kwala ma Mama kira, fitowa tayi da fara'a tana fadin ga yan makaranta, rungumeta Farida tayi tana fadin wai meyasa Malan beje ya dauko mu ba? Mama tace kede muje kicire kayanki.

Baki yayi shiyasa. Fatima ce tashigo tana goye da jaka, sosai takara kyau, kamar ba makaranta takeyi ba, tayi haske tayi kiba, kyanta seya kara fitowa, lokacin data shigo Mama harta juya tajiyo sallamarta.

Juyowa tayi tare da amsawa, sakin baki Mama tayi tana kallonta, gani tayi tazama cikakkar budurwa, gashi tazama me kyau, kamar ba a kauye take ba, jikinta kanshi yayi kyau se sheki yakeyi.

Risnawa Fatima tayi tana fadin Mama ina wuni? Seda ta maimata so biyu sannan Mama ta farga da maganar da take mata, daure fuska tayi tace lafiya. Juyawa tayi tashige ciki gaba daya bakin ciki ya gama kamata.

Saboda ba zaka hada Fatima da Farida ba awajen kyau, ita Faridar ma duk seta rame takara duhu. Wucewa Fatima tayi dakinsu domin ta cire kayanta tayi wanka, Farida kuwa tana dakin Mama, sosai Fatima tayi bakin cikin rashin dawowar Faisal, tasan wannan hutun zata yishi ne kawai amma bazataji dadin komai ba.

Amira ce da Saddik suka shigo da gudu, kai tsaye dakinsu Fatima suka shiga, suna shiga Amira ta rungume Fatima tana dariya, Fatimar ma dariyar take tana fadin Amira, Saddik yace Fatima an girma, hararshi tayi tace wallahi ka rai na ni.

Dariya yayi yace to sannu da zuwa, ai de mun rigaku dawowa. Fatima tace muma de ai gashi mun dawo. Amira tace ina Yaya na? Fatima tace ai Yaya baze dawo ba se hutun sallah. Turo baki Amira tayi ta saki Fatima ta juya tana kuka.

Dariya suka sa mata,Saddik yace yau akwai rigima, kinsan Mama tace tun jiya duk abinda aka bata seta ragema Yaya, yanzu haka bataci abinci ba wai shitake jira, ganin ba taji karar mota ba yasa tace inzo in rakata wai tsoron Mamar su Farida takeyi.

Fatima tace nima wallahi duk banajin dadin rashin dawowarshi. Saddik yace ai se hakuri bara inje inji dramar da takeyi, har yanzu yarinya tana SS 2 amma batasan ta girma ba. Fatima tace Amirar ce yarinya? Kasan de ai ta girmeka. Saddik yace ada ba. Dariya suka sa yafita.

A can gida kuwa rigima sosai Amira takema Mama wai Yaya bedawo ba, se kuka takeyi, da Mama tagaji da lallashinta ta dauko bulala tace wallahi ko kimun shiru ko inzaneki, wai ke se yaushe ne zakisan kin girma? To Yayan baze zauna yayi karatu ba? Tashi ki bani waje.

Baban Saddik ne yashigo yana fadin haba Maman Saddik, ya zaki hada mata zafi biyu, amma de kinsan tun jiya take dokin dawowarshi ko? Mama tace tun jiyan inda kafada mata gaskiya ai da yanzu bata ji ciwo sosai ba, amma ka biye mata kana fadin yau ze dawo, ai gashi nan bedawo ba.

Baba yace taso Mamana Yaya zedawo daya gama karatu, kuma ai zedawo hutun Sallah kinji? Haka yayita lallashinta da kyar ta hakura.

Zaune suke gaba dayansu a Falon Malan, bayan sunci abinci sunyi sallah suka shigo gaishe shi dan tunda sukazo basu ganshi ba. Fahad kuwa kasa fitowa yayi dan ko abincinshi sede Mama ta ai ka mashi dakinsu na can baya, datace yafito yace baze fito ba.

Bayan sun gama gaisawa, Malan ya tambayesu ya makaranta, sukace lafiya lau. Tambayarsu result dinsu yayi, Fatima ce ta fara mika mashi nata, gaba daya ta cinye subject dinta, duka excellent.

Farida kuwa da kyar ta mika result dinta, murmushi Malan yayi ganin irin result din data kawo mashi, kallonta yayi yace tabbas idan kika cigaba da kawo mani irin wannan result din, to bazaki wuce wannan ajin ba.

Kinsan de halin makarantarku, basa barin mutum yawuce haka zasuyi ta mashi repeating, to kisani hukunci daya zan yanke maki, matukar wannan karon baki wuce SS 1 ba, to kinbar makarantar kenan, zan maidoki Day, idan kina fita kinashan rana da tafiya zaki fi maida hankali. Kutashi Allah yayi maku albarka.

Lokacin da dare yayi haka Malan ya nufi dakin Fahad, lokacin Fahad yana zaune ya gama cin abinci ya kunna sigari yana sha, tunda Malan ya doshi dakin yafara jin wari, yana isa kofar dakin ya daga labulen, ido biyu sukayi da Fahad.

Da sauri Fahad ya wurgar da guntuwar sigarin ya mike tsaye, hannu Malan yasa ya kamo hannunshi tare da take sigarin suka fito waje. Kai tsaye falonshi suka nufa Fahad se zare ido yakeyi, dan tunda yadawo basu hadu da Malan ba.

Zaune Malan yake asaman kujera yayin da Fahad yake duke agabanshi. Kallon shi kawai Malan yakeyi, duk ya rame yayi yayi baki, bakinshi ya dafe kamar wanda ya dade yana shaye shaye.

Fahad! Malan yakira sunanshi, kasa dago kai Fahad yayi, Malan yace irin rayuwar daka daukarma kanka kenan ko? Yanzu wace riba kaci da aka koreka daga makaranta? Shikenan sauran yaran da kuka shiga makaranta tare sun wuceka.

Haka zasu gama karatunsu su zama wasu manya kai kuma ka lalata rayuwarka. Kana karaminka amma kasan kasha abinda ze bugar da kai. Shin kana sallah kuwa? Kara dukar da kai Fahad yayi, Malan yace gaba daya ka zanca.

Kuma ni bazan duke ka ba kamar yanda kake tunani, sede zan baka shawara kayi kokari kabar wannan halayyar da kakeyi, kada ka biye ta Mamanka, domin bata baka shawara me kyau.

Idan aka koma hutu zan maidaka Day kuma zanyi kokari su daukeka a SS 3, nasan ba'a gama registration na WAEC da NECO ba, idan suka yarda se inyi maka kazauna kasamu kayi jarabawarka kaga seka gama tare da sauran 'yan ajinku.

Idan kadena duk abubuwan da kakeyi zakaji dadin rayuwarka nan gaba. Kuma inaso ka koma islamiyar da kukeyi ada, dan nasan tunda kuka shiga makaranta kadena zuwa, amma Mamar ku tana fada mani kullum kuna zuwa. Tashi kaje, amma duk ranar dana kara ganinka kana sha mani sigari ko wani abu agida to aranar zakaga fushina.

Tashi Fahad yayi rai abace yafita, danshi maganganun Malan ma bata mashi rai sukayi, taya zece yadena biye maganar Mama, bayan yanzu ita kadai take son shi. Daki ya koma ya dauki wani abu kawai yazo ya fice. Yazo fita ya hadu da Farida, dariya tayi tana fadin Yaya yaushe ka dawo? Harara ya buga mata, dariya takara sawa tana fadin Yaya kalli wuyanka sahun duka waya dokeka? Kafa yasa ya harbeta yana fadin zanci uwarki wallahi. Ihu Farida tasa yafice yabarta.

Tun daga wannan rana Fahad yade zaman gida, kafin kace me labarinsu ya baza gari, mutanan unguwa se gulma sukeyi, duk yaron da yayi ma Fahad maganar korarshi seya dokeshi, haka yarika fasama yara baki.

Ganin irin illar da yake masu yasa suka fara tsoranshi, sede suyi maganar bayan idonshi, amma idan yafito babu me mashi magana. Sam baya zama gida, haka kuma baya dawowa da wuri. Maganar shaye shayenshi kuwa se abinda yaci gaba, domin inda suke haduwa da sauran abokanshi idan yadawo hutu can yake zuwa.

Gaba daya Mama tshiga damuwa, lokaci kadan duk ta rame, ta rasa abinda yake mata dadi, gashi Malan beyi mata maganar Fahad ba bare tasan yanda za'a bulloma abun, gashi Fahad baya zama gida, idan yadawo to abinci zeci.

Gashi yanzu seyaci abincin mutum 3, saboda shi yanzu takara yawan abincin gidan, dan idan be koshi ba seta sa Fatima ta dafa mashi wani abun, ita ko Fatima ba ruwanta dashi, dama can bata shiga harkarshi.

Farida ce kawai take shiga harkarshi, itama tunda yayi mata wani bugu tadena mashi magana. Gashi yanzu iskancinta ya kara yawa, kusan kullum tana dakin me shago, yanzu abubuwan da sukeyi ma yafi na da. Fatima so biyu tana kamata tafito daga dakinshi, amma sanin halin Farida dana Mama yasa taja bakinta tayi shiru, tunda taga Mama bata fadama Malan laifin da Farida tayi amakaranta ba wancan karin.

Malan kuwa ya saka ma Fahad ido, ganin Malan yaki ma Mama magana yasa ta yanke shawarar ta samehi da maganar, shiko Malan hidimar bikinshi kawai yakeyi.

Bayan su Fatima sun dawo hutu da kwana 4 yakirata yace tashirya ze kaita wajen Inne tayi hutu. Saboda mamaki kasa magana tayi, wani farin ciki ne ya kamata.

Haka taje ta hada kayanta taje ta fadama Mama, wani kulu kulun bakin ciki ne ya taso ma Mama, wato yanzu Malan ya canza, har ma hutu ze kai Fatima. Tana murnar aiki zemata sauki shine dan bakin ciki ze dauketa.

Farida ma sosai taji haushi, yanzu Fatima birni zata tafi gidan 'yan gayu amma banda ita, jitayi kamar tace itama zataje, amma saboda bakin ciki yasa tayi shiru. Ganin Mama batayi magana ba yasa Fatima ta tashi ta fita.

Mama kuwa jin Malan yashigo yasa ta tashi domin tana so tayi mashi maganar Fahad. A bincinshi ta kai mashi bayan ta zuba mashi ta zauna, kallonta yayi dan yasan akwai magana tunda tazauna, dan data kawo mashi abinci take fita.

Shiru yayi yana cin abincinshi, ganin bazeyi magana ba yasa tace Malan wai naji shiru tunda Fahad yadawo bakayi mani magana ba. Murmushi Malan yayi yace maganar me zanyi maki Hauwa? Ke da kika rigani sanin halin da Fahad yake ciki ai kece yakamata ki fara mani maganar.

Uhmm, Hauwa kenan, a tunaninki duk abubuwan da kikeyi agidan nan bansa ni ba? Wato kece kika hana Farouk ya fada mani halin da Fahad yake ciki, saboda bakiso nayi mashi fada.

Yayi kyau, ai ko yanzun da aka koreshi banyi mashi fadan ba, na barki dashi tunda zaki iya kula dashi, nide amatsayina na Uba zanyi kokarin sauke duk wani nauyi da yake kai na, kuma zan kara sama mashi wata makarantar yaje ya zana jarabawa kawai.

Sede a Day zan sakashi, kuma zanyi kokari wajen nema mashi duk abinda yakamata, idan ya tsaya yayi karatu yatemaki kanshi, sauran kuma nabar maki, tunda kina tunanin kece kikafi iya kula da yara ba se kinyi masu fada ba.

Mama tce ai shikenan, dama na dauka bazaka nema mashi wata makarantar bane, amma kasani wallahi irin wannan ban bancin da kake nunawa Allah seya tambayeka, yanzu gaba daya baka son yarana.

Gashi dan munafurci ma wai Fatima zaka kai hutu Katsina, wannan ai salon kwadai ne, dan kaga Uwarta tana gidan masu kudi shiyasa zaka kaita. Da can meyasa baka taba kaisu ba tsawon shekaru da dama? To yaran nawa daka tsana insha Allah sune zasu daukaka.

Malan yace dan Allah tashi ki bani waje tun kafin rai na ya baci, ba zakisan kin shiga damuwa ba senan gaba, kin tsani wasu kina nunama yaranki soyayya, kuma zakisan cewar kin dorasu akan turba marar kyau.

Tashi Mama tayi tana fadin kai zaka ga abun kunya agidanka, amma wallahi yarana sunyi gaba. Mugu kawai, murmushi Malan yayi aranshi yana fadin duk tsiyarki wallahi bazan sake ki ba, domin sakaran namiji ne yake sakin matar data cuceshi.

Kina nan tare dani, bazan sake ki kibarni da bakin ciki ba, yanda kika jawoshi gidan nan haka zaki zauna kishashi.🤣

***** *****

Washe gari da safe haka Malan ya tafi da Fatima su Farida kamar suyi hauka saboda bakin ciki, Fatima kuwa ko sallama batayi masu ba, dan taga Mama tun jiya take masifa. Haka suka tafi zuciyarta tana me cike da farin ciki.

A mota Malan yace insha Allah shima Faisal zanyi kokarin zuwa makarantarsu lokacin da za'ayi bikin yayesu, domin ban taba zuwa mashi visiting ba,duk da ba laifina bane, idan naso zuwa se Hauwa ta hanani. Fatima nasan akwai abubuwan da Hauwa tayi maki kiyi hakuri, kuma daga yanzu zan rika barinku kuna zuwa wajen Inne.

Kafin ki dawo ma zaki samu sabuwar Inne, kuma dakinta zaki koma da zama. Kallonshi Fatima tayi, yace E aure zanyi, bakiga na gyara dakinsu Faisal ba? Dukar da kai tayi batace komai ba. Dan ita har yanzu jitake kamar de Malan ba gaskiya yake fada mata ba, duk lokacin da ta tuno irin dukan da yayi masu se tsanarshi takara shiga zuciyarta, shiyasa kome zeyi mata bata farin ciki, yaune kawai tasan tayi farin ciki.

Wai sabuwar Inne, ai yanzu babu wata mace da zata kara yarda da ita amatsayin matar Malan, domin tasha wahalar Mama, dan haka bazata kara yarda da duk matar da Malan ze kawo ba, idan ada tana yarinya anyi mata abubuwa yanzu babu macen da zata kara dukanta. Allah yakawota lafiya,wai zeje ma Yaya visiting, dama can rashin sone yasa baya zuwa amma kaji zeje wai laifin Mama, kawide dan yaga yanzu mun girma shiyasa yakeso yajawo mu ajiki, ganin Malan ze dameta da surutu yasa ta kwanta.

A kofar gidan Malan ya ajeta, domin yasan gidan Alhaji, kuma yace ta gaishe mashi da Inne, sannan tace mata tayefe mashi. Ita de Fatima ta amsa ne kawai, haka tafita tabarshi dan har yanzu bata saba dashi ba.

Ihun su Khairat da Ansar ne yasa Inne tayi saurin fitowa. Tsayawa tayi tana kallonsu yanda suka rungume Fatima, kara murza idonta tayi dan ta tabbatar da abinda take gani. Da gaske itace. Ya akayi Malan yabarta tazo? Kuma ai Fatima batasan gidan nan ba.

Matsawa tayi ta kamota tana murmushi tace da gaske kece Fatima? Fatima tace nice Inne, kuma tare mukazo da Malan, amma yatafi. Inne da ta cika da mamaki tace mushiga ciki.

Bayan Fatima taci abinci ta bama Inne labarin abubuwan dasuke faruwa agidansu, hada labarin abinda Farida tayi amakaranta, kuma ta bata labarin abunda su Fahad sukayi har aka koreshi, kuma ta fada mata auren da Malan zeyi. Sosai Inne tayi mamakin Fahad.

Dama kuma duk cikin yaran Mama shine yakeda wata zuciya, kuma shine tafi sangartawa. Inne tace Allah ya kyauta kuma ya shiryasu, ashe su Hauwa za'a samu wata kishirya kuma. Fatima tace yanzu Inne kozaman gida Fahad bayayi, gashi da anyi mashi abu yayita zagin mutum, bakiga irin dukan da yayima Farida ba.

Inne tace kede ba ruwanki dashi, Fatima tace ni dama bana shiga harkarshi, Inne tace ina Farouk fa? Fatima tace Allah sarki Yaya me kirki ba, yana makaranta wannan karon bezo week end ba. Inne tace ai zan samu numbershi ince yazo mugaisa, haka sukayi tafira, abubuwa kala kala Inne takawo ma Fatima, da yamma kuma suka shiga kitchen tare.

Lokacin da Alhaji ya dawo shima yayi mamakin zuwanta, anan Inne tabashi labarin da Fatima ta bata, hada maganar auren Malan, sosai shima yayi mamaki, addu'a yayi shima yace Allah yashiryasu. Allah yasa kuma su Fatima suji dadin matar daze aura.

**** ****

A na gobe daurin auren Malan Farouk yazo gida sunyi hutun mid semister, dan yanzu suna a second semister ne, sosai yakara girma, gashi yakara hankali, bayan sun gaisa da Mama yaci abinci take fada mashi halin da ake ciki.

Sosai yayi bakin cikin abinda yafaru, yace kin gani ko Mama, shiyasa tun wancan lokacin naso kibari afadama Malan, domin Fahad yana jin tsoron Malan yanzu ga irin abinda yajawo ma kanshi.

Mama tace dan Allah kada ka bata mani rai, shege me hali irin na Ubanshi, abun bakin ciki yasamu Dan uwanka amma ka tsaya kana fadar maganar banza, to de abun kunya ba akan Fahad aka farashi ba.

Kuma ni nasan wadda tayi mashi haka, kasa ido kayi kallo wata rana akan yaranta asirin ze koma. Farida tace Yaya yanzu kana dinkin hular? Hararar ta yayi yana fadin bansani ba, sakarai ya kawai, inda Fatima ta fiki kenan.

Kina kallon mutun bazaki iya mashi sannu da zuwa ba bare ki gaisheshi, seyanzu zaki tambayeni abinda be shafeki ba. Mama tace tashi kabani waje, Fatimar taje tayi ta finta seme? Ai de har abada bazaka canza Farida ba.

Kuma Fatima bazata taba zamowa jikinka sosai ba, domin rabin jininka ce, Farida itace take cikakkar jininka. Fatimar da kake fadi yanzu ma tana ajen Uwarta, kaga kuwa dole ka rungumi Farida tunda a inuwa daya kuke zaune.

Sakarai wanda baya kishin yan uwanshi da ni kai na, wallahi idan kace irin wannan halin zaka kawo mani zakasha wuyata, domin bazan lamunci karika tsanar yarana kana fifita wasu banzaye can ba.

Tashi Farouk yayi rai abace, saboda halin Mama yasa ko week end bayason zuwa, mutum yadawo daga makaranta yana farin ciki amma daga zuwanshi ko hutawa beyi ba an fara zaginshi, ya kamata ace yanzu tadena zaginshi agaban Farida.

Shiyasa da akayi hutun waccan semister yayi zamanshi makaranta, dan dinkin hularshi yafiye mashi yazo gida, seda ana saura kwana 3 adawo sannan yazo gida. Dakinshi ya wuce yaje yayi wanka lokacin Malan yadawo yashiga suka gaisa.

Sosai Malan yaji dadin ganin Farouk dan duk wanda yaganshi seyaga nutsuwa atare dashi, komai cikin nutsuwa yakeyi, anan Malan ya mashi maganar Fahad kuma yace meyasa be fada mashi ba. Farouk yace kayi hakuri Malan.

Naso infara fada maka se Mama ta hana, Malan yace ai shikenan, amma daga yanzu duk abinda yake faruwa banaso karika boye mani, nafiso kome zaka fada kataho wajena muyi magana, kaga kaine babba idan ba ka sakin jiki dani kana fada mun komai ai sauran yan uwanka bazasuyi koyi da kai ba.

Farouk yace haka ne, kuma insha Allah zan gyara. Malan naga anyi mana dakuna, Allah yasaka da alkhairi mungode. Malan yace bakomai, wancan dakin ma gobe za'a kawo amaryata. Farouk yayi murmushi yace Malan aure zakayi? Malan yace ko na tsufa? Farouk yace a'a, amma Mama bata sani ba ko? Malan yace zata sani amma se an kawota. Farouk yace Allah yasa alkhairi.

Malan yace amin, kaima Allah yayi maka albarka, nan Malan yafada amshi ya bude shago, haka suka yita fira, daga karshe yajashi suka fita dan yaga shagon.

***** ****

Washe gari wajen karfe 12 Malan yashirya cikin babbar riga se kamshi yakeyi ko sallama beyima Mama ba haka yatafi dauri aure, Mama bata san wainar da ake toyawa ba, hatta da mazajen unguwar sunje daurin auren amma babu wadda ta fada mata.

Salamatu da Momyn Teema sosai wannan aure yayi masu dadi, Maman Sultan ma batasan zeyi aure ba dan mijinta baya gari.

Bayan angama daurin aure kowa ya nufi wajen da za'a ci abinci, domin suna gamawa zasu dauki amarya su taho da ita, dan yanzu andena daukar amarya da dare. Kowa yaga Malan yasan yana cikin farin ciki. Bayan sun gama reception sukayi la'asar sannan aka basu amarya.

Farouk ne yashigo dakin Fahad domin tun da yadawo basu zauna dashi ba, dan har yanzu Fahad yana jin haushin Farouk, ko magana baya mashi, har Mama seda Farouk ya fada mawa, amma babu abinda tace se cewa tayi tunda kaima ka tsaneshi ba dole ze kyaleka ba, jin abinda Mama tace yasa Farouk ya kyaleta.

Warin wiwi yaji daga bandakinsu, fita waje yayi yana jiranshi yafito. Fahad yana fitowa ya jawo dakinsu dan fita zeyi. Koda yaga Farouk be kalli inda yake ba haka ya nufi hanyar fita.

Farouk ne yace wai kai Fahad meyasa bakada hankali ne? Yanzu dan rashin mutunci acikin gida zaka rika mana shaye shaye? Duk irin abinda yafaru da kai be zamar maka darasi ba? Yakamata ace kaji kunyar abinda ka aikata har yasa aka koreka daga makaranta.

Wallahi inda nine kai daga ranar da aka koreni daga ranar nabar shaye shaye, domin shine silar jefani cikin halin da nashiga. Amma dayake kai ba kada tunani shikenan seka dawo kabude sabon iskanci agida.

Fahad yace na bude dan Ubanka, ai gidan banaka bane, nima ina da gado aciki, kuma naje nasha wiwin, idan dakinka nashiga nasha se kayi mani mgana. Da aka koreni kuma ai ba kai aka kora ba zakazo kana zagina banza kawai, wallahi yanzu na tsaneka.

Daukeshi da Mari Farouk yayi yana fadin ni kake zagi? Dun kule hannu Fahad yayi ya kaimashi naushi a hanci seda jini ya fita.

Haka suka fara kokowa suna ta dukan junansu. Farida ce ta taho kiran Farouk, ai tana ganin an danne Fahad a akasa ana duka ta ruga da gudu tana kiran Mama. Da kyar Fahad ya ture Farouk lokacin daya watsa mashi kasa a ido.

Yana tashi ya hangi wani karfe babu bata lokaci yadaukoshi ya caka ma Farouk aciki, dede lokacin da Mama da Farida suka zagayo, hannu Mama ta dora akai ta fasa ihu tana fadin Fahad bakada hankali.

Farouk kuwa tuni ya sume awajen. Kuka kawai Farida takeyi, haka Fahad ya fice yana huci, yana fita yaga motoci suna parking akofar gidansu, ko kallonsu beyi ba yayi gaba, Malan da yake fitowa daga mota yabishi da kallo.

Mutanan unguwa se lekowa suke suna kallon masu kawo amarya, da gudu Mama tayi waje domin ta nemo wani yazo akai Farouk asibiti. Tana zuwa bakin gate ana shigowa da amarya se guda akeyi.

Tsayawa tayi tana binsu da ido, da Zulai suka fara hada ido, ko kallonta Zulai batayi ba haka suka wuce wasu mata suna fadin Suwaiba kin samu gida dankari. Daskarewa Mama tayi a wajen tana maimaita sunan Suwaiba abakinta.

Farida ce tafito da gudu tana fadin Mama wallahi jini se zuba yake a cikin Yaya, zubewa Mama tayi awajen a sume dan batama san abinda Farida take fadi ba.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263

😘😘💋💋 Ina mika godiyata agareku, kucigaba da kasancewa dani. Love u all

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.