Trending Hausa Novels

A Wani Gida

Reading file: A_WANI_GIDA.txt

Chapter 5 of 6

Part 70 ⏩ 75

A cikin mota Malan se kame kamen labari yakeyi Zulai kadai take biye mashi. Sun kusa shiga Katsina Malan yace Zulai nide akwai maganar da nakeso inyi, sede bansan yanda zaki dauke ta ba.

Zulai da tun dazu ta dade da harbo jirginshi tayi murmushi tace haba Malan, ai babu wata magana daza ka fada mani in kasa fahimtar ta, kai fa namiji ne, kawai kafadi maganarka. Murmushi Malan yayi yace to shikenan bara mu isa.

Zulai ce tayi mashi kwatance har suka isa kofar gidan Yayansu. Malan yace Malama Suwaiba kishiga ciki zan danyi magana da Yayarmu. Murmushi Suwaiba tayi tace to bakomai mungode ka gaida gida.

Bayan ta tafi Malan yace Zulai dama ba wani abu bane, inaso in hada iri dake. Murmushi Zulai tayi tace to Malan Allah yasa alkhairi ne. Malan yace dama akan maganar Suwaiba ne, nide ina rokon abani dama inshigo cikin mane ma.

Amma ke nakeso kishige mani gaba dan naji kince bata son kula samari, bare kuma ni da nake tsoho. Dariya Zulai tayi tace haba Malan, ina wani tsufa anan? Kawai dan de kana zaune da mace ba 'yar zamani ba.

Duka yaranka biyar fa, wallahi kabari Suwaiba ta amince da kai nasan zata canzaka, domin Suwaiba akwai son gayu. Malan ya washe baki yace Allah ko? Zulai tace sosai mana. Malan yace amma ya kike gani ta wajen Hauwa gashi ke kawarta ce.

Zulai tace haba Malan, ai Hauwa cutar da kai kawai takeyi, na tabbata itace take kara tsufar da kai, domin Hauwa shu'umace, se mutum me zurfin tunani yake iya gane kai dinta. Amma shawarar da zan baka kafara sa mata ido musamman idan tayi baki.

Ko kuma lokacin da yara suka dawo gida hutu. Kuma ni badamuwata bace dan ka auri Suwaiba, domin ni ba garin nake ba. Kome zatace banida damuwa, idan kuma duniyanci takeji dashi na fita.

Kuma tabbas nayi maka sha'awar auren Suwaiba, kuma nasan itace zata maye maka gurbin Inne, domin kayi asarar mace ta gari, kuma ba kowa bane yayi silar rabuwarka da ita se matarka.

Idan kabi komai a sannu zaka fahimta da kanka. Kada kadamu zan samu Suwaiba, kuma nasan zata amince da kai. Malan yace amma nagode Zulai, samun Number dinki domin inji abinda ake ciki.

Bayan ta samashi number ya ciro dubu 5 yabata yace ta bama Suwaiba, dubu 2 yabata yace tayi kudin mota. Sosai Zulai taji dadi, godiya tayi mashi tana fadin aduba mejikin. Malan yace ai dama nine me jikin, kuma yanzu naga likitan gakinan azaune, maganin kuma yana ciki, idan kika amso mani maganin seki aika mani dashi. Ni yanzu gida zan koma. Dariya Zulai tasa ta bude kofa tana mashi asauka lafiya.

Bayan Mama ta gama gyaran gida tayi bakuwa wata 'yar uwarta da take aure a Shargalle, sosai Mama taji dadin zuwanta, bayan sun gama gaisawa Mama tace bara tashiga kitchen ta dora masu abinci, Matar me suna Amba tace muje mana nima ai banason zama ni kadai.

Haka suka shiga suka dora girki, bayan sun gama suka zauna suna fira. Har Malan yadawo Mama bataji karar motarshi ba, domin a waje ya ajeta, kai tsaye falonta ya nufa yana kiranta, yazo shiga yaji ana magana alamun mutum biyu ne.

A lokacin kuwa Mama tana bama Amba labarin irin abubuwan da tayi ta jawo hankalin Malan, da kuma yanda tasa ya saki Inne, da yanda takema su Faisal, har zuwansu Fatima Makaranta da abubuwan da take mata. Komai de seda Mama ta fadama Amba.

Sosai suke dariya, Amba tace amma Hauwa ke ta da bance, babu boka ba Malan kin kwace komai na gidan, kuma kin kama Malan a hannunki, Mama tace wallahi kuwa, ai yanzu ne nake iya daga mashi murya.

Shima gani nayi ze maida mani yara Saniyar ware, niko duk abinda mutum zemun zan iya jurewa, amma idan mutum yafara tabo mani yara wallahi anan zega bacin rai na. Damma de waccan munfukar matar ta shiga ta fita ta saka ma yarana rashin kokari, ai da har yanzu yarana su ke haskawa agidan nan.

To shi kuma Malan yanda halinshi yake, sam baya tunani da kwakwalwarshi, shi akullum duk yaron daya kasance me kokari agida to shine abun so awajenshi, haka kuma duk wanda yaga yana mashi aiki ko kuma yana wani abu da yakeso agaban idonshi to shine tauraro a wajenshi.

Irin wannan halin nashi nayi amfani dashi wajen saka kaunar yarana azuciyarshi, domin inde yana gida yarana komai sune sukeyi, kuma basa tafiya masallaci seda shi. Haka kuma na saka kiyayyar yaranshi a zuciyarshi, kinga ko ai nayi mashi babban aiki.

Nasan har yaran nan su mutu bazasu dena ganin bakin Malan ba, domin basu taso da soyayyarshi ba, ko yanzu da yake kokarin jawosu ajiki da kinga yanda suke mashi kinsan basu saba ba.

Ganin yanzu yafison yaranta da nawa yasa nake mashi masifa, domin naga idan na tsaya wannan kissar to nice zan kwana ciki, dama saboda wa nakeyi, saboda kishiya ne, kuma tunda na koreta ai se in kwatar ma yarana 'yancinsu.

Kinga yanzu na zamar mashi kargen kafa, domin yanzu Malan baze iya kallon wata mace yace ze aura ba, nidin de nice abokiyar zaman tashi. Amba tace gaskiya agaisheki, ai ban taba jin labari me abun al'ajabi ba kamar naki.

Idan zaki shiga gidaje goma masu kishiyoyi to da wuya ki samu masu irin halinki, domin abinda kowa ce mace ta yarda dashi na hanyar da zata mallake mijinta ko kuma ta kori kishiyarta to hanya daya ce, wato Boka.

Segashi ke cimin ruwan sanyi kin gama da komai. Mama tace aini dama can a rayuwata banyarda da wani abu waishi boka ba, ai duk macen data isa to wallahi base taje wajen boka ba zata kwaci kanta, aini abun da na dauki boka marar aikinyi.

Kuma idan kura tana maganin zawo tayima kanta mana. Kullum yanda kika sanshi ahaka zaki sameshi, sekiji yayi aikin miliyoyi amma idan kika kalleshi kome aikinki bazaki hada dashi ba.

In banda cutar da mata babu abinda sukeyi, su kwanta dasu, kuma su kwace masu kudi, daga karshe su kafa masu sharadin daze halakasu, domin duk wani boka idan yabama mace magani daga karshe sekinji yace idan ta kuskure kaza aikin ze dawo kanta.

Kuma abun haushin se yace mata ciwon daze sameta beda magani, kinga kenan suna sane suke aikata masu haka. Sede har yanzu su Matan basu gane ba, domin zuciyarsu ta mace akan bokansu.

Amba tace wallahi da gaskiyarki, gara mutum yayi amfani da kwakwalwarshi ya kwatoma kanshi 'yanci. Mama tace gani nan de ina zaune agidana lafiya. Amba tace kinga kada dare yayi mani gara intashi in tafi. Mama tace haba ki bari kiyi la'asar mana.

Amba tace ai zan tsaya Mashi. Tashi Mama tayi ta hado mata wasu kayanta dazata bayar da sabulun wanka ta bata da dari biyu tace ta kara tayi kudin mota. Malan da jikinshi ya gama mutuwa haka yaja kafa yashige dakinshi.

Har bakin kofa Mama ta rakata Amba tana ta mata godiya, ganin motar Malan yasa Mama tace ashe Malan din ma yadawo, bara in mashi magana ku gaisa. Amba tace dakin barshi ma. Mama tace kede kibari in mashi magana kila ma ki kara samun na mota.

Yanajin Mama ta taho yayi saurin shigewa bandaki, koda tazo taga yana bandaki seta fita tace tashigo yana bandaki. Amba tace Allah kibarshi wucewa zanyi. Mama tace toshikenan ki gaida gida da yaran.

Malan kuwa wanka yayi yafito, adaki ya iske Mama tana jiranshi, kallo daya yayi mata ya dauke ido, gaba daya tsanarta ce tashigar mashi zuciya, fuska a daure ya zauna. Murmushi Mama tayi tana fadin Malan har kadawo? Amma kayi sauri.

Be kalleta ba yace E, tashi tayi ta kawo mashi ruwa da abinci, alokacin yana kwance ya rufe idonshi. Mama tace Malan tashi ga abincinka, be bude idon ba yace kibarshi idan natashi zanci bacci nakeji.

Mama tace ko inzo in tayaka baccin? Bude ido yayi yace dan Allah kifita banason surutu. Tashi Mama tayi tana tsaki tace dan ma nace zan ta yaka shine zaka kore ni, anjima zaka gani idan ka nemeni ko zanzo, fita tayi tana masifa.

Runtse ido yayi lokaci guda wasu zafafan hawaye suka zubo mashi. A ranshi yana fadin Hauwa kin cuceni, Allah ya isa tsakanina dake, kin gama tarwatsa mani gida, amma kisani wallahi kema sekin dandani irin bakin cikin da kika sani. Kuma yanzu ne zan kara dagewa wajen karo aure.

***** ******

Tun daga wannan ranar Malan ya canza ma Mama, ita kanta shakkarshi takeyi, domin yanzu ko zama gidan bayayi sosai, daya dawo yaci abinci ze kwanta, ana la'asar kuma ze fita, kusan kullum ya kwanta seyayi kuka.

Babu abinda yake damunshi irin rashin mutuncin da yayi ma Inne, yanzu gashi Inne tayi mashi nisa da babu abinda ze hana yaje ya maidota, gashi kwata kwata su Faisal basa sonshi, basa son zama dashi.

Sauran yaran daya saba dasu yanzu sun canza hali, Farouk ne kadai yake ganin hankali yana shigarshi, ya ma rasa ta inda ze fara. Gashi ya aje aiki, tunani yayi akan ya ciro kudinshi da yake tarawa a banki ya gina babban shago a wani karamin filinshi da yake cikin gari, idan yaso se ya zuba provision da kayan masarufi.

Se ya rika zama da kanshi dama yana gajiya da zaman rashin aikin yi, danshi ba ma'abocin zama majalissa bane, saboda yanayin shi yasa beda wasu abokai da yawa.

Wayarshi ce tayi kara, har ta kusa katsewa ya dauka, sunan Zulai yagani hakan yasa ya katse kiran ya kirata. Bayan sun gama gaisawa Zulai tace albishir na bugo in maka. Murmushi Malan yayi yace ai na kosa inga kiranki, daurewa kawai nayi yasa bankira ki ba.

Zulai tace kasan halin Suwaiba, da kyar ta amince, sede tace ya za'ayi da aikinta? Washe baki Malan yayi yace haba wannan ai bawani abu bane, inada hanyar da zansa ayi mata transfer.

Zulai tace to babu damuwa, kuma nayima Yayanmu magana shima yaji dadi kuma ya amince da maganar sede yana son ya ganka. Malan yace wannan badamuwa bane, zan shirya zuwa gobe inje, amma kituro mani number Suwaiba bazan jira se zuwa gobe inganta ba.

Zulai tace toshikenan, godiya Malan yayi mata ya kashe, tana turo mashi number yakira Suwaiba.

Washe gari haka Malan ya caba ado kamar me shirin zuwa hawan sallah, sallama yayi ma Mama yanufi hanyar fita. Binshi Mama tayi tana fadin ina kuma zaka Malan? Kallonta yayi fuska adaure yace haifata kikayi ne? Cike da mamaki Mama tace bangane ba.

Tsaki Malan yayi yace dole duk inda zanje sena fada maki? Tunda nayi maki sallama aikin ki kice mani Allah ya kiyaye, in ba kuma yanzu kin dena Kissar ba. Juyawa yayi yafita.

Sakin baki Mama tayi tana kallonshi. To me yake nufi da wanna kalmar? Komawa falo tayi ta buga uban tagumi. To wai meyake samun Malan? Tunda yadawo daga Katsina gaba daya ya canza, sam yanzu baya mata fara'a.

Kuma baya son zama agida, gashi yanzu abu kadan se masifa. Gyara zama tayi tace to kode Inne tashiga tsakanina dashi ne? Mikewa tsaye tayi tana fadin wallahi bazan barta ba wannan karon, idan har Malan yaci gaba da yimani haka sena yimata babban tabon da bazata manta shi ba, kuma. Ba akan kowa zan dau fansa ba se akan Fatima.

**** *****

A cikin kwana biyu Malan da Suwaiba suka kulle, sosai suke zuba soyayya, gaba daya Suwaiba ta fara canza Malan, yanzu sam baya damuwa dan Mama batazo dakinshi kwana ba, haka suke kusan kwana suna waya.

Idan kuma yaga ranar tana jin kirki to baya dawowa gida da wuri seya gama wayarshi da Suwaiba sannan, gashi duk bayan kwana biyu seyaje Katsina, sam Mama takasa gane kanshi.

Gefe guda kuma ya fara gininshi na shago. Haka yaje ya samu Hajiyarshi da maganar aure, Hajiya ta rufe ido tana ta masifa tana fadin me ka nema karasa a wajen Hauwa? Mace me kirki, ai kaga yanda ka kare da kayi wancan auren, kuma yanzu zaka zo mani da maganar aure.

Malan yace Hajiya bakisan ko wacece Hauwa ba, nima se kwanan nan nasan asalin halinta................. Labarin duk abinda yaji tana fadama Amba ya bama Hajiya, sosai hankalin Hajiya yatashi.

Babu bata lokaci tace ta amince, kuma kada yafada mata zeyi aure yabari ta gani daga sama, domin ta cuceshi, kuma zata samu Kawunshi suje domin suyi magana da Yayan yarinyar. Sosai ran Hajiya ya baci, haka tayi ta masifa, haka Malan ya yi ta bata hakuri yayi mata godiya ya tafi.

Haka Kawun shi da wani abokinshi suka je Katsina wajen Yayan Suwaiba bayan sun gaisa suka ba da kudin neman aure, sosai sukaji dadin yanda Yayanta ya amshe su, kuma yace idan sukayi shawara suka tsaida rana zasu aiko masu, godiya sukayi masu sukace zasu aiko da kayan sa ranar.

Sosai Malan yaji dadin labarin da suka fada mashi, haka ya cigaba da shirye shiryen aurenshi ba tare da Mama ta sani ba.

A ranar visiting kuwa da Mama tayi mashi magana cewa yayi ta shirya masu kayan zeje masu shi kadai, sosai tayi mamaki, data taso mashi da masifa yace idan ita takeda iko da kanta se taje.

Haka yakawo mata kayan miya da nama yace tayi masu miya, kuma ta sama kowa tashi a cooler da abinci da ban. Haka yayo masu provision kowa da kwalinshi, dakinshi ya wuce dasu ko gani batayi ba.

Lokacin data gama hada masu komai ya dauka yasa mota, dakinshi yake ya dauko kayansu ya saka mota se kallonshi takeyi, haka yashiga mota yana fadin bakida sakon da za'a kaima Farida? Saboda mamaki kasa magana tayi haka ya tafi.

Kasa tsayuwa tayi, haka ta jingina tana tunanin kode Malan yasan wani abu daga cikin abun da take yima Fatima ne? Jin jina kai tayi tace tabbas Fatima itace ta fada ma Malan, wannan dalilin ne yasa ya canza mata lokaci guda.

Idan ko hakane wallahi zata dauki mataki, komawa tayi ta dauko hijabinta ta wuce gidan Maman Sultan.

Lokacin da Fatima taji ana ne manta tasha mamaki da akace babanta ne yazo masu visinting, Farida ta rigata zuwa itama tayi mamakin ganinshi, har take tambayarshi Mama, yace tana gida baki tayi shiyasa.

Haka suka gaisa yabama kowa kayanshi ya basu kudi, haka sukayi mashi sallama, har sun tafi ya kira Fatima, juyowa Farida tayi tana kallonsu duk bakin ciki yagama kamata, meyasa ita ba'a kirata ba? Tsayawa tayi tana kallonsu.

Malan yace Fatima nasan kinajin haushi na ko? Girgiza kai tayi tana dukar da kai kasa, Malan yace kiyi hakuri nasan Hauwa tana rage maki kayan abinci, shiyasa ma yau nazo da kaina, kuma daga yau bazata kara zuwa maku visiting ba.

Fatima tace to, murmushi yayi yace zan tafi kidage da karatu, juyawa Fatima tayi aranta tana fadin kaji malan, da can besan ana mata haka ba seyanzu da yaga takusa gamawa sannan zece haka, kuma gashi Innenta tana gidan me kudi shi kuma ya aje aiki shiyasa yanzu zece yana son mu.

Gaba daya ma ranta baci yayi haka ta wuce wajen Lubna, tana zuwa ta bata labarin abinda yafaru. Lubna tace kiyi hakuri Fatima, tunda ya fadi haka kila da gaske yakeyi be sani ba. Tashi Fatima tayi tana fadin Lubna bakisan ko waye Malan ba. Wallahi zan iya cika littafi da labarin gidanmu. Dariya Lubna tayi tace ai seki fara.

***** ****

Haka Malan ya dage da gyaran bangaren Inne, kuma ya tada wani gini me dakuna biyu daga bayan dakunan gidan, kasancewar daga can baya dama yabar fili saboda yanaso ya gina ma yaranshi maza dakuna hakan yasa yanzu yake gina dakuna biyu.

Ita de Mama kallonshi kawai takeyi, dan lokacin da tayi mashi magana cewa yayi ina ruwanta, ba gidanshi bane, tace to ai naga bangare daya kake gyarawa, yace kisa ido kiyi kallo idan zaki iya.

Bayan angama gyaran dayen part din yace itama ta kwashe kayanta da maida dakinshi za'ayi gyara, haka ta kira Maman Sultan ta ta yata suka kwashe. Maman Sultan tace anya Malan ba aure zeyi ba? Mama tace haba de aure.

Ai wallahi babu matar data isa takara shigowa gidan nan, kuma Malan sam beda son mata, ko bayan rabuwarshi da Inne cewa yayi dama rabo ne kawai yasa ya aureta amma shi beda ra'ayin mata biyu.

Kawai de yanaso yayi gyara ne saboda kinga su Farida sun zama 'yan mata kila bangaren su Fahad ze maidasu su kuma ga dakunansu can ana masu abaya. Maman Sultan tayi murmushi tace Allah ya temaka.

Bayan angama mata gyara ta maida kayanta shima aka gyara mashi nashi part din, cikin lokaci kan kani aka gama ginin dakinsu Fahad, kowane daki da banda kinshi, daya Fahad da Faisal, dayan kuma na Farouk ne. Haka ya maida masu gadonsu da kayansu ya kulle part din Inne.

Daga Katsina kuma suka aiko masu da sa rana nan da wata 2, amma idan sunaso akara to, babu bata lokaci sukace yayi. Kudi Malan ya bama Suwaiba yace ta hada lefenta da kanta dan bayaso ya bama wasu su siya mata kayan da bataso.

**** ****

Lokacin da biki yarage saura sati 3, a na saura kwana biyu hutu. A ranar laraba aka kama su Fahad shida abokanshi sun dira gidan wani malami da sukayi tafiya shida iyalanshi, lokacin da dare ne, Vice Principal shida wani malami sun dawo da school area bayan kowa ya tafi daki wajen karfe 10 na dare.

Vice Principal ne yafara ganin yaro na karshe daya dira katangar gidan, nuna ma malamin dasuke tare yayi, cikin sauri yace yaje yakira masu gadi guda biyu, haka ya nufi kofar gidan.

Masu gadin suna zuwa Vice Principal yace kawai su shiga, haka suka dira, da Fahad suka fara cin karo ya dauko wata bakar jaka hannunshi daya kuma ya kunna wiwi yana zuka.

Sauran ma kowa da abinda ya dauko sunata shan wiwinsu wasu kuma suna shan sigari, Fahad yana fadin kuyi sauri mufita, lokacin da suka fito su kuma masu gadin sun boye, suna zuwa zasu haura katangar Vice ya dallesu da fitila.

A kidime suka zubar da kayan suka fara neman hanyar guduwa, masu gadin ne sukayi saurin cafkesu. Gaba dayansu hankalinsu yatashi, saurin yadda abinda suke sha sukayi.

Vice yace kowa yadauki abunshi, haka suka dauka jikinsu yana rawa, sawa yayi dayan malamin ya haska mashi su, haka ya matso da kayan da suka yarda akusa dasu ya daukesu hoto.

Kuka sukasa suna rokonshi yayi hakuri, yace bade kune 'yan iskan makaranta ba, daga kanku wasu bazasu kara marmarin aikata irin wannan laifin ba, kushigo har cikin gidan malami ku rika sha mashi wiwi da sigari saboda ku 'yan iska ne.

Megadi, kutafi dasu su kwana a wajenku, domin gobe za'a yanke masu hukunci. Haka suka tafi dasu se kuka sukeyi, ba kamar Fahad, dan yasan ya shiga 3 awajen Malan.

Washe gari ranar alhamis bayan malamai sun gama meeting aka kada assembly, gaba daya makarantar kowa ya taru, kowa da abinda yake tunani, wasu ma suna fadin ko hutu za'a bada. Principal ne da Vice suka hau saman step din, sauran malaman kuma suna gefe.

Haka masu gadi suka fito dasu Fahad gaba dayansu sunyi zuru zuru, agaban mutane aka ajesu daga sama, kowa se dukar da kai ya keyi. Gaba daya 'yan makarantar kowa da abinda yake fadi, domin da yawa mutane sun san halinsu.

Hannu Vice ya daga hakan yasa kowa yayi shiru, bayan sun gaishesu yasa akayi addu'a, bayani yafara kamar haka:

Ina fatan kowa yaga wadan nan yara da suke agabanku, kuma kowa yasan suna daya daga cikin daliban makarantar nan, wasu daga cikinsu suna SS 2, wasu kuma SS 3, ajiya da dare nida Malan Shu'aibu muka kamasu sun haura gidan Malan Bala, kasancewar basa nan sunyi tafiya.

Bayan nakira masu gadi muka shiga gidan, ace bayan sata hada shaye shaye sukeyi, kuma ba sigari kadai ba, wiwi muka kamasu suna sha acikin gidanshi saboda rashin tarbiya.

Wayarshi ya daga sama yana fadin hotunansu suna nan ciki kuma zamu nuna ma Uban kowane yaro, bayan nan kuma daga yau su ba daliban wannan makarantar bane, mun yanke wannan hukunci ne saboda hakan yazamo jan kunne ga sauran Dalibai.

Kuma daga yanzu duk wanda aka kama yana mana shaye shaye acikin makaranta, ko a waje, tabbas shima ze fuskanci irin wannan hukunci. Me kuka sani arayuwa da zaku jefa kanku cikin irin wannan rayuwar? Me zaku iya zama nan gaba idan har baku dena wannan banzan halin ba.

Iyayenku sun kashe kudi abanza sun kawoku makaranta amma da abinda zaku saka masu kenan, to wallahi ko suwaye iyayenku daga yau kun bar makarantar nan, sede kowa ya koma gida iyayenshi su sake mashi wata makarantar.

Kuma kowannansu ze karbi bulala 20, kuma daga nan kayanku kawai zakuje kudauko Principal ya bada School bus domin akai kowa gida, badan komai ba saboda mu damka ku a hannun iyayenku kamar yanda suka kawoku suka damka mana ku.

Kuma mu nuna masu irin ta'asar da kukayi. Alhamdulilahi anyi sa'a acikin ku biyar mutum 3 a Katsina suke, suran biyun kuma daya dan Mani ne, dayan kuma dan Kaita ne, dan haka bayan kun amshi bulalarku masu gadi zasu raka ku kudauko kayanku kuzo mutafi.

Ina fatan wannan ze zama darasi agareku. Masinja aka kira wanda dama shine yake ma duk wani me laifi bulala, wata katuwar dorinace a hannunshi, haka Vice yasa masugadi suka rika turosu daya bayan daya ana zanesu.

Ihu kawai sukeyi, wasu daga cikin 'yan makaranta sunji tausayinsu ganin yanda suke kuka, jikinsu duk ya fashe, haka aka gama zanesu sannan aka sallami yara masugadi suka tasa su zuwa daki domin su dauko kayansu.

Da kyar suke tafiya haka kowa ya dauko kayanshi suka saka a mota, Vice da wasu malamai guda biyu ne suka shiga motar suka tafi dasu. Acikin mota se kuka sukeyi, anan ma Vice fada yayita masu.

Haka suka fara kai 'Yan Katsina su 3, kowa seda suka ga mahaifinshi, kuma suka nuna mashi hotonsu sannan suka damka mashi takardar kora, duk mahaifin da aka mikama danshi da takarda se yayi kuka.

Bayan sun gama da Katsina suka wuce Kaita, daga karshe suka dauki hanyar Mani, Fahad in banda kuka babu abinda yakeyi, Vice kuwa se fada yake kara mashi, domin yasan Malan, haka suka shiga cikin garin Mani nan suka tambayi Fahad ya nuna masu hanyar unguwar, yana kuka yana nuna masu.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[4/10, 12:19 PM] nabilalady5: ,🏡🏡 A WANI GIDA🏡🏡
😭😭😭

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.