Busa A Mutu Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Busa A Mutu Part 2 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 2 of 6
Zan dakata anan saikuma wani lokaci
ßµŠÅ Ä MµTµ
Littafi Na Biyu (2)
Part B
Na Abdulaziz Sani M /Gini
KAICO! Ashe tsuliyar dodo Muraisu ya tabo,
domin suna ganin ya kashe daya daga cikinsu sai
suka yì kukan kura suka afka masa gaba dayansu
aka sake kacamewa da azababben yaki.
Wannan karon dayansu bai samį damar koda
taba jikinsa ba, domin wata iriyar zulliya ya rinka
yi a tsakankaninsu
ya inka kama
hannaycnsu da kafafunsu yana kakkaryawa tamkar
yana karya sillen kara.
Gumbiya Husnaila da ke can cikin korama
tana ta wanka, sai ta fara jiyo ihun Dakarun
tsaronta. Al'amarin da ya matukar ba ta mamaki ke
Cikin hanzari ta karbi mayafi daga hannun
kuyanginta ta daura iya kirjinta, sannan ta fito daga
cikin koramar. Ko tufafinta ba ta tsaya sawa ba ta
durfai inda ake wannan gumurzu.
Su kuwa wadannan kuyangi na ta sai suka
ruga izuwa cikin daji a dimauce ba tare da sanin
inda suka dosa ba, saboda tsananin razanar da suka
yì domin sun san cewar bala'in da ya sa wadannan
samudawan dakarun ihu ba Karami bane.
Tun daga nesa gaimbiya Husnaila ta hango
dakarunta suna zubewa kasa tamkar ana sassabe a
gona.
Koda ta kara matsawa kusa sai ta ga ashe
wanda yake ragargazar su ma dan mitsitsı ne
akansu, bai fi ta kwatantashi da dan tsako ba a
cikin tsakiyar dubunnan Muzurai.
A iya rayuwar gimbiya Husnaila yau ne ranar
farko da ta ga abinda yai matukar ba ta mamaki,
amma ba wai burgcta ya yi ba.
Koda ta ga yadda Muraisu ke ta kakkarya
dakarunta suna zubewa kasa sai ta sunkuya ta
dauki mashin daya daga cikinsu ta ike ta tsaya
cak! Tana jiran ta ga abinda zai faru.
Kafin cikar rabin sa'a Muraisu ya zubar da
dukkan dakarun a kas suna ta koke-koke da iface-
iface, babu đayansu da ya iya mikewa tsaye.
Koda Muraisu ya ga ya gama da dakarun sai
ya yi arba da kyakkyawa Husnaila a tsaye a
gabansa ike da mashi, fuskarta a murtuke babu
annuri, kuma ga ta a tsayc kyam babu wata alamar
tsoro a tare da ita,
Koda ya ga kyakkyawar surar jikinta da kuma
wani kyakkyaw an gashin kanta sar ya rude ya
dimauce, bai san sa'adda ya nufeta ba gadan-gadan
da nufin ya rungumeta.
Koda ya ragc bai fi saura taku daya su hadu
ba sai ya kai ma ta raruma, ita kuwa ta goce ta soka
masa mashi a gefen kirjinsa.
Bisa mamaki sai ya ji mashin ya nutse a cikin
kirjin nasa, bai san sa'adda ya kwalla ihu ba.
Husnaila ta zare mashi jini yai feshi daga cikin
kirjin Muraisu, ya sake rusa ihu a karo na biyu. Jiri
ya debeshi ya yi luu!! kamar zai fadi kasa, amma
sai yaı ta maza ya tsaya bisa kafafunsa.
Husnaila ta sake saitashi da mashin ta tsaya
cak! A waje daya suka fara kallon-kallo. Daga can
sai ta dubeshi ta kyalkyale da dariya a cikin sautin
murya mai zakin gaske, sannan ta hade rai ta ce,
"Kai wayc, kuma me ka ke nufi da ni? Saboda mne
ka zo ka ragargaza mini dakaruna? Ka san kO ni
wace ce kuwa? Ka amsa mini tambayoyina da
gaskiya ko kuma na hallaka ka yanzzun nan!"
Koda jin wannan batu sai Muraisu ya bushe
da dariya sannan ya ce, "Ni ne yarima Muraisu dan
Sarki Salmar mai binin Laius, wato babban
makiyi ga dan uwanki Sarki Ishmar.
Ina mai sanar da ke cewa na baro gida ne
domin neman matar da zan'aura, kuna ba wata ba
ce wadda zan aura face ke din nan".
Koda jin haka sai Husnaila ta tuntsure da
dariya, 1lokaci guda kuma ta hade rai ta sunkui da kanta kas tana tunani. Muraisu ya katse ma ta
hanzari ya ce, "Ya ke Husnaila Sarauniyar mata,
me kike tunani ne?"
Husnaila ta dubeshi ta ce, "Mamaki nake bisa
daıyar da na yi yanzu, domin kaine mutum na
farko da ya ta6a ganin dariyata..
Hatta dan uwana kuwa Sarki Ishmar sai dai ya
Ce ya ga murmushina ko hawaye na, amma bai taba
ganin dariyatÄ… ba ko kukana'".
Da jin haka sai Muraisu ya yi mumushi ya ce,
"Al ni mutum ne na musamman a cikin mutane, da
sannu za ki gasgata haka".
Husnaila ta ce, "Ai kuwa na ga alama tunda
ban taba sukar wani abu da makami ba ya rayu sai
kai. Shin za ka iya gaya mini sirrin da ke tattare da
kai?"
Muraisu ya cire wani rawani da ke ikin
damararsa ya daure kirjinsa lamau don tsaida jini,
sannan ya dubi Husnaila a nutse ya ce, '"Ina zaton
dai irin sihirin da ke tare da ke shi ne a tare dani,
domin gashi dakarunki sun kasa cutar da ni da
makamansu, amma ke gashi kin cutar da ni".
Husnaila tayi murmushin mugunta, sannan ta
ce, "Ka yi babban kuskure da kake tunanin za ka
aureňi, domin abu ne wanda ba zai taba yiwuwa ba
Babu wani da namiji da ya isa ya mallakeni, idan
kuma kana ganin za ka iya ka jarraba!"
Muraisu ya gyara tsayuwarsa sannan ya ce,
"Ai babu wani abu wanda ba zai yiyu ba a wannan
duniya, sai dai ba a jarraba b.
Ina da labari cewa dan uwanki ya tsarcki da
dukkan sihirin tsafinsa, amma ni nayi imanı cewa
sirin da nake da shi a yanzu ke baki da shi tunda
shi kansa dan uwanki har yanzu bai samu ikon
shiga dajin Kirzufa ba.
Ba shi da wani buri wanda ya fi haka. Ina
tabbatar miki da cewa har ya mutu ba zai cika
wannan buri na sa ba, ni kuwa mahaifina ya shiga
dajin Kirzufa, Äima kuma zan shigeshi yanzu,
kuma tarc da ke, kuma dana ma sai ya shigeshi. Ina
mai shawartarki da ki bani hadn kai mu tafi cikin
salin-alin, idan kuwa kika ki, to fa ko ta tsiya-tsiya
sai mun je".
Sa'adda Husnaila taji wannan batu sai ta sake
bushewa da dariya a karO na biyu, sannan ta hade
fuska ta ce, "Ai sai na ga yadda za a raba hanta da
jini!"
Kafin Muraisu ya budi baki ya ce wani abu
luni Husnaila ta dako tsalle a sama daga inda.take
kamar an cillota daga cikin baka ta sake kawo masa
mummnunan hari da wannan mashi a ciki.
Gimbiya Ilusnaila ta ce, "Ta ya ya aka yi ka
san cewa ni ce Sarauniyar kyawawa ta duniya?"
Muraisu ya ce, "'Saboda mu a wannan nahiya
lamu gaba daya babu kamarki".
Gimbiya Ilusnaila ta cC, "Ba zan iya gaya
maka ba, saboda ba kowacce tambaya ce ke da
amsa ba"
Muraisu ya ce, "Maganarki dutse ce, amma
akwai gyara".
Gimbiya Husnaila ta cc, "To mene
gyaran?"
"Bari na matso kusa na yi miki bayani, domin
wani babban siri ne wanda ba kowa ake fadawa
ba'".
Kai tsaye Muraisu ya tali inda Gimbiya
Ilusnaila take tsaye kamar wani abu zai rada ma ta
a kunnc.
Koda ya iso daf da ita sai ya shammaceta
cikin bakin zafin nama ya debo hodar banju daga
aljihunsa ya watsa ma ta a fuska.
Nan take Gimbiya Husnaila taji jiri ya
kwasheta, la tafi luu! za ta fadi kasa, sai ya
sunkuya uya sabata a kaladarsa ya juya da baya ya
nufi inda ya baro su boka Rufyan suka tsaya suna
Jiransa.
Barde Kurzal, kuyan ga Sabirat, boka Rufyan
na tsayc suna hangen hanyar da Muraisu ya bi cikin
zullumi da fargaba. sai kawai suka hangoshi ya
nufosu sabe da Gimbiva Jusnaila a kafadarsa, ga
raunı a kirjinsa daure cikin shátar jini, yana tafe
yana raba kafa kamar wanda ya sha giya ya bugu.
Koda ganin haka sai Barde Kurzal da boka
Kutyan suka ruga gareshi cikin matu kar farin ciki
suka taroshi.
AA Misau
Barde Kurzal ya karbi Gimbiya Husnaila ya
taho da ita inda Sabirat ke tsaye, shi kuma boka
Rufyan ya dauko Muraisu suka kawosu bakin wata
bishiya suka shimfidesu.
Cikin hanzari boka Rufyan ya kwance raunin
Muraisu yana matukar mamakin yadda aka yi ya
sami raunin alhalin ya san cewa Sarki Salmar ya
bashi gashin sihirinsa.
Nan da nan yai sauri ya sa ma sa gan magani
akan ciwon nasa, sannan suka bashi ruwa ya sha.
Ita kuwa Gimbiya Ilusnaila, tunda aka
shim fideta ta ci gaba da barcinta ko motsawa ba ta
Bayan Muraisu ya dawo cikin haiyacinsa sai
boka Rufyan ya dubeshi cikin jınjinawa ya ce, "Ya
kai namijin duniya, dodon maza, ya ya aka yi ka
Saml Wannan gagarumar nasara har ka daukO
gimbiya Husnaila daga cikin tsaron da aka ba ta?".
Koda jin
wannan tambayar sai yarima
Muraisu ya kwashc labarin duk abinda ya faru ya
Zalyane musu. Koda jin al'amarin sai duk su ukun
suka sake cika da mamaki, musanman boka
Rufyan wanda ytai shiru ya shiga tunani mai zurli.
Daga can sai ya dago kai ya dubi yarima
Muraisu yÄ… ce, "Ya shugabana hakika shirin sarki
Ishmar ba na wasa bane, ban taba tsammanin yana
da karfin sihiri kamar haka ba. Ina tabbatar maka
da cewa duk wannan jarumtaka da Husnaila ta yi
ba gaskiya ba ce, tsabar karfin sihirin tsafi ne
kawai.
Tabbas itama tana da gashin sihiri a jikinta,
amma abinda na ke zargi shi ne, ba irin naka bane a
Jikinta, shi ya sa mahaifinta ya kasa shiga cikin
da in Kirzufa. Hakika ba don kayi wannan hikima
ba ta watsa ma ta banju a fuskarta da babu yadda za
a yi ka iya kamota har ka zo da ita nan wajenmu.
Ina son ka sani cewar dole ne yanzu ka
hanzarta zuwa dajin Kirzufa da Husnaila kafin
hodar banjun ta saketa nan da tsawon sa'a daya jal.
Idan har ta farfado ko duniyar nan za ta taru a kanta
ba za a iya taiya da ita ba, kuma idan ma ka shiga
da ita cikin dajin Kirzufa sai ka sa ido sosai a kanta
don za ta yi iya shammatarka tayi maka irin abinda
ka yi ma ta".
Koda jin wannan batu sai Muraisu ya mike
zumbur! ya dauki gimbiya Husnaila ya đorata akan
doknsa, sannan shima ya hau nasa dokin, suma Su
Rufyan sai suka yi sauri suka hau nasu.
Barde Kurzal ne ya wuce kan gaba suka
zaburi dawakansu da gudu suka bishi a baya. Basu
tsaya a ko ina ba sai sai a bakin dajin Kirzufa.
Lokaci guda su duka suka yi tirjiya, sannan
suka sauko daga kan dawakansu. Yarima Muraisu
ya sake đaukar gimbiya Husnaila a kafadarsa. Har
ya juya zai shigc cikin dajin na Kirzufa, sai ya
Waiga ya dubesu su ukun cikin wani iin kallo mai
nuna alamun bankwana, wanda ya sa duk su ukun
suka ji tsigar jikinsu ta tashi, kuma dukkaninsu sai
zuciyoyinsu suka karaya, nan take tausayin yarima
ya tumukesu, saboda sanin cewa masifar da zai
shiga yanzu ta ninka wacce ya shiga a baya sau
dubu.
Muraisu ya tsaida hankalinsa a kan boka
Rufyan ya ce, "Bani labarin mahaifina, shin hạr
yanzu yana raye ko kuwa ya mutu?"
Koda jin wannan tambaya sai boka Rufyan-
yai shiru ýa kasa cewa komai, kawai ya kurawa
Muraisu idanu.
Barde Kurzal da kuyanga Sabirat kuwa, sai
hankalinsu ya dugunzumna, suka kama raba idanu a
tsakanin Muraisu da Rufyan, jira suke kawai su ji
amsar da Rufyan zai bayar.
Tsawon 'yan dakiku Rufyan bai ce komai ba,
kuma bai fasa kurawa Muraisu idanu ba.
Koda ganin haka sai idanun Muraisu suka
domin
ciko da kwalla har hawaye ya subuto masa,
ya ji a jikinsa cewa MAZA SUN FADI!
Kawai sai ya juya ya durfafi cikin dajin
Kirzufa kai tsaye, a lokacin da ya ji dukkan tsoro
ya kau daga cikin zuciyarsa, ji yake ina ma
mutuwar za ta zo ta daukeshi da ya fis amun
nutsuwa.
Da shigar su Muraisu dajin Kirzufa sai ya fara
arba da dabbobin daji ii-ii, kuma manya-manyan
ababan tsoro, domin sun kasance na usamman ba
irin wanda ido ya saba gani ba. Tsananin kwarjinin
dabbobin ya wuce misali, ko kwatance.
Tsakanin Muraisu da dabbobin sai kallon-
kallo kawai, dayansu bai yi yunkurin koda zuwa
kusa da shi ba, shima Muraisu ko kallonsu bai yi
ba, kawai sau ya je karkashin wata bishiya ya
shimfide Husnaila, sannan ya koma gefe daya ya
tsugunna ya kura ma ta idanu, kuma ya fada kogin
tunani.
Abinda ya fara fado masa a rai shi ne, yanzu
ya zai yi da Husnaila idan ta farka ta tsinci kanta a
cikin dajin Kirzufa?
"Lallai akwai kazamar rigima a (sakaninmu"
Muraisu ya baiwa kansa amsa.
"Kuma saà tayi yunkurin guduwa...Amma
kuma ai boka Rufyan ya gaya mini cewar ba tưisa
ta fice daga cikin dajin ba har sai mun yi kWana
uku a cikinsa, saboda haka zan zuba ma ta idanu ne
kawai na ga iyakar gudun ruwanta. "
Haka dai Muraisu ya yi ta sake-sake a cikin
zuciyarsa har ya gaji, shima saà ya kishingida a
jikin wata bishiya.
Abinka da gajiyayye, bai dađe da kishingida
ba sai barci ya kwashe shi.
Bayan 'yan dakiku kadan kuma sai Husnaila
ta farka.
Koda la bude idanu ta tsinci kanta a cikin
wani iin daji na musamman sai ta takarkare ta
tsandara uban ihu. Muraisu ya farka firgigit! a
razane, dabbobin cikin dajin kuwa, hatta sauran
Rananan kwari da tsintsaye sai da suka razana, suka
kama guje-guje.
Duk dabbar da tayi arba da su Muraisu sai ta
yıyo kansu:
Nan fa aka kasa uban tserc tsakanin su
Husnaila da dabbobin dajin gaba daya.
Babu abinda zai baiwa mutumn mamaki face
Lsananin gudun da Muraisu da Husnaila ke yi
tamkar akan iska suke yinsa ba a kan kasa ba.
Duk su biyun sun yi matukar mamakin irin
gudun nasu, domin tamkar walkiya suke gifta
komai, sai dai karfin gudun nasu duk ya zama na
banza, domin duk sa'adda suka waiga bayansu sai
su ga dabbobi kusan guda dubu daf da su.
Duk inda suka dauke
dabbobin suke sa nasu.
sawayensu
anan
da
Babu abinda ya fi firgita su Muraisu face
cafka
kawo musu
yadda dabbobin ke
bakunansu, don su cinyesu, musamman wani katon
Zaki wanda idan ya wangame bakinsa sai ka ga
kamar ijiya mai zurfi da fadi aka bude.
Sai da su Muraisu suka shafe sa'a guda cif!
Suna falfala natsanaicin azababben gudu, sannan
suka hango wani katon tsauni a gabansu.
Basu tsaya jiran komai ba suka hau kan
tsaunin a guje, har sai da suka je can. samansa
sanann suka waigo baya.
Bisa mamaki, sai suka ga gaba dayan
dabbobin sun tsaya a kasan tsaunin đayansu bai yì
yunkurin hawowa ba.